LOKACIN DA WANNAN SIHIRTACCIYAR halittar ta make
sarki shardas ta luluka
sararin samaniya ta bace, a dai dai wannan lokaci ne
boka labarusa ya karaso bakin kogin a guje ya
isa inda sarki shardas ke kwance yana kumallon
jinin
koda yaga halin da sarki shardas yake ciki sai ya
dimauce hankalinsa yayi matukar dugunzuma
nan da nan cikin hanzari ya bude jakarsa ta guzuri
ya dauko wani garin magani ya hambadawa
shardas a bakinsa ya hadiye sannan ya dauko
wani farin mai ya shafe kirjinsa dashi
faruwar hakan ke da wuya sai sarki shardas ya
daina kumallon jinin da yake yi idanuwansa da suka
wurkile suka zama jajaye sai suka dawo dai dai
kuma ya dawo cikin hayyacinsa alhalin da yana .
Numfashi sama sama
A sannan ne boka labarusa ya dubeshi cikin
girmamawa yace
ya shugabana menene dalilin da yasa ka baro
can kogon dutse inda muke kwance kazo nan
kuma menene yayi maka wannan mugun naushi a
kirji haka wanda in ba don kana da nisan kwana ba
da tuni ka dade da shekawa barzahu ?
Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas ya
kawo gwauron numfashi ya ajiye cikin tsananin
mamaki gami da takaici sannan ya dubi boka labarusa
yace
yakai dirkar birnina kayi sani cewa ba komai ne yasa
na baroka ba a can kogon dutse sai saboda ina
sha awar na shiga daji nayi farauta na samo mana
naman da zamu yi kalaci dashi saboda na gaji da
irin abincinmu na guzuri, nan dai sarki shardas ya baiwa
boka labarin duk abinda ya faru gareshi har
izuwa sa adda ya hadu da wannan shirgegiyar halitta da yadda
aka sami sabani a tsakaninsu har yayi yunkurin hallakata
a karshe kuma sai tayi masa duka daya wanda yai
matukar galabaitar dashi, koda boka labarusa yaji
wannan labari sai ya kurma uban ihu cikin tsananin takaici
ya dubi sarki shardas a fusace yace, saboda me zaka
zubar mana da wannan gagarumar dama da muka samu ??
To ka sani cewa wannan halitta ba komai bace face
Aljani Arwasul masadul wanda muke nema ruwa a jallo
shin ka manta ne na fada maka cewa duk mutumin da
ya hadu dashi sai yayi masa jarrabawa tukunna sannan zai amince ya yarda dashi
har ya taimakeshi ?
A cikin jarrabawarsa guda goma guda daya jal yayi
maka yanzu kuma gashi ka fadi, haduwa da aljani arwasul
masadul sai babbar sa a bare mu sami damar haye ragowar
jarrabawar tasa guda tara
yana yin Adalci guda daya idan mutum yaci jarrabawa
biyar daga cikin goman yana iya taimakonsa kaga
kenan yanzu ka fadi jarrabawar farko,
Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square
koda boka labarusa yazo nan a jawabinsa sai
hankalin sarki shardas ya dugunzuma ainun ya
rasa abinda yake masa dadi a duniya kuma ya kamu
da tsananin takaici gami da bakin ciki mara misaltuwa
saboda haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba
wanda amsa kuwwarsa ta cika dajin gaba daya
har kwallar nadama ta cika masa idanu, koda
ganin halin da sarki shardas ya shiga sai boka
labarusa yaji ya kamu da tausayinsa don haka
sai yazo daf dashi ya zauna ya tallafo kafadarsa izuwa kan kirjinsa
yace ya shugabana kayi sani cewa mai dukkan rai
baya cire tsammani da samun rabo don haka
muna da sauran dama wacce indai muka yi amfani
da ita zamu iya kaiwa gaci, tashi mu ci gaba da
tafiya tunda dai himma bata ga rago kuma mai
nema yana tare da samu, koda jin wannan batu sai
sarki shardas yaji wani irin gagarumin karfi ya
shigeshi don haka sai ya mike tsaye da sauri cikin matukar kuzari ya dafa kafadar
boka labarusa ya dubeshi cikin murmushi yace kayi
gaskiya yakai amintaccena kawai mu kara himma
nan take suka juya suka koma izuwa wannan kogon
dutse inda suka yada zango
Wannan shine abinda ya faru ga su sarki shardas da
bokansa boka labarusa a cikin tafiyarsu ta neman
hular lamsara
'' '' ''
LOKACIN da aka tafka wannan tsawa da walkiya
bayan sake daurin auren shadila da hailur sai kowa dake
cikin dakin walimar yaji zuciyarsa ta buga da karfi
kuma tsoro ya baibayeshi amma sai aka basar aka
cigaba da shagali har sai da aka kammala komai
ango ya tafi da amaryarsa izuwa masaukinsa dake cikin
gidan sarautar taron ya watse kowa ya kama gabansa
lokacin da ango hailur ya kadaita da amaryarsa
shadila a cikin daki tana zaune akan gado ta sha
lullubi
kanta na sunkuye tana wasa da yan yatsun hannunta
koda hailur ya kamo hannunta da lafiyayyan hannunsa
sai tayi doguwar ajiyar zuciya ta dago kai ta dubeshi
cikin murmushi da tsananin farin ciki a lokacin da
hawaye ya subuto mata, koda ganin wannan hawaye sai
tsoro ya kama hailur ya dubeta a firgice yace yake
masoyiyata ina dalilin zubar wannan tsadadden hawaye nakai mai tsada?
Shadila ta sake yin murmushi a gareshi a karo na
biyu sannan tace yakai abin begena dare da rana
ka sani cewa ba komai ne ya sakani wannan
zubar hawayen ba face tsananin farin ciki na
tunowa da daren farko na auranmu ni dakai
ka tuna cewa daga wannan dare ban sake jin
dumin jikinka ba a jikina, kuma ban sake ganinka ba sai
a yau bayan shudewar wadansu shekaru dana jima
da fidda rai da sake ganinka a wannan duniyar
har abada
na rantse da darajar iyayena daga yau ba zan sake
yarda wani abu ya
Rabamu ba face mutuwa domin a yanzu daka dawo
gareni ka zama rabin ruhina idan babu kai ba zan iya
cigaba da rayuwa ba a doron wannan kasa
koda shadila tazo nan a zancenta sai farin ciki
ya sake lullube hailur ya rungumeta kuma ya kai
hannu izuwa fitilar dakin ya kashe ta, Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana Kenana, wannan shine abinda ya faru
ga sababbin ma aurata wato hailur da matarsa
shadila bayan an sake daura aure a karo na biyu
'' '' ''
ACAN dakin yarima barmas kuwa sai da suka kusan
raba dare suna hira shi da yarima hulkas akan
masifar da suke ciki ta sharrin sarki shardas
idan har ya gano halin da suke ciki, suna fara yin
wannan hira sai yarima barmas yaga yarima hulkas
yayi shiru yana tunani daga can kuma sai idanunsa
suka ciko da kwalla ya fara zubar da hawaye
koda ganin haka sai shima yarima barmas hankalinsa
ya dugunzuma ainun kuma ya kamu da tsananin
tausayinsa don haka sai ya shiga rarrashinsa yana mai
rokonsa da ya cire komai daga ransa
cikin sanyin jiki yarima hulkas ya mike zaune daga
kwancen da yake ya dubi yarima barmas cikin
nutsuwa yace
yakai abokina ka yi sani cewa ba komai bane ya
jefani cikin mugun bakinciki da takaici ba face rashin
sanin cewa sarki shardas bashi bane mahaifina na
jini
Na dauki duk wani SO DA KAUNA ta duniya na bashi
a zatona mahaifina ne shi, lallai bani da burin da yafi
naga na kasheshi da hannuna domin na huce
takaicin iyayena
haka dai yarima barmas ya cigaba da rarrashin yarima
hulkas amma sai ya zamana cewa shi yarima barmas
din ne yayi barci ya bar yarima hulkas da kuma
Yarima Al amin Ahmed Misau hm,
a zaune zuciyarsa cike da tarin bakin ciki
gami da sake sake
har gefen asuba idanun yarima hulkas a bushe suke
koda yaga barcin ya kauracewa idanunsa sai ya
mike ya fito daaga cikin turakar yarima barmas din
ya kama kai kawo a cikin harabar turakar, yana
cikin wannan hali ne kwatsam yaji wata irin iska
mai matukar karfi daga sama ta lullubeshi
kafin yarima hulkas yayi wani yunkuri ko ya daga
kansa sama yaga abinda ya haifar da iskar sai kawai
yaji an sunkuceshi anyi sama dashi nan take yaji
kamar an zare masa dukkan lakar jikinsa gaba daya
kuma sai idanunsa suka kama lumshewa a take barci mai
nauyi ya daukeshi
lokacin da yarima hulkas ya farka daga barcin da ya
daukeshi mai nauyi sai ya tsinci kansa a wani wuri na
ban al ajabi wanda ya kasa tantancewa ko a sama
yake ko kasa
take ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace wai shin anya kuwa a cikin
duniya nake
Hm Al amin Ahmed Misau, ba komai ne yasa yarima
hulkas ya yiwa kansa wannan tambaya ba face
ya tsinci kansa ne a cikin wani wuri mai dauke da
kayan kawa na gaban
kwatance kuma da ya dubi
kasansa sai ya ga babu kasa
babu shimfida tamkar akan
gajimare yake tsaye kuma dayaga kafarsa ya yi tafiya sai yaji kamar
akan daben lu'u lu'u yake
tafiya
shi dai wannan wuri ya kasance babbar fada wadda ta
kayatu ainun ga kujeru na zinare ba adadi a kowacce
kusurwar na fadar
a bangaren gabas a tsakiyar fadar an girke wata
kawatacciyar KARAGAR MULKI ta zinare da aka
kawatata sai dai babu kowa akan karagar mulkin
wani abun da ya kara daure masa kai kuma yayi
matukar bashimamaki shine yadda yaga
babu wata alamar kofa wacce za a iya fita ko shigowa
cikin wannan fada daya tsinci kansa a cikinta
kai tsaye yarima hulkas ya tunkari inda babbar
karagar mulkin nan take a tsakiyar fadar
Al amin Guyson ina biye dashi a baya, yana zuwa
daf da karagar mulkin sai ya risina ya sauke guiyoyinsa
kasa ya kwashi gaisuwa a gareta tamkar dama ya
ga wani akanta yana mai sunkui da kansa kasa cikin
yanayi na girmamawa
kwatsam sai yaji an bushe da dariya daga kan karagar
mulkin
A firgice yarima ya dago kansa yayinda Al amin na matsa baya
yayi arba da abinda yake
yin wannan dariya
ba wani bane ya gani face Aljani Arwasul amsabur a cikin
siffarsa ta ainihi
Aljani Arwasul masabul ya kasance gabjeje kuma katon
gaske mai matukar kwarjini da ban tsoro yana da
kaho guda biyu akan tsakiyar kansa kunnuwansa
biyu ne dogaye ne tamkar na zomo, amma idanunsa
da hancinsa tamkar na bil adama suke
fuka fukansa manya ne don zai iya lullube gaba dayan
jikinsa dasu
hannayansa guda hudu ne haka ma kafafunsa, daga
cibiyarsa zuwa kirjinsa siffar zaki ce dashi daga
cibiyar kuma zuwa kafafunsa siffar dokine dashi Hm
Al amin ahmed Misau nake Typing, kaga kenan ya hada
karfi biyu na zaki dana doki, tunda yarima hulkas yazo duniya
bai taba ganin halittar data firgitashi ba ainun
kamar Aljani Arwasul masadur Duk da cewa siyama ta
taba bashi labarin aljanin amma bai kawo a ransa cewa
shine wannan ba tunda bata siffanta masa kamanninsa
ba
cikin kaduwa yarima hulkas ya dubi Aljanin yace
yakai wannan halitta wanene kai kuma akan wanne
dalili ka daukoni daga can duniyarmu ta mutane
ka kawoni wannan duniyar ta daban?
