fatan alkhairi gareki Uwa mabada mama wato pharm. Mami Sadiya,Allah ya kara girma kuma ya bar zumunci. This page is dedicated to yhu```
Wanshekare da safe sufyan yakai Amira yayi mata registration a boko, dama ss1 take Dan haka ya biya komai da komai sannan sukace gobe tafara zuwa.
Islamiyan dake cikin masaurata nan ta fara zuwa dama zata shiga aji shida ne yanzu, Dan haka duk acikin satin ta fara zuwa makaranta, da yamma kuma taje hadda.
Daddy ya sami mai martaba akan zancen sufyan natafiya turkey, nan yake gayama mai martaba shawarar daya yanke, mai martaba ya bashi goyon bayan cewa "ai sai ta cigaba da karatun a can tunda anan tafara. Dan haka sufyan yafara shirye shiryen tafiya, Momy ce kegayawa safiyya cewan tafara shiryawa zatabi mijinta Turkey,ranar haka ta wuni sukuku dama gashi safina ita ranar Khalil ya dauketa suka koma gida
" tabi sufyan Turkey har suyi tsayon shekara daya! Gaskiya ita bazata iya zama dashi ba, wannan ma zaman dasuke a daddafe ne kuma tanada yakinin akwai 'yan uwanta a garin Wanda take ganinsu hankalinta na kwantawa, amma can fa? Ba dangin iya ba na baba, taje ya tsiri mata rashin mutunci ba kowa",
Tayi tsaki ita kadai a dakinta " dama ga 'yammatan shi na can, sudinga zuwa haushi ya kasheta, dama kuma ga Momy yadda take gyara aunt Amina mai jego haka suma take gyra su itada safina",
Ganin tunanin baida wani fa'ida yasanya mikewa ta nufi falo wurin umma Inda takejin hiransu itada aunt Amina, zuwa tayi ta kwantar da kanta akan cinyar umma yayin da ta dauki jannat tana mata wasa.
Aunt Amina tayi murmushi tace "ooh auta! Yanzu inkun tafi bazamu sake ganinki ba sai nan da shekara daya",
Safiyya ta kakalo murmushi tace "kai aunty! Sai kace inna tafi na tafi kenan",
Umma ta shafi gashin safiyya tace "ai ma dashike akwai waya shike nan zamu dinga jinsu".
"Nasan kafin Allah yasa mudawo jannat ta mance dani" safiyya tafadi a shagwabe.
Aunty Amina tayi dariya "ai lokacin insha'allahu da taki 'Yar zaki dawo",
"Ai ba 'dan sufyan dazai zauna a cikina" ta fadi a cikin zuciyarta.
Umma tayi murmushi tace "ooh ni mairo, sai kace ba auta ke makalewa yaron nan ba, ayi ayi ta zo amma a wurinsa take kwana, tun Dana haifeta yake dawainiya da ita har yabar kasarnan. Ashe matarsa yakeyiwa",
Aunt Amina tayi murmushi "ai duk cikin fada ba Wanda baisanta da shiba,sabida kullum tana manne dashi tunda tafara tafiya",
"Umma kin mance da kyar muka rabata dashi lokacin dazai wuce Turkey",
"Ai ban mance ba Dan har zazzabi tayi,amma duk yanzu ai ita ta mance"
Safiyya dai najinsu bata tanka ba, nan dai sukayita hira har aka kirayi sallahr magriba.
Sufyan ya gama musu komai game da tafiyansu, daran ranar kafin su tafi gidan momy ta kwana tayi mata lalle ja mai kyau aka yi mata kitso, momy har turaren jiki sai da tayi mata sai kamshi takeyi duk inda ta gitta.
ranar dazasu tafi safiyya ansha kuka musamman ita da safina da Amira. Umma da Momy dai daurewa sukayi amma sai da sukayi kwalla, safwan shima duk jikinsa yayi sanyi, har airport safwan, Momy da dady suka kaisu,
Momy na rike da hannun safiyya , sufyan ya dafa kafadan safwan yace cikin sanyin jiki "duk laifin Dana ma kowa bayan munwuce kace suyafemin dannima nayefema duk Wanda yamin laifi, bansani ba Kozan dawo ko kuma tafiyan kenan, banason tayarwa da Momy hankali ne amma bayan na tafi kace tayafemin", share hawayen daya gangaro mishi yayi sannan ya rungume safwan.
Safiyya kuwa na nan manne da Momy tanata gunjin kukan dabatasan dalilin ta na yinsa ba...
[3/8, 12:46 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<33>>```
Safwan ya dafa kafadan sufyan yace "karkadamu Dan Uwa, insha'allah babu abinda zai faru kuma Allah ya kare mana Ku, ya kiyaye hanya.
Amira ta rungume sofy tanata kuka, hannunta ta rike gam
Da kyar Momy ta banbareta daga jikinta suna dagawa juna hannu suka hau jirgi domin yanzu ta abuja zasu tashi, yanzu nan zasu fara zuwa su kwana sannan gobe jirginsu ya tashi zuwa Turkey.
Tana zaune a gefensa yana kallonta, Bini Bini saita share hawaye ,tunowa da maganar da Momy tamishi jiya yayi "sufyan ka Kula da yarinyar nan,kar ka wulakanta min ita, dannaga har yanzu bawani jituwa sosai kukeba kuma nasan Kaine da laifi Dan ita kowa ya Santa da saukin kai, karkaga kaman kadauketa kuntafi kadinga wulakanta ta yadda ranka keso, mata su rauni garesu kuma nasan kasani cewan mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace _kurike mata da amana_, ita mace karamar kwakwalwa gareta kuma yace _su mata kaman kashin awaza(hakarkari) ne, a lank'washe kashin yake ,Indan kabarshi baka gyra shi to zai cigaba da lankwashewa ne, idan kuwa kace zaka mikar dashi to zaka karya ne, to su mata haka suke, yadda kayi da ita a haka zata taso, kai zaka koya mata yadda zata soka ta hanyar kyautata mata Dan haka kasani safiyya amana ce a wajenka_",
Sufyan ya sauke ajiyar zuciya yama rasa tunanin dazaiyi, jirginsu na sauka ya daukan musu taxi zuwa hotel din aka tanadar musu, yana zuwa aka bashi mukulli da kuma nombar dakinsu.
Itadai safiyya duk Inda yabi tana biye dashi a baya, jakar kayansa guda dayane kacal, tata kuwa guda biyu da Yar karama, Dan haka shiya taimaka mata yace ta dauki daya shi zai rike mata biyun.
Haka har suka isa dakinnasu Wanda dakine guda daya da toilet.
Tana shiga ta zube a kasa Dan jinta take gabadaya jikinta ba karfi.shikuwa toilet ya shige domin yayi alwala ganin ana kiran sallahr la'asar.
Yana gamawa ya fice zuwa masallacin dake cikin hotel din. Hakan yabata daman mikewa tashiga bayin Don yin wanka tunda ba ta sallah.
Tana fitowa daga wanka ta sanya wasu Riga da sket masu ruwan toka, rigan roba ne duk ya tattare sai sket din ya Dan kamata daga sama kasan kuma ya bude, ba wata kwalliya tayi ba hoda kawai ta shafa da lip gloss sai ta fesha turarenta Wanda umma ta bata.
Tayi sosai sai ta dauki hula ash mai gashi tasaka.kwanciya tayi a gefen gadon ta dauko wayarta ta kunna, turo kofar yayi hade da sallama cikin muryarsa mai dadi, can Kasa itama ta amsa sannan ya shigo bayansa kuma wani ma'aikacin hotel dinne da ledojin abinci a hannunsa.
Sufyan ya amsa sannan mutumin ya juya, tsakiyar dakin ya zauna sannan ya ajiye ledan.
Yitayi kaman bata Ganshi ba, dakansa ya fiffito da komai ya juye musu a plate yasa spoons. Sai yoghurt din daya siyo shima ya juye a cups biyu,
Juyawa yayi yana kallonta sabida tabashi baya tana kallon dayan side din "ki sakko muci abinci",
Saida ta dauki seconds biyar kafin ta sauko, ta zauna akan center carpet din dake tsakiyar dakin, a plate daya yasa musu, yana zaune yana latsa waya, ganin ta taso yasashi mikewa ya nufi wurin kayan kallo ya fara kunnawa.
Ci tafarayi sannan shima yazo yazauna kusa da ita sunaci tare a hankali (ina ruwan ban saba ba), ita yoghurt din tafisha tabar masa abincin, Satan kallonta yayi yadda tayi kamar Yar under 18 , tayi kyau cikin Riga da sket din sai kamshi take zubawa mai dadi.
Tana gama sha ta mike tashiga toilet ta wanko bakinta sannan ta koma gefen gado ta jingina ,yayinda kafafunta ke Kasa. News din dayasa suketa kallo kuma alokacinne dady ya kirasa yake tambayensa ko su sauka "mun sauka lafiya dady ina Momy",
Bataji mai dady yace ba amma taji alamun momy ta ansa sabida ganin datayi ya kalleta ya yafichota da hannu alamun taje.
Mikewa tayi taje ya mika mata wayan suka gaisa da ita "inata kiran wayarki akashe bata shiga safiyya",
Murmushi tayi ganin yadda Momy ke kulada ita kamar mahaifiyar data haifeta "Momy wayan ba chargi ne amma na kunna",
"Aito Dan ga mutuniyarki nan Amira yau ko islamiya taki zuwa zazzabi ke Neman lullubeta",
Safiyya tayi dariya tana fadin "Momy bata in mata magana",
Momy ta mikawa Amira waya nan suka dinga hira harda dariya, sufyan sai kallonta yake yadda dariyan ke kara bayyanar da kyawunta. Saida ta gama hiran sannan sukayi sallama ta mika masa wayar.
