Cikin zafin nama ta janyo wani kwalbar humra ta k'wala masa a ka,bata tsaya ganin yanayinsa ba kawai ta dai ji yayi k'ara mai k'arfi,ita kuma ta haye gadon a gigice ta d'auki key ta bud'e k'ofar ta fice a guje....
A farfajiyar gidan taci karo da Rabi'atu batama lura da ita bace kawai ita k'ok'arin fita take daga gidan..
Itama Rabi'at cike da mamaki ta rik'eta gam tana jijjigata "Sumayya lfya?kanki d'aya kuwa"
"Ki kyaleni in tafi" Sumayya tayi maganar cikin matsanancin kuka,
"Idan kin tafi ina zakije?ina kika sani a garin kaduna?"
Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta..
Kuka ta k'ara fashe wa dashi kuka na nadama yau kam taga k'arshen rashin kunyarta da ace ba tayi da yanxu tana cikin 'yan uwanta duk da gallazawar da baba yake masu zaman gidansu ya fiye mata dad'i..
Da k'yar Rabi'at ta rarrasheta tayi shiru,tana jin dawowar 'yan gidan amma ta kasa fita,jikinta sai rawa yake kallon ko ina take tana tunanin ta inda *Aryaan* zai fito kuma da wane makami zai fito..
"Sumayya" Rabi'at ta kira sunanta a hankali,bata ko kalleta illa hawaye da yake ta zuba a idonta...
"Meyasa kike b'oyemin damuwarki bayan a da ba haka kike ba?"
Kallonta tayi ta share hawayen idonta sannan tace "ada kika ce amma a yanxu na gane cewa akwai sirrin da dole sai ka barshi a zucuyarka kiyi hkri bazan iya fad'a miki ba"
"Shikenan yanxu ina *Aryaan*?kirawo min inji ko shine ya b'ata miki rai"
Gabanta yayi mummunar fad'uwa da k'yar ta samu tace "tare suka tafi airport"
"Okay ai naji dawowarsu bara naje"
Ta tashi ta fita,Sumayya kam ji take kamar tacewa Rabi'at Dan Allah ta dawo..
Tana ganin ta fita ita kuma tayi bedroom d'inta,ga mamakinta tana tura k'ofar taga ta bud'e kuma babu *Aryaan* a ciki sai dai bedsheet da taga an cukwikwiye an ajje a tsakiyar gadon sai wayarta da tayi pieces a k'asa,a hankali ta k'arasa ta d'auki wayarta ta had'a ta kunna sannan ta nufi kan gadon ta bud'e bedsheet d'in mai zata gani?
Jini ne kaca2 a jikinsa, bata san lokacin data k'walla k'ara ba sai kuma tayi shiru taja da baya..
Hannunta na rawa tayi dialing number *Arish* yanxu kam zata fad'a masa matsayinta a gurinsa Dan tana tsoron cigaba da zama da *Aryaan*..
Har kira biyu bai d'aga ba sai a na uku ya d'aga...
Bata ma jira taji mai zaice ba ta fara magana cikin kuka " *Arish* nice Sumayya matarka dan Allah kaji k'aina ka dawo ko takardar saki ce ka rubuta min kafin rayuwata ta wulak'anta ina cikin matsala *Arish* ka taimaka ka dawo gar...........ji tayi an fizge wayar tana juyawa taji an wanke ta da mari har sau biyu..
Tana d'ago kai taga *Aryaan* ne,
"Ashe Ke baki da hankali baki da mutunci?Ashe Ke dabba ce ban sani ba"
Hawayene ya cigaba da kwarara a idonta ta kuma tsaya cak tak'i matsawa daga gurin....
Wayarta ce ta fara ringing a tsorace ta kalli wayar tata dake hannun *Aryaan*
Murmushi yayi sannan ya d'aga ya kara a kunne..
"Sai dai kayi hkri *Arish* dama kana sonta ka bari aka d'aura aurenta da sunana?aka kawota gidana?ka tafi kusan wata shidda baka sake waiwayarta ba,am srry to say *Aryaan* ya dad'e da Sanin Sumayya a 'ya mace"
"Karya yakeyi wallahi" kafin ta fad'ama tuni *Aryaan* ya kashe wayar yayi wurgi da ita..
Caraf taji ya rik'ota ya fara kissing d'inta tako ina,kuka sosai take tana Neman k'watar kanta amma ta kasa,
Har sai da ya kaita k'asa yana neman cire mata kayan jikinta dan lokacin tuni ya fita a hayyacinsa,cikin ikon Allah da addua ta samu damar kai masa cizo mai k'arfi a kunne,ai tuni ya saketa ta tashi da gudu ta fice....
Bata tsaya ko ina ba sai tsakiyar main falon part d'insu momma wanda duk kan 'yan gidan an baje ana hirar yaushe gamo na dawowar triple,Zahra ce ta fara rik'ota a gigice tace "lfyarki k'alau Aunty?"
Ta d'ago kai ta kalli zahra sai kawai ta zube anan ta sume.
A kid'ime *Asrar* ya matso zai rik'eta,Zahra ta tareshi da hannunta "karka tab'a ta matar aure ce"
"Matar waye?"
*Ashaz* ya tambaya "uhmmm matar yaya *Aryaan* ce" Asiya ta fad'a tana tab'e baki,da gudu *Asrar* yaje fridge ya d'ebo ruwan sanyi ya kawowa Zahra...
Momma na tsaye Kansu ta karb'i ruwan ta yayyafa mata,a tsorace ta bud'e ido ta kallesu,
Hawaye tuni ya wanke mata ido,kuka sosai takeyi duk falon an rasa Wanda zaiyi magana kowa ya zura mata ido kawai..
Gaban momma ya cigaba da fad'uwa,a hankali tacewa Zahra "kirawo min *Aryaan*" ai Sumayya na jin an ambaci sunanshi tayi saurin tashi ta rungume momma tana fad'in "ki rufamin asiri momma kada ki kirashi ki taimakeni zai lalata min rayuwa dan Allah karki kirashi"
"Koda bata sa an kirani ba zanxo,lalata rayuwa kuwa shaid'an ya rigada ya ci galaba a kanmu domin na tabbatar a yanxu haka baza'a rasa kwai na a cikiñta"
"karya yake wlh momma sharri zai min"
Cikin jin zafin maganganun *Aryaan* momma ta tashi ta hau dukansa tun k'arfinta, "ka cuceni kaci amanar d'an uwanka" tana dukansa tana kuka,da k'ar triple suka janye momma..
Falon yayi tsit sai sautin kukan momma dan sumayya ma kukan zuci kawai take sai yanxu ta gane sharrin da *Aryaan* ke son yi mata..
"Kukanki a yanxu baya da wani amfani kawai ki fito fili ki fad'a mana abinda ke faruwa Dan kun sakamu a duhu"
Cikin kuka da nadama momma ta fara bashi labarin yadda akayi auren sumayya da *Arish* aka juya shi kan *Aryaan* Dan kar daddy ya gane,sannan ta k'ara da fad'in "nayi nadama danasan haka *Aryaan* ya zama da ban had'a ba Dana fad'a maka gskya"
Duka falon ya d'auki salati,yayinda daddy ya fara fad'a na rashin sanar dashi gskya Al'amar...
"Dole a k'i sanar da kai gskya domin ko an sanar da kai a lokacin k'ilan ka d'auki mataki mai tsanani fiya da yanda ka d'auka a lokaci da akayi k'aryar *Aryaan* ne mijinta" maganar Malam ce da basu san ya shigo ba sai lokacin..
Ya k'araso ciki ya kalli *Aryaan* yace ka fad'a mana gaskiyar al'amari,domin *Arish* ya kirani yana ta kuka yace mahaifiyarsa batayi masa adalci ba yayinda yace kai kuma d'an uwansa kaci amanarsa,matar da ya dad'e yana tattali yana fatan ta kasance matarsa amma ka ha'ince sa"
Ko gezo babu yace "Malam nima inasonta shiyasa idona ya rufe abinnan mun riga mun aikata sai dai Allah ya yafe mana *Arish* yayi hkri ya saketa a maida aurenta dani domin dama ni ta Sani a matsayin mijinta"
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" kawai daddy yake nanatawa tabbas yau yayi nadamar hana 'ya'yansa aure a lokacin daya dace...
Sumayya kam ta kasa magana jin yadda *Aryaan* keta sharara k'arya a ranta kawai ta furta _waye *Arish* d'innan?zan kasan ce tare da kai kamar yadda ka soni ba tare da nasani ba,ni takace har abada_…
Momma kam kuka kawai take, *Asrar* yana gabanta yana bata hkri..
"Arish yana kan hanyar dawowa Nigeria" Malam ya fad'a yana kallon momma babu Wanda ya sake cewa uffan..
Yau gidan haka aka yini babu mai cewa wani komai gidan ya zama tamkar gidan makoki,momma kuwa tunda ta shiga d'akinta ta saka key ta kulle bata sake bud'ewa ba Allah kad'ai ya San irin kukan da tasha a ciki.
*05:36pm*
Tana zaune jikin bangon part d'in su momma,har lokacin hawaye sai yawo yake a fuskarta,zahra na gabanta tana ta fama rarrashi duk da itama kukan takeyi,haka kawai Allah ya had'a jininta da Sumayya,Rabi'at kam tagumi kawai tayi ta kasa magana gani take kamar ita Allah zai kama da laifi...
kamar daga sama taji ance "ga Yaya *Arish* ya dawo,a kid'ime ta d'aga kai ta hango shigowarsa shi da *Ashaq*,gabanta bai idasa fad'uwa ba har sai lokaci daya k'araso gabanta...
Da k'arfi ta furta " *gentle!* Dama Kaine *Arish*?"
Wani wawan mari ya wanketa dashi Wanda har sai da ta kusa kaiwa k'asa,sannan ya shak'o wuyanta "kin cuceni,kinci amanata Sumayya"
Ya fad'a idonsa na zubar da hawaye..
Itama hawayen ne yake zuba a idonta,tension ya mata yawa k'wak'walwarta ta kasa d'aukar abinda Ke yawo a cikinta,Taja wani dogon numfashi tare da sulalewa k'asa,da sauri *Arish* ya rik'ota tare da mannata jikinsa...
"Karka manta yanxu ba muharramarka bace"
Yaji *Aryaan* yayi magana a fusace,yana juyowa yaga *Aryaan* d'in ya bud'e masa wani bedsheet kaca2 da jini.
*Yaya take ne?*🙄
_zamu so jin ra'ayinku_✍
```Contact us 4 comments
07038363997```
_Nafsal_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_*CONTINUATION*_
_Written by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```dedicated to beebahluv & Munay```
4⃣9⃣↗5⃣0⃣
A gigice ya saki Sumayya ya mik'e tsaye tare da k'urama bedsheet d'in ido...
_innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ ka cuceni kaci amanar d'an ka sab'i Allah,karkayi tunanin Allah zai k'yaleka haka..
Momma ta fad'a tana kuka,da sauri shima *Aryaan* ya juya yana kallonta yayinda hawaye ya zubo a idonsa,
"Meyasa kuka aura mata *Arish* bani ba?nina dace da Sumayya nine na zauna da ita cikin so da k'auna sannan ta ginu k'ark'ashin kulawata momma shin *MENE AIBUNA* dan nace ina sonta?,meyasa kuka sa ta zauna dani bayan bazaku halal tamin aurenta ba,
Ya tafa hannu ya juya ya kalli *Arish* yace "kayi hkra ka bar min Sumayya domin aikin gama ya gama dan na gama saninta a cikakkiyar 'ya mace"
Wani abu yaji yaxo ya caki k'irjinsa a gigice ya k'arasa gaban momma idonsa hawaye wani na bin wani,
"Momma meye wannan kenan?shin *HALACCI* ne ko *RASHIN HALACCI*?d'an uwana jinina ya yaudareni ya ci amanata?matata fa momma,yayi amfani da ita abinda na dad'e ina tattalinsa"
Ya sunkuya k'asa yana zubda hawaye sosai,kansa ya d'aga sama cikin sumbatu ya fara fad'in..