Lallai daka san gagarumin aikin dake gabana da baka
rabani da iyayena ka kawoni wannan duniya ba
koda yarima hulkas yazo nan a zancensa sai aljani
Arwasul masadul ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko
masa da sakon mutuwa kuma ya dakawa yarima hulkas
Tsawa al amarin da ya kara firgita
shi kenan ainun
har ma yaji hantar cikinsa ta fara kadawa cikin
alamun fishi Aljani Arwasul madadul
ya dubi yarima hulkas yace wane irin yaro ne kai
haka mara da a da har zaka rinka yiwa manya tambaya ?
Kamata yayi ka zuba ido ka ga yadda zamuyi da kai
tukunna
ka sani cewa mun daukoka ne domin mu taimaka
maka bayan munyi maka jarrabawa ta tsawon kwana uku, koda jin wannan batu
sai yarima hulkas ya zube kasa bisa guiwoyinsa cikin
alamun tsoro da girmamawa yace
kayimin afuwa
ya shugabana idan ka rukeni anan har tsawon kwana uku ba karamar asara zanyi ba yanzu dai kaga gobene
da safe yar uwata jaruma siyama za tayi wasanta na karshe
da SADAUKI DARKUS a GASAR JARUMTAKA
lallai ina son naga yadda wannan gumurzu nasu zai
kasance
Baya ga haka zamuyi wata gagarumar tafiya mai
matukar darari nida.....
Caraf sai Aljanin ya tari numfashinsa yace na sani
cewa kai da mahaifinka sadauki hailur da mahaifiyarka
shadila tare dasu sarki hulbasu kuna son ku tafi
neman HULAR LAMSARA
to ka sani cewa jarrabawar da zanyi maka a cikin
wadannan kwanaki uku indai har ka samu nasarar
cinye su ina tabbatar maka zaka sami nasara abisa
abinda zaku tafi nema
ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa kwana uku
anan dai dai yake da jini daya na
duniyarku
kuma ka sani cewa nan kana inda kake kana cikin
wata duniya ne daban dake cikin duniyoyin sama amma
kuma zan saukar dakai izuwa taku duniyar domin ka fara
fuskantar jarrabobinka, kafin yarima hulkas ya budi
baki yace wani abu sai kawai yaji jiri ya kwasheshi
kuma idanunsa sun lumshe, kawai sai ji yayi ji da ganinsa
sun dauke dif ! Nan da nan hankalinsa ya gushe ya kasa gane halin da yake ciki
Al amin Ahmed Misau Bayan cikar yan dakiku kadan
kuma sai yaji komai ya dawo masa dai dai
yana bude idanunsa ya tsinci kansa kwance a kasa bisa
ciyawa a cikin wani
kungurmin daji
bayan ya dubi kowacce kusurwa na cikin wannan
daji baiga Aljani Arwasul masadul ba kuma ya duba ko
ina a jikinsa yaga ko wuka babu bare ya san cewa yana
da wani makami wanda zai iya kare kansa dashi
sai kawai ya mike tsaye yai shiru yana nazari da tunani
abin da ya fara fado masa a rai shine wai shin wacce
irin jarawaba wannan aljani yake son yi masa har
da zai kawoshi cikin wannan dokar daji ya ajiyeshi
Anya kuwa wannan Aljani ba shi bane Aljani
Arwasul masadul wanda yar uwata siyama ta
bani labari?
Tabbas idan kuwa shine to lallai na yarda cewa taimakona
zaiyi ba cutar dani zaiyi ba, koda gama aiyana hakan
sai hulkas ya nufi gabas ya kunna kai izuwa cikin
dajin kai tsaye ba tare da fargabar komai ba
dajine mai dauke da manyan duwatsu dogayen
bishiyoyi gami da koramu, tun da hulkas ya fara tafiya cikin
wannan daji bai hadu da wani abu ba face kanana
dabbobin daji irinsu birrai sai kuma kananun
tsuntsaye amma ko dabbar datakai girman barewa
bai gani ba
haka dai yarima hulkas ya cigaba da tafiya a cikin
dajin yana waige waige har tsawon sa a guda
kwatsam sai yayi kicibis da wata gada a kwance male male
cikin jini tana ta faman nishi tamkar ranta zai
fita saboda yawan raunikan dake jikinta sannan kuma
kafarta guda a karye take har ta fara kumbura
kallo daya yarima hulkas ya yiwa gadar ya kau dakai
har ya giftata zai yi tafiyarsa sai yaji tausayinta ya
kamashi saboda ya tabbatar da cewa indai wannan
jini na jikinta bai daina zuba ba mutuwa zatayi
cikin gaggawa yarima hulkas ya dawo da baya
ya tsugunna a gaban gadar yasa hannu ya yagi rigar
jikinsa ya daure dukkan raunikan dake jikinta ya zamana cewa jinin ya daina zuba
sannan sai ya mike tsaye da sauri ya ruga izuwa wata
bishiya ya karo kirare yazo ya gyara karayar dake kafar
gadar ya daureta
A dai dai wannan lokaci ne hadari ya gangamo aka fara
tsala tsawa da walkiya, koda yarima hulkas ya lura
da irin yanayin garin ya gane cewa ruwa ne mai
yawa zai sauko kawai sai ya sunkuya ya dauki
wannan gada ya sabata a wuyansa ya ruga izuwa
cikin dajin yana neman inda zasu fake, har sai
da ruwan saman ya fara zuba sannan ya hango wani
kogon dutse dan karami mara tsawo da fadi
wanda baifi mutum uku ba kacal su iya shiga ciki
kawai sai ya kunna kai ciki ya ajiye gadar a gefe
daya shima ya zauna dirshan a kasa
zaman sa keda wuya sai aka tsuge da ruwan sama mai
karfin gaske tamkar da bakin kwarya
tun safe aka fara wannan ruwa amma har goshin magariba ba a tsagaita ba
nan fa yunwa da sanyi suka addabi hulkas da wannan
gada
babu shiri yarima hulkas ya mike tsaye ya karyo wadansu
busassun itatuwa na wata yar karamar itaciyar
sannan ya dauko duwatsu biyu a cikin kogon yayi kyastu
dasu dakyar ya kunna wutar, nan da nan kogon yayi
dumi amma sai yarima hulkas ya rinka yawan kallon
wannan gadar yana kallon wannan dutar da ya kunna zuciyarsa na cewa dashi.
Ga nama kuma ga wutar gasa nama me zai hana
ka yanka wannan gada ka fedeta ka gashe domin kayi maganin wannan yunwa da ta addabeka
wata zuciyar kuma sai tace dashi A a ai tunda har ka ceci rayuwarta da farko bai kamata ka kasheta ba yanzu kawai
kayi hakuri ai yunwa bata kisa face kwana ya
kare
haka dai
yarima hulkas ya mike tsaye da nufin ya fice daga
cikin wannan kogon dutsen domin ya nemo musu
abinda zasu ci shida wannan gadar, Kwatsam ba
zato ba tsammani sai yaga wannan gada ta rikide
ta zama Aljani Arwasul Masadul yana mai kyalkyala
dariya....
