Ahankali tace to insha Allah, amma kaima yaya kacika ,saurin fushi karage, murmushi yyi yace to zandenama baki daya. Haka yacigaba da driving dinsa yana tunani azuciyarsa shin wacce anguwa zasu nufa gashi yace mata yason anguwarsu can dubara tafado masa dayatuna aiyasan gidansu Ahmed Nasir kuma Fatima tace s makwabtane dasu Hafsat, kawai sai yanufi can anguwar Hafsat kuwa murna tayi Ashe da gaske sir Aliyu yasan gidansu,muryansa taji yana cewa gobe zakije gun deener din? Bata kallesaba tace eh insha Allah ahankali yace goben zanxo da karfe 7:00na kaiki ko,to tace ganin zai wuce gidansu yasa tace yaya yyi nan katsaya da sauri yace Aina San nan ne zan saukeki parking zanyiko,ahankali yatsaya tabude zata fito ,hafsatttttttttttt! Yakira sunanta ahankali kallonsa tayi yace to saida safe kink'agara kije gd ne murmushi tayi tace ehmana yace to nacema sa,ada kina gaida ita da sauri tace eh wai yaya ni yaushe zatazo gidanmu ne ahankali yace saikin fara zuwa gidansu t uro baki tayi tace shikenan ,amma goben kasameni gidansu Fatima yac meyasa?tace hakanan OK yace tare da cewa ko murmushi n baza amunba sai narok'a murmushi tayi masa ,harda daga masa hannu ta rufe motar bebar gunba saida yaga ta shiga gida tukum sannan yyi tafiyarsa.
Agajiye takoma gida bayan tacire kayan tayi wanka tayi sallah.
Fura kawai tasha dan Laure tadena bata abinci kumafa tanasata aiki,taje tayima baba saida safe takwanta.
Amma me data rufe ido sir Aliyu take gani yana mata murmushi.
Itama murmushi ntayi afili tace oh yaya sarkin fushi sai kuma tayi yar dariya dahaka bacci Yy gaba da ita.
A6angaren sir Aliyu shima hakan take dan yana kwanciya tunanin Hafsat ya addabesa.
Tunawa yyi da wayarsa da sauri yadauka yashiga video, yaita kallon irin yadda take shagwaba da murguda baki sai murmushinsa yake shi daya.
Can kuma yabud'e pics yana ganin wani itada Fatima wani ita daya.
Can yaga wani ita daya tayi wani fitinan nan kyau Atake yamayardashi akan screem din wayar.
Sai kallo yake yana tuna gobe k'ila tafi haka kyau tunda betaba ganinta da parsonal ba.
Wayarce tayi ringing yaduba yaga Zakiyya ce tsaki yaja afili yace aikin banxa wasu matan ba class wlh .
Tunawa yyi da irin kamun kai had'e da tarbiyya irin na Hafsat yyi murmushi afili yace ke dabance acikin mata .
Kashe wayar yyi ganin xata matsa masa yyi kwanciyarsa cikin farinciki.
Washe gari takama Friday, Hafsat tun10:am tagama shara da wanke wanke ta gyara dakin ta dana babanta.
Tana zaune dakinta saiga baba yashigo da shirinsa zaije kauye sariin kayan miya dana masarufi dayake siyarwa.
Kallon Hafsat yyi yace, yar albarka ni tafiya zanyi kuma nasan sai gobe zan dawo sbd inason insami daurin auren yaronnan Ahmed, tunda kince zakuje parti yake ko mene?
Murmushi tayi tace party baba deenar ko ,yace to kidai kula da kanki kinji dannaga abun nagidane shiyasa nabarki,inkun dawo kinga dare yyi kikwana gidansu Fatima dan nasan Laure zata rufemiki kofa da wuri .ahankali tace to baba nicanma zanje ayimun kunshi bari nabika mufita kada inna ta hanini fita,to yace sannan yyita mata nasiha takula da kanta nan tadauki abinda zata bukata tarufe dakin suka fita itada baba. Laure nadaki ita da y'ayanta suna tsinewa Hafsat.
Har bakin get din gidansu Fatima baba yyimata rakkiya sannan yatafi.
Tun a compound din gidan suka hadu da Fatima ana mata kunshi,murmushi Fatima tayi ta harari Hafsat tace shine jiya bbu ban kwana ko kikayi tafiyarki.
Dariya Hafsat ta yi tace sorry sis yanzun in angama miki waza'ayimawa?
Fatima tace ke mana dama niyata in angama bakixoba naje gd nakiraki,amma dai kinxo kenan harzuwa lokacin deenar bazaki koma gd ba sai dare.
Murmushi Hafsat ta yi tace eh, nanma zankwana,ihunmurna Fatima ta yi tace pls da gaske kike?
Hafsat ta ce eh, bari naje dakinki na aje kayana mugaisa da umma,Fatima tace ok nan tayi cikin gidan bbu jimawa tadawo anagama wa Fatima itama akafara mata .
"""""" sunkai awaya guda da wani abu sannan akagama ,bayan yabushe ta wanke kada kuso kuga yadda kunshin yyima Fatima da Hafsat."'''''';;
*****************
Sir Aliyu ne zaune a part dinsa ,yana ta aikin tunanin Hafsat jiyayi yanason ganininta nan yatashi yadau key din mota yabar gidan.tunani yake shin inama zai fara zuwa Aida kunya yanuna gun Hafsat yaje saima ayimasa wata fahimta,bari yaje gidansu Ahmed Nasir kawai tunda har gidan yanashiga dukda yadade rabonsa da gidan gsky inyaje yaga Fatima k'ila takira masa Hafsat da wannan yyi horn gidansu Fatima get man yabudemasa get ,bayan yyi parking yafito da niyar shiga cikin gidan ,dedegun wasu flowers yaji sweet voice din Hafsat ta nacewa nifa sis bawani kitson da za,amun steaming kawai zaki rakani amun ko ammun Kitso zai warware,Fatima tace aike kinfini gashi ni kaina zaiyi Kitso ai,hararanta Hafsat ta yi tace kodanafikin saidai ko tsawo amma ba yawab...........maganar ta makalemata sakamakon sir Aliyu da suka yi ido biyu dashi yana nufo inda suke zaune.........
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿55&56
"da sauri Hafsat ta sunkuyadda da kanta k'asa."
Shikuma yakafesu da idanu yana aikinkallo.fatimace tayi saurin gaidashi,ya amsa had'e da tambayarta ko Ahmed na part dinsa?
"Fatima ta mik'e tace bari naje nagani ko yayan naciki." Nan tabar gun ,sir Aliyu yakalli Hafsat yaga kanta aduke.
" ahankali yace to bara nakoma tunda bakyason ganina?"
da sauri tace ah ah yaya bahaka bane, ina kwana?
"Murmushi yyi yace lfy lau." Muje inkin shirya nakaiki gun steamin dinko?"
da sauri tace ainafasa zuwa ma yaya, da idanu yatsaretadasu yana kallon k'unshinta yana yaba kunshin azuciyarsa.
"Mik'ewa tsaye yyi yace jeki saka hijab dinki muje banason musu ko gaddama."
Adedenan Fatima ta iso cikin girmamawa tace sir yayan bayanan.murmushi yyi yace kada kidamu zankirashi ma,dama yafad'ane dan karsu Dhaka itada Hafsat gun Hafsat yazo shiyasa yanuna gun Ahmad yazo.
""" Hafsat kuwa Jan Fatima ta yi gefe waitazo tarakata sir Aliyu zaikaita gun steaming. """"
Fatima tace sis bazaniba kije dan Allah kina bata masa lokaci gsky,haranta Hafsat ta yi tace wai bazaki rakaniba da gaske?
"Fatima tace eh,"
Hafsat ta kalleta tayi kwaba taje zaki nemi wani abu guna nima,tafad'a had'e da Barin gurin.
"Shikuwa sir Aliyu yacika yyi fam da shanyawar da Hafsat tayimasa".
Jira kawai yake takara 5minit inbatazoba yyi tafiyarsa,can sai yahangotota jikin madubi ,yacigaba da kallonta harta iso gun motar.ahankali ta kwankwasa yabud'e mata, murmushi tayi tace yayanah kayi hakuri nabarka kanata jirana ko? da d'in maganarta yaji besan likacinda yyi murmushi ba.motar yatada yace bakomai my sister kinsan inaji dake ne zanjiraki ko minti nawa zakiyi,amma wanne colour din kaya zaki saka agun deener din?
" ahankali tace gawnt ce dark blue da yarciki fara"!
Murmushi yyi yace kice zakiyi kyau sosai ko ?
"Batace komaiba",
Juyoya yyi yace wanne gu zamuje ayimiki steaming din?
Turo baki tayi tace duk inda kakaini yyi,ok kawai yace yacigaba da driving dinsa.
dede gun wani shago nayin gyaran kai yyi parking, kallonta yyi yace inazuwa bejira amsartaba yafita. Jim kad'an,yadawo yace kije zandawo nanda 30minit to tace tafita.
"""" harcikin shagon ta shiga nan suka hau yima steaming din kasancewar bab layi har aka gama .aka gyareshi ga bant akayima donut sai yyi kamar tasaka acuci maza. Sai fuskarta tasake fitowa gwanin sha,a
Wa ,tana daura dan kwalinta sir Aliyu yakira matar awaya yace Hafsat ta fito n an tafito ,sai kallonta yake shiko ba make up ganin kyawunta yake.bayan tashiga yajamotar suka fara tafiya."""";;;;;;;
Can Sir Aliyu yace Hafsat dina kinajin yunwa ko?
"Da sauri tace ah ah naci abinci!
" ahankali yace Toni meyasa baki tambayeni nima naci abinci ba?"
Cikin shagwaba ta ce yaya aikai babbane nasan kaci ma abinci ,nikuwa yarinyace shiyasa ka tambaya ko naci hakane,?
Murmushi yyi yace bahaka bane, ninagama bakyamurna da zuwana gunki,kallonsa tayi suka had'a ido tayi masa dariya.
"Tace wlh inajin farinciki inmuna tare bama murnaba kayarda?, ahankali yace nayarda tawan.murya k'asa k'asa tace yaya kazomin da sa,ada yace me zaki biya nazomiki da ita? Turo baki tayi tace oh yaya komai saikace saina biya,indebaza kazo min da itaba shikenan."""";;
Dedenan kuma suka iso k'ofar gidan su Fatima,Hafsat takallesa tace yayanah nag.....shiittt yace babu godiya tsakanunmu ki kulamun da kanki kinji?
" wani killer smiling tasakarmasa tace to kaima ka kulamun da kanka, allah yakiye kagaida mundasu mommy, kuma kaci abinci da yawa inma bakaciba jikina zai bani.""
Cikin jin dadin kalamanta yace to Tawan nima haka bye bye suka ringa d'agawa juna hannu har yabar gun cike da farin ciki.
********************
Da misalin karfe 3:pm sir Aliyu ne a dining area, sai cin abinci yake axuciya rsa yanacewa nasan yanzun jikinta yabata inacida yawa nasan kuma zatayi farinciki da hakan.
Mommy datayi masa kuri da ido tana mamakin wannan cin abincin dan tunda take bata taba gani yaci abinci da yawan hakaba.
"Kallonsa tasake tace wai babana me yasameka kake cin abinci haka."
