Tana tashi daga bacci data koma bayan tayi Sallah Asuba, sawti ta'keji ana hayaniya dan haka ta taso da nufin ta'leko taga ko su waye dan rigar bacci ce a'jikin ta iya g'wiwa babu ko kallabi a kan'ta, yaya Saif ta gani wanda Mama ta tit'siye'shi tana fadin" haba Saif kai'de k'afadamin gaskiya k'awai ni'dai nasan bazaka'zo gidan nan'ba daga zuwan'ka jiya cikin dare ba'tare da wani dalili'ba?" Sosa k'eya yayi yace" da gaske Mama na'ke fadamaki babu komai, k'awai nazo na'ganku ne" k'afin tace wani abu Zeinab ta d'anno da gudu sai'ko a kirjin Saif ta fada cike da farin ciki tana fadin" yaya Saif y'aoushe kadawo?" shiru yayi sabida sanhin da jikin'shi yayi cikin ran'shi yana fadin, ko'dai Zeinab ta manta yanzu ita matar aure'ce bah'da bane da'shi ya'ke tinanin samun'ta ta'zama mallakin'shi, cikin murya kasa kasa yace" kanwa'ta ashe har'yanzu baki girma'ba?" dago da kan'ta tayi cikin sigar shag'waba tace" kai yaya na'girma fa ai'kai kadai nakewa haka kai'ma dan nayi missing din'ka ne" daga'ta yayi daga jikin'shi yana fadin" nima haka kanwa'ta, to ya ki'ke?" k'afin tayi magana Mama ta k'arbe da cewa" ke! wani irin iskanci'ne wannan kamar wata karamar yarinya zaki'zo ki'fada kan'mutum haka k'awai, in'kinsan kina'san jikin'shi miyasa kika'ki auren'shi Mutumniyar Banza k'awai?" tin'da ta fara magana hawaye suka cika idan Zeinab dan haka ba'tace komai ba ta juya ta koma d'akin ta, Saif ma da bai'jidadi ba yace" kiyi hakuri Mama har'yanzu ai yarinya ce" hararan'shi tayi tace" a g'unka ba kai'da ke Namiji ai haka zaka'ce dama tin'da Zeinab ce wacce bata laifi a wajen'ka" k'eya ya sak茅 sosa'wa ya mike t'saye yace" Mama kin'bata ran gimbiya bari naje nayi rarrashi" bai'jira abinda zatace ya wuce d'akin Zeinab, Mama k'am bin'shi tayi da k'allo ta rasa Wace irin soyayya Saif ya'kema Zeinab haka shi'ko kishi'ma bayaji a zuciyar shi, yanda yaga tayi ta'gumi yasa yayi dariya lokacin da yake zauna'wa kusa da ita saida ya gama mata k'allo sannan yace" kanwa'ta miye na'kuka kuma?" ba'tare da ta goge hawayen'ta ba cikin kuka tace" yaya Saif har'yanzu fa Hushi suke da'ni Mama ma ta'ki ta'yafemin" cike da tausayawa yace" kin'ga kar'ki damu Insha Allah komai zai'zo k'arshe, tin'da na'zo bazan'tafi ba har'sai nasa sin'yafe maki kin'ji ko" Murmushi tayi ta goge hawayen tace" to yaya Saif, dama nasan kai ba'zakayi Hushi da'ni ba" s'awya a'kalar zancen yayi ta hanyar Tambayar ta" wai'ke mi'kikeyi gida ne?" cikin jin'kunya ta rufe ido tace" yaya b'ari nayi" dammm! yaji gaban'shi ya fada zuciyar shi yaji ta'fara bugawa kamar zata fito Waje, baisan sanda yace"Mi! b'ari Zeinab?" d'uk da ta t'sora'ta ganin yanayin'shi amma haka ta basar tace" eh yaya Saif Avortement nayi" b'ugun zuciyar shi'ne ya k'aru amma sai'ya d'aure yace" halan har'yanzu baki dai'na t'salle t'salle ba'ko, ba'kisan karamin ciki baya'san k'waramniya ba?" rufe Ido ta sake'yi cikin kunya tace" a'a yaya ni'fa ba laifi'na bane, k'awai dai Allah ne yasa ba'zai fito duniya ba" maganganun Zeinab sosai suke k'ona masa Ray dan bazaijuri jin' Zeinab ta samu ciki da wani ba shi'ba, dan haka ya mata sallama ya tafi tare da alk'awarin zai'sake d'awowa....,
K'oda ya shiga gida ganin babu kowa a t'sakar gida da'ma falo k'ait'saye d'akin shi ya shiga ya fada kan'gado yana k'allan sama idan'shi rufe kamar mai bacci yana tinanin abin k'aunar'shi Zeinab wacce ya raine'ta yaci burin mallakar'ta amma y'aou g芒ta a Karka'shin milkin wani ikon wani mallakin wani ba'shiba, NASREEN ce kanwar'shi ta shigo dan ta'ji kamar an'buda d'akin ganin'shi k'wance yana aikin tinanin dan ta tabbatar ba k'wana ya'keba, saida ta kare ma d'akin k'allo taga yanda d'uk ya barbaza k'aya daga shigowar dare zuwa sanyin safiyar'nan ga photo nun Zeinab da d'uk ya c'ike bangon ko'ina da'su, wasu ma sai in'anfada maka ita'ce sannan ka'sani sabida wasu tin'batafi shekara uku zuxa hudu ne a duniya har'girman'ta i'yanzu zaka'iya cewa kamar kowace Rana'ce yake d'aukar photo na'ta sabida yawan'su wani irin'ma ko kayan kirki babu a jikin'ta wani tana kuka wani tana dariya wani bata'masan an'd'auka ba wani tana'cin Abinci wani tana bacci ga'sunan bar'katai,
cikin bacin Ray ta fita daga d'akin ba'tare da ya sani'ba, tana'ta g'unguni har'ta zauna kusa da Mamar tasu Hajia KARIMA k'allan'ta tayi tace" ke kuma miye?" cikin bala'i tace" Mama Dan Allah yanzu haka yaya Saif zai'mayar da kan'sa wani mahaukaci akan yarinyar'nan ?" t'saki Mama tayi tace" to sai'me miye naki a ciki dan'ya h'aukace ai'shi yakama kan'shi ina ruwa'na ni?" cike da damuwa Nasreen tace" haba Mama idan'fa haka ta faru sai'kinfi kowa shiga damuwa ai,ita'kuma tanacan tana Soyayyar ta ki'duba yanzu kiga d'akin dana'sha Wahalar g'yara jiya amma shi'ne d'uk ya yamut'sa shi lokaci daya da t'summokaran yarinyar can da wasu banzayen photo nun'ta" da k'arfi Mama ta k'alli k'ofar d'akin shi sannan ta k'alli Nasreen tace" wallahi ki'rufama k'anki asiri ki'daina zagin wannan k'ayan dan yanzu'ne zai'huce a kan'ki kinsan kuma ni'dai ba'iya masa nake'ba idan ran'sa ya bace sai'ya k'wana yana dukan'ki ba abinda zan'yi kin'ji na'fadamaki" t'abe baki tayi tace" haba Mama ai'bazaki yarda ba,amma Dan Allah ki'masa magana ya fitar da kayan'nan haka k'awai ya tarawa kan'sa t'summa" dariya Mama tayi tace" wannan k'ayan bazasu fita daga gidan nan ba in'ko aka'ce su'fita to saidai ya fita tare da su, Shekara Goma sha'bak'wai kenan Daya fara ajiyar'su har'kayan da Zeinab tasa'ka tana shekara biyu idan ki'ka duba a bolar'shi zaki samu kin'ga kenan ki'fita harkar'shi da k'ayan'shi" Murmushi tayi tace" wai'ni Mama ta'yaya y'a samu k'ayan ne wai?" cike da Zolaya Mama tace" Satar su ya'ke mana wasu kuma bayan ta'gama anfani da'su yake d'aukowa" cike da Girmama lamarin tace" lalle, nasan yana ajewa'ne dan yasama diyar'su k'ayan wasa kuma yaba diyan'su suyi wasa yace, kayan da Maman sune tayi aiki dasu tana kamar su" dariya Mama tayi sosai tace" shi'dai y'a sani Sarkin soyayya".