Nima kuma Al amin Ahmed Misau,
a nan zan daka ta saboda
ganin wannan Abin mamaki yasa na kas ci gaba
Kafinnan karku manta
It's Real Al amin Ahmed Misau
Inkiya
Guyson Ko A square nake
cewa Mu
zama lafiya Sai
Allah ya kaimu Gobe
zakujini da cigaban sa
[4/25, 12:03 AM] Al Amin Gysn: TSATSUBA
Littafi Na Takwas (8)
Part B.
.
.Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau. Me magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga wannan gada
ta rikide ta zama Aljani Arwasul masadul yana
mai Kyalkyala dariya, al amarin da yai matukar razana
yarima hulkas kenan yaja da baya a firgice yana
mai tokare jikinsa a jikin dutsen kogon yana mai
takure jikinsa gami da zazzare idanu,
Koda ganin haka sai Aljani Arwasul Masadul yayi shiru
ga barin dariyar yace Yaro kaci jarrabawar farko saura
jarrabawa ta biyu kacal ! Sannan na cika Alkawarina na taimakonka a maimakon na cikasa
sauran jarrabobi bakwai a gareka, ba don komai ba sai
saboda wannan jarabawa ta farko dana yi maka tafi dukkanin
sauran muhimmanci
gama fadin hakan keda wuya sai aljanin ya bace bat
tamkar bai taba wanzuwa a wajan ba al amarin da yai
matukar fusata yarima hulkas kenan bai san sa adda
ya takarkace ya kurma ihu ba ya kama naushin kogon
dutsen da hannunsa har sai da yaji kamar yatsunsa
zasu kakkarye sannan ya daina, ba komai ne ya fusata
yarima hulkas ba face ganin irin rainin hankalin da
wannan aljani yayi masa wato yazo masa a siffar
wannan gada
Tabbas inda ya san cewa shine daba zai taba
taimakonshi ba kai ko kallonsa ma ba zaiyi ba balle
har takai ga ya taimaka masa, haka dai yarima
hulkas ya fito daga cikin wannan kogon dutse a jigace yana
layi kamar zai fadi kasa saboda yunwa.
Al amin Ahmed Misau Guyson nake ko A square nake
koda yayi yar gajeriyar tafiya sai yayi kicibis da wani
lambu a gabansa cike da yayan itatuwa nunannu,
kamarsu tuffa, inibi, ayaba, fasa dabur, baure , ruman
da sauransu
Ba tare da jin tsoro ba ko shakkar komai sai yarima hulkas
ya kunna kai cikin wannan lambun abin ka damai jin yunwa da zuwansa sai
kawai ya kama cin yayan itatuwan dake cikin lambun ba sassauci sai kace
dabba
wani ma idan ya gwawiya sau biya sai ya jefar
ya tsinko wani ya kama ci saboda ganin abin a banza
haka yarima hulkas yayi ta ci ya yan itatuwan nan har
sai da yaci ya koshi kuma yayi barna mai yawa
a cikin lambun wato ya zubar da wadansu yayan itatuwan a kasa ya tattakasu
bai sani ba
faruwar hakan keda wuya kuma sai ya hango wata yar
karamar korama a gefen lambun, kai tsaye yaje ya durkusa
a gaban koramar wacce ke dauke da ruwa mai kyau
garai garai ya sha ya koshi har da yin gyatsa
kawai sai yaji motsi a bayansa a lokacin da yake dago
kansa daga cikin koramat, kafin ya juyo yaga abin dake
bayan nasa sai yaji an gabza masa wani mummunan
naushi a wuya
saboda karfin naushin sai da yayi sama sannan ya fado
cikin wannan koramar ya jike sharkaff
cikin tsanani fishi yarima hulkas ya waigo da sauri da
nufin ya ga wanda yayi masa wannan naushi ya mayar
da martanin dukan da akayi masa amman sai ya kasa
sakamakon ganin wanda ke tsaye a gabansa, Al amin
Ahmed Misau Guyson nake magana
ba wani bane a tsaye a gabansa face wata kyakkyawar
yarinya ta gaban kwatance wacce shekarunta a duniya
basu da yawa wato ko yarima hulkas din zai
girmeta to da yan shekaru ne kadan ya girmeta ma
tun da yarima hulkas yazo duniya bai taba ganin ya
mace mai kyan wannan yarinya ba, a karon farko yana hada
idanu da ita yaji ya kamu da tsananin kaunarta fiye da komai dake wannan duniya
kuma ya aiyana a cikin ransa cewa lallai idan wannan
yarinya ta zama cikakkiyar budurwa sai ta zama sarauniyar kyawawa ta duniya
gaba daya
domin ba za a taba samun wata mace wadda ta kai ta
kyau ba
Kai Nifa tawa sarauniyar tafi wannan kyau Ehem Al amin nake
Yarinyar na sanye da kaya ne na fatar damisa riga
da wando a kuibinta na dama daure a jikin cinyarta
wata zabgegiyar siririyar takobi ce a bayanta kuwa
kwanson kibiyoyi ne a sakale, hannunta baka ne da
ta daga kibiya a jikinsa ta tabe zaren bakan tana mai
saita kirjin yarima hulkas da shi , da yi masa alamar yana
motsawa zata sakar masa harbi, gashin kanta dogo ne
kuma baki sidik wanda ya zuba har kasan mazaunanta sai
sheki da walwali yake, idanunta manya ne kuma farare kal kal tamkar ruwan madar
hancinta kuwa dogone siriri a saman dan karamin baki tamkar da wuka aka yankashi
yarinyar ta dubi yarima hulkas fuskarta a murtuke kuma
ta daka masa tsawa tace wanene ya baka izinin ka shigo har cikin
lambuna kayi mini irin wannan mummunar barna haka
ko kuwa tsautsayin mutuwa ne ya kawoka
koda jin wadannan tambayoyi guda biyu daga bakin
wannan kyakkyawar yarinya sai yarima hulkas ya
tuntsure da dariya sannan yace yakai wannan Aljani ka
daina tunanin cewa zaka iya yaudarata a karo na
biyu
in banda ma toshewar basira irin taku ta aljanu ta yaya za ayi
na yarda cewa mutum zai iya rayuwa shi kadai jal
a cikin wannan mugun daji bare ma kuma yarinya karama
kamar wannan wadda ke tsaye a gabana? Ai wannan aiki
sai daiku
Aljanu
Al amin Ahmed Misau, koda jin wannan batu sai yarinyar
ta fusata a karo na biyu ta tari numfashin yarima
hulkas tana mai sake daka masa tsawa tace kai
shashasha kalleni da kyau ka gani ni mutum ce kamar
ka ba Aljan ba
anan cikin dajin uwata ta haifeni muka rayu mu
biyu kacal har tsawon shekaru shida sannan ta mutu
ta barni
a haka na cigaba da rayuwa ni kadai
Har na kawo i yanzu duk wata dabba ko tsuntsu ko
aljan dake cikin wannan daji a karkashin ikona yake
amma kaine mutum na farko da na taba ganin yazo
har nan inda nake
shinka taba haduwa da Wani Aljani wai shi Arwasul Masadul ?
