Bismillahi Rahaman Rahim
馃挐馃挐馃挐馃挐馃挐馃挐馃挐馃挐
1-5 馃摋
Zaune take cikin Kananan kaya riga da Siket iya Gwiwa ta saki Gashin ta iya wuyan ta Kwalliya ce sosai a fuskar ta ga wasu dogayan takalmin d'脿 tasaka Kyakyawar Gaske ce gata Fara tas ga Manyan Idan nu da Allah ya wadata ta dasu, remonte ce a hannun ta tana canza tasha Buda kofar da tabi yasa ta taso tsaye tayi kofar dakin tana Kallan mijin nata dake shigowa da babur kinshi har saida ya shigo da shi a dan karamin filin kewayen nasu ya ajeshi a inda ya Saba sannan ta karaso rumgumeshi tayi cikin farin ciki tare da fadin" El moc sannu da zuwa ya aiki? jin bai amsa ba yasa ta dago daga Jikin nashi tana Kallan shi kokadan babu Annuri a fuskar shi yana kare mata kallo fara'ar tace ta koma ciki cike da Kulawa tace" El moc lafiya Miyake damunka naga gaba daya Baka farin ciki kodai namaka wani Abu ne?" wucewa yayi cikin dakin batare da yace kala ba dafe Kai tayi cikin damuwa tace" Oh Allah yaou kuma kome nayi?" bin bayan shi tayi tana shiga tsaye ta sameshi da wayar ta a hannunshi yana dubawa Murmushi tayi dan tasan Abinda ya ke Fara dubawa kenan duk lokacin da ya shigo gidan karasawa tayi kusa dashi cikin nuna rashin damuwa tace" Yaya har zuwa yaoushe zakakai kana binciken waya ta?" wata Muguwar harara ya wurga mata sannan yace" har sa茂 Lokacin da naji zuciya ta tadaina sakamin cewa kinacin Amana ta idan bananan" kauda kai tayi lokaci guda ta Kalleshi tace" Walahi Baka kyaoutawa bantaba ganin irin haka ba kana zargina akan Abinda ko Tinanin shi bantaba yiba koda a Mafarki, miyasa kake Tinanin zanci Amanar ka?" Mtsssss ! Dan Allah gafara can ta yaya zanyarda dake bayan kina dauke da wannan Babbar Waya wacce babu Abinda bazaki'iya yi da Ita, Watakila ma wannan Kwalliyar da kikayi tini wasu sun rigani ganin ta" kai tadan Girgiza sannan tace" su wa kake Tinanin zasu gani kenan, karfa Kamanta MUKHTAR akwai Abubuwa da dama Wadanda na hakura da su badan Komai ba saidan farin Cikin ka, daga cikin Abubuwan danasa kafa nashuru farin ciki su harda Mahaifiya ta da sawran yan Uwa badan Komai ba Sabida San da nake maka amma a karshe ace cikin zargin ka zankare a gaskiya wannan ba Adalci bane kuma BASO BANE kake nunamin Kishi ne kawai na Banza da bashida tushe" wata dariyar kan labba yayi ya Zauna akan Kujera sannan ya kalleta yace" ai Wanda ake So ake kishi kenan Kinga tsabar Sanki ne yasa nake kishin ki,ke kuma Abinda kikace kinyi Sabida farin ciki na KO kuma So na to ba gaskiya bane kawai kinyi ne sabida wata manufa taki da ke kadai kike boyema kanki sani,amma Walahi BASO BANE ".
Hawayen da suka makale mata ne suka zubo cike ta takaicin halin mijin nata tace" El moc kadaina abinda kake Walahi baidace Bakada dalilin zargina, har yanzu kakasa samun hujjar da ka jima Kane nema akaina , ka hanani Wast up bare kace tanan nake samun damar yin abinda naga dama ya zamar maka kamar Ibada duba waya ta dan kaga wana kira waya kirani wayamin message wana ma message kuma duk da haka bakasamu abinda kakeso mizaihana kahutar da kanka kasama Zuciyar ka Salama kasa kani daya daga cikin Amintantun ka ka Yarda dani yardar da zaka'iya Dogon zango ba tare da Kaji dar a Zuciyar kaba" wata irin Dariya yayi kafin ya kalleta yace" Yarda dai ke din haba ai bari kiji infada maki Walahi ko kujerar Makka aka biyamin to cikin Biyu za'ayi daya,kodai azubamin natafi tare da ke,ko kuma dai nafasa tafiya ta yaya zantafi inbarki kisamu damar da zaki Fara kawomin irin Mutanen da kike mu'amula da su kuci amanata har cikin gida na ko" Kuka ta fashe dashi Jiyake kamar ta kuma Ihu cikin Kuka tace"Mukhtar miyasa kake zagina da aikata Abinda ko a baya ina budurwa baiyi ba miyasa" saida ya tsaya gab da ita yace" sabida kawai banyarda da ke ba" kuryar daki ya shiga ya cire kayan shi ya fito douche ya shiga wacce ke cikin dan karamin kewayan su dan yayi Wanka" Kuka ZEINAB tadinga yi kamar ranta zaifita ta rasa wannan hali na Mukhtar ta rasa irin Wannan kishi nashi da bayada tushe, a haka ya fito ya sameta zaune yayi kusa da Ita rumgumota yayi Jikin shi cikin Rarrashi yace" Kiyi hakuri Zeinab ina sanki Walahi bana Kaunar naga wani ko wata a kusa da ke shiyasa take miki duk wannan Abubuwa amma ba inayi bane dagangan, kiyi Hakuri kinji kidaina Kuka kitashi ki dauko min Abinci taci Yinwa nakeji" tashi tayi dan ta dauko mashi inda ya bita da kallo wani irin kucci ya sakeji da ya Tina idan fa wani ya ga wannan shirin da tayi idan fa ta dauki photo ta tura ma wani, wata zuciya ce tace mashi ina haka baya Faru ba ma tinda bata shiga social media,wata Zuciyar ce tace kaidai kaga mace kawai zata'iya yin Komai zata'iya maka rufa rufa sannan Sharrin mace ai yanada yawa zata'iya yin Komai domin ka Yarda da ita.
12/01/19 脿 22:18 - Mme Sami馃槝: 馃挃BASO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna (Meerah)
5-10馃摋
Koda ya kammala cin Abinci sudan taba kallo kafin ya bukaci da sutafi su kwanta dan yanada 1er heur a ajin yan 3e B, bayan sun saka kayan baccin su sun kwanta ne suka Fara kokarin raya Daren nasu sati daya kenan Mukhtar baya samun damar Sawke Wannan Hakkin sabida karatu daya tsananta hakan yasa Zeinab tayi kewar mijin nata sosai cire kunya tayi ta dinga nuna mashi zalamar ta akan hakan wannane yasa ran Mukhtar ya baci tsayawa yayi da Abinda yake yana kare mata kallo kafin ya ja dogon Tsaki yace mata" Zeinab wannan ba halin ki bane ba Zeinab kita bace Zeinab kinda nasani tanada kunya bata'iya nuna hadamar ta a fili sannan bata Yarda muhada ido da ita har zuwa lokacin da Komai zai kammala amma Kiduba kigani ke da kanki kike kokarin shigar dani,walahi wannan ba dabi'ar ki bace koyanta kikayi ko kuma ankoya maki" ficewa yayi daga dakin bayan ya saka Doguwar rigar shi Bandaki ya shiga ya tsarkake Kanshi koda komi bai Faru ba amma dukkan Jikin shi ya amsa cewa yana tare da Zeinab,yana dawowa baya ya bata ya kwanta tana ganin haka ta tashi itama ta garo Jikin ta ta dawo ta kwanta tana Kallan keyar shi tana Hawaye har bacci ya dauketa bata sani ba.