Please kuyi manage da wannan馃憦馃憦馃憦..
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
65-70馃摋
Makara da Mukhtar yayi wajen k'wantawa sabida wayar da sukayi da Zeinab ne yasa ya Makara wajen tashi, a gaggauce ya shirya ya fita yana zuwa makarantar ya nufi hanyar ajin'shi cikin s'awri ya zuwa daidai k'ofar shiga yayi k'aro da MARYAM wacce ta taho a guje bata an'kara ba, faduwa taje tayi saidai d'uk da Mukhtar baisan ko'wacece ba yayi hanzarin riko kugun'ta, sallatin da yan ajin sukayi'ne yasa yayi s'awrin sakin'ta sunata raba ido irin na marassa gaskiya, cikin i'ina Maryam tace,
"ka'kayi Hakuri ban'lura bane" wucewa yayi ba'tare da ya amsa mata ba, take ya fara abinda ya k'awo shi...
Bayan yazo gidan'su Inna yaci abinci ya kira Zeinab bayan sun'gaissa take tambayar shi" el moc ya kake?" saida ya s'awke wani goran nunfashi sannan yace" ba'dadi" cikin kulawa tace" miya'faru kuma?" cikin tausassan murya yace" Zeinab za'fada maki amma kimin alk'warin bazakiji h'aushi na'ba?" cike da k'warin g'wiwa tace" yaya'na indai nice to ka k'wantar da hankalin'ka bazan'taba yin'hushi da'kai ba har'abada" yaji dadin maganar ta dan haka ya fada mata d'uk abinda ya faru t'sakanin shi da Maryam dan yana ganin bazai'iya boye'mata ba dan ba'hallayar sa bace, d'uk da Zeinab taji harbawar k'irjin'ta amma bai'hana ta yafe'masa ba suka'kula ci'gaba da hirar'su irin'ta Massoya...,
Maryam ce ta t'ari Fauziya K'anwar Zeinab bayan sun'gaissa tace" Fauziya wai miyasa mu wayar Zeinab ne ana kiran'ta ba'a samun'ta?" cike da rashin damuwa Fauziya tace" ai'ko wayar ta lafiyar ta k'alaw,watakila mat'salar network ne" eh kuma hakane, to Dan Allah ko'zaki k'watantamin gidan'ta kinsan banta'ba zuwa ba?" cike da Mamaki dan Fauziya a iya sanin'ta babu wani abu t'sakanin Zeinab da Maryam ko gaissawa bata taba ganin sun'yiba hasali'ma ak'wai ranar da Zeinab kin'take cewa Maryam tana bata h'aushi dan batada halin k'warai fit'sararriya'ce ta gaske, cikin shakku da mamaki tace" amma ai'yanzu bata gidan'ta tana gida tana jinya" wani irin sanhi Maryam taji a'ran'ta dan faduxa ce tazo dai'dai da zama, cike da kissa tace" ayya, Dan Allah to kifadamin gidan naku da gidan'ta koda bansamu damar tafiya gidan'naku ba sai'naje gidan'ta idan ta koma" ba'tare da tinanin wani abu ba Fauziya ta fada'mata duka adresse kin gidan...,
Mukhtar na zaune da littatafai a gaban'shi ya kasa duba ko daya sabida k'ewar Zeinab d'uk ta'ishe shi ita k'adai yake tinani yake gani, hirar'su suke cikin farin ciki da annashuwa suna'ji kamar ace Suna tare ne, Buda k'ofar da yaji'ne yasa yayi s'awrin kashe wayar ya mike t'saye cike da mamaki dan baiyi tinanin k'ofar bude take'ba, mamakin'shi ne ya sak茅 ninkuwa lokacin da sukayi tozali da Maryam cikin wata irin shiga da bai'taba tinani ba, cikin mamaki yace" ke mi'kike anan, mi'yakawo ki'nan, wanne wace irin shiga'ce kuma?" cike da Izza da jin'kai ta zauna saman Kujera tana t'aunan shewin'gum kafin tace" na'zo ne na'tayaka hira" cikin rashin Fahimtar yace" hira kuma, Wace irin hira yanzu, ke ko'bakida hankali?" wani irin murmshi tayi iya labbanta tace" nasan matar'ka bata'nan Namiji kamar'ka kuma dole kana bukatar kulawa, shiyasa nazo na'debe maka k'ewar'ta" cikin bacin Ray ya fizgo hannun'ta yana fadin" ke zo'ki fita daga gidan'nan tin'kafin ran'ki ya'bace" ganin zai'fitar da ita ta karfi yasa ta'mashi rada" wallahi ka'bini sannu ko'na tona maka asiri,babu wanda zai'karya tani idan nace kai'kakawoni gidan nan kuma muna soyayya da'kai" s'akin'ta yayi yana huci ya nuna'ta da hannu yace" to maza ki'bar gidan'nan kafin na kakkarya'ki" Banza tayi da'shi ta komo cikin d'akin ta zauna kafa daya bisa daya, yana shigo'wa cikin zafin nama ya d'auko wata doguwar waya ya'yo kan'ta ganin babu alamun wasa yasa ta tashi da gudu ta shige uwar dakin bin'ta yayi yana fadin" wallahi zoki fita ko naci uwar'ki gidan'nan ni zaki nuna'ma ke yar iskace,wane budadden ido'ne bamu gani'ba ki'tsaya mana mara kunya k'awai" yana dosa kai cikin d'akin yayi turus ya t'saya sabida ganin tana cire kayan jikin'ta da s'awri ya juya mata baya yana cewa" ke wai miye Haka kin'san abinda ki'keyi kuwa?" bata ce'mashi komai'ba sai'jinta da yayi a bayan'shi ta rumgume'shi cikin wata irin kissa da salon Iskanci d'uk da yayi yin'kurin k'aucema Sharrin Maryam amma hakan ya'ci tira har'saida tasa'shi ya aika'ta Babban zunubi ya aikata sabo ya aika'ta zunubin da bai'taba aika'tawa ba t'sawon rayuwar'shi, cikin dare Maryam ta'bar gidan ba'tare da wani ya san tazo ba, Mukhtar bai rint'sa ba ko kadan yanda yaga rana haka yaga dare yana'ta kuka da Nadamar abinda ya faru yana kara kambama girman laifin da yayi idan ya tina yaci Amanar Zeinab kin'shi, takaicin nashi ya kara karuwa ganin babu wani abu da'yaji dan'gane da tarayyar'shi da Maryam babu dadi babu nut'suwa babu kimt'si babu'ma tayi yawa gashi babu wani abu da tama'shi wanda Zeinab kin'shi bata mashi saidai banbancin'su shine Zeinab tana nuna k'unya ita kuma babu k'unya a Al'amarin'ta ko kadan,da haka har'ya Wayo gari ba'tare da ya rint'sa ba...,
