Kafin ya fito ya kira Asmau a waya ya sanar da ita zai zo. Jikinta a sanyaye ta amsa masa don ita yanzu kunyar ganinsa take yi. Ko ba'a fada ba daga nasihar Anti Bintu tasan cewa duk abinda ya faru laifinta ne.
Har daki taje ta sanar da Anti Bintun zai zo kamar yadda ta saba.
"Ki dora abinci dashi amma ki bar dan waken sai gobe don bazan bawa suriki dan wake ba"
Ita da Asmau duk dariya sukayi sannan ta wuce ta dora shinkafa da miya.
Wuraren karfe uku ya iso Anti Bintu tazo suka gaisa sannan ta basu wuri.
Yau Asmau hijab ta saka dogo har kasa fuskarta babu kwalliya sai hoda da kwalli. Jikinta duk babu kwari tayi nadama sosai. Abubakar kuwa tamkar ya hadiyeta da kallo. Anyi sa'a yaran gidan suna ta gilmawa a falon. Da laasar suka tafi islamiyya shi kuma yaje yayi sallah.
Ana idarwa ya dawo ya kalli Asmau dake zaune a can gefe.
"Asmy dawo nan kusa dani nafi jindadi". Ya nuna kujerar gefensa.
Tashi tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tana zama ya kama hannunta ya rike yana lumshe idanu. Can kasa take jin muryarsa
"I love you so much Asmy. Ina ma anyi aurenmu kiga irin abinda nake nufi."
A kwanakin baya har so take ya rike mata hannu amma yau sai taji ta tsani hakan. Tana son nuna masa kuskuren abinda tasan ya fita sani amma dole tabi lamarin a hankali kada yayi mata mummunar fahimta ko yace ta mayar dashi dan iska.
Har lokacin tafiyarsa yayi bata iya sakin jiki dashi ba. Shi kuwa gabadaya ya kasa samun nutsuwa. Bakin motarsa da ya ajiye a wajen gate ta raka shi ai kuwa yana bude motar ya rungumota jikinsa. Dama layin ba mutane sosai saboda unguwar bata gama cika ba ga duhun dare.
Wasu hawaye masu zafi Asmau taji sun taho mata ta hadiye. Dole ta sami lokaci suyi magana da Abubakar akan wannan abin. Rungumar da take jindadi daga gareshi yau bata so. Tana wannan tunanin taji yayi mata abinda bai taba yi ba. Abinda take ta mararin faruwarsa. Bakinsa ya hada da nata yayi mata rikon da bazata iya kwatar kanta ba koda tayi niyya.
Hawayen da take boyewa ne suka sakko ganin Abubakar tamkar baya cikin hayyacinsa. Abubuwan da yake mata sun fara wuce gona da iri. Ba shi ya saketa ba sai da don kansa yaji hankalinsa ya fara dawowa gareshi.
Ganin tana kuka ya soma bata hakuri.
"Asmy kiyi hakuri please. Na rasa dalilin da yasa nayi miki hakan. Ki sani ina sonki tsakani da Allah kuma in sha Allah bazan sake kwatanta miki haka ba sai munyi aure".
Yadda yake maganar sai ya bawa mutum tausayi. Tabbas baya son abinda yake yi sai dai karfin sha'awarsa da tsananin rudin shaidan yasa ya kasa hakuri.
A hankali ta share idonta "Yaya Abubakar don Allah mu dena irin wannan abin kaga babu kyau."
"Na sami Asmy, ni kaina na rasa gane yadda akayi muka fada ga wannan masifar. Ki share idonki kinji matar Abubakar".
Kafin ya tafi sai gashi ta sake sosai hankalinta ya kwanta. Suka rabu zuciyar kowa tana nata sake saken.
*****
Abubuwan da suka gudana tsakanin Abubakar da Asmau su suka rinka yi masa yawo a kwakwalwa. Yayi tunanin zaiji saukin sha'awar dake damunsa sai abin yayi tsanani sosai. Kullum cikin mafarkinta yake yi. Baccin kirki ya gagare shi sai tunanin yadda zaiyi ko dai a matso da aurensu ko ya kashe yunwarsa ko sau daya ne.
A nata bangaren hatta hirar da suke yi a waya yanzu tana kame bakinta daga hirar da bata dace ba. Ta tarkarta tunaninta kaf zuwa lokacin aurensu ko sa sami nutsuwa da kwanciyar hankali saboda tasan duk su biyun yanzu a matse suke da ganin wannan lokacin.
Bayan kwana biyu ya sake zuwa wannan karon ko waya baiyi mata ba. A hirarsu da Anti Bintu ya nemi izinin ranar asabar da Asmau zata tafi zai zo ya kaita da kansa a cewarsa baya so ta shiga motar haya.
Anti Bintu tayi shiru na dan lokaci saboda ba haka sukayi da yayarta ba. Dama tasha za'a kaita ta tafi saboda motar Kawu Yusuf tana gareji wurin makanike. A duk dan tunaninta bata hango wata matsala ba duba da irin siffa ta kamala da suke dashi su biyun.
Asmau kanta bata ji komai ba saboda yau hirarsu duk irin ta da ce. Cikin nutsuwa da kiyayewa. Soyayya mai tsafta irin wadda masu yinta basa son rabuwa da juna.
Kwanaki ukun da suka zo kafin tafiyarsu Abubakar yaji babu dadi. Har wani zazzabi ne ya kamashi saboda ji yake tamkar ana hura masa wutar sha'awar kasancewa da mace. A yadda yake ji ko ba Asmau bace wannan karon zai iya nema.
Ranar da zasu tafi wurin karfe goma ya iso. Asmau da yaran harda dan kukansu na rabuwa.
Suna mota ita da Abubakar babu wata hirar kirki don basu taba kadaicewa a mota haka ba na tafiya mai nisa.
Hanyar cikin gari ya nufa ya kashe motar a gefen titi. Asmau ta kalle shi zata yi magana sai ta kasa ganin idanunsa sunyi wani iri kamar wanda yake cikin tashin hankali.
A raunane yake dubanta har sai da tsigar jikinta ta tashi don tsoro da ya dora hannunsa a kan nata.
"Asmau"
Yaushe rabon da ya kirata da sunanta haka. Gabanta na dukan uku-uku ta amsa.
"Idan na rokeki alfarma zaki yi min?"
Ita fa Yaya Abubakar tsoro yake bata da yanayinsa na yau.
"in sha Allahu idan baifi karfina ba".
Gwauron numfashi ya ja.
"Asmy ina cikin matsala kuma ke kadai ce zaki iya yi min maganinta. Ko sati ba'ayi ba da muka amince mun dena taba jikin juna.."
Bugun zuciyarta ne ya karu tana ganin kamar ta fara fahimtar inda zancensa ya dosa.
"Ni mutum ne mai yawan bukata, ina tsammanin baki san me hakan yake nufi ba."
A ranta kuwa tace sai dai na fadawa wani. Rabe-raben mutane ta fannin sha'awa tuni ta san shi a posts din waya. Muryarsa wadda take rawa taji a kusa da ita.
"Ina cikin tashin hankali da son kasancewa tare dake. Wallahi bazan iya kaimu Kano ba a yanayin da nake ji yanzu musamman da kike zaune kusa dani. Ki taimakeni ko sau daya ne na kawar da wannan masifaffen tunanin."
Kofar motar ta kama a gigice hawaye na wanke mata fuska jin ya saka lock. Sanyin AC bai hanata gumi ba.
"Yaya Abubakar ka rufa min asiri ka mayar dani gidan Anti Bintu. Duk ni na jawo wannan matsalar da na rinka saka kaya masu matse jiki ina zama kusa da kai. Sharrin shaidan ne da na zuciya don Allah kayi hakuri nan da wata hudu zamuyi aure fa".
Magiyar da take masa jin muryarta yake kamar tana masa busa. Wannan wace irin masifa ce??? Shiyasa tun a da yake nisanta daga duk abinda zai jawo masa sha'awa tunda ya gane yanayinsa.
Hawaye ne ya zubo a idonsa wanda bai san dalilinsu ba.
"Ke kadai nake so kuma da ke kadai na amince Asmy. Idan baki amince ba wallahi nayi miki rantsuwa zan nemi wata. Bani da lafiya duk a dalilin sonki da son kusantarki. Ko kinsan satin nan ko sau daya banje wurin aiki ba saboda halin dana tsinci kaina a ciki".
Kuka Asmau take yi sosai gashi tausayinsa ya mamaye zuciyarta.
" Yaya kada mu aikata haram. Kuma idan ka rabani da abinda duk budurwa take takama dashi yaya zanyi?"
Hannuwanta duka biyun ya rike. "Asmy kinsan dai nine mai aurenki ko? Kuma ni ba wai zanyi miki yadda zaki tashi daga budurwa bane. Akwai yadda zanyi babu wanda zai ce namiji ya kusanceki. Ki taimake ni.
Har bincike nayi wasu malaman sunce kudin aure daidai yake da sadaki. Ko baki ga iyayenmu maza ke zuwa ba ayi a gaban shaidu. Al'ada ce kawai sake taruwar da ake yi a daura aure. Amma yanzu ma a haka ni da ke matsayin mata da miji muke." Shi da yake fada mata hakan ya tabbatar karya yake yi amma babu yadda ya iya da zuciyarsa.
Roko da rarrashi haka ya rinka yiwa Asmau tana kuka haka ta amince saboda tausayin da ya bata da tsoron kada ya nemi wata.
Wani hotel ya sama musu kuma da yake duk sunyi shigar mutunci babu mai cewa ba ma'auratan gaske bane. Haka ya karbi mukullin dakin zuciyarsa tana kwabarsa da abinda yake shirin aikatawa amma gangar jikinsa bazata iya hakuri ba.
A kofar dakin da kyar Asmau ta shiga. Yana rufe kofar ta kara fashewa da kuka. Abubakar yayi nisa duk da yana tausayinta hakan bai hanashi biyan bukakarsa ba. Alkawarin da yayi mata na yin dabara kada ta rasa budurcinta tuni ya manta dashi.
Sai da komai ya kammala yaji kamar tashin hankalin duniya duk ya kare a kansa. Gefen gado ya koma ya dafe kai ya rasa inda zaisa kansa.
Asmau tana kwance sai sautin kukanta ke tashi. Ga ciwo ga bakinciki.
Sun kusa awa daya sannan yayi wanka ya umarceta da itama tayi. Wannan masifa da yawa take...Ya Allah Ka tsare mana imaninmu.
Haka suka fito babu wanda yake yiwa dan uwansa magana. Ya biya kudin hotel suka wuce Kano yana ta zabga gudu a hanya.
A bakin gate din gidansu ya sauketa zuciyarsa tana kuna. Ya rasa me yake ji game da Asmau. Ko kayanta bai taimaka mata da dauka ba haka ta fito dasu ta shige gida fuska a kumbure.
Su Umma sai murna suke yi ta dawo amma ganin yanayinta Umman ta tsorata tana tambayarta abinda ya faru.
Asmau ta fashe da kuka ta rungume mahaifiyarta. Yau taci amanar addininta kuma taci amanar Umma.
Taruwa suka yi a kanta Jafar ya taba jikinta. Zazzabi ne sosai a jikin hatta kanta ya dau zafi.
Ya danyi murmushi "Umma wannan 'yar taki ta fiye shagwaba da raki. Daga zazzabi kuma sai kuka?"
Sai a lokacin tayi dan murmushi ganin cewa idan ta cigaba da kukan zata tonawa kanta asiri.
