Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi
"Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba".
Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa. Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan. Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta mata rayuwa.
"Wane suna zaki saka mata?"
Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani.
"Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne".
Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina. Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki boye mata suna ne?"
"Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu."
Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi.
"Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar radiyo yana nemanki".
Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji muryarsa.
"Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a aljihun wando yanzu na duba babu".
Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa.
"Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan gida?"
Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace "Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi."
Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai, ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai zan tambayeki na nawa za'a siyo?"
Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata. Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye. Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma babu wanda ya kama kafarsa.
Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki."
Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan hakan shine kike zaune dashi"?
"Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru to sai dai hakuri."
Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan.
Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta zauna bawa Asmau nata labarin.
"Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado. Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar.
A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya. Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji. Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta. Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata. Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda take sona ba."
Zulaiha ta share hawaye
"A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa. Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan shiga duniya."
A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai
"Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan babu abinci. Matar da ta ranta min kudi jiya makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana. Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina da ya taba zuwa gidan nan."
Asmau taji tausayin Zulaiha sosai.
"Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya"
"Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu zauna tare mu rufawa juna asiri".
Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi ba.
*****
Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a jiyan zai taho.
Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita. Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo basa nan.
Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami wadda ta ga jikata Asmau."
Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa "yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?"
"Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa.
Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba. Kuma da kake cewa su ba wata tsiya bane to a wurina sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali.
Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma, Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar , Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi. Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta ba.
Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua suke yi Allah Yasa su dace a sameta.
Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta.
Ai tunda matan gidan suka ga bakin dake shigowa tare da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai, kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai barkwanci da yawan wasa.
Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma.
"Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan fa?"
Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take"..
Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali. Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba".
Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace 'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki zanyi sai naga wanda ya tsaya miki."
Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na basu hakuri.
Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya aureta.
Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada musu inda Asmau taje.
Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...."
Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin da kayan Asmau suke.
Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi kayan tana kuka.
Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida.
Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki idan aka ji wacece ta haifeki."
Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba. Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine da goro suka fito.
"Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma kinyi kin gama da yardar Allah."
Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta."
Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki. Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti.
Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida tayi iyaye da miji in ce dai shikenan."
Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar kyautatawa Asmau.
*****
Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan Sada.
Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama. Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa.
"Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya da gaskiya kun hau kun zauna."
Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...."
Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba. Wayyo Allah na"
Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda ya janyo shigowar sauran mazan.
Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?"
Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau.
Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace "amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba."
Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini tsufa"
Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora bazasu fi goma ba"
Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da tsufansu suke fadan shekaru.
Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace ya ganta?"
Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare har zuwa Jos ne.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽27
Batul Mamman💖
Qasim yayi alkawarin zuwa neman Asmau daga kauyen farko har Jos din. A sanyaye suka koma gidan Sada wadanda suke ganin sun zame musu 'yan uwa sakamakon kyautatawar da suka yiwa Asmau. Duka kayanta Rashida ta hada musu harda na jariran. Umma dai tasha kuka har ta gode Allah. Su Anti Binta, Shema'u da 'ya'yan Mama su Suwaiba duk sunyi ta kira su ji yaya ake ciki.
Da zasu tafi har bakin mota Rashida da Sada suka yi musu rakiya aka karbi numbar wayar juna.
Qasim ya cika alkawari wurin binciken Asmau sai dai babu wani abin arziki da ya samu duk da haka bai hakura ba. Duk inda yaji alamar anga mace da ta bata sai ya duba ko za'a dace.
*****
Humaira babbar 'yar Zulaiha ke zaune gaban Asmau tana jira ta gama sakawa Amatullah kaya a goya mata ita. Zulaiha tace "Asmau kada ki goya mata ita kin santa da rawar kai. Tsorona daya kada garin rashin nutsuwa su fadi shiyasa idan tace na goya mata nake hanawa".
"Umma da gaske zan nutsu bazan yar da ita ba. Ni da har girki nake yi miki amma sai ki hana ni goyo".
Asmau ta dauko zani cikin wanda Zulaiha ta bata "tashi kinji babbar Yaya na goya miki ita. Ai nasan ko bakin kofar gidan bazaki je ba a nan zaku zauna"
Duk yadda Zulaiha taso hanawa haka akayi goyon Humaira ta fita tsakar gida tana murmushin jindadi. Asmau ta sauke ajiyar zuciya. Watansu uku a gidan nan lokaci yayi da ya kamata ta fara neman aikin yi ko don ta ragewa Zulaiha nauyi. Ga Zinaru kullum tayi zancen kudin haya sai Zulaiha tace mijin Asmau ne ba'a samunsa ko da a waya. Gori kala kala take sha akan abincin da suke bata wanda ba danta ke nema ba. Gyara zama tayi yadda zata rinka hango Humaira da kyau sannan tace da Zulaiha
"Nasan kina kokari sosai tun zuwana Allah Kadai zai baki lada. Amma ya kamata na nemi aiki. Saboda Amatullah dai nasan babu gidan da zasu daukeni kuma gashi bani da wata takardar makaranta. Shine nayi tunanin ko zan sami irin naki sai nayi".
Zulaiha ta katse ta "haba Asmau, yarinyar nan har nawa take da zaki fara neman aiki? Ki bari ta kara kwari. Ni zamanmu dake duk wahalar da zan sha ban dauketa komai ba. Na dade ina rayuwar kunci da rashin makusanci kafin zuwanki."
"Duk da haka gara nayi aikin ko don na taimaka miki. Ki duba fa tunda nazo su Muhsin basu taba zuwa makaranta ba saboda rashin kudi."
Zulaiha tasan gaskiya Asmau ke fada sai dai kuma tana tunanin kankantar Amatullah. Shawara suka yanke washegari da taje aiki ta sami makociyarsu wadda tayi mata hanya. Da taimakon matar nan Allah Yasa Asmau ta sami aikin itama.
Yanayin aikin nasu da wuya suje tare. Juya musu akeyi idan wasu suka yi na safe wasu sai suyi da yamma. Hakan yayi musu dadi kodayaushe akwai mai zama da yaran a gida.
Asmau sai ta goya Amatullah ta tafi aikinta tunda bata isa a fara barinta a gida ba. Da yake yarinyar akwai dariya ga dan jiki sai tayi saurin shiga ran sauran ma'aikatan. Idan Asmau zata wanke bandaki sai a rike mata ita taje tayi aikin. Tunda ita mace ce mai ilimi sai ya zamto tafi sauran mayar da hankali wurin tsaftace duk inda ta gyara. Albashinta na farko kaya ta siyawa Amatullah har kala biyar da Ali autan Zulaiha. Sauran kudin kuwa kayan abinci ta siyo musu. Zulaiha sai godiya take yi mata har tayi mamaki ita da ake ta dawainiya da ita.