*Waiwaye*
MUKHTAR ABDOU: haifanfan garin Maradi kuma ma Zauna unguwar dan Tudu Mahaifin shi ba wani Babban Mutum bane Ladani ne a Massalaci dake Unguwar tasu yana Mace daya Wato Mahaifiyar su mai suna Hajara suna Kiran ta da Inna su Bakwai ne suka Ha茂fa Mukhtar ne na Biyu bayan mace daya kebima, Mukhtar ya kammala karatun shine duk a makarantar Gwamnati sabida yanayin Rayuwar babu halin da Zai'iya yin karatu a Makaranta Kudi burin shi shine ya zama malami mai koyar wa kuma ALLAH ya cika masa burin sa inda ya Fara koyar da English a Makarantar Kudi CSP Wangari kafin ya kara samun wata damar ta koyarwa a CSP Moufida amma anan iya en Lyc茅e yake koyarwa.
Mukhtar Sawrayi ne dan kimanin Shekara Talatin da Biyar a Duniya ba Kyakyawa bane sannan baki ne saidai ba baki can ba dogo ne kuma daka ganshi kaga kakkarfa Wanda Jinin shi ke tafasa Mutum ne mai sha'awar barin saje wanne ne yake dan kara masa kyaou.
ZEINAB NAFI'OU MAI KUDI: ita ma Yar garin Maradi ce wacce suke zaune Unguwar Cit茅 Casse kafin su tashi daganan su koma ADS da zama Mahaifin ta shahararran mai Kudi ne na ganina fada, yana da Mata Biyu Mahaifiyar Zeinab itace uwar gida Wato RAMATOU tanada Yaya Shida kuma Zeinab itace autar ta, Abokiyar zaman ta kuma NADIA wacce Takeda yaya hudu.
Alhaji Nafi'ou cikakken dan Boko ne hakan yasa yakeda ka'ida a gidan shi ko wajen Haihuwa bai Yarda mata sudinga mashi ita ba barkatai, Zeinab sunan Mahaifiyar shi ce ya saka mata sakamon itace mace ta Farko da aka Fara Ha茂fa a gidan tindaga kan Mahaifiyar ta har Tantin su Nadia, hakan yasa taci wannan sunan Wanda yasa aka fifita Santa akan Kowa dake gidan daga uwayen mata har Uban ba'a taba Zeinab a Kwashe lafiya saidai Babbar Sa'ar da akayi shine Zeinab yarinya ce mai matukar hakuri gata batada fada ko hayaniya wannan yasa Mahaifin ta ya kara Santa yake kuma taussaya mata dan tin Yarintar su ita da yan uwan ta zakaga suna Cutar ta amma idan aka tambayeta saita rufamasu Asiri bazata fadi laifin suba, hakan yasa ta kara shiga ran Kowa.
Kamar Yanda Zeinab ta kasance mace ta Farko a gidan su haka ta kasance Kyakyawan Farko a gidan su dama a mujalla Fara ce Allah ya hada mata Komai tanada kabrin jiki gata kuma Doguwa.
Zeinab da Mukhtar sun hadu a 脡cole wangari inda yake Matsayin Malami ita kuma daliba anan Soyayyar su ta kullu shiya Fara firta lata Kalmar so dan natsuwar yarinyar tana Birgeshi duk da kudin Mahaifin ta amma batada girman kai sabida halayar Monsieur Mukhtar yasa Zeinab ta amince da shi suka Fara tada Soyayya a cikin 脡cole har Basu san rabuwa ko bayada koyawar a makaranta yakan zo Kodan yaga Zeinab Soyayya lai karfi ta shiga tsakanin su ya na Fara mata Maganar Aure Zeinab ta amince da bukatar shi dan Yanda yake kasheta da irin Salan tashi Soyayyar burin ta kawai taga ta zama matar shi, duk da tasan lokacin baizama lalle Mahaifin ta ya mata Aure ba sabida gaba daya a lokacin ne ta shiga 4e kuma shekarar ta sha Bakwai amma haka ta rufe Ido ta tura Mukhtar gidan su dan yasamu Mahaifin ta d'脿 Maganar.
Sai a lokacin ne Mahaifiyar ta ta bijiro da Magana dan Magajiyar ta Tanti MARI Wanda yace a kama mashi Zeinab tin tana karama yana massifar san Zeinab yana so ta zama matar shi a lokacin da Mahaifiyar ta tazo da Maganar shi baya garin Yana Canada inda ya zama Babban Docteur acan, baya ga Shi akwai Yayan Abokan Mahaifin ta saidai Zeinab soyayya ta rufe mata Ido hakan yasa duk ta watsa ma Iyayen ta kasa a ido tace sa茂 Mukhtar.
Hakan ba karamin tashin hankali ya jawo b芒 anyi ta kai komo ankai ruwa rana sosai saida Alhaji Nafi'ou yaga mai Sunan mama tana neman saka Kanta a hadari dan tayi ikrarin indai akace Za'a Aura mata SAIFULLAHI ne dan Uwan ta to cikin Biyu daya zaifaru kodai ta shiga Duniya ko kuma ta kashe Kanta,bayada wani zabi daya wuce ya bata abinda takeso ya amince Mukhtar ya turo Iyayen shi sun tsaida magana akan a bari tagama 3e inyaso ta Karasa gidan mijin nata saidai ina Mukhtar ya nuna ma Zeinab halin da yake ciki bazai'iya bari harna da wata Shekara ba dan lokacin girma yazo mashi sosai yana da matukar bukatar Mace a wannan lokacin, akaro na Biyu Zeinab ta sak茅 biga kai ga kasa akan ita kawai a mata Auren ta yanzu sawrayin yace idan aka kai wannan lokacin to zaiyi Aure ya kyaleta.
Hakan ne yasa Mamar ta ta kara Tsanar Mukhtar sosai dan gani ta yi dagangan ne yake hure kunnuwan Zeinab dan ya ganta karama kuma marar Wayo, Dole aka saka Yanda Zeinab takeso badan Kowa ya soba hatta yan uwan ta babu bai Goyon bayan ta gaba daya dangi sun juyama Zeinab baya idan kacire Mahaifin ta amma Mahaifiyar ta da Tanti Nadiya ma duk sun fita harkar ta Musammam da sukaga Mukhtar cewar Mama sunan shine kadai abin birgewa, shi mummuna ga yawan shekaru ga bayada Kudi kuma Shi ba dan wani ba., haka dai Zeinab Takesa ruwa tana hadiye komi da aka fada mata har Lokacin kawo kaya yayi aka kawo da goro.
