Suna fitowa daga kotu direct safiyya gida ta wuce dan kuwa bataso su hadu dasu inna luba.sufyan shi ya dauko su a mota inna luba take cemasa "sufyanu naga safiyya amma bamusamu mun gaisa ba kan tawuce. Naga kaman aiki ya mata yawa ne" (dan kuwa su basu fahimci cewa kare ma faisal takeba)
yayi dan murmushi yace "eh inna da yake tare muke banaso ne su faisal su fahimta akwai aikin danasata ne", maidasu asibiti yayi Nan nurse din tace ai yau ma za'a sallamesu tunda mai jinyar taji sauki,
Sufyan yayi jim yana tunanin ina zai kaisu saiga safiyya ta shigo dauke da flasks na abincin rana. Da sauri amira taje ta tarbota cikin dariya tace "laa ga antynmu , ansa kayan tayi tana fadin aiko kin makara dan kuwa yayo mana takeaway mukaci amma nidai sai na dandana girkin antyna", "yo aikya bari ta kariso mugaisa ko kabarai uwar zance" cewar inna da take kwashe sauran kayayyakinsu .
Safiyya tayi murmushi wanda beauty point dinta ya dan motsa tace "ai inna ba surutu take ba hira muke",
Sufyan mamaki yacika shi a tsaye" lallai sofy bata tsoron allah, ace misali yanzu su inna sun gane ta itace lawyern faisal fa.baisan menene manufarta ta ansan case dinnan ba .to bata tsoron bakin mutane duk da ya kula dayawa basu san mijin ta bane, but she is his wife kuma ko'ina taje dole ta amsa sunarsa na shi mijin ta ne amma zai kyaleta amma ta bashi mamaki fa .hmmm lallai safiyya _green snake under green grass_ ce
Fari tayi da ido hade da cewa "ashe kana nan, dama naga baka dawo gida ba tun dazu",
"Hmm ina nan na kawosu" ya fada a takaice
Amira tace "anty kinjifa sun sallamemu, gashi nan inna sai hada kayan mu take
"Aikuwa sai mu wuce gida dama da mota nazo",
Ganin haka yasa sufyan yimusu sallama ya wuce . Su kuma suka dinga shigar da kaya mota sannan sofy ta jasu suka wuce gidanta.
Dakin dake gefen na sofy nan ta zuba musu kayansu. Ta gyra shi itada amira sabida kuran da yayi sannan inna ta shige abinta ta kwanta. Safiyya kuwa ita da amira suka shige bedroom dinta tana yiwa amira tsifar kai " amira kanan naki akwai cika",
"Kai anty ai naga naki tsawo ne dashi. Dama nawa ne da nadinga gayu dashi a gari"
Safiyya ta waro ido "amira gayu kuma! Niko kinga ummata tayita fama nayi kitso amma nakiyi sai ta kamani tamin",
Amira tace "yawwa anty dazun a kotu baki bari mun gaisa ba kika tafi, da inna tayiwa yaya sufyan magana sai yace ai kina sauri ne domin ya saki wani aiki ne akan su faisal. Ba kyaso su ganki damu",
Safiyya a zuciyarta take fadin "hmm aiko yayi gaskiya dan kuwa batason su faisal su san cewa tasan inna kawai ta ansa case dinne dan itama ta taimakawa su inna ta bayan fage.. dakuma jan fada tsakaninta da gogan nata dan wulakanchi",
A fili sai tace "eh ai na ganku amma ina sauri ne, lokacin suka gama tsifar sannan safiyya tasa shampoo ta wanke mata kan dashi .hand dryer ta dauka ta busar mata da kan tare da samata mayuka masu kamshi gashin nata yakeyi . Sannan tadauko mata ribbon ta daure mata kan dashi .
Tare sukayi girkin dare inda suka tuwon semo da miyar agushi taji bushashshen kifi sai sukayi kunun aya mai kauri.
Sai da suka ga anata kiraye kirayen sallahr magriba sannan suka tashi inna dan tayi sallah domin kuwa tana daki tanata bacci.amira tayi wanka tareda sofy sannan sukayi sallah. Da yake amira bata taho da kaya ba sai safiyya ta bata doguwar rigarta baka tasaka tayi kyau abinta sofy tayi mata simple make up
"Inyeh.. amira kinga yadda kikayi kyau kuwa kai yau inna baxata gane ki ba?",
Amira tayi dariya tace "anty ai duk kyau na kinfini kawai dai kina tsokanana ne,
Ji sukayi ana knocking kofar dan haka amira taje ta bude masa. Koda ya ganta murmushi yayi ita kuma tana fadin "yaya sufyan sannu da dawowa,
"Yawwa sannu da gida amira",
Safiyya tana daga zauna akan kujera da flat shoe a kafarta ta daura kafa daya kan daya tana sanye da wata brown din riga da sket na atamfa kayan sun amsheta tayi kyau abinka da farar mace .gashin nan kwance luf luf a jikinta da kuma na kanta daya kusan rufe mata goshi. ya zo ya shige dakinsa bata ko dago ta kallesa tym din inna na daki tana lazimi .
Amira ta dawo kusa da ita tana fadin "anty bakiga yaya ya dawo ba ne",
"Naganshi mana amira" ta fada a gajarce
Amira tayi jim amma sai ta share tunda ba ruwanta dashiga shirgin mata da miji.
Ana kiran sallah issha'I sufyan ya fito kenan ita kuma sofy ta sauko daga dining zata wuce ta kofar dakinsa ya fito sukaci karo. Zata fadi yayi saurin tarota gaba daya jikinsa ya rungumeta
[3/7, 11:50 PM] +234 703 962 5239: *````MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```NA UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<14>```
Kamshin turaren ta ne yake dokan mishi hanci, a hankali ya lumshe ido kafin tunaninsa ya saisaita sannan cikin sanyin jiki ya raba jikinsa da nata, ganin amira na falon.
Yana saketa da sauri ta shige bedroom dinta bata juya ta kalli amira ba.zama tayi a kan gado tana sauke ajiyar zuciya dan kuwa inda ace bai tareta ba da mummunar faduwa zatayi, lumshe ido tayi jin kamshin turarensa a hannunta na special " gayen nan akwai san kamshi",
Tana zaune amira ta shigo ta dane jikinta tace "kin kuma barni nikadai daga zuwa dauko turaren wuta",
Safiyya ta shafi gefen kumatunta "sorry lil na mance ma ni shaf.bari na dauko muje muci. Kin kaiwa inna nata?,
"Eh tun dazun nazuba mata, kinsan inna wai ita a daki zataci tunda shi ya sufyan ya dawo",
Dariya sukayi dukkansu sai amira tace " na ya sufyan a daki zai ci ko dining din?",
Safiyya tayi jim sannan tace "I don't know but ki bar masa a dining din, muje",
Suna zaune amira tana serving dinsu yayin da safiyya ke waya da cwt safina, sai dariya take yi, sufyan ya dawo , ganin safiyya na waya ya sanya amira ce masa " yaya ga fa abincinka a nan",
Dakatawa yayi, kamar kar ya juyo amma wata zuciyar tace masa "karfa yarinya karama tagane meke tsakaninsa da sofy",
Juyawa yayi yana murmushi mai kara masa kyau sannan yasamu daya daga cikin kujerun ya zauna, yana fadin " ina inna ta shiga ne",
"Tana dakinta, sannan ta zuzzuba masa abincin da tun kafin yaci yawunsa ya tsinke, dama rabon dayaci girkin sofy tun zuwansu safina.hannu yasa yafara ci sai a sannan safiyya tagama wayan sannan tafara cin nata. Baka jin karan komai sai na cokula dakuma fanka dake ta aiki, sai da sufyan ya cinye mulmule biyu, ita kuwa sofy tana ci tana satar kallonsa yanda taga yamata kyau cikin rigar blue wanda aka rubuta _handsome_ ajiki sai wando jeans .gashi kansa a kwance kamar balarabe ga saje luf wanda yawa fuskar kyau .dan bakinsa dan karami gashi kamar ya shafa pink lipstick, a zuciyarta tace "kacika sunanka handsome din amma ba hali",
Shiya fara gamawa sannan ya shanye kunun ayan, shikansa ya kanyi mamakin cinsa inda na sofy ne. Ni kuwa ummu nace ai girkin sofy ba baya ba gun dadi .
Ita da amira ne suka gyra dining area din sannan sukaje sukayi sallah, safiyya ta mike tana cire kaya dan ta shiga wanka "kai anty ba dazun mukayi wanka ba",
Safiyya tace "eh ai wannan wankan na bacci ne amira.ke bazakiyi ba?",
"Tafdijan yanda nakejin sanyin nan",
Safiyya tayi dariya "aini komin sanyi sai nayi wanka, umma tace ta koyamin, allah sarki ummata na dade banganta ba.insha'allahu aunt amina na haihuwa sai nayi wata daya a masarauta",
Amira ta kalleta"laa anty masaurautar ina?
"Ta gombe"?
"Har yaya ma dan gidan sarauta ne"?,
Safiyya tayi murmushi "eh mana. Unguwar mu daya",
Amira tayi dariya hade da gyada kai "shiyasa nake ganinsa bai fiye san magana ba ",
Safiyya tayi dariya harda kyalkyalawa tace "lallai amira akuwa zan gaya masa kinyi gulmarsa",
Amira ta toshe baki "rufamin asiri dan allah , jan bargo tayi "sai da safe",
Safiyya ta wuce toilet a zuciyarta tace "miskili kawai",
Wanshekare da safe inna tanata yiwa amira fada bayan tazo gaisheta "tayaya zakije ki kwana a dakinta banci kinsan cewa idan taganki ba korarki zatayi ba, zama zatayi ku kwana tare bancin ga dakin mijinta nan, kar na sake gani, kina jina ko?,
Amira ta shagwabe fuska "to inna",
Safiyya ta shigo suka gaisa da inna, inna sai shi musu albarka takeyi ita da sufyan irin halaccin da suke musu.
Bayan sungama breakfast ne wayar safiyya tafara ruri alamun kira, data duba sai taga nomba abdul, da sauri ta shige daki sannan tayi picking...
