LOKACIN DA TAKOBIN SHUMAIRA TA ISA kirjin sarauniya
larbisa sai ta dan soketa a kirji, tana kokarin danna takobin a cikin kirjin nata
kafin larbisa tayi kara sai shumaira taji an daka mata tsawa
daga baya
bisa dole ta fasa dannan takobin izuwa cikin kirjin larbisa,
ta mike tsaye daga kanta ta waigo tayi arba da wanda yayi
mata tsawar, ba wani bane face mahaifinta mafarauci
imshal.
Mafarauci Imshal ya kasance dogon mutum mai kirar sadaukai sai dai girma ya
kamashi sosai domin shekarunsa zasu kai kusan arba in
gaba daya gashin kansa sajensa da gemunsa duk farin
gashine, yana rike da wata doguwar sanda a hannunsa ya rataya kwari da baka
a bayansa
rigarsa, wandonsa da takalminsa dake kafarsa duk anyi
sune da fatar damisa
Koda jaruma shumaira ta hango mahaifinta Imshal sai
ta rugo izuwa gareshi ta dukar daki tana mai nuna
girmamawa a gareshi, A wannan lokaci ne sarauniya
larbisa ta mike tsaye tana mai dafe gefen kirjinta inda
shumaira ta soka mata takobi don har dan jini ya fito
kawai sai sarauniya larbisa ta sunkuya cikin biyayya
ta gaisheda tsoho Imshal. Imshal ya karbi gaisuwar
yana mai kare mata kallo sama da kasa sannan ya karewa
dakarunta kallo ya dubi shumaira yace akan wani dalili kike yaki da wannan mace mai
daraja? Shin bakya ganin alamar cewa mai mulki ce
koda jin wannan tambaya sai shumaira ta dago kai ta
dubi imshal ta ce yakai abbana kayi sani cewa haka kawai
wannan sarauniya tare da dakarunta suka shigo cikin dajin nan suka dasawa
dabbobinmu wawa, bisa wannan daliline na tarwatsa dakarun nata kuma na
umarcesu da su fice daga cikin dajin nan tun kafin fishinmu ya tabbata a kansu
amma saboda naci sai wannan sarauniya ta biyoni
har cikin
garken dabbobi, ni ina ganin cewa kawai ka kyaleni na
gama da ita yanzu domin da ita da yaran nata su gane
cewa ruwa ba sa an kwando bane kuma bakin rijiya ba wajan wasan yaro bane
koda jin wannan batu sai tsoho imshal ya bushe da
dariya sannan ya hade fuska ya dubi shumaira yace
ai ruwa baya tsami banza, shin a farkon bayaninta gareki
bata gaya miki cewar tana da wata bukata ba a wajanki?
Cikin alamun sanyin jiki shumaira tace ta gaya mini cewar
tana da wata bukata a wajena amma saina gaya mata
cewar bata da abinda zata iya biyana da shi don haka babu abinda zan iya yi mata
koda jin wannan batu sai imshal ya gyada kai yace
yarinya kinyi hanzarin yanke hukunci shin bakya
tunanin cewa bukatar da tazo mana da ita wata kila
a sanadinta ne muma zamu fita bakin cikin da ya addabemu
tsawon shekaru bakwai.. Shin kin manta ne
cewar na gaya miki zamu iya nasarar samun abinda
muke nema a cikin wannan shekara idan kin hadu da wadansu bakin
jarumai guda uku?
Koda jin wannan batu sai jikin shumaira yayi sanyi ta
sunkui da kanta kas ta kasa cewa komai daga can kuma sai
ta dago kai da sauri ta dubi tsoho imshal tace amma ai wannan
sarauniya ba ta da kama ko siffa irin ta mutane ukun dakayi
mini bayani
imshal yace hakane amma dai ki tsaya muji abinda ya
kawota wajanmu babu mamaki a sanadin hakan a samu dacewa
cikin nutsuwa
tsoho Imshal ya dubi sarauniya Larbisa yace yake wannan
sarauniya ma abociya kyawu da karjini
wace bukata ce dake tasa har kikayi tattaki kikazo
har wannan daji namu?
Kafin larbisa ta budi baki tace wani abu sai tsoho Imshal ya kara tarar numfashinta
yace
amma kafin kice komai ya kamata ku fara yiwa raunikan
jikinku magani yana gama fadin hakan sai ya bude
wata jaka dake rataye a bayansa ya dauko wani farin
magani me maiko da kauri kamar daskararren nonon shanu
ya mikawa yarsa shumaira yace ungo ki shafa a rauninki
kuma ki shafawa bakuwar tamu
cikin alamun damuwa shumaira ta karbi maganin ta fara shafawa kanta sannan
taje ta zauna a gaban larbisa ta kama shafa mata
fuskarta a daure babu annuri, su kuwa su sadauki Humaisu
sai hankalinsu ya kwanta sukayi murna da ganin yadda
tsoho Imshal ya karbesu hannu biyu, bayan shumaira ta gama sawa larbisa magani
a rauninta sai tsoho Imshal ya dubi larbisa yace yake
wannan sarauniya kiyi sani cewa ni yanzu na karbeku
keda jama arki a matsayin bakina saboda haka yanzu zan
kaiku zuwa gidana domin ku huta in yaso bayan kun nutsu
saimu zauna mu tattauna mu dake idan har zamu iya
taimakon juna zamu iya yarda da buqatarki, idan kuma ke
kadaice zaki amfana damu to sai dai muyi miki fatan
samun nasara ki kara gaba, koda jin wannan batu sai
farin ciki ya lullube sarauniya larbisa , Tare dani Al amin Guyson mai Rubutu,
ta dubi Tsoho Imshal cikin murmushi tace nayi farin ciki da wannan tayi da
ka bani ya kai Abul Shumaira kuma zuciyata ta
bani cewa nima zan iya baku taimako bisa taku bukatar
Tsoho Imshal yayi
murmushi yace sai an gwada Sannan ake sanin na kwarai
yana gama fadin hakan sai ya kama hannun shumaira suka nufi bayan wani katon
dutse yana mai yafito su larbisaa
Da hannu cikin hanzari larbisa taje ta kama dokinta ta hau
tabi su.
Tsoho Huzallatul marwas ne ya fara bin bayanta sannan
sadauki Humaisu da sauran Dakaru.
Ana zagayawa bayan wannan katon dutse sai kowa
ya cika da mamaki bisa ganin wani dankareren gida
wanda aka ginashi da duwatsun wuta
Gidan katone kuma anyi masa fasali na gidan sarauta
dauke da bangare bangare, banbancinsu da gidan sarauta kawai shine
babu bayi, dakaru da kuyangi mutum daya kacal suka gani a cikin wannan gida
kuma ba wani bane face larisa mahaifiyar Jaruma shumaira
lokacin da larisa ta hango mijinta imshal da yarta
shumaira tare da bakin mutane sai tsoro ya baibayeta
domin wannan shine karon farko a iya zamansu a cikin
wannan daji da ta ga sun zo mata da mutane har
gida don haka bata yarda ta bude kofar gidan ba sun shigo
har sai da suka matso kusa taga cewar babu wata alamar
damuwa akan fuskar mijinta da 'yarta
Ita kanta larisa shekarunta sun kai hamsin da biyu koda
uku amma saboda tsananin kyawun jikin da Allah ya bata mutum ba zai taba zaton
ta kai hakan ba
Da isowarsu tsoho Imshal ga larisa sai ya gabatar da sarauniya
Larbisa a gareta sannan ya gaya mata cewa ita da jama arta bakine masu mahimmanci
cikin farin ciki larisa ta karbi sarauniya larbisa
tana maiyi mata barka da zuwa, nan take aka kaisu
sadauki Humaisu izuwa wani bangare daban na gidan ita kuma larbisa sai tabi jaruma
shumaira izuwa dakinta
Cikin hanzari shumaira ta dafa ruwan dumi ta kaiwa larbisa kewaye ta shiga wanka
kafin larbisa ta fito daga wankan tuni shumaira ta shirya
musu abinci. Larbisa na fitowa daga wankan sai itama
shumaira ta shiga wankan sai da ta fito daga wankan sannan
suka zauna tare bisa wasu kujeru dake karkashin wani
tebur suka fara cin abincin, tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice
uffab ba
Abinda ya daurewa shumaira kai shine ganin yadda larbisa
ta saki jiki take ta cin abincin Alhalin ba abinci ne mai
dadi ba irin nasu na sarakai Abincine irin wanda kowane talaka zai iya ci
musamman mazauna daji
cikin matukar mamaki shumaira ta dubi sarauniya larbisa
tace yake wannan sarauniya menene dalilin da yasa kika saki jiki kike ta cin irin wannan
abinci namu na talakawa alhalin nasan a guzurinki akwai
irin naki abincin da kika taho dashi?
Koda jin wannan tambaya sai sarauniya tayi murmushi tace ai dokar bakunta
itace yin koyi da irin mutanen da ka riska, ni kaina nayi mamakin yadda akayi naji ina
matukar jin dadin wannan abinci naku amma fa babu abinda
ya bani mamaki a yanzu sama dake
hm Al amin Ahmed Misau, Guyson sunana kenan
koda jin haka sai shumaira ta dago kai da sauri ta dubi larbisa cikin mamaki tace
ke kuma me nayi wanda ya baki mamaki? Larbisa ta ajiye cokalin da take cin abinci
gami da yin ajiyar numfashi sannan tace gani nayi da
farko baki karbeni da wata daraja ba har ma yakata kikayi
kikauda batun matsayina na sarauta yanzu kuma sai
gashi kina yin biyayya da hidima a gareni
Yayin da shumaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace ai nima nayi amfani
da maganar manya da suke cewa idan babba ya rike
girmansa dole ne karami yayi masa biyayya. Lokacin da kika shigo cikin wannan daji namu ke da jama arki baki
hanasu kokarin yi mana sata ba
dalilin
da ya sa na ki karbar bakuncinki kenan tun da farko
amma yanzu dana gane cewar wata kila kina da
mahimmanci ga rayuwata shi yasa nake yi miki
ladabi da biyayya
larbisa ta bushe da dariya sannan tace ai kowane mutum
yana da rana komai kaskancinsa shin zaki iya
gaya mini babban burinku na duniya keda mahaifinki
wanda har kuke tunanin zan iya taimaka muku a kansa?