Haka suka zauna zaman kurame sai shidayake amsa waya lokaci lokaci,tanajinsa yayi waya da mai martaba ya gaya masa sun sauka dakuma umma.Haka har aka kirayi sallah magriba da issha'i ya fita masallaci, nan ma saida ta shiga ta tsaftace jikinta tasake wanka, tafito taji ana knocking, kodata duba mai kawo musu abinci ne, yace ta tattaro masa kwanukan da yakawo musu dazun ya tafi dasu.
Shinkafa ne fried rice taji kayan lambu sai naman kaza farfesun kayan ciki, sai ruwa da fresh yo,
Daukan cup tayi ta zuba ruwa tana kensn ya shigo, zama yayi gefenta yana fadin "zuzzuba mana amma kadan Dan banajin yunwa sosai",
Zubamusu tayi sukaci tare, sufyan duk lokacin dasuka kasance tare sunacin abinci yakanji nishadi a cikin ransa " dama haka cin abinci da matar ka keda dadi? Inama ace shida ita masoya ne. Hmmm" ,
Lumshe ido yaketayi har ya gama ita kuma ta mike ta shiga toilet , ya kula batason cin abinci sosai sai yoghurt, kwanciya taje tayi a gado can gefe daya shikuma ya yi zamansa ya kunna system dinsa yanata bincike bincikensa har wajen karfe goma lokacin taga ya kashe wutar dakin amma fitilan gefen gadon a kunne take dayake batayi bacci ba idanunta biyu, hayo gadon yayi ya kwanta kusa da ita yana mai laluben blanket bai saniba hannunsa ya kai kan wuyanta...
[3/8, 12:48 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<34>>```
```sakon gaisuwa gareki maman haneep, Allah ya barmu tare```
Dippp ta dauke numfashi jin hannunsa a wuyanta, shikuwa wani Yarr yaji kuma ya Kasa dauke hannunsa a jikinta,lamon datayi ne yake tunanin kamar ai tayi nisa da bacci Dan haka yayi sama da hannunsa yana shafar gashin kanta dayake birgeshi, a haka har bacci ya daukeshi, tanajin yayi bacci ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya itama da hakan bacci ya dauketa.
Wanshekare da asuba shiya fara tashi ya nufi masallaci bai tasheta ba sabida yasan ba sallah zatayiba ,dalilinsa na ganin pad a dustbin, yana ficewa ta shige toilet ta gyra jikinta tayi wanka ta shirya cikin atampa blue mai zanen fanka a jiki, doguwar rigace ta kamata daga sama kasan kuma ya bude sosai anyi tattara, ta daura dankwali tayi kyau sosai hardasu makeup, koda yadawo binta ya dinga yi da ido a zuciyarsa yana fadin "uhmm wannan yarinyar bazata kasheni da gayu da kamshinta ba",
Mai kawo musu abinci ya kawo sukacyi breakfast cikin Sauri domin yace mata tayi Sauri yanzu zasu tafi, hijjabi ta dauka light blue tasaka Inda yasaukar mata har gwiwa ta saka safa sannan wani yazo ya fitar musu da akwatinansu.
Shikuwa yasaha kananan kaya Riga da wando, rigan purple sai wando baki , sai kamshi yake zubawa mai dadi na turarensa na koda yaushe, driver shi ya kaisu airport , cikin mintinan da basu fiye goma ba jirginsu ya daga.
Zaune take kusa dashi amma duk jikinta yayi sanyi ,wayarta ta dauko ta rubatawa safina messg kamar haka "muna cikin jirgi zamu wuce , cwt kimana addu'a"
Tura mata tayi sannan ta Dan juya idonta gefensaz idanuwansa na kallon window ya natsu komai yake tunanin ohoo amma ta kula kamar azkar yakeyi ganin yadda yatsunsa ke motsa.
Tsintar kanta tayi da fadin "handsome knn",
Jinda tayi kamar jirgin ya daki wani Abu yasanyata fadin "innalillahi wa inna ilaihi raji'un",
Shima da Sauri ya juya yana kiran sunan Allah, kawai sai gani sukayi jirgin ya fara kamawa da wuta, hayaki ta ko'ina.
Sanarwa akafarayi cewa jirgin is in danger, passengers kowa ya rude daga masu kuka sai masu ihu.
Safiyya ta zaro ido tama Kasa cew komai ganin jirgin na kasa-kasa. Da Sauri ya riko hannunta yama rasa mai zaice, tuni idanuwanta suka fara hawaye kukanta ya karu ta rukunkumeshi "ya sufyan mutuwa fa zamuyi",
Zufa taga yana keto masa sosai ya kara kankameta a jikinsa yana fada mata a kunne "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, La haula wala quwwwmata illah billah",
Jikinta yafara rawa Dan ita lokacin hankalinta baya jikinta sai kukan datake rusawa. Gum! Gum!! Gummm!!! Kakeji jirgin ya tawarwatse.
Safwan na zaune rike da jannat a falon umma sai aunt amina dake gefensa Suna hira, yayinda umma ke cikin dakinta, hankalinsu ne yakai kan t.v daketa aiki manne a bangon dakin.
"Jirgin daya tashi da safennan daga Nigeria zuwa turkey yayi crash, yayinda ba passenger daya tsira acikinsu hade da pilot din",
Safwan ta fizge remote din dake hannun Amina yana kara karan magana, aunty Amina ta mike tana salati "inna lillahi ,umma! Umma!! Umma!! Auta da sufyan, umma auta ",
Da Sauri umma ta fito jin kiran kaman a haukace. Gani sukayi safwan ya duga ya kurawa t.v ido kamar Wanda ya zauce.
Daddy ma anashi dakin hakane, Inda yake zaune shida mom Suna breakfast kenan sukaga ana nunowa breaking news na plane crash,
Dady ya mike yana salati yakasa magana. Momy kuwa tuni tafara kururuwa tana fadin"wallahi abban twins jirgin su sufyan ne, shikenan innalillahi wa inna ilaihi raji'un",
Dady dayake namiji ne zuwa yayi ya rike kafadarta "haba maman biyu, daga ganin plane crash sai kice sune, waya cemiki jirginsu ne kawai ya tashi yau, Dan Allah ki kwantar da hankali bari nashiga fada insamu sarki muje mu bincika , insha'allahu ba jirginsu bane",
Momy zubewa tayi a Kasa tana gunjin kuka "wallahi tun jiya da suka tafi gabana keta faduwa , shikenan"
Dafe kirjinta tayi tana fadin"allahumma ajirr ni fi musibati",
Daddy na shiga fada ya wuce sassan sarki Inda safwan ya sume musu anan, sarki ya kalli daddy yace "yanzu ka tafi ka binciko mana muji gaskiyan labari, ni bari muwuce da safwan asibiti",
Aunty Amina ta jabe akan kujera ganin safina sai kiranta takeyi awaya Dan ta kira wayar Momy da safwan ba'adauka ba.
Daddy da Sauri ya fita yana kiran sunayen Allah a harshensa Dan kuwa kwata-kwata jikinsa ya mutu.
Cikin Sauri Momy ta dauki mayafi ta wuce gidan sarki, nan sukaci karo da umma da sarki an dauko safwan ga aunt Amina sai kuka takeyi. Lallai tashin hankalin da ba'asa masa rana kenan
[3/8, 12:49 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<35>>```
```wannan naki ne big sis (aunty sis)```
Umma dayake akwai dakakkiyar zuciya batayi ko hawaye ba saima hakuri datake ta bawa Momy da aunt Amina,
Safina tana daki taga labarin ,hankalin ta a tashe ta kirayi nombar Khalil take fada masa dayake yana asibiti ya fita, cikin Sauri tadinga dialing nombobin su Momy amma ba'a dauka ba ,hakan yasa hankalinta kara tashi, Khalil na zuwa ya dinga kwantar mata da hankali ganin ciki gareta karami. Flight suka dauka zuwa gombe.
Daddy koda yaje akabashi tabbacin cewa jirginsu sufyan ne yayi crash hawaye yadinga fitarwa har ya iso asibitin da aka kwantar da safwan.
Momy na zaune tanata goge hawaye sai umma da aunty Amina a gefensu. Shi kuma sarki ya shiga cikin office din Dr. Dady ya karaso yana kokrin share hawayen dake kokarin zubo masa.
Momy ta nufeshi da Sauri ta rikesa gam "Sune ko baban twins, sune ko?",
Janta yayi suka zauna lokacin da mai martaba ke fitowa daga office din Dr. Isowa yayi cikin Sauri yace taso muyi magana usman,
Wajen asibitin suka fita mai martaba ya dafa daddy yace "ankirani bayan fitanka ancemin jirginsu ne, kuma bawanda ya tsira da ranshi a cikin jirgin har pilots din, Dan haka kayi shiru kadaukesu Ku wuce gida dukkansu, in kaje can sai ka fada musu, ni ka barni anan wurin safwan sunce suma yayi kuma jininsa ya hau, kar su kara tayar masa da hankali in aka barsu anan" ubangiji Allah ya jikan sufyan da safiyya ,Allah yayi musu rahama kuma ubangiji ka hada su da manzon tsira .
Mai martaba ya goge hawayen daya zubo masa ganin dady na hawaye sosai, wai danma su maza ne.
Komawa ciki sukayi yayinda mai martaba yace sutashi su tafi gida shi zai tsaya anan, dady yace wai sunce zasu kirasa dan basu da tabbacin ko jirginsu sufyan ne",
Da kyar Momy ta bisu suka koma gida, kai tsaye gidan sarki ya ajiyesu, tundaga nan jikinsu yayi sanyi sabida sai musu gaisuwa akeyi mutanen fada wasu nata kuka.
