Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus
suka bingire kasa suna fitar da numfarfashi kamar
ransu zai fita a dai dai wannan lokaci ne aka buga
gangar tsayar da yaki sannan alkalin gasa ya
rugo izuwa cikin tsakiyar fili ya fuskanci jama a
yace yaku jama a kuyi sani cewa wannan gumurzu
tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama babu
zakara a tsakaninsu wato sunyi MUTUWAR KASKO
don haka zasu sake haduwa a zagayen karshe
na wannan wasa wanda za ayi rana i ta yau
don haka yanzu zamu kirawo jarumai na gaba
domin aci gaba da wannan gasa, gama fadin hakan
keda wuya sai aka dauke sadauki Darkus da jaruma siyama
daga cikin filin aka kaisu can gefe daya maimakon
a shigar dasu cikin wannan asibiti wanda aka tanada
domin yiwa jaruman gasar magani, dalilin da yasa
kuwa ba a shigar da su cikin wannan asibiti
ba shine babu mai wani babban rauni a cikinsu
akan hancinsu da bakunansu ne kadai jini ke diga
lokacin da jaruma siyama ta dawo cikin haiyacinta
sai ta dubi inda su sarki hulbasu ke zaune tana
mai mamakin dalilin da ya hana mahaifinta zuwa
inda take a lokacin da hankalinta ya gushe bayan an
tsayar da wasansu, bisa mamaki sai siyama taga
babu mahaifinta a inda yake zaune amma kuma
sai taga shardila ta kura mata idanu ko kiftawa
batayi duk da cewa kuwa ta rufe fuskarta da bakin kyalle idanunta kadai
ake gani
nan fa hankalin siyama ya dugunzuma ainun
in ba don ma ta hango mahaifiyarta ba ta taso daga inda take zaune
ta taho wajenta ba da mikewa zata yi ta bazama
mahaifin nata Hailur, da isowar zalima wato mahaifiyar
siyama sai ta rungumete cikin murna tana
mai yi mata jinjina bisa bajintar da ta nuna a wannan
wasa da tayi
A dai dai wannan lokaci ne wani likita yazo garesu
da nufin zai duba tafiyar siyama amma sai zalina ta tsaidashi tace babu wani
likita da zai duba lafiyar yata face ni don haka mun
gode bama bukatar taimakonka, koda gama fadin
hakan sai zalina ta bude wani kullin tsumma dake
hannunta ta dauko wani ruwan magani a cikin
wata yar doguwar kwalba ta mikawa siyama
siyama ta karba ta bude murfin kwalbar ta sa abakinta
tasha mukurwa biyu kacal sannan ta rufe kwalbar ta
mai dawa zalina
Faruwar hakan keda wuya sai jinin dake yoyo a
hannun siyama da bakinta ya tsaya cak kamar bai
taba diga ba kuma nan take taji duk gajiyar dake
jikinta ta dauke fuskarta ce kawai da idanunta a
dan kumbure sakamakon naushin da darkus ya yi mata
a can gefe daya kuma likita ne ke duba sadauki darkus
ana sa masa magani a kan hancinsa don tsaida
jinin dake yoyo koda darkus ya dawo cikin
hayyacinsa ya waiga bayansa yayi arba da jaruma siyama
sai ya daka mata harara yaji ya tsaneta fiye da
komai a rayuwarsa, nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone bisa ganin cewa yarinya karama ta
gagareshi a filin gasa, nan fa ya fara tunanin cewa ta kowanne hali sai ya kaita kas a zagaye
na biyu da zasu hadu wato
a wasan karshe da za ayi na gasar idan rana ta
zagayo kuma babu abinda zai yi ya dawo da kimarsa
da mutuncinsa a birnin face ya kashe wannan
karamar yarinya siyama ya zamana cewa ta mutu murus har lahira
a cikin filin gasa kuwa mai gabatarwa yazo
tsakiyar fili yaci gaba da jawabi sannan ya kirawo
sunayan jarumai na gaba wadanda zasuyi
fafata a wannan gasa
A dai dai wannan lokaci ne sarki hulbasu ya dubi
Hailur yace yakai abokina hakika ka baiwa yar
ka horon yaki na ban al ajabi domin ta bani mamaki
matuka
kuma akwai alamun cewa zata iya lashe wannan gasa
amma ka sani cewa lashe wannan gasa ba abune
mai sauki ba saboda babu irin abinda jaruman
gasar nan basayi don ganin sukai gaci, suna yin
tsafi tuggu da makirci iri iri don ganin sun sami
nasara ta kowacce hanya don haka dole ne kasa ido
akan yarka domin daga yanzu rayuwarta
na cikin hadari kada ka tafi izuwa gida kai tsaye
daganan ina son ku biyoni izuwa cikin gidan
sarautata domin ku dauke hankalin makiya
dolene ku sauya gidan zama kuma nima zan baku shawarwari da taimako
wai shin ma kasan kuwa irin ladan da yarka zata samu
idan ta lashe wannan gasa ta jarumtaka ? Koda
jin wannan tambaya sai hailur ya sunkui da kansa
kas saboda yaga shardila ta kalleshi don kada taga
kwayar idanunsa ta shaidashi sai yaki yarda ya dago
kansa
sa ar ma da yayi ko kadan bata jin abin da suke
tattaunawa shi da sarki kasancewar suna magana ne cikin kus kus
yadda babu mai iya jin abinda suke tattaunawa
hailur ya risina cikin girmamawa yace yakai
abokina wane irin lada za a baiwa yata idan ta lashe
wannan gasa
sarki hulbasu yayi murmushi sannan yace
da farko dai za a bata babbar gona guda daya
daga cikin manyan gonakan garin nan gami da
dinare dubu dari bakwai sannan kuma zan bata
mukamin shugabar dakarun dake tsaron lafiyata
muddin zata iya rantsuwa bisa rike amanata da
kuma siyar da rayuwarta don kare tawa idan har ta
sami wannan mukami zata rinka samun albashi
mafi tsoka a kan duk albashin da ake biyan dakaruna
daga wannan matsayi kuma zata iya zama sarkin
yakin birnin nan gaba daya bayan ta fuskanci wadansu
jarrabobi da matakai
Al amin Ahmed Misau, Guyson
.
