Lokacin da Sarki Hulbasu ya gama fadawa dansa
yarima Huzein wannan bayani sai ya rufe idanunsa
a lokacin da hawaye ya zubo masa cikin tsananin
bakin ciki mara misaltuwa ya yanga Yarima Huzein
tare jini yai tsartuwa daga cikin wuyan huzein a
lokacin da Hulbasu ya kurma uban ihu na takaici da
bakin cikin ganin cewa ya yanka dansa da hannunsa
shi kuwa mahaifin Sarki hulbasu wato Sarki yana
ganin sa adda Hulbasu ya yanka yarima huzein da
hannunsa sai nan take ya hadiyi zuciya ya sulale ya
baje a kasa matacce
koda sarki hulbasu yaga mahaifinsa ma ya
mutu kuma ga gawar dansa yarima huzein a gabansa
sai ya kama sambatu yana kai kawo a tsakanin
gawarwakin biyu tamkar mahaukaci sabon shiga
shi kuwa sarki Shardas sai ya bude da dariyar farin ciki
yayi ta kyalkyala dariyar tamkar ba zai taba dainawa
ba
lokacin da sarki hulbasu yazo dai dai nan a labarin
da yake baiwa hailur sai yayi shiru sa adda hawaye
ya zubo masa
yana hada idanu da hailur sai yaga shima hawaye ke
sartu akan kumatunsa yana mai kurawa hulbasu idanu
cikin tsananin tausayawa
hailur yaja dogon numfashi yace tabbas cin zarafin da
sarki shardas yayi maka ya ninka nawa saboda kai
ya tilastaka ka yanka danka da hannunka kuma
ya zamo sanadin mutuwar mahaifinka kuma
yanzu gashi ya mai daku bayinsa tunda duk arzikin
kasarku wajansa yake komawa, hakika damu daku
yanzu bamu da wani makiyi a doron kasa wanda
yafi sarki shardas, kuma a halin yanzu yafi karfinmu
babu abinda zamu iya yi masa kuma muna cikin
mugun hadari na masifarsa domin da zarar ya
fahimci cewa ina raye kuma ina tare dakai mu duka
har iyalanmu tamu ta kare, koda hulbasu yaji wannan
batu sai yai ajiyar zuciya cikin alamun tsananin
fargaba da takaici sannan sai jikinsa ya kama tsuma
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, yace
to yanzu shike nan haka zamu cigaba da zaman jiran
ranar da sarki shardas zai gano sirrinmu sannan yazo
ya gama damu
hailur ya girgiza kai yace babu wani abu wanda ba zai
yiyu ba a cikin wannan duniya face ba a jarraba
shiba komai nisan jifa kasa zai fado kuma komai karfin
mutun da isar mulkinsa akwai ranar da zai fadi
babu wata cuta wacce bata da magani kamar yadda boka
zamaranu ya shaida maka cewa zaka iya hallaka sarki
shardas amma sai an mallaki hular lamsara to me zai
hana mu tafi neman wannan hula tunda ance mai nema yana
tare da samu
gwara mu rasa rayukanmu a kokarin neman
wannan hula da dai mu zauna har makiyinmu yazo ya samu
nasarar hallaka mu muna ji muna gani ka sani cewa
ba karamin aiki bane a gabanmu idan har muna son
mu ga bayan wannan babban makiyi namu
dolene sai mutum ya sadaukar da wani abu idan
yana son ya sami wani
da farko dai dolene ka ajiye sarautarka kuma ka
cire dukkan tsoro daga cikin zuciyarka dolene mu kawai da gaba dayan
dakarun sarki shardas da hadiman da suka rako
matata domin mu aiwatar da abinda ke gabanmu
ka ayyana a ranka cewa zamu fita neman hular lamsara ne ba don komai ba sai domin
mu dauki fansa akan sarki shardas
shin yanzu zaka iya
hakura da karagarka ta mulki da kuma kasarka da
jama arka domin cika wannan buri naka
koda jin wannan batu sai hawayan takaici ya
zubowa sarki hulbasu yace ai bani da wani zabi wanda
yafi na hakura da komai din nayi wannan gagarumar
tafiya in ba haka ba kuwa zan rasa komai da kowa nawa
yanzu akwai abu daya nake tunanin yadda zamu
sami nasarar yinsa a cikin nasara wato yadda zamu iya
kawai da dakarun da suka rako shadila, koda jin
wannan batu sai hailur yayi murmushin yake yace
haba ya shugabana a cikin kasarka fa suke wadannan
dakaru ai kowa a gida sarkine, ni ina da shawara bisa
yadda zamu kawai da su cikin kankanin lokaci a
saukake
ba tare da mun fuskanci wata matsala ba
shawarar kuwa guda biyu ce da farko zamu iya amfani
da sanya musu guba a cikin abincinsu duk suci su mutu
idan kuma wannan hikima bata yi aiki ba sai mu ritsasu
a cikin masaukinsu mu da dakarun masu yawan da ya
ninka nasu sau uku mu yakesu, ni ka bar mini jagorancin
dakarun da za suyi wannan aiki
iana mai tabbatar maka da cewa zan yi iya
kokarina na tabbatar da cewar dayansu bai tsira
da rayuwarsa ba don kada yaje ya kai wa sarki
shardas labarin abinda muka aikata, lokacin da
sarki hulbasu yaji wannan shawara guda biyu na
hailur sai yaja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya kuma ya dubeshi cikin
alamun damuwa da fargaba sannan yace
da farko dai idan muka yi yunkurin kashesu
da guba ba lallai bane ya kasance cewa dukkaninsu zasu
ci abincin kaga kenan akwai yiyuwar wani daga
cikinsu ya tsira da rayuwarsa kuma ya sulale daga cikin birnin ya gudu bamu sani ba
idan kuwa hakan ta faru asirinmu ya gama tonuwa haka kuma
muka ce zamu yakesu anan cikin birnina a
masaukinsu jama a zasu jiyo kururuwar yakin koda
kuwa cikin dare ne sannan kuma ka san cewa suma fa
zakwakuran mayaka ne wadanda suka san TUGGUN YAKI
za a iya samun wani daga cikinsu ya sami damar sulalewa
ya gudu
idan ma hakan bata faru ba babu mamaki a cikin
jama ar gari akwai dan leken asirin sarki shardas mai sa ido
akan wadannan dakaru
Nasa da suka rako gimbiya shadila izuwa kasata don
haka ko wani dan motsi ya gani wanda bai yarda dashi ba
yana iya garzayawa yakai labari, lallai akwai mummunan
hadari a cikin duk wadannan batu sai ya numfasa yace ya kai
abokina yakamata ka sani cewa matsoraci bashi zama
gwani ko waye don haka dolene mutum ya siyar
da ransa wajan neman sa a bisa bukatar dake
gabansa
ko ka so ko kaki ko ka gudu ko ka tsaya watarana sai sarki
shardas yazo ya cika da yaki har gida tinda shi makiyi
har abada a cikin kokarin ganin bayan makiyinsa yake
lokacin da hailur yazo nan a zancensa sai jikin
sarki hulbasu yayi sanyi ya gamsu a ransa cewar bashi
da wani zabi wanda yafi ya yi amfani da wannan shawara
ta hailur don haka sai yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon
yan dakiku daga can kuma sai ya dago kai ya dubeshi
yace
na amince da duk shawarar da ka bani a daren yau zan
hadaka da amintaccen sarkin yakina domin
ku shirya duk abinda kuke ganin ya dace akan
wannan makiyi namu nidai kawai na baku wuka da nama
amma ina son ku gaggauta shirya yin wannan gagarumar
tafiya tamu ta neman hular lamsara Al amin Ahmed Misau
nake magana
koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube hailur yayi
godiya sannan ya mike tsaye da nufin ya fice daga
cikin dakin sai sarki hulbasu ya ruko hannunsa yace
ya zaka tafi baka tsaya kagana da tsohuwar matarka ba
babu wanda ya isa ya raba Hanta da jini
soyayyarka da matarka shadila tafi gaban wani dan
adam ya rubuta saboda tsoron sarki shardas ba zan hanaka
ka gana da ita ba tuni na shirya wannan ganawa naku
koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya tafi zuwa bakin
kofar wannan daki da suke zaune ya kira sunan wani hadimi
nasa yace dashi ya ruga izuwa can cikin gidan sarautar bangaren matarsa ya taho
da shadila cikin hanzari hadimin yace an gama ya shugabana
nan take ya ruga da gudu izuwa cikin gidan sarautar shi
kuwa sarki hulbasu sai ya yiwa Hailur sallama ya tafi
tafiyarsa keda wuya sai farin ciki mai dumbin yawa ya turnuke hailur yaji
kamar duniyar nan gaba daya aka bashi don haka sai ya
mike tsaye ya kama kai kawo fuskarsa cike da annuri
gami da farin ciki wanda ba zai misaltu ba
yana cikin wannan haline yaji an turo kofar dakin
an shigo cikin sauri ya waigo kawai sai yayi arba
da shadila a tsaye ta kura masa idanu tana zubar da hawaye
daki daki nan take shima idanunsa suka ciko da kwallar
ya fara zubar da hawaye tsawon yan dakiku sun kurawa
junansu idanu suna ta zubar da hawaye kamar ba zasu
daina ba
daga can kuma sai suka yi murmushi a tare suka ruga suka rungume
junansu kuma suka fashe da kukan farin ciki na
sake saduwa suna masu kankame juna sosai
ba tare da son saki juna ba sai shadila ta ce yakai
mijina yanzu ashe kana nan raye a cikin wannan duniya