Akwati Bakwai aka kawo saidai Vide ne sa茂 Kudi da aka azo Jikka Dari Biyar da Goro kasancewar Conjen PAC ya kusa hakan yasa aka saka wata daya da rabi, ba tare da bata lokaci ba ALLAH ya kawoni ranar duk da akwai Wadanda suka fito kiri Kiri suka nuna bakin cikin su da Auran Tanti Mari bata saka Hannun ta b芒 a cikin Komai d'脿 yashafi bikin Zeinab Yayan tane dai tace babu ruwan ta idan sunga dama suje idan basuyi niya ba bazata takura Kowa ba, Saifullahi yashiga damuwa sosai yaji fa莽on rashin Zeinab Komai na Yarinyar yana Birgeshi amma yanzu Tinda tazama ta wani Dole ya Fara cire ta a ranshi.
Tin kafin a daura auren su aka turo masu gyaran daki, gidan haya ne ya kama masu su hudu ne a gidan duka suma duk sababbin aure ne Kowa da kewayen sa a cikin Kowane lungu da douche kinshi sa茂 daki ciki da falo , kayan da akama Zeinab basu shiga dakin ba Dole tasa baban ta yasa aka hurhura su aka dauko daidai da sakin su, shagalin biki kawai akayi lura da Mukhtar yayi kamar akwai cin Mutunci a tare da dangin Zeinab yasa yace damu ma abarshi tinda ba al'ada bane saidai duk da haka Mahaifin ta Sa茂da yayo masu wata Babban Mota cike da kayan Abinci Hatta Lipton da Sucre saida aka saka a ciki haka ma Attarugu da Gishiri babu Abinda aka rage su da shi.
Daren ranar da aka kawo Zeinab kokadan Mukhtar bai sawrara mata ba Haushin shi ne ya huce a Kanta kamar Wanda yayi kwana Goma ne baici Komai ba ya kuma samu Abincin mai Ray da lafiya kaga Dole ya masa cin Wulakanci da keta,to haka yama Zeinab sakamakon haka yasa taji ta tsaneshi tsawon kwana Biyu haushin shi ta dinga ji kwana Biyu tayi bata iya zama daidai da tafiya gashi babu Wanda aka turo daga gida haka shima bai turo Kowa ba Sai shi ya taya ta jinyar Kanta, saida aka dauki tsawon sati Zeinab tana gudun Mukhtar dan ba karamar wahala tasha ba Daya shiga ciki ita zata fito idan ya kwanta ita zata tashi sa茂 a kwana na tara ne kadai ya samu y'a shawo Kanta daya ce mata tana cikin tsinuwar Mala'iku da ALLAH sannan ta bashi Hakuri tare da gindaya masa Sharadi akan karya sak茅 mata keta irin ta wacan ranar.
Tinda Mukhtar ya Saba da Lasar zumar Zeinab a lokacin ne ya Fara jin wani Azabanben kishin ta yana ratsa gaba daya Illahirin Jikin shi, Kasancewar shi Wanda yake shiga cikin mata da yan mata da Samari yana ganin yanda Rayuwar take tafiya babu Amana wasu Matan auren kamar ba Matan aure ba Yanda suke sheke ayar su hakan ne yasa ya Fara Tinanin Zeinab zata'iya anfani da wayar ta wajen yin sabo wajen aika ta badaidai ba tinda Babbar waya ce K9.
Ya karbe puce kinta ya canza mata wani ya kuma hanata bude Wats up da Instagram kin da take acan ta kuma babu sabida ta faran ta mashi,saidai abin na Mukhtar baya yin baya Kullum saidai gaba, gaba daya yanzu Watan su Uku ne da Aure amma Zeinab Kullum cikin Takurar Mukhtar take.
12/01/19 脿 22:18 - Mme Sami馃槝: 馃挃BASO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna (Meerah)
10-15馃摋
Mukhtar ya hana Zeinab shiga cikin Jama'a duk wani taro na biki ko rassuwa da za'a fada mata baya bari taje saidai idan ya dawo wani lokacin ya kaita da Kanshi Hatta gidan su idan zataje saidai ya kaita y'a dauko ta shima idan zataje nasu gidan shi yake kaita koda bayada dama to zaisab Yanda zaiyi dan ya kaita kuma baitaba bari ta Wuni a canba ko wadanda Suke gida guda yanzu ya Hana ta shiga sashin kowace ace warshi mazan su zasu'iya shigowa a Kowane lokaci su tarada ita dan haka bayaso kamar Yanda ya Hana ta shiga sashin kowace Haka ya Hana ta fitowa tsakar gidan sabida maza zasu'iya Shigowar bazata, ya zama Dole idan Zeinab zata fita ta saka hijaban daya shine yasa aka dinka mata su Wanda suka sawkar mata kasa har suke sharar kasa ga nikab da safar kafa sannan ko nikab tasa bai Yarda ta fito da idan ta waje ba dan yace duk Wanda ya Santa idan ya kalli Idan ta zaigane ta, da wannan tsananin yasa Zeinab duk batajin dadin zaman gidan idan bayanan kadaici ya isheta idan ya dawo gidan saiya kakaro Abinda zaicewa tayi sannan ya mata fada.
*Cigaban Labari*
tinda tayi Sallah bata kwanta ba yan gyare gyare ta shigayi koda gari ya ida Wayewa abinda yafisan Karyawa dashi shi ta hada mashi Tea babu Madara sa茂 Indomie da Fritte tana idawa ta shiga Wanka har tagama shiryawa baitashi ba, a hankali ta Karasa Kusan gadon saida ta Durkusa cikin Tautausan murya ta Fara shafar kumatun shi tare da fadin" Yallabai Yallabai Safiya tayi Karka Makara" cikin rada take dumin a hankali ya Fara bude Ido yana ganin ta ya saki wani Murmushi tare da mutsutsuka idan shi mikewa yayi zaune a Sawke nunfashi tsaye ta Mike tace" na gama hada ruwan Wanka Abinci ma is ready" Kallanta yayi yana dariya yace" to yaou kuma hada turanceni" gira ta daga masa tana Murmushi tace" to ba Dole naba au zama da ma daukin kanwa shike kawo farin kai" kai ya jinjina mata Alamar eh tare da sawkowa daga kan gadon ya nufi bandaki.