Zamansu haka yayi ta tafiya cikin lumana da taimakon juna. A hankali likitoci da dama suka san Asmau saboda tsaftarta zance har wajen Chief Medical Director (shugaban asibiti). Da yaji yadda ake yabonta da son cigabanta tunda har turanci ta iya sosai ya canja mata aiki daga shara zuwa bada kati. Ba karamar murna sukayi ba saboda albashi ya karu. Ko kadan babu hassada tsakaninta da Zulaiha. Karshe ma aka mayar da ita bangaren bada sakamako idan anyiwa mutum gwaji a asibitin. Dan ihsani kuwa daga nurses da likitoci tana samu sosai a dalilin Amatullah.
Bata da wata matsala a lokacin sai Gidado da Zinaru. Daga ita har Zulaiha basa jindadin zama dasu. Kudin hayar daki kuwa taki bawa Zinaru a hannunta kamar yadda take ta naci. Su Humaira aka mayar makaranta. Shi kuma Gidado baya shakka ko a gaban Zulaiha baya iya boye son da yake yiwa Asmau. Ya sha nemanta sai dai taki bashi hadin kai kuma kullum haka ta faru sai ta fadawa Zulaiha don gudun matsala. Tayi ta yiwa Zulaiha nasihar rabuwa dashi sai dai tayi murmushi kawai. Wannan ya tabbatar mata da cewa har yanzu Zulaiha na son mijinta. Sai ta kyaleta suka cigaba da zamansu.
*****
Annur yana kwance a daki bayan ya dawo daga makaranta yana dan danna wayarsa aka turo masa wani text da hoto. Da farko baiyi niyar bude hoton ba sai da ya karanta labarin yarinyar a matsayin wadda mijinta ya rasu ranar aure kuma aka gane tana da ciki. Tsaki yayi sannan ya bude hoton don shi da Gaddafi yanzu karatu suka saka a gaba.
Matar ya gani kyakkyawa da ita har ya ajiye wayar sai ya sake daukowa ya duba hoton. Hannunsa na rawa ya turawa Gaddafi yace ya duba ko ya gane ta. Ba jimawa Gaddafi ya kira yace sai ya ga kamar matar nan mai ciki da suka taimakawa mai suna Asmau. Matar da suka je nema a asibiti basu sameta ba.
Tausayinta suka ji musamman da suka tuna halin da suka tsinceta da irin nasiharta garesu. A cikin sati daya suka yi ta bincike da tambaya ko akwai wanda ya santa har suka dace da samun wani dan makarantarsu da yace a unguwarsu abin ya faru a Kano. Yaron har gidan Umma ya kaisu suka sanar da ita labarin haduwarsu dai Asmau. A wannan ranar an sha kuka sannan Umma tace ita ta hakura zata cigaba da yi mata addua. A duk inda take Allah Ya tsareta kuma Yasa ta dawo gida da kafarta.
*BAYAN SHEKARA BIYAR*
Idan kaga Asmau bazaka ce itace tazo garin Jos a rame da tsohon ciki ba. Duk da bata da jiki kamar da amma ta dan samu nutsuwa. Ita da Zulaiha kuwa ko 'yan biyu bazasu nuna musu kusanci ba. Tana tuka tuwo Zulaiha na tsinke zogale taji sallamar Amatullah da Aliyu.
Da gudu Amatullah tazo ta rungumeta ta baya
"Ummina tuwo kike yi?"
Asmau ta bata rai "Ama so kike na kone zaki fado min haka. Me ya dawo daku yanzu bayan ba'a tashi ba?"
Zulaiha tayi dariya "tunda kika ji ta kiraki da _Ummina_ kema kinsan akwai abinda take so".
Amatullah ta kama kasan dan hijab dinta tana wasa dashi, Zulaiha ta dubi Ali "kai da kayi mata rakiya sai ka fadi me ya dawo daku ai"
Ya ja baya da sauri "Umma nifa fitsari tace zata yi na rako ta".
Asmau ta nuna hanyar bandaki "wuce kiyi kizo ku koma".
Sum-sum Amatullah ta wuce bata dade ba ta dawo ta sake tsayawa a bayan Asmau. Zulaiha ta kula akwai abinda take so ta janyota jikinta
"Amatullah ta Ummi me kike so ne, fada min naji"
Dan turo baki tayi wanda duk lokacin da tayi sai Asmau ta ga kamarta da babanta ta fito sosai Nabila ce take shan kafi kaza kuma Ummi ta hanamu roko shine nazo ta bani biyay na siyo".
Zulaiha ta kwashe da dariya "bakinki ne biyay din ai"
Amatullah ta dan buga kafa "Umma biyay nace fa ba biyay ba".
Wannan karon Asmau ma tayi dariya. Amatullah bata iya fadan duk kalma ma harafin *r*, idan ka fada yadda tayi kuma tace sam ba haka ba.
Zulaiha ce ta basu naira biyar biyar ita da Ali suka tafi. Asmau tace
" da baki basu ba. Sun baro makaranta takanas saboda kwadayi. Yanzu gobe idan taga wani abin sake dawowa zatayi."
"Na sani, rokon ne bana so tayi. Idan suka dawo sai a kwabesu akan hakan. Amma da ban bayar ba karshenta nan gaba bazamu sani ba sai da su roka a makarantar.
Asmau ta dage sosai kullum tana yiwa yaran lesson musamman na turanci da larabci. Duk wanda yake da homework zata zauna ta koya masa. A makarantunsu 'ya'yan gidan sun fita daban saboda kokarinsu. Ita kam Zulaiha zuwan Asmau ya janyo mata alkhairi. Manyan yaran Humaira, Muhsin, Amina da Habib duk makarantar gwamnati suke yi. Anisa, Aliyu da Amatullah kuwa a makarantar kudi mara tsada irin ta cikin unguwa suke. Gabaday Asmau ta tattara hankalinta ga 'yarta. Burinta a rayuwa yarinyar ta sami kulawa sosai ta kuma san addininta don gujewa [truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽28
Batul Mamman💖
Da yamma Asmau ta dawo daga wurin aiki tun kafin ta bude gate din taji kukan Amatullah. Ji tayi kamar an tsikareta. A duniya babu abinda ta tsana kamar a taba mata 'ya da rashin adalci domin kuwa indai Amatullah tayi kuka a cikin gidannan baya wuce aikin Zinaru. Su Humaira ji suke yi da ita balle tace anci zalinta. Da sauri ta shiga ta sami Zinaru tsaye da bulala ta daga zata sake dukan Amatullah ga Ali da Anisa a tsaye suna nasu kukan. Asmau tayi saurin dauke 'yarta bulalar ta sauka a bayanta. Don ma da mayafi amma ba karamin shigarta tayi ba. Bata damu ba ta duba jikin Amatullah sai ga shati lafcece a bayanta tana ta kuka da sheshsheka.
