LOKACIN DA SHADILA TA tambayi kanta a cikin zuciyarta cewar
'Anya kuwa Hailur yana raye a duniya amma bai nemeta ba?
Kuma ta kasa baiwa kanta amsa sai idanunta suka kekashe ga barin barci ta kasa koda risinawa a wannan dare
haka dai taci gaba da mutsu mutsu akan gadonta
taci gaba da tunanin jarumi hailur
A wannan rana dai
shadila kwata kwata bata rintsa ba har sai da alfijir ya keto
a sannan ne barcin ya saceta ba tare da ta sani ba
Al'amarin su yarima hulkas kuwa lokacin da gari ya waye
ya farka yaga mahaifiyarsa na ta barci bata ma da niyyar
farkawa sai ya ki tashinta cikin doki da zumudi
hulkas yaje yayi wanka ya kimtsa
gama hakan ke da wuya
sai ga yarima barmas ya shigo cikin dakin shima ya caba ado fuskarsa cike da annuri
ko da yaga hulkas ma ya gama shiri tsaf sai yayi murmushi yace hakika naga alamar cewa ka fini
dokin son zuwa kallon wannan gasar jarumtakar da
za ayi Yau.
Hulkas ya maida masa da martanin murmushin yace Ai ji nake ina ma kamar na zama tsuntsu na ganni a can
ba don komai ba sai don ma kawai na sake ganin kyakkyawar fuskar nan ta jaruma siyama
kuma naga yadda zata fafata yaki da manyan mazaje
barmas ya kyalkyale da dariya yace Ai dama nasan cewa
tatsuniyar Gizo Bata wuce ta Koki, to ai saikayi sauri kazo muje
muyi buda baki a can turakar mahaifiyata
amma me ya faru naga har yanzu mahaifiyarka tana yin
barci bata farka ba?
Koda jin wannan tambaya sai yarima Hulkas yayi ajiyar
zuciya yace ina kyautata zaton cewa jiya da daddare ba tayi barci da wuri ba
shi yasa yanzu take ramuwarsa
cikin alamun damuwa yarima
barmas yace
aikuwa ummina ma ba zatayi buda baki ba sai tare
da mahaifiyarka
don cewa tayi nazo na tafi da ku muje muyi buda bakin gaba daya
kuma tare zamu tafi can filin yin wannan gasa
har da sarki da kansa kana ganin cewa ba zaka tasheta daga barcin ba?
Hulkas yace A'a bai kamata na tasheta ba tunda akwai
bashin barci a tare da ita muje a yiwa mahaifiyar taka
bayani
koda jin haka sai yarima barmas ya juya ya fice dagacikin
dakin shi kuma yarima hulkas ya bishi da sauri suka durfafi
turakar Luzuraina.
Turakace babba wadda aka cikata da kayan kawa irin
na sarakai
Al amin Ahmed Misau Guyson ko Shagala Inkiya Kenan
A gefe daya an ajiye wani dogon teburin cin abinci mai
dauke da kujeru goma sha biyu, A kan wannan teburi an
shirya abincin kalaci iri iri har kala goma sha daya bisa farantai
luzuraina ce kadai zaune akan wannan babban tebur
tana jiran isowar sushadila
kwatsam ! Sai ta hango yarima hulkas tare da danta
barmas su biyu kacal sun shigo cikin falon
Al amarin da yai matukar bata mamaki kenan domin
su uku ya kamata ta gani
tun kafin su karaso gareta luzuraina ta dubi yarima hulkas cikin alamun damuwa tace
ina mahaifiyarka?
Me yasa bata biyoku ba kun taho tare, yarima hulkas
ya risina cikin biyayya ya gaida luzuraina yace ina zaton cewa
ummina batayi barci ba jiya
da wuri sakamakon labarin dana bata akan inda muka je jiya
nida barmas
koda jin wannan batu sai luzuraina tayi shiru tana tunani na tsawon yan dakiku
sannan ta mike tsaye ta dubi
yarima barmas tace ku zauna kuyi kalaci
kai da abokinka ni ba zan yi ba har sai shadila ta tashi da kanta
idan kun gama cin abincin kuje ku jira sarki a falonsa domin yana fitowa sai ku tafi
filin gasa tare
idan ya tambayeni ku gaya masa cewa zamu riskeku a can
nida kawata shadila
koda gama fadin hakan sai luzuraina ta mike tsaye daga kan kujerar da take
zaune ta tafi can cikin turakarta ta barci,
barmas da hulkas kuwa sai suka zauna suka yi
buda bakinsu cikin sauri, suna kammalawa sai suka tafi zuwa
can falon sarki hulbasu
ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai ga sarki hulbasu
ya fito a cikin gagarumar shiga ta
alfarma da kasaita
fuskarsa cike da annuri
kallo daya mutum zaiyi masa ya gane cewa yana cikin
walwala da murnar zuwan wannan rana ta gasar jarumtaka wacce ake yi a
birninsa a karshen kowacce shekara,
koda sarki hulbasu yaga yarima hulkas da yarima barmas
su biyu kadai
a zaune babu iyayansu sai annurin fuskarsa ya dauke ya dubi
barmas cikin alamun damuwa yace ina iyayan naku mata?
Me yasa basu zo nan ba tare daku?
