LOKACIN DA SARKI HULBASU YA ZO NAN A ZANCENSA SAI HAILUR YA
jinjina kai gami da yin murmushi sannan ya tattara hankalinsa gaba daya kan sarki hulbasu
yace ina saurarenku yakai abokina , koda jin wannan batu
sai shima sarki Hulbasu ya mayar masa da martanin murmushin
da yayi masa sannan ya fara bashi labarin kamar haka....
''KIMANIN SHEKARU GOMA SHA DAYA DA SUKA SHUDE, Sa adda satki shardas ke nahiyar nan yana cinsu da yaki sai ya zama dodon maza kuma ki gudu sa gudu
domin kuwa duk kasar da ya durfafa sai ya sami nasara akanta, a wannan lokaci mahaifina ne akan karagar mulki ni kuwa nine sarkin yakinsa, kuma nine kadai dansa a duniya kuma nima
dana guda daya ne tal a duniya wato YARIMA HUZEIN
Lokacin da labari ya riski mahaifina cewar sarki shardas yaci kasashe guda ashirin da
daya da yaki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi
da farko yayi shiri ya dauki matakin yin yaki da sarki shardas don har ya bami umarni na tara
gaba dayan mayakanmu mu tanadi abinci da kayan yaki da nufin mu yi riga kafi
wato muje mu tari sarki shardas da yaki tun gabanin yazo ya yakemu amma sai wani tunani ya zo masa ya dakatar da fita
yakin yayi shiri ya tafi izuwa gidan wani mashahurin boka wanda ake kira ZAMARANU IBINI KALBIYA,, boka zamaranu na zaune a cikin wani
daji ne dake gabam iyakar wannan birni namu kuma masana tarihi da bincike sun tabbatar
da cewar boka zamaranu yafi shekara dari zaune a ciki
wannan daji shi kadai, babu wanda yasan abinda yake yi a cikin dajin ko kuma dalilin
zamansa amma dai an tabbatar da cewar da shi da bukkar
da yake zaune a cikinta kwai rana guda aka gansu sun wanzu
ba a san mafarinsu ba,
mahaifina Ya durfafi dajin DANYUL shi kadai kai tsaye ba tare
da fargabar komai ba alhalin tsawon bayyanar boka zamaranu a dajin babu wani
mahaluki daya sake shigarsa walau MUTUM KO ALJAN ba don komai ba kuwa face sai don mugayen bakaken aljanun dake cikinsa, AA Misau Sunana, Komai gawurtar ayari na
fatake basa iya ratsa dajin duk tsautsayin da ya sa suka shiga
kuwa shi ke nan sun bata har abada ba za a sake jin
duriyarsu na
a tsawon shekara dari da baiyanar boka zamaranu a cikin dajin
Danyul fatake ko yan fashi ba sa sake shigarsa ba, don haka
nema ake yiwa dajin lakani da BIRNIN FATALWA, AA Misau Sunana
Duk da sanin tsananin hadarin dake cikin wannan dajin
haka mahaifina ya kunna kai cikinsa, kai da ganin yanayin fuskar mahaifina a lokacin
da yake tafiya bisa dokinsa a cikin dajin ka san cewa babu
batun tsoron mutuwa a ransa, in da ma mutuwar zata zo masa to zai marhaban da ita
ai kuwa tunda ya shigo cikin dajin ya rinka yin arba da wadansu irin mugayen bakaken aljanu
masu tsananin muni da ban tsoro, duk sa adda wadannan mugayen aljanu ska tasamma mahaiina da nufin su dasa masa
wawa sai su ga ko gezau baiyi ba alhalin duk bil adaman da
yayi arba dasu take yake zaucewa ko sumewa hm AA Misau
Sunana, haka dai Aljanin suka yi ta kokarin firgita mahaifina da
razanashi amma ko kadan yaki razana wani lokacin ma sai yayi kamar bai gansu ba ko baijisu ba, sai da ya shafe kwana tara
yana tafiya kuma baya yarda ya yada zango a ko ina ko
barci zaiyi akan dokinsa yake yi, kuma a tsawon kwana taran
baiyi bawali ba ko bayan gida, kuma baya tsayawa da tafiya face idan dokin nasa ya gaji
ya tsaya don kansa yana hutawa, a ranar kwana na tara ne
ya iso kofar bukkar boka zamaranu wacce ke tsakiyar dokar dajin Danyul.
++ ++
ACAN BIRNIN ASKANDARIYYA KUWA, hankalina dana yan majalisar sarki ya dugunzuma ainun, domin mun nemi sarki sama da kasa a cikin birnin nan mun rasa babu wanda ya san cewa ya tafi izuwa dajin Danyul, Ashe cikin tsakiyar dare ya sulale ya fice daga cikin birnin ta hanyar batar da kamanninsa
++ ++
MAHAIFINA NA isa can kofar bukkar boka zamaranu sai yaja linzamin dokinsa ya
tsaya cak ! Kafin ya sauko daga kan dokin nasa ne yaji an
kyalkyale da dariya kuma sai yaji sautin dariyar yana fitowa
daga kowanne bangare wato gabas da yamma, kudu da
arewa
AA misau Sunana sarki ya leka cikin wannan bukka sai yaga wayam babu kowa a ciki
kawai sai yaji an dafa kafadarsa ta baya, a firgice ya juya da
sauri yayi arba da abinda ya dafa kafadarsa boka zamaranu ne!
Boka zamaranu ya kasance dogon mutum kuma siriri mai
kwala kwalan idanuwa kunnuwansa wasu iri ne kamar ba na mutum ba domin a tsaye suke tamkar na zomo
yana da tarin gashin girar ido mai kauri da tsawo kuma yana da dogon hanci tamkar alkalami, Gaba daya gashin kansa gemunsa da sajensa fari ne saboda tsufa
ga masana ilimin karanta shekarun dan adam ta hanyar lura da yanayinsa za su iya bashi
shekaru dari biyu da yaya na haihuwarsa, domin gaba daya fatar jikinsa ma ta yankwane ta bushe kai kace ma ba mutum
bane
Siffofinsa gaba daya sun juye sun zama abin tsoro koda
sarki yayi arba da boka zamaranu sai yaja da baya a tsorace
a karon farko tunda ya shigo cikin dajin Danyul,
koda ganin haka sai boka zamaranu ya sake bushewa da dariya a karo na biyu yace haba yakai sarki mai birnin askandariyya
akan wani dalili
Zakaji tsorona alhalin ka wuce abubuwan tsoro sama da guda dubu a baya wadanda suka fini firgitarwa?
Ka sani cewa kaine kadai mahalukin da ya ratso wannan daji ya iso har nan a raye
tsawon shekara dari da suka gabata kuma kaima din bawai jarumtakarka ko sihirinka bane suka kwaceka ba face
cire tsoron da kayi a cikin ranka AA Misau Sunana
rashin tsoro a cikin zuciyar mutum shine sirrin shigowa cikin
wannan daji na Danyul har mutum ya cimma burin da yake dashi dashi acikin
dajin ba tare da ya hallaka ba, shin zaka iya gaya mini
dalilin da ya saka siyar da ranka ka shigo wannan daji alhalin
ga mutanenka can sunyi shirin yin yaki da sarki shardas ?
Lokacin da boka zamaranu yazo nan a zancensa sai sarki yayi ajiyar zuciya ya kasa cewa
komai domin a sannan ne yaji bawali ya matse shi kuma wata irin azababbiyar yunwa
da kishirwa sun kamashi, AA Misau Sunana Kenan kuma Nine
Jagoran Wannan typing din Littafin Gaba daya, saboda dama tun a kwana na takwas
da tahowarsa dajin danyul guzurinsa ya kare, da yunwa da kishirwa ya kwana
Kwatsam! Sai sarki yaji boka zamaranu ya sake bushewa da dariya sannan yayi nuni da cikin bukkar sa yace da sarki
sauko daga kan dokinka ka shiga cikin bukkata ka kawar
da bukatarka
duk abinda kake so zaka samu a ciki koda jin wannan batu sai sarki ya sauko daga kan
dokin nasa da sauri ya ruga izuwa cikin bukkar AA Misau Sunana
Yana shiga sai kansa ya juye ya firgita ainun domin ba a dakin bukka ya tsinci kansa ba, cikin wata
makekiyar fada ya tsinci kansa wacce ta kawatu ainun fice da tasa
take kofar wani makewayi ta bayyana tare da bude kanta
ba tare da wata fargabar komai ba sarki ya ruga
izuwa ciikinta ya kawar da bukatarsa, yana fitowa daga cikin kewayen kuma saiga Abinci
da abin sha iri-iri akan wani dogon tebur na alfarma
sarki ya karasa kan wannan tebur jikinsa na tsuma zuciyarsa cike da tunani da mamaki
domin sa adda ya shigo fadar babu wannan teburi bare
abincin dake kansa
ba tare da fargabar komai ba mahaifina ya zauna yaci gaba da sha sai da yayi gyatsa mai nuni
da alamar Ya koshi
Al amin Ahmed Misau Sunana, faruwar hakan keda wuya
sai boka zamaranu ya baiyyana tsulum a gabansa
yace yauwa tun da yanzu ka sami nutsuwa saika bani amsar
tambayata ?
Mahaifina yayi gyaran murya yace yakai wannan boka mai
daraja kayi sani cewa ba komai ne ya sa na sai da raina na
shigo cikin wannan daji ba alhalin na san cewa duk wanda
ya shigeshi sai ya mutu face sai domin gudun kada nayi
garaje na zuwa yakar sarki shardas saboda masu iya magana sunce mai laya ya kiyaye
mai zamani
A iya sanina ban taba ganin sarkin da ya yaki kasashe ashirin
da daya ba a wannan nahiya tamu har ya sami nasara a kansu
face sarki shardas
duk da na san cewa a nahiyar nan tamu kaf babu wata kasa
mai yawan dakarun yakina, amma duk da hakan sai da
zuciyata ta buga kuma tsoro ya darsu a cikin raina bisa
al amarin sarki shardas, naji daga bakin bokaye da yawa cewa
kaine kadai zaka iya gaya mini wani abu akan sarki
shardas
bisa wannan daliline yasa nazo gareka domin ka sanar dani
shin idan nayi yaki da sarki shardas zan samu nasara a kansa? Baya ga wannan ina so nayi
maka wata tambaya guda daya ? Tambayar kuwa itace
wai shin menene ya zaunar dakai a cikin wannan daji har tsawon shekaru dari ??