Duk mutumin da ya sami wannan dama wacce yarka
ta samu dole ne ya fuskanci makiya da yawa
daga cikin manyan fadawana domin sun san cewa
zaizone yafi su matsayi da arziki, lokacin da sarki
hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin hailur ya
dugunzuma ainun take yaji yayi nadamar sanya
siyama a cikin wannan gasa saboda dalilai guda biyu
dalili na farko shine yanzu ya sanya rayuwar
siyama a cikin hadari domin zata tara abokan gaba
wadanda za su rinka farautar rayuwarta kamar
yadda mai jin kishirwa ke neman ruwan sha, abu na
biyu kuma idan ta tsallake kowanne hadari
da dukkan matakai da zata nisanta dashi
inma bai yi sa a ba ya rasata gaba daya kamar yadda ya
rasa matarsa shardila wacce ya tabbatar da cewar
tana dauke da juna biyu a lokacin da suka rabu
A yanzu da hailur yaga yarima hulkas sai ya fara
tunanin ko dansa ne wannan yaro ko kuma dan sarki
shardas ne
tabbas babu mai bashi amsar wannan tambaya
face shardila da kanta kuma yana shakkar ya sadu da ita
domin idan wani daga cikin dakarunta ya
gansu komai ya dagule kenan domin sai sarki
shardas ya samu labarin cewa yana raye to ba mashi ba matarsa zalima da yarsa
siyama ma rayuwarsu ta shiga hadarin da shiba
zai iya kare suba
hailur ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace ta
yaya zan iya saduwa da shardila a sirrance ba tare
da kowa ya ganni ba ko yaji babu wanda zai iya
taimaka mini na iya ganawa da shadila asirrance
face sarki hulbasu, hailur baya son sarki hulbasu ya san
cewa shine ainihin abokin gabar sarki shardas wanda tuni aka
dauka cewa ya mutu tun shekaru bakwai baya, hailu na cikin wannan tunani ne
yaji an ruguntsume da wani masifaffen azababben
yaki a tsakiyar filin gasa koda ya daga kansa yayi
arba da jaruman biyu dake fafatawa a filin
gasar sai ya cika da mamaki, ba komai ne ya sashi
wannan mamaki ba face ganin cewar dayansu amintaccen
yaronsa ne sadauki Ruhaisu jarumin da ya aminta
dashi dari bisa dari a cikin dukkanin yaransa lokacin a yake kan matsayin
shugaban kabilarsu
koda hailur yayi arba da ruhaisu sai farin ciki ya lullubeshi
domin indai ruhaisu na tare dashi zai iya nemo
masa ire iren sauran jama arsu da sukayi saura a raye
domin su sake tayar da kabilarsu kuma su taimaka
masa wajan bashi kariya dashi da iyalansa
jarumin da yake karawa da ruhaisu kuwa wani
narkeken katone wanda ya ninkashi girma
da tsayi sau uku
kuma a zahiri ma yafi shi surar sdaukantakada
jarumtaka ana kiransa da suna Jamar, amma suna
fara artabu sai jamar ya raina kansa domin ruhaisu yafishi zafin nama da
iya yaki
nan da nan ya rikitashi kuma ya kuntatashi sai
gashi Jamar yana ta ja da baya kuma yana ta
kokarin kare kansa baya ma iya kai hari koda
ruhaisu ya tabbatar da cewar yafi jamar iya yaki
da fadan hannu sai kafa sai ya shammaceshi ya
daka tsalle sama ya doki habarsa da guiwarsa ta dama
saboda karfin dukan sai da jamar yayi sama a
lokacin da jini yai tsartuwa daga cikin bakinsa yana saman kafin ya fado kasa sai
ruhaisu ya kara dukan kirjinsa da karfin gaske
kawai saiji akayi jamar ya fado kasa tim kamar
giwa ta fadi kuma ya baje kas a sume ko kyakkyawan
motsi ba yayi
koda ganin haka sai filin gasar ya rude da shewa aka
kama yiwa ruhaisu tafi da jinjina ba don komai ba
sai don saboda shine jarumi na farko da ya fara
lashe wasansa na farko a cikin kankanin lokaci
da fara gasa tunda ko rabin sa a ba ayi ana gumurzun
ba ya sami wannan nasara
ana cikin wannan
yanayine hAilur ya dubi
sarki hulbasu yace hakika wannan jarumi ya burgeni
matuka zan so na gana dashi, koda jin haka sai
sarki hulbasu ya yi murmushi yace ai wannan mai
saukine zan shirya duk yadda zaka gana dashi nan
ba da dadewa ba
yanzu ina so kaje ka ruko yarka da matarka ka shigo
cikin tawagata domin mu shiga cikin gidan sarautata
tare
koda jin haka sai hailur ya dubi sarki hulbasu cikin
alamun damuwa yace bana son na shiga cikin
filin nan ranka ya dade ka taimaka min ka aika wani daga
cikin hadimanka ya taho da siyama da zalina
koda jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi
murmushi yace shikenan an gama, nan take sarki ya
kira wani hadiminsa ya turashi yaje ya taho da jaruma
siyama da mahaifiyarta suka shigo cikin tawagar sarki
hulbasu
koda hailu ya yunkura zai mike tsaye daga kan
kujerar da yake zaune sai santsi ya kwashe shi ya
zame zai fadi kasa
a lokacinne rawanin da hailur ya rufe fuskarsa dashi
ya zame kafin ya mayar da rawanin kan fuskarsa
shadila ta yi arba dashi domin ya hada idanu da ita
cikin kaduwa yai sauri ya mayar da rawanin
ita kuwa shadila sai ta kame a inda take tsaye saboda
tsananin mamaki da kaduwa da murna bata san
sa adda hawaye ya fara zubo mata ba...
Zidane kd
.