[3/8, 12:02 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```NA UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<<15>>```
Sallama tayi sannan abdul ya dauka hade da gaisheta
"Brr. Inason ganinki ne,ko nazo ne",
"No bari ni nazo, a ina kakeson muhadu",
Abdul yace "muhadu gidansu faisal dan shima alhaji yana son ganinki",
"Ohk to ganinan zuwa,"
Abdul yayi dariya"dafatan dai ban takura miki ba ko ",
"Uhmm ba komai sai nazo",
Abdul yayi mata godiya ya kashe wayar.ita kuma safiyya tana nan zaune da wayar a hannunta tana tunani
"Yanzu dai shedunsu a kotu hajiya ce kawai sai kuma doctor din dayayiwa amira theater",
Da sauri ta mike jin wata idea ta fado mata na yadda zata taimaki sufyan bai sani ba.
Hijjabi ta dauko dogo maroon colour tasaka sannan ta fito tare da key na motar a hannunta. Amira daketa game a dayan wayarta ta dago tana kallonta da murmushi
"Amira bari naje nadawo kinji, kicewa inna nafita",
"To anty saikin dawo",
Da sauri taje parking lots ta dauki motar ta ta wuce asibitin dake girke a dutsimma .
Bayan tashiga ta hadu nurse din ta take kula da amira suka gaisa dashike morning duty takeyi. Nurse din mai kirki sunanta feenah
, ta tambayeta ya amira da jiki, safiyya tace mata ai ta warware .
Safiyya ta kalleta tace "sis feenah wani taimako zaki min dan Allah, inason ganin doc. Din dayayiwa amira theatre ne plss",
Sis feena ta muskuta "aikuwa antyn amira kin taki sa'a dan kuwa shekaran jiya ya bar nan ya tafi Cyprus",
Safiyya ta dan waro ido waje "kash! Wallahi gashi wani taimako zai min",
"Wani taimako kenan antyn amira?",
Safiyya ta danyi kasa da murya tace "kinsan case din amira fyade aka mata, to case din yanzu yana kotu to shine zai bada shedan cewa tabbas fyade aka mata tunda shiyayi treating dinta",
Sis feena ta yi jim can tace "ai akwai folder dinta wanda ya kunsa komai, zan je na fiddo miki sannan ina tunanin daya ga watan October doc. Zai dawo .kuma nima zan iya zuwa na bada sheda a kotu indai akan abinda akayiwa amira ne.domin kuwa tabani tausayi karamar yarinya haka,",
Farin ciki ya ziyarci zuciyar safiyya "nagode sosai sis feenah, amma kin gane ni ina daya daga cikin lawyer datake kare wanda yayi fyaden. So zamuzo dasu zuwa gobe wurinki, zamuce muna bukatar ganin doc, sai ki gayamana ai anyi masa transfer ya koma Cyprus .inkuma sunyi miki maganan folder sai kice musu ai tunda aka sallame su amira aka bawa yayanta folder din",
Sis feena tayi murmushi tace "bakomai antyn amira insha allahu kar kiji komai a ranki.bari na dauko miki",
Mikewa tayi taje ta binciki mata sannan ta kawo mata duka.
Safiyya ta ciro kudi dayawa a jaka wanda momy da umma ke yawan aiko mata dasu ta bata.aiko sis feenah sai godiya take zubawa. Dan kuwa duk zuwan sofy sai ta mata ihsani .
Kai tsaye gidan alhaji usman ta nufa.parking lots taje ta aje motan sannan takira Abdul cewan gata ta iso. Hangosa tayi tafito daga cikin gidan sannan yayi mata iso zuwa ciki.
Alhaji ne a zaune ya zuba uban malunmalun yanata hura hanci .sai faisal a gefensa yana cin fruits. Abdul ya shigo ya zauna tare da safiyya a bayansa .
"Sannu da zuwa Zauna mana brr.cewan faisal daya mike yana mata murmushi
Karasowa tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun dake fallon sannan suka gaisa da alhaji .
Abdul ne yafara magana "yawwa brr dama abinda yasa muka kiraki shine ko kinada wata shedan ko shawarar dazaki bada ",
Safiyya tayi murmushi bayan masu aiki sun cika gabanta da drinks da kuma fruits " ai shedanmu yanzu nafarko itace hajiya",
Alhaji ya washe hakora yace "ai tuni ya tura hajiya ibadan.nasa driver na nacan ya zo ya dauketa.dan haka koda kotu tana bukatar ganin hajiya to zamu bata da lafiya mun kaita london . Kuma ance ba'ason ta cikin hayaniya ",
Faisal da abdul sukayi dariya dukkansu ganin alamu na cin nasara,
Safiyya tace" na biyu kuma sai doctor din dayayiwa amira aiki",
Da sauri alhaji ya dago yanafadin "wayeshi doc din kuma wani asibiti ne",
Abdul ya kalleta yace "dadina dake akwai kwakwalwa brr.munagodiya gaskiya.yanzu yaushe kike ganin zamuje asibitin",
Safiyya tace "to yau ko gobe.kaga yau friday kila bazamu samu doc ba tunda gashi yanzu har 12 tayi ko zamu bari sai goben?",
Abdul yace "to a bari goben
Alhaji yace "kinsan nafiso komai ayishi zafi zafi yanzu haka banasi wannan shegen lawyer nasu ya rigamu zuwa, danni fa da zan ganshi ko...mai rabani dashi sai Allah",
Faisal yayi dariya yace "daddy ka kwantar da hankalinka ai muzamuci nasara insha'allah",
Safiyya dai ta mike tace musu to ni zan wuce gida ,
Alhaji ya dibo kudi bandir bandir ya bata tace ya barshi ita bata bukatan kudi a yanzu.
Faisal da Abdul suka rakota ta hau mota ta nufi gida.
Tana shiga da motar ta shima sufyan ya kunnu kan tashi motar a jiye dai-dai nata suka fito a tare
[3/8, 12:07 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<<17>>```
Sai da yayi sallar magriba sannan ya shiga fada,falo ya samu mai martaba da umma zaune,sunyi mutukar farin cikin ganinsa,
ya tsugunna yana gaishe su mai martaba ya mika masa hannu suka gaisa "saukan yaushe sufyanu",
sufyan ya dan sadda kai yace "dazunan nazo gaf da sallah magriba,
ya juya suna gaisawa da umma. Umma ta fita tayiwa kuyangu magana cewan sukawo masa abinci .
Nan umma ta sashi sai da yaci. Sai kasa kasa yake da kai wai shi yana gaban sirikai, tare sukayi sallah da mai martaba sannan ya wuce gida.
A safiyar monday karfe bakwai dai dai, safiyya tana breakfast yayin da amira ke lafe akan kujera tana kallonta .
Safiyya ta bude jakarta ta ciro folder ta kira amira "kinga ungo wannan, naga yayan naki baya nan yayi tafiya (dan kuwa tanada yakinin cewa indai bataji duriyarsa ba, to yayi tafiya zuwa gombe ne), dan haka idan yazo kibashi kinji. Kice masa kawai gashi naki ne",
Amira ta amsa tace "to, sannan safiyya ta dauki key din motarta ta bar gidan.
yana gama yin breakfast ya nufo kaduna, lokacin da yaje gidan safiyya bata nan. Amira ce kawai a falo tana kallon mbc 3, ya shigo da sallama , amira ta amsa cikin murmushi ta mike "sannu da zuwa yaya",
Shima murmushin yayi mata yace "yawwa amira ina inna?,
"Tana ciki, kila bataji zuwan ka bane.bari nayi mata magana",
"A ah barta bari nashiga, shiga yayi ya sameta zaune bayan ta idar da sallah azahar, sannu inna ya fada tare da zama a daya daga cikin kujerun dake dakin.
Gyara zamanta tayi tana murmushi"yawwa sannu sufyan ya kokari",
"Alhmdllh .kuna lafiya",
"Kalau muke ,Allah ya shi albarka kuma baku zuri'a dayyiba kai da matarka da kan irin taimakon da kuke mana.kuma Allah ya taimakeku",
Murmushi yayi yana maijin dadin addu'oin datake masa , Amira ta shigo dauke da folder dinta na asibiti ta tsugunna ta mika masa tace "ya sufyan gashi inji anty tace nabaka",
Ansa yayi yana dubawa, bayan ya gama dubawa ne, yaga wata yar takarda ansa _doctor daya dubata ya tafi Cyprus sai 1st October zai dawo_,
Kallon amira yayi yace "ita tace kibani?",
"Eh ita tace na baka lokacin dazata fita dasafe",
Ya kalli inna yace "bari nashiga ciki inna.
Yana kwance a daki yayi rigingine yana kallon sama, "to menene nufin safiyya na a bashi wannan folder, kuma alhalin gobe yakeson zuwa asibitin domin ya anso domin yazama evidence a kotu, to menene nufinta?",
Kodai taimakonsa takeyi ne, Allah kadai yasani, rike folder yayi yana murmushi sabida jibi yakeson ya koma gidan alhaji
Ranar sati sufyan ya koma gidan alhaji inda ya tarar da musa driver .nan ya gaya masa address din gidan alhaji na ibadan aikuwa sufyan ya basa kudi sosai sai godiya suke.
Ranar sukuma su Abdul da safiyya sukaje asibitin da aka kwantar da amira domin ganin doc.
Sis feena suka samu aikuwa ta musu kyakkyawan tarba.
Abdul shi yayi mata bayani akan yanason ganin doc din daya duba amira (ya mata kwatance akan cewa shi dan uwanta ne)
Safiyya yi tayi kaman basu san juna ba ita da sis feenah, "aikuwa baya nan antura shi Cyprus",
Safiyya ta dafa kai alamun jimami tace " kash. Yaushe zai dawo ne?",
Sis feenah tace " gaskiya banida masaniya akan ranar dazai dawo",
Abdul yayi shiru can yace "amma inason information akan kwanciyan datayi a asibiti ne.zamu iya samun file dinta",
Sis feenah tace "ai tun ranar da aka sallamesu wani yayanta yace mubashi dan allah",
Safiyya ta kalle Abdul akan cewa su tashi su tafi, sallama suka mata sannan suka fita, a kofar asibitin Abdul ya kalli safiyya
"Yanzu ya muke ciki ne brr.?"
"Ai wannan ba abun damuwa bane, tunda doc bayanan.",
" To ni tunani na wane ne yayan ta din da akace an bawa?"
Safiyya tace "atunanina bata da yaya sai dai ko lawyer su",
Andul yayi dariyar keta yace "indai ko shine wallahi ya shiga uku.dan kuwa da kansa zai dawo mana dashi, yanzu kawai muje munemo address din gidan lawyern",
Safiyya ta hadiyi yawu a zuciyar ta tace "ai gidan lawyer dinsu shine gidana, amma a fili tace "ok mutafi gidan alhaji muji tukun ko.