Nan take barmas ya yiwa sarki hulbasu bayani kamar yadda
luzuraina tayi masa
koda jin haka sai sarki hulbasu ya dubesu yace
shi ke nan ku tashi mu tafi filin gasar nan domin na san cewa tuni an gama hallara
ni kadai ake jira a fara wannan gasa
nan take su hulkas suka mike tsaye suka bi sarki a baya
suna isowa babbar haraba ta bangaren turakar sarki hulbasu sukayi kicibis
da dakaru a tsai tsai cikin shigar yaki bisa dawakai wadanda za su yiwa sarki rakiya izuwa filin
gasar a gefe daya kuma ga dokin sarki tare wadansu
dawakan guda hudu
The Guyson On top Ba tare da bata wani lokaci ba aka kawo wa sarki dokinsa ba tare da bata
Wani lokaci ba aka kawowa sarki dokinsa ya hau
barmas da hulkas ma sai aka kawo musu biyu
daga cikin wadannan dawakai guda hudu suka
hau aka dunguma gaba daya aka nufi filin gasar
kuma hardani kaina Guyson Ina binsu a baya
sai dai wannan filin anyi shine a tsakiyar gari
kusa da babbar kasuwa ta garin wacce take
gagarumin ci a duk ranar da za ayi wannan gasa
Filin ya kasance katon gaske kuma an kewayeshi
da katanga doguwar gaske daga cikinsa an
kewayeshi da kujeru sama da guda miliyan
biyu
amma duk ranar da za ayi wannan gasa sai
mutane sun rasa wajan zama saboda cikowa
sai dai ka rinka ganin jama a akan katanga, kai
wasu ma basa samun damar shigowa cikin filin
gasar sai dai su hau saman benayen gidaje da
bishiyoyi suna hango abinda ke faruwa a cikin filin
A gefe daya ne na filin aka gina inda sarki da
mukarrabansa ke zama don kallon wannan gasa
duk wanda bai kasance jinin sarauta ba to bai
isa yaje ya zauna ba a wannan wuri ba face ya
kasance babban attajiri ko mashahurin boka ko
kuma makusancin sarki kamarni Al amin Guson
kenan
Al' amarin siyama kuwa da iyayanta lokacin da
gari ya waye suka gama shirin tafiya filin gasa
si mahaifinta ya rufe fuskarsa da rawani ya zamana
cewa idanunsa kadai ake gani sannan suka hawo
dawakai guda uku suka durfafi filin gasar jarumtakar
Lokacin da suka iso bakin kofar filin gasar sai suka
iske gurin ya cika makil da mutane babu masaka
tsinke ganin hakan ne yasa hankalinsu ya
dugunzuma ba don komai ba sai don sun san
cewa siyama ce kadai za a bari ta shiga cikin
filin gasar tunda tana da shaida ta jaruman takara
su kuwa sai dai su hau kan bishiya ko wani gidan
mai bene
koda siyama ta lura da irin damuwar da iyayanta
ke ciki sai ta nunawa masu gadin filin shaidarta
ta jarumar gasa kuma ta gaya musu cewa ga
iyayanta a tsaye tana son ta shiga tare dasu ciki
koda jin haka sai shugaban masu gadin wani
narkeken katon badakare ya dubi siyama sama da
kasa cikin raini ya bushe da dariya yace yanzu ke
wane ganganci ne ya sa kika shiga wannan gasa
kina matsayin mace, kuma yarinya karama haka ?
Shin iyayan naki sun gaji da ke ne shiyasa suke so
su ga irin kisan gillar da za ayi miki? Toki sani
cewa indai fili ya cika babu mai sake shiga ciki
face sarki da mukarrabansa, ko ki shiga ke kadai
ko kuma ki fasa yin gasar gaba daya, a wannan
lokaci su kansu tsirarun 'yan kallon dake tsaye a kofar filin wasan kallon siyama
suke yi kawai
wasu suna mamaki wasu suna ta sheka mata dariya
suna yi mata kallon mahaukaciya wacce ta
gaji da zaman duniya, wasu ma sai suka kama
tsegumi suna cewa bata da iyaye, baiwa ce kawai
iyayan gijinta suka gaji da ita, lokacin da jaruma
siyama ta ji cewar ba za a bar iyayanta su
shiga filin gasar ba sai ranta ya baci ta yunkura
zata bude kofar da karfin tsiya su kunna kai
ciki kawai sai mahaifinta ya dubeta yayi mata
inkiyar kada ta aikata hakan ta hakura, cikin
sanyin jiki ta juyo ta fuskanceshi tace yakai
abbana yanzu mene ne abinyi? Zamu koma
gida ne ko kuwa zamu hau sama ne muyi kallo
abul siyama ya gyada kai yace mu dakata har sarki
ya iso na tabbatar muku da cewa zamu shiga
wannan fili na gasa yayin da sarki yazo nan, koda
jin wannan batu sai mamaki ya kama siyama
domin bata ga dalilin da zai sa a barsu su shiga
cikin filin wannan gasa ba idan sarki yazo tunda
dai su basu kasance masu sarauta ba ko wani matsayi
haka dai siyama tare da mahaifanta suka koma gefe daya suka tsaya suka
zuba idanu kawai
A wannan lokaci tsirarun attajirai da masu fada
aji ne kadai ke wucewa cikin filin gasar kuma
suna shiga sai a janyo kofa a sake rufewa kawai
jim kadan kuwa sai ga sarki Hulbasu tare da
yarima basmar da yarima Hulkas sun nufo kofar
filin gasar bisa dawakai dakaru na take musu baya
ana busa Algaita gami da buga tambura nan
da nan jama a suka dare aka basu hanya jama ar
gari kuwa suka kama yiwa sarki Hulbasu kirari
gami da jinjina sabo da nuna soyayyarsu a gareshi
koda ganin wannan al amari sai yarima hukas
ya tuno da rayuwarsa ta can birninsa yadda jama ar
gari ke sonsa da nuna masa soyayya sannan kuma
ya tuno da yadda talakawa ke tsananin tsoron
sarki Shardas saboda rashin imaninsa da cin
zalinsa
nan take hulkas ya tambayi kansa a cikin ransa
yace wai shin menene dalilin da yasa mahaifina
ya kasance azzalumi ? Kuma sabo da me halayansa
suka banbanta da nasa alhalin ance barewa
bata gudu danta yayi rarrafe amsar da yarima
hulkas ya kasa baiwa kansa kenan yana cikin
wannan haline sarki hulbasu da tawagarsa
suka sake kusanto wajen tun daga nesa dasu
yarima barmas suka hango jaruma siyama tsaye
a wajan tare da iyayanta sai suka cika da mamaki
sabo da kamata yayi ace ta dade da shiga ciki
tun daga nesa da sarki hulbasu ya hango
mahaifin siyama tare da matarsa a tsaye da kuma
'yarsu siyama sai ya kura musu idanu kawai har
suka iso bakin kofar shiga filin gasar da
isowarsu sai mahaifin siyama ya risina ya gaida
sarki
ba zato ba tsammani sai akaga sarki yaja
linzamin dokinsa ya tsaya cak
Take Nima Al amin Ahmed Misau wanda ake wa
lakabi Da Guyson ko A square na tsaya nima
saboda tsananin mamaki da kuma ganin wannan
mahaifina siyama a wajan nan, amma kafin
nan zanso ku biyoni a labari na gaba domin
jin yadda za a kaya a tsakanin su shin
meye dalilin da yasa shi tsayawa yana kallonsa
hm
nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko A square
wanda ke zaune a garin
Kaduna,
garin Gwamna
sai Kuma Allah ya kaimu Gobe kenan ku
huta lafiya.......