Duk da cewa itama ta rufe idanunta da bakin kyalle sai
da sarki hulbasu ya lura da halin da take ciki amma
sai ya basar yayi kamar bai fahimci komai ba
ita kuwa luzuraina sam bata lura da duk abinda ke
faruwa ba yarima hulkas ne ya lura da irin satar
kallon da mahaifiyarsa ke yiwa abul siyama
kuma yaga sa adda hawaye ya zubo mata, nan take
hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa dalilin faruwar
wannan lamari don haka sai zuciyarsa
ta kama zargi da wasu wasi amma ya kasa
gane abin ma da yake zargi da wasi wasin a kansa
haka dai sarki da mukarrabansa suka mimmike tsaye a cikin filin gasar aka kawo
musu dawakansu suka hau sannan suka
fice daga cikin filin gasar dakaru na zagaye dasu gaba
da baya da kuma tsakiyarsu
Ashe Tun sa adda aka gama fafatawa tsakanin
sadauki darkus da jaruma siyama tuni sadauki darkus ya
kebe da wadansu zakwakuran yaransa ya basu
umarni akan cewa da zarar sun ga jaruma siyama da
iyayanta sun fito daga cikin filin gasar a kashe su a
sirrance ba tare da kowa ya gane abinda ya kashe sun ba
baya ga wannan mugun abu da sadauki darkus ya shirya
ashe shima sarkin yakin sarki hulbasu ma ya
tura wadansu yaran nasa ma a sirrance sun je
can hanyar bayan gari sun labe rike da da kwari da baka sun dana kawai jira
suke suga giftawar jaruma siyama da iyayenta
akan hanyarsu ta komawa gida su sakar musu
harbi su kashesu
lokacin da shi sarkin yaki wanda ake kira suna
RINZALU da kuma sadauki darkus suka ga cewa
siyama tare da iyayanta sun shiga cika da mamaki kuma
hankalinsu ya tashi saboda sun san cewa lallai
dukkan shirinsu ya watse, nan take sarkin yaki
rinzalu ya nufi tawagar ta sarki da nufin ya shiga
cikinsu amma sai yaga dakarun sarki na musamman
masu tsaron lafiyarsa sun shiga gabansa sun hanashi
shiga cikin tawagar, Al amarin da yai matukai baiwa
sarkin yaki rinzalu mamaki kenan kuma ransa ya baci
saboda ba a taba hanashi shiga cikin tawagar
sarki ba sai yau
nan take ya fara tunani a cikin zuciyarsa yace
wai shin wane irin matsayi ne da jaruma siyama da
iyayanta a wajan sarki hulbasu haka har da yake
kare rayuwarsu
wai shin ma yaushe ya san su har da suka sami matsayi
a wajansa kamar haka amsoshin da rinzalu ya kasa baiwa
kansa kenan
haka dai ya hakura yana ji yana gani ya juya da
baya yaje ya shiga cikin sauran yan uwansa
--
Al amin Ahmed Misau Lokacin da aka iso cikin
gidan sarautar sarki Hulbasu sai ya kama hannun hailur
ya jashi har izuwa cikin kuryar turakarsa suka zauna
aka kawo musu abinci da abinsha
shi kansa hailur
yayi mamakin yadda sarki hulbasu ya aminta dashi haka cikin kankanin
lokaci alhalin sau daya rak suka taba ganin junansu
ma
wannan haduwar ta yau itace ta biyu amma ya aminta
dashi kamar
haka
Hailur yace a cikin ransa wata kila saboda abin
karamcin da nayi masa ne a daji shi yasa ya saka
mini da irin wannan tarba, bayan an kawo musu
wannan abinci da abin sha na alfarma sai sarki
yayiwa hailur tayi amma sai hailr ya kasa cin
abincin ya kura masa idanu kawai a lokacin da tuni
sarki ya gabatar da wajan loma biyu yana shirinkai
ta uku kenan sai ya lura da cewa hailr baya cin abincin
kuma yayi shiru fuskarsa na nuna alamun tunani
koda ganin haka sai sarki Hulbasu yai murmushi
a gareshi yace kwantar da hankalinka ya kai
abokina kayi sani cewa a halin yanzu matarka
da yarka jaruma siyama suna can tare da matata da kuma
gimbiya shadila matar sarki shardas cikin
aminci suna cin irin wannan abinci dake gabanmu
koda jin haka sai hailur ya saki ajiyar zuciya tare da
jinjina kai alamar gamsuwa da furucin da sarki Hulbasu
yayi masa
nan ya saki jikinsa ya fara cin abincin, har suka ci
suka koshi dayansu bai kara cewa uffan ba sai
bayan sun nutsu sannan sarki ya dubi hailur yace
yakai abokina kayi sani cewa hankali shine
yake gani amma ba idanu ba tabbas akwai boyayyen
al amari a tare dakai wanda kake boye mini
amma ina so ka sani cewa ba a boyewa abokin
kuka mutuwa
yakamata ka gane cewa shi masoyi na kwarai
har abada masoyi ne shi kuwa masoyi zaka sameshi
mai rike amana da kare masoyinsa da sallama
rayuwarsa a gareshi a koda yaushe komai
RINTSI DA TSANANI, na rantse maka da girman
iyayena da kakannina ba zan taba cin amanarka bakona
juya maka baya musamman idan kayi la akari da
irin taimakon da kayi mini a cikin daji wanda har na
mutu ba zan manta dashiba, ina son ka saki
jikinka da zuciyarka ka sanar dani duk abin dake
faruwa
shin menene tsakaninka da shadila matar
sarki shardas?
Na lura da duk abin da ya faru dazu a tsakanin kai
da ita a filin GASAR JARUMTAKA, naga hawaye na
zuba a cikin idanunta sa adda rawanin fuskarka
ya kwaye tayi arba dakai, shin kun san juna ne dama ?
Ka sani cewa ko ka sanar dani wannan sirri ko ka ki tuni
yanzu rayuwarka da ta iyalanka tana hannuna
domin inda ban shigo daku nan ba cikin gidan sarautata
tuni kun dade da zama gawa, lokacin da sarki
yazo nan a jawabinsa sai hailur yaja dogon
numfashi ya ajiye sannan ya dubeshi a lokacin da
idanunsa suka ciko da kwallah yace yakai
wannan sarki mai
Adalci kayi sani cewa gimbiya shadila matatace
a baya kafin sarki shardas ya mallaketa, koda jin
wannan batu sai idanun sarki hulbasu suka zazzaro
tsoro ya kamashi kuma jikinsa ya kama kyarma shi
kuwa hailur sai yaci gaba da bayani yana mai cewa
a ranar angwancina da ita ne sarki shardas da dakarunsa
suka kawo ma kabilarmu harin Mamayar bazato sukayi
ta ragargazar dakarunmu kuma suka kame matayanmu
da yawa a matsayin bayi ni ne kadai jarumin da
na gagaresu har ma nayi gumurzu da sarki shardas
amma a karshe ya jefani kasa daga saman wani
tsauni mai tsananin tsawon tsiya sanadiyar da na rasa
hannuna guda daya na hagu kenan kuma kafata
guda daya itama ta sami wannan nakasa ta shagidewa, nidai kawai farkawa
nayi na tsinci kaina a cikin wata bukka a tsakiyar daji
koda na yunkura domin na mike zaune sai naji na kasa
domin gaba daya jikina babu kuzari, yayin da na sake
yunkurawa domin na yaye mayafin da aka lullube
ni dashi akan shimfidar da nake kwance sai naji
babu hannuna guda daya na dama, nan take na kwarara
wani uban firgitaccen ihu cikin tsananin bakin ciki
da razana
faruwar hakan keda wuya sai ga wani dattijo tare da
wata kyakkyawar budurwa sun shigo izuwa cikin
bukkar
da shigowarsu sai suka durkusa a gabana dattijon ya dubeni
a dimauce yace yaro me ya faru gareka ka tsandara
wannan uban ihu haka shin wani mugun mafarki
kayi ko kuwa wani mugun abune ka gani
sa adda naji wannan tambaya sai hawaye ya zube mini
na dubi dattijon cikin nutsuwa nace me yasa kuka ceci rayuwata baku barni
na mutu ba
yanzu menene amfanin rayuwata a doron kasa
tunda na rasa komai da kowa nawa kuma na rasa
lafiyata
ina mai rokonku daku gaggauta kasheni yanzu
domin na huta da bakin cikin dake nukurkusar
zuciyata
yayin da na zo nana zancena sai dattijon da wannan
kyakkyawar budurwa suka kamu da tsananin
tausayina.