_mahaifiyata na bawa amanar matata amma taci amanata d'an uwana jini d'aya yaci amanata mahaifina baya k'aunata,meyasa kuka min haka?wa zan k'ara yarda dashi a duniya? babu_...
Ya mik'e tsaye ya k'arasa inda Sumayya take a zube har lokacin bata motsa ba,
Jijjigata ya farayi yana fad'in "ki tashi ki fad'an wanda zan k'ara yarda dashi bayan kunci amana ta,ki tashi"
Jijjigata yake tun k'arfinsa,Zahra da Rabi'atu kuka sosai sukeyi daddy da triple suka fito da sauri suka rik'esa,
"Ka sakeni" ya fad'a da k'arfi tare da fuzge hannunsa daga na daddy "na tsaneka kamar yanda ka tsaneni kun tsaneni babu mai sona a duniya zan cigaba da rayuwa ni kad'ai,zuciyata ce kad'ai ke sona"
Da gudu momma ta k'araso gabansa tana kuka tana fad'ar "ina sonka d'ana ka yarda duk duniya babu mai sonka kamar ni"
"K'arya kike ko kinason k'ara yaudarata ne" yana fad'a ya tashi ya shiga part d'in da sauri,momma ta sunkuyar da kanta tana kukan nadama...
"Daddy a kira likita kaga itama tun d'azu take a sume tak'i tashi ga yaya *Arish* naga shima kamar baya cikin hayyacinsa" *Asrar* yayi maganar cikin kuka,a hankali daddy ya d'ago kai ya kalleshi kafin ma yayi magana suka jiyo k'arar *Arish* da gudunsu suka nufi cikin gidan,
Hauka tuburan suka tarar yanayi,dan gaba d'aya ya farfasa kayan dake falo ya hargitsa komai,tafukan hannunsa sai jini suke sai maganganu yake marasa kan gado,da k'yar triple da daddy suka rik'esa aka kira dr....
*_3 HOURS LATER_*
Yana kwance a d'akinsa yana bacci kasancewar allurar da akayi masa ta bacci, *Asrar* na rik'e da hannunsa wanda aka saka drp ya rik'e dan karya goce,duk kansu kowa yayi shiru ko wanne da damuwa a fuskansa Allah kad'ai yasan abinda kowannensu ke sak'awa a zuciyarshi.
Tana bud'e idonta tayi saurin tashi zaune,ta k'arewa d'akin kallo babu shakka d'akin momma ne,
Kanta ne taji ya sara yayinda duk abubuwa daya faru suka dawo mata aka..
Hawayene ya sake samun gurbin sauka a fuskarta,tayi saurin sauka daga kan gadon ta fita daga d'akin...
Hango Asiya tayi ta fito daga d'akin Arish ,da sauri ta k'arasa Asiya tayi saurin tararta "kin tashi?sannu"
"Ina yake?" Bakinta ya furta cikin shashek'ar kuka,
"Banaso ki shiga saboda zaki iya sakamu kuka idan kika ganshi kiyi hak'uri ki koma ki huta kinji,kinga kema ba lfyar gareki ba"
Rinannun idonta ta d'ago ta kalli Asiya,bakinta na rawa tace "dan Allah ki barni inga gentle wlh hankalina bazai kwanta ba,pls ki barni in ganshi"..
Tunda sumayya taxo gidan Asiya bata tab'a jin tausayinta kamar yau ba,tausayinta take ji sosai ganin yadda rana d'aya ta fita hayyacinta...
Haka ta hak'ura ta barta suka shiga,amma da k'yar aka fita da ita,kuka sosai kamar mai tab'in hankali.
Ranar haka suka yini cikin rashin sukuni,gashi *Arish* daya tashi zai fara sunbatu da buge2 duk ya jiwaa jikinsa ciwo,Sumayya kam baya son ganinta dan daya kalleta xaiyi k'ara sosai yana fad'in a fitar masa da ita.
*_09:50pm_*
Suna zaune a babban falon gidan,Daddy ne ya fara magana "kaji tsoron Allah *Aryaan* ka tsarkake zuciyarka,ka duba halin da d'an uwanka ke ciki ka tausaya masa ka fad'a mana gskyar al'amarinnan,
Muryarsa ko rawa batayi ya furta "iya gskyata na fad'a. Maka daddy,da ace akwai akasi a maganar dana fad'a da tuni na gyara ko dan ganin halin da *Arish* ke ciki,munyi kuskure sai dai hkri kuma har yanxu ina tambaya shin *MENE AIBUNA* dan naso macen dana zauna da it.......................... " *Aibunka* shine sab'awa Allah da kayi,,kabi son xuciyarka dan kawai ka cimma wata manufarka to ka sani Allah baya bacci" cikin tsawa yaji maganar ta bayansa..
Duk kansu suka juya dan ganin wanda ke magana.
_Muma juyawa mukayi dan muga wanda ke maganar👀_
```Readers ku juya kuma ku gane mana ko waye/wace yayi maganarnan?```
*_daga Alk'alaminmu_*✍
_Sadeey S_
_&_
_Nafsal_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
&
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
sanazdeeyah.wordpress.com
5⃣1⃣↗5⃣2⃣
Sumayya suka gani gaba d'aya idonta ya rine saboda kuka,Zahra taje ta rik'ota suka cigaba da kukan tare.
Yau kwana biyu da dawowar triple,kwana biyu da faruwar wannan rikitaccen al'amari,duk wani wanda akasan ya isa da *Aryaan* tun daga kan 'yan uwan babansa da kuma abokai har ya kai kan malam,anyi juyin duniya ya fad'i gaskiya amma yace iya gaskiyar kenan,har ta kai kowa ya yarda da hakan,suna ganin kamar sumayya borin kunya kawai take.
*Arish* kam baya cikin hayyacinsa dan koda yaushe d'akinsa kaca2 yake,da an gyara zai sake b'atawa dan duk abinda ya samu watsi yake dashi,abinci kuwa sai yaga damar ci shima baya ci kamar yadda mutum mai hankali zaici,babu wanda yake k'aunar gani a gidan hatta momma,dan haka kullum asrar ko Asiya ke kai masa abinci dan ko zahra idan ta kai masa zai kamata ya daka koya watsa mata abincin a jikinta,Sumayya kuwa ba'a magana dan duk ranar da sukayi ido biyu da ita ranar ba zaman lafiya a gidan,dan haka *Asrar* ne kawai ke kula dashi ya gyara d'akin yayi masa wanka da duk abinda ya dace.
Tana zaune a gaban daddy da momma kanta a k'asa hawaye sai zubowa yake a indonta dan kullun cikin kuka take ko gajiya bata yi,
Daddy ne ya fara magana cikin sanyin murya "duk abinda ya faru ya rigada ya faru,kuskure ne dai mun aikata Allah ya yafe mana,ke kuma Allah ya miki albarka dan biyayya kikayi bakiyi dan son zuciyarki ba,kiyi hkri ki koma gidanku,kiyi istibura'i sannan in kin samu miji kiyi aure,na bata 100k a baki ko sana'a ce ki fara"
A lokacin kukanta ya k'aru babu magiyar da batayi ba akan su barta ta zauna su gane cewar duk maganganun *Aryaan* ba gaskiya bane,amma sam suka k'i aminta,momma ma bata ce komai ba sai hawaye,tausayin Sumayya da *Arish* kawai take tana tuno lokacin da *Arish* ke bata labarin sumayya yana fad'in idan ya rasata zai iya rasa rayuwarsa,ashe haka ne maganar daya fad'a tana neman faruwa,ta sake goge guntun hawayenta.
***
Ta gama shirya kayanta a trolley tana ta kuka ta zuge sannan ta tashi ta nufi side d'in momma,har lokacin momma da daddy suna zaune inda ta barsu,jikinta a sanyaye ta k'arasa gabansu tare da russunawa,bakinta na shaking tace "na gama shiryawa zan tafi,momma nagode da irin abinda kika min a rayuwa kin rik'eni tamkar 'yar da kika haifa,bazan manta alkhairin da kika min a rayuwa ba" kuka yaci k'arfinta ta kasa cewa komai,sai da ta d'auki lokaci mai tsayi tana kuka sannan tace "kuyi min alfarmar naje na duba yaya *Arish* domin ba lallai na sake ganinshi a rayuwata ba k'ila har nI mutu"
Basu hanata ganinshi ba kai tsaye suka bata izini,haka ta tashi ta nufi side d'insa,tun daga corridor takejin kukanshi k'asa2, gabanta na fad'uwa ta k'arasa d'akin.
Kayansa ta fara gani a k'asa ya bazasu ko ina tare da duk wani takardun d'akin ya watsa su kaca2,sai da ta tattara komai ta gyara tas, a hankali idonta ya kai inda yake,yana zaune a gefen side drawer can k'arshen gado ya kifa kansa da gwiwa yana kuka kad'an2,jikinta a sanyaye ta k'arasa gabansa ta tsugunna,a hankali ta furta *"gentle"*
Da sauri ya d'ago kai tare da sakin wani k'ara,ya kuwa cafki wuyanta ya shak'e "kaine kaine kaci amanata kaine ko?"
Idonta kawai zubar hawaye yake,gashi ya shek'e wuyanta sosai gaba d'aya ta gama tsorota,idonta ta lumshe wasu zafafan hawaye suke zuba a fuskarta tare da sauka a hannunsa,da sauri ya janye hannunsa daga shak'ar da yayi mata sannan ya saukar da idonsa akan k'wayar idonta....
"Kin santa?kinsan Sumayya da Aryaan?sune wanda suka ci amanata"
"Banci amanarka gentle wallahi tab'a iya cin amanarka ba"
Shima cikin kuka yake fad'in "k'arya ne" yana ta nanatawa,
Sai kuma ya mik'e tsaye ya bar inda take ita kuma ta bishi da ido,wuk'a taga ya d'akko hankalinta ya gama tashi lokacin da taga ya nufo inda take gadan2,
"Kece Sumayya kece maci amanata wlh sai na kashe kaina dan in daina ganinki,ya d'aga wuk'ar zai tab'awa kansa,cikin zafin nama ta ruga da gudu ta rik'e hannunsa suka fara kokowa,duk ya yanka mata tafukan hannu amma tak'i sakin wuk'ar a haka su daddy suka shigo,da k'yar aka samu aka k'wace wuk'ar,yana kallonta yana ta zantuka marar dadin ji,tana ji tana gani ta bar Arish aka fitar da ita daga d'akin,daddy ya bada umarnin a kaita asibiti ayi treating nata,Asrar da Ashaq ne suka tafi da ita.
*KANO STATE*
Tunda ta sauka a tashar kano line ta zauna tana sharar kuka ga hannu duk bandage,ganin mutane sun fara taruwa a kanta ne yasa ta tashi ta samu d'an napep ta shiga,bai ajjeta a ko ina ba sai k'ofar gidansu,dubu d'aya ta zaro a cikin kud'in da daddy ya bata ta biya mai napep d'in bata tsaya jiran canji ba ta shige gida.
Tun a tsoro ta jiyo ihun hadiza wanda duk wasu jijiyoyin jikinta sai da suka tsarga,ji take kamar ta juya ta koma kasancewar ihun yak'i tsayawa.
_Na aurar dake na huta dan haka kada ki kuskura ki dawo min gida da sunan yaji ko saki dan bazan d'auka ba_...