Lokacin da boka zamaranu yaji wadannan tambayoyi sai yayi shiru yana mai sunkui da kansa kasa kamar ba zai ce
komai ba, daga can kuma sai ya dago kansa ya dubi mahaifina cikin nutuwa yace yakai
wannan sarki kayi sani cewa babu wani jarumi ko matsafi
daga jinsin MUTUM KO ALJAN wanda zai iya kashe sarki shardas a yanzu domin kuwa
yana kan sharafinsa ne kuma zamaninsa ne
wow AA Misau Ke magana Babbar Magana Kenan, ina tabbatar maka
da cewa idan har ka ce zaka yakeshi sai gaba dayan dakarunka sun kare, kuma sai
ya shigo har cikin birninka ya yi maka KISAN GILLA idan kana son ka tsira daga sharrinsa
sai dai ka shirya masa kyauta ta dukiya da bayi mai yawa
ka aika masa kuma ka tambayeshi duk abinda yake bukata daga gareka
domin kai da jama arka ku zauna lafiya, dangane da tambayar
dakayi mini kuwa ta karshe amsar tambayar ka itace
yau shekarata dubu biyu ina jiran zuwan ranar da wata
hula zata bayyana wacce ake kira da suna HULAR LAMSARA
Zamana a cikin wannan daji ba na komai bane face na
binciken gano inda hular lamsara take da kuma yadda zan
iya mallakarta amma har yanzu na kasa gano hakan
sa adda boka zamaranu yazo nan a zancensa sai mamaki ya
kara kama mahaifina yace, yakai wannan boka mai
daraja da abin al ajabi an ce shekaranka dari a cikin wannan daji kuma gashi a yanzu da bakinka ka gaya mini cewa yanzu shekararka dubu biyu
kana jiran bayyanar hular lamsara to waishin anya kuwa
kai mutum ne ?
AA Misau Sunana koa a zamanin baya sosai na kakannin
kakanninmu mutane basa yin shekaru dubu biyu a doron kasa, sannan kuma ita wannan
hula ta lamsara yaushe ne za ta bayyana kuma me kake so
kayi da ita da har ka shafe shekaru dari a cikin wannan
daji saboda ita?
Koda jin wannan tambayoyi sai boka zamaranu ya bushe da dariya mai karfi har
Dariyar ta kama amsa kuwwa ta cika fadar gaba daya, mahaifina
yaji kamar
kunnuwansa zasu dode ba shiri ya sa hannayansa ya toshe
kunnuwan nasa har sai da ya daina dariyar sannan ya dago ya kalleshi, boka zamaranu
ya mike tsaye yayi tafiyar taku biyar sannan ya juyo ya fuskanci sarki yace ni
mutum ne kamar kai ba aljan ba amma na fito daga cikin
mutanen da suka fi kowanne kabila dadewa a duniya
domin a yanzu haka da kake ganina shekarun haihuwata sun kai dubu biyu da dari hudu da arba'in, nine kadai mutum
da ya rage a duniya daga cikin jinsinmu kuma nine
kadai na san sirrin kayan yakin MAZAN JIYA guda hudu makaman yakin da babu kamarsu
a duk fadin wannan duniyar gaba daya, idan na mallaki
hular lamsara sai na mallaki duniyar nan gaba dayanta, kuma a sannan ne kadai zan iya
yin aure har na haifi irina wanda a gaba zaiyi shekara dubu takwas yana mulkin duniya
Jikana kuma zai karbi karagar a hannunsa ya ninka shekarunsa
haka dai zuri ata zata ci gaba da mulkin duniya har abada
ba zan taba cika wannan burin nawa ba face na mallaki
hular lamsara
yakai wannan sarki kayi sani cewa babu wanda zai iya hallaka
sarki shardas face wanda ya fara mallakar wannan hular ta lamsara
A A Misau Sunana Kenan,
da wannan furuci nake yi maka bankwana kuma ina mai shawartarka daka gaggauta barin dajin nan ka koma izuwa
ga kasarka domin idan ka kara dakika arba in anan zaka
iya rasa rayuwarka
duk amsar da baka ji ba daga tambayoyinka ba zan iya sanar dakai bane
gama fadin hakan keda wuya sai boka zamaranu ya bace
bat
tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen, koda ganin haka
sai mahaifina ya mike zumbur ya fice da gudu daga
cikin fadar sai gashi ya bayyana a gaban wannan bukka
a dimauce ya karasa inda dokinsa yake ya daka tsalle ya haye kansa sannan ya
sakar masa linzami ya kama gudu ba sassauci
sai da mahaifina ya sake shafe kwana tara yana tafiya sannan ya dawo gida, yana isowa ya bayar da umarnin a janye
batun yaki
nan take aka sallami kowa mayakan suka koma izuwa ga gidajensu tare da kwance damarar yakin da suka daura suna cike da dumbin mamakin
dalilin da ya sa aka fasa zuwa yakin, kashe gari kuwa, da
sassafe sarki ya tashi ayari na dakaru dubu uku dauke da bayi dubu ashirin da kuma dukiya mai dumbin yawa
ta dinare, lu'u lu'u da murjani cikin akwati dubu suka tafi
izuwa ga birnin sarki shardas da kuma wasika, lokacin
da wannan ayari suka riski sarki shardas yaga dukiyar da
mahaifina ya aiko masa kuma ya karanta wasikarsa wacce ke nuna mubaya a gami da neman
zaman lafiya sai ya bushe da dariyar mugunta sannan yace'
tabbas na cika zaki uban dawa a wannan nahiya kuma dole
ne sarakuna su durkusa a gabana su nemi tsira da jaddada muba ya arsu gareni
nan take sarki shardas ya sa aka rubuto amsar wasikar mahaifina aka maido masa da
ita
bayanin dake cikin wasikar shine kamar haka...........
Danjin wani bayani ne sarki shardas ya aiko sai ku tarbeni a Post na gobe ehem Dafatan wannan labarin yana kayatar daku Idan hakane kawai ku sauke mun comments dinku
gami da likes
kafinnan Nidinne Dai
Al Amin Ahmed Misau
AA Misau Ke Magana
Daga Zauran Labarai Fb.
[4/15, 9:40 AM] quчrαєmєч 🏠: TSATSUBA
Littafi Na Shida (6)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
NAN TAKE SARKI SHARDAS YA SA AKA RUBUTO AMSAR WASIKAR
MAHAIFINA AKA MAIDO MASA DA ITA, BAYANIN DAKE CIKIN WASIKAR SHINE...
Yakai mai birnin askandariyya kayi sani cewa sakonka
na bayi da dukiya ya riskemu, kuma mun gode da wannan karramawa da kayi
mana gami da mubaya'a, amma ka sani cewa ba mu karbi
mubaya'arka ba har saika zo da kanka fadata ka zube
kasa a gabana ka kwashi gaisuwa sannan zamu aminta
da mubaya'arka a garemu, sharadi na biyu kuma shine dole
ne duk shekara ka rinka kawo mini irin wannan kyauta daka
kawo mini ta bayi dubu ashirin da dukiya akwati dubu
sharadi na uku shine dolene ka baiwa wakilina matsayi
da mazauni a kasarka domin su dinga kawo mini rahoto duk abin dake gudana
a cikin birninka da kauyukan kasarka, sako daga sarki mai cikakken iko kuma
sarki dodon maza gallabar sarakuna sarki shardas
** **
Lokacin da wannan wasika ta riski mahaifina aka karanta a
tsakiyar fada sai hankalin kowa ya dugunzuma ni kuwa sai
raina ya baci jikina ya kama tsuma, cikin tsananin fishi na mike tsaye ina mai zare takobina
na dubi sarki nace yakai abbana kayi sani cewa idan muka bi
wannan sharadi na sarki tamkar mun zamo bayin sane
domin zamu rike masa saniyar tatsa ne ya rinka tatsar
nononta
AA Misau Sunana zamu zamo bamu da wani sirri na
kanmu a cikin kasarmu kuma tattalin arzikin mu zai raunana mutanenmu zasu iya fuskantar fatara da talauci
kafin na gama rufe bakina tuni sarki ya daka min tsawa
yana mai tarar numfashina ya ce, idan muka ki bin umarnin sarki shardas sai ya kashe
kowa a kasar nan ya mallake komai namu idan mukace
zamu yakeshi komai yawan nan namu sai ya karar damu
saboda yana kan sharafinsa abin da boka zamaranu ya
gaya mini kenan
A matsayinka na dana kuma yarima mai jiran gado ya kamata ka zamo mai kishin
kasarka da jama arka, abinda sarki shardas ke bukata kawai
shine na kaskanta kaina a gareshi kuma mu bashi dukiya
kada ka dubi matsayina da kimata a wannan nahiya, zan iya
sallama rayuwata ma gaba daya don kare jama ata da
kasata dukiya kuwa shirme ce idan ka rasata zaka iya samun wata, ina mai dada ja
maka kunne babu batun yaki tsakaninmu da sarki shardas kuma kada ka kuskura
ka yi wani abu wanda zai jefa kasarmu ko jama armu cikin hadari
ina mai umartarka da ma za kaje kasa a shirya mana tafiya
gobe gobe zamu durfafi birnin sarki shardas don amsa kiransa, kuma dakarun da zasu yi mana rakiya kada su wuce su
dari biyu don samun kariyar hanya daga sharrin
yan fashi da dabbobin daji, koda gama fadin hakan sai sarki
ya mike tsaye daga kan karagar mulkinsa ya shige cikin
gidan sarautarsa, ni kuwa sai bakin ciki ya lullube ni
na sunkui da kaina kasa a lokacin da idanuna suka ciko da kwallar takaici
a wannan lokaci ne fadar ta watse kowa ya kama gabansa
aka barni ni kadai a zaune babban abin da ya kona zuciyata shine idan na tuna cewa
mahaifina zaije gaban sarki shardas ya durkusa masa alhali a nahiyar mu gaba daya
babu wata masarauta mai tsohon tarihi da daukaka sama
da tamu
AA Misau Ke Magana, idan har sarki ya durkusawa sarki shardas shikenan darajarsa da kwarjininsa a idanun
jama a sun zube har abada kuma ba za su kara dawowa ba
ina zaune cikin wannan halina bakin ciki dana yarima
huzein ya zo gareni ya dafa kafadata koda na dago kai nayi arba dashi sai naga
shima yana zubar da hawaye, cikin sanyin murya huzein ya dubeni yace yakai abbana
ka zamo mai hakuri da juriya bisa wannan kaddara data same mu
ina so ka sani cewa komai nisan jifa kasa zai fado
don haka komai dadewa akwai ranar da sarki shardas zai fadi
duk wulakancin da zamu fuskanta daga gareshi yanzu
yana da iyaka wataran sai labari, ina mai tabbatar maka da cewa
idan sarki shardas ya kuntata mana a yanzu da zamaninka to nan gaba namu zamanin
sai komai ya sauya
sa adda huzein yazo nan a zancensa sai na cika da mamaki bisa dalilin yin
wannan jawabi tamkar wanda ya jiyo wani abu daga
wajen bokaye
nan take na rungume huzein iana kuka nace yakai dana
zan kasance mai fatan ganin ranar da sarki shardas zai fadi
kafin mutuwata
koda jin wannan batu sai huzein ya janye jikinsa daga cikin
nawa ya dubeni cikin murna da murmushi yace yakai abbana ina neman alfarma guda daya a wajenka
cikin mamaki na dubeshi nace yakai dana kai kuwa wacce
irin alfarma kake nema a wajena ? Huzein yace ina son kuyi
wannan tafiya tare dani gobe zuwa birnin sarki shardas
koda jin haka sai idanuna suka zazzaro na dubeshi cikin alamun damuwa nace
haba yakai dana ka tuna cewa idan sarki baya nan
nima bana nan kuma babu kai babu wanda zai gajemu kenan
koda tsautsayi yasa mun hallaka
wannan tafiya da zamuyi mai hadari ce komai zai iya faruwa
a garemu ko akan hanya
ko kuma a can birnin sarki shardas, bugu da kari a halin yanzu mahaifiyarka na dauke da tsohon juna biyu haihuwarta yau ko gobe idan babu ni
babu kai a kusa da ita wa zata kalla taji dadi?
