Tunani babu wanda bai zo min ba a lokacin,ina nan zaune kan kujera naji shigowar Hafsat.
Tsayawa tayi a gabana ba tare da tace min komai ba,nima kuma nayi shiru ban mata magana ba,dan tashin hankalin dake gabana yafi k'arfin na tsaya nayi mata magana ma.
"meke damunki Sumayya?kinko san waye wannan mutumin?"
na d'ago idona da ya gama rinewa ya koma jajir tsabar kuka.
"bana son sanin ko shi waye".
Tab'e baki tayi sannan ta zauna a kujerar dake facing d'ina
"Wallahi kibi a hankali in kinason tsira da mutuncinki Sumayya"
Na sake kallonta cikin rashin fahimtar abinda take nufi nace "ban gane ba?"
"wannan mutumin da kike gani sunanshi *fu'ad* kuma wannan estate d'in nashi ne,da hayar gidan za'a d'aukar mana amma da yaji cewa mu 'yan nigeria ne sai yace ya mallaka mana a matsayin gudunmawar shi muyi karatunmu na shekara 7 a ciki,kuma flat d'inshi na jikin naki shine duk ya zuba miki kayan buk'ata kafin kizo tun kafin ma ya san koke wacece,shin meyasa bazaki masa godiya ba sai dai ki wulak'antashi?"
Kallonta kawai nake da ido na kasa furta ko kalma d'aya,babu abinda yake bani mamaki irin yadda na zama a yanxu,a zuciyata kuwa na furta.....
_wai ni Sumayyar da nake rashin kunya bana ganin kowa da gashi bana shakkar mutum amma yau nice na zama saliha?gaskiya aure da zaman gidansu Arish ya saka min nutsuwa_.
"Sumayya ko kin san cewa Fu'ad Saurayine amma mai kud'i mara misaltuwa?tun yana d'an shekara 4 aka kawoshi London sanadin rasuwar mamanshi,babanshi ya kawoshi nan dan baya son yasha wuya bare ya wulak'anta,anan yayi duk wani karatu da kika sani har ya samu damar aiki anan,shima haifaffan nigeria haifaffen zazzau ne amma fiye da rabin rayuwarshi yana yinta a nan England shiyasa ma zakiji hausarshi bata fita sosai tunda baya zuwa sai ta kama kuma fa har yanxu baiyi aure ba"
Na dafe kaina da hannuna wasu hawayen suka samu damar zobowa,nasa hannuna ina gogewa tare da fad'in
"Hafsat ni wannan ba damuwata bace,Allah ya jik'anta amma ni babu abinda ya shafeni da rayuwarshi,gida shi yaga damar badawa ba tirsasa akayi ba".
Ta kalleni cikin jin haushina ji take kamar tayi min duka saboda haushi..
"haba Sumayya wannan wace irin magana ce haka?kin san kuwa yadda ya damu dake ya damu da damuwarki amma ke kina nuna halin ko in kula,yanxu dana fita magana nake son yi masa amma bai tsaya saurarata ba sai kawai cewa yayi inje in rarrasheki dan yaga kamar kina cikin damuwa,amma ke kalli abinda kike fad'a".
Na kalleta cikin kuka nace "dama na san ba wanda ke k'aunata kowa yana zaune da nine kawai,amma babu wanda zai rarrasheni yaji damuwata sai dai ya k'ara k'untata min"
Na tashi na nufi bedroom d'ina ina kukan da ba zan iya tantance damuwar dana shiga ba....
ina jiyota tana ta fad'a tana cewa "dubeki fa ke ba fara ba wata bak'a dake na san kyau kam nima ina dashi kuma gani fara sol ga gashi ga hanci amma ke da kike da kyau sai kika kasance bak'a meye ma abin so a bak'ar mace?me kike dashi wanda bani,aikin banza kawai dan ana rarrashinki shine zaki rik'a rainawa mutane hankali"
ban san dalilin wannan maganganun ba,ni dai banbi ta kanta ba kawai na fad'a kan gado ina kukan kunci,gentle ya sake fad'omin a rai na cigaba da kukan zuci ina mai tausayin irin rayuwar dana shiga.
*************************
Cikin Zumud'i na fito daga wanka ina tsane jikina da towel,na kalli madubi..
tabbas na rame sosai nayi kuma haske kamar wadda tayi shekara tana cuta kodan nayi fiye da shekara a cikin k'unci da damuwa...
A gurguje na shafa cream a jikina,na d'an shafa powder sai lining da nayi da eye liner a idona,na d'an goga lip gloss a bakina,banyi makeup ba tunda na san ni matar aure ce...
wardrobe na bud'e na kalli 'yan kayana,sannan na jayo wani swiss lace wanda malam ya d'inka min lokacin da zan taho, purple ne da touch d'in brown,na janyo dogon hijab d'ina mai hannu shima brown color ne na saka....
Na d'auki 'yar handbag d'ina na zuba kud'in da zan sayi k'aramar waya idan na dawo,ya feshe jikina da turare (secret)bashi da k'arfi amma yana da sanyin k'amshi,ban tsaya bi ta kan breakfast ba kawai na fice.
Ta Window ya hango ni,wanda dama tun d'azu yana tsaye yana jiran fitowa ta.
_wowww black is beauty_
ya fad'a a ranshi,bai saki labulen ba har sai dana bar gurin,shima ya cigaba da shirinsa...
Ina tsaye bakin titi ina jiran taxi,ba kamar nigeria bane su titinsu kamar ba titi ba,babu hayaniya babu cikowa..
Ina tsaye kawai naga mota ya tsaya a gabana,Hafsat ce a gefen driver,na d'an kauda kaina saboda maganar da ta fad'a min jiya banji dad'i ba..
"k'awata shigo mu tafi karmu makara"
Da banyi niyar shiga ba amma danaji ta ambaci makara sai nayi saurin bud'e seat d'in baya..
wasu frnds d'inta ne su biyu a zaune a gidan baya duk kansu sunyi indecent dress.
Hafsat ta d'an juyo ta kallesu tace "guys ga flower Fu'ad fa"
suka kalleni suka yi dariya,raina ya b'aci na k'yalesu bance komai ba,ta k'ara juyowa ta kalleni tace "Sumy ga guy d'ina fa baku gaisa ba"
k'awayenta suka k'ara saka dariya...
"Hafsy wai ina kika samo wannan?baki fad'a mata anan ba'a saka hijab ba gskya ni kam bazan jera da ita ba dan kuwa duk inda muka je sai anyi mana dariya"
Hafsat tayi dariya tace "tare muka zo da ita fa,tana cikinmu bagu ganta ba a airport lokacin da ake mana screening?"
"cab wa ma ya lura da zamanta" suka saka dariya,d'ayar kuwa cewa tayi
"Ni kam naji dad'i domin yau zamu zama celebrities tunda mun taho da Auntyn hijab"
Suka sake saka dariya har da hafsat d'in,hakanne ya bani damar cewa dama ta janyoni ne dan ta cimin mutunci.
Mun isa skul d'in mukaje muka gama komai ko wanne aka bashi fannin daya dace dashi,cikin sa'a aka kaini fannin matsatsoli da abubuwan dake sawa k'wak'walwa ta tab'u,anan muka rabu da su hafsat kowa yayi nashi wurin,Zuby show wata k'awarta wadda tana d'aya daga cikin matan da suka yimin dariya a mota itama department d'inmu d'aya amma ban bari mun jera da ita ba,abin mamaki babu wanda ya damu da dressing d'in jikina sai dai duk inda nayi ana bina da ido,dan akwai wanda in ya wuce sai ya juyo....
*04:00pm*
mun fito daga lecture,yunwa gaba d'aya ta dameni har inajin kamar zan fad'i..
Haka na taho da sauri da niyyar in shiga taxi in koma gida,bana ganin gabana sai ji nayi munyi karo,wani irin hajijiya naji a hankali na d'ago kai na kalleta da niyyar in bata hak'uri kawai sai ji nayi ta wanke fuskata da mari,a gigice na kalleta hafsat na gefenta ina shirin yin magana naji ta k'ara wankeni da mari a d'ayan kuncina,gaba d'aya mutanen take gurin aka hau ihu har da masu snapping a waya....
Ji nayi gaba d'aya an matsar dani gefe tare da wanka mata mari sau uku a lokaci d'aya,na d'ago kai na kalleshi...
Fu'ad ne ya mareta sannan yaja hannunta da k'arfi ya nufi can bayan block,ban k'ara sanin meke faruwa ba dan gaba d'aya hankalina ya gushe.
A hankali na bud'e idona na kalli inda nake,bedroom ne wanda na tabbatar ba nawa bane,na tab'a gefen fuskata naji shi a kumbure ga yunwa na cina.
Da k'ar na sauka daga kan gadon kafin in tashi tsaye naji wata hajijiyar,na d'an kishingid'a ina hawaye.
ji nayi an turo k'ofar,nayi saurin d'ago idona na kalleshi....
Babu tantama a gidanshi nake,
"meya kawoni nan?"
murmushi yayi sannan ya zauna kusa dani,na d'an ja gefe,ya sakeyin dariya sannan ya tashi daga kan gadon ya koma kan sofa ya zauna..
"me kika masu ne?"
"pls ka k'yaleni ka daina shiga rayuwata"
"dole sai nasan abinda kika yi masu da har basa son farin cikinki harda k'awarki hafsat"
Na kalleshi cikin jin azabar yunwa nace "Fu'ad"
shima da sauri ya kalleni dan yau ce rana ta farko daya ji na ambaci sunanshi,yana shirin yin magana nace "yunwa nake ji wlh na kusa mutuwa"
Da saurin ya tashi ya fita,ni kuma na lumshe idona ina fitar da numfashi.
Da cup da plate ya shigo,
"tashi ga abinci kici"
,na fara kurb'ar ruwan tea a hankali,shi kuma yana rik'e da plate d'in chips,nasha kusan rabi kawai naji amai ya taho min da sauri na ajje cup d'in na nufi toilet da sauri,aikuwa nayi ta amai tun inayin aman shayin har ya zama saura ruwa,sai da k'yar ya tsaya,na kuskure bakina na juya zan fita na ganshi tsaye a k'ofar toilet hannunsa sark'e a k'irji...
"Sannu Sumy"
kai kawai na gyad'a hawaye na zuba a idona.
ina fita na d'auki hijab d'ina na zura sannan na fita,baice komai ba sai bayana da yabi...
