Inna asabe tana ganin *jiddah* ta amshi kayan ta koma daki tana murna ita da 'ya'yan ta.
rabi ta fara magana cikin gatsali tare da fadin."inna anya kina ganin wannan aikin yayi kuwa"
kallon ta inna asabe tayi sannan tace" ke yarinya ce amma nina yadda da aikin sa saboda yadda mutane ke tururuwar zuwa gurin sa"
kin san da aikin sa bayayi ai ba za'a rinka masa wannan layin ba.
kuma ai na fara ganin canji nifa naji a raina tabbas wannan karon wahala ta tazo karshe.
ba abinda zai hana *jiddah* wulakanta a idon duniya.
nayi alkawrin haka ko zanyi yawo tsirara kuwa.
rabi ce amshe tana cewa"ai innah idan har wannan aikin baiyi ba to ki hakura kawai ki barmu da ita tunda yanzu wancan mahaukacin *ammar* din baya nan"
ke dallah rufe mana baki ke mai zaki iya yi mata duk abinda zaki mata sai dai taji rauni a zuciyar ta.
amma idan har abinda nake so ya tabbata tofah ba ita ba duk wani maisonta sai ya shiga bakin cik....maganar ta ce ta katse tare da kallon bakin kofar.
mikewa sukayi gaba daya tare tare da zare ido.
duk cikin su ba wanda ya iya furta kalma ko guda daya.
kallo nakai ga kofar domin inga me ya kada su inna asabe haka.
nima kaina idon na zaro ganin *jiddah* sanye da daya daga cikin kayan da rabi ta bata.
wando ne dogo pencil amma sa crazy ya kamata sosa.
sai rigar pink colour da kadan ta wuce cibiyar ta itama ta kama ta tsam kirjin nan kamar zai fashe saboda cika.
karasowa tayi cikin dakin tana murmushi.
rufe baki inna asabe tayi tare da kallon gefen da rabi take.
a tare suka maida kallon su kan jiddah,
kusa da rabi tazo ta tana fadin"inna baki ga yadda kayan suka mun kyau bane naga baki yaba ba".
washe baki tayi sannan tace"ai ni bakin magana ma na rasa saboda kyan da kika yi bazai fadu ba"
dama cewa nayi barin ingwada kayan ko zasu min kyau bari inje in cire.
da sauri inna asabe tace"A'a ke ko daga saka kaya sai ki cire ki bari mana sai anjima.
kinga kuwa dama rabi zataje kome suke cewa abin ma batdee ko?ta juyo tana kallon rabi.
dariya duka suka kwashe da ita ganin inna asabe bata iya fada ba
sai da suka gama dariyar su kafin rabi tace"inna birthday ake cewa fa"
yauwa to naji zaki raka rabi can kinji ko jiddah.
amsawa tayi saboda hakanan taji tana son zuwa wajen birthday din.
karfe 8 daidai rabi ta gama shiraya wa cikin wasu kaya da marabar su da tsirara kadan ne.
wasu kayan ta kara ba *jiddah* ba irin na dazun ba wannan ma dai wandone pencil black shima duk an masa crazy.
sai riga me hannun vest itama ta matse ta sosae sai er karama wadda zata daura a sama.
dama kanta a tsefe yake gashin nan ya zubo har gadon bayan ta tayi kyau har ta gaji.
suna gama shiryawa suka yima inna asabe sallama wadda ke farin cikin ta ya kasa boyuwa.
wata tsaleliyar mota ce a kofar gidan da alamu dama su ake jira.
rabi ce a gaba saboda haka ita ta fara nufar inda motar take.
tana zuwa aka bude mata bayan mota ta shiga kafin jiddah ta zauna a kusa da ita.
sai a lokacin wa inda ke cikin motar suka lura ba rabi bace kadai.
su hudun e uku maza mace daya.
dukan su kallon jiddah suke cike da maita dan sunga er yarinya gata kuma komai yaji.
wani ne a cikin su yace ma rabi wannan bea din fa.
bata kalle shi ba tace"kanwata ce"
gaskiya kanwar nan taki ta tafi dani ya fada yana lashe baki kamar tsohon maye.
kada ka damu kawai kawai rabi tace"
har suka isa gurin bai daina kallon ta ba.
ita kuma gaba daya jinta take a takure ganin irin kallon da yake mata.
fita gaba daya sukayi a motar har *jiddah* gurin tsiit da alamu dae har anfara.
mu shiga kawai mansu inaga fa har an fara.
wanda a ka kira da mansu din ne ya karasa kusa da tare da kamo hannun ta.
kallon shi tayi da sauri tare da kokarin janye hannun ta.
rabi ta kalle ta girgiza mata kai hakan ne yasa ta kyale shi.
shi kuwa wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar shi.