[4/17, 8:42 AM] Al Amin Gysn: TSATSUBA
Littafi Na Hudu (4)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Ba zato ba tsammani sai akaga sarki yaja lin
zamin dokinsa ya tsaya cak, take kowa dake
bayansa ma ya tsaya sarki ya sauko daga kan
dokinsa fuskarsa cike da annuri ya durfafi mahaifin
siyama, yana riskarsa sai ya rungumeshi sannan
ya janye jikinsa daga cikin nasa ya dubeshi cikin
mamaki yace yakai babban masoyi menene
dalilin da yasa baka amsa kirana ba bayan mun
rabu a daji a wannan rana, koda jin wannan
tambaya sai mahaifin siyama yayi murmushi
yace ya shugabana kayi hakuri mu sami lokaci
saimu tattauna yanzu kamata yayi mu shiga
cikin filin gasa domin zuwanka kadai ake jira
koda jin haka sai sarki yayi murmushi ya
kama hannunsa yaja shi izuwa cikin filin gasar
shima sai ya ruko matarsa yarima barmas da
yarima hulkas kuwa sai suka jera tare da jaruma
siyama suka shiga cikin filin gasar, yayin da shima
Al amin Guyson ya shiga domin cigaba da kawo
muku labarin, koda su sarki Hulbasu suka shiga
cikin filin gasar sai kowa ya mike tsaye don
nuna girmamawa a gareshi filin ya cika da shewa
aka ci gaba da yiwa sarki jinjina da gaisuwa ehm
har sai da sarki da mukarrabansa suka je suka
zauna a inda aka tanadar musu sannan filin yayi
tsir aka yi shiru kamar mutuwa ta gifta
a dai dai wannan lokaci ne mai gabatar da taro
ya tashi yayi jawabi kamar yadda aka saba
sannan yaci gaba da fadin sunayan jaruman
da za su yi gasar a yau da gobe har tsawon
kwanaki bakwai, a wannan lokaci jaruma siyama
na zaune a tsakiyarsu yarima hulkas da yarima
barmas amma sai ta lura da cewar yarima hulkas
yana ta satar kallonta kuma yana son yayi mata
magana, haka ma yarima barmas koda ganin haka
sai ta murtuke fuska taki yiwa dayansu magana
kuma taki basu damar yi mata magana ta hanyar
kin sakar musu fuska, ba tare da bata wani
lokaci ba aka buga gangar fara gasa aka kirawo
sunan wadansu jarumai guda biyu suka shigo
cikin filin kowannansu na rike da takobi da
garkuwa daya dogo ne kuma kakkaura mai
kwarjini da kirar sadaukai ana kiransa da suna
MULAGUS,
dayan kuwa gajere ne amma shima yana da kirar sadaukantaka ana kiransa
da suna KUMAR, A cikin dokar wannan gasa
an yarda a soki mutum ko a sareshi da a ko ina
koda kuwa hakan zai iya zama sanadin ajalinsa
amma ka idar nasarar gasar shine kawai akai
mutum kasa ya kasa mikewa tsaye kafin
a kirga bakwai, Malagus da kumar suka gyara
tsayuwarsu suka fara kallon kallo kowannansu
yana nazarin abokin gwaminsa, a dai dai wannan
lokaci ne Hulkas ya dubi yarima barmas yace
yakai abokina a ganinka wane ne zai lashe
wannan gasa tsakanin Mulagus da Kumar? Koda
jin wannan tambaya sai Barmas ya tuntsure da
dariya sannan yace haba ai da ganin kura an
san taci mutum Ga abu nan a zahiri kowa yana
gani ai ko a ba a gwada ba linzami yafi
karfin bakin kaza.... Kafin Hulkas ya budi baki ya
sake cewa wani abu sai jaruma siyama ta tari
numfashinsa tace ai sai an gwada akan san na
kwarai tunda komai zai iya faruwa a ko yaushe
koda hulkas da barmas sukaji siyama ta tsomo
baki a cikin zancensu sai farin ciki ya lullubesu
hulkas ya dubeta ya ce ashe dama mahaifinki
da sarki sun san junansu amma baki gaya mana
ba
sa adda siyama taji wannan tambaya sai tayi
murmushi tace ni kaina nayi mamaki ban san
cewa sun san junansu ba sai yanzu, amma
dai abin da na ke zargi shine a daji suka hadu a
wajan farauta sabo da duk su biyun babu
abin da suke so a rayuwarsu sama da farauta, zan
tambayi abbana dai naji daga gareshi, gama
fadin hakan keda wuya sai sukaga mulagus
da kumar sun ruga izuwa kan juna sun kacame
da azababben yaki suna masu kaiwa juna SARA
DA SUKA cikin zafin nama juriya da bajinta, ana
fara gumurzun ne filin yayi tsir ba a jin sautin komai
face karar takubbansu ihunsu da karajinsu da
takun sawayan kafafunsu, nan take kowa ya gane
cewa Mulagus yafi karfin damtse to amma kuma
shi Kumar yana da tsananin naci juriya da
kwarewar iya yaki da farko duk sa adda mulagus
ya kawowa kumar sara idan kuma ya kare da
takobinsa sai kaga har darkushewa kasa yakeyi
saboda karfin saran da nauyinsa, wani lokacin
kuma sai kaga mulagus ya gabzawa kumar naushi ko bugu da hannu ko
da kafa har kumar na durkushewa kasa amma
kafin mulagus ya kaiwa kumar sara ko suka
sa adda yake durkushen tuni kumar ya mike
tsaye zumbur ya ci gaba da kare kansa kuma yana
maida martani.