Suna sauka suka shiga ciki aunt Amina tayi falo da gudu ta zube sai kuka, Momy ta rike dady tana fadi cikin kuka mai taba zuciya "nasan wallahi sune bakaso kagayamana ne, ko ka boye yazamuyi tunda mu musulmai ne dole muyadda da kaddara, shikenan sufyan da auta , Allah ya sadasu da mala'ikun rahamaaaa", nan ta zube anata bata hukuri.
Zancen da safina tajine yasanya kayan cikinta hautsinewa "Allah ya jikan safiyya da sufyan, Allah kasada su da mala'ikun rahama".
Hasbunallahu wa ni'imal wakil shi kawai ta iya furtawa tayi taga-taga zata fadi ,da Sauri Khalil ya tarota ta zube a hannunsa.
Karasawa yayi da ita ciki shima hankalinsa duk a tashe idonsa jajur,
Umma ce zaune da hijjabi tana jan innalillahi sai aunt Amina gefenta tana ta kuka ba kakkautawa, Momy kuwa tana tsakiyar wasu yana uwanta da suka iso anata rarrashinta.
Umma da Sauri ta kalli Khalil tace "kwantar da ita nan, ta mike ta shiga ciki ta dauko Goran ruwa ta zo ta yayyafa ma safina.
Daddy dake waje ya shigo idonsa jajir "kozamu wuce da ita asibiti ne",
Umma ta girgiza kai "Ku bata zata farka da ikon Allah",
A hankali ta bude idonta ta fara kallon mutanen dakin. Tunowa da abinda Momy taji tana fadi tayi "Allah ya jikan safiyya da sufyan",
Da Sauri ta mike ta cakume umma dake gefenta "umma ina safiyya, Dan Allah umma Ku kiramin ita , kar kucemin ta mutu",
Sai a sannan umma ta rushe da kuka "safina! Su safiyya sai dai addu'a,Allah ya bamu hakurin rashinsu",
Nan dakin ya kara kaurewa da wani sabon kuka ,ita kuwa safina Umma ce ta rirriketa ganin tana Neman ta gudu" Dan Allah kubarni naje nagansu , umma kiyimin rai ki kaini gun cwt, umma Ku kyaleni kuyimin rai",
Aunt Amina da Sauri tashige daki hade da rufe bakinta tana kuma wani uban kukan, duk dakin anrasa mai bawa wani hakuri kowa kuka.
```bayan awa biyu```
Khalil ya shigo a hankali falon ya isa garin umma ya duka "umma ya hukurinmu",
"Hakuri mungode Allah Khalil",
"To ubangiji Allah ya jikansu. Dama yan uwurin aikinsu ne suka iso to zasu shigo sumuku gaisuwa ne",
"To bisimillah su shigo", Khalil ya musu iso zuwa falon ,nan sukayiwa su umma gaisuwa Dan ita Momy ba uhm ba uhm uhm sai kuka".
Safina ansamu tayi shiru, Dan umma tace tadinga addu'a ba kukaba, amma in abun yafado mata sai kaga ta cigaba da surutai.
Inna luba itama shiru Dan carbi kawai take ja takasa magana
Mutane sai tururuwa ake wajen yimusu gaisuwa domin fada ba karamin asara tayiba, safiyya yarinya mai mutunci da biyyaya ga ban dariya batada problem da kowa a masarauta, shiko sufyan ba Wanda bai sansa da kyauta ba ga mutunta jama'a
Amira dawowanta kenan daga makaranta ta shiga gidan Momy ta tadda ba kowa Dan haka ta nufi gidan sarki. Tun daga bakin gidan mutane ne cike. Nan gabanta yayi mummunan faduwa "to maiya faru?",
Wuce wa tayi kanta a Kasa har falon umma. Tana zuwa ta isa wajen inna idanuwanta sunyi kwala kwala " inna maiyafaru",
Inna bata iya furta mata komai ba sai ta fara kuka,
Umma ta yafito ta da hannu alamun tazo gareta.
Kasa mikewa tayi jin abinda safina ke fadi tana kuka "Allah ka hada cwt safiyya da ya sufyan gidan rahama kuma kayafe musu kuakuransu, shikenan cwt ta tafi tabarni, Allah yabani hakurin rashinki safiyya",
Amira ta mike a tunzure tana Murza ido"sum...summ...mu..mutu...no wallahi karyane
[3/8, 12:50 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<36>>```
```gaisuwa ga duk matan grp din muqaru da juna 1&2, munagodiya akan badan goyon bayanku da kukeyi, kune masoyan littafin mace kadara ce mai tsada, Dan haka wannan page din naku ne```
Zubewa tayi da Sauri umma ta mike ta tarota itada inna Sadiya yayar Umma, cikin bedroom din umma suka shiga da ita ,inna Sadiya ta ibo ruwa ta tattofa mata addu'oi sannan ta yarfa mata, nan taja ajiyar zuciya mai karfi amma bata farka ba.
Inna Sadiya ta dauki jannat dake ta kuka "uhm haba Amina ki dauketa kibata nono ko bacci zatayi",
Aunt Amina ta dago da kananun idonta dasuketa zubarda hawaye tace "Dan Allah inna kibarta, da ita zanji koda rashin 'yan uwana".
Inna ta mike itama tadan share hawayen daya zubomata ,bataso tayi kuka a gaban umma domin ita ke kwantarwa da umma hankali, mika wa Amina yarinyar tayi "ai su insha'allahu munasamusu ran gidan rahama domin halayensu nagari dakowa ke fade, ita yarinyace Dan haka karbeta kibata tasha ina gani",
Da kyar Anty Amina ta bawa jannat nono sannan inna ta bar dakin , kanta ne yakaiga wani hoton safiyya da sufyan ranar dinner aka musu,girke yake a jikin bango Dan haka da Sauri taje duk ta juya hotunan",
Safina takara fashewa da wani kukan "Allah sarki rayuwa, wato sai Kanada rai akeyi dake, yanzu kalle ko hotunansu ma juyawa ake, Kai Allah ka mana kyakkyawan karshe ubangiji kabamu ikon cikawa da imani",
Kawayensu na schl tadinga kira tana fada musu cewa safiyya ta rasu, kowa sai yace "haihuwa tazo yi ne" safina takance musu a ah ita da mijinta ne sukayi hatsari a jirgi, wasu suce "badai sofy maikudi ba",
Bayan tagama ne ta duba text mssg din data gani. A firgice ta mike tana karanta text din da sofy tamata , saida ta duba time din sai taga Ashe tun karfe takwas da minti hudu tamata, nanfa kuka yadawo sabo. Ta mike ta nunawa umma da Momy text din , itama Momy ta kara rushewa, itadai umma akwai karfin hali Dan kuwa kukan zuci kawai takeyi. inna sadiya tace "safina ki yi hakuri Dan Girman allah, kinga karamin ciki gareki karkima kanki illah, ansan abun akwai ciwo but take hrt, addu'a yanzu kawai suke bukata".
Daddy ma yanacan cikin fada domin sarki yana tare da safwan Wanda ko motsi bayayi a asibiti, Dan haka shike karban gaisuwa, gwamnan gombe shima yazo da tashi tawagar kowa yana musu jaje dankuwa mutun biyu ai ba wasa ba.
Amira ba ita ta farka da akayi sallah magriba, inna Sadiya na kan dadduma tana lazimi da Sauri ta isa gareta ganin tana fizge fizge ita aunty ita ya sufyan, addu'oi ta fara tofa mata har ta bari sannan ta bude idonta, a daburce ta mike inna sadiya ta kara danneta "ina kuma zakije Amira",
"Dan Allah inna ai mafarki nakeyi ko",
Inna tayi shiru takasa bata amsa, "inna tun safe nake bacci ko, ya ubangiji mahallicina ,Kasa mafarki nayi wai sun mutu, Allah Kasa ba gaskiya bane".
Umma ta shigo itada inna lubabatu jin surutan Amira , umma tazo ta dafata tana fadin "Amira ina imaninki da Allah yake, ko baki yadda da kaddara bane, Allah daya daukesu yafimu sonsu kuma dama shiyaba musu, Dan haka banason surutan nan kinaji",
Inna luba ta matsa kusa da ita ta dafa ta "Amira idan bamuyiwa wadannan bayin Allah addu'a ba mai zamuyi musu, bancin su suka taimakemu alokacin da ake Neman wulakantamu, suka bamu wajen kwana alokacin da aka koremu, suka tallafemu alokacin da aka kyamacemu, suka bamu abinci alokacin da akabarmu da yunwa, suka mana sitira lokacin da ake Neman ganunmu tsirara", inna ta kuma rushewa da kuka "ya ilahi ka jiqan wadannan bayi naka, Allah ka yafe musu kurakuran su, halinsu nagari ya bisu",
Inna Sadiya ta iya amsawa Dan ita umma da Sauri tabar dakin ta shiga toilet tana maimata "innalillahi wa inna ilaihi raji'una.
Ranar gidan babu Wanda ya iya runtsawa, momy , safina, Amira da aunty Amina sai da aka tasasu gaba suka sha kunu, Dan kuwa wuni sukayi ba ci ba sha.
Ita Momy dama ko sallah ma a zaune takeyi, amsa gaisuwa sai da kai, sai idan anyi musu addu'a ne takan bude baki tace amin. Aunty Amina na jego, safina karamin ciki ,sai da inna Sadiya tasasu gaba kafin aka hada musu tea suka sha.