"Cikin subutar baki yace hmmm inaso naci da yawane dan nasan Hafsat zatayi farin ciki da hak......", da sauri yyi shiru yafara tarin karya danbesan sadda maganar tafitoba.itakuwa mommy axuciyarta ta tabbatar da zargita na sir Aliyu yafad'a tarkon soyayya, kuma tabbas yarince hatsat."";;
Ruwa sir Aliyu yasha sum sum yabar parlourn danjin kunyar da yyi.
Bayan sallar magarib Sir Aliyu yashirya cikin suit dark blue sai yarciki fara, yasaka takali da agogo farare,yyima jikinsa wankan turare yaja motarsa yadauki hanyar gidansu Fatima.
Akuma lokacin hafasat da Fatima sungama shiryawa cikin gawnt dinsu ga make up ammusu sunsha kyau kamar kasace su kagudu ga kamshi natashi ajikinsu.
"""""" yanzun haka suna tsaye a compound din gidan,Hafsat tace kinga sis yayan shiru be zoba! Kallonta Fatima ta yi tace k'ila yana hanya kuma ke zai dauka tunda akwai wadd'anda zasubini kinsan bayason surutu muje wajema kada yaxo yyita jiranki nan suka fito kuma alokacin sir Aliyu yyi parking. "";;
Zuge glass din motar yyi ga haken fitilun k'ofar gidan sun haske ko ina Atake yahangosu wani sanyi yaji am ma yaso Hafsat ta sa kodan gyale ne sbd kada ayita kalleta ,haka yafito fuska ba walwala yana yaba kyawunta azuciyarsa Hafsat naganinsa taga kaya kala daya suka saka itadashi wani dad'i taji da sauri harda dan gudunta ta nufi gunsa,dan tamanta da Fatima na gun,Fatima naganin haka takoma ciki dantafito da sauran yan,uwa sutafi danga motoci yayanta yaturo akwashe mutane.
" kafeta yyi da sexy eyes dinsa ,tana isowa tasaki murmushi shima murmushi yyi mata yace kinyi kyau tawan amma bana hanaki yin guduba?"
Turo baki gaba tayi tace na manta yi hakuri kada kayi fushi dani.
"Dariya tabasa sosai ganin ta turo dan bakinta gaba", saida yadara yace to muje ko?
Bud'emata gidan gaba yayi tashige hade da Jan rigarta dke Jan k'asa,shima yashige yaja motar duk sunyi shiru su duka,shi yana tunanin dasunje mazan gun zasuyita kallonta ,ita tanatuninin dalilin yin shirunsa.da haka suka isa hotel d'in da za'ayi deenar din.
Gaba daya gun duk yanmata da maza anfito dg mota ,ga tauwagar ango can gefe suna layi ,mace gefe namiji gefe,ango da amarya na gaba ,MC sai cewa yake muna Neman babban aminin ango ,inyanagun ya,iso dan Allah shi kawai ake jira amarya da ango su shiga ciki.
" duk abinda ake fada akunnan sir Aliyu da Hafsat. "
Amma basu fitoba ,can yabud'e motar yakalleta yace muje ,ahankali suka jera suka nufi gun,gaba daya anmusu caaaaaaaaaa da idanuwa.
Ango kuwa yasha mamakin ganin sir Aliyu da Hafsat atare amma baice komaiba.
Wasu sun birgesu,wasu masu son sir Aliyu sunji tsanar Hafsat .
Haka suka tsaya bayan ango da amarya ,sainan nan sir Aliyu yake da Hafsat duk wani motsinta aidonsa.
Bayan anshiga ciki ,MC yagabatar da abinda yatarasu,yabukaci abokin ango yazo yabada tarihin ango.
Cikin kasaita had'e da aji sir Aliyu yamik'e tsaye dan tafiya,Hafsat naganin haka fuska ba walwala ta kauda kanta gefe da sauri yace mene ne ?gayamun kinji?
"Ahankali tace bakaine zaka tafiba kabarni", da sauri yace inxakije to muje? Nadauka bazakije ba shiyasa amma kid'anyimun murmushi kinwani d'aure fuska .
Murmushi tayi tabisa sukace yakarbi laspeaker yafara bada tarihin ango da harshen turanci har yagama.
Wasu y'amma dke gefe daya ta ce kai gayen nan yaga hadu kamar karya dena magana ,voice din sa tamun,itakuma waccan chiweengum din tawani manne masa duk inda zashi tana biye dashi harda wani saka kaya kala d'aya dashi.
D'ayar tace da gaskiyarta wlh dankoni nasami wannan dole nalik'e masa ,aibatayi wasaba,wlh Sundance da juna sosai ji kayansu kala d'aya naji harsun burgeni.
" MC ne yafara kiran sir Aliyu dan yaxo yazauna kan high table kusada ango".
Aiko yatashi had'e dacema Hafsat suje ahankali tace ah a h yayay kaje niba ka'awar amaryaba aibana aibana zauna a high table ba."
Fuska adaure yace muje nace,ba musu ta bisa akahau musu tafi raf raf,bayan sunxauna akakira k'awar amarya tazo,kuma gunda zata zauna nanne Hafsat ta zauna.
"Agadarance kasancewar tunda taga kyawun Hafsat taji tatsaneta,tace ke mlm zaki iya tashi wani kallo Hafsat ta watsamata had'e da Jan tsaki."
MC yalura da hakan yaxo yace pls kiyi hakuri nan zata zauna kitashi.
Tunda akafar abun sir Aliyu bece komai sai sannan jinkalaman MC yasa yace fine Hafsat muje dan bazan iya zama gun da bbukeba dan nan duk band'aukesu mataba ,muna matane.
Anglo yaya Ahmed yalura da hakan da sauri yagirgixama mc kai alamar yabari. dan yasan sir Aliyu kaifi dayane har gun deener din zai iya bari yyi tafiyarsa.
MC yajuya yacigaba da aikinsa,itakuwa yarnyar ta zauna wani gun cike da jin haushin kalaman sir Aliyu...
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿57&58
""""""bayan MC yagama kiran abokan ango dana amarya,yasaki kid'a. Sir Aliyu kuwa gashi ga Hafsat gefe yana kallo itakuwa kanta aduke sbd kallon jama 'a yyi mata yawa."""
Can MCyabuk'aci ango da amarya had'e da k'awayansu su fito fili su cashe.
"Fatima ce taga Hafsat batada niyar tashi xuwa gun rawar hakan yasa tanufi gunta.tana xuwa taja hannun ta tace muje dan Allah bansan musu.
Kallon sir Aliyu tayi dan tantana gudun yimasa laifi,shikuwa ganin haka yasa yad'agamata kai alamar taje.
Nan suka tafi gun rawar ,shikuma sir Aliyu beda niyar tashi Balle yaje gun rawar.
Wani abokinsane yata6osa yace friend wad'annan yaran k'annanka ne?"
Fuska atamke yace eh kasan bansan tambaya ko?
Murmushi yyi yace gsky wadda taxo taja hannun wadda kuke tare yanzun tamun dan Allah kaji!
Tsaki yyi yace saikaje kashigar da kanka nibazanjawa kaina rainiba gun yara.
"Amma azuciyarsa yaji Dadi daba Hafsat yace ta masaba."
Juyowa yyi yaga har Al-ameen ya isa gun rawar yanata yiwa Fatima lik'i,dubawa yyi yaga Hafsat tsaye wasu maza su ukku suna mata lik'i da y'an dubu dubu d a sauri ya mik'e tsay ejin wani abu yasoki zuciyarsa,yanufi gun tareda fito da dollars yan ammuru ka,yana xuwa yafinciki hannunta fuska a tamke yakaita dedegun da amarya da ango suke yafara mata lik'i da dollars. gaba daya kallo yadawo gunsu ganin bbu namijin da yyi lik'i da dollars sai shi, sa ida yalik'e mata Rafa biyu sannan yy iwa ango da amarya
"Ahankali sir Aliyu yarik'e hannun hafs at yasaka mata Rafa daya,yakai bakinsa saitin kunnanta yace nima yimun lik'in ,yafad'a yana murmushi itama murmushi tay I adede nan camera man yadaukesu pho to."
"" Ahankali Hafsat ta rik'a yiwa sir Aliyu lik'i suna kallon juna suna murmushi hartagama masa,ya jata sukabar gun .""
Bayan sun zauna me photo yaxo yaba sir Aliyu dan shi yad'auka su masoya ne.karba sir Aliyu yyi yabashi kud'in yatafi.
Kallon pic in kawai yake ganin irin kyawun dasukayi a pic din,satar kallon Hafsat yyi yaga hankalinta baya gunshi,da sauri yad'aga suit dinsa yasaka pic din .
Wayarsa ce ta yi ringing, yana dubawa yaga daddynsa ne.
Kallon Hafsat yyi yace Hafsat dina bari naje waje nayi waya nadawo.
Turo baki tayi ta kauda fuskarta gefe,girgiza kansa yyi yace oh Hafsat rigimarki tayi yawa meye abun fushi anan ?
"Cikin shagwaba ta ce Toni saika tafi kabarni ni daya."
Murmushi yyi yace aikema d'axun kinje gun rawa kin barni ko?
Wayar ce ta sake ringing, cikin rarrashi yace bara naje kinji tawan kinga dad d'ina ke kirana, kanta tad'aga da sauri yabargun.
Samir da dama haka yake so ,sir Aliyu nabarin gun yazo yazauna gunda yatashi,ahankali yace ranki yadad'e! Ykk ya gida??
Batare da takallesaba tace lfy atak'aice ,samir yace dan Allah ke k'anwar Aliyu Suleiman rabo ce?
da mamaki Hafsat ta kallesa tace lfy daiko ,meyasa kamun wannan tambayar?
Samir yace wlh inasonki ina kaunar ki bada wasaba amma naga Aliyu yyi Kane Kane yaha na kowa kulaki,shin e nike zaton kodai k e ba k'anwarsa bace pls kifad'amun gsky kinjiko.Hafsat na shirin yin magna taj i k'amshin turaren si r Aliyu,da sauri ta d'ago kanta sukayi I do biyu dashi,Atake taji gabanta yafad'i ganin yadda idanun sa sukayi jajir fuska rsa ad'aure bbu ala mun wasa ga jijiyoyi n kansa suntashi rad'a rad'a alamar ra nasa ab'ace yake.
Da sauri yabar gun Hafsat ta rufa masa baya tana kiransa ko juyowa beyiba ,yashige motarsa yajata atsiyace.
Shikuwa samir dalilin dayasa yatambayi Hafsat shine yana zargin kamar sir Aliyu sonta yke.ganin abinda yafaru yanxu yasa ya yarda sonta yake dan yaga zallar kishi akwayar idanunsa.
Hafsat kuwa cikin kuka ta dawo dan tacewa Fatima gida zata je.
Tana cikin tafiya hankali tashe ko gabanta bata gani,taji muryar Fatima na kiranta da sauri ta juya taganta tare da Al-ameen tsaye suna magana.
"Ahankali Fatima ta zo gunta tana tambayarta lfy meya faru?dantaga lokacin da sir Aliyu yafito afusace taga Hafsat ta bisa yashige mota be saurari Hafsat d'inba.
Cikin kuka Hafsat ke labarta mata komai ,had'e da cewa yanxun yatafi yana fushi dani kadama yyi accident da gudufa yabar gunnan.
Rarrashinta Fatima ta yi tace sis Ai Sir bazai iya fushi dakeba,gobe zaku shirya kinji.
Cikin kuka Hafsat tace ni mukoma gd yanxun,Fatima tace ai anma tashi danyanxun12: fa .