A k'ofar flat d'inmu na ga Hafsat da k'awar tata a tsaye,da alama jiran fitowarmu sukeyi,
kallonta kawai nake ina ganin kamar a mafarkine abinda tayi min,nazo zan bud'e flat d'ina tayi saurin rik'e hannuna "Sumayya pls am sorry,wlh nayi regretting. abinda mukayi miki"
na d'an janye hannuna daga nata nace "babu komai ya wuce"
"to pls ki bawa Fu'ad hak'uri yace wlh bazai bud'e mana flat d'inmu ba sai dai mu bar estate d'innan mu koma wani ko kuma otel"
na juya na kalleshi nace "kayi hak'uri pls"
ya d'an mak'ale kafad'a kamar yaro alamar baxai hak'ura ba...
Nayi ajiyar zuciya nace "kayi hak'uri for my sake"
abin mamaki kawai naji yace "babu damuwa amma idan suka k'ara wlh zasu bar min gida ke har Oxford sai sun bari"
"ni dai na yafe masu shikenan komai ya wuce".
godiya suka yi masa suka wuce hafsat tace min zata zo ta k'ara bani hak'uri ban ce mata komai ba na shige flat d'ina.
Haka rayuwata a England ta cigaba da tafiya kullum cikin b'acin rai nake saboda Fu'ad ya takurawa rayuwata,
karatuna kam ina ganewa sosai a wata biyar da nayi na san abubuwa da yawa wanda har nake tunanin karatun ya isheni haka,a yadda nayi tunanin karatun shekara bakwai ne ashe ma na shekara biyar ne gashi tun a 'yan watanni na fara fuskantar abubuwa da yawa.
Fu'ad kam ya jawo min bak'in jini a gurin 'yan estate d'inmu both maza da mata duk namijin daya zo gurina koda da friendship ne sai ya wulak'anta shi,mata kuwa babu wacce ta isa ta ci min mutunci domin kamar ma bibiyata yakeyi da anyimin abu sai dai kawai na ganshi a gurin...
Gidana kuwa kamar nashi dan wani lokacin dana dawo daga lectures sai dai na tarar dashi a parlor yana kallo ko karatu ko ciye ciye,haka zamuyi ta fad'a dashi ga bashi da zuciya sam kullun cikin kuka nake da nadamar rayuwa amma a haka na jajirce nake karatu kuma ina fahimta sosai.
_written by_
_Sadeey S✍_
_&_
_Nafsal_
[9/24, 9:26 AM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_written by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
6⃣9⃣↗7⃣0⃣
Kallonta kawai yake cike da mamaki tabbas yanayinta ya nuna cewa duk abinda ya karanta a cikin diary d'in gaskiya ne.
'Debo pictures d'in yayi had'i da diary d'in,ya sakko daga kan gadon yazo daf da ita sannan ya watsasu a jikinta,ta d'ago idanunta take zubda hawaye ta kalleshi,ranshi a b'ace yake tunda take bata tab'a ganin b'acin ransa ba sai yau,dan kullun cikin smiling yake koda ta fad'a masa bak'ar magana.
A hankali yake tafiya kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki,yana kaiwa k'ofar bedroom d'in ya juyo ya kalleta sannan yaja k'ofar da k'arfi ya fita.
Da sauri ta mik'e tsaye zuciyarta na zafi,ji takeyi bazata iya barinsa ya fita ba ba tare data fad'a masa gaskiyar al'amarin ba,dan tana tsoron idon dazai kalleta dashi,ta san zai rik'a mata kallon 'yar iska maci amana kuma makira.
A falo tayi saurin shan gabansa,cikin kuka mai k'una ta fara fad'in...
"wlh ba haka bane Fu'ad,duk abinda ka gani ba gaskiya bane shi kanshi Arish ya rubutane ba tare da yayi bincike ya gano gaskiya ba,dan Allah kar kay..........................."
Hannu ya d'aga mata alamar ta tsaya da maganar da takeyi,shiru kawai tayi tana shashshek'ar kuka,tsaki kawai yaja sannan ya fita ya barta anan tsaye.
Ta bishi da ido cike da mamakin irin fushin da yayi yau..
"ka cuceni Aryaan kayi min tabon da kowa ya ganni sai ya gujeni"
hannunta duka biyun ta saka tu rufe fuskarta tana kuka mai tsanani...
Ranar haka ta yini a parlour tana kuka,sai kusan k'arfe d'aya da rabi na dare sannan ta lallab'a ta shiga bedroom d'inta...
'Yar k'aramar wayarta ta janyo ta kunna da niyyar kiran Nasiba,
da k'yar ta lalubo number dan hasken wayarma k'ara saka mata wani zugin yake,tayi dialing number har sau biyu amma switched off dan haka ta hak'ura ta janyo pillow ta rungume tana kuka.
Yadda taga rana haka taga dare,sallahr asuba ma sai da rarrafe taje toilet tayi alwallah sallah kuwa a zaune tayi ta.
Kwananta hud'u tana fama da zazzab'i mai zafi wanda ko lectures bata samu taje ba,babu wanda ya lek'ota dama shine ke nacin zuwa amma wannan karin yak'i shigowa lallai yaji zafin abinda ya karanta,
ita kanta taji kewarshi duk da bata son zuwan da yakeyi amma sai da tayi kewa daya daina zuwa.
Yau kam abin yayi worst,ta kasa koda bud'e idanunta,karkarwa take sosai a cikin bargo,bakinta yak'i kasa daina adduoin neman gafarar Allah ta san sai dai azo aga gawarta ta rub'e,babu wanda zaizo yaga lafiyarta babu mai tausayinta kowa ya gujeta.
Ranar kuwa sallah ma da k'yar tayita a zuciyarta dan ko tashi ta kasayi....
************************
Da yamma lik'is ya shigo plat d'inta dan ya dubo ko lafiya dan yaje skul d'in ance kwananta hud'u bata zo ba.
Yana shigowa parlourn yaga d'ankwalinta a k'asa wanda idan bazai manta ba ranar da ya karanta diary d'in ta fito ta tarar dashi da d'ankwalin rik'e a hannunta ya nuna cewar kwananta hud'u rabonda ta fito falo dan yadda ya barshi haka ya dawo ya tarar da komai.
Da sauri ya nufi bedroom d'inta,ya hangota can tsakiyar gado jikinta ruf a rufe da blanket.
Yayi saurin k'arasawa gurin ya yace blanket d'in,hannunta na kan goshinta hawayen fuskarta duk ya bushe,ya d'an tab'ata yaji bata motsa ba jikinta kam kamar garwashin wuta,ya rik'a jijjigata amma babu alamar ko motsi a tattare da ita.
A gigice ya d'auketa yayi waje,baima tsaya neman taimakon wata a cikin plat d'in ba,ya sawa motarshi key.
*8 hours later*
A hankali take bud'e idonta,tana jin ciwon kai kad'an,har ta bud'e idon nata duka amma bata shaida inda take ba,kallon gadon tayi da d'akin,a hankali ta tashi zaune ta jingina da bango...
_Asibiti!to waye ya kawoni?waye yaje yaga halin danake ciki ya kawoni nan_.....
Ta dad'e a zaune tana ta sak'e2.
Shigowarshi ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba,tare da likita suka shigo,ya duba ta sannan ya fara yi masa bayanin yadda zata yi amfani da maganin...
Yadda taji turancin Fu'ad na fita _Fluently_ abin ba k'aramin burgeta yayi ba kanajin turancin nashi kasan baiyi rayuwar 9ja ba,tunda daman hausanshi ma a sark'e take.
Sai da ya tsaya a wani shopping mall yayi siyayya,ita dai kam bata bishi ciki ba,ta zama kurmar k'arfi da yaji dan tana ganin fuskarshi babu yabo babu fallasa shiyasa tasan baya cikin mood d'insa dan kuwa shi mutum ne mai yawan fara'a.
Yanayin parking yaga hafsat da zubaida,da saurinsu suka k'araso gurin,cikin damuwa hafsat ta dafa shoulder d'in Sumayya tace "k'awata lafiya?munje plat d'inki bakya nan meya sameki?wlh ni ban san baki da lafiya ba sai da zuby tace yau kusan 1wk bakiyi attending lectures ba"
"Hafsat kamata yayi kina zuwa duba ta time 2 time"
wani farin cikine ya lullub'e ta jin yau Fu'ad ya mata nagana,dan rabonda yayi mata kalma mai dad'i anfi shekara dan shi bai iya fushi ba.
"insha Allah zan kula da ita yadda ya kamata"
"okay mungode"
"never mind fu'ad"
"I have to!yanxu ina zakuje?"
"kawai zamu d'an je shak'atawa,amma mun fasa bara mu shiga da Sumayyar"
"no!ai yanxu inanan kuje kawai ba damuwa"
"okay Allah ya k'ara sauk'i"
"amin"
Ita kam bata ce komai ba sai dai binsu da ido da take yi.
Cikin kulawar Fu'ad da Hafsat ta samu ta warware sosai ta samu sauk'i amma tafi 2wks babu zuwa ko ina duk lectures ya wuce ta.
***********
Cikin sauri take shiri dan yau tana son shiga skul,ta gama shirinta tsab tana fitowa falo ta ganshi a tsaye.
Gabanta yayi mummunar fad'uwa duk da dai ranshi ba a had'e yake ba.
Shima kallonta yake yana karantar yanayin fuskarta,ya hard'e hannunshi a baya.
Cikin tsananin tsoro da in-ina tace "zanje lecture ne?"
ya d'anyi murmushi yace "ki bari sai gobe mana"
"a'a yau gaskiya saboda na dad'e banje ba"
Yayi murmushi ya juya yace "okay baba bismillan ku"
abin ya bata mamaki wane baba yake kirawo mata,bata gama shan mamaki ba sai da taga shigowar malam da ummanta.
Da gudu ta ruga ta rungume umma cikin murna mai had'e da kuka,
"umma yaushe kuka zo?"
"yanxunnan Sumayya"
"ya karatun"
cikin jindad'i tace "Alhamdulillah"
Juyawa tayi tana kallon Fu'ad a zuciyarta tana fad'in wane irin kulawa ce wannan?
"bara nayo masu takeaway abinda zasuci"
Har ya fita tayi saurin binshi mota ya tada kenan ya hangota,yayi saurin goge hawayen idonshi kafin ta k'araso
"Fu'ad ban san da wane kalami zan maka godiya ba"
"kimin addua Allah ya bani ke ya mallaka min ke a matsayin matar aurena matata wadda zan rayuwa da ita har abada,Sumayya kece macen da daddyna kemin fatan aura ya dad'e yana min addu'ar samunki amma meyasa na sameki a matsayin matar aure?meyasa bakizo min a matsayin budurwa ko bazawara ba?"