Koda jin wannan tambaya sai jikin yarima hulkas yayi sanyi
kuma ya kamu da tsananin mamaki ya
dubi yarinyar yace ke ya akayi kika sanshi wacece ke
kuma menene dalilin zamanku a cikin wannan daji
keda mahaifiyar taku har ta haifeki a cikin sa
koda jin wadannan tambayoyi sai yarinyar taja bakanta ta kara tabeshi tana mai
kara saita kirjin yarima hulkas tace maza ka gaggauta
amsa mini tambaya ta ta farko a gareka kafin
kibiyata ta huda kirjinka saye ya baka izinin ka
shigo har nan cikin lambuna kayi mini barna haka
koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas ya tsugunna
kasa bisa guiyoyinsa cikin
alamun kaskantar dakai yace kiyi min afuwa yake
wannan ma abociyar kyawu da kwarjini kiyi sani
cewa yunwace ta galabaitar dani har ta sani nayi miki
irin wannan barna gami kuma da rashin sanin cewa
akwai mai wannan lambu, koda jin wannan batu sai
yarinyar ta sauke kwarinta kasa sannan ta nufo kansa
gadan gadan tana zuwa daf dashi sai ta sa kafarta ta doki
kirjinsa saboda karfin dukan sai da ya kife kasa yana mai
aman jini
Al amin Ahmed Misau, kawai sai yarinyar ta
durkusa a gabansa ta kamo habarsa da hannu daya ta dago kansa sama
ta dubeshi tace wannan shine hukuncin barnar da kayi
min yanzu babu bashi a tsakanina dakai, saboda haka yanzu
sai ka bani labarinka ta yadda akayi ka sami nasarar
zuwa wannan daji
idan naji labarinka ya kasance zamu iya taimakon juna
nida kai don na san bazaka rasa wani buri ba wanda ya gagareka kamar yadda nima
nake da nawa burin
sa adda yarinyar tazo nan a jawabinta sai yarima
hulkas ya mike cikin tsananin takaici ya tuno da
cewa wannan shine karo na biyu da mace jaruma kuma
yarinya ta nuna masa tafishi karfi da jarumta yar
uwarsa jaruma siyama ce ta farko saikuma wannan
bakuwar jaruma wacce basan komai a kanta ba
yarima hulkas ya goge jini dake kan lebensa sannan
kuma ya dan karkade kurar jikinsa ya dubi yarinyar
cikin nutsuwa yace ta yaya zan iya baki yardata har na
sanar dake koni waye ba tare dake kin fara gabatar min da kanki ba
babu mamaki ke wakiliyar abokan gabata ce
koda jin wannan batu sai wannan yarinya ta bushe da dariya
sannan tace wanda ya ajiyeni anan bashi da abokin gaba
ko daya a cikin fadin wannan duniya tunda baka
da yarda shikenan ni yanzu zan fara gabatar da labarina
amma ba anan ba ka biyoni muje gidana
tana gama fadin hakan sai ta juya tabi wani surkuki mai
yar duhuwa shi kuwa hulkas sai ya kama binta da
sauri yana mai mamakin yadda za a iya samun gida
a cikin wannan kasurgumin daji, yar gajeriyar tafiya sukayi
suka iso wani wuri daban mai ban al ajabi, wadansu irin duwatsu
ne wadanda kallo daya mutum zai yi musu ya
san cewa sassakesu aka yi akayi gida a jikinsu mai
dauke da katuwar fada ba wai haka suke ba tun fil azal
abinda ya kara daurewa yarima hulkas kai shine shin
wane gwanin iya gini ne yayi wannan gida haka,
Tabbas wannan aiki yafi gaban aikin bil adama sai
dai aljanu aljanun ma sai dai idan sune sarakan gini
na duniya
shi dai wannan dutse asali kato ne tamkar tsauni amma
sai gashi an fafeshi an yanyankashi kuma an fikeshi kai kace kasa ce aka kwaba
akayi tubali sannan aka gina, ta kan wata matattakala yarinyar tabi da yarima hulkas
suna fara tafiya akan matattakalar wacce ta nufi cikin
wata katuwar kasaitacciyar fada mai wadansu manyan
dakaru na aljanu ma abota kwarjinin gaske dauke da
muggan makamai su da yawa babu adadi suka bayyana suna masu tokare kofar
shiga fadar suka raste suka baiwa yarinyar nan hanya ta
shige suna masu dukar da kawunansu kasa don
gaisheta
amma yarima hulkas na isowa daf dasu sai suka tare masa
hanya suka zare takubbansu cikin razana da firgici
hulkas yaja da baya su kuwa aljanun sai suka yi
caa izuwa kansa da nufin su gididdibashi,
cikin hanzari suka ja da baya suka koma inda suke
tsaitsaye
yarinyar nan ta dawo da baya ta dubi dakarun gaba
dayansu tace
wannan bakona ne na musamman, koda jin haka sai gaba dayan dakarun
Aljanun suka risina suka gaishe da hulkas kuma suka
dare suka bashi hanya, sannan nima Al amin Ahmed Misau suka dare mun suka
bani hanya saboda ganin Kwarjini na ehem suna
shiga cikin fadar sai yarima hulkas ya rude kuma ya
dimauce domin bai taba ganin fadar da ta kawatu
kamar wannan fada ba,
sai dai babban abin bakin cikin shine fadar kango ce
babu bafade ko guda daya a cikinta bare ma a sami
talakawan da za a mulka
kai tsaye wannan yarinyar ta nufi kasaitacciyar karagar
mulkin dake cikin fadar wacce akayita da zallan Dutsen
lu'u lu'u aka kawata shi da adon sarauta
Da isarta kan karagar mulkin nan sai ta zauna tana mai
harde kafa daya bisa dayar sannan tayiwa yarima
hulkas nuni da ya zauna akan wata kujera dake daf da karagar tata
ba tare da gardamar komai ba yarima hulkas ya zauna yana
mai fuskantarta
zamansa keda wuya sai yarinyar ta tafa hannunta
sai ga tambulan na zinare tare da
Kofuna sun bayyana a gaban su akan iska babu mai
rike dasu
kawai sai tambulan din ya karkata kansa ya zuba ruwan
inibi a cikin kofunan nan biyu kofi na farko ya tafi ga
yarima hulkas ya tsay dai dai hannunsa
yarima hilkas ya dubi yarinyar cikin alamun tsoro
ita kuwa sai tayi masa murmushi tace karbi mana kasha
idan so nake na zutar dakai ai tun kafin muzo nan zan cutar dakai
din
koda jin haka sai yarima hulkas ya saki jikinsa ya karbi
kofin ya kurbi ruwan inibin, a dai dai wannan lokaci ne
itama yarinyar ta kurbi nata ruwan inibin shima kuma
Al amin Ahmed Misau mai typing sai ya kurbi nashi
ruwan inibin
sannan tayi gyarar murya gami da gyara zama kuma ta
dubi yarima hulkas cikin nutsuwa ta ce yakai wannan
bako yanzu saika saurareni da kyau domin kaji labarina
... .... ..... ...
DA FARKO DAI sunana RULAIYA IBINI AMSAR IBINI WARHAS,
Kuma mahaifina ya kasance babban attajiri
a birnin kisra, amma tun mahaifiyata na dauke da cikina wata uku aka
kasheshi sannan kuma wanda ya kasheshi din yayi
yunkurin kashe mahaifiyata sau goma sha daya amma
bai samu nasara ba
ita kanta mahaifiyar tawa tayi matukar mamakin
yadda akayi take tsira da rayuwarta a duk sa adda aka kawo mata hari
caraf sai yarima hulkas ya tari numfashin Rulaiya yace
wane ne wanda ya kashe mahaifin naki kuma
saboda me ya ke son kashe mahaifiyar taki
koda jin wannan tambaya sai rulaiya tayi tsaki tace
hanzarin me kake yi haka ka bini a sannu mana
zakaji komai a cikin wannan labari da nake baka
kamar yadda na gaya maka baya a gaba dayan
birnin kisra babu attajiri da kai mahaifina tarin
dukiya da karfin arziki na fatauci, cinikin bayi da na
makaman yaki duk wani isashshen sarki dake nahiyarmu mahaifina yana
da kyakkyawar alaka dashi saboda yana yi musu matukar biyayya kuma a
duk karshen wata yana aika masa da kyautar bayi da
dukiya
don haka babu kasar da mahaifina baya zuwa don gabatar
da fataucinsa
ban da sarakai ma hatta mashahuran bokaye wadanda suka yi
shuhura a duniya suna da kyakkyawar mu amala da
mahaifina kuma suna taimakonsa da sirrinakan tsafi shi
kuma yana yi musu alheri mai yawa, akwai wadansu
amintattun rantsatstsun dakaru guda dubu daya
wadanda ke baiwa mahaifina kariya ta musamman
a duk sa adda zai yi tafiye tafiyensa na fatauci da kai ziyara izuwa ga sarakai
ko matsafa na duniya
Al amin Ahmed Misau, su dai wadannan dakaru
kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu kuma fiye da shekaru goma
baya suke yiwa mahaifina aiki ba a taba shiga masifar
da suka kasa kareshi ba ko dukiyar sa
A duniya babu abinda mahaifina yake so sama da mahaifiyata
mahaifiyata ta kasance yaga shugaban yan kasuwar
birnin hindu
kuma masana da masu bincike sun tabbatar da cewa a zamanin
da take budurwa babu wata ya mace mai
kyanta
kafin mahaifina ya sami nasarar auranta sai da yayi
fama da abokan hamayya har ma ya kusan rasa rayuwarsa
in ba don ma yana da kyakkyawan tsari ba na bokaye da tuni ya hallaka
Al amin Ahmed Misau, A duk sa adda mahaifina ya
ziyarci isassun bokayansa suna yi masa gargadi akan cewa
ya cigaba da boye amaryarsa kuma kada ya kuskura ya
rinka shiga manyan birane tare da ita, bisa wannan dalili ne
ya zamana cewa duk sadda mahaifina zaiyi tafiya
tare da mahaifiyata koyaushe fuskart da jikinta
a lullube suke sosai ta yadda mutum ba zai iya ganin
siffarta da kamanninta ba
kuma in dai wani babban birni za a shiga to saidai a
yada zango a bayan gari in yaso shi da tsirarun dakarunsa
tare da hajarsu su shiga cikin garin ya bar mahaifiyata a
hannun sauran dakarun nasa, A cikin irin wannan yanayi
ne watarana mahaifina ya
tunkari birnin wani gawurtaccen sarki wanda ake kira da suna
SARKI SHARDAS shi
dai wannan sarki anyi ittifakin cewa a duniya kaf
babu wani jarumi wanda ya fishi karfin damtse iya
yaki da kuma karfin sihirin tsafi, shi kansa mahaifina
ba a son ransa zaije garin wannan sarki ba sai don kawai
saboda ya amsa gayyatarsa ne domin gaba dayan mashahuran
attajiran duniya sarki shardas ya gayyata domin ayi
gasar siyen wani gida na musamman wanda aka
ginashi a tsakiyar wani kogi a wannan lokaci shi dai
wannan gida an ginashi ne da zallan hadin duwatsu uku,
wato lu'u lu'u zinare jauhar da zubarjadu
shi dai gidan ya sami shekaru goma sha biyu da ginawa
amma ba a taba shigarsa ba, a tsawon wadannan shekaru
sarki shardas yana tallaka gidan ne ga manyan sarakunan
duniya da manyan fatake yana cika baki akan cewa
tun daga farkon wanzuwar duniya kawo iyanzu lokacin
ba a taba gina gidan da yayi wannan gida nasa kyau, kawatuwa da kuma tsari ba
don haka a ranar da za a budeshi an yiwa kowa izinin yaje ya
shiga ciki domin ya baiwa idanunsa abinci, kuma wanda duk ya sayi gidan da
farashi mafi tsoka shine zai mallakeshi, kuma shi
kansa sarki shardas din ya shiga gasar siyen wannan
gida nasa
kafin sarko ko Attajiri ya shiga wannan gasa sai ya ajiye
dinare miliyan daya tukunna
a cewarsa wai hakan shine shaidar cewa ya isa
ya shiga wannan gasa, an ce a haka ma sarki shardas
ya tara miliyoyin dinaren da bai taba zaton zai
Samu ba, A tunanin sarki shardas zai yi amfani da
wannan gasa ne ya talauta gaba dayan sarakunan
nahiyar da attajirai domin ya kasance duk karfin
arzikinsu ya dawo hannunsa, shi kuwa wannan gida da aka gina
akan tsakiyar kogi sai da aka shafe shekaru goma sha shida
ana gininsa
ba wai mutane ba hatta aljanu tsegumin gidan suke
suna ta yadashi a duniya, lokacin da aikin ginin
yayi nisa sai da sarki shardas ya sare, domin gani yayi
tattalin arzikinsa na neman karyea, bisa dole ya kara ninka harajin da mutane ke
biya a kasarsa kuma ya tsananta farautar bayi da kai
harin sumame ana kwace dukiyoyin jama a wata nahiyar ana maishe su bayi
A haka dai aka samu aka kammala wannan kasaitaccen gida
na gaban kwatance, bayan an kammala ginin gidan ne
sarki shardas yasa rana ta wannan gasa wacce a ranar za 'a
bude wannan
gida
wohoho tun kafin ranar tayi da tsawon sati hudu
birnin nasa ya cika ya tumbatsa da baki daga ko'ina
na duniya, yazamana cewa ko ruwan sha mutum ke
siyarwa a garin yana samun kudade masu yawa a
wannan lokaci kudin shiga birnin ma da aka samu ba'a
taba samun kamarsu ba
Al amarin mahaifina kuwa wato Attajiri Amsar............