Kawar da kan da take yiwa Zinaru yazo karshe. Bazata zuba ido a kashe mata 'ya ba. Cikin tsananin bacin rai ta dago ido tana kallon Zinarun da ko a jikinta an kamata tana dukan karamar yarinya haka.
"Me tayi miki kike mata irin wannan dukan?"
"Lallai Asamau wuyanki yayi kauri. Ni kike tsarewa da ido haka kamar wata sa'arki. Ko zaki rama mata ne?"
Amatullah sai wani irin kuka take yi, Asmau ta tambayi su Ali me suka yi.
Zinaru tace "jikokina babu abinda suka yi. Ba su nake duka ba. Wannan afiruwar yarinyar da har yau ba'a san ubanta ba ita na daka ehe. Na fada na sake nanatawa ta dena kiran Gidadona da Baba taki ta dena. Kun zo kun tare mana a gida kamar tare muka gina shi daku"
Rai a bace tace "akan wannan kike neman kashe min ita. A iya zamanmu ban taba tanka miki ba idan kina cin zalinta. Zulaiha ke shiga kullum. To ina so ki sani wallahi kika kara taba min 'ya za'a ji kanmu dake. Na baki girman da zan baki a matsayinki na uwa amma tunda hakan baiyi miki ba zan zauna dake yadda kike so. Kuma da kike cewa ba'a san babanta ba don Allah ki nuna mana naki dangin ko na baban Gidado. Mtsww, gida kuma yanzu na fara zama tunda kema ba naki bane."
Zinaru taji zafin maganganun Asmau "ni kike fadawa haka saboda baki da mutumci. Ita Zulaihan ce ta fada miki bamu da 'yan uwa?"
Asmau bata tsaya ta karasa sauraron Zinaru ba ta shige daki. Da kyar ta rarrashi Amatullah tayi shiru har bacci ya dauketa tana ta ajiyar zuciya. Kuka ne yazo mata da ta tuna irin rayuwarta. Yau da a gidan aure ta haifi Amatullah babu abinda zai fito da ita daga cikin danginta har wani ya sami damar fada musu magana irin haka. Ta tabbatar har ta mutu duniya bazata taba mantawa da cewa a zina tayi cikin 'yarta ba. Ta cuci karamar yarinya saboda soyayya.
Su Humaira sun dawo daga makaranta suma kannensu ke fada musu abinda Zinaru tayiwa Amatullah. Duk sun zo sun dubata har lokacin bacci take yi.
Bata farka ba sai bayan magriba da zazzabi mai zafi jikinta sai rawa yake yi. Lokacin Asmau tana kan abin sallah tana karatu taji fadowar Amatullah daga kan katifarsu. Sauri tayi taje ta dagata taji jikinta yayi mugun zafi. Hankalinta ya tashi ta rasa me zata yi mata. Da kuka ta fito da ita a kafada ta tafi dakin Zulaiha wadda bata dade da dawowa gidan ba. Har tana jin muryar Ali yana fada mata Zinaru ta zane Amatullah. Ko sallama bata yi ba ta shiga "Zulaiha taimakeni don Allah Amatullah zata mutu."
Zulaiha ta bar kokarin cire kayan aikinta ta karbi Amatullah tana salati. Kwantar da ita tayi akan katifa tana ta karkarwa. Asmau ji take inama ciwon ya dawo gareta. Ta matsa jikin bango ta jingina tana jira kawai ace mata ta cika.
Amina ce ta shigo Zulaiha tace ta samo mata ruwa mai kyau a roba da sauri. Asmau na kallo ta tubewa Amatulla kayanta duk da sanyin da take ji da aka kawo ruwan ta cire dankwalin kanta ta rinka guga mata ruwa a jikinta. Kukan Asmau kai kace Amatullah ta rasu. Zulaiha tana bata hakuri. Da taji zafin ya dan ragu tace bari ta cire kayanta su tafi asibiti. Asmau ta dauki Amatullah ta goyata suka fita. Yaran gidan duk jikinsu yayi sanyi. Kafin su karasa asibitin da suke aiki numfashin Amatullah har wani sama yake yi.
A asibitin emergency suka wuce likita da nurses suka karbeta. Ana ta gwaje gwaje Asmau tana kuka kamar ranta zai fita. Likitan ya fito ya bata takardar magani sannan yace zazzabi ne mai zafi da kuma alamun pneumonia(ciwon nemoniya ko sanyi da yake kama kirjin yara).
Hankali a tashe Zulaiha ta karbi takardar da kudin magani a hannun Asmau ta tafi ita kuma ta shiga dakin da aka mayar da Amatullah. Idonta a bude sai dai ta fada kamar ta dade babu lafiya. Tana ganin Asmau abinda ya fara fitowa daga bakinta shine "Ummi ni waye Babana ne? Zinayu tace Baba Gidado ba babana bane."
Wani kukan ne yazo wa Asmau. Yana daga cikin _abinda ake gudu_ ki haifi yaro kafin aure ya tambayeka mahaifinsa ki rasa amsar bayarwa. Tun farkon haihuwarta take fargabar irin wannan lokacin. Ta tabbatar idan Amatullah ta kara girma abin sai yafi haka. Cike da nadama take tunanin da tana gidansu Yaya Jafar, Yassar , Yaya Abdulhalim da Umar duk bazasu bar 'yarta tayi maraici ba. Allah Sarki Abubakar ta fada a ranta. Yau ga sakamakon rashin hakuri ta kusantar zina wanda ya janyo musu fadawa ga yinta. Shekara biyar da faruwar abin amma babu ranar da zata wayi gari bata tuna da wannan yinin ba. Hawaye ta share ta kirkiro murmushin dole "Ama babanki yana aljannah kinji ko. In sha Allah yana can yana jiranmu. Kullum kika yi sallah kice Ya Allah Ka yafewa babana Kasa shi a aljannah."
Ta zauna a kan gadon Amatullah tayi pillow da cinyarta."Ummi yaushe zamu je aljannah wurin babana? Ni yau nake son zuwa na fada masa Zinayu ta dokeni. Sai ya yama min ko."
Asmau tace "zamu je watarana kinji. Amma ba yau ba don Allah. Sai kin girma kin zama babbar malamar addini kin tara yara da yawa".
