Sai'da suka kammala ma Aida d'uk aikin gidan sannan Zeinab ta shirya ta Zauna ta'na Jiran zuwan Mukhtar, lokacin da yazo ya shiga ciki ya'ga Jariri sannan suka fito, a kofar Gidan suka'ci karo da Maman Zeinab tare da Tanti sun'zo ganin b茅b茅 su'ma, saida Mukhtar ya Durkusa dan girma'mawa ya gaishe'su amma Mama tayi banza da'shi,Zeinab ma gaishe da ita ta yi amma budar bakin ta cewa tayi" ke! bance ki'fita harka'ta ba idan ban wuni ba da zaki ganni?" kafin Zeinab tayi magana Mama tace" Dan Allah gafara'cen Sakariya k'awai" wuce'wa tayi tabar'su nan sai Tanti tace" Dan Allah kuyi hakuri kunji kar'ranku ya'bace, wata rana sai labari" godiya suka'yi suka wuce, Zeinab kamar ta yi Kuka takeji, ace sabida ka auri Wanda ranka ke'so shike'nan sai ka zama Abokin gabar Mahaifiyar ka, da haka har suka'kai gida babu wanda yayi magana a cikin'su...
saida tadan hada mashi Abinci mai s'awkin sarrafawa sannan sukayi kallo suka kwanta.
Washe gari, Zeinab ita kadai'ce zaune a d'aki ta'gaji da zama sosai, hakan yasa ta sanyo hijabin'ta ta fito tsakar gida, su AISHATOU da ABIDA ta samu suna'ta hirar'su saida suka gaissa sannan ta Zauna akan Tabarma suka fara taba hira cikin nishadi....,
Karar B芒bur kin da Zeinab taji'ne yasa ta tashi da gudu ko ta'kalama bata tsaya d'auka ba ta rumtuma a guje da k'aton hijabin'ta kamar zata ta'shi sama, d'aki ta'shiga ta cire Hijabin da s'awri tayi zaune kamar ba ita'ba, shiru shiru babu Mukhtar babu labarin sa fito'wa tayi filin'ta anan taji muryar SANI hakan ya tabbatar mata da Mijin Abida ne ya shigo, ajiyar zuciya ta s'awke ta koma d'aki ta zauna, dan k'unyar sak茅 fita ta'keji, su Aishatou Kallan mamaki su'kabi Zeinab da'shi ,sauda su kaga Sani ya shigo suka fahimci abinda Zeinab ta'guje ma, ta d'auka mijin ta'ne, sun jinjina Al'amarin sosai hakan yasa suka jima suna hira a'kan zaman Zeinab da Mukhtar cikin murya kasa kasa.
Ta kammala shirin'ta Shigo'war shi k'awai ta'ke jira, ta najin B芒bur kin'shi ta tafi'to ta tarbe sa d'aki suka shiga ya Zauna ta kawo masa Ruwa, zaune tayi tana kallan'sa kafin ya kalle'ta yace" wayar ki?" mike'wa tayi ta d'auko wayar ta Mika mashi ba'tare da taji Wani Abu a ranta ba dan hakan ya zamar mata jiki, saida ya duba Kap kafin ya kalle'ta yace" Zeinab kina goge abu a wayar nan ko?" cikin ladabi tace" a'a wallahi ban'taba ba,tinda na'san kana dubawa" kin Tabbata?" eh!" ka'fada ya daga yace" Allah ya'sa da gaske ne" Murmushi kawai ta'yi, Abinci ta k'awo masa ya'ci sannan ya yi d'uk abinda ya saba'yi.
Abinda Zeinab bata'taba tinani ba'ne ya Faru, batayi zatan Mukhtar zai'sake barin ta taje gidan Aida ba idan b芒 ranar suna ba,amma k'o'da ya shirya zai'fita yace ta tashi su'tafi tare, farin ciki baya misaltuwa wajen Zeinab har suka'kai gidan bakin'ta bude yake.
Ta samu su WASILA da ANISSA a gidan kannan Saif, gaishe'su tayi amma su'kayi banza da ita, ita'ma bata sak茅 kula suba dan suma suna cikin makiyan'su, ta d'auka abin zai'tsaya iya haka amma ina sai suka fara mata habaici iri iri, duk tayi banza da'su Wasila ce tace" humm! ai wallahi d'uk wanda yace baya k'aunar mu, to banga dalilin da zai'sa muci gaba da zama da'shi ba" Anissa ce tace" ah to ai'ke ki'ka k'ula ma da tsiyar ta wallahi, dan'ni idan na raina Kassuwa ko sabtun ta bana'ci, ita bata zabi Namiji a'kan yan uwa ba?" to wallahi muje zuwa in'dai mutan'mune zasu mata halin na'su" Wasila ce ta harari Zeinab sannan tace" ta'ina zan'iya kwana Mahaifiya ta na hushi da'ni, ai bazan'iya ba, amma ita dadi miji babu ruwan'ta Mahaifiya na kwana da bakin cikin ta amma ita ko a jikin'ta dan H'auka" Tsaki su'kayi a tare, hakan ba karamin Sosa ran Zeinab yayi'ba, cikin tattausan murya tace" babu Mahaifiyar da'take kwana da bakin cikin yayan'ta Musammam ma ni da na zama Auta a wajen'ta, ku yan uwa na'ne Dan Allah ku rike girman'ku" Anissa da'ma jira ta'ke dan haka ta Mike cikin Massifa tace" ke Zeinab wa'kike fadma wannan maganar,?" autar banza autar wofi tinda ki'kasa sharewa Mahaifiyar ki hawayen'ta ki nuna baki k'aunar ta ita da yan uwan'ta" Zeinab bata kula su'ba har Allah ya k'awo Maman ta gidan tazo ta k'awo ma A茂da Maganin nono, tambayar su tayi miha'ke faruwa, anan suka fada mata, maimakon ta k'ashe Wutar sai tace" Auta fa ki'ka ce, ai ni tini nayi Wuri na aje'ki da zaki cire kanki a sahu'n yaya'na da yafi miki Alkairi, ai Tinda kina nuna kinfi'san wannan banzan mijin naki akai'na, nima na'daina sanki dan haka kiji ki kara'ji ni Ramatou wallahi babau'ni babbu'ke", kuka Zeinab ta'fara sosai hakan yasa Mama ta sak茅 cewa" na'fada maki ki dai'na shiga har'kata da na yaya'na dayafi'miki" cikin bacin Ray Zeinab ta tashi dama bata'aje Komai ba tinda tazo ficewa tayi tabar gidan tana kuka, saida ta fita ta Tina Mukhtar ya kawo'ta, Adaidaita ta tare ta shiga kai tsaye gida ta tafi, tinda ta shiga d'aki suka ta sak茅 a'zawa sabo tsawon lokaci.
