Uztaz"uztaz"uztaz" tayi kururuwa yanda wayanda suke
nesa da ita ma sai sunji muryarta
.
Kyakkyawar budurwace take tafiya sauri sauri don ta
cimma wani mutum dake gabanta,
Da ganin fuskar budurwan kasan tana dauke da abu mai
muhimmanci, wanda ya shafi rayuwarta
.
Azuciyan budurwan nan kuwa ta tabbata komai zaiyi
sauki muddin ta samu suka tattauna da wannan bawan
Allah din
.
Da Sauri sauri gudu gudu ta karisa har wajen wannan
mutumin , kuma bata daina kiran sunan sa ba Uztazz
.
Mujahid yana cikin tafiya akan hanya a yayin daya ke
nazarin wata littafin Addini , kaman daga sama sai yaji
ana kiran sunansa
.
Nan ya juya don ganin mai kiransa , toh anan ne yayi
arba da wata budurwa tana sauri don ta iso wajen da
yake .
Kallo daya yayi mata yasan ba lafiya take ba dole akwai
wani abun dayake damunta
.
Koda ta kariso gabanshi sai ta cigaba da maida numfashi,
duk tabi ta jike da zufa a dalilin gudun da tayi
.
"Ina yini yallabai ,nasan na takuramaka bisa tsareka a
hanya da nayi ,ina baka hakuri Uztazz,
Ina da wasu batutuwa danake son mu tattauna dakai izan
ban takuramaka"
Budurwar ta fada a lokacin da take tsaye agabanshi,
.
"Babu damuwa ina sauraronki" uztaz ya fada
"Suna na Rufaidah, nasan baka sanni ba , Ni dalibace a
makarantar Mu'azu bin jabal ,
Satinnan nayi rigestration" rufaidah ta fadi
.
.
Mujahid ya dubeta da kyau sannan yace "toh malama
rufaidah ina sauraronki shin wata maganace kike son mu
tattauna akai,
Shin maganar da zamuyin magana ce wacce zamu iya
yinta a tsaye, ko kuwa sai mun samu wajen zama"
mujahid ya tambaya
.
"Uztaz gaskiya yana da kyau mu samu wajen zama domin
kuwa , dogon zance ne zamuyi, domin kuwa bazan taba
runtsawa ba muddin ban fadi maka ba"rufaidah ta fada a
lokacin har hawaye sun fara zuba daga idanuwanta
.
Yafara waige waige ko zaiga wani dan inuwa ,
Cikin sa'a kuwa sai ya hango wani dakali a kofan gidan dake nesa da su, rufin gidan ya yayiwa dakalin inuwa
Ya dubeta yace "toh mu karisa can sai kiyi mani bayanin "
"Toh "
.
Suka nufi dakalin
Bayan sun zauna sai mujahid ya dubi rufaida yace "malama rufaida ina sauraronki"
Rufaida wacce hawaye suka bata mata fuska ta goge da mayafin jikinta ta budi baki tamkar ba zata iya magana ba ta fara bada labarinta kamar haka
"Sunana Rufaidah...........
.RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih 99% - 2017
Part 2
.
"Sunana Rufaidah ina zaune ne a lafiya, mahaifiyata ta rasu tun ina yar shekara goma sha shida,
Babana yana matukar sona,
Hakanne yasa ya karo aure don ya samu wacce zata runga kula dani,
,
Nayi zaman kadaici lokacin da mahaifiyata ta rasu, duniya tayi mani baki kirin sanadin rashin mahaifiya, akullum nakan zauna nayi shiru ina tunanin mahaifiyata da duk wasu abubuwan da suka wakana tsakanina da ita
,
Matar da babana ya auro inna ladi, ta tsaneni matuka tana azabtar dani sosai,
Arana in ban sha bulala ba kenan tayi mani dari,
,
Kwanan kullum wuni takeyi tana azabtar dani na zama abun tausayi , a wajen mutanen angwanmu kowa yana matukar tausaya mani
,
Nasan zaka yi tambayar ina mahaifina yake lokacin da take gana mani irin wayannan azabobin,
Tunda mahaifina baba sallau ya auri inna ladi shikenan duk wata kauna daya ke nuna mani ta rikide ta koma kiyayya sam baya kaunar ganina cikin gidansa don kuwa bazan taba mance wata rana ba ranar da itace ta janyo mani duk wannan ukubar dana ke ciki,
,
Bana fatan irin wannan ranar ta sake zuwa cikin rAyuwata,
Wata rana da safiya Na futo daga cikin dakina daga ni sai wani yamutsatsen shimi da wani kodadden zani, buta na rike a hannuna
Na je na bude randar gidanmu na debi ruwa
Na nufi bayi, ina shiga bayin ta kurma mani ashar
"Ke dan uwarki ina cikin bayin shine har zaki shigo"
Da guduna na fice daga bayin,nazo na rakube a gefen dakina jikina sai makyarkyata yake, a tsorace nake dun nasan yau sai naci duka sosai,
,
"Yau zaki ci uwarki dani, sai na kure rashin kunyarkin nan"
Inna ladi ta futo daga bayin tana fadin haka,
Ta harbeni da butan dake hannunta, butan ya sameni aka tsinin bakin butan ya sokeni cikin kaina, sai ganin jini nayi yana bulbulowa daga kaina,
,
Maimakon inna ta razana sai ma kara harzuka tayi ta nufoni gadan gadan, tana zuwa ta wankeni da mari, nayi kokarin sanya hannuwana na rufe kuncina, nan ta hau jibgata tamkar tarin dawa, tun ina kururuwa ina bata hakuri har nayi lamo , bakajin sautin komai sai nishi na dake tashi a hankali,
,
Saida tayi mani likis sannan tayi shigewarta cikin daki,
Ina nan a kwance akas ina nishi sama sama, har baba sallau ya dawo daga wajen aiki,
Kallo daya yaimani ya watsar, daga nan yayi shigewarsa cikin dakin inna ladi,
.
