Koda dare tayi gimbiya ta zo gurin sufyan, tayi mamakin ganin fuskarsa a sake, dan haka ta zuba mishi ido tana murmushi "Kanada kyau sosai , i luv yhu so much".
Murmushin sa mai kyau ya mata hannuwansa harde a kirjinsa "luv yhu too dear".
Ai gimbiya najin haka taji kaman ta Fasa ihu Don dadi, da gudu taje ta rungumesa dan farin ciki, janye ta yayi daga jikinsa , kallonsa tayi "to naga bakaci komai ba a cikin abubuwan da aka kawo maka".
Dan yatsina fuska yayi yace a hankali "banajin yunwa ne amma karki damu zanci".
Nan ta zauna tana mishi hira har dare yayi sosai sannan ta wuce dakin baccinta,shikuwa daurewa yakeyi dan ba yaddda ya iya ,tunanin sofy ne fal a zuciyarsa, inya rufe ido ma ita yake gani.
Safiyya tunda aka kaita dakin a kulle babu mai waiwayensa sai masu kawo mata abinci, tayi kuka har idonta sun kumbura ta tausayawa kanta da irin wannan jarabawa da suke ciki. Ranar tayi kukan rashin umma har ta bawa uku lada.
Yayinda gimbiya take kashewa sufyan kudi, dan kullum sai sun fita wajen gari da shi shan iska, kayan dayake sawa kuwa duk masu tsada ne.ita dai burinta ta aureshi su kasance tare.
_Gombe_
Ranar asabar da misalin karfe goma na safe safina ta haifi yarta mace a asibitinsu safwan, murna a fada ba'a magana, kowa sai farin cikin saukanta lafiya yakeyi musamman Khalil.
Kai tsaye gida suka dawo ,yan barka sai shigo wa suke ,mai jego tayi fess abinta.
Umma ta mikawa safina yarinyar "asheta ki bata tasha ko auta".
Safina tayi murmushi sannan ta anshi baby" kura mata ido tayi ganin yadda tayi mugun kama da cwt safiyya, hawaye kawai taji yana bin kuncinta ,Allah sarki cwt Allah ya muku rahama gashi yanzu har sun shiga wata na bakwai knn".
Umma ta kalleta cikin kulawa "auta lafiya kike hawaye ko duk murna ne".
Girgiza kai tayi "umma murna nake yau gashi Allah ya sa na haifi safiyya".
Umma tayi murmushin jindadi "to auta Allah ya jikansu ,ita kuma wannan Allah ya rayamana ita rayuwa mai albarka.
Koda Khalil yazo safina tace masa ga sunan datakeso baiyi musu ba, sai ma farin ciki dayaji kuma ya musu addu'a.
Amira dayake tana waec ne yanzu karatu yayi zafi sai can yamma ta dawo. Koda taji sunan antyn ta akasa ranar taci kuka rungume da yarinyar dake mugun kama da safiyya.
Ranar Suna yarinya tayi goshi dan kuwa ankashe kudi kuma tasamu kyaututtuka iri iri. Yayinda safwan yanzu hannunsa ya fara aiki dan kuwa ya ji sauki dan kuwa ana gama Suna suka koma gidansu.ita kuma safina ta cigaba da wanka gidan Momy ita da lil sofy.
_kauyen su papa_
Ana gobe su su sufyan zasu cika sati biyu tun safe waziri yace ya shirya yau cikin dare zasu gudanar da komai. Sufyan da ya samu kudi sosai wurin gimbiya ya Tara dan ba karamin kudi take bashi ba.
Waziri ya je yagayawa su papa cewan yau yakeso ya kubutar da su sufyan dan haka su tsaya ta wajen gari su jira su.
Sarki camara sai washe baki yake yau zai kasance da sofy, sabida kullum sha'awarta kara ninkuwa takeyi a ransa. Da daddare yasa aka hada juice ya zuba maganin bacci yasa a ka kai ma ta har daki.
Waziri dama yana labe a gefen dakin sarki dan haka ana zuwa aka kaimata shikuma ya shiga ta toilet din baya ya sameta.
Safiyya data ganshi jikinta ya hau rawa tafara ja da baya tana gwalo ido "ba cutar dake zanyi ba , taimakon ki zanyi keda dan uwanki, anjima zan shigo intafi dake dan haka kizauna cikin shiri .
Daukan juice din yayi ya fita dashi dan lokacin duk ana wurin bauta ba kowa. Dakin da sufyan yake ya shiga ya bashi juice din yace "gashi nan, in gimbiya tazo kabata tasha, daganan sai kajira bacci ya dauketa dan kuwa sarki yasa maganin bacci aciki dan kanwarka tashi yayi Mata fyade ne".
"Bayan tayi bacci nikuma zan zo da safiyya sai ta cire kayanta a sawa gimbiya, na gimbiya kuma asamata".
Sufyan farin ciki ya lullube zuciyarsa ya fara yiwa waziri godiya
"Karka damu nayiwa kanina magana shi zai kaiku airport a mota ,jirgin Ku zai dagane da asuba zuwa Nigeria.
Su sarki ana can wajen bauta shida gimbiya , sufyan ya fita yace ma wani bafade daya kira masa gimbiya ,dayake kowa yasan sufyan shine saurayinta a fada shiyasa da Sauri yaje hagaya mata.
Cikin dakin ta shigo tana karairaya, murmushi Yamata sannan ta zauna kusa dashi hannunta a kafadarshi dan ita yanzu tagama mutuwa kan sufyan,
Dauko jiuce din yayi cup ya mika mata . ansha tayi ta fara sha harda lumshe ido, hira ya cigaba da Mata mai dadi , kafin kace me! Ta bingire tanata bacci.
Da Sauri shikuma waziri yaje ya dauko safiyya suka fito sukazo dakin. Tana ganin ya sufyan taje da gudu ta rungumeshi tana kuka, shafa kanta ya dinga har tayi shiru.
Falo suka koma suka umarci safiyya data cire kayanta tasawa gimbiya ita kuma tasa nata. Cikin hanzari tayi hakan , dayake doguwar rigace mai hula ,dan haka ta saka dan baka iya ganin fuskarta .
Kudi dayawa sufyan ya kwasa , waziri ga dauki gimbiya ya kaita dakin da aka aje sofy shikuma ya fito dasu sufyan ta wata kofa ya sada su da kaninnsa a mota domin ya kaisu su yi sallama da su papa a wajen gari kafin su tafi airport
Samun su papa sukayi sunyi jugum jugum, Camila Naganin sofy suka rungume juna sunata kuka. Jass ma yana ta hawaye , sufyan ya kalli papa "da ikon Allah watarana zndawo gareku , in saka muku da Mafi abinda kukamin".