*Ur's princes deejerh*💝
[11/03, 18:00] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
✨✨ *BA DON SHIBA* ✨✨
*By*
*KHADIJA AHMAD*
*Princes deeja*
*Hey guys i am so sorry for d late update,i have been busy ne wallahi dis days,kuma bana jin dadi amma in komai yayi normal zan dawo kamar kullum ina GODIYA da damuwa da kuka nuna akan jina shiru da kukai,hakan ya tabbatar min da kuna biye dani,and masu tambaya daga farko ina kara hakuri dan allah ku tambaya a group na sani ko daya ne ba zaa rasa mai shi dika,thank u so very much for d luv and care* 💘💘
*Page* 8⃣6⃣ *to* 9⃣0⃣
*Ammar* dai har yanzu hankalin shi ya kasa kwanciya duk da saura 1yr ya kammala karatun sa.
duk inda yake tunanin zai samu labarin *Jiddah* abin ya faskara har Nura sai da ya kira a waya amma yace mai shi fa ko ganin ta baya yi.
har cikin zucyar sa yana tausaya ma *Ammar* domin haka yasa ya boye mai halin da *Jiddah* ke ciki dan yasan tabbasa sai idan har yaji to sai ya bar karatun shi ya dawo shiyya duka abokan su ba wanda yake fada masa gaskiya.
Haka suka gama waya da Nura bai samu wata magana akan *Jiddah* tunda ya ga haka ya tabbatar da ba lafiya ba kuma tunanin yafi karkata akan Asabe idan kuwa hakan ta tabbata ko bai kashe ta sai ta kare rayuwar ta a prision.
kwafa yayi tare da jan wani dogon tsaki wannan karatun shine duk ya sashi a damuwa amma da sai tafi Nigeria ya gano halin da masoyiyar sa ke ciki amma ba komai yana rokon ALLAH ya kare masa ita a duk inda take.
*NIGERIA*
Fitowar ta kenan daga toilet da alamu wanka tayi kai tsaye zama tayi a bakin gado tare da dauko wayar ta dake ta faman neman agaji dauka tayi amma kuma sai tayi shiru daga can bangaren aka fara magana haba *Jiddah* sarauniyar mata saboda yau duk na kashe wani aiki dake gabana ku.....katse shi tayi cikin zazzakar muryar ta ta fara magana"na fada maka yau babu inda zan fita amma sai faman naci kake min idan zaka iya jiran next week to idan kuma kaga yayi maka tsawo to sai ka kara haba bansan nacii wallahi.
haba sarauniya ayi hakuri ni ai ko na shekara zan iya jiranki meye wani week allah ya kaimu.
bata gamajin mai zaice ba ta katse kiran har zata ajiye wayan kiran Mansur ya kara shigowa kamar ba zata dauka sai da ya katse ya kara kira sannan ta dauka shima kamar yadda sukayi da wancan haka sukayi dashi zai fara mata magiya ta katse kiran tare da kashe wayan ma gaba daya.
shiri ta fara yi kamar me shirin fita gidan biki mamaki ni,kaina nake yi duk kuma inda tabi sai na bita da kallo ina kara mamakin wai wannan Jiddan ammar ce wannan er karamar yarinya marainiya me sanyin hali ita ce ta koma haka ku kanku readers nasan zaku yi mamaki.
ta zama wata big gurl fatar nan tata glowing kawai take saboda mayuka masu tsada da take using da shi gashin kanta ya kara tsawo dan har ya wuce gadon bayanta sai baki da ya kara gashi sai sheki yakeyi woww gaskiya dole maza su mutu a kan *Jiddah* domin kuwa ta koina ta hadu bata da makusa.
wani dogon wando tasa baki legis sannan ta dauko wara er top ta saka ta daure gashin ta duk da ba kwalliya a fuskar ta amma tayi matukar kyau.
cikin gida ta nufa inda ta tarar Inna Asabe zaune shirim kamar kayan wanki can nesa da ita ta zauna kafin tace"wai ina su Rabi ne".
tabe baki tayi kafin tace su indo ni bansan inda suka je ba Rabi gata can har yau bacci take ni na rasa me take sha haka yake saka ta wannan mugun bacci kamar kasa.
dariya kawai *Jiddah* kafin tace"banda abinki Inna mutum ya wuni a waje me xai hana shi inya dawo gida ya huta ke matsalar ki kenan nima fa haka jiya kika min idan kudi kike so sai kiyi magana da wuri a baki.
tana gama fadin haka ta mike dan wani yalolon gyale da ya tsaya mata iya wuya shi ta yafa a kanta tayi waje a haka da wannan kayan da yake jikin ta.
harara Inna Asabe ta bita dashi tana tuno wani abu kuma ta fashe da dariyar mugunta tabbas boka na nakan tudu aikin ka yana kyau ta nemo min kudi ni kuma in kai maka ka karq lalata rayuwar ta.
isan har *Jiddah* bata yi yawo tsirara ba to tabbasa ban cika Asabe er halak kuma muje zuwa wannan kadan kika gani.
tafiya take a hankali kamar bata so kuma inda ta wuce sai anyi da ita masu zagi nayi masu addu'ar neman shiriya nayi ita kam ko a jikin ta bai dame ta ba dama gidan maman salaha yau taji tana son zuwa domun taji labarin ammar duka kwana2 har mantashi take.
wata majalisar maza tazo wucewa irin samarin nan area boyz da kallo suka bita kafin wani tsagera daga cikin si ya bude baki da karfi yace karuwar gidah anfito.
maganar ta daki ranta sosai dan har kwallah sai da tarun mata amma kawai ta share ta wuce zuciyar ta na tafasa.
