🅿21&22
Tsaye Hafsat tayi ,tayi shiru ,axuciyarta tace oh yaya fushi yyi kenan, Toni nafasa tafiyar.
Dan haka toilet na tsakar gd ta shiga tayi alwalla tazo, parlour tayi sallar la,asar.
Bayan ta idar, ta fito ta nufi kitchen danyima Sir Aliyu girkin dazaici da dare.
6angaran sir Aliyu kuwa ,yanashiga bed room toilet yashige yyi wanka da alwarla.
Bayan yyi sallah yacire jallabiya dg shi sai 3 quarter yakwanta.
Tunani yake meyasa yadamu dan Hafsat ta tafi?
Wani 6angaren na zuciyarsa haushin kansa yakeji ,akan
Yadda yadamu da ita,
Tsaki yaja,danshi atunanunsa ,ta tafi hostel , yana nan kwance har bacci yyi gaba dashi.
Hafsat bewar allah tanacan kitchen tana hak'ilon girka masa sakwara da miyar agushi.
Sai sauri take batason magrib tayi mata agidan sir Aliyu.
Ba,ita ta idarba sai 6 saura, tasaka komai ature takai parlour.
Sannan tashiga bed room din,kwance tasamesa ba Riga, ga uban gashi kwance a faffad'an kirjinsa.
Ta d'an tsorata dan bata saba ganin babba ahakaba, amma arantace oh ji mutum ko ina jikinsa gashi.
Da sauri tadawo bakin k'ofar shiga dakin ,ta bada baya ta shiga knocking ahankali.
Da addu ar tashi da ga bacci ,yafarka abakinsa, jin knock yasa yakalli k'ofa.
Amamakin sa yaganta tsaye ta bada baya.
Tsaki yaja yace ke lfy ,zakiyimun wani tsaye, meyasa kika dawo dakka tafi?
Batare da ta juyoba tace katashi magrib takusa, ga abincin da zakaci nan da dare ni xan tafi.
Haushin kansa yaji, da ya6a mata magnar da yayi,ashe da bata tafiba.
Ahankali yace muje na rakaki sarkin jin tsoro, kamar yason abinda ke ranta.
Dama sotake tace yarakata sbd tanajin tsoro,amma tanagudun fad'a masa ya disgata.
Jallabiyarsa yasaka ,yasameta a parlour ,nan yafito tabi bayansa ,
Wani gun amfara, kiran magrib,ahanya yace ke bakauya kincika tsoro wlh.
Sarai tasan Jan maganane sai ta sharesa, har gab da hostel yarakota, anan sukaga Pripet din da aka kora nashigowa da kyansu.
Kallon ta Yy yace ke ni nakoma, ahankali tace, Allah yak'ara sauk'i,saida safe.
Kallon ta Yy yace ameen ngd kinji, bejira amsartaba yyi gaba.
Ita kuwa daki ta wuce, tasami Fatima zata yi sallah Fatima, tace sis ina kkje tun dazu naketa nemanki.
Zama tayi tasanar da ita,ai sir Aliyu ba lfy, nan ta jajanta mata, Hafsat taje tyi alwalla tazo tayi sallah.
Washe gari byn sun gama shiryawa ,suka nufo area class, Aiko hadu da sir Aliyu xe bud'e office insa.
Nan Fatima ta ce lah sis ga sir can ze bud'e office yamaji sauki ,muje mu gaidasa da jiki.
Nan suka nufi office ,nasa bayan sun gaidashi sukamasa yajiki,suka fito,yaso yatsayadda Hafsat ,
Amma ganin ba ita1 bace yakyaleta.
********** bayan kwana2 sir Aliyu yawarware yasami sauki sosai,
Ya Tara Pripet, yasanar dasu kullum,sai sun share staffroom
Sun wanke toilet na malamai, sun share bakin get,
Kamar su mutu dan bakin ciki, bbu damar su Musa masa dole suyi,wani sabon tsanar Hafsat suka sake ji.
Yau Yakama talata, kullum sir Aliyu ,a step quarters yaje kwana ,amma yau saiyaji yanason kwana,
A office nasa sbd akwai bed room, aciki ,dan haka bayan isha,I yaje yakwanta can..
Da misalin karfe1:30 am,katti3 suka shigo skul din, kasancewar ba wadatattun masu gadi.
Gaba daya sun hargitsa skul in, sai ihu kato ake, ,students sun hade gu 1 bbu zancen wni Senior retie.
Atsakiyar makarantar inda suke ihun nan kattin suka zagaye su suka nuna masu wuk'ak'e, da sanduna akan sun atsu.
Dayan cikinsu ya kunna touch light, yana haska students koxaiga wadda ta yi masa,yabiya bukatarsa da ita.
Nan yafito da wata ss1 da ss 3 yasake haskawa cikin rashin sa,a yahasko Hafsat, atake yakwadaita da ita dan tanada kira me daukar hankali.
Fisgota yyi yanuna mata wuka, yafito da ita,tsabar kad'uwa saida Hafsat tasaki fitsari.
Atake students duka suka saki uban ihu ,kasancewar dare ko ina saida ya amsa.
Sir Aliyu kuwa cikin baccinsa ,yaga Hafsat tana kuka tana kiran sunansa yazo yatai maketa.
Atake yafarka ,yyi sharkaf da zufa ,dedenan Kuma yaji ihun students.
Da sauri. Yasaka jallabiyarsa ,afili yace skul din nan ba lfy wannan ihu haka, mlm rabe yakira, yasanar dashi su hadu a hostel dan bbu lfy.
Nan yace gashinan ,shima yaji kamar ihun students, kasancewar shima mlm rabe yana cikin step quarters na makarantar.
Da sauri. Sir Aliyu yafito yana haska wayarsa, jin ihun yyi yawa yasa yahada da gudu,
Yana shiga hostel din yabi inda yakejin ihun students, yana shan kwana, yahangosu sun cure gu1
Sannan ga wasu maza biyu da wukake ahannusu suna nuna masu.
Agefe Kuma ga wani yana cire kaya ga yaro 3 gefensa.
Innalillahi wa inna ilaihir raju, kawai yake maimaitawa atake yagane meke shirin faruwa.
Ai da sauri , yaciri wani rashe na bishiya dake bayansa batare da yaji tsoroba ,yasa wayarsa a aljihun wandonsa.
Da sauri yayi gunsu ,Dede nan dayan katon yyi gun daya daga cikin 3 dke gefensa.
Amamakin sir Aliyu ,sai yaji muryar Hafsat tana cewa wayyo Allah na yaya aliyu kazo katai makeni.
Kada suketamun haddi, yaya Aliyuuuuuuuuuuu!!!
Ai azabure had'e da fad'uwar gaba sir Aliyu ya ida isa kamar wani mayunwacin zaki,abunka da karfeffen mutum.
Hannu 1 yasa yadamk'osa ,sannan yasa ,reshen dayaciro yabugo sauran kattin dasuka nufosa .
Dan ceton dan uwansu,atake suka fadi kasa ,
Wani wawan punch yakaima na hannunsa a fuska ,yasake masa,
Atake bakinsa yafashe da hancinsa yafadi awahalce,
Sannan sir Aliyu yacigaba da suburbud'ar biyun dake kwance,
Akuma lokacin Hafsat ta fahimci sir Aliyu ne ,yakawo masu wannan agajin.
Da sauri ta buya abayansa tasa hannuwanta ta xagaye cikinsa,
Tana abayansa ,yacigaba da suburbudarsu, kamar actor nadukan yan gidan both lolx....
Duk students sunyi mmkin jarumtar si aliyu, shikuwa mlm rabe tsaye yyi yana ganin ikon Allah.
Dan bayan yafara dukansu yazo
Cikin 15 minit Sir Aliyu yabazar da kattinnan 3 nan mlm rabe yazo da igya ya dauresu.
Gaba daya Hafsat ta rud'e kuka kawai take, ta lik' e jikin sir Aliyu. Wai sai ya kaita gidansu ,kamarma bata hayyacinta.
Sai dukansa take akirji akan yakaita ita de gidansu.
Kok'arin rabata yake da jikinsa , amma sake manne mai take.
Mlm rabe ne yace mlm gsky bata hayyacinta ,tunda taki sakeka ,kaje da ita gdanka ta kwana ,
May bee ansan yadda za,ayi dasafe ,amma ko ka barta hankalinta bazai kwantaba,
Tunda dai k'anwarkace inaganin ba matsala.
Nan mlm rabe yacema students ko wacce ,ta tafi d'akinsu.
Fatima kukan tausayin.kawarta kawai take, haka ta tafi daki jiki ba k'wari.
Akan dole sir Aliyu ,yaja Hafsat ,kamar cingam suka tafi a step quarters.
Ko acanma babu yadda beyiba da ita akan ta kwana bed room, shi yatafi parlour.
Amma Hafsat tasa rigima ,ita gunsa zata kwanta,lura yyi da kamar bata hayyacinta yasa yakyaleta.
Ken bed din yakwanta tare da janyota Jikinsa ,
Yajamusu bargo,tareda shafar kanta ,itakuwa sai ajiyar zuciya take.
Wani kwance akan faffad'an kirjinsa,tasa hannunta daya ta zagaye cikinsa dashi.
Batafi minti 10 ba yaji tayi bacci, ahankali yazo kwantar da,ita gefensa, da nufin Yakima parlour.