Papa ya goge hawayensa suka rungume juna. Haka Suna dagawa juna hannu suka shiga Motan kanin waziri ya wuce dasu airport...
[3/8, 1:00 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<47>>```
Safiyya ta mike da Sauri ta nufi umma ta rungumeta hawaye na bin idanuwanta,umma ta runtse ido tana fadin "innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Safina tayi taku daya biyu ta karisa gun sufyan tana tattaba jikinsa tana zaro ido, kuka ne yaci karfinta ta rungumesa "ya sufyan kai nake gani ko mafarki nake".
Dady ne da mai martaba suka shigo cikin Sauri sabida Anty Amina ta kirasu a waya.
Sufyan ya matsa kusa da dady wan da farin ciki sa ya Kasa boyuwa.
Mai martaba yace kowa ya shiga ciki,Momy inna suka kama aka kaita falon sarki. Ruwa aka dauko aka yayyafa mata , a hankali take bude ido lokacin safwan da Amira suma suka shigo a birkice jin labarin su sufyan sun dawo.
Safiyya dai na makale da umma, sai hawaye umma ke zubawa tana hamdala,
"Ku kuma sufyan haka Allah ya kaddara muku, to Allah mungode maka".Cewar mai martaba daya Kasa tsaye ya Kasa zaune
Safwan ya isa gaban sufyan yana tattaba fuskarsa ya na surutai, dady yazo ya jashi suka zauna "safwan ka kwantar da hankalinka, dan uwanka ne kake gani ba mafarki ba".
Amira kuwa da gudu ta karaso ta zube a jikin safiyya ta rukunkumeta tana kukan dadi, safina ma ta karaso sukayi ta kuka, a hankali Momy ta bude ido tana kallan kowa daya bayan daya,
Kaman an tsikareta ta mike da Sauri ta ja jikinta zuwa gaban safiyya tana shafan kanta, yafito sufyan tayi da hannu alamun ya tago, zuwa yayi ta kwantar dasu a kirjin ta tana kuka , kowa a dakin sai hamdala ya keyi, sai kiran 'yan Uwa Anty Amina keyi tana Sanar dasu
"Wallahi kullum jinake a jikina kaman basu mutuba zasu dawo gareni, Allah sarki ,ubangiji nagode maka". Momy ta fadi tana share hawayen dake gangaro mata.
Mai martaba yayi gyran murya sannan yayi ma kowa sallama, bayan haka yayima Allah godiya daya dawo musu dasu sufyan cikin koshin lafiya,"to kai sufyanu ya akayi ne hakan ta faru".
Sadda kai yayi yana murmushi sannan ya bawa mutanen dake fada labarin yanda jirgin yayi hatsari suka fada gonar papa da taimakon daya musu".
"Ikon Allah kenan, lallai Allah ya somu da rahama, Allah mungode maka", Cewar umma da itama takasa boye matsanancin murnan datake ciki.
Haka taron ya tashi kowa farin ciki kamar ya zuba ruwa a Kasa ya sha.
A falon umma, Amira na jikin safiyya ta kankameta kamar jaririya, sai safina kusa da ita "Allah sarki cwt, kin haihu bana nan".
Safina ta dan harareta "ni da akacemin kintafi murna nayi ,na huta da surutun ki".
Amira tayi craf "ai Anty bari kiji, Anty safina kullum kuka intazo gidan nan, ranar da Akace mana kun mutu sumanta bakwai".
Safiyya ta fashe da dariya tana jijjiga lil sofy dake kuka a hannunta.
Anty Amina ta kariso dauke da plates din abinci kala kala ta aje a gabansu "to mukuma yaufa ba bacci auta ta dawo".
Safiyya ta kalli Anty "kai Anty ke sumanki nawa da akace miki na mutu".
"A ah ni ai nafi damuwa da ya sufyan, kedai dama ta Momy ce".
Khalil ne ya bankado ba ko sallama "ina autar take ,ooh munaga rasulu! Wai mai gari da kukan aski!. Da gaske safiyya ke nake gani bayan muncire rai daku".
Dariya ta kwacewa safiyya hadi dan goge hawayen daya zubo mata " yaya nice ".
Mika mata hannu yayi yadda yasaba in zasu gaisa, ta mika mishi nata itama tana dariya "kai ba Inda ya gida dadi kuma cikin yan uwanka".
Nan suka dinga hira Suna kwasar dariya , mutane kuma nata shigo wa dan kuwa labari ya baza gari Cewar su sufyan yaran sarki sun dawo.
Shikuwa sufyan yana tare da safwan Inda aketa musu jaje amma zuciyarsa na gun sofy. Yasan dai yau bazaiji dumin jikin matatshi ba, lumshe ido yayi dalilin tunota dayayi...
Ranar haka kowa kwana cikin farin ciki. Raba dare sukayi safiyya nabasu labarin kauyen su papa.
Da kyar umma ta tilasta musu suka kwanta.wanshekare kuwa da safe Suna gama breakfast suka dunguma gidan Momy, safiyya na rungume da lil sofy a hannu.
Momy ta rasa Inda zatasa safiyya, daga ta dauko wannan ta bata sai ta dauko wannan ta bata. Suna zaune sai ga sufyan ya shigo, safiyya ta dan kallesa , Sanye yake da Riga baka da wando jeans, kannan sajen fuskarsa yasha gyra ba kaman yadda suka dawo jiya ba,
Gaishe shi sukayi snnan ya karasa wajen Momy Wanda take ta zuba murmushi. "Wai ni auta ina Yar dakika Haifa ne, ba kikawomin ita ba". Sufyan ya fadi yana kallonta
Momy tayi dariya "ina zata tuna dakai bancin Aminiyar ta tadawo".
Safina tayi dariya sannan ta anshi baby ta mika mishi "ya sunanta?".
"Sunan matarka taci" inji Momy
Murmushi ne mai kyau ya subuce masa jin sunan yarinyar, dama gata kamarta daya da safiyya, sai yaji yarinyar ta shiga ranshi, kuma yaji shima dama tashi ce dan kuwa yanason kananan yara sufyan, to amma yanzu da sofy ta dawo cikin dangi zata yarda dashi kuwa?.
[3/8, 1:01 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<48>>```
Safina ta kalli safiyya cikin zolaya tace "wai ke matar yaya bawani baya ni ne, shiru dai".
Safiyya ta ja mata kunne "ke wallahi ki kiyayenifa, kindai San yanzu antyn ki ce tom".
Safina ta fashe da dariya."wai ni wallahi hankalina na kan makaranta".
"Kar ki damu mai martaba zai musu magana tunda munkusa gama, ai kaddara ce ta fado muku".