Sa adda shumaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace me kikeci
na baka na zuba ehm wato ( what are you eating na baka is falling down )
zakiji amsar wannan tambaya taki idan mukayi
zama na musamman mu dake kuma a sannan ne
muma zamuji taku bukatar a wajanmu, kodajin
wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace
tabbas zancenki dutse ne, haka dai shumaira da larbisa suka ci gaba da hira har
suka gama cin abincin kuma dare ya raba sannan
suka kwanta sukayi barci, kamar yadda aka karrama
sarauniya larbisa hakama aka karrama sadauki
humaisu da dukkan dakarunsa suka ci suka sha sukayi
hani'an kuma suka kwanta a masauki mai kyau
Al amarin da yayi matukar daure musu kai kenan
suka cika da tsananin mamakin yadda wadannan
mafarauta suka tara arziki mai yawa haka
++
Kashe gari da safe bayan sarauniya larbisa ta yi
wanka ta kimtsa sai ta ga shumaira bata kawo musu abincin
kalaci ba
kawai ta zauna tana jiranta ta gama kimtsawa tana gama
kimtsawa kuwa sai shumaira ta mike tsaye ta dubeta
tace iyayena suna jiranmu acan turakarsu domin
muyi mude baki tare dasu kuma mu sami damar
tattaunawa akan abubuwan da muka sa a gaba
koda jin haka sai sarauniya larbisa ta mike da sauri
cikin murna ta bi shumaira a baya suka fice daga cikin
dakin suka nufi hanyar da zata kaisu bangaren da
iyayen shumaira suke, sai da sukayi yar tafiya mai
dan tsawo kadan sannan suka iso wani babban falo mai
dauke da
Wani faffadan tebu A karkashin teburin kujerune guda
biyar
tsoho Imshal tare da matarsa larisa na zaune
akan kujeru biyu ga abinci nan wajen kala uku
akan teburin dake gabansu, da isowar shumaira da
larbisa sai tsoho imshal da larisa suka mike tsaye suna
musu girmama
sarauniya larbisa gami dayi mata barka da isowa
nan take larbisa da shumaira suka janyo kujeru daga cikin
karkashin teburin suka zauna aka fara cin abincin
Tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice
uffan ba daga can sai tsoho Imshal yayi gyaran murya
yace
yake wannan sarauniya mai daraja yanzu saiki gaya
mana abin da ya kawoki garemu kafin muma mu
gaya miki bukatar da muke da ita a wajanki
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi sannan tayi
gyaran murya tace ba wani abu bane ya sa na baro
kasata ba
mulkina da jama ata face don na riski kogon
Kitabul sihir inda littafin TSATSUBA yake, littafin da shine kadai zai cika mini babban
burina na duniya na samun damar yin aure gami
da samun magaji kuma na mallaki komai da kowa dake
cikin wannan duniya ba zan iya isa inda kogin
yake ba face na ratsa ta cikin dazuzzuka guda uku
Daji na farko shine ake kira da Shajarul Shaljuma
wanda ke dauke da mugayen dabbobi da mugayen
tsuntsaye. Bokaye sun tabbatar mini da cewa babu
wani mahaluki wanda zai iya wucewa dani ta
cikin wannan daji a raye face wannan ya taku shumaira
daga nan ne zamu wuce izuwa dajin Ujurul Majnun bisa
jagorancin Jaruma Larifat, daji na uku kuwa wanda ake kira
darul maut zamu shigeshine bisa jagorancin jaruma Lubaina
muna wuce wadannan dazuzzuka sai kuma mu tunkari
dajin da kogon Kitabil sihir yake
shi kuwa kogon
babu mai iya yi mana jagora izuwa cikinsa face
jarumi Ruhaisu dan sarki Zaiyanu na birnin kufa
A cikin kogon kitabul sihir ne zan iya dauko littafin
TSATSUBA domin na lalata duk sihirin tsafin dake
cikinsa don na sami damar yin aure na sami da ko
yar da zata gajeni idan ban lalata sihirin dake cikin
wannan littafi ba na tsatsuba har abada burina ba zai
cikaba
Koda sarauniya larbisa tazo nan a zancenta sai tsoho
Imshal ya tuntsire da dariya Al amarin da ya baiwa
larbisa dasu shumaira mamaki kenan daga can
kuma sai Tsoho Imshal ya murtuke fuska tamkar an
aiko masa da sakon mutuwa a lokacin da idanunsa
suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa..
Nan fa sarauniya Larbisa ta kara cika da tsananin mamaki
ta dubi tsoho Imshal tace yakai Abul Shumaira ina
dalilin yin dariyarka gami da zubar hawayenka a bisa
abinda kaji na fada??...
.
Wow Nima a nan nake son dakatawa
Kuma sai Allah ya kaimu Gobe zamuci gaba
Amma kafinnan
NIDINNE DAI
Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana Kenana
Daga Zauran Labarai
Page 2017
Nake cewa Ku zama
lafiya
[4/13, 11:10 PM] +234 806 459 4218: TŠÅTŠµßÄ
Littafi Na Biyu (2)
Part B.
.
• еYŠºN • ke magana
.
Marubucin Littafin..
Abdul aziz Sani M/Gini
Typing by.
Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana Kenan
Daga Zauran Labarai
Call 08064594218
Doka ban yarda Ayi edit na post dinaba
.
Labari ya isowa Guyson Cewa...
.
Yayinda tsoho Imshal yaji wannan tambaya sai yayi
Ajiyar numfashi ya dubi sarauniya larbisa cikin
nutsuwa yace yake wannan sarauniya mai daraja
kiyi sani cewa ba wani abu bane ya sakikaga na bushe
da dariya ba sai saboda nasan cewa kin daukowa
kanki gagarumin aikin da sai kinyi nadamar yinsa
domin aikine wanda babu tabbacin samun nasara
a kansa, sannan kuma zaki iya shan bakar wahala
da bata da misali kuma dake da duk abikan
tafiyar taku zaku iya rasa rayuwarku ko lafiyarku.
Ke a takaice dai fiye da shekaru dari baya ba a
taba samun mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan
dazuzzuka guda uku har ya isa kogin sihir a raye
ba
don haka ni yanzu ina kallonki ne a matsayin wacce
ta gaji da rayuwar duniya take neman mutuwa ruwa
a jallo! Ko kuma ince wacce ta sami tabin hankali !!
Dalilin da yasa kikaga ina zubar da hawaye kuwa shine
biwa wannan TAFARKI da kike son bine na rasa
iyayena da kakannina domin suma sun bar gida
sun tafi izuwa kogon kitabul sihir domin magance wata matsala data addabi gaba
daya zuri armu tsawon shekaru masu yawa
amma dayansu bai dawo a raye ba, wannan matsala
kuwa ba komai bace face wani sihiri wanda wani abokin gabarmu ya yiwa kakanninmu, shi dai wannan abokin
gaba namu mafarauci ne kuma takadarin boka ne
tunda akayi GASAR FARAUTA a birninmu kakanmu ya lashe gasar sai wannan
boka yayi masa sihiri ya kasa ci gaba da zama a cikin
gari shi da iyalinsa yaji kamar ana konashi da wuta
Matansa da 'ya'yansa da jikokinsa ma haka suka rinkaji
ya zamana cewa ba shiri suka hada nasu 'i' nasu suka koma cikin daji da zama
bisa dole kakan namu ya hakura da sarautar sarkin
daji da aka bashi ya daina zuwa fada gaba dayan
zuri armu sai suka tsani cikin gari daga wannan rana kawo
iyanzu babu sauran mutum daya daga cikin zuri armu
wanda ke rayuwa a cikin daji duk mun watsu a cikin
dazuzzuka har yau har gobe ni din nan da matata da
yata shumaira da kike ganinmu bamu taba shiga cikin gari ba mu tsaya
tsawon rabin sa a sai dai muyi siyayya a kasuwa mu
fito babu irin kokarin da bamu yi ba wajan neman
yadda zamu karya wannan sihiri amma abu ya gagara
kafin mahaifina ya rasu ya shaida mini cewa ba
zamu taba iya samun nasarar karya wannan sihiri
ba face mun bude littafin TSATSUBA mun karanta wata kalmar tsafi guda
daya wadda ke shafin tsakiya , yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani
cewa bukatarki kusan iri daya ce da tamu amma ni ba zan
iya barin yata shumaira tayi wannan tafiya ba
tunda ita kadai gareni a wannan duniya kinga nidai tsufa ya riskeni mahaifiyar tama gata nan ta fara manyanta , yau idan babu ita shikenan zuri armu gaba daya ta shude kenan tunda
mu ne kadai mukayi saura
kafin tsoho Imshal ya gama rufe bakinsa sai jaruma shumaira ta mike zumbur ta durkusa bisa guiwoyinta a gabansa ta rike hannayansa biyu
a lokacin da hawaye ya zumo mata tace ya kai abbana kayi
sani cewa ko ka barni ko ka hanani yin wannan tafiya watarana sai mutuwa
ta daukeni
shin ka manta cewar ka gaya mini cewa dukkan mai nema
yana tare da samu lallai ina son na karya wannan asiri wanda ya gagari
iyayenmu da kakanninmu domin na barwa birninmu
abin tarihin da baza a taba mancewa dashi ba ka tuna cewa har yanzu sarautar
sarkin daji tana hannun zuri ar babban makiyinmu boka zarratu tunda mu mun kasa
zama a cikin gari
lallai ta kowanne hali saina kwato mana yancinmu na dawo mana
da sarautarmu mun koma mun zauna a cikin
wannan gidan sarauta namu na sarkin daji wanda
kai kanka rabonka da shi tun kana jariri ina mai rokonka daka bani wannan dama ayi
wannan tafiya dani
da izinin iyayenka dake kwance cikin kabari saina sami nasara
na kwato mana
yancinmu.
Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana kena Admin A zauran Labarai nake magana
koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal
da matarsa larisa suka kamu da tsananin tausayinta suka
rungumeta sunamasu fashewa da kuka itama
saita tayasu kukan
Al amarin da ya karya zuciyar sarauniya larbisa
kenan a karon farko a rayuwarta taji tausayin wani
ya kamata har itama idanunta suka ciko da kwalla kuma ba komai bane
ya janyo hakan ba face ganin matsalar ta tazo
iri daya da tasu
Saida tsoho Imshal da larisa suka dan jima a kankame
da shumaira sannan imshan ya janye jikinsa
daga cikin na shumaira ya
dubeta cikin Alamun tsananin damuwa yace yake
yata hakika kinzo mini da babban Al amari wanda ya dugunzuma hankalina kuma wanda a halin yanzu ba zan iya yanke
hukunci ba a kansa lallai ina bukatar ki bani lokaci daga nan zuwa gobe muyi
tunani da nazari akan al amarin nida mahaifiyarki
koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya larbisa ya dugunzuma
ainun fiye da ko yaushe domin ta fara tunanin
cewa tsoho Imshal ba zai yarda da wannan tafiya
ba don haka duk shirinta ya rushe,
Nan dai shumaira ta mike tsaye ta kama hannun
sarauniya larbisa ta jata suka fice daga cikin falon
duk su biyun jikinsu a sanyaye, lokacin da dare ya sakeyi
sai shumaira da sarauniya larbisa suka kasa barci saboda
zulumi da fargabar sakamakon shawarar da iyayen
shumaira zasu yanke akan wannan tafiya suna cikin wannan hali ne shumaira ta mike
zaune daga kan gadonta ta dubi larbisa tace
ranki ya dade ni fa tunda ina cikin zulumin abinda
zai biyo baya ba zan iya barci ba, ina mai tabbatar miki
da cewar rayuwata gaba daya yanzu babu wani
abu da ya shiga raina sama
da yin wannan tafiya koda kuwa ina da yakinin zan
mutu
nafi son na mutu jaruma akan na mutu raguwa a
cikin rashin yanke wannan bakin ciki na zuri armu
saboda haka yanzu zanje na gana da mahaifina domin naji
hukuncin da ya yanke
koda gama fadin hakan sai shumaira ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin
ita kuwa sarauniya larbisa saita bita da kallo kawai
cikin alamun tsananin damuwa, jikinta na tsuma
zuciyarta na dukan uku uku tana fargabar abinda zaije
ya dawo
lokacin da shumaira ta isa falon mahaifinta saita iske
mahaifiyarta zaune akan kujera tayi tagumi kanta a sunkuye tana zubar da hawaye
shi kuwa tsoho Imshal yana tsaye yana kai kawo duk
su biyun fuskokinsu na nuna alamun tsananin damuwa da fargaba
koda shumaira taga iyayenta a cikin wannan hali sai
hankalinta ya dugunzuma ainun taji kamar ba zata iya tunkararsu da maganar ba
tunda su ma suna cikin irin halin da take ciki
kawai sai shumaira ta juya da nufin ta koma izuwa dakinta
take tsoho Imshal ya kira sunanta shumaira , kada ki koma kizo mu tattauna wata muhimmiyar
magana
koda shumaira ta juyo tana mai amsa kiransa
saita ga fuskar tsoho Imshal ta juye izuwa murmushi
da annuri
cikin mamaki shumaira ta tunkari mahaifin nata
ta iso daf dashi yadda har suna iya jin numfashin juna
tsoho Imshal ya dafa kafadar shumaira yace, yake
yata ki kwantar da hankalinki kiyi sani cewa ba zan iya hanaki
yin wannan tafiya ba saboda ganin muhimmancinta
Amma akwai sharadi guda daya da zamuyi dake
wannan sharadi kuwa shine ba zamu yarda kiyi
wannan tafiya ke kadai ba sai tare damu
koda jin wannan sharadi sai idanun shumaira suka
zazzaro hankalinta ya dugunzuma ainun ta dubeshi
tace haba yakai Abbana tayaya zanyi wannan tafiya tare daku alhalin girma ya
kamaku baku da karfin jiki gami da jarumtaka irin tawa
koda jin wannan batu sai tsoho Imshal ya sake yin
murmushi a karo na biyu yace Ashe kin manta da cewar
nine na koya miki yadda ake farauta a cikin daji
da yadda ake yin yaki a cikin dandazon mayaka??
To kiyi sani cewa ko giwa ta fadi tafi gaban a dasa mata
wawa malami har abada malami ne akan dalibansa
ina mai tabbatar miki da cewa ni da mahaifiyarki
zamu baku gagarumar gudumawa a cikin
wannan tafiya yadda zaku sha dumbin mamaki saboda
haka ki koma dakinki ki gayawa sarauniya larbisa cewar
ku fara shirin
wannan tafiya tun a daren yau amma ina son ta turo
mini babban abokin tafiyarta tsoho Huzallatul marwas
yanzu take kuma ta gaya masa cewa ya taho tare da jakar
sihirinsa shumaira ta juyo jikinta a sanyaye ta koma izuwa can
turakarta zuciyarta cike da zulumi. Fargaba da tsananin damuwa
lokacin da shumaira ta isar da wannan sakon mahaifinta
izuwa ga sarauniya larbisa ta firgita kuma ta kamu da tsananin mamakin yadda
akayi tsoho Imshal ya san da batun jakarsa ta sihiri
alhalin bata gabatar dashi ba a wajansam nan take larbisa ta gano cewar lallai
shi ma tsoho Imshal ya cika boka masanin abinda ke boye
Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana Kenan
Admin a zauran Labarai
ba tare da boye komai ba sarauniya ta tashi ta tafi izuwa masaukinsu tsoho
huzallatul marwas ta jashi izuwa gefe daya ta sanar
dashi sakon tsoho Imshan, koda jin hakan sai huzallatul
marwas ya bushe da dariya Al amarin da ya baiwa
larbisa mamaki kenan kuma ranta ya baci ta dubeshi
a fusace tace menene kuma abin dariya a cikin wannan Al amari??
Huzallatul marwas ya numfasa yace
hakika mahaifim shumaira ya cika hatsabibin boka domin ban taba zaton zai gano
da batuna ba a cikin wannan tawaga taki bare ma har ya san da batun jakar sihirinsa
babu komai ki kwantar da hankalinki yanzu jamuje na riskeshi domin
naji dalilin da yasa ya bukaci ganina,
koda gama fadin hakan sai tsoho huzallatul marwas
ya yunkura da nufin ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi inda turakar tsoho Imshal yake
Tsulum sai suka ga aljani subauratu ya baiyana a sama daf da fuskarsa yana mai
kyalkyala dariya lokaci guda kuma sai ya hade fuskarsa
ya risina ga huzallatul marwas yace ya shugabana
kayi sani cewa zuwanka kai kadai izuwa ga tsoho Imshal yana da hadari don haka duk yadda za ayi ka tafi tare da sarauniyarka
komai rintsi da tsanani kada ka yadda kayi wata magana dashi sai sarauniya na kusa tana sauraronka, kafin tsoho Huzallatul marwas ya budi baki ya tambayi subauratu dalilin
da yasa ya bashi wannan shawara tuni subauratu ya bace bat,
sai jin motsinsa yayi a cikin jakarsa ta sihiri
Huzallatul marwas ya dubi larbisa yace ranki ya dade menene
abinyi? Larbisa tayi murmushi tace yadda
Aljani subauratu ya fada haka za ayi, nan take suka
dunguma su biyun suka koma can turakar tsoho Imshal inda suka
iskeshi tare da yarsa shumaira da matarsa larisa a zaune
koda Isham yaga larbisa ta biyo tsoho huzallatul
marwas sun dawo tare sai ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dubi larbisa yace ai sai ku bamu wuri
don ina son na gana da huzallatul marwasu
koda jin haka sai huzallatul marwas ya matso gaban Isham ya mika masa hannu
suka gaisa sannan yace yana daga cikin sharaddan tafiyarmu
nida sarauniya cewar komai tare da ita zanyi, ba zan boye mata komai ba
koda jin wannan batu sai jikin tsoho Isham yayi sanyi kawai
sai ya kyalkyale da dariya ya rungume huzallatul marwas yana mai cewa lale marhaban
da babban aboki ma abocin hikima da hangen nesa shi kenan kuje ku
kwanta domin ku dan rintsa kafin gari ya waye mu kama hanya
dajin haka sai larbisa da tsoho Huzallatul marwas marwas suka dubi junansu suka yi murmushi nan take suka yiwa su tsoho isham sallama suka
juya suka fice daga cikin falon,
fitarsu keda wuya sai jaruma shumaira ta dubi isham fuskarta cike da alamun tsananin
damuwa tace ya kai abbana yanzu ta yaya kenan zamu san shafin da ya kamata mu karanta
a cikin littafin tsatsuba domin kawai da wannan
matsala tamu tunda gashi sarauniya larbisa taki yarda ta barka ka kebe da tsoho huzallatul marwas bare
har kuyi wannan yarjejeniya damu ka tsara?
Koda jin wannan batu sai tsoho isham ya bushe da dariya yace ai maso abinka
ya fika dabara kuma masu iya magana sunce samu yafi iyawam idan har muka
mallaki littafin tsatsuba a hannunmu munyi
mai wuyar da sannu zamu gano duk wani
sirri dake cikinsa
da jin wannan batu sai hankalin jaruma shumaira ya kwanta
zuciyarta ta cika makil da farin ciki amma da ta tuno irin
mugun hadarin dake cikin tafiyar da zasuyi kuma gashi tare da iyayen nata za ayi
wannan tafiya sai hankalinta ya
dugunzuma ainun ta rasa abinda yake yi mata dadi
haka dai ta yiwa iyayen nata sallama cikin sanyin jiki
ta tafi izuwa turakarta
kashegari kuwa tun kafin Alfijir ya keto kowa ya gama shirin
tafiya nan take aka hau dawakai aka kama hanya aka nausa cikin daji tsoho huzallatul marwas, sarauniya larbisa da sadauki humaisu ne akan gaba
jaruma shumaira da iyayenta kuwa sune a karshe domin
dakarun larbisa ma suna gabanta
bayan an shafe sa a guda ana tafiya sai tsoho
huzallatul marwas ya dubi sarauniya larbisa a
lokacin da suke tafiya kafada da kafada bisa dawakansu
yace ya shugabata kiyi
sani cewa ruwa baya tsami banza lallai akwai wata hujja mai karfi
wacce tasa iyayen shumaira suka siyar da rayuwarsu wajen
biyomu a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske.
Yayinda sarauniya larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene
a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu bata
hana zuwa sai dai a dade ba a jeba
.
Kamar yadda sannu sannu ba zata hana Guyson
ci gaba da rubuta muku wannan littafi ba saidai
a jima ba ajeba..