Wow Domin jin yadda zata kasance mu hadu a part na gaba
amma kafinnan
nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko A square
nake cewa mu zama lafiya
.
[4/25, 8:18 AM] Al Amin Gysn: TSATSUBA
Littafi Na Takwas (8)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
AL'AMARIN MAHAIFINA KUWA WATO ATTAJIRI AMSAR, a
cikin daji ya yada sansani da tazarar kwana uku
a sannan ne ya debi dakaru dari biyu kacal ya bar
ragowar dari takwas domin suyi gadin mahaifiyata
koda yazo zai yi sallama da mahaifiyata sai ta
fashe da kuka tace yakai mijina ban taba rabuwa dakai ba
tsawon yini guda amma yanzu gashi zaka tafi halartar
wannan gasa har tsawon kwanaki bakwai lallai zan
kasance a cikin kewarka da begenka,
ka sani cewa na sami labari cewa wannan gida da sarki
shardas ya gina a duk fadin duniya a yanzu babu
kamarsa a kyau da kawatuwa lallai ina yi maka
fata da addu ar ka mallakeshi, kuma lallai ina son
naga wannan gida da idanuna koda kuwa ba zan
sami damar shiga cikin sa ba
sa adda mahaifyata tazo nan a jawabinta sai nan take
idanun mahaifina suka ciko da kwallah ya dubeta cikin alamun
tsananin takaici
yace ki gafarceni ya masoyiyata kiyi sani cewa wannan
ne karo na farko da kika tambayeni abinda ba zan iya
baki shiba a cikin wannan
duniya
ki sani cewa idan na kuskura na shigar da ke cikin
wannan birnin karshen zamana dake yazo bare ma
har na kaiki kiga wannan kasaitaccen gida wanda za ayi gasa a kansa, wannan
shine kashedin da bokayena suke yi mini idan kuma
kina son mu rabu ne to shikenan sai na kaiki kiga
wannan gida
koda jin wannan batu sai mahaifiyata ta rungume attajiri amsar ta
fashe da matsanancin kuka tana mai kankameshi a
kirjinta tace ai ko duniyar nan kaf za a bani in dai za a
rabani dakai bana bukatarta, koda jin haka sai farin ciki ya
lullube mahaifina
Al amin Ahmed Misau, sai da sukadan jima a kankame
da juna sannan ya janye jikinsa daga cikin nata sukayi
sallama ya hau kan dokinsa, kafin ya tafi sai da ya dada
jan kunnen dakarun nasa su dari takwasa da zasu yi gadinta
da kuma kuyangi uku da zasu yi mata hidima yace
lallai su tabbatar da cewar wani abu bai kusanceta
ba bare ya cutar da ita
nan dai mahaifina attajiri amsar tare da dakaru dari
biyu suka nufi cikin birnin sarki shardas , mahaifiyata
da sauran jama arsa suka bisu da kallo har sai da
suka ga sun kule
'' '' ''
BIRNIN ya ciki ya tumbatsa da al uma duk inda ka duba
babu abinda zaka gani face kawunan bil adama
rututu babu masakar tsinke, sai da ta kai cewa an rasa
gidaje na haya inda ake saukar baki, dole jama a
suka rinka kwana a kasuwa wasu ma a gefen gari suka
rinka kafa tantuna sai dai siye da siyarwa ya shigo dasu
cikin birnin
gidan sarautar sarki shardas kuwa ya cika da manyan
sarakuna manyan attajirai manyan bokaye da
manyan yarumai kuma kowannansu an bashi masauki mai daraja kuma
an girmamashi
A rayuwar sarki shardas yana son zama tare da wadannan
mutane guda hudu wato sarakai, attajirai bokaye da
jarumai
wato Mu ke nan ehm Al amin nake, har izuwa
safiyar ranar da za ayi wannan gasa hankalin sarki shardas bai
gama kwanciya ba duk da cewa shi ya tara
dukkanin sarakunan nahiyar da kuma amsu gayyata
Al amarin daya sa wazirin sarki shardas ya fahimci
cewar sarkin nasu yana cikin wata damuwa don, haka sai
ya dubeshi cikin girmamawa yace wai shin menene yake
damunka ?
Naga sai kallon kofar fada kake yi shin akwai wanda kake
son ganin zuwansa ne, sarki shardas yayi ajiyar
zuciya sannan yace ai banga sarkin attajiran ba attajiri
Amsar ibn Warhas,
anya kuwa zai amsa wannan gayyata tawa, koda jin
wannan batu sai waziri ya dafe kirjinsa kuma ya
zazzaro idanu yace, haba ya sarkin sarakuna , kaine fa zaki
uban dawa kuma kaine dodon maza sa gudu maganin
ki gudu
yanzu kai a tunaninka akwai wani daya isa a wannan
duniya
da zai ki amsa gayyatarka, kome mutm yake takama
dashi kafishi, kuma duk wanda yaja dakai sai yakai
kasa
sarakuna nawa ne suka mutu a dalilin bakincikin da ka
kunsa musu
bokaye nawa ne suka jarraba karfin tsafinsu akanka
suka mutu
Attajirai masu tarin dukiya nawa ne ka talautar dasu
ai ina tabbatar maka da cewar ajali ne kadai zai
hana attajiri amsar halartar wannan gayyata taka
kuma ko don ma ya nuna matsayinsa akan sauran attajirai dolene ya amsa gayyatar ka
amma abin tambayar shine wai shin menene dalilin da yasa
ka damu da zuwan attajiri Amsar ibini warhas ?
Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas yayi dan
guntun murmushi sannan yace lallai ina son attajiri
amsar yazo wannan gasa saboda sai yafi kowa siyan
wannan gida nawa da daraja, to amma fa ina tsoron
abu guda daya
shin baka ganin cewa yana da kudin da zai iya siyen
wannan gida nawa har ni kuma ya hanani mallakarsa ?