Dattijon ya kalleni yace samari hakika kana da nisan
kwana a duniya domin a tarihin wannan tsauni
wanda ka fado daga kansa fiye da shekaru dari bakwai
baya ba a taba samun mahalukin daya fado daga
kansa ba ya rayu sai kai
muma nan da ka ganmu muna zaune a cikin
wannan daji mun fitone daga cikin wata babbar
kabila da ake kira BANU IKHLAS. kamar yadda
sarki shardas ya karar da kabilarka haka muma ya
karar da tamu kabilar ni da wannan ya tawa ce
zalina kadai muka tsira da rayuwarmu alokacin
sa adda ya kawo farmaki zuwa kauyanmu nida ita
bama nan muna cikin daji muna yin farauta
bayan mun dawo mun iske iyayanmu da yan
uwanmu da duk danginmu sun zama gawa sai
muka kama kuka mutum daya kacal muka samu
da sauran numfashi a jikinsa shine ya gaya mana
cewa sarki shardas ne da kansa shida dakarunsa
suka zo sukayi mana wannan mummunar barna
da dai muka ga cewa ba zamu iya daukar fansa a kan
sarki shardas ba sai muka hada kayanmu muka sake
komawa cikin daji muka ci gaba da farauta, amma
bamu zauna a waje daya ba sai muka ci gaba
da tafiya muna ketawa ta gefen garuruwa
da kauyuka amma bama zama a inda babu cibiyar
ruwa
Tabbas ruwan dake kasan wannan tsauni da ka fado
ne ya kawoka nan domin daga can zuwa nan tafiya
ce ta kwana saba in da hudu, sa dda mahaifin
zalina yazo nan a zancensa sai na cika da tsananin
mamaki kuma na sake kamuwa da bakin ciki
mara misaltuwa don haka ban san sa adda na fashe
da kuka ba ina mai cewa ina ma na mutu ban rayu ba sakamakon fadowa daga
kan wannan tsauni tun da yanzu bani da kowa
kuma bani da komai a wannan daji, koda jin
wannan batu sai tausayina ya kama zalina da
mahaifinta
zalina ta dubeni tace yakai wannan jarumi
ma aboci kwarjini da jarumtaka ka yi sani cewa yadda
baka da komai da kowa a wannan duniya haka muma
muka kasance ni da mahaifina amma tunda yanzu
kaddara ta hadamu mun sameka ka samemu, zaifi
kyau mu rungumi kaddara bisa yadda ta samemu
mu ci gaba da rayuwa ko don nan gaba mu ga yadda
karshen mulkin sarki shardas zai kasance koda kuwa
mu bazamu iya ganin karshen nasa ba, ka sani cewa
babu wani abu madawwami kuma komai
nisan jifa kasa za fado, don haka duk abinda sarki shardas
ke takama dashi watarana sai ya fado kasa tunda
idan ba mutuwa akwai tsufa akwai lokacin da yanaji
yana gani ba zai iya yin zaluncin da yake yi ba yanzu
koda mu bamu ga wannan lokaci ba ina son ire irenmu
sugani
Al amin Ahmed Misau, Guyson Ko A Square nake magana
lokacin da zalina tazo nan a zancenta sai jikina
dana mahaifinta yayi sanyi saboda mun san cewa
duk abinda ta fada gaskiya ne, tun daga wannan rana
zalina da mahaifinta sukaci gaba da jinyata har na
sami lafiya ya zamana cewa ina iya mikewa tsaye
na dogara sanda na bisu izuwa daji don yin
farauta amma fa duk sa adda na dubi hannuna na
hagu naga babu shi kuma naga kafata ta dama ta
shagude sai na fashe da matsanancin kuka na bakinciki domin gani nake kamar
rayuwata bata da wani sauran amfani
duk sa adda na fara wannan kuka sai zalina da
mahaifinta sunyi da gaske sannan suke rarrashina na
dawo cikin hayyacina....
Duk sa adda na fara wannan kuka sai zalina da mahaifinta
sunyi da gaske sannan suke rarrashina na dawo
cikin hayyacina
wani abin mamaki wanda ya daure min kai
shine duk da cewar na rasa hannu daya da kafa daya
ko kadan ban rasa karfin damtse na ba da kuma
iya yakina don haka duk sa adda muka shiga
daji farauta duk muguwar dabbar da ta zo gabanmu
take nake gamawa da ita, komai yawan gungun
yan fashi kuwa idan mukayi gamo dasu ni kadai
nake tarwatsa su, amma zalina da mahaifinta suna
taimaka mini saboda sun kware ainun a iya harba
kibiya
A lokaci guda kowannansu na iya harba kibiyoyi
bakwai
sai dai kaga maza na zubewa kasa yayinda tsinin
kibiyoyinsu suke ratsa kirazansu, A kwana a tashi
sai na sami wata bakwai tare da su zalina ya zamana
cewa na shaku dasu ainun musamman zalina
wacce komai tare muke yi shimfidar barci kawai
muke rabawa
A hakane na fuskanci cewa soyayya ta shiga
tsakaninmu amma dana tuna cewa ni fa
yanzu masaki ne bani da hannu daya da kafa daya sai
na ga cewa idan na nemi soyayyar zalina na cutar
da ita
Haka kuma idan na tuna cewa na rasa masoyiyata
shadila sai naga cewa ai na gama soyayya a duniya
don ba zan taba samun wacce zan sota ta soni ba
kamarta
bisa wannan daliline na rinka danne soyayyar
zalina a cikin zuciyata kuma duk sa adda naga zata
nuna mini soyayyar tata saina bagarar, hm
Ni abinda yake bani mamaki ma shine me zata yi da masaki muna cikin wannan hali ne
mahaifin zalina ya kamu da cuta mai tsanani wacce
takai shi ga kwanciya, abu dai kamar wasa
kullum sai ciwo ya rinka gaba ya zamana cewa ba a
samun sauki
Al amarin da ya dugunzuma hankalinmu kenan
muka rasa sukuni da kwanciyar hankali ita kuwa
zalina kullum bata da aikinyi sai kuka da bakin ciki
da kyar nake iya rarrashinta, ba komai ne yake sata
wannan yawan kuka ba sai ganin cewa babu alamar
samun lafiya ga mahaifinta kuma ga dukkan alamu
ciwon nasa bana tashi bane, wata rana na tashi da