Ai sai ta sake mannemai,aiba yadda ya iya haka suka kwanta.
Yanajinsa atakure dan betaba kwanciya da maceba a haka aayuwarsa sai yau.
Gaba daya tudin nashanunta sun tokaremasa kirji ga wani bak'on yanayi dayakeji atare dashi.
Addua kawai yake gari yawaye, lfy ko Hafsat tadawo tunanin ta,
Akan dole ya yard a su kwana gu daya dukda ya yarda da kansa, amma yasan shaid'an ze iya rays maka abu marar kyau.
Da wannan tunane tunanen bacci Yy gaba da shi,
Da misalin karfe5:30 am Hafsat ta farka da adduar tashi dg bacci.
Atake abinda yafaru yadawo mata, amma tyi zaton mafarki take.
Maido nefa akayi dakin yadauki haske ,kallon dakin tayi da sauri tajuya junta jikin mutum.
Kawai taga sir Aliyu kwance yana bacci, abinda yafaru jiya ta tuna.
Da sauri tabar jikinsa cikin jin kunya da ganin rashin dacewar hakan.
Ahankali yabude idonsa ,yaga Hafsat bata ,d'akin .
Da sauri yafito parlour, azaune yaganta tayi tagumi, ahankali,
Yace kintashi bata kallesaba tace eh ,yace jekiyi sallah lokaci yyi.
Tsakar gd ta fito ta yi alwalla a toilet, tazo parlour tayi sallah.
Bayan ta idar ,sir Aliyu yafito dg bedroom.
Yaxauna kan kujra , yakalleta, da sauri tace yaya ina kwana?
Lpiaqlau matsoraciya,turo baki tayi tace aide tsoro halak ne .
Tsaye ya mike yanufeta yana cewa kin rainani ko,
Da sauri ta zura aguje atsakar gd yarufa mata baya,su ka hau zagaye gdan.
Har hatsat tagaji da gudu ta koma parlour ta fada kan kujera tana maida numfashi.
Biyota yyi ,said hakuri take basa,yak'i sauraranta.
Zama yyi yajanyota kan cinyarsa ,ya matse mata hanci da baki.
Sai mutsu mutsu take yak'i saketa.
Can tasa hannunta a hamurtarsa tafaramai chakul kuli.
Da sauri yacikata yana dariya,had'e da aza kansa gefen wuyanta.
Har sajen fuskarsa na gugar gefen wuyanta, wani yanayi hafsat ,taji,
Da sauri ta kalli agogon bango tace yaya bara naje na shirya har 7 tayi kada na makara.
Nan ta tashi dg jikinsa ,tasaka hijab ta fito, bata kallesaba ,tayi ficewarta xuwa hostel....
Ina godiya ga masoya nida D'ALIBATA🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Dan Allah masu bina ta PC akan natura masu dg farko pls kutambaya agrps dina zaku samu.
Share pls
NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿23&24
Tana isa hostel tasami ,Duka malamai da dalibai, da police, antaru ga kattin nan zahiri suna a daure.
Nan principal tasa mlm rabe yakira mata sir Aliyu, ba bata lokaci yyi masa waya.
Ba,afi minti10 ba yazo, yasha kananun kaya sai zabga kamshi yake.
Gaba daya Kallo yakoma kansa , musammun ss3 kowace ji take inama yace ya k'yasa.
Nan malamai da principal suka jinjinamasa akan namijin k'okarin da yyi.
Sannan akatasa kattin gaba zuwa police station, dan ayi musu hukunci.
Sannan kowa ya watse ,Hafsat taje ta shirya suka nufo class itada Fatima.
*******
Yau Yakama Saturday, aranar Kuma ake visiting, kowa murna yake amma banda Hafsat dan tasan bazata ga yan gidansuba.
Sir Aliyu kuwa yana gidansu week end, zaune yake kan dinning area ga Kula's agabansa na abinci.
Yyi shiru yana ta tunani,mommynsa ce wato hjy Aisha ta fito ta na masa magna amma bejiba yana tunani.
Bubbuga table din tayi ,da sauri yakalleta yace my mommy.
Kallon sa tayi tace babana lfy me damunka kwana2 naganka kana yawan tunani?
Murmushi yyi yace no mommy ba komai, yanxunma zan wuce a skul nayi mantuwa,
Da sai dare zantafi, amma bari naje asamun abincin a basket.
Kallon sa tayi tace to, amma badan ta yarda bashida damuwaba.
Nan akasaka masa abincin a basket, yadauka, yasa agidan baya, yashige gaba yaja mota sai skul.
Hafsat na zaune a block din admin block, tana kuka harda hawaye.
Tunani take azuciyarta, tunda ta zo skul din bbu wani nata da yataba zuwa,wasu k'ayensu har ca suke basu taba ganin yan gidansu ba.
Saidai Fatima ,tace musu da safe ake xomata shiyasa.
Komai da ba Fatima suke amfani,ita tsoronta daya kada Fatima yau da gobe tagaza da ita.
Dukda bata tunanin Fatima zatayi mata hakan.
Amma tason dan Adam ,ze iya canjawa.
Sir Aliyu yyi horn aka bud'e masa get , yashigo yyi parking, yafito ra basket a hannunsa
Yanufi office dinsa ,ya bud'e ,yashi ga, ya zauna, tsintar kansa yyi da son yaga Hafsat.
Tashi yy dan yasan yau ake visiting, yanufi gundake da students ko xai ganta acikinsu.
Kamar ance yakalli gefensa, yahango Hafsat zaune tayi tagumi,tana kuka.
Yah salam! Yace afili da sauri yanufi gunta, ganin bata gansaba.
Yasa yarungume hannuwansa akirji yana Kallonta, k'amshin turaren sa taji da sauri ta d'ago kanta.
Idanunta tsab cikin na sir Aliyu, murya a sarke yace,hafsat ttttt!
Meke faruwa ,me Akamiki kike kuka haka?? Shiru tayi ,can Kuma tace ba komai.
Kallon ta Yy danbe yarda ba yasan da dalilin dayasa take kuka,
anacikin haka ,Fatima taxo. Nemanta ,tasame su tare da sir Aliyu, nan yakalli Fatima yace meyasa take kuka.
Fatima tace dan ba,azo mata visiting ba ,kumafa ba,a mata fashin xuwa duk month ,tayi masa karya.
Nan Fatima ta ce, dama naga ban gankiba nazo nan muna hostel kisamemu a can,
Bata jira amsartaba tayi tafiyarta cike da tausayin kawar tata.
Sir Aliyu yyi gyaran murya yace, dan ba zo miki visiting ba shine kke wanna n kukan.
Ai xasu zo,kobasuzo yauba zasuzo gobe da safe,kiyi shiru kinji kidena kukan haka nan.
Goge hawayen take wasu na sake zubowa,kallonta yyi fuska atamke yace .
Bazaki dena kukanba ko,wato ni ban isa kiji maganatabako, kinfi son kibatamun rai dankinga nadamu dake ko?
Da sauri ta girgiza kanta hade da hadiye kukan ,tace ,kayi hakuri na bari bazan sakeba.
Har cikin ransa yaji dadin maganar ta ,nan yace share hawayen.
Bamusu ta goge,yace muje ko,kallon sa tayi,yace yes muje, ba musu tabi bayansa har office.
Bayan sun zauna yace ta yi serving in su ,nan tayi serving a plate daya tatura masa gabansa .
Kallon ta Yy yace to bissimilla,nan suka faraci har suka gama batare da Hafsat ta yadda sun had'a ido da sir Aliyu ba.
Har ransa yaji Dadi daskaci abinci atare ,dan besan daliliba, yanajin farin ciki duk sadda suke atare ko suke cin abinci.
Bata kallesaba tace yaya natafi ,sai anjima, ji yake kamar yace ta zauna suyi fira.
Amma girman kai yahanasa ,ya furta,dan kada tama yimasa wata fahimta. Kawai sai yace
Ok sai anjima ,nan tafita, tayi hostel dan dama anxoma Fatima tun dazu.
Washe gari Monday , suna class after break ,aka turo wata ss1 ana kiran Hafsat Aminu a bakin get.
cikin mamaki Hafsat tabi bayan yarinyar,suna zuwa get me gadi yace gashi inji babanki,
Yana sauri yace abaki, baki bud'e ta kalli uban kwalayen da akace inji babanta da kaya Niki nik'i,
Kallon baba me gadi tayi tace gsky bani bace k'ila dai watace.
Harararta yyi yace kece mana, dama kwanaki yakawo sak'o abaki kikace wai bake bace ,amma kika karbe.
Dan haka in bakiso ,zaki iya tafiya ,jiki ba lakka ,ta kira wata mate dinsu zata wuce ,
Ta tayata suka kwashe kayan suka kai hostel , tana mamakin kayan.
Koda ta fada ma Fatima,ita wai ji take kamar ba,ita ake nufi ba.
Fatima ,ta nuna mata cewa,itace tason ko babanta yasami budi,Kuma ai bakomai ke tabbata ga dan adamba.
Da haka Fatima ta shawo kan Hafsat ,harta saki ranta.
Koda sir Aliyu yashigo class dinsu yalura Hafsat nackin farin ciki.