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
35-40馃摋
Haka ta wuni jikin ta d'uk babu k'wari sai kasala haka har takammala ai'kinta, tana gama shirya'wa k'wance tayi a'kan gado daga bacci ya d'auke ta bata Ankara ba, Mukhtar da ya shigo a kufule kai t'saye d'akin ya shigo cikin bacin Ray, Zeinab d'ake bacci cikin jin'dadi taji an'jawo kafar ta da karfi har saida ta fado daga kan gadon cikin Firgici da t'soro ta saki wata kara da s'awri ya rufe mata baki dan kar makotan su suji, zaune yayi bakin gadon ya saka kafafun shi ya sata t'sakiya ya t'aushe kafafun ta da kafar sa Kallan da yake mata ko'kadan babu wasa da karfi yace mata" ina kika'je, miyasa kika'ki d'aukar waya ta?" diririce'wa Zeinab tayi dan har'ga Allah ta'manta da Wayar ta tinda tazo gidan bata Buda Jakar ta ba, tana cikin piki piki da ido ne taji Wani G'oron mari a fuskar ta dafe Kunci tayi cikin kidimewa ta zabura tana kokarin gusawa daga wajen cikin Hushi ya finciko'ta ya sak茅 k'wada mata Wani marin yana fadin" bazaki fadamin ba, ni zaki Mayar dan Iska Zeinab ? " cikin kuka ta fara magana" a'a wallahi babu in'da naje gida nazo tin'da rana kuma ni ni wallahi", ta rasa abinda zatace k'awai ta sak茅 fashewa da kuka, shako rigar ta yayi da karfi yace" karya kike sai kin fadamin gidan Uban da kika'je, naje gidan A茂da amma akace da zuwan'ki da Tafiyar ki bakifi Minti goma sha'biyar ba, dan haka wallahi kifadamin in'da kika'je ko kuma jikinki ya fada maki" kai ta dinga Girgiza'wa tana fadin" a'a Dan Allah kayi hakuri El moc wallahi wayar tana cikin jaka'ta dan Allah kayi hakuri kar'ka dakeni Wallahi...., Wani s'awkar marin ne ta'ji a fuska, da iya karfin'ta ta fashe da kuka ganin zata tara mashi Jama'a yasa ya Mike yana nunata da Hannu yace" ki'shirya fadamin in'da kika'je dan Bazan Yarda ba da wannan iskancin'ba" wucewa yayi yabar'tanan kuka ta dinga'yi kamar ranta zai'fita ta jima nan t'sawon dare har bacci ya d'auke ta...,
Tin'da safe Mukhtar ya sak茅 tit'siye Zeinab a'kan ta fada mashi in'da ta'je, cikin rawar murya da kunburan'ran fuska tace" wallahi Grand fr猫re baije ko'ina ba tin'da naje gidan mun'samu mat'sala ne da su Wasila kuma Mama ta goyi bayan su shiyasa na baro masu gidan, kuma tin'da nazo gidan ina k'wance banajin'dadi Shiyasa ban duba waya ta'ba, Dan Allah kayi hakuri wallahi ba dagangan nayi ba" Zeinab ban'yarda ba dan Na-san bak'ya barin wayar ki ne sa da ke, saidai idan k'awai..." shirun da yayi ne yasa ta dago ta k'yaleshi idan ta Tap da Hawaye tace" saidai in'mi?" kafadu ya daga tare da tabe baki yace" watakila kina tare da Wani ne" zaro ido tayi cikin mamaki ta Mike daga durkushin da tayi tace" kamar ya Wani, Mukhtar kana nufin kana zargina da cin amanar'ka, kana nufin Baka Yarda da ni ba"? Tsaki yayi ya Mike zai'fita daga d'akin, s'awrin rike hannun shi tayi tace" ka'fadamin mika'ke nufi dani, Mukhtar wai zargina kake Wani fa kace?" Fizge Hannun shi yayi ya fita ba'tare da yace mata kala ba....,
Zaune tayi tana Tinanin Rayuwa, wai Mukhtar Zargin ta yake to miyasa wai kodai ba Mukhtar kin da ta sani ba'ne, wanda ya shagala adah wajen fada mata kalamai masu dadi, yaou shine ya'ke fada da bakin shi wai tana tare da Wani Namiji ba shiba sabida Kishi, indai irin Wannan kishin za'ace sabida So ne to wallahi BA SO BANE,.
har dare bai'dawo gidan ba Kusan 22:30 ya shigo, lokacin Zeinab ta'gama galabaita da matsanan'cin Ciwon ciki da ya addabeta tin rana, taki fita kuma bare ta fada ma Wani dan gudun sak茅 Wani laifin kuma ba'tada Kudi a waya haka tayi'ta fama har'sai yanzu da ya shigo ganin abin k'warai ne yasa ya d'auke ta suka tafi Likita, bayan dubata da akayi ne ma'aikaciyar lafiyar ta fito a t'sait'saye take fadama Mukhtar cewa" am! Malam gaskiya Yarinyar nan tana cikin hadarin,cikin tane ya fita daga mahaifar ta Kasancewar shi Karami ya dawo a mara Dole yanzu tana bukatar a mata aiki" cikin mamakin jin Zeinab tanada ciki yace" aiki kuma, wane irin aiki kenan?" saida ta nisa tace" Dole a zubar da cikin sabida lafiyar ta, dan bazai'yiyu a barshi a jikin ta'ba, yanzu dai muna bukatar ka saka mana Hannu dan aikin" ba tare da bata lokaci ba yasa Hannu aka fada aikin, kafin nan ya kira Inna suka'zo tare da Mahaifin shi har lokacin Zeinab na ciki Inna ce ta tambayi Mukhtar " Muntari ya nagan'ka kai kadai a wajen ta, ko yan gidan na su basu sani ba?" saida yadan Sosa kai sannan yace" Inna ban kira suba," to miyasa , Yarinya na cikin Wani hali ace kuma gidan su basu sani ba, kaga bana san haka ka kira ka'fada masu halin da take ciki, dan a yanzu tana bukatar Mahaifiyar ta a kusa da ita" ya kira Mahaifin Zeinab ya fada mashi, ya shiga tashin hankali sosai jin'yar autar shi bata lafiya cikin Gaggawa ya'zo Asibitin tare da Tanti Nadiya dan Mama ta tace sam wallahi ko mutuwa Zeinab tayi ko Allah ya jikanta ba'zata ceba, haka ya taho ranshi a bace ya'zo Asibitin dai ya fara gajiya da halin na Ramatou tana nuna ma Zeinab kiyayya kamar ba ita ta haife taba, sabida k'awai ta ki amince'wa da zabin'ta dan yana Dan yar uwar ta...,