Sufyan karfe 10 na safe ya dira a ibadan inda ya bi address din da musa ya bashi ya nufi gidan alhaji na ibadan. Kwankwasa kofar yayi sannan mai gadi ya fito. Sufyan yace "hajiya kulu nake nema",
Mai gadi ya bude masa sannan yamasa iso zuwa falon. Mai aiki hajiya ita taje ta kirayi hajiya sannan ta kawo masa ruwa tace masa ga hajiyar nan zuwa..
[3/8, 12:12 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```NA UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<<16>>```
Kallo ya dan bita dashi na 'yan seconds sannan ya juya ya shige ciki .ajiyar zuciya ta sauke sannan ta tabe baki itama tabi bayansa.
Tana shiga Amira tazo da sauri suka rungume juna "anty kin barni shiru ni kadai gashi inna tana bacci",
Safiyya tayi dariya "to ai gani na dawo.kuma ai akwai wuta saikiyita kallo, bari nashiga ciki na watsa ruwa",
Amira ta kalleta "to anty kifi",
Dariya sukayi dukkansu sannan Safiyya ta wuce ciki,
Sufyan yana daki kwance rigingine akan gado yana tunanin abinda zaiyi game da case din amira .can ya tuno cewa daga ji hajiya wato mahaifiyar faisal bata goyon bayan abinda mijin ta da 'danta sukeyi dan haka ya yanke shawarar samunta.
Kai tsaye gidan alhaji ya nufa.yana isa yayi parking motarsa a waje sannan ya fita ya fara kwankwasa gate din, maigadi ne ya bude ya na fadin"wanene?",
Sufyan ya matso kusa dashi hade da mika masa hannu suka gaisa, sufyan yace "dan allah inason ganinka ne",
Nura maigadi ya bude masa gate din ya shigo sannan ya ya dauko masu kujeru ya ajiye musu yana fadin "biamillah zauna",
Sufyan ya zauna suka kara gaisawa."sunana sufyan.dama nace dan Allah hajiya kulu nakeson gani, dan uwanta ne ni ko tana ciki",
Nura ya washe baki jin cewa sufyan 'dan uwan hajiya ne "ai malan sufyan hajiya bata gidan dan kuwa kusan kwananta uku bata nan",
Sufyan ya girgiza kai yace "kash! Ina taje ne gashi aiko ni wurinta akayi",
Nura yace "ai dashike alhaji shi yana nan da faisal, sai dai in zaka jirasu zuwa anjima dan kuwa yanzun suma suka fita",
Sufyan yayi dan jim sannan yace "to amna ita hajiyar ne inata kiran wayarta bana samu.shiyasa nace bari nazo nasameta muyi magana",
"Aiko hajiya bata nan ",
Sufyan ya mike yace inazuwa.fita yayi ya dauko wayarsa da kudi kimanin 10k sannan ya dawo wurin nura yace "ga wannan kudin nagode sosai .dan kuwa naga kanada kirki.amma ina mai aikinta fa inna da 'yarta?",
Nura jiki na rawa ya tsugunna ya amsa yana zuba godiya.aiko ba shiri yace masa "ai ita inna zasuyi sati daya rabonsu da gidannan dankuwa ranar bazan manta ba akazo momy da ita suka zo suka wuce da amiran sai naji ita innar nacewa ai shikenan faisal ya kashe mun ita, nashiga uku hajiya fyade yayi mata.tana fadi tana kuka suka shiga mota da sauri suka wuce da ita.to nidai inata tambayansu naga kaman ma basujini ba, sai can da jimawa ne hajiya ta dawo, itama batace min komai ba shiyasa nima ban tambayeta ba,
Sufyan ya gyra wayarsa dayake recording aciki yace "amma nura ya alakar ka take dashi alhaji a gidan nan?",
Nura ya gyara zama yace "ai ba'a cewa komai, amma yasin alhaji bashi da mutunci kwata kwata 'yan aikin gidan baya ganin mutunchin kowa. Kusan nine mai gadi na goma sha biyu gidan nan , kuma sauran ma duk tsiya ta koresu, ya daurewa dansa gindi basa ganin kowa da gashi, hajiya ce kawai mutuniyar azziki amma idan akace maka alhaji to zance ya kare .dan albashin namu ma sai muyi wata da watanni bai bamu ba dan mugunta , sai dai hajiya ta kiramu ta bamu. Au alhaji azzalumi ne , bazaka sani ba sai ka zauna dashi.kuma bazan yi musu ba dan ancemin faisal fyade yayiwa amira dan kuwa halinsa daya da ubansa kuma haka yake wucewa da matan banza cikin gidannan",
Sufyan ya girgiza kai alamun jimami yace "amma yanzu baxaka iya nemomin ko hajiya ina ta tafi ba",
Nura ya dan duko gudun kar wani yajishi yace "ai dazun ban fada maka bane dan kar a daukeni munafiki amma jiya naji alhaji yana magana shida faisal lokacin inaba flower ruwa cewan ai hajiya sun tura ta ibadan gidan alhaji na can dan kar taje tayi sheda a kotu",
Sufyan yace "ibadan kuma?",
Eh ibadan ai alhaji yana yawan zuwa can dan yanada kampany a can"
Sufyan ya maida wayarsa aljihu yace "kaga malam nura inaso in taimaki su inna da kuma hajiya, dan kuwa alhaji so yakeyi ya kashe su",
Nura ya gwalo ido , sannan sufyan ya cigaba da cewa "dan haka yanzu zaka taimaka min nasan adireshin gidansa na ibadab din",
Nura ya furzar da goron dake bakinsa yace "cabdi! Wannan sai dai idan musa driver ya dawo sati mai zuwa.dan kuwa shima yayi tafiya",
Sufyan yayi murmushi mai kara masa kyau yace "to bakomai nura zanzo ranar satin amma zan kwankwasa maka kofa ne sai kafito muyi magana dan kar kowa ya ganmu",
Nura ya gyada kai yace "indai wannane bakomai.sai kazo",
Sufyan ya mike sukayi musabaha sannan ya fita ya hau motarsa, kai tsaye gombe ya nufa dan yafito da shirin zuwa.
Lokacin daya isa yamma tayi sosai dan haka gidan momy yafara zuwa. Mommy sai murna take , takawo masa wannan ta kawo masa wancan.
Tazauna gefensa tana fadin "ita yar tawa baka tahomana da ita ba.kusan watan ta takwas fa rabon da na ganta tunda tazo gaida sarki lokacin baida lafiya kodai tayi nauyi ne?",
Sufyan ya dan sosa keya ya ce "uhm.. momy kinsan makaranta take to yanzu karatun nasu yazo karshe shiyasa.amma tace na gaisheku",
Momy tayi murmushi na jin dadi "muna amsawa.to kagama kaje fada ka gaishe su ko",
"To momy bari nayi sallah tukun dan nan zan kwana zuwa gobe sai na wuce",
Mikewa yayi ya wuce dakinsa a zuciyarsa yana tunanin maganar momy wai ko safiyya rayi nauyi "kwazo ku dauketa yadda kuka kaita",
Lumshe ido yayi tuno ta jiyan nan da ta fadi jikinsa, gaskiya sofy ta mallaki komai na macen data amsa sunanta mace amma sai dai kash batada hali irin na matar dayakeso, sofy batada kunya at oll, danma yana yawan azumi dakuma kauda idonsa akan mata sabida yasan halinsa amma da jiyan nan inda bai saisaita kansa ba .da yayi abin kunya",
Lashe lebansan yayi na kasa sannan ya sauke ajiyar zuciya "sofy kenan, kaman ba ita ya rena tana yar mitsitsuwa ba",
[3/8, 12:17 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```NA UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<<18>>```
A hankali take saukowa daga stairs din har ta iso inda sufyan ke zaune, samu wuri tayi ta zauna tana fadin "sannu da zuwa",
Sufyan ya dago yace cikin girmamawa ganin yadda ta karbesa "mun wuni lafiya hajiya",
"Alhamdulillah ya gidan",
Sufyan yace "mungode Allah, shiru sukayi na 'yan seconds sannan yace mata "nasan hajiya baki sanni ba.to dai sunana sufyan kuma daga kaduna nake",
Hajiya ta gyada kai alamar gamsuwa sannan ya cigaba "ni dan uwan inna luba ne wacce ta miki aiki",
Hajiya gabanta ya dan fadi tare da fadin "Allah sarki.kazo lafiya",
Sufyan yayi murmushi hade da ciro wayarsa ya duba sannan ya ce "dama nazo ne akan maganar abinda faisal yayiwa amira, inna tace min indai nasameki to zaki tabbatar min da zancenta na cewa faisal fyade yayiwa amira.dan tare dake suka kamashi hannu dumu dumu, bawai nazo ne ta tirkeki da zancen ba ko kuma dan na dauki mataki ba, kawai dai naga anamin yawo da hankali ne akan zancen .kuma tace ke mai gaskiya ce akan komai dan haka nazo na sameki",
Hajiya ta numfasa cikin sanyin jiki tace "gaskiya ne, faisal mun kama shi hannu dumu dumu kan fyaden daya yiwa amira, ko da nakareshi a nan duniya dan yana 'dana to fa banmasa adalchi ba dan kuwa alahira babu mai kareshi, nan hajiya ta bashi labarin abinda ya faru ranar da asibitin da ta kaisu,
Sufyan yace mata "hajiya amma tacemin tunda kika kaisu asibitin baki dawo ba",
Hajiya ta danyi murmushin dayafi kuka ciwo "tayaya zan dawo sufyan bayan Allah ya hadani da azzzalumin miji .wanda kansa da dansa kawai yasani.wanda son zuchiya ya masa yawa, ina dawowa nataradda ya dawo dan haka na labarta masa abinda dan sa yayi dakuma cewan yanzu su inna suna asibiti, budan bakinsa sai yace min sharri za'ayiwa dansa dan haka bai lamince min nakoma asibiti ba ki na kara fita gidan nan. Shine ranar da aka kawo masa sammaci daga kotu ya kawoni ibadan kuma yayi ma security magana akan cewa bani ba fita, sabida yasan ni bana goyon bayan zalunci", share hawaye tayi tana fadin " alhaji ya cuceni, ya lalata min tarbiyyan yaro wadda nake kokarin ginashi akai , ganinsa a yaron shi daya tilo garemu dan haka dole bazamu kwaba masa ba ",
Fashewa tayi da kuka tana fadin "ya Allah kaga nayi iya bakin kokarina akan tarviyyan yaronnan , Allah ka shirya min shi ",
Sufyan yayi shiru na 'yan seconds sannan cikin tausayawa hajiya yace "kiyi hakuri hajiya. Yanzu dai tunda naji gaskiya daga bakinki shikenan , ina ganin duk matakin da muka dauka akan alhaji to ba problem",
Hajiya ta share hawayen dake zubo mata tace "wallahi ku dauki duk matakin da kukaga dama akansa ba abinda ya shamin kai",
Sufyan yayi murmushi sannan ya kwashi phones dinsa yana cewa "to hajiya bari na wuce dan inason komawa gida da wuri",
"To Allah ya kiyaye hanya .a gaishemun dasu amira kuma dan Allah akara basu hakuri",
"Bakomai hajiya.nabarki lafiya",
Kai tsaye airport ya nufa domin wucewa kaduna.gashi dai saura kwana bakwai su koma kotu yanzu dai yana ganin yasamu kwararan bayanai da kuma sheda akan cewa faisal fyade yayiwa amira.