Ina jin muryansa yana tambayar inna me yafaru dani,
"Shegiyar yarinyace, dubifa ina cikin wanka a bayi ta shigo kanta gade, shi yasa na lakada mata wannan duka"
,
Baba sallau yace "ai kaji irinta saida nace maki duk randa yar iskarnan tai maki abu, kiyi mata dukan da bazata ma iya motsa koda dan yatsanta ba yo gata can har ta fara mikewa",
Fuu ya fito daga cikin dakin hannunsa rike da dorina mai baki hudu, ina kallonsa ya nufoni, nayi kokari na mike don na ceci rayuwata amma babu hali sakamakon ji dana keyi tamkar an dora mani mirginenen dutsene a bayana
A Haka ya cimmini ya dunga tsala mani dorina a bayana, tun ina iya bashi hakuri har na fara ganin dishi dishi, daga nan ban san abun daya biyo baya,
Abun da zan iiya tunawa shine kamar naji muryan makwabcinmu malam buba yna cewa "haba sallau kasheta zakayi, wannan wani irin jahilci ne , yarka ce fa ta cikinka"
"Toh ba gwamma na kasheta na huta da irin bakin cikin datake kunsa mani ba"
**********
Bani da farkawa ba sai a gadon asbiti inda nayi arba da malam buba a gefena, sai wani doctor fari dogo yana sanye da rigan asibiti (lab coat)
Na daga kaina don ganin rufin dakin anan ne naga ledar ruwan da ake karamani
,
Kwalla ne ya fara gangarowa akan kuncina,
Ji nayi na tsani mahaifina, na tsani kishiyar babata, inna ladi,
Na kasa yarda cewa mahaifina ne yai mani wannan dukan,
Duk irin kiyayyar da mahaifina yake nuna mani ban taba tsammanin takai ga yana neman ya kasheni ba,
.
Malam buba ya dafa hannuna yace "rufaida kiyi hakuri, kinji Allah sai ya sakamaki, akwai ranar kin dillanci"
Nayi shiru ban ce masa kala ba ya mike yace min "ina zuwa rufaida bazanje gida na dauko maki abinci na dawo, kinsan uwargidana tayi tafiya"
Ya dubi likitan dake gefensa yace "likita daga nan zanzo da cikon kudin "
Likitan yace "ok ina jiranka a ofishina "
Dukkansu sukai ficewarsu ,
.
Bayan fitar malam buba sai na daddage na daure na mike zaune, na cire ruwan da ake karamani, na ajiye a gefe,
Na mike na shiga tafiya ban san ina na nufaba, ko kadan bana kaunar komawa gidan mahaifina
Bayan na fito daga cikin asibitin sai na wuce tasha, anan ne na hawa motar keffi,
,
Acikin motar na hadu da wata mata , wacce na lura tun shigata motar take kallona,
Cikin kankanin lokaci matar ta gama shawo kaina na amince zan zauna wajenta a garin keffi,
Matar me suna jummai itace ta fara dora ni a turban KARUWANCI,
Tun daga wannan lokacin karuwanci ta zama sana'ata da ita nake ci da ita kuma nake tufatar da kaina,
Na tsinci kaina cikin wani yanayi, wadda cikin sati muddin namiji bai kusanceni ba toh banajin dadin jikinah,
Sai a kwanakin baya ne nayi wani mugun mafarki wanda ya rikita mani kwalkwalwa nan take naji nadama tazo mani,
Naji na tsani kaina da kaina, naji ina kyamar irin rayuwar danayi a baya,
Nayi yunkurin na kashe kaina, daidai zan sha guba shine naji WA'AZINKA a gidan rediyon maloney fm,
Shi yasa na fasa kashe kaina,
Uztazz ! Shin Allah zai iya yafemani wayannan laifukan nawa kuwa?"
.
Mujahid wanda tun lokacin da rufaida ta fara bada labarinta yayi shiru ya kuma natsu sai yanzu yayi gyaran murya sannan yace "malama rufaida hakika Allah maji roqon bawansa ne.....
0 comments:
Post a Comment