A nan nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe domin
jin Yadda zata kaya a cikin wannan Littafi Na tsatsuba
Amma kafin nan Nidinne
dai Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana Kenan
Daga Zauran Labarai
[4/13, 11:10 PM] +234 806 459 4218: TŠÅTŠµßÄ
Littafi Na Biyu (2)
Part C.
.
• еYŠºN • ke magana
.
Marubucin Littafin.
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing by
Al amin Ahmed Misau
Guyson Inkiyata Kenan
Daga Zauran Labarai
Call 08064594218
Doka Ban yarda ayi edit na Post dina ba..
.
Labari ya isowa Guyson Cewa..
.
YAYINDA SARAUNIYA larbisa taji wannan batu
sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai
zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana zuwa
sai dai a dade ba aje ba, Tsoho Huzallatul marwas ya
gyada kai yace tabbas zancenki Dutse ne
Larbisa tace wai shin yanzu ina Muka dosa ne?
Huzallatul marwas yayi murmushi yace in banda abinki
ya zaki tambayi kaza hanyar rafi, ni kaina ina bin
jagorancin jaka ne, duk inda naga ta nuna nan nake
bi damu
Amma ai idan baki manta ba zamuje neman jaruma
larifat ne wacce zata yi mana jagora a cikin
daji na biyu wanda shine dajin Ujurul majnun
ki kwantar da hankalinki don nasan cewar ba
zamu dauki wani dogon lokaci ba muna tafiyar zamu riske ta
bisa taimakon wannan jakar sihiri nawa.
Koda jin haka sai Larbisa tayi shiru bata kara cewa
komai ba
haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba rana
babu abinda yake sawa a tsaya ko a yada zango face
gajiya ko yunwa da kishirwa, har tsawon kwana uku
sannan suka iso wani babban birni mai kyau
gaske wanda aka kawatashi da gine gine masu
kyau da kawa
ita kanta sarauniya larbisa sai da wannan birni
ya birgeta ta raina kyawun nata birnin harma tana
cewa a cikin ranta lallai duniya da fadi hakama
abin cikinta a iya tunanin sarauniya larbisa ba za a taba samun birnin da
yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya da yafi nata
girma da kawatuwa ba a duniya amma sai gashi tun
kafin ma tafiya tayi nisa ta fara ganin cewar ba haka
bane
Tun daga nesa da masu gadin kofar birnin suka hango
tawagar sarauniya larbisa sukaga alamar cewar
manyan mutane ne masu daraja sai suka bude musu kofada sauri har daya daga
cikinsu yayi musu jagora izuwa fadar birnin
tun akan hanya kafin a isa fadar sai jaruma shumaira
ta matso kusa da larbisa ta dubeta tace to wai shin mu
yanzu menene yashigo damu cikin wannan
gari alhalin mun zo ne neman jaruma larift kuma ga
yadda aka bayar da labarinta ba zata yi rayuwa ba
a cikin gari sai dai a daji?
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace ai da dan gari
akanci gari, yanzu idan muka ce zamu tafi neman jaruma larifat
bamu san a cikin dajin da take ba amma da zarar
mun shiga cikin birnin zamu sami labarin inda take
wata kilama mu sami karin haske akan yadda zamu tunkareta ba tare da mun fuskanci
wata matsala ba
Al amin Ahmed Dan Garin Misau, Guyson Inkiyata Kenan
koda shumaira taji wannan batu sai tayi ajiyar
zuciya tayi shiru bata kara cewa komai ba...
Fadace kasaitacciya abar kwatance domin lokacin
da aka shigo dasu sarauniya Larbisa cikin fadar sai gaba
dayansu suka kama kalle kalle suka zama kamar yan kauye
saboda ganin irin kyan fadar da kawatuwarta
A wannan lokaci ne larbisa ta dada tabbatar
da cewar gaba da gabanta Aljani ya taka wuta
Ita dai a iya saninta a can nahiyoyin dake bangarenta
babu wata kasa mai
girma da karfin Arziki kamar kasarta don haka sai ta
fara tunanin cewa a duniyar ma gaba daya ba a taba samun kamarta ba amma a yanzu
da ta tsinci kanta a cikin wannan birni da wannan
bakuwar fada sai ta karyata kanta, wani kyakkyawan
saurayi ne na kwatance bisa karagar mulkin wannan fada ya yi babbar shiga ta
alfarma irin wacce attajiran sarakai da suka gawurta
ne kadai ke iya yinta
domin tufafin dake jikinsa darajarsu takai jarin
wani mashahurin attajirin, hatta takalminsa da kwagirin dake
hannunsa na lu'u lu'u ne a yatsun hannayensa na
hagu da dama akwai zobuna guda shida kuma duk na
zinare ne masu tsadar gaske, shi kansa rawanin dake
kansa da falmaran din dake jikinsa da zaren zinare
a aka dinkasu
koda jaruma shumaira da sarauniya larbisa
sukayi Arba da wannan sarki sai kyawunsa da kwarjininsa
ya dimautasu sukaji nan take sun kamu da tsananin sonsa
Hakika babu wata 'ya mace da zata ga wannan sarki
bataji ta kamu da tsananin sonsa ba, saboda baiwar
da allah yayi masa ta kyau da arziki, gashi idan
yayi ado sai kaga tamkar dawisu ne
koda shigowar su sarauniya larbisa cikin fadar
sai sarkin ya dubesu sau daya ya kau da fuska kuma
babu annuri akan fuskar tasa, Al amarin da ya dugunzuma
hankalinsu kenan domin a tunaninsu kyawunsu
kadai zai iya sawa sarkin yayi marhaban dasu bare
kuma ga matsayi na sarautar larbisa, cikin sanyin
jiki suka karasa kusa da karagar mulkin sukayi cirki
cirko
caraf sai tsoho isham ya zube kasa gaban sarki ya
kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da sarauniya
larbisa da jaruma shumaira ya kara da cewa
yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ba
wani abu bane ya kawomu birninka ba face neman
jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen nesa
saboda muna son tayi mana rakiya izuwa dajin ujurul majnun domin biyan
wata muhimmiyar bukata ta sarauniya Larbisa.
Koda jin wannan batu sai sarkin ya mike tsaye zumbur
daga kan karagarsa ta mulki. Fuskarsa cike da annuri
ya kama kafadun tsoho Isham ya tashe shi tsaye
ya jashi har kan karagarsa suka Zauna tare, su sarauniya larbisa ma sai yasa aka
basu kujeru na alfarma suka zauna sannan aka kawo
musu abinci da abin sha na alfarma suka kama kimtsa
cikinsu suna masu murna da mamakin yadda akayi
nan da nan ra'ayin sarkin ya sauya bisa jin abindake
tafe dasu
sai da kowa ya gama kimtsawa ya sami natsuwa sosai
sannan kyakkyawan sarkin ya dubi tsoho isham
yace yakai wannan dattijo kayi sani cewa yau shekara
bakwai kenan ina fama da tsananin so da begen
wannan jaruma larifat amma ko sau daya bata taba
kallona ba tayi mini murmushi bare ta karbi tayin
soyayyata sai dana kwanta rashin lafiya sau bakwai
sakamakon ciwon sonta da ya kayar dani amma bata
taba zuwa ta dubani ba ni da ita bata taba yi mini magana
ba kuma bata taba amsa gaiyatata ba izuwa
wannan gidan sarauta
Lokacin da na dameta da aika manzanni da kyaututtuka
iri iri na duniya sai ta tattaro duk abinda nake
bata na tsawon shekaru bakwan ta dawo mini dasu
gami da wasika
A cikin wasikar ne ta shaida mini cewa na daina bata lokaci
na da tunanina a kanta
domin ta daukarwa kanta alkawari cewar ba zata taba yin aure ba ko soyayya
har sai tayi gagarumin abin gwanintar da wani bai taba yi ba a duniya
lokacin da naji wannan batu sai na kamu da tsananin
bakin ciki kuma na fashe da kuka na takaici
domin banga ranar da larifat zata cika wannan buri
ba
daga wannan rana ne nima na yi alkawarin na
daina cin abinci mai dadi na daina kwanciya a wuri
mai kyau kuma na daina murmushi da sukuni
har izuwa karshen rayuwata face a ranar da naji cewar ta sami damar da zata cika burinta
A tsawon shekaru bakwai da suka gabata wannan dama bata
samu ba sai yanzu naji kunzo mini da wannan batun
na zuwa kogon Kitabul sihir inda littafin tsatsuba yake sai naji
a jikina cewar lokacin samun yardar larifat yayi a gareni
domin a yanzu ne zata iya yin jarumtakar da har abada
ba za a mance da ita ba a duniya, ko shakka babu na san cewa
larifat zata karbi wannan
tayi naku domin bata tsoro ko shakkar wani abu
mai rai akan biyan bukatarta, babu wani abu wanda
zaku iya biyanta da shi domin ta wuce daku ta cikin
dajin ujurul majnun face kwadayin cika na ta burin
ba wani abu da yake burge jaruma larifat a cikin wannan duniya, saboda ta rasa iyayanta yan uwanta da dukkan danginta
bisa wannan daliline ta kebe kanta daga cikin mutane
ta koma cikin daji da zama inda ta zabi ta karasa sauran
rayuwarta gaba daya
yanzu dai a gajiye kuke, don haka zan sa a kaiku
masauki ku huta washe gari da safe ni da kaina
zanyi muku jagora izuwa dajin Da jaruma larifat
take domin ku gana da ita, ku sanar da ita bukatar dakuka zo da ita a gareta.
Amma ina neman wata alfarma guda daya a wajanku?
Alfarmar kuwa itace ina son nima nayi muku
rakiya a cikin wannan tafiya domin idan kuka tafi
kuka barni fargaba tunani da begen halin da
larifatke ciki zai iya jefani cikin wani mugun hali
koda sarki AYUBUL HASNU yazo nan a zancensa sai kowa
ya cika da mamaki musamman sarauniya larbisa
da shumaira
Kai ni kAina Guyson saida na cika da mamakin
wannan sarki
sarauniya larbisa ta dubi sarki Ayubul hasnu cikin
mamaki tace yakai wannan sarki mai daraja kayi
duba izuwa wannan daula da kake ciki ka dubi
girman kasarka da tarin arzikin dake cikinta ka sani cewa
akwai mata da yawa masu kyau a sassan duniya
wadanda zaka iya mallakarsu da karfin dukiyarka
da mulkinka saboda me yanzu zaka siyar da
rayuwarka don baiwarka?