*Ur's princes deejer*💝
[11/03, 18:00] 80k: ✨✨ *BA DON SHIBA* ✨✨
*By*
*KHADIJA AHMAD* *Princes Deejerh*
*AMEENTA WRITERS ASSOCIATION* 🤝
*Wannan shafin sadaukar ne gare ki AICHATOU😍 ta group din PRINCESS DEEJERH NOVEL kinfi kowa son wannan novel din nan nima ina yinki irin sosai din nan*
*Page* 8⃣1⃣ *to* 8⃣5⃣
Suna shiga cikin hall din gaba daya kallo ya dawo kansu musamman ma *jiddah* duka itama rabi tana kyau.
duk inda suka ratsa sai maxa sun bi *jiddah* da kallom maita ita kuma hakan yasa gaba daya take jin wani iri na rashin sabo.
a can baya suka zauna saboda cewar mansur wai baya son ana kalle masa *jiddar* sa.
sai a lokacin *jiddah* ta lura da irin mutanen dake zaune a hall din.
gaba daya yan matan wurin bamban cin kayan su da tsirara kadan ne.
ba abinda suke banda iskanci wannan na kan cinyar wannan wasu kuma suna can gefe suna matse yan matan su.
maganar da mansur yayi ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta afka sai a lokacin ta lura daga ita sai shi a wajen.
kara maimaita yayi yace"baby me zaa kawo miki".
girgiza kai kawai tayi da alamu dai bata son komai.
ki gama jan ajin ki a yanzu zaki shigo hannu ne har sekin fi rabi budawa a harkar duk a zuciyar shi yake wannan tunanin.
matsowa yayi kusa da ita har cinyarta na gogar tashi sannan ya riko hannun ta ya fara murza wa a hankali.
tana son kwacewa amma hakanan sai taji kamar ana hanata.
haka ya cigaba da murza hannun ta har ita kanta ta fara jin dadin abun.
lura da yayi hakan ne ya tabbatar masa da ba zata wuyar bada kai ba.
mikewa yayi tare da fadin"ina zuwa".
bai fi 5mnt ba ya dawo hannun sa rike kofi guda 2 zama yayi a inda ya tashi sannan ya mika mata kofi 1 kasa musawa tayi ta amsa amma bata shaba.
kallon ta yake irin kallon samarin da suka nutsa a harkar bariki kisha mana.
kadan tasha ta ajiye sunanan sunfi 30 mnt a zaune ba abinda yake banda kallon ta yanzu takai ma rabin jikin ta na jikin shi.
a lokacin duk yawanci samari da yan matan wurin duk a buge suke kowa jan tasa yake yi su fita.
sai da rabi ta kusan kwashe 1hr sannan ta dawo itama da alamu a bugen take kallon ta *jiddah* keyi amma ba bakin magana saurayin nata shima haka.
sai karfe 12 na dare suka bar wajen.
suna sauke su a kofar gida suka fito dukan su a motar rabi na jikin ameer saurayin ta ita kuma jiddah mansur na rike da waist din ta yana mata magana a hankali.
a nan ma sunfi rabin awa kafin mansur ya sake ta tare da fadin goben fa zan zo.
murmushi kawai tayi sannan ta rike rabi wadda har yanzu take a buge suka shige gida.
dakin inna asabe ta kai ta wadda ke ta sharar baccin ta cikin kwanciyar hankali.
fita ta koma dakin ta sai da ta cire kayan ta sannan ita ta kwanta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*BAYAN WATA BIYU*
A wannan lokacin sai dai mutane subi jiddah da fatan shiriya domin kuwa mansur ya riga ya bude mata ido da kudi kashe mata su yake kamar bai san zafin su ba waya me tsada ya siya mata ga suturu n alfarma.
idan kaga *jiddah* a yanzu ba zaka ce itace jiddan da ammar yake matukar so da tausayi ba mutanen unguwa kuwa ba abinda suke sai tsine mata da kiran ta da karuwar gida dan ita bata komai a boye.
maman salaha ce kadai ke bakin cikin irin rayuwar da *jiddah* kuma tana zargin inna asabe da hakan.
yanzu takai ba madmsur kadai take kulawa ba domin kuwa kowa burin sa a ganshi *jiddah* saboda tsabar kyanta gata kuma karamar yarinya.
burin innah asabe ya cika a yanzu domin kuwa yanzu bata yar gaban goshi kamar *jiddah* domin kuwa yanzu fanta mawa take da kudin da *jiddah* ke samowa gashi kuma ta fito da *ATM* din da ammar yaba jiddah zaron kudi take a koda yaushe tana kara siyoma mata kayan matsu.
*INA LABARIN AMMAR MUTAN INDIA*
*KU BIYO NI A NEXT PAGE*
0 comments:
Post a Comment