"k'addara Fu'ad ka yarda da hakan"
"ban san k'addara ba kuma bazan iya jurar k'addara ba"
Kallonshi kawai take ta kasa tantance irin damuwar da take ciki bare ta samu damar fassara maganar Fu'ad.
hunnu biyu🤝
Sadeey
&
Nafsal
[10/5, 3:21 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
*_SaNaz deeyah_*
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
7⃣1⃣↗7⃣2⃣
Ganin ta kasa magana yasa shi jan motarsa ya bar cikin estate d'in.
Jikinta a sanyaye ta koma ciki,tana ganin umma wata murna ta sake rufe ta,tayi saurin zuwa ta zauna gefenta ta d'aura hannayenta akan cinyar umma...
"umma nayi kewarku sosai,shekara uku ba wasa ba,na san su farida da Fatima duk sun girma"
"Sun girma amma ba sosai ba,duk sun koma makaranta yanxu suna Ss2 auta kuma tana nursery1"
"Allah sarki nayi kewarsu,su yaya Nasiba fa?"
"Nasiba tayi aure watan hud'u da aure,duk sunce in gaisheki suma sunyi kewarki"
"umma amma ayi bikin Nasiba a kasa gaya mini last week ma munyi waya da ita fa"
"ni nace kar a fad'a miki dan karki d'aga hankalinki"
"Allah sarki yaya Nasiba Allah sanya alkhairi"
"Amin"
"kina yin karatu dai ko?" malam yayi tambayar.
Cikin jindad'i tace "sosai ma malam,ni ji nake a yanxu haka karatu ya isheni malam na k'agu inje in sama ma Arish sauk'i da yardar Allah,yanzu nasan magungunan da zanyi amfani dasu wajen magance cutar dake damunsa,babu su a nigeria sosai duk yawanci fake zanyi ordering d'insu tun anan kafin in tafi"
Jikin malam yayi sanyi sosai saboda ya samu labarin Arish ya fara samun sauk'i.
Ya kalleta cikin nasiha yace "kiyi karatun da zaki taimakawa al'umma ba Arish kad'ai ba"
Tayi murmushi tace "insha Allahu,amma dai nafi damuwa dashi malam"
"Allah ya baku ikon gamawa lafiya,yaron nan yazo gurina nayi masa bayani akan yadda aurenki yake,Allah sarki yana da kirki kuma yayi tawakkali yace zai cigaba da tsare maki mutuncinki dan zaman nan dole sai da guardian"
Jikinta ya k'ara yin sanyi amma bata nuna masu hakan ba,sai umma ce dai taso ta gane
"ya kika yi shiru?"
"babu komai umma"
Haka suka cigaba da hira har zuwa dawowar Fu'ad,yayi masu takeaway na abinci,snacks,da drinks.
Da ido kawai ta rik'a binshi,shi ya shiga kitchen ya d'ebo plates,ya d'aura kan dining table.
Suna cin abinci suna ta hira da malam jefi2 umma na saka baki cikin maganar,Sumayya kam tayi shiru,abincin ma ci kawai take ba dan tana jindad'in sa ba.
Satin su umma d'aya a london,Fu'ad ya zagaya dasu ko ina,sunga k'asar sosai iya kacin iyawarsu.
Har yanzu Fu'ad bai samu sunyi magana da sumayya ba kasan cewar kullum tana tare da umma.
Hafsat ma tunda tazo suka gaisa shikenan ta samu gurin zuwa musamman da ta lura da Fu'ad yana gidan a koda yaushe,Umma kullum cikin nasiha take tana fad'akar dasu akan illolin zamanin nan namu,Hafsat kuwa tana tsayawa ta saurara wani lokacin ma har kuka takeyi.
Ranar da su umma suka koma kuwa Sumayya tasha kuka sosai,Hafsat na ta rarrashinta amma ta k'i dainawa har sai da tayi mai isarta.
Haka ta cigaba da karatu taa k'ara dagewa wajen fahimtar abubuwa daban2.
*****************
A falo suka zauna har shi,amma baya cewa um bare um um.
momma ta kalleshi ta share hawayen fuskarta dan rabonda Arish ya fito falo shekara hud'u kenan har da 'yan watanni,ilham ma hawaye take ganin momma na hawaye.
"yaya sannu,meya na fitowa dashi falo kuma ai saiki bari ya k'ara samun sauk'i sosai"
Zahra ta fad'a rai a b'ace.
"meyasa baki da kunya Zahra,meyasa bakya ya ba k'ok'arin ilham?ki duba ki gani wane irin miliyoyine daddy bai kashe ba amma ki duba zuwan ilham wata bakwai har ya fara samun sauk'i" Asiya tayi maganar
Zahra ta murgud'a baki ta kauda kai.
Ilham ta kalleta kawai tayi murmushi sannan tace "momma ina son zamu fita dashi saboda ya samu sauk'i sosai inason ya d'an motsa jikinsa"
"okay bara nazo na kaiku" Ashaq yayi maganar tare da mik'ewa tsaye.
"a'a ka barshi kawai zanyi driving"
"taya zamu bari ki tafi dashi bayan bamu san inda zaku ba,nifa banma yarda dake ba" Ashaz yayi maganar cikin shouting...
"toooooo yau naga ikon Allah" ilham ta fad'a.
"duk wanda ya k'ara magana sai ranshi ya b'aci,meyasa baku da kunya ne?" haj karima tayi maganar cikin fad'a sannan ta kalleta tace "ku tafi Allah ya tsare kinji,mungode da kulawarki"
Taji dad'in kalaman haj karima sosai,ta tashi ta d'au jakarta tace "Yaya Arish muje"
Tashi yayi ya bi bayanta kamar mutum mutumi.
Ta bud'e masa motar ya shiga sannan itama ta koma zata shiga driver sit
"a'a ina zaki kaishi?" Asrar yayi saurin yin maganar yana k'arasowa gun.
"zamu fitane"
"zuwa ina?"
"zuwa inda bai zama lallai ace ka sani ba"
"babu inda zaki dashi"
"wallahi saina fita dashi tunda baka da iko a kanshi wanda suke da iko sun yarda mu fita,Asrar na gane take takenku kaida Zahra kuna taya Sumayya kishi ko,wadda yanzu haka ta manta dashi bata k'aunarshi taci amanarshi yanxu ta koma outside da zama cikin jindad'i da kwanciyar hankali shi kuma ta barshi da damuwa akan me?"
"k'arya kike wallahi,kinason b'ata mata suna a gurinshi to ta Allah ba taki ba"
Shi kuma gogan tsaye motsawa,Asrar yayi saurin kamoshi "yaya muje cikin gida"
Da k'arfi ya fuzge hannunshi,Asrar ya tsaya yana masa kallon mamaki,zagawa tayi ta shige motar ta rufe sannan ta jata da gudu.
Maigadi ya bud'e masu gate suka fice,Asrar ya bisu da ido cike da mamaki.
*PSYCHIATRIC(Gidan Mahaukata)*
A k'ofar psychiatric tayi parking,suka shiga ciki,jikin wata bishiya tace ya tsaya sannan ta shiga ciki.
Bata fi minti 10 ba ta fito tare da wani ma'aikaci.
"yaya taho"
ya biyota suka jera zuwa ciki.
Gurin mahaukata mata da maza suka zagaya,wasu mahaukatan ma d'aure su ake da sark'a.....
"my man kaga wasu bama su cikin hayyacinsu suna jin inama sune kai da sunyi amfani da damarsu dan su inganta rayuwarsu"
ta cigaba da fad'in "ka samu lafiya Arish kayi amfani da damarka ka shigo cikin mutane ka cigaba da mu'amularka kowa da irin tasa jarabawar ka yadda da k'addara ka kuma manta abinda ya faru a baya dan Allah yayanah"
Kamar k'aramin yaro haka ya rik'a kuka,har suka bar psychiatric d'in yana kuka ba tare da yayi magana ba.
*ORPHANAGE(Gidan Marayu)*
Horn tayi sannan aka bud'e gate,tayi masu bayani sunzo ziyara ne,sannan ta kira shugabar gidan a waya kasancewarta
K'awar mamanta,ta kuwa bada damar a barsu su shiga.
Suna sauka ya hango wata budurwa tayi tagumi acan gefe da yaro rungume a cinyarta.
Da sauri ya k'arasa gurin ya durk'usa a gabanta cikin sanyin murya yace "kiyi hak'uri ki cire damuwa a ranki kowa da irin tashi k'addarar"
ta d'ago kai tana hawaye tace "ka gode ma Allah tun da kuka shigo nake jin dama nice ku,iyayenmu sun haifemu sun wulak'antamu,inaji a jikina inda zanga mamana zanje na tambayeta meyasa bata zubar da cikina ba tun kafin nazo duniya inda ta san bazata iya rik'eni ba wular dani zatayi dama bata bari nazo duniya ba,mufa shegune babu uwa babu uba bamu da asali"
"ki daina fad'in haka kinji,ku ba shegu bane Allah yana tare da ku"
"na san da hakan amma ka duba ka gani ko aure mukai to a wulak'ance muke a gurin dangin miji wani lokacin ma har da mijin,gashi auren mu baifiya lasting ba,dama nice kai, da iyayena a gabana da bani da wata damuwa"
"wannan ma good example ne my man" Ilham dake bayansu tayi maganar.
Ya juyo ya kalleta yayi ajiyar zuciya sannan ya kalli budurwar yace "wannan yaron fa?"
"Shima maraya ne kamar ni,tunda aka kawo shi baya yarda da kowa saini,kuma nima bana so yana shiga cikin yaran dan zasu koya masa halin banza"
"ya sunanki?"
"Sunana Sumayya"
Yayi saurin mik'ewa tsaye.
"mu bar nan"
ya cewa ilham.
"kowa guduna yake babu mai sona a duniya" yajuyo ya kalleta sannan ya dawo.
"meyasa kika ce haka?"
"saboda hakanne ma"
ya kalli yaron kan cinyarta da ke ta bacci yace "meye sunanshi?"
"khalid"
Yayi ajiyar zuciya tsowon minti biyu sannan yace "zaki bini gidanmu ki zauna da mamana?"
da sauri ta d'aga kai alamar eh.
"amma har da khalid?"
"eh har dashi,ku taso muje office d'in.