"Yaya Jafar ji nake kamar kan zai tsage biyu"
Umma ta tasheta tsaye
"Ki dena tsorata ni irin haka Asmau. Baki ji yadda gabana ya fadi ba. Muje ki dan watsa ruwa sai kici abinci kisha magani. Ina Abubakar din?"
Har zuciyarta ta razana jin an ambaci sunansa.
"Ya tafi gida amma yace zai shigo ku gaisa anjima".
"Babu komai ai kun sha hanya ga rana. Allah Yasa ba kukan nan naki kika rinka yi masa ba saboda baki jindadi."
*****
Har washegari Asmau tana kiran wayar Abubakar saboda bai zo ba kamar yadda tayi tsammani. Babu waya babu text. Nata kiran kuma yaki dauka. Hankalinta yayi matukar tashi. Yanzu idan ya fasa aurenta saboda abinda suka yi yaya zata yi da ranta.
Shima a gida kwana yayi kuka. Idan yaga wayar Asmau ji yake kamar yasa ihu. Zuciyarsa ta kasa rabe masa haushinta yake ji don ta bashi kanta ko kuwa haushin kansa da ya tilasta mata.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽18
Batul Mamman💖
Bacci barawo ne ya sace Asmau ba don taso ba. Ta raba dare tana kuka wanda ya haddasa mata mugun ciwon kai ga jikinta da yayi tsami. Washegari wurin karfe takwas da rabi ta fito daga dakinsu zata shiga kitchen dora ruwan tea ta tarar Umma har ta dama kunu tana buga kosai.
Gaishe da Umman tayi sannan ta yunkura zata karbi aikin ta karasa Umma tace ta bari ya jikin nata. Kafin ta amsa Umma ta dakatar da ita
"Asmau ki fada min gaskiya meye yake damunki? Ji yadda fuskarki ta kumbura ga wata tafiya kina yi kamar me tatata".
A dan tsorace Asmau tace "zamewa nayi a toilet da zanyi alwala."
Umma ta bita da kallo na rashin gamsuwa.
"To fuskar taki fa? Kinsan bana son boye-boye idan rigima kuka yi da Abubakar jiya ki fada min tun wuri ayiwa tufkar hanci."
Murmushi Asmau ta kalalo "Umma lafiya kalau muke. Kaina ne har yanzu yake ciwo sosai kamar bansha magani ba".
"Idan anyi breakfast sai Jafar ya kaiki asibiti tunda dai kin sha magani jiya bai warke ba gara kiga likita sosai. Allah Ya sauwake. Bari na soya kosan sai kici kiyi wanka."
Jikinta a sanyaye ta fita ta koma daki tayi wanka. Zuciyarta ta gama raunana amma cigaba da kukan bazai amfaneta da komai ba sai tonon silili.
Umma kuwa sai tattalinta take yi har daki ta kai mata abinci tana ta sannu. Wannan ya kara sawa taji ta tsani kanta. Ji yadda mahaifiyarta ke kula da ita bayan ciwon nata baya bukatar tausayawa daga kowa.
Sunje asbiti tasha allurai saboda zazzabi sannan aka bata magunguna.
Da suka koma gida Umma ta sanar da ita Abubakar yazo amma ya wuce Kaduna ana nemansa akan wasu takardu da ya kulle a office. Kai kawai Asmau ta gyada ba don ta yarda ba. Daga dawowarsu zuwa wayewar gari tayi masa text yafi goma banda waya da ba'a kirgawa. Gani take yi kawai zai gujeta ne kamar yadda take yawan jin labarai na samari da suke yaudarar 'yan matansu.
*****
Kafin azahar Abubakar ya isa Kaduna. Jiya ko kadan bai runtsa ba sau tunani da ya addabi zuciyarsa. Ji yayi Kanon tayi masa zafi shiyasa ya dawo saboda baya son yawan tambaya akan me yake damunsa.
Kwanansa biyu da dawowa baya zuwa ko ina daga office sai gida sai ko masallacin unguwar da yake. Rabonsa da abincin kirki ma ya manta. Yana kwance ya kurawa fanka dake juyawa ido wayarsa tayi kara.
Sunan Qasim ya gani shiyasa ya dauka. Qasim ya sanar dashi wani aiki zai kawo shi garin yanzu zai kamo hanya. Addua Abubakar yayi masa sannan ya dan gyara dakin da ko shara baya samu.
Tun zuwan Qasim ya kula da canjawar da abokinsa yayi. Yayi tambayar har ya gaji babu amsa. To me zai fada masa?
A nata bangaren Asmau ji take yi kamar tayi hauka. Tayi wayar har ta gaji. Hawayenta ma ya kafe jira take kawai azo ace Abubakar ya fasa.
*****
Ranar juma'a da safe Abubakar ya gama shirin tafiya office Qasim yace
"Karfe nawa zamu tafi Kanon?"
"Wannan satin bazan je ba ayyuka sunyi min yawa" Abubakar ya bashi amsa.
Kayan da yake sawa a 'yar jakarsa ya ture ya koma kallonsa "Abubakar nayi nayi ka fada min abinda ke damunka kaki na rasa dalili. Ni mai sonka ne da alkhairi idan ka fada min ko addua sai na tayaka".
Kwalla yaji ta cika masa ido ya dan dake "na fada maka babu komai bari naje na dawo mu tafi. Shikenan ko".
Qasim dai bai gamsu ba. Yana nan zaune aka kawo wuta ya saka wani CD na wa'azi da ya gani a kusa da tv din dakin. Ko minti goma ba'ayi da farawa ba Abubakar ya shigo lokacin shabiyu saura.
Zamansa ke da wuya aka yiwa malamin dake wa'azin tambaya akan ZINA. Malamin yace
"Lallai zina tana daga cikin manyan kaba'ira da Allah SWT Yayi hani dasu. Ban da lalacewar zamani yanzu da muka dauketa ba a bakin komai ba zaka ga yawanci duk addinin duniya yayi hani da zina saboda muninta da kazantar dake cikinta. A cikin suratul Furqan ayoyi na 69 zuwa 71 Allah Yana cewa
*WADANDA BASA DAUKAN WANI BAYAN ALLAH A MATSAYIN UBANGIJI KUMA BASA KASHE RAI BA BISA SHARI'AH BA, KUMA BASA ZINA WANDA DUK YA AIKATA HAKA ZAI SAMI ZUNUBI DAIDAI AKIN DA YAYI*.
*ZA'A NINKA MASA AZABAR RANAR ALKIYAMA KUMA ZAI KASANCE A CIKINTA HAR ABADA*.
*SAI WANDA YA TUBA KUMA YAYI IMANI KUMA YA AIKATA AIKI MAI KYAU, WADANNAN SUNE ALLAH YAKE CANZA MUSU ZUNUBANSU ZUWA GA LADA. ALLAH MAI RAHMA NE MAI JINKAI* Abin duba a nan shine an lissafa zina da ayyuka masu matukar muni wato shirka da kisan rai ba tare da hakki na shariah ba"
Haka malamin ya cigaba da janyo ayoyin AlQurani da hadisan Annabi SAW wadanda suka yi hani da zina ko azabar dake jiran masu yinta.
Ya kawo aya ta 32 a cikin Sural Isra' wadda Allah Madaukakin Sarki Ya umarce wadanda suka yi imani da kada su kusanci zina.
Sai aya ta 2 a cikin suratun Nur wadda Allah SWT Yake cewa: *MAZINACIYA DA MAZINACI IDAN SUKA YI ZINA KU BULALI KOWANE DAYA DAGA CIKINSU BULALA DARI. KADA KUWA WANI TAUSAYI YA KAMAKU GAME DA TABBATAR DA HUKUNCIN ADDININ ALLAH IDAN KUN KASANCE KUN BADA GASKIYA GA ALLAH DA RANAR LAHIRA. KUMA LALLAI NE WATA TAWAGA DAGA MUMINAI SU HALARCI WURIN YI MUSU HADDIN*
Abubakar da Qasim duk hankalinsu yana ga bayanin wannan malami. Duk su biyun jikinsu yayi sanyi musamman Abubakar da yasan abinda ya aika.
Malam mai wa'azi cikin bayaninsa ya kawo hadisin Bukhari wanda Annabi SAW yake cewa _MAZINACI BA SHI DA IMANI A LOKACIN DA YAKE AIKATA ZINA...._
Da wani hadisin na Abdullahi ibn Mas'ud wanda yake cewa _MUN KASANCE TARE DA ANNABI SAW MATASA MARASA KOMAI NA DUKIYA_. _SAI ANNABI SAW YACE DAMU_:
_YA KU SAMARI, WANDA YA SAMI IKO A CIKINKU YAYI AURE DOMIN YAFI AKAN KARE KALLO DA MUTUMCI. WANDA BAZAI IYA BA SAI YAYI AZUMI SABODA ZAI ZAME MASA KARIYA._
Kallon kallo ne ya koma tsakanin Abubukar da Qasim a lokacin da malamin ya soma bayanin lahira da tanadin da Allah SWT Yayiwa bayi masu biyayya da masu sa6o. Ya karanto ayoyin Suratul Haaqqa wurin da Allah SWT Yake fadan irin farincikin da masu aikata aiki nagari zasu shiga idan sun karbi littafinsu da hannun dama da tanadi mafi kyau da Yayi musu a aljannah. Da kuma tashin hankalin ma'abota sabawa Allah a lokacin da suka karbi nasu littafin da hannun hagu(Ya Allah Kasa bama cikinsu. Amin) da azabar da zasu tarar.
Duk da Qasim ya shiga tashin hankali da jin wadannan bayanai saboda abinda yake aikatawa na shafa jikin 'yan matansa saboda gusar da sha'awa, yayi matukar mamaki ganin Abubakar ya fashe da kuka. Dafa abokin nasa yayi yana cewa
"Ba kaine zaka yi kuka ba Abubakar. Ni ne ya kamata nayi kuka saboda nasan na sabawa Allah sosai. Irin wannan abin da na fada maka akalla nayi da mata wurin biyar."
Abubakar ya kalle shi hawaye na kwararo masa." Qasim nawa sabon yafi naka. Na cuci kaina na aikata zunubin da bana hangowa kaina komai sai azaba."
A tsorace Qasim ya dago kan Abubakar dake kallon kasa" ban fahimceka ba, kada dai kace maganarmu ta rannan tasa kaima kaje kayi romancing wasu. Na shiga uku, ai ni ne cikin matsala tunda duk wanda yayi umarni da mummunan aiki yana da zunubi kwatankwacin na wanda ya aikata kamar yadda yake ga mai umarni da kyakkyawa".
Dafe kansa kawai yayi yana tunanin wannan sabon tashin hankali da ya saka kansa a ciki.
Zuciyar Abubakar cike da danasani yace "Qasim zina nayi"
"What??? Abubakar garin yaya? Da wa?"
Sai da ya hadiyi yawu da kyar ya iya amsawa "Asmau".
Qasim yana girgiza kai yana karanto La haula...
"Marainiyar yarinya, wayyo Abubakar ni ne sila ko? Tun yaushe ne? Garin yaya ka aikata hakan kai da ka kusa aure? Idan aka gane fa? Ga mahaifiyarta mutuniyar kirki."
Tambayoyin da Qasim keyi shima Abubakar din sune suke masa yawo a kansa. Yana hawaye ya sanar da Qasim abinda ya faru da irin kunya da bakincikin da ya sami kansa a ciki. "Yanzu shikenan nima da hannun hagu zan karbi littafi na ranar lahira. Lallai Annabi SAW yayi gaskiya da yace a hadisi na hudu cikin arba'una na Annawawi wanda aka karbo daga Ibn Mas'ud yake cewa ..