Gaban tane kawai keta Faduwa Allah Allah take ya gama cin Abinci su rabu lafiya kafin yace ga Abinda ya Faru, tana ganin ya Mike ya dauki Jakar shi data aje mashi akan Kujera wata ajiyar zuciya ta sawke kafin ta Mike ta rakashi daga iya inda ya mata iyaka daga kofar daki yana ficewa tadawo ta tattare kwanukan ta fita ruwa ta hada ta wanke su sannan ta shiga bandaki ta wanke kamar Yanda ta sabayi Kullum sannan ta komo daki ta Zauna ta Fara kallo, gajiya da tayi yasa ta kwanta daganan bacci ya dauketa.
koda ta tashi Sallah Azahar ta farayi kafin ta soya Kwa茂 da Indomie taci ta koma ta Zauna a haka har Yamma tayi saida taji Matan gidan sun fito tsakar gida suna hira tare da yan aikace aikacen su lekowa kawai tayi suka gaissa ta koma ciki sa茂 Khadija Diya Aisha da bata fi Shekara Biyu va ta shigo tanata wasar ta.
Bayan ta kammala aikin ta Wanka tayi kamar Yanda bata Yarda yafa kazanta a Jikin ta har Kanta ta wanke dan tanaso ta kira mai Kitso gobe tazo tamata sabo tinda bata samun damar tafiya koda salon Tsap ta gama shirin ta tana Jiran Shigowar shi, sa茂 bayan Isha'i ya shigo gidan batasan dalilin jimawar ba kuma bata isa ta tambaya ba ko ta tambaya ma zauce shifa namiji ne, Tarbar shi tayi Yanda ya dace bayan duk ya gama abinda ya sabayi ya ci Abinci zaune sukayi akan Kujera 3 siter kallanta yayi sosai kafin yace" waini yanaga sa茂 wani Fari kike kina kara kyaou kodai ammana ajiya ne bansani ba" yayi Maganar ne cikin sakin fuska tare da shafar cikin ta,kunya ce tasa ta rufe Ido tana dariya tare da fadawa kan kafafun shi shafar Kanta ya farayi saidai yanajin lema ya daga Kanta yana mata wani tuhumamman kallo Kallan shi take itama har saida yace"Zeinab ruwa ne a kanki?" kai ta daga masa tana nufin eh fuska daure yace"garin yaya kenan haka ta Faru?" duk da batasan Miyake nufi da tambayo yin nashi ba ce masa tayi" ina so zanyi Kitso gobe kuma ma har nakira mai kitson tace zata zo"kin tabbata?" cikin mamaki tace" eh na Tabbata" OK kawai yace ya maida hankalin sa a TV Zeinab data kasa Fahimtar komi ce masa tayi" El moc Maganar karatu na Har yanzu kaki kace komi fa kaga anbar ni baya sosai?" kare Hade fuska yayi baida niyar amsa mata dan haka ta sak茅 cewa"Dan Allah El moc kataimaka min kabar ni naci gaba da zuwa kar karatu na ya lalace kaga dama ina tsaka da yine" saida ya mata wani Banzan kallo kafin ya Mike tsaye tare da aje remonte kin hannunshi yace" Zeinab ni ba Mahaukaci ne ba zantaba Yarda ki koma Makaranta a haka ma ya muka kare bare kinkoma Makaranta" daki ya shige inda ta bishi tana fadin" amma miyasa Bazan komaba Karka manta fa Alkawari kamin ba zanci gaba da karatu na" juyowa yayi cikin bacin Ray yace" Zeinba kinada damar yin karatu idan kinaso amma fa ba a gida na ba" cike da mamakin Maganar shi tace" kana nufin bazaka cika Alkawari daka Dauka ba, kana nufin Bazan koma Makaranta ba kenan, kana nufin indai zanyi karatu saidai nabar maka gida, kana nufin zaka'iya rabuwa dani akan wannan har Matsalar?" saida ya kalli kwayar Idan ta yace" kwarai kuwa haka nake nufi" Kallan cikin idan shi tayi kafin tace mashi" aiko zanbar gidan ka dan bazan'iya datse karatu naba, haba wannan ma ai abin kunya ne ace kana daya daga cikin Wadanda suke cin anfani Ilimi amma ace ina matar ka bazanyi karatu ba bayan kafi Kowa sanin yanke karatu na ne nayi sabida na aure ka bazaiyiyu ba gaskiya" Kafada ya daga tare da fadin" Tempie pour toi" tare da hayewa kan gadon ya barta nan.
Tajima kafin tayi bacci Har saida Zuciyar ta ta bata hakuri akan ta Zauna gidan mijinta Watakila hakan Shine mafi Alkairi a gareta shiyasa ma ALLAH ya Kaddara auren ta da Wuri kuma ma ai ance darajar mace gidan mijin ta,sannan ta Tina da furucin Mahaifiyar ta da tace duk ranar da tazo gida da sunan yaji to ina kuma zatabar gidan Mahaifin su nabar Abada, uwa Uba kuma ace sakin ta yayi dan haka zata hakura ta Zauna duk da tasan akwai kalubale sosai dan tasan Dole Mahaifin ta zaifara mata magana dama kuma magajinta NAZIR ya fada mata cewa Baban yasa mata Ido ne kawai yaga iya gudun ruwan ta,da wannan Tinani bacci ya dauketa.
kamar Yanda ta Saba bata koma bacci ba bayan sunyi Sallah hankali kwance ta kammala Soyayyar doya da Kwa茂 da Miyar sardine da lemon Orange, haka tayi Wanka gaba daya batajin dadin Jikin ta kasala duk ta rufeta gashi idan ta yi tsaye saitaji kamar jiri zaidebeta ya kayar da ita haka ta ida ta fito,tana gaban madubi tana shiryawa ta tsinkaye shi ta madubi ya duba wayar sa ya gyara kwanciyar shi hakan na nufin bayada fita da Wuri tana gamawa falo ta koma ta Zauna tana Kallan TV bata jima ba taji ana kwankwasa kofar su tinnin ta Khadija ce dan haka ta dauki Hijabin ta iya Gwiwa ta dora akan Doguwar rigar Atanfar budewa tayi tare da leko kai saidai va Khadija bace Jamilou ne Baban ta cikin Sawri tace" ina kwana?" lafiya kalaw madame, ko mai gidan yana ciki?" kai ta daga Alamar eh sannan yace mata" OK dan Allah ko zaki mishi magana zanje biyan kudin wuta ne dama" kai ta sak茅 daga masa dan hajinta ya mutsawa Sukeyi tana Tsoron kar Mukhtar ya ganta komowa tayi koda taga har yanzu yana bacci saida taji Wani sanhi a hankali kamar Yanda ta Saba ta shinshi daga baccin saida ya tashi zaune yace" tinda kikaga banta shia kinsan kenan banfita da Wuri miyasa zaki tasheni" dama Jamil ne yace namaka magana" mamaki ne ya bayyana a fuskar shi sannan yace" Bangane ba wane Jamil kin?" Jamil baban Khadija " What! Ya fada iya Karfin shi yana sawkowa daga kan gadon" Zeinab kunnuwa nane basuji daidai ba Komai kina nufin ke kika bude kofar kuma a haka kikaje fuskar ki a bude?" sa茂 lokacin Zeinab ta gane baram baramar da tayi shiru tayi tana Jiran hukuncin ta jikinta duk ya dauki bari"dake nake magana kinajina kinyi shiru" Tsawar daya mata ce tasa ta ja da baya tana fadin" Dan Allah Kayi Hakuri El moc walahi bansan shibane shiyasss''' gigitancen marin daya sawka akan fuskar ta ne yasa bata Karasa ba dafe Kunci tayi duk maganganun daya fada mata bataji ko Daya b芒 sabida ganinta da jinta duk sun dauke.
fita yayi inda ta fada kan gado Zuciyar ta na mata kuna, yana shigo y'a sak茅 dora fadan daga inda ya tsaya bata kula shiba har yayi ya gajiya ya shirya ko takan Abincin datayi baibi ba ya fita.