Suna cikin tafiya ne ilham ta kasa jurewa tace "amma momma bazata ji dad'i ba"
"momma na son duk abinda nake so".
Anyi cakwakiya kafin shugaba ta yarda Arish ya d'auke su dan cewa tayi tana son zama da sumayya mutum ce mai tausayi ilmi da biyayya uwa uba nutsuwa shiyasa ko anzo d'aukarta take k'in bada ita dan tana tunanin aure ne zai rabasu.
_halinsu d'aya da sumayyatah amma ita waccan akwai son zuciya da rashin imani_...
haka ya fad'a a zuciyarshi lokacin da shugaba ke lissafo halayen sumayya.
Haka Sumayya taje tayi sallama da sauran 'yan orphanage d'in da masu kula dasu ta d'ebo kayansu da takardun makarantarsu ta fito.
Jikinsa duk a sanyaye yake amma yana jindad'in yadda ilham ke kula dashi.
Tana yin parking tayi saurin fita da gudu ta shiga gidan,a falo ta tarar dasu ta rungume haj karima tace "mama wallahi Arish ya samu sauk'i kinji yadda yake magana kuwa sosai.
Da sauri suka tashi suka nufi hanyar waje cikin farin ciki.
Suna fitowa suka ganshi a tsaye shi da Sumayya da Khalid.
Momma ce ta fara isa gurinshi ta shafa fuskarshi,hawaye na zuba a idonta,shima hannu yasa yana goge mata hawaye yayinda shima nasa hawayen suka kasa daina zuba,
"Ashe zan sake jin muryarka?,shekara hud'u sai yau Allah ya baka lafiya,Allah na gode maka daka bani ikon ganin d'ana tun kafin in bar duniya"
"momma" ya fad'a tare da fashewa da kuka.
suka rungume juna suna kukan farin ciki.
'Yan uwansa duk suka zo cikin farin cikin ganin samun sauk'insa a cikin watanni kad'an.
*2 Hours Later*
Su biyar ne zaune a d'akin daddy,dashi daddy da momma sai Aryaan da Arish da haj karima.
Daddy ne yayi gyaran murya yace "to Alhamdulillahi,Allah shine abin godia daya kawo mu ranar nan,gamu gaka Arish cikin lafiyar ka"
yayi murmushi kanshi a k'asa,daddy ya cigaba da fad'in "sai ku yafi juna da kai da d'an uwanka kuskurene anyi shi kuma muna fatan duk Allah zai gafarta mana"
Arish ya d'ago kai ya kalli Aryaan sannan ya kalli daddy "daddy na yafe ma d'an uwana komai ya wuce daddy abar maganar ma dan ni ko sunan ta bana son ji"
Momma tayi dariya tace "a haka naga kaje ka d'akko wata sumayyar a gidan marayu"
"momma wlh tausaya mata nayi,danaji sunanta sumayya wlh har na tashi zan tafi sai tace kowa gudunta yake shiyasa na d'akkota amma momma na tsani sumayya bana son k'ara ganinta a rayuwa ta"
"a'a Arish babu kyau kace ka tsani mutum ba'a tsanar mutum sai dai a tsani halinsa" daddy yayi maganar cikin nasiha.
Aryaan dai yayi shiru baice komai ba,shi yanzu rashin haihuwa ne ke damunsa.
"karkaga laifinta Arish,ka dai yarda da k'addara Allah ya tsare gaba"
"hmmm zaiyi wuya na manta da wannan azzalumar na tsaneta wlh na tsaneta sosai"
Momma ce tayi saurin kawar da maganar dan gani take kamar idan anayi zai dawo masa da cutar.
"ya maganarka da ilham?"
shiru kawai yayi ya kasa cewa komai..
"Aryaan baka ce komai ba?" daddy yayi maganar
"duk abinda kace haka za'ayi daddy" ya fad'a babu yabo ba fallasa.
"okay zamuyi magana da iyayen yarinyar idan son samuna ne a had'a dana Ashaq duk ayi kuma bana son ya wuce 3 months" daddy ne ke maganar.
"okay shikenan ku tashi ku tafi"
har sun mik'e daddy yace "oh na manta Arish kana ganin yarinyar nan daka d'akko mana babu matsala?"
"daddy babu inaso ku rik'eta tamkar ku kuka haifeta dan Allah"
"insha Allahu a wannan karin zakaji dad'i dan zamu cika maka alk'awarinka,Allah ya maku albarka"
duka suka amsa da "Amin"
A b'angaren Asrar kuwa d'akinshi ya shige yana ta yawo yana juya maganar Sumayya a ranshi.
_shin ya zataji idan ta dawo ta tarar anyi bikin Arish da ilham?gaskiya ba'ayi mata adalci ba,zanje na same shi na k'ara fahimtar dashi gaskiyar al'amari_.
_*Hannu biyu🤝*_
_Sadeey_
_&_
_Nafsal_
[10/5, 3:21 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
7⃣3⃣↗7⃣4⃣
Fitowa yayi main parlour ya tambaya ina Arish,
"yana side d'inshi" Asiya ta bashi amsa.
Da sauri ya nufi side d'in ji yake kamar yayi flying dan ya k'agu ya sanarwa da Arish komai.
Ya tura k'ofar cikin sallama ya shiga,gaba d'aya hankalin Arish baya jikinshi dan haka bai ma san shigowar Asrar ba.
Ya tsaya ya kalli pix d'in Sumayya dake rik'e a hannunshi ya k'ura masu ido,wani farin ciki ya lullub'e asrar, dan haka yaji ya sake samun k'warin gwiwar yin magana.
Tafa hannuwanshi yayi Arish yayi saurin d'agowa ya kalleshi....
"lfya?yaushe ka shigo?"
"kusan minti talatin da shigowata kawai na tsaya ne ka gama kallon hoton"
Hmmmm yayi ajiyar zuciya sannan yace "Ina tunanin yadda na yarda da ita na bata amana taci,ban tab'a tunanin Sumayya na da son zuciya ba sai yanxu,ta cuceni taci amanata"
Asrar ya zauna kusa dashi yace "yaya ba haka bane wallahi bata ci amanarka ba,babu mai sonka a duk duniya babu wanda zai maka irin son da Sumayya tayi maka"
"k'arya ne,ta tafi ta barni cikin k'unci ta koma outside da zama saboda mission d'in ya k'are"
ya sake kallon hoton ya d'aga su ya yaga su duka..
"yaya bai kamata kayi mata haka ba,wlh karatun da ta tafi saboda kai tayi haka,karka yarda da maganar Yaya Aryaan wlh sharri yayi mata,karka yarda da maganar ilham itama tana da son kanta yaya wlh Sumayya bata da laifi"
Hannu ya d'aga masa cikin tsawa yace "kada ka sake kawo min maganar Sumayya,kana hauka ne da zaka ce Aryaan ne ya cuceni? d'an uwana bazai tab'a ha'inta ta ba kuma zanje in fad'awa daddy a cikin wata d'aya za'ayi bikina da ilham"
Cikin zafin rai ya fita ya barwa Asrar d'akin.
_Allah kana gani nayi iya bakin k'ok'arina,ya Allah ka sa haka shine mafi alkhairi ka bawa Sumayya ikon yin hak'uri da juriya,insha Allahu bazan k'ara yin magana akan Sumayya ba tunda baya so, rainane zai ta b'aci_.
Da wannan tunanin Asrar ya bar d'akin.
Shi kam Arish hanyar waje yayi,yana fita ya hango Sumayya da khalid can a zaune gefe guda ta k'ara had'a tagumi,da sauri ya isa gurin...
"k'anwata lafiya?meyasa baki son shiga cikin mutane?"
Ta d'ago kai ta kalleshi tace "ban san kowa ba shiyasa"
"ai a haka zasu saba dake kema ki saba da su"
"kar suce nayi masu shishshigi"
"ki k'addara a ranki kema tamkar dama a gidannan aka haifeku kinji?"
"to shikenan"
"khalid baya magana ne?naga tunda kuka zo baya cewa komai"
"yana yi amma sai yaga dama miskili ne"
"ayya"
suka d'anyi shiru na d'an wani lokaci sannan tace "yaya dan Allah inada tambaya?"
"Allah yasa na sani"
"ni kam wacece Sumayya a gidannan?"Ji yayi gabansa ya fad'i,a hankali ya d'ago ido ya kalleta itama shi take kallo,
"babu sumayya a gidannan"
"Amma naji wata sister d'inka na cewa Allah sarki Sumayya akwai kirki da son mutane da alkunya,lokacin da nace mata sunana sumayya,na tambayeta tace min matarka ce?"
Ya d'anyi dumm sannan yace "matata ce ada amma yanxu bama tare"
"ohh shiyasa da nace sunana Sumayya shine ka tafi kace kubar gun,ta maka laifine mai k'arfi?yaya ka yafe mata domin Allah yana son mai yafiya"
Yayi saurin kawar da maganar da fad'in "ku tashi mu shiga cikin gida".
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya,Arish ya k'ara samun lafiya sosai,sumayya da khalid kuwa sun zama 'yan gida,biki kuwa k'ara matsowa yake dan wata uku aka saka kamar yadda daddy ya buk'ata kuma tare za'ayi dana Ashaq.
Soyayya mai k'arfi sukeyi tsakanin Ilham da Arish kullum k'ara cusa masa soyayyarta takeyi tare da mantar dashi wata Sumayya.
***** ***** *****
*ENGLAND*
A zaune take a kan kujera ta dunk'ule jikinta guri d'aya,idonta d'auke da k'walla.
Tana jin sallamarshi ta amsa ba tare da yaji ba,bata kuma koda motsa daga inda take ba.
Kanta ya tsaya yana kallonta yadda ta k'ara ramewa sosai kana ganinta kasa tana tattare da damuwa.
"meyasa karatunki ya fara samun rauni?meyasa bazaki cire damuwa a ranki ba?"
Ta d'ago kai ta kalleshi d'an hawayen daya mak'ale ya samu damar zubowa...
"kuka akan me kike kuka?"
"a kanka Fu'ad" ta fad'a cikin muryar kuka,ta cigaba da fad'in "ya kake so inyi?kace baka yadda da k'addara ba,ni kawai ku kasheni ku huta na gaji da rayuwarma"
Kujera ya janyo daf da ita ya zauna ya tsura mata ido na tsawon minti biyu sannan ya fara magana "waya fad'a miki ban yarda da k'addara ba?ni fa Musulmine Sumayya,na yarda da k'addara amma dai na san nayi babban rashi a rayuwata na san bazan samu kamarki ba sai dai kwatankwacinki,ina ji a jikina duk ranar da kika koma gidan mijinki daga ranar bazan sake ganinki ba"
Hawaye ya cigaba da zuba a idonta,shima hawayene a idonsa amma yak'i yarda su zubo dan karya k'ara sawa ta karaya.