y'aou gida babu kowa d'uk sun'tafi harakokin gaban'su, Fauziya da Fadila sun'tafi kit'so da kunshi dan k'wana biyu ya rage bikin Aida Mama ta fito Siyo wasu s'awran kayan da zasu bukata a wajen Tuya, sai Zeinab da Tanti Nadiya da yan aikin'su guda biyu, yaya Saif ne Yazo bayan sun'gaissa fitowa sukayi farfajiyar gida shi'da ita Suna hira, saida ya kare mata Kallo na t'sanake yaga ta kara k'yaou da gari saidai ta'dan rame kadan dan haka cike da Zolaya yace" kanwa'ta kin'ga yanda kika'kara k'yaou ki'kayi fari, ko'dai cikin nan bai'zube ba duka?" dariya tayi ta turo baki tace" wallahi yaya bana'san haka, babu'shi fa yanzu ya fita" dariya yayi yace" to naji, yanzu baki jin Komai a jikin'ki?" kai ta girgiza tace" a'a yaya bana'jin Komai saidai wani lokaci mara'ta takan dan'yi min ciwo" bata fuska yayi yace" amma kula kinajin haka an'baki fadaba ko jiya na'tambaye'ki ba'kijin Komai?" cike da shag'waba tace" kayi Hakuri bazan sake'ba" daya daga cikin hallayar da suke birge'shi kenan danga'ne da Zeinab gane kuskuren'ta bayar da Hakuri lokacin da ta gane kuskuren'nata, Murmushi da take'yine yasa ya manta da abinda suke magana akai, wani irin mayan k'allo ne yake mata hakan yasa ta t'sargu kasa tayi da k'anta sabida kunya a hankali ya dago da kan'ta yana Kallan ida'nunta d'uk da taki Hada ido da'shi kamar s'awkar Aradu taji muryar'shi yace" Zeinab dan Allah kice kina sona ko sau'daya ne" da s'awri ta daga ida'nunta saidai ina Hawayen dake makale suka zubo dan haka ta ruga a guje ta koma cikin d'akin ta tana kuka, tabbas tasan wani bangare na zuciyar ta yana san yaya Saif haka kuma tana k'aunar shi da dukkanin ilahirin zuciyar shi amma ya'zatayi Soyayyar Mukhtar ita ta mata pin'tink'au...,
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
70-75馃摋
Tin'da Saif ya'dawo gida ya shiga d'aki ya rufe kan'sa a ciki ya d'inga sheka kuka kamar dai yaro Karami, hankalin Mama ne ya fara tashi jin'yanda yake'ta kuka bata'so ta kula'shi ba amma haka ta d'aure ta fara bubbuga d'akin da k'yar ya bude, tausayin'shi ne ya kamata da'taga d'uk ya fita hayyacin'sa, zaune tayi kusa da'shi tin'kafin tace wani abu ya d'ora kan'shi a saman kafafun'ta ya kara fashewa da kuka yana fadin,
" Mama Zeinab bata'sona ba'kuma zata taba so'na ba, Mama adah Zeinab tana K'allan cikin k'wayar ido'na tace'min tana so'na amma y'aou ta kasa k'allo'na ta fada'min haka, Mama yanzu Zeinab ta t'sane'ni ban'san mina mata'ba, Mama Zeinab ta'ci amana'ta ta y'audare'ni, miyasa tamin haka miyasa ta ki'ni, miyasa lokacin da ta'ke yarinya kullum ta'ke cemin yaya Saif ina san'ka tin harufan bakin'ta basu fita har'na fara gane mi'take nufi, saida ta'bari na'kamu da san'ta sai'ta juyamin baya ta guje'ni tace bata'sona miyasa Mama miyasa tamin haka, idan wani laifi na'mata miyasa taki hukunta'ni dai'dai da abinda na'mata miyasa taki min hukuncin da zan'iya d'auka amma saita zabi ta nisan'tani da kan'ta" ran' Mama na bace'wa sabida yanda taji d'uk ya rude akan wacce bata masan yanayi'ba, daga kan'shi tayi ta k'alli idan'shi tace" Saif miyasa kake haka, miyasa ba'zaka manta da wacce ta manta da kai'ba?" wani irin k'allo yama Mama yace" bazan'iya ba idan'da zan'iya da tini nayi hakan Mama" ki'karin boye bacin ran'ta tayi tace" to dama ta yaya zaka manta da ita bayan kana ta're da ita a kullum, ai kokartawa zakayi ka cire'ta a ran'ka k'awai" kai ya'keta giegiza'wa kafin yace" Mama kiyi hakuri, Allah ne yasa'min san Zeinab bazan'iya cirewa da kai'na ba k'awai ki'tayani da Addu'a" mai'da kan'shi yayi saman kafafun'ta cikin muryar kuka ya kara da cewa" ina san'ta Mama ita'ce a mafarki'na ita'ce a tinani'na ita'ce buri'na, na'so na same'ta ta zama Matata uwar yaya'na amma waccen banzan Mukhtar kin ya raba'ni da ita" tashi yayi zaune cikin gushewar hankali da baiyyana t'sant'sar abinda ke zuciya cikin bacin Ray yace" Mama mi'waccen ya'fini mi'yake da'shi da bana'da miye gare'shi da har Zeinab ta'juyamin baya ta zabe'shi ta bar'ni, miyasa zata d'auke'shi bayan gani ni'ne na'jima ina jiran'ta na raine'ta har'ta girma amma karshe abinda zata saka'min da'shi kenan?" Mama ganin abin zaifi karfin'ta yasa ta jawo kan'shi da karfi ta maida kan'ciyen'ta ta d'inga rarrashin'shi tana bashi hakuri tana daddaba'shi , haka ya'keta sambatu ba'a kojin abinda yake fada sabida shakewar da muryar shi tayi, bacci'ne ya d'auke shi daga haka badan yayi niyar yin'baccin ba...,
d'uk abin Duniya ya'ishi Zeinab ga tinanin makomar yaya Saif ga tinanin halin'da Mukhtar ya'ke ciki tin'daren jiya har y'aou bai'kira ba bai'kuma zo'ba, gashi SALISOU da AMINA kannan'shi sun'zo sunce yana gida sun'baro shi k'wance yana zazzabi hakan yasa d'uk hankalin'ta ya kara tashi
tin'da ya tashi jikin'shi babu k'wari a'haka har'akayi Sallah Magriba da Isha'i, bayan yaci abinci yace ma Mama" zan'dan fita na'dawo" ganin yanayin shi yasa Mama tace" amma Saif ina zakaje ai'da kayi zaman'ka ka huta'ma ran'ka?" kamar mai'jin bacci yace" a'a Mama zanje naga Zeinab ne nasan yanzu kan'ta yana ciwo kuma bata'sha magani ba, watakila ma har'yanzu kuka ta'ke" cikin bacin Ray Mama tace" Saif kanada hankali kuwa anya Baka h'aukace ba, maganar Zeinab fa ka'keyi har'yanzu har'ma kake tinanin tafiya gidan'su to kamata Wace uwar?" jiki asanyaye yace" Mama kuka fa nace maki na'baro tanayi, kuma kinsan da'ta fara kuka kan'ta ne ke fara ciwo"cike da massifa Mama tace" to sai a'kayi yaya dan tana kuka yar zinariya'ce data Wuce kuka, kai'ba kuka ka'gama da'zu ba" wani irin murmushi yayi yace" Mama ai'ni Namiji ba'gashi yanzu nayi shiru ba, ita'kuma yanzu babu wanda zai'yi rarrashin'ta kema kinsani Mama tin'da babu wanda ke shiri da ita idan kika cire Abban'ta" k'allan bakada hankali ta mashi tace" to shine mi basai ka'bari idan uban'nata yazo ko Mijin'nata wani ya lallaba'ta ba, sannan ma gidan uban'wa kasan tana kukan har'da kan'ta zaiyi ciwo?"Murmushi ya sake'yi yace" Mama a hannu'na fa Zeinab ta girma dole nasan Komai a game da ita, in'har bazan'iya sanin halin'da take ciki ba ai'ina ganin bai'kai mat'sayin a kira'ni masoyin'ta ba" cikin kossawa Mama tace" kaga Kaje kayi abinda ran'ka yake'so tin'da dai ban'isa na'fada maka kaji'ba" sunkuya'wa yayi cikin ladabi yace" kiyi hakuri Mama'na kitaya'ni da Addu'a k'awai" wucewa yayi ya fita bin k'wanan da'ke gaban'ta tayi da k'allo zuciyar ta na kara t'sanar Zeinab.