AA Misau Ke Magana sa adda yarima huzin yaji wannan batu nawa sai jikinsa yayi sanyi
amma duk da haka sai yaci gaba da rokona akan na
Rarrashi sarki ya amince ayi wannan tafiya tare dashi, muna cikin wannan hali ne muka ji takun sawu a bayanmu
cikin sauri muka waiga mukayi arba dashi, ba wani bane
face mahaifina fuskarsa cike da annuri kawai sai ya karaso
garemu ya zauna a tsakiyarmu sarki ya dubeni sannan ya
dubi yarima huzein yayi murmushi yace naji duk abinda kuka tattauna, kuma na amince zamu tafi tare dakai
gobe
koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube yarima huzein ya
rungume sarki yana mai sumbatar goshinsa kawai sai sarki ya janye jikinsa daga cikin
na huzein ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa kamar
zaiyi kuka yace yakai jikana kayi sani cewa na amince muyi
wannan tafiya tare dakai ne saboda dalili daya rak
dalilin kuwa shine nima sa adda na taso a wannan gidan
sarauta daga san da aka haifeni zuwa lokacin dana kai
shekarunka wato shekaru bakwai a duniya sau daya rak aka
taba barina na fita wajen birnin na, bai kamata ace yarima guda wanda zai mulki al umma da yawa ba ya kasance
kifin rijiya
yana da kyau ka shiga duniya kaga yadda talakawa
ke rayuwa kuma kayi gwagwarmaya kasha wahala sosai domin ka san menene rayuwa amma ka sani cewa akwai sharadi guda uku a
kanka daga ranar da muka fita daga cikin garin nan,
sharadina farko shine ba ka da ikon zuwa ko ina walau
a cikin daji ko a cikin gari face da izinina ko na mahaifina sharadi na biyu shine duk abinda zakayi
saika shawarcemu sharadi na
uku kuwa shine ba zaka ci ko ka sha wani abu ba
face wanda muka baka da hannunmu,
shin ka amince da wannan sharadai guda uku
dajin wannan tambaya sai yarima huzein yayi murmushi kuma
ya zube kasa a gaban sarki ya kama godiya cikin farin ciki tare da tabbatar da amincewarsa
ga wadannan sharudda
Kashe gari kuwa da sassafe aka yi shirin tafiya dakaru dari
biyu ne suka yi mana rakiya dauke da isashshen guzuri sai kuma
kuyangi goma wadanda za su rinka yi mana hidima
tsakanin yan fashi da mugayen dabbobin daji sai da
mukayi karo da rukuni rukuni har guda bakwai kafin mu
isa birnin sarki shardas amma sai da muka tarwatsa su muka kashe na kashewa masu gudu
suka tsere dakaru guda arba in kacal muka rasa a cikin
wannan gumurzu AA Misau Ke Magana, da la asar sakaliya muka iso birnin sarki shardas
koda muka tsaya a bakin kofar gidan sarautar akaje akayi
mana iso sai sarki shardas yaki fitowa saboda jin izzarsa da takamarsa kawai sai ya turo wani hadiminsa aka kaimu
masauki
bayan mun zauna munci abinci muna hutawa sai tunanin
gida ya fado min inda na tuno lokacin da muke yin bankwana
da matata luzuraina wacce ke dauke da tsohon juna biyu hm Kunya AA Misau, sa dda ta rungumeni mu biyu ni da yarima huzein ta fashe da kuka
tana mai cewa
yakai mijina kayi sani cewa bana son wannan tafiya da zakuyi
domin ina bukatarku a kusa dani a yanzu fiye da ko
yaushe ba don komai ba sai don saboda ita haihuwa bata da
tabbas
zan iya rasa rayuwata a wannan tafarki ko kuma na rasa abinda na
ke dauke dashi
haka zan iya rasaku tunda kuma tafiya zakuyi mai hadari
tun a jiya da sarki ya shirya wannan tafiya sai naji zuciyata ta kama bugawa
yadda naga rana haka naga dare ina mai tabbatar muku da cewa ba zan taba samun sukuni da kwanciyar
hankali ba face naga dawowarku lafiya, koda luzuraina ta zo
nan a zancenta sai ni da huzein muka kamu da tsananin tausayinta muka kara kankameta a jikinmu mukaci gaba da
kuka kamar ba zamu daina ba, daga can sai na janye jikina daga cikin nasu na dubi luzuraina cikin nutsuwa da murmushin
karfin hali nace yake matata kiyi sani cewa bana son nayi
wannan tafiya saboda rashin sanin halin da zaki iya shiga amma kuma idan har na bar sarki yayi wannan tafiya shi
kadai zan shiga cikin tashin hankali da wasi wasi akan halin da shima zai iya shiga don
haka dole ne na bishi ko don na bashi kariya
ina son ki kwantar da hankalinki ki sani cewa nayi miki
alkawari duk wuya duk tsananin sai na dawo gareki a raye
kuma na dawo miki da yarima huzein cikin koshin lafiya
gama fadin hakan keda wuya sai ga babban hadimina ya shigo cikin falon nawa ya risina
gareni yace
ya shugabana sarki ya fto ku kadai ake jira
koda jin haka sai ni da yarima huzein muka mike tsaye da
sauri muka nufi kofar fita, a guje luzuraina ta sha gabanmu
tana kuka ta sake rungumemu sannan ta janye
jikinta ta dubeni tace idan na haihu baka nan wanne suna za a sakawa abinda
na haifa
ka sani cewa yarima huzein zai samu kani koda jin wannan batu sai mamaki ya kamani na dubeta
nace yaya aka yi kika san cewa da namiji zaki haifa
luzuraina ta ce sau uku ina yin mafarkin na haifi da
namiji don haka ina ji a jikina cewar lallai da namiji zan haifa
sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi sannan na dubi
yarima huzein na ce na baka dama ka zabi sunan da za a sawa kaninka yayin da yazo duniya
cikin murna yarima huzein ya daga kansa sama yayi dan tunani sannan ya dubi mahaifiyata
yace
ki sawa kanina suna YARIMA BASMAR, kuma kiyi masa bushara da cewa ya jira yayansa yazo suyi was
Lallai nine zan koya masa yadda ake sarrafa doki da takobi
koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa luzuraina ta
sake rungume yarima huzein tana mai sake fashewa da
wani sabon kukan
A dai dai wannan lokaci ne muka jiyo muryar sarki yana mai
kwala mana kira cikin hanzari na fisge yarima huzein daga
cikin luzuraina na ja shi da gudu muka fice daga cikin falon
huzein na waigen mahaifiyasa yana hawaye itama tana
kuka
lokacin da na zo dai dai nan a tunanina sai yarima huzein ya dafa kafadata na
dawo cikin hayyacina
yarima huzein ya dubeni cikin alamun damuwa yace yakai abbana anya kuwa babu
wani mugun nufi a zuciyar sarki shardas a kanmu ? Yakamata ace ya fito ya tarbemu a bisa irin
matsayin mahaifinka da daukakarsa a wannan nahiya amma kuma sai kawai ya aiko da hadimi aka taho damu nan
masauki
sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi nace kada ka damu ya kai dana
duk wannan ba komai bane, babu wani mugun abu da sarki
shardas zai yi mana, kawai dai wulakanci ne irin nasa
da son nuna isa, A A Misau Ke Magana, koma menene ai da zarar mun isa gabansa za a yita
ta kare yaz sallame mu mu koma izuwa kasarmu
burina kawai shine mu koma gida mu iske mahaifiyarka
ta haihu lafiya
kafin na rufe bakina saiga sarki ya shigo cikin dakin namu
kuyanginsa guda hudu na biye dashi dauke da abinci
cikin hanzari muka zube kasa muka kwashi gaisuwa
su kuwa wadannan kuyangi sai suka ajiye wannan abincin
da abinshan a gabanmu suka juya da baya suka fice
sarki ya zauna a gabanmu ya dubemu cikin annashuwa yace na kasa cin abincina
shi yasa na yanke shawarar na zo har nan dominku muci tare
koda jin wannan batu sai mamaki ya kamamu
na dubi sarki nace yakai abbana kai kuwa menene dalilin
daya hanaka cin abinci ? Sarki ya yi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kasa sannan yace
tun da muka shigo cikin garin na naji zuciyata tana bugawa
abu ne mawuyaci mu bar garin nan lafiya cikin farin ciki
musamman idan muka yi duba da irin karbar da sarki
shardas mana ta wulakanci da rashin nuna muhimmancina a gareshi
ya yinda sarki yazo nan a zancensa sai nayi dariya nace haba yakai abbana
akan wane dalili zakayi irin wannan tunanin alhali mun kasance masu biyayya ga sarki shardas gami da bin
umarninsa, ni na san cewa babu wani tsautsayi da zai same
mu lafiya kalau zamu koma gida
kawai mu jira muga yadda
zata kasance tsakaninmu da sarki shardas
koda jin wannan batu sai sarki ya saki ransa hankalinsa ya
kwanta nan take muka kama cin abinci cikin raha da nishadi
muna ta hira da ban dariya har sai da muka koshi......