"Sumayya had'uwa ta dake na koyi abubuwa da yawa,sannan na rabu da duk wani miyagun halayena bazan manta dake ba a rayuwata sai dai dole in barki domin akwai igiyar aure a kanki"
"Fu'ad zaka samu wadda ta fini saboda Hafsat na sonka fiya da tunaninka"
"a'a bamu dace ba"
"saboda me?"
"saboda halinta baya da kyau,duk ta rigada ta gama nunawa maza surar jikinta?bazan iya auren mara tarbiyya ba,amma kimin alk'awari?"
"in har bai sab'awa addininmu ba"
"bai sab'a ba Sumayya ina son a duk lokacin da naje nigeria zanje gombe sannan idan naje duk wadda nagani a cikin k'annenki na kuma ce inaso zaki bani?"
Tayi murmushi mai d'auke da hawaye tace "zan baka Fu'ad a cikin Farida da Fatima duk wacce kake so nayi maka alk'awarin zata kasance matarka insha Allahu"
Shima murmushin yayi sannan yace "ummmmmmmmm.........na zab'i Fatima"
dariya sosai tayi "tun kafin ka gansu?Fatima fa shegen surutu ne da ita farida ce saliha"
"kinga kuwa na iya zab'e tunda na zab'o mai halinki"
ta rufe baki tana dariya, "kenan ni surutu ne dani?"
"no bance ba ooo"
haka sukayi ta hira suna dariyar har ya mantar da ita damuwarta.
Amma ranar ko runtsawa baiyi haka ya rik'a tunanin yanzu shikenan ya rabu da Sumayya.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum Fu'ad yana tare da Sumayya yana kula da ita sosai kamar yadda ya d'aukarwa kanshi alk'awari.
Duk wata matsalarta tare dashi take warwareta,ya zame mata babban yaya,ya hana ta amfani da waya sannan baya yarda ta kira kowa inba malam da umma ba kuma shima a wayarshi.
Idan bata gane wani abu ba a cikin karatunta shi zai nuna mata ko kuma ya nemo wanda zai nuna mata.
Yau kwananta biyu bata je lectures ba.
Tana zaune k'asan gado ta rungume pillow sai kuka take,ya turo k'ofar ya shigo.
Abin ba k'aramin mamaki da d'aga masa hankali yayi ba yadda yaga yau tana ta kuka kamar k'aramar yarinya,kukanta fita yake a fili sosai,gaba d'aya jikinta ta had'a zufa.
Ya k'araso gurin jikinshi a sanyaye ya zauna gabanta .
"meya sameki?waya tab'o ki?"
"na shiga uku Fu'ad"
ta fad'a tana kuka.
"kin shiga uku?menene?meye matsalarki?ki fad'amin damuwarki Sumayya"
"wallahi Fu'ad inajin umma ko wani a cikin 'yan gidanmu ya mutu,ni dai gida zan tafi gabana fad'uwa yake"
"ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru"
"wallahi akwai,tun last week nakejin fad'uwar gaba har yanzu,na kira malam nace ya bawa umma yace min a'a in zauna in cigaba da karatu banda yawan yin waya"
"fad'uwar gaba stress d'in karatu ne,malam kuma ya fad'a miki haka ne saboda ki zauna ki dage kinga saura one nd half year ku gama karatu"
"a'a ni wallahi sai naje na gansu"
"to bara na kirashi a waya kiji"
Tayi saurin rik'e hannun da wayar take,sai kuma tayi saurin saki,
"a'a pls karka kirashi wlh zai hanani zuwa kamin wannan alfarmar dan Allah fu'ad".
Da k'yar ya samu tayi shiru,tare sukaje suka nemo visa sukayi booking jirgi harda shi,cikin kwana biyu komai ya daidaita.
A cikin jirgi ma,haka tayi ta tagumi yana hanata,k'arshe kuma kawai dafe kanta tayi.
K'arfe 12:30pm jirginsu ya sauka a babban airport na Abuja,Fu'ad ne ya janyo masu trolley,tunda ta sauke k'afarta a kan steps d'in taji gabanta yayi mummunar fad'uwa...
Haka tayi ta addu'a sannan taji ta d'an samu relief,ya barta a zaune yace bara yaje ya dawo.
Tana ta tunani ta sak'a wannan ta kwance,shekara uku da watanni ta san komai ya canza.
Fu'ad ya dawo yaja trolley d'insu ya saka a mota,
"ina driver?"
"gani" ya bata amsa
"ina ka samu mota?"
"ta frnd d'ina na karb'o kafin muje zaria saboda bana iya shiga motar haya"
"to ka kira malam yanxu kafin mu fara tafiya"
yayi dialing number sannan ya mik'a mata...
"salamu alaikum Fu'adu ya kuke?"
"wa alaikumussalam malam Sumayya ce ba fu'ad ba"
"ohh sumayya ya karatun?"
"lafiya k'alau malam gamu a Abuja munzo nigeria"
"me kuka zo yi? ko kin gama karatun?"
"a'a nazo ganinku ne"
"kuma shi Fu'adun ya biye miki?to karku tsaya ko ina ku taho gombe na san halinki yanzu sai kice sai kinje kaduna,ku taho nan yanzun nan kinji na fad'a miki"
Gabanta yayi mummunar fad'uwa zuciyarta taji ya fara bugawa da sauri da sauri...
a sanyaye tace "to malam sai munzo"
"Allah kiyaye hanya"
"amin"
Ta kalli Fu'ad tace "muje"
Sun fara tafiya kenan tace "Kaduna zamu fa"
"kaduna kuma?"
"eh"
"me zamuyi a kaduna?"
Ta kalleshi shi kuma driving d'insa yake ba tare daya kalleta ba sai dai yana ganin duk abinda take ta gefen idonshi..
"naji kinyi shiru?"
"kasan baxan iya zuwa banga halin da gentle ke ciki ba,pls Fu'ad mu fara xuwa kaduna sai mu wuce"
"okay as u wish,bara muje kadunar"
Kan motar ya juya suka d'auki hanyar kaduna,yana ta mata hira amma da k'yar take amsawa dan hankali a tashe yake sosai.
*Hannu biyu*
_Sadeey_
_&_
_Nafsal_
[10/5, 3:21 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
7⃣5⃣↗7⃣6⃣
Ya lura da sam hankalinta ya tafi wani tunanin,ga fuskarta ta bayyanar da damuwa.
Dan haka shima yayi shiru,ya kunna karatun al-qur'ani mai girma dan ya san zai rage mata damuwar,aikuwa a hankali ta rik'a bin jabir cikin suratul Ankabut.
Suna shiga garin kaduna kawai ya lura da zufa ta tsatstsafo a goshinta duk da cewar ya kunna Ac a cikin motar...
"ya dai?" ya tambaya,
a d'an tsorace ta kalleshi sannan tayi ajiyar zuciya tace "kawai naji gabana ya yawaita da fad'uwa gani nake kamar ba lafiya ba"
Ya mik'a mata handkerchief cikin muryar rarrashi yace "calm down sister,babu komai insha Allah ki goge zufar fuskarki"
a sanyaye ta karb'a ta goge.
Ita ta rik'a nuna masa hanya har suka isa cikin unguwar,tunda suka shigo take ganin giccen motoci ga kuma mutane a k'asa suna tafiya,fad'uwar gabanta ya k'aru ta dafe k'irjinta tsoro ya kamata dan ta san unguwar da wuya ka fito kaga mutane da basu gaza uku ba wani lokacin ma babu gicce ko ina shiru kasancewar unguwar masu kud'i ce.
Street d'insu Arish cike yake da mutane ana ta kai kawo,ta hanga idonta ya hango mata mutanen dake shige da fuce a gidan.
Da sauri ta rik'e hannun Fu'ad dake driving wanda saura kad'an tasa su bigi gini...
"lafiyarki k'alau kuwa?" ya tambaya lokacin daya ja burki ya tsaya,kasa cewa komai tayi ta bud'e motar a gigice zata fita yayi saurin rik'o hannunta,
"ka sake ni in je in duba,bazan yarda Arish ya mutu ba,bazai mutu ba, zai warke fu'ad zan sama masa maganin cutarshi da yardar Allah"
da k'arfi ta fuzge hannunshi daga nata ta ruga da gudu,yayi saurin fitowa ya kulle motar ya biyota..
Gudu take baji ba gani,mutane sai kallonta suke,wasu na salati ana tunanin ko mahaukaciya ce duk da babu alamar hauka a tare da ita.
A bakin gate taci karo da Aryaan,tayi turus ta tsaya,suka fara kallon kallo...
k'walla ta cika idonta tace "ina Arish?ina gentle d'ina karkace min ya mutu please Aryaan"
"Kamar yadda kike so ko?to ban mutu ba,ina nan da raina sai dai ko yanzu zaki k'arasani ban sani ba tunda naga burin naki har yanxu bai cika ba" taji anyi maganar ta bayan Aryaan tare da fitowa fili dan ta ganshi.
Suman tsaye tayi,dan tunda take a rayuwarta yauce rana ta farko da ta tab'a jin daddad'ar muryar shi duk daya furta tane tare da munanan kalamai.
Kusan minti uku sannan harshenta ya lalubo kalmar "ka samu lafiya gentle?"
"na samu lafiya kuma na san ba haka kika so ba,kinso na mutu ko?"
Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta ta girgiza kai tace "nafi kowa farin cikin samun laf.........................."
"k'arya kike makira" ya katseta cikin tsawa..
Hawaye wani na bin wani a idonta ta cigaba da kallonshi tana fad'in "kar kayi min haka gentle,dan Allah k....................."
"ki rufamin baki jahila,maci amana" ya sake dakatar da ita.
Ta juya ta kalli fu'ad dake bayanta sannan ta juyo ta kalli Aryaan tace "yaushe zaka fad'a masu gaskiya?dan Allah ka fitar dani daga wannan k'uncin ka taimaka min Aryaan menayi maka?menayi maka ka tsaneni?"
Hannu ya d'aga mata yace "kinga bana son kina nuna kin sanni kin gane ko?"