amma ban sani ba
koda jin wannan tambaya sai hilairu ya janye jikinsa
daga cikin nata suka fuskanci juna yace yake abar begena
dare da rana
Al amin Ahmed Misau kiyi sani cewa ban taba mancewa
dake ba tsawon dakika daya daga
sa adda muka rabu
kawo i yanzu ban taba zaton cewa zamu sake
saduwa ba a cikin wannan duniya tunda ke kanki kin
sa a ranki cewa na mutu na sani cewa sarki shardas
ya aureki bisa dole to amma abu daya nake so na gani
shin kin haife cikin dana dana barshi a tare dake
ko kuwa sarki shardas ya kasheshi, koda jin wannan
tambaya sai shadila tayi shiru ta kasa bashi amsa
cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin na shadila ya girgiza
kafadunta ya ce cikin daga murya ki gaya mini
gaskiyar ala amari kada ki boye mini komai shin
dana yana raye ko ya mutu koda jin haka sai shadila
ta fashe da kuka ta kasa bayani saboda tsoron abinda
zai biyo baya
kwatsam sai sukaji an turo kofar dakin an shigo duk su biyun
suka waiga bayansu a firgice da sauri don ganin ko wane ne ya shigo ba wani bane
face yarima Hulkas tsaye idanunsa suna zubar da hawaye
kuma ya kurawa hailur idanu koda shadila taga hulkas
tsaye a gaban hailur kuma taga irin kallon da yake yi
masa har yana zubar da hawaye sai ta kamu da
tsananin tsoro jikinta ya kama tsuma saboda ta
fahimci cewar abinda take tsoron kada ya faru ya gama
faruwa
cikin sanyin jiki da alamun tsananin takaici
hulkas ya nufi inda shadila ke tsaye a lokacin da hailur
yabi hulkas da kallo ko kiftawa baya yi domin ya gane
cewa lallai wannan yaro hulkas dansa ne domin hatta irin gabobin jikinsa iri daye ne
nan take shima hailur yaji idanunsa sun ciko
da kwallah
lokacin da hulkas ya iso daf da shadila sai ya kama
hannayanta ya ruke yace yake ummina menene
dalilin da yasa tuntuni baki shaida mini cewa sarki shardas
ba shine mahaifina ba, kinsan irin tsananin son da nake
yiwa sarki shardas, kuma kinsan yadda na shaku da shi ainun
tun ina kankani kawo i yanzu, yanzu da wanne ido
zan fuskanceshi
Al amin Ahmed Misau Nake magana A matsayin babban makiyina Alhalin
shine ya rene ni ya inganta rayuwata
ki sani cewa sarki hulbasu ya bani labarinki kaf
da asalinki da yadda sarki shardas ya murkushe
jama arku kuma ya jefe mahaifina karkashin wannan
tsauni mai mugun zurfi sannan ya kamaki da karfin
tsiya ya
Maisheki matarsa har da dub irin barazanar da yake
yi miki akan kada ki sanar dani komai sannan ya sanar
dani yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka
dansa na cikinsa sanadin da ya zamo mutuwar mahaifinsa
ya kunsa masa bakin cikin da har abada ba zai gushe ba a doron kasa
tabbar sarki shardas ya cika babban azzalumi da babu
kamarsa a doron kasa kuma dolene na
kasheshi da hannuna, koda yarima Hulkas yazo nan a zancensa sai
ya kurma uban ihu kuma ya durkushe kasa bisa
guiwoyinsa biyu ya fashe dda matsanancin kuka
koda ganin haka sai itama shadila ta fashe da kuka ta kasa rarrashinsa
cikin sanyin jiki hailur ya dingisa ya isa gaban hulkas
ya sunkuya ya dafa kafadar hulkas, koda hulkas yaji
hannun hailur ya tabashi sai yai shiru tamkar daukewar
ruwan sama sannan ya dago kai suka kurawa
junansu idanu a lokacin da kowannansu ke zubar
da hawaye har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma
sai hulkas ya mike tsaye zumbur ya rungume hailur
suka fashe da kuka a tare
komai rashin tausayin mutum idan yaga lokacin
da wannan da da mahaifinsa suka rungume junansu
alhalin basu taba ganin juna ba basu san juna ba
sai yau
dolene zuciyarsa ta karaya ya tausaya musu
Al amin Ahmed Misau Sunana, Koda ganin abinda ya
faru sai farin ciki ya lullube shadila
sai da hailur da
hulkas suka dan jima a kankame da juna sannan hailur
ya janye
jikinsa daga cikin na hulkas ya dubeshi a cikin
nutsuwa yace yakai dana ina son ka yayyafawa zuciyarka
ruwan sanyi ka sani cewa komai yana da lokacinsa
ina mai tabbatar maka da cewa a halin yanzu in da
duniyar nan gaba daya zata taru kaf ba zata iya
kawar da sarki shardas ba saboda yana kan sharafinsa
babu mai iya ganin bayansa a yanzu face jarumin
da ya mallaki HULAR LAMSARA; Kai ni Al amin naji
sai wani Zancen Hular Lamsara suke da wahalar Samunta
Naga dai Nima jarumine fa Saboda haka nima bari
na dauki Takobina Na je neman wannan Hula domin na
kawar da Sarki shardas Hahahaha
zan iya Kuwa Freinds ?
Bisa wannan dalili ne ni da sarki Hulbasu muka yanke shawarar
mu rokeku kuma mu
kawar da dukkanin dakarun da suka rakoku sannan
mu bazama duniya neman Hular lamsara saboda kai
kanka yanzu rayuwarka na cikin mugun hadari idan har shardas ya gano ka san cewa shine ya tarwatsa rayuwar
mahaifinka na asali ba zai barka da raiba to amma
akwai wata matsala guda daya, koda jin wannan batu sai
hulkas ya dubi hailur cikin alamun matukar mamaki yace yakai
abbana me cece matsara kuma
Hailur yace sarki shardas ma ba zai iya hallaka ka ba
face ya samo wannan hula ta Lamsara kuma a halin
yanzu tuni shida bokansa sun fita farautar wannan hula
sun bar garinku a cikin mugun hali domin yanzu haka ana fama
da fatara yunwa da fari a kasar tun daga ranar da kuka
baro birnin kai da mahaifiyarka
ya zamana wajibi
mu gaggauta tafiya neman hular lamsara tun
gabanin makiyinmu sarki shardas ya rigamu samu
Koda jin wannan batu sai
hankalin yarima Hulkas ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi
a duniya
musamman da yaji cewar mutanan kasarsu na can cikin
mugun hali na fatara
da yunwa kuma ga batun gagarumar tafiyar dake gabansa ta neman hular
lamsara
hular da babu wanda ya san inda take....
Kai bari dai na dakata A nan domin nima naje nayi
shirin tafiya neman wannan hUla saboda naga Alamar
sun tsorata suna tsoron fita nemanta
amma akwai wanda zai iya rakani kuwa hahahaha
Kafin nan Nine
Al amin Ahmed Misau
Guyson Ko A square
nake cewa sai gObenku
TSATSUBA
Littafi Na Bakwai (7)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Hular da babu wanda ya san ina take
Shikuwa yarima barmas tunda suka shigo cikin wannan
daki tare da yarima hulkas ya zauna a gefe daya yana
ta sauraran bayanin da Hailur ke yiwa hulkas sai takaici
da tausayi suka sashi ya kama zubar da hawaye
dama da dadewa mahaifin sarki hulbas ya bashi tarihin
yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka dan uwansa
yarima Huzein wato yaya ga yarima barmas
sanadin da ya zamo na mutuwar kakansa kenan
nan take zuciyar yarima barmas ta kama tafarfasa
kamar zata kone babu abinda ya tsana a duniya
sama da sarki shardas A cikin wannan haline
aka ga kofar dakin ta sake budewa saiga Hulbasu
tare da matarsa Luzuraina da kuma jaruma siyama
tare da mahaifiyarta zalina har da sadauki ruhaisu
tsohon yaron hailur
koda ruhaisu yayi arba da hailur sai ya kamu da
tsananin mamaki kawai sai ya ruga gareshi suka
rungume juna cikin farin ciki mara misaltuwa suka kama
kyalkyala dariyar murna sannan ruhaisu ya janye
jikinsa daga cikin na hailur ya risina a gareshi
cikin
girmamawa yace ya shugabana ko a mafarki ban
taba zaton zan sake ganin wannan fuska taka
ba bare har na rungumi jikinka mai daraja ka sani
cewa har yanzu akwai sauran jama armu da yawa
suna rayuwa a boye cikin dazuzzukan wannan birni da muke ciki,
koda jin wannan batu sai farin ciki ya sake lullube
hulkas yace nayi matkar farin ciki da jin wannan
albishir naka kuma lallai ina bukatarka tare da
sauran wadannan jama a tamu, ka sani cewa ga
shadila Allah ya dawo mun da ita don haka akwai
gagarumin aiki dake gabanmu wannan yaro da kake
gani wato yarima hulkas shine dan da nabar shadila
tana dauke da cikinsa
koda jin wannan batu sai hawayan farin ciki ya zubowa sadauki ruhaisu
ya ruga wajan hulkas ya rungumeshi
a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas ya dubi
siyama sa adda hawaye ya zubo masa sannan ya bude
hannayansa yace da ita ' ashe ke yar uwata ce ban
saniba?