yana gaissawa da su Mama ya'wuce d'akin Zeinab, zaune take idan'ta sun'kumbura sunyi jah, t'saye yayi yana k'allan'ta kamar mai wani tinani kafin yace" har'yanzu baki dai'na kukan'ba?" sai lokacin ka'dai ta daga ido ta k'alle'shi ta shafi Fuskar ta da hannu sannan tace" ba kuka na'keba k'awai dai kai'na ne ke ciwo" ajiyar zuciya ya s'awke yace" kin'sha magani?" kai ta girgiza cewa yayi" to abinci fa kin'ci?" nan'ma kai'ta girgiza, juyawa yayi zai'fita tasan in'da zaije da s'awri ta rike hannun'shi ta fashe da kuka, juyowa yayi ya k'alke'ta yace" lafiya miye na'kuka kuma?" ba tace komai'ba dan haka ya sak茅 Tambayar ta" Zeinab lafiya miye na'kuka, ki'bari in'dawo zan'kawo maki magani ne da abinci" cikin kuka tace" yaya Saif ko ka kawomin bazan'iya ci'ba" cikin mamaki ya Tambaye'ya" miyasa?" kara fashewa tayi da kuka ta daga kai tana k'allan'shi hawayen'ta na s'awka akan hannun'shi kamar karar an'sa kuwa yaji muryar'ta tana cewa" dan Allah yaya Saif ka'taimaka min ka kai'ni gidan'su Inna naga el moc tin'jiya bai'kira ni'ba kuma bai'zoba sabida zazzabi" tin'da ta fara magana ya rint'se idan'shi dan zaifi mashi s'awki ta d'inga soka mashi wuka akan abinda take fada, cikin t'sananin bacin Ray baisan sanda ya d'auke'ta da wani gigitancen mari ba sabida ta'kaici,dafe Kunci tayi tana k'allan'shi yaci gaba da fada" Zeinab wai'ke ma'h'aukaciyar ina'ce miyasa bazaki gane mai'sanki, Zeinab ko kinsan cewa d'uk t'sawon rayuwa'ta na bata tane da tinanin'ki da burin ganin na mallake'ki kin'zama tawa ni kadai,miyasa ke baki taba tinani naba ko na second daya, Zeinab kinsan yanda nakeji cikin rai'na idan kika anbaci sunan wani da'namiji ba'niba, amma Zeinab har k'allo'na kinyi kin'fadamin kinyi barin cikin wani, shine bai'isheki ba yanzu kine cewa na'kaiki kinganshi d'uk kin'damu sabida k'awai kin'yini baki gan'shiba bai'kira kiba, Zeinab ki k'watanta abinda kikeji a Ranki na wuni daya da wanda kina hadu da'shi cikin yan watanni, da wanda ni'nakeji a game da'ke na t'sawon shekaru." zaune yayi ya d'inga s'awke wani irin huci mai karfi, Zeinab kam kamar ruwa sun'cinye ta ido k'awai ta sakar masa dan tasan abinda ke ran'shine zuciyar shi ta kasa boyewa ta fallasa d'uk da kokarin da yake na boyewa.
ganin k'allan da take'mashi yasa ya'dan saisaita nut'suwar shi yace" kin'ga kiyi hakuri kar'ki damu da abinda ki'kaji yanzu k'awai dai rai'nane a bace shiyasa" k'allan mamaki ta mashi cikin murya kasa kasa tace"
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
75-80馃摋
"akan'mi yaya Saif kake bani hakuri, bayan zuciyar ka ta fallasa'min halin'da kake ciki a'game da'ni" share Hawayen'ta tayi tana fuskan'tar shi tace" yaya Saif miyasa kake'so sai'ka nuna babu abinda ke damun'ka?" kan'shi kasa yace" to ya kike'so nayi?" hawaye'ne suka cika idan'ta Karfin hali tayi tace" yaya Saif kayi hakuri hakika bancancanci Soyayyar'ka bai'kamata Kaci gaba da so'na ba sabida ban'maka hallaci'ba yaya Saif ban'zamar maka yar Halak ba..." shhhhhh! ya d'ora hannun'shi a labben'ta yace" miyasa zaki fassara kan'ki da irin wannan Mumunar fassara, Zeinab ina'so kigane wani abu da ace Allah ya kaddara aure'na da'ke to da babu mahalukin daya isa ya dakatar da'shi, nasani Allah ne bai'nufa ke Matata bace shiyasa ban'same ki ba" dora kan'ta tayi akan kafafun'shi taci gaba da rera kuka mai'ban tausayi, kan'ta ya d'inga shafawa har'bacci ya d'auke'ta a hankali ya g'yara mata k'wanciyar ta ya aza kan'ta saman pillow durkushe yayi yana k'allan fuskar'ta tayi wani haske kamar ya sumbace ta Haka wata zuciyar ke raya'mashi amma sai ya'tina auren da'ke kan'ta hannu yasa ya shafi fuskar'ta ya tofa mata Addu'ar bacci sannan ya fita, ko sallama bai'ma su Tanti yabar gidan ya rasa mike mashi dadi yayi Nadamar dawowar shi dan haka ya fara tinanin koma'wa a cikin satin nan...
tin'da safe wanka tayi ta koma ta zauna kan gado tana tinanin halin'da Mukhtar yake ciki, tana tinanin halin'da yaya Saif yake'ciki, Mukhtar ne ya shigo dakin cikin sallama sabida ya yanke shawarar ya fada mata abinda ya faru dan ta'yafemasa, tana ganin'shi da gudu ta tarbe'shi rungume juna sukayi cikin sh'aukin juna a hankali Mukhtar ya dagata ya kamo hannun'ta suka zauna saman gado Suna k'allan juna cike da damuwa tace" Grand Fr猫re lafiya miyasa meka k'wana biyu?" ya kasa Hada Ido da ita haka cikin kunya yace" kiyi hakuri aiki'ne yamin yawa kuma da zazzabi daya takura'ni" ajiyar zuciya tayi tace" ai'na d'auka bazaka fadamin kayi rashin lafiya ba dan dama su Amina sun'fadamin" mannewa tayi a jikin'shi tana fadin" nasan d'uk rashina'ne a kusa da'kai yaja maka haka, amma nima nayi missing din'ka" idan'shine suka cika da k'walla daga kan'ta yayi ya k'alli fuskar'ta yace" Zeinab i have someting to teld you but am scared" yanda ta k'alleshi ya tabbatar mata da ak'wai mat'sala cikin nuna t'sant'sanr kulawa tace" what happend,teld me what happend to you?" hannayen'ta ya kamo ya rike yana zubar da hawaye yace" promise me you c'ant leave me?" d'uk da faduxar da gaban'ta keyi haka ta d'aure tace" yaya Moc zan'rayu da'kai bazan'taba barin'ka ba har'abada" Suna Hada Ido yayi s'awrin s'awke nashi cikin i'ina da Sarkewar murya ya fara bayyana ma Zeinab abinda ya faru t'sakanin shi da Maryam a gidan su....,
Tin'da Zeinab ta'kura mashi ido ta kasa s'awkewa hawaye'ne kebiyar fuskar'ta kamar panpo, Mukhtar na ganin haka ya durkeshe kasa ya fara magiya" Zeinab Dan Allah kiyafemin wallahi ba'asan rai'na na'aikata ba Sharrin shedan ne bansan garin yaya haka ta faru ba, Zeinab na'zabi in'fada maki ne dan bana'so na mutu da hakkin'ki Zeinab wallahi...." cikin Sanyanyan murya Zeinab tace" kafitar'min daga d'aki " k'allanta yayi a marairaice yace" Zeinab kimin alkawarin bazaki guje'ni bakar'kimin haka wallahi bazan'iya rayuwa babu ke'ba" k'allan'shi tayi cikin bacin Ray da kunar zuciya tace" nace ka'fitar min daga d'aki wallahi bana'san ganin'ka, kafita nace" tayi maganar cikin Daga murya a hankali jiki asanyaye ya mike ya fita yana k'allan'ta ba'tare da ta k'alle'shi ba harya fice daga d'akin, kuka mai t'sanani ta fashe da shi tana jin'nadamar auren Mukhtar karara Tanti Nadiya ce ta shigo ta fara rarrashin'ta da k'yar ta samu taci abinci tasha magani sabida Ciwon kai sannan ta'koma bacci.