Hafsat ta ce wancan gayenfa?
Murmushi Fatima ta yi tace abokinsu yayane wai sona yake ni....shiru tayi ganin Al-ameen yanufosu.
Yana zuwa yakalli Fatima yace baby nah kinga antashi muje nakaiku gida.
Da sauri Hafsat tace to, Fatima nahararanta ,nan sukabisa yabud'e ma Fatima gidan gaba yace my Princess kishiga nan ko?
Da sauri Hafsat ta turata murmushi Al-ameen yyi yace friend pls kishigardani gun my Princess naga kamar bata sona.
Murmushi yak'e
Hafsat ta yi dan gaba daya hankalinta nagun Sir Aliyu, tace ai inde wannan ne kada kadamu zata soka,murmushi yyi yace Allah yasa, nan yashige gidn gaba yatada motar suka nufi gidansu Fatima.
6angaren sir Aliyu kuwa driving yake zuciyarsa na tafarfasa hade da k'una,axuciyarsa yake hangen fuskar samir da Hafsat .tambayar kansa yyi me samir yake nufi? Kada dai yace da gaske son h afsat yake! Taf dole yyi maganin samir akan yabar kula k'an warsa inbahaka ray uka su b'aci.wata zuciyar tace masa to kai sonta kke ne? Tsaki yyi afili yace habadai aibazanso D'ALIBATA ba gsky danni har yanxun banga wacce nakes oba.amma kuma agefen zuciyarsa jin zafin samir yake da haushin Hafsat data kulasa yake.
Haka yyita tunanin xuci da tambayoyin da beda me amsa masa su.
Daga karshe yyi anguwarsu Hafsat yyi parking can nesa ,yadda baza ,aganshiba.
Dan yad'aukarwa kansa alk'awarin sai yaga waye zai maidota gida ,kuma itada wazasu dawo??
""" befi minti 20ba agun yaga ana maid o mutane ,da sauri yafito yajingina bayansa jikin motar yana ganin kowa.
Can yaga motar Al-ameen yyi parking, Fatima ta fito gidan gaba ,Hafsat tafito gdn baya,sannan Al-ameen yatsare Fatima da mgana .Hafsat nage fe tana jiransu su ga ma tazo sutafi."";;
"Wani sanyi yaji acikin ransa ganin ba samir ya maido hafsat ba."
Kuma yalura da Al-ameen son Fatima yake,tsaki yaja afili yace basuda wani aiki sai suce suna son mace.koma ya SO d'in yake ne?
"Wata zuciyar tace masa oho."
Mota yakoma yajata yanufi gida.
Hafsat kuwa gaba ta yi dan bata iya jure jiran fatima.
Tanashiga cikin gidan straight d'akin Fatima ta wuce,tacir e kayanta tayi wank a,had'e da sallar isha'i.ranta babu dad'i ta kwanta sak amakon fushin da sir Aliyu yake yi da ita,Fatima tayi rarrashin amma Hafsat tak'i Baron damuwa da abun k' arshema tasaka kuka,hakan yaba Fatima haushi dan bataga abun kuka akan abinda yafaruba.saita k'yaleta tayi kwanci yarta,Hafsat bata de ne kukaba saida ba cci yyi gaba da ita.
Sir Aliyu kuwa bayan yyi shirin bacci kewar Hafsat ta ishesa yadauko pic din da akamusu daxu yyita kallo yana murmushi.
Tunawa yyi da d'azun Hafsat ta biyosa tana kiransa yak'i kulata,duk sai yaji bbu dad'i,afili yace allah yasa kada tayita kuka dan nasan Hafsat kuka baya mata wuya.
Gaba daya saiyaji bbu dad'i dan bayason ganin tana kuka.
Tunawa yyi datanada waya da yakirata,afili kuma yace Hafsat tayi k'arama da rik'e waya.
Haka yyita tunanin Hafsat har bacci yyi gaba dashi pic d'insu na a k'irjinsa.
***************
Washe gari haka Hafsat ta tashi idanu duk sun kumbura sbd kukan datasha yi jiya da dare.
Duk sai Fatima ta ji tausayinta ,haka suka yita hidima,Hafsat na sukuku,bayan sunyi break suka zauna ,kasancewar sai karfe2:30pm za,a daura auren yaya Ahmed ,sunanan saiga umman su Fatima ta shigo d'akin tacema Fatima taje can bayan layinsu akwai bak'i taje ta taho dasu ,bazasu ganeba.
Bayan umman ta fita Fatima ta ce kalli Hafsat tace sis muje kirakani!
Hafsat ta ce kije kaina namin ciwo ,Fatima tace Allah yabaki lfy dan ta lura batasan rakata,nan tasaka hijab ta fita.
Sir Aliyu kuwa koda yatashi da tunanin halin da Hafsat take ciki yakeyi,yanxun haka gaban dinning yake zaune gasu mommy da kabeer da sa,ada da sadeek suna fira ana break amma shi yakasa cin komai tunanin Hafsat yake,can yamik'e ,mommy tace babana ina zakaje?
Da sauri yace xanje gun telan danaba yyi mun d'inkin d'aurin auren Ahmed begamaba bari naje.
Bejira amsarta tafita yaja motarsa ,bai tsaya ko inaba sai gidansu Fatima.
Ya na fitowa Fatima na dawowa da mutanen dazasu je gidansu.
Da sauki ya tsaidata ,mutanan suka wuce ciki,yakalleta bayan sun gaisa yace Fatima kifada mun gsky kada kimun k'arya ina Hafsat tayi kuka jiya kobatayiba kifada mun dan Allah.......
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿59&60
"Ajiyar zuciya Fatim a tayi tace", gsky sir tayi kuka dan haka nature d'inta yake,b atason yiwa mutum laifi koda yarone ga ba daya saita damu. Nibanma son kai ta yiwa lafiba naga dai tana kuka nabata b aki amma taki haku ra har na k'yaketa y anzun haka tana ci kin gidan .
" ahankali yace jeki kiramun ita kinji dan Allah ki lallab'ata."
Nan Fatima ta ce to ta nufi cikin gdan.
Shikuwa sir Aliyu du k tausayin Hafsat yajeji axuciyarsa,yak'agu taxo ya rarrasheta .
Fatima nazuwa ta sameta zaune tayi tagumi ,tace sis ki zo sir Aliyu nakiran ki awaje.da sauri ha fsat tace sis dgaske kike?
Fatima ta ce eh am ma ni shawarar da zanbaki kada kije.
Da sauri Hafsat tace me yasa ?
Fatima ta ce haba mana kema kija masa aji kuma in ki n masa laifi kidena saurin kuka.
"Yanxun bara naje n ace masa na lallab' aki kink'i zuwa,alam un kema kina fushi dashi sosai.
Nan Hafsat tace to shikenan sis ,fatim ata fita tasami sir Aliyu, tasanar dashi yadda suka tsara .
Cikin damuwa yace wai da gaske bazat ata zoba tayi fushi s osai?
Fatima tace eh gsky sir,girgiza kansa yyi yace to shikenan a mma dan Allah kiku lamun da ita ,natafi yafad'a had'e da shiga mota yabar gun.
" Fatima taje tasanar da Hafsat yadda sukayi da sir Aliyu, tace sis yafa damu kinga yadda yawani marairaice wai dan Allah nakulamishi dke.murmushin jin Dadi Hafsat ta yi, nan suka tashi Hafsat ta cigaba da walwalalta cikin jin dad'in sir yadena fushi da ita.
Sir Aliyu kuwa duk yinin ranar beci komaiba sai tunanin Hafsat da halin datake yakeyi.
Ana yin azahar yyi shirin zuwa d'aurin aure ,cikin shadda light blue tasha dinkin hannu yar ci ki da babbar Riga sai kamshi yake. Yanufi gun daurin auren ya k'udurta aransa ko cikin gidan ne sai yashiga yaga Hafsat dinsa ya rar rasheta ta dena fus hi dashi.bayan anga ma d'aurin aure duk abokan ango suka bisa zuwa cikin gida nsu,shima Al-ameen yaci marun d'in sha dda yanaso yaga sa hibarsa wato fatima .
Har ciki suka shiga adede compound din gidan duk mutanene kuma ha fsat da fatima nagu nsun saka anko d'insu sunyi kyau so sai .sir Aliyune yahango Hafsat take away ahannunta tarike ta nama fatima gwalo, murmushi yyi afili yace sarkin tsokana.
Karasawa yyi gun ,saidai kawai Hafsat ta ji k'amshinsa da sauri ta juyo sukayi 4eyes.
Wani killer smile yasakarma,saita turo baki tajason tagudu ,da sauri yatare gabanta,fuska kalar tausayi yace haba mana tawan nifa bakonkine ,kuma anason ka girmama bak'onka shine ni kike guduna zakiyi tafiyarki kin kyauta?
Murgud'a dan bakinta tayi tace to yaya bakaine jiya kayi tafiyanka ba kabarni,ni ina ruwana dakai tunda banda wani mahimmanci agunka kanaso nayita kuka dan namaka laifi.
"Ahankali yace I'm really very sorry kinji tawan ,banso kina fushi dani, dakuma yawan kukanki ,Amma kema kin fad'ane kawai aikin San nadamu dke sosai.
Shiru tayi ,yace meye a take away din?
" anhankali tace snacks ne."
Murmushi yyi yace to nike nan baza 'a baniba saina roka?
Kinga ga fatima can tanaba Al-ameen ha rma murmushi take yimasa ,Amma ni k'inki mun ko?
Cikin shagwaba ta ce, aiyanxun zanmaka bamun shirya ba .
Wasu kujeru dake gefen flows suka koma suka zauna, sir Aliyu yace hafsatttttttttttt dina!
Murmushi tayi tace yayanah,shima murmushi nyyi yace ai yanxun munshirya kindena fushi dani ko?
Ahankali Hafsat tace eh yayanah munshirya dariya yyi ,yafito da wayarsa yace kinyi kyau sosai bari nayi miki pics ko?
Ba musu tace to dan batason su cika fada dashi.
Nan yyita mata masu kyauhar yagama,yakalleta murya k'asa k'asa yace pls Hafsat d'ina kada na koma ganinki da kowa ne namiji kinjiko.
Ahankali Hafsat tace to yaya koda d'an uwanane?
Tunawa yyi da fatima tace masa Hafsat ce first born agidansu batada yaya,Amma axuciyarsa yace bari nagwadata shin tad'aukeni d'an uwanta bazata boyemun komaiba.
Kallon ta yyi yace Hafsat ,inaso kifada mun labarinki kuma ke wacece?
Da sauri ta kallesa da mamaki afuskarta,yad'aga mata kai alamar yana sauraronta.
Axuciyarta taji bazata iya boye masa komaiba,nan taduk'ar dakai tafara sanar dashi tarihin rayuwarta da labarin yanxun batason ina mahaifiyarta takeba.takuma sanar dashi labarin deeni gidoga.
Sir Aliyu yatausaya mata,har idanunsa sunyi jajir sbd koda can baya akwai abunda fatima tab'oye masa a labarin Hafsat.
Abu biyu yatsare masa arai,shine ba'ason ina mahaifiyarta takeba sai labarin deeni gidoga.yaji zafi aransa sosai da Hafsat ta ce wai har my wife deeni gidoga yake cemata,ya k'udurta aransa duk ran da yagamu da deeni saiya koyamasa hankali.