Lokacin da sarki ayubul hasnu yaji wannan tambaya daga
bakin sarauniya larbisa sai ya bushe da dariya
kamar ba zai daina ba daga bisani kuma sai ya
hade fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa
nan fa fadar tayi tsit kamar babu mai rai a cikinta
kawai sai aka ga idanun sarki ayubul hasnu sun ciko
da kwallah har hawaye ya zubo masa, sarki ayubul hasnu
ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace
yake sarauniya larbisa kiyi sani cewa a duniya babu
wani abu wanda yafi soyayya karfi da hadari
masoya da yawa sun rasa rayuwarsu akan tafarkin mallakar masoyansu
ba komai ne ya janyo hakan ba face duk rayuwar
da babu masoyi dai dai take da zama a cikin kurkukun
daurin rai da rai kisan sani cewa ke da jaruma
shumaira duk kun kasance kyawawan matan da babu kamarsu a duk cikin fadin kasata da
nahiyarmu amma kuma baku kama farcen kafar
jaruma larifat ba a fagen kyau kunga kenan
a yanzu babu wata ya mace da zata iya maye gurbin
larifat a wajena banda fagen kyau a bangaren jarumta
kuwa ina mai tabbatar muku da cewa in daku biyun
nan zaku hada karfinku ku yaketa ba zaku taba samun galaba a kanta ba
koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da
jaruma shumaira suka bushe da dariya domin su a
ganinsu ma tatsuniya ce abinda sarki Ayubul hasnu yake fadi
shumaira ta dubeshi tace aiko yarima RUHAISU dan sarki ZAIYANU na birnin kufa wanda masana da masu
bincike suka tabbatar da cewar babu mai karfin
damtsensa da sa arsa idan muka hada karfi nida larbisa sai mun gama dashi bare wata jaruma larifat wacce ta
kasance 'ya mace kamarmu
yayinda sarki Ayubul hasnu yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ai
shi kenan inda babu kasa nan ake gardama
Kokowa, ni dai shawarata guda daya ce a gareku
duk abinda zakuyi kyi shi da cikakkiyar hujja
domin banson ku yi irin kuskuren da SADAUKI HULKAS MAI HULAR LAMSARA YAYI.
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma shumaira suka
dubi junansu cikin mamaki larbisa ta juyo ta dubi sarki
Ayubul hasnu tace wanene kuma sadauki Hulkas
mai hular lamsara?
Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubu
hasnu yayi ajiyar zuciya gami da sauke dogon
numfashi sannan yace labari ne mai tsawon gaske sai dai nayi
iya kokarina na gani ko zan iya gajarce muku shi...
SADAUKI HULKAS YANA DAGA CIKIN MANYAN JARUMAN DUNIYA GUDA UKU
wadanda akayi musu lakabi da MAZAN JIYA
jarumai ne wadanda ba a taba yin kamarsu ba kuma ba za ayi ba
a yanzu da nan gaba domin sun bar abin tarihin
da ba za a taba mancewa dasu ba
sai dai kash
duk su ukun rayuwarsu ta salwanta ne a
tafarkin soyayya
Yanzu dai saiku saurara da kyau kuji wannan labari domin
akwai dumbin darasi a cikinsa, nan take sarki
AYUBUL HASNU ya shiga basu labari kamar haka......
.
Hm yanzu ne zamu shiga cikin labarin gadan gadan
a yayinda zakuji Labarin sadaukin sadaukai Hulkas mai hular
lamsara
kuma daya daga cikin jaruman duniya Mazan jiya
saboda haka
sai ku gyara zamanku
Amma kafin nan Nidinne
dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana kenan
Admin Na zauran Labarai
nake cewa sai Allah ya kaimu gobe zamu ci gaba.....
Guyson By nickname
2go Nickname
The King Of PSP Group..
[4/13, 11:10 PM] +234 806 459 4218: TŠÅTŠµßÄ
Littafi Na Biyu (2)
Part D.
.
• еYŠºN • ke magana
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Rubutawa..
Al amin Ahmed Misau
Guyson Inkiyata Kenan
Admin Na Zauran Labarai
Call 08064594218
Doka Ban yarda ayi edit na post dina ba..
:
labari ya isowa Al amin Guyson cewa...
.
NAN TAKE SARKI AYUBUL HASNU YA SHIGA BASU LABARI KAMAR HAKA.
kimanin shekaru Ashirin da hudu da suka shude a birnin Romaniya
anyi wani azzalumin sarki mai suna SHARDAS IBN KAUMIL
sarki shardas ya kasance gawurtaccen jarumin sadauki mai tarwatsa maza
a filin daga yana da tsananin karfin damtse na Allah ya isa
don ance ko giwa ya yiwa naushi daya saita fadi kasa
kisan kai kwace da cin zali kuwa bai maidasu komai ba
A cikin wata daya yakan shirya dakarun sumame
su kai mamayar bazato izuwa ga ayarin fatake ko
izuwa ga manyan garuruwan da suke da karfin
arziki
cikin bad da kama su kwato bayi da dukiya da mata ba
tare da an shaida ko su waye ba, a bisa wannan halaiya ne ya
addabi gaba dayan kasashen
dake nahiyar gaba daya kuma gashi an kasa gano
mutanen dake yin wannan barna, babu irin matakin da sarakuna
basu dauka ba kuma babu irin binciken da bokaye basuyi ba don gano rundunar
dakarun dake wannan mummunar barna amma
abu ya gagara
babban abin bakin cikin ma shine sarki shardas ya
tara dukiya mai tsananin yawan da jikokinsa ma da
tattabakunnansa ma ba zasu iya cinyeta ba amma duk da haka
bai daina yin wannan fashi
da kwace ba
Masana da masu bincike na wannan zamani sun
tabbatar da cewar duk duniya babu wani sarki da ya kai
sarki shardas tarin dukiya kuma babu wani gidan
sarautar da yakai nashi girma da kawatuwa,duk
bayin da ya kamo da mata ana boye sune a gidajen gonarsa
da wani bangaren daban na gidan sarautar inda har
abada ba za a sake ganinsu ba bare ma wani ya
shaida dayansu asirinsa ya tonu a gane cewa shine
dan fashin da ya addabi Mutane a nahiyar
Tunda yake kamo Bayi da mata ba ataba samun wanda ya
taba guduwa ba daga cikinsu ya tsira da rayuwarsa
face sarki shardas yasa anbi bayansa an kasheshi
saboda tsananin tsoron da ake yiwa dakarun sarki shardas ne
yasa aka musu lakabi da suna DAKARUN AJALI
wata rana sarki shardas tare dakarunsa kimanin
mutum dubu uku sun fito mamayar bazato izuwa wani babban kauye da ke gefen wata makociyar kasa da ake
kira salmas sai suka kai
hari izuwa ga ayarin wadansu matafiya masu
yawan gaske wadanda suka yada zango a gefen kauyen
wanda ake kira Malgur.
Su dai wadannan matafiya suna da tarin shanu
tumaki da raguna masu yawan gaske kuma Allah
ya albarkacesu da kyawawan mata ababan kwatance
ga kuma tarin zuri'a
Al amarin ya faru ne da yammaci sakaliya daf da
faduwar rana shugaban wannan ayari saurayi ne
ma aboci kyau kwarjini da jarumtaka ana kiransa
da suna Hailur, a wannan rana ne hailur yayi
aurensa na farko a duniya kuma matar da ya aura
budurwace yar shekara goma sha takwas a duniya wacce
babu mai kyawunta a duk cikin zuri ar ayarin gaba
daya
A wannan lokaci wannan ayari sun shagala a cikin
bikin auren hailu ana ta kade kade da raye raye saboda murna
kowa da kowa ya zage yana ta rawa
maza da mata yara da manya gaba daya dakarun
ayarin dake tabbatar da tsaro sun ajiye makamansu
sun shiga cikin taron 'yan rawa suna cashewa
kwatsam ba zato ba tsammani sai gani akayi dakarun Ajali sun bullo daga kowace
kusurwa gabas da yamma kudu da arewa bisa
dawakai aguje kuma sun zare makamai suna ihu da
kururuwa nan fa taron biki ya watse mata, yara da tsofaffi suka kama ihu da guje
guje suna neman maboya, a dai dai wannan lokaci
ango Hailur na tare da amaryarsa shadila a cikin tantinsa
suna more amarcinsu kwatsam sai suka jiyo iface iface
da guje gujen jama arsu
a rude ango Hailur da amarya shadila suka mike
tsaye zumbur daga kan shimfidarsu suka suri suturarsu suka sanya
hailur yayi waje ya dauko takobinsa da garkuwarsa ya
dubi shadila yace komai
wuya komai rintsi kada ki fito daga cikin wannan tanti
indai kika kiyaye wannan umarni nawa ni dake duk zamu
tsira daga sharrin wadannan yan harin bazati
kada ki kuskura kiyi ihu ko maganar da wani zai jiyoki
shadila ta kada kai cikin alamun tsananin damuwa
tace lallai zan kiyaye wannan umarni naka
nan take hailur ya sumbaci goshin shadila sannan ya
juya zai fice daga cikin tantin sai tayi wuf ta
ruko hannunsa ta rungume shi tana mai fashewa da kuka
ba komai ne ya sa tayi hakan ba face taji a jikinta
cewar abune mawuyaci su sake ganin juna,
ba komai ne ya tabbatar mata da hakan ba face ta
dan leka wajan tantin daga tsananin yawan dakarun
sumamen da suka kawo musu hari tasan cewa
tabbas an shammaci nasu dakarun ba zasu iya kare kansu ba
Al amin Ahmed Misau
Guyson inkiya ta kenan
Daga zauran Labarai page.
Facebook..
Cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin nata ya
sake dubanta cikin yanayi mai nuna yarda dakai
yace ki barni kamar yadda kika saba
ni nasan dabarar da zanyi na kubutar da rayuwarki da tawa, shin kin
manta ne da cewar irin wannan ta taba faruwa shekaru
uku baya sa adda wata rundunar yan fashi suka
ritsamu a daji mu biyu rak nidake muna kiwo?
Ko dajin wannan batu sai
Shadila ta gyada kai cikin murmushin karfin
hali tace haba ya masoyina ai ba zan taba mancewa da
wannan gagarumar jarumtaka da kayi ba, koda
jin haka sai fuskar hailur ta fadada da murmushi yace
to wannan karon ma abinda zai faru kenan baya ga
wannan ina mai yi miki wani babban albishir
cikin matukar mamaki da zakuwa shadila ta zaro
idanu tace wane irin albishir kuma zakayi mini yanzu?