_kauyen su papa_
Sarki camara ana gama bauta ya wuce dakin da yasa aka aje masa safiyya, murna ya dinga yi ganin tayi bacci . kashe bulbs din dakin yayi sannan ya afkama 'Yar shi bada sanin ita din bace.
Sai da yagama abinda zaiyi da ita sannan ta fara motsi, lokacin yana saka wandonshi, dayake darene kuma ba haske , ihu ta kwarma "daddy".
Jin muryar 'yarsa yasanya shi kunna wuta da Sauri yana dube dube, kallonta yakeyi ido waje.
Kuka ta Sanya tana mai dudduba jikinta, jikinsa ne ya hau rawa "se...seri...serinah".
Daura hannu yayi akai ya isa kusa da ita shima yana kuka, tureshi tayi ta Sanya kayanta da kyar ta ja jiki ta nufi dakinta tana kuka, yayinda sarki ya bazama Neman su safiyya zuciyarsa na tafasa "wato shi zasu rainama wayyo su sashi ya lalata 'yarsa daya tilo, aikuwa duk inda suke a garin nan sai an nemo su".
Koda aka kirayi su papa Sumu suka rantse basu San Inda sukeba , hura hanci ya hau yi "wato sun gudu ko, to duk Inda suke basu tsira ba".
****
Tunda safiyya tayi kwanan farko a gidan umma bata kara kwana gidanba, kullum Suna tare da safina a gidan Momy, sai dai da safe takan leka dan kuwa Momy ta riketa , duk gyran da akewa safina na jego itama Momy na mata.
Kimanin kwana hudu kenan yanzu da dawowansu, tana zaune rike da lil sofy a kan cinyarta ta jingina da kujera kanta na kallon sama ta murmushi ita daya , tunanin sa take dan kuwa kwana biyu kenan bata sashi a ido ba, kuma taji kaman Momy tace wai sunje Kaduna wurin aikinsa shida safwan, tuno irin salon soyayyar shi dayake nunamata a tibilis tayi, lumshe idanuwanta tayi tanajin wani yanayi a cikin jikinta Wanda sai in Suna tare take yawan jinsa, ji tayi tanason shakar kamshinsa mai dadi.
Ta jima a haka kafin taji mararta ta wani kulle, dafe cikinta tayi "oouuch!!".
Kirjinta ne ya buga sabida tuno da kwanan wata yau "na shiga aljanna!".
Dan kuwa ta San yau ba bacci sabida ciwon Mara.
Zuwa tayi ta kwantar da lil sofy a gefen safina dake bacci a bedroom din Momy.
Ji tayi ciwon da karuwa kamar ana niqa mata kayan cikinta. Komawa tayi falo da Sauri, cin birki tayi dalilin jirin dataji yana dibanta, durqusawa tayi tana fadin "innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Washh Allah!".
Murqususu ta shiga yi a Kasa tana salati, Momy ce ta karaso da Sauri tana fadin" subuhanallahi, auta maiyafaru, innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Tallabota tayi ganin bata motsi, da Sauri ta fita tana kwalawa driver kir cewan ya fito da mota su je asibiti.
Cikin minti biyar suka isa cikin asibitin, daukanta akayi a wheel chair aka wuce da ita a sume, Momy data rasa menene babu irin tunanin da baizo mata ba.
Minti sha biyar suka dauka sai ga likita ya fito daga dakin da aka shiga da safiyya , da Sauri ta isa gareshi "Dr meke damunta, ta farka kuwa?".
Dr saddiq ya kalleta cikin kulawa "karki damu hajiya bacci takeyi yanzu, kibiyoni office dina".
Yana shiga Momy itama ta samu wuri ta zauna tana mai sauke ajiyar zuciya jincewa tasamu bacci.
Cire gilashin fuskarsa yayi "dama bawata Matsala bace, ciwon Mara ne na period,kuma dama wash Matan yakan zo musu a haka, sai dai shan magani, amma gaskiya ita nata yayi yawa tunda gashi harda suma , dan haka da da dama kuyi mata aure kawai ,domin intayi aure zata samu sassauci koma ta daina gabadaya".
Momy da tunda Dr ya fara maganarsa tunaninta ya tsaya cak" aure kuma na yaushe, to meke faruwa ne, nufinshi safiyya har yanzu ba abinda ya shiga tsakaninta da sufyan?shekara biyu kenan!! Lallai da magana akasa, to meke tsakaninsu, inko shine da laifi wallahi sai ta dauki mataki mai tsauri akanshi dan kuwa ya cuci yarinya kuma ya dauki alhakinta , to kodai basuda lafiya ne suka 'ki fadi?".
Dr ne ya katse mata tunanin datake "yanzu inta tashi zatasha magani, jikin inyayi sauki zuwa dare zamu sallameta".
"To Mungode Dr, bari naje gunta".
Tana kwance tana bacci mommy ta ja kujera ta zauna kwakwalwarta a ya mutse "bari ta farka naji daga bakinta"...
[3/8, 1:02 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<49>>```
Baccin awa biyu safiyya tayi kamun ta farka, Momy tagani zaune gefenta ta rafka uban tagumi, kokarin mikewa ta farayi nanne Momy ta juyo ta taso da Sauri tana mata sannu "kin tashi Ashe auta, sannu kinji, bari na hado miki tea kisha".
Safiyya dai kanta akasa dan kuwa kunya taji takamata, Momy ta kawo mata roba ta kuskure bakinta sannan ta hada mata shayi ta sha.
Maganinta ta ballo mata ta bata ta sha sannan ta jingina mata pillow ta kishingida. Zama tayi a gefenta ta zuba mata ido kamin ta nisa "safiyya".
Kirjin ta ne ya bada dumm! Dan kuwa Momy bata kiran sunanta sai dai tace auta ko 'yata.
"A tsakanina dake ba boye boye kinsani ko".
Safiyya ta gyada kai idonta a Kasa "yawwa dan haka nikeso kifadamin gaskiya ya zamanku yake tsakaninki da sufyanu?".
Safiyya ta hadiye wani miyau da taji ya tarun mata a baki , a hankali ta bude baki "babu komai Momy ".
Momy tayi murmushin gano karya a zancen safiyya "bakomai a tsakaninku duk yana sauke miki hakkinki na aure dake Kansa?".
Safiyya a dan daburce tace "e..e..eh Momy bakomai".
"Shine Dr yacemin ke budurwace har yanzu , nufinsa ba abinda ya taba shiga tsakaninki da sufyan na auratayya".
Cikin safiyya ne ya bada qululululu, "bazaki fadamin gaskiya ba in cutar dake yakeyi ko kuma wanin Ku ne bashi da lafiya?".