Kuka ta cigaba dayi jikinta na tsuma ta kasa tsayawa a tsaye ta durk'ushe anan tana kuka...
Taku uku yayi ya k'araso gabanta,kallonta yayi ido cikin ido ranshi a b'ace yace "ina cikin farin ciki kina son ruguza min,yau an d'aura aurena ranar da ko wane ango ke farin ciki amma kinzo kina son b'ata min farin ciki,wlh na tsaneki na tsani ganinki a idona"
Tun kafin ya k'arasa maganar ta mik'e tsaye cikin tsanani tashin hankali....
"karkayi min haka Arish nice fa,matarka ta sunna,aurenka Arish kana nufin kayi aure"
"k'warai ma kuwa,ki daina yaudarar kanki,ki daina suffanta kanki a matsayin matata domin bazan iya rayuwa da fasik'a ba"
"ya isa haka ya isheka kuma" Fu'ad ya fad'a cikin zafin zuciya...
mutane kuwa duk an tattaru a wajen dan dawowarsu daga d'aurin aure kenan sumayya tazo, wasu na bashi hak'uri suna janye shi amma yana fad'in saiya wulak'anta Fu'ad da Sumayya,duk ya bi ya gigice kamar mahaukaci,da gudu wani ya shiga cikin gidan ya kira daddy.
Aryaan kuwa kallonta yake a zuciyarshi yana fad'in...
_kin k'ara kyau,komai naki ya canza bazan iya bari a san sirrinnan ba,kodan kar su momma suga bak'ina,kin d'an bani tausayi kad'an_'...
Arish kuwa sai k'ara fad'i yake "ke fasik'a ce jahila wadda batayi amfani da ilminta ba,dama gidanku bama su tarbiyya bane"
Fu'ad ya matso zai dake shi aka rik'e shi,
"ku k'yaleni in masa rauni,idan bata da tarbiyya meyasa ka haukace akan sai ka aureta?kuma yayanka wanda kuka fito ciki d'aya shine annamimi fasik'i shine ya ha'ince ka"
Arish yayi yunk'urin zuwa gurin fu'ad mutane suka k'ara rik'eshi,
"idan ya k'ara danganta yayanah da mugayen kalamai wallahi saina muzantashi" Arish ya fad'a yana huci.
Fu'ad ya fuzgi hannun Sumayya zasu tafi,tayi saurin fincikewa
"ka sakeni Fu'ad sai ya bani takardar saki kafin na bar nan bazan rik'a zama da igiyar aure ba"
Ya k'ara fuzgarta cikin b'acin rai yace "bazan iya jurar wulak'anci ba bazan iya zama ina gani ana wulak'anta ki ba"
Arish kallonsu kawai yake yana huci,an rik'e shi sosai dan kar suyi fad'a.
A dai dai lokacin 'yan gidan gaba d'aya suka fito,da gudu Zahra taje ta rungume sumayya tana kuka,kuka sosai suka cigaba dayi tare.
Asrar ya k'araso gurin shi da daddy fuskarshi sam babu fara'a,daddy ne yace "ku shigo cikin gidan"
"a'a Alhaji dama dage wa tayi sai munzo rabon dai aci mana mutunci amma gaskiya gombe zamu wuce yanxu,dama shigowarmu kenan nigeria muka iso nan" Fu'ad ya fad'a fuskarshi sam babu annuri.
Ya kalli sumayya yace "ku shigo 'yata mutane kar ayi ta magana dan Allah"
bata ko kalleshi ba ta cigaba da kuka ji take bazata iya shiga ba,tana ganin idan ta bar nan ita da kaduna har abada dama aurene ya kawota...
"daddy baza su shigo ba su ta da mana hankali daga dawowarmu daga d'aurin aure" Aryaan ya fad'a yana muzurai.
"babu inda zasu shiga,gidanmu tattare yake da masu tarbiyya amma wannan jahilar wallahi bazata shiga ba" Arish ya fad'a yana nuna Sumayya da yatsa.
Momma ce ta fashe da kuka,duk aka juyo ana kallonta,tazo ta rik'e Sumayya tana fad'in "na jawo miki,nice silar fad'awarki ga halaka nice na sakaki a k'unci" kawai sai gani akayi ta sulale ta fad'i k'asa..
Babu shiri aka d'auketa aka shiga cikin gidan,dole tasa Sumayya da Fu'ad suka shiga.
Ita ta amshi ruwan da Asrar ya kawo ta yayyafa mata,ta tashi ta kalli Arish dake gefenta ta sake fashewa da kuka,
Zahra,Asiya,Asrar,duk kansu kuka suke,
Sumayya ta saka hannu tana goge ma Momma hawaye tana fad'in "baki da laifi momma,dan Allah ki daina kukannan saboda kina k'ara karya min zuciya,ina ganin kamar na aikata babban zunubin da Allah bazai yafe min ba,momma ki d'auka a komai ya wuce,na yarda da cewa wannan itace k'addarata,zan tafi bazan sake dawowa ba bare hankalinku ya tashi,dan Allah nima ku yafe min kuskuren da nayi muku dan idan na bar kaduna bazan sake dawowa ba na rok'eku daku goge tarihin rayuwata a zukatanku dan nasan duk sanda kuka tuna zaku k'ara tsanata ne amma idan kuka manta dani komai zai shud'e ina ma yaya Arish da matarshi fatan alkhairi Allah ya basu zaman lafiya" ta fad'a tana matsanan cin kuka...
Wannan karin kuwa ba haj karima ba,ba daddy ba hatta Sumayya(namesake d'inta) da bata san komai ba sai da tayi hawaye...
Ta mik'e tsaye da idanunta sun gama k'ank'ancewa sun yi jajir,ta kalli Fu'ad tace "ka tashi mu tafi"
Momma tayi saurin rik'ota ta dawo da ita ta zaunar "ki yafe min sumayya dan Allah ki furta inji"
"na yafe miki duk da baki min komai ba,kin jure wahalhalu da yawa a gidannan duk saboda ni kin soni kamar yadda kike son Arish,kin kula dani kamar yadda kike kula da kanki godia ce tsakanina dake"
Ta tashi ta nufi inda Asrar yake yana ta share hawayen fuskarsa,tayi murmushin k'arfin hali tace "ina alk'awarina?"
Ya kalleta ya kasa cewa komai,har sai da ta sake maimaitawa sannan yace "yak'i bani Sumayya na rasa yadda zanyi dashi"
'Durk'ushewa tayi da gwiwoyinta a gaban Arish cikin kuka tace "zan tafi amma har yanzu da igiyar aurenka a kaina dan Allah ka taimaka ka tsinke ta kona samu sassauci"
Cikin shouting yace dalla malama ki matsa daga gurina na tsani ganinki wallahi k'yank'yaninki nake ji saboda ke babu tsarkin musulunci a tare dake"
"duk da haka dan Allah ka furta inji ka furta kace ka sakeni"
Hannu biyu yasa ya hankad'ata,tayi saurin dafa carpet d'in,
Cikin matsanancin kuka tace "ka ha'inceni Allah zai saka min ka barni da igiyar aurenka kada ka manta akwai igiyar ka uku a kaina kak'i rabani dasu,ni dai nasan ban ci amanarka ba Allah ne shaida"
yayi tsaki ya kauda kai.
Fu'ad yayi saurin tasowa ya fuzgeta da k'arfi ya fita,suka rufa masu baya amma momma daddy,haj karima da Arish basu fita ba.
Asiya tayi saurin shan gabansu ta dafa Sumayya tace "ki d'au dangana ki cire damuwa a ranki pls"
Zahra kuwa kuka ya hana tace komai.
Ta kalli Aryaan tace "Akwai Allah kuma zai saka min"
"na fiki sanin akwai Allah tunda na rigaki zuwa duniya"
Ta kallesu d'aya bayan d'aya sannan ta fita da sauri tana kuka mai tsanani.
Mutanen dake waje sunyi cirko2,suna ganin futowarta suka tsaya kallonta, kowa tausayinta yake yadda kamanninta suka canza lokaci guda.
Suna cikin tafiya tana ta kuka ya rasa yadda zaiyi ma,driving yake amma gaba d'aya ta d'aga masa hankali,ta d'anyi shiru tana shashshek'ar kuka sai ji yayi taja dogon numfashi ta zube a jikinsa.
A gigice ya taka burki ya tsaya a tsakiyar titi,yama manta baiyi parking ba,,ya manta inda yake,jijjaga ta kawai yake amma bata motsi....
"Sumayya dan Allah karki mutu ki rufa min asiri ki tashi please"
Gaba d'aya ya had'a go slow sai horn ake zabga masa amma bai ma san anayi ba...
Cikin zafin rai wani mutum ya fito daga motarshi zuwa motar Fu'ad.
*Kash😩nima bansan sanda na saki wayata ba na nufi motar fu'ad dan bada agajin gaggawa kafin yasha mazga😅*.
hunnu biyu🤝
Sadeey
&
Nafsal
[10/5, 3:21 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
*_Nafisa S Adamu_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
7⃣7⃣↗7⃣8⃣
Cikin zafin rai yayi knocking glass d'in motar,daya lura Fu'ad baya da niyyar bud'ewa kawai ya kama murfin motar ya bud'e.
"haba malam wannan wane irin rashin mutunci ne da son zuciya,ka duba fa kaga yadda ka had'a go slow a gurinnan kuma ana maka horn ka mayar da mutane shashashai".
Kafin kace me,har gurin ya cika da mutane ko wanne na fad'ar albarkacin bakinshi,wasu kam har suna neman dukanshi.
Shi dai kawai hak'uri ya basu tare da fad'in rud'ewa ce ta saka shi yin hakan.
A gigice ya tashi motar da gudu,tambaya yayi aka nuna masa wani private hospital dan shi ba ko ina ya sani a zaria bama talkless of kaduna tunda shi ba wani zama yake a k'asar ba.
*_2h Later_*
Allah sarki Fu'ad,duk wanda ya ganshi a lokacin nan zai tausaya masa,ya shiga damuwa sosai ga zaryar siyo magunguna idan babu a pharmacy d'in cikin asibiti,gashi bai saba da wahalhalu ba shiyasa duk ya bi ya k'wanjame ya rame cikin hours da basu fice 3 ba.
Yana tsaye a office d'in likitan,ya kasa zama ma,kawai yana son jin sakamakon gwajin da akayi mata.
"ka zauna inyi maka bayani" likita yayi maganar...