Wow littafi fa yanzu ya fara tafiya domin yanzu ne zaku san
an fara karanta TSATSUBA zakuji yadda zata kaya tsakaninsu
da yadda Ake tsantsan yaudara da cin amana gami da rashin
imani
Kafinnan dai Nidinne
Al amin Ahmed Misau
AA Misau Ke Magana
Admin Na Zauran Labarai
Page.
Ke cewa Ku huta Lafiya...
[4/15, 9:41 AM] quчrαєmєч 🏠: TSATSUBA
Littafi Na Shida (6)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
NAN TAKE MUKA KAMA CIN ABINCI CIKIN RAHA DA NISHADI
MUNA TA HIRA DA BAN DARIYA HAR SAI DA MUKA KOSHI,
A wannan rana sarki bai koma dakinsa ba anan dakinmu
ya kwana saboda ko kadan baya son nisanta damu
sai da muka kwana uku a cikin gidan sarautar sarki shardas
amma wai har tsawon
wadannan kwanaki sarki shardas bai kirawo mu ba duk da
cewa kullum yana zama a fada, duk sa adda ya bukaci
ya gana da shi sai yace a gaya masa cewa ya kara sauraro
KAJI MANYA MASU JI DA KAI SARKI SHARDAS KENAN HM
a ranar kwana na ukun ne da safe bayan mun gama kalaci sai
ga hadimin sarki shardas yazo mana take hadimin ya shaidawa mahaifina cewar sarki yace muje mu riskeshi a fada
cikin farinciki muka mike tsaye muka yi shiri sarki ya
taramu gaba dayanmu dakarunsa da kuyanginsa sannan aka
debo wadannan bayi guda dubu ashirin gami da akwatunan
dukiya guda dubu muka wuce izuwa fadar sarki shardas
fadar ta cika makil ta batse da mutane ko ina ka duba saikaga fadawa dakaru
da manyan attajirai da sauran masu fada aji a kasar
A gefe daya kuma mutanen gari ne maza da mata a durkushe
a kas babu wani mutum guda daya a tsaye ko akan kujera face sarki shardas wanda ke kan
karagarsa ta mulki, koda muka shigo cikin fadar mahaifina na kan gaba muna biye dashi
gaba dayanmu sai naga an zubawa mahaifina idanu kawai mutane so suke su gani shin zai iya durkusawa a gaban sarki
shardas ya kaskantar da kansa? Babu abin takaici sama da
ganin yadda mahaifina yayi gagarumar shiga ta alfarma mai tsananin tsada wacce ta
ninka ta jikin sarki shardas sau uku amma kuma gashi
zai kaskanta a gaban dubunnan talakawa
a wannan lokaci ina rike da hannun yarima huzein muma munci ado na kwatance
domin ko a cikin fadawan sarki shardas da duk jama arsa babu wanda ya sa suturar data kai tamu daraja
ni da huzein ke bin bayan sarki sai kuma kuyangi da sauran
dakarun da muka taho dasu daga birninmu don yi mana rakiya lokacin da ya rage
saura baifi taku goma ba tsakanin mahaifina da karagar mulkin
da sarki shardas ke zaune a kai sai yaja da baya cak
muma da muke bayansa sai dukkanmu muka ja muka tsaya cak a bayansa
nan take mahaifina da sarki shardas suka fara kallon kallo fuskar sarki shardas
a murtuke take ko kadan babu annuri kuma jikinsa ya kama tsuma har fuskar tasa na yin gatsine saboda fishi bisa tunanin cewa ko mahaifina
ba zai durkusa masa ba kawai sai akaga mahaifina ya durkushe
kasa bisa guiwarsa guda ya risina yana mai dukar da kansa
ga sarki shardas cikin murya mai dauke da ladabi yace
gaisuwa gareka ya shubana a madadina da al umar kasata nazo domin mu jaddaja mubaya armu a gareka ya sarkin duniya
kuma na amsa kiranka, gani nazo da duk abinda ka bukata
koda mahaifina yazo nan a zancensa sai fuskar sarki shardas ta fadada da murmushi
ya mike tsaye daga kan karagarsa ta mulki cikin matukar murna sannan ya tako yazo har inda mahaifina ke durkushe
ya kama kafaduna ya tashe shi tsaye suka fuskanci
juna yace lale marhaban da sarki mai birnin Askandariyya
lallai ka tsira daga dukkan fishinmu kuma daga yau ka zama amintaccenmu
nan take fadar ta rude da shewa aka kama yiwa sarki
shardas jinjina da kirari bisa ganin yadda sarki mai daraja da cikakken iko kamar mahaifina
ya mika wuya a gareshi
a wannan lokaci takaicida bakinciki suka lullubeni har idanuna suka ciko da kwallah
ban sani ba
A A Misau Sunana , sarki shardas ya daga hannu sama sai
fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta , A sannan ne sarki shardas ya bushe da dariyar
farinciki ya kirawo wani hadimi nasa mai dauke da tambulan na ruwan giya gami da
kofi guda biyu
da zuwan hadimin sai sarki shardas ya dauki kofi guda hadimin ya tsiyaya masa ruwan giyar sannan ya dubi
mahaifina yayi masa tayi, batare da fargabar komai ba
mahaifina ya dauki daya kofin shima aka tsiyaya masa ruwan
giyar amma sai yaki yasha
koda ganin haka sai sarki shardas ya bushe da dariya
sannan ya kurbi ruwan giyar har sau biyu ya dubi mahaifina yace kwantar da hankalinka
abokina ai ba zan shayar dakai guba ba, saboda me kake tsoron shan wannan giya mai
albarka wacce nasa aka yi ta musamma don tarbarka?
Koda jin wannan batu sai mahaifina yayi murmushi yace ai ba komai bane yasa naki sha ba
sai don yin ladabi a gareka
kada na rigaka dandana dadinta
dajin haka sai sarki shardas
ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya kamo
kafadar mahaifina ya juyo dashi suka fuskancemu
sarki shardas ya dubeni sannan ya dubi yarima huzein yace wannan danka ne yarima hulbasu mai
jiran gado tare da dansa yarima huzein ko ?
Mahaifina ya gyada kai yace kwarai kuwa sune sannan ya dubemu yace kuyi gaisuwa ga
sarkin duniya
AA Misau Sunana, da farko sai na dan noke a lokacin da
huzein tuni ya duka kasa ai kuwa sai nan da nan
fuskar sarki shardas ta juye izuwa fishi har sai da nima na durkusa na gaisheshi sannan
yayi murmushi yazo ya dafani ta yadda har muna iya jin
numfashin juna ya budi baki cikin karamar murya yadda babu
mai iya jinmu ba sannan yace,
Samari nasan abinda kake ji a ranka bisa kaskantar da
kan da mahaifinka yayi a gareni domin jaddada min mubaya arsa amma ina mai
shawartarka da ka zamo mai biyayya idan har baka
son daular birnin Askandariyya ta fadi, yana gama fadin
hakan sai ya wuce gabana ya shiga duba bayin da aka kawo masa guda dubu
ashirin har sai da ya tabbatar da cewa gaba dayansu lafiyayyune
sannan yaje kan akwatunan dukiya guda dubu
sai da aka bude gaba dayan akwatunan yaga dukiyar dake cikinta
nan take sarki shardas ya sake bushewa da dariyar farin ciki sannan ya dawo
wajen mahaifina ya kama hannunsa ya jashi har
zuwa kan karagar mulkinsa suka zauna tare
a wannan lokaci fadar tayi tsit ko tsinke ne ya fadi kasa
sai an ji kararsa
sarki shardas ya dubi mahaifina cikin nutsuwa ya ce ya
batun sharadin da muka gindaya maka a cikin wasikarmu?
Shin ka amince zaka yi abinda muke so ko kuwa ba zaka bi ba ? Sa adda mahaifina
yaji wannan tambaya sai ya risina cikin biyayya yace
ya sarkin duniya na amince da duk bukatarka amma
ina neman wata alfarma guda daya, alfarmar kuwa
itace ina son ka rage yawan bayin da zan rinka kawo
maka duk shekara da kuma yawan akwatunan dukiya su koma rabin wadanda na kawo maka yanzu
ba don komai ba sai saboda hakan zai iya kawo karyewar tattalin arzikin kasata
domin a halin yanzu bayi sunyi karanci a kasata
kuma bayin nan sune suke yi mana aikin noma a gonakinmu
noman kuma shine yake kawo mana dukiyar da zamu tara mu kawo maka
koda jin wannan batu sai sarki shardas ya fusata ya dakawa
mahaifina tsawa yace babu ruwanmu da wannan matsala domin kai ta shafa bamu
ba
don haka sai ka san hanyar da zaka bi ka nemi bayi koda
kuwa sai kayi farautarsu ne a sauran kasashen da ke kusa daku
ka sani cewa gobe goben nan zan hadaka da wakilina
mutum uku wadanda zaka tafi dasu izuwa fadarka a dinga
gabatar da harkokin mulki tare da su domin su rinka kawo mini
rahoton duk abubuwan dake gudana, a karshe ina mai gargadinka da cewa digon jini daya na wadannan
wakilai nawa dai dai yake da digon jinin saba in na jama arka don haka a kula da su da kyau kuma a basu
duk abinda suke bukata
sa adda sarki shardas yazo nan a zancensa sai nayi wuf
na matso gaba kusa da karagar mulkin sa na dubeshi nace yakai wannan sarki
ka yi sani cewa idan ka hadamu da wadannan wakilai naka
tamkar ka rushe karfin mulkin mahaifina ne gaba daya
tunda ba shi da ikon yin wani sirri a cikin harkokinsa na mulki kuma ba shi da ikon zartar da komai sai da saninka da amincewarka
ni ina ganin A A Misau Ke magana, wannan ba adalci bane
zalunci ne da kaskantarwa....... Kafin na gama wannan jawabi tuni jikin sarki shardas
ya kama tsuma saboda fishi har gumi ya fara tsatstsafowa daga fuskarsa
shi kuwa mahaifina a wannan lokaci ya firhita ainun
so yake ya hanani ci gaba da magana amma ya kasa, kawai sai sarki shardas ya mike tsaye
zumbur
daga kan karagarsa ya zo daf dani ya zare takobinsa ya dora kaifinta akan wuyana
yana mai ci gaba da tsuma ni kuwa ko gezau ban yi ba
A lokacin gaba dayan mutanen dake fadar sun firgita ainun
kowa ka kalla sai kaga jikinsa na bari don gudun kada
laifin wani ya shafeshi, sarki shardas ya daka min tsawa ya ce kai dan samari kaine
mahaluki na farko wanda ya taba shigowa har cikin fadata
yayi mini bakar, don haka yanzu zan kasheka domin na gusar da kishirwar
karya wannan lago nawa da kayi, koda gama fadin hakan sai
sarki shardas ya daga takobinsa sama da nufin ya
sareni amma sai mahaifina yayi wuf ya janyeni daga gabansa sannan yayi sujjada a
gareshi ya dago kai yace ya sarkin duniya ina nemawa dana
afuwa
ka san cewa har yanzu akwai kuriciya a tare da shi
koda jin wannan batu sai sarki shardas ya sake
bushewa da dariyar mugunta sannan ya mayar da takobinsa cikin kufe ya dafa
kafadata yace samari ka tsira daga kaifin takobina yau, amma ka
sani cewa idan ka sake aikata kuskure irin wannan ba zaka taba tsira ba
yana gama fadin hakan sai ya juya ya fuskanci fadawansa ya kirawo wadansu mutane uku
daga cikin dan uwansa wanda ake kira MUHAIRU wanda ya
kasance dan yayarsa
sarki shardas ya dubi muhairu ya ce yakai dan uwana
daga yau na cireka daga matsayin gwamnan birnin DAILUFA
a yanzu kaine shugaban wakilaina na birnin Askandariyya saboda haka kaje ka fara shirin binsu gobe
amma kafin goben ina so ka zauna da yarima hulbasu
ya sanar dakai iya adadin biranensu da kauyukansu da kuma duk harajin da suke
tarawa a kowacce shekara ka rubuta komai ka kawo min
muhairu ya risina yace an gama ya shugabana
kawai sai sarki shardas ya juya ya fice daga fadar ya wuce
izuwa cikin gidan sarautarsa, shi kuwa muhairu sai ya zo
gabana ya tsaya yana mana wani irin murmushi na mugunta
da raini ya dubeni yace ka saurari zuwana nan da lokaci
kankani
yana gama fadin hakan sai ya kyalkyale da dariyar mugunta ya wuce abunsa
sauran wakilai guda biyu na take masa baya suma suna
kyalkyala mana dariya
Nan take dakarun sarki shardas suka ingiza keyar bayin da
muka kawo guda dubu ashirin aka wuce dasu izuwa can wani
bangare na gidan sarautar sarki shardas, kuma aka kwashe
Wadannan akwatunan dukiyar da muka kawo , A sannan ne fadar
ta watse ya zamana cewa daga mu sai jama armu kacal a tsaye cikin tsananin bakin ciki
da takaici
A dai dai wannan lokaci ne zuciyata ta kama tafarfasa
kamar zata kone ban san sa adda na kurma uban ihu ba
mai tsananin firgitarwa na durkushe kasa ina mai fashewa da matsanancin kukan bakin
ciki
Al amarin daya janyo hankalin dakarun sarki shardas kenan
suka zare takubba suka rugo izuwa kanmu, koda suka ganni durkushe a kasa ina
kuka sai suka kama dariya suka tafi suka barni
a wannan lokaci ne mahaifina da yarima huzein suka durkusa a gabana sa adda
suma suka fara zubar da hawayen bakinciki
kawai sai sarki ya rungumeni tare da fashewa da kuka sosai
mu duka sai muka kama kukan, sai da muka dan jima zaune a cikin fadar muna kuka sannan muka mike tsaye muka tafi izuwa masaukinmu.......