_......Hakika dayanku zaiyi ta aikata aiki irin na 'yan aljannah har sai ya kasance tsakaninsa da ita bai wuce zira'i ba sai littafinsa ya rinjaye shi sai ya aikata aiki irin na 'yan wuta sai ya shigeta...._
Qasim ya soma hawaye " in sha Allahu bazamu shiga wuta ba. Ka manta Allah Yayi alkawarin yafe zunubin masu tuba.?"
Sai da suka sha kukansu sannan Abubakar ya bawa Qasim wayarsa ya karanta wasu cikin sakonnin text da Asmau ta turo masa.
_Yaya Abubakar ka dubi girman Allah ka daga wayata. Kada ka gujeni a wannan lokacin_
_Idan ka rabu dani rayuwata bazata kara wani amfani ba. Me zan fadawa duniya nan gaba._
_Kai kadai ne zaka iya taimakona a wannan halin. Ka daure kada ka fasa aurena._
_Na amince ko washegarin aurenmu ne ka sakeni wallahi bazan yi korafi ba. Amma yanzu idan ka kini duk wanda ya aureni zai iya tona min asiri._
Kasa kara karatun Qasim yayi saboda tausayin Asmau da ya kama shi. Sun dauki wasu mintuna babu mai magana sai muryar malamin nan kawai suke ji yana kara tsorata mutane game da aikata zina.
Qasim ya tashi tsaye yana kashe kayan wuta na dakin dake kunne "ka tashi mu tafi ka bawa yarinyar nan hakuri sannan mu san yadda zamuyi su Baba su amince a matso da bikin nan zuwa wata biyu tunda kace mai hayar naka har ya gama ginin da wuri."
"Kana ganin zasu amince? Wata hudu ya rage da 'yan kwanaki yanzu nace a maido shi baya?"
"A nawa ganin hakan ne zai kara kwantarwa Asmau da hankali tasan cewa da gaske bazaka gujeta ba. Wallahi Abubakar ban taba zaton zamu wayi gari mu ga rana irin wannan ba. Ba don da bakinka ka fada min ba Allah bazan taba yarda ba."
Rufe dakin suka yi sannan suka fita zuwa motar Abubakar. Qasim ne zai tuka su. A hanya suka sami masallaci sukayi sallar juma'a sannan suka wuce Kano suna ta tattauna yadda zasu bullowa su Baba domin su yarda a dawo da bikin baya. Kafin su rabu sai da Abubakar yasa Qasim yayu masa alkawarin wannan zancen zai zama sirri a garesu har mutuwa.
*****
Ko gida Abubakar bai shiga ba yana sauke Qasim ya tashar unguwar kabuga zai wuce Shanono, gidansu Asmau ya wuce kai tsaye. Lokacin Umma na wurin aiki ita kuma tana daki tana sana'ar kuka. Ta gama sawa ranta Abubakar ya gujeta kenan yanzu abinda ya faru matsalarta ce ita kadai. Jafar ne ya buga mata kofar daki ya sanar da ita zuwan Abubakar.
A zabure ta tashi ta lulluba mayafi ya rufe mata rabin fuska ta fita ta same shi a wurin da Umma ke ajiye mota.
Tana zuwa gabansa bata yi la'ari da cewa wani zai iya ganinsu ba ta zube gwiwoyinta a kasa tana kuka mai sauti.
"Don Allah Yaya Abubakar kada kace kazo rabuwa dani. Gara na mutu da in ga ka juya min baya a wannan yanayin."
Waigawa yayi ya tabbatar babu mai ganinsu sannan yayi mata alama da ta tashi. Shima hawayen yake shirin yi.
"Asmy kiyi hakuri ki yafe min. Naci amanarki na cutar dake. Amma ina so kisan cewa bazan gujeki ba. Wannan tsautsayin ni ne na tilasta miki saboda haka tare zamu fuskance shi. Idan kin amince zanyi magana a gida a dawo da bikinmu nan da wata biyu".
Wani hawayen ne ya sakko mata ga dariyar farinciki duk a lokaci daya.
"Da gaske? Wallahi na amince. Na yarda. Nagode Yaya Abubakar."
"Ki dena yimin godiya. Ni dake duk bamu fi karfin kaddara ba. Kuma kowane bawa akwai irin jarabawarsa a duniya. Dama Annabi SAW yace _Shaidan yana gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake yi._
Kinga ashe bamu fi karfin fadawa tarkonsa ba. Sai dai Ubangijinmu mai rahma ne da gafara. Idan muka tuba sai kiga kamar ba'ayi ba."
A sanyaye yake maganar ciki da nadama.
Daga wannan lokacin suka fara azumi da tashi cikin dare neman gafarar Allah. Yaso samun matsala da su Baba amma daga baya sun amince an matso da auren. Tun daga lokacin Asmau take bashi girma fiye da na da, tsoro take yi kada ta kuskure yace ya fasa asirinta ya tonu.
Haka lokaci ya tafi har zuwa bikinsu da abinda ya faru bayan nan.
*****
*CIGABAN LABARI*
Asmau ta share hawayenta bayan ta gama bawa Zubaida labarinta. Ita ma Zubaidan kukan take yi na tausayi ga bakuwar da kwanansu daya da haduwa amma jininsu ya hadu.
"Tabbas kinga tashin hankali a rayuwarki Asmau. To amma abinda ya daure min kai shine yadda kuka tuba amma duk da haka kika tsinci kanki a irin wannan rayuwar".
Dan murmushi Asmau tayi "Zubaida kenan, tubanmu ba shi zai hana faruwar kaddarar rayuwarmu ba. Komai da kika gani ya faru ga bawa rubutaccen al'amari ne tun kafin zuwansa duniya. Wani abin yana faruwa ne domin ya zama darasi ga wasu don su kiyaye. Ni bana bakinciki da ikon Allah. Nasan bazai barni na tabe ba albarkar Annabi SAW."
Zubaida ta gyada kai ta gamsu da bayanin Asmau.
"Allah Ya jikan Abubakar"
Asmau tace "Amin " tana share kwalla.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽20
Batul Mamman💖
Wani mugun fitsari ne ya tashi Asmau daf da kiran assalatu. Ta fito zata je bandaki amma ko ruwan tsarki bata dashi. Haka ta koma daki tana ta matse shi da adduar Zubaida ta fito da wuri ko dan yaya ne ta sammata. Har aka idar da sallah a masallaci Zubaida bata fito ba. Zuwa lokacin Asmau sai gumi take yi tana cilla kafa. A hankali taji ya fara zubowa dole ta tafi bandakin da gudu tayi batare da tayi tsarki ba. Haka ta dawo dakinta ta shafi kura tayi taimama sannan tayi sallar asuba.
Batun jin yunwa dama ba'a magana. Wannan yanayin da ta tsinci kanta a ciki hakurinta ya fara karewa. Ace tayi fitsari ko ruwan tsarki babu gashi tana gani amma gidan nafsi nafsi (kowa na ta kansa)kawai ake yi.
Yau Zubaida bacci sosai take yi don har tara ta wuce bata farka ba. Asmau ta gaji da jiran tsammami ta duba hijabinta wanda yafi kowanne dauda ta saka ta fita bakin titi. Ga rana ta kwale haka ta daure zuciyarta ta zauna duk wanda yazo wucewa tace.
_Sadaka fisabilillah_
Mutumin farko da ya bata naira goma yana yin gaba ta saka kuka. Wai ita da watanni kadan da suka wuce take cikin rayuwar jindadi tare da masoyinta da iyayenta, ita ce take bara tamkar mara galihu. Bara sana'ar da take tattare da kaskanci da mutuwar zuciya. A ranta addua take yi Allah Yasa mufi karfin zukatanmu Ya nesanta mu da kaddara mai muni irin wannan.
Ita kenan ma da tayi nadama amma Allah Ya zabeta don gwada imaninta da kuma nuna aya ga sauran mutane. To ina masu aikata zinar duk da sun san laifine amma basu dauketa a bakin komai ba. A ganinsu suna da sauran lokaci. Ina masu bada muguwar shawara a baki ko a rubuce batare da yin la'akari da tasirin da hakan yake yi a zukata masu rauni ba. Da Abubakar bai tuba ba shikenan haka mutuwa zata riske shi yana halin sabawa Mahalicci.
Taci kuka har ta godewa Allah a wurin. Har rana ta take naira hamsin da biyar ta hada. Ga jiri na dibanta saboda tsabar yunwa. Tashi tayi ta kama hanyar gidan da yanzu shine matsuguninta. A hanya ta sayi fanke na naira hamsin din da pure water guda daya.
Dakinta ta wuce wanda ko jawo kafar batayi ba. To me zata rufe bayan bata da komai. Fanken nan ta janyo tana ci hannu baka hannu kwarya. Ko uku bata ci ba sai amai ya taso mata. Dole ta hakura ta dan jingina da bango tana adduar kada ya fito don ta dan ji kwarin jikinta.
Ba don tana gudun mutuwar kafirci ba gani take yi a wannan lokacin gara ta mutu ta huta. Tana jin shigowar Uwargida ta tashi ta bita daki. Bazata iya cigaba da bara ba gara kawai tayi abinda zai fishshe ta a nata ganin.
" 'Yar Da6as yau tun safe kina ina?"
Asmau ta dan waiga bayanta tana dube dube.
Uwargida tace "indai Zubaida kike nema na kaita wurin uwargijiyata a wannan sana'a. Girma ya fara kamani dolenta ta nema mana kudi. Yaya Babba zata koyar da ita ta karfin tsiya sannan ta dawo gidan nan ta taimaka wurin dago darajarsa kamar da."
Tausayin Zubaida ya kama Asmau. Yarinyar da bata kaunar zaman gidan ma bare sana'arsu ace wai mahaifiyarta da kanta take son lalata mata rayuwa. Sai dai babu taimakon da zata iya yi mata yanzu. Kanta a kasa tace "idan kina da maganin zubar da cikin ki bani".
Wata shewa da tafi Uwargida tayi cike da murna. Tasan za'a rina. Wannan yanzu idan ta fara bawa Asmau abinci na sati tuni zata murmure ta fara caskar kudi da ita.
" kin taimaki kanki kuma na tabbatar bazaki yi dana sani ba muddin kika fara jin jakarki da nauyi. Bari na dauko miki wani jiko da na bawa Darling kwanaki."
Uwar dakinta ta shige ba jimawa ta fito da wata robar swan da ta dafe da datti. Ruwan ciki kore ne fatau ga wasu 'ya'yan ball suna ta shawagi a ciki. Asmau na ganin robar taji amai na yunkurin fitowa. Toshe bakinta tayi ta karbi robar ta fita bayan Uwargida tayu mata bayanin yadda zata sha.
Tun da ta ajiye robar ko kallon wurin bata sake yi ba. A matsayinta na wadda take da ilimi daidai misali tasan shan wannan kazantar babbar illah ne gareta.
Washegari wurin karfe goma ta tashi ta shiga cikin kasuwa. Tasha yawo sannan Allah Ya sa taga abinda take nema wato chemist(kemis). Daga saman an rubuta *SADA AND SONS CHEMIST*.
Mutane ne suke ta shige da fice a wurin ta rakube daga can gefe tana jira suyi sauki ta je ta roki mai kemis din ko zai taimaka mata da maganin zubar da ciki. Sama da awa daya bata ga alamun mutanen zasu yi sauki ba har ta gaji ta soma gyangyadi a gefen wani benci da aka ajiye a wurin shagon.