Maganar baba ta tuna ranar da aka d'aura aurenta,
_wannan yaji ne ko saki?shin taya zan yiwa baba bayani ya fahimceni?na shiga uku_
Abinda ta fad'a a ranta kenan,bata da yadda zatayi kawai ta saka k'afa ta shiga ciki.
Mata wajen shidda a tsakar gidan duk suka juyo suka kalleta,baba dake tsaye jikin k'ofar d'akin hadiza yana tofa addua a cikin ruwa shima tsayawa yayi yana kallonta,hakanne ya tabbatar mata da cewa hadiza nak'uda take amma ba wannan ne a gabanta ba illa kallon tuhuma da baba ke mata,batayi aune ba taji ya wurgo mata tambaya...
"Kinyi hatsari ne?" Da sauri ta kalli hannunta hawaye na fitowa a idonta,kafin tayi magana kukan jariri ya gama karad'e gidan,sai ganin baba tayi ya d'aga hannu yana fad'in "ya Allah kasa namiji ne" jikinta gaba d'aya yayi sanyi dan ta san tabbas idan hadiza namiji ta haifa kashinsu ya bushe.
*1 Minute later*
Yayar maman hadiza ce ta fito nannad'e da jariri a hannunta fuskarta sam babu fara'a,da sauri baba ya tashi ya k'arbi jaririn yanata murmushin farin ciki,sai daya rik'e a hannunsa sannan ita kuma ta gyara tsayuwa tace "gata nan 'ya mace ce,kuma tun kukan da tayi na farko bata sake yin wani ba Allah ya karb'i kayarsa" cikin kad'uwa baba ya sa hannunsa jikin hancinta yaji bata numfashi,da sauri ya mik'awa Aunty jamila gawar,ta k'arb'a ta k'ara da cewa "haka Allah yake ikonsa dan wani bai isa yayi masa katsalandan cikin sha'aninsa ba"...
Sumayya ya shak'e sosai yana fad'in "hadiza tace d'a namiji ne a cikinta,ke mayya ce kin canza mana da 'ya mace irinki sannan kin kasheta,to shari'a ce zata rabani dake"
*tofa😳 kunji wata sabuwa inji 'yan caca*
*Uba zaiyi shari'a da 'yarsa akan gaibu ne,ko kuwa zautuwa ce kawai da rashin tawakkali?*
*Me hakan ke nufi?*
*Readers yaya take ne?*
*Ku biyomu*
_whatsapp me 4 more details 07035111671(Sadeey)_
*Alk'alamin Sadeey & Nafsal*
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
&
*_Nafisa S Adamu_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
*🤝ALHERI WRITERS ASSOCIATION🤝*
_motto:Fasaharmu jarinmu_
5⃣3⃣↗5⃣4⃣
"Wallahi bansan komai ba baba,babu Wanda ya San gaibu sai Allah"
Baba kam hannunsa biyu ya shiga dukanta tun k'arfinsa,aka rasa Wanda zai ceceta a gurinsa sai da mak'obcinsa Malam lado yazo ya rik'e sa.
"Haba Malam sai kace baka da imani?ko kuwa baka san kaddara ba?"
Cikin zafin rai yace "na san kaddara amma wallahi wannan ba kaddara bace tun kafin ta bar gidannan take furucin sai taga k'arshen cikinnan gashi an haifa babu rai"
Haka ya cigaba da maganganu tare da fad'in sai ta bar masa gida,tun ana d'aukar abin wasa har yazo ya fara bawa mutane mamaki,Sumayya kuwa kuka kawai take saboda abubuwan sun mata yawa.
*********
Tunda ta hau motar gombe babu abinda take sai kuka,ta lullub'e fuskarta da hijab sai kuka take k'asa2 wasu daga cikin 'yan motar sai mita sukeyi akanta,har sai da wata tsohuwa ta hau fad'a "dame zataji? da damuwar dake tattare da ita ko kuma da fad'an da kuke mata,tunda har kukaga ta shigo motar haya ta kasa tsayar da hawayenta ai kunsan damuwar dake tare da ita ba ta wasa bace amma duk kunbi kun ishemu da maganganu da tsaki" haka tsohuwar tayi ta fad'a sannan sukayi shiru suka daina damun sumayya da mita.
*Gombe State*
Jikinta a sanyaye ta shiga cikin gidansu umma,a tsakar gida ta tarar dasu suna zaune suna hira kasan cewar lokacin yamma ne lik'is,
Farida ce ta fara ganinta, "la Aunty Sumayya oyoyo" da sauri su fatima suka mik'e tare da hugging d'inta...
Umma kuwa kallonta kawai take da ido dan kana ganinta zaka gano tsantsar damuwar dake tattare da ita,kasa matsawa kusa da umma tayi saboda kallon da umma take mata yasa ta tsure ta kuma tsorata da irin kallon..
Umma da kanta ta taso ta kamo hannunta,tana zaunar da ita kuwa ta fara kuka,sai da tayi mai isarta babu Wanda ya tanka mata sai dai duk ilahirin jikinsu yayi sanyi musamman Nasiba da ta dawo daga kasuwa ta tarar da Sumayya kuma cikin kuka ba murna ba tabbas ta San akwai matsala.
Sai bayan anyi sallah magrib umma taja Sumayya d'aki ta saka a gaba tace sai taci abinci,anan ma wani kuka ta saka,har sai da goggo ta dage da yi mata nasiha sannan ta samu taci abincin d'an kad'an dan jinsa take tamkar d'ata,ko minti biyu ba tayi da gama ci ba ta amayar dashi..
Ranar haka ta kwana da zazzab'i ta kuma kwana tana kuka yadda taga rana haka taga dare,duk kanin ilahirin gidan hankalinsu ya tashi musamman Malam daya dawo yayi2 ta fad'a masa damuwarta amma tak'i fad'a "ban San yaushe Sumayya zata ajje taurin kannan nata ba" abinda Nasiba ta fad'a kenan.
Kwana biyu da zuwanta amma tak'i fad'awa kowa abinda ya sameta,duk ta bi ta rame fiye da k'ima,hatta umma sai da ta tsorata da irin ramar da Sumayya tayi,gashi in banda gaisuwa babu abinda ke had'ata da kowa,kullun tana d'aki tana tunani.
******
Suna zaune a tsakar gida suna hira amma hankalin umma na kan Sumayya kwana biyunnan duk bata cikin hayyacinta kasancewar yadda kaga Sumayya ta canza,tashi tayi ta shiga d'akin,a zaune ta tarar da Sumayya tayi tagumi hawaye wani na bin wani a fuskarta,umma ta samu guri ta zauna ta zura mata ido na tsawon lokacin kafin ta fara magana cikin nutsuwa "wannan kukan da kike kina tunanin shine mafita a gareki?dama akwai abinda zaki b'oye min a cikin rayuwarki?Sumayya idan baki fad'a min damuwarki ba wa zaki fad'awa?na zura miki ido yau tsawon kwana uku amma kink'i ki fad'an meke faruwa dake"
Ta d'ago idonta da suka k'ank'ance saboda kuka sannan ta fara magana muryarta a dashe "umma ban San ta ina zan fara baki labari ba,ban san taya zanyi maki bayani ki fahimceni ba,ina ganin kamar in na fad'a miki kema bazaki yadda dani ba"
"Ko kowa bai fahimceki ba kinsan umma zata fahimta domin ta San abinda zamuyi da Wanda ba zamuyi ba,amma har yanzu da girman kai a tattare dake" Nasiba ta shigo tana maganar tare da samun guri kusa da umma ta zauna,ta kai hannunta kan kafad'ar Sumayya ta cigaba da fad'in "idan kika sanarwa umma sai kinfi samun sauk'in abin domin babu Wanda ya dace mu fad'awa matsalarmu sai ita"
Kanta a sunkuye ta cigaba da zubda hawaye tare da basu labarin duk abinda ya faru tun daga ranar da aka kaita gidan su *Aryaan* har dawowarta kano da kuma irin korar da baba yayi mata.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda umma take ta nanatawa,farida da Fatima da suke lab'e a k'ofar d'aki da saurinsu suka shigo suka zube a gaban Sumayya "Aunty kina nufin kinga gentle d'inki?"
Nasiba ta dalla masu harara tare da fad'in "dalla Ku tashi ku fice,dama kunajin duk abinda ake fad'a ko?kun koyi gulma,to Kubar nan"
Sum2 suka tashi suka fice,Nasiba ta kalli umma tace "umma kinga yadda Allah yake ikonsa ko?gashi hadiza ta haifi 'ya mace kuma ta mutu baba yaga ishara yanzu zai yadda babu mai yi sai Allah"
Hmmmm umma tayi ajiyar zuciya tare da kallon Nasiba "ba wannan ne a gabana ba Nasiba,ina tunanin yadda makomar auren Sumayya take a yanxu,sannan ina tausayin halin da gentle ya shiga,ina mamakin irin son zuciya na mutanen yanzu".
Basu da wani Abu Wanda ya wuce suje gurin malam(maihaifin umma), a lokacin suka d'unguma zuwan d'akin Malam...
Nasiba ce ta labarta masa duk abinda ya faru kamar yadda Sumayya ta fad'a musu....
"kin tabbatar abinda kika fad'a gaskiya ne"
"Wallahi duk abinda na fad'a gaskiya ne babu abinda na sauya a magana ta"
Tabbbb lallai a cikin wannan al'amari akwai Babban matsala da aka tafka,gaban Sumayya yayi mummunar fad'uwa lokacin da Malam yace "yanxu xan fad'a miki makomar aurenki"
Idonta k'yar a kan Malam yayinda hawaye ya cigaba da gudana a fuskarta ta san yanxu shikenan an rabata da gentle mutumin data so tun kafin ta San yana da hankalinsa tun lokacin da yazo kano a matsayin mahaukaci.
Yayi gyaran murya sannan ya cigaba da fad'in "aurenki da *Arish* yana nan har sai ranar daya sake ki da kanshi,amma babbar matsalarmu a yanxu itace yadda xa'ayi shi *Aryaan* ya fad'i gaskiya dan idan bai fad'a ba to xasuyi ta ganinki a matsayin babu aure tsakaninku da *Arish*...
" na shiga uku umma,ya zanyi wlh ina son mijina bazan iya rayuwa idan babu gentle ba,umma ban San halin da yake ciki yanxu ba,meyasa suka kasa gane irin son da nake ma mijina meyasa suka kasa gane gaskiya?umma dan Allah ku taimaka Ku barni na cigaba da zama da gentle harya samu sauk'i koda xai rik'a yanka jikina koda yaushe" kuka sosai Sumayya take,umma ta rungumeta tana ta rarrashi,Nasiba ma sai da tayi hawaye dan ta tausayawa Sumayya sosai.
Malam sau biyu yana zuwa Kaduna amma su momma sun kasa fahimta sun ce a k'ara bawa Sumayya hak'uri kuma in ta samu miji tayi aure,malam kam ya tausawa halin da *Arish* ke ciki,yayinda *Aryaan* ya koma London kamfanin takalma na daddy,as manager na company.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullun Sumayya cikin damuwa take da kuka,Malam ne ya yanke shawarar ta cigaba da karatu kawai dan hakanne zai sa ta d'an samu sukuni,Dan haka shi da kansa yaje kano ya karb'o credentials d'inta,bata wani samu result mai kyau ba Dan bata da maths a both waec da neco,haka ya samu yayi ciku2 ya sama mata damar zana waec,haka ta saka a ranta zatayi k'ok'ari tayi karatu akan matsala data shafi k'wak'walwa kodan ta gano wace cuta ke damun gentle,Dan haka tun kafin lokacin yayi ta fara amsa past questions sannan ta rink'a zuwa extra mural lesson anan wata government skul dake anguwarsu.