Dan haka yyi ta mata tambayoyi ,tana bashi amsa ,da haka har akayi ring in ,dazai fita yace su dage da karatu dan sauran 1 week exam....
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿23&24
Tana isa hostel tasami ,Duka malamai da dalibai, da police, antaru ga kattin nan zahiri suna a daure.
Nan principal tasa mlm rabe yakira mata sir Aliyu, ba bata lokaci yyi masa waya.
Ba,afi minti10 ba yazo, yasha kananun kaya sai zabga kamshi yake.
Gaba daya Kallo yakoma kansa , musammun ss3 kowace ji take inama yace ya k'yasa.
Nan malamai da principal suka jinjinamasa akan namijin k'okarin da yyi.
Sannan akatasa kattin gaba zuwa police station, dan ayi musu hukunci.
Sannan kowa ya watse ,Hafsat taje ta shirya suka nufo class itada Fatima.
*******
Yau Yakama Saturday, aranar Kuma ake visiting, kowa murna yake amma banda Hafsat dan tasan bazata ga yan gidansuba.
Sir Aliyu kuwa yana gidansu week end, zaune yake kan dinning area ga Kula's agabansa na abinci.
Yyi shiru yana ta tunani,mommynsa ce wato hjy Aisha ta fito ta na masa magna amma bejiba yana tunani.
Bubbuga table din tayi ,da sauri yakalleta yace my mommy.
Kallon sa tayi tace babana lfy me damunka kwana2 naganka kana yawan tunani?
Murmushi yyi yace no mommy ba komai, yanxunma zan wuce a skul nayi mantuwa,
Da sai dare zantafi, amma bari naje asamun abincin a basket.
Kallon sa tayi tace to, amma badan ta yarda bashida damuwaba.
Nan akasaka masa abincin a basket, yadauka, yasa agidan baya, yashige gaba yaja mota sai skul.
Hafsat na zaune a block din admin block, tana kuka harda hawaye.
Tunani take azuciyarta, tunda ta zo skul din bbu wani nata da yataba zuwa,wasu k'ayensu har ca suke basu taba ganin yan gidansu ba.
Saidai Fatima ,tace musu da safe ake xomata shiyasa.
Komai da ba Fatima suke amfani,ita tsoronta daya kada Fatima yau da gobe tagaza da ita.
Dukda bata tunanin Fatima zatayi mata hakan.
Amma tason dan Adam ,ze iya canjawa.
Sir Aliyu yyi horn aka bud'e masa get , yashigo yyi parking, yafito ra basket a hannunsa
Yanufi office dinsa ,ya bud'e ,yashi ga, ya zauna, tsintar kansa yyi da son yaga Hafsat.
Tashi yy dan yasan yau ake visiting, yanufi gundake da students ko xai ganta acikinsu.
Kamar ance yakalli gefensa, yahango Hafsat zaune tayi tagumi,tana kuka.
Yah salam! Yace afili da sauri yanufi gunta, ganin bata gansaba.
Yasa yarungume hannuwansa akirji yana Kallonta, k'amshin turaren sa taji da sauri ta d'ago kanta.
Idanunta tsab cikin na sir Aliyu, murya a sarke yace,hafsat ttttt!
Meke faruwa ,me Akamiki kike kuka haka?? Shiru tayi ,can Kuma tace ba komai.
Kallon ta Yy danbe yarda ba yasan da dalilin dayasa take kuka,
anacikin haka ,Fatima taxo. Nemanta ,tasame su tare da sir Aliyu, nan yakalli Fatima yace meyasa take kuka.
Fatima tace dan ba,azo mata visiting ba ,kumafa ba,a mata fashin xuwa duk month ,tayi masa karya.
Nan Fatima ta ce, dama naga ban gankiba nazo nan muna hostel kisamemu a can,
Bata jira amsartaba tayi tafiyarta cike da tausayin kawar tata.
Sir Aliyu yyi gyaran murya yace, dan ba zo miki visiting ba shine kke wanna n kukan.
Ai xasu zo,kobasuzo yauba zasuzo gobe da safe,kiyi shiru kinji kidena kukan haka nan.
Goge hawayen take wasu na sake zubowa,kallonta yyi fuska atamke yace .
Bazaki dena kukanba ko,wato ni ban isa kiji maganatabako, kinfi son kibatamun rai dankinga nadamu dake ko?
Da sauri ta girgiza kanta hade da hadiye kukan ,tace ,kayi hakuri na bari bazan sakeba.
Har cikin ransa yaji dadin maganar ta ,nan yace share hawayen.
Bamusu ta goge,yace muje ko,kallon sa tayi,yace yes muje, ba musu tabi bayansa har office.
Bayan sun zauna yace ta yi serving in su ,nan tayi serving a plate daya tatura masa gabansa .
Kallon ta Yy yace to bissimilla,nan suka faraci har suka gama batare da Hafsat ta yadda sun had'a ido da sir Aliyu ba.
Har ransa yaji Dadi daskaci abinci atare ,dan besan daliliba, yanajin farin ciki duk sadda suke atare ko suke cin abinci.
Bata kallesaba tace yaya natafi ,sai anjima, ji yake kamar yace ta zauna suyi fira.
Amma girman kai yahanasa ,ya furta,dan kada tama yimasa wata fahimta. Kawai sai yace
Ok sai anjima ,nan tafita, tayi hostel dan dama anxoma Fatima tun dazu.
Washe gari Monday , suna class after break ,aka turo wata ss1 ana kiran Hafsat Aminu a bakin get.
cikin mamaki Hafsat tabi bayan yarinyar,suna zuwa get me gadi yace gashi inji babanki,
Yana sauri yace abaki, baki bud'e ta kalli uban kwalayen da akace inji babanta da kaya Niki nik'i,
Kallon baba me gadi tayi tace gsky bani bace k'ila dai watace.
Harararta yyi yace kece mana, dama kwanaki yakawo sak'o abaki kikace wai bake bace ,amma kika karbe.
Dan haka in bakiso ,zaki iya tafiya ,jiki ba lakka ,ta kira wata mate dinsu zata wuce ,
Ta tayata suka kwashe kayan suka kai hostel , tana mamakin kayan.
Koda ta fada ma Fatima,ita wai ji take kamar ba,ita ake nufi ba.
Fatima ,ta nuna mata cewa,itace tason ko babanta yasami budi,Kuma ai bakomai ke tabbata ga dan adamba.
Da haka Fatima ta shawo kan Hafsat ,harta saki ranta.
Koda sir Aliyu yashigo class dinsu yalura Hafsat nackin farin ciki.
Dan haka yyi ta mata tambayoyi ,tana bashi amsa ,da haka har akayi ring in ,dazai fita yace su dage da karatu dan sauran 1 week exam....
Share pls
NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿26&27
Washe gari, su Hafsat na class anata karatun exam,kasancewar ba teachers,sbd ankusa exams,sai noise aketayi wasu na karatu.
Can wani copper, yashigo yace duka class ,din suyi kneeling.
Nan yafita,yadawo da bulala,,yafara dasu Hafsat yan first sit,gaba d'aya ta tsorata,
Yanagamawa da Fatima ,yafara da Hafsat,hakadai ta daure, akayi mata har yafasa mata hannu.
Bayan yyiwa kowa ya fita , duk jikinta ba Dadi ga masassara ta sakko mata.
Nan Fatima ta kai ta dispensire,Dan akula da lfiyarta ,sannan tadawo,
Ahanyarta tadawo wa taga sir Aliyu bakin staffroom, da Hannu yyi mata alama taxo nan taje.
Dan yaga sadda takamo Hafsat ta rakata dispenser.
Bayan ta gaida shi, yadan matsa gefe ,yace dama Fatima zan miki wata tambaya 2 ne inafatan zaki bani amsar.
Nan tace in sha allah sir.
Kallonta yyi yace meke damun hafsat.?, nan ta sanar da shi dalilin ciwon.
Azuciyarsa yace k'ila jikinta beson wahala shiyasa duk sadda aka daketa sai tayi ciwo.
gyaran murya yyi yace nayaba da hankali,Kuma na lura hafsab batada,
K'awa,yar uwa,aminiya, sama dake,inaso kisanar dani wacece hafsat,? Kuma banason kisanar da ita munyi maganarta dke.
Shiru Fatima ta yi,da har zata boye masa,sai Kuma ta tuna da yadda yake taimaka ma Hafsat din.
Dan haka ba ,bata lokaci ta sanar da shi komai game da Hafsat. Harda sakin da mahaifin Hafsat yyiwa mamanta.
Kuma a yanzun Hafsat batason ina mamanta takeba saidai ta boye masa labarin deeni gidoga.
Ajiyar zuciya yyi cikin rudani ,da tausayin hafsat,din lallai hafsat tana cikin jarabawa,dole tayi kuka.
Ace mahaifinka anrabaka dashi,tana skul, betaba zuwa ba ko siyamata wani abu.
Kallon Fatima yyi, yace kada ki sanar da ita nasan komai game da ita kinji.
Na gode zaki iya, tafiya,nan ta barsa zai shiga office, ita Kuma ta nufo class da tambayoyi fal aranta..
A office kuwa sir Aliyu, zama yyi cike da tausayin hafsat,dan rashin uwa ga mace babban hadari ne ga rayuwarta.
Nan yakira mlm rabe a waya yace yatafo masa da doctor.