Waziri ya gyada kai yace haba ya shugabana yanzu ashe
akwai attajirin da zai fika kudi a wannan nahiya tamu
ai a ganina ko nawa attajiri amsar ya siyi wannan gida kai
kuma sai ka kara kudinka ko ka ninka akan nasa
sau talatin tunka ka san cewa babu asara a cikin aikata
hakan ka tuna fa cewa daga cikin dokar wannan gasa shine
duk kudin da mutum ya taya wannan gidan ba za a dawo
masa dasu ba
Al amin Ahmed Misau, kaga kenan komai yawan kudaden
da aka tara naka ne kai kadai, koda jin
wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki shardas ya
kama yin murmushin murna yana mai cigaba da kallon
bakin kofar fada sannan ya dubi wazirinsa yace gaba
dayan manyan sarakuna da attajiran da na gayyata
sun iso tare da iyalansu tun tsawon yan kwanaki
kafin zuwan wannan rana ta yau me ya sa shi attajiri
amsar baizo da wuri ba bare da iyalansa alhalin na
dade ina son naga matarsa saboda naji ance agaba
dayan birnin hindu babu mai kyanta, abinda yake bani
mamaki shine duk karfin shirin nan nawa na tsafi na
kasa ganin hoton siffar matar tasa a cikin madubin
tsafina kuma a iya bincikena nakasa ganin ranar da zan
ganta
bisa wannan daliline yasa na ke dan shakkar al amarin
attajiri amsar ibn warhas, domin lokacin dana fara zurfafa
a cikin binciken sirrinsa sai na gano cewa yana samun
kariya ne daga wani takadarin aljani wanda ni
kaina ban sanshi ba kuma na kasa gano ko waye shi
hatta bokana abin dogarona ya kasa gano min aljanin
da yake baiwa attajiri amsar kariya, sarki shardas na zuwa dai dai nan
a jawabinsa
kwatsam sai ga attajiri amsar ibn warhas ya shigo cikin
fadar dakaru dari biyu kacal nakewaye dashi
Da shigowar attajiri amsar cikin fadar sai gaba dayam
jama ar dake wajan suka mimmike tsaye suka rinka dukawa suna gaishe da
attajiri amsar saboda kwarjininsa tamkar ya kasance
wani babban sarki, tufafin dake jikinsa ma babu wani
basarake a wajan daya sanya mai kyansa da tsadarsu
saini Al amin Ahmed Misau hatta shi kansa sarki
shardas din kuwa
kai ko mutum bai san attajiri amsar ibn warhas ba yana ganinsa dole ne ya girmama
shi saboda tsabar kamalarsa da kwarjininsa
ko shi kansa sarki shardas wanda kowa ke tsoronsa da
yi masa biyayyar dole ba shi da irin wannan kwarjini
da kamala na attajiri amsar don hatta manyan fadawan
sarki shardas basu san sa adda suka rinka rugawa izuwa
ga attajiri amsar suna kama hannunsa suna sumbata ba
haka ma sauran sarakunan da ke cikin fadar domin kowa
gani yake kamar idan har ya sami nasarar sumbatar hannun
attajiri amsar ya sami tabarrakin da shima zai zamo gagarumin
attajiri kamar attajiri amsar din, koda sarki shardas
yaga yadda ake girmama attajiri amsar sai ya kamu da
tsananin kishi gami da matukar baki ciki ya fara
tunanin cewa babu abinda yafi attajiri amsar dashi face
jarumtaka, tunda yana da mace mai kyan da bashi da
kamarta kuma yana da dukiyar da wata kila tafi tasa yawa
bayan attajiri amsar ya gama gaisawa da manyan
mutane wadanda suka yi ta shan gabansa suna
hanashi zuwa wajan sarki shardas sai ya kukuta da kyar
ya isa inda sarki shardas ke zaune bisa karagar mulki
yana zuwa daf dashi sai ya zube kasa wanwar ya kwashi
gaisuwa tamkar zaiyi masa sujjada don girmamawa
al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan
shi kuwa sarki shardas sai farin ciki ya lullubeshi yaji
kansa yayi nauyi don haka sai ya mike tsaye daga kan
karagar sa ya taka matattakalar ya sauko har kasa har
gaban attajiri amsar ya kama kafadun sa ya tasheshi
tsaye ya rungumeshi cikin tsananin farin ciki tamkar wanda yaga dan uwansa na jini
sannan kuma sai ya kama hannun sa ya jashi zuwa kan karagar
mulki suka zauna tare akan karagar, Al amarin da yai
matukar baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin sarki shardas ya girmama
wani mutum ba kamar haka yadda ya yiwa attajiri amsar
nan take sarki shardas ya bada umarni kuyangi suka shigo cikin fadar dauke da
abinci da abin sha irir iri na musamman irin wanda ba a taba kawowa ba tun daga
ranar da aka fara saukar baki, sai da aka gama ciye ciye da shaye
shaye
ya zamana cewa kowa ya sami nustuwa sannan sarki shardas ya mike tsaye a lokacin
da fadar tayi tsir tamkar mutuwa ta gifta yayi gyaran murya
yace
yaku manyan baki kuyi sani cewa yanzu taro ya cika
tunda sarkin Attajirai amsar ibn warhas ya iso
saboda haka yanzu ba tare da bata lokaci ba zamu
dunguma gaba daya mu tafi izuwa inda wannan gida
yake wanda nayiwa lakabi da suna
DARUL DAULAT !
Duk wanda ya san zai shiga wannan gasa to ya
tafi da dukkan shirinsa amma yanzu za a fadi dokoki
uku na shiga wannan gasa, doka ta farko itace dole ne kowanne
sarko ko kowanne attajiri
ko boka ko jarumin da ya amsa gayyata ya shiga wannan gasa
kuma duk kudin da
ya zuba a gasar ba za a dawo masa dasu ba walau yayi
nasara ko bai yi ba
doka ta biyu itace idan aka shiga cikin wannan gidan gasa
babu wanda zai fito har sai an kammala kuma kowa ya
kwantar da hankalinsa domin an tanaji masauki da isashshen
abincin da kowa zaici har a kammala
Al amin Ahmed Misau, doka ta uku wacce itace ta karshe
itace duk wanda ya lashe wannan gasa dole ne ya baro
kasarsa ya dawo wannan gida da zama tare da iyalansa
har izuwa karshen rayuwarsa, koda sarki shardas
yazo nan a zancensa sai hankalin gaba dayan masu
gasar ya dugunzuma ainun musamman attajiri
Amsar
domin wannan doka ta karshe ba karamar tayar masa
da hankali tayi ba
Nan take ba tare da bata lokaci ba aka fito daga cikin
fada aka debo jakunkunan dinare aka loada akan dawakai
da rakuma da alfadarai sarki shardas ne da kansa ya
jagoranci gaba dayan yan gasar kowa dakarunsa
Na bashi tsaro da kariya aka nufi bakin kogi inda gidan
Darul Daulat yake
sauran jama ar gari kuwa sai da wannan zuga tayi gaba
da tsawon rabin sa'a sannan aka sa dakaru suka yi
musu rakiya
tafiyar kusan rabin sa a akayi aka iso bakin katon
kogin dake bayan gari tun daga nesa hasken gidan
darul daulat ya fara dallare idanun mutane kuma
tsananin girman gidan da kyawunsa ya dimauta kowa hatta su attajiri amsar
kuwa duk da cewa gidan a can nesa yake a tsakiyar
kogi amma kowa ya firgita da ganin irin gini da
akayi masa
a bakin tekun an ajiye manyan jiragen ruwa sama da
guda dari wadanda za a shiga a ketare kogin a isa gidan
na sarakai , attajirai da wadanda suka isa sannan kuma akwai
kwale kwale kimanin guda
dubu na talakawa
da zuwan su sarki shardas bakin tekun sai kowa ya sauka
daga kan dokinsa suka rinka shiga cikin jirgin ruwan
jirgin sarakai daban haka mana na attajirai da sauran
bokaye da jarumai
ko kyakkyawan motsi sarki shardas baya barin
attajiri amsar yayi ma ana baya yarda yayi nesa dashi
don gudun kada wani tsautsayi ya rabasu lokacin da
jiragen ruwan suka yi nisa a cikin kogin suka kusanci
tsibirin da aka gina gidan darul daulat sai kowa ya sake
cika da tsakanin mamaki ba komai ba sai domin ganin tsananin
girman nasa ya kai rabin birnin gaba daya na
sarki shardas
abin da yafi daurewa mutane kai shine' wai shin ta yaya
aka iya gina wannan gagarumin gida ? Tabbas aikin
ginin wannan gida yafi karfin ace mutane ne sukayi
shi dai sai aljanu aljanun ma sai dai idan wadanda suka
gina birnin farisa ne suka yi ginin wannan gida
nan fa kowa ya zama cikakken dan kauye aka rinka
wangame baki ana kallo wasu ma basu san sa adda suka fara
dalalar da yawu ba
sai da gaba dayan jiragen suka iso bakin gabar kogin
daf da kofar gidan sannan kowa ya fito daga cikin jirgin
aka bi sarki shardas a baya, ita kanta kofar wannan
gida inda za a cireta a baiwa mutum ta isheshi
gudanar da sauran rayuwarsa ta duniya kai Madaki Al amin Ahmed Misau Sunana
domin jarine babba saboda anyi tane da zallan dutsen
lu u lu u mai tsawo da kaurin gaske gami da fadi
inda karti dubu zasu taru ba zasu iya daga kofar sama ba
saboda nauyinta su kansu aljanun da suka kerata sai da
aka zabo majiya karfi arba in sannan suka iya
dagata sama suka kafata a jikin ginin, nan take
sarki shardas ya zaro wata kuba ta zinare ya mitsitsiya kuma
siririya ya zurata a cikin kofar mukulli, shigar kubar
keda wuya sai aka ji sakata na zare kansu, wani
zagayayyen mukulli mai kauri da tudu ya rinka zagaya kansa
a tsakiyar kofar har sai da ya kewaya sau goma sha
biyu sannan sakatun suka gama zarewa duka, take
kofar ta bude wanwar da kanta, a dai dai wannan lokaci
ne sarki shardas ya waigo cikin murmushi ya dubi gaba dayan yan gasar yace
duk wanda ya lashe wannan gasa shizan damkawa
kubar wannan gida, yana gama fadin haka sai ya zura
hannunsa cikin kofar mukullin ya zare kubar ya zurata
a cikin Aljihun wandonsa sannan ya kama hannun
attajiri Amsar ibn warhas yaja shi suka kunna kai izuwa
cikin wannan gida na darul daulat, take suma sauran, sarakai
Attajirai da jaruman gasar suka rufa musu baya
Wohoho !! An dade ana bautawa kasa anyi mata ado da
dukiya !
Duk wanda ya sanya kafarsa ya taka lu'u lu'un da aka
shinfida a kasan gidan ya ga yadda ko ina ya kasance
fes fes ! Babu ko kura ko guda daya bare yanah, sai
ya cika da al'ajabi kai kace kullum akwai hadimai sama da
miliyan goma masu share ko ina da gogewa alhalin
babu wata halitta guda daya mai rai a ciki
ba tare da wani bata lokaci ba sarki shardas ya wuce
kai tsaye izuwa cikin wani babban falo na gidan wanda ya
ninka fadarsa sau goma a girma da kawatuwa...
Nima kuma sai nabishi a bayaaaa.