Kanta ta kara saddawa Kasa ganin Momy ta gano gaskiyar zancen "lafiyar mu kalau Momy",
"OK, hakanan ya danke ke ki a gida yana kallo, shine kebazaki iya fadamin ba kice cutar dake yakeyi"
Safiyya tayi tsit kaman ruwa ya cinyeta, Momy ta cigaba cikin fushi "bari yadawo tunda ba sonki yakeba sai na raba auren kowa ya huta, shiyasa! Ace duk sa'o'in aurenku daga masu yara biyu sai mai daya ashe abinda ke faruwa kenan,yana cutar da ke kinyi shiru,gwara ya sawwake miki kowa ya huta".
Gaban safiyya ne yayi mummunan faduwa "saki kuma!". Itadai bazatace tana son ya sufyan ba amma tanajin wani Abu gamedashi mai girma a ranta Wanda ta Kasa tantance ko menene, bata kara tabbatarwa ba sai da taji Momy ta furta Kalmar saki",
Koda likita yazo yace zasu iya tafiya gida tunda ba abinda takeji, dashike drivern daya kawosu yanan,shi ya kwashe su ya maidasu gida.
Safina na ganinsu ta mike "Momy inata nemanku ko'ina ba kwanan har gidan sarki, kuma naga wayarki ma kin batta a gida".
Momy ta karaso cikin fuska mai nuna damuwa tace "autace kanta ke ciwo shine na kaita asibiti mukaga Dr".
Safina ta riko safiyya tanafadi "sannu cwt,wallahi ni banma San kuntafi ba inata bacci".
Kakalo murmushi safiyya tayi sannan ta zauna jiki a sanyaye kusa da ita, Momy ta mike "ai kinanan kina baccin nan naki na masifa, Allah yasa baki bar 'ya nata kuka ba".
Safina tayi dariya "ai kema Momy kanki shaidace kan irin jarabbaben kukanta na dare, kuma ta hanani nima runtsawa".
Mintsininta sofy tayi " 'yar tawa ce jarababbiya ko".
Dariya tayi tace "ai halinku daya.
Sai da akayi sallah magriba sannan su sufyan suka dawo, dukkansu suka shiga side din Momy, safwan bai Dade ba ya wuce gida.
Sufyan kuma ya mike ya wuce sasan shi aiko Momy ta bishi.
Yana shiga ta fada dakin , juyowa yayi "momy!".
Dakatar dashi tayi da hannu "magana Nazo muyi ka saurareni".
Zama yayi a Kasa ganin kaman ranta a bace yake ita kuma ta zauna kan kujera "dazun safiyya batada lafiya ta fadi "
Ai yanajin zancen sofy ya dago kai da Sauri "Momy maiya sameta? Tana ina yanzu".
Momy ta kara murtuke fuska ba alamar dariya "ai rashin lafiyarta bai dameka ba sufyan, Ashe bakada kirki ban saniba, wallahi kabani kunya, Ashe cutar da yarinyar mutane kake bawanda yasani dan kaga tanada hakuri".
Shiru sufyan yayi na rashin sanin meye dalilin fadan Momy din. Cigaba tayi "sabida tsabar rashin mutunci ka aje yarinyar nan a gida ba abinda ya taba shiga tsakaninka da ita na auratayya, sai dazun ne da Dr ke gaya mana cewa ciwon ciki take na period kuma maganinsa daya muyi mata aure, Ashe abinda kake kenan, wato muda muka aura maka ita muzo mu dauketa in mun gaji ko, to bari kaji
"Bazaka maida mu mutanen banza ba, gwara ka sawwake mata, kasamu yarinya mai hakuri da mutunci haka amma kake wulakan tata".
"Umarni nake baka cewan ka sawwake mata aurenka dake kanka dan kuwa yarinyar nan bazata taba komawa gidan ka ba gwara ta auri Wanda yake sonta".
Wani zufa ne ya karyo masa idanuwnsa sukayi jajir, fuskar nan tayi jaa ya bude baki zaiyi magana Momy ta daga masa hannu " banason jin komai daga bakin ka sufyan, kawai ka kawomin takardarta wallahi tun muna mu biyu kafin na gayawa mahaifinka, Kasan kuwa yaji ranka zaiyi mummunan baci.
Hankalinshi inyayi dubu ya tashi ganin hawaye a idanun Momy ,abinda ya dade bai sata ta zubar ba,
"Bakada mutunci Ashe, duk irin mutuncin da muke da iyayenta, iyayenku fa aminai ne, yanzu wani ba sai ya mana dariya ba ,na gode sosai da hallaci sufyan. mikewa tayi tabar dakin da Sauri hawaye na bin kuncinta.
Dafe kanshi yayi dayake wani irin sarawa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shj kawai ya iya maimaitawa ya dukushe a wurin...
[3/8, 1:02 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<46>>```
Anan airport din suka zauna , shi baima iyayin bacci ba sabida farin ciki , itakuwa kanta na kafadarsa tana bacci har asuba lokacin da aka kirasu.
Sun isa Nigeria cikin iko Allah, inda jirginsu ya sauka a abuja, sufyan yana rike da hannunta suka je tashar mota sukace sunason su dauki mota daya ne zuwa gombe, nan suka gayawa sufyan kudin yace "ohk mutafi".
Safiyya da tun da ta shaki iskar Niger taketa lumshe idonta. wata bakwai (littafin cwt loobna sufyan) ai ba wasa ba Awanni hudu suka dauka a hanya kafin su isa , kai tsaye gidan safwan yace mai Motan ya kaisu.
Suna isa drivdr yayi parking a kofar gidan sannan suka fito. Kwankwasa kofa yayi mai gadi ya bude .
Sannu da zuwa alhaji Cewar mai gadi daya dauka safwan ne sabida kama dasuke. Jan hannun safiyya yayi suka shiga ciki. Dayake mai gadin baisan sofy ba.
Sallama ya dinga yi amma shiru dan haka
Bedroom din safwan ya shiga ya dinga duba drawers dinsa , nan yasamu kudi dayawa ,dan haka da Sauri ya fita ya sallamin mai Motan daya kawosu.
Kallon mai gadi yayi "mutanen gidan basa nan ne?".
Mai gadi ya kalleshi cikin mamakin ba safwan bane "eh ai basanan yau ne ake walimar wai Amira tagama hadda to duk Suna fada".
Amma kai 'dan uwan alhaji ne ko ,naga kamarku ta baci".
Sufyan yayi murmushi yace "eh yayansa neni".
Wucewa yayi yabar mai gadi cikin rudani dankuwa shidai yasan yayan alhaji daya ne kuma ance ya rasu, to kodai yayansa ne amma ba Uwa daya uba daya ba"
Koda ya koma ya iske safiyya tashiga wanka a dakin Anty Amina, dan haka shima wankan ya shiga ya shirya cikin kayan safwan.