Abin ka da wanda yafi ka karfi cikin kankanin
lokaci mulagus ya hadawa kumar jini da majina
kuma ya sami nasarar yankarsa da takobinsa har
sau uku ya zamana cewa jini na zuba a jikin
kumar kuma jiri na dibarsa amma saboda masifaffen
naci da azababbiyar juriya yaki yarda ya fadi
a wannan lokaci gaba daya jama ar dake wajan
sun saddakar da cewar mulagus ya gama samun
lagon kumar don haka a ko yaushe zai iya bazar
da shi kasa
a haka dai suka ci gaba da gumurzu har
tsawon rabin sa a mulagus bai sake samun
wata nasara ba akan kumar abin ka da jiki
da jini sai shima mulagus ya fara gajiya haki ya
yawaita gareshi da yawan numfashi shi kuwa
kumar sai ya samu karfi a wannan lokaci tamkar ma a
sannan ne ya fara gumurzu sai gashi nasa
karfin
Saran da sukan yafi na mulagus nauyi da karfi
hakika masu iya magana sunyi gaskiya da
sukace sai miya ta kare sannan ake sanin maci
tuwo !
Al amin Ahmed misau Guyson ko A square daga
zauran labarai nake magana, kuma ance
a dade ana yi sai gaskiya domin dadewar da
jaruman biyu sukayi suna fafata wannan
masifaffen fada yasa aka gane jimrau a tsakaninsu
kuma aka fahimci wanene mayakin kwarai
cikin kankanin lokaci kumar ya kuntata mulagus
ya hanashi sakat ya zamana cewa kwata kwata
mulagus baya iya maida martani sai kokarin kare
kai, koda kumar yaga ya sami wannan nasara
sai ya shammaci mulagus ya daka tsalle sama
ya doki fuskarsa da kafa, saboda kargin dukan
sai da mulagus ya juya sau biyu a tsaye, kafin
kumar ya duro kasa tuni ya sa takobinsa ya
sarewa mulagus hannunsa na dama mai
rike da takobi, take hannun ya fice fit jini ya
kama feshi da tsiri daga cikin dungulmin
a lokacin da mulagus ya kwarara uban ihu
wanda ya firgita komai da kowa dake wajan
har dama halittun dake cikin gari da kewaye
take mulagus ya kife kasa sumamme, ai kuwa
sai filin gasar ya rude da shewa gami da jinjina
a lokacin ne shima kumar ya durkushe kasa
bisa guiwoyinsa sakamakon gani da yake
dishi-dishi da idanunsa da kuma jinin dake
zuba a jikinsa nan take likitoci suka rugo
cikin filin gasar da dakaru aka dauke jaruman
biyu aka shige dasu izuwa cikin wani babban
daki dake gefe daya a cikin filin gasar wanda
aka tanadeshi a matsayin asibitin da za a rinka duba jaruman gasa, ganin
yadda aka zubar da jini ne a filin wannan gasa
yasa hankalin yarima hulkas ya dugunzuma
ainun kuma ransa ya baci take ya aiyana a
ransa yace in da zan zamo wani babban sarki
a wannan nahiya tamu da sai na hana gabatar
da irin wadannan wasanni wadanda ake zubar
da jini
domin ban ga amfanin ace zubar da jini shine
Jarumtaka ba
Bayan an gama dauke jaruman gasar biyu
daga cikin filin gasar sai mai gabatar wa ya
kirawo sunan jarumi na gaba wanda yayi
wasa waishi DURKUS, koda yan kallo sukaji
sunan wannan jarumi sai filin ya cika da shewa
tamkar dodon kunne zai dode, shidai wannan
jarumin Dukrkus din a gaba daya nahiyar babu
wani jarumi da ya kaishi girma, da iya yaki tare
da kuma daukaka kuma duk shekara shine yake
lashe wannan gasa ta jarumtaka dukkanin
jaruman da suke zuwa wannan gasa daga
sauran kasashe na duniya komai girmansa da iya
yakinsu suna tsoron durkus babu wanda yake
son a hadashi dashi, ba don komai ba sai don sadauki Durkus
ya kasance gabjejen kato mai kirar mutanan Farko sannan kuma yana da
tsananin karfi na Allah ya isa gashi da
tsawon tsiya kamar ba mutum ba kuma kakkaura
ne sosai a takaice dai kirarsa ta samudawa ce
baya ga wannan rashin imanin Darkus yayi yawa
domin duk jarumin da ya hadu dashi sai ya mutu
sadauki Darkus bai taba yin wasa ya bar abokin gwaminsa
da raiba don tsantsar zaluncinsa, kuma kafin
ma ya kashe abokin gasar tasa sai ya sassare
masa gabban jiki yai gungudwa gungudwa da
sassan jikinsa sannan ya kashe shi kisan wulakanci
bisa wannan daliline yasa duk sa adda zaiyi
yaki a filin gasa masu raunin zuciya basa iya
kallon wasansa, domin duk sai dai kaga suna ta
kumallo a filin gasar suna koke koke yayinda
yake aiwatar da zaluncinsa ga abokin gasarsa
koda aka kirawo sunan wannan Jarumi wato
Darkus ya shigo tsakiyar filin gasar sai aka kama
yi masa jinjina da kirari sai shima ya kwarara
uban ihu mai karfi da firgitawa ya fara dukan
kirjinsa da tafkeken hannunsa ya shiga rerowa
kansa kirari yana mai cewa,,,
Ina bakon lahira to ya fito ya tareni, Nine bakin
takobi mai raba kowa da masoyi, nine dajin
mutuwa kowa ya shige ba rai zai fita ba a raye ba
Kuma nine ISKAR ANNOBA kowa ya shakeni sai
ya kwana kiyama. Guguwar kan dutse nake
ban fito ba sai da na shirya sawun giwa nake
wanda na take na dukkan dabbobi Ina
mai jida jarumta da juriya da naci to ya fito ga
dillalin mutuwa
hm Guyson nake haka dai Darkus yaci gaba da yiwa
kansa kirari har ya gama ya tsaya cak a waje
daya yana huci da muzurai tamkar wani bakin
kumurci
kai yaran dake cikin wannan filin gasa boye fuskarsu
suka kama yi domin da zarar sun hada idanu da
darkus sai suga kamar dodo ne tsaye a gabansu
wanda zai suresu da hannu daya ya jefa baki ya
lankwame...