Al amin Ahmed Misau
zan dakata Anan
saikuma Allah ya kaimu
Gobe zamu cigaba
Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Inkiya
Guyson Ko A square
Dan garin Kaduna
[4/25, 8:18 AM] Al Amin Gysn: TSATSUBA
Littafi Na Takwas (8)
Part D.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
BA TARE DA WANI BATA LOKACI BA SARKI SHARDAS YA WUCE
KAI TSAYE IZUWA CIKIN WANI BABBAN FALO NA GIDAN
WANDA YA NINKA FADARSA SAU GOMA A GIRMA DA KAWATUWA
hatta kujerun da shimfidar dake cikinsa babu wanda ya
taba ganin makamantansu, duk yawan jama ar da suka
halarci wannan gasa suna shiga cikin wannan falo sai
suka zama yan kadan tamkar an sanya kwayar gero
guda daya jal akan faranti, har izuwa wannan lokaci
sarki shardas na rike da hannun attajiri amsar ibn warhas,
shi kuma attajiri Amsar yana dogara wani dan karamin
kwagiri na zinare dake hannunsa, kwagiri ne na zinare
wanda aka kawatashi da adon sarauta, irin sane
kwagirin da manyan sarakai ke dogarawa yayin da suke
tafiya don kawata kwalliyarsu, kai tsaye sarki shardas
yaja attajiri amsar suka je suka zauna akan wata
luntsumemiyar doguwar kujera mai daraja, shi kuwa
wazirin sarki shardas tare da sauran fadawansa
sai suka rinka kai sauran manyan baki izuwa mazaunin
da ya dace dasu
Kafin kowa ya zauna sauran talakawa sun iso a cikin
kwale kwale dakaru na shigowa dasu suma ana zaunar
dasu a inda ya dace duk a cikin wannan babban falo
sai da kowa ya gama zama sannan sarki shardas
ya mike tsaye yayi jawabin farinciki na ganin wannan
rana gami da godiya ga dukkanin manyan baki da suka
amsa gayyata sannan yace yaku jama ata ina mai sanar
daku cewa inda zan jagoranceku mu zagaya cikin wannan
gida domin muga ko ina da ina kuma muga duk irin
daular da aka shirya a cikinsa da sai mun shafe a kalla
tsawon kwaanaki bakwai bamu gama shiga kowanne
daki da kowacce fada ba
A cikin wannan gida na darul daulat akawai dakuna
guda casa'in da tara
sannan akwai fadoji guda arba in kowacce fada guda ta
ninka fadata sau talatin a girma, akwai kasuwa da asibiti
a cikin wannan gida kuma akwai gidajen gona guda arba in
da bakwai
Sannan lambu na shakatawa kala tamanin da bakwai
Al amin Ahmed Misau , duk wanda ya lashe wannan gasa
ya mallaki wannan gida to a ranar da ya tare a cikinsa
ne hadiman Aljanu dubu dari tara da casa in da tara
zasu fara kular masa da gidan, sauran hadimai na aljanu kuwa ya nemo iya adadin
da yake bukata
Yanzu take ba tare da bata wani lokaci ba zamu fara
wannan gasa kuma ta kaina za a fara don haka ni na
bude wannan ciniki da dinare miliyan uku
ga kudina lakadan yanzu zan dankasu a hannun
alkalan Kasa !!?
Sarki shardas na gama fadin hakan sai ya tafa hannunsa
nan take hadimai sukaje can wajen kofar gidan
suka fara dauko buhunhunan dinare daga kan dawakai
da rakuma na sarki shardas suna shigowa dasu suna zubesu
a tsakiyar wannan babban falo har sai da suka ajiye jaka
talatin wato kowacce jaka na daure da dinare dubu
dari
koda ganin wannan al amari sai sarakai da attajirai
suka kama yin murmushi saboda sun raina kudin da sarki
shardas ya fara bude wannan gasa dasu duk kuwa da cewa
kudade ne masu yawan gaske sun ishi talaka iya rayuwarsa
koda sarki shardas yaga yadda sarakai da attajirai keyin
murmushin murna
don ganin suna da ninkin kudin da aka fara gasar dasu sau da yawa sai yayi
dariyar mugunta a cikin ransa yace a zuciyarsa
Uhm ! Ai sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo
muje zuwa wai mahaukaci yahau kura, tsawon yan dakiku
sai falon yayi tsit ba a sami wanda ya sake taya gidan
ba har sai da sarki shardas ya sake budar baki yace, wai shin
babu yan kasuwa ne a wannan waje ? Koda jin wannan tambaya sai sarkin birnin
misra yace ya ninka wannan kudin da sarki shardas ya siyi gidan sun koma dinare
miliyn dubu shida
take aka kawo kudin aka zube a gaban jama a
daga nan ne fa kowa ya sami bakin magana sai da
sarakai da attajirai dari uku suka ninka kudin kuma aka
kawo kudaden aka zube a tsakiyar fadar ya zamana cewa
yan gasar mutum dubu uku da doriya gaba dayansu
kowa ya zuba kudinsa saura mutum daya ne jal bai sa
ba
ba wani bane fwannan mutum guda da ya rage ba
face ATTAJIRI AMSAR IBN WARHAS wanda har izuwa
wannan lokaci ba a daina kawo rakuma da dawakan
dake dauke da dukiyarsa izuwa bakin kofar wannan gida
na darul daulat ba
Kaji Manya Hm dama ance ta safe ta yara ce Ai Al amin
amma kowa an gama kawo tasa dukiyar sai ta sarki
shardas take ta bayan tasa, kafin a gama shigo da dukiyar
wacce ta ninka duk ta sauran attajiran gasar dare ya
raba
a sannan ne fa gaba dayan sarakunan da attajiran
suka tsorata ainun da al amarin Attajiri amsar
suka fara tunanin cewa Aljanu ne ke sato dukiya daga
bangarorin duniya suna kawo masa, haka kuma a sannan ne
suka tsinke da al amarin sarki shardas ma domin har a
sannan shima ba a gama shigowa da dukiyar daya tana da ba don wannan gasa
koda sarki shardas ya fahimci cewa dare ya raba kuma
kowa ya gaji ana jin yunwa da barci sai ya mike
tsaye yace to a halin yanzu dai babu wanda yafi attajiri
amsar farashi na wannan gasa, kuma tunda jama asun gaji
kuma gashi dare ya raba to za a tsayar da wannan gasa domin akai kowa masaukinsa
yaci abinci ya kwanta yayi barci sai gobe da safe
a cigaba da wannan gasa
A zagaye na biyu
Koda gama fadin hakan sai fadawan sarki shardas
suka yiwa manyan baki jagora aka kai kowa masaukinsa duk
wanda ya shiga falonsa sai dai ya iske abinci da abin sha
a shirye yana jiransa na kasaita kuma kala kala
wani kalar abincin ma mutum bai taba ganin irinsa ba
da idanunsa
Al amarin daya bai wa kowa mamaki kenan kuma ko ya
kwayar abinci daya ta dira a kasa sai dai aga ta bace bat
Don kada a sawa wajen datti kai da gani ka san cewa
wannan aiki ne na mutanen boye, bayan sarakuna da
attajirai sun ci sun sha sai kowa ya zauna tare da jama arsa
aka shiga tsegumi ana tattaunawa akan gasar inda kowacce
jama a ke baiwa shugabanta shawara akan cewa kada
ya kara zuba kudinsa a cikin wannan kasa tunda Al amarin ya shallake tunanin
mutum
Duk sarkin da ya ce zai fara zuba kudi ko attajiri
to lallai
karayar arzikinsa tazo, nan take kowanne sarki ya gama
yanke hukunci a ransa cewa sai dai ya zama dan kallo
a wannan gasa yabar wa manyan giwaye biyu dama kuma kudin
da ya zuba a yanzu ya bar su a matsayin asara da
kaddara
Al amin Ahmed Misau, Kashi gari kuwa da sassafe aka
sake haduwa a wannan babban falo na cikin wannan
gidan darul daulat
sauran jama ar gari ma yan kallo duk a wajen kofar gidan suka
kafa tantuna suka kwana don kada wannan gagarumar gasa ta wuce su
bayan dakin gasar ya gama cika ga tarin jakunkunan
dinare jibge a tsakiya sai gaba dayan sarakunan da
attajiran gasar suka sanar da alkalan gasar cewa su sun janye sun barwa sarki
shardas da attajiri amsar sun sallama cewar ba zasu iya ba
koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe
da dariyar mugunta gami da farinciki saboda ganin
cewa gaba dayan wadannan makudan kudaden
da yan gasar suka zuba sun yi asararsu kuma shine
zai mallake su
a banza.