Karasawa dakin da sofy ke ciki. Idanuwansa masu rikita ta ya zuba mata, sanye take cikin wani swiss orange colour sai aka masa kwalliya da golden, tayi kyau sosai ,rigar ta kamata Cass, tasaka flat shoe golden shima, dankwalin kayan na hannunta tana saka dan kunne, ta kara haske jikin nan nata mai daukan ido.
Tsayawa yayi abakin kofa ya harde hannunsa a kirji yana sakan kamshinta mai rikita mishi kwakwalwa.
Karasowa tayi Inda yake ganin yaki shigowa ya na mata wannan kallon nasa mai kashe jiki. Hure masa ido tayi
"Mutafi ne?".
Tayi tambayar tana mai kada kwayar idonta".
Janta yayi ys hadata da jikin bango kamshinsu ya hade guri daya, yatsa ya saka a wuyanta yana mata waiwayi dashi , duk ya gama kashe mata jiki, "kinyi kyau" ya furta a wata wahallaliyar murya , a hankali cikin sanyi jiki ta raba ta kwace kanta dan tasan yanzu sai su shashance anan, gashi kuma ita Allah Allah take su je fada.
Hijjabi ta dauka milk colour sannan ta fita tabi bayansa dayake jiranta a waje. A mota sai murmushi take zubawa " ohh Allah ko ya zatayi intaga umma ohoo?".
Yana kallonta ta mudubi, yadda take dariyar ya birgeta "ya salam, soyayyarta yakeji tana azalzala a zuciyar shi, jiyakeyi kaman ya maidata jikinshi Don so, lokaci guda da kuma zamansu a kauyensu papa soyayya sofy ta masa gagarumin kamu".
Lashe lebansa yayi na Kasa "insha'allahu sai sofy ta soshi kaman yadda yake jinta a rai"
Dayake glass din motar tinted ne shiyasa haka suka shiga cikin fada, ba mutane a wajen sai securitys , parking lots ya aje motar sannan ya bude , fitowa tayi cikin murna, tama rasa ina zata sa kanta dan dadi, sai barinshi tayi a baya.
Da gudu ta ruga cikin gida Inda ake walimar anan, wasu hankalinsu baya gunta sabida mutane ne dayawa, hango Momy tayi kusa da safina, sai jaririya a hannun Momy ,Anty Amina na bayansu a zaune.
Kwala kara tayi da gudu taje ta rungume momy "Momyna".
Daskarewa mutane sukayi awurin aka fara kallon kallo. Anty Amina ta gwalo ido baki na rawa tana nuna safiyya da hannu "au........au......ta".
Ko kafin kace wani Abu momy ta sulale Kasa ta fadi sumammiya .
Safina ko motsi takasayi dagudu ta Kwasa tana kwalawa umma kira, sufyan ne ya karaso cikin takunsa na Jan hankali ,kawai sai kallo ya koma Kansu, nan wasu suka hau kwasa a guje sukayi cikin fada ana ihu ga gawaa
Da Sauri safiyya ta tallabo Momy tana kuka ta rungumeta "Momy please wake up , nice fa"
Sufyan ma ya kariso ya shafi gefen fuskar Momy yana murmushi.
Umma ce da sauran yan Uwa suka fito Suna sallalallami "innalillahi wai inna ilaihi raji'una,"
topah ((matattu sun dawo))
[3/8, 1:03 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<50>>```
Kwakwalwarshi ta tsaya cak, yama rasa tunanin da zaiyi "ai wannan ma abin ba mai yiwuwa bane, ya saki sofy! Inna I can't do dis".
"To kuma zai gwammace bacin ran Momy ne. Kai innalillahi wannane irin masiface".
Gwiwarshi ce tayi sanyi tunowa da cewan sofy bata sonshi dan ko an tambayeta yasan zata fadi, sabida ta Riga ta fadi tun farko a gaban kowa cewan bata sonshi.
Zamiyewa yayi ya kwanta a Kasa jin kanshi ya mishi nauyi, ido ya runtse "i love yhu sofy, I can do without yhu, wallahi bazan iya rabuwa da ita ba Momy ina sonta, itace rayuwa ta".
Haka ranar sufyan ya kwana cikin tashin hankali Inda bacci ya kauracewa idonsa, sai salloli ya dinga yi yana kai kukansa ga Allah madaukaki.
Wanshekare da safe koda ya shigo gaida Momy bata amsa shiba lokacin safina safiyya da Amira Suna daki basu tashiba. Tsugunnawa yayi yasoma mata magiya akanta ta ya hukuri wallahi bazai iya rabuwa da safiyya ba yana sonta.
Momy ta watsa masa kallo "Kasan kana sonta kake wulakanta ta kake tauye mata hakkinta?".
Shiru yayi dan bashida amsar bata kuma baisan yadda zai gayawa Momy ta fahimci yanzu ba da bane, wallahi safiyya itace rayuwar shi.
Numfasawa yayi "wallahi Momy kibani last chance komai zai dai-dai ta, kiyimin rai Momy kiji tausayi na dan Allah Momy na".
Banza ta mishi ta mike zata wuce, riko rigarta yayi "Momy dan Allah kiyi hakuri wallahi harga Allah inasonta,kawai dai kaddara ne".
Bige hannunshj tayi tana fadin "zan bata maka rai fa sufyan, umarni nake Baka kan cewa cikin satin nan ka kawomin takaddar safiyya ko kagamu da bacin raina".ta bar wurin
Dafe kanshi yayi "ya salam, yau naga ta kaina, Momy wallahi ko zaki kasheni bazan iya sakin sofy ba.
Nan ya zauna yayi shiru ,da kyar ya mike ya bar falon ,yamarasa wazai tunkara da wannan mummunan zance, dan inya gayama wani ma dariya zai mishi gwara yayi solving matsalar da kanshi.
Kwananshi biyar yana yiwa Momy magiya amma taki saurarenshi , har 'yar rama yayi dan rashin kwanciyar hankali. Ranan har kuka ya mata abinda bata taba ganin yayiba da girmansa. Nuna mishi tayi ko ajikinta gashi ta hana safiyya zaman falo kullum tana bedroom dinta sabida safina ta koma Kaduna gidan mijinta sabida makaranta tunda yanzu watanta daya kenan da haihuwa wato kwananta talatin.
Abun ya taru yayiwa safiyya yawa, ga rashin ganin ya sufyan, ga kullen da Momy ke mata ga shi kuma tanata dura mata kayan gyra, duk tayi fresh ta ji kyau .
Dady ne ke tambayar Momy "wai yaushe yaran nan zasu koma gida ne, ai mun gaggaisa haka nan ko?".
Momy ta dan gimtse fuska "no akwai abinda nakeyi ne ba yanzu zata koma ba".