Haka har lokacin yayi ta zana waec ta gama successfully,sai jiran result kuma.
_*Alk'alamin Sadeey S*_ ✍
_daga_
*A.W.A*
_motto:Fasaharmu jarinmu_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
&
*_Nafisa S Adamu_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
*🤝ALHERI WRITERS ASSOCIATION🤝*
_motto:Fasaharmu jarinmu_
5⃣3⃣↗5⃣4⃣
"Wallahi bansan komai ba baba,babu Wanda ya San gaibu sai Allah"
Baba kam hannunsa biyu ya shiga dukanta tun k'arfinsa,aka rasa Wanda zai ceceta a gurinsa sai da mak'obcinsa Malam lado yazo ya rik'e sa.
"Haba Malam sai kace baka da imani?ko kuwa baka san kaddara ba?"
Cikin zafin rai yace "na san kaddara amma wallahi wannan ba kaddara bace tun kafin ta bar gidannan take furucin sai taga k'arshen cikinnan gashi an haifa babu rai"
Haka ya cigaba da maganganu tare da fad'in sai ta bar masa gida,tun ana d'aukar abin wasa har yazo ya fara bawa mutane mamaki,Sumayya kuwa kuka kawai take saboda abubuwan sun mata yawa.
*********
Tunda ta hau motar gombe babu abinda take sai kuka,ta lullub'e fuskarta da hijab sai kuka take k'asa2 wasu daga cikin 'yan motar sai mita sukeyi akanta,har sai da wata tsohuwa ta hau fad'a "dame zataji? da damuwar dake tattare da ita ko kuma da fad'an da kuke mata,tunda har kukaga ta shigo motar haya ta kasa tsayar da hawayenta ai kunsan damuwar dake tare da ita ba ta wasa bace amma duk kunbi kun ishemu da maganganu da tsaki" haka tsohuwar tayi ta fad'a sannan sukayi shiru suka daina damun sumayya da mita.
*Gombe State*
Jikinta a sanyaye ta shiga cikin gidansu umma,a tsakar gida ta tarar dasu suna zaune suna hira kasan cewar lokacin yamma ne lik'is,
Farida ce ta fara ganinta, "la Aunty Sumayya oyoyo" da sauri su fatima suka mik'e tare da hugging d'inta...
Umma kuwa kallonta kawai take da ido dan kana ganinta zaka gano tsantsar damuwar dake tattare da ita,kasa matsawa kusa da umma tayi saboda kallon da umma take mata yasa ta tsure ta kuma tsorata da irin kallon..
Umma da kanta ta taso ta kamo hannunta,tana zaunar da ita kuwa ta fara kuka,sai da tayi mai isarta babu Wanda ya tanka mata sai dai duk ilahirin jikinsu yayi sanyi musamman Nasiba da ta dawo daga kasuwa ta tarar da Sumayya kuma cikin kuka ba murna ba tabbas ta San akwai matsala.
Sai bayan anyi sallah magrib umma taja Sumayya d'aki ta saka a gaba tace sai taci abinci,anan ma wani kuka ta saka,har sai da goggo ta dage da yi mata nasiha sannan ta samu taci abincin d'an kad'an dan jinsa take tamkar d'ata,ko minti biyu ba tayi da gama ci ba ta amayar dashi..
Ranar haka ta kwana da zazzab'i ta kuma kwana tana kuka yadda taga rana haka taga dare,duk kanin ilahirin gidan hankalinsu ya tashi musamman Malam daya dawo yayi2 ta fad'a masa damuwarta amma tak'i fad'a "ban San yaushe Sumayya zata ajje taurin kannan nata ba" abinda Nasiba ta fad'a kenan.
Kwana biyu da zuwanta amma tak'i fad'awa kowa abinda ya sameta,duk ta bi ta rame fiye da k'ima,hatta umma sai da ta tsorata da irin ramar da Sumayya tayi,gashi in banda gaisuwa babu abinda ke had'ata da kowa,kullun tana d'aki tana tunani.
******
Suna zaune a tsakar gida suna hira amma hankalin umma na kan Sumayya kwana biyunnan duk bata cikin hayyacinta kasancewar yadda kaga Sumayya ta canza,tashi tayi ta shiga d'akin,a zaune ta tarar da Sumayya tayi tagumi hawaye wani na bin wani a fuskarta,umma ta samu guri ta zauna ta zura mata ido na tsawon lokacin kafin ta fara magana cikin nutsuwa "wannan kukan da kike kina tunanin shine mafita a gareki?dama akwai abinda zaki b'oye min a cikin rayuwarki?Sumayya idan baki fad'a min damuwarki ba wa zaki fad'awa?na zura miki ido yau tsawon kwana uku amma kink'i ki fad'an meke faruwa dake"
Ta d'ago idonta da suka k'ank'ance saboda kuka sannan ta fara magana muryarta a dashe "umma ban San ta ina zan fara baki labari ba,ban san taya zanyi maki bayani ki fahimceni ba,ina ganin kamar in na fad'a miki kema bazaki yadda dani ba"
"Ko kowa bai fahimceki ba kinsan umma zata fahimta domin ta San abinda zamuyi da Wanda ba zamuyi ba,amma har yanzu da girman kai a tattare dake" Nasiba ta shigo tana maganar tare da samun guri kusa da umma ta zauna,ta kai hannunta kan kafad'ar Sumayya ta cigaba da fad'in "idan kika sanarwa umma sai kinfi samun sauk'in abin domin babu Wanda ya dace mu fad'awa matsalarmu sai ita"
Kanta a sunkuye ta cigaba da zubda hawaye tare da basu labarin duk abinda ya faru tun daga ranar da aka kaita gidan su *Aryaan* har dawowarta kano da kuma irin korar da baba yayi mata.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda umma take ta nanatawa,farida da Fatima da suke lab'e a k'ofar d'aki da saurinsu suka shigo suka zube a gaban Sumayya "Aunty kina nufin kinga gentle d'inki?"
Nasiba ta dalla masu harara tare da fad'in "dalla Ku tashi ku fice,dama kunajin duk abinda ake fad'a ko?kun koyi gulma,to Kubar nan"
Sum2 suka tashi suka fice,Nasiba ta kalli umma tace "umma kinga yadda Allah yake ikonsa ko?gashi hadiza ta haifi 'ya mace kuma ta mutu baba yaga ishara yanzu zai yadda babu mai yi sai Allah"
Hmmmm umma tayi ajiyar zuciya tare da kallon Nasiba "ba wannan ne a gabana ba Nasiba,ina tunanin yadda makomar auren Sumayya take a yanxu,sannan ina tausayin halin da gentle ya shiga,ina mamakin irin son zuciya na mutanen yanzu".
Basu da wani Abu Wanda ya wuce suje gurin malam(maihaifin umma), a lokacin suka d'unguma zuwan d'akin Malam...
Nasiba ce ta labarta masa duk abinda ya faru kamar yadda Sumayya ta fad'a musu....
"kin tabbatar abinda kika fad'a gaskiya ne"
"Wallahi duk abinda na fad'a gaskiya ne babu abinda na sauya a magana ta"
Tabbbb lallai a cikin wannan al'amari akwai Babban matsala da aka tafka,gaban Sumayya yayi mummunar fad'uwa lokacin da Malam yace "yanxu xan fad'a miki makomar aurenki"
Idonta k'yar a kan Malam yayinda hawaye ya cigaba da gudana a fuskarta ta san yanxu shikenan an rabata da gentle mutumin data so tun kafin ta San yana da hankalinsa tun lokacin da yazo kano a matsayin mahaukaci.
Yayi gyaran murya sannan ya cigaba da fad'in "aurenki da *Arish* yana nan har sai ranar daya sake ki da kanshi,amma babbar matsalarmu a yanxu itace yadda xa'ayi shi *Aryaan* ya fad'i gaskiya dan idan bai fad'a ba to xasuyi ta ganinki a matsayin babu aure tsakaninku da *Arish*...
" na shiga uku umma,ya zanyi wlh ina son mijina bazan iya rayuwa idan babu gentle ba,umma ban San halin da yake ciki yanxu ba,meyasa suka kasa gane irin son da nake ma mijina meyasa suka kasa gane gaskiya?umma dan Allah ku taimaka Ku barni na cigaba da zama da gentle harya samu sauk'i koda xai rik'a yanka jikina koda yaushe" kuka sosai Sumayya take,umma ta rungumeta tana ta rarrashi,Nasiba ma sai da tayi hawaye dan ta tausayawa Sumayya sosai.
Malam sau biyu yana zuwa Kaduna amma su momma sun kasa fahimta sun ce a k'ara bawa Sumayya hak'uri kuma in ta samu miji tayi aure,malam kam ya tausawa halin da *Arish* ke ciki,yayinda *Aryaan* ya koma London kamfanin takalma na daddy,as manager na company.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullun Sumayya cikin damuwa take da kuka,Malam ne ya yanke shawarar ta cigaba da karatu kawai dan hakanne zai sa ta d'an samu sukuni,Dan haka shi da kansa yaje kano ya karb'o credentials d'inta,bata wani samu result mai kyau ba Dan bata da maths a both waec da neco,haka ya samu yayi ciku2 ya sama mata damar zana waec,haka ta saka a ranta zatayi k'ok'ari tayi karatu akan matsala data shafi k'wak'walwa kodan ta gano wace cuta ke damun gentle,Dan haka tun kafin lokacin yayi ta fara amsa past questions sannan ta rink'a zuwa extra mural lesson anan wata government skul dake anguwarsu.
Haka har lokacin yayi ta zana waec ta gama successfully,sai jiran result kuma.
_*Alk'alamin Sadeey S*_ ✍
_daga_
*A.W.A*
_motto:Fasaharmu jarinmu_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S Adamu_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
5⃣5⃣↗5⃣6⃣
Yau ta kasance ranar lahadi,su umma na zaune a d'aki su duka suna hira,yayinda sumayya ta rakub'e a gefe ta zuba uban tagumin data saba...
Cikin sallama malam ya shigo da murna yana fad'in "Alhamdulillah" duk Kansu idonsu akan malam yake hake har had'a baki suke wajen fad'in "Malam lfya" Sumayya ta tsaida hawayen idonta ta kalli Malam dan tuni zuciyarta ta gama raya mata cewar *Arish* ya samu lfya,yayinda take kallon takardar hannun Malam a matsayin takardar saki ne.
Har ya zauna kan tabarma bakinsa bai daina murmusawa ba,kowa ya k'agu yaji sak'on dake tafe dashi,
"Gashinan sakamokan jarabawar Sumayya na k'arb'o bata da gyara ko d'aya"
"Masha Allahu" shine abinda umma ta fad'a tana murmushi,Malam ya cigaba da fad'in "center da tayi jarabawar sun d'auki nauyin duk Wanda ya samu distinction a subjects biyar wanda akeso duk wani d'alibin Science ya samu sunce wani kamfanine ya biyawa mutane 10 da suka samu wannan distinction a subject biyar zasuje k'asar England dan kammala digiri(degree) d'insu kuma Sumayya na d'aya daga cikinsu"
Duk kan d'akin aka d'auki murna da hamdala,umma hadda yin sujudush-shukar,Sumayya kuma hawaye takaici ke tsiyaya a idonta,
"_England_" ta maimata Kalmar a zuciyarta..
_zan tafi karatu *Arish* da aurenka a kaina,zanje na nemo maganin da zan warkar da kai,zan tafi in barka har na tsawon shekaru,dan Allah ka yafe min mijina_....
Abinda zuciyar ta keta nanatawa kenan,tashi tayi ta fice ta bar d'akin dan hayaniyarsu ta fara sata ciwon kai..