Amatullah tayi dariyar jindadi "idan munje shine zai kaini school. Ya siya min jaka mai kyau irin da takalmi. Har kayan sallah fa." Kula tayi da hawayen da Asmau take yi tace "Ummi ki dena kuka zai siya miki kema. Sai mu tafi namu gidan ko?"
"Uhm" kadai ta iya cewa hankalinta yana wani wurin. Yaya zata yi da Amatullah yarinya mai dan karen wayo. Nan gaba kadan tasan zata sake tayar da zancen.
A haka Zulaiha tazo ta same su. An bawa Amatullah maganinta da allurai sannan Zulaiha ta koma gida dauko musu kayan kwana.
Cikin dan lokaci labari ya karade asbitin 'yar Asmau bata da lafiya. Ma aikata da yawa suka rinka zo duba ta. Sai da sawu ya dan dauke wata likita tazo tana yiwa Asmau fadan irin dukan da take yiwa Amatullah wanda take tunanin harda shi da kukan da tayi ya sa mata zazzabi. Asmau ta tabbatar mata ba ita tayi dukan ba. Likita tace to dai ta kiyaye don babu mai kular mata da 'ya kamar ita kanta. Sannan dole a kula da hanata shiga sanyi da kura don tana ganin alamun asthma gareta ba pneumonia ba. Sake tsorata Asmau tayi. Tabbas Abubakar yana da asthma ba abin mamaki bane idan 'yarsa tayi. Amma irin halin da taga yana shiga ga kashe kudi wanda bata dasu sosai ya tayar mata da hankali.
Kwanansu uku sannan aka sallamesu. Kullum Zulaiha da su Humaira indai ba aiki ba ko su suna makaranta a nan suke zama sai dare su koma gida. Asmau kuwa taci alwashin bazata sake yarda da Zinaru ta taba lafiyar gudan jininta ba.
*****
Zinaru ce zaune a gaban wata kawarta da suke kasa kaya a kasuwa take fada mata irin maganganun da Asmau ta fada mata ranar da ta zane Amatullah
"Wato Kande maganganun sun kona min rai. Yarinya kamar wannan ina ta kawar da kai duk da bana son zamanta damu sai da ta kaini bango. Kuma ina ji lokuta da dama tana ziga shegiyar nan Zulaiha akan ta rabu da Gidado. Ni yanzu idan auren ya mutu ai ta tona min asiri. Ina zamuje mu zauna. Gashi dan banzan yaron har yau bai san ya girma ba. Daga shaye shaye sai neman mata ya iya."
Kande ta tabe baki "tun farko ke kika yi sake. Ke da kike da jari a hannu. Gidado ai *farar haihuwa* ne. Kina kalli ya rasa matar aure sai Zulaiha ga 'ya'yan masu kudi a gari. Kinsan mu da rauni akan mai kyau. Idan da hali kisa ya saketa ita kuma bakuwar ku koreta ya auro sabuwa 'yar masu kudi".
"Kin kawo shawara Kande. Amma babbar matsalar shine gidan nan nata ne. Ga yara har shida don bala'i haihuwa kamar zomo. Don ma Allah Ya takaita mana ta tsaya. Babbar fa zatayi shahudu yanzu. Kinsan auren kuruciya suka yi."
"Duk wannan ba matsala bane. Ke dai ki samu yaron nan ya dau saiti ya gyara kansa. Da kanki zaki bani labari. Kin sanni da shige shige sai na tayaku neman mai maiko."
Tafawa suka yi sannan kowacce ta cigaba da ihun azo a sayi kayanta.
*****
Kwanaki hudu a tsakani wurin karfe tara na dare Asmau ta fito zata je bandaki taji Zinaru tana ambaton sunanta. Tsayawa tayi taji abinda za'a ce tayi.
Daga cikin dakin Zinaru ke cewa Gidado "dole ne ka rabu da Zulaiha hakan ne kawai zai sa Asamau ta bar gidan nan. Zulaiha ma da dabara zaka saketa yadda zamu tsira da gidan nan. Ka santa da son 'ya'ya sai ka ce mata ka saketa amma tare da yaran zamu tafi. Nasan idan taji haka zata bar maka gidan ita ta fita. Kande ta riga ta samo mana 'yar wani kusa a gwamnati da zaka yi auren jari da ita."
Gidado cikin muryar wanda giya bata gama sakinsa ba yace "amma Zinaru idan muka yi haka kamar bamu kyautawa Zulaiha ba. Kuma Asmaun nan na fada miki ita ma sonta nake yi."
"Sakarai mara lissafi, Asama'un me. Ana maka zancen 'yar masu kudi. Yanzu dai ko da safe ne sai kayi yadda nace."
Asmau ta jinjina bakin hali irin na Zinaru. Gashi Zulaiha laulayi take yi babu wanda ya sani sai ita. Har kuka tayi saboda bata son cigaba da haihuwa ga talauci da rashin gata. Sauri tayi taje dakin Zubaida ta fada mata abinda taji sai tayi tuntube da kwaftareren takalmin Gidado. Zinaru ta fito da sauri taga ko waye suka hada ido da Asmau. Ta dan ji tsoro da farko sai kuma ta dake ta soma kwalawa Zulaiha kira.
Cikin bacci taji kiran da Zinaru ke yi mata ta fito tana murza ido. Zinaru tace "munyi magana ne da Gidado akan yadda Asamau ta raina ni da irin rashin jituwar dake tsakaninmu shine yace zai koreta. Ni kuma sai na tuna masa cewa gidan nan ba namu bane. To yanzu yake fada min wai ko dai ki sallameta da kanki ko kuma ya sakeki mu tafi mu bar miki gidan."
Zulaiha ta rude "me yayi zafi Gidado har da zancen saki? Zinaru ki bashi baki don Allah."
Asmau tace "wallahi karya take yi Zulaiha. So take ya sakeki ki bar musu gidan".
Zinaru ta kalli Gidado
"Ince dai kaga irin yadda take yi min. Ni bazan zauna a gidan nan ana wulakanta ni ba".
"Zinaru kiyi hakuri indai Zulaiha ce yanzu zan saketa mu tafi"
Yaransu duk suna kallo ita Asmau har ta soma jindadi sai kawai Zulaiha ta durkusa a kasa ta rike masa kafa tana kuka"ka rufa min asiri Gidado kada ka sakeni. Ina zani da yaran nan."
Muhsin ya dagata tsaye "Umma kawai ki bari ya sakeki kema kya huta da duka da wankin amai. Dama don ke kike yi ne nake tayaki amma daga yau sai muga mai wanke masa"
Bakin Muhsin din ta daka "waye ya saka bakinka. Ku bar wurin nan kafin na bata muku rai."