Ido kawai ya tsurawa likitan na tsawon mintuna sannan yace "Doctor dan Allah ka fad'a min halin da sumayya take ciki,wlh hankalina ya tashi gashi malam sai kirana yake na kasa d'agawa dan bansan me zan ce mashi ba,kusan awa biyar kenan da gaya masa mun taho gombe yanzu yaci ace munje ko mun kusa zuwa"
Doctor da kanshi ya tashi ya janyo shi ya zaunar dashi "ka kwantar da hankalinka kaji"
"tayaya?hankalina bazai tab'a kwanciya ba in ban san halin da Sumayya ke ciki ba"
Komawa yayi kan kujera ya kalli shi yace "Ya kuke da ita?"
shiru yayi na 'yan seconds sannan yace "k'anwata ce kuma itace matar da zan aura"
"amma ko zaka iya fad'a min damuwarta?"
gabanshi yayi mummunar fad'uwa,a sanyaye ya kalli doctor yace "abin sirri ne doctor,damuwa ce wadda babu yadda za'ayi dole sai ta shiga cikinta"
"aikuwa kuna gab da rasata"
da Sauri Fu'ad ya mik'e tsaye cikin tsananin tashin hankali yace "ban gane ba doctor"
"ina nufin idan ba kuyi maganin damuwarta ba,to zaku iya rasata,dan zata iya mutuwa,saboda d'azu da ka kawota na duba jininta naga ya hau 140 yanzu kuma har ya k'ara zuwa 160/90 ya kamata ku gaggauta samo mafita"
"Inna lillahi wa inna ilahi raji'un,shine abinda Fu'ad yayi ta nanatawa"
Shawarwari doctor ya bashi ta yanda zasu magance mata wannan matsalar.
Gashi dole kwanan asibiti ya kama su sannan ya rasa ta yadda zai kira malam ya fad'a masa abinda ke faruwa,yana cikin wannan tunanin yaji kira ya sake shigowa wayarshi
_Malam_! Sunan ya bayyana akan screen,gaban shi ya cigaba da fad'uwa har sai da ta katse sannan ya kira.
"Salamu Alaiku Fu'adu kuna inane?hankalinmu ya tashi munji shiru gashi har yamma na shirin yi"
Ji yayi kamar ya fad'a masa gaskiya amma sai ya fasa.
"malam wallahi har mun d'akko hanya aka kirani a waya marik'iyata babu lafiya shiyasa muka wuce Zaria amma insha Allahu muna hanya gobe ko jibi"
"Allah sarki Allah yasa kaffara ne ya kuma sawwak'e mata"
"Amin malam mungode"
"ina Sumayyar bata mu gaisa"
Gabanshi ya fad'i.
Cikin rawar murya yace "malam na fito ne zanje chemist Sumayya kuma tana can gidan amma in na koma zan bata"
Malam har ya so ya gane dan sai da yace "ka fad'a min gaskiya Fu'adu,dan Allah ka tsare mana mutuncin 'yarmu kamar yadda ka d'au alk'awari"
"insha Allahu malam"
"ka duba mai jiki"
"zataji,mungode"
Haka sukayi sallama ya katse,sai yake jin dama ya fad'a masu gaskiya.
A b'angaren su Arish kuwa tun bayan fitar Sumayya ya shige d'aki ya kwanta yake tunani barkatai,gaba d'aya ya kasa samun nutsuwa.
Duk ilahirin gidan haka suka yini fuska babu,fara'a Zahra kuwa d'aki ta shige tana ta dirzar kuka kamar wadda aka yiwa mutuwa,haka dai ake bikin kawai saboda an rigada an fara.
Ashaq daya dawo yaji labarin abinda akayi,babu abinda ya k'ara ji irin tsanar Sumayya,ya kuma kirawo ilham ya fad'a mata duk abinda ke faruwa.
Shi kad'ai ya rik'ayin komai,shi ya saka aka je aka turare flat d'insu,nashi na Aryaan dana Arish,dan shima Aryaan ya dawo nigeria gaba d'aya.
Kuma duka matan yau zasu tare a gidan,idan ka d'auke Bilkisu(matar Aryaan) ita sai gobe zata zo k'asar,dan a can ya baro ta.
kowa flat d'insa tsab,jiransa kawai yake,dan daddy ya zuba furniture da komai na gida, amare daga su sai lefensu zasu shigo cikin gidan.
*HOSPITAL*
Ana gab da kiran sallar magrib Sumayya ta bud'e ido,zubur ta mik'e zaune ta kalli d'akin data tabbatar asibiti ne.
"na shiga uku!ina fu'ad?yanzu me zamu cewa malam,na saka Fu'ad a damuwa"
Ta sakko daga gadon kenan,ya turo k'ofa ya shigo...
Hannunshi rik'e da manyan ledoji,yayi saurin zuwa ya ajje a gefe sannan ya k'araso gurinta.
"kin tashi?sannu bara na kirawo doctor"
ya juya da sauri ya fita,ita kuma ta bishi da ido.
_meya ramar da kai lokaci d'aya Fu'ad?kalli yadda ka koma_...
ta fad'a a zuciyarta.
Bayan doctor ya dudduba ta,yace wa Fu'ad ya sameshi a office.
Gabanshi yayi mummunar Fud'uwa,gaba d'aya zuciyarshi ta karaya,doctor na fita ya juyo ya kalleta har zaiyi mata magana,sai kuma ya juya zai bi doctor,tayi saurin rik'o rigarshi ya juyo ya kalleta yace "bara naje na dawo kinji"
ta girgiza kai alamar a'a
"me kike so?"
a hankali tace "Fu'ad malam ya kiraka?"
"eh,amma nace masa muna Zaria gidanmu,bara naje na dawo pls"
Ta saki rigarshi yayi saurin fita.
A office ya samu doctor zaune ya dafe kanshi,Fu'ad na turo k'ofa yayi saurin kallonshi.
Yau kam ya zauna a kujera sannan yace "Doctor lafiya?"
Inaso ka kwantar da hankalinka kuma ka nutsu kafin in fad'a maka abinda nake son fad'a maka,sannan inaso ka zama mai hak'uri da juriya"
Tsaye ya mik'e cikin kad'uwa yace "Doctor kar kace min Sumayya mutuwa zatayi"
"ka kwantar da hankalinka Fu'ad mutuwa da rayuwa duk na Allah ne"
Bayani yayi masa yadda jininta ke ta k'ara hawa bama sauka ba,ya dai k'ara rubuta magunguna da drip sannan yace ya kwantar da hankalinshi.
A sanyaye ya koma d'akin ya tarar da ita tana waya,da alama da umma sukeyi,Ya zauna ya k'ura mata mata ido.
Ranar daya fara ganin ta shiya tuna a cikin zuciyarshi.
Tana ajje wayar tayi murmushi wanda kana gani ka san na k'arfin haline.
"d'an uwana me doctor ya fad'a maka naga yanayinka ya canza?ko cewa yayi zan mutu?"
A d'an tsorace ya kalleta yace "a'a amma yace min idan baki cire damuwa a ranki ba to da matsala,kuma yace kici abinci sosai"
"to yaya Fu'ad" ta fad'a tana murmushi,ya kalleta kallon mamaki,yau ce rana ta farko da ta kirashi yaya,kamar ta karance shi,sai kawai cewa tayi "kayi mamaki dana kiraka da yaya ko?"
baice komai ba kawai yana binta da ido ne.
ta sake cewa "kai yayana ne wanda bazan manta dashi ba a fad'in duniyar nan nagode da kulawarka a gareni yaya Fu'ad"
"am...................kici abinci Sumayya" ya janyo leda d'aya ya bud'e ya ciro,da kanshi ya rik'a bata dan ya lura idan yace taci bata son ci da yawa,yana bata yana had'a mata da hollandia,sai da taci fiye da rabi sannan tace yaya na k'oshi kaima kaci.
"Na k'oshi Sumayya"
ta b'ata rai tace "na san baka ci komai ba yaya Fu'ad dan Allah kaci"
Ganin ranta ya b'aci ne yasa yake cin abincin ba dan yana son ci ba.
_zan daure in b'oye maka damuwata ko dan a sallamemu mu koma gida_...
ta fad'a a ranta sannan tace "yaya na cewa su malam ina gidanku,amma a satin nan zamu dawo,pls karka yarda ka fad'a masu ina asibiti dan hankalinsu zai tashi sosai"
"in har kin daina damuwa to bazan fad'a ba"
"na daina yaya Fu'ad,"
ta fad'a tana murmushin k'arfin hali.
hannu biyu🤝
Sadeey
&
Nafsal
[10/5, 3:21 PM] Little ngel👄: *🍁MENE AIBUNA🍁*
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S Adamu_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
7⃣9⃣↗8⃣0⃣
*_10:21:08pm_*
Da sallama momma ta shigo d'akinsa,yana kwance a kan gado idonsa na kallon silin,hannunsa dafe akan goshinsa.
Gefen gadon ta zauna tana kallonshi tsahon minti biyar sannan tace "Arish ya kamata ka tashi kaje ka,an kawo amarya tun d'azu ga abokanka can a falo suna jiranka zasuyi maka rakiya"
Sai daya tashi zaune sannan yace "Momma yaushe aka kawo amarya ban sani ba?"
"kana nan kana tunani"
"haba dai Allah kiyaye,wallahi momma haushi kawai nakeji ki duba ki gani gaba d'aya ta lalata bikinnan,na san da Zahra da Asiya babu wanda yaje ko d'akko Amarya ko?"
"uhmmm ai Asiya ma ta fito da aka kawo amarya,amma zahra kuwa tun bayan tafiyar Sumayya tak'i fitowa tama k'i cin komai,gaskiya shak'uwarsu tayi yawa"
"Allah ya kyauta"
"amin" momma ta fad'a sannan ta tashi ta bar mai d'akin shima ya shirya ya fita...
A falo ya tarar da abokanshi su uku,Farouq,fahad,da Aiman...
"a'a ango kasha k'amshi,na ilham bada kanka a sare,uwargida kuma amarya a gidan Arish" Aiman ya fad'a yana murmushi...
Kirarin kuwa ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba.
_Zan tafi bazan sake dawowa ba bare hankalinku ya tashi,dan Allah nima ku yafe min laifikan danayi muku dan idan na bar kaduna bazan sake dawowa ba,na rok'eku da ku goge tarihin rayuwata a zukatanku dan nasan duk sanda kuka tuna zaku k'ara tsanata!_
Kalaman Sumayya ya tuna wanda har yaji kansa na zugi....