tana tashi tayi wanka tasa Doguwar rigar Atanfa tayi mata k'yaou Sallah Azahar tayi sannan ta fito falo Tanti Nadiya k'adai ce a gidan dan har masu aiki Suna gidan Aida ko'da abinda zasu kama, Mama kuma tana'can gida wajen tuya dan ita ta d'auki n'auhin'ta, koda taci Abinci ta tashi da nufin komawa falo Abba ne ya shigo cikin hanzari yana ganin'ta ya t'saya yana fadin" Mama'na har'kin tashi, ai'na shiga dubaki dazu kina bacci" cikin sanhin jiki tace" eh Abba na'tashi, ina wuni" mat'sowa yayi kusa da ita ya dafa kan'ta yace" Mama'na ak'wai abinda kedamun'ki ne?" kai ta girgiza tace" babu komi Abba" a'a ya zakicemin babu Komai d'uk wanda ya gan'ki yasan ak'wai wani abu da'ke damun'ki" Abba babu Komai k'awai dai ina'jin baccin da nayi'ne shiyasa d'uk jiki'na yayi sanhi" d'auke hannun'shi yayi daga kan'ta yace" to Shikenan tin'da haka kika'ce amma kisani barin kashi a'ciki baya maganin yinwa, yanzu kifadamin abinda kike'so in anjima in'siyo maki" Murmushi tayi tace" Abba gafarar'ka k'awai na'ke nema nasan ban'k'yaouta maku ba amma....." kat'seta Abba yayi da fadin" haba Mama'na yafiya kuma akan me, kinga nidai babu abinda kika'min kuma nayafe'maki Duniya da Lahira kin'ji ko" cike da jin'dadi ta rungume mahaifin'ta kafin ya wuce bangaren shi ya d'auko abinda ya mai'do shi gidan....,
Bayan Sallah La'asar tana zaune kumshe akan gado tana kuka maganganun Mukhtar ne ke'dawo mata a'cikin k'wak'walwa, yaya Saif ya k'wak'wasa ya shigo cikin sallama bayan ta amsa Sallamar shi, zaune yayi yana k'allan fuskar'ta d'uk ta Kumbura sabida kuka yace" miya faru kuma miye haka?" cikin kuka kamar jira'take dama tace" yaya Saif ya'ci amana'ta ya cuce'ni wallahi bazan'yafe mashi ba" cikin rashin fahimta yaya Saif yace" wanene ya'ci amanar'ki Zeinab?" sabida ta bacin Ray yasa bata Boye komi ba d'uk abinda Mukhtar ya fada mata ta kara da cewa" sabida cin'amana da ke'ta haddi ya rasa in'da zai'ci amana'ta sai a cikin gidan'mu a d'akin mu a saman gado'na na sunna wallahi Allah sai'ya saka'min" fadawa tayi akan kafafun'shi taci gaba da rera kuka shiru yayi yana s'awraran ta kafin yace" Zeinab bana'so na'saje jin kina cewa wai mijin'ki ya'ci amanar'ki, dan d'uk Macen Arziki tana rufama Mijin'ta asiri bata fadan Sirrin shi, sannan kafin ki'yanke ma mijin'ki Hukunci kiyi tinanin mijin'ki wane irin mutum ne, ina nufin kiyi tinanin akan yanayin mijin'ki shin mai'karfin sha'awa ne ko kuma ya nada r'auni sannan miye yafi s'awrin daga mishi hankali a tare da mace, idan kikayi haka sai'kiyi abinda ya dace" ba'tare da ta dago da kan'ta ba tace" yaya Saif wannan ba hujjaba'ce da zatasa ya'ci amana'ta" a'a kanwa'ta na'sanki da fahimta da kuma hakuri, ina fada maki wannan ne daga zuciya ta zan'so ma mijin'ki abinda zan'soma kai'na idan da ni'ne haka ta faru zanji dadi ba ka'danba idan kika yafemin, kinga Dole na'mashi fatan ki'yafema shi".
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
80-85馃摋
K'allan'shi tayi tace" yaya Saif idan kai'ne kai'ma haka zaka'min?" shirun da yayi ne yasa ta d'ora kan'ta a kafadar'shi tana kuka, cikin ranshi cewa yayi( ta'yaya zan'iya haka Zeinab nayi hakuri tin'kina karama har'kika girma, bayan na'same'ki na sati biyu ne zan'kasa jiran'ki wallahi bazan'iya ba zan'iya kokari'na na kare kai'na da taimakon Ubungiji na) a hankali yace" Zeinab ki'nemi gafarar Mama idan ba'haka to irin Wannan zata dinga faruwa da'ke" daga kan'ta tayi tace" yaya Saif zaka rakkani to, watakila idan Mama ta'gan'ka ta hakura?" kai ya daga mata yace" zamu'je tare idan Mama ta'dawo zan'zo sai'na rakka'ki" a haka suka rabu.
