Mujahid wanda tun lokacin da rufaida ta fara bada labarinta yayi shiru ya kuma natsu sai yanzu yayi gyaran murya sannan yace "malama rufaida hakika naji dukkan labarinki na kuma tausaya maki bisa ga halin da kika tsinci kanki abun dana ke son ki sani shine Allah maji roqon bawansa ne, muddin kinyi imani kan ba zaki koma ki sake dulmiya cikin wannan sabon ba, toh Allah zai yafe maki shi kansa Allah yana son bayinsa masu Tuba, kuma a kowani lokacin Allah yana amsar tuba"
.
"Uztazz yanzu me da me yakamata na dunga aikatawa na wanda zai nisantani daga alfashan dana bari"
"Ki yawaita yin Azumin litinin da alhamis da yin Sallah akan lokaci,sa'annan ki yawaita karatun al'qurani da yaddar Allah zaki ga rayuwa tazo maki da sauki sannan kuma akwai darasi na musamman da ake dauka a makaranta ranan asabar da lahadi, na matan aurene kiyi kokari ki runga zuwa"
.
Ta mike tsaye yanzu kam fuskarta sai sheki yake tayi wa uztazu mujahid sallama, ta yi tafiyarta
,
Uztazu mujahid
Asalinsu mazauna kaduna ne daga bayane lokacin da aka yi wani rikici a kaduna shine sukai hijra suka zo keffi, jihar nasarawa
Mujahid ya taso a gidan mutunci, tun yana dan shekara biyar mahaifansa suka sanya shi a makarantar islamiya na mu'azubin jabal,
.
Wannan yasa yataso cikin tarbiya da sanin ya kamata, gashi fasihi da an biya masa karatu yake dauka,
Wani lokacin sau daya yake karanta abu ya haddacesa akansa,
,
Malamai da mutanen angwansu suna yabonsa , bisa matukar kokarinsa,a haka har ya sauke alqur'ani,
,
Mujahid dogone baki mara duhu, fuskarsa a shimfide take, dararan idanunsa gami da dogon karan hancinsa, da dan mitsitsin bakinsa, su suka karawa fuskarsa kyawu,
,
Arayuwar mujahid bai damu da mace ba, babu ruwansa da neman mata, haka kuma bai cika magana da mata ba, gaba dayan al'amuransa ya karkatasune ga karatunsa,
,
Ahaka har Allah ya sanya ya zama malami , yana koyarwa a makarantar mu'azu bin jabal makarantar data fara haska kwalkwarsa,
.
Haka kuma yanayin program da dama a gidajen talabijnin na garin keffi,
Kaf mutanen keffi babu wanda zaka tare shi ka tambayeshi wanene Uztazu mujahid yace maka bai sanshi ba,
,
Ayanzu haka yana 100 level zangon farko a karatunsa na jami'a wanda yake a jami'ar NSUK
,
Bayaune karo na farko da mujahid yake haduwa da mutane masu matsaloli a rayuwarsu ba
Shi ya sa ma bai nuna damuwarsa sosai ba ga labarin da rufaida ta bashi,
,
Ya mike ya nufi gida,
********
Wa she gari mujahid ya shirya ya nufi makarantar mu'azu bin jabal,
Yana karisowa ana kiran Sallan La'asar,
Bayan ya ja sallah ya idar lokacin mutane sun fara watsewa daga masallacin,
Ya mike ya fita daga masallacin ya nufi wani lungu wanda yake cikin makarantar,
.
Gajeriyar Tafiya yayi takawoshi ga wasu ajujuwa guda biyu,
Ya nufi ajin dake farko ya bude kofar hade da sallama, sannan ya shiga
"Wa'alaikassalam" matan dake cikin ajin suka amsa masa
.