Suna tafiya ta cigaba da rokonsu shi da babarsa. Zinaru ma tasa kukan karya ita dole su bar gidan. Ganin haka Asmau tace "indai saboda ni ne to in sha Allah da safe zan tafi. Zulaiha ki tuna da gatan da Allah Yayi miki ki koma gaban iyayenki. Gobe nima gidanmu zan tafi na roki nawa iyayen gafara".
Daga haka ta bar wurin. Wannan wane irin so ne Zulaiha ke yiwa Gidado. Tausayi take bata don wannan ba karamar jarabawa bace. Mutum ya mayar da kai bolarsa amma ka kasa rabuwa dashi.
Da kuka Zulaiha ta biyo bayan Asmau."kiyi hakuri Asmau ki zauna gobe zan sake rokonsu."
"Zulaiha a kaina bazan so kiyi ta zubar da mutumcinki a gaban su Humaira ba. Ni dai shawarata ki koma gida ki roki gafarar su Inna".
Zulaiha tayi shiru. A yadda zuciyarta ta karaya bata jin zata iya zuwa gaban iyayen da ta yiwa rashin kunya harda kaisu kara.
*****
Karfe goma na safe Asmau ta gama hada 'yan kayanta da na Amatullah. Tayi mata wanka suka shirya tafiya. Daga kan Humaira har Ali kuka suke yi basa son tafiyarta. Itama kukan take yi amma gara ta koma gida. Kewar iyayenta ta dameta gashi duk inda ta zauna sai wani dalili ya koreta.
Kamar bazasu rabu ba ita da Zulaiha kowa kuka ta rike hannun Amatullah suka fita.
Tasha suka je bata dade ba motar Kano ta cika suka fito. Sunyi tafiya mai dan nisa sun wuce wani gari Saminaka ba jimawa suka ga wani mutum yana daga hannu alamar neman taimako. Gefensa mace ce babba da dogon hijab sai wata 'yar budurwa da bazata kai shekara ashirin ba. Dreban farko kamar kada ya tsaya sai kuma yaji tausayin dattijuwar suka tsaya. Motarsu ce ta lalace ga makanike yana dubawa amma yace injin ya buga sai an sauke shi. Su Asmau suka marmatsa matar da yarinyar suka shigo. Aka bar dreban da makanike.
Sallama tayi musu suka gaisa tare da yi musu godiya.
Ta kalli Amatullah da ke zaune a cinyar Asmau tayi mata murmushi.
"Yan mata yaya sunanki"
"Safinatu Abubakay. Amma Ummina Amatullah take ce min ko Ummi"
Asmau tayi dan murmushi kawai. Fargabar zuwa gida ce fal a zuciyarta. Ita kuwa dattijuwar tace "Safinatu Abubakay ko Abubakar" tana yar dariya.
Amatullah tace "Abubakay nace ba Abubakay ba"
Mutane da yawa a motar sai dariya. Can ta dan taba matar nan "kema aljannah zaki je? Ni da Ummi can zamu wurin Babana. Ban taba ganinsa ba, Zinayu zai zane saboda tana duka na."
Asmau ta dan kai mata duka saboda suruta sannan ta share hawaye. Matar nan tana kallonsu sai taji tausayinta ya kamata. A hankali yadda Asmau zata ji tace "Allah Ya jikansa"
Asmau ta dago kai tace "Amin" wani hawayen yana fita a idonta.
Sun iso Kano garin da hadari ga kura. Tana kokari daukar kayansu ne ta ga Amatullah ta dafe kirji numfashi baya sauka. A gigice ta saki jakar ta rungumota tana kuka. Yau kam ta tabbatar asthma gareta saboda yadda take kokarin numfashi yaki sauka.
Wannan matar da wasu maza suka taho wurinta. Dreban da yazo daukar matar yana zuwa tace Asmau ta tashi su tafi asibiti. Kuka take yi kawai ga Amatullah ta sandare.
Wani asibitin kudi suka je aka karbi Amatullah. Tana ji matar tana waya tana sanar da wani inda suke.
Bayan kamar awa daya an samu Amatullah ta dawo hayyacinta suna wani daki Asmau sai godiya take yiwa matar taji an turo kofar dakin tare da sallama. Wani daddadan kamshi ne ya mamaye dakin kafin ta kula da mutumin da ya shigo cikin shigar sojoji masu babban mukami.
Amatullah dake kwance ta tashi zumbur tace
" Ummi wannan ne baban nawa?".
ABINDA AKE GUDU🙆🏽29
Batul Mamman💖
Dan tsayawa yayi yana kallon kyakkyawar yarinyar. Tana daga zaune harda ware hannuwa ta dan bata rai "Baba bazaka yi min oyoyo ba? Nima bazanyi maka ba. Shine ka taho aljannah ka barmu ni da Ummi."
Asmau kunya ta isheta ta kai hannu zata hana Amatullah sai matar ta girgiza kai.
Taku yake mai cike da kamala da kuma kwarjini ya karasa daya barin gadon ya zauna yana murmushi. Asmau ta kasa daga ido ta kalle shi. A kan gadon ya zauna ya janyo Amatullah ya dorata akan cinyarsa.
"Oyoyo baby din Baba. Kiyi hakuri bazan kara tafiya na barki ba kinji"
Amatullah ta kankame shi ya dago kai ya kalli mahaifiyarsa yana murmushi. Juyowa yayi inda Asmau take zaune suka hada ido ba shiri ta kara sunkuyar da kanta. Mutumin ba karamin kwarjini yayi mata ba. A kalla zai kai shekara arbain. Kayan jikinsa sun kara masa kyau. Shi kuwa mayar da hankalinsa yayi ga Amatullah yana shafa mata kai. Girmansa da matsayinsa bai sa ya kyamaceta ba. Muryarta ya sake ji tace "Baba idan anje aljannah ba'a zuwa gida ne. Kullum ni da Ummi bamu ganka ba. Kuma Zinayu sai tayi ta dukana baka zuwa ka yama min".
Sake hada ido suka yi da Asmau ya kula da kwallar da ta cika mata ido. Wani tausayinsu ne ya shige shi a lokaci daya. Ko ba'a fada ba yasan baban yarinyar nan ya rasu. Wannan ne dalilin da zaisa yarinyar ta rinka ambaton an tafi aljannah an barsu.
Tana daga jikinsa yace "daga yau duk wanda ya sake tabaki sai na rama miki kinji."
Matar da tayi masa waya tace "ai wannan Zinayu taga ta kanta. Tun dazu ake kawo kararta."