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
40-45馃摋
An d'auki lokaci Kafin aka fito da Zeinab aka kaita d'akin hutu, dungumu sukayi suma cikin d'akin dan ganin halin da Zeinab kin take ciki, nurse kinn'da ta kawota ce ta fada masu cewa" Dan Allah a'kula da ita sosai sannan a daina barin'ta tana zama ita kadai hakan yana haifar da kadaici Musammam ga mai ciki, sannan ta rage yawan damuwa da tinani dan da muka auna tension kinta bai kamata ace kamar wannan jinin'ta yana hawa haka ba, sannan abu na karshe kunga yanzu an'mata aiki dan haka akw'ai bukatar ta samu hutu ya kamata a d'auke mata d'uk Wani aikin gida irin wanda mata Sukeyi na'yaou da kullum a'kalla na t'sawon sati Biyu." Kallansu tayi daya Bayan daya Kafin ta nuna Mukhtar da Hannu tace" ai kaine mijin ta ko?" cikin Sanhin jiki ya amsa mata da" Eh! nine" dorawa tayi akan" yawwa to ka'biyoni dan ak'wai magungunan da za'a Siyo mata ta fara aiki da su yanzu" kai kawai ya Girgiza ya'bi Bayan ta, yana fita Inna ma da Malam binshi sukayi dan abu daya ne a ransu, suji ko yanada kudin Siyan Maganin, hakan yaba Baban Zeinab damar Tambayar yar'ta shi da ke k'wance d'uk a galabaice ya gyara Zama yace,
" Mamana, kifadamin idan ak'wai Wani abu dake damunki ni Mahaifin kine bakida wanda zaki fada ma damuwar ki sama dani, kifadamin ko na'iya taimaka maki tin'kafin kijama kanki Wani ciwo dan da kunnan ki kinaji abinda likatar ta fada" cikin kasala da Siririyar murya tace" Abba babu Komai wallahi, babu abinda ya ke damuna idan ma ak'wai bazai wuce zaman kadaicin ba, kuma shima ba sosai ba tin'da inada makota kuma muna wuni tare da su" cikin rashin gasgatawa Abba yace" haba Zeinab ai d'uk wanda ya ganki ya san kina cikin damuwa in'kika duba aiba haka kike ba a baya, kifadamin abinda ke faruwa kinji Auta ta" cikin sigar Rarrashi yayi Maganar, Tanti Nadiya tace" gaskiya ne Zeinab ba haka kike ba kin rame in'banda haske da kikayi shima kuma Na-san na ciki ne kuma yanzu babu shi Kinga Komai zai'fito kenan a fili har'sai kowa ya gane halin da kike ciki, ki fadama Mahaifin ki abinda ya ke damunki kinji ko Hajia" kuka ne ya k'wace ma Zeinab badan ta soba da k'yar ta fara magana cikin muryar kuka tace" Abba yaushe Mama zata daina Hushi da ni, miyasa Mama na ta kasa Yarda da Kaddara ta Yarda cewa aure na da Mukhtar Allah ne ya Kaddara faruwar shi sabida Wani dalili, miyasa Mama ta kasa gane Mukhtar shine wanda nake'so nake'san zama da shi a Matsayin Miji na ba Yaya Saif ba, miyasa Mama ta ke Hushi da ni har yanzu, shin idan aure na da Mukhtar aure ne na mutu ka Raba hakan na nufin zata cigaba da hushi da ni kenan har Abada?" tsagaita kukan ta tayi ta kalli Tanti Nadiya tace" kamata yayi ace Mahaifiya ta ce anan amma sabida tana Hushi da ni bata zoba hakan na Tabbatar min cewa ko mutuwa nayi bazata zo kan Gawa taba bare na samu Addu'ar Rahama daga wajen ta" Hannun Tanti Nadiya cikin Kuka tace" Tanti Nadiya ke kadai kika tsaya tare da ni, ke kadai kika zamar min Uwa da sawran yan uwa na, Tanti kinmin abinda Mahaifiya ta ta kasa yimin Nagode Sosai" fadawa tayi jikin ta tana kuka daddaba ta ta dinga tana bata hakuri haka'ma Abba hakurin yake bata bai'kuma jidadin abin ba Hakan yasa ya daura damarar gyara t'sakanin Uwa da Diyar.
Inna dake kofar d'akin Tsaye d'uk taji abinda ya faru, ba karamin taussaya ma Zeinab ta yi ba kuma Babban Abin dubawa ma ace d'uk wannan ta yi ne Sabida San'da take ma Dan'su, Abin Alfahari ne a wajen Mukhtar samun macen da ta ke san'ka kamar haka, wannan yasa ta dauki Niyar tirsasama Mukhtar rike Zeinab da Hannu Biyu tare da burin fada mashi ko da bata ma Zeinab yayi to bata yafe mashi ba, badan Komai ba saidan wannan itace sakayyar da zasu'iya yima Zeinab akan Soyayyar da ta nuna masu dan d'uk wanda ya'so naka to Tabbas kai ya'so, shigowar da tayi yasa Zeinab ta yi shiru sai Ajiyar zuciya ta ke sawkewa a hankali babu wanda ya yi magana har Mukhtar ya dawo da magungunan daya sawo.