Babban ajine wanda ya isa akirashi da falo,
Ajin ya kawatu da ire iren kayayyakin da ake bukatan agansu cikin ajin makarantun islamiya,
,
Zazzaune akan kujerori, sanye da bakaken hijab mai hade da nikab,
Matane burjik
Mujahid ya samu kujera ya zauna sannan ya mika hannu ya dauko abun daukan sauti Microphone,
,
Anatse yake masu karatun, yana kawo masu hujjoji, cikin hadisai da qur'ani,
Fuskarsa yana kallon littafin dake ajjiye akan teburin gilashin dake gabansa,
,
Bayan ya iddar da darasin, sai ya daga kai ya dubesu yace
"Masha Allah mun iddar da darasin wannan satin, in Allah ya yarda sati mai zuwa zamu yi bayani akan Jinin NIFAS , amma kafinnan dakwai mai tambaya akan wani abu da bata gane ba"
.
Ajin yayi shiru, ya dade yana kallonsu koda zaijji mai tambaya a cikinsu,
Dayaji shiru sai yace "tun da bakwada tambaya ina ganin lokacin tashi ma yayi sai kuyi mana addu'a?"
Dukkansu suka hada baki sukai Addu'a
.
Ya fito daga ajin lokacin da hayaniya ta fara gauraye ajun,
Da sauri ya nufi bangaren da zai sada shi da masallacin makarantar,
"Uztazz" yaji an kirasa daga bayansa
Ya juya da sauri saboda ya gane mamallakiyar muryan
,
Rufaidace a gabansa sanye da wani murgujejen bakin hijabi har kasa, ta yaye nikab din dake fuskarta sama,
Hakanne ya fallasa asirin zunzurutun kyawun dake tattare da fuskar, wanda sam mujahid bai lura da shi jiya ba
.
Kyakkyawace fara doguwa, ta mallaki faffadan fuska ma'abocin sheki,
Mujahid na kallonta yaji zuciyarsa ta buga,
Tunda yake bai taba kallon mace zuciyarsa ta buga ba sai a wannan karon
.
Yasha arba da kyawawan mata wayanda suka dare rufaida kyawu, amma bai tabajin hakan ba sai ayau da suke tare da Rufaidah
,
Cikin takun nutsuwa ta kariso inda yake yadda take tafiya sai ka rantse mara lafiyace,
Murmushine dauke akan fuskarta,
"Inayini uztazz" ta fada lokacin data kariso
"Lafiya malama rifaida? Ya karatu da makaranta"
"Lafiya lau ?dama uztazz tambaya nake so nayi game da darasin yau"
.
"Mai yasa dana tambaya ko akwai mai tambaya baki tashi ba" ya tambayeta fuskarsa na kallon kasa
"Kunyar mutane naji ? Amma kai hakuri"
Ta bashi amsa
Ya jinjina kai yace "malama rufaida in har kina so ki karatu ki san addini sosai dole sai kin cire kunya da tsoro acikin zuciyarki, ya kasance kina yawan tambaya akan dukkan wani abun da baki gane ba, ko baki sani ba, Tambaya mabudin ilmine, dafatan dai kin gane"
Ta gyada kai
Yacigaba
"Yanzu ina sauri da kwai inda zani izan mun hadu gobe cikin aji sai kiyi tambayan"
"Toh uztazz sai anjima" ta fada cikin marairaice murya,
Mujahid ya juya yacigaba da tafiyarsa
******
.
Alkalamin 99%
RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih 99% - 2018
Part 4
.
Tun daga wannan rana sai ya kasance rufaida ta zage dantse sosai kan karatunta, a kowani rana akayi darasi sai ta yi tambaya akalla goma
.
Sosai mujahid yake jin dadin yadda take da matukar kokarin ganin tayi tambaya kan duk wani abun daya shige mata duhu,
.
Ta hakanne mujahid ya gane cewa rufaida mace ce nutsatsiya bata cika son magana da mutane ba,
Haka kawai yaji tana burgeshi, duk da kasancewar magana bata cika hadasu ba sai in ana dau kan darasi
,
"Malama rufaida ina jin dadin yadda kike da kokarin fahimtar darasi sosai,
Ki cigaba da aiki mai kyau sannan a kullum ki runga rokon ALlah ya yafe maki zunuban ki na baya, "
Mujahid ne yake fadawa rufaida haka wani lokaci da suka hadu bayan an fito daga daukan darasi
Rufaida tayi murmushi tace "nagode uztazz, ina matukar godiya ga taimakon ka, Allah yayi maka sakayya da kyakkyawan karshe, kuma in sha Allahu bazan gaza ba wajen karatuna, da halayyana,"
.