Taho gareni yake yar uwata rabin jiki cikin matukar
murna siyama ta ruga izuwa ga hulkas suka rungume
junaa
A sannan ne zalina da shadila ma suka durfafi junansu
suna murmushin saduwa suna haduwa sai suma
suka rungume junansu
zalina na kuka tace yake gimbiya hakika kaddara ce ta rabaki
da mijin kwarai wanda babu kamarsa a wajena a cikin
dukkan mazajen duniya amma tunda gashi yanzu ubangijinmu ya dawo miki
dashi inaso mu hadu mu biyu nida ke mu bashi
farinciki irin wanda bamu taba bashi ba a rayuwa
ki dauka cewa yaune wannan dare na farko na amarcinku ehm keda shi don haka
na baki kwanaki goma domin jiya ta dawo yau
koda jin wannan batu sai shadila ta sake kankame
zalina a kirjinta da kyau cikin matukar farin ciki tana
mai yi mata godiya
Al amin Ahmed Dan mutan misau wato A square
nan take sarki hulbasu ya dubi matarsa luzuraina yace
dake da shadila da zalina ku tafi ku bamu wuri zamu
yi ganawa ta musamman mu shida dinn nan
ba tare da wata gardama ba kuwa sai matan uku suka
fice daga cikin dakin suka bar sarki hulbasu, hailur da
sadauki ruhaisu , siyama da hulkas da kuma barmas
sannan kuma sai Al amin Guyson saboda shine typer ehem
nan take dukkaninsu suka zauna tsawon yan dakiku
dayansu bai ce uffan ba can sai sarki hulbasu yayi
gyaran murya yace abinda yasa na taraku a nan shine
kowannanku ya san cewa gimbiya shadila tazo nan
birnina tare da tsaro na dakarun sarki shardas su
dubu bisa jagorancin SADAUKI MARZANU, yanzu ina
son na ajiye mulkina na tafi neman HULAR LAMSARA domin mu kare kanmu
gaba daya daga sharrin sarki shardas don haka ina
neman shawararku bisa yadda zamu yi dasu
sadauki marzanu a mataki na farko da kuma yadda
zamu kai ga cimma burinmu lallai ina son kowannanku
ya bude kwakwalwarsa yayi tunani mai kyau
koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai kowa
yayi shiru aka rasa wanda zai fara yin magana
koda ganin haka sai Hulkas yayi gyaran murya
ya dubi sarki hulbasu cikin natsuwa yace
ya shugabana ni shawarar da zan bayar itace kada muce
zamu kawar da su sadauki murzamu a nan cikin birninka kawai a bari a gama
kammala wannan gasa ta jarumtaka sai muyi
shiri gaba dayanmu a matsayin zamuyi musu rakiya
izuwa can karshen gari muna isa can saimu shammacesu
mu afka musu mu kawar dasu gaba dayansu, mu tabbatar
da cewar dayansu bai tsira da rayuwarsa ba amma
idan mukace anan cikin wannan gidan sarauta zamu yakesu
babu mamaki akwai yan leken asirin sarki
shardas
anan cikin garin wadanda suka sa ido akan su murzanu
wanda da zarar abu ya samesu zasu iya gaggauta
sanar da sarki shardas, koda hulkas yazo nan a
zancensa sai ruhaisu ya dubi hailur da sarki
hulbasu yace a matsayina na wanda ya dade yana
jagorantar mayakan hari na sumame na yarda da
shawarar yarima hulkas
dajin haka sai hulbasu da hailur suka yi murmushi
sannan sarki hulbasu ya dubi hailur yace yau nima
zan fara shirye shiryen wannan tafiya a sirrance ba
tare da kowa ya sani ba sai a ranar da zamu tafi ne
zan tara yan majalisata na sanar dasu cewar zan
raka gimbiya shadila izuwa ga kasarta don
tsoron kada a sami wata matsala
Akan hanya na fuskanci fishin mijinta kuma nan take
zan bar galadima jiran karagata saboda shine kadai
mutumin dana tabbatar da cewar zai iya rike amanata
idan kuma akwai wani mai wata shawarar ne a cikinku
ya fada
koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai jaruma
siyama tayi murmushi tace ina so ku sani cewa sai munyi
taka tsantsan sosai akan dukkan shirinmu saboda
maso abinka yafika dabara, kuma ma su iya magana
sunce
kifi na ganinka mai jar koma, ina mai tabbatar muku da
cewa sadauki marzanu da sauran dakarunsa mutum
dubu biyu ba kanwar lasa bane domin sun zuba ido
sosai akanmu ko yaya suka ga wani mosti wanda basu
yarda dashi ba sai sun dauki mataki, abu na biyu kuma shine sarkin yaki sadauki
darkus ma yanzu dolene su sa ido akanmu gaba daya
musamman bisa ganin cewa sarki ya bani kariya nida
iyayena shin bakwa tunanin cewa zasu iya hada kai
dasu sadauki murzanu domin gano sirrinmu
koda jin haka sai sarki hulbasu ya girgiza kai yace tabbas hakan
zata iya faruwa amma zanyi amfani da damata ta sarki nima nasa amintattuna su
zuba ido akansu suyi nazarin dukkan motsinsu da shirye
shiryensu
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko A square
abinda nake so daku shine mu dukkannan jarumaine
don haka ina son kowa ya jajirce iya yinsa a ranar da
zamu gama dasu sadauki marzanu domin mu tabbatar da cewar gaba dayansu ba wanda
ya tsira mu bar ganin cewa
zan tanaji amintattun
dakaruna masu yawa a ranar da zamu fita wannan yaki
wadannan mutane suna da matukar hadari
da wannan furuci nake sallamarku amma banda
abokina hailur
koda jin haka sai kowa ya mike tsaye ya nufi
kofar fita daga cikin dakin amma banda yarima hulkas
domin tsayawa yayi yana ta kallon hailur har saida
sarki hulbasu ya dubeshi yace kada ka damu yakai
yarima yau tare da mahaifin naka zaka kwana don haka
kabi abokinka barmas nan da wani lokaci ma a cikin daren yau zamu sake haduwa
gaba dayanmu
koda jin wannan jawabi sai yarima hulkas yayi
murmushi sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin
dakin
fitarsa keda wuya sai sarki hulbasu da hailur suka mike tsaye Hulbasu ya kama
hannun hailur lafiyayyen ya jashi yana dingisa
daya kafar suka fice daga cikin dakin suka durfafi wani
bangare daban a cikin gidan sarautar yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso wani
babban falo wanda aka kawatashi ainun da shimfidu na koren
kilishi da kuma korayen kujeru manya na alfarma
kai ! Hatta labulayen dakin koraye ne komai a wajen kore
abin gwanin ban sha awa
Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square sunana
babu mutum ko
daya a cikin wannan katon falo kuma ga shi tsaf tsaf
sannan an zuba kayan Alatu iri iri a cikinsa masu tsananin
ban sha awa akwai dakuna guda bakwai a cikin
wannan falo gami da kewaye guda biyar kowanne
daki an sanya luntsumemen gado a cikinsa mai dauke
da shimfidu masu taushin gaske, su kansu kewayen
sama da kasansu da jikin bangwayensu dutsen
lu'u lu'u ne kuma bahon wankan a cikinsu na zinare ne
cike da ruwa mai kamshin
turaren miski
ga furanni kala a cikinsa
sai da sarki Hulbasu ya zagaya da hailur cikin gaba dayan
wadannan dakuna da kuma makewayin duka
sannan ya dubeshi yace yakai abokina anan nake son
kaci amarcinka da matarka ta farko shadila
koda jin wannan batu sai mamaki turnuke hailur yace
haba ya shugabana ya nida nake talaka ba dan kowa ba