Cikin bacci taji an soma kiraye kirayen sallar azahar ta bude ido tana hamma sannan ta dan kalli kofar shagon ta ga akwai mutum daya a ciki har yanzu. Daga can nesa ta hango wani yaro da kayan makaranta da flask din abinci ya nufo wurin shagon. Ta tashi ta kade jikinta da niyyar idan ya iso zata roke shi ko ya rage abinci ya bata.
Yana zuwa kuwa ta dan sauke murya.
"Don Allah in ka rage abincin makarantar ka bani in ci".
Yaron da zai kai shekara goma yana da dan jiki ya kalleta yayi murmushi
"Kwanon abincin makarantana na mayar gida. Wannan na babanmu ne na kawo masa".
Daga haka ya shige cikin shagon. Ba dadewa suka fito wurin 'yar rumfar kofar shagon inda bencin yake. Yaron ya ce "Baba kaga almajirar da tace na bata abincin naka".
Mal Sada mai kemis ya dan kalli Asmau. Tabbas babu wanda zai mata wani kallo daban da na almajira. Dogon mutum ne mai dan haske da kiba. Fuskarsa kadai zata nuna wa mutum yana da kirki.
Da hannu ya yafito wata mai awara yarinyar ta karaso da gudunta don kada 'yan talla 'yan uwanta su riga ta zuwa. Ya zira hannu a aljihu ya dauko naira dari ya mika mata.
"Zuba wa matar nan ta sittin sai ki bata canjin. Abba miko mata ruwa a cikin fridge dinnan guda biyu."
Mai awara da Abba suka yi yadda Mal Sada ya saka su. Asmau na karba ta rinka yi masa godiya da fatan alkhairi sai ka zata ta dade tana sana'ar bara.
Mal Sada ya dan daure fuska "nan ba wurin zaman almajirai bane kinji ko. Idan kin gama ci ki tafi."
Ta gyada kai ta koma gefe ta zauna. Da ledar ruwa daya ta wanke hannunta ta fara cin awarar cikin jindadi. Rabonta da abincin kirki ta kwana biyu. Tana gamawa tasha ruwa sannan ta dauki daya ledar ruwan tayi alwala ta shimfida dankwalinta tayi sallah. Lokacin tuni Abba ya tafi. Sada yana kallonta sai ta burge shi da bara bata hanata ibada ba.
Bayan ya dawo daga masallaci yana bude shagon kafin kowa ya shiga ta bi bayansa. Sai kuma kunya ta hanata fadin abinda ya kawota.
"Kina bukatar wani abu ne?"
Kamar mai rada tace "nawa ne maganin zubar da ciki?"
Cak ya tsaya yana kallonta. Wato ban da bara har jikinta take sayarwa. Ransa a bace yace "idan baki fice min daga nan ba ranki zai baci. Ku baro gidajenku kuna bara saboda mutuwar zuciya karshe almajirai da marasa zuciya irinku su rinka yi muku ciki. Ko ina dashi bazan bayarba."
Asmau ta soma kuka tana rokonsa ya taimaka mata.
Daga hannu Sada yayi kamar zai maketa shiyasa ta fita. Amma a kofar shagon nan ta zauna har taran dare lokacin da yake rufewa. Ko kallonta baiyi ba da zai wuce tana ta masa magiya.
Washegari tun kafin yazo shagon ta iso. Yinin ranar da ta ga babu mutane sosai sai ta shiga ta roke shi. Tun yana mata fada ta fita har ya dena kulata sai ta ga wani zai shigo ta fice a sanyaye.
Dansa Abba ya sake kawo masa abinci amma yau bai bi ta kanta ba. Yana ciki yana cin abincin ne ya jiyo kakarin amanta. Tun awarar jiya bata sake samun wani abincin ba.
Kamar ya share sai ta bashi tausayi ya dauko flask din ya mika mata. Idanunta sun kara fitowa waje sai hakora gayau kamar ta shekara tana jinya. Kusan fizgar flask din tayi ko wanke hannu bata yi ba ta soma cin abincin. Abinda bata taba ji bane ya faru a wannan lokacin. Motsi taji a cikinta wanda ya kara tabbatar mata lallai ba ita kadai take rayuwa ba. Yanayin da ta shiga da jin motsin yasa ta farinciki ta dafe cikin. Tunowa da Abubakar da halin rayuwarta kuma yasa ta koma yin kuka. Abincin da bata iya cinyewa ba kenan.
Da Sada zai tafi ta mika masa flask din yace ta rike ya bar mata. Yana kallonta ta tafi har ta bace masa.
*****
Sau biyu kenan Rashida tana fadawa maigidanta ta kai masa ruwan wanka sai yace to ina zuwa. A karo na uku ta zauna kusa dashi cikin damuwa.
"Baban Abba me ya faru ne? Allah Yasa ba laifi nayi ba."
Dan murmushi Sada yayi yana kallon abar kaunarsa.
"Ko kadan Maman Abba. Bari nayi wankan dai."
Sai da ya gama cin tuwo sannan ya bata labarin Asmau mai zuwa kofar shagonsa.
"Ni bansan daga ina take ba sai dai ta bani tausayi. Muna ganin kanmu kamar marasa arziki amma wallahi cikin rufin asiri muke akan wasu. Tsorona daya kada taje wurin wani mara imanin ya bata maganin."
Rashida tace "to ai dama kaine kullum kake ganin kamar shagonka kadai baya wadata mu. Amma gashi yara hudu duk suna makaranta kuma bama rasa abinci.
Idan bazaka damu ba gobe sai na kawo maka abincin da kaina na ganta. Kila idan na bata shawara ta hakura da zubar da cikin ta koma gida".
*****
Asmau ta dauko robar da Uwargida ta bata. Tana son sha kuma har ranta bata son zubar da cikin. Dama gudun zubarwar yasa ta fito daga gida. Dan motsin nan da taji ya sa ta kara son abinta. Robar ta dauka ta zubar da kadan a bakin rariya sannan ta mayarwa Uwargida. Bakin Uwargida a washe tace
" nan da wayewar gari ma yana iya zubewa. Kinyi kyan kai 'Yar Da6as."
Yau ma ta riga Sada zuwa shagonsa. Ita kanta bata san me ya dawo da ita ba. Da yazo har kasa ta durkusa ta gaida shi. Ya amsa mata fuskarsa babu yabo babu fallasa. Yayi mamaki da ko sau daya bata sake batun maganin ba. Tana dai zaune ne kawai a gefe guda.
Wuraren shabiyu wata mace ta sha katon mayafi ta iso kafar shagon da flask din abinci. Matar tayi mata murmushi Asmau ta gaisheta. Sada ya fito daga cikin shagon yace "wannan ce yarinyar".
Rashida taji tausayin Asmau ba don komai ba sai don yanayin da ta ganta. Har wani wari take yi saboda rashin wanka. Sada yace su shigo ciki ya dan kara kofar alamun ko anzo kada a shiga.
Asmau na zaune a kasa a gabansu Rashida tace ta fada musu daga ina take kuma ina uban dan dake cikinta.
"Kada kiyi mana karya domin kuwa Allah Yana kallonmu".
Karo na biyu kenan tana bada labarinta. Kafin ta gama Rashida tayi ya6e ya6e da hawaye don tausayi. Mata da yawa idan an tambayesu game da ciki a irin wannan yanayin sai suce fin karfi aka yi musu. Amma wannan yarinyar ta zabi ta fada musu abinda suka fi tunanin gaskiya ne. Wato biyewa rudin shaidan da son farantawa masoyi. Shi kansa Sada yaji tausayinta matuka. Lokaci guda tarbiyarta ta wargaje a dalilin kawa da kafafen sada zumunta.
Waje suka ce ta fita ta jira su. Muhawara sukayi inda yace su mayar da ita gida Rashida tace kada ta koma sai ta haihu ta yiwu iyayen su yafe mata idan suka ga dan a hannu. Duk da suna tsoron halin Dan Adam yanzu. Kayi masa rana yayi maka dare amma zukatansu sun amince da taimakonta musamman ma suna jin tsoron kada ta zubar da cikin ta fada sana'ar banza.
Sada ya rufe shagon suka ce ta biyosu. Babu musu tabi bayansu tana adduar Allah Yasa alkhairi ne a tattare da mutanen.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽22
Batul Mamman💖
Zahra 'yar Rabe ta biyu ke zaune tana waya da mahaifiyarta Laraba wadda Raben ya dade da saki. A hirarsu ne take fadawa Laraban zancen haihuwar Shema'u wadda akayi kwanaki goma da suka wuce. Tun ranar da akayi haihuwar Yassar yazo ya sanar sai akayi rashin sa'a Rabe da Zahran ne kadai a falon. A wurin ya ci mutumcin Yassar sannan yace da Zahra kada ta fadawa Hajjo babu mai sake zuwa gidan Bara'atu.
Laraba duk ta gama sauraren 'yarta tace mata su kara hakuri da babansu. Dama ita ta bata shawarar dagewa taje bikin Asmau. Tace idan ta shigo Kano zata zo tayiwa Umma jajen abinda ya sami Asmau da barkar Shema'u.
Hajjo tana tsaye a bakin kofa ta fahimci duk hirar Zahra da Laraba. Ko kwanaki uku da suka wuce sai da ta cewa Rabe wai har yanzu Shema'u bata haihu bane yace wa ya sani ne. Bara'atu da bakin hali kuma. Ta rasa gane irin wannan tsana da yake nunawa iyalin dan uwansa.
Dakinta ta koma jiki a sanyaye ta dauko mayafi ta fito. Karnukan Garzali ne suka yo kanta ba shiri ta koma ciki. Dakinsa ta je yana bacci ta daka masa duka a baya. Shi babu arabi babu boko sannan auren ma ya gagara. Sai dai yaje yawo ya dawo gida ya kwanta bacci.
A zabure ya bude ido ganin wace ke kansa ya turo baki "haba Hajjo yau kuma me nayi zaki doke ni? Na rantse jiya ban sha komai ba. Sansana bakina kiji".
Ta kau da fuska "Allah Ya tsareni na kai hancina bakinka. Ni tashi ka daure karnukan ka fita zanyi. Ka mayar mana da gida kamar dandalin 'yan daba. Motsi kadan sai haushin karnuka."
Dariya yayi tare da zuro kafafunsa zai sauko daga kan gadon. Daga bayanta taji ance "ina zaki je?"
Gabanta sai da ya fadi don firgici ta juya tana kallon Rabe wanda bata san ya dawo gida ba. Murmushin da bai kai zuci ba ta kakalo
"Yaushe ka dawo Alhaji?"
Ya basar da tambayar. "Naji kina cewa zaki fita".
Kamar ba mahaifiyarsa ba duk ta kidime tace "uhmm dama gidan waccan mara kunyar zani. Ashe Shema'u ta haihu shine ko ta aiko mana. Ai bata isa ta rabamu da 'ya'yan Shuaibu ba ko?"
Rabe ya soma jin tsoron yawan ambaton su Bara'atu da take a kwanakin nan sai ya dan dake.
"Yanzu a kanta zaki fita cikin ranar nan? Ki kyaleta kawai da halinta. A ce har 'yar dan uwana ta haihu bamu ji ba kawai don bata daukemu a bakin komai ba. Ni daga yanzu na kafa doka babu mu babu su. Tunda haka ta zaba kowa yayi ta kansa."
Hajjo ta jinjina kai tama mamakin yadda yake gilla mata karya haka. Ta tabbatar maganar da Zahra keyi a waya ba karya bane. Ta sake gwada sa'arta ta hanyar cewa
"Wai dama nace muje ko tare da kai ne mu dan zagesu mu huce haushi"
Juyawarsa yayi don kada ta sake jan zancen.