Saida tasha Maganin ta kwanta, Abba ya kalli Mukhtar cikin Tautausan murya yace" Mukhtar dama kai muke jira ka dawo ina so ne zan nemi wata Alfarma a wajen ka?" gaban Mukhtar ne ya fadi dan Tinanin shi kar ace Zeinab ta fada masu Wani abu a game da shi, cikin i'ina yace" Abba Alfarma kuma, a waje na?" kai Abba ya daga tare da fadin" k'warai a wajen ka kuma ina fata zan'samu" Murmushin yake yayi yace" Abba ai kun'wuce neman Alfarma a waje na saidai ku bada Umarni kawai, ku fada Insha Allah za'ayi maku" cike da jin'dadi Abba yace" dama wai ina Tinanin ko zaka amince mutafi da Zeinab gida, tin'da Likitocin sunce babu d'uk wani aiki da zatayi shiyasa ne ke'so mutafi da ita sai ta samu tadan huta nan'da sati Biyu saita koma d'akin ta,koya kuka gani?" ya karashe maganar yana Kallan d'uk mutanen dake d'akin, Mukhtar kam jiyayi kamar za'a tabashi da Zeinab ne ta hanyar dabara da wayo dan haka ya yi shiru ya kasa cewa Komai, Malam daya fahimci Mukhtar yasan zaiyi Wuya ya amince dan haka yace" ai wannan ba Abin damuwa bane Alhaji, Zeinab yar'ku ce muma kuma yar'mu ce bazaku Cutar da ita ba dan haka Zaku'iya tafiya da ita, kuma hakan bayana nufin zamu cire Hannu Daga Al'amarin ta ba a'a zamu dinga kula da ita kamar tana tare da mu" Abba yaji dadi sosai Godiya ya fara masu Malam yace" haba Alhaji miye na Godiya, Zeinab fa yar'ka ce ai mune da Godiya muda aka ba" Murmushi Abba yayi yace" ai ya mace daga lokacin da aka d'aura mata aure to ta fita daga Hannun iyaye ta koma Hannun mijin ta Dana Iyayen shi, Iyayen ta suna nan ne a Matsayin su na Wanda Suka haifeta amma ba masu jibanta Al'amuran taba, Zeinab yanzu ai tana Karkashin kulawar Mukhtar ne shi zaisa tayi zai kuma hanata ta hanu ba niba, idan yace bai amince ba wallahi bazanji Komai a Rayna ba zan hakura da tafiya da Zeinab sai ta Zauna d'akin mijin ta dama shi yafi Alkairi a gare ta ya kuma fi da cewa tayi jinya a ciki, ina da dalilin da yasa nake'son mutafi da ita ne"cike da jindadin Kalaman girma da Abba yayi ne yasa Mukhtar ya saki fuskar shi yace" wallahi Abba babu Komai ni dai a waje na na amince kutafi da ita, fatan mu dai Allah ya bata lafiya" saida Abba ya dafa kan Mukhtar yace" Ameen Nagode Allah ya yi maku Albarka, Allah kuma ya maida maku da mafi Alkairin wanda ya lalace" keya Mukhtar ya Sosa dan jin kunya sai a Zuciyar shi amsa da Ameen.
Tanti Nadiya har race zata k'wana anan kuma Abba ya amince dan yanajin dadin yanda ta ke nuna kulawa ga Mamar tashi, amma sam Inna taki Yarda tace taje gida ita zata kula da yar'ta, haka kowa yabar Asibitin kamar kar ya tafi, Mukhtar ma saida Inna ta matsa mashi ya tafi dan har ya ce anan zai k'wana shima, haka akabar Inna da Zeinab wacce take ta bacci cikin nishadi.
Koda su Abba Suka shiga gida Mama ta kasa zaune ta kasa t'saya Tinanin abinda yake faruwa take, tana Ganin su tayo kansu da sawri tana fadin " Alhaji lafiya Miyake Faruwa ne naga kun'dade?" wata harara ya bita da ita yace" bansani ba, ko kin aike mune?" baki ta saki tace" Alhaji lafiya miyayi Zafi shi ba wuta ba?" cikin bacin Ray yace" ai wallahi ya mafi Wutar , ina ruwan ki da dadewar mu, kefa nace kizo mutafi kikace bazaki ba, karshe ma kikace ko mutuwa ce ta yi to bazaki ce Allah ya jikanta ba to miye na tambayar mu a inda ke faruwa" har ya juya zai wuce ya tsaya tare da juyowa yace mata" kuma kiji Gobe Mama na zata dawo gidan nan da zama zatayi jinya har na tsawon sati Biyu, bama bukatar sa hannunki a kula da ita haka bama bukatar Addu'ar ki gareta mu muna tare da ita, kuma wallahi so daya idan kika daga mata hankali to zaki tafi gidan ku tin'da ai kince kinada gidan Uba ko to itama nan gidan Uban tane Dole tayi yanda ta keso, sabida ita Mama nace" wucewa yayi ya bar tanan ita da Tanti Nadiya Suka bishi da kallo...,
Tanti Nadiya ce ta kalle'ta tace" Hajia Dan Allah kiyi Hakuri kidaina Hushi da hajia, wallahi tana cikin damuwa da rashin ki a kusa da ita Abin yana damunta sosai kuma wannan damuwar tana daya daga cikin abinda yayi sanadiyar lalace'war cikin ta har saida aka zubar da shi, kiyi Hakuri kiyafe mata ki d'auka auren ta da Mukhtar tsananin Rabo ne" wata Harara ta galla wa Tanti Nadiya cikin Massifa tace" to uwar kicihi da kinibibi ina ruwan ki da rayuwar m没, ke zakisa inyafe mata to ko wanda ya ajeki gidan bai isava wallahi bare ke Karan kada miya" Tsaki tayi ta wuce ta barta nan, Tanti Nadiya kuma binta tayi da kallo tana Murmushi tace" toh yaou kuma kishin ya motsa, hum kina so ki na kai Kassuwa, Da'da Mahaifiya ai sai dai Allah kina damuwa da halin da ta ke ciki amma saiki dinga shafama fuskar ki toka kia muzurai" wucewa ta yi ita ma nata dakin dan ta k'wanta.