zakace na zauna a cikin irin wannan kasaitaccen daki
alhalin ni gaba dayan rayuwata ma a daji nayi ta
lokacin da sarki hulbasu yaji wannan batu sai nan
take yaji ya kamu da tsananin tausayin hailur har
lwallah ta cika masa ido amma sai ya dubeshi cikin
murmushi yana mai dafa kansa yace yakai abokina
shin ka manta ne cewa kai shugaba ne guda na
kabila babba
kaima sarkine kuma bana fidda ran cewa nan gaba zaka
zama sarki don haka komai kyan daki da cikar
kawarsa dai dai ne dakai, ni yanzu zan tafi izuwa ga
iyalina ka zauna a nan ka jira Uwargidanka shadila
ehem Al amin Guyson kenan sunana, zata zo ta
riskeka nan ba da dadewa ba amma ka sani akwai
walima ta musamman wadda na shirya a tsakanin iyalina
da naka iyalin kadai domin tayaka murnar sake
saduwa da danka da matarka a cikin daren yau don
haka kayi zaton amsa gayyata koyaushe, koda gama
fadin hakan sai sarki hulbasu ya juyaya fife daga cikin kasaitaccen falon ya bar
hailur a tsaye yanata kalle kalle cikin tsananin farin
ciki
domin ji yake kamar a yau an mallaka masa komai
dake cikin wannan duniya
'' '' ''
A can turakar gimbiya luzuraina kuwa wato matar
sarki hulbasu tuni ta zauna tare da gimbiya shadila
zalina da siyama an kawo musu gasashshen naman
kaji da yayan itatuwa suna ci suna hira cikin nishadi
amma kuma hankalin shadila a tashe yake domin ta
kasa cin komai ta sunkui da kanta kas tana tunani
a lokacinda zuciyarta ke ta bugawa da karfi
cikin alamun tsananin tsoro da fargaba
koda luzuraina ta lura da halin da shadila ke ciki sai ta kama
hannayanta ta rike
ta dubeta cikin alamun nutsuwa tace yake kawata
wai shin wane irin tunani mai zurfi kike yi ne
haka wanda har ya hanaki sukuni ?koda jin wannan
tambaya
sai shadila tayi doguwar ajiyar zuciya
Sannan ta dubi luzuraina dasu siyama tace a cikinku
kaf babu wanda yasan sharrin sarki shardas sama dani
yaki dashi dai dai yake da mutum daya jal yace zai tari
gaba dayan halittun duniya saboda karfinsa da
sharrinsa ya wuce tunanin mai tunani, ta yaya kuke
zaton cewa gaba dayanmu nan zamu iya tsira daga sharrinsa
alhalin ya fimu duk wani abu da muke takama dashi
koda jin wannan batu sai luzuraina ta numfasa
tana mai dafa kafadar shadila tace yake kawata kiyi
sani cewa masu iya magana sunce mai laya ya kiyayi mai
zamani !
Ko shkka bana yi cewar komai nisan jifa kasa zai fado
a saboda haka dole ne karen bana yayi maganin zomon
bana
ki sa a ranki cewa wannan yaki ne tsakanin Gaskiya Da Karya da karfin gaskiyar
mu ne zamu sami nasara akan wannan babban
azzalumi wanda ya dade tsawon shekaru yana
cutar da al umma
haka dai luzuraina tayi ta kwantar da hankalin shadila
tana lallabata har ta shawo kanta taci abinci ta koshi
suna kammala wannan cin abincine sarki hulbasu da hailur suka shigo
cikin turakar
koda ganinsu sai kunya ta kama shadila ta sunkui da
kanta kas ta kama murmushi na murna da farinciki
ita kuwa zalina sai ta mike da sauri ta tarbi su sarki
hulbasu tana mai yi musu barka da zuwa sannan ta
dubi hailur cikin raha da zolaya ta ce to ango saboda
doki ma ba zaka bari nakai maka amaryar taka ba
shine ka biyota ?
Al amin Ahmed Misau Guyson ko A square sunana kenan
caraf sai sarki hulbasu ya tari numfashin hailur ya dubi zalina yace ke kuwa waya
gaya miki cewa ta zama amaryar tasa ai dole
ne da farko mu warware auren dake tsakaninta
da sarki shardas sannan a daura mata sabo da hailur
a sannan ne ta cika amaryarsa, tuni na gama shirya
yadda za a tafiyar da bikin wannan aure a yau din nan cikin
dare za a kara gabatar da gagarumar walima
koda jin wannan batu sai mamaki da farin ciki ya kama
hailur da shadila har dama yarima dasu siyama
sarki hulbasu ya dubi luzuraina yace dama wannan
sakon muka zo mu sanar da ku kawai don haka
idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi daku
izuwa can inda za a gabatar da ita, Al amin nake cewa
haka kuma idan
lokacin cigaba da wannan littafi yayi zakujini wato dai Gobe
kenan
kafinnan kuma
Nidinne dai Al amin Ahmed Misau
Guyson Ko A square
Dan garin Kaduna
nake cewa Mu zama
lafiya...
TŠÅTŠµßÄ
Littafi Na Bakwai (7)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
.
Idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi
daku izuwa inda za a gabatar da ita, koda gama fadin
hakan sai sarki hulbasu ya kama hannun hailur suka
juya suka fice daga cikin turakar, fitarsu keda wuya sai
shadila ta rungume zalina tana mai cewa godiya a
gareki mara adadi yake abokiyar zamana domin na
san cewa duk wannan shiri naki ne tabbas kin dawo
mini da farin cikin rayuwata wanda ya fiye mini
komai a cikin wannan duniya kiyi sani cewa koda
zan sami dare daya ne jal na wannan farin ciki na
mutu ya fiye mini shekaru dubu da zanyi nan gaba na zauna tare da babban
makiyi shardas
koda zalina taji wannan batu sai tausayin shadila ya
turnuketa har hawaye ya zubo mata ta sake kankameta
a jikinta tace yake abokiyar zamana kiyi sani cewa dole ne nasoki kuma na
kaunaceki dari bisa dari kuma na san martabarki a cikin
zuciyarsa kece masoyiyarsa ta farko a rayuwa kece kika sha wahalarsa duk da cewa nima nayi wahala dashi
amma ai kin kunshi bakincikin dako rabinsa ni ban kunsa
ba
sa adda shadila taji wannan batu na zalina sai taji
itama ta kamu da sonta fiye da ko yaushe don haka
sai ta kara kankameta a jikinta suka kama kukan murna
Al amin Ahmed Misau Inkiya Guyson ko A square
yayinda yarima hulkas da jaruma siyama suka ga
haka si suma suka kamu da tsananin tausayin iyayen
nasu har hawaye ya zubo musu a tare, kawai sai siyama ta
kama hannun hulkas ta ja shi suka fice daga cikin
dakin suka nufi wani bangare daban a cikin harabar
gidan sarautar
sai da suka iso wani fili mai fadi inda babu jama a wanda
ya kasance mai shirun gaske sannan suka zauna
tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba sannan siyama
tayi gyarar murya tace yakai dan uwana kayi sani
cewa nayi matukar farinciki dana san cewa ashe ina da
dan uwa a cikin wannan duniya wanda muke uba
daya
A farkon haduwata dakai naji ina sonka So irin wanda
mace ke yiwa namijin da take fatan zama abokin
rayuwarta
amma yanzu da na gane cewa kai muharramina ne
sai naji nafi kaunarka fiye da ko yaushe a matsayinka na jinina don haka
kukanka kukana ne kuma farincikinka nawa ne
mahaifin nan namu ya dade yana bani horon yaki
saboda kawai na dauki fansa akan ubanka na karya
wato sarki shardas ko a bayan ransa, shin yanzu zaka
bani hadin kai mu hada karfi da karfe domin
cika wannan bavvan buri na mahaifin mu?