Abdul da faisal zaune gaban alhaji .sai kuma wasu maza guda biyu manya manya inda alhaji yake umartansu da cewa yana so suje su kawo masa full labari akan lawyer din su inna. Domin tabbas file din amira yana hannunsa. Kuma dole file din yadawo hannunsu kar asirinsu ya tonu. A bdul ya kurbi lemon dake hannunsa yace musu zuwa gobe muna jiranku, kunga saura kwana biyar yau mu koma kotu.
Dayan su ya fashe da dariyar mugunta yace "ai alhaji bama labarinsa ba, in gawansa kakeso nan da mintu talatin zamu kawo maka",
Alhaji yayi dariya hade da fadin "kai badaru dadina da kai akwai cika aiki.yanzu dai kuje sai na jiku goben.
Aikuwa Wanshekare suka kawo wa alhaji bayanai "sunansa sufyan a garin gombe yake tare da iyayensa.yaron wazirin sarkin gombe ne Kuma'yan biyu ne shida 'dan uwansa safwan.sai autarsu mai suna safina",
Alhaji bai tsaya jin sauran bayanin ba yace "ita autar tasu a ina take?",
"Tana nan cikin zaria a hanwa low-cost",
Alhaji ya karkace yace "tanada aure ne ko yara.kuma ina take karatu ko aiki",
"Eh tanada aure kuma tana karatu a jami'ar Ahmadu Bello dake zaria",
Alhaji ya fashe da dariya yace "inaso kuje kumin kidnapping dinta inzata wuce makaranta a boye.sai akaimin ita gidana dake unguwan rimi a jiye.sai na jiku",ya ciro dubunnai ya mika musu suna dariya"hahahaha".
[3/8, 12:22 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<<19>>```
Ranar laraba safina tayi parking motarta a cikin schl sannan ta dauki jakarta ta shiga domin daukan lectures, karfe 1 ta fito gashi duk a gajiye take zuciuarta sai tashi take Dan haka ta nufi cikin motarta ta bude ta dauki ruwa a gora ta sha ,tana cikin sha Nusaiba wata a class din su tazo tana mata magana Dan haka tafito daga motar batare da ta rufe ba suka fara magana.
Badaru dake labe ta bayan wani gini shida yaransa su uku da sauri ya umarci henry ta yaje ya bude mortar yadda ba mai ganinsa ya shiga gidan baya ya zauna ya lafe a seat din.
Bayan safina tagamane ta juyo ta wurga handouts din da Nusaiba ta bata cikin mota sanan ta kulle motar taja ta fita daga harabar makarantar .
Taje dai-dai wurin wasu masu nama kenan taga ansa mata kan bindiga.saura kadan ta bige wani mai rake.da sauri henry yayi mata nuni datayi shiru kuma su cigaba da tafiya.
Dan haka a firgice da kuma tsananin tsoro ta cigaba da driving tare da kiran sunan Allah a zuciyarta, saida suka je wani wuri dake duk bishiyoyi ne da wurin yace tayi parking. Tana parking sai ga su badaru nan sunfito.
Safina ta fara kuka tana fadin"Dan Allah kuyi hakuri,karku kasheni.in kudine zan Baku abinda ke gareni",
Badaru ya fashe da dariya sannan ya umarceta da ta koma bayan mota henry yaja motar ,sai badaru a baya ya seta mata bindinga yana fadin "ba abunda muke bukata wurinki yarinya sai dai hadin kanki,kar ki mana taurin kai kuma karki kara magana",
Safina ta toshe bakin tana cigaba da kuka "to sukuma wadannan daga ina suke? Kuma mai suke nema a gunta.
Minti 30 suka iso KD sabida tsabar gudun da suke shararawa kamar zasu tashi sama .
A wani tafkeken gida tsaya sannan suka yi horn maigadi ya zo ya bude musu sannan suka shiga, tasa safina sukayi agaba har cikin gidan, Wanda fadinsa yafi gaban a fadi.
Can wani daki suka shiga suka ajiyeta Wanda ,dakine da bayi aciki, Wanda ya kushi komai da komai. sannan suka kulleta suka fito.
Badaru ya dauki wayarsa ya sanar da Alhaji cewa ga ta nan sunkawota ,suna gidan hutawarsa.
Minti biyar alhaji ya dauka sannan yazo.koda yazo bai nemi ganinta ba ,
"Badaru bani nombar yaron mukirashi",
Badaru ya bashi nombar sufyan sannan yayi saving. Alhaji yayi dariyan mugunta sannan yace "yaro kenan, zaka gane dawa kake hada kafada a garinan.
Alhaji ya kira Abdul ya gayamasa.sukuma a can Zaria Khalil yanata Neman layin safina bai samu, gashi yamma nayi ,hankalinsa duk yatashi Sanin cewa bata da isashshen lafiya.
Alhaji ya dauki wayar sa ya rubutawa sufyan text kaman haka "yaro nafada maka ba'a ja dani a garinan,karamin kwaro dakai amma kanaso kasa kanka cikin matsala, inkanason karin bayani ka kira",
Lokacin sufyan yana dakinsa yafito daga wanka kenan yaji sakon shigowar mssg dan haka yaje ya dauki wayar ya duba. Koda ya karanta sai ya gane mai magana Dan haka yayi murmushi ya kirayi nombar.
Alhaji ya dauka .baima amsar sallamar da sufyan yake masa ba yafara fadin "yaro keman. Nasan zakayi mamakin abinda zanfada maka.amma kuma inkanason kanka da azziki just kawai ka aiko min da folder din Amira na asibiti sannan kazo mu baka yar uwarka safina dake wurinmu.idan ba haka kai kanka kasan rayuwarta na cikin hatsari. Mun baka nan da jibi wato ana gobe za'a shiga kotu,dipp ya kashe wayar.
Sufyan daya shiga cikin rudani ya bi wayar da idanu "safina kuma, auta! Ina take?",
Da Sauri ya dauki waya ya shiga Neman nomobar ta dakuma ta Khalil..
[3/8, 12:26 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<<20>>```
Yana kiran wayar Khalil ya dauka "assalm alaikum",
Khalil ya amsa da "wassalamu alaikum, dama yanzu nake shirin kiranka nace ai kwa dawomin da mata ko,nasan dai tana gidanku",
sufyan ya hadiyi yawu yana fadin "kai nifa kiranka nayi inji ko tana gida zamuyi magana ne da ita, na kira wayarta a kashe",
Khalil ya fadi cikin firgici kaman yana gaban sufyan "ka...ka...kana nufin bata gidan Ku",
"Wallahi bata gidanmu ,amma yanzu inason kazo gidanmu kasameni ,kar ka damu kaji",
Khalil yayi Jim sannan ya kashe wayar Dan gani yake kaman wasa sufyan ke masa.
Ana kiran sallahr issha'i Khalil ya isa Kaduna , Khalil ya fito daga gida kenan zashi masallaci ya hango motar Khalil,Dan haka ya tsaya , Khalil ya bude motar ya fito da Sauri ya nufi sufyan yana fadin "Allah yasa nidai inji labari mai dadi,Dan Allah banason wasa ,matata tana ina?,
Sufyan ya dafe kansa yana fadin "yanzu kagane ne, mushiga ciki",
Wucewa sukayi ciki suka zauna a falo tym din safiyya tana cikin dakin tana sallah tajiyo muryar ya Khalil .Dan haka tana idarwa ta fito ko hijjabin bata cire ba.
"Laah ya Khalil Ashe dai muryarka nakeji",
Murmushi yamata Wanda iyakansa baki yace mata "Dan Allah auta kawarki batazo gidannan ba?",
Safiyya ta zauna akan kujera dake falon takai kallonta ga sufyan daya dafe Kansa a tsugunne "ya Khalil wace kuma kawata yimin bayani",
"Ina nufin safina bataxo nan gidan ba.Dan kuwa tunda ta fita da safe ta nufi schl to bata dawo ba kuma wayarta switch off",
Safiyya ta sulale daga kan kujera ta zauna a kasa tana raba idanu" safina! Safina kuma, ba'a ganta ba.to ko ta wuce gombe ne",
Khalil ya Ciro waya yace "to ni banma kirasu ba amma ai bazata tafi gombe bansani ba,bafata da lafiya wallahi",
Sufyan ya dakatar dashi da kiran waya sannan ya labarta masa abinda alhaji yakira sa yacemasa ,
Safiyya hanjin cikinta suka kada yayin da Khalil ke tambayen shi waye alhajin "shine Wanda inna tayi aiki a wurinsa ,Wanda Dan sa yayiwa Amira fyade "cewar sufyan.
Sallama akayi aka shigo. Amira ce tadawo ita da inna dan kuwa sun fita ne,
Sufyan ya zubama safiyya ido yama rasa abinda zai ce mata, Khalil da baisan wainar da ake toyawa ba yace dasu "aikuwa wallahi zai San dawa yakeyi, ya fada a zuciye yana mikewa tsaye hade da goge hawayen dake zubomasa , inna da Amira suka tsaya cirko cirko, yayin da sufyan ya taro Khalil yace masa "kabi komai a hankali, yamin waya cewa yanaso ne nabashi file din Amira na asibiti sannan ya sake safina, ai inbaka iya kama barawo ba shi zai kama ka, dawo kazauna mu shirya komai da komai",
Safiyya ta mike ta shige dakinta sannan ta lalubi wayarta ta dannawa Abdul kira, bugu daya ya dauka sannan suka gaisa,
Cikin dabara safiyya tace masa "Abdul wai ya ake ciki ne,kunyi bincike akan lawyer din nasu kuwa kuma ya zancen folder din Dan kuwa ni Ku nake jira",
Abdul yayi dariya yace Mata"ai brr. Kar ki damu, file dinnan nanan dawowa gurinmu, kuma munyiwa sauran masu aiki a gidan cewa duk zasuje su mana sheda a kotu",
"To tayaya Zamu samu folder din"? Safiyya tayi tambayan cikin zakuwa.