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
45-50馃摋
Sammako Abba yayi ba tare da Matan shi sun sani ba yaje dan ya d'auko Zeinab idan aka Sallameta daga Asibitin, yana zuwa ya tarada Mukhtar hakan yasa Bayan sun gaissa yace mashi" Mukhtar halan nan ka k'wana kai'ma?" dariya yayi yace" a'a Abba nima yanzu nazo" saida ya jinjina kai yace" ah! Lalle kazo da Wuri, ai na d'auka babu wanda zai'riga ni ganin nayi Sammako Ashe kai asuban'ci kayi" dariya sukayi har'da Inna ma da Zeinab, hira Suka dinga'yi har ma'aikatan Suka fara zuwa sannan aka sallami Zeinab Suka tafi tare da Abba da kayan ta da Mukhtar ya taho mata da su, Mukhtar kuma 茅cole ya wuce dan har ya Makara sosai, Inna ma gida ta wuce Kafin ta sak茅 zuwa ganin jikin Zeinab kin...,
Duk Yaran sun'tafi 茅cole dan haka gidan yayi shiru, Mama ce kadai a Falo zaune tana gyangyadi Shigowar motar Alhaji ta farkar da ita Tanti Nadiya ma fitowa tayi dan taji ko lafiya ya fita basu sani'ba, ganin Shi tare da Zeinab yasa tasan inda yaje cikin murna ta tarbi Zeinab tana mata ya jiki sabanin Mahaifiyar ta data Mike Tsaye tace" Alhaji kenan da gaske kake, yarinyar nan zata dawo gidan nan?" saida Abba yadan Harare'ta K'afin yace" k'in d'auka da wasa Nake?" Girgiza kai tayi cike da Gamsuwa tace" to yayi k'yaou, ka nuna'min nan gidan Mahaifin ta'ne amma kasani nima fa a gidan Mahaifi'na ka d'auko'ni ba akan titi ba dan haka zan'bar maka gidan in'yaso sai'ka Zauna da ita" juyawa tayi ta nufi d'akin ta cikin daga murya Abba yace" Dan Allah Ramatou idan kin'tafi gidan ku kar'ki dawo kinji, Mama'na kuma zama daram da ita a gidan nan har'sai ta samu sawki sannan zata koma gidan ta, naga wanda ya' isa ya takura mata" wucewa Mama tayi ba'tare da tace Komai ba, Zeinab Kallan Mahaifin nata tayi cikin muryar kuka ta fara Rarrashin shi,
"Abba Dan Allah kayi Hakuri Karka bari Mama ta bar gidan nan, idan ta tafi wallahi Douniya ma sai'ta zagemu Abba inaso na Zauna gidan nan tare da Mahaifiya ta idan har ta tafi to nima saidai na koma can nayi jinya'ta, Dan Allah Abba ka'bata hakuri bai'kamata ace kuna samun irin Wannan sabanin a t'sakanin kuba Musammam ma ace a'kaina ne, Abba Dan Allah kuyafemin indai nice silar wannan takon sakar naku" fashewa tayi da kuka ta Durkusa taci gaba da rokon Mahaifin nata har'saida Mama ta'fito da katuwar jaka wai ita zata tafi gida, saida ta t'saya gaban shi tace" na'tafi ka aiko'min da takarda ta gidan mu" rike jakar'ta Zeinab tayi zata bata hakuri cikin Hushi ta fizge jakar'ta tayi gaba, Zeinab ta sak茅 Kallan Mahaifin nata a raunane tace" Dan Allah Abba ka'bata hakuri karta tafi, yanzu mi'kakeso taje gida ta fada da girman'ta ace taje gida a wannan halin Dan Allah Abba ka'bita" baya jurar ganin hawayen Zeinab dan Haka yabi bayan Ramatou wacce take'ta Addu'a a Zuciyar ta Allah yasa su'bata hakuri Kafin ta'fita dan wannan ba'karamin Abin kunya ba'ne gare'ta, tanajin muryar Alhaji ya kira sunan'ta ta t'saya cak ba'tare da ta juyo ba, saida ya fuskance'ta sannan yace" kibiyo'ni d'aki na muyi magana" wucewa yayi yabar'tanan cikin sanhin jiki tabi bayan'shi izuwa Bangaren shi...
Zaune sukayi dukan su dan su'fahimci junan su da k'yaou, Abba ne ya kalli ta cikin nut'suwa yace" Ramatou yanzu abinda ki'kayi kina ganin kinyi dai'dai kenan, sabida Allah ace a gaban yar'ki da kishiyar'ki amma kina'cin Mutunci na yanda kika'ga dama, ace tin'da Hajia tayi aure ni'da'ke bamu sak茅 samun k'wanciyar hankali ba d'uk kin'canza halin'ki kina gani'na da laifin na bawa Hajia wanda take'so ba dan yar uwar ki'ba",
" karfa ki'manta ni'kaina nama Hajia tayin Yayan abokanai'na amma taki tace bata'so, kinga ni'kuma banta'ma yara'na auren Dole ba Kinga ko ai bazan fara da Mama'na ba, Ramatou Dan Allah ki'nut'su kisan Annabi ya faku ki'gane cewa auren Hajia da Mukhtar Allah k'awai ya hada'shi wanda shi'kadai yabar'ma kansa sani, sannan badan abinda ya'ke cikin taba yanzu ya lalace kinga sai'muce hada t'sananin Rabi wanda Wallahi da Wani zaiyi yin'kurin hana wannan auren to'fa Zai'iya zama Ajalin'sa dan anriga da an'rubuta a Lauhil Mahfuz" cike da Gadara Mama tace" Wallahi Alhaji babu wata Kaddara Zeinab bata dace da wannan Yaron ba, wai'ke Baka gani ne, a haife fa ya haifi Zeinab amma ka'd'auki yar'ka ka bashi Haka k'awai bayan ga dan yar uwa'ta nan yana massifar san'ta da yanzu tana kasar Waje tana hutawar ta amma tazo ta d'auko mana wannan wanda ya aje'ta a gidan haya,ko gidan kan'shi ba shida'shi haba wannan ka'daina saka Kaddara a ciki", cikin Tautausan murya yace" yaou sunan hajiar ma ake kira gat'sau ba sakaya'wa Ko'dan Albarka'cina?" kara Hade Ray ta yi tace" ai'ko Hajia ma Hushi ta'ke da ita sabida abinda da tayi" kai ya Girgiza yace" a'a Hajia bata Hushi da tak'warar ta, sannan da kike cewa wai Mukhtar ya haifi Zeinab a haihuwa, in'kikace Haka kenan fa Mukhtar ya'kai sa'a na, wanda ni'kuma a gani'na Mukhtar baifi warin dan'ki ba SAMINOU" cikin sawri ta kalle'shi tace" ahan, ana nan'dai ace kamar Zeinab ta auri warin Saminou ai'takare mata, Saminou shine Babban dan'ka fa Kasan shekarar shi nawa, haba Alhaji wallahi basu dace ba" ganin har'yanzu basu fara magana akan sulhu'ba yace" kinga ni'yanzu ba wannan ne yasa nace kizo ba, Ramatou " ya kira sunan'ta cikin ka'kkausan murya yace" Mama'na ita'ce ta bani hakuri ta'kuma ce na dakatar da'ke amma Wallahi badan haka'ba, ke Kinsan ni Kinsan mi'zan iya yi da wanda bazan'iya yiba, dan Haka nake'so ki'bini a'hankali murabu lafiya, idan ki'kayi lissafi ma ni'da'ke Awa nawa ya rage mana a'douniyar da'har zamuyi kokarin rabuwa yanzu bayan shekarun da muka d'auka muna tare, tin Sawrayi da Budurwa, idan muka rabu yanzu wallahi sai'anzage mu sai'kuma an'mamu dariya dan za'aga kamar mun'haukace ne daga'ni har'ke din, dan Haka nake'so in gargade'ki da ki'kiyaye mu'zauna lafiya sannan mu'ida Karasa yar gutun Rayuwar da'tayi mana sawra a'mats'ayin miji da mata, dan Wallahi idan danyan kan'ki yasa kika fita daga gidan nan to nidai kiji ki'kuma sani baza'je ko'ina ba da sunan b'iko da girma'na Haka k'awai ki sani zarya, saidai idan kin'gaji da zama to