Ka sani cewa raina ba a bakin komai yake ba akan
wannan al amari shin zaka iya cire soyayyar sarki shardas
dake cikin ranka ka kasheshi da hannunka
koda siyama tazo nan a zancenta sai idanun yarima
hulkas suka ciko da kwallah nan da nan hawaye ya
kama sartu akan kumatunsa, Al amarin da ya karya
zuciyar siyama ke nan ta rungumeshi kuma itama ta fara kukan
cikin sanyin jiki hulkas ya janye jikinsa daga cikin
nata suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu
ke zubar da hawaye Al amin Ahmed sunana
hulkas yace yake yar uwata kiyi sani cewa bazan iya cire
son sarki shardas daga cikin zuciyata ba amma
zan iya kasheshi da hannuna ba don komai ba sai domin
a halin yanzu babu mutumin da na tsana sama dashi a doron
kasa
na tsaneshi ne saboda zaluncin da yayiwa iyayena da kuma
munafurtata da yayi ya rinka wahalar da mahaifiyata
tsawon shekaru da shekaru amma yana nuna mini
cewa shi masoyinta ne na kwarai, ban taba sanin cewa
har dukanta yake yi ba a boye a bayan idanuna, shin
yanzu ke a cikin zuciyarki kina da yakinin cewa zamu
iya gano inda Hular Lamsara take har mu mallaketa
mu sami damar da zamu dauki fansa akan sarki
shardas alhalin bamu san a inda take ba kuma bamu san
wanda ya san inda take ba
koda yarima hulkas yazo nan
a zancensa sai jaruma siyama taja dogon numfashi
sannan ta kama hannayansa biyu ta rike suka
kurawa juna ido
sannan tace yakai dan uwana kayi sani cewa a cikin
wannan duniya babu abinda ba zai yiyu ba face
wanda ba a jarraba yinsa ba shin baka da labarin yadda
akayi JARUMI HANTARU ya sami nasarar dauko
Takobin SAIFUL LUJARA ? yasha bakar wahala kuma yasha
gwagwarmaya da manyan sadaukai irinsu RABBASU
wadanda suka fishi karfi amma saboda sa a da naci
gami da rabo sai da yakai ga gaci.
Al amin Kenan Mai
shararo muku Typing, shin baka da labarin jarumin
nan mai mashin GALILUL HARAS ? wato SADAUKI SHADDADU
shima yasha bakar wuya gami da gwagwarmaya kafin
ya mallaki wannan mashi to a yanzu ma ina ji a jikina
cewa kaine jarumin da zai mallaki HULAR LAMSARA sai dai kuma ......
Koda siyama tazo nana a bayaninta sai muryarta
ta shake da kakarin kuka ta kasa karasa abinda take
son fada ta fashe da kuka sosai al amarin da yai matukar
dugunzuma hankalin yarima hulkas kenan ya sake
rungumeta a kirjinsa yana mai cewa haba yake
yar uwata menene na kuka me zaki boye mini alhalin
ni dan uwanki ne na jini to ki sani cewa na san abinda
kike boye mini
wannan abu ba komai bane face duk wanda ya mallaki
wannan hula ta lamsara sai ya rasa rayuwarsa kuma a
tafarkin SOYAYYA zai hallaka kamar yadda ragowar
JARUMAN DUNIYA biyu suka hallaka
Tuni na dade da jin tarihin wannan manyan makaman
yaki guda uku kuma na sani cewa nine na ukun
Nasu nasan cewa mutuwa zanyi to amma ki sani cewa
ni yanzu nayi matukar farin ciki da ya kasance bake bace
masoyiyar da zan mutu a tafarkin soyayyarta ba
ke yanzu yar uwata ce ta jini wadda na tabbata da
cewar ko bayan raina zata iya kula da mahaifiyata
lokacin da yarima hulkas yazo nan a jawabinsa sai jaruma
siyama taji kaunasa ta kara linkuwa a cikin ranta don haka sai ta sake
rungumeshi suka fashe da kuka gaba dayansu
sai da suka dan jima kankame da junansu sannan
jaruma siyama ta janye jikinta daga cikin na
yarima hulkas ta mike tsaye kawai sai ta juya masa
baya tace wane shiri ka fara yi domin ka kai ga wannan
matsayi na zama JARUMIN DUNIYA na uku mai
hular lamsara ?
Yakai dan uwana kayi sani cewa ba a zama wane
a banza dole sai an sha bakar wuya da tarin
gwagwarmaya, koda jin haka sai yarima hulkas ya mike
tsaye yasha gaban siyama yace yanzu wane irin shiri
kike nufi zanyi ?
Jaruma siyama tayi murmushi tace dole ne ka cigaba da
baiwa kanka HORON YAKI har ka sami wanda zaka
iya zuwa inda hular lamsara take ka daukota
Al amin Ahmed Misau Guyson ko
A square sunana
a halin yanzu bincike ya nuna cewa kai da sarki
shardas kuna bukatar wannan hula ta lamsara kafin
dayanku ya sami nasarar hallaka daya shi dai sarki
shardas a halin yanzu yana da karfin da zai iya zuwa wannan wuri da hular
lamsara take bisa taimakon bokansa to amma inda
matsalar take shine dashi da bokan nasa basu san
a inda hular lamsara take ba sai dai kuma akwai wanda suka
nema
wanda shine kadai zai iya yi musu jagora izuwa wajen
ba wani bane ba wannan jagora nasu face wani
hatsabibin Tsohon Aljani wanda a halin yanzu
duk fadin duniya babu Aljanin da yafishi yawan shekaru
babbar magana Al amin nake typing
yafi kowa sanin sirrin wadannan manyan makaman yaki
guda uku wato takobin saiful lujara, mashin galilul haras
da kuma hular lamsara
shidai wannan tsohon aljani ana kiransa da suna
ARWASUL MASADUL
Aljani Arwasul masadul yana da tsananin karfin gudu
a cikin sararin samaniya domin daga birnin hindu yana iya zuwa birnin sin a cikin abin
da bai wuce sa a biyu da rabi ba don tafiyar
da bata wuce ta kwana talatin ba kuwa a cikin abinda
bai wuce wasu yan dakiku ba yake kammalata
ya kasance bashi da takamaiman wajan zama kuma
yana iya zagaye duniya kaf a cikin yini daya kuma
kullum sai ya zagayetan ma ana dai baya zama waje
daya tamkar shanshani
komai karfin sihirin tsafin boka bai isa ya iya ganin
a inda aljani arwasul masadul yake ba kuma bai isa ya
kirashi ya amsa kiransa ba haduwa da aljani arwasul masadul sai babban
rabo da sa a kawai
neman Aljani arwasul masadul dai dai yake da neman
jaki mai kaho
idan kuma har mutum yayi dace haduwa dashi tofa
duk abinda ya bukata daga gareshi indai akwai shi
a cikin wannan duniya to zai kaishi inda abin yake
a cikin kankanin lokaci
Inda matsalar take shine aljani Arwasul masadul baya yawo
a cikin siffarsa
Al amin sunana wato Guyson, gaskiya Littafin nan
nikaina da nake
typing dinshi duk da na jima da karantashi yana sake
kayatar dani uhm kufa ? Yakan rikida ne izuwa siffar
bil adama sau tari ko ta dabba ko ta kwaro don haka
sai mutum yaci jarrabawarsa sannan yake
taimakonsa babbar illar aljani arwasul masadul itace ba a rudarsa da dukiya ko mace ko mulki, kuma bashi da
tausayi ko jin kai shi kawai yana da wadansu ka'idoji
ne wadanda sai ka cikasu sannan zai taimakeka kuma
dole sai ya zauna tare dakai tsawon kwana uku yaga
ka cika ka'idojin babu wanda yasan wadannan
ka'idoji na aljani arwasul masadul, baya ga haka aljani
arwasul masadul yana da karfin damtse na rikakkun
zakuna guda dubu dari da tamanin kuma duk duniya
babu mai karfin sihirinsa na tsafi amma wani abin
al ajabi a tare dashi shine babu abinda ya tsana sama da kudi
ko mulki kuma babu abinda yake so sama da jarumi
mara tsoro kuma mai sa a ya kai dan uwana kai mutum
ne mai tsananin sa a bisa duk abinda kasa a gabanka
sannan kuma na fuskanci cewa ko kadan baka da
tsoro bisa wannan dalili ne nake da yakinin cewa zaka
mallaki
hular lamsara kafin sarki shardas ya fita nemanta, ka sani
cewa sammako anema ba shine samu ba kai dai
kawai ka nemi sa a da dace, lokacin da jaruma siyama
tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas ya kamu
da tsananin mamaki ya dubeta yace yaya akayi kika
san duk wadannan al amura koda jin wannan tambaya
sai siyama tayi murmushi tace na taba haduwa da
Aljani Arwasul masadul kuma na cinye jarrabawarsa
a lokacinda nake yawon farauta a cikin daji kuma nayi mu amala da shi ta
tsawon kwana uku ba tare da na san ko shi waye ba
lokacin da yagabatar da kansa a gareni kuma ya
fito mini a siffarsa ta ainihi sai ya tambayeni abinda nake
bukata a cikin wannan duniya ya kaini inda abin
yake domin na mallakeshi, Al amin Ahmed Misau
koda naji wannan tambaya daga gareshi sai nayi
murmushi nace abinda nake bukata ba zaka iya
bani shi ba
cikin mamaki aljani arwasul masadul ya dubeni yace
ke yarinya kin yi babban kuskure da kika fadi haka
ki sani cewa komai yawan dukiyar da kike bukata zan
kaiki inda take kuma na kwasheta nakai ta inda
Kikeso a cikin dakiku kadan idan mulki kike so na
kowacce kasa a cikin wannan duniya zan iya baki
shi koda karfin tsiya a cikin dakiku kadan ke idan ma
duniyar gaba daya kike sonki mulka zan iya yi miki
sanadin hakan
to menene kuma abinda kike ganin cewa zai iya gagarata