Shiru dady yamata baice komai ba dan ya ga yau mulkin nata ne ya tashi "to Allah ya kaimu".
Momy tana sane da abinda takeyi "ta gano tsananin soyayyar da sufyan kema safiyya amma sai ta garashi inma maida mishi ita zatayi,sai ta bashi wahala yadda zai San ba'a yiwa mace haka domin su *kadarorine masu tsada* treating dinsu ake kamar gold.
Kallon safiyya tayi a tsanake "bawai ina miki haka bane dan wani Abu, inaso ne yasan darajarki, amma kina sonshi ke kuwa".
Sadda kai tayi Kasa tana murza zoben dake hannunta "ko bana sonshi zance miki banason 'danki ne Momy, hallacinki gareni ai ko nawaje ba jininki ba kika bani zan zauna dashi balle kuma sufyan datakejinsa a ranta" a fili kuma murmushi ta danyi sannan ta gyada kai.
Momy tayi murmushin jin dadi "good! Yanzu kinga kibani nanda wata daya kafinnan kinga na gama wahalar dashi kuma nagama gyran da nake miki sannan".
Gyada kai safiyya tayi sannan momy ta shimata albarka ta fita
Sufyan ne ya shigo dakin a hankali cikin sallama, Momy ce dai kadai a falon yanda yasaba gani, kallo daya ta mishi ta kauda kai ganin yadda ya zama abin tausayi kamar ba shi ba, gaisheta yayi ciki ciki ta amsa da alamun fita zatayi.
Hijjabi ta dauka tasa Fari sannan ta zura takalmi takai kallonsa gareta Inda ya kurawa t.v ido "zamu fita nidai umma, zamuje gaisuwa gidan inna Sadiya sannan mu biya asibiti mu gaisheda yarinyar Anty Sis da ba lafiya, ga safiyya nan a daki ta samu bacci dan kuwa kasan wata ya zagayo ciwon ciki take fama dashi, kar ka tasheta ka barta ta huta".
Tana gama fadin haka ta fice ya bita da adawo lafiya, "Momy inkikace kar na leqa sofy ai biki min adalci ba.
A hankali ya tura kofar dakin Momy ya shiga, hangota yayi kwance a tsakiyar gado da waya a hannunta tana game sai murmushi takeyi.
Sanye take da wata karamar Riga ja iya gwiwa ,rigar shara shara ce alamun ta shan iska ce dan kana iya hango undies dinta ta ciki
Bataji shigowarsa ba kawai sai ji tayi an rungumeta ta baya, kamshin turarensa shi ya tabbatar Mata da shine , juyo da ita yayi idanunta a lumshe "ya jikinki, shine kika biyewa Momy kuna wana ni ko".
Sadda idanuwanta tayi Kasa "ni lafiyata kalau ai".
Dago kanta yayi yana shakar kamshin dake tashi a kafa ilahirin jikinta "Momy tace kina ciwon cikin period, Ashe kawai batason na zo wurinki ne"
Kokarin kwace jikinta tayi dan momy ta mata kashedi kanshi kafin ta fita dan tasan halinshi ita safiyya yanzu sai labari ya canza ,Murmushi ne ya subuce masa dan ganin ya samu mafita.
Riketa yayi gam ya hanata motsi,yana sunsuna gashin kanta,shiru tayi gabanta da dukan uku uku Don tsoro.
Duk tagama rikitashi da kamshinta sai sunsunata ya keyi, cikin Wanda hankalinsa ya gama gushewa ya tura bakinsa cikin nata....
[3/8, 1:03 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<51>>```
```Sakon gaisuwa ga gareku mutan grp din miemie bee,muna godiya ga dimbin soyayyarku garemu,dis page is for yhu guys ,tnx for d luv,we luv yhu frm d bttm of our hrt```
Salon soyayyar shi da ke gusar mata da tunani suya shiga yi mata, kwata kwata baya cikin hankalinsa kamar zai cinyeta. So takeyi ta iya furta ko kalma daya ce amma lebanta ko motsi ya Kasa yi,ganin haka ya sanyata fara zubar da hawayen da bata san yama son ko Suna zuba ba. Gashi batasan abinda yasaba ta Kasa hanashi,zuciyarta ta mata nauyi jin irin sakonnin da ya sufyan ke aikama duk ilahirin jikinta
Kwata kwata tunaninta ya dauke tsoro ya shiga zuciyarta ganin abinda ya sufyan ke kokarin yimata, ya Riga ya gama kashe mata jiki dan haka kawai ta sadakar ta gama yawo jin yana karanto addu'a.
Sai da ya tabbatar ya kauda duk abinda yakeji game da ita sannan ya sassauta mata, dago kai yayi a hankali yana kallonta , Kasa tantancewa yayi a mace take ko a Raye. Mikewa yayi da Sauri ya mirgina ya kwantar da ita gefe,
Toilet ya shiga ya hada ruwa mai zafi yayi wanka sannan ya iso gareta, duba agogo yayi ganin kusan awa uku kenan yayi a dakin, tsoronshi daya kar Momy ta dawo gashi har karfe sha biyu da rabi.
Gyara mata gashinta yayi Wanda duk ya hargitse ya rufe mata fuska, ruwan dake ragowa a hannunsa shiya shafa mata a fuska.
Aikuwa tana bude ido ta fashe masa da kuka murya can Kasa , murmushi ya mata dan yasan dama hakan zai faru inta farka, langwabar da kai yayi gefe hade da mata fuskar tausayi "am sorry dear, plss stop carrying kinji kar Momy ta jiyoki".
Ai tana jin yace Momy wani karfi yazo mata ta Mike zaune ta fara yarfa hannun shagwaba "Momy ta dawo, shikenan yau nagama yawo".
Dariya ta bashi ganin yanda duk tabi ta rude, ai tana ganin ya fara dariya ta kara Fasa wani kukan, gimtse dariyar yayi "nifa wasa nake miki bata dawo ba, amma kitaso muje ki gyra jikinki kan ta dawo".
Da kyar da sidin goshi ya dauketa sukaje toilet, Shiya ya mata wanka sai kuka take masa ita zafi, barinta yayi yace ta kara gasa jikinta shikuma ya fita ya gyra mata gadon.
Ganin ta Dade bata fitoba yashi lekawa, tana zaune a bath tub idanunta a runtse, zuwa yayi ya dauko towel ya nannadota a ciki ya kaita kan gado ya kwantar da ita.
Cije lebe tayi , dasauri ya tallabota zuwa jikinsa "lafiya dear,ina ke miki zafi".
Kuka ta soma yi ita cikin ta ciwo, kanta ma ciwo gashi kafafunta duk sun rike kamar ana daddatsawa, cikin tausayawa ya kalleta " bari naje daki na dauko miki maganin kinji, in kinsha sai ki kwanta".