" Koma daki kiyi kwanciyarki ki huta Hajjo".
Tana kallo ya tafi itama ta juya zata koma dakinta. Hawaye ne ya sauko mata wanda bata san dalilinsa ba ta goge da habar zaninta sannan ta koma daki.
Garzali da bai tanka musu ba yaji tausayin mahaifiyarsa ya ratsa shi. Ya rasa dalilin da yasa dukkansu har Yaya Abu da Yaya Lami basu da katabus sai abinda Rabe yace. Amma zaiyi kokari ko yaya ya kai Hajjo taga jikokinta tunda wulakancin da suke musu yasa suka dena zuwa gidan.
A daki Rabe ya kasa sukuni. Sagira na masa magana ya daka mata tsawa. Dama ba wani matsayi gareta a wurinsa ba. A duniya babu matar da yake matukar so kamar Bara'atu duk da girma ya kamasu. Sai kuma batun Malamin tsibbunsa. Dama lokaci lokaci yake sake biya a toshe bakin Hajjo da 'yan uwansa. Yanzu idan asirin ya karya yasan Hajjo cewa zata yi su tashi daga gidan Bara'atu ta dawo. Matsalar idan suka tashi basu da wurin zuwa. Ya riga ya sayar da gidansu na kofar mazugal ya mutstsike kudin batare da sannin kowa ba.
*****
Baaba Ta Annabi tana zaune kofar wurin girki tana tsintar wake taji sallamar yayarta Hassana wadda suke kira da Yaya Tagwai. Farantin waken ta ajiye ta tarbo su cikin farinciki.
Ta Annabi ta kalli 'yar daya yayan nata Usaini tace "auta ba kya laifi kullum kina kuturin Yaya Tagwai. Naga alama idan anyi bikinki tare za'a kaiku."
Yaya Tagwai tayi murmushi tana kallon Harira autar dan uwanta . Ita Allah bai bata haihuwa ba shine ya bata Harira take ruko duk da a gida daya ma suke da zama.
Tabarma Ta Annabi ta dauko Harira ta shimfida musu suka zauna aka gaisa. Ta tambayesu ya suka baro mutanen Misau.
Sai da suka ci abinci ne Yaya Tagwai tace ina sauran yaran gidan. Ta Annabi ta fada mata sunje biki ne a dangin Babansu. Ita ma girki zata karasa ta tafi.
Yaya Tagwai tace " gara da nayi sa'ar ganinki. Ke Harira tashi ki tafi gidan yayarki kafin nazo na sameta ita ma."
Fitar Harira ke da wuya Yaya Tagwai ta kalli kanwarta rai a bace "kin kyauta Ta Annabi, wato don ni ban haihu ba shine kika kira Usani kina sanar dashi katobarar da 'ya'yanku suka yi. Allah Yasa ina labe a bakin kofa naji duk abinda kika fadawa Ado ya sanar dashi. Don shashanci sai ji nayi yana sanya musu albarka. Sai da na kare masa tanadi na taho. Duk tsiyarku nice babba dole kuyi yadda nake so daga ku har 'ya'yan naku."
Ta Annabi ta dukar da kanta. Yaya Tagwai akwai rikon zumunci sai dai bata da hakuri. Hakuri ta bata sannan tayi mata bayanin yarinyar da Sada da Rashida suke riko.
Sada da Rashida auren zumunci suka yi. Shi Sada dan Ta Annabi ne ita kuma Rashida 'yar Kawu Usaini. Tun farkon zuwan Asmau yayiwa mahaifiyarsa bayani a kanta kuma ta nuna amincewarta. Daga baya ne ta yanke shawarar sanar da Usaini don yasan me yake faruwa.
Bayan ta gama bayanin Yaya Tagwai taja dogon tsaki.
"Ina tsammani yarinyar dai da asirinta tazo gidan. Idan ba haka ba waye zai ajiye mace mai ciki a gidansa ba dangin Iya ba na Baba. Ni zanje gidan na same su. Lallai ne su koreta ko don tsare lafiyarsu da ta yaransu. Wa ya sani ma ko mayya ce ko kuma duk abinda ta fada musu karya ne."
ABINDA AKE GUDU🙆🏽23
Batul Mamman💖
Hanjin cikin Rashida sai da ya kada da Harira ta gama fada mata dalilin zuwansu.
"Bari na kira Baban Abba na fada masa kafin ta karaso gidan nan."
Ta dauko wayarta sai dai tayi ta kira Sada bai dauka ba.
Harira tace "kema Yaya me zaisa ki amince ku ajiye matar da baku sani ba. Wallahi yanzu duniya babu gaskiya."
"Na sani Harira. Sai dai karki manta mu musulmai ne. Idan har zamu biyewa halin mutane yanzu ko sadaka bazamu bayar ba. Kamar yadda Baban Abba ya fada kayi komai saboda Allah. Idan mutum ya cutar da kai yayiwa kansa kuma dama faruwar hakan rubutaccen al'amari ne. Asmau bata da matsala ko kadan,sai kin zauna da ita zaki gane hakan".
Suna hirar Asmau su Abba suka dawo daga makarantar boko. Dama jira tayi su dawo ta basu mukulli ta tafi gidan bikin da su Baaba Ta Annabi zasu je. Yanzu dole ta hakura tunda Yaya Tagwai ta zo gari.
Sai biyar da rabi Yaya Tagwai ta iso gidan tun daga bakin kofa take fada.
Rashida tayi tsuru tsuru da ita har ta shigo ciki. Gaisuwar ta ma bata amsa ba sai fadan rashin hankalinsu da ta gani sun ajiye matar da basu san asalinta ba. Tana wannan fadan Asmau ta shigo a gajiye tana jan kafa saboda tsufan cikinta.
Sallama tayi ta shigo ganin baki ta durkusa da kyar ta gaishe da Yaya Tagwai. Kamar gaske ta saki fuska "maraba da tsintacciyar mage. Babu kunya kike yawo da cikin shege a cikin gari."
Asmau tayi shiru tana kallon Rashida wadda kunya duk ta lullubeta. Rasa abin cewa tayi ita kuwa Yaya Tagwai ta cigaba da magana
"Rashida yanzu wannan mai kwalakwalan idanun kika ajiye a gidanki da sunan taimako. Kina kallon yadda jikinta ya mulmule babu mai cewa daga gidansu ta gudo."
"Yaya Tagwai don Allah kiyi hakuri. Idan kika ji labarin yarinyar nan sai kin tausaya mata. Kaddara ce ta afka mata. Adduarmu Allah Ya kare 'ya'yan musulmi daga fadawa makamancin halin da ta tsinci kanta a dalilin sharrin waya."
Hannu Yaya Tagwai ta kai zata doke Rashida "yi min shiru shashasha. Sai iya bayani rai-rai-rai kamar wata zabiya. Zabgegiyar mace kamar wannan kika sani ko barauniya ce, ko kuma rufeki Sada yayi cikin ma nasa ne".
Kukan da Asmau take yi ta tsayar ta dago kai da sauri tana kallon Yaya Tagwai.
"Wallahi duk abinda na fada ba karya nayi ba. Kuma ban taba ganin Kawu Sada ba sai a garin nan da ya taimake ni. Kiyi hakuri don Allah idan zuwana ya bata miki rai".
Rashida ma hawaye take yi tace "na yarda dake Asmau nasan amana ce a tsakaninmu.
Yaya Tagwai don Allah kiyi hakuri. Da zarar ta haihu zamu mayar da ita gaban iyayenta".
Ta juya wurin Asmau da take ta zubar da hawaye.
"Tashi ki koma dakinki. Bani mukullin Kemis din nasan ya kusa dawowa ya karba."
Su biyun Yaya Tagwai ta ke bi da kallo cike da mamaki." Mukullin wane kemis din ne?"
Rashida tayi shiru ita kuma Asmau ta tashi ta tafi dakinta.
"Nace mukullin wane kemis din ne?"
Rai a bace Rashida tayi mata bayanin tsarin da suke yi na zaman kemis da Sada.
Hannuwa ta shiga tafawa tana salati.
"Aahaf, ni nasan ba a banza ta barku ba. Yanzu hanyar samun naku ma tare kuke yin komai da ita. To na rantse sai ta bar gidan nan ko kunki ko kunso. Bazan koma Misau ba sai naga abinda ya turewa buzu nadi."
Asmau tana daki tana jin fadan Yaya Tagwai da muryar Rashida da Harira suna bata hakuri. Kuka take yi sosai tana cike da fargabar abinda zai faru a gaba.
Har kusan magariba Sada bai dawo ba. Dole Yaya Tagwai ta tashi ta koma gidan kanwarta saboda idan duhu yayi sosai ba gani take da kyau ba.
Gidan shiru har Sada ya dawo Rashida ta fada masa abinda ke faruwa. Ko zama baiyi ba ya wuce gidansu sai dai shima babu sa'a. Fada yasha sannan tace ya tashi ya bata wuri.
Haka suka kwana gidan kamar babu mutane. Asmau tasha kuka ga wani ciwon kai da ya kama ta.
Da safe Sada ya kirata suka kara kwantar mata da hankali yace zasu je gidan su sake bata hakuri. Har Kawu Usaini sun kira yace yana hanya zai zo a taru a bata baki. Batun zuwa kemis kuwa ranar babu ita.
Adaidaita sahun ya karbo bayan yaran sun tafi makaranta sannan suka fita shi da Rashida da Harira da ta kwana a gidan.
Ba suyi minti biyar da fita ba Yaya Tagwai ta shigo tare da kanin Sada mai suna Habu. Asmau na daki taji sallamarta. A tsorace ta fito ta bude mata kofa ta bata hanya ta wuce.
Yaya Tagwai ta soma kiran Sada, Asmau ta fada mata sun fita.
"To tunda saboda ke dama nazo ki fada min iyakar gaskiyarki. Shin cikin nan na Sada ne ko wani wanda ya sani?
Asmau ta girgiza kai tana hawaye.
"Alhamdulillahi tunda ba cikinsa bane ina so yanzu yanzu kafin su dawo ki fita ki bar gidan nan."
Gwiwa a kasa Asmau ta durkusa tana rokonta. Yaya Tagwai ta dubi Habu
"Kai da nazo da kai meye amfaninka ne? Ja min ita ka datse kofar gidan. Wallahi idan kika sake dawowa gidan nan sai na kirawo miki 'yan sanda. Haka kawai kin tsaface min yara basa jin maganar kowa sai taki. Kin gama karuwancinki zaki nemi bayin Allah ki hadasu da wahala. In dai cikin nan ba na dana bane to ki kama gabanki".
Asmau tana kuka tace "ki taimakeni don girman Allah. Bani da wurin zuwa idan na tafi."
Yaya Tagwai ta harareta "daga bishiya kika fado da zaki ce baki da wurin zuwa? Tun wuri ki koma gaban iyayenki."
Ta sake cewa Habu yaja Asmau sai ya kasa saboda tausayinta da yaji. Yaya Tagwai tace
"Idan baki fita ba zan sa iyayensu su zare hannuwansu daga kansu. Idan baki sani ba ina so kisan cewa ina da wannan ikon da kannena".
Jin haka Asmau ta juya zata shiga dakin ta debo 'yan kayanta. Yaya Tagwai ta tsare kofar dakin. "Bazan bari ki sake shiga ba bare ki kunna wani tsafin nima naji ina sonki. Fita tun kafin nayi yekuwa a unguwar nan nace ke mayya ce".