Ba,afi 15 minit ba sukazo da doctor din, nan sir Aliyu yace ma mlm rabe suje dispenser yaduba hafsat.
Nan yace to ,nan sukaje yarubuta mata mgani, mlm rabe yakaima sir Aliyu, yabashi kudi yasiyo.
Bayan antashi dg class, suka koma daki Kuma ta ji sauki ba laifi.
Pripet ne keta ringing dan lokacin dinning na rana yyi.
Dayake lebour ce on duty ,sai wani hauka take tana kora, har daki ,
Dakinsu hafsat ta shiga,batayi wata ,wataba, kasancewar tayi mugun tsanar hafsat.
Tacigaba da dukan hafsat da bulala wai tafita kitchen, ban tace bata lfy,sake dukanta tayi nan hafsat ta fito ta na hawaye.
Gaba daya sai taji skul in tafita aranta, taji gara taje gd inna Laure da abbanta suyita hantararta.
Fitowa tayi tabi layin mate insu, bata Dade da zuwa ba saiga sir Aliyu.
Jikinsa yabasa cewa ,hafsat na gun ,da sauri yabi layin mate insu yaganta.
Suna had'a ido ,tayi saurin sunkuyya da kanta,Dan ita , batasan yasan bata lfy ba.
Komawa yyi yazauna yana ganin yadda ake raba abincin,sai Wannan iyayi Pripet din keyi ko zai kulasu.
Amma basu sami hakanba,layi yazo kan hafsat,aka zuba masu har zasu wuce hafsat ta juyo ta saci kallon sa.
Carab suka had'a ido, alamayyi mata da ido tazo, nan ta tafi.
Gaidashi tayi be amsaba yakafeta da idanunsa, masu kwarjini.
Kallonta yyi yace yajinki, ahankali tace yaya ni lfiyata klau, ok xaki iya tafiya, yafada cikin basarwa had'e da nuna ko ajikinsa.
Itama data lura da yau sir Aliyu yan shan k'amshinsa sun motsa,sai tayi tafiyarta, dan itama yanzun bata son xuwa office insa ko yawan kebewa dashi.
Hakan najawo mata tsana ga waddanda suke son yarika kulasu,Kuma bataso suyi masu wata fahimta,dukda duka skul din daukar kanwarsa akemata.
Shikuwa sir Aliyu yaji haushin tafiyar datayi,azuciyarsa Yace zan dawomaki kamar da, dankinga nadamu dake.
Tunawa yyi be tambayi Fatima ,wanne gari suke itada hafsat.
Har zai kirata ,saiyafa komai yatuna oho.
***********
Yau laraba Kuma yau ake fara exam,gashi English ce farko,duk ss2 jininsu kan akaifa yake.
Dan sunsan sir Aliyu ko test ,shike tsarewa ayi ,Balle exam dinsa,Kuma da alama zaiyi muggan equations.
Anadawowa dg assembly, sir Aliyu yashigo class insu hafsat Yace duka sukoma assembly hole,anan ss2 duka zasuyi exam na English.
Ba bata lokaci ,duka ss2 aka halla ra ,yaraba masu equation paper,yaja kujera ya zauna.
Fuskarsa bbu alamar wasa,Yace duk wadda Yakama tana mgna zai kar6i paperta kobata gamaba.
Nan Yace su fara,shida hafsat suna satar kallon juna.
Aranta duk sai bataji dadiba ganin kwana2 duk sir Aliyu yanuna bedamu da itaba.
Ba bata lokaci suka cigaba da rubuta exam dunsu,abin mamaki hafsat ce farkon some meeting.
Ga yyi question da yawa,inbaki karatuba zakaci gidanku.
Koda ta gama ,kan dest din dayake zaune ta aza ,ta fita batare datace komaiba.
Hakafa su hafsat sukayi ta exam har suka gama, Kuma gobe Hutu,result finsu sai sundawo.
Sai parking kayansu suke duk students ana murna gobe kowa zaije gida amma banda hafsat.
Duk fargaba take ,gashi tasami kanta da kin jin dadin yadda sir Aliyu ya shareta,gashi taga yau kwana2 bata gansaba a skul din.
K'ila yakoma gidansu ko gidansa ,hakadai hafsat ta yini cikin damuwa.
Washe gari kowa murna yake ,anyi hutum,second term,4 weeks aka basu.
8:00 aka bud'e get students nata tafiya, wasu anxo daukarsu wasu nahawan motar haya.
Nan Fatima ,ta hango yaya Ahmad din gidansu da gudu tayi hugging nasa tana dariya.
Kallon sa tayi tace yaya ,ai nadauka bakai zakazo daukarmuba,murmushi yyi Yace to sarkin surutu,
Muje mana ina hafsat ma naga banganta ba,nan Fatima ta nuna masa gefenta ,
Tace gatanan, nan hafsat ta gaidashi ya amsa,yasamu su kayansu a boot ,
Suka shige mota, yajasu suka dau hanyar gd""""";;;;;;;
Sir Aliyu ne zaune a bed room dinsa dake gidansu,yana tunani ,yana ganin bedace yarika share hafsat ba.
Yau kwana3 kenan rabonsa da skul din ,yason yau ake Hutu, gashi yanason yaga hafsat kafin sutafi gd.
K'ila ma motar haya zata,hau wata zuciyar tace, ga Fatima ai tare zasu tafi,bazata bartaba.
Afili yace ,bari naje da kaina in nuna daukar ta ,naje dan kada ayi tunanin da Fatima ta dogara.
Musammun tunda ana mata daukar kanwata.
Da sauri yatashi ,yadauki car key yafita, awaiting parlour yahadu da mommy,
Da sauri ta ce babana lfy Wannan sauri haka,kamar zaka tashi sama.
Be juyoba Yace mommy zan dan karbi wani sako ne kiyimun addu ar ki ,
Murmushi tayi tace kullum inayi,saidai k'arawa.
Yana fita yaja mota atsiyace, dayake ba nisa sosai cikin 20 minit ya iso skul din.
Babu irin dubawar da beyiba amma ba hafsat ba alamarta.
Har yaci re jida kai yatambayi wasu mate dinsu hafsat cewa dazu sun ganta?
Nan sukace aisun fi 10 minit da tafiya itada Fatima.
Kallon duk mutanan gun yyi yagama ankusa watsewa, jiki ba lakka, yashiga mota,
Yanufi gd duk ransa ba Dadi,Kuma besan dalili ba,nikuwa nace dalili dan bakaga hafsatba......
Ashe haka masoyan NIDA D'ALIBATA suke da yawa,naga comments ba adadi agrps daban da ban,musammun, nida dalibata fans da nida dalibata fans grp 2 , kuyi hakurin jin. Bana yawan magana wlh sak' unna ssunmin yawa amma ina duaba comments dinku sosai, nagode love u so much😍😍🙏🏻🙏🏻
Share pls.
NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿27&28
Su Hafsat ,suna isowa ,unguwarsu,ita yaya Ahmed yafara saukewa, skul bag inta da trolley inta kawai ta dauka.
Tana musu godiya ,Fatima nace mata zata shigo anjima.
Haka ta nufo gidansu gabanta na dukan Tara Tara, tayi sallama, bakowa atsakar gidan, ko ina yyi kaca,kaca.
Dakin da ake aje kayan tarkace ,Wanda da shine dakin mahaifiyarta,can ta nufa ta ajiye kayanta ta fito.
Dakin babanta ,ta nufa ganin ,takalmi ak'ofar dakin alamar yana nan.
Ta daga labulen dakin ta shiga ,kwance tasame sa kan dan tsohon gadonsa,da alama kamar bashida lfy.
Amsa sallamar ta yyi yana murmushi, hakan yaba Hafsat mamaki,sosai,taje ta duk'a gabansa tace baba ina kwana?
Fuska kalar tausayi ya amsa ,yace ,Hafsat naji Dadi da Allah yamaidoki lfy,Hafsat ki yafemun na zalinceku keda mahaifiyarki,
Da akabani amanarta,naci amana ,mamanki bansan inda ta tafi ba ,batada kowa garin nan.
Wasu abubuwan bana hayyaci nayi kiyafemun kinji ,alhakinku bazai barni inji Dadi arayuwata ba.
Cikin kuka Hafsat tace na yafe maka baba,Allah yabaiyana mana mama ,yasa tana cikin kyakkyawan yanayi aduk inda take.
Ameen yah Allah Yace cikin damuwa, sannan Yace bayan kin koma makaranta.
Tsautsayi yagibta min aka bankeni ,nasami karaya, akafa, tsakanina da Laure sai kyara da tsangwama ,
Ganin bana iya fita inne momusu wani abu, ko waddannan yaran shamsu da hanifa, ban isa insasu su taimaka suyimun wani abu ,
Sai Laure ta hana,tace ai ba abunda nike tsinana musu dashi, ita ke wahala dasu.
Kuma alokacin ne duk wani sihiri na jiki nah da Laure tamun yakare,sbd Wanda ya kadeni da mashin malamine.
Shiyabani taimako dana kariyar jiki, dukda abinda nayi ba a haiyacina nayiba.
Cikin tausayin babanta,Hafsat tace ba komai baba ,Allah yaba ka lfy.
Ameen yar albarka,ai nasami sauki,sai dan abinda ba arasaba tunda da sanda nike yawo......