Nima dai bari na dakata a nan wajan saboda
tsaro Amma
kafinan
Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko A square
dake garin Kaduna
garin gwamna
kecewa mu zama lafiya....
[4/17, 8:43 AM] Al Amin Gysn: TSATSUBA
Littafi Na Hudu (4)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
A dai dai wannan lokaci ne filin gasar yayi
tsit tamkar mutuwa ta gifta kawai sai mai gabatarwa
ya kira sunan jarumin da zai kara da darkus
ba wani bane jarumin face jaruma SIYAMA, Koda
jama a sukaji an ambaci sunan ya mace sai kowa
ya gwale idanunsa domin yaga ko wacce jaruma
ce haka mai tsautsayi wadda ta gaji da zaman
duniya
Domin manyan mazaje ma da suka kasance
sadaukai kuma wadanda suka sha gwagwarmaya iri
iri a filin daga suna tsoron a hadasu gumurzu da
darkus don su san cewa ajalinsu ne ya zo
Kwatsam ba zato ba tsammani sai akaga wata yar
matashiyar budurwar yarinya ta taso daga wajan
da su sarki ke zaune tana sanye da kayan yaki
ta shigo cikin tsakiyar filin gasar ko garkuwa babu a
hannunta kuma takobinta ma na cikin kube sakale
a kuibin cinyarta ta hagum nan fa mamaki ya
turnuke jama a wasu suka kamu da tsananin
tausayin siyama har suna zubar da hawaye saboda
suna ganin cewa mugun kisan gilla darkus zaiyi
mata.
Wasu mutanan kuwa sai suka kama tsinewa
mutanan da suka yi sanadiyyar shigar wannan
kyakkyawar yarinya cikin wannan gaasa
yarima hulkas da barmas kuwa hankalinsu
ne yayi matukar dugunzuma ainun har jikinsu
ya kama tsuma bisa ganin cewa Siyama zatayi
Yakine da DARKUS
hm Nimafa nayi mamaki kamar na tsaya da typing
amma muje kawai
Duk da cewa sun ga irin jarumtakarta sai
da zuciyoyinsu suka karaya yarima barmas
bai san sa adda ya taso daga inda yake zaune ba
yaje inda sarki da mahaifin siyama ke zaune ya
dubi mahaifin siyaman a dimauce yace haba
ya abul siyama yanzu kana gani za a kashe
yarka amma kayi shiru hm Al amin Guyson nake
tabbas wannan hadi da akayi babu adalci acikinsa
kawai so ake a kashe yarka koda jin wannan
batu sai mahaifin siyama yayi murmushi ya
dubi yarima barmas cikin girmamawa yace
kwantar da hankalinka yakai yarima babu
abinda zai sami yata, ka koma wajanka ka
zauna ka morewa idanunka da kallon abin
mamaki
cikin alamun tsananin damuwa yarima barmas
ya juya ya nufi can wajen zamansa yana waigen
mahaifin siyama
amma duk sa adda ya waigo din sai yaga shima
ya kurawa hulkas idanu yana yi masa wani
irin kallo mai dauke da ayar tambaya, a
wannan lokaci ne sarki Hulbasu ya dubi mahaifin
siyama cikin alamun mamaki yake yakai abokina
wai shin mene ne dalilin da yasa ko yaushe
kake rufe fuskarka ne da mayafi, ni kaina ban
taba ganin irin kamanninka ba kuma ko yaushe
a haka kake koda kuwa a cikin daji kake
shin ina dalilin yin hakan? Sa adda mahaifin
siyama yaji wannan tambaya sai yayi murmushi
ya ce ya shugabana kayi hakuri ba zan iya
baka amsar wannan tambaya ba a yanzu saboda
wani muhimmin dalili da ya shafi rayuwata
amma nayi maka alkawarin idan lokacin da
ya kamata ka sani yayi zaka sani, ina boye wannan
sirri ne sabo da samar da tsaro ga rayuwata data
iyalina
ya shugabana idan ba zaka damu ba nima ina da
wata tambaya guda daya a gareka wai shin
wane ne wancan yaro wanda ke tare da danka
yarima barmas daga ina ya fito kuma mene ne
dangantakarsu da sarauta ?koda jin wannan tambaya
sai sarki hulbasu ya kyalkyale da dariya sannan
yace akan wanne dalili zan baka amsar wannan
tambaya da kayi mini alhalin nima ina da nawa
tambayoyin kwatankwacin irinsu a kanka kuma kaki
ka bani amsa tun daga ranar da na fara ganinka ?
Nima ba zan iya baka amsar wadannan tambayoyi na
ka ba saboda tabbatar da tsaro a kan wannan yaro
domin kuwa idan wani abu ya sami lafiyar wannan
yaro bama niba gaba daya jama ar dake cikin
wannan nahiya tamu sai sun shiga uku, sa adda
mahaifin siyama yaji wannan batu daga bakin sarki
sai kansa ya daure ya cika da mamaki fiye da
ko yaushe har ya budi baki da nufin ya sake
yiwa sarki wata tambaya sai kawai yaga dakus
ya ruga da gudu izuwa kan siyama yana mai
daga takobinsa sama kuma yana mai kwarara uban
ihu mai tsananin firgitawa irin wanda ka iya
tarwatsa dubunnan dakaru a filin daga kuma ya
furta tane a cikin mugun nufi na gamawa da ita
farat daya
ita kuwa siyama sai ta tsaya cak a inda take to
gezau batayi ba kuma ko kifta idanunta ba tayi ba
koda dakus ya iso daf da ita sai ya kawo mata wani
irin wawan sara a wuya da nufin ya cisge mata kai
cikin bakin zafin nama jaruma siyama ta tale
kafafunta tayi kasa, takobin darkus din ta
sari iska
darkus ya sake kai mata wani mugun sara a fusace
siyama tana durkushe a kasa tayi wata irin alkafira
cikin gwaninta ta kaucewa harin nasa, koda takobin
darkus tasari kasa sai ta nutse izuwa cikin karkashin
kasar gaba dayanta saboda tsananin karfin saran nasa
da nauyinsa
kafin darkus ya zaro takobin tuni siyama ta doki
kasa da tafin hannunta na hagu tayi sama sai
kawai ta doki gadon bayansa da kafafunta biyu
darkus yaji kamar wani dankareren kato ne
yayi masa dundu a gadon baya kuma duk da
tsananin girmansa da nauyinsa sai da ya tafi taga
taga da gaba kamar zai kife kasa, da kyar ya iya cijewa ya
tsaya kyam a tsaye, Al amarin da yai matukar
razanashi da bashi haushi kenan, domin wannan ne
karo na farko da aka taba samun jarumin da ya
sami nasarar
.