Ita safina fadi take "akawo mata gawawwakinsu ta gani ko hankalinta zai kwanta"
Amira ita ko kunun taki sha balle tea, sai da inna Sadiya da sauran kannen Momy suka mata Jan ido sannan ta da kurba. To safwan fa?
[3/8, 12:52 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<38>>```
Motsawa hannunsa yayi a hankali yake bude idonsa yana rufewa, ganin haka ya sanya budurwar dake gefensa fita da Sauri zuwa kiran mahaifinta, shima baban nata da Sauri yashigo dakin suka nufo garesa,lokacin idanunsa suka bude, binsu yayi da ido shikuma mutumin yayi murmushi, cikin wani kalan yaren da bayaji yaji Suna magana.
A hankali sufyan yafara tunano abinda yafaru, a firgice yayi nufin mikewa hade da fadin "safiyya!", kasawa yayi sabida daurin karayar dake kafarsa Wanda tasha nadi, da Sauri baban ya kalli budurwan yace cikin yarensu "kije ki kira yayanku yanzun nan",
Fita tayi yayinda sufyan yacigaba da kiran sunan safiyya, da yake shi mutumin bayajin abinda sufyan ke fadi. Budurwan tadawo dawani matashin saurayi da Sauri ya iso wurin sufyan yana masa magana cikin harshen turanci "sannu, ya jikinka".
Sufyan yayi kuri da ido yana kallonsu ganin bai taba ganin mutane irinsu ba,kayan jikinsu ma ba irin na wadanda yasaba gani bane ,tambayensa "plss ina sister na",
Matashin yayi masa murmushi ganin sufyan yana jin turanci ,dama sunyi gudun kar azo kuma ya tashi bayajin yaransu kuma bayajin turanci su rasa yadda zasuyi susan wanene shi "ka kwantar da hankalinka, kagaya mana ya kake ji yanzu sabida malamin daya ke maka magani yace inka tashi mukira shi".
Sufyan ya cije lebansa nakasa yace "banajin komai sai dai kawai jikina yayi tsami, amma please ku gayamin ko kunga sister na",
"Eh munganta itama tana daga cikin can dakin",
Sufyan ya sauke ajiyar zuciya mai sanyi, jin haka ya Sanya hankalinsa kwanciya, duk wannan zancen da sukeyi tsakanin sufyan ne da matashin sabanin mahaifin nasu dabajin turanci sosai sai yarensu.
Budurwan aka aika taje ta kira malamin dayake treating su, koda ya iso ya tattambayi Inda yake masa zafi.warware daurin yayi sannan yace "kana iya dinga takawa yanzu, shikuma ciwon dake hannunka ga magani sai kadinga shafawa safe da rana, ita yarinyar inta farka haka zaku mata, Dan ita nata ta bugu sosai a kanta.
Nan suka mishi godiya sannan ya tafi.sufyan ya mike daga kan tabarman dayake yanafadin innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ko kwanansu nawa yanzu oho. Ba sallah ba salati",
Matashin ya karaso yana fadin" sannu ya sunanka kai da sister dinka",
Sufyan ya danyi murmushi yace "sunana sufyan ita kuma safiyya, Dan Allah kwananmu nawa anan",
"Yanzu watan Ku uku kenan a kwance anan, wannan shie babana muna cemasa papa (yanuna wannan dattijon) wannan kuma kanwata ce sunanta Camila sai nikuma sunana jass, babana shine ya tsinceku cikin gonarsa, shine ya dauko Ku ya kawoku gida",
Sufyan ya kallesu yana musu godiya sannan ya bukaci sukaishi Inda sofy take. Dakin dake gefensu nan take kwance , kallonta yayi cikin tausayawa ganin duk taji ciwo a jikinta, ko'ina andaure ansa magani. Tsugunnawa yayi dai-dai kanta ya shafi gefen fuskarta sannan ya tottofa mata addu'oi.
Nan yace su nuna mishi toilet Dan yayi wanka, budurwan ita ta nuna masa sannan aka kaimasa ruwa, Dan kuwa shima tattaka kafar tashi yake a hankali sabida ciwo,
Wanka yayi sannan yayi alwala , dayaje daki ya dai-daici gabas sannan ta fara jero sallolinsa da ake binsa, tsakaninsu dukka sai aka soma kallon kallon. To shikuma wannan mai yakeyi haka.
Haka yayita jero sallolinsa har ya gama sannan ya zauna yana istigfari hade da godiya ga Allah daya tseratar dasu daga masifan hadarin jirgi.
Bayan yagama ne camila ta kawo masa abinci da ruwa sai kuma kayan sawa Riga da wando sababbi ganin irin kayan dasuka tsinceshi dashi a jikinsa.cire na jikinsa yayi sannan ya saka wadannan, tsayawa yayi yana kallon abincin "to wannan kuma menene" .
Wanda yaga kaman alale shi ya soma ci. A hankali ya dinga turawa har yacinye wannan, sauran kuma ya ajiye gefe. Shi tunaninsa yafi tafiya kan safiyya "yanzu in Allah yasa ta tashi yazatayi da irin wannan abincin?
A hankali ya taka ya shiga dakin datake kwance, Dan yanzu shi dingishin nashi kadan ne, zama yayi kusa da ita yana mai gyra mata gashin kanta daya rufe mata idanu..
[3/8, 12:53 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<39>>```
"Allah ne kawai ya tausaya musu yasa suka fada waje daya kuma har ya kaddara sunada rayuwa anan gaba, inba haka ba daya zasuyi".
A hankali hawaye ya gangaro a idanuwansa"Allah shikadai yasan abinda yasa suka fado wannan gari dabaya tsammanin ma musulmai ne, kwata kwata al'adunsu ba iri daya da namu ba".
Fita yayi yaje ya samu wuri ya zauna kusa da papa da jass "jass wai nan wani gari ne kuma wace Kasa",
Jass ya karyi raken dayake sha yace "sufyan ai nan ba gari bane kauye ne sunansa vergos , Tbilisi sunan garin kuma a acikin kasar Georgia, kai kuma ya akayi muka tsinceku anan"?,
"Mun samu plane crash ne zamuje Turkey shine muka fado nan",
Papa ya kallesa da gurgurarriyar turancinsa yace "to mai mukaga kanayi dazun up and down",
Sufyan yayi murmushi yace "inayin ibada ne, sunanta sallah, kuba kwayi ne",
Papa ya girgiza kai "ai mu namu bautan sai da daddare zamuje gidan sarki shi muke bautawa, kar ka damu anjima zamuje dakai kagani.
Camila ta dawo rike da tulun ruwanta a hannu ta ajiye sannan tazo tazauna gefen sufyan tana masa murmushi. Sufyan dai ya rasa ma tunanin dazai yi to, shi yanzu yazasuyi subar garin nan dankuwa daga gani mutanen nan talakawa ne, shikuma bashida ko sisi, babu ma phone a kauyen balle yayi waya zuwa Nigeria, tirkashi kenan.
Nandai suka zauna sunata hira ,Dan shi sufyan ba gwanin surutu bane amma bayadda ya iya dole yake tambayensu wasu abubuwan.Camila ke cemasa "kai da kanwarka kyawawa ne" murmushi kawai yayi mata
Duk lokacin sallah intayi yakan dai-dai ci lokaci yayi ,kuma Bini Bini yakan leka safiyya dake kwance kamar gawa. Ko da daddare wurinta ya kwana gudun karta tashi asamu matsala. Sabida dukkan su suntafi wurin bauta Dan haka shi yana zaune kusa da ita yana tunanani Momy da sauran yan uwansa "koya suka ciki yanzu Ohoo?".
Wanshekare da safe papa zai tafi gona sufyan yace zai bishi yayinda jass zai wuce makarantar dayake koyarwa. Yayi hakanne Dan yasamarwa safiyya abun da zataci kafin ta tashi.
Yaji dadin zuwa gonar kuwa Dan yasamu kayan marmari dayawa kamarsu , tuffa, lemu da ayaba sai rake da piya.
Yana dawowa ya shiga ya zube matasu sannan ya gabatar da sallah azahar. Zaune yake yana azkar yaji motsinta, da Sauri ya isa wurinta yana tofa mata addu'oi.
Bude idanuwanta tayi tangaran akan fuskarsa takura masa ido, can kuma tace "wash!" Ta dafe kanta dake sarawa
Sannu ya fada hade ya tallabota zuwa jikinsa, sun kwashi seconds 40 a haka kafin ya saketa tafara juye juye da kalle kallen Inda take , a hankali hawaye ya gangaro daga idonta "ya sufyan ina Momy da umma, waya kawoni nan",
Matsawa yayi kusa da ita, karo na farko ya fara share mata hawayen dake gangarowa daga fuskanta "shhiii kiyi shiru kinji, yanzu kigayamin ina ke miki zafi",
Nuna masa kanta tayi yace " to kinga banason kuka, kiyi shiru kar ki karawa kanki ciwon kai, bari na kawo miki ruwa ki wanke bakinki.
Itadai binsa kawai take da ido. Ya fita ya dauko mata roba da ruwa sai aswakin goge baki, zuwa yayi zai wanke mata ta shagwabe fuska "kabarshi zan iya faa",
Murmushinsa mai tsada yayi mata "OK. To wanke ingani",
A hankali ta wanke bakinta Tass sannan ya dauki ruwan ya je ya zubar. Dawowa yayi ya matsa kusa da ita ya riko hannunta ya hade da nasa yace "ki saurareni kinji sofy",Dan shi yanzu tausayinta yakeji yadda zatayi rayuwa anan, gwanda shi namiji ne kuma ansan maza da dauriya, ita kuwa mace ce mai rauni.