sa adda naji wannan batu na aljani arwasul masadul
sai nayi murmushi a karo na biyu nace yakai wannan
aljani ka sani cewa duk abinda ka ambata bana bukata
ko daya daga cikinsu face ina son ka hana aikata zalunci
a doron kasa a tsakanin al ummar mutane da aljanu
da kuma tsakanin dabbobi da kwari sannan ka hana
zubar da jini a ko ina na duniya ya kasance duk
duniya kowa na son kowa ana zaman lafiya babu batun
sata ko kwace
babu fyade kuma babu bambanci tsakanin attajiri da talaka da kuma tsakananin bawa
da sarki wadannan abubuwa sune kadai cikar
burina na duniya
idan har ka har ba zan gansu da idanuna ba bana
fatar nayi doguwar rayuwa a cikin wannan duniya domin
takaicin rashinsu ne zai zama babban bakin cikina
koda nazo nan a zancena sai naga hawaye ya zubowa
Aljani Arwasul masadul yasa hannayansa biyu ya
dafa kafaduna ya ce kece bil adama ta farko a duniya data taba
burgeni
a cikin jinsin mata kuma ban taba haduwa da mai irin
wannan ra ayi naki ba ba wani abu bane yasa kika ga
na zubar da wannan hawaye baface takaicin kin
tambayeni abinda har na mutu ba zan iya samarwa da
wani shi ba
Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana
ina mai tabbatar miki da cewa aduniya ba za a taba
zama lafiya ba domin a hakan ta fara kuma a hakan zata
kare wannan shine tarihin da na riska a wajan kakana na
dari da ashirin
kuma nayi imani da wannan tarihi, yake wannan
jarumar mata hakika ba zan taba mancewa dake ba
a rayuwata domin ni a wajena kece jarumar jarumai
wadda bata damu da komai na duniya ba
yaune ranar karshe ta saduwata dake kuma ba zaki
sake ganina ba har izuwa ranar da zan mutu ko ke ki
mutu
amma ina fatan nayi miki taimako a sirrance ba tare
da kin sani ba kafin karshen rayuwata ina mai yi miki
fatan nasara da sa a a rayuwarki bisa wannan buri naki
da naji kin ambata daga yau nayi alkawarin cewar ba zan sake
zaluntar wani bil adama ba a doron kasa kuma
ba zan taba taimakon wani azzalumi ba amma lallai ki bar wannan al amari sirri karki
gayawa kowa face jarumin da kika tabbatar da
cewa shine zai kawo karshen zalunci , shugaban azzalumai
na wannan zami a cikin jinsinku na
bil adama da wannan furuci nake yi miki bankwana
na karshe
koda aljani Arwasul masadul yazo nan a jawabinsa sai
hawaye ya zubo mini na rungumeshi ai kuwa sai naji shima ya fashe da kuka
daga can kuma sai haji babu shi a jikina
ina bude idanuna na nemeshi sama da kasa na rasa
yau shekara uku kenan da faruwar wannan al amari
kuma ban taba baiwa kowa labarin abinda ya faru ba sai yanzu da nake
sanar dakai saboda zuciyata ta yarda kuma ta
aminta cewa kaine jarumin da zai kawo karshen zaluncin
shugaban azzalumai na bil adama wato sarki shardas
koda siyama tazo nan a zancenta sai yarima hulkas
yaji gaba daya tsigar jikinsa ta tashi kuma yaji cewa
a zuciyarsa ta aminta da duk abinda siyama ta fada
dari bisa dari saboda haka sai ya sake kamo hannayanta
ya rike yace yake
yar uwata kiyi mini Alkawarin cewar zaki
kasance a tare dani a cikin wannan doguwar tafiya
da zamuyi ta neman hular lamsara kuma zaki taimakeni
da ranki da dukkan karfinki
kuma babu abinda zai rabamu face mutuwa domin a yanzu ne na tabbatar da cewa kece
rabin jikina idan babuke babu abinda zan iya
aiwatarwa na dangane da babban burin dake gabana
saboda ra ayina ya kasance iri daya da naki kinga kenan
burinmu duk iri daya ne ni dake
koda jin wannan batu sai siyama ta rungume
yarima hulkas ta fashe da matsanancin kuka
Al amarin daya karya zuciyar sa ke nan shima ya fashe
da kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani
a cikinsu
Lokacin da dare ya soma yi ne wata kuyanga ta taho turakar gimbiya
luzuraina ta risina ta kwashi gaisuwa gareta
sannan tace ya shugabata sarkine ya aikoni nayi muku
jagora zuwa dakin walima ke da amarya shadila
koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube luzuraina da
shadila dama tunda aka watse aka barsu su biyu suna
ta hira ko gyangyadi basuyi ba
tuntuni duk su biyun sun caba ado don haka sai
suka mike tsaye zumbur da nufin su fita
amma sai shadila ta rike hannun luzuraina suka tsaya ta dubeta tace ba zan iya
zuwa wannan dakin walima ba face bisa jagorancin
abokiyar zamana zalina don haka sai dai mu biya ta
dakinta mu tafi tare, koda jin wannan batu sai luzuraina tayi murmushi
tace ai rashin hakuri kikayi ai dole ne mu nemi sa hannun
uwar gida a cikin wannan al amari don haka muje
gareta yanzu
Nima kuma bari naje ga neman kudina yanzu
Kafinnan Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Inkiya
Guyson Ko Asquare
nake cewa
mu zama lafiya
it's Real Al amin Ahmed Misau
TSATSUBA
Littafi Na Bakwai (7)
Part D.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Ba tare da wani bata lokaci ba kuwa sai luzuraina
ta kama hannun shadila tajata suka fice daga cikin dakin
itama wannan kuyanga da tazo domin tayi musu
jagora izuwa dakin walimar
sai ta koma bayansu sukayi ta ratsawa ta gaban
dakarun dake tsaron gidan sarautar suna wucewa ta
cikin kofofi
Abinda ya daure musu kai shine a wannan dare gaba daya
hadiman gidan sarautar babu su wadanda komai
dare a cikin kai kawo suke suna gabatar da ayyukansu
su kansu dakarun tsaron a yau sun kasance kalilan basu da yawa kuma sune
amintattu wadanda koyaushe suna tare da sarki basa
rabewa
koda ganin wannan sauyin yanayi sai mamaki ya
turnuke shadila ta dubi luzuraina a cikin dan alamun
tsoro tace
yake kawata menene dalilin daya sa naga komai na
gidan nan ya sauya a wannan dare ba haka na saba
ganin abubuwa suna gudana ba, koda jin wannan batu
sai luzuraina tayi murmushi tace ba komai ne ya kawo
haka ba face tabbatar da sirrin daurin wannan aure da zai
gudana daga sanin makiyanmu.
Koda jin haka sai farinciki
ya lullube shadila ta kama
murmushi tayi shiru bata ce komai ba, haka dai suka cigaba da tafiya suka
iso kofar dakin da zalina take, da isowarsu sai luzuraina ta kwankwasa mata kofar
tace yake uwargidan hailur ki fito ki raka amaryarki
izuwa ga angonta
kafin luzuraina ta gama rufe bakinta tuni an bude
kofar dakin kawai sai suka ga zalina tsaye a gabansu ta caba ado na gaban kwatance tamkar itace amaryar kuma fuskarta
cike da annuri gami da murmushi kana kallonta ka san cewa
tana cikin matukar farin ciki
tana ganin shadila sai ta rungumeta tamkar wacce taga yar uwarta ta jini
sannan ta kama hannunta tajata suka yi gaba tana mai
cewa muje na damkaki a hannun masoyinki na kwarai
koda jin wannan batu sai shadila da luzuraina suka
cika da mura nan take wannan kuyanga ta shige gaba
tayi musu jagora izuwa dakin walimar, falo ne
babba mai matukar tsawo da fadi wanda sarki
hulbasu ke yin babban taro a cikinsa musamman
a lokacin da ya gaiyato manyan baki daga kasashen duniya
babu kowa a cikin wannan babban falo face
sarki hulbasu hailur da yarima hulkas dakuma jaruma barmas
sai kuma amintattun hadiman sarki hulbasu
da amintattun kuyanginsa gaba daya teburan dake
xikin wannan falo an cika samansu da kayan alatu na abinci dana shaye shaye kala kala
na alfarma babu irin kalar da babu, a gefe daya
kuma wadansu makadane da mawaka na sarki suma amintattunsa ne wadanda babu yadda za ayi su bayyana
sirrinsa domin tun zamanin kakansa suke yin wannan aiki
A can wani bangare na daban kuma wadansu kyawawan yan
mata ne su takwas sanye cikin fafaren tufafi wadanda suka kasance yan rawa sun kama tamkar gumaka da babu ruhi a jikinsu
koda shigowar amarya shadila da su zalina cikin
wannan babban falo sai makada suka fara wani
irin kida mai taushi da dadin gaske su kuma wadannan yan mata yan rawar dake kame suka fara yin rawar
Mawakan kuwa sai suka kama rera wata irin
waka mai dadi suna ambaton sunan shadila suna
kodata gami dayi mata kirari nan take wannan al amari
yayi matukar burge kowa a wajan
Abdul Aziz sani Madakin gini
yace' Hatta ni da nake baku wannan labari ban
san sa adda na kama yin rangaji ba ina jin wani
irin nishadi da farinciki a zuciyata' sannan kuma Ni Al amin
Ahmed Misau wanda nake typing din littafin nan nima
na dan tsaya da typing din na fara takawa oyah uhm
gaskiya ne.....