k'yamaido kan'ki" tabbas ta'san wannan ka'dan daga cikin aikin shi'ne babu abinda bazai aika'ta ba wanda ya fada dan Haka tama kan'ta kiyamar Laili tace" Lalle Alhaji ka'nunamin Banida Wani Mat'sayin a wurin'ka,yar'ka ma ita ta Baka hakuri ka t'sayar da'ni kenan da saidai na'tafi kai'kuma Kaci gaba da k'wasar amarcin'ka da Amaryar ka ko?" Murmushi yayi yace" ke Kinsan ba'gaskiya kika fadaba dan mace ta Biyu da na'fara samu a Rayuwa ta bayan Mahaifiya'ta to ke'ce, Mahimmancin ki a waje na baki ba'zai iya anbatan'shi ba, kuma da bana'san zaman'ki a tare da'ni aida ban'hakura ba ko" Wani parii aka mashi da ido daya aka bude mashi hauran makka'nan guda Biyu sai walkiya suke tare da fadin" Allah KO Alhaji na?" shi'ma dariyar ya yi yace" sosai ma ai'ke ta daban'ce babu kamar'ki ba'ayita ba kuma baza'a yi taba" wai dadi kashe'ni kamar ta d'auki Alhaji ta Goya dan tasan Gaskiya ce da ga Zuciyar shiyake yaje fadama'ta, shima Alhaji dadi'ne ya kama shi dan ganin ya shawo kan mat'salar dan shi'kanshi da Kuru ce zaiyi ya k'yaketa idan ta tafi gidan su dan Ramatou mace ce da bazai'iya manta'wa da ita ba har'karshen Rayuwar shi, k'awai dai rashin auren Hajia da Mukhtar ne ya canza kalar zaman su, amma ba'dan Haka ba itadin ta daban'ce kamar yanda ya fada.
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
50-55馃摋
Wanka Zeinab tayi tana fitowa Tanti Nadiya ta kawo'mata Abin Karyawa tana'ci ta k'wanta dan ta sak茅 hutawa, cikin kankanan lokaci bacci ya d'auke ta cikin nut'suwa da nishadi....,
Missalin 12:30 na rana yan makaranta Suka dawo, Fadila da gudu ta shigo d'akin da Tanti Nadiya ta fada mata Zeinab na'ciki, t'salle tayi ta haye saman Zeinab tana fadin" eyeeee! hajia ki'tashi na ganki,yaoushe kikazo gidan mu?" da k'yar Zeinab ta tashi zaune tana fadin" haba Fadila so kike ki'yarni ne ko baki'san Banida lafiya ba" cikin shag'waba tace" kiyi Hakuri Hajia dama ganin'ki nazo nayi" Murmushi tayi tare da kama bakin ta tace" yaou kuma hajia na'samu ba Abba yace ku'dinga kirana da suna naba" dariya Fadila tayi tace" ai Abba ne Rannan da nace inaso naje gidan Zeinab sai'yace wai Maman shi nake kira haka" shiyasa ni'kuma yanzu nace hajia" to naji yanzu dai tashi mu'tafi farfajiyar gida sai muyi hira" tare Suka fito kowa na zaune farfajiyar gidan ana ta hira ana aiki,Zaune tayi ta dora Fadila akan kafafun'ta, Tanti Nadiya ce dake yankan Albassa tace" a'a Zeinab Sawke ta Dan Allah, keda bakida lafiya kina fama da kanki" Murmushi tayi tace" ki barta Tanti ba Komai Fadila nawa take" Fauziya ce tace" Zeinab ke kuma yaoushe ki'kazo, k'wana ma kikayi ko?" tabe baki tayi tace" kenan baki'san ina ciki ba?" a'a bansani ba daga 脡cole muka dawo fa, to miyasa meki naji ana cewa baki lafiya?" ki'tambayi Tanti kiji zata fada maki" sai lokacin Mama tayi wani t'saki ta Mike cikin bacin Ray ta shige ciki, bin bayan'ta Zeinab tayi da kallo kafin ta maida kallan'ta ga Tanti Nadiya dake fadama Fauziya abinda ya Faru da Zeinab kin, cikin nuna rashin damuwa Fauziya tace" lalle, kwara ma da Cikin ya zube kinga yanzu saiki koma 脡cole ai indai kema kina'san karatun" shiru Zeinab tayi tana Kallan Fauziya tana mamakin Kalaman'ta Tanti Nadiya ce da ranta ya bace Matuka cikin daga murya tace" ke Fauziya Ashe bakida Hankali Miyake damunki, wannan ba Yayar'ki bace ba da zaki fada mata haka, wannan ai fatan t'siya ne kike mata" shiru tayi itama ta kasa cewa komi sai lat'se lat'sen waya da takeyi, Zeinab ce tayi murmushin yake tace" Tanti ki rabu da ita ai ba Komai Na-san ta naso'ne na koma 脡cole dan ta samu samu Yer uwa itama" cikin fada Tanti tace" to ina ruwan ta kuma KO kin koma ai ba'tare zaku dinga tafiya ba tin'da yanzu ke kina gidan Mijin kine ba gidan ku ba" fada Tanti ta dinga'yi hakan yasa Fauziya ta tashi ta shige d'akin ta dan surutun ya fara hawar mata kai....,
Kamar yanda Suka Saba a Al'adar gidan anan zaune waje daya a ciki a'ci abinci lokaci guda, yanzu ma kiran Zeinab akayi daga d'aki dan Taci abinci, zaune tayi kusa da Maman'ta tare da fadin" Mama sannu da hutawa?" ba'tare da ta kalle'ta ba tace" miye mat'salar ki da'ni, bance kar'ki sak茅 shiga harka taba?" cikin tausassan murya tace" Allah huci Zuciyar ki Mama,kiyi hakuri" cikin hassala tace" idan ya bani hakurin kibi dare ki k'wace" shiru tayi ba'ta sak茅 magana ba, sai AFDAL ne Dan Tanti Nadiya maibi'ma Fauziya yace" Tanti wai miyasa har'yanzu kike Hushi da Zeinab kiyi Hakuri mana, kinga fa ta dawo gidan mu yanzu" cikin bacin Ray tace" kai ina ruwan'ka da maganar mu, wayace ka sama'na bakin ki a ciki idan na sake'ji sai jikin'ka ya gaya maka" a ka'idar gidan kowa yana iya ladabtar da d'uk Wanda yake kasa dashi haka'ma koda ba daga cikin ka Dan ya fito ba, Tanti Nadiya taso tama Afdal magana kan ya k'yale amma gudun wata massifar yasa ta k'yaleshi dan Tantin tashi ta hukunta shi da kan'ta, tashi Zeinab tayi ta wanke hannun'ta ta nufi hanyar d'akin ta muryar Mama tasa tayi t'saye tare da juyowa tana sauraran ta danjin tana fadin" ke ba'wai kinzo bane dan ki dinga zama a d'aki idan lokacin cin abinci yayi kifito kisa Hannu kici, ya zama Dole ki dinga kama aiki kamar yanda kike adah tin'da ke ba bakuwa bace Kinsan d'uk abinda akeyi a gidan, kuma zaki fara ne daga anjima kinji na fada maki" wucewa tayi ba'tayi magana, sai Tanti Nadiya ce tace" amma Maman hajia kina ganin hakan ya dace, hajia fa jinya ce tazo tayi ba zaman jin'dadi ba rashin lafiya ce kina ganin ya dace ace zatayi d'uk wannan aikin da kika lissafa mata" cikin Gadara tace" Nadiya ince dai Zeinab ni na haife'ta?" kai ta Girgiza tare da fadin" eh diyar'ki ce amma nima Diya tace ai" cike da t'siwa tace,
" a'a ni na'haifi Zeinab dan haka tin'da bata'min abinda nake'so ba to itama bazata samu abinda takeso soba indai a gidan nan ne,saidai in'tana gidan mijin tane" shiru tayi kafin tace" gaskiya dai baidace a sata aiki ba tin'da dai ak'wai masu aiki kuma gamu muma ga yara d'uk muna kamawa a nayi kenan aikin mi ya rage da zatayi?" karamin t'saki tayi face" ke kika sani kuma Zeinab Diya ta ce sai'kuma tayi abinda nace" shiru akayi ba aka kara maganar ba...