Gyada kai tayi sannan yacigaba "ki San dai Abinda yafaru muna cikin jirgi ko", nanma daga masa kai tayi alamun eh.
"To nan dakika gani gidan mutanen dasuka tsince mune, kuma suka bamu kulawa har muka farka, ba musulmai bane kuma basu sanma addini mai suna musulunci ba, ba yarenmu daya da suba dan haka kisa a ranki cewa haka Allah ya kaddaro mana zama dasu har zuwa lokacin da zai kaddara mana komawa gida, danni banma tabajin sunan kasar nan dasuka gayamin ba",
Hawaye ne ya gangaro mata daga idanuwanta , kallonta yayi ya shiga girgiza mata kai alamun tadena.
Cikin muryan kuka tace "to kwananmu nawa anan yanzu?",
"Sunce min watanmu uku a kwance, dan haka yanzu ga fruits nan bari na wanko miki sai kici kiyi sallah kiyi wanka",
Saida taci kayan marmarin sosai sannan ya kamota sosai a jikinsa suka fito. Camila ta nufosu tana murmushi da Sauri safiyya ta boye a bayan sufyan tana zaro ido ganin kalan mutanen dabata taba ganinsu ba sai a t.v.
Shi sufyan ma dariya tabashi dan haka yamaida kallonsa ga Camila datakewa sofy sannu yace "ruwa zaki zubomin na zafi zatayi wanka ne".
Camila ta gyada kai sannan taje ta kawo masa. Shiya rakata har kofan bayi tayi wankan. Tare suka jero ya kaita har daki sannan ya bata wasu Riga doguwa purple yace tashirya ta yafa dankwalin yana jiranta.
Saida ta shirya sannan ya shigo ya bata wani babban mayafi yace tayi sallolin da ake binta.
Yana zaune harta idar sannan ya kara bare mata lemu yace tasha,
Girgiza kai tayi "nakoshi",
"Keda bakida lafiya yakamata kichi sosai. Suna cikin magana jass da papa suka shigo sabida Camila tace musu ai safiyya kanwar sufyan ta farka.
Ai da gudu kamar an tsikareta ta Fasa kara ta kankame sufyan dan tsoronsu...
[3/8, 12:54 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<40>>```
Kallon sufyan sukayi Suna fadin" Ashe ta farka",
"Eh ta farka gashi ma har tayi har tayi wanka taci abinci ma",
Jass ya kalli safiyya yana mata murmurshi "sannu ko",
Ko motsawa batayi daga bayan nasa ba balle ta amsa sabida tsabar tsoro. Sufyan ne ya amsa "karkudamu zata watstsake ,bata saba da nan din bane shiyasa",
Fita sukayi shikuma ya juyo gareta a rungumeta sosai a jikinsa ganin tana hawaye, zama sukayi a gefen katifan ya dinga rarrashin ta hartayi shiru. Da yamma yajata suka fito tsakar gida gefen bishiya suka zauna cikinsu Camila, itadai tana makale agefensa kamar zai gudu. Zama sukayi sunata hira da jass. Nan sufyan yaketa gaya musu menene addinin muslunci cikin dabara da Jan hankali. Camila ta muskuta tace "mu ai anan idan bakabin addinin garin nan kasheka za'ayi, kudinma papa yace kar mufadi ma kowa cewan akwai bak'i a gidan nan, dan duk bako Idan yazo sai ankaishi wajen sarki",
Sufyan yayi dan murmushi "mukuwa kunga musulunci bai yarje mana kashe Wanda ba musulmi ba batare da wani hakki ba. Domin manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi yace _duk musulmin daya kashe kafirin amana to bazaiji kamshin aljanna ba_",
"To kai waye Wanda kuke bautawa kuma yana ina?" Jass yayi tambayar cikin rashin fahimta.
"Mu ubangijinmu shine Allah mahaliccin kowa da komai. Yana sama kuma ba'aganinsa dan kuwa idanuwa bazasu taba iya haninsa ba, bashida farko kuma bashi da karshe, har wutan dakuke bautawa itama Allah Shiya halicceta Shiya cancanta a bautawa batare da anhadashi da kowa ba domin Allah madaukakin sarki yafadi acikin suratu nahali ayata ta (51)"kuma Allah yace kada Ku riki abubuwan bautawa guda biyu. abin sani kawai Wanda ake bautawa guda daya ne sannan sai kuji tsorona nikawai"
Papa ne yadawo daga gona suka mishi sannu dazuwa, zama yayi nan sufyan yadinga fayyace musu menene musulunci dakuma kyawawan dabi'u nasa har lokacin dayaga rana ta fadi ya kalli safiyya yace tatashi suyi alwala".
Tashi sukayi tana rike da hannunsa gam sukayi alwala suka gabatar da sallah magriba, basa bar wurinba saida sukayi sallah isha'i sannan , Camila ta shigo ta kawo musu abinci sannan ta Sanar dasu cewan su zasu wuce wurin bauta.wanka ya rakata taje tayi sannan ta kwaso turarukan Camila ta shashshafa a jikinta dan ba zata iya zama ita batare da kamshi ba. Cikin kayan dayazo mata dasu jiya ta dauka wasu Riga da pink tasa da wando tiet baki ya wuce gwiwa da kadan. Gashinta ta tufke ta kitse kasan. Sai tayi kyau kamar Yar tsana.
Dayake insuka tafi sukan kai awa hudu acan. Tana zaune ta jingina jikinta akan katifa tayi shiru , tunani takeyi "yanzu haka rayuwansu zai cigaba anan cikin rashin sanin madafa,cikin mutanen da bata sansu ba, dakuma garin da bata tabajin sunan sa ba, to ai zaman mata ko wajibi kullum idanunta sudinga zubarda hawaye".
"Yasan dai tunanin ta bazai wuce na gida ba, shiko yanzu kwata-kwata bayason ganinta tazauna dai-dai da Minti daya shiru duk dai yasan wajibi ne domin bawani shakuwa sukayi ba da har inyana wuri zata mance da kowa, yanzu abinda ya rage masa kenan a matsayinsa na mijinta daya Samar mata duk wani farin ciki, dole ya aje duk wani rashin jituwa dake tsakaninsu ya kwantar mata da hankali, tunda yanzu dai ba Wanda zata kalla ya kwantar ma, gashi dai ba gwanin surutuba amma zai kokarta".
Zuwa yayi dai dai fuskarta ya hura mata iska , firgigin tayi ta zuba zuba masa sexy eyes dinta , murmushi ya dan mata a yangance "lafiya kuwa?",
Cire nata idanuwan tayi daga cikin nasa dan yadda idanuwansa ke fizgar ta, zoben dake yatsanta ya kama yana murzawa a hankali, tsigar jikinta ne ta tashi jin lallausan fatar hannunsa akan tata, a hankali yake magana yadda inba kana kusaba sosai bazakaji ba "wani barawo ne aka kamashi ya saci akuya, mutane sukayo kanshi ganin yana kokarin daura akuya akan mashin, dayaga anyo kanshi gadan gadan sai ya daga murya yace 'nifa dama machine zan koya mata'.
Safiyya ta kyalkyale da dariya harda toshe baki dan dariya kuma gashi dare ne, kallonta ya tsaya yanayi cikin ban sha'awa yadda take dariya beauty point dinta na lotsawa
"Wato machine zai koya mata".
Mikewa yayi ganin yasamu abinda yakeso ya sata farin ciki, wanka yatashi yayi yabarta cikin mamakin halayen ya sufyan, ji yadda ya mike kaman bashi yagama bata labari ba, komai nashi cikin yanga da Jan aji kaman mace,amma a fuska zaka ga kaman bai magana koda yake ai ba a fuska bama haka halinsa yake ba kasafai ya cika magana ba , gashi dai yanzu lokaci daya yasata manta da damuwar dake ranta, ki tayi ya maye wani wuri a can kasar zuciyarta".
Haka ta dinga murmushi sai gashi ya shigo sanye da Riga da wando ja da baki,sai kamshi yake mai kwantar da hankali , lokacin tana zaune akan katifa ta kishingida da pillow tana kallon saitin window, kallonta yake sosai dan ba karamin birgeshi tayi ba yadda take lum lumshe idonta tana budewa alamun bacci, zuwa yayi ya yarfa mata ruwan dake hannunsa ,
Turo baki tayi tana fadin "auushh!".
Tsokanarta yayi niyyan yi "dama nace ko akwai abinda kike bukata zan wuce na kwanta",.
Gwalo ido tayi ta diro daga kan gadon "ai kadai san tsoron su nakeji dai ko",
Murmushi ya mata sannan ya ja hannunta suka koma gefen katifan suka zauna"wai meyasa kike tsoronsu, mutane nefa kamar ki",.
"No su ba mutane bane kamana ,ji su fa kamar wasu kwaduna ido mitsitsi",
Baisan lokacin da dariya ta subuce masa ba,kyau taga ya kara sosai, Ashe dama yana dariya".
Juyawa tayi ta dauki pillow ta kwanta abinta sannan taja blanket ganin wasa yake mata ba tafiya zai yi ba. Kashe hasken fitilan yayi sannan shima ya kwanta gefenta, dayake katifar ba wata babba bace dan haka jikinsu yana gogan juna dan kamshin su ya hade waje daya yabada wani launin kamshin na daban.
Mirginawa tayi ta juyo Suna fuskantar juna sabida nan ne barinta na dama. Shiru ya biyo baya amma kirjinta sai bugawa yakeyi da Sauri da Sauri jin saukar numfashinsa a fuskarta a hankaki, kwakkwaran motsi ta Kasa yi, so tayi ta juwa kawai taji ya janyota jikinsa ,bugun kirjin ta ya karu jin wasu Sumba dayake zuba mata a sassan jikinta.