Hailur yace boka zaifur ya gaya mini cewa a ranar
farko dana sadu dake juna biyu zai shiga don haka
yanzu ina mai tabbatar miki da cewa kina dauke da
cikin dana
kona mutu a wannan yaki bani da nadama ko takaici
na san cewa na bar wanda zai kula dake
Yayinda shadila taji wannan batu sai hawaye ya
zubo mata tace lallai ina son ta kowanne hali
ka rayu a wannan yaki kuma mu tsira tare domin babu abinda
na tsana a wannan duniya sama da dana ya
taso maraya
hailur yayi murmushi yace nayi miki alkawari cewar
danki ba zai taso a maraicin rashin uba ba
yana gama fadin hakan sai ya juya da sauri ya fice da gudu
daga cikin tantin
Ai kuwa yana fitowa yaga yadda ake ragargazar jama arsu ana saransu
da sukarsu suna ihu jini na tsartuwa
fallatsi da malala suna zama gawa sai ya fusata
ainun ya kwarara uban ihu ya zare takobinsa daga
cikin kufenta ya afkawa dakarun sumamen ya hausu
da sara da suka ya zame musu guguwar annoba
a wannan lokaci hankalin sarki shardas yana kan bayi mata
da ake ta kamawa da kuma dukiyar da ake diba
amma ko da yaji ihun dakarunsa ya yawaita a wani
bangare daban sai ya juyo da sauri izuwa wajan
take ya hango jarumi Hailur yanata ragargazar dakarunsa
duk inda hailur yasa gabansa sai dai kaga maza na.
Zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona Al amarin
da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan
dimin tunda yake fita sumame da yaki bai taba ganin jarumi
mai irin
zafin naman hailur ba gami da tsagwaron jarumtakarsa
duk da cewar a wannan lokaci dakarun sarki
shardas sun kashe kaso takwas daga cikin kaso goma na
jama ar jarumi hailur sai da ran sarki shardas ya baci
ainun
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone
cikin tsananin fishi sarki shardas ya takarkare ya
kwarara wani uban ihu wanda ya firgita komai da kowa
dake cikin dajin aka
daina yakin aka tsaya cak tamkar babu abu mai rai
a wajen
a lokacin da amon ihun sarki shardas ke tayin amsa
kuwa a dajin gaba daya
shi kansa jarumi hilairu sai da ya firgita bisa jin wannan kururuwa
ya kura idanu izuwa sashin da
kuwar ta fito
da yake a sannan ne kurar yakin take lafawa sai da yan dakiku
suka shude sannan ya hango sarki shardas ya tunkaroshi daga
can nesa kadan take zuciyar jarumi hailur ta buga da karfi ya ji tsoro ya
darsu a cikin ransa a karon farko a duk gwagwarmayar
da yakeyi da mazaje a rayuwarsa bakomai ne ya haddasa
hakan ba face a iya rayuwar jarumi hailur bai taba
ganin mutum mai kirar sadaukai da kwarjininsa
ba kamar sarki Shardas duk da cewar fuskar sarki
shardas a rufe take cikin rawani sai da jarumi
hailur ya gane cewa lallai wannan sadaukiba saurayi
bane shekarunsa sun kai arba in da 'ya'ya kuma idanunsa
ya kalla kawai ya gane hakan
Al amin Ahmed Misau
guyson sunana kenan
abinka da jarumi mai dakakkiyar zuciya kuma
wanda baya fidda rai ga samun sa a da rabo sai
hailur ya gyara tsayuwarsa ya rike takobinsa da
garkuwarsa da kyau
koda ganin haka sai sarki shardas yayi murmushin
mugunta kawai sai shima ya zare takobinsa daga cikin
kufenta wata irin takobi ce mai tsawo da kaifi kuma
anyita ne da wani irin karfe na musamman wanda sai kwararren makeri ne zai
iya gano hakan take sarki shardas ya falfalo
da gudun tsiya izuwa kan jarumi hailu
duk sa adda sawun kafafun sa suka taba kasa sai
kaji kamar takun giwa ne saboda nauyinsu
Koda jarumi Hailur ya hango sarki shardas ya rugo
izuwa kansa cikin mugun nufi haka sai shima ya ruga izuwa
gareshi duk su biyun suna ihu
da karaji
yayin da ya rage saura baifi taku biyar ba su hadu
sai kowannansu ya daka tsalle sama yakai wawan
hari
sarki shardas ya kaiwa hailur sara a wuya da
nufin ya cire masa kai hailur ya kare saran da
garkuwarsa take garkuwar ta rabe gida biyu tamkar
an yanka tsakiyar tufa da wuka cikin zafin nama hailur
ya kaiwa shardas suka da takobinsa a ciki
shardas yasa garkuwarsa don tare sukan amma duk da haka sai da takobin ta huda rigarsa
ta tsargeta in ba
don ma ya kare harin ba cikin zafin nama dasai
takobin ta huda cikinsa
koda suka duro kasa sai kowannansu ya cika da mamaki shi dai sarki shardas bai taba karo da jarumin
da ya taba samun nasarar ko da lakutar rigar jikinsa ba
amma yau gashi ya hadu da wanda ma ya tsargeta
da takobi shi kuwa jarumi hailur firgita yayi ainun
bisa ganin yadda takobin sarki shardas ta tsarge
garkuwarsa gida biyu
don haka ya tabbatar da cewar duk sa adda takobin
shardas ta sami jikinsa ba karamar illa zata yi masa ba
Guyson Sunana Kuma nake magana,
nan fa Hailur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya iya
kare kansa koda ya dubi garkuwar dake hannun sarki
shardas
sai yaga anyi tane da irin karfen da akayi
Takobin, cikin sauri hailur ya dubi kaifin takobinsa
sai yaga she har ta dan dakushe a wajen tsininta
sakamakon haduwa da tayi da garkuwar sarki Shardas
Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin
hailur kenan ya
tabbatar da cewar babu wata hanya da zai iya kare
kansa a wajen sarki shardas face ya kwaci garkuwar
dake hannunsa yin hakan kuwa yasan cewa ba karamar sa a bace da nasara
Al amin Guyson sunana
A wannan lokaci gaba dayan dakarun sarki shardas
da tsirarun dakarun su hailur da sukayi saura a wajan
sun zuba idanunsu a kansu kawai kowa so yake
yaga yadda karshen wannan gumurzu zai kasance
tamkar dacan ba yaki ake ba a wajan su kuwa
matan da aka kama amatsayin bayi aka daddauresu
tuni sun fara kuka tare da ya yansu kananan yara wadanda kusan su duka
an kashe iyayansu maza an mai dasu marayu
sai da kimanin dakiku dari da arba in suka shede ana
kallon kallo tsakanin sarki shardas da jarumi
hailur kowannansu tunanin dabarar da zaiyi
ya cutar da abokin gwaminsa yake sannan suka sake
rugawa izuwa kan juna a karo na biyu
suna haduwa asama sai sarki shardas ya kawowa
hailur sara a cinya shi kuma yakai masa sara a ka kowannansu
yayi iya kokarinsa
wajan kaucewa harin
cikin zafin nama amma sai da takobin sarki shardas
ta yanki hailu ta dara naman cinyar jini yayi
tsartuwa hailur ya kwala uban ihu sakamakon tsananin
zafi da zogin da yaji
shi kuwa sarki shardas bai ankara ba sai gani yayi
hailur ya tuje rawanin dake kansa ya fado kasa
sai ga fuskarsa ta baiyana a fili karara kafin su duro kasa
gaba daya tuni hailur ya doki hannun sarki
shardas mai dauke da garkuwa garkuwar ta subuto
kasa cikin bakin zafin nama hailur ya fada kan garkuwar
ya sureta kuma yayi 'yardungure sau uku
izuwa can gaba
yana mikewa tsaye yayi sauri ya yagi rigar jikinsa
ya daure raunin cinyar tasa don tsaida jini
shi kuwa sarki shardas ko da yaga tsirarun dakarun
su hailur sunyi arba da fuskarshi kuma sun shaida
ko shi wanene sai ya dakawa dakarunsa tsawa yace
su karasasu gaba daya
take dakarun suka hau tsirarun dakarun da sara da suka
suka karkashesu a cikin 'yan dakiku kadan
koda ganin abinda ya faru sai jarumi hailur ya kurma
uban ihu ya ruga izuwa kan sarki shardas
har dakaru sun yunkura zasu tareshi sai sarki
shardas ya tsaidasu yace ai wannan nawa ne
ba naku ba kuma abin kunya ne a ce nidaku munyi masa rubdugu
ku zuba ido kamar yadda
kukayi da farko kuga yadda
zamuyi dashi
koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya tari jarumi
hailur suka ci gaba da kaiwa juna mugayen hare hare
wannan karon dai sarki shardas yana kaiwa
hailur sara da suka ne da dukkan karfinsa cikin
azababben zafin nama na gaban kwatance
Kaico mai karfi sai Allah ya isa kuma na gaba yayi gaba
na baya sai labari
duk da irin tsananin juriya da jarumtaka irin ta hailur
wannan karon sai da ya raina kansa domin
bambancin a baiyane yake kuma sarki shardas
ya shammaceshi wajan sauya salon fadan, a lokaci
guda ya hada da kai masa naushi da bugu da
hannu da kafa sai gashi nan da nan ya hadawa
hailur jini da majina yana bal dashi kamar tamola...
.
Tab ganin wannan yanayi da hailur yashiga
ya sa ni Guyson na tsaya a nan kafin nan
kuma
Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana Kenan
Admin a zauran labarai
nake cewa sai kUma Allah ya kaimu Gobe zamu ci gaba
[4/13, 11:10 PM] +234 806 459 4218: TŠÅTŠµßÄ
Littafi Na Biyu (2)
Part E.
.
• еYŠºN • ke magana
.
Marubucin Littafin.
Abdul aziz Sani M/Gini
Typing By..
Al amin Ahmed Misau
Guyson Inkiyata Kenan
Daga Zauran Labarai
Call 08064594218
Doka itace ban yarda ayi edit na post dina ba
.
Labari ya isowa Guyson cewa..
.