sassafe ina shirin tafiya daji domin naje nayi farauta
naman da zamu ci da rana a lokacin zalina na can
wajan kogon da muke kwana ta dora tukunya akan
wuta tana dafa mana abincin kalaci sai mahaifin
zalina ya kira sunana a lokacin da nake daf da fita
daga cikin kogon
Cikin tsananin mamaki na juyo na dubeshi saboda
rabonsa da ya budi baki yayi magana tun daga
ranar da ya kwanta wannan cuta, cikin matukar sanyin
jiki na karasa daf dashi na tsugunna a gabansa inamai kura mas aidanuna ya
shi kuma sai ya kamo hannuna ya dora akan kirjinsa
ya dafe hannun nawa da dukkan hannayansa biyu
sannan ya budi baki da kyar yace yakai
hailur kayi sani cewa wannan ciwo nawa bana
tashi bane mutuwa zanyi kuma a koyaushe wa adina
zai iya cika
ina neman Alfarma guda daya jal a wajanka alfarmar
kuwa itace ina son ka auri zalina, koda jin wannan
batu sai zuciyata ta buga da karfi na dubeshi cikin
mamaki nace yakai abul zalina ai idan kace na
auri zalina bakayi mata adalci ba domin kana sone
ta auri nakasashshe koda jin haka sai tsohon yayi
murmushin karfin hali ya dubeni cikin nutsuwa yace yakai
hailur kayi sani cewa a zahiri kake nakasashshe amma
a zuciyarka kafi ta lafiya sannan kuma har yanzu
sadaukantakarka da jarumtakarka suna nan basu
ragu ba dai dai da matsayin kwayar zarra
ina son ka sani cewa yata ta kamu da tsananin sanka a cikin
wannan hali da kake ciki na nakasa kaga kenan ashe
soyayyarta itace soyayyar gaskiya ka auri yata
zalina ko don saboda ka samu zuri ar da zasu ga bayan
babban makiyinmu sarki shardas
ka sani cewa kowacce mace tana son ta auri
namijin da zai iya kare mutuncin ta da rayuwarta
koda kuwa shine yafi kowa nakasa a doron kasa
lallai ku cika mini burina na ganin bayan sarki shardas
wannan itace kadai wasiyyata a gareku, ashe duk wannan bayani
da mahaifinta
yake yimini zalina dake can kofar kogo tana sauraro don
haka sai ta kasa cigaba da aikin da takeyi ta koma
gefe daya ta zauna tana ta faman kuka, koda na fito
daga cikin kogon dutsen rataye da takobina da nufin
na shiga daji don gabatar da farautar sai naga
zalina tana ta kukanta
Al amarin da yasa na gane cewa lallai duk taji abinda muka tattauna kenan dani
da mahaifinta
cikin sanyin jiki na karasa gareta na zauna daf da ita
kanta na sunkuye sai na tallabo habarta da lafiyayyen
hannun nawa kuma na share mata hawaye
muka kurawa junanmu idanu sannan na dubeta nace
shin kin amince na zama abokin rayuwarki
koda jin wannan tambaya sai zalina ta murtuke
fuska
daga can kuma sai ta rungumeni ta kama kyalkyala
dariyar farinciki
muna rungume da juna mukaji motsi a bayanmu
a firgice muka juya da sauri sai mukaga she mahaifin
zalina ne ya fito daga cikin kogon dutsen yana dogara
sanda da kyar yana numfashi sama sama
A guje na janye jikina daga cikin na zalina na
karasa gareshi na rukoshi na zo dashi wajan zalina
itama ta kamashi muka zauna gaba daya sannan ta
dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace haba
ya kai Abbana yaya kai da kake cikin wannan hali zaka taso kayi tafiya
sa adda abul zalina yaji wannan tambaya daga
bakin yarsa zalina sai ya dubeta
yayi murmushin karfin hali yace yake yata ai dole ne na
taso ko don naga abin farinciki na karshe wanda idanuna
zasu gani wanda shine amincewar junanku akan aure
lallai ina so naga wannan aure naku da idanuna
kafin rai yayi halinsa, nan take tsohon ya yiwa hailur
bayanin yadda zasu daura auren bisa al adar su
kabilar
wato kowannansu ya yanki dan yatsansa ya diga jininsa
a cikin ruwa
bayan jinin biyu ya gauraye sai kowannan su ya sha
ruwan
nan take kuwa muka aiwatar da hakan, muka rinka
shan ruwan muna kallon juna cikin murmushi har
sai da ruwan ya kare kaf
A dai dai wannan lokacine farinciki ya lullube abul
zalina ya dubi hailur yace yakai babban gwaro kayi
sani cewa yanzu ka zama na zalina kuma zalina
itama ta zama taka babu abinda zai rabaka face
kaddara ko mutuwa, wannan dama shine manufar
shan jinin juna da kukayi, bisa al adar kabilarmu
a ranar da miji ya mallaki matarsa babu abinda zasu fara
face zuwa daji farauta tare, don haka yanzu saiku
tafi sannan da ku ka samo shi zaku kawo a gasa
muci muyi walima da farin cikin aurenku, koda
jin wannan batu sai na dubi abul zalina cikin alamun
damuwa nace haba yakai abul zalina yaya za ayi
mu tafi daji mu barka kai kadai a nan alhalin kana
cikin wannan halina rashin lafiya, koda jin haka sai
abul zalina ya dubeni cikin murmushi yace kada
ka damu dani lallai zakuje ku dawo kuma ku sameni
cikin koshin lafiya da sauki fiye da ko yaushe
wannan shine abinda na gani a mafarkina na daren
jiya
bisa wannan dalili ne ma a yau din nan na sami
saukin da har na iya mikewa tsaye na taka kafafuna
na fito daga cikin wannan kogo haka dai abul
zalina yaci gaba da rarrashinmu har ya samu ya
shawo kanmu muka amince da barinsa a wajen
amma kafin mu tafi sai da ya rungumemu yana ta dariyar
farinciki
bayan ya janye jikinsa daga cikin namune mun juya
zamu tafi izuwa cikin daji sai zalina ta waigo ta
dubeshi take ta hango kwalla a cikin idanunsa
al amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan ta
dubeni tace yakai mijina nifa zuciyata bugawa
take da karfi ji nake kamar idan muka dawo ba zamu
riskeshi a raye ba
ni kaina naga alamun hakan a tare da mahaifin nata
kuma duk kalaman da yake yi na bankwana ne amma don
kada hankalin zalina ya tashi sai naki sanar da ita
haka dai muka nausa cikin daji muna waigen Abul
siyama shi kuma ya bimu da kallo yana yi mana murmushi
har muka kule muka daina hangoshi
A sannan ne kuma muka falfala da azababbn gudu izuwa
cikin daji mukayi ta tsala gudu ba sassauci muna
neman dabbar dajin da zamu samu
babu abinda zai baka mamaki face yadda nake iya gudu
ina dogara sanda alhalin kafata guda daya bata da
kyau kuma har tserewa zalina nake yi a gudun
ni ina rike da takobi ne kuma karshen sandar da nake
dogarawa mashi neita kuwa zalina a hannunta
kwari ne kuma ta rataya kwanson kibiyoyin
kwarin a bayanta
don haka ita bata rike wani makami sai kwari da baka
koda muka nausa cikin daji sai muka rabu ni kuma
nayi gaba ita kuma tayi yamma sannan kuma muka
baiwa junanmu tsawon rabin sa a akan mu hadu a
bakin wani dutse dake can tsakiyar dajin
kowannanmu na rataye da kaho a bayansa wanda duk
sa adda ya shiga wani hadari wanda ba zai
iya kubutar da kansa ba sai ya busashi komai nisan
inda yake dan uwansa zai iya jiyowa har yakai mas
dauki
shidai wannan kaho na sihirine kuma gadon gado ne
a kabilar tasu zalina kuma mutum ba zai iya mallakarshi
ba face ya kasance dan kabilarsu ko kuma ya auri
jinin Kabilar
bayan mun rabu a cikin daji nida matata zalina sai muka wanzu muna masu
neman abin farauta baji ba gani, lokacin da naga
na
shafe dan dogon lokaci ina neman abin farautar ban samu ba
sai hankalina ya dugunzuma ainun saboda ina ganin cewa ai abin kunyane
ace a ranar daurin aurena na kasa farauto abincin da zamu
ci nida amaryata
Ehm Al amin Ahmed Misau, Guyson ko A square
Ina cikin wannan haline naga wata barewa ta
nufo inda nake cikin azababben gudu gashi dai
barewar ta hangoni a gabanta rike da makami
amma ko shakkar tunkaro ni batayi ba
dada durfafo ni takeyi al amarin da yasa na fahimci
cewar lallai masifar da ta korota ta nufoni don tsira
da rayuwarta ta wuce tawa hadari, ai kuwa ban ankara ba
sai naga ashe wani murjejen zaki ne ya tasota a gaba
tun daga nesa dana hango zakin ya falfalo da azababben gudu
har tashi sama yake saboda karfin gudun nasa
kuma harshensa na zazzagowa waje daga cikin bakins ana gane
cewa lallai
wannan zaki a cikin muguwar yunwa yake
koda naga cewa barewar nan so take ta wuce ta gabana
domin ta tsira da rayuwarta sai na yunkura cikin zafin nama na
daka tsalle sama a lokacin da itama barewar ta daka tsalle da nufin ta shallakeni
muna haduwa a saman na soketa da mashina ta
zama gawa na duro kasa bisa kafafuna barewar
na sakale a jikin mashin nawa, ai kuwa sai wannan zaki
yayi tirjiya a lokacin da tazarar dake tsakaninmu
bata wuce taku goma ba
nan fa muka fara kallon kallo tsakaninmu da murjejen zakin
nazarin da zakin yake yi shine ni zai farwa sannan
ya dauke barewar ko kuwa barewar zai karba
ni kuwa nazarin da nakeyi shine ta yaya zan iya
.Ya kasance shi ba karamin tashin hankali bane
duk da na san cewa na sha yin gumurzu da manyan
dabbobin daji ina samun nasara a kansu sai da
zuciyata ta karaya akan wannan zaki domin ban
taba yin gamo da tsohon zakimai girma da kwarjinin wannan ba
nikam tuni na gama aiyanawa a raina cewa
duk rintsi ba zan iya sallama barewar ba ga wannan
zaki koda hakan na nufin zan rasa rayuwata
kawai sai na cake mashin nawa a cikin kasa
wanda ke dauke da barewar sannan na buda hannuna
mai rike da takobi ina mai
gyara tsayuwata kuma na koma gefe daya na tsaya ina
mai baw azakin zabi tsakanin barewar da ni kaina
ya zabi wanda zai fara afkawa
take zakin yayi wani irin
gurnani mai ban tsoro wanda yasa hantar cikinsa ta kada amma da na tuna cewa
amaryata
zalina na can fa tana farauta a cikin wannan daji
wata kilama yanzu ita ta dade da samo nata abin
farautar taje inda mukayi zamu hadu ta zauna
tana jirana sai naji zuciyata ta kekeashe ga barin dukkan tsoro.....
Kamar hadin baki sai nida zakin muka falfalo
da gudun tsiya izuwa kan juna muka dako tsalle
sama a tare kafin nayi wani yunkuri na saran zakin
ko sukarsa da takobina tuni shi ya sa kirjinsa ya
bangajeni
ai kuwa sainaji kamar aksusuwan kirjina sun
kakkarye nayi can baya da karfi bayana ya gwaru
da jikin wata bishiya na fado kasa a matukar galabaice
ina aman jini ta hanci da baki, koda zakin yaga
halin da na shiga sa adda shima ya duro kasa sai
ya wangame baki ya kwalla wani uban ruri anda
ya fi wanda yayi a baya mai nuna kuranta kansa
da dai yaga na kasa tashi ina ta numfashi sai
ya wuce ta gabana ya daka tsalle da nufin ya suro
wannan barewa dake sakale a jikin mashina
ni kaina ban san yadda akayi ba na sami gagarumin
karfi da kuzari kawai gani nayi na mike tsaye zumbur
na daka tsalle daga inda nake na rungumo zakin
kafin bakinsa ya cafi barewar mun fado kasa tim !