Be rufe bakiba,inna Laure ta shigo kamar anjehota,bako sallama ta watsawa Hafsat wani mugun kallo
Tace to alhudda hudda sarkin karatu saiki fito ga aikin gd najiranki,ke me uba kinxo kun wani had'a kai ko,
To aibayada wani amfani yanakasa dukda nike ciyyadashi tunda beda zuciya.
Shiru Hafsat tayi zuciyarta na k' una , ta tashi, babanta Yace kiyi hakuri kinji duk tsanani yana tare da sauki.
Doguwar tsuka Laure taja,atsawace tace oya muje,ga wanki can kimun da wanke wanke,
In kin gama ki aza girkin rana,nan Hafsat ta fita dan yin aikin.
Tulin uban wankine,danata dana yayanta,harda na shamsu dan shekara 9,
Haka Hafsat ta zage taci uban wanki kamar jaka,
Bayan ta idar tayi wanke wanke, sannan ta aza girkin rana.
Dakin babanta ta koma ,ta gyareshi Ta's tahado kayansa masu datti ta wanke ta shanya.
Tacigaba da girkinta har ta gama ,tayi wanka,wata atamface tasaka red robber.
San taje gun inna Laure tace ,inna ina abincina?
Wani mugun Kallo tayi mata ta banko ashar ,tace eh ina abincinki ko ,
Tunda ubanki ya nemo ko,to akwai saura atukunya zaki iya tafiya ,ki kankaro.
Jiki asan yaye Hafsat ,taje ta kankaro abincin harda kanxo ,ta zauna ,ta fara ci.
Kamar dg sama saiga deeni gidoga yashigo gidan ,sai warin taba yake jiki na tsami.
Cikin muryar shi ta katti,yace ah my wife ,kindawo lfy.
Banxa dashi Hafsat ta yi, ta ida cinye abincinta ta tashi,saurin shan gabanta yyi ze tabata tayi saurin ja da. Baya taja tsaki.
Atake ta tuna da sir Aliyu, tasan da yananan bazai bari deeni har yayi yunkurin tabata ba.
Wani mugun kewarsa taji, sai taji kamar ta koma skul ta ganshi.
Muryan deeni ce tadawo da ita hayyacinta ,Yace miyasa kke guduna ,
Ai wlh inna Laure bazataci kudina abanxaba ,race Bakida miji sai ni,
Ko kiso ko kada kiso,deden nan babanta yashigo yana dogwara sanda,
Deeni naganinsa yabar gidan,nan tabi babanta dakinsa ,tayi masa sannu da wowa,
Yaga yadda dakinsa yyi kyau,ga wankin da ta yi masa, yaji Dadi sosai ,yaita sa mata albarka,
Yana mata sannu ,nan yabata fura da nono Yace ta dama musu,nan taje ta dauko kwano ta dama furar .
Bayan sun gama Shane,Hafsat tajita ta koshi tayi hamdala,
Suna nan zaune suna fira itada babanta, saiga inna Laure ta shigo,fuska ba yabo ba fallasa.
Takali Hafsat ta ce ke xomuje ga aya can gyad'a ki kaimun karshen layi ki siyar.
Wani mugun Kallo baba ,yawatsowa inna Laure ,cikin kakkausar murya ce,
Y'ata bazatayi tallaba ta girma haka ,aje a lalatamun ita,ki gode wadda ta yi miki abaya.
Cikin mamakin kalaman baba, Laure tace aiko saita dauki tallar nan dan bazan ciyar da ita a banzaba.
Tsaki baba yyi Yace meyahana kisawa ,shamsu ko hanifa tallar?
Aisu sunyi karanta, race ,afusace ,baba Yace ai itama Hafsat din tun kafin takaisu kke aza mata tallar.
Azuciyar Laure race dole in canja boka tunda mutumin nan nason fin k'arfina.
Afili Kuma sai ta harari Hafsat ta ce zakixo muje ko saina mangareki.
Muryar babace tadaki kunnan Laure ,yana cewa inhar kika samata talla wlh bakin aurenki.
Bakiji bud'e take kallon sa ,tace wai sbd yarka kke fadamun haka,
Yace ,eh Kuma ki barmun daki ayanxun.
Ai sai kaji tsit,su Laure ba bakin mgana, anji saki,dan tason kota rabu da Mlm aminu,
Da wuya ta shige ,ga batada hakoran gaba,sunxube ga goshi.
Haka ta fita tana ,mitarta, da zumar saita dau mataki.
**********
Bangaren sir Aliyu kuwa ,haka yakoma gd ,cikin son yaga Hafsat.
Ayanxun haka zaune yake, sai yanzun yafahimci yashaku da Hafsat sosai yyi missing dinta,
Lumshe idonsa yyi yana tuna in Hafsat tana cikin yanayin tsoro tafi kyau.
Murmushi yyi daya tuna lokacin da beda lfy duk ta rude harda kuka tayi.
,ga muryanta me sanyi hade da shagwabarta, muryan momi yaji tana cewa ,
Babana ko tasamu ne ,naga kana ta murmushi, kai daya.
Kallonta yyi Yace wani abun ban dariya natuna mommy shiyasa.
Hmmm banana kenan muje kayi lunch,tashi yyi yabai bayan ta.
Bayan 1 week
Hafsat ce zaune itada Fatima adakinta sunsaka kaya iri d'aya sunyi kyau musammun Hafsat.
Fatima ta kalli Hafsat ta ce oh sis wai baki jajan sir Aliyu, kin manta dashi.
Katsina fuska Hafsat ta yi tace to nikuwa tunawar me zanyi dashi,tunda agd muke ba a skul ba.
Murmushi Fatima ta yi tace amma sis. .labulen da aka daga yasata yin shiru.
Deeni ne yashigo ,ya kalli Hafsat Yace my wife xo ina son magana dake,ina fatan nikikayiwa ,
Wannan kwalliyar,doguwar tsuka Fatima taja dan tayi mugun tsanar deeni,
Da sauri deeni ya kalleta ,Yace ke dawa kke da kikeyin tsaki,
Agadarance Fatima tace da Wanda yatsargu da kansa nike.
Afusace Yace ke kishiga hankalinki wlh namiki shegen Duka ,inbatamiki wannan fuskar taki.
Mik'ewa tsaye Fatima ta yi race ,da allah mlm ka kama kanka dukana sai ruwan sama ,
Shima sai inna tsaya,katabani saikayi babban nadama arayuwarka,
Ai raggon nmj shike dukan mace,nan ta hau xaginsa da turanci da gayamai magana,
Itadai Hafsat batace komaiba ,tashige gaban Fatima ta na cewa ta kyalesa.
Shikuwa deeni kwa k'walwa bakomai sai iskanci bemajin me Fatima kecewaba yadai San turanci take.
Belt yake kokarin xarowa ahaukansa yadaketa baba yashigo Yace yafitar masa dg gida.
Fatima ta Kalli Hafsat ba yan baba yafita tace.
Wlh da sake haka kawai wani banxa yarik'a kiran ki da matarsa sai kace da gaske ke matar sace.
Cikin damuwa Hafsat ta ce to sis yazanyi shiyasa in ina skul hankalina kwance.
Nan Fatima ta ce ni natafi marece yyi,nan ta raka har k'ofar gdn su, takoma gd.
Da misalin 9:00 pm Hafsat ce kwance sai tunanin sir Aliyu take,takasa bacci,
Tana tuna bayason ganin wani ya zalinceta ko yaganta cikin kunci.
Ahaka bacci Yy gaba da ita,
Washe gari, bayan Hafsat tagama Duka aiyikanta tacema baba zata tafi islamiya .
Nan yyi mata addua ta fita,gidansu Fatima taje ta biya mata suka wuce tare...
Sir Aliyu ne kwance ,yana bacci amma Kuma yana murmushi.
Hafsa ce yagani ,wani suna tare sai was on guje guje suke suna dariya
Can yahango wani mutum baki k'irin bama a ganin fuskarsa,
Yatafi gunsu ,yasa hannu zai ja Hafsat ita Kuma tasaka ihu ta rike sir Aliyu.
Nan sir Aliyu ,yarika Jan Hafsat yanason rabata da mutumin amma taki saketa
Da kyar sir Aliyu ya kwaceta a hannunsa bayan yasha wuya.
Dede nan sir Aliyu yafarka yyi sharkaf da zufa....
Share pls.
NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿29&30
Addu a yyi, yana tunanin anya Hafsat ta na lfy, kuwa,atake yatuna ,wancan mafarkin da yyi sadda katti suka shigo musu.
Kwata kwata yashi ga ko kwanto,haka yatashi ,yashige toilet yyi alwarla yafito yanufi masjid.
Yadade a can ,Kuma yasaka Hafsat a aduarshi Allah yasa ,tana lfy.
Sannan yanufo gd,yana tunanin labarin Hafsat da Fatima tabashi,sai yanzun yaga wautarsa dabe tambayi ,
Garinsu ko anguwarsuba,wata zuciyar tace to inkasanima,inkaje kacemusu me?
Matsayinka na medinta ,zakaje afilili Yace a malaminta.
Dede nan yashi ga parlour, tunkan ya ida shigowa yakejin kabeer ,k'aninsa me bi masa.
Yana waya da mace sai wannan lallabata ,yake yanacewa baby kada kidamu zanshigo anjima ,kimun kwalliya kinji.