***************
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a kuma wannan lokacin ne su malam keta shirye2 tafiyata komai ya samu zaice na Sumayya ne,
Visa ce har yanxu ba'a samu ba da tuni mun tafi...
Babanmu kuwa har ya manta damu ya ciremu a sahun 'ya'ansa,dan lokacin da Malam yaje masa da maganar karatuna,wulak'antashi yayi tare da bada sak'o a fad'awa umma ya saketa kuma ya bar mata gayyar 'ya'ya mata ta rik'e kada ta sake ta jeramu a sahun 'ya'yansa,ranar da naji labarin nasha kuka tare da d'aukar alwashin na bar saka kaina a 'ya'yan baba har abada dan ko a hanya bazan sake nuna na sanshi ba.
****
Yau ta kasance ranar juma'a saura kwana uku jirgin su Sumayya ya Lula k'asar England, tana zaune a tsakar gida ta had'a kai da gwiwa tunani take ta wace hanya zata b'ullowa Malam akan maganar da ke cinta cikin zuciyarta...
Cikin rashin kuzari ta tashi ta nufi d'akinsa,gabanta na fad'uwa tayi sallama yayi mata iso,
"Da......da...dddd......dama" maganarta a sark'e gaba d'aya ta kasa kamo Kalmar da zata fad'a,kamar ya karance sai ji tayi yace "kina son kije kiyiwa mijinki sallama ko?" a firgice ta d'aga kai ta kalleshi,murmushi yayi sannan yace "yanxu maganar da nake yi da goggonku kenan,ki shirya gobe da safe zamuje Kaduna dani dake da farida" wani dad'i ya mamayeta hawaye mai had'e da murmushi suka sauka a fuskarta...
Ranar kasa bacci tayi jira kawai take gari ya waye dan daren ma yayi mata tsayi,fatima kam jin ance za'aje da farida yasa ta fara falIi itama sai taje taga *gentle* Dan haka umma ta yanke hukuncin babu wanda zaije a cikinsu sai Nasiba...
Tun asuba Sumayya ta gama wanka tayi sallah ta d'akko azkar tana zikirin safiya rabi kuwa tunanine taya *Arish gentle* d'inta zai karb'eta,sak'e2 babu Wanda ba tayi ba,ita ta tashi nasiba Malam kuwa dama ya tashi...
K'arfe bakwai a tasha tayi musu suna jiran mota ta cika a tafi.
*KADUNA*(garin Malam)
Tunda suka shiga garin zuciyarta ke bugawa,shekara d'aya da watanni har 6 rabonta da kaduna...
Gidan ma ya canza mata kasancewar paint da gate da aka sake ga unguwar ta k'ara cika,a harabar gidan ta d'an tsaya tana goge hawaye,rayuwata a gidan ta dawo mata sabuwa,sai da Nasiba ta jata sannan suka shiga ciki...
Sai hada2 ake da alama anyi bak'i a gidan kasancewar indai kaga gidan a rud'e to anyi bak'i dan iyalan gidan akwai karamma bak'i musamman idan masu kud'ine kamarsu...
"Lahh Aunty oyoyo"
Kallonshi take cike da mamaki ta San dai triple ne amma bazata iya cewa ga sunanshi ba kasancewar bata zauna da triple ba
"Nasan baki gane ni ba" ya katse mata tunani
Ya sake yin murmushi yace "Asrar ne"
Itama murmushi tayi kafin ta bud'e baki taji anyi hugging d'inta ta baya tare da k'walla k'aran murna,cikin zumud'i Sumayya ta juyo ta kalli Zahra suka rungume juna suna murna,sai kuma hawaye ya fara sauka a idon Sumayya cike da tariyo rayuwarta a gidan...
Duk wad'anda ke falon sai kallon su suke da alama dai an dad'e ba'a had'u ba duk haka suke fad'a,
"Ya nake jin hayaniya ko an dawo daga d'aurin auren?"
*gabana yayi mummunar fad'uwa muryar d'aya daga cikin mutanen da bazan tab'a mantawa ba,muryar momma ce*....
Kallon kallo muka tsaya yi nida ita an rasa Wanda zai yi magana,ko wanne da abinda zuciyarshi ke sak'a masa.
By
Sadeey
&
Nafsal
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
5⃣7⃣↗5⃣8⃣
Wasu zafafan hawaye suka sauka a idona da sauri na k'arasa gurinta na durk'usa ina gaidata tayi saurin d'agoni tare da share min hawaye da hannunta "bana son kina kukan nan Sumayya,ki barwa Allah komai kowa da irin tasa k'addarar wannan itace taku ke da *Arish* fatan Allah baku ikon cinye jarabawar,ki rage damuwa 'yata dubi duk kin rame kin zuge,Arish ai ya fara samun sauk'i ma" ita kanta momma tana maganar amma idonta duk ya ciko alamun tana k'ok'arin yin kuka.
Sai da mukaci abinci muka huta hankalina duk ya tashi fatana kawai inyi tozali da *Aryaan* wanda aka shaidamin yau d'aurin aurensa,inason inji dalilin bak'anta min da yayi shi kuma ya farantawa kansa,yayinda wani bangare na zuciyata ke matuk'ar son ganin *Arish*...
Sallamar Rabi'at ce ta katseni,da gudu ta k'araso ta rumgumeni tana murna "ashe da rabon zan sake ganinki Sumayya"
cikin farin ciki nace "gani a gabanki kina ganina wannan babyn fa?"
"d'anki ne gashinan har ya girma watanshi bakwai kenan"
na karb'eshi cikin murna na d'agashi nace "ya Sunanshi?" ta d'anyi shiru kafin tace "Sunan *Arish* yaci amma muna kiranshi da little" jikina duk yayi sanyi muryata a k'asa nace "Allah ya raya shi"
"amin"ta amsa.
Hira sosai Rabi'at ta din gayi da Nasiba kamar dama sun san juna,anan ne take fad'a mata cewar karatu zan tafi England,Rabi'at tayi min murna sosai tare da fatan alkhairi...
Kusan awarmu biyu dan Zahra ma zuwa tayi aka cigaba da hirar da ita,ni kam sama sama nake amsa musu kasancewar hankalina ya tafi wajen *Gentle*...
"yawwa ina kuke,momma tace tazo" muryar Asrar ce na jiwo wanda tun kafin ya k'arasa maganar na mik'e tsaye,tare da Nasiba muka je gurinta tsayin lokaci ta kasa cewa komai,daga k'arshe ta datse shirun da fad'in "karatu zaki tafi ko?"
"eh" na amsa a tak'aice
"sai yaushe kenan?"
"shekara bakwai ne,amma idan nayi shekara uku zanzo ganin gida"
"Ayya to Allah taimaka 'yata ki zauna ki nutsu kiyi abinda ya kaiki kinga rayuwar can da d'abi'unsu ba irin namu bane,ki tsare mutuncinki kinji ko,Allah ya kaiki a sa'a ya dawo dake a sa'a"
"Amin" muka amsa nida Nasiba yayinda hawaye ya sake samun gurbi a kuncina,nasan ta gani amma sai ta juyar da kai kawai tace *"Asrar* rakasu wajen *Arish* d'in" jikina a sanyaye muka bi biyan *Asrar* .
direct d'akin *gentle* muka nufa gabana sai fad'uwa yake,yau kam d'akin nasa a gyare yake bai b'ata ba sai dai d'akin duk ya gauraye da warin yawu duk da dai da k'amshin turaren wuta amma akwai d'an wari warin da alama shi nasa abin zubda yawu ne dan komai a kimtse yake tiles ya fari sol a goge tas,yana kwance akan gado ya lulub'e jikinsa da blanket sai kansa a waje amma idanuwanshi a rufe suke..
"bacci ma ya samu" Asrar ya fad'a,
"Allah sarki *gentle* Allah ya baka lfya" Nasiba ta fad'a sannan
ta juyo ta kalleni "mu fita idan ya tashi sai mu dawo ko?" na girgiza kai hawaye na zuba a fuskata nace "kuje ku kawai ni inanan har sai ya tashi,kinsan bazan iya fita ba" kallona suke gaba d'ayansu cike da jin tausayina,haka suka fita suka barni a d'akin.
Na sake k'arewa d'akin kallo,kai tsaye wardrobe d'insa na nufa na bud'e kayansa anyi hanging d'insu wasu kuma a ninke a ajje komai dai neat,idona ya kai kan wani d'an k'aramin diary,nayi saurin kai hannuna gurin na d'auka, wasu hotuna ne suka zubo k'asa na d'auka na fara dubawa,duk yawancinsu pix d'ina ne wanda bansan a ina ya samesu ba sai hotunansa guda hud'u a ciki,jingina nayi da drawer kuka sosai nake dan na kasa b'oye hawayena sai da nayi mai isata sannan na goge na zari pix d'insa guda uku na sakasu cikin diary d'in na b'oye a jakana.
Kusa dashi na zauna jikin side drawer har a lokacin bacci yake,na k'urama fuskarshi ido,ya rame sosai yayi bak'i da alama yana cikin matsannancin hali fiye da wanda na barshi a ciki dan yadda numfashinsa ke fita kasan baccin wahala yake...
Hannuna nakai kan blanket d'in tare da yaceshi daga jikinsa zubur ya bud'e ido tare da zare su,hanjin cikina ba k'aramin kad'awa yayi ba,nayi saurin mik'ewa tsaye zan bar gurin yayi saurin fuzgoni gaba d'aya nayo baya kamar zan fad'a kansa nayi saurin dafa bango...
A tsorace nake kallonsa kad'an ya hana inyi fitsari a tsaye,ya saki hannuna ya shak'en wuya "wace ce ke?"
yadda yayi maganar ne yasa fitsarin dana matse ya samu damar zubowa,jikina gaba d'aya ya hau tsuma,ya fincikoni ya kaini jikin drawer d'insa tare da jinginani da ita sosai "kashe ki zanyi Sumayya"
hawaye tuni ya gama wanke min fuska bakin na karkawa cikin in ina nace "ba.......ita..........bace" hab'a ta ya rik'e tare da jijjagamin fuska wasu stars d'in azaba na rik'a gani a cikin kaina "wace ce ke?" ya sake maimatawa "ki nemo min sumayya na kasheta" na sake kallonsa a tsorace,runtse idona nayi a hankali na fara magana *"gentle* nice Sumayya ka kasheni idan har hakan zai maka dad'i ni a yanzu na zab'i mutuwa da wannan hali dana saka ka a ciki *Arish*"
"waye *Arish*?,waye gentle?" yayi maganar cikin alamun kuka,bud'e idon da zanyi naga hawaye sharkaf a fuskarsa,
"ki fad'amin waye hakan?" yadda yake magana kamar k'aramin yaro,na tsaya na k'ura masa ido yana kuka yana k'ara tambayata waye Arish,
nayi ajiyar zuciya lokacin daya saki hannunsa daga fuskata dan rik'on da yayi min bana wasa bane "kana son sanin waye Arish?" kai ya d'aga alamar eh "to sai ka fad'amin wace ce Sumayya meyasa kake son kashet.............................da gefen hannunsa ya make ni wanda har saida naje k'asa,
nafi minti biyar ina maida numfashi na kasa tashi saboda zugin da fuskata kemin,ina tashi naga jini a gurin,da sauri na tab'a gefen fuskar na kuwa ji jinin ga kunburi ga rad'ad'i,a gigice na mik'e tsaye,wata hajijiyace ta kwasheni wadda ta sani k'ara zubewa a gun.
_by_
_*Sadeey*_
_&_
*_Nafsal_*
[9/23, 7:23 PM] Nafsal: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
6⃣1⃣↗6⃣2⃣
Fad'a sosai malam ya rik'a yi min a washe garin dawowarmu daga kaduna daya ga gefen fuskata ya kunbura.