Bayan idar da Sallah La'asar Zeinab na zaune akan Sallaya Mukhtar ya shigo d'akin da Sallama, juyawa tayi dan taga ko wanene tana ganin Mukhtar ta sakar masa wani Murmushi tare da mikewa cikin sawri ta Rungume shi sosai shima Rungume ta yayi yana shafa bayan'ta yana fadin" Zeinab nayi kewar'ki, Na-san kema kinyi kewa'ta ko?" kamar zatayi kuka tace" eh nayi kewar'ka sosai... daga Kanta tayi ta Kalleshi tace" ina so ka zauna tare ni" hannun'ta ya kama ya zaunar da ita akan gado yace"Zeinab kenan, a cikin k'wana daya har'kin fara damuwa da'ni haka, keda zakiyi sati Biyu anan" cikin shagwaba tace" eh wallahi ni jinake ma kamar na bika mutafi gida dan Na-san kaima zaka kula dani kamar yanda suma zasuyi" jinjina kai yayi yace" sosai zan'kula dake, amma Kinsan ni ai bana zama gida ba kamar yanda zasu kuka dake ba, kuma kinga yanzu muna kusa da jarabawa dan haka anata devoir akai'akai kinga bazaki samu lokaci na ba yanda ya kamata" a haka suna d'auki lokaci suna hira kafin Mukhtar ya tashi tafiya ta rakoshi, farfajiyar gida Suka tarada Mama da Tanti suna hira jefi jefi fitowar su ce tasa Mama ta maida kallan'ta garesu sannan tayi t'saki tana kunkuni sallama yama su cikin Girmamawa sai Tanti Nadiya kadai ta iya amsa mashi, ficewa yayi ba tare da ya damu da rashin amsawar ta dan inda sabo ya saba da wannan halin nata, Zeinzab ma komawa tayi ciki inda ta fara gyara Falo.
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
55-60馃摋
D'uk da Ciwon mara da takeji sama sama da jiri haka ta d'aure ta kammala tana idawa d'akin ta ta shiga k'wance tayi d'uk da anfara Kiran Sallah Magriba, ta jima kafin ta tashi tayi Sallah sannan tayi Wanka ta shirya cikin doguwar Riga ta Atanfa, fitowar ta falo yayi daidai da Shigowar Abba cikin Sanhin jiki ta zauna akan Kujera tana fadin,
" Abba sannu da dawowa?" cike da walwala yace" yawwa sannu Mama'na, ya jikin naki ina fata dai da sawki?" kai ta fara dagawa kafin tace" da s'awki sosai Abba" Bayan ya karbi gaissuwar s'awran Yaran d'脿 Matan nashi sannan ya kama Hannun Zeinab yana fadin" taso muje Mama'na na Siyo maki wani abu mai dadi" binshi tayi Afdal ne yace" Abba to mufa mi'aka Siyo mana?" to kai miza'a Siyo maku, ku da kullum muna tare da Ku ku bari taji dadin ta nadan wani lokaci" wucewa sukayi sai Fadila da tabi Bayan su...,
Ledar hannun'shi ya Mika mata ta bude ta fara fito da kayan ciki Fadila nata tabe tabe ta rasa wanne zata d'auka daga ciki, Zeinab kam samu tayi taci sosai daga gasassar Kaza da cake din da su chocolat ga kuma t'sire wanda yasha birji, taci ta koshi sosai ita da Fadila daga'nan Suka shiga hira ita da Abba kamar yanda Suka saba lokacin da take gida har Abba yaci abinci sun d'auki t'sawon lokaci kafin ta kamo Fadila Suka komo Bangaren su, Mama kadai'ce a falon tana kallo cikin ladabi tace" Mama ni zanje na k'wanta saida safe" mtssss! To ina ruwa'na miya'min Zafi da'ke, ke Idan ma zaki shiga taitayin'ki tin'wuri gw'ara ki shiga hankalin'ki kin'ji na fada maki" ba'ta sak茅 magana ta wuce d'aki ta k'wanta...,
Kiran Mukhtar ne ya tada'ta daga bacci, cikin magagin bacci ta fara da sallama ya amsa'mata kafin ya tambayeta,
" Mata'ta ya jikin naki?"
" jiki da s'awki Yaya el moc, ka'tashi lafiya?"