Kallon Hafsat yyi yaga tana hawaye,ahankali yamik'a mata hand chief yace ki goge hawayenki insha Allah za'a ga mama kinjiko.
Kuma shi baba ai lfy kuke dashi ko?
Ahankali Hafsat ta ce eh.
Mik'a masa hand chief din tayi murmushi yyi yace nabarmiki,duk sadda kika tuna dani toki kalli hand chief din kiyi murmushi xanji hakan ajikina.
Murmushin jin Dadin kalamansa tayi tace to Yayana nagode sosae Allah yabar zumunci.
Murmushi yyi yace ameen bbu godiya atsakanunmu.
Amma dai shi wannan deeni bedai yunkurin tab'aki ko?
Hafsat ta ce eh ai babana bazai bariba yanxun haka ma yahanasa shiga gidanmu.
Wani sanyi yaji axuciyarsa jin be yunkurin tabata kuma anhanasa shiga gidan.
Kallon ta yyi zomuje kirakani tawan kinji,murmushi tayi tace to yaya muje.
Har get suka fita ,yabud'e mata mota yace kishiga ranki yadade.
Murmushi tayi tace yaya kacika zolaya Allah kuwa,shiga yyi yaba motar wuta yace ai gsky na fad'a.
Kallon ta yyi yace wlh Hafsat banson muna batawa dake ko inga kina kuka pls kedena kinji tawan.
Murmushi tayi tace to yaya nah bazan koma yin kukanba ainima banason Bacin ranka wlh duk inkana fushi dani banajin Dadi arayuwata.
"Ahankali yace nima haka."
Parking yyi gaban wani shopping male, suka fito yace muje nan sukayi ciki...
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾 story & written by mmn fareesa
🅿61&62
Suna shiga Sir Aliyu nagaba Hafsat na baya , fannin kayan sawa sukayi .
"Ahankali sir Aliyu yace kixabi duk abinda kikeso kinji,murmushi tayi tad'an fara zab'a ,ga nin bata wani dauka yasa da kansa yashi ga jidar mata kaya h artace ya,isa amma be saurateta.dayaga abu sai kiji yace wa nnan zaimiki kyau ko?itadai sai tayi m urmushi kawai.
"""" haka yyita jidar mata kayan sawa da na kwalliya. "
Sungama siyan kom ai har sun biya,yatu na dawani turare ,da sauri yace Hafsat nayi mantuwa muje ki rakani ,mak'ale kafada tayi alamar bazatajeba ,murmushi yyi yace nine fa yayanki,hararansa tayi tace eh d'in,murmushi yyi yace haba yarinya nikike harara ko?
"daga masa kai tayi alamar eh, da sauri ya biyota tasaki ledar kayan ta zura aguje yarufa mata baya."
Sai d'an zagaye gun suke suna dariya abinsu, wasu na kallonsu suna birgesu.
Hafsat nashan yar kwana ta shigo fannin kayan provision, cikin gajiyawa tace yaya pls natuba muje narakaka kadauki abinda ka manta.
Sir Aliyu dke bayant a yana shirin yin mgn, kawai yaga Zakiyya itada wani d'an iskan boy friend d'inta.tasha kananun kaya surar jikinta abayyane,kallon sir Aliyu tayi da mamaki ganinsa tare da wata tace yaya wannan wawiyar ,jakar ina kasameta daga gani ta had'a iri da mayu, wa'annan kwala kwalan idanu nata haka.sir shiru yyi bece komai yanajin zafin kalaman da Zakiyya ta alak'anta Hafsat dasu. Saima yajuya yacigaba da duba wasu kayayyaki dke gaba nsa.
"Hafsat kuwa sarki ntsoro tana ganin y adda Zakiyya ke zare ido gata babba sai tasha jinin jikinta,tadawo bayan sir Aliyu tatsaya."
Zakiyya cikin jin haushin kin tankata da sir Aliyu yyi tace wai yaya Aliyu baka gannibane ina magana ka share?
Sir Aliyu yajuyo yakalleta sama da k'asa yyi murmushin takaici yace naganka me zanmaka ne?
Cikin mamaki Zakiyya ta ce kamar ya naganka saikace ni namiji ce ne?
d'aga kafada yyi alamar ko ajikinsa yace eh aini nan duk nan gurin Bacin wannan yanuna Hafsat dke bayansa yace banga mace anan gunba,dakai da wannan sokwan muna mazan duk daya na daukeshi dke.sannan daga yau kika sake kiran hafsat da kalmominki na hassada agareta sai nayi k'asa k'asa dke kamar yadda nakoyawa Mubarak hankali akan nagaba dashi. dan wannan dkike rainawa daya ce tamkar da dubu ,tafiki daraja ,matsayi ,aguna ,danke baki isa tayi magana dkeba sbd bakida d'a'a ,da tarbiya,itakuma bata hudd'a da marar tarbiya ,yana kaiwanan ya finciki hannun Hafsat sukabar gun azafafe.
"Cikin matukar jin kunya hade da bakin cikin kalaman sir Aliyu, Zakiyya tabar gun ko sallama batayiwa boy friend dintaba .
Shikuwa sir Aliyu suna barin gun yasake mata hannu yaje yad'auki ledar kayan suka fita.
Acikin mota yana driving yanajin d'acin kalaman Zakiyya datajefi Hafsat dasu ,axuciyarsa yace kwata kwata basuda tarbiya yan gidansu ko kad'an inbacin yanagudun Bacin ran su daddy da yyi mata abunda zatayi nadama har gaba ,da abada dan duk Wanda yanemi yataka Hafsat sai inda karfinsa yaka'r e.kallon ta yyi yaga alamar taji zafin kalaman Zakiyya,ci kin rarrashi yace kiyi hakuri kinji my hafs at zanyi maganinta banason Kisa damuwa aranki kinjiko?
" ahankali tace bakomai yaya yawuce nifa bandamuba."
Kallon sa tayi tace gidansu fatima zaka ajeni?
Batare da yakalletaba yace eh aizakije gun walimar gobe ko ? Tace insha Allah.
Koda suka iso yyi parking, dazata fito yasake cewa my Hafsat kiyi hkuri kan...da sauri ta katsesa da cewa kadaina bani hakuri yaya niban dauki abun wani laifiba.kaje gida kayi bacci kafin LA,asar dan Allah inkak'i jikina zai bani hakan murmushi yyi yace to namiki alk'awari my Hafsat zanyi yadda kkso. Yasake cewa kikulamun da kanki, nan yafito mata da kayan shopping din ta karba had'e da cewa nagode sosae Allah yak'ara budi yyima dukiyya albarka.
"Cikin jin dad'in kalamanta yace ameen,baibar gunba saida tashige ciki San nan yaja motar yanufi gd.
Hafsat nashi ga direct d'akin fatima ta wuce da kaya nik'i nik'i ahannunta.
Bayan ta zauna tasanar da fatima sir Aliyu ne yyimata shopping, murmushi fatima tayi tace mungode sosai gsky.
Hafsat ta ce mubarsu sai bayan biki muraba saiki kai mun gd kice abbankune yasiyamana tare.dan bansan yaya zanyiwa baba bayaniba gsky.
Fatima tace eh hakanma yyi ,nan suka chigaba da firarsu.
****************
Zakiyya kuwa rai bace tabar shopping male din ta nufi gida.
Tana shiga tasami mommy n ta da mubarak yayanta za une a parlour. da gudu ta fada jikin mommy ta saki kuka,nan mommy ta shiga tambayarta dalilin kukan dan dama itace ta bata yaranta ta kuma shagwabasu.
Cikin b'acin rai ta sanar da ita abinda sir Aliyu yyi mata akan wata.
Tsaki mommy ta yi tace wlh dakinbi nawa da kin hakura da yaronnan, yanun a baya k'aunarki ke. Kuma kinnace mas a yana wulak'antaki. Gashi yyimiki irin wannan tozarcin gaban bainar jama,a barito alh yadawo kaji d'an iskan yaro nanfa tahau tsinewa sir Aliyu had'e da aibatasa.
" Mubarak dke gefensu bece komai ba sbd be mance, suburbudarsa da sir Aliyu yyi ba dayaso yiwa daddy nsa rashin kunya. Tun daga lokacin yke masifar tsoransa.
Washe gari, sir Aliyu yana d'okin zuwa gun walima yaga Hafsat dan jiya saida yyi baccin datace yyi,yanaso yje gunta yatambayeta taji ajikinta yyi baccin ko be yiba.yana zaune daddy yakirasa yanxun yaje Lagos gun wasu kayansa,kamar yyi kuka yatafi ga bbu lokaci Balle yaje yyima ta bankwana.
6angaren Hafsat ma hakan take,tun 3:00pm take sauraron xuwan sir Aliyu amma shiru har 6:00pm yyi bbu shi ,hardai tacire rai tana tunanin k'ila yanada wani uxuri.
Haka takoma gida cike da tunaninsa,ta natuna tun dg sadda sir Aliyu yash igo rayuwarta tafara samun farin ciki. Tatuna bayan sun had'u a skul tadawo Hutu tasami babanta yashiryu asirin da Laure tamasa yakare. Murmushi tayi afili tace zan cigaba da yimaka addua Allah yasa kana lfy.
___________________
Bayan kwana10
"""" Hafsat ce zaune ita daya ad'akinta kasancewar baba yatafi sarin kaya yau kuma sai jibi sai dawo.fargabanta sh ine tasan Laure zata matsamata da masifarta,ga kuma. Tunanin sir Aliyu dan tafara tunanin anya yana lfy wannan shiru haka ,rabonta dashi kwana10kenan tun lokacin da yyi mata shopping .muryar Laure ce taji tadaki dodon kunnanta,tan a cewa to y'ar so tunda uban naki bayanan shida yadaure miki gindi kiyi yadda kkso ko? To saikitashi ki d'ebomun ruwa dan yau bazan sayi ruwaba ke zaki jidomana su!zaki tashi ko kuwa kintsareni da idanu irin na uwarki.cikin zafin kalaman Laure Hafsat ta tashi tad'a uki bucket tafara jid o ruwa a monon anguwar.)""";;
Sir Aliyu ne zaune a part d'insa jiya da dare yadawo dg Lagos ,gaba daya hankalinsa na gun Hafsat,yanxun haka tunani yake so yake yaje gunta yanxun.
Amma yana ganin kamar bazai gantaba duk da yasan gidansu to in ya aika yace kiranta yace injiwa? Kuma meke tsakanunsu?
"Wata zuciyar tace mutunci."
Tashi yyi be bari kowa yaganshiba yadauki motarsa yanufi anguwarsu Hafsat.
6angaren Hafsat kuwa haka tayita jido ruwa tana cika komai da'ake xuba ruwa agidan.
Komawa tayi ganinn saura d'auka d'aya tagama,ta sake d'ebo na karshe yana a hannunta sai ga deeni gidoga yatafo zaishiga gidansu,dan yakira Laure ko baba nanan tace ah ah bayama gari shine yatafo gidan yanxun.
Da sauri Hafsat ta matsa dan ya wuce amma sai yak'i shiga gidan yyyi tsaye yana kallonta.
Ganin haka yasa Hafsat ajiye bucket din ruwan kasancewar ahannunta yake.
Matsowa yyi gab da ita kamar zai rungumeta my wife nayi missing dinki!
da sauri Hafsat ta ja baya tace mlm meye haka bakada hankali?
Dariyar rainin hankali yyi yace yaude tsoho bayanan Balle ya kwaceki ga hannuna.