Bayan Sallah Magriba su Mama ta dawo bayan Isha'i kuma yaya Saif yazo dan'cika Alkawarin da'yama Zeinab, tare suka shiga d'akin Mama tana zaune bakin gado tana Hada kayan da zata fita da'su gobe dan bata'so ta manta wani abu, gaishe'ta sukayi bata amsa ba sai Saif ne yace" Mama dama Zeinab ce tazo ta baki hakuri akan d'uk abubuwan da suka faru a baya kuma ta gane kuskuren'ta Insha...." bai karasa ba Mama ta kat'se shi ta hanyar daga mashi hannu tace" kaga dakata, Saif ni'fa ina hushi'ne da ita Sabida bata aure'ka ba, kuma zan'daina Hushi da ita'ne k'awai idan ta aure'ka" ci'gaba tayi da abinda take cikin sanhin murya yace" Mama shifa aure nufi'ne na Allah idan ya kaddara shi babu abinda ke dakatar da'shi idan'da Allah ya kaddara aure'na da ita to'fa koda kune baku'so da sai'anyi shi kamar dai yanda da ya kaddara auren'ta da Mukhtar gashi d'uk da baku'so ba amma anyi" k'allan'shi Mama tayi tace" Saif wai'ke wane iri ne wane irin So ka'ke ma Zeinab anya'ko wannan So'ne?" Murmushi yayi yace" Mama d'uk San'da nake mata Dole na'hakura da hukuncin Ubangiji" cikin tausassan murya tace" hakane amma kasan abinda yafi ko'namin Ray a game da yarinyar nan?" kafin ya'bata amsa tace" Saif kai kasan Wahalar da'nasha tin'da nasamu cikin yarinyar nan nasha fama da Azabanben l'aulayi wanda ban'taba yin'shi kasancewar'ta mace ta farko da nasamu cikin'ta, Saif kasani ba'komi nake iya ci'ba ba komi yake birgeni'ba haka nabi d'uk na'lalace, nazo saida nayi sati biyu ina nakudar'ta kafin lokacin Haihuwar ta yayi mukaje Asibiti, sanin kan'kane saidai aka shiga d'akin tiyata da'ni ana shirin parka ciki'na a fiddo'ta Allah yayi Ikon'sa na'haife ta da kai'na, sannan nazo rainnan'ta aka muka dinga samun mat'sala da Mahaifin ta Sabida shi bai'yarda yaji kukan'ta ba koda da wasa take kukan kamar dai'kai, amma wai y'aou wannan Yarinyar ce dana rejeta t'sawon shekaru ita'ce takasa yi'min abinda zai'sani Farin ciki so'daya tak taki abinda nake'so" kuka ne ya k'wance ma Mama haka Zeinab ma kuka take kamar ran'ta zai'fita har'saida Mama ta ci'gaba da cewa" kin'gan shinan Zeinab wannan shi'ne na'so hada'ki da'shi amma kika'ki, ina'da Tabbacin Saif bazai'taba bari kiyi kuka ba, wannan da kike gani d'uk zama'na na Mahaifiyar'ki amma shine ya'ke kuka idan kina kuka, shine yake rashin lafiya idan baki'da lafiya shine yake shiga Farin ciki idan kina walwala, idan bakida lafiya baya bari a kai'ki ko'wace Asibiti da kan'shi yake duba'ki amma idan za'a maki Allura saidai wani ya'maki ita amma ba'shiba, Zeinab kin'gan shi'nan akan'ki saida ya koma kamar Sakarai akan'ki saida yasa hannu ya mari malamar Asibiti sabida ta maki Allura kin'fashe da kuka, nasan kin'san s'auran abubuwan daya maki sabida kinada Wayo wasu abubuwan suke faruwa, amma yaou wannan massoyin'naki shine kika'ki kika'ce baki san'shi, yanzu gashi'nan sabida bayada zuciya kula yana'ta zarya akan'ki" wani irin kukan Nadama da dana'sani ne Zeinab take'yi tashi tayi da gudu ta fita farfajiyar gida tanaji kamar ta ka'she kan'ta ko zata huta, ji'take wani gagarumin abu a game da yaya Saif haka'ma kuma tana jin'shi a game da Mukhtar to miye mafita, idan da Allah zai'd'auki ran'ta da taji dadi tasan Dole kowannen su zai'hakura.
Saif ne ya same'ta nan Kafin yayi magana Abba ya shigo, dukawa Saif yayi ya Gaishe shi ya amsa cike da Kulawa yace" lafiya miya faru na'ganku anan?" Saif ne yace" babu komi Abba" k'allan su Abba yayi kafin yace" to Shikenan, amma Dan Allah ku'rage kebewa ku'kadai sabida gujewa fadawa halaka, na'yarda daku amma kunsan zuciya da Sharrin shedan yanzu ne sainya kai'ku ya baro'ku Musammam yanzu da ta'ke matar wani bai'kamata ku'dinga taba juna ba kamar yanda ku'ke adah, akwai Haramci akan hakan ku'kiyaye kin'ji ko" cike da Gamsuwa Saif yace" Mun'gode Abba Insha Allah zamu'kiyaye Allah kara girma" Ameen ya amsa ya dafa kan Zeinab yace" Mama'na jikin da s'awki ko?" kai k'awai ta g'yada juyawa Abba yayi zai'wuce ta rike hannun'shi cikin kuka tana fadin" Dan Allah Abba ka'yafemin laifin dana maku, Abba ka'rokamin Mama ta'yafemin laifi'na" kan'ta ya dafa yace" Mama'na na fada maki ba kimin komi'ba idan'ma kinmin to na'yafemaki kin'ji ko" wucewa yayi ya'barta dan harga Allah ya san ak'wai abinda ke damun'ta.
Saif ne ya k'alle'ta yace" kiyi hakuri kin'ji kanwa'ta, Insha Allah Komai zai'yi daidai" hawayen'ta ta shahe tace" yaya Saif ina'ji kamar wani abu zai'faru da'ni Dan Allah ka'yafemin ka'kuma rokamin Mama ta yafemin, sannan ka'shaida na'yafema Mukhtar laifin da'yamin wala'alla nima ALLAH ya yafemin a dalilin yafemasa da'nayi" Murmushi yayi yace" haka ake'so kanwa'ta yafema wanda ya'maka ba'daidai ba Insha Allahu Allah zai'dubi wannan Jarumtar da kikayi ya yafe maki kurakuran'ki kema" kafin tayi magana mukhyya shigo gidan saidai ganin'su tare ba'karamin tinzira'shi yayi'ba, dan haka cikin hassala yayo kan'su da hanzari, yaci k'wallar rigar Saif yana fadin" kai miya hada'ka da matata mi'kake a wajen'ta?" cikin mamaki Saif ya k'alli Zeinab yace" a sani'na kamar an'ce mijin'ki malamin makaranta ne mai ilimi,amma naga aikin'shi baya nuna haka yafi kama da jahili?" kafin Zeinab tayi magana Mukhtar ya k'alle'ta yace" ni'dama nasani tin'da kika'zo gidan nan kika s'awya nasan ba banza'ba ashe kin'samu wannan kiba holewar'ki da'shi" maida k'allan'shi yayi ga Saif yace" wallahi idan na'sake ganin da matata to sai'nayi ajalin'ka" jin'haka ne yasa Zeinab ta mat'so cikin bacin Ray ta rike hannun'shi tana fadin" El moc kasan abinda ke keyi kuwa miye haka wannan fa yaya Saif ne dan Uwa'nnn..." ba'ta karasa ba ya'juya da karfi tare da g'alla mata wani Wawan mari ta bayan hannu, wanda akayi rashin sa'a ya sameta a wuya hakan kuma ya'zo daidai da Ajalin ZEINAB take ta fadi kasa babu rai'ajikin ta, ganin ta fadi ne yasa Saif fincike hannun Mukhtar daga rigar shi ya zube Kasa yana Kiran sunnan'ta hannun'shi ya kara Kusan hancin'ta taji babu sheda haka'ma ya dora dan yat'san shi a saman mashedar'ta a wuta nan'ma shiru, kara sunkuyawa yayi da nufin yajiyo bugun zuciyar'ta da karfi Mukhtar ya fizgo'shi yana fadin" Karka soma cewa zaka taba jikin matata" cikin zafin nama Saif ya'kaima Mukhtar wani Wawan n'aushi yana ya nuna shi da hannu yace" ba jikin matar'ka zan'taba ba ceto ran'ta nake'so nayi, idan kayi wasa to zata zama gawa'ne" juyawa ya yi da karfi ya dora kunnen'shi a kirjin'ta saidai ina babu ko alamun sheda, wata irin kara ya fashe da ita tare da ida faduwa zaune yana'ja da baya kamar gurgu yana Kiran" Shikenan ka kashe'ta ka kashe'ta ka kashe'ta Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un.