.
Wow Zan dakata A wannan guri saikuma Allah ya kaimu Gobe
zan cigaba daga nan
Amma kafinnan Nidinne Dai
Al amin Ahmed Misau
AA Misau Ke Magana
Admin Na zauran labarai
page.
[4/15, 9:41 AM] quчrαєmєч 🏠: TSATSUBA
Littafi Na Shida (6)
Part D.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
SAI DA MUKA DAN JIMA ZAUNE A CIKIN FADAR MUNA KUKA SANNAN MUKA MIKE
TSAYE MUKA TAFI IZUWA MASAUKINMU....
Bayan mun isa masaukinmu mun zauna cikin bakinciki
muna tunanin wannan hali da muka tsinci kanmu a ciki
na takaici da wulakanci, sai sarki ya dubeni a lokacin da
hawaye ya zubo masa yace yakai dana ka yi sani cewa
wadannan sharadai da sarki ya gindaya mana sai sun janyo
fari da talauci a kasarmu kuma wannan shine lokacin da
na dade ina tsoron gani a rayuwata
fadin hakan keda wuya sai sarki ya fara wani irin tari mai
karfi kafin a jima kuwa sai ya kama aman jini
cikin rudewa na kwallah ihu ina mai kiran likitan sarkiwanda
muka taho tare
dashi tun daga birninmu domin duba lafiyarmu, nan
da nan wata kuyanga ta ruga taje ta kirawo likitan yazo ya shiga duba mahaifina
dan ceto rayuwarsa
da kyar likitan ya samu ya shawo kan cutar sarki ya
tsayar da jinin dake zuba a bakinsa sannan kuma ya bashi magani ya sha
faruwar hakan keda wuya cikin dakika kadan nannauyan
barci mai karfi ya sace sarki
a wannan lokaci ne ni da huzein muka dawo cikin hayyacinmu
na dubi likitan sarki cikin alamun mamaki nace
yakai likita wannan wane irin ciwo ne ya sami mahaifina alhalin ina tare dashi
tsawon shekaru amma ban taba ganinsa a cikin irin wannan
hali ba sai yau
koda jin wannan batu sai likitan ya sunkui da kansa kasa
yayi shiru kamar ba zaice komai ba har sai da na daka masa
tsawa sannan ya dago kai ya dubeni a tsorace bakinsa na rawa yace ka gafarceni ya
shugabana ka sani cewa sarki ya haneni da na sanar da kai komai dangane da
rashin lafiyarsa, sa add anaji wannan batu sai na sake fusata na zare takobina na
dora kaifinta akan wuyan likitan nace na rantse da
darajar sarki idan baka sanar dani wannan al amari ba yanzun zan kashe ka
koda jin haka sai jikin likitan ya kama tsuma ya budi b baki
cikin in ina ya ce tun ranar da wasikar sarki shardas
ta iso birninmu na askandariyya fadar mahaifinka yaji sakon
da ta kunsa a lokacin ya kamu da ciwon zuciya ina mai sanar dakai cewa
wannan ciwo yana da tsananin hadari domin zai iya zama
sanadin ajalinsa a ko yaushe cikin kankanin lokaci muddin zai rinka fuskantar abinda zai bata masa rai koda likita
yazo nan a zancensa sai na durkusa kasa na fashe
da matsanancin kuka
al amarin da ya karya zuciyar yarima huzein kenan, shima
ya fashe da kuka AA Misau Ke Magana
nan take naji na tsani sarki shardas fiye da komai
a duniya kuma na kudurce a raina cewar in dai wannan ciwo
ya zamo sanadin ajalin mahaifina sai na yaki sarki shardas gaba
da gaba duk da na san cewa hallaka zanyi
muna cikin wannan haline muka ji an kwankwasa mana kofa
sai ga wakilin sarki shardas kuma dan uwansa mubairu
ya shigo cikin dakin da muke, koda ya ganmu muna kuka kuma
ya ga sarki a kwance a gefe daya yana barci
ga likita zaune a kusa dashi sai yayi dan guntun murmushi
sannan ya dubeni yace yakai yarima hulbasu ka sani cewa nazo ne gareka domin ka sanar
dani abubuwan da sarkina ya umarceka daka sanar dani
domin na rubutasu nakai masa, koda jin haka sai na dago kai na dubeshi
cikin tsananin fishi nace ashe baka da hankali da nutsuwa?
Kana ganin halin da mahaifina yake ciki ne zaka zo min
da wannan maganar banzar ? Ta yaya kake tsammanin zan iya maka bayani a yanzu bayan
ina cikin tashin hankali da damuwa, koda jin haka sai ran mubairu ya baci
ya daka min tsawa mai karfi tare da nunani da dan yatsa
yace
babu ruwana da batun halin da mahaifinka yake ciki domin kuwa umarnin sarkina na gaba dashi
maza ka sanar dani abinda nazo sani kafin fishin sarki ya
tabbata a kanka
yana gama fadin hakan sai ya zauna a kusa da ni ya fiddo littafi, tawada da alkalami domin yin rubutu
ni kuwa sai na tattare hannun rigata kamar zan zauna a
gabansa amma sai na shammaceshi na gabza masa wawan naushi a
fuska
sabo da karfin naushin sai da ya wuntsila da baya sau uku a lokacin da jini
yai feshi daga cikin bakinsa, ai kuwa sai ya taso da alkafira yai tsalle ya doki
tawa fuskar da kafarsa, nima na gwaru da bango na fasa baki
kafin na mike tsaye ya danneni kuma ya zaro wata wuka zai caka min a kirjina
sainayi wuf na rike hannunsa, a sannan ne likita da sauran
hadimanmu suka kurma uban ihu suka ruga waje da gudu
suna kiran dakaru domin su kawo dauki, yarima huzein
ne kadai tsaye a gabana yana kallon abinda ke faruwa
jikinsa na karkarwa sabo da tsananin razana
mubairu yaci gaba da kokarin dannan wukarsa a cikin kirjina, ni kuma naci gaba da kokarin
hanashi samun nasara, amma sai karfinsa ya rinjayi nawa
har wukar tasa ta dan sokeni na kwalla ihu sakamakon
tsananin zafi da zogin da naji, a lokacin da jini ya fara bulbulowa daga cikin kirjina
duk wannan abu dake faruwa sarki na kwance a gefe daya
yana shara barci bai sani ba
Koda yarima huzein yaga saura kiris mubairu ya sami nasarar hallakani sai yai
wuf ya zare wuka a jikinsa ya dako tsalle sama ya sokawa mubairu a wuya
take wukar ta lume ta faso makogwaronsa ya sulale
kasa matacce
huzein ya sunkuya a rikice ya kama
Wukar tasa domin ya zareta daga cikin wuyan mubairu
A dai dai wannan lokaci ne dakaru
sarki shardas suka rugo
izuwa cikin dakin su da yawa rike da makamai, koda suka
ga yarima huzein yana zare wuka a cikin wuyan muhairu
kuma gashi ya zama gawa sai suka yi caraf suka daureshi
ni kuwa sai na taso da sauri izuwa kansu na hausu da sara
da suka domin na kwaci dana a hannunsu
duk da cewa suna da yawa amma sai da na tarwatsa su na kashe sama da mutum arba in
Al Amin Ahmed Misau Ke Typing,
ina cikin tsakiyar yin
yaki dasu ne naji anyi min wani wawan duka a kirji
saboda karfin dukan sai da nayi sama na gwaru a jikin
katangar dakin na fado kasa a galabaice
lokacin dana farfado sai na tsinci kaina a tsakiyar fadar
sarki shardas kwance a kasa
A gefen damata yarima huzein ne a daure cikin sarka
a haguna kuma mahaifina ne tare da dukkan dakarunmu da
kuyanginmu suma duk a daure cikin sarka zaune akan karagar mulki sarki shardas ne
rungume da gawar dan uwansa muhairu yana ta
faman rusa kuka, nan take zuciyata ta buga da karfin gaske na kamu da tsananin tsoro irin wanda ban taba jinsa ba a rayuwata
ba komai ne ya sa ni jin wannan tsoro ba face tunanin cewa
sarki zai kashe mune gaba dayanmu, idan ya kashemu
kuma matata luzuraina ta mutu a wajen haihuwa shike nan fa duk
burinmu ya tarwatse kuma lokacin faduwar kasarmu yazo
a dai dai wannan lokaci ne yarima huzein ya dubeni a lokacin da
hawaye ya zubo masa yace yakai abba na ka gafarceni
domin na janyo mana abinda zai kawo karshen mu gaba daya
AA Misau Sunana
sa adda naji wannan batu sai hawayen takaici ya zubo min na
dubeshi nace
yakai dana baka bukatar rokona gafara domin baka aikata
laifin komai ba
tabbas ka kashe muhairu ne domin ka ceci rayuwata
babu wani da da zai bari a kashe mahaifinsa a gaban idanunsa
muddin zai iya hanawa
koda jin wannan batu sai mahaifina ya dubi yarima huzein cikin alamun tsananin
tausayi a lokacin da shima hawaye ya zubo masa yace yakai jikana huzein hakika
kayi babban kuskure daka ceci rayuwar mahaifinka a
hannun muhairu domin hakan zai janyo asarar da babu abin
da zai biyata
gama fadin hakan ke da wuya sai sarki shardas ya mike
tsaye daga kan karagar mulkinsa ya ajiye gawar muhairu akan karagar sannan
ya share hawayansa ya dubi mahaifina fuskarsa a murtuke sannan ya dubeni
kuma ya dubi huzein yace yaro ka kashe mini dan uwa
wanda shi kadai ne ya rage mini a duniya inda zan kashe gaba dayan mutanen kasarku mazanku da matanku
jininku ba zai goge bakincikin abinda na rasa ba
zan dasawa mahaifinka bakin cikin da har ya mutu ba zai manta da ni ba domin hakan ne kadai zai sa zuciyata ta lafa daga
ruruwar wutar bakinciki
koda gama fadin haka sai sarki shardas ya sa aka kwanceni daga cikin sarkoki