Wani mugun kallon tsana Hafsat ta aikamasa dashi tace kai wawa Wanda besan darajar iyayansaba,inbakasan darajarsuba ninasan darajar nawa.
Afusace deeni ya cafki hannun yariketa gam tasaka dayan hannun dan kwatar kanta agunsa.
Adedenan sir Aliyu yashigo anguwar,yana parking yafito,yana d'aga kansa yahango Hafsat tsaye ga wani gardi rik'e da hannunta tanason kwatar kanta amma takasa.
Be auneba yaga yadauke Hafsat damari,wani irin abu sir Aliyu yaji axuciyarsa yace ko wannan ne deeni? azafafe yanufi gun ko motar be rufeba...
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿63&64
Inamik'a godiya ta ga dukkan masoyan wannan novel nagode sosae naga comments dinku bbu adadi agrps da PC ,inamugun yinku irin totally din nan🤝🤝🤝😍😍
Hafsat dke kok'arin kwatar kanta takasa addua ta ke Allah yakawomata d'auki. Kamar dg sama taji muryar sir Aliyu tad aki dodon kunnanta yanacewa mlm saketa!
Deeni da sarai yaji a mma yak'i juyawa b alle yasaketa,cikin karaji had'e da tsaw a sir Aliyu yace bazaka saketaba? d asauri deeni yajuyo sukayi 4eyes da sir Aliyu take yaji wani mugun kwar jininsa azuciyarsa yace ko ina tasami wannan dan gayun dg ganin sa ba dan Nigeria bane gsky.
Wata wawar cafka hade da wani mugun punch sir Aliyu yakaimasa Atake yasaki hannun Hafsat ta koma gefe tana kallonsu.
"binsayyi yacigaba da bashi kyawawan maruka,"
Deeni yaso yafara ramawa,Amma sai yaga abin bahaka ba,cikin yan mintina har jama'a sun fara taruwa suna gani.
Hafsat kuwa duk ta rud'e ganin irin yadda sir Aliyu ke suburbudar deeni,tsoron ta kada yakasheshi.
"Deeni kuwa dayafara jin kamshin lahira tuni yafara cewa ,me gida natuba narabu da ita har abada kakyaleni."
"""" sir Aliyu bedena dukansaba saidayaga baya motsi ,Hafsat hartagaji dabasa hakuri,anacikin hakan wani yaje yasanar da Laure,saigata zani ahannu,ta fito cikin masifa da bala 'I tana cewa ,oh Kaine kwarton nata data turo kayi kisan kai ko? To wlh hukuma zata rabamu bazaka dakesaba kaci bilis Allah kuwa.wani mugun kallon tsana sir Aliyu yawatsawa Laure koba a'fad'ab a yasan wannan ce Laure matar baban Hafsat.cikin isa da gadara yace kafin kikaiga hukumar ni zankirasu su rufemunke da wannan wawan!
Aituni Laure tayi tsit dan saitaji wani mugun kwar jininsa ga kuma akwaita da tsoron hukuma,tafad'ane dan tayi musu burga Amma bawani karar dazatakai.Hafsat ta jefa da wani lallon zamu had'u tace ke kuma karyar maza zamu had'u dke ba gida daya muke kwanaba,ai ubanki zai dawo zansanar dashi maza kika ko ma bi.
"doguwar tsuka sir Aliyu yaja yakalli Hafsat yace muje."
da alamar tambaya ta kallesa, saitaga ya tamke fuska hakan yasa ta bisa.
Laure kuwa mai adaidaita ta tsayar Yakama mata deeni suka saka shi ciki ,suka nufi asibiti dashi danko motsin kirki bayayi.
"Sir Aliyu kuwa mota yabud'e ma Hafsat ,bayan sun shiga yakalleta yace inane inda baban yake zama muje Nayi masa bayani?
" ahankali tace ai bayanan yyi tafiya sai jibi zai dawo."
Shiru yyi can kuma yadauko wayarsa yasaka kira,bayan and'aga yace friend kana ina?
"Ok ganinan anguwarku kafito zamuyi wata magana.
Befi minti,5ba dayin wayar aka kwankwasa glass din motar,sir Aliyu yakalli Hafsat yace jirani zamuyi mgn yanzun zandawo.
"Hafsat tace to shikuma yafita."
Can baya suka tsaya da yaya Ahmed bayan sun gaisa ,sir Aliyu yalabarta masa abinda yafaru yanzun. Ciki tausayi yaya Ahmed yace hmm ai yarinyarnan na ganin abubuwa wlh gwanin tausayi allah dai yasaka mata,sir Aliyu yace ameen.yaya Ahmed yace Amma kai meke tsakanunku da ita? Yatsina fuska yyi yace mefa?inbaccin mutunci,inakuma tausayawa rayuwarta ,kuma d'alibata ce!
"Yy Ahmed yace dalibarka banganeba?" Nan sir Aliyu yabashi labrin xuwanshi skul da governor yyi,sannan yace naga Ku makwabtane shin babanta yanada waya dan tacemun baya gari?
"Yy Ahmed yace eh bari nakirasa ,tunda dai bazamu bari ta koma gd ba ,tunda Laure tayi wannan kalami."
"Sir Aliyu yace hakane."
Nan yy Ahmed yakira baba yasanar dashi komai da kuma taimakon da sir Aliyu yyima Hafsat.
Nan baba yyita sama sir Aliyu albarka,da fatan gamawa da duniya lfy.
Duk sir Aliyu yanaji kasancewar a hansfree yasaka wayar,har cikin xuciyarsa yaji dadin adduar baba yaji kuma kaunar dattijon.
Nan yaya Ahmed ya ce to baba ,Aliyu zai tafi da Hafsat gidansu ta zauna sai jibi inkadawo zai maidota,da gidanmu zata zauna to su umma da Fatima basanan suna abuja,ka,amince dan na yadda da abokina ?
Baba yyi gyaran murya yace to shikenan nima har raina nji na yarda dashi kuma ai malaminsune ,inde bazai sami matsalaba da iyayansa to yaje da ita inkuma da matsala zan iya komowa yau dukda zanyi dare a hanya.
Sir Aliyu ne ya karbi wayar yyi sallama yace baba kada kadamu ,mahaifiyata Nada fahimta kuma zanriketa amana kafin kadawo .baba yace to aliyu nagode sosae Allah yyimaka albarka.nan sukayi sallama sir Aliyu yasaka number baba awayarsa ,yakalli Ahmed sukayi musabiha yakoma mota,Ahmed yabar gun cikeda zargin sir Aliyu son Hafsat yake.
Yanashiga yatada motar yakalli Hafsat yace ,gidan mu zanje nakaiki kizauna sai xuwa jibin in baba yadawo dan munyi waya dashi yanzun kuma ya amince muje,bayan mun isa zankirashi sai kuyi magana ko?
Mak'e kafada tayi tace nidai yaya inajin kunya,bazanjeba kabari naje gun Fatima mana.
Murmushi yyi yace aisu fatima basa gari shiyasa,kuma momin tawa kikejima kunya?
Sunkuyadda kanta tayi tana murmushi,tace wai yaya ina kaje har kwana10 bangankaba?
Ahankali yace Nayi tafiya Lagos ne dadinah yaturani,kuma jiya nadawo da dare yaukuma naji inason inganki shine nazo natarar da abinda yafaru.
Ahankali tace yaya nagode s..... da sauri yace bbu godiya tsakanunmu kidena mun godiya.
Murmushi tayi tace kacancanci hakanne yaya.
Amma ,Sa'ada na gida ?
Murmushi yyi yace eh tana gida nasan zatayi murna da ganinki,Amma zancewa mommy kunyarta ma kikeji.
Turo baki tayi gaba,ahankali yace saina murde wannan bakin da kike turowa gaba.
Dariya Hafsat ta yi tace Taf baka iyawa,kwafa yyi yace haba yarinya zankamakine kin rainani ko,?
Dede nan suka iso gidansu ,yyi horn get man yabud'e masa get yyi parking, Hafsat jitayi gabanta yafadi,haka ta daure ta fito sai tsokanarta yake Amma tak'i kulasa yana gaba tana bite dashi suka shige parlourn gidan...
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story &written by mmn fareesa
Dedicate to all my fan's ana mugun tare,yan nida dalibata grp fan's 3 comments dinku na yau yafi nakowa ina mugun jidaku irin sosai dinnan.😍😍
🅿65&66
Suna shiga sir Aliyu yyi sallama suka sami mommy da sa ada zaune ,sai Mubarak yyan zakiy ya abbansa ya aiko sa gun daddy nsu sir Aliyu,yasami daddy baya k'asarm a. Cikin fara'a mom my ta amsa sallam mar,kafin ta sake mgna taga wata kyakkyawar yarinya na bayan sir Aliyu.
" murmushi mommy ta yi tace bakuwa mukayi."
Aida gudu sa'ada tazo tayi hugging din Hafsat tana dariya had'e da cewa oyoyo my friend.
Shikuwa Mubarak mutuwar zaune yyi ganin wannan sura ta Hafsat me d'aukar hankali.
Sa'ada ta kalli mommy ta ce mommy wannan ce Hafsat.
Da sauri Hafsat ta xube k'asa tana gaida mommy, ta amsa cikin sakin fuska had'e da k'ura ma Hafsat ido tana tuna kamar tasanta ko wani me kama da ita.
"""" shikuma sir Aliyu zama yyi gefen kujera yana me jin Dad'in yadda Hafsat ta girma ma mahaiyarsa,kuma itama mommy ta karbeta da hannu biyu.gefen da Mubarak yake ya kallah dan sai yanzun yalura da shima.kawai yaga yak'ure Hafsat da ido yana mata kallon k'urullah.wani mugun tsaki sir Aliyu yaja Wanda besan lokacin dayayisa ba,hakan yadawo da Mubarak haiyacinsa yadena kallon Hafsat cikin in ina yace yaya barka dah dah ....dare ina wuni? Wani kallo sir Aliyu yyi masa atak'aice yace lfy,na n Mubarak ya kalli mommy yace natafi mommy ,zan sanar da abban daddyn bayanan,nan mommy ta ce ok kagaida yan gidan,nan yafita sum sum.""";;
"Mommy takalli sa'ada tace bazaki kawowa bakuwar komai ba?"
da sauri tace ah ah mommy yanzun zankawomata drinks.
Mommy ta ce oh Hafsat kisaki jikinki kinji nan gidankune naga sai kunya kkeji,sir Aliyu yace hmm mommy haka takefa,yanxunma wai kunya takeji bazatazoba.murmushi mommy ta yi har cikin zuciyarta taji kaunar Hafsat dan ta lura yarinyar Nada tarbiyya da kunya had'e da kawaici,kallon sa'ada tayi tace Auta kuje da Hafsat d'akinki ta huta saikuzo muyi lunch ,nan sa'ada ta ce to takama hannun Hafsat suka mik'e koda zasu wuce saida Hafsat ta saci kallon sir Aliyu aiko shima yasaci kallonta suka had'a ido yakashe mata ido daya had'e da wani killer smile. Abinda basu saniba duk mommy na lura dasu,kuma tagane sir Aliyu da Hafsat suna son junansu, dalilin dayasa tace su Hafsat sukoma dakin sa'ada dan ta tambayesa meke tsakaninsa da Hafsat dan tana kwad'aita masa au ren ta,co's yarinyar Nada kamun kai.
"Bayan su sa'ada sunbar gun mommy ta kalli sir Aliyu tace babana meke tsakaninka da wannan yarinyar kuma wacece ita??"