[3/8, 12:55 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<41>>```
Shafan tsakiyar kirjinta yayi jin yadda yake bugawa da Sauri da Sauri,bai mata komai ba baccin wannan ,ji tayi yana karanto musu addu'oin bacci, ya tottofe ko'ina da sannan ya rungumeta sosai a jikinsa nunfashin su na sarke na juna. Kasa bacci tayi dan fargaban dake cike da zuciyarta, jikin ta duk ya mutu saida tajima kafin bacci ya kwasheta.
Jiki dayake ya saba tashi sallah asuba, abinda ya farkar da sufyan kenan, dan kuwa dukkansu bacci mai dadi sukayi Daren ranar "Ashe haka kwana da matarka a gefe keda dadi". Alwala ya cikin Sauri kafin ya matso kusa da ita yana hura mata iska a kunne, juyi tayi harda Jan bargo ita nan bacci dadi ,rike bargon yayi yana mai tattare mata gashin kanta daya barbazu.
Cikin idon da bacci bai isa ba ta turo baki a shagwabe tana Neman yimasa kuka dan jin yana fesa mata ruwan hannunsa a fuska "wai ke kuka baya miki wuya ko, koda yake na manta auta ce",
Maganarsa yasa tayi murmushi sannan ta miko masa hannu alamun ya daga ta dan har yanzu ita tana dingishi da kafarta.sai da ya rakata bayi tayi tsarki sannan suka dawo daki.
Ruwan dumi ya kawo mata a buta da dan roba tayi alwala, shiya jasu sallah sukayi, "ina kwana" ta fadi kanta na kasa.
"Kin tashi lafiya" ya fadi a takaice dan karatu yakeyi ta katse shi.
Mikewa tayi tana takawa a hankali ta haye gado tayi kwanciyarta dan bacci takeji sosai. Sai da rana ta fito yana zaune yana azkar sannan ya hau gefenta shima ya kwanta, basu suka farka ba sai karfe sha biyu a yanda sufyan ya kiyasta kenan.
Papa ne kawai a gida shi jass ya tafi makaranta ita kuma Camila taje kasuwa.sufyan ya zo ya zauna kusa dashi suka gaisa, papa yace "bari nakawo muku breakfast".
Sufyan ya dakatar dashi "bari na dauka papa basai ka tashi ba".
Fanke ne mai zafi sai kuma madarar shanu a kufi mai kyau. Daki ya kaima ta suka sha madaran tare dan ita tace bazata iya cin fanke ba sai anjima, sai da ya tabbatar taci sannan yace "ina ganin zan dan fita, ki zauna anan karkifita kinga ba hijjabi a nan, sai ko idan toilet zakije".
Raurau tayi da ido "amma bazaka Dade ba ko".
Gyada mata kai yayi sannan ya fita ya kullo mata kofan.
"Papa nace ko akwai wani abun dazan taimaka maka dashi".
Papa yayi murmushin jin dadi dan kuwa halayen sufyan Suna birgeshi yan kwanakin nan kawai da sukayi tare ya fahimci yaro ne mai hankali da natsuwa "basai kamin komai ba yarona, domin jiya na fitar da wasu kayan gona na nasiyar kuma ba karamin riba nasamu ba. Yanzu kabari jass yadawo sai rakaka cikin birni Ku siyo abunda zaku bukata kai da kanwarka na kayan amfani".
"Halayensu masu kyau kamar musulmai, insha'allahu sai ya janyo su daga bata zuwa shirya" to papa muna godiya sosai da sosai .
"Bakomai ai kunzama yarana".
Suna cikin magana jass ya dawo, dan haka suka dunguma zuwa birni Inda suka dunga keta daji nan dai Allah yasa suka sami mota . dayake papa ya basu kudi mai yawa dan haka duk siyayyan Mafi aksari nata ne, kaya ne dama riguna kanana da dogaye wanduna sabida sune kayan su a can sai turaruka da takalma da under wears, sai cosmetics Wanda yasan zata bukata, har pad saida ya siyanmata, shi kawai riguna yasiya da wando sai perfumes nashi, da soson wanka da takalmi.
Nan yaga wasu chocolate da biscuit ya siyan mata itada Camila. Sai yamma likis suka baro dan haka basu suka iso gidaba sai dare.
Ita daya a daki duk tsoro ya kamata dama Camila ta shigo kawo mata abinci dazun sunyi hira dan ta dan saki jikinta da ita ganin yarinyar Nada mutunci har tana cemata "tanaso suzama kawaye".
Murmushi safiyya tayi sannan ta mika Mata hannu suka gaisa alamun she is wlcm. To gashi kuma yanzu sun tafi wurin bauta itada papa. Ba tunanin da baizo mata ba. Shidinma ita ya dinga tunani yasan yanzu su papa sun tafi wurin bauta.
Suna isa jass ya wuce wurin bauta da sauri shikuma ya isa dakinsu. Ta hade kanta da gwiwa sai sharar kwalla take . jin anturo kofan yasata firgicewa zata mike , ajiyar zuciya tayi ganin Ashe ya sufyan ne.
Karasowa yayi yana girgiza mata kai, zama yayi gefenta ya zuba masa idanuwanta masu firgitashi ,sai da ya gama yanganshi sannan yace cikin damuwa "banace banason in kara ganin hawayen nan nakiba sofy".
Yadda ya kirata da sofy ya mata dadi har tana dan murmushi , a hankali ta sadda kai Kasa ta bude dan mitsitsin bakinta cikin shagwaba "to ba...ba sun tafi sun barni nikadai ba".
Mikewa yayi sannan ya kwaso kayayya kin daya siyo mata ya ajiye a gabanta "bari nayo alwala nayi sallah".
Bude ledojin tayi ta dinga Ciro kayayyakin cikin farin ciki, ita tamafi jin dadin gani undies din ,dama batada ko daya fadi tayi cikin ranta "ko ya akayi yasan size dina ohoo". Allah sarki bawan Allah sai hidima yake dani, nice daman ban fahimcesa ba, dama cwt safina tace sai na zauna dashi zansa ko shi wanene. jitayi ya kara samun wani matsayi a zuciyarta Wanda bazatace gashi ba.
Madara ta zuba masa a cup sannan ta yayyanka masa apple da inibi a plate ta ajiye. Yana shigowa ya zauna a gefenta , tura masa plate din tayi da madaran gabansa ya bisu da ido "Ashe ta damu da yunwar cikinsa", ba karamin dadi yaji ba.
Murmushi ya mata sannan ya dauki madaran yana sha a hankali , sai da ya sanye sannan yaci kayan marmarin.
"Ke kinci abincin kuwa sofy?".
Gyada masa kai tayi alamar eh sannan ta dan sakko daga kan gadon datake "nagode ya sufyan da kaya".
Harga Allah yaji dadin Abinda tayi , murmushinsa yayi mai ban sha'awa "sai kiyi manajinsu sofy kinga nan ba gidanmu bane, kiyi hakuri dasu kinji".
Gyada kai tayi "ai hakan ma sunyi Allah ya saka da alheri
" Kinyi wankanne "
"A ah jira nake kadawo,
Ruwan zafi ya juye mata sannan ya rakata har bayi ya jira tagama ta fito sannan shima ya shiga yayi.
Ko kafin yadawo ta shirya cikin wata Yar karamar Riga fara Sol jikin rigar net ne sai dan karamin wando shima Fari iya gwiwa. Sai kamshi take zubawa tana taje kanta. Kura mata ido yayi dan ba karamin tafiya da imaninsa tayi ba, ko'ina na jikinta ka kalla kasan ta amsa sunanta na cikakkiyar mace.
Cikin kasalar jiki data saukar mai ya karasa , ya zauna gefen gadon, kayan daya siyo musu ta jera a cikin wani akwatin karfe "akwai biscuit da chocolate ki dauka ki ajewa Camila nata".
Da Sauri ta bude ledan jin an anbaci abokinta wato chocolate. Hawowa gadon tayi tana tsotsa sai kallon dan mitsitsin bakinta yake. Kallonta kadai tayar masa da hankali yake kuma shi bayason wani lamari yashiga tsakaninsa da ita a garin daba nasu ba, amma anya zai iya daurewa kuwa?.
[3/8, 12:56 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<42>>```
Mikewa tayi bayan tagama shan chocolate din taje ta wanke bakin ta ,motsi taji a dakin kamar na bera, da dugu tayi wani tsalle ta fada kanshi akan gado.
Tambayan ta yayi murya can Kasa "sofy lafiya,menene kuma".
"Wallahi bera ne a dakin nan ko kandangare".
"Sai kuma suka zama abin tsoro, tunda ke komai tsoro ke baki".
Duk tabi ta wani kankame kamar zata shige jikinsa, kamshin jikinta ya saukar mai da kasala duk ta birkita masa lissafi,mirgino ta yayi Suna fuskartan juna ya na mata wani irin kallo Kasa Kasa, duk da ba wani haske bane a dakin dan kuwa torchlight ce Yar madaidaiciya amma tagane kallonta yake yana fitar da numfashi da Sauri da Sauri.
Tunaninta ne ya katse jin bakinsa cikin nata, wani salo ya fara mata mai wuyan fassara dakuma mance damuwa.sarrafa ta yake cikin dabara har ya rabata da Yar rigar jikinta, ta Kasa tabuka komai sai kawai bugun kirjinta kakeji da numfashi.