Dukan jikinsa har ma ya kusan kaishi kasa, koda
yan kallo sukaga wannan gagarumar jarumtaka
da siyama tayi sai suka cika da tsananin mamaki
filin ya kaure da ihu gami da shewa aka shiga
yiwa siyama kirari gami da jinjina, yarima hulkas kuwa
saboda murna ma bai san sa adda ya daka tsalle
ba daga kan kujerar da yake zaune yana shewa
shewar tasa ce tasa har siyama ta juyo ta dubeshi
kawai sai tayi masa murmushi, take hulkas yaji
wani irin farin ciki mara misaltuwa da dadi
ya lullubeshi saboda wannan murmushi da tayi
masa
shi kuwa sadauki Darkus fusata yayi ainun ya
juyo da sauri ya sake rugowa izuwa kan siyama
aikuwa itama sai tayi wuf ta zare takobinta ta
tareshi suka ruguntsume da azababben yaki
mai tsananin ban tsoro da razanarwa, gaba daya
jama ar dake filin wannan gasar sai da hankalinsu ya
dugunzuma gaba daya saboda tun da aka fara
wannan gasa ta jarumtaka tsawon shekaru
ba a taba ganin gumurzu ba irin wannan mai tsananin
hadari
wow Al amin Ahmed Misau Guyson ko A square
A can gidan sarauta kuwa gimbiya shadila bata farka
ba daga barci har sai bayan lokaci mai dan tsawo koda
ta bude idanunta taga ashe ma tuni gari ya dade
da wayewa har rana ta kwalle kuma taga babu
jarumi hulkas kwance a kusa da ita akan gadon da
take kwance sai ta mike zaune zumbur a lokacin
da zuciyarta ta buga da karfin gaske, kawai sai
ta sauko daga kan gadon da sauri ta leka bandaki
don tunanin ko hulkas na ciki yana wanka amma
sai ta iske bandakin wayam babu kowa a cikinsa
a gigice shadila ta gaggauta tayi wankanta sannan
ta kimtsa
gama shirinta keda wuya sai taji an kwankwasa mata
kofa saiga wata kuyanga ta shigo, kuyangar ta zube
kasa bisa guiwoyinta ta ce ya shugabata
sarauniya ta turoni nayi miki jagora zuwa can
turakarta domin tana jiranki kuyi kalaci, cikin mamaki
shadila ta dubi yadda rana ta kwalle ta cikin tagar
dakin nata sannan ta dubi kuyangar tace yanzu kina nufin kice har
yanzu sarauniya bata yi kalaci ba, kuyangar ta sake
risina tace ai saboda kina barcine shi yasa taki
tayi kalacin da kanta, amma tafi sa a biyu da gama
kimtsawa har ma sarki dasu yarima sun dade da
tafiya kallon GASAR JARUMTAKA, koda jin wannan
batu sai shardila taji zuciyarta ta buga da karfi
kuma ta ji babu abinda take so sama da ta ganta a
filin wannan gasa, don haka cikin sauri tace da
kuyangar yi maza ki kaini wajan sarauniya
ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai kuyangar
ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin shardila na
biye da ita, luzaira na zaune akan teburan cin abincin
dake falonta ita kadai tana jiran sai ga kuyanga tare
da shardila sun shigo, cikin murna luzaira ta mike
tsaye da sauri ta taryo shardila ta kamo hannunta
ta kawota izuwa kan kujera suka zauna tare, ba tare
da bata wani lokaci ba suka kama cin abincin
har suka kusan gama cin abincin dayansu baice kala ba
a sannan ne shardila tayi gyarar murya ta dago kai
ta dubi luzaira tace yake kawata ki gafarceni na bata
miki lokaci da kika kawo har yanzu baki yi
kalaci ba domin barcina ne yayi nauyi, kafin shardila
ta gama wannan magana sai luzuraina ta tari numfashinta tana mai kallonta cikin murmushi
tace haba yake kawata kada ki sawa kanki damuwa
akan hakan domin danki ya gaya mini cewar yana
zaton jiya bakiyi barci da wuri ba shin kina da wata
lalura ne ta rashin lafiya ko kuwa akwai wata matsala
dake damunki
koda jin wannan tambaya sai shardila ta yi murmushi tace kawata babu
abinda yake damuna kuma bani da wata matsala
haka kawai dai naji idanuna sun bushe jiya da
daddare wata kila bakunta ce ta janyo hakan
koda jin haka sai luzuraina ta kyalkyale da dariya
ta yiwa shardila wani irin kallo na rashin yarda domin
ba ta yarda da abinda ta fada ba sai dai ta dubeta tace
ko dai kewar sarki shardas ce ta hanaki barci
kinga tashi mu hanzarta mu tafi filin gasar nan domin
na san cewa yanzu tuni an dade da fara wasa
babu mamaki ma an shiga kewaye na uku. Kafin luzuraina ta gama rufe bakinta
tuni shardila ta wanke hannayanta ta mike
tsaye saboda dokin zuwa wannan filin gasa, nan dai suka
gama kimtsawa suka nufi wani babban fili inda aka tanadar
musu keken dokin da zasu hau tare da dakarun
da zasuyi musu rakiya tun daga nesa shardila ta
hango dakarun sai tayi sauri ta rufe fuskarta da wani
bakin kyalle ya zamana cewa idanunta kadai ake
gani ba komaine yasa shardila ta rufe fuskarta ba face
a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da mutane suyi
ta kallonta,
abinda bata sani ba shine tsananin kyawun fuskarta da kyan
surar jikinta ne ya janyo mata kallon da ake yi mata
nan dai su luzuraina suka shiga cikin keken dokin aka ja
aka fice daga cikin gidan sarautar aka durfafi filin
GASAR JARUMTAKA.