sannan ya zare wata sharbebiyar wuka ya cillo mini ita na
cafe kuma ya zare takobinsa yace nine na doki kirjinka dazu ka suma sa adda kake kashe dakaruna
koda ka manta cewa na gaya maka cewa digon jinin
daya na wakilaina da zan tura birninku dai dai yake da digon jinin mutanenku saba in
to ku sani cewa a yanzu jinin mutum saba in ba zai zamo fansar dan uwana ba
abinda nake bukata shine ina son uba ya yanka dansa
da hannunsa yanzu a gabana ko kuma na kashe ka da dukkanin jama arsa gaba daya
koda jin wannan batu sai mahaifina ya fashe
da kuka ya risina ga sarki shardas kuma ya zube kasa gaba daya ya yi masa sujjada
sannan ya dago kai ya dubeshi a lokacin da hawaye ke
shatata bisa kumatunsa ya kuma dubi gaba dayan fadawan
sarki shardas da mutanan gari yace yakai sarkin duniya ka dubi yadda na kaskanta kuma na wulakanta haka a gaban
talakawanka a matsayina na sarkin da ya gawurta a wannan nahiya tamu ka dubi darajarr sarauta ka canja wannan nufi naka
koda jin haka sai sarki shardas ya girgiza kai yace
ai bana yin magana biyu na gama yanke hukunci
ko danka ya yanka nasa dan yanzu take ko kuma na kasheka a gaban idansa kuma na kashe gaba dayan dakarunka
da kuyanginka da duk hadimanka, mahaifina ya fashe da kuka yace yanzu
jinina ni kadai ba zai fanshi jinin dan uwanka ba ? Sarki shardas ya dubi katon badakarensa mai rike da wata katuwar gudumar danko yace dashi
yakai KALBAN ka buga gangarka sau goma idan yarima
hulbasu bai yanka dansa ba kafin bugu na goma zan kashe mahaifinsa da duk jama arsa
koda jin wannan umarni sai kalban ya daga gudumarsa ya
doki wata katuwar ganga dake rataye a jikin wani
dogon karfe
take sautin gangar ya cika birnin gaba daya
a dai dai wannan lokaci ne huzein ya kama jan guiwarsa
kasancewar a daure yake cikin sarka ya iso gabana ya kwanta kasa ya dubeni yana mai murmushi gami da zubar da hawaye yace yakai abbana ma za ka yankani domin ka kubutar da mahaifinka da jama armu
ka sani cewa zan mutu a cikin farin ciki tunda da jinina ya zama fansa ga rayuka masu yawa
a wannan lokaci kalban yaci gaba da buga gangarsa
har yayi bugu na biyar
sa adda naji wannan batu na dana huzein sai hawaye ya zubo mini na
dubeshi nace ka gafarceni yakai dana kayi sani cewa
zan yanka ka ne ba don na ceci rayuwata ba ko ta ubana ba sai don Rayuwar jama armu ga su can wadanda suka sallama
rayuwarsu don biyayya a garemu lallai ina son su koma
gida a raye domin su rungumi iyalinsu.........
BABBAR MAGANA KENAN
SHIN HULBASU ZAI YARDA YA YANKA DANSA YARIMA HUZEIN ?
.
IDAN YA KASHE SHI IDAN YA KOMA BIRNIN ASKANDARIYYA MAI ZAICE DA MAHAIFIYARSA ?
.
SHIM MAHAIFIYAR YARIMA HUZEIN TANA HAIHUWA LAFIYA?
.
INA LABARIN JARUMA SIYAMA DASU YARIMA HULKAS ?
.
Marubucin Littafin Yace Mu Hadu A Littafin Tsatsuba Na gaba Don Jin Ci Gaban Wannan Kasaitaccen Labari.
Marubucin Littafin Wato
The King Of Adventure Story
Malam Abdul aziz Sani M/Gini
Saikuma Ni Al Amin Ahmed Misau wanda nake jagorancin typing din wannan littafi
nake cewa Mu zama lafiya saimun hadu a littafi na bakwai....
Dont Forget My Name
an makiyinmu sarki shardas
ka sani cewa kowacce mace tana son ta auri
namijin da zai iya kare mutuncin ta da rayuwarta
koda kuwa shine yafi kowa nakasa a doron kasa
lallai ku cika mini burina na ganin bayan sarki shardas
wannan itace kadai wasiyyata a gareku, ashe duk wannan bayani
da mahaifinta
yake yimini zalina dake can kofar kogo tana sauraro don
haka sai ta kasa cigaba da aikin da takeyi ta koma
gefe daya ta zauna tana ta faman kuka, koda na fito
daga cikin kogon dutsen rataye da takobina da nufin
na shiga daji don gabatar da farautar sai naga
zalina tana ta kukanta
Al amarin da yasa na gane cewa lallai duk taji abinda muka tattauna kenan dani
da mahaifinta
cikin sanyin jiki na karasa gareta na zauna daf da ita
kanta na sunkuye sai na tallabo habarta da lafiyayyen
hannun nawa kuma na share mata hawaye
muka kurawa junanmu idanu sannan na dubeta nace
shin kin amince na zama abokin rayuwarki
koda jin wannan tambaya sai zalina ta murtuke
fuska
daga can kuma sai ta rungumeni ta kama kyalkyala
dariyar farinciki
muna rungume da juna mukaji motsi a bayanmu
a firgice muka juya da sauri sai mukaga she mahaifin
zalina ne ya fito daga cikin kogon dutsen yana dogara
sanda da kyar yana numfashi sama sama
A guje na janye jikina daga cikin na zalina na
karasa gareshi na rukoshi na zo dashi wajan zalina
itama ta kamashi muka zauna gaba daya sannan ta
dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace haba
ya kai Abbana yaya kai da kake cikin wannan hali zaka taso kayi tafiya
sa adda abul zalina yaji wannan tambaya daga
bakin yarsa zalina sai ya dubeta
yayi murmushin karfin hali yace yake yata ai dole ne na
taso ko don naga abin farinciki na karshe wanda idanuna
zasu gani wanda shine amincewar junanku akan aure
lallai ina so naga wannan aure naku da idanuna
kafin rai yayi halinsa, nan take tsohon ya yiwa hailur
bayanin yadda zasu daura auren bisa al adar su
kabilar
wato kowannansu ya yanki dan yatsansa ya diga jininsa
a cikin ruwa
bayan jinin biyu ya gauraye sai kowannan su ya sha
ruwan
nan take kuwa muka aiwatar da hakan, muka rinka
shan ruwan muna kallon juna cikin murmushi har
sai da ruwan ya kare kaf
A dai dai wannan lokacine farinciki ya lullube abul
zalina ya dubi hailur yace yakai babban gwaro kayi
sani cewa yanzu ka zama na zalina kuma zalina
itama ta zama taka babu abinda zai rabaka face
kaddara ko mutuwa, wannan dama shine manufar
shan jinin juna da kukayi, bisa al adar kabilarmu
a ranar da miji ya mallaki matarsa babu abinda zasu fara
face zuwa daji farauta tare, don haka yanzu saiku
tafi sannan da ku ka samo shi zaku kawo a gasa
muci muyi walima da farin cikin aurenku, koda
jin wannan batu sai na dubi abul zalina cikin alamun
damuwa nace haba yakai abul zalina yaya za ayi
mu tafi daji mu barka kai kadai a nan alhalin kana
cikin wannan halina rashin lafiya, koda jin haka sai
abul zalina ya dubeni cikin murmushi yace kada
ka damu dani lallai zakuje ku dawo kuma ku sameni
cikin koshin lafiya da sauki fiye da ko yaushe
wannan shine abinda na gani a mafarkina na daren
jiya
bisa wannan dalili ne ma a yau din nan na sami
saukin da har na iya mikewa tsaye na taka kafafuna
na fito daga cikin wannan kogo haka dai abul
zalina yaci gaba da rarrashinmu har ya samu ya
shawo kanmu muka amince da barinsa a wajen
amma kafin mu tafi sai da ya rungumemu yana ta dariyar
farinciki
bayan ya janye jikinsa daga cikin namune mun juya
zamu tafi izuwa cikin daji sai zalina ta waigo ta
dubeshi take ta hango kwalla a cikin idanunsa
al amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan ta
dubeni tace yakai mijina nifa zuciyata bugawa
take da karfi ji nake kamar idan muka dawo ba zamu
riskeshi a raye ba
ni kaina naga alamun hakan a tare da mahaifin nata
kuma duk kalaman da yake yi na bankwana ne amma don
kada hankalin zalina ya tashi sai naki sanar da ita
haka dai muka nausa cikin daji muna waigen Abul
siyama shi kuma ya bimu da kallo yana yi mana murmushi
har muka kule muka daina hangoshi
A sannan ne kuma muka falfala da azababbn gudu izuwa
cikin daji mukayi ta tsala gudu ba sassauci muna
neman dabbar dajin da zamu samu
babu abinda zai baka mamaki face yadda nake iya gudu
ina dogara sanda alhalin kafata guda daya bata da
kyau kuma har tserewa zalina nake yi a gudun
ni ina rike da takobi ne kuma karshen sandar da nake
dogarawa mashi neita kuwa zalina a hannunta
kwari ne kuma ta rataya kwanson kibiyoyin
kwarin a bayanta
don haka ita bata rike wani makami sai kwari da baka
koda muka nausa cikin daji sai muka rabu ni kuma
nayi gaba ita kuma tayi yamma sannan kuma muka
baiwa junanmu tsawon rabin sa a akan mu hadu a
bakin wani dutse dake can tsakiyar dajin
kowannanmu na rataye da kaho a bayansa wanda duk
sa adda ya shiga wani hadari wanda ba zai
iya kubutar da kansa ba sai ya busashi komai nisan
inda yake dan uwansa zai iya jiyowa har yakai mas
dauki
shidai wannan kaho na sihirine kuma gadon gado ne