Sun dade a cikin wannan yanayi yana jagwalgwalata son ranshi har saida ya samu natsuwa sannan,babu wani Abu daya shiga tsakaninsu inbada haka, rungumeta yayi sosai ya zagaye hannunsa a kirjinta gashi ba Riga jikinta haka bacci mai dadi ya daukeshi.
Lamo tayi tana sauke ajiyar zuciya lokaci lokaci, murmushi ta tsinci kanta dayi Wanda batason dalili ba kuma ta tsinci kanta da jin kunyarsa "dama akwai ranar da zata zo da zata kwanta a fadadden kirjin ya sufyan?",
Daga idonuwanta tayi tana kallonsa , jin wani Abu take yana zirgan mata,gaskiya ya sufyan namiji ne ,kalli muscles din hannunsa murtuka murtuka, gashin kanshi sai kamshi yakeyi,kai duk macen data samo miji irinsa ta more ,ga kyawun jiki gana hali. Haka Takara cusa kanta cikn kirjinsa tana sakar kamshin sa mai sanyi tare da tuno abinda ya faru tsakaninsu har bacci mai dadi ya dauketa, motsi kadan tayi cai ya kara kankameta.
Wanshekare da safe da kyar take iya daga ido ta kallesa dan duk nauyinsa takeji, ya kula da haka amma sai yayi fuska. Ko lokacin da tagaishe shi idonta a Kasa , amsawa yayi cikin murmushi a zuciyarsa yana fadin "shifa mutun ne ba dutse ba, kuma balle yanzu dayake wuni da ita yake kwana, ai ko ba matarsa bace bazai yiwu ya iya daurewa ba ,balle kuma matarsa ce, mace kaman sofy".
Sajensa ya shafa yana murmushin da shi kadai ya San nufinsa dan kuwa yanajin yarinyar har cikin ransa.
Yauma haka yayi kamar yadda yasaba, baya barin Inda yayi sallah sai rana ta fito. Koda ya koma kan gadon rungumota yayi sukayi baccinsu.
Da rana bayan sungama cin abinci safiyya tabawa Camila chocolate din da ya sufyan ya siyo musu, sai murna take lokacin Suna zaune gefen bishiya Suna hira, shikuma sufyan yana wurin papa da jass yanata musu wa'azi akan menene musulunci da fa'idojinsa. Sai anyi la'sar yake barin wurin sai yabi papa gona daga nan yake taho mata da fruits da kuma madarar shanu dayazama Abincinta na koda yaushe.
Yanzu kimani sati hudu kenan wato wata daya su sufyan Suna kauyen su papa,yayin da safiyya ta saki jikinta da su,tsakaninta da sufyan kuwa wata shakuwa ce ta shiga tsakaninsu ,Wanda baya iya zama bai ganta ba, itama Idan yabi papa gona to tadinga damuwa kenan duk da Camila na debe mata kewa. Inko yana gida to tana kusa dashi kodaba hira suke ba. Abinda ke damunta daya game dashi shine "kullum kafin su kwanta sai ya gama jagwalgwla har yasamu natsuwa, kuma ya kan dauki lokaci mai tsawo a hakan, sai ya gama tayar mata da hankali da salonsa kuma sai ya kyaleta.ko menene nufinsa ohoo Ta rasa yadda zatayi, ai ko ba komai ita mutun ce kamar kowa kuma mai sha'awa ya kama inyasan haka zai dinga mata to ya kyaleta dan kuwa ciwon ciki kullum na matsa mata".
A hakan suka cinye watanni biyu, itada bata ciwon ciki na period amma gashi watan nan saida tayi kuma taci wahala dan shima ya tausaya mata kuma tasan duk shi ya janyo mata,
bayan kwana uku ta warke dan haka ranar ta dauki aniyar bazata bari ya tabata ba, sun dawo daga gona kenan shida papa, ya shiga yayi wanka yayi sallah , kan shi sai sheki yakeyi , tun kan ya shigo kamshinsa ya iso gareta.
Zama yayi gefenta hade da fadin "ya salam" alamun gajiya,
"Sannu da zuwa"
"Yawwa sofy ya cikin naki?".
"Ai naj sauki, ya gajiya".
Ruwa ta je ta kawo masa da madara ya karba ya sha sannan ta jujjuye abubuwan daya kawo dan yau harda naman kaza daya wa,a plate tasa musu sukaci tare.
Tana gamawa ta je yi brush ta haye gado abinta, doguwar rigace iya gwiwa yellow irin mai igiyan nan a tsakiya ce a jikinta. Harda Jan bargo wai ita alamun bacci zatayi.
Saida yagama abinda yakeyi sannan ya matsa gareta, riko hannunta yayi yana murza zoben daya siyo mata rannan,shiru tayi tanajinsa , juyo da ita yayi Suna fuskantar juna, idanunsa sun kankance, da Sauri ta janye jikinta ta matsa can, tana kokarin kara rufa da blanket.
Mirginowa yayi ya rungumeta tanajin saukan numfshinsa a wuyan ta, kiss ya sake mata a wuya ,cikin muryar wadda ya gama kashewa jiki tace "ya sufyan plsss..."
Shiru ya mata dan yagane nufinta na ya kyaleta, hannunsu ya hade waje daya da fuskarsa dan har hancinsu na gogan na juna, ji yakeye wani abu na fizgarsa game da ita , ko shine so din ohoo? Shi dai yasan kullun tunanita na zuciyarsa domin ta mamaye masa ko'ina.
sai da ya gama Jan ajinsa sannan yace " kiyi hakuri kinji"
Furzar da iska yayi ya juya ya kwanta
Hawaye ne ya zubo mata a fuska a ranta tace "nikuma sai indinga cutuwa akanka ya sufyan".
Juyowa yayi jinta shiru bata kwanta ba, hawaye ya gani nabin kuncinta ,Goge mata hawayen yayi yana girgiza mata kai, janta yayi suka kwanta batare daya mata komai ba, amma tanajinsa sai juyi yake alamun ya Kasa bacci.
Bayadda ta iya, batason mai yasa ba sai kuma taji ya bata tausayi kuma batason baccin ransa, dan haka ba yadda zatayi sai tayita hakuri tunda batasan nufinsa na kin kasancewa da ita ba.
Matsawa tayi ta shige jikinsa, bude idonsa yayi da sukayi kanana yana kallon ta ta kasan ido , batare da ta dago ido ba tace "I am sorry..."
Ba karamin birgesa tayi ba, jiyayi kawai wani sabon sont na shigarsa. Murmushi yayi hade da shafan libs dinta dasuke jaa..
[3/8, 12:58 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<43>>```
Sadda kanta tayi Kasa tana jinsa, ranar ya jata kirjinsa ta kwanta lamo anan bacci yayi awon gaba dasu batare daya mata komai ba.
Wanshekare a safiyar laraba, safiyya na sanye da wata goguwar Riga lemon green wadda ta tattare daga samanta kasan kuma ya bude yafa dankwalin rigar a kanta, hoda tasaka da lip gloss tasaka dan kunne ta fesa turare tayi kyau sosai.
Camila ta kalleta cikin murmushi "kai frnd,ke da yayanki kunada kyau, kun huta abinku".
Dariya taba wa sofy, Camila tace "ki tambayi yayanki yau mufita tare dake kiga gari".
Murna safiyya tahau yi dan dama tagaji dazama wuri daya, fitowa sukayi suka nufesu papa da suke zaune tareda sufyan yanata musu wa'azin daya saba kullum , safiyya ta duka ta gaida papa sannan ta kalli ya sufyan daya zuba mata kyawawan idanu wansa "Camila tace zata kaini muga gari".
Shiru yayi na yan seconds, Inda sabo ta saba da yangar nan tasa Wanda tazame masa jiki " haka zaki tafi ba hijjabi".
Sadda kai tayi Kasa dan ita kanta tasan bai dace tafita haka ba, da karamin mayafi, "ki bari anjima da yamma sai na rakaku muje tare. Mikewa tayi tabar wajen sannan ta Sanar da Camila abinda yace.
Da yamma da kanshi ya rakata bayan ya bata wani babban mayafi yace ta rufe jikinta dashi, haka suka dinga tafiya shi yana daga bayansu, Camila na nuna mata gonaki da tekuna. Iska mai dadi sai shigarta yakeyi, tunowa tayi da cwt safina "Allah sarki cwt kota haihu ohho,Allah ya sa da haduwarmu anan gaba".
Ba wasu mutane dayawa sai dai-dai ku , sai kuma manoma dasuketa aiki a gonarsu, wasu insunzo gittawa suyita kallon sofy da shi ganin ba irin fatarsu ba , wani manomi haka ya dinga binsu da ido har suka wuce.
Gaf da sallahr magrib suka dawo dukkansu cikin nishadi, alwala sukayi ya jasu sallah, yayinda su papa sukayi shirin fita.
Dama ace yanada abubuwan dazai aiwatar ko akwai system dinsa ko waya ,daa bazai dinga zama shiru yana yawan kallonta ba, to rashin aikin yi, Shiba karatu ba, sai dai yayita azkar a zuciya, ko kallon nata kadai ya isa yadinga jin sha'awarta, dawowa tayi daga wanka daure da towel tunda tasan ba kowa a gidan. Yana kishingide Kansa akan katifar jikinsa kuma a Kasa yana kallonta amma ita a ganinta idonsa a rufe yake sabida yadda ya dan lumshesu ,shiyasa tata zauna ta shafa mayukanta da turaruka masu kamshi dan yawanci ba'a gabansa take shirya wa ba yakan fita saita gama.