Bayan mawakan sun gama koda amarya shadila
saikuma suka kama wasa ango hailur shima suna
yi masa kirari bisa irin gwagwarmayar da yasha a rayuwarsa tamkar a gabansu komai ya wanzu
dolene abin ya burge mutum saboda irin hikimar
da aka yi amfani da ita kuma dole ne mutum yaji
ya kamu da tsananin tausayin wannan ango
da amarya
domin kuwa a takaice aka bayar da tarihin
soyayyarsu da yadda aka rabasu da karfin tsiya
hatta sarki hulbasu dasu yarima hulkas basu san
sa adda suka kama zubar da hawaye ba
nima Al amin Ahmed Guyson Saida na zubar
marubucin littafin ma yace Nikaina a yanzu naji idanu na sun ciko da kwallah
ana cikin yin wannan waka ne falon yayi tsit
tamkar babu wani mahaluki daya mai numfashi a
cikinsa sakamakon tsayuwar masu kida da wakar
suma yan matan nan yan rawa suka kame kam
yayinda ni kaina Al amin Na kame kam, A dai dai
wannan lokaci ne kofar falon ta bude sai ga sadauki
ruhaisu ya shigo tare da wani dattijo wanda shima
asalinsa dan kabilar su hailur ne
kai tsaye suka nufi inda hailur da shadila
suke suka kamo hannayansu suka taho dasu
izuwa tsakiyar falon suka daura musu sabon aure bisa
al ada irin tasu
faruwar hakan keda wuya sai yanayin sararin samaniya ya sauya nan take ya zama
tamkar na damina hadari ya gangamo aka fara wata irin TSAWA DA WALKIYA mai tsananin ban tsoro
A dai dai lokacinne da wannan abu ya faru sarki
shardas na cikin wani kurgurmin daji tare da bokansa
abin dogaronsa sun yada zango a cikin wani kogon
dutse suna barci amma ana tafka wannan tsawa sai
sarki shardas ya farka firgigit A firgice zuciyarsa
na daka da karfi, babu abinda ya fado masa a
Rai face matarsa shadila, take yaji a jikinsa cewa lallai
wani abune ya faru ga shadila domin wannan tsawa
da walkiya da aka tafka ba na zahiri bane
ishara ce, Aljanunsu na tsafi suka yi masa bisa
abinda ya
faru
cikin gigita sarki shardas ya tashi bokansa daga barci
ya
dubeshi yace yakai abin dogarona kayi sani cewa
lallai akwai wani abu ya sami matata shadila
maza ka duba mini abinda ke faruwa
koda jin wannan batu sai bokan ya kawo gwauron numfashi
ya ajiye sannan ya dubi sarki shardas cikin
nutsuwa yace ya shugabana ai dama tun kafin mu
baro gida idan baka manta ba na gaya maka cewa
a cikin wannan tafiya da yarima hulkas zaiyi ne zai
sami damar da zai iya cutar da kai
to ka sani cewa
duba maka wannan al amari ba zai haifar da komai
ba face dakushe maka zuciya gami da karyar da ita
akan babban aikin dake gabamu na nemo inda
hular lamsara
take
ka sani cewa baka da wata mafita wacce tafi ka
hanzarta mallakar wannan hula ta lamsara kafin
makiyanka su rigaka lallai kana da babbar dama ta
samun haka tunda ka rigasu fitowa neman nata
amma ko yaya ka darsa batun soyayyarka akan
shadila a cikin ranka to lallai zaka rasa nasara
koda bokan yazo nan a zancensa sai hankalin sarki
shardas ya dugunzum ainun fiye da ko yaushe
ya dubeshi a fusace sa adda zuciyarsa ke tafarfasa yace ka gaya mini
cewa mun fito ne neman wani Aljani wai shi
arwasul masadul kuma tunda muka baro gida
muke ta keta dazuzzuka birane da kauyuka barkatai
amma ko alamun wannan aljani bamu gani ba
bamu san yaushe zamu hadu da shi ba, kuma bamu
san a inda zamu ganshi ba anya kuwa baka ganin
cewa wahalar banza muke yi ? Koda sarki
shardas yazo nana a zancensa sai bokan ransa ya
baci
yace
Al amin ahmed Misau ; guyson Sunana Ko A square
ashe akwai ranar da zaka yi kokwanto akan abinda
zan gaya maka shin ka manta ne cewa nine
na tsareka na baka dukkan kariya daga sharrin dukkan
makiyanka tun kafin ka hau karagar mulki
shin ka manta cewa zuri ar gidanmu sun shafe sama da shekaru dari
suna bauta a gidanku cikin amince da kauna ??
Babu yadda za ayi na bata yaudararka ko na
gaya maka karya dolene ka kasance mai hakuri
gami da juriya komai dadewar shekarun da zamu yi muna yin wannan tafiya
kafin mu hadu da aljanu Arwasul masadul koda
kuwa sai mun tsofe tukuf fatanmu dai shine nasara
da sa'a
koda gama fadin hakan sai bokan ya koma ya kwanta yaja
bargonsa ya lullube jikinsa gaba daya saboda
hunturun sanyin dake kadawa a cikin dajin
yaci gaba da barci abinsa tamkar a cikin dakin matarsa yake
a lokacinn da kuune baya jin sautin komai face na manyan dabbobin
daji ababan tsoro
shi kuwa sarki shardas saboda zuciyarsa na suya
don tsananin fushi idanunsa sun bushe babu alamar
jin barci kuma ko kadan baya jin uban sanyin da
ke kadawa
haka dai ya zauna yana ta tunanin zuci gami da
wasu wasi a ransa bisa yin abinda yake ganin cewa
shine zai fishsheshi
wata zuciyar tace dashi : wai shin yama za ayi ace
duk irin wannan masifaffen karfin damtsen nawa da kuma
karfin sihirin tsafi ace ba zan iya kashe wannan yaro
hulkas ba ?
Wai shin ma menene dalilin da yasa duk abin da wannan
bokan yazo mini
dashi sai na amince
shin bokaye basa yin karya ko kuskure ne a
bincikensu da furucinsu,?
Aljanu ne fa suke sanar dasu komai kuma su kansu
aljanun suna shirya karya kuma
suna yin son
zuciyarsu
kamata yayi na yi watsi da shawarar wannan
boka akan batun neman wannan hula ta lamsara
kawai na juya da baya na tafi izuwa birnin hulbasu
naje na kama yarima hulkas a gaban mahaifiyar
tasa shadila nayi masa yankan rago duk da cewa
ina kaunarsa !!
Al amin Ahmed Misau, koda sarki shardas yazo nan
a zancensa sai hawaye ya zubo masa kuma wata zuciyar tasa ta daka masa tsawa
tace
shin baka da hankali ne yanzu kana nufin kace zaka yanka
yaron da ka raina da hannunka wanda ka
kaunaceshi tamkar dan cikinka, idan har zaka iya
aikata hakan to tabbas dan da ka haifa da kanka
ma zaka iya kasheshi !!
Koda gama aiyana hakan sai hawaye ya zubo wa
sarki shardas a karo na biyu ya kishingida akan
shimfidarsa ya lumshe idanunsa domin yayi barci
amma sai barcin ya gagara
A takaice dai yadda yaga rana haka yaga dare
da asubar fari boka nata faman shara barci abinsa
sai sarki shardas yaji yana sha awar ya shiga daji yayi farauta ko ya harbo
wani tsuntsu ko kuma ya samo musu dabbar
da zasu yi kalaci da ita saboda ya gaji da cin irin abincinsu
na guzuri wanda suka tanada, ba tare dasarki shardas
ya tashi bokansa daga barcinsa ba sai ya mike tsaye
ya dauki damararsa ya daura ya gyara zaman
takobinsa a cikin kufenta sannan ya dauko kuttun
kibiyoyinsa ya sakashi a kafadarsa ya rike sandar
bakan a hannunsa
yana gama wannan shiri sai ya fice daga cikin wannan
kogon dutse da suka kwana yana sanda don kada ma boka labarusa ya farka daga
barcin
ya hanashi fita wannan farauta, nan da nan sarki
shardas ya kutsa cikin dajin yayi nisa cikinsa yana ta
dube dube leke leke da neme neme sama da kasa
gabas da yamma kudu da arewa a cikin kowanne
sako kwari da tudu har cikin ramuka sarkakiya da
duhuwoyi amma ko gafiya bai
Gani ba bare ya sami abin farauta har tsawon sa'a guda
Al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan
nan har tsoro ya dan darsu a cikin zuciyarsa yace
ya za ayi ace duk girman wannan daji da kuma
tarin ni'imar dake cikinsa amma ace babu dabbobi dake
rayuwa a cikinsa?