Habu ma sai da yasa baki akan ta bari ta dauko kayanta amma taki. Haka ta ja hannun Asmau daga ita sai kayan jikinta Allah Yasa da mayafi tayi waje da ita ko takalmi babu. Kuka take yi sosai amma a haka Yaya Tagwai ta ja hannunta har suka bar layin. Sai da suka yi nisa ta jefa mata naira dari biyu.
"Matsiyaciya sai ki dauka ki kara gaba wasu masu tsautsayin su dauke ki amma ba gidan 'ya'yana ba. Allah Ya isa idan kika dawo."
Kukan Asmau ba karamin tausayi ya bawa Habu ba amma yana kallo tayi gaba Yaya Tagwai ta kama hannunsa suka koma gidan Sada.
*****
A gidansu Sada ne Baaba Ta Annabi ta fada musu tun dazu Yaya Tagwai ta tafi gidan nasu. Suna jin haka suka kama hanyar gida hankali a tashe. Suka yi rashin sa'a titin da ya biyo wata mota ta lalace ta hada uban goslow.
Kusan tsalle Rashida tayi da suka iso gida ta fito daga dan sahun. Tana shiga ta tarar da Yaya Tagwai tana yin boli boli da kayan Asmau. Kuka ta saka tana tambayarta ina take Habu yace ta tafi.
Sada na jin haka cikin fada ya tambaye shi hanyar da tabi ya kwatanta masa. Tare suka bi hanyar ko zasuyi sa'ar ganinta. Sai dai sunfi awa biyu suna nema daga baya wani yace ta shiga wata bus amma bai san inda bus din tayi ba.
Da suka dawo gida Rashida ya gani a tsakar gidan ta rungume kayan jariran da Asmau take tarawa tana ta kuka. Yaya Tagwai tace "idan kin gaji kya yi shiru. Irin wannan kuka da kike yi sannan ace ba aikin asiri bane."
Ayatul Kursiyyu ta shiga karantawa tana tofawa Rashida a ka wai maganin sihiri. Sada ya dagata ya shigar da ita daki tana ta kuka. Habu da Harira kuwa sai kallo. Yaya Tagwai ko a jikinta. Tasan komai daren dadewa zasuyi mata godiya saboda ta rabasu da masifa.
*****
Yaya Babba ke bacci harda minshari Zubaida ta samu ta lallaba da kyar ta fito daga gidan.
A iya watannin da tayi duk shegantakar karuwanci 'yar tsohuwar nan ta koya mata. Tun tana nuna bata so har ta hakura tana biye mata saboda a rage matakan tsaron da aka saka mata. Bata taba yarda wani yayi amfani da ita ba. Tace sai ta koma gidan Uwargida. Yaya Babba bata damu ba ita dai aikin da aka sakata tayi.
Tunda tazo gidan sai yau ta samu damar fita. Kullum tana tunanin Asmau. Bata sani ba ko ta haihu yanzu.
Gidan Uwargida ta tafi da niyyar idan Asmau tana nan su gudu tare. Daga bakin kofa ta hadu da wata cikin matan gidan.
"Zuby kin dawo?" Ta fada tana kallon irin shigar Zubaidan da yadda ta kara cikowa.
Zubaida ta rage murya
"Shiga ki kirawo min Asmau bakuwar nan. Don Allah kiyi sauri ga wannan kada ki fadawa Mama kin ganni." Dari biyar ta bawa matar ta karba sannan tace "wannan bakuwar baki dade da tafiya ba ta gudu. Har an sami wasu bakin biyu bayan tafiyarta."
Zubaida tayi wani murmushi cike da jindadi."Alhamdulillah nasan taji shawarata ta koma gidansu."
Daga nan ta dauki jakar kayanta ta juya ita ma. Matar ta biyota tana tambayar ina zata je Zubaida tayi gaba ko kulata bata yi ba.
Daga nan bata zame ko ina ba sai tasha ta nemi motar Kano. Basu dade ba motar ta cika suka hau titi. Indai bata manta ba Asmau tace sunan umguwarsu Hotoro layin kwamishina Adamu. Gidansu zata nema don tasan in Allah Yaso yadda Asmau ke bata labarin Umma zasu riketa har ta sami mijin aure. Ta dan yi murmushi "ko me Asmau ta haifa" ko meye ma zata tayata raino tunda dai taji shawararta ta koma gida. Allah Yasa dai ta gane gidan.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽24
Batul Mamman💖
Zuciyar Asmau banda zafi babu abinda take yi. Ji take kamar ta haye tsakiyar titi mota tayi gaba da ita kowa ya huta. A tunaninta babu sauran mai kaunarta a duniya. Tana wannan jan kafar ne taji kwandastan wata hayis yace Hajiya zaki hau? Kai ta gyada tare da shiga motar da bata san inda suka nufa ba.
Sunyi tafiya mai dan nisa wasu na sauka wasu na hawa kwandastan nan yana ta tambayarta kudin mota hankalinta baya wurin saboda kukan da take yi. Wata mata ce a kusa da ita ta dan taba ta sai ta kula da yadda kafafun Asmau suka yi futu-futu ko takalmi bata dashi. A tsorace matar ta ja jikinta gefe ta karewa kodaddun kayan jikinta kallo. Daga murya tayi iya karfinta tace
"mahaukaciya ce"
Nan da nan hankalin jama'a ya dawo kanta aka fara cewa za'a sauka. Dreban hayis din ya hau yiwa kwandasta fadan ya dauko musu mahaukaciya. Tsayawa yayi suka janyo hannunta aka fitar da ita daga motar. Bakincikin da take ji ya hanata magana. Wai yau ita ake yiwa kallon mahaukaciya.
Tana kallo motar tayi gaba sannan ta kula da cewa inda take ya danyi wajen gari babu gidaje sosai. Ga wani irin ciwon baya da mara da ya taso mata lokaci guda. Runtse idonta kawai tayi tana tafiya zafin kwalta yana kona mata kafa sai ji tayi an taka burki da karfi motar tayi wata irin kara.
A razane ta bude idonta. Wata mota ta gani mai kyau ashe da tana tafiya ta dan hau titi bata sani ba. 'Yan samari biyu ne suka fito suna ta zaginta ta uwa ta uba. Dukkansu bata jin akwai wanda ya shekara ashirin sai tsayin kafa kawai. Kayan jikinsu sun nuna yaran sun fito daga gidan arziki sai dai daga yanayin maganarsu ta kula a buge suke.
Wanda ya danfi tsahon yayo kanta kamar zai doketa dayan yayi saurin rike masa hannu
"Haba Annur, duba da kyau mahaukaciya ce. Tunda Allah Yasa bamu tabata ba kawai zo mu ware".
Mai suna Annur ya ja tsaki "da ka barni na mareta. Haka kawai zata janyo mana makara a wurin party din. Sai an gama zabe fine chicks din"
Ciwo ne ya sake kwasarta tayi kasa tana rike baya. Jajayen idanunta da suka rine don kuka ta daga tana kallonsu tace
"don Allah ku taimaka min"
Wanda ya hana a mareta yace "kai Annur it seems matar nan haihuwa zata yi".
"Gaddafi bazan tsaya a wurin nan ba. Kaima kasan yanzu haka an fara nemanmu a gida. Allah Ya kawo wani amma ba mu ba. "
Da sauri yaja hannun abokinsa suka shiga mota. Gaddafi ya leko da kansa ta taga yana kallon Asmau kwance a kasan gefen titi. Motoci basu da yawa saboda har lokacin goma na safe bata yi ba. Gashi titin fita gari ne.
Annur ya fizgi motar da gudu Gaddafi yana rokonsa da su taimaka ko wane gari suka gani su sauketa a nan wani ya kaita asibiti. Tsaki da zagi Annur ya rinka yiwa abokinsa kafin ya juyo da motar suka dawo inda take. Ransa a bace yace Gaddafi ya shigo da ita. Kuma ya zauna a baya tare da ita saboda kada ta kai masa duka. Shi duk saurinsa ya isa party din abokinsa da za'ayi a Jos batare da sun sami matsala a hanya ba domin kuwa ko license na tuki basu dashi.
Da sauri Gaddafi ya taimakawa Asmau ya shigar da ita motar. Ciwo ya fara tsananta a gareta sai gumi take yi. Annur ya soma yiwa Gaddafi magana da turanci
"Tun farko da nasan haka zaka yi min da ban ce ka raka ni Jos dinnan ba. Amma babu komai zanyi maganinka. Hmmm yau 'yan matan Jos suna da manyan baki" ya karasa maganar yana wata shu'umar dariya.
"Kayi hakuri Annur ni kaina bansan meyasa ta bani tausayi ba. Ji fa yadda take gumi ko magana bata iyawa. Allah Ya tsinewa wanda yayi mata cikin nan dai"
Ciwon taji ya lafa mata ta kallesu tayi dan murmushi. Ga dukkan alamu Yassar zai girmesu duk su biyun. Ita ma turancin tayi musu wanda hakan yasa hankulansu dawowa gareta
"Wanda yayi min ciki ya rasu fatana Allah Ya jikansa. Ku kuma ina yi muku fatan shiriya daga Allah kada ku fada mummunan hali nan gaba."
Annur ya juyo kamar ba shine yake tuki ba yana kallonta da mamaki dan sauran mayen da yake duk ya tafi "wai dama ke ba mahaukaciya bace. Gaddafi kaga ka dauko mana masifa ko? Ke police ce ko 'yar mafiya?"
Kasa bashi amsa tayi saboda ciwo. Yana maida kansa titi saura kadan ya bugawa wani. A haka ya cigaba da tukin Gaddafi yana yi mata sannu. Sun isa wani gari yayi kokarin tsayawa su sauketa sai ya kula da 'yan sanda a gefen wurin. Dolensa ya sake taka mota yana ta sharara gudu. Basu tsaya a ko'ina ba sai da suka shigo garin Jos. A wannan lokacin ba karamin tausayin Asmau duka su biyun suke ji ba. Wai dama hake ake nakudar gaske ba ta fim ba. Idan taji ciwo tana addua sai taji suna tayata suna yi tare. Idan ka matso kusa da motar sai ka zata duk su ukun suke nakudar, sai sharba gumi suke yi kamar babu AC a motar . Bakin gate din wani asibiti da yayi musu kama da na gwamnati suka tsaya. Sai da Annur ya taimakawa Gaddafi suka fitar da ita daga motar. Tsoronsu daya kada a kamasu ayi tunanin ko sato ta sukayi ko suna da alaka da ita.
Cikin tsananin jin ciwo Asmau ta tambayi sunansu suka fada mata.
"Bansan daga ina kuke ba amma ina muku fatan alkhairi da shiriya don nasan iyayenku ba rayuwar da suke yi muku fata ba kenan. A duk inda kuke ku rinka tunanin lahirarku. Nagode sosai."
Daga haka ta lallaba ta karasa bakin gate din. Wannan karon sai da Gaddafi yayi da gaske Annur ya ja motar suka tafi.
Kasa daga kafarta tayi taji kamar zata fadi wata mata mai uniform din masu shara da wanke bandaki ta tareta daga baya tana yi mata sannu. Daga nan bata san da yadda aka shigar da ita asibitin ba. Ko awa daya bata cika ba Allah Ya taimaketa ta haihu.
Tana jin wannan kukan na jarirai taji gabadaya damuwarta ta gushe burinta kawai taga abinda ta haifa. Nurse din da ta karbi haihuwar tace mata kin sami 'ya mace. Asmau tayi murmushi tare da dago kai ta kalli kyautar da Allah Yayi mata tana hamdala. Gata da 'yar Abubakar sai dai babu shi kuma babu iyayensu. Kaddara ta riga fata a kansu. Ba don haka ba da yanzu iyayensu za'a mikawa jaririyar.