"Ai ya sa ankamo masa kanwar lawyern yanzu haka tana gidansa na unguwan sarki",
Safiyya tayi dariya tace "dadina da alhaji baya wasa" sannan sukayi sallama takashe wayar,
Da ta fito falon ta tadda inna tanata kuka sufyan nabata hakuri cewa karta damu insha'allahu za'a ganta",
Safiyya ta isa wurin ya Khalil tana fadin"yaya karka damu,ni zan nemo safina, kabani nanda kwanaki biyu, ni nasan waye alhaji",
Khalil yamata murmushi yace "to Auta amma banason wani abu yasameta ne",
Sufyan dai baice komai ba, shidai bai san meyasa bai gayawa kowa ba cewsn safiyya ce lawyer din alhaji ba, ganinsa ai matar sa ce, Dan haka ba kowani abu Nasuh zai dinga gayaba,",
Sufyan ya ce masa " bari a kawo maka abinci, plss banason kowa yaji zancen nan na bata safina a gombe",
Safiyya ta kallesa "gaskiya koba komai sufyan namiji ne Wanda ya amsaa sunansa na namiji, jibi abin da tamasa amma bai taba nuna mata cewa yasan tana zuwa kotun ba ma, can wata zuciyar tace mata "ai dama ba shine bakya so ba, halinsa ne na wulakanci bakiso, amma kuma tanajin wani Abu game dashi.
[3/8, 12:28 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<21>>```
Safiyya ta kalli inna tace "inna ku shiga muci abinci ko",
Mikewa sukayi dukkansu jiki ba kwari sannan suka nifi ciki, Amira taja hannun safiyya suka shiga dakinta tace mata "ni wallahi Anty jikina duk ba dadi, alhaji bashida kirki, kar wani Abu yasami Anty safina",
Amira ta shafi fuskar ta tace "nasani Amira, insha'allahu babu abinda zai sameta kinji, oya shiga kitchen ki kwaso abinci ki jera mana",
Anan gidan Khalil ya kwana hankalinsa dai bai kwanta ba, wanshekare da bayan sun gama breakfast ne safiyya ta ke cewa Khalil "ya Khalil karka damu safina na nan cikin koshin lafiya",
Kallonta yayi da alamar tambaya a fuskarsa yace "autar umma ke tayaya zaki sani tunda baki da hadi da alhaji?",
Safiyya tayi murmushi tace "ai ya Khalil nikeda hadi da alhaji sabida ba abunda bansaniba gameda case din Amira, Dan kuwa ni suka dauka Dan na karesu a kotu",.
Khalil ya kura mata ido yace "bangane zancenki ba",
"Ya Khalil da Kansu sukazo wai sunaso na karesu a kotu ,nikuma sabida nasan da zancen na ansa, gudun kar a kai ma wani bare kuma azo a cuci AMira",
Sufyan dake can daga gefe daya yana latsa system yayi shiru yana sauraronta,
Dan ko a hankali take ma Khalil zancen yadda ba Wanda zai ji . jikinsa yayi sanyi kalau ,Allah sarki sofy ashe ita nata kudirin daban, yanzu yana jin zuciyarsa tafara kwanciya da halayenta Dan kuwa a hankali yana fahimtar wacece ita.
"To ya akayi suka sanki, Khalil ya ce da ita cikin zakuwa.
Safiyya tayi murmushi tace "aiki ya hadani da abdul dashi fa shine ya kirani yace sunason na kare shi Faisal din a kotu, Dan haka zuwa 10 zan je gidan alhaji sai mu tafi da daya daga cikin Ku, ko kai ko sufyan, zan bukaci inje gidansa na unguwan sarki Inda safina take , bayan munje sai in tura wani cikin ku ",
Sufyan ya mike ya dawo kusa da Khalil jin abunda sofy ke fada, Khalil ya ce "ai ni zan biki wurin matata kawai",
Safiyya tayi murmushi tace "to ya Khalil kanaji ko.in mukaje kashiga to dama kaga bazuwa suke suna shiga Inda take ba balle asan kana ciki. Sai kubari sai da daddare ,a lokacin zamusan yadda zamuyi kufito",
Sufyan ya dago yana kallonta yanda taketa jawabi sai kace mai karantowa "Allah yasa dai adace",
"Ameen ameen cewar Khalil.
Karfe goma safiyya ta dauki motarta tare da Khalil a bayan motar amma ya lafe yadda baka hangosa ,kuma dama glass din motar tinted ne, Kiran nombar Abdul tayi tace masa tana kan hanyar zuwa gidan alhaji, shin ko yana gida?",
Amsa yabata cewan "yana gidansa na unguwan sarki",
Safiyya tayi mugun jin dadin maganarsa Dan dama ta rasa ta yadda zatace yamata kwatancen gidan" yawwa kwatantamin naje can nasameshi"?
Kwatantamata yayi sannan ta dauki motar suka nufi gidan.tana isa tayi horn mai gadi ya bude mata.
Can taje daga wurin ciyayi tayi parking motar sannan tafito, tafiya ta dinga yi mai gadi na jagorantar ta har falon da alhaji yake ,
Yana ganinta yafara dariya "a ah brr. Kece Ashe.sannu da zuwa",
Yake tamishi sannan ta zauna a kujera tana mai gai sheshi,
"alhaji dam Nazo ne akan maganar folder din ya muke ciki ne",
"Ai na rigada na gama komai yanzu jira mukeyi juma'a tayine mu shiga kotu. Shikuma lawyern nasu na bashi nan da zuwa gone,idan bai kawo nana folder din ba to zamu hallaka 'Yar uwarsa",
Kirjin safiyya ya buga "wai mi yasa mutumin nan bashida imani ne ko mis-kala-zarratin?, amma a fili sai tace "ohk tana nan gidan kenan",
Eh tana nan a nan gidan mun boyeta,kar ki damu nasan zaikawo",
Safiyya tayi yake tace "to alhaji bari na wuce,tana mikewa ta rubutawa Khalil text cewan gatanan fitowa, yayi Sauri ya fita a Motan ya shiga ciki,.
Alhaji ya mike yana fadin "to brr. Kin dai ki karban ko sisi har yau a hannunmu",
"Karku damu alhaji,ni dai burina komai yazamana ya tafi dai-dai",
Tana fitowa Khalil ya fita ya bude wata 'Yar kofa daya gani,nan yaga ashe toilet ne ,Dan haka ya shiga, nan ma yaga wata kofa a ciki ya murda sai ya gansa a wani makeken falo, a hankali ya isa ga kofan ya danna mata sakata ya kulle Kansa ta ciki Dan kar kawani ya shigo, nan ya tsaya a falon ,in lokacin sallah yayi sai yayi sallah har lokacin da yaji tashin motar alhaji sannan..
[3/8, 12:31 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```January 2017```
```<<22>>```
Sai da yaji Barina alhaji gidan sannan hw fara shishshiga cikin dakunan yana bullewa , daga can bangaren yakejin surutun wasu maza suna hira da dariya, a hankali ya ke tafiya har ya isa wani sassan Wanda shine na karshe, tafiya ya yayi can ciki Inda ya ga wani daki kulle amma mukullin yana jiki , Dan haka da Sauri ya isa ya murda dakin ya bude,
Hangota yayi zaune kan tiles ta kife kanta a kan gado, ga drinks nan iri iri a gaban ta da takeaway, zuwa yayi a hankali ya tugumota ta baya, a firgice ta bude baki zata kwarma ihu kenan yayi Sauri ya toshe mata baki da hannunsa "safina nine fa, Khalil",
Aiko da Sauri jikinta na rawa ta fado jikinsa tana kuka, shafa bayanta yadinga yi har yasamu ta sassauta kukan nata "
Ya akayi kasan ina nan",
Murmushi yamata ya na mai shafa kuncinta "ya za'ayi bazansan inda matata take ba, bancin zuciyar mu na hade ne",
"Ya Khalil nidai ka daukeni mufita a gidannan , wallahi zasu kasheni ne",
Shiiiii ya mata alama datayi shiru, "kidnapping dinki sukayi amma karki damu, ina tare dake , zamu bar nan.ya shafa cikinta "ina baby na, dafatan dai kina cin abinci ko",
Murmushi ta mishi tace "wani abinci hankalina a tashe, kaganni nan ko wanka banayi",
Khalil ya rike hanci yana dariya "shiyasa naketa jin wari Ashe",
Dukkansa tafara a kirji "nike wari ko, shikenan,
"A ah nifa bance komai",yanzu dai kinajin yunwa ko kuwa",
Girgiza kai tayi "uhm uhm ni banajin cin kai, amai zanyi kona ci",
Lallabata yayi tasha yoghurt, a lokacin ne safiyya ta masa text cewa ko ya ga safina, ya mai da mata da amsar eh gana nan kusa dashi , ta mishi text cewan su kwana ana gobe zatazo da safe .
Wanshekare safiyya tayiwa alhaji way a cewan tanason ganinsa, a gidansa na hutawa, yace mata ba matsala su hadu a can.
Suna falon sa zauna safiyya tace masa "tunda naga har yau bai kawo ba alhaji me zai hana a dau wani matakin,
Alhaji ya kalleta yace "ai brr. Dole fa sai ya bamu ta karfi da yaji,ko na tura yarana suyi attacking dinsa su anso",
Safiyya ta dauki wayarta ta rubutawa Khalil text cewa "ya fito ta Inda ya shiga ,zai ga motar ta Baka a wurin ,su shiga su jirata",
Khalil na gani ya kama hannun safina a hankali har suka fita suka shiga motar suka lafe,
Bayan safiyya tagama magana da alhaji ne ta mike ta ce masa bari ta tafi,tana Sauri ne",
Tana zuwa ta dauki motar ta ta bar gidan, sai da suka bar unguwan sannan tafara dariya tana cema safina "raguwa mike inga yadda kika rame mana",
Safina tayi murmushi kanta na kafadar Khalil tace "yarinya zaki gane dani kikeyi, bari muje gida.
Suna isa safina ta shiga tayi wanka , sunata hira da su inna, "nifa wallahi Dan wake nake son ci kawai",
Inna tayi dariya tace "indai akwai garin bari na miki",
Safiyya tace mata "aikuwa inna akwai, dafa mana mu zakalkala",
Amira ta lashe baki tace "ai kuwa Anty kamar kinsan inna akwai iya dafa Dan wake.
