*cigaban labari*
Hanny ce zaune sai faman tunani takeyi Ummah ce take kiranta " Hannatu,Hannatu wai tunanin menene kikeyi haka kinaji Ana kiran sallah kina zaune" Hanny tace " toh Ummah yanzu zan tashi" ta tashi tashiga tai sallah tana zaune a kan darduman da tai sallah sefa man kiran number Babson takeyi ammah bayashiga aranta cewa takeyi" Babson Allah ya bimun haqina Allah ya isa tsakanina da kai" tafad'i tana hawaye ahaka tacigaba da kiranshi Ammah wayarsa akashe .
"Friend sanunku"cewar Hanny,Hassy tace" Hanny yanaga kin rame? please Hanny ki cire damuwa a ranki kimanta da cewama Allah ya halici Babson Hanny tace "Hassy wallahi ni ba tunaninshi nakeyi ba ina baqin cikin rabani da *budurcina* ne da Babson yayi be bani tsaraban ba ammah yarabani da abunda ba zan sake samu ba" Meena ce tazo take cemusu"friend lecturer yazo kumu shiga class" dukan su suka wuce ahaka dai aka gama karatun Ammah Hanny bata fahinci komai ba har kowanesu ya wuce gida .
Kullum Hanny seta kira Babson ammah har yanzu phone d'inshi akashe take ta duba what's app, face book ammah duk bata samunshi,kullum se aikin tunani da danasani .
Su Hanny ne suka fito daga class du Kansu a galabaice suke Hassy tace " nifa yunwa nakeji kumu qarasa cafeteria muci abinci"dukansu sukace "wallahi muma yunwan mukeji muje kawai" suka wuce cafeteria kowa tafad'i abunda za'a kawo mata ammah ita Hanny drinks kawai tace zatasha .ana kawo masu Hassy abinci Hanny ta fara rufe hanci tana kau da kai Meena tace " a a Hanny lafiya kike rufe hanci? "Hanny tace wallahi kawai qamshin abincin ne be mu......kafun ta ida fad'i se amai Hassy ta taso ta riqeta tana " subhanllahi sannu Hanny zauna a can tana nuna mata wani kujerar kafun mugama sena rakaki hospital"Hanny tace "toh"
Meena tace Hanny Allah yaqara lafiya wallahi nima kaina yake ciwo da munje tare Hassy tace bakomai bari mu wuce tare kema Allah ya qara lafiya"Meena tace "Ameen" suka wuce .
Suna isa hospital suka tararda babu layi Hanny tashiga d'akin likita tace "sanu likita da Aiki" likita yace "Hajia meke damunki? " tace " wallahi kwana biyu banajin qarfi ajikina,ga yawan tashin zuciya ,d'azuma har amai nayi danaji qamshin wani abinci."
Likita yace "Matso mugani "ya duba hanunta da idon ta .
Se yabata wani roba yace " gashi kije ki kawo urine d'inki se kikai lab a miki wanan test d'in"ya rubuta mata yabata ta fito ta samu Hassy tace " Hassy muje nai test dinan wai na urine inaga dai maleria ce " Hassy tace" nima haka nake tunani" sukaje akai mata test sukajira result ya fita suka karb'a ta koma gun likita ta bashi likita yace Hajia congratulation you are pregnant "
zumbur Hanny ta miqe tana " nashiga uku likita ka taima keni kamun rai ka ciremun cikinan yau nashiga uku na "se ihu takeyi jin ihuntane yasa Hassy ta shiga tana shiga Hanny ta riqeta tana " Hassy wallahi wanan shegen mutumin ya cuceni Hassy Babson ya yaudareni bayan rabani da *budurcina*da yayi har ciki ya mun nashiga uku ni Hannatu" ta na kuka me ban tausayi takoma gun likita tace" likita,ka taima keni yanda Allah ya taima keka kaciremun cikinan " likita yace "Hajia sedai kiyi haquri wallahi bama zubar da ciki anan"seji sukai Hanny ta fad'i Tim a qasa sumamiya Hassy tazo da gudu tana kuka tana "Hanny,Hanny please kitashi ,kitashi kitashi Hanny".
Nikaina danake gefe seda nai kuka saboda hanny rabani tausayi,ita bataci *TSARABABA* ammah ta samu unborn.