Ilov.... Duguwar tsukar da sir Aliyu yaja ne ,yasa kabeer kin karasawa ,yyi saurin kashe wayar.
Yana Sosa kai, harara sir Aliyu ya aiko masa da ita ,tare da cewa tsoron Allah zakaji ba mutum ba.
Wai duk Dan alsbd mace kake wannan rawar kan ,hmm indai matane gaka gasu.
Mommy ce ta karaso,Dan duk tanajinsu,dariya tayi tace ah ah babana, kabarshi yyi soyayya,
Tunda kai bazaka yiba,sai kazama tuzuru munbada kai sadaka, ai kabeer ya isa fara kula mace,
Yanada 27 years ace bazai kula ,mace ba, dukda kaimai 35 kaki aure,dukda kai kaso,
Hade rai yy Yace to nidai mommy abar maganar, shikuma ,yaje yyita soyayya, anacikin haka,sa ada ta shigo dawowarta kenan dg islamiya,
Ta fada jikin sir Aliyu, tare da cewa ,yaya nagaji,wlh, dan tureta yyi Yace to sarkin son jiki,
Tunda kin gaji saiki sauketa akaina ke bakison kin girmaba,turo baki tayi tace yau wa yaya,
Wai ina wannan Hafsat din take?
Atake yaji gabansa yafadi, amma dayake jarumine ,be nuna hakanba, agundure ,Yace oho ,aidayake da ita zanrika yawo,bacin kinsan anyi Hutu.
Lah hakane yaya ,amma gobe tunda Tuesday muje ka kaini gidansu inaso tazama kawata.
Hararanta yyi Yace surutunki marar ma,ana ya isheni, dan tana dalibata ,dole sai nason gidansu.
Juyawa yy yanufi. Part dinsa, yabarsu, nan ,mommy ce ta kalli sa ada ta ce ,wacece Hafsat ? Kuma.
Sa ada ta ce, dalibarsace ,mommy kinganta kyakkyawa ta hadu karshe wlh,
Shiru mommy ta yi tana tunani ,anya ba akwai wani abu ba ,dama ta lura kwana2 nan Aliyu na yawan tunani ,kodai so yakamashine?
Hmmm kodai minene zan cigaba dayimasa addu a,""";;;;
***********
Hafsatce zaune a tsakar gidansu ,tagama ayyukanta ta gaji sosai ,ga girki a kicin data idar.
Inna Laure take jira tazo ta raba amma ba ta fito ba
Tana zaune anan baba yashigo,yanata fara a,fuskarsa shar da farin ciki, yanzun yaji sauki banda sanda yake yawo.
Yakalli Hafsat yace sannu yar albarka,kinji,murmushi tayi ta masa sannu da zuwa,tace babana,
Da alama yau kana cikin farin ciki, yau Yace kedai bari, yau nasamu jarin da zandogara da kaina kema na miki abinda kkso.
Murmushi tayi tace Allah yatai maka yasa alkhairi, cikin jin Dadi Yace allahumma ameen.
Inna Laure ta fito dan ta labe bakin window taji duk abinda suke cewa,
Tace Ashe ansamu abinyi shine kk'i fad'amun sai yarka kke fadamawa,to ai naji dg gobe ,zakaci gaba da kula da gidanka,
Kuma ka biyani kudin da naciyar maka da yara,ehe, ko kallon inda take baba be yiba,yashe daki yabarta nan.
Hafsat itama ta bisa,ai sai Laure ta hau aika mata da zagi da tsinuwa,
Sannan ta ce kinja ma kanki, bazakici abincinnan ba dukda ke kika girkasa.
Adaki baba da Hafsat sun ba banxa ajiyar ta sunshareta sai firarasu suke.
Can Hafsat ta ce baba bara naje gidansu Fatima,murmushi yyi Yace adawo lfy tasaka hijab ta fito.
Inna Laure dke cin abinci tayi dariyar mugunta hade da hataran Hafsat tace to yawan maular za ako,
Saidai kije can kyaci abincin amma bawai na gidan ubankiba,
Itadai Hafsat batace komaiba tafitarta,tanama inna Laure,adduar shiriya.
A parlour tasami Fatima,da ummanta suna Kallo,da gudu Fatima ta yi hugging in Hafsat suna dariya.
Hafsat tagaida umma,ta amsa cikin sakin fuska ,nan Fatima ta ja Hafsat ska tafi dakinta.
Suna shiga Fatima ta bude wardrobe, ta fito da yunifoam da checks, dinkakku tace sis ga kayanki dazu aka kawosu dg gun dinki.
Umma ce ta dinka mana, cikin jin Dadi Hafsat ta ce ,nagode Allah yasa ka da alkhairi, Baku gajiya da mun hidima,meye zanyi insaka muku sis keda iyayanki.
Murmushi Fatima ta yi tace, kibarmun godiya ,dan bbu ita tsakanunmu,nadaukeki,yar uwata ta jini.
Murmushi Hafsat ta yi tace, Allah yabar zumunci,nan Fatima ta kira me aikinsu ta kawo masu abinci sukaci tare da Hafsat.
Bayan sun gama, Fatima ta ce, sis hutufa yakusa karewa sbd ke ma zamu koma ,ka,ida ko kin huta,
Da jarabar Laure da deenin bantsarnan.
Hafsat tace eh nasani ai gara mukoma ka,ida zai fi gaskiya, Kuma kinga ,
Wahalar mu tazo karshe damun koma third term za a bamu shadows babu batun xuwa compound,
Hankali kwance kayita karatunka,eh wlh sis nan suka ta6a ,sai gab da magrib sannan Hafsat ,
Ta fito tayima umma godiya sosai sannan taje gd,
Bayan1 week
Yau yarage jibi su Hafsat zasu koma a skul,mlm aminu yyi mata provision nagani nafada yasa adakinsa yarufe sai ,
Sai ranar da zasu koma zai fiddo mata sbd yasan halin Laure zata iya sace kayan.
Hakan yyima Hafsat Dadi,dan yanxun jinta take kamar ko wace y'a.
Damuwarta ,daya shine sanin halinda mahaifiyarta take cikine.
Saidai ita da babanta basu sareba dayin addua ba dare ba rana akan allah yabaiyanata.""""
Alh Suleiman rabone ,wato senator zaune a dining area shida iyalansa suna cin abincin .
Dayake duk dare gaba daya sukeyin dinner.
Sa ada na kusada dadtnta tana shagwaba,
Daddy yy gyaran murya Yace wai aliyu yaushe zakayi aure ne wai?
Nagaji da ganinka a haka duk randa ka cikamun ciki,sadakarka zanbayar kaji nagaya maka.
Sosa kai yyi Yace daddy adan k'aramun lokaci,zan fitar.
Itakuwa sa ada sai dariya take jin wai za abada sir Aliyu sadaka in be fitarda mataba.
Sir Aliyu yadago yawatso mata kallon zamu hadu, murguda masa baki tayi,
Atake ya tuna Hafsat,dan itama akwai murgud'a baki.
Murmushi yyi da yatuna jibi ake komawa ,Hutu,, mik'ewa yyi yanufi part dinsa.
Yason yakusa ganin Hafsat dan yyi kewarta da yawa,wata zuciyar tace kasan koba jibin zasu komaba.
Sai sun kara 1 week ,atake murnarsa takoma ciki, amma yadau alkawarin xuwa jibin in basu dawoba to sai yadawo gd.
____________
Yau asabar Kuma gobe su Hafsat ke komawa, zaune take tana daka yaji a turmi.
Gasu kuli da mai a gefenta cikin roba ,tanata dai shirye shiryen ta.
Tana tuna k'ila gobe kamar yanzun suna skul ,k'ila ma taga sir Aliyu.
Batason sadda tayi murmushiba,said tsintar muryar deeni tayi yana cewa,
My wife da alama kinfara sona gashi kina murmushi da kka ganni.
Doguwar tsuka taja rai bace ,tace kai wawa ,jakancinka ya isheni haka nan.
Kada kasake kirana da matarka, dan bazan taba zama mallakinkaba .
Laure ce ta fito zani a hannu cikin masifa tace karya kke wlh Bakida mj sai deeni.
Ki rubuta ki aje na fada Miki wlh, dariyar bosawa deeni yakece da ita ,
Yace lallai yarinya wuyanki yyi kauri ,nikike gayama magana haka,hmm ai wlh koban aureki ,
Tabbas sai na lashi zumarki kota halin kak'a,dan kudina bazasu tafi abanxaba.
Laure tace kada kada kadu ,batada miji saikai,aitakusa gama Wannan k'addararrar makarantar.
Muryan baba sukaji Yace ,gsky kunyi kyan kai kedashi ,
Inaso kusani ,bazan aurawa y'ata dan iskaba sai mutumin kirki, Kuma bazan mata auren dole ba.
Maganar karshe kada kasake shigomun gd,yakalli Laure Yace ,
Ke Kuma kibi sannu da duniya, duk randa ta huta miki baya bazakiji da dadiba.
Ashe ke deeni ya kalli baba Yace ,wlh daukewar numfashi kawai zata hanani shigowa gidan nan,
Amma gani canma nashigo, murmushi baba yyi Yace allah yabaka sa,a.
Nan deeni yafita afusace yabar gidan,inna Laure tashige daki tana surutanta.