Dariya sukayi dukkansu sannan inna ta mike ta wuce kitchen,
Minti ashirin ta dauka sannan ta shiryo musu komai, sai da sukaci sukayi nak, sannan Khalil ya dauki safina suka wuce Zaria,
Safiyya na zaune ita da Amira ,sufyan ya shigo, sanye yake da wata farar rigar wacce aka rubuta nectar a jini da wando jean baki, yayi kyau sosai gashin kannan kamar na larabawa,
Kai tsaye wurinsu ya iso ,Amira ta mike daga datake kwance tana fadin "sannu da zuwa",
Murmushi yamata sannan ya amsa mata, safiyya ya kalla datake yanke kunbarta ko dago kai batayi ba, sanye take da doguwar Riga yellow, tayi mata kyau, kanta ba dankwali , a zuciyar sa yace "ko mai yasa bata son zama da dankwali ohoo, shidai gashin nan nata na burgeshi kullum a gyra "Ku shirya yanzu zamu je gidan wani abokina dake cikin gari ,sabida ina tunanin alhaji zai turo yaransa gidan nan anjima tunda gobe zamu koma kotu ",
Yana gama fadi ya mike ya shige dakinsa, Inda safiyya ta visa da ido, can kuma sai ta tsinci kanta da yin murmushi..
[3/8, 12:35 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<37>>```
Safwan sai da ya kwana uku baisan Inda Kansa yakeba. A rana ta ukun ne ya fara motsawa, dayake yanzu dady ne da Khalil a wurinsa ,mai martaba ya koma sabida baki masu zuwa gaisuwa daga wurare daban daban.
Dama Dr. Yace yana farawa motsi a kirashi Dan kar asamu matsala.dagudu Khalil ya je ya kirayi Dr. Sukazo suka masa wata allura. Nan bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi.
```Bayan awa biyar```
A hankali ya fara bude idonsa yana kallon Inda yake kwance, gani yayi kaman a asibiti yake, Khalil ya gani ya buga uban tagumi duk yayi wani fayau dashi, da Sauri abinda ya gani a t.v yafara dawo mishi.
Mikewa yayi yana rike kansa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shi yadawo da tunanin Khalil, lokacin dady yashigo domin ya tafi masallaci domin yin sallah la'asar. Zuwa sukayi s tare gefensa daddy ya dafa Kansa yana tofa masa addu'a. Ruwan zamzam ya dauko yayi masa addu'a a ciki ya kafa masa a baki ya sha.
Kallon daddy yayi yace "daddy gaske ne su sufyan summutu ko,Dan Allah daddy kafadamin",
Daddy yayi shiru Dan bayaso ya fada masa suzo yanzu sukoma gida abun yadawo sabo.Ansamu an lallaba su Momy yanzu kuma yana komawa mutuwar tadawo sabuwa.
"Ba abinda ya faru dasu ka kwantar da hankalinka kaji".
Duk da hankalin safwan bai kwanta da maganar Daddy, amma baice komai ba, Daddy yaja Khalil gefe "kaji abinda likita yace, muddin hankalinsa ya kara tashi to zai iya samun paralysis (mutuwan wani Bari na jikin) Dan haka kayi shiru kabari indan aka sallame mu ,mukaje gida yaji",
Khalil ya girgiza alamun gamsuwa. Koda aunty amina tazo kawo musu abinci sai da daddy ya gargadeta akan karta fada masa.
kwana daya suka kara aka sallamesu, Daddy dakanshi ya tukasu zuwa gida. Kai tsaye gidan sarki suka wuce, safwan yaga taron maza a waje kuma duk inda suka gifta sai ana kallonsa ana girgiza kai alamun tausayawa.
Falon mai martaba suka shiga dukkansu, Daddy yace da Khalil yaje yakira kaf ahalin gidan. Dukkansu zaune suke , umma ita ta riko Amira duk tabi ta rame kamar kudin guziri ita da safeena yayinda inna Sadiya ta riko safina suka zauna mai martaba yana zaune a sama sai Daddy a gefensa. Sarki ya fara da addu'oi dakuma jajantawa ga rashin da akayi yakuma yiwa kowa wasilci akan hakuri , bayani yayi mai ratsa zuciya, sannan ya daura da "Allah daya bamu su shiya fimuson su, shiyasa ya daukesu a lokaci daya, kuma babu abinda zamu bisu dashi sai addu'a domin ita kawai suke bukata yanzu, Allah ya jikansu mukuma ya bamu hakurin rashin su",
Safwan kwakwalwar Kansa ta dena aiki a lokaci guda kuma numfashinsa ya tsaya cak. Kawai gani sukayi ya dungure ya fadi. Da Sauri Momy ta isa wurin sa "safwan kaima tafiya zakayi kabarmu, bancin kai kadai zangani ina jin dadi maimakon 'Dan uwanka" jijjigashi ta hau kafin daddy da Khalil kinkimeshi zuwa bedroom din sarki. Mai martaba ya dauki waya ya kirayi Dr. Cewa yazo jikin safwan ta kuma tashi.
Safina da Amira umma tajasu suka koma ciki Dan kuwa sunfi kowa jin jiki a gidan. Momy tana wajen safwan itada matarsa Anty Amina sai sharar kwalla suke.
Cikin mintunan dabasu wuce goma Dr ya iso, cewa yayi su Momy su fitar, dudubashi yayi mishi allurori, ajiyar zuciya safwan ya sauke , sannan ya mike, jiyayi kaman hannunsa na gefen dama ba ajikinshi yakeba, Dr ya kallesa yace ya kakejin wurin?".
Safwan ya yatsina fuska "kaman ba'a jikina yakeba.
Dr ya girgiza kai kawai sannan ya masa wata allura nan da nan baccci yayi awon gaba da shi.fitowa falon sarki yayi yasamesu jugum jugum, kallonsu yace "yanzu yasamu bacci amma hannunshi na barin dama ya samu paralysis",
Momy bata bari yakai aya ba"Dr karkacemin hannunsa y daine aiki ya shanye, innalillahi wa inna ilaihi raji'una",
Dr ya kalketa yace "ki kwantar da hankali hajiya, cikin ikon Allah Idan aka fara mishi gashi zai warke, ai ba sosai ya kamashi ba.
Dan haka zan turo muku Wanda zai dinga mishi gashin hannun everyday",
Mai martaba yayi masa masa godiya sannan ya wuce, Momy sai gunjin kuka takeyi. Haka dai akayita jinyan safwan a fada Wanda kullum yake shiru, kwata kwata bazaka Ganshi yana fara'a ba inba ya nawa jannat wasa ba.
Anty Amina kullum tana wurinsa yayinda Momy ta koma gidanta bayan kwanaki bakwai datayi a fada Suna Ansan gaisuwa, safina itama ta Khalil ya dauketa suka koma gida aiko ranar taci kuka, Allah sarki rayuwa kenan. Yayinda Amira ta koma marainiyar karfi da yaji Dan ko makaranta taje shiru kake jinta ,a gida to saidai insuna hira da Momy ko inna. A haka har su safiyya sukayi wata uku. Wata ukun nan da fada tayi kowa a daddafe yayita cikin kunci, jikin safwan kuwa alhamdulillahi yana samun sauki da kuma kulawa amma kullum ya tuno da 'Dan uwansa sai ya zubda hawaye . Yayin da cikin safina y shiga watanni biyar...
[3/8, 12:38 AM] +234 703 962 5239: *````MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
``` dis is for yhu Zuhra,thanks for d care, luv yh many many ```
```<<28>>```
Umma tayi matukar murnan ganin safiyya, ta rasa Inda zatasa auta ganin yadda hankalinta kwance tayi kyau abinta, safiyya da Amira na nan makale da jarirya kaman zasu lashe ,aunt Amina sai dariya take musu,
Safiyya ta kalli Yar "amma aunty Yar nan katuwa, sannu fa",
Aunt Amina tayi dariya "ai ni jiran ranar haihuwanki nake auta, ummm zamusha kallo",
Umma dake jinsu ita da inna sukayi dariya "kyaleta auta ai inbazaki iyaba ni sai nazo na ansa na haifan miki, menene amfanina",
Safiyya ta turo baki "barta dai umma, ai ga inna ma tana nan",
Dariya suka dingayi lokacin sufyan ya shigo shida safwan Dan ganin jaririya,
Suka gaisar da umma cikin girmamawa sannan umma tace "auta mika masa yarinyar ",
Safiyya ta Dan turo baki sannan ta ansa 'Yar ta matsa tabawa sufyan, garin mika masa hannusa da nata suka shafi juna , yarrrr sufyan yaji a jikinsa, da Sauri safiyya ta sake masa 'Yar sannan ta ja Amira suka shige bedroom din umma.
Sufyan nagama musu barka ya fice fada ya mika gaisuwarsa gun sarki sannan yayi gidan Momy, kai tsaye dakinsa yanufa domin kuwa duk a gajiye yake dama ya rigada yayi sallah isha'i,
Kwanciya yayi rigingine yayi shiru, "duk lokacin da fatar jikinsa ta shafi na sofy to ya dinga jinyar Kansa kenan ranar, kwatakwata bashi da sukuni, Dan ma ya na hadawa da azumi", lumshe ido yayi domin shi Kansa ya San safiyya ba matan dazaka kalla ka kauda ido bane, muryarta kadai kaji Kasan ta amsa sunanta na cikakkiyar mace, matsalarta daya abunda ta mishi farkon haduwarsu da kuma rashin kunyar data mishi, shiyasa ya kudiri aniyar horas da ita, amma kuma tunda ya aureta ta bata masa duk plan dinsa akanta,domin ita ba irin Matan da ake wulakantawa bane, yanzu dai gashi saura kadan su shekara Dan kuwa watanninsu goma kenan da aure, kuma a Dan zaman da sukayi yana fahimtar ko ita wacece, tunowa yayi lokacin datake karama, kullum jikinshi take kwana take tashi, kafadarsa shine wurin baccinta, bayansa shine dokinta, amma ita yanzu ai baxata tuna ba tunda lokacin tana karama",
Mirginawa yayi ruf da ciki "anya zai iya takura Kansa ya kyale sofy har sai ya samu macen data mishi ys aura, kai anya , "subhanallahi" ya fadi jin wani Abu na tsiga mishi cikin jikinsa.