[10:55PM, 8/13/2017] +234 806 677 6651: *A SANADIN 🙆 TSARABA*🙆
*written by*
🖋🖋 *Minash*💝💝
*Affuwan jiya baku jiniba banajindadine shiyasa ammah nasamu sauqi zakudunga jina yanda akasaba nagode da kulawarku da qaunar da kuke mun my fans*
*DEDICATED TO MY LOVELY SIS NAFISA UMAR 7UP nagode na kulawarki Allah ya bar qauna*😘😘
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*We don't just entertain and educated we touch the heart ❤ of the readers*
P.M.L
PAGE 30-35
Likita yace "mik'o ruwa a samata" ya nuna Hassy takawo akasawa Hanny ta farka tana kuka hanunta na dafe a mararta tajuya ta Kalli likita tace "likita katai makeni yanda Allah ya taima keka kacire mun cikinan Dan Allah likita " ta zauna ak'asa tana kuka me karya zuciyan mutun likita yace " yan mata kiyi hak'uri ammah wallahi mu bama wanan aikin awanan asibitin,ammah meya kaiki kika yarda kikai cikin sanan yanzu kice aciremiki ,kinsan hadarin dake tare da zubar da ciki kuwa? "
Hanny tace " Wallahi likita wanine ya yaudareni da kuma kwadayi irin nawa"nan Hanny tabama likita labrin abunda ya faru ita atunaninta idan yaji ze tausaya mata.likita yace "yanzu yan mata *A sanadin tsaraba* kika zubar da darajarki kika Bawa wani kanki " Hanny tace "wallahi likita yaudarata yayi "
" Duk da haka" likita yace " yakamata yan mata kuyima kanku fad'a kudaina biyewa San zuciyanku kuna barin samari suna kisses d'inku suyi romance daku watama har tai sex duk Dan kud'in da za'abaku ,kusani cewa aure shine yafi dacewa daku dakin mijinku shine darajarku Ammah ba kutsaya kuce sekunyi nisa Akaratu ba kinga yanzu wanan yazama darasi akanki da sauran k'awayenki".
Taimakon da zanmiki shine, "ga wanan kisha guda biyu yabata wasu drungs yace" indai kinsha toh zakifara bleeding daganan insha Allah zefita"
Hanny ta k'arba sukai godiya ita da hassy suka tafi .
Hassy ta wuce gida tana cewa" Friend Allah yasa adace kuma Allah ya tsinewa Babson Albarka "Hanny tace "ameen" itama ta wuce gida .
Tana zuwa gida ta d'auka magani guda 4tasha don yay saurin fita da wuri ,( Niko nace a a Hanny ba biyu likita yace kishaba Ammah INA bata saura reniba harta shanye )
Shiru har dare Hanny bataga ko d'igon blood ba ta qara d'aukan hudu tasha ta kwanta.nace ( a suba ta gari yar gidan Babson)😂
Washegari Hanny ta tashi lafiya lao bataga alaman komaiba nan Hankalinta ya tashi ta kira Hassy tana dauka tace"friend wallahi be futaba zanfito school yanzu mukoma gurin likita nan" Hassy tace OK Nima ganinan a hanya "
Adaidai bakin gate na school Hanny ta had'u da Hassy suka wuce wurrin likita suka masa bayanin ciki fa be fitaba likita yace"gaskiya iya taimakon da zanbaki kenan "haka suka mai godiya suka fito Hanny se kuka takeyi tana cema hassy" ya zasuyi yanzu?.Hassy tace" zo muje ga wani asibiti can maybe su sunayi "Hanny tace friend " jifa asibitin wanan ma dayake me kyau basu yiba se wanan danake ganin ko likitan kirki babu" Hassy tace mujedai bamusan Inda za'a daceba"
suna ko zuwa suka samu likita yace sunayi Ammah 25k Hanny ta zaro ido 😳 tace" likita kataimaka mun wallahi bamu da wanan kudin "yace " toh taimako dayane zan iya yimuku a 20k wanan shine kawai "Hassy tace toh " mungode bari muje mudawo" suka fito Hanny tace " Friend yazamuyi yanzu? wallahi ni 200 kawai gareni kuma ko wayata nasiyar ko Rabin kudin bazekaiba oh! ni Hannatu wallahi Babson ka cuceni Allah ya tsinema Albarka tanafadi tana hawaye" Hassy tace "muje asiyar harda nawa nasan nawa zekai 20k " suka tafi akasiya wayan Hassy 25k na Hanny kuma 9k Hassy tace"friend kinga kud'in nawama kawai ya isa sekibani naki phone din yanzu seke kisiya ko baby Nokia ne da sauran 5k din " hakanko akayi Hassy ta karba na Hanny itakuma tasiya Nokia 3k suka tafi,suna zuwa akashiga akaimata cikin 15 mnt angama akabata magani sukasiya 1500 da sauran cancin wayah suka fito .