*******
"Rufaida wata shawara nake so na baki mai matukar muhimmanci? Wacce nasan ba za ki yi nadama ba muddin ki kayi aiki da ita "
Mujahid ya fada yana kallon. Teburin gilashin dake gabansa,
Rufaida wacce take tsaye a gabanshi tana sanye da burgujejen hijab dinta fuskarta na boye cikin nikab,
Kwayoyin idanuwanta ne kadai a bayyane
Tace "ina saurarenka uztaz dun na san baza ka taba sani a hanyar da zanyi danasani ba"
.
Mujahid ya dago kanshi ya dubi rufaida a karon farko kwayan idonsa ya ci karo da nata
Nan take yaji zuciyarsa ya buga da karfi,
.
" mutuncin ko wacce ya mace shine tayi aure tta samu kanta a Gidan mijinta,
Alokacin da akace maki mace tayi aure, kimarta yana karuwa a idon mutane, darajarta yana daukakuwa a wajen ubangiji, sam bai kyautu ace mace kamarki tana zama babu aure ba, kiyi nazari sosai ki duba maganata zaki ga cewa gaskiya nake fada maki"
.
Rufaida tace "nagode uztaz da shawarar daka bani ni kaina abun dayake cimin tuwo a kwarya kenan, bana da wani buri da ya wuce nai aure , toh amma bana da yadda zanyi don shi aure nufin Allah ne shi yasa na fawwala dukkan lamurana ga Allah"
.
**********
"Kwankwan! Kwankwan!! Kwankwan!!!" Sautin Karan kofan dakin ya gauraye dakin
Yana zaune akan kujera yana nazarin wani karamin littafi
Sai ji yayi ana kwankwasa kofan dakinsa
Yana daga zaunen yace "waye wannan, "
Maimakon abashi amsa sai aka cigaba da kwankwasa kofan dakin
"Ina zuwa " mujahid yafada yana yunkurin mikewa
.
Cire sakatar dake jikin kofan yayi sannan ya bude
Cikin matukar mamaki ya ce "malama rufaida kece a gidan namu, "
Rufaida wacce take tsaye a jikin kofan dakin, sanye da burgujejen hijabi ruwan kasa, hannunta na rike da Kulan zuba abinci,
Tayi murmushi tace "eh wallahi uztaz nice "
"Shigo daga ciki mana" yafada lokacin daya juya ya koma cikin dakin,
Ta shigo cikin dakin tana duban yanayin dakin
Komai na dakin cikin tsari yake,
Ta zauna akan tangamemen katifarsa wanda ya kusa mamaye dakin,
Shi kuwa mujahid sai ya zauna nisa da ita sosai akan kujeransa,
Har alokacin zuciyanshi yana bugawa,
"Dafatan dai komai lafiya malama rufaida
Mujahid yafada
.
Rufaida tace "komai lafiya ustazz dama abuncine na girka na kawo maka"
"Na gode rufaida , Allah yabar zumunci "
Sun danyi hira sosai kan batun karatu, kafin ta mike ta tafi
.******
Tun daga wannan rana sai ya kasance kusan kullum sai rufaida ta girka abinci ta kawo ma mujahid,
.
Aduk lokacin da ta kawo abuncin mujahid yana kokari yaga ya nisance ta, saboda gujewa RUDIN SHAIDAN,
.
Rufaida ce a tsaye. A bakin kofan dakin mujahid wanda dakin ya kasance a wani gefe daban na gidan na su,
,
Tana sanye da riga da siket, wayanda sukayi matukar dame ta, ta yafa dan fingilallen mayani, inda mayanin ya samu nasarar rufemata daga kan kirjinta zuwa cibiyarta,
,
Sake-sake take a zuciyarta na ganin ta samu cikar burinta,
"Wannan daman itace dama ta ta karshe ba zan taba yin sakaci da ita ba"
Rufaida ce take fadin haka cikin zuciyarta,
Ta dade a tsaye kofan dakin tana saka abubuwa cikin zuciyanta,
Kafin daga karshe ta fara kwankwasa kofan
.