Dalilin fad'an kuwa shine meyasa ban fad'a masa da ciwo a fuskata ba a siyo magani,gashi har jibi ne tafiyarmu.
Nasiba kam bata da wata magana da ta wuce maganar gentle tausayinshi duk ya mamaye zuciyoyin 'yan gidanmu.
Ana gobe zan tafi kuwa,kwana nayi ina shiri ina kuka tun suna bani hak'uri har suka gaji suka k'yaleni dan sun lura da cewa yanzu kuka baya min wahala.
*************
Mu goma da zamu tafi duk mun hallara a airport muna ta zirga2 karb'ar number...
goggo da malam dasu Nasiba duk sun rakoni,umma ce kad'ai bata zo ba mun barta a gida.
k'arfe tara jirginmu ya lula k'arsar England(London),nasha kuka kuwa kamar raina zai fice haka na tafi ina d'aga ma 'yan uwana hannu suma suna d'agomin..
a cikin jirgi ma haka na had'a tagumi jefi2 hawaye kan zubomin in saka handkerchief in goge,haka har bacci ya kwashe ni.
*ENGLAND*
A babban airport na london jirginmu ya sauka,har lokacin bacci nake,sai da wata daga cikinmu ta tasheni sannan na tashi naja trolley d'ina muka fice.
an gama tsara komai na zuwanmu,babban gidane aka bamu mai flat 10 a ciki but kowane flat gida biyu ne a had'e,d'aya mace d'aya namiji,hakanne yasa na tsorata na tuno fad'an da malam da momma sukayi min jikina ya k'ara yin sanyi addua kam koda yaushe bakina ita yake yi...
Yau kwananmu biyu a gidan bana fita ko k'ofa dan a tsorace nake,kuma ko wane gida an zuba duk kayan buk'ata komai akwai hatta kayan abinci da fruits da su d'anyun kaji duk na gani a cikin fridge,haka nan koda yaushe nake tunanin yadda muke rayuwa cikin talauci amma nan ga daula sai kace aljannar duniya,a kullum idan zanyi bacci nakan k'udundune a cikin bargo in takure a gadon saboda ina tsoron gidan yadda yake da girma haka.
Tunda nazo k'asar ban tab'a jin anyi kiran sallah ba sai dai in kintata lokaci kawai inyi sallahta.
Yau kwananmu uku a gidan amma har na gaji,so nake kawai in fara karatu,gashi inason in sayi waya saboda kiran gida tunda muka xo bamuyi waya ba,akwai waya a gidan a falo da cikin d'akunan amma irin cellular d'innan ce tafi da gidanka,ni kuma ban iya ta ba,kuma bazamu fara lectures ba sai munyi sati guda da zuwa.
ina zaune a d'aya daga cikin kujerun parlor bayan na gama breakfast, _littafin du'a'ul mustajaba_ne a hannuna ina duba wa kawai na tsinkayi ana kad'a bell d'in gidan,gabana yayi mummunar fad'uwa,a hankali na tashi na nufi k'ofar na d'an lek'a,ganin macece yasa nayi ajiyar zuciya na bud'e..
Doguwar riga ce a jikinta ta atamfa sai rolling da tayi da d'an k'aramin veil,hakanne yasa na tabbatar itama 'yar nigeria ce,kuma tare muka zo.
"bismilla shigo"
"okay" ta amsa sannan ta shigo cikin gidan..
bayan mun gaisa ne tace "Sunana Hafsat nima 'yar gombe ce tare aka turo mu karatu nan"
"okay Allah sarki ya zaman bak'unta?"
"Alhamdulillah,dama zuwa nayi ince miki ki shirya muje super market siyan kayan abinci da kuma wasu kayan sawa kinga bazai yuwu ace muna yawo da atamfa ko lace a cikin k'asar nan ba dan duk inda mukayi za'ayi mana dariya,sauran duk sunje sun siyo shine nace bara nazo muje dake dan wallahi na gaji da shan lemo da cheese"
"amma ai naga komai akwai danni har kaji da fruits da duk wani kayan buk'ata wanda na tsani da wanda ban sani ba duk akwai"
kallon mamaki ta bini dashi dan bata yarda ba har sai dana jata na nuna mata komai.
"to gaskiya sai dai idan neighbor d'inki ne ya sa aka kawo miki komai,ke babu tantama shine ma wallahi,kiyi masa godiya,danni nawa gaisawa kawai yazo mukayi babu wani alkairi da yayi min"
gabana ya fad'i na kalleta nace "to meyasa yayi min?"
dariya tayi sannan tace "oho masa" ni dai shirya ki rakani..
jikina a sanyaye na shirya na zura dogon hijabina mai hannu har k'asa yake hijabin sannan na d'ebi 'yan kud'i da zan sayi waya da sim card dama already mun canza kud'inmu tun a nigeria...
dariya sosai tayi lokacin da taga dressing d'ina banji haushi ba kawai na bita muka tafi,
maganarta ta tabbata dan duk inda mukayi ana kallonmu,a d'arere na rakata ta gama siyayyar kayan abinci ta kuma siyo English wears masu yawa dan akwai wanda nace mata kai gaskiya hafsat bai kamata kina 'yar musulmai amma kiyi wannan shigar,da taga na dameta da mita sai tace a gida zata dunga sawa kawai.
Haka muka hayo taxi da kaya nik'i2,a lokacin ne na gane cewa tabbas d'iyar wani hamshak'in mai kud'ice a gombe,dan turaruka dana d'auki guda biyu sai ta k'aromin guda uku kuma ta hana in biya kud'in ita ta biya,sannan naji taya waya da babanta tana yi masa shagwab'a har take ce masa ta gama siyayya kuma akwai sauran kud'i sosai a hannunta bata buk'atar wasu..
hawaye ne ya cika a idona a zuciyata nace
_ni in samu soyayyar mahaifi ma ban samu ba,amma dai malam yayi min k'ok'ari tabbas,sai dai fatan Allah ya bayashi da gidan aljannah_.
"tunanin me kike Sumayya?"
"babu komai"
"tunanin gida ko?"
na girgixa kai alamar a'a
"lokaci yayi da zaki ajje duk wani tunani kiyi karatu dan ki farantawa iyayenki Sumayya"
haka tayi ta rarrashina ni kuma kamar ta tunxura ni na rik'a kuka,nan danan idanuna suka kunbura sukayi jajir dan indai akayi maganar gida nafi tunowa da *Arish*.
Sai da na rakata har cikin flat d'inta na gani saboda ban san inda take ba,sannan nayi mata sallama ta zubomin turarukan a leda na fito,ina fitowa siyan waya fad'omin na dafe kai cike da jin haushi..
Ina isa flat d'ina na ganshi a bud'e,abin ba k'aramin d'agamin hankali yayi ba,dama ban rufe ba?na tambayi kaina,nidai a iya tunanina na rufe kuma na saka code,jikina a sanyaye na shiga ciki.
Babban abinda ya d'aga min hankali ya kuma bani tsoro wanda har na tsaya cak na kasa motsi bai wuce abinda na hangowa idona ba shin mafarki nake ko gaskene?
abinda zuciya ta ta rik'a tambaya kenen...
*hmmmmmm muje xuwa dai*📝
_hannu biyu_🤝
_*Sadeey & Nafsal*_
[9/23, 7:23 PM] Nafsal: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
5⃣9⃣↗6⃣0⃣
Kusan minti ashirin ban motsa ba,har sai da naji zugin na d'an raguwa sannan na tashi da sauri na fad'a toilet d'insa,wani zarni da wari ne suka bugoni wanda kad'an ya hana inyi amai,da sauri na toshe hanci sannan na bud'e snk na wanke ciwon da ruwan dumi na rik'a tsoma handkerchief ina mannawa a gurin ciwon har sai da naji d'an dama2 sannan na barshi...
idona ya kai kan basket d'in dake cike da kayan wanki,nayi saurin k'arasawa gurin na bud'e wani mugun wari ya k'ara bugoni da zarni duk yanda akai kwandon kayan ne ya haddasa wari a band'akin.
Da sauri na fito daga band'akin, na hangoshi a rakub'e a kan gado,idonsa na kallon k'asa,banyi masa magana ba na ajje mayafina sannan na koma cikin band'akin ina hawaye....
_Allah sarki gentle,ko lokacin da kaiyi haukan k'arya bakayi wannan k'azantar ba,nasan da kana da hankali bazaka tab'a zama cikin datti ba,nasan da lafiyar ka k'alau d'akinka bazai babanta da band'akinka saboda k'amshi,amma ta sanadina ta sanadinmu nida *Aryaan* ka shiga mawuyacin hali,inama zasu barni da kai in zauna dakai wlh da baza'a tab'a jin d'akinka da band'akinka haka ba_....
Cikin kuka na k'arasa band'akin na d'ebo kayan, duk inners d'inshi ne,haka na had'a ruwan wanki tare da tsiyaya turaren wanki mai k'arfi a ciki na hau wankewa baji ba gani,na gama sab'i na farko inayin na biyu naji an bud'e k'ofa ana shigowa...
"a'ah Aunty ai da kin barshi ma mai wanki zaizo anjima ya wanke"
Na d'ago kai idona cike da hawaye nace "mai wanki?hmmm idan har yanzu baku yarda cewa *Arish* mijina ne ba,tabbas akwai ranar da gaskiya zata bayyana zaku gane komai *Asrar* ,bana k'yank'yamin mijina da ace a gidannan zan zauna da bazan gaji da tsabtace shi ba so ba adadi a ko wace rana"
kuka yaci k'arfina na fara reroshi a fili sannan na cigaba da fad'in
"bana jin *Aryaan* zai gama da duniya lafiya,shi yanxu gashi yayi aure zai zauna da matarshi amma ni yanxu ya barni da auren *Arish* a kaina sannan ya haddasa masa ciwo wanda ba wanda ya san lokacin warkewarshi,Allah ya saka mana"
na cigaba da kuka mai tsanani ina fad'in "meyasa *Aryaan* zai min haka meyasa zaiyi k'ok'arin rabani da farin cikina,na rantse da Allah *Asrar* babu abinda ya tab'a had'ani dashi na zamantakewar aure wlh wlh in har akwai Allah ya sa in dawwama a wuta"
Shima *Asrar* hawayen yake,ya juya ya kalli *Arish* wanda a lokacin ya kama k'asan rigarshi yana ci abin tausayi,
"amma idan hakane meyasa yaya *Aryaan* zaiyi haka?meye ribarshi?"
cikin kuka nace "ribarshi itace ya rabani da *Arish* kuma ya raba yaji dad'i,lokacin da aka kawoni gidan nan a matsayin matar *Aryaan* ya gana min azaba sosai baya kulani bayason ganina amma da yake na jajirce wajen yi masa biyayya kullum yana kyarata da asuba zai shigo d'akina ya shek'an ruwan sanyi haka zan tashi a tsorace,to kasan zuciya na son mai kyautata mata hakan ne yasa yazo ya fara sona,ranar daya nemi mu had'a gado nace yaje zanzo wlh ina zuwa naji yana yiwa abokinsa waya kan cewar zai yi amfani dani sbda ya fara sona sai dai duk abinda zai faru ya faru,a ranar ban kwana a part d'inmu ba dan pretending nayi na ciwon ciki na kwana a part d'in momma kawai saboda in kare darajar aurena,a ranar nayi chatting da *Arish*wanda a wayar momma na d'auki wayar nace mata inason kiran gida ta bani wayarta kusa sa Aryaan ya siya min waya duk a ranar da abin zai nemi in kwana dashi,nayi chat a Arish a matsayin frnd d'insa da safe na koma part d'inmu a ranar da zaku dawo kenan,kawai sai gashi yazo d'akina lokacin da waya a hannuna still ina chatting da *Arish* ya fuzgi wayar yayi wurgi da it ya fuzgoni da niyar yin lalata dani da k'yar na tsare daga gurinsa na nufo falo,bayan ya fitane na dawo na d'auki waya na gayawa Arish komai lokacin ma ban san shine gentle d'ina ba,ina wayar ya shigo ya warce wayar ya fad'a masa maganganu marar dad'i sannan ya fara k'ok'arin b'ata min rayuwa da k'yar na k'waci kaina na gudu nayo part d'inku lokacin duk kuna zaune sai kawai shigowa yayi da cewa ya rigada ya sanni a 'ya mace kuma ya nunama *Arish* bedsheet wanda duk ya b'aci da jini ban san a ina ya samo jinin ba" ta k'arashe maganar tana zubda hawaye...