Amatullah tace "Zinayu nace fa ba Zinayu ba".
Daga matar har danta sai da suka yi dariya sosai. Asmau ta gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake yana kallon Amatullah. Yarinyar ta shiga ransa lokaci guda.
Matar ya kallo yace "Hajiya gara kizo ku tafi gida nasan kin kwaso gajiya da yunwa. Munyi waya da Falalu za'a janyo motar gobe. Da kinyi min waya tun kuna hanyar ai da na turo mota daga Jos din."
Murmushi tayi "kai babu komai fa. Na tura Bilkisu da Shafiu a siyo musu abinci ne kafin mu tafi."
Ta dubi Asmau "kin kira 'yan uwanki kuwa? Ya kamata a san halin da kuke ciki kada suji shiru"
Shiru Asmau tayi, to ita wa zata kira bayan yanzu bata da numbar kowa a gidansu. Ta sunkuyar da kanta kasa kawai ta sako karya "babu kudi ne a wayar, amma nasan zasu kira idan suka ji shiru."
Hajiya ta dan bata rai "haba ke kuwa, me ya hana tun dazu kiyi min magana da tuni an siyo ko na baki tawa ki kira. Kai taimaka a samo mata kati ta kira gidansu. Wane layi gareki?"
Ba karamar kunyar taji ba. Tayi karya sun dauka gaske ne. Duk da dai kudin wayar dama bai wuce flashing ba tace "MTN".
Cikin ladabi ya mike zai fita Amatullah ta riko masa riga kamar zatayi kuka "Baba zan bi ka"
Wata waya da Asmau ta tabbatar mai tsada ce ya zaro daga aljihunsa ya mika mata "gashi ki rike min yanzu zan dawo"
Bata so ba haka ta sake shi ya fita. Kafin ya dawo Bilkisu ta shigo dauke da ledojin take away na abinci. Shima mutumin sai gashi ya dawo ya mikawa Hajiyarsa katin ta bawa Asmau. Na dubu daya da dari biyar ne guda hudu duka matar ta bata. Tayi ta godiya a son ranta daya ma ya isa.
Bilkisu ta durkusa har kasa tace "Uncle ina wuni"
"Lafiya kalau, ya gajiyar hanya?"
Ta amsa masa da lafiya, ya shiga tambayarta kanwarsa dake Jos wadda ta kasance mahaifiya ga Bilkisun.
Asmau dai kashe wayarta tayi sai tayi kamar ta saka katin guda daya sannan ta tashi ta koma gefe kamar tana waya don karfin hali harda kwatancen asibitin.
Bata san duk abinda take yi Soja na kallonta ba. Mamaki ne ya kama shi da ya fuskanci me take yi. Tana juyowa suka hada ido yayi mata wani irin kallo. Babu shiri ta sauke nata idon ta basar duk da idanunsa sun tsorata ta.
Hajiya ta tashi "to mu zamu tafi ni sunana Hajiya Lubabatu wannan jikata ce."
Bilkisu na dariya tace "Uncle kuma dan fari da ba'a fadar sunansa"
Ya kai hannu zai rankwasheta "Hajiyar tawa kike tsokana ko. Hajiyata kyaleni da wannan yarinyar zan miki maganinta."
Kana ganin Haj Lubabatu kunya take ji bata son wasa da dan nata.
Asmau tayi murmushi tace "ni sunana Asmau. Nagode sosai Hajiya Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi"
"Amin, gobe in sha Allah zamu dawo don nasan dakyar a sallameku. Idan mutan gidan sun zo ki gaishesu"
Asmau tace to ta tashi zata rakasu Haj Lubabatu ta dan tsaya ta dauko wayarta daga jaka ta mikawa Bilkisu "bani numbarki saboda kira ko da akwai wani abu."
Duk da ta gode da taimakon da matar nan tayi mata amma bata so alakar tayi tsaho. So take yi ta koma gida asirinta a rufe. Yanzu da Amatullah babu lafiya dai bazata iya tafiya ba don bata san yaya zasu tarbeta ba, bai kamata taje musu da lalurar 'yar da suka so a zubar da cikinta ba. Number kawai ta kirkira da ka ta karanto Bilkisu ta kwafa a wayar Hajiya.
Hajiya sai sake cewa tayi "yauwa to kirata sai ta samu tawa numbar a wayarta ko."
Ji tayi cikinta ya murda kada asirinta ya tono. Sa'arta daya ta kashe wayar tace "wayar ta mutu yanzu amma zan saka chaji idan an kawo wuta"
Haj Lubabatu tayi murmushi "to babu komai. Ga abinci nan ki tabbatar kin bata yanzu. Safinatu Allah Ya baki lafiya kinji".
Daga haka Haj Lubabatu ta fita Asmau na binta da sakon addua. Shima dan nata zai fita Amatullah ta dage shi zai bata abinci ba Umminta ba. Da murmushi a fuskarsa yace mata yanzu zai dawo ba nisa zaiyi ba. Yana dago kai Asmau ya gani tana kallonsa don tabbatar da abinda yace. Wannan karon murmushin da yayi mata mai nuni da ta kiyayi dawowarsa sannan ya fita. Ai kuwa ta hau Amatullah da fada akan me zata ce ya bata abinci. Yarinya ta bare baki tana kuka, takaici duk ya ishi Asmau don ta tabbatar zai dawo tunda ya sake barin wayarsa.
*****
Har bakin mota ya raka su Hajiya tana tambayarsa yaushe zai tafi gida yace yana son lallaba yarinyar nan ne saboda kada tayiwa mamanta rigima.
Haj Lubabatu tace "Allah Sarki ai nima ta bani tausayi. Karshenta tana yarinya sosai uban ya rasu shiyasa ta damu da ganinsa yanzu. Nasan dole hakan ya rinka dagawa babarta hankali."
"Nima haka kawai naji ta shiga raina Hajiya"
Da alamun tausayi a fuskarta tace "ai na sani, kai da son yara kuma. Bari mu wuce sai ka dawo"
Bai bar wurin ba har sai da motar ta fita daga gate din asibitin sannan ya koma ciki. Hankalinsa sam bai kwanta da Asmau ba. Yana tunanin ko dai irin matan nan ne masu damfara ko kuma tana da sirrin da bata so a sani.
*****
Amatullah sai kuka take yi saboda irin fadan da Asmau take yi mata.
"Idan baki rufe min baki ba nida ke ne. Haka kawai daga ganin mutum sai ki dage shine babanki. To nan ba aljannah bane kuma na fada miki yana can. Bude bakinki ki karbi abincin...."