Nan fa muka kama kokawa a kasa muna ta birgima
idan zakin ya danneni yana kokarin kafa min
hakoransa sai na juye dashi nima ina kokarin
turmushe shi da karfin tsiya domin na hallakashi
sai da muka shafe kusan sa a daya muna ta bakin
artabu ya zamana cewa zakin ya karkarce jikina
da kaifin faratan hannayansa yai mini raunika
masu yawa jini na zuba a jikina amma kuma ya kasa
kafa min hakoransa a jikina
lokacin da jiri ya fara dibana na tabbatar da cewar ina daf
da halaka sai zuciyata ta kufulo cikin tsananin
zafin nama na suri zakin na dokashi akan wani
katon dutse nan take kan zakin ya dagwargwaje ya
zama gawa
A sannan ne na yanke jiki na fadi kasa cikin mugun yanayi
da kyar na iya bude jakar guzurina na fiddo magani
na shafa akan raunikan jikin nawa da hannu daya
wadansu raunikan ma dake gadon baya na in da
hannuna ba zai kai ba ban sami damar sa musu
maganin ba
a sannan ne na dauko battar ruwana na bude nash
Sai da na dan huta naji karfin jikina sannan na mike
tsaye na dauki gawar zakin na saba a kafadata
amatsayin abincinmu na rana itama barewara
sai na barta a jikin mashin nawa naci gaba da tafiya
na nufi inda zamu hadu da matata zalina
hakika SADAUKANTAKA tana da rana tabbas in ba don
na kasance sadauki ba da babu yadda za ayi na iya daukar
wannan katon zaki har na sabashi a kafadata da
hannu daya kuma naci gaba da tafiya alhalin ina
rike da barewa bisa mashina, haka dai naci gaba da
tafiya har na iso inda zan hadu da zalina matata
tun daga nesa kuwa na hango zalina zaune akan
wannan dutse tana hange hange da waige waige
ko zata gano ni, har ma ta zaku tana mikewa tsaye
akan dutsen
ai kuwa tana hangoni dauke da zakin da kuma barewa
sai ta cika da tsananin mamaki, cikin tsananin
murna ta duro kasa daga kan wannan dutse ta farfalo
da gudu izuwa gareni ta rungumeni koda taji
raunika a jikina sai ta janye jikinta daga cikin nawa
da sauri ta dubi sauran raunikan na jikina, take
hawaye ya kwararo daga cikin idanuwanta ta
dubeni cikin alamun tausayi tace yakai mijina me yasa
ka sai da rayuwarka don kawai ka cika wannan ka ida
ta al adarmu
Sa adda naji wannan tambaya sai na bushe da dariya
nace
yake matata kiyi sani cewa ko a tamu al adar namiji
baya samun matar aure a cikin sauki har sai ya
sha bakar gwagwarmaya ta hanyar gasa a neman
auren,
kuma gasa ce mai hadarin gaske wacce mutum ma
zai iya rasa rayuwarsa gaba daya, nan dai muka juya
da baya muka nufi hanyar gida, muna cikin
tafiya ne na dubi zalina na bushe da dariya, Al amarin
da yai matukar bata mamakikenan
ta dubeni tace yakai mijina kai kuwa menene dalilin
yin wannan dariya taka, kawai sai nayi ajiyar numfashi
nace gani nayi nidake mun shafe sama da sa a biyu
a cikin nan muna farauta amma ke ko fiffiken dan
tsako baki samo ba, dajin wannan batu sai itama ta
kyalkyale da dariya tace ni kaina na yi matukar mamakin
yadda ko tsuntsu guda ban iya harbowa ba daga sama
alhalin ga su nan birjik suna ta kaiwa da komowa
a sararin samaniya sai dana yi asarar kibiyoyina
sama da guda talatin, kai bama tsuntsaye ba hatta
kananan dabbobin daji sai dana kasa tsere da wajan
guda bakwai amma da zarar sun shiga cikin duhuwa
saina nemesu sama ko kasa na rasa su
koda jin haka sai nayi dariya nace ai kin san cewa komai
sa a ne da rabo
haka dai muka ci gaba da hira har ya rage saura tafiya
kadan mu iso gida
kwatsam muna cikin tafiya sai zalina tayi tuntube ta fadi a lokacin da zuciyarta
ta fara bugawa da karfi, cikin sauri na ajiye mashina
mai cake da barewa na tasheta zaune na dubeta
cikin kaduwa ina mai dudduba jikinta nace lafiya
kuwa menene ya sameki, zalina tayi ajiyar zuciya
ta dubeni cikin alanun firgici kawai sai naga hawaye
ya zubo mata take ta fashe da kuka tana mai cewa
naji a jikina cewa mahaifina yayi kaura, koda jin haka sai
nima hankalina ya tashi na dubeta cikin kwarin guiwa
nace ke haba ! Tashi mu karasa gida mahaifinki na
nan raye
kawai dai zuciyarki ce take raya miki hakan
nan dai na tasheta muka mike tsaye har zuwa wannan
lokacin ina dauke da wannan katon zakin a kafadata
ga kuma barewa a jikin mashina
haka dai muka
cigaba da tafiya harmuka
Iso gida
tun daga nisa muka hango Abul zalina kishingide
a jikin dutsen kogon da muke kwana ya dora
kafarsa daya akan daya yana barci, kuma ga sanda
a hannunsa in ba don dora kafarsa da yayi ba daya bisa
daya da kuma sandar da ya rike a hannunsa da dole ne
ace ya mutu
Al amarin zalina kuwa lokacin da ta hango mahaifinta
a cikin wannan hali tun daga nesa sai jikinta yayi sanyi
Al amin Ahmed Misau Nake Guyson Ko A square
zuciyarta ta karaya kawai sai ta yarda bakan dake
hannunta ta falfala da gudu izuwa gareshi tana
isa gabansa sai ta kura masa idanu koda taga
idanunsa a kafe suke ko kiftawa basa yi kuma babu
inda yake motsi daga cikin gabobin jikinsa sai ta
fada kansa ta rungumeshi tana mai tsandara uban
ihu sannan kuma ta fashe da kuka
koda ganin abin da
ya faru sai nima na rugo da gudu ina dogara sandata
ina isowa na warbar da wannan zaki na kafadata
kuma nayi jifa da sandata da mashin da barewar
ke tsire akai
kawai sai na tsugunna kasa bisa guiwoyina na fara
kuka aka rasa
wanda zai rarrashi wani tsakanina da zalin
nikaina Al amin Na tausaya musu gaskiya
da wannan gagarumin rashin mahaifin ta da sukayi
sai da muka shafe kusan sa a guda muna kuka sannan na
mike tsaye naje na kama kafadar zalina na
tasheta tsaye na shiga rarrashinat, sai da ta dawo cikin
hayyacinta sannan muka fara shirye shiryen
binne gawar mahaifin nata, tun daga wannan rana
muka bar wannan daji ba tare da fatan komawa cikinsa
ba
ko don ziyara ga kabarin mahaifin nata wanda ke cikin
wannan kogon dutse
haka dai mukaci gaba da tafiya a cikin daji mu
kwana nan mu tashi can ba tare da sanin inda muka
dosa ba muna neman inda yake da ni ima mu zauna
muci gaba da rayuwarmu, sai da muka shafe watanni
shida cur muna tafiya sannan muka iso wani daji dake
cikin nan kasarka ta Askandariyya, A nan ne muka zauna
muka ci gaba da rayuwa nida matata zalina inda
muka gina wata yar bukka a gefen wani tsauni
inda muke kwana har ma muka kafa wani garken dabbobin
gida muna kiwo bamu da wata sana a face farauta
kuma mu kan kai fatun dabbobi cikin birnika mu siyar
mu siyo abin da muke bukata da silallan da muka
sayar da fatan dabbobin dajin sannan mu dawo
dajin da muke da zama ba tare da mun taba sha awar
yin rayuwa ba a cikin gari har muka samu rabon