Zazzabi ne ya rufe ta hakan yasa koda mai kitso tazo sa茂 manya tace ta mata dan dai karta taxi hakan nan, haka ta wuni da Zazzabi gashi batayi ajiyar koda Parac茅tamol ba kuma babu yaro da zaisawo mata tayi Kiran wayar Mukhtar amma bai Dauka ba dan Tinanin shi hakuri ne zata bashi da haka ta galabaita da Zazzabi nan sosai,baidawo gidan ba sa茂 misalin 21:40 ba tare da ya kula taba ya shiga yayi wanka saida yagama kimtsawa sannan ya zaune kusa da Ita fuska daure yace"ko zaki'iya kawomin Abinci na?" faruwar gaban tane taji ya kara tsananta cikin Sarkewar murya tace" Kayi Hakuri banda gaba nayi ta Kiran ka dan infada maka banda lafiya amma Baka Dauka ba" wani kallo ya watsa mata yace" to yanzu ya kikeso ayi kenan a wannan Daren yanzu ina zan samu Abinda zanci?" cikin Sanhin murya tace" Kayi Hakuri dan Allah bari na soja maka koda kwaine da Indomie tinda Jikin ma yayi Sawki" batajira abinda zaice ba ta wuce gaz kinta Fara fiddawa kafin ta Fara aikin gadandan.
12/01/19 脿 22:18 - Mme Sami馃槝: 馃挃BASO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
15-20馃摋
Indomie da Kwa茂 ta hada mashi gaban shi ta dire tiren ta dauko Ruwa da exotic a yar karamar frige kin su ta aje mashi kasa ya sawko ya mike kafa daya ya fara ci zaune tayi itama kasa tana Kallan shi, kallanta yayi yace" kefa bazaki ci ba ne?" kai ta Girgiza gira ya daga Alamar mamaki yace" mikika ci to?" murya kasa kasa tace" Komai kawai dai bana san ci ne?" ajiye Cokalin Hannun shi yayi yace" kawai ba Magana bace kifadamin dalilin da yasa bazakici ba" wuyanta tanan shafa kafin ta Kalleshi da Manyan idanun ta wanda suka cika da Kwalla tace" banajin dadin jikina" matsawa yayi kusa da ita ya jawota tare da dora hannunshi akan wuyanta Zafi sosai yaji kwalo ido yayi cikin razani yace" Zeinab haka abin yayi tsanani dama amma kikayi shiru kikaki fadamin kinaso ki illatar min da kanki, kinga tashi mutafi Asibiti ya duba minke ko Allura ce a miki" tsaye ya mike yana kokarin daga ta kara Narkewa tayi da taji maganar Allura cikin shagwaba tace" a'a kabar shi ni basai munje Asibiti ba ma kawai dai kasamomin magani idan nasha zan warke" girgiza kai yayi yace" a'a ban yarda ba tashi mutafi kawai idan kika sha Magani zata iya dawowa ai dan haka kitashi kawai matsoraciya allurar ce bakiso Shiyasa" hawaye ne suka fara taho mata ganin haka yasa yace" to Shikenan naji zantafi na Siyo maki amma kisani idan har ta dawo to saidai mutafi Asibiti dan Bazan Yarda da wannan Shaye Shaye Maganin ba barkatai" kai ta daga Alamar ta Yarda haka ya fita dan nemo mata Maganin, ganin ya fita ta rufe mashi Abincin shi tana mai fadada murmushin fuskar ta har yanzu tana tsananin san Mukhtar kuma shima yana Santa Kishi ne kawai gareshi wanda yake san kaishi ya baro shi.
bayan ya dawo ya kawo mata maganin tasha taci Sanduite kin daya taho mata da shi dan karta kwanta da yinwa shikuma ya kammala Cin Abincin shi kafin nan suka kwanta.
kida sukayi Sallah bai bari tayi Wani aiki ba yace ta kwanta ta huta hakika taji dadi sosai akan kulawar da ya nuna mata daren jiya zuwa yanzu, bacci tayi sosai shikuma da gari ya waye Falo ya Zauna yana kallo dan bai cika baccin safe ba kuma yaou bashi Cour ganin Goma na shirin yi yasa ya tada Zeinab tare suka shiga Wanka suka fito Suka shirya bakin Zeinab Yaki rufuwa dan Rabon da haka ta faru harta manta suna fitowa Mukhtar da kanshi ya buga Kwa茂 ya soya masu tare dankalin turawa ya hada masu Tea sannan sukayi break.
Kallanta yayi yace" tashi ki shirya zan kaiki gida daganan na wuce dan innabar ki nan zakiyita bawa kanki wahala ne ki dauko waccen aiki ki dauko waccen" farin Ciki ne ya bayyana a fuskar ta saidai tinawa da tayi ya tsani idan zata fita yaga tana zumudi hakan yasa ta hadiye farin cikin ta cike da san basarwa tace" amma da ka barni ai idan kace karnayi aikin ai bazan yiba" Wani irin murmuchi yayi Wanda shikadai yasab fassara shi yace" kinga kiyi abinda nace kawai" to " tafada ta shiga kuryar daki saida ta daka Wani Tsalle tare da jujjuyawa tana fadin" wai bayan wata uku yaou zanje gidan mu na wuni" kayanta ta dauko hijab safar kafa da nikab wacce ko ido ba'a gani ta saka Tsap ta fito ta sameshi mikewa yayi yazo kusa da ita saida ya duko da kanshi ga Hijabin ta ya shinshina yaji babu kamshin turare saidai kamshin da yazama kamar dashi Aka haifeta alama yamata da kai sutafi, bin bayan shi tayi tana fada a ranta*El moc kenan taya kake Tinanin zan saka turare ai saidai in banasan tafiya* da haka suka kama hanyar gidan su Zeinab Tinanin ta duk ya koma ga Mahaifiyar ta ko Wace irin tarba zata mata wacce ko tare da Mukhtar suka tafi kai tsaye sudawo sai Ray ya bace bare kuma yaou zata wuni, da haka suka kai gidan Mukhtar ya tabbatar yanzu Mahaifin Zeinab baya gida Mahaifiyar ta kuma bazaiji dadin abinda zai fito Daga bakin taba dan haka ma bai shiga ba yace ta gaishe su idan ya dawo daukar ta zaishiga su gaissa, bata damuba itama dan tasan ranshi zaibace idan yashiga, har ta juya zata shiga ya kira sunanta " Zeinab " juyowa tayi tare da tahowa Hannu ya tara mata yace" wayar ki zakiban" cike da mamaki tace" yaya waya ta kuma?" eh ita nake nufi ko dan bani nasaya ba banda yancin da zan amsa?" cikin inda inda tace" a'a Walahi na daiyi mamaki ne da kace inbaka" tayar da B芒bur kinshi yayi Hannu tasa sacs kinta ta fiddo ta Mika mashi, karbar wayar yayi yasa Aljihu ya sak茅 karbar sacs kin tata dubawa yayi dan yaga abinda ke ciki daga makullin dakin su sai yan canjin ta sai karamin littafin Husnul Muslim, Wani banzan kallo ya bita da shi ya burka B芒bur kin shi ya barta nan kai ta girgiza cikin rashin jin dadi ta shiga cikin Gidan.