"Ahankali sir Aliyu yy gyaran murya yafara bawa mommy labarin Hafsat tun daga farko har yanzun da dalilin dayasa yakawota gidan ."
Be auneba yaga mommy na hawaye sbd tsabar tausayin Hafsat.
""""" ahankali tace insha Allah za'aga mahaifiyarta,kuma Laure aniyarta zata bita gara da kakawota nan sai ta zauna har babanta yadawo.sir Aliyu yace eh mommy Ai ankusa ma komawa Hutu dan yau saura8days sukoma,mommy tace allah yakaimu lfy,Amma babana kuna soyayya da Hafsat ko? da sauri yad'an zaro ido yace haba dai mommy d'alibata ce fa! Allah yakiyaye,nibanma San yaso yakeba.
Murmushi kawai mommy ta yi batace komaiba dan ta lura sir Aliyu besan yafad'a tarkon so bane shiyasa yake haka ,Amma zata saka masa ido taga iya gudunsa.kallonta sir Aliyu yyi yace mommy bari naje Nayi wanka!ok kawai tace,amamakinta saitaga yanufi part din sa'ada."""
"da sauri tace baban a kaida zakayi wanka ina kuma zaka?
Waigowa yyi yana d'an Sosa k'eya yace am am dama..dama zansanar da Hafsat zanshiga ciki kada tajini shiru tayita nemana,ko tayi kuk...saurin yin shiru yyi dan yana Neman yin subutar baki.mommy data guntse dariyar datazo mata tace ai baza nemekaba tunda sunsaba da sa'ada.bece komaiba sum sum yy part dinsa.
************
Bangane sa'ada da Hafsat kuwa ,sun baje kan gadon sa'ada suna fira abinsu can sa'a taje ta had'a ma Hafsat ruwan wanka tace sis jekiyi wanka.
Bayan ta fito sa'ada ta fito mata da black arebian gown tasaka,wow sai Hafsat ta yi kamar balarabiya,sa'ada sai wasata take hade da kod'a kyawun datayi take.can sa'ada tace naso ace daddy na yana gari kikazo wlh dan inabashi labarin inada k'awa Hafsat.murmushi Hafsat ta yi tace Allah sarki, Dede nan mommy ta shigo tace yarana kuxo muje muyi lunch, ta kalli Hafsat hade da kama hannun ta tace y'ata kidena jin kunya ta kinji ki daukeni tamkar mamanki kinjiko?
" ahankali Hafsat ta ce to."
Nan suka fito suka nufi dining area, a can suka sami sir Aliyu yasha kananun kaya ,kyawunsa da kamalarsa sunsake bayyana atare dashi.
Murmushi yyi ya kalli mommy yace oh mommy naga baki wani damu dani ba yasu Hafsat da sa'ada kawai kike.
Murmushi mommy ta yi tace eh ta y'ayana nike mana,kai ai kazama tsohon yyi,sa'ada da Hafsat suka yi dariya atare,murtuke fuska sir Aliyu yyi yace kai ina wasa dakune wlh innarike yarinya hmm zata gaya masu,Hafsat ta faki idonsu mommy ta yi wa sir Aliyu gwalo,kallonta yyi yanuna kansa wai dashi take ?d'aga kanta tayi alamar eh, kwafa yyi yamata alamar zai kamatane.
Duk abinda suke mommy na lura dasu tadai sharene.
Nan suka zauna sa'ada tayi serving dinsu,suka fara cin abinci ,Hafsat naci akunyace .
Sir Aliyu ne yak'ara turakafarsa k'ark'ashin table din ,kasancewar suna pessing juna da Hafsat yatake mata k'afa da k'afarsa mai takalmi sawu ciki.
Wani mugun zafi taji,har zata fasa ihu ta tuna inda take sai tayi shiru tad'an rintse ido alamar tanajin zafi.shikuwa sir Aliyu murmushin mugunta kawai yake ,yana satar kallon Hafsat,ita kuwa ta d'auka wani abu ne yadatse mata k'afa ganin sir Aliyu yana murmushi kuma ita yake kallo yasa tagane shine.fakar idonsu mommy ta yi ta galla masa harara,kara take k'afar yyi,da ido take basa hakuri,sai can dayaga dama ya janye kafarsa,itakuwa ta murgud'a masa baki had'e da harararsa, ta had'e k'afafunta yadda bazai sake take mata suna .nan Hafsat ta ce ta koshi sir Aliyu yace aidama mommy haka take batason cin abincin sosai, murmushi mommy ta yi tace kiladai bakunta take mana. nan sa'ada ta ce ita ta koshi ,taja Hafsat sukabar gun.
"Shima sir Aliyu yatashi yatafi masjid."
___________________ Zakiyya ce zaune kan bed adakinta tanajin wak'ar music awayarta.
Mubarak yashigo yazauna kan bed side,yakalleta yace sis yasu nan yarinyar da kikaga yaya ALiyu da ita a shopping males?
"da mamaki Zakiyya ta kallesa tace lfy yaya?'
Murmushi yyi yace ki amsamun tambaya ta.
Zakiyya tace sunanta Hafsat!
Mubarak yace to naganta da yaya aliyu yau agidansu yaje da ita!, kutumar uba zakiyya ta fad'a cikin karaji,murmushi Mubarak yyi yace minene abun tada jijiyar wuya ,ni yarinyar tamun wlh danko bansame taba inason inhuta da ita dan kalar skin d'inta yamun,saidai inatsoron yaya Aliyu wlh dan naga kamar sonta yake.
Wata muguwar dariya irinta basawa Zakiyya tayi tace naji Dadi data maka dan nadau ki alk'awrin kota halin kak'a saina auri yya Aliyu.
" kabarmin komai zanbincike akanta ."
Mubarak yace to shikenan dan ni inzan aureta inaso inkuma bazan auretaba inason in lashi zumarta.
Wani mugun murmushi Zakiyya tayi tace kada kadamu ko satota sai muyi ko mu nunawa iyayanta kudi su aura maka ita.
"Dan ina tunanin yar talakawa ce."
Nan Mubarak yace to shikenan yafita.
Da misalin 8:00pm sir Aliyu yashigo parlourn gidansu yasami sa'ada zaune a parlour ,yace ina mommy da Hafsat?
Sa'ada ta ce mommy na d'aki sallah take ,itakuma Hafsat ta na d'akina tana game.
Da sauri sir Aliyu yanufi dakin,yana shiga yasami Hafsat ta na game tana dariya ,kawai tagansa kamar daga sama.
Kusa da ita ya zauna ya kalleta yace wana kama?
Shiru tayi tana zare ido,can tace to bakaine kayita takemun k'afaba.
Murmushi yyi yace hmm saina gyaramiki wannan bakin da kike turowa.
"Ahankali tace yauwa yaya kiramun baban mu gaisa saika bani inyi game da wayarka.
Kallonta yyi yace bazan kiraba.
Aisaita hau kukan shagwaba harda dire dire ita sai yakira mata babanta.
Sir Aliyu kuwa lumshe idanunsa yyi ,azuciyarsa yanace wa yah salam sakamakon wani abu dayakeji ganin yadda Hafsat ke Wannan shagwaba r dan yalura akwai kuruciya da ita.
Share plsNIDA DA'LIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿67&68
"""" Ahankali Hafsat ta ce bara naje nafad'awa mommy kak'i kiramun baban a."bud'e idonsa yyi yace hmm aibazaki iyaba ,abinda kunya r momin kike,marairaicewa tayi tana lallab'a sa sannan yakira baba n,Hafsat tayi mama kin yadda sir Aliyu ya saba da babanta ganin yadda suke fira dashi.
Sir Aliyu ya mik'a mata wayar yafita nan Hafsat suka sha fira da baba yyita mata nasiha tayi hakuri da rayuwa kuma ta rik'e mutuncinta.sannan sukayi sallama,tafit o dg dakin dan kaiwa sir Aliyu wayarsa."";;
A parlour tasamesu harda mommy, nan taje ta mik'ama sir Aliyu wayarsa sai kallonta yake da idanunsa dasuka canja kala.
Mommy ce tace suje ayi deener,Hafsat tace ta koshi,wani kallo sir Aliyu yabita dashi yace mekika ci da har kika k'oshi?
Sunkuyadda kanta tayi tace nasha fura gun sa'ada ai.
Girgiza kansa yyi yace banyarda fura zata k'osar dakeba oya muje kici abinci.
Murmushi mommy ta yi tana kallonsu cikin birgewada sha'awarsu ,tace kai babana kacika takura dole sai taci aboncinne?kallon Hafsat ta yi tace y'a ta zakici ko kin koshi?Hafsat ta saci kallon sir Aliyu taga yyimata alamar intace ta koshi in yakamata zata gayamusu ai da sauri tace eh mommy zanci!murmushi mommy ta yi danta lura da abinda sir Aliyu yanuna wa Hafsat. Dining area suka nufa,bayan sun zauna mommy ta yi serving in kowa,harsuka gama sannan ,sukayi sallama kowa yawuce makwancinsa.
Washe gari da misalin karfe 6:30am ,Hafsat ce ta fito da ga d'akin sa'ada,kasancewar bayan sun idar da sallah sa'ada ta koma bacci.itakuma ta kasa komawa Dan tasaba agidnsu da anyi sallar asuba Laure zatayi ta sakata aiki,zai zirga xirga take bata waiting parlour bata part din sa'ada,gash I tanason ganin sir Aliyu, kuma batasan inda yakeba,mommy dake part dinta taji motsin yyi yawa ta fito ta sami Hafsat zaune kan carpet ta yi shiru.
"Ahankali mommy ta ce y'ata yaya dai?"
Da sauri Hafsat ta gaida,ita ta amsa fuska cike da walwala,kan kujera mommy ta zauna ta ce zonan kinji,ba musu Hafsat ta je ,hannunta mommy ta kama ta zaunar da ita kusa da ita.tace kifad'amun mekkso?inde kin d'aukeni mamanki kinji?
"Ahankali Hafsat ta ce ina yaya yake banganshiba?"
Murmushi mommy ta yi tace, yana part dinsa ,k'ila bacci yake,amma ai lokacin motsa jikinsa yyi ,yanzun kingansa yazo,inkuma xakije ga kwana can inkikabi har part dinsa sai kije.
Da sauri Hafsat tace ah ah mommy basai najeba.
Murmushi mommy ta yi, dan tasan da k'yar taje,dan talura yarinyar akwai tarbiyya da kamun kai.
"Can kuma Hafsat ta mik'e tace mommy na tafi gun sa'ada!mommy tace to y'ata,nan ta nufi dakin,kafin ta ida isa taji kamshin turaren sa da sauri ta juya sukayi4eyes dashi yana sanye da kayan motsa jiki wani killer smile yasakar mata ,itama tayimasa.
" murya k'asa k'asa yace my Hafsat kintashi lfy ?"
Turo baki tayi tace lfy had'e da duk'awa ta gaida shi murmushi yyi ya amsa tare da cewa sarkin rigima to menene kike wani tura baki gayamun kinji?
"Ahankali tace bakaibane bangankaba sai yanzun."
Kallon ta yyi yace to sorry ina part dina ai yanzun gani ,mujema kirakani gun exersic . mak'e kafada tayi alamar ah ah bazata jeba.murmushi yyi yace shikenan zamu bata kuwa.....muryar mommy yaji tana cewa Auta sai yanzun kika tashi har Hafsat ta rigaki tashi,wata irin kunya sir Aliyu yaji,itakuwa Hafsat bata juyaba da gudu ta shige dakin sa'ada, shima ko kallon mommy be iyaba sum sum ya wuce.