SAI GASHI NAN DA NAN YA HADA MISHI JINI DA MAJINA
YANA BAL DASHI KAMAR TAMOLA, ashe duk wannan abu
dake faruwa shadila ta leko ta cikin tantin da take
tana ganin abin dake faruwa cikin tsananin fargaba da tashin
hankali kwatsam
sai sarki shardas ya sami nasarar saran kafadar hailur ta
hagu hailur ya kurma
ihu a lokacin da jini yayi tsartuwa a kafadar tasa amma sai yayi sauri ya rike
takobin ta
sarki shardas a lokacin da shi sarki shardas ke son ya danna
takobin ta nutse a cikin kafadar
koda shadila ta hango abinda ya faru ga mijinta saita
kurma ihu bata san sa adda ta fito da gudu daga cikin
tantin da take boye ta rugo izuwa inda suke
jiyo ihunta da gudun tane yasa sarki shardas ya waigo
yayi arba da ita koda yaga irin tsananin kyawunta sai ya dimauce ya juya
da sauri ya doke kirjin hailur da karfin gaske saboda
karfin dukan saida hailur yayi tsalle sama da baya
kamar an janyeshi da majajjawa ashe bayan nasa
wani rami ne mai tsananin zurfin tsiya wanda karshensa
kwazazzabo ne da magudanar ruwan wata korama
koda hailur yaji ya fada cikin wannan rami sai ya
kwarara uban ihu irin na wanda ya saddakar mutuwa zaiyi
ita kuwa shadila tana ganin abinda ya faru ga mijinta sai ta sulale kasa sumammiya
sarki shardas ya bushe da dariyar farin ciki ya
ruga da baya izuwa inda shadila ke kwance ya dauketa ya azata
akan dokinsa
nan take
dakarunsa suka kwashe gaba dayan dukiyar wannan ayari nasu hailur suka ingiza keyar bayin da suka kama akayi gaba
ana tunkarar birnin Romaniya
Al amin Ahmed Misau Guyson inkiyata Kenan
Ana fara tafiya sai sarki shardas ya sake rufe fuskarsa da
bakin rawani kuma ya shakawa shadila banju barcinta ya sake nauyi
don haka bata farka ba har aka isa birnin romaniya
da tsakiyar dare
lokacin da shadila ta farka daga barci sai ta tsinci
kan wani luntsumemen gado na alfarma a cikin
wani kasaitaccen daki na sarauta cikin razana ta mike tsaye da sauri ta sauko daga
kan gadon, ta kama
kallon kowacce kusurwa
koda tagama ganin kayan kawar dake cikin dakin sai
tunanin mijinta da sauran jama arsu ya fado mata
ta tuno da duk abinda ya faru a sansaninsu sa adda
aka kawo musu sumame na mamayar bazato
nan take shadila ta dafe kunnuwanta da hannayanta biyu ta kurma uban
ihu tana mai fashewa da matsanancin kuka
faruwar hakan keda wuya sai taji an bude kofar
turakar
ba wani bane ya shigo cikin turakar face sarki shardas a cikin wata irin
kyakkyawar shiga ta sarakai fuskarsa cike da annnuri
ya durfafeta
koda tayi arba dashi sai ta razana ainun taja
da baya tana mai nunashi da yatsa a lokacin
da hawaye ya zubo mata tace ka cuceni ka kashe
mini miji
kuma ka kashe dukkan mazajen ayarinmu ina sauran
yan uwana mata?
Me kake nufi dani ka kawoni nan ni kadai
kawai ka kasheni na huta da kunci da bakincikin
rayuwa tunda ka rabani da masoyina da dukkan
zuri ata
koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe
da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dubeta yace
yake wannan ma abociyar kyawu da cikar zati
kiyi sani cewa kece mafi sa a bisa dacewa da zama
matar sarkin birnin Romaniya a yanzu
duk wata rayuwa da kikayi a baya ki manta da ita
ki manta da komai da kowa ki fuskanci
sabuwar rayuwar da tazo miki wacce zaki tsinci
kanki a cikin daular da baki taba ji da gani ba
koda jin wannan batu sai zuciyar shadila ta kama tafarfasa kamar zata kone
saboda tsananin fishi taji ta tsani sarki shardas
fiye da komai a doron kasa koda idanunta suka kai
kan wata wukar dake kan wani faranti babba mai
dauke da tuffa masu yawa sai tayi zumbur ta suri wukar
ta ritsa sarki shardas da ita tace kada ka kusanceni
idan ka matso kusa dani zan kasheka.
Al amin Guyson. Sarki shardas ya bushe da mahaukaciyar
dariya ya durfafeta kai tsaye
ai kuwa yana kusantarta sai ta caka maza wukar a kirji take wukar ta balle gida biyu taji kamar akan
dutse ta bugata
kawai sai sarki shardas ya hankadata ta fada kan gadon dake bayanta sannan ya bita izuwa kan
gadon bai rabu da ita ba har sai da bukatarsa ta biya
tana ta faman rusa ihu da kukan bakin ciki
daga wannan rana shadila ta zama matar sarki
shardas da karfin tsiya ya zamana cewa kullum a cikin daula take
babu abinda takeyi da hannunta sai dai kuyangi da barori
suyi mata duk da cewar ta tsinci kanta a cikin daula irin
wacce bata taba ji da gani ba sai ya zamana cewa
kullum a cikin kuka da bakinciki take musamman
idan ta tuno da tsohon masoyinta kuma sabon
angonta hailur da kuma sauran danginta da zuri arta
lokacin da shadila ta matsawa sarki shardas
akan sai taga inda aka kai sauran +yan uwanta mata wadanda
aka kama a matsayin bayi sai yayi mata jagora
izuwa wani bangare daban na gidan sarautar wannan ranace
ta farko wacce shadila
ta sami damar fita daga bangaren da turakarta take
koda taga yadda girman gidan sarautar yake da yawan dakarun dake tsaro a ko ina sai hankalinta ya dugunzuma ainun domin take
burinta na son guduwa ya yanke, haka dai sarki
shardas yaci gaba da yiwa shadila jagora suna ta
ratsawa ta cikin lunguna da sakuna har sai da
sukayi tafiya mai nisa
duk inda suka ratsa sai dai kaga bayi barorim hadimai da dakaru suna risinawa suna
gaishesu har suka iso wani katon gida wanda ke cike da bayi mata
koda shadila tayi arba da yan uwanta mata
yan zuri arsu suna ta yin ayyuka na bauta iri iri sai ta ruga garesu tana mai
kiran sunayansu daya bayan daya tana zubar da hawaye
take suma bayin suka rugo gareta suka rungumeta suna kuka
bayan ta dan jima a kankame dasu sai ta janye jikinta daga cikin nasu ta juyo ta dubi sarki
shardas tace ina neman alfarmar ka yanta wadannan yan uwa
nawa daga matsayin bayi masu aikin bauta zuwa ga kuyangina.
Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi
shiru yana mai sunkui da kai ya dubi shadila
cikin murmushi yace yake matata kiyi sani
cewa babu wani abu da zaki nema a wajena ki rasa
saboda tsananin irin son da nake yi miki don haka
zanyi miki wannan alfarma bisa sharadi guda
shardin kuwa shine wadannan bayi idan suka koma can wajanki ba zasu
taba fita ba daga cikin harabar gidanki
duk wacce aka kama da laifin hakan hukuncin
kisane a kanta
koda jin haka sai farinciki ya lullube bayin suka fara
rungume shadila sunayi mata godiya ita kuwa shadila sai ta dubi
sarki shardas
tace na amince da wannan sharadi naka
nan take sarki shardas ya sa dakarun dake kula da
wadannan bayi suka kwankwance musu
sarkokin dake wuyansu da hannayensu sannan aka
tafi dasu izuwa can bangaren gidan shadila a nan ne aka basu suturu masu
kyau sukaje sukayi wanka suka sanya suturu
Guyson nake Magana Daga Zauran Labarai Page
tunda aka kawo shadila wannan gidan sarauta na birnin
romaniya bata taba yin farin ciki ba sai a wannan rana
da aka 'yanta wadannan bayi kuma bata taba yiwa
sarki Shardas murmushi ba sai a yau din nan
Hakika shadila ta tsani sarki shardas fiye da
komai a duniya kuma inda tana da ikon kasheshi
ko guduwa daga gidan sarautar da tuni ta aikata
haka dai dai da rana daya shadila bata taba
mancewa da mijinta ba Hailur kusan kullum sai
tayi mafarkinshi
sau tari a mafarkin nata ana nuna mata cewar hailur
yana nan a raye bai mutu ba amma idan ta tuno
da tsananin zurfin ramin da ya fada sai taga cewar
mafarkin nata ba zai taba zama gaskiya ba
babban abinda take yin nadamar aikatashi shine karya sharadin
da tayi a lokacin da hailur ya gaya mata cewa
komai tsanani kada ta kuskura ta fito daga cikin
wannan tanti da take amma sai ta mance da sharadin
ta fito da gudu bisa dimaucewar da tayi a lokacin
da taga sarki shardas ya sareshi da takobi a kafada
ta kwalla ihu ta fito da gudu ta baiyana kanta
Tabbas inda bata fito ba da sai hailur ya kubuta
daga sharrinsa kuma da sai sun gudu tare
lokacin da shadila ta sami wata uku a cikin gidan sarautar
sarki shardas sai alamun juna biyu suka baiyana
a gareta
ya zamana cewa tana fama da tashin zuciya, kumallo
da zazzafi da ciwon kai
ko da sarki shardas yaga shadila bata da lafiya
sai hankalinsa ya dugunzuma nan take ya tura aka
kirawo wata likita tazo ta dubata cikin murmushi
likitar
ta dubi sarki shardas tayi masa bushara cewar matarsa
ta sami juna biyu
Koda jin haka sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin
ciki amma da ya tuno da wani al amari sai hankalinsa
ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci take zuciyarsa
ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama kyarma bai san sa adda yasa
hannu ya zabgawa shadila mari ba, saboda karfin
marin saida ta fadi kasa bakinta ya fashe jini yazubo
sarki shardas ya sunkuya ya kamo kafadunta yana mai
daka mata tsawa yace wanene yayi miki ciki ban sani ba
a cikin gidan sarautata kiyi sani cewa yau shekara
ashirin kenan ina neman haihuwa ban samu ba kuma matana
na aure guda goma sha shida ne a cikin gidannan
bokana ya tabbatar mini da cewar ba zan taba haihuwa
ba har sai na mallaki wata hular sihiri wacce ake kira
LAMSARA.