A wani dan zani aka nade 'yar aka miko mata. Ta zuba ido tana kallonta. Sai kuma kuka ya kwace mata da ta tuna bata da wata hanyar kulawa da 'yar. Ko suturar da zata saka mata bata da ita. Wannan mai sharar tayi mata Allah Ya raya sannan ta fita daga dakin. Ba jimawa ta dawo da wasu tsofaffin riga da zani amma a wanke ta bawa Asmau fuskarta a sake.
"Ga wannan akwai ruwa a bandaki ki gyara jikinki sai ki saka. Idan kin fito sai ki fadi wa za'a kirawo a danginki."
Asmau kamar kada ta bata yarinyar haka take ji. A rayuwarta bata taba son wani kamar yadda take jin son jaririyarta ba. Tayi godiya ta karbi kayan ta wuce bandakin.
Bata dade ba ta fito aka kaita dakin hutu. Wani likita yazo ya dubata yace babu wata matsala amma sai da safe zasu sallameta. Ya bata takardar magungunan da zata siya. Bayan fitarsa mai sharar ta kara dawowa wurinta ta sake tambayarta ina 'yan uwanta saboda a bakin gate ta ganta ita kadai. Ya kamata a sanar dasu ko don su kawo mata abinci da kayan baby.
Asmau bata da amsar da ta wuce kuka. Matar sai ta kyaleta ta koma bakin aikinta. Ita kuma ta cigaba da kallon jaririyarta tana bacci. Ikon Allah, yarinyar kama take yi da Mama Yalwa. Asmau sai ta rantse duk 'ya'yan Mama babu mai kama da ita kamar wannan yarinyar. Dama duk sunfi kama da Alh Adamu. Da namiji ta haifa dama sunan Abubakar zata saka masa. Amma tunda mace ce zata saka sunan mahaifiyarsa kamar yadda suka yiwa juna alkawarin sai sun sakawa 'ya'yansu sunayen iyayensu. Da wannan tunanin ta danyi murmushi. Babbar matsalarta yanzu bata san ta ina zata fara ba? Bata da komai bata da kowa. Sannan bata san irin tarbar da za'ayi mata ba idan ta koma gidansu.
Wannan tunanin ya isheta ga kudin asibiti duk da na gwamnati ne tasan ko yaya za'a bukaci ta biya kudin wani abin. Hakan ne yasa tana ganin duhun dare yayi ga cikinta kamar anyi mata yasa don yunwa ta kwance dankwalinta ta goya jaririyar da shi sannan ta zura hijab dinta tayi waje. Gara ta gudu tun kafin ace ta kawo kudin da tasan bata da su. Ta kusa karshen barandar da zata kaita bakin gate ne taji muryar mai sharar nan tace "ba dai guduwa zakiyi ba".
*****
Hajjo ce ta farka daga bacci a gigice ta rinka juyi akan gado har ta tabbatar dai a dakinta take. Hawaye ne kwance a fuskarta sakamakon mafarkin da tayi da jikarta Asmau. Kuka ta ganta tana yi tana kiran Hajjon da ta taimaketa. Duk yadda taso ta kama hannun Asmau ya gagara har ta farka. Jikinta sai karkarwa yake ta tashi ta dauko mayafinta a gefen kujerar dakin ta tafi dakin Garzali. Ko agogo bata duba ba tayi sa'a ta same shi yana fesa turare da alama fita zaiyi.
Tsayuwar kirki ta kasa cikin tsawa tace yazo ya kama karnukansa zata fita.
"Hajjo ina zaki je da yamman nan. Biyar da rabi fa".
Harararsa tayi fuska a murtuke don kada ya kawo mata wargi "inda ka aike ni zani. Kaga kada ka bata min lokaci wuce muje".
Suna fitowa yayiwa karnukan fito suka yo kansa Hajjo ta samu ta fice. Don sauri kafarta har zafi take yi mata taji takun mutum kamar ana binta da gudu. Duk da a tsorace take haka ta dake bata juya ba take magana
"Rabe wallahi yau ko me zaka ce sai naje wurin Bara'atu. Ba kai ka haifa min Shu'aibu ba shiyasa baka san ciwon iyalinsa ba."
Garzali yayi yar dariya
"Ni ne Hajjo. Raka ki zanyi. Nima rashin mu'amala dasu ba karamin damuna yake yi ba."
Tayi murmushi "Allah Yayi maka albarka" daga nan ta bashi labarin mafarkin Asmau da tayi suna tafiya.
*****
Tun kafin azahar Zubaida ta iso garin Kano ta samu mai tasi suna ta yawo a unguwar Hotoro basu gane gidan ba. Gajiya yayi ya sauketa bayan ya karbi dubu biyu a hannunta. Har zai tafi sai ya dawo saboda ta bashi tausayi yace ta sami mai adaidaita sahu sunfi sanin layukan cikin unguwa.
Tayi sa'a kuwa ta sami wani ta fada masa inda take nema. Da ya kula bakuwa ce a garin ya tsula mata kudi sai dai bata damu ba. Biyan bukata yafi dogon buri. Kusan dubu talatin ta dauko a cikin kudin da Uwargida ta bawa Yaya Babba.
A cikin layin mai adaidaita sahun ya nuna mata gidan kwamishina. Tayi masa godiya ta bashi kudinsa. Daga nan tasan Asmau tace gidansu babu nisa. Wata tsohuwa ta hango da wani mutum a bakin gate din wani gida tayi saurin karasawa kafin su shiga.
Sallama ta rinka yi musu suka juya suna kallonta a tare. Riga da siket ne a jikinta sun dameta sosai ga katuwar jakar kaya sai wani siririn mayafi da ta rataya a wuya. Da murmushi a fuskarta ta dan rissina ta gaishesu sannan tace "don Allah gidan Umma nake nema. Umman Asmau".
Garzali ya sake kallon Zubaida sannan yace "nan ne".
Ko jiransu batayi ba ta shige ciki tana kwalawa Asmau kira. Yassar da yake shanya ne ya fara ganinta bai san lokacin da ya saki wandon da yake kokarin dorawa a igiya a kasa ba ya nufota. Zubaida na ganinsa ta saki murmushi.
"Tabbas nan ne gidan don naga kamarku. Kai ne Yasir ko?"
Kallon rashin sani yake mata yace "a'a sunana Yassar"
Zubaida tace "hakane kaini wurin Asmau".
Hanyar falon ya nuna mata sai ya kula da Hajjo da Kawu Garzali. Har dan tsorata yayi sai yaga Hajjo tana hawaye
"Zo nan Yassar, zo naji duminka a jikina"
Ji yayi kamar mafarki yake ya fara tunanin gudu Garzali ya damko wuyan rigarsa ya hada shi da jikin Hajjo. Kuka ta fashe dashi na takaicin yadda jikanta yake nuna tsoro da fargabar ganinta har yana neman gudu. Tana rike da hannuwansa tace "kuyi hakuri Yassar. Ku yafewa wannan tsohuwar".
Shima kukan ne ya zo masa ya kankameta. Ashe akwai ranar da Hajjo zata nuna masa so? Tana rike da hannunsa suka shiga cikin falon.
Umma suka gani da Aina'u da kuma Jafar sun saka Zubaida a gaba suna kallonta jin tace daga Azare tazo wurin Asmau.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽25
Batul Mamman💖
Cikin matsanancin tsoro Asmau ta juyo tana kallon matar. Hakuri ta soma bata murya na rawa ga hawaye na wanke mata fuska tana sanar da ita bata da kudi kuma bata kowa da zai taimaketa. Matar sai tayi murmushi "kada ki damu ni ba wani abu zanyi miki bane. Hasali ma na rasa dalilin da yasa tun da na shigo dake cikin asibitin nan hankalina yake kanki. Amma dai biyoni mu koma ciki".
Ba yadda ta iya haka tabi bayan matar suka tafi wurin wata mai sharar. Matar babba ce don da gani zatayi sa'a da Umma. Wadda ta biyo ta gaisheta cikin ladabi sannan ta gabatar da Asmau a matsayin 'yar uwarta wadda bata da komai. Rokonta tayi akan ta ranta mata kudi su biya a sallameta ita kuma tayi alkawarin biyanta a hankali cikin albashinta.
Babbar matar ta kalli Asmau tayi wuri wuri da ita tana jijjiga goyonta. Da gani ma a tsorace take tace "kudin ba wasu masu yawa bane Zulaiha, ga wannan kije ki biya. Sai mu warware daga baya. Ki gaida mutan gidan."
Zulaiha tayi mata godiya itama Asmau ta saka baki suka yi tare. Bayan sun fito ne Asmau ta rasa bakin godewa wannan matar mai suna Zulaiha. Matar bazata girmeta da yawa ba. Tuna mata take da Anti Rashidan Azare. Bayanta tabi suka koma wurin likita aka sallameta duk da yaso kwarai ta kai washegari.
Zulaiha tace "babu komai yiwa kai ne. Bari na canza kaya nazo muje gidana tunda dare yayi".
Asmau sai mamaki take yi meyasa wannan matar ta taimaketa alhali bata san komai a game da ita ba. Suna fita daga asibitin bus suka hau maleji suka sauka a wata unguwa da Asmau bata sani ba. Daga nan suka bi cikin lunguna suka karasa wani gida mai karamin gate. Idan kaga gidan dole zakayi tunani masu shi suna da rufin asiri. Sai ka shiga zaka ga babu wasu abubuwan more rayuwa. Yara ne har shida suka fito suna yi mata sannu da zuwa ta amsa fuska a sake sannan suka gaishe da Asmau. Zulaiha ta dauki karamin ciki da baifi shekara ba ta soma shayar dashi. Falon da ta kai Asmau ko leda babu ta dauko tabarma ta shimfida mata.
Yaran ta tambaya ko su kadai ne a gidan suka ce eh. Babbar cikinsu mace ce da bata fi shekara tara ba sai namiji dake binta. Duk yaran babu wata tazara tsakaninsu. Ta dauko naira hamsin daga gefen zaninta ta bawa namijin "Muhsin siyo mana kan kifi, ke kuma Humaira dauko attaruhu hudu da rabin albasar nan ta safe ki jajjaga min. Sannan ki dauko katuwar tukunyar nan ki wanke a cikata da ruwa yanzu zan zo na dora"
Da murna yaran suka fita tunda suka ji batun kan kifi sun san yau gidan za'a ci dadi. Asmau na nan zaune Zulaiha ta kunna kyandir sannan ta tashi ta dora mata ruwan wanka ita da baby ta kuma dora girki.
Wankan Zulaiha ta fara yiwa jaririyar itama Asmau tayi da taimakonta dai. A ranta sai mamakin matar take yi. Haka kawai daga haduwa sai taimako? Bayan tayi wankan taji dadin jikinta tana zaune Zulaiha ta sakawa jaririyar kayan karamin danta Ali irin wanda suka yi masa kadan. Allah Sarki wannan jaririya ko kayan sakawa bata dashi. Ta gama ta nado mata ita a zani ta bata sannan aka kawo mata dafadukan taliya 'yar hausa harda yaji da ruwa. Asmau ta zauna ta narki abincin nan tana yi tana godiya. Sai da ta koshi sannan Zulaiha ta tambayeta sunanta da kuma abinda ya fito da ita. A nan Asmau ta soma kuka. Tana yi tana bawa Zulaiha labarinta mai cike da ban tausayi da gargadi ga sauran mutane. Sosai Zulaiha ta tausaya mata. Tace
" Tun da na ganki haka nan Allah Yasa naji ina son na taimaka miki. Kinga nima ba wani abu gareni ba. Ganinki da nayi sai ya tuna min da tawa rayuwar shiyasa na zabi na taimakeki ko Allah zai kawo min sassauci a cikin kuncin da nake ciki. Kinga dare yayi ki kwanta zuwa gobe zaki san nawa labarin. Allah Yasa ki sami ruwan nono da wuri kafin hakurin 'yar tamu ya soma karewa ta fara kuka".