Sannan kuma har a can karkashin zuciyarsa yana ganin
cewa lallai shine zai lashe wannan gasa saboda ya yarda
da dukkan shirin da yai akan gasar da kuma tanadin da
yayi na tsawon shekaru goma sha, ba tare da wata
fargaba ba sai sarki shardas ya dubi Alkalan gasar cikin takama
da jin izza yace
na linka kudin da attajiri amsar ya siyi wannan gida
a yau
koda jin wannan batu sai falon ya rude da shewar jama a
aka shiga yiwa sarki shardas kirari ana kodashi, saboda
ana ganin cewa ya gama lashe wannan gasa domin attajiri
Amsar ba zai iya linka wannan kudin ba
nan take aka fara shigo da kudin da sarki shardas ya siyi wannan
gida adadin ninkin wadanda ke zube a wajen saboda yawan wadannan kudade sai da
aka yini ana shigo dasu sannan aka kammala
duk yawan dabbobin da suka dauko kudaden na sarki
shardas sai da kaso daya da rabin dukiyar cikin uku
ya kare
Shi kansa attajiri amsar yayi mamakin yadda akayi
sarki shardas yayi wannan kundunbala
shi kuwa sarki shardas sai ya kamu da tsananin farinciki
ya rinka washe baki saboda gani yake kamar attajiri
amsar ba zai iya sake ninka wadannan kudade ba sai
dai ya hakura da gasar
tsawon dakiku alkalan gasa suna tambayar attajiri amsar
shin zai iya ninka wadannan kudade ko kuwa ya sallama
amma sai yai shiru ya kasa cewa komai saboda jinjina
wautar sarki shardas yake yi a cikin ransa
har alkalan gasar sun mike tsaye zasu fadi jawabin cewa
gida ya zama na sarki shardas sai attajiri amsar ya tari
numfashinsu yace na sake ninka wannan kudi wanda sarki
shardas ya siyi wannan gida
Koda jin haka sai gaba dayan jama ar da ke wajan suka kame
kAm ! Inji Gwanja Haha Al amin Ahmed Misau Nake
Kamar Gumaka kowa ya wangame baki tamkar
matattun kadoji
a wajen saboda tsananin mamakin kasassabar da attajiri amsar yayi, nan take
kuwa aka fara shigowa da jakunkunan kudin har sai da aka gaji , lissafi ya kwace
musu a lokacin da zakara ya fara carah sakamakon wanzuwar
asubahi
Duk da haka a kofar wannan gida na darul daulat dawakai
da rakuman dake dauke da jakunkunan dukiyar
Attajiri Amsar sai ketaro kogin ake yi dasu
bisa dole alkalan gasar suka dakatar da gasar domin
kowa yaje ya kwanta yayi barci
nan fa jama a suka watse kowa ya tafi
yana fadin albarkacin bakinsa
wasu suka rinka cewa
' duk yadda akayi wannan dukiya ta attajiri amsar dukiya ce
ta iska kawai wato aljanu ne ke kawo kudin
Wasu kuma suka rinka cewa
' to ai shima sarki shardas din ai tasa dukiyar ta iska ce
tunda ba a gama kureshi ba
nan fa jama a suka yi ta dokin ganin gari ya waye ayi zagayen
karshe na wannan gagarumar
gasa domin aga wanda zai yi nasara tsakanin sarki
shardas da attajiri Amsar
'' '' ''
CIKIN farin ciki da kwanciyar hankali attajiri
ansar ya je masaukinsa ya kwanta yana mai ayyana wa a ransa
cewa lallai idan gari ya waye aka dawo zagayen karshe
na wannan gasa shine zai yi nasara, koda ya kwanta akan
luntsumemen gadon dakin
fuskarsa cike da murmushi sai tunanin mahaifiyata
ya fado masa ya tuna cewa yau fa kusan kwanaki biyar
ke nan fa rabon da suga fuskokin junansu
nan take yaji wani irin bakin ciki yayi
katutu a cikin
ransa amma daya tuna cewa yana daf da lashe wannan
gasa sai zuciyarsa tayi fari fat kuma idanunsa suka fara
kekashewa ya
Fada cikin sabon kogin tunani inda ya rinka ganin
su a cikin wannan gida na darul daulat wato shi da mahaifiyata suna ta kewayawa
suna shiga daki daki da ko ina na cikin gidan yana nuna mata irin gagarumar daular da
aka shirya a cikin gidan a haka ne barci ya sace shi bai sani
ba
-- -- --
AL AMARIN sarki shardas kuwa tun da aka baro dakin
gasa ko zama kasawa yayi bare ya kwanta yayi barcin
kawai sai ya kama zarya a cikin dakin yana ta ciza yatsa
da lebe yana tsaki gami da mamaki da takaici
Zuciyarsa kuwa sai ta kama tafarfasa kamar zata
kone
saboda tsananin bakin ciki ya fara tunanin cewa lallai a
gobe idan gari ya waye watan jin kunyarsa zai
tsaya muddin aka yi zagayen karshe na wannan gasa
domin tun a daren jiyan ne dawakai da rakuman dake dauke da dukiyarsa
suka daina ketaro kogin domin sun kare, amma na attajiri
amsar cigaba suke da zuwa tamkar ba zasu kare ba
tabbas idan ya ninka dukiyar da attajiri amsar ya sayi wannan gida abu ne ma wuyaci kudin
nasa da suka rage sukai adadin hakan
koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai ya zura hannu
a cikin Aljihun Alkyabbar sa ya fiddo madubin
tsafinsa ya shiga sabon bincike
Yana cikin wannan bincike ne yaga bokansa ya baiyyana
tsulumm
a gabansa yana mai kyalkyala dariya Al amin Ahmed Misau, cikin fushi
sarki shardas ya dubi bokan ya ce sabo da me tuntuni zaka
tafi ka bar ni a cikin wannan zullumi da fargaba ko kuwa
so kake daraja ta ta zube a idon duniya
kuma arzikina ya karye ?? Koda jin wannan tambayoyi
sai bokan ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin dariyar
sannan ya matso daf
da sarki shardas yayi masa rada a kunne
tun kafin gari ya waye gari yayi haske, falon gasa ya cika ya batse da jama akowa ya hallara a wajan babu wanda ake jira
face mutum daya jal
ba wani bane ba ake jira face sarki shardas da kanshi
Al amarin da yabaiwa kowa mamaki kenan aka rasa dalilin da yasa
ya makara
Ashe sarki shardas kwanciya yayi yana ta shara barci
abinsa
shi kadai ne ya rama bashin barcinsa na jiya da
daddare sai kuma attajiri amsar wanda barcin ya
daukeshi yana tsakiyar tunanin mahaifiyata, har sai
da hasken rana ya fito sosai sannan aka ji bugun
tambura gami da bushin algaita alamar cewa ga sarki
Shardas nan zai shigo falon gasar, nan fa dakin
gasar ya kaure da shewar jama a gami da ihu da tafi
jim kadan sai ga sarki shardas ya shigo cikin falon
cikin ado na kwatance kuma fuskarsa cike da annuri
dakarun dake bashi tsaro na take masa baya
nan fa kowa ya mike tsaye don girmamashi har sai da ya je ya zauna a kusa
da attajiri amsar sannan kowa dake falon ya zauna
ba tare da bata lokaci ba mai gabatar da gasar ya fara jawabi
yana mai cewa yaku jama akamr
yadda kuka sani cewa ayau ne
za ayi zagayen wannan
gasa na karshe don haka yanzu zamu ji daga bakin
sarkinmu mai daraja shin zai iya ninka kudin da
attajiri amsar ya sayi wannan gida nasa, ance dai waka
a bakin mai ita tafi dadi don haka mai wuri yazo sai
mai tabarma ya nade
koda gama fadin hakan sai mai gabatar da jawabin ya
koma mazauninsa
take sarki shardas ya mike tsaye ya dubi gaba dayan
taron jamar dake cikin falon cikin murmushi
maimakon yace wani abu sai ya juya ya kama hannayen
attajiri amsar ya tasheshi tsaye ya dubeshi cikin
murmushi a lokacin da falon gasar yayi tsit
tamkar babu mai rai a cikinsa
yace yakai abokina ina tayaka farinciki ka lashe wannan
gagarumar gasa daga yau wannan gida na darul daulat ya zama naka
kuma mallakinka
koda jin wannan batu sai falon gasar ya rude da shewa da ihun jama a
shi kuwa attajiri amsar sai ya rungume sarki
shardas cikin tsananin farinciki mara misaltuwa yana mai yi masa godiya
ba zato ba tsammani sai sarki shardas ya yi wuf
ya fisge kwagirin dake
hannun attajiri amsar sannan ya zato wata wukar tsafi
daga cikin alkyabbarsa ya lumawa attajiri Amsar
ita a ciki
Nan take wukar tsafin ta lume a cikin attajiri
amsar jini yai
tsartuwa
Attajiri Amsar ya kwallah kara tare da sulalewa
kasa yana kakarin mutuwa, Al amarin da ya razana
kowa ke nan a dakin gasar aka yi tsit ana kyarmar jiki
saboda tsabar tsoro
shi kuwa sarki shardas sai ya dubi dakarunsa ya daka
musu tsawa yace
maza ku ruga izuwa can bayan gari tafiyar kwana uku
zaku riski matar attajiri amsar tare da dakarun dake
tsaronta
lallai ku kashe gaba dayan dakarun ita kuma matar tasa kuzo min da ita
nan a raye
koda jin wannan batu sai dubunnan dakarun
suka ruga waje da gudu suka shiga cikin jiragen ruwa
suka ketare kogin
A wannan lokacin falon gasar yayi tsit tamkar babu
mutum daya mai numfashi a cikinsa, ba ma
attajirai, bokaye da jarumai dake wajen ba hatta sarakunan
jikinsu karkarwa yake yi sabo da tsananin tsoron sarki
shardas !!
Kai Nima Kaina Al amin Ahmed Misau, Saboda tsananin
tsoro yasa nakasa ci gaba,
SHIN ATTAJIRI AMSAR YANA MUTUWA SAKAMAKON
SUKAN DA SARKI SHARDAS YAYI MASA??
.
YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI GAMA LASHE JARRABAWAR DA
ALJANI ARWASUL MASADUR YAKE MASA HAR YA TAIMAKA
MASA YA MALLAKI HULAR LAMSARA ?
.
TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE
YAKE MALLAKAR HULAR LAMSARA??
.
SHIN YARIMA HULKAS YANA SAMUN NASARAR KASHE SARKI
SHARDAS DA HANNUNSA KAMAR YADDA YA DAUKI ALKAWARI
DUK DA CEWAA BAYA SHI YAKE DAUKA A MATSAYIN
MAHAIFINSA KUMA AKWAI SOYAYYA DA SHAKUWA A TSAKANINSU ??
.
Marubucin Yace Mu Hadu A Littafi Na Gaba Don Jin Cigaban Wannan
Kasaitaccen Kayataccen Daddadan Labari
Author Abdul Aziz sani Madakin Gini
Typer Al amin Ahmed Misau
Inkiya Guyson Ko A square
A karshe nake cewa Ku meye ra ayinku dan gane da
yadda labarin littafin nan yazo karshe haka
yaya haduwar zata kasance ne kam sai naji daga
gareku
...
It's Real Al amin Ahmed Misau
0 comments:
Post a Comment