haihuwar Yata SIYAMA
tun siyama tana da shekara biyar a duniya na fara bata
horon yaki har ta cika shekara tara kuma duk irin horon da za a baiwa
babban mutum shi nake bata
hakika siyama tasha bakar wahala sosai a wajen
horon yaki kamar zata rasa ranta kuma sau tari sai
uwarta tayi ta
kuka idan taga tana shan wahalar taji kamar ta
hanani bata horon amma idan ta tuno da irin
kisan gillar da sarki shardas yayiwa kabilarsu da
zuri arsu da tawa sai ta hakura, haka dai siyama taci
gaba da koyon yaki har ya zamana cewa nima
ta fini jarumtaka juriya da naci, a bangaren iya farauta kuwa
ni kaina sai da na cika da mamaki bisa ganin irin
abubuwan al ajabin da take yi a daji da kuma irin
kwarewar da ta samu ta iya harbin kibiya fiye
da mahaifiyarta
bamuyi shawarar sanya siyama a cikin gasar jarumtaka
ba don komai sai saboda mu jarraba karfin
damtsenta da kuma iyakar jarumtakarta kuma
burinmu shine taci gaba da baiwa kanta horo gami da
tanadin daukar fansa akan sarki shardas, ina mai tabbatar
maka da cewa
yanzu haka ko sunan sarki shardas siyama taji
an ambata sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata
kone saboda irin kiyayyar da muka cusa mata
kuma a kullum bata da burin da yafi na mu kyaleta
ta tafi zuwa birnin shardas ita kadai ta shiga har
cikin fadarsa ta kashe shi amma na gaya mata cewa
ba zata taba samun nasara ba a kansa a yanzu face
idan ta mallaki wata Hula da ake kira HULAR LAMSARA
koda Hailur yazo nan a labarinsa sai idanun sarki
hulbasu
suka zazzari ya kamu da tsananin tsoro gami da
mamaki saboda rabonsa da yaji an ambashi sunan
wannan hula ta LAMSARA tun yana yaro karami sai kuma
yanzu da yaji a bakin hailur, tabbas ya sami labarin
hular lamsara a wajan kakansa wato wanda ya haifi ubansa amma bai kara jin
labarinta ba kawo i yanzu
sai da sarki Hulbasu ya baza fatake jarumai da
mayaka izuwa sassan duniya domin su nemo
masa wannan hula ta lamsara amma ba a samu wanda ya jiyo labarin inda
hular take bama
sarki hulbasu yayi gyaran murya sannan ya dubi
hailur a natse yace hakika jikina ya bani cewa lallai
akwai wani babban sirri a tsakanin shardila matar sarki shardas
kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan sarki shardas ya gano cewa kana nan
a raye kuma anan cikin yankin kasata tobama kai ba
ko iyalinka hatta nida kaina bz an zauna lafiya ba
don zai iya zuwa ya yakeni ya kawai da mulkina
koda jin haka sai hailur ya dubi sarki Hulbasu yace
yakai wannan sarki mai Karamci me yasa ka taimakeni
Alhalin ka san cewa yin hakan hadarine ga rayuwarka
da mulkinka
koda jin haka sai sarki hulbasu yayi gyaran murya
gami da ajiyar zuciya sannan yace A rayuwata
babu abinda na tsana sama da zalunci kuma mahaifina
kafin ya gushe ya bar mini wasiyya akan cewa
idan har ina son nayi nisan kwana akan karagar mulina to
dole ne
Na guji aikata zalunci ga talakawa na dama duk
wadanda suke karkashina ko kasa dani kuma na
kwatanta adalci a tsakaninsu gwargwadon iyawata
ina so ka sani cewa har yanzu sarki shardas bai san
komai ba dangane da wanzuwarka ko baiyanarka a cikin aksata kuma
dolene kaci gaba da boye kanka har izuwa lokacin da
zaka iya fuskantarsa, duk da cewa yanzu kaga matarka
shadila da kuma danka yarima Hulkasa
amma dole ne ka hakura da mallakarsu har sai nan
da zuwa lokacin da ya dace, idan ba haka ba kuwa zaka
rasa su ne gaba daya kuma kai kanka ma zaka rasa kanka
ba zan hanaka ka gana da shadila ba amma kada ku
kuskura ku bari wannan yaro hulkas ya san cewa
kaine mahaifinsa kuma kada ku bari ya san duk abinda
ya faru a baya
hakan ba zai haifar muku da komai ba face rugujewar dukkanin burikanmu
gaba daya da kuma salwantar rayukanmu
yayinda sarki Hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin
hailur ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe har hawaye ya zubo masa kuma
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda
fishi
ya dubi sarki hulbasu yace yanzu kana nufin kace dani
inaji ina gani zan hakura da matata wadda aka
rabani da ita a daren angwancinmu da ita na farko kuma na hakura da
dana wanda tun yana ciki bai san cewa nine ubansa ba
gashi har ya cika shekara bakwai a duniya, ka sani cewa har kwnaan gobe zuciyata bata
bayar da soyayyarta ta gaskiya ba ga kowa face shadila
ina son shadila fiye da yadda nake son kaina
Al amin ahmed Misau Nake Shin tayaya kake tunanin
zan
yarda ta sake kubuce min a karo na biyu al halin ban taba
zaton cewa zamu sake hadu wa ba a cikin wannan
duniya
koda hailur ya zo nana a zancensa sai hawaye ya zubowa
sarki Hulbasu al amarin da yai matukar girgiza
hailur kenan kuma yai matukar bashi mamaki
ya dubeshi yace yakai abokina inda dalikin zubar
wannan hawaye naka mai tsada koda jin wannan
tambaya sai sarki hulbasu yaja dogon numfashi
sannan ya sa hannu ya goge hawayansa ya dubi
hailur cikin alamun karayar zuciya yace yakai abokina
kayi mini tambayar da ta fama min tsohon ciwon dake cikin
zuciyata ne kuma shine asalinsanadin da yaja
mummunar kiyayya tsakanina da sarki shardas inaso
ka sani cewa duk irin kiyayyar dakake yiwa sarki
shardas bata kai koda rabin wacce nake yi masa ba
domin duk ladabin da nake yi masa a yanzu na
dole ne saboda yafi karfina kuma bana son abinda zai
taba kasata da jama'ata, ka sani cewa bakincikin
sarki shardas ne ya kashe mahaifina kuma sarki
shardas ne sanadin dana rasa dana na fari YARIMA
HUZEIN
Cikin alamun tsananin mamaki da kaduwa hailur ya
dubi sarki hulbasu yace tayaya mahaifinka da danka
huzein suka gushe
koda jin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa
sarki hulbasu ya dubi hailur cikin nutsuwa yace
yakai abokina ka saurari labarin da zan baka yanzu
dukkanin amsar tambayar da kayi min yanzu tana
cikinsa......
.
JARUMA SIYAMA DA MAHAIFINTA HAILUR SUNA CIKA
BURINSU NA DAUKAR FANSA AKAN SARKI SHARDAS ?.
.
MAI ZAI FARU IDAN SARKI HULBASU YA GAMA BAIWA HAILUR
LABARIN MUTUWAR DANSA DA MAHAIFINSA ?
.
A WANNE HALI SHADILA TAKE CIKI BAYAN TAYI ARBA DA TSOHON MIJINTA HAILUR ?
.
YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAN CEWA HAILUR SHINE
MAHAIFINSA NA GASKIYA
.
Marubucin littafin Wato Abdul aziz sani M/ Gini yace
mu hadu a Littafin Tsatsuba na (6) Don jin
cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari
mai dumbin darasi fadakarwa da nishadantarwa
Mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe.
Suleiman Zidane Kd 09064179602:
0 comments:
Post a Comment