Rigarta tasa mai santsi red colour mai stones ajiki Wanda ta sauka har gwiwarta, ta taje kanta ta bazashi a bayanta ,tazamo kamar balarabiya, kullum kara kwanta masa a rai take kuma kowani lokaci tayi kwalliya kara birgeshi take kuma sonta na ninninkuwa a zuciyarsa amma yanzu tunaninsa daya "yaushe zata so shi?". Dan shidai bazaice tana sonshi ba amma kuma yasan ta damu dashi, dole yasan yadda zaiyi ya koya mata yadda zata soshi, tun tana karama yake dawainiya da soyayyarta a zuciya kuma bai taba ji a zuciyarsa ya tsane ta ba dai dai da second daya, abubuwan daya mata abaya ma shi kawai yayi mata ne ganin abinda ta mishi tun farko amma shikanshi yasan yana son sofy da duk wani Abu daya shafeta.
Tana gamawa ta isa kusa dashi "ya sufyan! Ya sufyan!!".
Bude idonsa yayi ya zuba mata hade da daga mata gira alamun menene
A dan daburce a dalilin kallon dayake mata tace "nagane kafara bacci a Kasa".
Jawota yayi ta fado jikinsa yana shakar kamshinta mai dadi ,shiru sukayi dukkan su kowa da abinda ke masa yawo cikin jiki, "itafa yanzu tsoronsa take domin inya sameta kamar zaki yasamu nama, duk da ba abinda ke gittawa tsakaninsu sabanin haka amma tana shan wuya dan kuwa duk jiKinta sai yasan ta jagwalgwalu hannunsa. Daukanta yayi suka kwanta akan katifar ya kwanto ta jikinsa yana shakar kamshin dake fita a gashinta, jin ya zamiye rigar ta dake jiki ta numfashinta ya fara sama sama dan tasan sauran zancen.
Sarki ya kalli jama'ar dake gefensa da kuma wadanda suke jagaye da wutan dake ci anata wake wake. Daya daga cikin fadawansa ya aika cewan ya kira papa yace yana nemansa. Tahowa sukayi shida jass sannan suka tsugunna suka gaida shi jiki na bari sabida sanin halin sarkin na zalunci da mugunta,
"Dakanka papa za'a hade kai a munafinceni"
Papa jiki na bari yace "my Lord, bangane maganar naka ba.
Sarki camara ya kara tamke fuska "kasan dokar kauyen nan, na in anyi baki da ba yan gari ba sai ankawosu fada mun gansu".
Kirjinsu ne ya buga da karfi cikin firgicin abinda zai biyo baya," tsoronsu daya sarki camara yagane ba addininsa sufyan suke biba, kuma gasu ba yan Kasa ba",
Cigaba yayi da fadin "sai dazun ne ake kawomin rahoto cewa anga wasu baki Suna yawo a garinan kuma tare da danka jass aka gansu,dan haka gobe inaso katahomin dasu nan da rana".
Jiki na rawa suka amsa da "to angama my lord".
Barin wurin sukayi sannan suka matsa kusa da gimbiya sirenah ('ya daya tilo wajen sarki camara,kuma Yar lele) suka tsugunna suka gaisheta suka wuce.
Dukkansu su ukun cikin rudu da tashin hankali ranar suka dawo gida. Wanshekare da safe ne papa ya kira sufyan ya gaya musu abinda sarki yace ,yakara da "mugune kuma azzalumi bashida tausayi shida 'yarsa. Abinda sukeso shi sukeyi, tunda matarshi ta mutu bai karayin aure ba ,sai dai inyaga matarka tamishi sai akai masa ita tayi kwana biyu wurinsa, ita kuwa yarinyar tana gidan tazama itake juya kowa, tsoro Nike kar ya kashe Ku, dan ba karamin aikinshi bane".
Murmushi sufyan yayi "karku damu papa Allah yana tare damu, insha,allahu ba abinda zai samemu",
Safiyya dai gabanta sai faduwa yakeyi , Camila kuwa harda kukanta dan ba karamin shakuwa sukayi da su ba.
Kai tsaye jass da papa suka tasa sufyan da sofy (wacce ta lullube jikinta da mayafi duka) har fadan sarki camara...
[3/8, 12:59 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<44>>```
Har cikin fadan sarki a kaisu, su papa suka zube Suna gaishe shi,amma sufyan Suna tsaye ya rike hannun safiyya katam.
Kallo kowa ya bisu dashi na mamakin yadda basu duka ba. Sarki camara yayi gyran murya "kai marasa kunya ya sunanku kuma daga ina kuke".
Sufyan a dake ya amsa masa "sunna sufyan sai kuma wannan kanwata safiyya , kuma mu ba anan kasar muke ba, plane crash muka samu a hanyar mu tazuwa wata Kasa shine muke nan".
Safiyya wani kololon bakin ciki taji yana taso mata ganin yadda gimbiya serinah ta tsare sufyan da ido
"Meyasa bama ganinku wurin bauta kullum?".
"Sabida mu abun bautarmu shine Allah ubangijin kowa".
Sarki ya mike daga zaunan da yake a firgice "muzaka nunama rashin kunya zakazo mana dawani sabon addini"
Umarni yabada cewan a wuce da sufyan prison ita kuma safiyya a kaita dakin cikin gidansa a kulleta. Sufyan na jin haka ya kara rike safiyya gam wadda jikknta ya soma rawa.
Gardawa guda uku sukazo Suna kokawon rabasu. Gimbiya ta dakatar dasu ,sannan ta matsa ta yiwa babanta magana kunne. Murmishi yayi sannan ya juya yamusu umarni dasu wuce da sufyan dakin gimbiya.
Sunaji Suna gani aka wuce da kowannensu.gimbiya da tunda taga sufyan taji soyayyar shi na azazzalarta, ta mike ta nufi daki tayi wanka tasa ke gayu dan ba laifi fara ce amma doguwa siririya.
Sufyan tunda aka kaishi dakin aka kulle ya rasa mai ke masa dadi ,addu'oi ya dinga ma sofy akan Allah ya kareta daga sharrin sarki, dan tunowa da zancen da papa ya mishi "Indai yaga matarka ta mishi kyau zai bada umarnin adauko mishi ita suyi kwana biyu".
Idanunsa sun kada sunyi jajir , ya fesar da iska mai zafi.
Jin tafiya yayi kamar a bayansa, yana juyowa ya ganta taci kwalliya tana murmushi, kauda Kansa yayi daga kallonta ita kuma tasamu waje a gefensa ta zauna "sannu ko"
Banza yayi mata dan ji yake kamar ya shaqeta ." dama nacene a turo min kai nan sabida tunda na ganka naji inasoka , kuma kamin, dan haka zaka cigaba dazama anan har ranar da za ayi bikinmu nida kai".
Aiko ta hadu da dan yanga ,ko dagowa baiyiba balle yasan tana magana, ganin bashi da niyyar amsa ta tasa ta mike tana rangwada tabar wajen.
Tana fita aka dinga shigo masa da kayan abinci iri iri, ko kallonsu bai yiba kawai ya mike ya shiga toilet dan yo alwala.
Papa kuwa tunda suka koma suketa shawarar yadda zasuyi su kubutar dasu. "Hanya dayace papa. Ta hannun wazirin sarki abokina". Cewar jass
Papa ya mike cikin farin ciki yace "kabari anjima sai muje musameshi in munje wajen bauta. Haka kuwa akayi, da daddare jass dasuke fada ya samu waziri abokinsa ya gaya masa duk abinda ke faruwa.
Dashike shima waziri yasan halin sarki tass na zalunci dan wasu abubuwan ma shike gayawasu jass inya faru. "Karku damu jass ,yanzu bari naje dakin gimbiya inyi magana da sufyan din dannasan bata ciki tana nan wajen.
Waziri dakanshi ya nufi sashen gimbiya , ba'a hanashi shiga ba sabida ansa shi wanene a fada. Zaune ya samu sufyan yayi shiru idanunsa a lumshe. Karasawa yayi ya dafa kafadarsa da Sauri sufyan ya bude ido dan a tunaninsa gimbiya ce.
Waziri yayi masa murmushi sannan yayi masa bayanin ko shi waye "tashigo wurinka kuwa ,kuma metace maka?".
Sufyan yayi ajiyar zuciya "please ka je ka dauko min sister na kar wani Abu ya sameta".
"Karka damu zanje wurinta kuma babu abinda zai faru da ita"
Nan sufyan ya danji zuciyarshi ta kwanta "eh tazo wai tana sona kuma zata aureni".
Waziri yayi dariya "Kasan yadda zamu tsara komai, anjima inta shigo kace mata ka yadda kanasonta, to ta hakanne zamu tsara yadda komai zai tafi".
Sufyan ya gyada kai sannan waziri ya fita, kai tsaye wajen sarki yaje ya mika gaisuwarshi sannan ya zauna gefensa " my lord naji ance wasu baki ankawosu mace da namiji sun maka taurin kai ko".
Sarki ya fashe da dariya ya kurba giyar dake hannunsa "ai nasa an kama munsu shida kanwar tasa Mara sa ji".
Waziri shima ya fashe da dariya" kace sarki akwai nama kenan".
"Ai gaskiya yarinyar nada kyau, inka ganta kamar ba mutum ba , jikinta sumul".
Waziri ya gyra zama yace "amma sarki karka ji gaggawa, kasan bamusan was irin mutane bane su, kabarta a kulle har sai nan da sati biyu mugani".
Sarki ya zaro ido "kumafa maganar ka gaskiya ne waziri, to bari na kyaleta har sai mungani tukun kuma ta kara sake jikinta".
Waziri ya yi dariya "ai kamarka sarki ba yarinya ko matar dazata k'ika".
Sarki ya fashe da dariya shikuma waziri sai yabonsa yakeyi.
0 comments:
Post a Comment