a kabilar tasu zalina kuma mutum ba zai iya mallakarshi
ba face ya kasance dan kabilarsu ko kuma ya auri
jinin Kabilar
bayan mun rabu a cikin daji nida matata zalina sai muka wanzu muna masu
neman abin farauta baji ba gani, lokacin da naga
na
shafe dan dogon lokaci ina neman abin farautar ban samu ba
sai hankalina ya dugunzuma ainun saboda ina ganin cewa ai abin kunyane
ace a ranar daurin aurena na kasa farauto abincin da zamu
ci nida amaryata
Ina cikin wannan haline naga wata barewa ta
nufo inda nake cikin azababben gudu gashi dai
barewar ta hangoni a gabanta rike da makami
amma ko shakkar tunkaro ni batayi ba
dada durfafo ni takeyi al amarin da yasa na fahimci
cewar lallai masifar da ta korota ta nufoni don tsira
da rayuwarta ta wuce tawa hadari, ai kuwa ban ankara ba
sai naga ashe wani murjejen zaki ne ya tasota a gaba
tun daga nesa dana hango zakin ya falfalo da azababben gudu
har tashi sama yake saboda karfin gudun nasa
kuma harshensa na zazzagowa waje daga cikin bakins ana gane
cewa lallai
wannan zaki a cikin muguwar yunwa yake
koda naga cewa barewar nan so take ta wuce ta gabana
domin ta tsira da rayuwarta sai na yunkura cikin zafin nama na
daka tsalle sama a lokacin da itama barewar ta daka tsalle da nufin ta shallakeni
muna haduwa a saman na soketa da mashina ta
zama gawa na duro kasa bisa kafafuna barewar
na sakale a jikin mashin nawa, ai kuwa sai wannan zaki
yayi tirjiya a lokacin da tazarar dake tsakaninmu
bata wuce taku goma ba
nan fa muka fara kallon kallo tsakaninmu da murjejen zakin
nazarin da zakin yake yi shine ni zai farwa sannan
ya dauke barewar ko kuwa barewar zai karba
ni kuwa nazarin da nakeyi shine ta yaya zan iya
.Ya kasance shi ba karamin tashin hankali bane
duk da na san cewa na sha yin gumurzu da manyan
dabbobin daji ina samun nasara a kansu sai da
zuciyata ta karaya akan wannan zaki domin ban
taba yin gamo da tsohon zakimai girma da kwarjinin wannan ba
nikam tuni na gama aiyanawa a raina cewa
duk rintsi ba zan iya sallama barewar ba ga wannan
zaki koda hakan na nufin zan rasa rayuwata
kawai sai na cake mashin nawa a cikin kasa
wanda ke dauke da barewar sannan na buda hannuna
mai rike da takobi ina mai
gyara tsayuwata kuma na koma gefe daya na tsaya ina
mai baw azakin zabi tsakanin barewar da ni kaina
ya zabi wanda zai fara afkawa
take zakin yayi wani irin
gurnani mai ban tsoro wanda yasa hantar cikinsa ta kada amma da na tuna cewa
amaryata
zalina na can fa tana farauta a cikin wannan daji
wata kilama yanzu ita ta dade da samo nata abin
farautar taje inda mukayi zamu hadu ta zauna
tana jirana sai naji zuciyata ta kekeashe ga barin dukkan tsoro.....
TSATSUBA
Littafi Na Biyar (5)
Part D.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Kamar hadin baki sai nida zakin muka falfalo
da gudun tsiya izuwa kan juna muka dako tsalle
sama a tare kafin nayi wani yunkuri na saran zakin
ko sukarsa da takobina tuni shi ya sa kirjinsa ya
bangajeni
ai kuwa sainaji kamar aksusuwan kirjina sun
kakkarye nayi can baya da karfi bayana ya gwaru
da jikin wata bishiya na fado kasa a matukar galabaice
ina aman jini ta hanci da baki, koda zakin yaga
halin da na shiga sa adda shima ya duro kasa sai
ya wangame baki ya kwalla wani uban ruri anda
ya fi wanda yayi a baya mai nuna kuranta kansa
da dai yaga na kasa tashi ina ta numfashi sai
ya wuce ta gabana ya daka tsalle da nufin ya suro
wannan barewa dake sakale a jikin mashina
ni kaina ban san yadda akayi ba na sami gagarumin
karfi da kuzari kawai gani nayi na mike tsaye zumbur
na daka tsalle daga inda nake na rungumo zakin
�����������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������kafin bakinsa ya cafi barewar mun fado kasa tim !
Nan fa muka kama kokawa a kasa muna ta birgima
idan zakin ya danneni yana kokarin kafa min
hakoransa sai na juye dashi nima ina kokarin
turmushe shi da karfin tsiya domin na hallakashi
sai da muka shafe kusan sa a daya muna ta bakin
artabu ya zamana cewa zakin ya karkarce jikina
da kaifin faratan hannayansa yai mini raunika
masu yawa jini na zuba a jikina amma kuma ya kasa
kafa min hakoransa a jikina
lokacin da jiri ya fara dibana na tabbatar da cewar ina daf
da halaka sai zuciyata ta kufulo cikin tsananin
zafin nama na suri zakin na dokashi akan wani
katon dutse nan take kan zakin ya dagwargwaje ya
zama gawa
A sannan ne na yanke jiki na fadi kasa cikin mugun yanayi
da kyar na iya bude jakar guzurina na fiddo magani
na shafa akan raunikan jikin nawa da hannu daya
wadansu raunikan ma dake gadon baya na in da
hannuna ba zai kai ba ban sami damar sa musu
maganin ba
a sannan ne na dauko battar ruwana na bude nash
Sai da na dan huta naji karfin jikina sannan na mike
tsaye na dauki gawar zakin na saba a kafadata
amatsayin abincinmu na rana itama barewara
sai na barta a jikin mashin nawa naci gaba da tafiya
na nufi inda zamu hadu da matata zalina
hakika SADAUKANTAKA tana da rana tabbas in ba don
na kasance sadauki ba da babu yadda za ayi na iya daukar
wannan katon zaki har na sabashi a kafadata da
hannu daya kuma naci gaba da tafiya alhalin ina
rike da barewa bisa mashina, haka dai naci gaba da
tafiya har na iso inda zan hadu da zalina matata
tun daga nesa kuwa na hango zalina zaune akan
wannan dutse tana hange hange da waige waige
ko zata gano ni, har ma ta zaku tana mikewa tsaye
akan dutsen
ai kuwa tana hangoni dauke da zakin da kuma barewa
sai ta cika da tsananin mamaki, cikin tsananin
murna ta duro kasa daga kan wannan dutse ta farfalo
da gudu izuwa gareni ta rungumeni koda taji
raunika a jikina sai ta janye jikinta daga cikin nawa
da sauri ta dubi sauran raunikan na jikina, take
hawaye ya kwararo daga cikin idanuwanta ta
dubeni cikin alamun tausayi tace yakai mijina me yasa
ka sai da rayuwarka don kawai ka cika wannan ka ida
ta al adarmu
Sa adda naji wannan tambaya sai na bushe da dariya
nace
yake matata kiyi sani cewa ko a tamu al adar namiji
baya samun matar aure a cikin sauki har sai ya
sha bakar gwagwarmaya ta hanyar gasa a neman
auren,
kuma gasa ce mai hadarin gaske wacce mutum ma
zai iya rasa rayuwarsa gaba daya, nan dai muka juya
da baya muka nufi hanyar gida, muna cikin
tafiya ne na dubi zalina na bushe da dariya, Al amarin
da yai matukar bata mamakikenan
ta dubeni tace yakai mijina kai kuwa menene dalilin
yin wannan dariya taka, kawai sai nayi ajiyar numfashi
nace gani nayi nidake mun shafe sama da sa a biyu
a cikin nan muna farauta amma ke ko fiffiken dan
tsako baki samo ba, dajin wannan batu sai itama ta
kyalkyale da dariya tace ni kaina na yi matukar mamakin
yadda ko tsuntsu guda ban iya harbowa ba daga sama
alhalin ga su nan birjik suna ta kaiwa da komowa
a sararin samaniya sai dana yi asarar kibiyoyina
sama da guda talatin, kai bama tsuntsaye ba hatta
kananan dabbobin daji sai dana kasa tsere da wajan
guda bakwai amma da zarar sun shiga cikin duhuwa
saina nemesu sama ko kasa na rasa su
koda jin haka sai nayi dariya nace ai kin san cewa komai
sa a ne da rabo
haka dai muka ci gaba da hira har ya rage saura tafiya
kadan mu iso gida
kwatsam muna cikin tafiya sai zalina tayi tuntube ta fadi a lokacin da zuciyarta
ta fara bugawa da karfi, cikin sauri na ajiye mashina
mai cake da barewa na tasheta zaune na dubeta
cikin kaduwa ina mai dudduba jikinta nace lafiya
kuwa menene ya sameki, zalina tayi ajiyar zuciya
ta dubeni cikin alanun firgici kawai sai naga hawaye
ya zubo mata take ta fashe da kuka tana mai cewa
naji a jikina cewa mahaifina yayi kaura, koda jin haka sai
nima hankalina ya tashi na dubeta cikin kwarin guiwa
nace ke haba ! Tashi mu karasa gida mahaifinki na
nan raye
kawai dai zuciyarki ce take raya miki hakan
nan dai na tasheta muka mike tsaye har zuwa wannan
lokacin ina dauke da wannan katon zakin a kafadata
ga kuma barewa a jikin mashina
haka dai muka
cigaba da tafiya harmuka
Iso gida
tun daga nisa muka hango Abul zalina kishingide
a jikin dutsen kogon da muke kwana ya dora
kafarsa daya akan daya yana barci, kuma ga sanda
a hannunsa in ba don dora kafarsa da yayi ba daya bisa