Tunda sukazo gombe safiyya gidan momy take wuni in dare yayi kuma ta wuce gidan ummanta ta kwana, haka aka cigaba da shirye shiryen biki, Momy ta kula cewa tunda sukazo sufyan baya neman safiyya, itama haka bata nemansa, ko haduwa sukayi a falonta to safiyya ce ke gaishesa kawai, "to kodai hanyanzu basa son juna ne?", Dan haka a gobe suna yamma suna gidan Momy sunata aiki, safiyya da safina suna aikin donut, yayinda da Amira ke rike da wayar safiyya tana game, sai Anty Amina mai jego ana mata kitso, Momy na rike da jaririya wacce taci sunanta,
Safiyya ta mike tana fadin "wallahi sai gumi nake, bari na shiga na watsa ruwa",
Safina ta bude baki " to basai kibari mugama ba tukun, kwata kwata nawa yarage",
Amira ta kalli safina "ai wallahi Anty safina Indai Anty ce to zaki gaji ,Dan kuwa ni dai at least tana wanka sau bakwai a rana",
Dariya dakin ya dauka yayin da safiyya ta tsatstsallekesu ta wuce tana fadin "banason sharri fa irin naki naki Amira",
Tana wucewa sufyan na shigowa falon , sanye yake da Riga T-shirt brown da wando jeans, Momy ya gaisar sannan sauran yan dakin suka gaidashi,
Karba yarinyar yayi a hannun Momy yace "Momy sai naga kaman da safina yarinyar nan ke kama",
Momy ta rufe baki tana dariya" kar Kasa auta tahau murna, ance yarinya na kama da ita",
Safina dariya tayi "ai nasan ya sufyan akwai fadin gaskiya".
Kudi ya Ciro makudai ya sawa jaririyan a hannu, sannan ya Ciro wasu ya mikawa aunt Amina,",
Aikuwa sunata masa godiya ,safina tayi rau da fuska "ya sufyan Kasan ni me nikeso?',
Girgiza kai yayi alamun a ah, motar nan da ka hau ranar bikinka, wallahi kullum mafarkin motar nake , kuma har yanzu ban taba ganin irinta ba",
Safwan daya shigo ya tsinkayi zancen ya bude ido "Baki da kai ne hala auta, kinsan kudin motar nan kuwa?",
Sufyan yayi murmushi yace "Indai motar ne dama tana nan gidan a parking lots ,Dan haka kije ki dauka na baki", yana gama fadi wayarsa tayi ringing Dan haka ya mike ya fita ya nufi sasansa ,
Safina harda tika rawa Don murna, safiyya dabatasan wainar da ake toyawa ba tafito sanye da wata Yar karamar Riga marron colour, rigar iya cinya Wanda rigar net ne daga gaban kirjin kuma Dan zare ne kawai aka kulle sai wando tite baki, ya sauka kasan gwiwarta, sai kamshi take zubawa, safina ta kalleta " aifa lalle an ga humrar Momy ta bati ",
Momy tayi dariya tace "ke kuma ina ruwanki, komawa safiyya tayi ciki yayin da Momy ta ni bayanta, suna shiga ta kalleta tace "kije mijinki na kira ya shigo kina wanka,yana sasan sa",
Mikewa safiyya tayi ta fita ta bayan dakin Momy dayake ba kowa ta wurin Dan haka ko dankwali bata dauka ba , kanta tsaye ta fada dakin ganinsa a bude hade da sallama,
Rigace vest fara a jikinsa sai dogon wonda jeans, yana kishingide jikin wata kujera akasa, karasa tayi ciki Dan ita bata hangosa, tana zuwa taci tuntube da kafarsa ta fada Kansa,
Cikin Sauri ya bude idonsa da suke a rufe ya rungumota zuwa jikinsa, kamshin turarenta duk ya rudashi, s hankali ya kai hancin sa kan gashin kanta yana shinshinawa har zuwa wuyanta, sumbantar ta yayi a wuya Inda safiyya ta kame kamar dutse domin abun yazo mata a bazata,
Zare dake gaban rigarta yaja ,aikuwa rigar ta zamiye, sufyan Wanda ya manta dawa yake tare bakinsu ya hade sannan ya shiga aika mata da zazzafan sakonni duk Sassan jikinta yana fidda numfashi,
Aunty Amina da safina suka fito daga falon Momy suka nufi sasan sufyan Dan yimasa godiya kan kayautar da ya musu
[3/8, 12:41 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<29>>```
Safina ce tafara kutsa kai cikin dakin batare da sanin su safiyya na falon zube a Kasa ba, cikin Sauri ta ja da baya tareda Jan hannun aunt Amina da ita ta waro ido, da Sauri suka fita dakin ganin cewa su bama su San sun shigo ba.
Cin karo sukayi da Amira wai zata kaiwa safiyya wayarta na ringing ,safina ta dakatar da ita "Amira bata ciki ki shiga cikin gida ki dubata",
Amira ta ce "ai Momy tacemin kaman nan tayo",
Amina ta kalli safina sannan tace "ke Amira ance miki bata ciki ko, ki amsa kice bata nan mn",
Amira ta juya hade da fadin"ohk",
A hankali tunanin sufyan ya fara dawowa, da Sauri ya saketa ita kuma jiki ba kwari ta koma gefe, rigarta ta ja ta gyra ta juya masa baya tana sauke ajiyar zuciya, shima runtse idonsa yayi sannan ya waresu a kanta, numfashi ya dinga fiddawa a hankali ,yayin da dakin yayi shiru, bakaji komai sai karan a.c da kuma bugun zuiyoyinsu.
A hankali sufyan ya furta mata "sorry for disturbing yhu",
Batace masa komai ba ta mike ko juyowa batayiba ,gudu gudu ta bar masa dakin.
Binta yayi da wani irin kallo ta kasan ido, sannan ya kara lumshe idanuwansa wandan da suke nunomasa moment din daya kasance tare da sofy "OMG, meyafaru da ni ne",
Lashe lebansa yayi na Kasa sannan ya ciza " kai! Subhanallahi! Lallai yau da idan baya saisaita tunaninsa , data rusa masa komai nasa",
"Ya illahi" ya fada domin idanuwansa baya nuna masa komai sai abinda ya faru, mikewa yayi ya nufi toilet jikinsa a mace ko zai samu ya rage abinda yakeji yana masa yawo daga Kansa ya kafarsa.
Tana shiga falon Momy ta zube akan kujera dake kusa data safina, kallonta sukayi su biyun sannan kuma suka kalli juna sukayi dariya, safina uwar tsokana tace da ita "ya zaki wani shigo mana daki ba sallama kuma kinyi kamar Mara lafiya, daga ina haka?",
.
Safiyya idanuwanta a lumshe tace a hankali "har kingama aikinne ",
Safina ta harareta "to zan tsaya jiranki ne tunda ki tafi turakar miji kin barni da aiki",
Safiyya najin haka ta galla mata harara ta mike ta shige bedroom din Momy sabida aunt Amina dake wurin, safina ta bita da "ai dole ki gudu",
Su biyun suka dinga dariya itadai tana jinsu ta na kwance gadon Momy tana jinyar kanta,
Hannu tasa a kirjinta jin yadda yake bugawa fat fat fat, can kuma ta fara magana ita kadai "to wai ba kirana Momy tace yanayiba , shine zai kama ya tumurmushe ni" , murmushi tayi hade da turo baki " uhmm Ashe shima ya sufyan bashi da dama.
Kiran sallah magriba taji Dan haka ta ware ido daga tunanin datakeyi "har magrib tayi, lallai na Dade a dakin shi, kila shiyasa su safina suka gane", tsaki tayi sannan ta shiga bayi Don tayi wanka hade da alwala.
Wanshekare ranar suna kenan, yarinya taci sunan Momy wato Fatima , Inda zasu dinga cemata jannat", dukka gidajen biyu a cike yake da jama'a , su safiyya da safina da mai jego anko dukkansu sukayi, sunyi kyau kamar ka sace, abokan sufyan da safwan Wanda sukayi karatu dasu a Turkey sunzo Dan haka , safwan ya ja hannu sufyan yace "kaga nabawa auta tamin komai, kuma ni banma San zasu zo ba. Dan haka kazo muje muyi mata magana tayi preparing wani Abu mai sauki yanzu.
Safiyya na falon sai safina tareda ya Khalil, tana masa pepper meat, ana hira safiyya nata tsokanansu, sallama sukayi su biyu suka shigo,
Safiyya tunda ta hango sufyan ta sadda kai kaman ba ita ke surutu yanzu ba,
Kujeran dake gefenta yazauna shida safwan, sufyan ya kalli safina "auta Dan Allah taimako zakimin , frnds dina ne sukazo yanzu, inaso ki shirya musu Abu mai sauki plss",
Khalil yayi caraf ya capke zance "aifa lallai samun wuri, kalle matarka zaune bata aikin fari balle na baki, lafiyarta lau, sai ni matata dakeda lalura ne zakace tama girki yanzu ko",
Safwan da abin ya bashi dariya yace "to mai mata, daga taimako",
Safiyya ta Dan yi murmushi tace " ya sufyan ka kawo sai nayi maka",
Safina itama dariya tayi musu yayin da sufyan din yace "OK, bari ni sai na tayata,
Khalil ya ce "oho dai kai kasani , suna gamawa yaja hannun safina suka bar dakin shina safwan ya fita.
Kallonta yayi na 'yan seconds yadda tayi kyau sosai kamar wata Zara acikin taurari ,da yake less din dake jinkinta chocolate colour ne kuma ita fara ce shiyasa ya amshi jikinta, ita ta katse masa tunanin ta hanyar cewa bata tare da ta dago kanta ba "bari ayimusu zobo, tunda akwai abinci da snacks, sai na hada musu salad , da plantain da Irish"
Murmushi ya mata yace "OK , bari na tayaki. Dauko irish din na fere miki ",
Mikewa shima ya bita suka shiga kitchen din Momy ta kwaso masa sannan ta Debi zobon ta kunna gas ta Dora, daukan wuka tayi ta fara yayyanka irish din dayake ferewa, aiko bata saniba ta Dan yanke hannunta , cikin Sauri ta yarda wukan tana fadin "subhanallahi, washhh",
Da Sauri ya kamo ta fado jikinsa ta rukunkumeshi Dan saura kadan ta taka wukar dake bayanta.
[3/8, 12:42 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<30```
```wannan page din naki ne my lil sis Amiraty , I am so bless to hv a sister lyk yhu, much luv dearie```
Hannun yakama yana hura mata iska , ita kuma dan raki irinna sofy sai wash wash takeyi ciwo ba wani ciwo ba, sai da suka dauki second talatin a haka sannan ta janye jikinta daga garesa idanunta na Kasa ,
"Sannu" ya ce mata hade da dauke wukar da ke gefenta.