12/01/19 脿 22:21 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
85-90馃摋
Sambatun da Saif keyi'ni yasa Nazir da'ke cikin d'akin shi tare da abokan'shi suka fito cikin s'awri dan ganin abinda ke faruwa, to basu fahimci wani abu ba gadai Zeinab k'wance a kafafun Mukhtar Saif kuma a gefe a kidime dan haka suka fara tambaya ganin babu wanda ya basu amsa yasa Nazir ya shiga cikin gida da gudu ya fada masu halin'da suka same'su, Abba da Tanti Nadiya ne suka fito da s'awran Yaran gidan Mama kuma tace babu inda zataje koma miye ya faru da ita ita tasani ita babu ruwan'ta,
Abu dai kamar wasa haka aka d'auki Zeinab zuwa Asibiti inda aka tabbatar masu da rassuwar Zeinab kin, t'sananin tashin hankalin da naga'ni a wajan ba'zai misaltu'ba saidai nafi t'ausaya ma Saif sabida har'yanzu abu daya yake firtawa shine" ya kashe'ta ya kashe'ta shikenan ya raba'ni da ita" tinani nayi kodai k'wak'walwar shi ta samu mat'sala, Mukhtar kam hawaye ne k'awai ke'iya fita daga idan'shi haka Suna k'allo har'aka nufi da gawar Zeinab izuwa d'akin ajiye gawa ( Morgue) tin'lokacin akayi Karfin halin Kiran mutane ana sheda masu mutuwar ta'ta dare yayi sosai su Abba sukabar Asibitin amma banda Saif da Mukhtar wanda akayi'ta masu Magana kamar basuji suma'dai kamar gawawwakin...,
a takaice dai anan suka k'wana basu masan cikin halin da suke ba, Abba ne ya shigo gida tare da s'awran magajiyan Zeinab kin dukan'su, Mama ce Zaune a falo ta kasa bacci sabida rashin dawowar'su amma tana ganin'su saita waye ta nuna bata cikin wata damuwa, zaune sukayi sai Abba daya wuce ya nufi d'akin Tanti Nadiya jin bata masu magana ba yasa ya t'saya ba'tare daya k'alle'ta ba yace" ki'shirya daga safiyar gobe zaki fara karbar ta'aziyar ta, ki'taimaka ki karbi gaissuwar'ta koda baki mata Addu'a" dammmm! gaban'ta yayi wata irin faduwa da s'awri ta k'alle'shi ta yunkura ta tashi amma sai'jiri ya debe'ta dan haka ta zauna da rarrafe ta karasa wajen'shi cikin kidimewa tace" Alhaji ina ya'ta miyasa'mu ya'ta ina ta'ke Dan Allah ka'fadamin?" wani irin Murmushi yayi mai'kama da kuka yace" yar'ki yar'kifa kikace, ko kin'manta kince kin'cireta daga yayan da'kika Ha茂fa sannan ba'ke ba'ita har'abada?"dafe kirji tayi ido waje cikin daga murya tace" a'a Alhaji kar'kemin ya'ta ta rassu dan Allah ka'fadamin gaskiya, nasan Zeinab bazata bar'niba ya'ta bazata mutu yanzu ba, ita kadai gare'ni mace mutuwa zanyi idan narasa'ta ka'taimakamin ka'kaini naga ya'ta" t'saki yayi ya wuce ya barta'nan k'allan yayan nata tayi gaba daya ta ma rasa kama sunan koda daya daga cikin'su dan haka k'awai sai'tace" kai" hakan yasa dukan'su su Shida suka juyo cikin kuka tace" ina ya'ta take miyasa'meta?" Nazir da'ke Karami a cikin'su ne yace" Mama kiyi hakuri Allah ya mata" bai karasa fada'ba AABOUBACAR ya wurga mashi harara, hakan yasa Mama ta fadi k'wance some da s'awri sukayi kan'ta na'dai ita'ma ta k'wana batasan inda take ba...,
*Washe Gari* haka kowa ya samu labarin rassuwar Zeinab ba'karamin kidima da Damuwa kowa ya shiga'ba babu wanda bai'zubar da k'walla ba idan ya tina Zeinab matashiya amma Allah ya karbi abar'sa ( to Allah kenan baya barin wani dan wani yaji'dadi haka Mutuwa bata Duban Yaro'ne ko Babba, Tsoho ko Tsohuwa idan lokaci yayi to bamakawa zaka'tafi, Saidai muyi fatan Allah yasa mu'cika da Imani)馃憦
farin ciki ya koma bakin ciki shiyasa akace( wai ana bikin Duniya akan'yi na'kiyama) gashi'dai ana jiran Safiya tayi asha bikin Murnar karuwa da Aida ta'samu, amma yanzu ya koma bakin Cikin rasa uwa ga wasu kuma kamar Kaka take a wajen'su, abindai kam babu dadi Masha Allah gida ya cika da mutane kasancewar su masu hannu da shuni da kuma yawon familly gida yayi shiru ga Mama da'ke k'wance har'yanzu bata farfado'ba, haka aka d'auko gawar Zeinab daga Asibiti ake wuce da ita gidan'ta na gaskiya( To Allah yasa k'wanciya Hutawa ce).
Shigowar Abba yayi daidai da fitowar Mama tana Kiran a kawo'mata yar'ta Abba ne cikin kunar Ray yace" Ramatou kenan wai'kece kike wannan h'aukan akan Zeinab ta rassu ai'kamata yayi kiyi farin ciki sabida ta rabu da wanda baku'so, haba Ramatou ace yar'da kika Ha茂fa ta cikin ki amma ki'ts'aneta sabida kaddara Ubangiji kina ganin da Allah bai'nufi auren ta da Mukhtar ba da zata aure'shine ai'kod muna'so to bazata taba Zala matar shiba, yanzu dai babu Mama'na dan haka sai'ki zauna kiyi farin ciki" Saif ne ya shigo a gigice rike da wuyan rigar Mukhtar yana dariya Yana fadin" kun'ganshinan wallahi shine ya kashe'ta shine ya bige'ta ta fadi ku'rike'shi kar'ya gudu" dakin rigar shi yayi ya nufi wajen Maman shi dake kokarin rike Mama ya rike hannun'ta yana fadin" Mama kin'gani ko ta'mutu shi kenan yanzu wazai kular mana da yayan'mu guda uku da muka Ha茂fa gashi kuma dan karamin yana'shan nono, kuma kinga Mama ni'dama na'fadamaki bana'san yarinyar nan k'awai dai ina san'ta ne amma ni ba k'aunar ta nake'ba k'awai tana birge'ni ne ko dariya yayi sai'takara k'yaou wallahi Mama sai'na bita, jiya mafa saida tace'min na'jirata a Aljanna amma gashi kuma ta tafi bamu hadu ba"kowa dake wajen ya fuskanci wani abu wanda nima na fuskan'ta wato Saif ya samu gushewar hankali, Mukhtar ya biyo Saif ne dan ya samu hukuncin shi dan rayuwa babu Zeinab batada wani anfani, Mama ce cikin tsananin fitar hayyaci ta shaki wuyan Mukhtar tana marin'shi iya Karfin ta har'saida hannun'ta yayi ciwo ta bari dan kan'ta sannan ta sake'shi tana kuka tace" miyasa miyasa Mukhtar miyasa zakayi haka mi ya'ta ta'maka, shin'kokasab Zeinab zallah soyayya ta nuna maka ta so'ka so'na hakika taki'bin umarni'na sabida san'da take maka,amma ka rasa hanyar da zaka saka mata saita hanyar rabata da ran'ta, wallahi wannan BA SO BANE ka nuna mata ko kadan BA SO BANE kuma wallahi sai Allah ya tada'ku ranar gobe kiyama ya Maku Hisabi mugu k'awai dama dan ka'rabani da ita ka'shigo Rayuwar ta ka raba'ta da dan uwan'ta" Kalaman Mama Suna kona mashi Ray Matuka ya Zaiyi yanzu saidai kafin ya farga Mama dake t'saye sukaga ta fadi,