Lallai wannan ciki da kike dauke dashi ba nawa bane
maza ki hanzarta sanar dani maishi kona shakeki ki
mutu yanzu
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai shadila ta
bushe da dariya al amarin da yayi matukar baiwa sarki
shardas mamaki kenan kuma jikinsa yayi sanyi ya
mike tsaye yana mai kura mata idanu, shadila ta yunkura
ta mike tsaye ta dubi sarki shardas a fusace tace shin kana
tunanin ina tsoron mutuwa ne? To ka sani cewa duk wannan
daula da nake ciki a wannan gidan sarauta daidai
yake da kurkuku a wajena, gaba daya rayuwar duniya
ta fita daga raina tun daga ranar da ka wargaza
rayuwata ka rabani da babban masoyina hailur
kuma ka tarwatsa ayarinmu, ka sani cewa wannan hari
da kuka
kai mana an kashe uwata da ubana da dukkan dangina
a yanzu bani da sauran masoyi a doron kasa face masoyina
hailur wanda har yanzu xuciyata ke wasu wasin
cewar yana nan a raye bai mutu ba idan har yana raye ina tabbatar maka da
cewa sai yazo har nan gidan sarautar ya daukeni
mun tafi domin wannan juna biyu da nake dauke dashi nasa
Ne bana wani ba, kafin shadila ta gama rufe bakinta ya
sake zabga mata mari ta baje a kasa sumammiya nan take
kuyangi suka rugo izuwa kanta suka shiga ceto rayuwarta
koda ganin haka sai sarki shardas ya rude yayi nadamar
abinda ya aikata saboda tsananin son da yake yiwa
shadila don haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba har kwallar takaici ta zo masa
A fusace ya baro turakar shadila ya aika aje a kirawo
masa babban bokan birnin wanda ake kira da Barwas ibn Mus ab
Lokacin da ya isa wajan boka barwas sai ya labarta
masa duk abinda yake faruwa
nan take bokan yake shaida masa abubuwan
matakin da ya kamata ya dauka yake cewa akan
wannan juna biyu data samu ya kasance mai nuna
mata kauna kulawa da soyayya irin wacce ma baka taba nuna mata ba
ka zamo mai tarairayarta kada ka bari koda kuda ya
taba lafiyarta
kuyi renon cikin tare kai da ita har izuwa sa adda zata haihu
lafiya kuma har izuwa sa adda yaron zai cika shekara bakwai a wannan lokaci kun shaku ainun
da yaron kawai saika tsiri tafiya wannan tafiya kuwa nine zanyi maka jagora a cikinta
kuma ba zamu dawo ba har sai mun sami nasarar
mallakar hular lamsara ina mai tabbatar maka da cewar
da zarar mun mallaki hular lamsara tamkar mun dora duniyar nan ne dukanta a tafin hannunka
komai da kowa sai ya
dawo karkashin ikonka kuma babu wani makiyinka da zai
iya samun nasara a kanka
.
Anan zan dakata haka
amma kafinnan
Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana kenan
Admin Na
Zauran Labarai
[4/13, 11:10 PM] +234 806 459 4218: TŠÅTŠµßÄ
Littafi Na Biyu (2)
Part F.
.
• еYŠºN • ke magana
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz sani m/gini
typing by..
Al amin Ahmed Misau
Guyson Inkiyata Kenan
Daga Zauran Labarai.
.
Labari ya isowa Guyson cewa...
Lokacin da boka Barwas yazo nan a zancensa
sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki
bai san sa adda ya rungume boka barwas ba yana mai
kyalkyala dariya daga can kuma sai ya janye jikinsa
daga cikin
nasa suka fuskanci juna ya dubeshi yace
tabbas yanzu na sami nutsuwa da kwanciyar hankali
saboda haka ka zuba idanu kawai kasha kallo
zaka ga abin da zai biyo baya, koda jin haka
sai boka barwas ya kyalkyale da dariyar farin ciki yayi ta kyakyatawa kamar ba zai daina ba daga can kuma
saiya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dubi sarki shardas cikin alamun tsananin
damuwa yace ya shugabana yaya batun
alkawarinmu idan bukata ta biya? Koda jin wannan
tambaya sai sarki shardas ya bushe da dariya yace
ai alkawarina dakai dutse ne babu abinda zai kankareshi
face rashin biyan bukatata, daga wannan rana sarki
shardas ya fara aiki da shawarar boka barwas ya zamana
cewa ya karbi juna biyun shadila hannu biyu
ya rinka riritata da kyautata mata fiye da kowa
Al'amarin da yayi matukar baiwa shadila mamaki
kenan tun tana ganin abin kamar yaudara ce taga ashe
zahiri ne kuma gaskiya domin babu abinda fuskarsa
da zuciyarsa ke nunawa face tsananin soyayya da kulawa
Abu dai kamar wasa a cikin wata uku kacal
sai gashi shadila ta fara sakin jiki da sarki shardas
duk da cewar ta daukeshi babban makiyin da babu
kamarsa a cikin zuciyarta sai gashi ta fara rayawa a cikin
zuciyarta cewar ya kamata ta danne wannan gaba a ranta
ta dauki komai a matsayin kaddarar da ta wuce
nan fa zuciyarta taci gaba da raya mata cewar ya kamata
ta manta da duk rayuwarta ta baya ta fuskanci
sabuwar rayuwar da take ciki yanzu domin samun
rayuwa ta gari ga abinda take dauke dashi a cikinta
kamar sarki shardas ya san abindake cikin ranta
watarana shadila na zaune ita kadai a cikin turakarta
bisa wata doguwar kujera ta alfarma irin ta sarakai a wannan lokaci tana sanye
da wata doguwar riga fara mai shara shara wacce ke
nuna tsiraicin jikinta koda ta dubi
cikinta taga ya dan fara
girma sai ta shiga shafa cikin tana murmushi
ba komaine ya sa ta wannan murmushi ba face
tunowa da babban masoyinta wato mahaifin abinda
zata haifa nan take ta shiga tunanin irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi tun farkon
soyayyarsu kawo izuwa sa adda su sarki shardas
suka kawo harin sumame ga sansaninsu lokacin da yake gaya mata cewar
kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take
ciki
koda tazo dai dai inda taga sarki shardas ya sareshi da
takobi sai ta kwalla uban ihu, ihun ne sarki shardas ya jiyo
a lokacin da dama ya nufo turakar tata cikin
firgici da razana sarki shardas ya rugo da gudu izuwa
cikin turakarta yana shigowa sai yayi turus bisa ganin cewar babu kowa a cikin turakar face
shadila ita kadai
a zaune hawaye na zuba daki daki a kan kyawawan
kumatunta
cikin sanyin jiki sarki shardas yaje ya zauna akan
kujerar dake fuskantar wacce shadila ke zaune
ya kama hannayanta biyu ya
rike suka kurawa
juna idanu sannan ya budi baki a cikin murya mai
taushi
da sanyi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla
wannan shine karo na farko da shadila taga kwalla a cikin
idanun sarki shardas tun da aka kawo ta gidan sarautar
sarki shardas yace ya ke matata na sani cewar a
duniya babu wani mutum wanda kika tsana kuma kika
daukeshi babban makiyinki sama dani saboda na
kashe miki miji a ranar farko na amarcinku sannan
na rabaki da duk zuri'arki na kawoki kasata da
karfin tsiya inda nayi miki fyade kuma na maishe dake
matata ta dole
har abada babu abinda zan yi na goge wannan tabo
nawa akan idanunki ko kuma na burgeki bare harna
sami gafararki
ki sani cewa ni masoyinki ne na har abada duk
da nasan bakya kaunata dai dai da tsawon dakika daya
ba zan taba so naga rayuwarki da ta abinda zaki
haifa ta kasance a cikin farin ciki, alfarma daya nake
so na nema a wajanki ina son ki boye laifin da na yiwa
mahaifin abin dake cikinki a tsakanina dashi har
izuwa kamar tsawon shekaru bakwai nan gaba a sannan zaki iya sanar dashi komai idan yana ganin zai iya daukar
fansa a kaina sai ya dauka , kin san cewar ni ba zan taba
haihuwa ba face na mallaki Hular lamsara kamar yadda
na fada miki a baya burina kawai shine na reni dan mijinki
hailur a matsayin dan cikina, wannan zai kawai
mini da bakin cikin rashin samun da kuma nayi miki
alkawarin cewar daga nan har izuwa tawon shekaru
bakwan ba zan taba cutar dashi ba amma fa ki sani
cewar a ranar da ya cika shekara bakwai zanyi shiri na bar kasar
nan don tafiya neman hular lamsara
bokana ya tabbatar mini da cewa shima wannan da naki idan
ya zama saurayi zai tafi neman hular lamsara to a sannan ne nake
son ki sanar dashi gaskiyar asalinsa da mahaifinsa
domin daga wannan rana mun zama ABOKAN GABA na sani cewa a wannan lokaci
bana gida don boka barwas ya tabbatar mini da cewar
sai mun shafe shekara goma sha daya kafin mu
gano inda hular
Lamsara take, kinga a wannan lokaci ban san
kamannin danki ba shima bai san nawa ba don haka
ko da zamu hadu a wani wurin daban ba zamu shaida
juna ba zamu iya abokai kuma ko kuma abokan gaba
idan kuwa na rigashi mallakar hular lamsara tofa
duk inda muka hadu saina gane cewa shine dan hailur kuma nan take zan kasheshi
Sai kiyi tunani bisa wannan alfarma dana nema a wajanki
kuma ki tuna cewar
kin taba neman alfarma a wajena kuma nayi miki
tun da kinsa na 'yanta matan zuri arku daga matsayin
bayi sun koma kuyanginki idan har kikayi mini
wannan alfarma guda daya dana nema a wajanki
babu mamaki ungulu ta Koma gidan ta na tsamiya.
A lokacin da Nikuma Guyson Zankoma Inda nafi Wayau wato Neman na Aure,,,
..
Anan ne Littafin TSATSUBA NA BIYU YAZO KARSHE
marubucin Littafin yace.
.
SHIN SHADILA ZATA IYA YIWA SARKI SHARDAS ALFARMAR DA YA NEMA A WAJANTA?
.
SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU?
.
WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON KITABUL SIHIR? SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA
.
Anayi Muna jin dadi
ReplyDeleteAnayi Muna jin dadi
ReplyDeleteAnayi Muna jin dadi
ReplyDelete