Kallonta yayi yace "ko na dauko auduga da spirit na goge miki ne?",
A shagwabe ta kallesa "A ah kabarshi ai ba sosai bane",
Murmushi yayi kadan sannan yace "to ki koma falo sai na karasa ko",
Girgiza kai tayi" ai zan iya cigabawa, kar kadamu",
Gyada kai yayi" kin tabbata zaki iya",
Murmushi tayi sannan ta mike ta suke zobon dayaketa tausa. Da taimakonsa ta gama shirya komai cikin kankanin lokaci. Ta sassaka a kuloli da jugs masu kyau "
Ya kalleta cikin murmushi yace " thanks once again",
Bata ce komaiba sannan yace mata ta dauko tabiyo shi. Hajjabi ta dauka sannan ta kwashe wasu kayan , shima ya kwasa suka nufi side dinsa, koda sukaje sun iske safwan a cikinsu sunata hira.
Cikin harshen turanci suka gaisa da safiyya. Safwan ke ce musu "ai itace matar sufyan",
Nan suka kara gaisa ,wata mace acikinsu sai bin sofy take da ido, sufyan ya zauna ita kuma safiyya ta fara zuzzuba musu.
Gani tayi matar ta Mike ta koma kusa da sufyan, tawani matsa kusa dashi sosai domin har kafadansu na gogan na juna.
Cikin Sauri ta gama zuzzuba musu tabar dakin Dan jin wani Abu ya tokare mata wuya.tana isa dakin safina ta shige ta zube akan gado, shiru tayi jin zuciyarta nata tafasa , safinan ce ta shigo ta jata wai tafito suyi hotuna.
Bayan sungamane suka bukaci sufyan daya kira musu safiyya wai Don sumata godiya, Dan haka kiran wayarta yayi , dayake tanada nombarsa sai ta dauka hade da sallama , bayan ya amsa ne yace da ita "kizo Ku gaisa wasun su zasu wuce",
Amsawa tayi da "OK" badan zuciyarta nason zuwaba sabida abinda tagani.
Tana zuwa suka fara tsokanarta wai girkin nata yayi dadi, murmushi kawai ta dinga musu, ita dai matar dake cikinsu bata cemata komai ba, kudi suka irgo suka bata Don nuna mata jin dadinsu. Itama godiya ta musu sannan ta fita.
Da daddare za'ayi dinner, Dan haka su mai jego ansha kwalliya , safiyya da safina anko sukayi na wani yadi pink, sun yi kyau kowacce ta kashe dauri.
Mota daya suka shigo itada safina , sai da aka fara gudanar da dinner din sannan sufyan ya iso, shigowansa keda wuya sai ga yarinyar itama ta shigo. Dama oga safiyya idanunta na kan kofan shigowa, ta gimtse fuska kamar kamu. Nan da aka cigaba da gudanar da dinner din cikin annashuwa ,Inda naira tayi kuka, Dan kuwa sufyan da safwan sunyi barinta. Safina ta tabo safiyya "cwt, wai wannan ita bata bisu sun koma bane, mai ya zaunar da ita Dan kinibibi",
Safiyya dama kiris take jira tace cikin fada "uhmm, ohon mata, dama bata bisu ba?",
"Eh sufa sauran duk sun wuce itakuwa tana manne da ya sufyan, Niko sai na tambayi ya safwan ko wacece",
Safiyya tayi tsaki a hankali tare dacewa "nifa wallahi yarinyar batamin ba",
Safina tayi dariya "dama tayaya zata miki bancin sai likewa mijinki take",
Sufyan ya fito a fusace , gognur ta biyosa, kallonta yayi yafara magana "kinga guognur nace miki kidaina bina ko. Nan wurin duk yan Uwa nane,kuma na gayamiki cewan matata tana wurin ko", wannan duk zancen dayakeyi ya cikin harshen turanci yakeyinsa.
Dafa kafadansa tayi ,ya fizge tace "haba sufyan. Dan kaga inasonka shine kakemin wannan cin fuskar, amma kai kanka kasan irin sonda nake maka. Nakiyin aure a Turkey nacewa iyayena kai nakeso domin kacemin zaka dawo. Shine zakaci amana ta kazo kanacemin kayi aure",
Sufyan ya kara daure fuska yace "ai kinsan dai nibanmiki alkawarin cewan zan aureki ba ko",
"Ko bakama kanka alkawariba to nidai inasonka kuma zan aureka. Kai kanka kasan ka wahalarmin da zuciya sufyan".
Juyawa yayi ya figi motarsa ya barta a wajen. Yayin da gognur tayi tsaye ranta ya baci,"har yanzu sufyan baxai daina wulakantata ba duk da gashi ta biyosa Nigeria!!!".
Koda safiyya ta kula sufyan da gognur basa wajen,sai kawai ta kudurta a ranta cewan suna tare,Dan haka, haka aka gama dinner din ranta a bace.
Wuraren karfe shadaya ta fito daga wanka kenan daure da karamin towel, lokacin shikuma sufyan ya shigo, ba tare da zaton ita bace a ciki ya kunna kai cikin dakin.
Hada ido sukayi sabida wutan dakin a kunne yake ga haske, daure fuska tayi Dan ita yanzu haushinsa takeji. Shikuwa zubama santala santalan cinyoyinta idanuu yayi...
[3/8, 12:44 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<31>>```
```jinjina da gaisuwa gareku Anty maijidda tare da Ummu beenah (Sanah S Matazu), Allah ya barmu tare cikin aminci, nagode da kulawarku wannan page din naku ne
```
Ganin kallon dayake mata yasa ta tsargu tace masa "lafiya kuwa?",
A Dan daburce yace mata "Momy fa",
"Tana bangaren dady"ta fada a takaice.
Juyawa yayi yafita, tsaki tayi a hankali ta zauna gefen godon tana shiryawa, shigowan safina ya katse mata abinda takeyi , dafata safina tayi tace "cwt na tanbayo mana ya safwan akan wannan yarinyar ",
Safiyya harda gyara zama , safina tafara rattabo mata "sunanta gognur, ajinsu daya itama lawyer ce, tun suna can takeson ya sufyan amma shi yana goce mata. Ba irin wulakancin da bai mata ba amma taki barinsa, ganin haka yasa yake Dan kulata Dan ya safwan yace har dakinsu takanje Shine dataga kusan shekara daya bai dawo ba sai ta biyo abokanansa, jin cewa matar ya safwan ta haihu zasu zo masa bayarinyainefa taketa like masa, amma karkiyi blaming dinsa Dan shi Bayama kulata",
Safina ta duketa a baya "aifa zaki karesa tunda yayanki ne",
Safina ta kanne mata ido daya tana dariya tace "haba matar yaya, kar kishi ya rufe miki ido kimance soyayyar Ku, Dan dakaina na shaida danna gani",
Safiyya ta kada idanuwa tana dariya "to kwalba! Uwar sharri",
Safina ta mike tana tafiya da baya da baya "uhmm ai jiya mun ganewa idonmu abinda yafi karfinmu nida aunt Amina, uhmm ai munga lobayya, wannan kashe kashe haka kamar zaku cinye juna",
Safiyya ta dauki pillow ta wurga mata yayinda safina tabar dakin da gudu.
Sufyan dayazo yin magana da Momy bai iya wucewa wurinta ba, kai tsaye dakinsa ya wuce dafe da Kansa,yadda yaga sofy shike yawo masa a ido, "dama yarinyar nan haka take",
Juyi yayi yana tunanota yadda suka kasance jiya, a hankali yakejin wani abu game da ita yana ratsa jikinsa.
Wanshekare da safe da kyar sufyan ya lallaba gognur ya kai ta airport da alkawarin cewa yananan zuwa Turkey din, dama ankirashi a wurin aiki ance masa ya shirya zai wuce ranar Monday wato nan da kwanaki bakwai kenan Dan haka ranar da daddare ya samu daddy da Momy yake fada musu .
Mommy tayi masa murna da fatan alheri, dady yace dashi "to ita matar taka fa",
Sufyan ya shafa kai Dan shi gaskiya bayason zuwa da ita, kar yaje ya karyawa Kansa alkawarin daya dauka akanta, Dan zamunsu waje daya akai problem,
"Ai dady bada ita zan tafi ba, zan barta nan ne",
Momy ta watsa mishi kallo "inko bazaka tafi da mai dakinka ba sai di bazakayi tafiyar ba",
Daddy ya katseta "ai baza'ayi hakaba, sai ki bari muji uzirinsa,ya juya ga sufyan " ko akwai dalilin ka na kin tafiya da ita?",
Kanshi a Kasa yace "dady naga sabida tana karatu ne shiyasa",
Dady ya gyada kai yace "inka tafi kimanin kwanaki nawa zakayi ko ince watanni ?",
Sufyan yace "dady shekara daya zanyi indawo",
Momy ta bude baki" shekara guda shine zaka tafi kabar matarka , gaskiya bazai yiwuba",
Dady ya kallesa da kyau yace " gaskiya sufyanu kwanakin sunyi yawa.ai sai aga rashin hankalinmu ,har shekara daya, gwanda katafi da ita can, dama a can tafara ai, kuma dayake akwai alaka mai kyau tsakanin hukumar makarantar zan sa mai martaba ya kirasu ya musu magana sai ta cigaba a can tunda dai takusa karewa",
Sufyan yayi shiru sannan ya musu sallama ya bar dakin da tunani iri iri acikin ransa" to yaya zamansu zai kasance ne da ita acan gashi rayuwa nata tafiya, kaninsa har ya aje yarinya, shikuwa bama alamar aure yake,
Tun farko tarigada ta furta cewa ita batason shi ta tsaneshi, kuma dama basa jituwa tun farkon haduwarsu, gwara yasan abinyi Dan yasan in dady ya tsaida magana shikenan ta tsayu,
Shidai yanaji ajikinsa bazai iya rabuwa da safiyya ba, amma kuma bazai iya zama da ita ba ita kadai ,inko yasake ya tafi da ita to yana kara bata ma Kansa lokaci ne, tun safiyya na karama yake sonta amma kuma gashi haduwarsu ta farko bayan ta girma yazo da Matsala shiyasa yake ganin kaman tafi karfinsa, kullum yana kara gayawa Kansa safiyya ba irin matar da za'a kalla a kauda ido bane, gwara ya nisanta Kansa da shi ko zai rage jin abunda ke damunsa akanta ganin shi batasanma yanayi ba...
0 comments:
Post a Comment