Kwankwasawa biyu tayi taji alamun ana zare sakatar kofan,
Da sauri ta gayra ttsayuwarta,
Mujahid ya bude kofan dakin,
lokaci guda numfashinsa ya tsaya sakamakon Ganin irin shigan da rufaida tayi
Ita ko rufaida koda taga haka sai tayi murmushi sannan ta wuce cikin dakin ,
Kai tsaye kan katifarsa ta nufa tana zuwa ta zauna akan katifar,
.
Mujahid wanda abun ya matukar rudashi, ya juyo ya dubeta lokacin daya dan bata ransa yace "menene ya faru"
Ganin irin yadda yayi maganar shi ya sanya rufaida ta sha jinin jikinta, mikewa tayi ta matso inda yake a bakin kofa tace
"Farin ciki nazo ka tayani" tana maganar cikin wani irin salo
"Na me" ya tambaya
Batare data bashi amsa ba sai ta rungumeshi,
Ya fara kokarin ya bambare jikinsa daga nata, sai ji yayi ta kama kanshi ta hada bakinsa da nata
,
Duk yanda mujahid yayi don ya hanata abun datake kokarin sashi aikatawa amma ya kasa,
Ji yayi gaba dayan lakar jikinsa sun mutu, yanaji yana gani ta tureshi kan gado sannan tabi bayansa,
,
,
RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih 99% - 2018
Part 5
.
.
Cikin magagin barci ya farka,
Mikewa yayi daga kan katifarsa , ganinsa da yayi a tube babu ko singeliti shi ya tayarmai da hankali,
.
Sai a sannan madaukin kwalkwalwarsa ta fara haska mai duk abun daya faru baya tamkar a majigi,
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'uun"
Shine abun dayake ta furtawa a fili,
Kafin ya fashe da kuka
Ya dau lokaci yana kuka shi daya a cikin daki
Zuciyansa na tuna mai da abun daya aikata ji yayi ya tsani kansa da kansa,
"Shike nan na biyewa son zuciyata na gurbata rayuwata, da wanne irin ido zan fuskanci mahaliccina ,"
Mujahid ne yake fadin hakan cikin zuciyarsa
,
"Rufaida TA CUCE NI ta bata mani rayuwa, "
Waige waige ya farayi yana neman wani abu, ya dau lokaci yana tsaye
Yana kare ma dakin kallo zuciyarsa na ci da wuta,
.
Wani farin takarda ne ajjiye akan katifarsa ya dau hankalinsa, ya mika hannu ya dau takardan,
Gajeran rubutu yagani, ya fara karanta rubutun
"Assalam social Uztazz, burina ya cika , na dandani abun dana ke kwadayin dandana wanda yake tattare da kai, daga wannan rana baza ka sake ganina ko jin labarina ba,
Daga Rufeeeee."
.
Katon makwallaton hushine ya tokare mai makogwaro, shakka babu da zai hadu da rufaida a wannan lokaci da babu abun da zai hana bai kasheta ba,
.
hankalinsa ya dugunzuma ransa ya baci,idanunsa suka yi jajur da su kamar garwashin wuta. Da kyar yake numfashi kamar kumurcin maciji,
Ya yayyaga fallen farin takardar
********
Tun daga wannan rana mujahid ya dena futa daga gida hatta makaranta ya dena tafiya babuu inda yake zuwa kullum yana kulle cikin daki
.
Lokaci daya ya fara ramewa ,babu irin dabon duniya da mahaifiyarsa batayi ba don ya fadi mata me ke damunsa amma yaki,
A kullum babu abun dake ci masa zuciya face zullumi, da tunanin irin babban sabon daya aikata wa ubangiji,
.
Ga duk wanda yasan uztaz mujahid, kallo daya zai mashi ya gane cewa da kwai abun da ke damunsa,
Rufaida kuwa tun daga ranan da wannan abu ya faru, aka daina ganinta a makaranta, ko duriyarta an daina ji
.
**********
.
.