.
NIMA KUMA sai na dakata anan na nufi Filin daga
Wato neman na Abinci Kuma sai Allah ya kaimu Gobe
zamu ci gaba
Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson Ko A square
nake cewa Ku zama
lafiya
[4/17, 8:43 AM] Al Amin Gysn: TSATSUBA
Littafi Na Hudu (4)
Part D.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
A can filin gasat kuwa lokacin da aka ruguntsume da
azababben yaki tsakanin sadauki darkus da jaruma
siyama sai da suka shafe rabin sa a cif suna kaiwa junansu
SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama juriya da
bajinta amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar
jikin daya ba
Al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan
da yawa daga cikin yan kallo dai sun firgice ne da
al amarin siyama
kai harni Al amin da nake wannan typing din na
rikice da lamarinta, Kai wasu ma sai suka rinka cewa
siyama ba mutum bace Aljana ce don babu yadda
za ayi ace tana ya mace yar shekara tara kacal
a duniya ta sami irin wannan gagarumin karfin
damtse da iya yaki haka, lallai akwai aikin sihiri
acikin lamarin
Abinda basu sani ba shine siyama tasha Sadaukantaka
ne a nono kuma tun tana da shekaru hudu kacal a
duniya mahaifinta ya far bata horon yaki
Ana cikin wannan haline aka jiyo sautin tashin
tambura da bushin Algaita alamar cewar ga sarauniya
Luzuraina nan ta iso, take farinciki ya kama sarki
hulbasu ya dubi mahaifin jaruma siyama yace
abokina ga matata nan ta iso tare da kawarta babbar
bakuwarmu
koda jin haka sai abul siyama ya budi baki da nufin
ya tambayeshi ko wacece bakuwar, amma sai ya kasa
sakamakon ganin wani irin mugun naushi da
darkus ya yiwa siyama a fuska cikin tsananin shammace,
saboda karfin naushin sai da jini yai tsartuwa daga
cikin hancinta kuma ya yi feshi daga cikin bakinta
ta tafi luuu ! Kamar zata kife kasa da baya amma sabo da
tsananin juriya sai ta mike tsaye kyam ta doki kasa
da kafarta guda tayi sama cikin shammace itama
ta doki fuskar darkus da tafin kafarta ta dama
tana mai jera masa duka uku a saman, sannan ta
duro kasa
ai kuwa sai gashi shima hancinsa da bakinsa na yoyon
jini har shima yaji wani jiri ya kwashe shi ya tafi
luuu ! Zai kife da rub da ciki amma sai yai sauri ya
tokare jikinsa da hannu guda ya taso sama kamar
sifirin suka ci gaba da sabon masifaffen yaki
kamar ma lokacinne suka fara yakin, A dai dai
wannan lokaci ne gimbiya luzuraina da shardila
suka shigo cikin filin gasar suka durfafo inda su
sarki ke zaune dakaru na take musu baya , tun daga
nesa Abul siyama ya hango shardila sai yaji
zuciyarsa ta buga da karfi irin bugawar da bai tabaji
ba a rayuwarsa
koda ya sake yin arba da dakarun dake yi mata
rakiya wato su sadauki Murzanu sai jikinsa ya
kama tsuma nan da nan gumi ya fara karyo masa
domin a sannan ne ya tabbatar da abin da yake zargi duk
da cewar kuwa shardila ta rufe fuskarta da bakin kyalle
Al amarin shardila kuwa tunda ta shigo filin sai ta
kama raba idanunta a cikin yan kallo ba don komai
ba sai domin taga Abul Husna wanda danta yarima Hulkas ya bata labari
domin ta gusar da wasu wasin dake cikin zuciyarta
bisa wannan daliline ta yi ta ware idanuwa ko zata
ga mutum mai hannu daya da nakasashshiyar
kafa kuma ta rinka kallon fuskokin mutane don ta tabbatar
da cewa tana yin arba da fuskar tsohon mijinta take
zata shaidashi,
amma har suka iso inda su sarki hulbasu ke zaune
amma bata ganshi ba, abin da ya sa ko kadan
hankalinta bai kawo kan Abul Siyama ba shine
ta san cewa babu mai ikon zuwa kusa da sarki Hulbasu
ya zauna face ya kasance jinin sarauta ko kuma
wani mai fada aji a birnin, bugu da kari kuma fuskar
Abul siyama a rufe take cikin rawani kuma ya lullube gaba dayan jikinsa da
wanibabban mayafi na alfarma, luzuraina da shardila
suka zo suka zauna kusa da sarki hulbasu daga hagunsa
shi kuwa abul siyama yana zaune a damansa
tun da suka zauna abul siyama bai yarda ya kalli
inda suke ba
shi kuwa hulbasu da yake gaba daya hankalinsa ma
yana kan gumurzun da ake yi a tsakiyar filin
gasar tsakanin jaruma siyama da sadauki durkus ko
tunanin gabatar da Abul siyama bai yi ba awajan
su Luzuraina
Al amin Ahmed Misau, Guyson Ko kuma A square nake
yayin da shardila ta kyalla ido ta hango siyama a
tsakiyar filin gasa wacce ke ta faman gumurzun yaki
tayi arba da fuskarta sai taji zuciyarta ta buga
da karfi
ba komai ne ya haddasa hakan ba face jaruma siyama
tana matukar kama da mahaifinta, nan take shardila ta
gane cewa lallai jaruma siyama yar tsohon mijinta
ce wanda take tunanin cewa ya mutu fiye da shekaru
bakwai baya
lallai hakan ya tabbatar mata da cewar kenan Hailur
na nan a raye kuma a cikin wannan gari
koda gama aiyana hakan sai shardila taci gaba