Shi kansa *Asrar* hawaye yake zubdawa yayinda ya fara fahimtar maganar Sumayya gaskiya ne.
_yaya ya naga gwiwar hannunka da ciwo a ina kaji?_
maganarsu da *Aryaan* ya tuna wanda a lokacin sai da ya duburburce sannan yace bugewa yayi da k'arfe a gurin aiki...
Duk abinda sukeyi momma na jikin k'ofa tana jinsu,hawaye sosai take zubdawa dan a yadda Sumayya ke magana tana tunawa abubuwan da duk suka faru...
"Asrar wlh karatun nan da zan tafi zan tafi ne akan nemo matsala da ta shafi *Arish* zan nemo masa magani zanyi karatu ne saboda shi amma ba dan haka ba da babu abinda zai sa in bar k'asarmu in tafi karatu da aure a kaina sannan in nisanta da mahaifata,alfarma d'aya nake nema a gurinka idan har Allah yasa kafin in dawo Arish ya samu sauk'i dan Allah ka taimaka ka karb'ar min takardar saki a gurinsa dan in daina zama da igiyar aure a kaina dan wlh nasan ba zasu yarda da duk abinda zan fad'a ba Aryaan ya rigada ya tarwatsa farin cikina"
"zaki dawo gareshi kece matar yaya Arish ta har abada insha Allahu"
"Asrar hakan baxai yuwu ba an riga anyi min tabon da bazai b'ace ba babu wanda zai yarda da duk abinda zan fad'a in har Aryaan bai fito ya fad'i gaskiya ba"
Ajiyar zuciya Asrar yayi sannan yace "zan samu momma inyi mata bayani na san idan ta tsareshi zai fad'i gaskiya"
tayi saurin kallonsa idonta sharkaf da hawaye tace
"a'a kada ka fad'a mata dan Allah,banason ace daga zuwana na k'ara haddasa wata matsalar,da ace zai fad'i gaskiya da tuni ya fad'a tunda yana ganin halin da *Arish* ke ciki, ka k'yaleshi na san akwai sakayya ko bai ganta a duniya ba zai ganta a lahira,kaima abinda yasa na baka labarinnan saboda ina son idan *Arish* ya samu sauk'i ya bani takardata kasan babu yadda za'ayi inyi wani auren tunda da wani auren a kaina"
Momma kukanta na daf da fitowa fili,hakanne yasa tayi saurin fita daga d'akin tana hawaye tare da k'udirin sai tayi bincike akan abubuwan nan...
*Asrar* ne ya taya ni muka k'arasa wanke kayan sannan ya fita yaje ya shanyasu,ni kuma na wanke band'akin tas sannan na fesheshi da turaruka nan da nan k'amshi ya bayyana labarin wari ya kauce.
k'arfe uku da rabi mukayi shirin tafiya babu abinda ya k'ara had'ani da *Arish* dan tun ina wankin band'akin naga yayi bacci har mukazo tafiya yana bacci,haka muka tafi ban ga *Aryaan* ba wanda naso ace na ganshi dan in fad'a masa maganganun dake cikin raina.
_hunnu biyu_🤝
_*Sadeey & Nafsal*_✍
[9/24, 9:26 AM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```dedicated to beebahluv & Munay```
6⃣3⃣↗6⃣4⃣
Gaba d'aya tsoro da fargaba ya gama kamani,na kasa ko da motsi daga inda nake tsaye,
_shin zahiri ne ko mafarki nake_?
abinda zuciyata ta cigaba da tambaya kenan jikina na tsuma,ya ajje remote a gefe sannan ya taso ya iso inda nake,ya hura min iska a fuska,nayi saurin dawo da idona gareshi,tsoro da fargaba ya bayyana a fuskata....
Zagayani yayi har sau biyu sannan ya dawo gabana ya karkad'a hannunsa cikin isa da rainin hankali ya fara magana "kinyi mamakin ganina a gidanki?hmmm ba abin mamaki bane tunda kin yarda ina sonki kuma ina kishinki,amma sai dai ke kanki kin kasa gane hakan shin *MENE AIBUNA* dan naso matar k'anina?kin san kuwa menene so?sumayya na so ace kin amince mun zauna da zakiyi matuk'ar alfahari dani,amma tunda naga ke kanki rawa yake sam bakyaji babu imani da tausayi a ranki shiyasa nayo visa nayo tattaki tun daga nigeria har london saboda in miki warning na farko kuma na k'arshe".
Kallonshi nake kawai a zuciyata kuma ina neman tsari daga sharrinsa,ban ankara ba naji ya fuzgo hannuna,na d'an saki wani k'ara a firgice na fuzge hannunsa daga nawa,
"azzalumi maci amana wanda bai san darajar aure ba,kai ba'ace maka mugu marar imani da tausayi har kaine zaka ce min,wlh Allah ba zai tab'a barinka ba sai ya saka min akan duk abinda kayi mana ni da Arish"
Na cigaba da kuka ina haki tare da fad'in "kuma duk abinda ka min sai anyi maka, ka rabani da farin cikina ka rab......................" wanke ni da mari yayi,ya d'aga hannu zai sake mari na kawai yaji an rik'e hannun ta bayanshi tare da fad'in "enough is enough guy"
ya saki hannun Aryaan sannan ya dawo gabanmu ya kallesa "me tayi maka,meyasa ka mareta?" duk kanmu kallon tuhuma muke masa yayinda gabana ya cigaba da fad'uwa hannuna akan kuncina hawaye na bin kuncin,
"waye wannan sumayya?".
"Aryaan menayi maka?meyasa ka tsaneni meyasa baka son ganin farin cikina *MENE AIBUNA* a wajenka ka fad'amin laifin da nayi maka?" cikin kuka nake maganar muryata a sark'e...
Shima ransa a b'ace ya fara magana "dama iskanci kika zo yi a london ba karatu ba,dama ku 'ya'yan talakawa haka kuke baku iya samun guri ba sai kun nuna tsiyarku banza maci amana, dama nazo in miki warning ne akan ki fita a harkar 'yan gidanmu,kinje kin fad'awa Asrar k'arya ko?yazo yana gaya min bak'ar magana son ranshi,magana tana son komawa kunnen momma,to wlh in kika yi wasa sai kinyi nadamar da baki tab'a yi ba,kink'i zama dani na hak'ura nayi aure kuma kinason kashe min aure sannan kina neman rabani da mahaifana da 'yan uwana,wlh ki fita a harkata in ba haka ba zan shayar dake ruwan mamaki in k...................."
"ya isa haka malam,zaka iya fita"
"idan nak'i fa"
"yanzu in saka security su fitar min da kai "
da ido na bisa hawaye na bin kuncina ta ko ina,
da Aryaan yaga da gaske wannan mutumin zai iya sawa a ci masa mutunci sai ya fita yana fad'in "idan kunne yaji jiki ya tsira ya zan koma nigeria kuma in sanarwa da momma da sauran 'yan uwana har maza kike kawowa gidanki" yana gama fad'a ya ja k'ofar da k'arfi,nayi saurin juyawa da niyyar in bisa,mutumin yayi saurin tare ni da hannu,idanuna duk sun firfito tsabar tsoro na kalleshi muryata na rawa nace "dan Allah ka barni inje zai ruguzamin rayuwa zai k'ara muzanta ni a gurin mutanen da har yanzu suke ganin na cucesu"
"babu abinda zai iya ki nutsu"
Da gudu na k'arasa kan kujera na kwanta na fara dirzar kuka ina fad'in Arish ya yafemin....
ya tsaya yana kallona nasha kukana kamar mahaukaciya nayi na gama,
na tashi tsaye na kalleshi
"me kakeyi a gidana ka fita"
na fad'a cikin tsawa kamar mai iskokai.
Ya gyara tsayuwa tare da hard'e hannunshi a baya
"hmmmmm amma fa nayi mamaki sosai,dan a fuska kamar bazaki iya abinda akace kinyi ba,shin mene ribarki idan kin raba 'yan uwa?"
zaro idanu nayi cike da mamakin kalmarsa wasu zafafan hawaye ne ya sake kwararowa daga cikin idona.
Shi kuwa guri ya samu ya zauna sannan ya d'auki littafin addu'an ya fara kalla yana magana
"gaskiya ki daina pls Sumy,kinga a ido kamar baza kiyi ba"
Cikin kuka nace "babu wanda yake sona a duniya babu mai sona sai ummana,na shiga uku"
da gudu na shige bedroom na barshi a tsaye a gun.
Yafi minti biyar a tsaye sannan ya fita ya jawo min k'ofar.
*******************
Yau saura kwana biyu mu fara lectures,dad'i nakeji sosai saboda na gaji da zaman kad'aici..
Bayan nayi wanka naci abinci kawai na kwanta a kan gado na janyo hutunan Arish ina kallo,wasu zafafan hawaye suka ziraro daga k'wayar idona,nayi saurin tashi zaune na nufi falo dan in kunna kallo kona kawar da damuwata.
A kwance na ganshi hannunsa rik'e da remote yana kallo a tv,gabana ya fad'i nasihar umma ta dawo min a rai.
_Sumayya sai kinyi a hankali kuma kin jajirce,domin samari acan har zuwa gidanki zasuyi su nemi lalataki bawai sai kin gayyatosu ba,ki dage da addua da kuma neman tsari daga sharrin duk wani wanda zai cutar dake_...
"ya dai! naga kamar mamaki k'unshe a fuskarki?"
_tayaya ya shigo gidana bayan a kulle yake?lamarinshi ya fara bani tsoro_
"calm down sumy ba wani abu nazo yi ba kawai naga banyi miki introducing kaina ba kuma kema bakiyi min naki ba"
Da hannuna na nuna masa k'ofa tare da fad'in "fitar min a gida kafin ka wulak'anta"
Murmushi sosai yayi kafin ya mayar min da amsa "ban tab'a wulak'anta ba kuma bazan tab'a ba,kuma dole ki saurareni"
ya taso daga kan kujerar ya matso inda nake ya k'ura min ido,
sai na lura ashe babu hijab ko gyale a jikina,da yake d'an kwalin kaina babba ne sai na ware na yafoshi a jikina.
Ya sake yin dariya sannan yace "babu macen da ban sani ba, ki fita iga yadda mata ke yawo kamar tsirara baka banbance religion bare tribe, 'yammata da kansu suke kawo kansu gurina dan haka ki daina b'oye jikinki idan naga dama babu abinda zai hanani yin amfani dake"
Bugun zuciyata ya k'aru na kalleshi hawaye na bin kuncina muryata na rawa nace "dan Allah kayi hak'uri ni matar aure ce pls karka zubda min mutuncina"
Nan ma murmushi ya sakeyi sannan yace "Meyasa lokacin da kikazo gidannan ba'a gaya miki waye ni ba?meyasa basu fad'a miki waye *Fu'ad* ba?hmmm kije ki tambayi securities d'in gidannan waye ni su sanar miki dan ki daina fad'amin magana son ranki wlh xan iya k'ask'antar dake"
ya k'arasa maganar cikin shouting.