Fita yayi yaje dakinshi ya kawo mata maganin da ruwa ya bata tasha, nan baccin wuya yayi awon gaba da ita kanta na cinyarshi.
"Sofy rigima kenan, balle kuma na yau mai dalili, wani irin sanyi yaji zuciyarsa na masa,kai Allah na gode maka da ka azurtani da mata saliha kuma natsatstsa, Allah ya miki albarka safiyya Allah ya bamu yara nagari, gaskiya ita baiwa ce a gareshi, dama ance duk wanda yayiwa iyayenshi biyayya to bazai taba ganin ba dai-dai ba, Allah ka barni da matata har abada, I luv u sofy".
Gyara mata kwanciya yazoyi yaji jikinta da zafi "Allah sarki dear, nasone wannan rana ya kasance a gidanmu to amma Momy ta hanani ke".
Shafa gefen kumatunta yayi sannan ya fita ya dauko towel ya jika a ruwa, fuskarta ya fara daddanna mata da towel din, bude ido tayi cikin magagin bacci da kuma zafin zazzabi "dan Allah ka daina" tana ture towel din.
Cikin tausayawa ya ce "kiyi hakuri kinji sofy, jikinki akwai zafi ne".
Da dubara ya dinga sa towel yana daddanna mata towel din a ko'ina na jikinta sai kukan shagwaba take masa har bacci ya sake kwasheta.
Ganin tayi bacci ne yasanya shi mikewa kuma jin ana ta kiraye kirayen sallahr azahar, sumbarta ta yayi a libs dinta sannan ya dauki bedsheet din daya cire ya nufi dashi side dinsa dan kar Momy ta lura.
Karfe daya da rabi Momy ta shigo gidan, lekawa tayi taga safiyya nata bacci ta lullube da bargo. Sallah tayi sannan ta zauna a falon tana cin abinci. Tunani tayi karfa ace safiyya batayi sallah, amma bari taje ta tambayota dan daga ganin baccin nan nata mai nauyi ne.
Yaye bargon tayi tana fadin "auta auta, kinyi sallah kuwa".
Da kyar ta bude ido sabida baccin da ke idonta , Momy ta bita da kallo cikin damuwa "lafiyar ki kuwa auta, kinga yadda idanunki sukayi luhu luhu fuska tayi jajir, mekedamunki".
A dan daburce ta lalubo abinda zatacewa Momy "Momy kaina ke ciwo tun safe, shine na kwanta".
"Allah sarki sannu kinji, kinsha magani kuwa?",
"Eh nasha paracetamol shine na kwanta,bari nayi sallahn tukun".
Momy ta fita yayinda safiyya ta ja jiki zuwa toilet tayi alwala ta yi sallah a zaune, dan zazzabi taji yana dibarta.
Karfe uku sufyan ya shigo dakin Momy,tana zaune tana kallon labarai ganinsa tayi cikin walwala da hango tsananin farin ciki a idonsa Wanda rabon data ganshi haka tun lokacin ta tamishi maganar rabuwa da safiyya, ledoji ne a hannunsa farare .
Binsa tayi da ido lokacin daya zauna yana gaisar da ita. "Ya mai jiki Momy".
Momy ta wani gimtse fuska, "da sauki gashi ma ciwon cikin ya Sakar mata zazzabi".
Nuna alamun damu wa yayi "dan Allah Momy kibarni na shiga na ganta gaishe da ita kawai zanyi".
Kara daurewa Momy tayi "ko menene ka bani na kaimata, amma Kasan Allah ba zaka je kusa da ita ba"..
Shiru ya mata dan sanin halinta na rashin son magiya "ga wannan inta tashi a bata".
Binshi tayi da kallo lokacin da yabar falon "yaro da ni kakeyi" ( na yaushe kuma Momy an shuka ki).
Sai dare safiyya ta samu dama dama, siyayyan da sufyan ya mata shita iya ci ranar dan kuwa kaji ne gasassasu da yoghurt mai Sanyi sai snacks iri iri har saida ta rage.
Kwananta biyu ta warke tas, matsalanta daya yadda bata ganin sufyan dan Momy ta kashe ta tsare. Ranar tacewa Momy bari taje wurin umma.
Sanye take da Riga da sket, rigar mai zip a gaba pink ne akamishi kwalliya da baki tayi kyau sosai ta dauki hijjabi ta sa sai kamshi take.
Tana fita dai dai parking lots sai ga motarshi nan, ganinta yasashi Saurin yin parking ya fito da Sauri ya nufeta, murmushinsa mai tsada yake mata dan ji yake kamar ya hadiyeta Don son.
A hankali ya jata har bedroom dinsa suka zube a kan gado, runguma ya kaimata "shine Bakya nema ne ko sofy".
Kanta a Kasa dan yanzu tana kallon idonsa to zai kashe mata jiki , hannu yasa ya tallabo fuskarta "ya jikinki".
Dan mitsitsin bakinta mai birgeshi ta bude "da sauki". Kwata kwata ji takeyi ya mamaye ko'ina a cikin zuciyarta, kaman ba ya sufyan abokin fadanta ba, ko dai abinda takeji game dashi shine so ohoo, amma gaskiya tanaji yanzu bayan iyayenta to shine na biyu a cikin ranta, jin kamshinsa take har cikin ranta, ga kyawun zuciya gana jiki, kai itadai ta more miji, amma itadai har yanzu bai furta mata Kalmar so ba, sai Wanda tajisu jiya da suka Kasan ce tare..
Rau rau tayi da ido ganin yana kokarin zuge mata zip din gaban rigarta "gidan umma fa zani ina bukatar ganinta yanzu"
Idonsa masu kashe mata jiki ya zuba mata "ke ma mijinki na bukatar ki a yanzu"..
[3/8, 1:04 AM] +234 703 962 5239: *```MACE KADARA CE MAI TSADA```*
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<52>>```
```kullum cikin gaisuwa muke ga duk masoyanmu, ba mu manta da kuba mutan dandalin meesha luv & hauwa Hausa novel,mungode da soyayyarku garemu, bunch of kisses to u all```
Abinda ya fara Shiya cigaba da yi, ganin bazai kyaleta yasata barinshi yayi abinda yakeso da ita
Janta yayi suka Lula wata duniyar ta daban,gaskiya ya sufyan ya iya mantar da mace duk damuwar da take ciki in Suna tare.
Sai da yaji ana kiran sallah magrib sannan ya kyaleta badan ranshi ya soba, dan kuwa kwata kwata baya gajiya da ita.
Kanta na kan kirjinsa yana wasa da gashin kanta, yanata mata magana amma tayi shiru sai sauke numfashi take, ,Jan gashin yayi da Sauri ta kara kankameshi "oouucchh, akwai zafi fa".