Zaune suke a Babban Falon da yasha kayan more rayuwa kala kala da gudu Fadila ta tarbe ta tana Murnar ganin ta Dauke ta tayi sama sunata murna kafin ta karaso da ita da karfi ta fada saman Kujera cikn Massifa Mahaifiyar tata tace" wannan wane Iskancin ne kuma idan da haka ake zaunawa da karfi da ke zaki samu Kujerun a haka, koda yake ma na manta Ashe Bakuda irin su Dole idan kikazo kiyi haka Kodan kiji laushi" ta karashe maganar tare da tashi ta shige dakin ta tabar sunan, binta tayi da kallo kafin ta kalli tantin tata tace" Tanti ina kwana" lafiya kalaw hajia ya kike ya gida da mai Gidan?" lafiya kalaw Tanti ina su Yusra duk sun tafi 脡cole ki?" duk suntafi saidai idan sun dawo" Tanti Abba fa ko ya fita?" ah ai neman kinsan bazaki samu Abban kiba yanzu ana wajen kujuba kujuba" dariya tayi tace" ai yaou ina nan har sai Abba ya dawo" da gaske kike kinga ko ai da kin kyaouta dan kullum maganar ki yake yana san ganin ki shima" nasani dama Tanti zanjira har sai ya dawo" to kinga kafinan tashi kije ki gaida Mahaifiyar ki kinji ko" tashi tayi rike da hannun Fadila suka shiga zaune ta samu Mahaifiyar ta ta a bakin gado tana danna wayar ta tin kafin ta karaso ta Mike tsaye cikin fada ta fara nuna ta da Hannu tana fadin" wuce karki shigomin daki , ko ban fada maki bani ba ke ba ki ficemin daga daki kodai ki koma Gidan tsinannan mijin naki ko kuma kije ki Zauna can amma ni va Wuri na kika zoba Shashasha kawai yar dadi miji wacce ta zabi namiji akan farin cikin Iyayen ta kije zaki gani walahi tinda kikace Iyayen ki Bazasu rintsa ba sabida bakin cikin ki to walahi kema bazaki rintsava kuma bazaki samu kwanciyar hankali Gidan auren kiba har sai kin gudo da da kafar ki ki amshi zabin mu lokacin kuma tu est d茅j脿 trop tard" rufe kofar Dakin ta tayi da karfi Dole Zeinab ta dado Falo ta zauna Kuka ta fariyi sai Tanti ta ta fara rarrashin ta cikin Kuka tace" haba Tanti kijifa abinda mama take fadamin a Matsayin ta na wacce ta Haifi bakin ta ba karamar Massifa a gareni bakin ta daya tak daya yake da bakin baba so goma amma duk da haka har yanzu bansamu sa albarkar ta ba kullum sai mummunan fatan da baki takemin har tana fatan kar nasamu kwanciyar hankali a Gidan da Kowa mace anan ne take takama dashi take kuma fatan samsamu ingantaciyar soyayya da farin cikin mai dorewa" ( ALLAH Sarki ).
da kyar ta shawo Kanta ta kwantar mata da hankali haka ta wuni a dakin tantin ta kwance Tanti ta lura da Zeinab kamar tanada ciki saidai bata fada mata ba gani da tayi ita kokadan babu wannan a ranta, har bayan Sallah Magriba sannan Abba ya dawo lokacin ne Zeinab taji dadi dan tinda ta shiga dakin Abban bata fito ba Hira sosai Sukeyi suna nishadi na da da Uba Abba ya tambaye ta zaman Gidan nata tace babu Komai tare da Abba sukaci Abinci har saida Mukhtar yazo lokacin ne fadila tace da ita Za'aje saida Zeinab tayi ta Rarrashi sannan Tanti tabari suka tafi tare da sa bakin Abba, ta shiga dan tama mama ban kwana saidai dakin nata a rufe bata bari ta ganta ba har suka tafi...
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
馃憠 Yan Uwa ku gafarce ni a bisa kuskuren da nayi馃憦馃憦馃憦 Akasi ne馃憟
Na馃摎
Samira Harouna
20-25馃摋
Kayan shi ya shiga cirewa yanaso yayi Wanka cike da Ladabi Zeinab tace masa" Grand Fr猫re mikake so Kaci na dafa maka dan ni naci Abinci tare da Abba,banajin yinwa" Murmushi yayi yace" ahan kenan wayo kikamin kikaci Abinci tare da Abba kika manta da mijin ki, ni kuma lokacin da zanci nawa abincin tare da Inna saida na tinaki a Rayna nace ko kinci abinci yanzu sabida ina Tsoron Allah ya kamani da Hakkin ki" dariya ce ta kwace ma Zeinab tace" oho kenan bani kadai ba za'a hukunta ba harda kaima" umm! to shikenan nayafe maki kema nasan kinyafe ko?" kai ta daga masa alamar eh sannan ta sak茅 cewa" to fadamin mizakaci?" a'a kibarshi nima naci abinci kije ki huta kawai, ya jikin naki da sawki dai ko?" umm da Sawki Sosai ma" to yayi kyaou" ya fada lokacin da yake kokarin fita daga dakin.
bayan ya fito ita ma ta shiga wankan taayi sannan sukayi zaune suna kallo har zuwa karfe 23:30 kafin suka kwanta ita da fadila a kuryar daki shi kuma a Falo akan karamar katifar da Zeinab ta shinfida mashi, har gari ya waye.