Wata irin kara naji mai karfi ana fadin Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un.馃ぃ馃ぃ馃ぃ
13/01/19 脿 13:33 - Mme Sami馃槝: 馃挃BA SO BANE馃挃
*Gajeran Labari*
Na馃摎
Samira Harouna
90-95馃摋
A firgice ta mike zaune tana'ta maimaita kalmar Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un ta dafe kirjin'ta da hannu biyu, juye juye ta farayi bataga kowa a cikin d'akin ba da s'awri ta diro akan da gudu ta Buda kofar douche bataga kowa ba ko rufe kofar batayi ba ta fita da gudu tana k'walla kiran sunan" Honney, Honney, Honney" har'farfajiyar gida ta fito, kai t'saye wajen da aka kebe domin mot'sa jiki ta nufa tana'ci gaba da kiran sunan Honney, to nima dai ido na baza ina'so naga wannan Honney...,
juyowa yayi tare da jefar da Ball kin dake hannun'shi ya na k'allan'ta cikin mamaki yanda take gudu kamar ta manta cikin da'ke jikin'ta, k'yak'yawa ne sosai gashi dogo sanye da kayan sports bude hannayen'shi duka biyu ta fada ciki ya mat'seta yana fadin" miye faru ne Mon Chouchou waya taba'min ke, keda nabari kina bacci?" dago da kan'ta tayi cikin kuka tace" yaya'na wallahi Mafarki nayi mara dadi" dariya yayi yace" haba Ma Belle yanzu mafarkin ne keda wannan hawayen?" cikin shag'waba tace" dan baka'san ko wane iri bane shiyasa kace haka, amma d'uk mafarkin da zai'sa naga bana tare da'kai ai ba'karamin mummunan Mafarki bane a gare'ni" shima cikin shag'waba kamar yanda ya rene'ta yace" Ohh My Gosh, sorry kin'ji Chouchou'ta hakan bazata sak茅 faruwa ba" ita'ma cikin kuka mai kama da shag'waba tace" kuma fa Baka gani'ba wai na auri wani b芒 kai'ba, kuma wanda na aura shiyayi sanadiyar mutuwa ta, sannan Mama ma ta fadi ina'jin t'soro kar'ace ta'mutu ita" hannun'ta ya kama suka koma falo ya zaunar da ita yace,
"kin'ga kanwa'ta ta kai'na ki k'wantar da hankalin ki babu abinda zai'faru, ga'ki nan a raye babu abinda ya same'ki, sannan ga'ni tare da'ke kuma a mat'sayin mijin'ki sannan d'auke da cikin da'na na wata biyar" Murmushi tayi tace" hakane kuma fa, to amma ai a mafarki'na ma nasa'mu ciki amma dai shi zubewa yayi" ti kin'gani ko, amma ni naga nawa'nan a jikin'ki ba kuma jiya kinje awo an'tabbatar mamu da lafiyar shi" amma kasan abinda ya sani jin'dadi?" kai ya girgiza yace" sai'kin fada" cikin karsa'shi tace" naji dadin yanda naga ko a Mafarki irin Soyayyar da ka'ke nunamin a zahiri ita nagani a badini ma" jawota yayi ya Rungume ta yace" Zeinab ina san'ki sosai nasan ko a zahiri ko a Mafarki abinda zaki gani kenan" dago kan'ta tayi tasa bakin'ta a nashi ta t'sot'sa kafin ta k'alle'shi tace" ni'ma ina san'ka yaya Saif, wallahi naji nakara san'ka yaya'na tabbas bazaka iya Rayuwa Babu ni'ba kamar yanda bazan'iya rabuwa babu kai'ba" Murmushi yayi yace" to da kika mutu a Mafarki ni'kuma yanayi?" cikin kunya tace" haukacewa kayi" tabbas Zeinab ko ban'biki ba nasan abinda zai'faru da'ni kenan idan narasa'ki" tashi tayi tace,
" ni Yinwa ma nake'ji bari na dafa'mana wani abu mu'ci" rike hannun'ta yayi yace" ai'kema kinsan tin'da kika samu cikin nan ba'kullum kike girki ba, yanzu ma Mama ta aiko maki da abinci kina bacci wai karki'sha wahala" zaune ta koma tana fadin" gaskiya su Mama suna'san su shag'waba'ni sosai karfa nazo na zama bukekiya" wani k'allo ya bita dashi yace" to zama bukekiya kuma ba y'aoushe ai saidai kiguji karawa" k'wabe fuska tayi tace" kaga fa bana'so ko wallahi zan'fa ma su Mama kana cemin bukekiya" dariya yayi ya jawota yace" yi hakuri kar'ki fada kinfa san yanzu yanda su Mama ke ji'dake basu'son wani abu ya tabaki ni narasa dalilin wannan shag'waba kin da suke" cikin ji'dakai tace" sabida ina d'auke da jikan'su ne kuma Mama ni'kadai gare'ta mace shiyasa sukemin haka".
Abinci sukaci inda Zeinab ta takura sai sun'buga Ball kamar yanda suka saba, ba yanda ya iya Dole suka'yi kafin yace ya gaji gashi kuma La'asar ta'kusa t'saye tayi waise ya goya'ta ko taki shiga d'akin yana sunkuyawa tayi kalam ta Haye bayan'shi haka har'saida ya kai'ta douche wanka sukayi suka fito cikin shirin sannan ya nufi Massalaci ita ma tayi Sallah, ta jima tana Addu'a da Allah yasa Saif ya zama miji'ta ya kula nuna mata ai'nahin wane'ne Mukhtar sannan tayi farin ciki da taki karbar Soyayyar Monsieur Mukhtar Ashe ba Alkairi bane a gare'ta, da haka ta sak茅 daga hannu sama tace" Allah Nagode maka da ka bani Yaya Saif a Mat'sayin Mijin aure'na Allah ka kara Bamu zaman lafiya mai dorewa Allah ka sa na'haihu lafiya, Allah ka kare'min Yaya Saif ka bani ikon K'yaoutata mashi da yi'mashi biyayya" Ameen.
Yana dawowa daga Massalaci suka zauna akan Kujera Zeinab d'uk ta nar'ke a jikin'shi taki zaune da kugun'ta, cikin Zolaya yace" ke dan Allah ki'daga ni d'uk kibi kin haye'ni haba sai'san jikin t'siya" dariya tayi tace" to ai d'uk kai'ne ka sabamin kai'ka kaya'min koma minene" eh to dan nakoya maki sai'kuma akace bazaki z'auna da kugun'ki ba kamar wata marar lakka" bata Ray tayi kamar zata'yi kuka ta bashi baya wai ita antaba'ta, rarrashi ya fara kuma" haba yar Mama da Abba da Mama da yaya Saif kiyi hakuri wasa nake maki dama" cikin shag'waba tace" ni ban hakura ba wallahi sai'kaban wannan abun sannan" sanin ko miye yasa ya tashi ya shiga d'akin shi ya fito yana Mika mata Chocolat Babba yace" to ga Shi sai a hakura yanzu ko?" kara juya baya tayi tace" ni ba Daya nake'so ba sai guda biyu" ya sani dan haka ya fito da Daya hannun da yasa Aljihu ya Mika mata yace" to g芒ta shi kenan yanzu?" da karfi ta jayo'shi ya zaunar dabas ta Rungume' shi tace" Merci beaucoup Mon Ange" to nidai na peceee Alla bar Soyayya鉂ゐ煓忦煆�.
*Yan Uwa anan nakawo karshen Wannan littafi mai sunan BA SO BANE ina fatan za'a anfana da shi*
Idan Zeinab ta haihu zan'fada maku muje biki馃榿
*My Meelat bazan manta da'ke ba*馃槝
Alhamdu lillahi Kassiran馃憦
0 comments:
Post a Comment