Hanny ta rungume Hassy tace " bansan dabakin da zan gode miki ba friend Allah ya bar qauna " Hassy tace "haba mana what a friend is idan ban mikiba wazemiki bayan nasan k'adarane Nima ze iya fad'awa kaina muje kawai Allah ya tsare gaba " Hanny tace "hakane yanzu ai munga darasi Allah ya yafemana" Hassy tace "ameen"
suka fito suna tafiya saboda basu samu abun hawaba kusaba seji sukai ana tamusu Horn ammah basu waigaba har suka samu me sahu suka shiga wani saurayine black beauty me d'an tsayi da cikan zati ya leqo yace"Assalama alaikum y'an mata inata sallama tudaga can nake binku Baku kulani ba please kuzo na kaiku gida sonake nai magana dake ya nuna Hanny don naga bekamata na tsayar daku atiti bane" Hanny jin muryan sa tayi yayi mata dad'i ammah bata cemai komaiba se Hassy ne tace"mallan mungode kagama munriga munshiga sahu "yace toh Dan Allah taimakeni da number k'awanki ya nuna Hanny" Hassy seda takali Hanny sanan ta bashi yana sawa yayi dailing Sega yar qwaman Hanny data siya dazu yafara qara 😂Seya dago ya kaleta ya CE "sunana Shamsudeen se kinjini " yabiya musu kudin sahu ya wuce.
Yana tafiya Hanny tace" kinsani ko shima irin Babson ne? kika bashi number na "Hassy tace" wallahi haka kawai naga yayi mun alamun mutumin kirki"Hanny tace "hmmm" suka wuce .
Tana zuwa gida ta ga Ummanta afalo tace"sanu Ummah da gida."ummah tace "Hannatu zonan" Hanny tazo tana dingisawa saboda mararta dake d'an mata ciwo kad'an kad'an tazauna kusa da umanta .umah tace"Abbanki ne yabani sak'o nafad'amiki kifitar da miji nan kusa idan ba hakaba zebaki duk Wanda yaso tashi kije"Hanny ta miqe tana tafiya seji tai ummah tace "meyafaru dake kike tafiya haka" Hanny tace "ummah bigewa nayi"ummah tace " Allah ya sawaqe" ta wuce .
Hanny na kwance tana godema Allah dayasa cikinan ya Fita ta dauko phone dinta takira Hassy ta sake mata godiya tana kashe wayan Sega kira ya shigo da bak'uwar number tana gab da katsewa ta dauka tace"Assalama alaikum" jiyayi muryanta ya daki har cikin kuneshi yana lumshe ido don jin dadin muryanta se da Hanny ta sake sallama sanan ya amsa da "waalaikum sallam amincin Allah ya tabata agareki ya ma'abociyar kyau,kina magana da Shamsudeen " lumshe ido Hanny tayi sanan ta bude tace"nagane Deen ya kake"jiyayi Deen d'in datakirashi dashi yayi mishi dad'i daga nanfa yafara mata bayin shi da aure yazo kuma so yake ayi nankusa domin ya yaba da nutsuwanta kuma yaganta alamun tana da kamun kai don shi bayason mace Mara natsuwa "nanfa cikinan Hanny yabada qululu............
Ahaka suka sha firansu har. Baci ya dauketa .
Bayan wata biyu Hanny soyaya suke da Deen me Tsafta don har ankawo kudin aure ansa rana wata daya. (Hanny natayaki murna Allah yasa alkhairi inji Minash)
Hassy tace" friend Ku so mu je wancan kantin don naga ya nada kaya masu kyau" Meena tace"wani kanti?" Hassy tace "kantin samanin fatihu mana" Hanny tace "ku muje " suka Shiga suka siya anko suka fito suna tafe suna yaba kyanshi meena tace"ammah Hanny za mudauko me make up ko saboda dole afitomana dake "Hanny kawai dariya tayi tana sunkuyar da kanta seji tai tayi karo da mutun ta dago tace " sorry..................
0 comments:
Post a Comment