Murya can kasa yake magana idonsa a lumshe "ko mu sake ne, naga kaman bai isheki ba".
Da Sauri ta mike ya riketa gam "ya sufyan kasheni kake sonyi, wallahi wannan ma..."
Murmushi ya mata ya manna mata Sumba a goshi "wannan ma me?".
"Uhm uhm ni dai kasake ni kar Momy ta zo ta gammu".
Daga mata gira yayi "ai wallahi nasan ke kike biyewa Momy , inkikace ta barki ki dawo nasan zata barki, kinsan yanzu tafi sonki a kaina"
Dariya tayi hannunta na kan kirjinsa tana wasa dashi "ka manta sharadin data sama maka, tacefa wata daya ta Baka".
Dago kanta yayi ya hade goshinsa da nasa, yana mata wani irin kallo ta Kasan ido "sofy yanzu zaki iya rabuwa dani".
Tambayarce tazo mata a bazata "in tace eh wallahi ta ma zuciyarta karya dankuwa koya tayi kokari ta yaficeshi daga ranta to sai zuwarta ta dinga azalzala mata shi a rai".
Shiru ya biyo baya na 'yan seconds,gashi ta Kasa dago ido ta kalleshi sabida yadda idanuwan nasa keda tasiri a zuciyarta, hannunsa ya hada numfashinsu na sarkewa da na juna " I luv yhu ".
Jin maganar tashi tayi daga kanta har tafin kafarta,jikinta yayi wani lakwas, Suna nan a haka sai sakar numfashin juna suke ,sai can ya furta " tun kina karamarki nake kaunarki safiyya,kuma ni na raineki na koya miki sona a lokacin da bakisan menene so ba, kullum muna tare dan har bacci kike wurina sai kinyi bacci ne nake kaiki gun umma, bansan ya akayi haduwata dake bayan shekaru da muka dauka bana tare yazo da problem ba, kuma nasan hakan ya farune sanadiyyar rashin gane juna da bamuyiba, dan Allah safiyya kisoni ko kwatan yadda nakesonki ne, kanki nafara sanin menene so,Allah shiyasan wani alheri ke cikin aurenmu, ina sonki safiyya, kece rayuwata".
Kalamansa sun gama kashe mata jiki, kanta a Kasa ta Kasa ko motsi, dago kanta yayi da Sauri ta runtse ido "sofy bude idonki ki kalli cikin idona".
Kin bude wa tayi domin tasan tana kallon idonsa zai gama da ita, kuma zai karanto soyayyar da take masa a ciki.
Chakulkuli ya fara mata, kyalkyala dariys ta hau yi "plss ya sufyan ka yi hakuri zan kalleka".
"To oya, bude idonki ki kalli nawa".
Bude wa tayi a hankali ta zubasu cikin nasa,bakinta ya kama cikin nasa, ganin antada sallah kuma tasan yanzu sai ya zarce "washh, ya sufyan cikina".
Dagowa yayi da Sauri ya cikata "subhanallahi, meya samu cikin".
Daukan hijjabinta tayi da Sauri ta dira daga kan gadon ta fice tana dariya. Murmushinsa yayi na "zan kama ki yarinya".
Gidan umma ta wuce tayi wanka sannan tayi sallah,wasu kayan tasaka Riga doguwa mai ruwan toka, tayi mata cis cis, rigar daga Kasa an tsatstsaga.
Umma ta bita da kallo cikin murmushi "wai Niko auta yaushe zaku koma gidane".
Sosa kai tayi"umma nima bansaniba, Momy tace wai saita sa rana".
"To ai ya kamata kibi mijinki Ku koma, dan kuwa ya mungaisa haka ko".
Share zancen tayi ta kawowa umma wani hiran, sai karfe takwas ta koma gidan Momy.
Bayan kwana biyu, aunty Amina ta kira Momy cewan dan Allah tabar safiyya tazo ta mata kwana biyu,Momy bata Musa ba tacewa safiyya ta shirya taje itama sai murna take.
Da daddare sufyan ya shigo sashen Momy, bayan ya gaida ita yake cemata "Momy sofy fa".
"Ina ruwanka da ita, mai zaka mata".
Ka kalo karya yayi "Momy dama takardu zan tambayeta na makarantar ta, munyi magana da mai martaba ne cewan zata koma".
"To saidai kabari inta dawo tana gidan safwan can zata kwana".
Baice komaiba dan shi gaskiya yafara gajiya, wai ace baza'a bashi matarshi ba sai ja mishi rai akeyi, wanka yayi ya dauki mota yayi gidan Anty Amina. Suna zaune a falo sai gashi ya shigo da sallama,
Waro ido safiyya tayi yayinda Anty Amina ta hau murmushi "a ah sannu da zuwa ya sufyan".
Murmushi yamata sannan ya dauki jannat dake wasa a zaune. Gaisawa sukayi safiyya itama ta gaidashi kanta a kasa.
Ruwa Anty tace safiyya ta dauko mishi."dama nace Anty dan Allah ki dan aramin ita zamu fita ne".
Aunty Amina tayi murmushi "OK ba komai sai kundawo, bari tazo nagaya mata".
Mikewa aunty tayi tabi safiyya kitchen din ,"kiyi Sauri yana jiranki fita wai zakuyi".
Safiyya ta shagwabe fuska "aunty fita yanzu karfe Tara da rabi, kawai dai ni..ni...ni uhm",
Anty Amina tayi murmushi " nidai kiyi Sauri yana jiranki a waje, nima nasan nawa mijin na hanya ai".
Fita tayi ta dauki hijjabi ,Anty Amina ta kalleta a sheke "ko dan turare bazaki fesa ba auta, wurin miji fa zaki".
Turarukanta ta bata ta shafa sannan ta bata wata Zuma wai tasha, "Anty kibarni haka bafa dadewa zamuyi ba".
"Hmmm kedai sai da safe, dan daga ganin mijin nan naki yau, to da akwai abinda yake bukata".
Safiyya ta turo baki sannan ta shirya cikin less blue Mara nauyi ta fita tana kunkuni "ni wallahi wannan ya sufyan din yacika damu..".
Aunty dariya tadinga mata "tunda kun tsaya masa kwalele keda Momy ai dole kiga damu kuwa".
Motar ta bude ta shiga, lumshe ido yayi jin kamshin dake fita a jikinta. Jan motar yayi Suka fara tafiya, sai da ya gama yangarsa sannan yace "wakika tambaya kafin kifita".
Itama shan kunu tayi "Momy".
"Momy ke auranki".
Shiru ta masa ganin so yakeyi ya ja zancen.
Wani babban hotel taga ya shiga yayi parking ta bisa da kallo idonta taf da hawaye...
Copied By
0 comments:
Post a Comment