Motace kirar peogeut ta faka a gaban dan kareren Asibitin
Daya daga cikin masu bayarda tsaro a sibitin ya na sanye da uniform din aikinsa ya mike daga kan kujeransa ya nufo wajenda da peugeot din ta faka, koda ya kariso sai ya karkato da kanshi kasa ta yadda zai iya ganin mutanen da suke cikin motar,
.
"Sannu maigida"
Mai bada tsaron yace
"Yauwa sannu"
Mutumin daya ke cikin motar ya amsa
Mai bada tsaron ya sanya hannunsa aljihu ya ciro wata karamar kati ya baiwa ya mika wa direban motar,
Direban motar ya sa hannu ya karfa yana mai kallon katin wanda yakasance korene ajikinsa an rubuta, F M C passing card,
"Nagode "direban ya fada
A daidai lokacinne mai bada tsaron ya daga wa dan uwansa wanda yake nisa da shi hannu,
.
Aka bude musu gate suka kusa kai cikin dankareriyan asbitin mai suna FEDERAL MEDICAL CENTRE KEFFI wanda ya shahara a gaba dayan fadin jihar nasarawa,
.
Motar bata tsaya ako'ina ba sai a harabar asibitin inda direban ya sauko da gudu, ya nufi wajen wasu mata ma'aikatan asibitin
Saurayin direban wanda bazai wuce shekaru ashirin da biyar ba yana sanye da doguwar riga tazarce wadda tayi mai yawa ya kifa hula akansa, yadda ya kifa hular sai yafi kama da masu tallan alawa
.
Aka bude kofan bayan motar wata matace fara mai dan jiki tana da zanen kalangu a gefen kunnenta guda biyu,
Matar bazata wuce shekaru arba'in ba, fuskarta kadai mutun zai kalla ya fallasa asirin zuciyanta,
Idanuwanta sai bulbulowa suke da kwalla tana amfani da handkicin wajen share kwallan,
,
Bata dade da fitowa daga cikin motar ba dan saurayin direban nan ya dawo ma'aikatan asibitinne su biyu dauke da gadon tura majinyaci a bayansa
Suna isowa basu tsaya bata lokaci ba direban ya bude masu kofan motar ta baya, ya shiga cikin motar ya kinkimo majinyacin dake ciki, a hankali ya kwantar da sHi akan gadon majinyatan,
Ma'aikatan asibitin suka gungura gadon sukai bangaren kudu da ita,
Da gudu direban da matan suka bisu a baya
Kai tsaye emargency aka wuce da majin yacin, wata nurse ta dakatar da direban ganin yana kokarin shiga dakin da aka shigar da majinyacin
"Kui hakuri mama ku jira anan yanzu za aje a gwada shi don ganin meke damunsa"
Nurse din ta fada tana kallon farar matar
Gyada kai kawai matar tayi alaman taji
,
Farar matar ta ciro kudade a cikin karamin jakarta sannan ta dubi direban tace "Abdullahi amshi wannan nagode Allah yai maka albarka"
Dan saurayin da aka kira da Abdullahi fuskarsa na cikin alhini yace "A'a mama Tani ki barshi kawai ai kun wuce haka a wajena, don kuwa mujahid aminina ne tun yaranta yayi mun abun da bazan taba mantawa da shiba a rayuwata"
.
"Allah yaimaka albarka abdullahi"
Ta fadi kwalla na gangarowa daga idanunta
"Ameen mama hafsa, kibar kuka mama ,shima In Allah ya yarda zai samu lafiya
"Abdullahi ya fada fuskarsa na kallon kasa
"Ameen Abdullahi"
Mama hafsa ta amsa
,
Sun kai awoyi biyar suna zaune a bakin dakin da aka shigar da mujahid
Dukkansu suna cikin zullumi, Abdullahi kam babu abunda yake face Addu'a Allah ya baiwa abokinsa lafiya,
A karon farko suka ji kofan dakin ya bude dukkansu suka mike da sauri wata nurse ce ta kariso garesu tace "kuna iya shiga amma kada ku fada mai wani abun da zai tayarmai da hankali"
.
Dukkansu suka gyada mata kai sannan suka shiga cikin dakin,
0 comments:
Post a Comment