Baba yakalli Hafsat Yace kashe kayan kikai daki tunda kin gama .
Ki kyalesu kada kidamu ai nine mahaifinki ko to bazan badake ga deeniba.
Nan ta kwashe kayan ta bi baban daki, tashirya komai da komai nata tafiya kawai take jira.
Ina mika godiyata ga duk masoyana aduk inda suke ,inaganin comments da godiya da addua agareni ,nagode sosai ina mugun yinku irin sosai dinnan.😍😍🌹🌹
Love u all💋💋
Share pls
NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿31&32
Washe gari ,bayan duk Hafsat ta gama abinda take tashirya kayanta tsab a trolley.
Lokaci kawai take jira, yyi dan da karfe4:00pm,zasu koma skul din.
Bacci taje tayi bata farkaba sai, 3:00pm ba bata lokaci ta shirya cikin check pink dinta.
Tana fitowa dg daki Fatima nashigowa,tace sis kinde gama had'a kayanko?
Eh Hafsat tace,nan takama mata suka fito da kayan driver yasa a boot,suka shige mota, yajasu,suka dau hanyar skul.
6angaren sir Aliyu kuwa,beson daliliba yau yanajinsa cikin farinci,karfe 4 a skul dinsu Hafsat tayi masa.
Dede bakin get yazauna kusada baba me gadi,yatsare k'ofar get din da ido.
Ba a fi,30 minit ba da zamansa ,saiga su Hafsat da Fatima suna shigowa da kayansu.
Kwata kwata Hafsat bata lura da sir Aliyu ba ,shikuwa yakafeta da mayun idanunsa, yana Kallo.
Can tana kokarin komawa tadakko wasu kayan dan har Fatima ta koma,kamar ance ta juyo jin kamar kamshin turaren sa, da sauri tawaiga carab idanunta cikin na sir Aliyu.
Gaba daya yakasa dauke idonsa akanta,ita kuwa sunkudda kanta tayi.
Cikin husky voice insa Yace ke zonan ,shiru tayi batace komaiba, yasake cewa bazakizoba ko?
Turo baki tayi tace sunana Hafsat,murmushi ya kubce masa dama zolayarta yake,ganin ga baba me gadi yasa yarabu da ita.
Fatima ce ta dauko sauran kayan nan ta ga Sir Aliyu, tagaidashi,sannan yatashi dg bakinget yanufi office.
Hafsat data dauko sauran kayan,tasaci gundayake zaune da Kallo taga wayam bbu sir Aliyu.
Tsintar kanta tayi da kinjin n dadin tashin da yayi.
Jiki ba lakka suka koma hostel dan jera kayansu,Fatima na lura da ita kamar tana cikin damuwa.
Shikuwa sir Aliyu gd yakoma sai Monday zai dawo.
Washe gari, suna gaban class zaune Hafsat ta hango sir Aliyu zai bude office dinsa.
Da sauri ta tashi ta karasa,bakin office din,cikin sanyin murya tace yaya ina kwana.
Harararta yyi Yace kirik'e gaisuwarki ,kinji,ko?
Kallon sa tayi tace yaya miyasa?
Tsaki yaja yashige office dinsa yabarta tsaye.
Cikin jin haushin barinta da yyi ta koma class dinsu.
Bayan kwana2 ba laifi students andawo,skul din takara yawa.
Su Hafsat na tsaune a class ,saiga wani guy ba laifi yahadu yaci wankan kananun kaya, Kallo daya zakamasa kasan beda kunya waishi kamal.
Yashigo bayan sungaisa da class yyi introducing din kansa,akan ammasa transfer ne ,zai rik'a daukarsu chemistry.
Sai wani kallon yan matan class din yake yana wani murmushi, can yahango wata ,budurwa Yace wow baby yasunanki?
Wata had'add'ar murya mai zaki' hade da taushi yaji tace pls uncle ba tambayar suna zakayiba ka fara mana abinda yataramu anan.
Da sauri yajuyo yakalli Hafsat,a azuciyarsa kuwa cayake wai allah yaxuba halitta anan wannan kyau ,kamar aljana.
Cikin iyayi yaketa kallon Hafsat Yace ok ba damuwa.
Yatsina fuska tayi dan ita kwata be kwanta mataba,ita tama k'agara yagama yafita sir Aliyu yashigo.
Dan da yafita zai shigo,haka yaci gaba da explanation, Rabi yana kalle yammata.
Amma yadarsa wani nufi aransa game da Hafsat.
Har ringing anyi amma yaki fita,saima ya matsa gun sit dinsu Hafsat, yanabinta da shu ummin kallon.
Dede nan sir Aliyu yanufo class din dan prieod dinsa ce,kawai yahango sabon malamin da aka gabatardashi dazu agun sauran teachers.
Gaban sit dinsu Hafsat yana mata shu umin kallo, damashi sir Aliyu hakan yaji be masaba sadda aka nunama teachers.
Wani abu yaji yatokare masa kirji atake yaji mugun tsanar uncle kamal ta shigesa.
Shikuwa kamal sai kallonta yake Yace tabasa not book dinta ze duba wani abu,kafin Hafsat ta ce wani abu, Fatima ta ce ,uncle ga sir nan awaje kai yake jira kafita dan kashiga period dinsa.
Kallon Fatima yyi azuciyarsa Yace kema xamuje dake .
Nan yafita,yakalli sir Aliyu yabashi hannu sukayi musabiha yayi tafiyarsa shikuma yashiga class din.
Fuska a tamke bbu wasa dan yau miskilanci ya motsa ko tambayarda yake mata be mataba .
Haka yyi lesson ,kowa ya natsu sosai gudun kada yasa mlm rabe ya suburbud'esu,haryafittta ta be kalli inda Hafsat takeba.
Itakuwa fushi take dashi ,kan disgin da yyi mata washe garin dasukadawo skul.
Bayan antashi ,su Hafsat na bakin tape ,sir Aliyu yazo zai wanke hannunsa ,tana ganinsa da sauri tabar gun.
Shikuwa mamakinta yyi ,nan yatabe baki yawanke hannunsa ya wuce office.
Haka akayi kusan kwana4 in Hafsat taga sir Aliyu saitabar gun in Kuma class dinsu yashigo bata kallonsa kota yarda su had'a ido.
Tun abun be damunsa har yafara tambayar kansa ,wai me yarinyarnan take nufi ne wai?
Wata zuciyar tace kashareta kaima,wata tace tokodai kayi mata laifi ne .
Tashi yyi ya lek'a window ,atake yaji gabansa yafadi, ganin uncle kamal yana kokarin tsaida Hafsat ita Kuma zata class nasu .
Da sauri yazagayo yaga tatsaya suna nesa da juna,fuska adaure yakarasa gunsu,ko kallon kamal beyiba ,Yace ke xo nan.
Da sauri kamal Yace mlm yi hakuri zan aiketane,wani kallo sir Aliyu yawatsowa kamal,
Atake yasha jinin jikin sa sbd sir Aliyu akwai kwarjini,
Cikin isa da bada umarnin sir Aliyu Yace ,bana bukatar sa insa dakai dan kai basa ana bane,Kuma da ba,itace bace katsaidaba bazan kulakuba daga Kai har ita.
Harara ya aikama Hafsat Yace ,kifada masa matsayina agunki.
Hafsat takalli uncle kamal tace ,Yayana ne...
Doguwar tsuka sir Aliyu yaja Yace ,oya kiwuce kitafi class kafin na sa6amiki.
Nan tajuya tashiga class ,nan sir Aliyu yawatsawa kamal wani kallon kyama yawuce abinsa.
Shikuwa kamal yatsorata da sir Aliyu Kuma yadauka yayanta ne uwa daya uba daya, dan har wani kama yaga sunayi.
Sannan yaga kaf malamai bbu Wanda yyi haduwar sir Aliyu da ita wanka,da hawan babbar mota.
Azuciyarsa Yace anya gara kawai na rabu da yarinyarna danko mun gwada k'wanji dashi da alama ni zansha wuya dan dg gni karfaffane.
Da wannan tunanin yatafi staffroom.
Ana tashi braek sir Aliyu yanufi kitchen yaja kujera ya zauna ,yana kallon yadda ake raba abinci,
Can yahango Hafsat da hannu ytimata alama tazo,nan taxo ta duk'a gabansa,
Kallonta yyi Yace daga yau kada insane ganinkin tsaya da wannan yaron kina jina koya kira ki kice masa na hana ki, xuwa .
To tace ,amamakinsa yaga hawaye da sauri Yace mene kike kuka fadamun me aka miki kinji??
Turo baki tayi cikin shagwaba ta ce bakai bane ka disgani sai Karina shareni.
Murmushi yyi jin ba wani abu bane kedamunta,ba ahankali Yace to naji nadena shikenan ko?
Shiru tayi,Yace hhafsatttttttt!
Kallonsa tayi tace share hawayen kidena saurin kuka kinjiko?
Share hawayan tayi yace yauwa kokefa to yi mun murmushi kinji.
D'agowa tayi suka had'a ido ,atare suka sakarma juna murmushi.
Ahankali Yace ,sa ada na gaidake sosai.
Murmushi tayi tace lah yaya ina amsawa ,nima ina gaida ita dama inason taxa ma kawata.