daya da kuma sandar da ya rike a hannunsa da dole ne
ace ya mutu
Al amarin zalina kuwa lokacin da ta hango mahaifinta
a cikin wannan hali tun daga nesa sai jikinta yayi sanyi
zuciyarta ta karaya kawai sai ta yarda bakan dake
hannunta ta falfala da gudu izuwa gareshi tana
isa gabansa sai ta kura masa idanu koda taga
idanunsa a kafe suke ko kiftawa basa yi kuma babu
inda yake motsi daga cikin gabobin jikinsa sai ta
fada kansa ta rungumeshi tana mai tsandara uban
ihu sannan kuma ta fashe da kuka
koda ganin abin da
ya faru sai nima na rugo da gudu ina dogara sandata
ina isowa na warbar da wannan zaki na kafadata
kuma nayi jifa da sandata da mashin da barewar
ke tsire akai
kawai sai na tsugunna kasa bisa guiwoyina na fara
kuka aka rasa
wanda zai rarrashi wani tsakanina da zalin
sai da muka shafe kusan sa a guda muna kuka sannan na
mike tsaye naje na kama kafadar zalina na
tasheta tsaye na shiga rarrashinat, sai da ta dawo cikin
hayyacinta sannan muka fara shirye shiryen
binne gawar mahaifin nata, tun daga wannan rana
muka bar wannan daji ba tare da fatan komawa cikinsa
ba
ko don ziyara ga kabarin mahaifin nata wanda ke cikin
wannan kogon dutse
haka dai mukaci gaba da tafiya a cikin daji mu
kwana nan mu tashi can ba tare da sanin inda muka
dosa ba muna neman inda yake da ni ima mu zauna
muci gaba da rayuwarmu, sai da muka shafe watanni
shida cur muna tafiya sannan muka iso wani daji dake
cikin nan kasarka ta Askandariyya, A nan ne muka zauna
muka ci gaba da rayuwa nida matata zalina inda
muka gina wata yar bukka a gefen wani tsauni
inda muke kwana har ma muka kafa wani garken dabbobin
gida muna kiwo bamu da wata sana a face farauta
kuma mu kan kai fatun dabbobi cikin birnika mu siyar
mu siyo abin da muke bukata da silallan da muka
sayar da fatan dabbobin dajin sannan mu dawo
dajin da muke da zama ba tare da mun taba sha awar
yin rayuwa ba a cikin gari har muka samu rabon
haihuwar Yata SIYAMA
tun siyama tana da shekara biyar a duniya na fara bata
horon yaki har ta cika shekara tara kuma duk irin horon da za a baiwa
babban mutum shi nake bata
hakika siyama tasha bakar wahala sosai a wajen
horon yaki kamar zata rasa ranta kuma sau tari sai
uwarta tayi ta
kuka idan taga tana shan wahalar taji kamar ta
hanani bata horon amma idan ta tuno da irin
kisan gillar da sarki shardas yayiwa kabilarsu da
zuri arsu da tawa sai ta hakura, haka dai siyama taci
gaba da koyon yaki har ya zamana cewa nima
ta fini jarumtaka juriya da naci, a bangaren iya farauta kuwa
ni kaina sai da na cika da mamaki bisa ganin irin
abubuwan al ajabin da take yi a daji da kuma irin
kwarewar da ta samu ta iya harbin kibiya fiye
da mahaifiyarta
bamuyi shawarar sanya siyama a cikin gasar jarumtaka
ba don komai sai saboda mu jarraba karfin
damtsenta da kuma iyakar jarumtakarta kuma
burinmu shine taci gaba da baiwa kanta horo gami da
tanadin daukar fansa akan sarki shardas, ina mai tabbatar
maka da cewa
yanzu haka ko sunan sarki shardas siyama taji
an ambata sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata
kone saboda irin kiyayyar da muka cusa mata
kuma a kullum bata da burin da yafi na mu kyaleta
ta tafi zuwa birnin shardas ita kadai ta shiga har
cikin fadarsa ta kashe shi amma na gaya mata cewa
ba zata taba samun nasara ba a kansa a yanzu face
idan ta mallaki wata Hula da ake kira HULAR LAMSARA
koda Hailur yazo nan a labarinsa sai idanun sarki
hulbasu
suka zazzari ya kamu da tsananin tsoro gami da
mamaki saboda rabonsa da yaji an ambashi sunan
wannan hula ta LAMSARA tun yana yaro karami sai kuma
yanzu da yaji a bakin hailur, tabbas ya sami labarin
hular lamsara a wajan kakansa wato wanda ya haifi ubansa amma bai kara jin
labarinta ba kawo i yanzu
sai da sarki Hulbasu ya baza fatake jarumai da
mayaka izuwa sassan duniya domin su nemo
masa wannan hula ta lamsara amma ba a samu wanda ya jiyo labarin inda
hular take bama
sarki hulbasu yayi gyaran murya sannan ya dubi
hailur a natse yace hakika jikina ya bani cewa lallai
akwai wani babban sirri a tsakanin shardila matar sarki shardas
kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan sarki shardas ya gano cewa kana nan
a raye kuma anan cikin yankin kasata tobama kai ba
ko iyalinka hatta nida kaina bz an zauna lafiya ba
don zai iya zuwa ya yakeni ya kawai da mulkina
koda jin haka sai hailur ya dubi sarki Hulbasu yace
yakai wannan sarki mai Karamci me yasa ka taimakeni
Alhalin ka san cewa yin hakan hadarine ga rayuwarka
da mulkinka
koda jin haka sai sarki hulbasu yayi gyaran murya
gami da ajiyar zuciya sannan yace A rayuwata
babu abinda na tsana sama da zalunci kuma mahaifina
kafin ya gushe ya bar mini wasiyya akan cewa
idan har ina son nayi nisan kwana akan karagar mulina to
dole ne
Na guji aikata zalunci ga talakawa na dama duk
wadanda suke karkashina ko kasa dani kuma na
kwatanta adalci a tsakaninsu gwargwadon iyawata
ina so ka sani cewa har yanzu sarki shardas bai san
komai ba dangane da wanzuwarka ko baiyanarka a cikin aksata kuma
dolene kaci gaba da boye kanka har izuwa lokacin da
zaka iya fuskantarsa, duk da cewa yanzu kaga matarka
shadila da kuma danka yarima Hulkasa
amma dole ne ka hakura da mallakarsu har sai nan
da zuwa lokacin da ya dace, idan ba haka ba kuwa zaka
rasa su ne gaba daya kuma kai kanka ma zaka rasa kanka
ba zan hanaka ka gana da shadila ba amma kada ku
kuskura ku bari wannan yaro hulkas ya san cewa
kaine mahaifinsa kuma kada ku bari ya san duk abinda
ya faru a baya
hakan ba zai haifar muku da komai ba face rugujewar dukkanin burikanmu
gaba daya da kuma salwantar rayukanmu
yayinda sarki Hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin
hailur ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe har hawaye ya zubo masa kuma
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda
fishi
ya dubi sarki hulbasu yace yanzu kana nufin kace dani
inaji ina gani zan hakura da matata wadda aka
rabani da ita a daren angwancinmu da ita na farko kuma na hakura da
dana wanda tun yana ciki bai san cewa nine ubansa ba
gashi har ya cika shekara bakwai a duniya, ka sani cewa har kwnaan gobe zuciyata bata
bayar da soyayyarta ta gaskiya ba ga kowa face shadila
ina son shadila fiye da yadda nake son kaina
Shin tayaya kake tunanin
zan
yarda ta sake kubuce min a karo na biyu al halin ban taba
zaton cewa zamu sake hadu wa ba a cikin wannan
duniya
koda hailur ya zo nana a zancensa sai hawaye ya zubowa
sarki Hulbasu al amarin da yai matukar girgiza
hailur kenan kuma yai matukar bashi mamaki
ya dubeshi yace yakai abokina inda dalikin zubar
wannan hawaye naka mai tsada koda jin wannan
tambaya sai sarki hulbasu yaja dogon numfashi
sannan ya sa hannu ya goge hawayansa ya dubi
hailur cikin alamun karayar zuciya yace yakai abokina
kayi mini tambayar da ta fama min tsohon ciwon dake cikin
zuciyata ne kuma shine asalinsanadin da yaja
mummunar kiyayya tsakanina da sarki shardas inaso
ka sani cewa duk irin kiyayyar dakake yiwa sarki
shardas bata kai koda rabin wacce nake yi masa ba
domin duk ladabin da nake yi masa a yanzu na
dole ne saboda yafi karfina kuma bana son abinda zai
taba kasata da jama'ata, ka sani cewa bakincikin
sarki shardas ne ya kashe mahaifina kuma sarki
shardas ne sanadin dana rasa dana na fari YARIMA
HUZEIN
Cikin alamun tsananin mamaki da kaduwa hailur ya
dubi sarki hulbasu yace tayaya mahaifinka da danka
huzein suka gushe
koda jin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa
sarki hulbasu ya dubi hailur cikin nutsuwa yace
yakai abokina ka saurari labarin da zan baka yanzu
dukkanin amsar tambayar da kayi min yanzu tana
cikinsa......
.
JARUMA SIYAMA DA MAHAIFINTA HAILUR SUNA CIKA
BURINSU NA DAUKAR FANSA AKAN SARKI SHARDAS ?.
.
MAI ZAI FARU IDAN SARKI HULBASU YA GAMA BAIWA HAILUR
LABARIN MUTUWAR DANSA DA MAHAIFINSA ?
.
A WANNE HALI SHADILA TAKE CIKI BAYAN TAYI ARBA DA TSOHON MIJINTA HAILUR ?
.
YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAN CEWA HAILUR SHINE
MAHAIFINSA NA GASKIYA
Wow gaskiya yayi
ReplyDelete