Ita kuwa mommy murmushi tayi ,axuciyarta tace allah yasa kunada rabon mallakar juna ,dan daga gani Hafsat saita canja maka ak'ida,gashi dama bakason raini ita kuma tana girmamaka ,ko dazata gaidashi saida ta duk'a fg ita harshi sun manta da ina gun ,amma zan cigaba da adduah allah yazaba abinda yafi alkhairi.
Bayan su Hafsat da sa'ada sunyi wanka ,sukayi break fast Wanda sir Aliyu be zoba dan yanajin nauyin mommy sai dai sadik , shikuwa kabeer yana skul. Nan sa'ada taja Fatima suka wuce islamiyarsu.
"Sir Aliyu da ke bed room dinsa yaga fitarsu ta window."
Basu jima da fitaba yaji k'arar anbude get ,da sauri yaduba yaga ko sadiq zai fita da mota dan anhanasa fita da mota yyi karanta aceawar sir Aliyu. Kawai saiyaga motar Mubarak yyi parking ,hakanan sir Aliyu yaji wani mugun fad'uwar gaba, yajikuma be yadda da zuwan Mubarak ba dan yasan dagashi har Zakiyya basa zuwa gidansu saida dalili,be auneba yaga sun fito mota tare da Zakiyya, nan yasake mamaki,amma sai yasake bude labulan windon dan yagansu sosai ,amamakinsa sai yaga sun nufo setin windon dayake da sauri yasaki labulen windon,har zai juya yakoma kan bed sai yaji muryarsu suna magana k'asa k'asa.
"da sauri yatsaya yafara sauraransu."
Ji yyi Mubarak yace kin gane sis inkinje ki nuna kinzo musu yini ne ,Nina kawoki zanzo na d'aukeki .
Kinsan sa'ada fa surutu sai kibigi ciki nta kiji inane anguwarsu da kuma iyayanta,kinga in talakawane ta kwana gidan sauki,sai muje muyi musu b'arin kudi ,kin gane? Wata yar dariya Zakiyya tayi tace babu damuwa Allah yasa zan iya dan mugun haushi suke bani daga Hafsat din har sa'adar.
"Ahankali Mubarak yace kinga inmun sami information akanta shikenan, sai mubita gidansu dg nan inta yarda zata aureni ba matsala."
Inkuma tak'i kawai sai insaka asatomun ita nabiya buk'atata da ita.
Dariyar mugunta Zakiyya tayi tace kaga ko yaya aliyu ya aureta bazata yi daraja gunsaba tunda abud'e zai sameta,ballema bazan bari ya auretaba.
"""" mutuwar tsaye sir Aliyu yyi agun ,sai wata irin zufa ke keto masa,innalillahi wa inna ilaihir raju un kawai yake maimai tawa,had'e da jin wani fad'uwar gaba da b'acin rai,Atake idanunsa sukayi jajir suka k'ank'ance,da sauri yaja glass din windown.
Arazane Zakiyya da Mubarak suka juyo sukayi 4eyes da sir Aliyu.
Ai take yan hanjin cikin Mubarak suka kulle dan tsabar firgita yatsorata da yadda yaga idanun sir Aliyu.
Ita ma Zakiyya ta tsorata sosai musammun data lura da sir Aliyu yaji duk firarsu da sukayi.
Basu auneba sukaga sir Aliyu baya bakin window din,arazane Mubarak yace muje mukoma mota wlh zagayowa zaiyi ,kinsan kuwa mukayi arba dashi kashina ya bushe asukwane suka nufi gun da suka yi parking.
Adede nan kuma Hafsat da sa,ada suka turo get suka shigo ciki.
Sir Aliyu kuwa da sauri yafito dg part dinsa, zai nufi k'ofar fita parlour n, da sauri mommy ta tsaidashi ganin yanayinsa dan tasan ba lfy.
Da sauri tace ina zakaje ne haka ranka bace?
Cikin damuwa yace pls mommy kibarni naje kada su gudu .
Mommy ta ce su wanene? Da sauri yace Mubarak da Zakiyya,kara su cutarmun da Hafsat mommy ki barni naje dan Allah yafad'a kamar zai yi kuka.
Cikin mamaki mommy ta basa hanya ya futa afusace kamar zai tashi sama.
Ya fita ya hango har get man yabud'e masu get zasu fita, da gudu yakoma ciki ya dauko key din motarsa ya fito mommy na tambayarsa ina zaije be kulataba ya fito asukwane.
Parking spaces yawuce,nan yahango su Hafsat zasu shiga ciki,da sauri yashige motar yabata wuta.
Dan yyi alk'awarin ko gaban abbansune karshe kenan sai yakoya musu ahankali.
Da mugun gudu ya isa gidansu Zakiyya,a parking spaces yaga motar Mubarak da alama suna ciki shida Zakiyya.
Azuciye yafito dg motarsa yyi cikin gidan afusace....
Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿69&70
Ko sallama bbu ya afka cikin parlourn fuska ba annuri.yas amesu zaune a parlourn Mubarak yana shan lemo,ai yana ganin sir Aliyu yasaki cup d'in lemo n had'e da mik'ewa tsaye yana tari sbd k'warewar da yyi.
Shikuwa sir Aliyu gu n mubarak yyi gadan gadan,mommy na ganin haka afusace tace kai lfy zakashigo min gd bako sallama? Ko gun datake sir Aliyu be kallaba ,fisgo Mubarak kawai yyi yafara basa kyawawan maruka masu rai da lfy Atake Mubarak yasaki ihu had'e da cewa mommy ki ceceni dan Allah. Ita kuwa mominsu tsinewa sir Aliyu kawai take yi had'e da aibatasa.shikuwa ko ajikinsa,dukan Mubarak kawai yake yana cewa dakaji dukan dnayi maka a farko dabakayi yink'urin abinda kayi yanxunba ,bedena suburbudarsaba sai da yakumbura masa fuska tukum .sannan yanunasa da yatsa yace wlh wlh wlh duk abinda yasami Hafsat Kaine da Zakiyya dan wlh zan aje yan uwantaka gefe Nayi muku hukunci da abinda kuka aikata,ai inkacika tantiri basai kasaka asato maka ita ba kabiya bukatarka da itaba ah ah har gidansu zakaje da kanka gaban kowa saika d'aukota ammafa in zaka iya.
Ita kuwa Zakiyya part dinta ta gudu ta rufe.
Koda sir Aliyu yajuya yaga bbu ita yasan guduwa tayi.
Cikin masifa mommy ta ce wlh saina dau mataki akanka dan kafi k'arfinsa saika rik'a zalintarsa ,kuma akan wata banzar mace ma .
"Ahankali sir Aliyu yakalleta yace mommy ina ganin girmanki kidena zagina haka,yaradai k'annena ne kuma na isa dasu insunyi laifi na hukuntasu. "
Wani tsaki taja tace wlh z....muryar abbansu Zakiyya taji yana cewa kincuceni Hajara kin b'atamun tarbiyyar yara gaba d'aya kuma Nayi duk abinda Aliyu yafad'a kinaji yace zaisa asato masa yarinya ya aikata masha'a da ita amma bazakiga laifinsaba,saikirik'a zagin Aliyu.cikin b'acin rai Abba yakalli sir Aliyu da kansa ke duke yace inaso kaje d'akin Zakiyya kazanemun ita,umarni na baka yafad'a had'e da mik'a masa wasu keys yace kabud'e dakin inta rufe.
"Da sauri sir Aliyu ya karba dan dama haka yake so dukda bayason dukan mace amma yaci ace Zakiyya jikinta yagayama ta."
Ita kuwa mommy ba bakin magana dan ta lura Abba ransa b'ace yake.
"Bayan sir Aliyu yanufi dakin Zakiyya," Abba yakalli mommy yace hukuncinki zai biyo baya ai naga sadda aliyun yashigo gidan nikuma dawowata kenan nabiyo sa natsaya bayan labile naji koma.
Wata harara yaaikaea Mubarak dake kwance da k'asa da kumburarrar fuska yace Allah yashiryeka yafad'a had'e da barin parlourn.
""" sir Aliyu kuwa bude d'akin Zakiyya yyi yasameta kwance da earpiece akunnabta,saidai tagansa kamar dg sama beyi wata wataba ya zare belt d'in dake k'ugunsa yashiga jibgarta tana ihu hade da basa hkuri be k'yaletaba saida ta daku,sannan ya kalleta had'e da nunata da yatsa yace inaso kisani duk abinda yafaru da Hafsat kune kuma bazan taba k'yalekuba,sannan kince saikin aureniko?to bari kiji da in aureki gwara na tabbata bbu aure har k'arshen rayuwata.yafad'a tareda da Jan doguwar tsuka yabar parlon.""";;
Yaje yadauki motarsa yabar gidan.
Ko a hanya tunani yake azuciyarsa yace meyasa masa keson keta mata haddi ne?
Ko wanne gaja yanason b'ata mata rayuwa,wata zuciyar race sbd tana da kyawu had'e da k'ira me daukar hankali.
Wani mugun tsaki yaja ,koda ya isa gd straight part dinsa yanufa be kulasu sa'ada dake zaune parlour itada Hafsat suna firaba.
Mommy ce ta tashi tabisa d'akinsa dan ta lura yana cikin damuwa har yanzun.
Ta samesa kwance rigingine yyi tagumi yak'urawa seeling ido yana tunani.
Da sauri ta karasa gunsa ta hau tambayar lfy me yafaru dazu kuma me su Zakiyya suka masa??
Cikin damuwa ya zaiyane mata abinda yafaru,salati kawai mommy keyi tace lallai yarinyar da aka bamu amana suke shirin aikata hakan akanta,amma ai alhmdllh tunda Allah yatoni azirinsu.
"Amma bbna kayi hkuri kaje kayi break fast ."
"Ahankali yace na k'arya awaje na koshi ,yafad'a had'e da rufe idanunsa."
Fitowa mommy ta yi, ta isa kusada Hafsat ,ahankali ta dafata tace y'ata kije gun yayanku yana cikin damuwa ki lallab'asa ,sannan kixo kikai masa kayan break dinsa dan beyi break ba dan naga kunshak'u dashi kinji ko?
"To Hafsat ta ce ta tashi tanufi dakinsa."
Tana shiga tasamesa kwance idonsa arufe ,sallama tayi ta zauna nesa dashi,murya k'asa k'asa tace yaya shine na shigo d'akinka ka shareni?
Bud'e idanunsa yyi yana kallonta,ta sunkuyadda da kanta k'asa.
Cikin shagwaba ta ce yaya natafi tunda kak'imun magana ka shareni,ahankali yace ni ban sharekiba.
Murmushi tayi tace hmm hakane ,amma kasan kamun alkawarin dena saurin fushi amma naga kamar fushi kke yanzun badai nice Nayi laifinba ko?ta fad'a had'e da langabe kai tana kama kunnanta.
Besan sadda yyi dariyaba,yace my Hafsat bake bace kuma yanzun naji na huce nabar fushin murmushi tayi tace eh hakane amma meyasa bakazo mukayi break tareba ?
"Shiru yyi tanatunanin me zai ce mata?"