Murmushi yyi Yace itama haka tace ,amma banda momina kike gaidawa ,sa ada kawai zance kina gaidata.
Da mamaki ta kallesa tace to inagaida momin itama,tafad'a had'e da tashi tsaye.
Kallonta yyi Yace ah ah saida na rokar mata,sa ada kawai zan fadama wa.
Dariya tayi tace inbaka fada ma mominba zamu bata ,nan ta ce sai anjima ganin dinning ba mutane sosai.
Har cikin ransa yaji dadin yadda ta nuna kulawarta ga familynsa.
Yau Yakama Friday Kuma yau wasu dg cikin ss3 da ss2 za a tafi dasu outing a wata skul boarding ta maza.
Cikin waddanda aka xaba harda Hafsat ,zasuje ayi debate dasu.
Da sir Aliyu be yi niyar zuwaba ammajin da Hafsat za aje Kuma skul din ta mazace sai yayi niyar binsu.
Nan students din da aka zaba suka shige skul bus din makarantar ,malamai 4 daxa ayi tafiyar dasu su shige motar sir Aliyu suka dau hanya..
Barkanku da dare my fans .
😍😍
Share pls
NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿33&34
Readers gsky abinda kukamun banjin dadi da yawanku ba dukaba suna korafin in kara typing, kusani sbd page din beda yawa sosai nike 2 page arana .amma bazaku godeba sai arika bina a PC anacewa page yyi kadan nakara typing.
Ai nima inada hidindimuna ,amma nake 2 page. Wasuma korafin nasu har agrp suke to wlh in akanemi abatamun rai zandena 2 page arana koma nadena typing din gaba daya.
Bayan sun iso skul din ,hole din makarantar suka shige,kasancewar yuk students din skul din na ciki.
Bayan annutsu angabatar da ,dkyl dinsu Hafsat aka fara debates.
Hafsat ce takasance second speaker,ta fito cikin nutsuwa ,hade da kamun kai,tafara sakin point .
Gaba daya skul din sunyi mamakin kokarinta,dantabirgesu,ss3 kuwa ta tafi da imaninsu.
Shikuwa sir Aliyu duk wani motsinta akan idonsane,gaba daya hankali sa na gunta dan itama tna satar kallonsa.
Gab da ankusa gama debate din lokacin sallah yyi.
Nan akayita fita students da teachers.
Sir Aliyu ne yake sakkowa kan step din hole din dan zuwa masjid,wasu as 3 maza nagabanshi.
Yaji daya yace kai gsky babyn nan ta hadu da yawa wlh har naji tamun wlh.
Dazamu ganta dana shigar da kainaagunta.
Dayan yace ta kwana gidan sauk' I nasanta ai a unguwarmu take ,amma ina zatan bata sanniba dan tana da tarbiya bata shiga huddar kowa gsky.
Amma ai tana masjid muje muyi sallah tukum saimu dubata.
Sir Aliyu wani yanayi na Bacin rai yaji yashiga afili yace oh ji dan Allah wai yara kanana,harsunsan soyayya.
Ko secondary skul basu lammalaba,suke cewa wai wata ta musu ,tsaki yaja yawuce masjid din dake skul din,na malamai,da niyarsa yaje na cikin garin.
Amma jin kalaman yarannan sai yafasa dan bayaso su tsayar da Hafsat.
Bayan sir Aliyu ya idar da sallah, yafito ya nufo hole din, dan yaduba Hafsat ko tana ciki.
Kamar dg sama yahangota tare da yarannan suna mgana.
Wani fad'uwar gaba yaji Wanda besan dalilinsaba.
Yadago dan niyar yawuce,suka had'a ido da Hafsat yabanka mata harara.
Da sauri tabar gun,harda dan gudunta, ta nufi sir Aliyu.
Da sauri tace yaya wlh nasansu ,dayan dan anguwarmu ne.
Tsaki yaja yace to sai me dan dan anguwarkune?
Kin ji nace miki wani abu ne ,zaki iya komawa gunsu,Ku cigaba da mgana.
Ni zancire hannuna akanki,tunda bakyajin magana,kinfi son kibatamun rai.
Bejira abinda zatace ba yashige hole din, ransa abace.
Hafsat ma bi bayansa dan shiga ciki,jiki a sanyaye.
Aranta tace oh mutumin nan yacika saurin fushi,ga zuciya, lallai matarsa na fama da shi wlh.
Jitayi gabanta yafadi data tuna koya yanada mata,wata zuciyar tace tome ruwanki in yanada mata.
Tsaki tayi a fili tace ballema daga ganin sa beda mata,da wannan tunanin ta zauna.
Tana satar kallonsa taga fuskar nan tasa murtuk,saitaga yafi kyau in yadaure fuska.
Shima sir Aliyu anasa bangaren bayan yashiga hole din, saidayaga Hafsat ta shigo sannan hankalinsa yakwanta.
Nan dai aka ida debate din, skul din su Hafsat ta yi weaning.
Nan suka shige mota, dan komawa skul din su.
Koda suka iso,ban sun firfito dg mota, sai satar kallonsa take,taga yarufe motarsa yawuce,beko kalli gun datake ba.
Nan suma su ka wuce hostel dan hutawa sbd agajiye suke.
Washe gari after break, labour ce da asistanta,bayan window din class dinsu suna mgna .
Ahankali labor tace wlh inaso kafin mubar skul din nan inyiwa yarinyar nan bakin fentin da bazata manta dani arayuwartaba.
Dayar tace ai matsalar wannan mugun dan zafin kan ,yayanta kinsan bazai bariba.
Lebou tace danaso muyi mata sharrin Sata,ko muhada Baki da js 1or2 muce tanason batasu wato tayi lesbian dasu.
Tafine raf raf raf sukaji abayansu ara Zane suka juyo,dan ganin wanene?
Sun dan tsorata,da ganinsa,bakowa bane sai uncle kamal ,kasancewar harda ss3 yake dauka chemistry.
Ahankali yace duk naji abinda kke tattaunawa akai ,bari naxagayo akwai gudumuwar da zan Baku aciki..
Nan yafita yazagaya yasamesu ,yace abinda nike so daku guda dayane kuyimun dubara ,Ku kamun ita sai nayi repping dinta inaga zaifi.
Shewa sukayi su kace uncle aikinka na kyau ka kawo shawara ,saidai yadda zamu kawota gunka batare da kowa yagammuba.
Dariyar keta kamal yyi yace shawara ta rage taku,dan nidai tunda naganta na kwadaita da ita.
Tunda a step quarters nake ,Kuma Ku Pripet ne baa hanaku zuwa bayan isha I yau sai Ku kaimun ita gidana.
Nan sukace kada kadamu ai burummu yacika sbd Pripet gaba daya muntsaneta .
Sir Aliyu yaci mana mutunci sbd ita ,yadixgamu sbd ita dan tana kanwarsa.
Kamal yace bari naje naga students na kallonmu kada agane akwai wani abu tsakanunmu.
Har yajuya yace ai zaku gne gidan danike ko?
Sukace eh sai bayan isha in ,nan yyi tafiyarsa ,sukuma suka koma class.
**********
Da dare bayan sungana shirya yadda plane nasu zai kasance .
Sai sukaje bakin dakinsu Hafsat suka tsaya,ckin sa sai ga Hafsat zata shiga ,dawowarta dg masjid kenan.
Dayake akwai hasken farin wata,sunganeta.
Da sauri daya tace ke zo nan ,ba musu Hafsat ta je ,kayane a trolley suka bata sukace biyomu dasu,ba musu taja trolley ta bi bayansu.
Fatima ce ta fito zuwa tape dan wanke hannunta.
Kafin ta ida isowa taji wasu Pripet na cewa yanxunnan naga yar iskar tabi bayansu da trolley ,din Muka bada shawara abata tabisu dashi yadda zasu kaita cikin sauki.
Dariya daya tayi tace ai sir Aliyu in yaji amma kanwarsa fyade yazaiji?
Kuma mun shirya yadda za ayi ,bayan komai yafaru,sai ace ita tazo gunsa,har gidansa kinga sai akoreta ,kilama ahada da sir Aliyu shima mugu.
Nan sukayi shewa baki daya sukace ai duk Wanda yashiga gonarmu a skul din nan ,zaisha wuya.
Dede nan Fatima ta juya asukwane ,da mugun gudu tana kuka ,hade da adduar kada allah yabasu. Sa ar abinda suke shirinyi.
Ko 7 minit batayiba ta isa gidan sir Aliyu, ko knocking bbu ta banka kanta ciki.
A parlour tasamesa zaune yanashan coffee.
Ko sallama batayiba tana nishi ta kora masa , bayani.
Azabure ya mik'e yana cewa,meyasa sukeson ganin rayuwarta ta kuntata ne?
Muddin hakan ta faru wlh har principal din skul dinnan sai abun yasha feta.
Dan bazan dagawa wa kowa bace wlh dan sai sun koni wanene da dalilin dayasa nashigo skul din.
Ko ta kalmi besakaba suka fito asukwane shida Fatima.
Suna isa suka sami gidan kamal arufe,sun murda k'ofar amma gam take.
Azuciye had'e da fad'uwar gaba Sir Aliyu yyima k'ofar naushi biyu ta bude.
Suka kunna Kansu cikin gidan.........
Yawan comments yawan typing😍😍
0 comments:
Post a Comment