"kai karkayi mana fulako mana,muna maka kirari ka wani sharemu kazo muje amarya na jiranka dan ku raye ranar farin cikinku"
duk suka saka dariya,shima yayi murmushin k'eta.
Suna tura k'ofar d'akin wani dad'd'an k'amshi ya doso hancinsu..
Ya hangota zaune tsakiyar gado,k'awayenta su biyu a gefenta..
_duk da haka ka furta inji dan Allah ka furta kace ka sake ni_
"bazan iya ba,inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"
Ya furta a fili tare da dafe kanshi.
"lafiya Arish?mene bazaka iya ba?" Farouq ya tambaya tare da ruk'oshi.
Ganin kamar yana son fita hancinshi yasa suka koma zuwa falo.
Ilham ta yaye mayafin fuskarta ta kalli Fauzah tace "Cab dole sai nayi da gaske fauzah dan naga alama yarinyar nan yake tunawa"
"nima dai abin ya bani mamaki" Fa'iza ta fad'a
"ki dai rufe fuskarki karsu shigo" cewar Fauzah.
A falo kuwa ya dafe kanshi sai magana suke masa amma yak'i kulasu.
Fahad ne yace "Haba Arish kai fa ba yaro bane,tayaya zaka ringa yin abu na yara"
"Fahad kai mai bawa wani labari ne akan yadda muke da Sumayya"
"na san da haka amma ai dole kayi hak'uri tunda yanzu ta haramta a gareka"
"maganganunta ne ke yawo a kaina na rasa ya zanyi duk da dai ina jin tsanarta amma wallahi na kasa mantawa da ita"
"ya kamata ka manta kuwa ka bud'e shafin sabuwar rayuwa da ilham ka manta da macuciyarnan" cewar Aiman.
Haka sukayi ta rarrashinsa,sannan suka koma akayi siyan baki aka gama.
_*11:49:23pm*_
Bayan sun idar da sallah Arish ya dafa kanta yana k'wararo addu'oi tare da fatan zaman lafiya a tsakaninsu,bayan sun shafa ne ya umarceta da taje kitchen ta d'akko ledan kayan albidi.
Ranta cike da farin ciki ta nufi kitchen ta d'akko ta had'o da plate da cup,da kanta ta bud'e kaza ta zuba a plate sannan ta tsiyaya fresh milk a cup.
Ta gutsuro ta mik'a zata saka masa a baki,ya goce,ya d'auka ya bata,shi ya rik'a d'ura mata yana fad'in nasan baki ci komai ba"
a haka har ya tabbatar da ta k'oshi.
Kayanta ta cire ta saka wata 'yar yaloluwar riga wadda batakai gwiwa ba,shi kuma tuni ya saka jallabiya ya kwanta.
A hankali ta hayo kan gadon,ta rungumeshi ta baya,yayi saurin juyowa sai jin kiss yayi a bakinshi....
_wannan wace irin mace ce?_
Ya furta a zuciyarshi sannan ya mik'e zaune.
"haba ilham ki kwanta ki huta mana"
"wane hutu kuma my man?ka manta ba hutu nazo yiba bautar Allah nazo yi"
Ya d'an dafe kanshi....
_bazan iya ba,tunanin Sumayya bazai bari nayi komai ba,itace macen dana fara so a rayuwata,ban san halin dana barta ba yanzu,tabbas Sumayya ta cuci kanta kuma ta cuceni_...
Ya sake furtawa a ranshi.
Ilham ta kwanto kan k'irjinshi tace "hak'k'ina na aure nake so my man,ya kamata mu raya darenmu na aure"
Ya janye ta daga jikinshi ya tashi ya d'auki pillow yana fad'in "kinga bacci nake ji,naga ke kin fiya wasa"
yayi saurin fita ya shige d'ayan d'akin ya kulle da key.
Da sauri ta biyo shi tana knocking amma yak'i bud'ewa,haka ta hak'ura ta koma ta kwanta tare da tunanin dole ta fitar mai da tunanin wannan banzar Sumayyar a zuciyarshi dan tasan ita ta hanasu rawar gaban hantsi.
Shi kuwa Arish yana kwance yana tunani ko yanzu ina take?ko a wane hali take?shin meyasa ya wulak'anta ta da tazo,gaskiya bai kyauta ba,wani b'angaren zuciyarshi kuwa na k'ara saka mashi tsanarta tare fad'a masa irin girman laifin da ta aikata,maganganunta kuwa sukayi ta yawo a brain d'inshi,ranar yadda yaga rana haka yaga dare.
_Washe gari_
K'arfe goma ya fito daga d'akin,cikin shiri,ya saka shadda coffee color kanshi babu hula,yayi kyau sosai.
A falo ya tarar da ita kamar had'in baki,itama sanye take da Shadda coffee color,gown ce,tayi makeup sosai,idonta na kan k'atuwar plazma dake manne jikin bango,tayi tagumi da alama ba kallon take ba.
Gefenta ya zauna tare da cire hannunta daga tagumin,tayi saurin juyowa ta kalleshi,sai kuma ta tashi zata bar gun yayi saurin fuzgota da hannu ta fad'o kan k'irjinshi.
"am sorry my wife na san nayi miki laifi amma ki yafe min"
Sarkin hawaye kawai sai ta fara kuka,ya k'ara rungumeta a k'irjinshi yana rarrashi.
"karki b'ata min makeup d'in mana haba dear"
haka yayi ta rarrashinta,da yake an kawo abinci daga can part d'in su momma,haka ya jata yana ta rarrashi ita kuma tana k'ara mannewa a jikinshi sai wani shagwab'a take,akan cinyarshi taci abinci shi da kanshi ya bata a baki har ta k'oshi,amma still ya kasa saka komai a bikinshi.
"oyaa d'akko gyale muje mu gaida su momma" ,da sauri ta shiga bedroom cikin murna.
Ya bita da ido...
_ina tausaya miki kawai dan nima kin tausaya min a lokacin da sumayya ta gujeni_...
Ta Fito sanye da gyalenta,hannunta rik'e da hula coffee,ta k'araso ta zura masa a kanshi...
"my man kafi kyau da hula"
"da gaske?"
ta gyad'a kai tare da gyara masa lings sannan suka jera suka fita.....
_Fantastic couple(sunyi kyau sosai😃)_.
A b'angaren Sumayya kuwa ranar bata runtsa ba,ga zafin ciwo ga tunanin Arish,Fu'ad ma kuwa kwana yayi yana nafilfili.
Da sassafe yaje ya siyo masu abinci,taci sosai kuwa dan ita kawai so take ta tafi gida.
K'arfe takwas doctor ya shigo ya sake dubata,bayan yayi rubutu a file d'in sannan yaja kujera ya zauna.
Ta kalleshi tayi murmushi tace "Doctor amma yau zaka sallamemu ko?"
ya k'ura mata ido cikin tausayinta yace "meyasa bazaki cire damuwa a ranki ba?"
"bani da wata damuwa fa"
Fu'ad ya matso kusa dashi yace "amma doctor isma'il naga ta daina damuwa gashinan yanzu hankalinta ya kwanta nima ina tunanin yau zaka sallamemu mu tafi"
"tana cikin damuwa Fu'ad mune take b'oyewa damuwar dan karmu gane,ya kamata ka sanarwa iyayenta su san halin da ake ciki,dan wallahi akwai matsala jininta ya hau sosai dan yanzu har ya kai 210/90,ka gaggauta sanarwa iyayenta suzo,sannan kaxo ka sameni yanzu a office"
Duk ilahirin jikin Fu'ad ya gama mutuwa,kusan minti biyar da fitar doctor amma yak'i motsawa,sai daga baya kawai ya tashi zai tafi.
"yaya Fu'ad"
tayi saurin kiran sunanshi,ya juyo ya kalleta.
"dan Allah kamin alk'awarin bazaka fad'awa su malam ba,wallahi hankalinsu zai tashi,zan cire damuwa a samu a sallamemu daga yau zuwa gobe"
"Sumayya kinaji doctor yace komai zai iya faruwa,ya kamata su malam su san halin da kike ciki"
"babu abinda zai faru insha Allah,amma pls karka sanar musu"
Baice komai ba ya fice kawai.
******* ***** *******
Falon ya cika da amare Ilham da Ayrah,angwaye Arish da Ashaq,sai sauran 'yan gidan Ana zaune a falo sai hira ake ana dariya,ilham da sun had'a ido da Ayrah sai su sakarwa juna murmushin jindad'i,martar Aryaan ma ta iso,tun k'arfe takwas dan haka family d'in ya gama had'uwa idan ka d'auke Zahra da Asrar sune basa nan.
Cikin sallama suka shigo tare,daddy ya d'ago kai ya kallesu yace "ku kuma daga ina kuke ana ta raha banda ku?"
"munje kasuwa ne"
Asrar ya bashi amsa.
"kasuwa kuma da sassafe me kuka je siya?"
Asrar ya kalli Zahra yayi mata signing,ta kalli daddy tace "daddy munje cafe d'in cikin kasuwa dan ya d'anfi sauk'i kuma mun biya mun siyo memo's"
Guri suka samu suka zauna babu wanda suka yiwa magana bare gaisuwa,kafin daddy ya cigaba da jero musu tambayoyi Zahra tayi saurin cewa "dama wata alfarma muke nema a gurinka daddy"
"inajinku"
daddy ya fad'a yana kallonsu.
Asrar ya gyara zama yace "daddy ka min izni in auri Sumayya"
A gigice Arish ya kalleshi,yayinda Aryaan cikin rud'ewa yace "wace Sumayya?"
Zahra tace "wace Sumayya kuwa wadda ta wuce tsohuwar matar yaya Arish,daddy amincewarka kawai muke nema dan har mun siyo memo da za'a saka pix dinsu a raba kuma munaso a saka bikin cikin satin nan"
"Dalla rufa mana baki marar hankali kawai" Aryaan yayi maganar cikin tsawa.
Hankalinta kwance ta kalleshi tace "ai ba haramun bane,tunda ya halatta kuwa babu komai sai amincewar daddy da muke jira"
Arish tuni ya mik'e tsaye cikin tsananin tashin hankali,Zahra na kallonshi ta gefen ido,ta maze ta k'ara cewa.
"daddy kace kowa a cikinmu zaka aura masa zab'insa,daddy na san zaka amince da buk'atar yaya Asrar,please daddy ka furta kowa yaji cewar ka amince ya auri Sumayya"
Ta fad'a idonta akan daddy.
0 comments:
Post a Comment