Zeinab nata hada hadar abin Karin kummalo Mukhtar na shiri shima sai fadila dake tare da Zeinab tana wasa Kiran wayar ta akayi sai lokacin Mukhtar ya Tina baimaida ma Zeinab wayar taba dan haka yafito daga dakin ya Mika mata dan yaga Sunan kawar tane Haulatou, cike da mamakin kiran da Haulat kin ta mata a Safiyar nan ta dauka da Sallamar ta sannan suka gaissa, a daya bangaren ne akace,
Haulat" dama banace maki idan nazo zan kiraki nabaki su Muhssina ba to gasu sai kifada masu Abinda ya hanaki dawowa 茅cole tinda ni nace masu dadi aure ne amma sunki yarda"
Zeinab " ni dai narasa wannan jaraba da Kuka takuramin sai kunji abinda ya hanani dawowa, nace maku Zandawo nanbada dadewa ba Insha Allah"
Haulat" banga alama ba aiba yaou kikayi aure ba yanzu ma haka nasan anfara amaye amaye kinga monsieur zaice sai kin haihu idan kika haihu yace sai kin yaye kafin nan kinsamu Wani cikin da haka zaiyita miki yawo da hankali walahi"
Zeinab " to inma hakane saime Mijina nefa kuma ina san shi ina san haihuwa da shi kinga ai ba Wani Abu bane, kinga ni kibani sawran mugaissa kawai aiki nake" Muhssina Aka ba suka gaissa sosai suna cikin magana wani dan ajinsu Okasha ya shigo Haulat ce ta fada mashi suna magana da Mutumniyar shi Zeinab cikin zumudi ya roki Alfarma abashi su gaissa, sun gaissa da Zeinab jikin ta duk a darare tanayi tana juyawa cikin alamun rashin gaskiya tace" Okasha dan Allah kabawa Haulat Waya" cikin Zolaya yace" Zeinab kin manta da karatu ko, Zanzo Gidan ki da kaina nama Monsieur kin magana akan ya barki kidawo Makaranta Cin amarcin ya isa Haka nan" cikin sawri Zeinab harda alama da Hannu kamar tana gaban shi tace" a'a Dan Allah ka rufamin Asiri karkazo kaidai kabari nadawo nace, kawai kabata wayar" tin kafin ya Mika mata Zeinab na juyowa ta Sawke idan ta akan Mukhtar daya Hade Ray kamar Bani shedan sakin wayar tayi ta fadi daga Hannun ta jikin tane ya fara Rawa ganin haka yasa Mukhtar ya tako har inda take kafin tace wani Abu ya Dauke ta da Wawan mari kuncinta kawai ta dafe batare da tayi kara ba, Fadila dake zaune tana wasa Tsoro ne ya kamata da karfi ta fashe da Kuka ta Rungume Zeinab iya Karfin ta wucewa yayi ya barta tsaye va tare da yace kala ba.
Tinda ya fita bai sak茅 dawowa Gidan ba, da kyar Zeinab ta Rarrashi Fadila Kuka ta dingayi ita sai anmaida ta gida har saida ta goyata sannan tayi Bacci, da Rana sai gida Mukhtar yaje yaci abinci Inna ta lura yana cikin damuwa dan haka saida ya gama ya nutsu cikin kwanciyar hankali tace" Mukhtar lafiya Miyake damunka naga gaba daya ranka a bace yake?" saida ya wani cilla Ido kafin yace" babu Komai Inna kawai dai wani dan karamin soucis ne" Mukhtar nifa banasan ganin ka cikin irin Wannan yanayin, banaso fa kullum ina gaya maka Sawrin Fushi babu Abinda yake haifarwa sai aikin da nasani,haka ma Sawrin Hannu wata rana Zai'iya jefaka cikin matsala Dan Allah karage wannan zafin Zuciyar kaji ko mai Babban suna" to kawai ya fada ya tashi ya Tafiyar shi.
Bayan Sallah Isha'i ya dawo gidan shima dan yasan zai maida Fadila gida ne koda yazo suka tafi dagacan baidawo ba sai 00:30 Zeinab harta gaji da Zuba ido bacci ya Dauke ta Akan Kujera bai ko bi ta Kanta ba ya shiga ya fito yayi wanka ya kimtsa yayi Kwanciyar shi a daki, koda Zeinab ta Farka Karfe 06: 10 dan haka ta farayin Sallah bayan ta ida ta shiga kuryar daki inda ta sameshi zaune yana lazimi Zaune tayi a bakin gado tana kallo har ya gama, gabanta Faduwa kawai yakeyi ga Zuciyar ta daketa Rawa tana bugawa kamar zata fasa Kirjinta ta ta fito waje kasa ta durkushe cikin Sarkewar murya tace" El moc Dan Allah kayi,,,,,,mtssss! Dogon Tsaki yaja tare da tashi ya koma falo, bin bayan shi tayi jiki a sanyaye ta sak茅 durkusawa zatayi magana cikin bacin Ray da tijara yace" da zaki Adana hakuri watakila tamiki anfani nan gaba amma ba yanzu ba karki soma cewa zaki bani hakuri dan hakan sai yafi konamin ray, Zeinab walahi kinbani mamaki kinci Amana ta bantaba tinatib haka daga gareki ba" wucewa yayi kurya ya bartanan durkushe Kuka ta fashe da shi dan shine kadai mafita data rage mata.
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
25-30馃摋
Tana cikin hada abin Karya'wa ya fito cikin shirin shi ya fita b芒'tare da'ya kulata ba,tsayar da aikin tayi ta koma d'aki ta'aza wani sabon Kuka, har'saida rana ta fito sosai kafin ta tashi ta samu abin Karya'wa taci.
Haka ta'wuni jikin'ta d'uk babu k'wari sai kasala da tsargin yawu take har'dare Mukhtar bai'dawo ba,koda ya shigo kamar kullum wanka yayi ya kwanta a'binshi, wasu Hadan'dun kayan bacci Zeinab tasa'ka inda yake k'wance ta fuskan'ta ta sak茅 durkusawa dan'taba shi hakuri,Yana ganin haka ya sawko daga kan Gadon dan'yabar mata d'akin, da sawri ta Mike tsaye ta'sha ga'banshi tare da rike hannuwan shi duka biyu'n, k'asa magana tayi sai ido data zuba'mashi cikin daka'kkiyar murya yace,
"Sake'ni " kai'ta girgiza masa cikin Kuka tace" dan Allah Grand Fr猫re kayi Hakuri ka sawra'reni nafada maka abinda ya faru" kallan'ta yayi sosai kafin yace" ki'fadamin me Zeinab, kinga,,,,, bai'karasa ba Zeinab ta fada jikin'shi tana Kuka, cikin zafin nama ya dago da kan'ta daga jikin'shi bakin'shi ya saka a'nata ya fara tsutsa da iya karfin'shi , ta'ke suka fita hayyacin'su da haka Mukhtar ya manta da Komai sabida Zumar Zeinab da'yake lassawa.
Yaou Zeinab da'kanta ta'ke saka'ma mijin'ta kaya har'takai ga Balla masa botle 'kin rigar'shi ba'tare da ya kalleta'ba, ta lura da hakan saidai ta rasa dalili, ko kunya ya'keji? Ko'ko hushin'ne har'yanzu? Oho!