"to da dama zance, amma Kinsan tin'da baki kusa da'ni ai bazanji dadi ba"
Murmushi tayi kamar ta'na gaban'sa sannan tace" nasani dama el moc nima haka nakeji" cikin sigar Zolaya yace"Anya ko kin'kaini ke fa kina gida tare da su Abba suna kula da'ke yanda ya kamata, ni'kuma kin'ganni nan ni na kai ruwan Wanka da kai'na ni nasa kaya da kai'na na shafa mai da kai'na sannan yanzu sai'na fita sannan na'siyi Abinci naci, kinga kenan na'fiki shiga wani hali" ( Allah sarki Zeinab uwar taussayi) take ta fara mat'so k'walla sabida taussayin mijin ta, jin'tana kuka yasa yace" kinga Dan Allah ni rufamin Asiri daga yar wannan maganar sai kuka Salan kisa ace wani abu na'miki ko kiyi Hakuri kinji karki damu da'ni zan'kula da kai'na yanda ya kamata" saida ta share Hawayen'ta sannan tace" amma haka zaka z'auna har t'sawon sati Biyu kana Siyan Abinci a waje, gaskiya ina ganin ka dinga zuwa nan kana karya'wa" dariya ce ta kubuce mashi kafin yace" haba Zeinab ta'yaya zan'dinga zuwa gidan'ku da sanhin Safiya dan naci Abinci, kema Kinsan hakan ai bazai Faru ba" to naji yanzu kana'ina harka fita ne?" a'a banfita ba yanzu dai zan'fita, daina dawo"to Grand Fr猫re sai'ka dawo Allah ya t'sare ya ki'yaye hanya" Ameen Nagode sai mun'yi waya" sallama sukayi sannan ta shiga tayi Wanka ta fito falo su Fauziya nata hada hadar tafiya 茅cole, gaishe da Iyayen nasu tayi sai Tanti Nadiya ta amsa mata zaune tayi tana Kallan su har'suka fita taji a ranta kamar ta bisu, Abba ne ya shigo cikin Shirin fita Kusan tare Suka gaishe'shi har'da Zeinab, cikin kulawa ya amsa kafin ya maida hankalin shi ga Zeinab yace" Mama'na kin'tashi lafiya ya jikin naki da s'awki dai ko?" Murmushi tayi tace" da s'awki sosai Abba" to yayi k'yaou Allah ya kara s'awki" Ameen Suka amsa tare da Tanti Nadiya juyawa yayi zaifi'ta Mama tace" Alhaji Shikenan kaman'ta da Al'amuran mu tin'da yarinyar nan tazo gidan nan ko?" dariya yayi yace" Hajia Ramatou kenan kinshin kuma akan diyar'ki ya koma yanzu?" murguda baki tayi tace" ba wani Kishi gaskiya ce na fada maka, jiya abinda kasawo mata ko kannan'ta basu gani ba bare kuma mu uwa'ye" kai ya'dan girgiza dan in'ya Biye mata to sai an'samu mat'sala dan haka yace" indai akan wannan ne ki'bari kema zan'siyo maki in zan'dawo" d'auke Kanta tayi daga kallan'shi tace" hum in'madai Baka Siyo ba ai'kasan inada kudin da zan'iya Siyan koma minene" wucewa yayi baice komi ba, Abin Karin kumallo Tanti Nadiya ta kawo'ma Zeinab taci Bayan ta gama anan Suka dinga hira ita da Tanti Nadiya Mama kuma tana d'aki...,
Tare da Zeinab aka'yi Girkin rana d'uk da Tanti Nadiya tayi kokarin Hana ta amma sabida tana'so ta shirya t'sakinin ta da Mahaifiyar ta hakan yasa ta kama aka'yi da ita, Bayan sun ida taci abinci tayi Sallah ta k'wanta dan tadan huta, sai Kusan La'asar ta tashi Bayan tayi Sallah Mukhtar ya kira'ta suka'sha hirar su sun'jima kafin sukayi Sallama...,
Bayan Sallah Magriba Inna da Malam sun'zo ganin jikin Zeinab, saidai karbar da Maman ta ta'masu bata masu dadi ba ita kadai Suka samu zaune a falon duka Yaran suna d'akin Tanti Nadiya tana masu leson, d'uk gaissuwar da Suka dinga mata bata amsa ba t'saye sukayi suna Kallan Ikon Allah kafin ta masu wani Kallan banza tace" lafiya dai'ko, ku wani t'sayamin a'ka?" cikin mamaki Inna tace" a'a dama Munzo duba jikin Zeinab, ko dai baki gane'mu ba Hajia?" hhhhhhh! ta sheke da wata dariya kafin tace" ni'ko na'gane ku, ko ba Iyayen wannan Sakaran Mukhtar din'bane?" toh! Mukhtar dinne Sakarai Hajia, amma ai naga..., Malam ne ya kat'se Innar ta hanyar daga mata hannu, Mama ce tace" ai'da ka barta Dan'naki wani kayan kishi'ne da baza'a ce mashi Sakarai ba, ko wata t'siya yaje t'sinana ma yarinyar?" Malam ne yace" Hajia Dan Allah in Zeinab tana ciki ki'mana magana da ita mu gaishe'ta da Jiki, in kuma bata'nan sai mu tafi idan tazo a gaishe mana da ita" muryar da Zeinab kiji kamar ta mutanen da ta sani yasa ta fito ganin su Inna yasa ta saki fuskar ta tana Fara'a ta karaso cike da Girmamawa ta Durkusa tana gaishe'su har'saida Inna ta dago da ita tana fadin,
" haba diya'ta keda bakida lafiya ai'da kin zauna ma da mun'shigo da kan'mu" Murmushi k'awai tayi sai tambayar ta da sukayi jiki, kafin ta basu amsa Mama ta ta kat'se su da fadin" Wallahi Zeinab kinyi asara ace kina yar gidan Alhaji Nafi'ou mai Kudi amma wai ki durkusa gaban wadannan mat'siya tan kina gaishesu a mat'sayin surukai tirrr da ke wallahi" cikin zafin nama ta tashi ta shige d'akin ta dan bazata iya ganin wannan kayan takaicin ba, Hakuri Zeinab ta soma basu har'da Hawaye suna cewa babu Komai kafin ta nemi Alfarma a wajen'su, Inna ce tace" Wace Alfarma kuma Ya'ta?" cikin jin'nauhi tace" Dan Allah Inna karku fadama Yaya abinda ya Faru,kin'san shi da zuciya bazaiji dadi'ba" Murmushi sukayi dukansu kafin Malam yace" haba Zeinab kamar wasu Yara, karki damu bazai'sani ba Insha Allah kinji ki k'wantar da hankalin ki" kai ta girgiza cikin ladabi rakasu tayi d'uk da tayi tayi su shiga ciki ko ruwa su'sha amma suka'ki dan yanda Suka fahimci Mamar'ta batada k'irki zata iya masu wani cin mutin'ci....
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
0 comments:
Post a Comment