Sallamarsa ta sake ji cikin muryar da ta gama ganewa yanzu. Amatullah na ganinsa ta matsa daga kusa da Asmau har allurar da ake yi mata karin ruwa ta soketa ta tsala ihu. Kukanta yaji har ransa ya matsa da sauri ya gyara mata ya bi Asmau da harara, ita kuwa ta matsa gefe rai a bace.
Rarrashin Amatullah yayi sannan ya bata abincin kamar ba soja ba ya mayar da kansa yaro a gabanta. Ko sau daya bai yiwa Asmau magana ba har sai da Amatullah tayi bacci sannan ya tashi.
Wayarsa ya miko mata fuskarsa babu alamun wasa ta dan ja da baya.
"Karbi mana, numbarki zaki saka min"
Tayi kicin kicin da fuska
"Na bawa Hajiya"
"Na sani, ina son karba saboda na kira 'yata anjima".
"Da ka barshi ma, saurin mantuwa gareta kana fita zata mantaka"
Ya dan daga gira "ke kadai kike son faruwar hakan banda ni da ita. Nasan bazata manta ni ba."
Duk da haka Asmau taki karbar wayar tana adduar ya fita kawai. Tunda an biya musu kudin asibitin ba yau ta fara ba, guduwa zatayi idan dare yayi.
Ya tsareta da ido "na fa san ba numbar daidai kika bawa Hajiya ba. Kuma nasan baki kira kowa ba dazu. So ki bani numbar tun girma da arziki kafin na fara bincike a kanki."
Duk da ta tsorata harararsa tayi tana magana a dan tsorace
"A wane dalili zaka yi bincike a kaina? Daga taimako, dole ne na bada number?"
Yadda ya kalleta yasa tayi shiru. Wayarta ya dauka daga kusa da Amatullah ya kunna sannan ya saka numbarsa ya kira tasa wayar.
Mayar da wayar yayi inda take ya kama hanyar fita "saura kuma kiyi tunanin cire sim din. Na bar sojoji biyu zasuyi min gadin 'yata don kada ki gudu cikin dare".
Gabanta sai da ya fadi da ya fadi haka. Ji tayi kamar yana karanta abinda ke ranta. Ba'a fi minti biyar da fitarsa ba taji wayarta na kara. Da sauri ta dauko a tunaninta Zulaiha ce sai ta sake jin muryarsa.
"Baban Safina ne, Colonel Ishaq Muhammad Jikamshi. Na bugo ne don na tabbatar baki cire sim din ba." Bai jira tayi magana ba ya kashe wayar yaja motarsa yayi gaba.
Asmau ta tsaya tana kallon wayar cike da mamaki. Tsoro ne ya kamata don da gaske ta yarda ya bar masu tsaronta kada ta fita su bindigeta a banza. A hankali ta sake maimaita sunan nasa. Dama a jikin rigarsa ta ga inda aka rubuta I.M Jikamshi.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽30
Batul Mamman💖
Sau biyu Asmau na leka waje amma bata ga soja ko daya ba. Ga tsoro kada sai ta fita su tsareta. Haka nan ta hakura zata zauna don dole. Dadin dadawa tana so Amatullah ta kara samun sauki.
Sallah tayi ta ci abinci itama sannan ta saka kati daya a wayar ta kira Zulaiha ta fada mata inda suke. Sauran ukun kamata yayi ta sayar dasu ta fada a ranta.
****
Col. Ishaq gidansa ya wuce dake Tudun yola. Gidan da a yanzu baya son zama cikinsa saboda abubuwa da dama da yake tuna masa dasu. Dakinsa ya shiga ya dauko wasu takardu ya jira akayi har sallar isha sannan ya tafi gidan Hajiyarsa.
Babu kowa a falon lokacin da ya shiga shiyasa ya wuce dakin kaninsa wanda yayi aure kwanakin baya inda yanzu ya mayar nasa. Yayi wanka ya saka kananan kaya sannan ya hau gado ya kwanta. Tunanin Amatullah yake yi yana dan murmushi. Yarinyar ta tsaya masa a rai. Sai kuma ya koma tunanin mamanta. Ji yayi yana son sanin ko ita wace ce. Tunani kala kala ya rinka yi game da ita. Da ya gaji wayarsa ya dauko yana karanta sakonnin da aka turo masa wasu ya share wasu ya bada amsa.
Sunan da baiyi tunanin gani bane ya dauki hankalinsa da sauri ya bude sakon. Sallama tayi masa sai hoton baby da ya biyo baya. A kasan hoton ta rubuta _Alhamdulillah mun sami baby boy_.
Da kyar Ishaq ya iya hadiyar yawu don tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki. Har wani guntun zazzabi ne ya nemi rufe shi. Ya tashi ya fita zai je wurin Hajiya a daki sai yaji muryarta a falo.
Labarai take kallo ita kuma Bilkisu tana zaune a kasa suna hirar sanyin Jos da mai aikin gidan Hinde. Motsinsa yasa Hajiya kallon kofa tace "yaushe ka shigo gidan ban sani ba?"
"Dazu ne bayan Isha"
Ya zauna akan kujerar kusa da ita tare da mika mata wayar. "Kin gani Badar ta haihu"
Hajiya ta kalli su Bilkisu "ku dan bamu wuri"
Tashi suka yi Bilkisu sai da ta waiwayo ta kalli Kawunta tana mai tausaya masa.
Bayan sun wuce Hajiya ta karbi wayar ta kalli hoton jaririn tayi guntun murmushi "Allah Ya raya" ta gyara zama sosai tana fuskance shi
"Mai sunan Alhaji, nasan irin damuwar da kake ciki amma ina so ka sani ba'a yiwa Allah dole. Duk yadda kaso Allah bai nufa zaku kare rayuwarku da Badariyya ba. Duk kuma yadda kuka nemi haihuwa kasan wani baya haifar dan wani."
Kansa a kasa yace "na sani Hajiya. Yanzu na tabbatar mun rabu har abada kuma kamar yadda Mami take yawan fada ya tabbata nine bana haihuwa" a yadda yake ji a wannan lokacin gara yayi kuka ko zaiji sauki a ransa. Tausayi ya bata sosai.
"A matsayinka na musulmi ka sani cewa babu abinda bawa zai samu a rayuwarsa sai wanda Allah Ya kaddara masa. A bisa tsari da hikimarSa *Yake azurta wasu da 'ya'ya mata, wasu da 'ya'ya maza, wasu Ya hada musu duka biyun, wasu kuma Ya barsu haka* duk inda Allah Ya jarabceka da fadawa kasan babu wayo ko dabararka. Ka zama mai hakuri wata rana zaka ci ribarsa".