Murmushi Asmau tayi tana kallon fuskar 'yarta ta hasken kyandir. Sun tashi Zulaiha zata nuna mata dakin da zata kwanta don gidan akwai dakuna suka ji an shigo falon.
Wata dattijuwa ce rike da wani mutum yana ta tangal tangal kamar zai fadi. Daga bakin kofa ta tsaya tana jifan Zulaiha da harara "yau kuma wani sabon iskancin ne ya tashi kina jina ina fama da Gidado bazaki zo ki taimaka mu kaishi daki ba?"
Idonta ne ya sauka akan Asmau ta daure fuska
"Wannan kuma fa, daga ina?"
Zulaiha tana saka hannuwan mutumin a kafadarta tace " 'yar haya na samo dazu a asibiti. Zata karbi hayar daki daya a gidan nan, kinga kudin ko cefane sai mu kara dashi".
"Cefanen banza, ni zan rinka karba ina karawa a jari na."
Asmau ta dan duka ta gaishe da matar ko kallonta bata yi ba ta fara tambayar ina abincinta. Shi kuwa mutumin da Zulaiha ke ja surutai yake marasa kan gado. Da suka zo wucewa ta gabanta wani irin wari yake fitarwa.
A falon ta jira Zulaiha ta kaishi daki sannan ta nuna mata wurin da zata kwana. Tana kwance rungume da 'yarta tana jin wannan dattijuwa tana masifar anyi kaza anyi kaza ba daidai ba. Can kuma taji mutumin wanda ta tabbatar mijin Zulaiha ne ya soma zage zage bata bashi abincinsa ba zata kashe shi da yunwa. Har Asmau tayi bacci babu abinda take ji yana fitowa daga bakin Zulaiha sai "kuyi hakuri".
*****
A can Kano kuwa lokacin da Yassar ya shigo ciki rike da hannun Hajjo sai da gaban Umma ya fadi. Aina'u tayi saurin labewa a bayan Umma a tunaninta daukarsu tazo yi.
Hankalin Umma ya bar Zubaida ya koma wurin Hajjo. Cikin sanyin jiki ta gaisheta sai dai sabanin da sai taji Hajjon ta amsa cikin kuka. Har inda Umma ke tsaye taje ta kama hannuwanta tana hawaye "Bara'atu nasan ke mai hakuri ce da kawaici. Ki dubi girman Allah ki yafewa wannan tsohuwar banzar hakkinku da ta dauka."
Umma ta saki baki cike da mamaki. Me kunnenta yake jiye mata ne? Hajjo ta cigaba da magana tana kuka "nayi nadamar abinda nayi miki tsahon shekarun nan. Ni kaina bansan dalilin yin hakan ba. Bakiyi min komai ba na dora miki tsana da tsangwama."
"Alhamdulillah" Umma ta fada a fili itama da nata hawayen. Hajjo ta cigaba da rokon gafara Umma tace ai zuwanta kadai yasa komai ya wuce. Hajjo ta mika hannu "zo nan autar Bara'atu. Taho wurin kakarki kinji 'yar albarka. Jafaru baka ce komai ba. Ku yafeni ko don darajar babanku"
A darare Aina'u ta matsa jikin Hajjo. Garzali ma a kunyace ya gaishe da Umma ta amsa bakinta yaki rufuwa don murna. Jafar ma murna yake yi sai dai hankalinsa yafi karkata ga Zubaida dake tsaye tana kare musu kallo.
Sai da aka dan sami nutsuwa a falon sannan Jafar yace "Umma bakuwar nan fa tana jiranki"
Hakuri Umma ta bata ko wurin zama basu bata ba suna farincikin fara daidaituwar al'amuran danginsu. Aina'u ta kawowa Zubaida lemo da abinci tana ci suna kallonta. Jira suke yi ta gama ta fada musu abinda ta sani game da Asmau.
Da ta gama ne Umma ta fada mata Asmau tayi wata bakwai rabonta da gida. Zubaida ta dan cije lebe fuskarta ta nuna rashin jindadi "nayi tunanin gida da dawo da na koma aka ce min bata nan. To ina ta tafi?"
Hajjo tace "kinga yarinya, bayani zakiyi mana yadda zamu fahimceki sosai. A ina kika ga Asmau'un?"
Zubaida ta fada musu komai game da zamansu da Asma'u. Umma da Hajjo sai kuka jin Asmau ta zauna a gidan karuwai. Tace hatta yadda ta sami cikin duk ta fada min.
Umma ta share hawaye
"Ta fada miki sunan wanda yayi mata cikin?"
"Eh tace sunansa Abubakar".
Umma ta toshe bakinta da hannu tana wani kukan. Dama Qasim ya tabbatar musu cikin Abubakar ne amma basu bawa wacce abin ya shafa damar bayani ba. Yassar ta nuna "tashi maza kaje ka kira Mama Yalwa. Ka fada mata bakuwa ce tazo daga Azare wadda tasan Asmau".
Ba'a dade ba sai ga Mama suka zauna Zubaida ta fada musu duk labarin da Asmau ta bata na waya da yadda al'amarin ya cigaba. Falon sai salati suke yi ana jimamin wannan abu. Ace tarbiyar shekara da shekaru wasu can da basa kishin addini suyi ta fito da samfurin yada alfasha salo salo suna turawa 'ya'yan musulmi.
Hajjo tace "to shi shegen giruf (group) din aje a tarwatsa mana kowa ya huta. Haka kawai an janyowa marainiya fadawa mummunar rayuwa. Kada na kaiku da nisa ko mu da babu waya a zamaninmu waye ya koya mana yadda ake yi tsakanin mata da miji. Gashi mun rayu dasu cikin kwanciyar hankali mutuwa ce ta raba. Duk wannan shaidancin kuma da ake yadawa ai bai hana mutuwar auren yara kanana ba."
Mama da batasan yadda akayi Hajjo ke nuna damuwarta akan Asmau ba tace " ai group din a waya ake bude shi. Ni abinda ya fi damuna bai wuce yadda zakiga yara da matan aure a dauki waya tun safe har dare ki rasa me ake gani. To ashe duk harkar lalacewa ce duk da dai ana samun karuwa ta wani fannin. Yaranmu da sunyi waya sai kiga basu da lokacin komai sai nata."
Zama sukayi ana ta mayar da zance kowa na tofa nasa. Kawu Garzali a fusace yace "ita wacece wannan Walidar ne? Tayi fatan kada mu hadu don wallahi sai nayi mata rauni. Kawaye da abokan banza sunfi saurin lalata tarbiya. Ni ba daga abokin bane muka kare a haka." Ya dubi Jafar da Yassar
" yanzu kuna da uba saboda haka duk yaron da na gani baiyi min ba kafin na kore shi ta kanku zan fara".
Umma tayi murmushin jindadi. Duk da tasan Garzalin kansa baya sahun mutanen kirki amma dai taji dadin kulawarsa ga 'ya'yan dan uwansa.
"Walida kawar Asmau ce tun primary. Kuma itama nata mahaifin yana kokari. Don ranar da abin ya faru kafin mu dawo daga asibiti yazo ya dauketa."
Hajjo taja tsaki wanda har Zubaida da Aina'u sai da suka yi dariya "anyi ta baya ta rago. Shi da 'yarsa ta bata ta wani ai ya jira nasa lokacin. In Allah Ya yarda sai ta dauko masa abin...."
Mama da Umma suka dakatar da Hajjo daga yin mummunar addua. Daga nan suka yanke shawarar washegari da sassafe zasu tafi Azare neman Asmau. Anti Bintu da Shemau duk an sanar dasu haka Abdulhalim da Qasim.
*****
Annur da Gaddafi tunda suka isa masaukinsu ko abinci sun kasa ci. Abokin da suka zo wurin party dinsa yayi ta damunsu da su tashi suyi wanka a tafi sai su kalli juna su sunkuyar da kawunansu kasa. Gabadayansu dana sanin baro gidajensu suke yi. Sun baro iyayensu musamman matan cikin tashin hankali domin sun san yanzu ana nan ana nemansu. Yau da suka ga yadda mace ke wahala wurin haihuwa kowannensu shiriya ta saukar masa. Sannan ga adduar da tayi musu bayan taimakonta da suka yi. Suna kallo aka shirya duk 'yan samari sa'aninsu suka fice sai su kadai. Karshe ma shawara suka yanke gobe zasu koma asibitin neman wannan matar daga n[truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽26
Batul Mamman💖
Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi
"Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba".
Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa. Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan. Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta mata rayuwa.
"Wane suna zaki saka mata?"
Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani.
"Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne".
Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina. Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki boye mata suna ne?"
"Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu."
Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi.
"Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar radiyo yana nemanki".
Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji muryarsa.
"Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a aljihun wando yanzu na duba babu".
Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa.
"Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan gida?"
Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace "Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi."
Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai, ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai zan tambayeki na nawa za'a siyo?"
Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata. Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye. Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma babu wanda ya kama kafarsa.
Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki."
Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan hakan shine kike zaune dashi"?
"Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru to sai dai hakuri."
Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan.
Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta zauna bawa Asmau nata labarin.
"Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado. Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar.
A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya. Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji. Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta. Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata. Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda take sona ba."
Zulaiha ta share hawaye
"A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa. Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan shiga duniya."
A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai
"Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan babu abinci. Matar da ta ranta min kudi jiya makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana. Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina da ya taba zuwa gidan nan."
Asmau taji tausayin Zulaiha sosai.
"Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya"
"Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu zauna tare mu rufawa juna asiri".
Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi ba.
*****
Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a jiyan zai taho.
Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita. Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo basa nan.
Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami wadda ta ga jikata Asmau."
Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa "yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?"
"Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa.
Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba. Kuma da kake cewa su ba wata tsiya bane to a wurina sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali.
Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma, Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar , Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi. Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta ba.
Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua suke yi Allah Yasa su dace a sameta.
Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta.
Ai tunda matan gidan suka ga bakin dake shigowa tare da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai, kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai barkwanci da yawan wasa.
Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma.
"Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan fa?"
Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take"..
Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali. Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba".
Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace 'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki zanyi sai naga wanda ya tsaya miki."
Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na basu hakuri.
Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya aureta.
Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada musu inda Asmau taje.
Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...."
Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin da kayan Asmau suke.
Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi kayan tana kuka.
Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida.
Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki idan aka ji wacece ta haifeki."
Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba. Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine da goro suka fito.
"Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma kinyi kin gama da yardar Allah."
Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta."
Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki. Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti.
Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida tayi iyaye da miji in ce dai shikenan."
Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar kyautatawa Asmau.
*****
Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan Sada.
Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama. Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa.
"Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya da gaskiya kun hau kun zauna."
Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...."
Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba. Wayyo Allah na"
Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda ya janyo shigowar sauran mazan.
Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?"
Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau.
Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace "amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba."
Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini tsufa"
Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora bazasu fi goma ba"
Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da tsufansu suke fadan shekaru.
Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace ya ganta?"
Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare har zuwa Jos ne.
0 comments:
Post a Comment