Ko dai wata annoba ce ta kashesu gaba dayansu a
lokaci guda ?
Idan hakane kuwa ai yakamata ace annobar ta bar gawar
koda daya ne daga cikinsu, koda sarki shardas ya gama aiyana
hakan a cikin zuciyarsa sai yaji wata irin iska mai
karfin gaske ta giftashi ta samansa, cikin
hanzari ya daga kansa sama domin yaga ko menene
ya gifta din
kawai sai yaga ashe wata jibgegiyar halitta ce
mai manyan fuka fuki amma saboda tsananin karfin
gudunta ya kasa gane ko dabba ce ko aljan ko kuma tsuntsu
domin kafin giftawar ido halittar ta bace a cikin
sararin samaniya
cikin matukar karfin hali sarki shardas ya yunkura
da nufin ya tashi sama da karfin sihirinsa na
tsafi amma sai yaji ya kasa tashi saman al amarin da yai
matukar razanashi kenan kuma yai matukar bashi mamaki saboda wannan shine
karo na farko a rayuwarsa da ya taba jarraba amfani
da karfin sihirinsa na tsafi yaki yayi tasiri
amma da yake shi sarki shardas mutun ne wanda
bai san tsoro ba kuma yana da dakakkiyar zuciya
sai kawai ya falfala da masifaffen gudu yabi bangaren
da wannan jibgegiyar halitta tabi, sai da ya shafe sa a guda
yana gudu yana daga kansa sama ko zai hango halittar
kuma yana duba kasa ko zai ga alamun sawunta
idan ta sauko kasan amma bai gani ba, kwatsam
yana cikin falfala wannan azababben gudu da dube duben halittar nan ko
sawunta kawai sai ganin wani katon kogi yayi a
gabansa saura kiris ma ya fada cikinsa yayi turjiyar bazata
ba a bakin gabarsa cikin
tsananin sauri da zafin nama, tsayuwarsa a gaban
kogin keda wuya sai yaga tsakiyar kogin ya
kumburo sama wani abu mai girman gaske na
shirin fitowa daga karkashinsa
aikuwa kafin yayi wani yunkuri sai ga wannan
jibgegiyar halittar ta taso izuwa saman kogin ta dora
kafafunta guda hudu a samansa tamkar kasa ta taka
ita dai wannan halitta mutum bai isa yace ga abin da
take kama dashi ba ita ba tsuntsuwa ba, ita ba dabba ba, kuma ba aljana ba
tana da tsananin muni gami da matukar kwarjini da ban
tsoro
kawai sai halittar ta juyo da kanta ta kurawa sarki
shardas idanu ba tare da tayi wani yunkuri ba
koda ganin hakan sai sarki shardas ya durfafi halittar har sai da yaje dab
da ita sannan ya dubeta ba tare da nuna alamun wani
tsoro ba yace yake wannan halitta waye kai kuma menene
dalilin da yasa kaine kadai halittar dake rayuwa a cikin
wannan daji mai tarin ni'imomi haka ? Al amin Ahmed
misau Guyson
koda jin wannan tambaya sai halittar ta bushe da
mahaukaciyar dariya mai kama da saukar kwarankwatsa
tayi ta dariyar kamar ba zata daina ba lokaci guda
kuma sai ta turbune fuskarta ta dubi sarki shardas cikin nutsuwa tace
yakai wannan hatsabibin bil adama kayi sani
cewa babu wata dabba ko wani kwaro ko mutum
ko aljan da ya isa ya shigo cikin wannan daji har ya rayu
na tsawon dakiku dari face ya kasance mashahurin
matsafi abin kwatance don haka nayi maka jinjina
kai da bokanka labarusa
kafin halittar ya gama rufe bakinsa tuni sarki
shardas ya tari numfashinsa yana mai cewa wane ne kai
kuma menene dalilin da yasa wannan daji ya zama daban da kowanne daji dake nahiyar nan
koda jin wannan tambayoyi
sai halittar ta sake bushewa da dariya akaro na biyu sannan
tace ni kaina bansan kaina ba tunda ban san
asalina ba
amma dai na san na kawo i yanzu babu uwa babu uba
don haka ko suna bani dashi, koda jin wannan batu
sai sarki
shardas ya fusata, sannan nima Al amin Guyson na fusata
ya dubi halittar cikin fishi tare da daka mata tsawa yace
kada ka raina mini hankali mana ai ko a ina ka rayu
zaka iya sakawa kanka suna ko kuma a saka maka
tunda ba zai taba yiwuwa ba ace ka ray a inda babu
aljan ko mutum
koda jin haka sai halittar tayi murmushi tace
yakai wannan sarki kayi sani cewa hakuri na daya
daga cikin tafarkin dake kai mutum izuwa ga nasara
bisa abinda yasa a gabansa kai kuwa baka da hakurin
sarki shardas najin haka sai ya kara fusata da fishi mai
tsanani ya zare takobinsa ya dubi halittar cikin fushi yace tabbas bani
da hakuri kuma babu wani mahaluki wanda ya taba gaya mini magana haka cikin
gadara kamarka
haka kuma babu wani abu da na taba sashi a gabana ba tare da nayi nasara ba
saboda haka kaima sai na jarraba sa a ta akanka domin
na san ko kai waye ne
koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya daka tsalle sama tamkar an
harboshi daga cikin baka yayi sama izuwa kan halittar
yakai mata wawan sara a wuya cikin bakin zafin nama
halittar ta sunkuya takobin sarki shardas ta sari
iska kafin sarki shardas yayi wani yunkuri tuni
halittar ta maka masa jelarta akan kirjinsa
saboda karfin dukan sai da sarki shardas yayi baya a sama tamkar an janyeshi
da majajjawa yaje ya gwara bayansa a jikin
wata katuwar bishiya sannan ya fado kasa tim a cikin
matukar galabaice yana kumallon jini ta baki da
Hanci kuma ya kasa mikewa tsaye koda halittar taga
ta sami wannan nasara sai ta bushe da dariya tare
da bude fuka fukanta tayi sama tana mai cewa ya kai
wannan sarki hakika ka cika wahalalle kuma
asararre domin girman kanka da rashin kunyar ba zasu
taba kaika ga samun nasara akan abinda ka sa a
gabanka ba ina yi maka bushara da cewa kayi
babbar asarar damar da ba zaka kara samun kamarta ba
kafin sarki shardas ya daga kansa sama domin yaga
bangaren da halittar tayi a sama tuni halittar ta bace bat
a cikin gajimare tamkar
bata
taba
wanzuwa
ba.......
.
SHIN WANNAN WACCE IRIN HALITTA CE
.
SHIN WACCE IRIN DAMA SARKI SHARDAS YAYI ASARA WADDA BA ZAI SAKE SAMUN KAMARTABA?
.
YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR HULAR LAMSARA HAR YA GA BAYAN MAKIYINSA DA YA DAUKA A MATSAYIN MASOYINSA WATO SARKI SHARDAS ?
.
INA LABARIN SU SARKI HULBASU DA HAILUR DA SABUWAR AMARYARSA SHADILA DA AKA SAKE DAURA MUSU AURE A BIRNIN SARKI HULBASU ?
.
SHIN SU SARKI HULBASU SUNA SAMUN NASARAR HALLAKAR DA DAKARUN DA SUKA YOWA SHADILA RAKIYA BA TARE DA SUN BAR KODA DAYANSU YA TSIRA BA BALLE YAJE YA SANAR DA SARKI SHARDAS ?
.
WANNE IRIN AZABABBEN YAKI ZA AYI A GABA ?
.
SHIN YARIMA HULKAS YANA FADAWA TARKON SOYAYYA WADDA HAR ZATA ZAMO SANADIN RASA RAYUWARSA ?
.
TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR HULAR LAMSARA ?
.
SHIN AL AMIN AHMED GUYSON ZAI SAMU DAMAR KAMMALA MUKU WANNAN TYPING DIN ?
.
Marubucin Yace Mu Hadu A Littafi Na Gaba Wato Littafi Na 8
Don Jin Cigaban Wannan Kayataccen Kasaitaccen Labari
wanda ni
Al amin Ahmed Misau Nake Jagorantar Typing Dinshi
kuma mai son ganin Farin cikinku
nake cewa sai
Allah Ya kaimu Gobe
A littafi na Gaba
0 comments:
Post a Comment