da kalle kallen ko ina a cikin filin gasar ko zataga Hailur
shi kuwa Hailur da ya lura da ita da kuma halin
da take ciki sai ya noke yana mai sunkuyar da
kansa kasa yaki yarda su hada idanu, saboda ya
tabbatar da cewa suna hada idanu zata shaidashi
duk kuwa da cewa ya rufe fuskarsa da rawani
idan kuwa ta shaidashi a gaban kowa zata fashe da kuka
ta rungumeshi, tana yin hakan kuwa asirinsa
zai tonu su sadauki Murzanu su shaidashi
idan kuwa suka shaidashi komai ya tabarbare ke nan
domin sai labari ya riski sarki shardas cewa har yanzu yana nan a raye, da zarar
hakan ta faru kuwa hatta sarki hulbasu ya shiga
cikin tashin hankali kenan da masifa don sarki
shardas
Cewa zaiyi ya boye babban makiyinsa a birninsa
don haka sai ya yakeshi ya kau dashi kuma ya
mallake kasar ma gaba daya, nan take idanun Hailur
suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye
domin shi a zatonsa ma tuni shardila ta dade
da mutuwa, amma yanzu da ya ganta a cikin shiga
ta alfarma irin ta sarakai, kuma yaga su sadauki
Murzanu na take mata baya sai ya kamu da tsananin
bakinciki mara misaltuwa domin ya gane cewa lallai
a yanzu ta zama matar sarki shardas, aikuwa
bayan su shardila sun zauna sai hailur yaga yarima
hulkas ya mike zumbur ya tafi izuwa wajan shardila
ya rungumeta
nan take zuciyar hailur ta sake bugawa da karfin
gaske a karo na biyu ya tambayi kansa acikin
zuciyarsa yace ' shin wannan yaro dana ne ko kuwa
dan sarki shardas ne
tabbas wannan yaro da uwarsa yake kama don
haka bani da tabbacin cewa dana ne, tabbas
shardila na dauke da cikin dana, wai shin kana zaton
cewa sarki shardas zai amince ne shardila ta haife
danka a cikin gidan sarautarsa, kai hailur ! Idan ma
mafarki kake yi toka farka ''
wannan shine gargadin da zuciyar hailur takeyi masa
nan fa yaji cewar babu abinda yake bukata sama
da ya sami damar tattaunawa da shardila domin ta
bashi amsar wadannan tambayoyi dake yi masa yawo
a cikin zuciya
lokacin da shadila tayi arba da jaruma siyama taga
fuskarta a zahiri sai hankalinta ya dugunzuma ainun
kuma taji zuciyarta taci gaba da dukan uku uku
ba komaine ya janyo hakan ba face ganin cewa tabbas
siyama tana tsananin kama da tsohon mijinta hailur
babban abin ma da ya kara dugunzuma hankalinta
shine ganin irin yanayin yadda take yin yakinta
Al amin ahmed nake Guyson, iri daya ne sak dana
tsohon mijinta Hailur
kafin shardila ta ankara tuni ta fara kuka tana mai
zubar da hawaye gami da ci gaba da kalle kalle da
waige waige a cikin filin gasar ko zata hango masoyinta
hailur amma shiru kamar maye yaci shirwa
ashe duk wannan hali da ta shiga Hailur ya lura da
ita duk da cewar fuskarsa a rufe take cikin rawani
kuma yana zaune a daman sarki ita kuma tana
tare da luzuraina abarin hagun sarkin,
Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus
sukaci gaba da fafata kazamin yaki a karo na biyu sai
ya zamana cewa karfi yazo daya an rasa wanda zai
iya cutar da wani a cikinsu, duk da tsananin karfin
damtse irin na darkus sai gashi naci da juriyar
siyama da tsabar horon yaki da ta samu a wajen
mahaifinta yasa ta iya kwatar kanta awajensa
tun suna kaiwa junansu sara da suka da takubban
hannayansu har sai da suka gaji ainun makaman nasu
suka subuce daga hannayansu suka ci gaba da gabzar
juna da hannu, Duk irin naushin da darkus yayiwa
siyama sai aga ta rama wato dai itama tayi masa irinsa
kai ! Tun suna tsaye akan duga dugansu tsabar
masifar yaki sai da takai ga sun durkushe kasa a tare
kuma a lokaci guda suka ci gaba da gabzar junansu
a hakan
kowannansu ya kama layi kamar wanda ya sha giya
suka bugu har izuwa lokaci mai tsawo suna cikin
wannan hali
daga can kuma sai duk su biyun suka bingire da baya
luuu ! Suka baje a kasa tare suna numfarfashi kamar
ransu zai fita...........
.
A nan ne Littafin Tsatsuba Na Hudu Yazo Karshe
Marubucin Littafin yace....
.
YAYA KARSHEN WANNAN GASA ZATA KASANCE TSAKANIN
SADAUKI DARKUS DA JARUMA SIYAMA ???
.
WAYE ZAI SAMU NASARAR ZAMA ZAKARAN GASAR
JARUMTAKA A TSAKANINSU ?
.
MAI ZAI FARU IDAN GIMBIYA SHARDILA TA GANE
MASOYINTA KUMA TSOHON MIJINTA HAILUR DA SUKA RABU
TSAWON LOKACI ?
.
SHIN ASIRIN ABUL SIYAMA YANA TONUWA HAR LABARI
YA KAI KUNNEN BABBAN MAKIYINSA SARKI SHARDAS WANDA ABUL SIYAMA KE ZARGIN
YA AURI MASOYIYARSA KUMA MATARSA?
.
MAI ZAI FARU IDAN YA SAMU LABARI ?
.
Marubucin littafin yace mu hadu a littafi na 5 donjin
cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari
Daga mai debe muku kewa a ko yaushe
Ni Al amin Ahmed Misau Wanda keda inkiyar Guyson
ko A square nake cewa Mu zama Lafiya.
Amma Ku meye kuka hango a haduwar Hailur da
shardila wata irin Dambarwa za a yi ne kam
sai naji daga gare ku...
0 comments:
Post a Comment