Can yace banajin yunwa,ai turo baki tayi race amma ni jiya ka tursasani saida naci abinci to yanzun zan kawomaka break kayi dan bakayi break ba nikuma banason yunwa takamamun kai ko?
Ai sai yyi kamar wani dolo dan besan sadda yace to kawomun my Hafsat innaci zakiyi farinciki?
Da sauri tace eh hade da fits.ba jimawa tadawo da plate chips ne aciki da cup din tea mai kauri ta aje masa gabansa.
Tace yauwa Yayana kacigaba da ci kaji ba musu yafara cin abincin sa tana masa fira har ya cinye komai Ta's,cikin jindadi tace yauwa ko kaifa.
Murmushi yyi yace gobe bayan sallar axahar zanmaidake gd dan lokacin baba yadawo ,dan munyi waya dashi dazun.
Murna sosai Hafsat ta hau yi,had'e rai sir Aliyu yyi yace wato ke murna ma kike ko bazakiyi missing dinaba kinfiso mu rabu?
Shagwabewa tayi tace Allah Yayana bahaka bane ,ai naga saura 6days mukoma skul kuma zan ganka a can shiya sa.
Shiru yyi bece komai ba.
Fita tayi takai dan kai plate din da cup din waje,koda mommy ta ganta taji Dadi sosai aranta dama tasan sir Aliyu bazaima Hafsat musuba kuma tasan yanzun yahuce daga Fushun da yake,sai murmushi mommy keyi tanasa ma hafsat albarka.
Bayan ta kai kayan kitchen tadawo dakin tasamesa yana latsa waya gefensa ta zauna cikin shagwaba ta ce yayaaaaa!
Kallonta yyi da sauri yace my Hafsat yar rigimata kimun firanki kinji?
Tashi tayi tace barama nagyaramaka dakinka amma saika fita.
Murmushi yyi yafita ,cikin yan mintoci ta gyare dakin parlour da bed room.
Sannan ta koma toilet ta wanke shi Ta's,harzata fita taga fararen vest dinsa da jallabiyoyi guda biyu ajik'e a bucket, bbu bata lokaci ta duba taga bbu boxes aciki ,saita wankesu Ta's ta shanyasu a toilet din ta had'a masa ruwan wanka ta fito da ga toilet din .
Tana fitowa ,yanashigowa kallonsa tayi tace yaya kaje kayi wanka kaji?
Murmushi yyi yace to my Hafsat yaude anaji dani sosai.
Murmushi tayi ta fito,shikuma ya shige toilet.
Wani farin ciki yaji aransa,yaji Hafsat ta sake samun.matsayi me girma agunsa.
Yaji Dadi sosai da yadda yaga ta wanke masa kayansa sai murmushi yake har yagama wankan ya fito.
Bayan ya shirya ya fito cikin farin ciki dan yanason xuwa campaninsa,yaga ba kowa a parlour ,motsinsu yaji a kitchen can yanufa.
Yasami du Hafsat itada sa'ada suna aikii.
Murmushi yasakarma Hafsat ya ce sannunku da aiki, murmushin itama Hafsat ta yi masa tace yaya sai ina?
Ahankali yace zan je office muje kirakini mota kimun addua.
Sa'ada tace haba yaya saita wani rak.... Hararar da ya aiko mata yasa tayi shiru.
Hafsat kuwa ba kunya ta bisa har parking spaces yayi masa adduar da yabukata ta dawo cikin gidan.
Washe gari....
Share pls[12/26, 6:17 PM] اختى حفصة: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿71&72
Washe gari.
Bayan sallah azahar sir Aliyu ne tsaye a waiting parlourn gidansu yana kallon Hafsat sun rungume juna da sa'ada suna ban kwana,Hafsat kamar tayi kuka sbd sabon datayi agidan dakuma batasan rabuwa da sa'ada.
Mommy ce tazo taja hannun Hafsat tasaka mata wata babbar Leda ahannunta ,hafsat zatayi magana mommy ta rufe mata baki,takalli sir Aliyu dake tsaye yana aikin kallonsu. Tace babana kuje dan Allah ka lallab'ata kaji?
"Yatsina fuska yyi yace haba mommy lallabata d'in me zanyi,ya kalli Hafsat yace oya muje."
"Turo baki tayi tabi bayansa."
Ya shige mota yabarta ,yak'i bud'e mata ,itakuma tak'i shiga sbd yasaba shike bud'e mata duk in zata shiga motarsa.
Shikuwa yana sane yyi hakan Dan yaji haushin yadda ta nuna damuwa kan zata rabu da sa'ada amma shi bata damu dan zasu rabuba.jin shirun yyi yawa yasa yafito ya kalleta fuska daure yace wai bazaki shi ga bane kome kkejira?
Kauda kanta tayi gefe tace cikin shagwaba tonika bud'e mun nashi ga. Kallonta yyi yace keko kin rainani kwa nannan ko? batace komaiba can yabud'e mata sannan ta shiga yaja motar ,saida yabiya yasiya mata su ice cream da ga sassun kaji dasu biscuits da chacoolat,sannan suka wuce anguwarsu.
Bayan yyi parking da sauri ta kai hannunta dan bude k'ofar ta jita yasa lock,shiru tayi dan dama tunda suka shiga motar batayi masa magana dan zama da shi yasa takoyi miskilanci.
Kallonta yyi murya k'asa k'asa yace wato dan zakiga baba ki koma gunsa shine kikemun haka ko?
[12/26, 8:42 PM] Amina Lgs: "Ahankali tace nifa ba haka bane bakaine kayita d'aure fuska ba k'ak'i yin dariya."
Kallonta yyi yace to kalleni,ba musu ta kallesa suka had'a ido murmushi yyi,turo baki tayi tace bemunba gsky ka canza wani.dariya yy yace aigarani Nayi murmushi keko murmushin bakiyiba .da sauri tayimasa murmushi har yar wushiryarta ta bayyana,tace to yaya nayimaka bud'e mun,bece komaiba yabud'e mata suka fito.
Dede bakin soron gidan suka had'u da baba da sauri sir Aliyu ya iso gunsa ya duk'a yana gaidashi, ya amsa cikin sakin fuska ,had'e da yimasa godiya da tambayarsa mutanan gida.Hafsat kuwa bayan baba yagama gaisawa da Sir Aliyu da sauri ta rungumesa tana masa shagwaba,shikuwa sir Aliyu se kallonsu yake azuciyarsa yana cewa oh anyi shagwab'ab'b'iyar yarinya.
Babane yace Aliyu inafatan dai bata yi muku wani shirmenba?murmushi sir Aliyu yyi yace ah ah baba .
Baba yace masha Allah ,azuciyarsa kuwa ca yake kaga yaro kamar balarabe ko bature ai ban dauka yanajin hausaba.
Sir Aliyu ne yakatsewa baba tunani gun cewa ni xan wuce baba sai munyi waya,da fara,a baba yace to Aliyu bazaka shiga ciki ba? Murmushi yyi yace zanshiga wani lokacin ,har mota baba yarakasa yana sa masa Albarka da yimasa godiya, sannan yadawo yasami Hafsat tsaye zaure yace muje ciki ko,ahankali tace lah baba na mance kayana amotarsa bara naje na d'auko.
"Nan ta wuce ,baba yashiga ciki."
Tana zuwa tasame sa cikin motar yad'ora goshinsa kan sitiyarin motar,ahankali tace yayanah nagode sosae Allah yabar zumunci Allah... Da sauri yadago yace ya,isa haka my Hafsat kinji bbu godiya atsakanun mu ko aike k'anwatace ko?
Murmushi tayi tace eh hakane wlh yaya dakai da familyn ka kunada kirki sosai amma mommy duk ta fiku kirki tafad'a hade da yimasa gwalo taja ledar tsarabarta ta gudu.
Dariya yyi yace haba yarinya zamu hadu askul nanda 5days,yafada had'e da Jan motar yabar anguwar da kewar Hafsat aransa.
Hafsat nashi ga gida tayi sallama Laure dake tsakar gida tayi salati had'e da cewa oh ni duniya ,ainad'auka gun yawan karuwancin zaki tabbata ,wlh anji haushi waya sani koma ciki yyimiki kuka je aka zubar shiyasa kika kwana biyu gunsa to allah yatoni asirinku,kuma deeni ma yayafeki ko kyauta aka bashike bazai karba kina kingin wani dan Wannan ba aurenki zaiyiba saidai ya lalataki.
Hafsat hawaye ne ke ta zuba akumatunta ,tanajin zafin maganganun Laure.
Babane ya fito afusace sbd yagaji da jin irin kalaman da Laure ke alak'anta Hafsat dasuba,beyi wata wataba ya wanke Laure da maruka2 lafiyayyu yanunata da yatsa yace wlh kinci albarkacin Hafsat dan inna rabu dake bbu dacewa in zauna dagani sai itada k'annantaba,da tuni na dad'e da rabuwa dake,amma inaso ki rubuta ki aje duk ranar danaga matata to wlh aranar zamana dake yak'are ,yafad'a azafafe tare da kallon Hafsat yace muje.
Su Laure saikaji tsit baki yamutu tana matsar hawayen munafunci.
Ko ad'aki baba yyita rarrashin Hafsat har tayi shiru ,tahaubasa labarin gidansu sir Aliyu da kirkinsu,kuma baba yaji Dadi sosai ,be fitaba saida aka kira la'asar sannan yace bara yaje yyi sallah .
Bayan ya fita ita Hafsat tayi tata sallar .
Bayan ta idar ba jimawa ,taji sallamar Fatima,nan tashigo d'akin,had'e rai Hafsat ta yi, tayima kamar bata gantaba.
Murmushi Fatima ta yi tace ayya sis dan Allah kiyimun uxuri kiji bayanina dan Allah ba fushi zakiyi daniba.
Harararta Hafsat ta yi tace hmm aini kin bani mamaki ace duk yadda muke dake har kije wani gun bansaniba.
Da sauri Fatima ta ce yi hakuri sis wlh dawiwarmu kenan,nace bari nazo na goge laifina.
Kinsan mahaifiyar ummanmu bata lfy tana asibitin abuja,to jikinta yyi tsanani,shine aka kira umma taxo 'sainabita da harda yaya Ahmed zamuje dan yazo gaidasu umma yatarar zamuje to sai daddy yace ah ah yazauna tunda shi angone shine Muka barsa gida mukatafi.
Ajiyar zuciya Hafsat ta yi tace ayya sis allah yabata lfy yanzun yajikin nata?
Fatima ta ce da sauki sosae
Nan Hafsat ta labar tawa Fatima abinda yafaru tsakaninta da deeni dakuma zuwanta gidansu sir Aliyu.
Sosai Fatima ta yi murna da yadda sir Aliyu yyi maganin deeni,sannan tak'ara
Yarda aranta cewa sir Aliyu yanason Hafsat.
Nan Hafsat ta nuna mata tsarabarta da mommyn sir Aliyu tabata da abinda sir Aliyu yasiya mata,nanta tayata murna ,suka raba kayan har Fatima tak'i karb'a amma ganin yadda Hafsat ta ji haushi yasa ta karba kasancewar komai suka samu tare suke rabawa.
Har soro Hafsat ta rako Fatima dazata tafi gida ,harta Fatima ta fita tadawo tace sis saurafa 5 days mukoma skul kizama cikin shiri.
Murmushi Hafsat ta yi tace eh ai nasani Allah yakaimu, Fatima ta ce ameen tareda tafiya,Hafsat takoma ciki.
0 comments:
Post a Comment