Ba'tare da ta kalleshi'ba ita'ma cikin Tautausan murya tace" Grand Fr猫re, i am very Sorry for Evrything's, is not my Faulte, but I promise i can't repeat' again by God Gr芒ce" tinda tafa'ra maganar yake kallan'ta cikin tsananin mamaki, dan baiyi Tinanin zata'iya turanci haka'ba, Baisan Sanda dariya ta kubuce masa ba kallan'ta yayi yace" Zeinab dama kin'iya turanci haka?", "Ashe'dai Zamuje da'ke" bata kalli kwayar idan'shi ba tace" to ai ya'zama Dole na na'iya ina matar theather" kai ya girgiza yace" haka'ne kam, gaskiya kinyi kokari sosai" Thank you"
Murmushi yayi yace" da'alama an'kusa daina haussa a gidan'an ko?" tare sukayi dariya har'suka Karasa Falo suka gama Karyawa har'ya tashi zai'fita sannan ya kalli Zeinab da k'yaou yace" Zeinab ina sanki Dan Allah ki'kiyaye duk wani abu da zai'dinga sani Sawrin Hushi akan'ki,kinji" Insha Allah El Moc,bazan'sake ba" Good" ya fada tare da sumbatar'ta a baki, ta rakashi har'ya fita sannan ta dawo d'aki, farin ciki karmar zai'kashe ta Soyayyar Mukhtar na'kara ratsa duk ilahirin jikin'ta, a cikin farin ciki ta wuni ranar,
Mukhtar ya dawo da rana ya'ci abinci ya sak茅 fita, haka'ma dare sunyi'shi cikin farin ciki.
Washe Gari, Zeinab ce k'wance akan Kujera tana kallo bacci yana'san d'aukar ta, NAZIRU Yaya ne a wajen'ta wanda take bima.
k'wank'wasa mata k'ofa, cikin kasala ta tashi ta b'ude, da farin ciki ta tarbe'shi suka gaissa ya shigo ciki, bayan sun'gaissa ya fada mata Haihuwar Kanwar ta'ta Diya ta Biyu ga Tanti Nadiya wato AIDA.
Tayi farin ciki sosai ta'kuma ce mashi zata'je ta'gano B茅b茅, a nan'ne taga yar karamar wayar'shi TECNO tace ya bata, bai tsaya lissafi'ba ya karbi tata ta amshi tashi, a ganin'ta tarage matsalar da'ke shiga tsakanin ta da Mukhtar Musammam a'kan Waya.
Saida ta'bari yayi d'uk abinda ya dace ta'tabbatar ya samu Nutsuwa sannan ta'fada masa Haihuwar A茂da, ya taya'ta murna sosai ya kuma'ce ta'shirya gobe tinda baya fita da Wuri idan zai'fita sai su fita tare, murna sosai Zeinab tayi dan batayi Tinanin haka'ba, sai lokacin ne ta nuna ma shi sabuwar wayar'ta, budar bakin shi cewa ya'yi....
"Sabida Abban'ki ya saya maki ita shiyasa bazaki'iya shawar'ta taba,ko kijira umani'na?" cikin sauka'kar muryar'ta tace" kayi Hakuri Dan Allah, ko'kadan ba haka'ba bane" ba'tare da'ya kalle'ta ba yace" to miyasa kika canza'ta?" cikin Fara'a tace" naga muna samun matsala ne da waccen shiyasa na sauya'ta" wani Shu'umin Murmushi yayi yace" Zeinab a'she har'yanzu baki'da Wayo kur'ciya na damun'ki, in'banda abinki Waya ai waya'ce, zaki kira da wannan za'a kira'ki, zakiyi message da'ita za'ayi miki, to miye banban'ci a ciki, kinga Zeinab ni matsala'ta bawai da waya bane a'a da'ke ne ke kanki gaba daya" maida kallan'shi yayi ga TV yana kallo, Zeinab kam ta ma rasa mi'zata ce dan haka ta yi shiru har Lokacin k'wanciyar su yayi basu kara wata magana'ba ba.
K'oda suka tashi da safe kamar ba suba cikin farin ciki sukayi w'anka tare s'uka shirya tare sannan sukayi break, bayan nan suka kama hanyar gidan A茂da, har kofar gida Mukhtar ya'aje ta bayan ta sawka yace mata" Zeinab ki'kula da k'anki ki'rike min Amanar k'anki, sannan ban'yarda ba kije ki'cire hijab kiyi'ta yawo haka'nan a cikin gida,bare kuma ki'fito waje, kinji'ko?" kai'ta girgiza tace" amma Grand Fr猫re ai'naga d'uk mata'ne a ciki ko?" Eh! Mata'ne amma yanzu mata nawa ki'ka sani masu kamar maza, suna biyan bukata da yan'uwan su mata, kedai kiyi abinda nace kawai" cike da Gamsuwa tace" Insha Allah zan'kula maka da kaina" OK prend bien soin de toi,compris?" Murmushi ta'sakar masa duk'da ba ganin fuskar'ta yake'ba,sannan tace" J'ai Compris " har'saida ta shiga ciki sannan ya tayar da B芒bur kin'shi ya tafi.
Koda ta'shiga ta samu sawran yan uwan'ta duka suna'ta hira, suna ganin'ta suka sheke da dariya, haushi'ne ya kamata dan'tasan da ita suke saidai abin takaicin d'uk kannan'tane babu sa'an ta a cikin su dan haka ta ki kula'su, saida suka gaissa da Aida ta'karbi Jaririyar tana mata wasa, FAUZIYA cike da Raini tace" haba Zeinab wai'ke dan Allah a'cikin gidan'ma bazaki hidda kayan'an kisha Iska ba duk kinbi kin'rufe jikin'ki ana Rumtuma wannan zafin" kafar Zeinab ta'jawo ta cire mata safar kafar'ta tana shirin cire mata hijab Zeinab tace" ke Dan Allah ki'rabu dani ina ruwan'ki ne?" baki sak茅 Fauziya tace" ah! Kema ya koya'maki wannan mur'tukewar ko,to Allah ya shirya'ku" Zeinab ce tace" Ameen idan da gaske ki'ke" A茂da dake'ta masu dariya tace" shi'kenan Hade Ray yake Fauziya?" cike da kara kambama maganar tace" kam,walahi sai kingan'shi a 茅cole baya dariya sai yaga'dama, ko Murmushi bai'cika yiba walahi, tinda Zeinab tabar 茅cole ya sauya'mamu" wani irin dadi'ne ya kume Zeinab hakan ya tabbatar mata mijin'ta Yana kula mata kan'shi ko bata tare da'shi, A茂da ce tace" yo'ai taji dadin'ta walahi, yaou ace kasa'mu wanda zai'bada shedar mijin'ka baya kula mata a waje ai'ba Karamin abu bane, da'nice ita da'naji dadi walahi" Zeinab ce tace" Voil脿 Yer Uwa fada'mata dai, ita dan bata'san mi'ake cema miji'ba" Tsaki Fauziya tayi tace" kudai kuka'sani kishin tsiya ne da'ku shiyasa, to mima zamu'yi da mazajen na'ku, daga mai tsoho sai'me Katon kai kamar dan gwara'wa" duk'da magana'ce ta fada'masu amma bai'hana suka dara'ba haka sukaci'gaba da hirar'su har yamma.
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
0 comments:
Post a Comment