"babu ruwana da sanin ko kai waye,ni dai ka fita a gidana kuma ka daina zuwa tunda bakaso ina fad'a maka magana dan Allah ka daina zuwa kar a fara zargina" na k'arasa maganar cikin matsanancin kuka.
Ya matso daf dani yana smiling wanda na kasa gane ko na menene
"dole inzo gidannan ko dan inga hawayen baby tunda naga kuka baya maki wahala ko"
ya mik'o min handkerchief na tsaya kawai ina masa kallon mamaki yayinda wasu hawayen ke zubowa a fuskana..
"ko na goge miki da kaina?"
da sauri na girgiza kai alamar a'a.
"oyaaa k'arb'i ki share hawayenki kinji"
hannuna na shaking na mik'a zan karb'a kawai mukaji an turo k'ofa.
Dukanmu idonmu ya koma gurin,hafsat ce ta shigo tana smiling amma kuma tana ganinmu sai naga fuskarta ta sauya daga fara'a zuwa b'acin rai...
Kallonta kawai nake,wani three quarter ne blue a jikinta sai riga body hug fara tas,kanta sanye da bandana blue, ta watso kalabar dake kanta a gefe da gefen kafad'arta....
na d'auke kaina daga kallonta saboda yadda naga tayi dressing d'in banji dad'i ba maganar fu'ad ta tabbata tun kafin na bar gidan naga example.
"yawwa Hafsat pls ki rarrashi frnd d'inki zanje office karna makara" ya k'arasa maganar tare da lek'amin handkerchief d'in a fuska sannan ya fice da sauri...
Yana fita hafsat ta bi bayansa,ni kuma na samu kujera na zauna tare da zabga uban tagumi,
_meke neman faruwa dani?anan d'inma ban tsira ba?wannan wace irin rayuwa ce._
*ku biyoni fans📝*
_Sadeey S✍_
[9/24, 9:26 AM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_written by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluvv & Munay```
6⃣7⃣↗6⃣8⃣
**********************
Tare suka jero da ita zuwa falo,ta durk'usa tayi ma haj karima da momma sallama sukayi mata godia.
Zahra dake gefensu kallon jindad'i take kasancewar yadda gidansu ya samu zaman lafiya babu kishi babu fad'a,yanzu kuwa gidan nasu abin sha'awa ne ga kowa.
A farfajiyar gidan *Ashaq* ya tsaya ya had'e hannunshi tare da fad'in "mun gode Aunty ilham Allah ya saka da alkhairi nd my regards to my future wife Ayrah"
Murmushi tayi tare da fad'in "zataji insha Allah,am..........Ashaq ku k'ara kula dashi sosai tunda kunga ya d'an fara samun sauk'i gobe insha Allah k'arfe 10am zanzo"
"babu damuwa Aunty"
ta bud'e murfin motarta kenan taga shigowar motar Asrar dan haka ta tsaya tana murmushi tun kafin suyi parking...
Yana fitowa ya k'ara had'e rai ya kalli Asiya da Ashaz yace "ga waccan makirar ta zo ni fa haushin ta nake ji"
Asiya tace "ni kuma inajin dad'i saboda har yaya Arish ya fara samun lafiya a Sanadin kulawarta".
Jerawa sukayi zuwa inda take tsaye ita da Ashaq....
"a'a Dr ashe kinzo"
Ashaz yayi maganar babu yabo ba fallasa
"wallahi kuwa gashi har inason tafiya"
"sai yaushe kenan?ya jikin yayan namu?"
Asiya ta tambaya...
"da sauki k'anwata"ta fad'a tana murmushi,Asrar kuwa ya k'ara had'e ranshi,ta lura da hakan amma bata nuna masa ba.
Sai da motarta ta fita sannan yaja dogon tsaki,Ashaz ya kalleshi yace "sai hak'uri Asrar nima wallahi haushinta nake ji amma babu yadda zamuyi"
Ashaq ya kallesu yayi tsaki
"wannan matar fa tana k'ok'ari yayar budurwata ce,daga na fad'awa Ayrah halin ta yaya Arish ke ciki na bata labarin abinda ya faru ta tausaya mana sannan tace yaya ilham ma akan fannin k'wak'walwa tayi masters kuma bata dad'e da dawowa daga karatun ba a india,taje ta sanar mata ita kuma tace zata zo ta dubashi tazo kuma taga ya mata tace tana sonshi,ku duba irin kukan da tasha wanda har tana cewa ita a aura mata shi a haka,Cikin wata biyar kalli yadda yaya Arish ya fara samun sauk'i kamar bashi ba,dan tace tana sonshi so what?ita Sumayyan kun manta irin cin amanar da tayi?ku baku isa ku hana abinda Allah ya k'addara ba,kuma tunda momma da daddy sun amince ku baku isa ku hana ba,mararsa godiya kawai"
yana gama fad'a ya juya zai shige gida Asrar yace "haka ne bazamu hana ba kuma a sannu zaku gane gaskiya"
Ran Asrar ya b'aci sosai,ranar haka ya yini yana tunani,ya kasa jurewa dan haka ya nufi d'akin momma da la'asar lik'is,a zaune ya sameta kan dadduma tana lazumi da alama tun da tayi sallar la'asar bata bar gurin ba.
Gefenta ya zauna ya jira ta gama sannan ya gyara murya ya fara magana "momma dan Allah inason ki binciki wannan al'amari wallahi Sumayya bata da laifin komai bata aikata abinda kuke tunanin ta aikata ba ta tafi karatu dan nemowa yaya Arish maganin ciwonshi me kuke tunani idan ta dawo kuka kasa fahimtarta?"
"Asrar tun ranar da Sumayya ta baka labari na fara bincike hatta mak'obciyarta na kira amma still abu d'aya ne yanda Aryaan ya fad'a gaskiya ne,dan mak'obciyarta ta sanar min cewa lokacin da Aryaan baya kusantarta ita ta rik'a bata shawara kan yadda zatayi ta jawo hankalinshi,laifi dai mun riga munyi Allah ya yafe mana,amma nayi alk'awarin Arish na samun lafiya zan aura masa ilham saboda nayi bincike akanta tana da nutsuwa kamar yadda sumayya ke da ita,tabbas munyi rashin Sumayya mace mai kawaici da zurfin ciki" ta k'arasa maganar tana mai zubda hawaye....
"momma shekarar Sumayya uku a london tana can tana yiwa yaya karatu dan ta warkar dashi momma ku tausaya mata"
Shima ya fad'a yana kuka...
Ta dafa kanshi tace "Asrar karatunta zai amfani wasu ba sai shi ba, tunda bazamu bar Arish haka ba muce sai ta yi shekara 7 ta dawo sannan ta sama masa lafiya,lafiya daga Allah take dan haka idan ilham ce sanadin samun sauk'inshi babu yadda zamuyi in kuma sumayyace shima babu yadda zamuyi"
Haka momma tayi ta tausasa shi har dai ya hak'ura amma dai bai yarda da maganar Rabi'atu ba.
Washe gari kuwa kamar yadda ilham ta fad'a k'arfe goma ta iso gidan duk kan 'yan gidan suna kan dining suna breakfast,amma babu Asrar,
Abin ya bata sha'awa har a zuciyarta ta furta _Allah sarki my man( sunan da take fad'awa Arish) Allah ya baka lafiya kaima a dama da kai_
'Karasawa tayi ta gaida su,sannan ta dubi Zahra da ta b'ata rai dan itama ta tsaneta....
Murmushi ilham tayi a zuciyarta tace _gaskiya wannan Sumayyar ta ciri tuta a gun Zahra da Asrar dan nagane kishi suke tayata tun kafin ta ganni na ganta_...
"Idonshi biyu ma,amma dai yau baza'ayi masa allura ba ko?"
daddy yayi maganar
"za'ayi amma bazata sakashi bacci ba,ai yanxu ya shiga stage na biyu lafiya ta fara samuwa"
"Allah bashi lafiya shekararshi hud'u har da 'yan watanni a kwance babu lafiya,babu asibitin da bamuje ba a cikin nigeria da kewaye amma da yake Allah ya k'addara kece sanadin fara samun sauk'inshi gashi nan yana warwarewa Allah ya miki albarka" momma ta fad'a..
"Amin momma" ta amsa cikin jindad'i...
"ki shiga yana ciki,Asrar ma na can yana bashi breakfast"haj karima ta fad'a
"okay" ta fad'a tare da ficewa zuwa part d'in Arish..
Tana fita Zahra taja dogon tsaki,kowa ya juyo ya kalleta ta sadda kai k'asa babu wanda yace mata uffan.
Da sallama ta tura k'ofar ta shiga,Asrar na zaune gefen gadon yana bashi chips da ruwan tea yana kurb'a a hankali
"my man jiki ya fara warwarewa" ta fad'a lokacin data zauna gefen gadon ta ajje jaka,sai jin k'arar fashewar mug tayi,da sauri ta juyo bata ankara ba taji ya shak'e wuyanta yace "kece Sumayya ko"
Asrar kanshi abin ya bashi mamaki da tsoro dan rabonda yayi wannan abin har sun manta tun farkon zuwanta daya rik'a yi mata amma ya daina sanadin magunguna na hausa da turanci tare da addu'oin da Asrar ke masa...
Kuka ta fashe dashi,yayinda Asrar ya fara addu'oinshi a fili,Sai kuma ya saketa ya zube k'asa yana fad'in "Sumayya kin cuceni kin cuceni" yana ta fad'a yana kuka
Ita kuma sarkin kuka ta cigaba da kuka ta janyo allurar tayi masa..
ta kalli Asrar tace "d'aurashi kan gadon na saka masa drip"
Da k'yar ya d'orashi,suka saka drip yanata fizgewa dole tasa ta zuba allurar bacci a cikin drip d'in,ko minti biyar ba'ayi ba ya samu bacci.
Tana tsaye jikin gadon shi kuma Asrar yana zaune ya rik'e hannunshi dan karya goce...
Ilham ta girgiza kai tace "tabbas Sumayya ta cuceka my man"
"Sumayya bata cuceshi ba,kuma bazata tab'a ba, duk duniya babu wanda zai yi masa son da Sumayya tayi masa dan tun yana haukan k'arya ta fara sonshi ta soshi son da babu wanda zaiyi masa irinshi kuma bata cuceshi ba kada ki sake fad'in haka"
Ta juya dan ganin mai yin maganar,Zahra ce ta shigo tana maganar,jikinta sanye da hijab da alama unguwa zataje
Murmushi Ilham tayi da niyyar tayi magana Asrar ya katseta da fad'in "kina son cusa masa tsanarta to baki isa ba.
"yaya zan tafi skul ka kular mana da yaya Arish please"
Ta sake dallawa ilham harara sannan ta fice,har ilham ta bar gidan bata sake fad'in magana maka manciyarta ba.
*ENGLAND*
Tafi minti uku a tsaye k'ofar plat d'in abin ya fara zarce misali a gurinta.
_meya mayar min gidane?da kullum in na fita sai dai in dawo in tarar dashi a ciki?_
Ganin babu wanda zai bata amsa ne ya sakata shiga cikin gidan kai tsaye.
Abinda ya bata mamaki shine,parlor babu kowa jikinta kawai ya bata cewar yana bedroom ko kitchen,
Kai tsaye ta nufi bedroom d'inta,yana kwance a kan gado, ba ganinshi bane ya bata tsoro illa abinda ta gani a gefensa.
Gaba d'aya books d'in hannunta ta saki suka zube a k'asa,itama binsu tayi zuwa k'asa tayi zaman dirshan jikinta ya kasa daina karkarwa.
0 comments:
Post a Comment