Ajiyar zuciya yayi ya gamsu da bayananta wanda ya sani dama.
"Nagode Hajiya, bari naje na kwanta"
"Abinci fa"
"Bana jin yunwa. Sai da safe"
Tasan halin da zai shiga kenan shiyasa tun tana Jos shekaranjiya da maman Badariyya tayi mata waya ta sanar da ita haihuwar bata fada masa ba.
*****
Sake kwanciya yayi yana tuno rayuwarsa ta baya. Auren soyayya suka yi da Badariyya suna zamansu lafiya. Har suka shekara biyu da aure ko batan wata bata taba yi ba. Gashi Allah Yayi shi da son haihuwa tun bata fara damuwa ba ya matsa su je asibiti. An duba su aka tabbatar musu duk lafiyarsu kalau su jira lokaci.
A haka har suka yi shekara shida babu labari. Maman Badariyya duk ta damu. Magunguna har da na gargajiya kawo musu take yi amma shiru. Ishaq ya tayar da hankalinsa sosai gashi ko ina suka je sai ace babu matsala. A wani asibitin Jiddah ne ma aka ce kwan haihuwarsa bashi da karfi. Ya shiga damuwa sosai sai gashi Badariyya ke bashi baki.
Sun sami shekara goma da aure Mamanta taje har gidan Hajiya ta roketa arzikin asa Ishaq ya saketa tunda anfi tunanin matsalar daga gareshi. Hajiya Lubabatu tayi ta rokonta akan tayi hakuri sai tace to nan da wata shida idan ba'a saki canji ba dole ya saketa.
A wannan wata shidan Ishaq yaje asibitoci sunkai takwas. Magani kuwa duk wanda aka bashi sha yake yi. Lokaci na cika har gida Mami tazo ta bukaci ya saki 'yarta. Badariyya kanta tace ko waye da matsalar a cikinsu zasu hakura tunda suna son juna. Mami ta dage abu har kunnen manya a danginsu duka. Ganin al'amarin yana neman lalacewa dole ya yi mata saki daya suka rabu ba don suna so ba. Tana gama iddah da wata biyu yaji labarin aurenta, gashi yanzu har ta haihu ko shekara bata cika ba. Ya amince bashi da rabon ganin dansa. Kannensa duka sun haihu hatta autansu matarsa ciki gareta.
A haka bacci ya dauke shi zuciyarsa cunkushe da tunani.
*****
Da safe likita yazo ya duba Amatullah yace jikin da sauki amma zasu barta sai gobe a sallamesu. Asmau masa tayi godiya sannan ta tashi tayi wanka ta gogewa Amatullah jiki ta canja mata kaya.
"Ama zan fita na siyo miki abinci kinji. Duk wanda ya shigo ki ce masa ina bandaki"
"Ummi kayya ko, ashe kema kina yi kika ce na dena"
Kafin ta iya bata amsa taji tace "yeeey Babana ya dawo"
Asmau ta dago kai a kunyace. Karshenta yaji abinda Amatullah ta ce. Yau ma kayan sojan ne a jikinsa sai dai babu fara'a kamar jiya. Duk da haka yayi kyau ga cika ido.
Gaishe shi tayi ya wuce bai amsa ba. Wani mutum ne ya shigo da kwandon abinci ya gaisheta ya ajiye a gefe ya fita.
Col. Ishaq yana zaune akan kujera yana yiwa Amatullah wasa da tambayar ya jikinta. Asmau duk ta takura ta rasa abin yi.
"Ki zuba mata abinci mana idan ke baki jin yunwa."
Wai mutumin nan ina ruwansa da ita ne. Me yasa ya kara dawowa ma. Ta danyi tsaki a hankali sannan ta hada abincin ta zauna a daya gefen zata bawa Amatullah ya miko mata hannu alamun ta bashi plate din. "Kema ki zuba kici".
Gefe kawai ta ja tana kallon ikon Allah. A baki ya rinka ciyar da Amatullah tana ta yi masa surutu. Asmau tana satar kallonsa.
"Abinci nace ki zuba ba kallona ba"
Ya Salaam! Ba karamar kunya taji ba ta tashi da sauri ta zuba abincin ta dawo tana tsakura da cokali.
Ya tashi saboda ya fuskanci kunyarsa take ji. "Safina bari na je naga likitan da ya dubaki na dawo"
Fita yayi ko waige babu. Asmau ta tuttura abincin kada ya dawo ya sameta.
*****
Tambayoyi ya yiwa likitan game da ciwon Amatullah. Da ya fito ya tsaya bata lokaci don ya bata damar gama cin abincin. Gara da Allah Yasa yayi tunanin kawo musu abincinsa da yake tafiya office dashi ba don haka ba don ganganci fita zata yi ta bar yarinya ita kadai a daki. Wasu na nema ido rufe ita ta samu bata rike da kyau ba.
Kafin ya dawo ta gama ta dauke plates din ta dauraye a toilet. Ya shigo yayi mata alama da ta fito waje.
Darajar girmansa da take gani da tsoronsa da take ji a yanzu yasa ta fita. Ta tsaya can gefe ta sunkuyar da kanta.
"Da ban zo ba sai ki fita ki Safina ita kadai a daki? Kuma shine harda koya mata karya. Allah kadai Yasan me kike koya mata kafin yanzu"
Taji haushin maganarsa ta dago kai zata yi masa rashin kunya "ina ruwanka da abinda nake koya mata".
Yanayin kallon da yayi mata kadai yasa ta kawar da kanta gefe
"Ni kike fadawa haka?"
Da wadanda ke karkashinsa zasu ji abinda ta fada kila idan ta fara tsallen kwado sai kafarta ta kumbura. Lallai tana da tsaurin ido. idan kayan jikinsa basu yi mata kwarjini ba ai shekarun da yake jin zai bata shabiyar ko sama da haka ya isa yasa taji kunyar idonsa.
Da yake rashin kunyar ba dabi'arta bace sai taji babu dadi "kayi hakuri wallahi nagode da taimakon da kuka yi min. Abinda kaji na fada mata ma don babu wanda zai zauna min da ita ne"
"Its ok, zan aiko muku da abinci anjima saboda haka kada ki fita ki barta ita kadai."
"Nagode"
"Har yanzu baki kira kowa a gidanku ba?"
"Uhmmm sun ce zasu zo anjima".
"Maman Safina kin iya karya" ya fada yana shafa kansa.
Asmau taji kamar ta nutse a wurin. Kai wannan mutumi da bin kwaf yake.
"Ance gobe za'a sallameku. Na fadawa likitan kada yayi sallamar sai nazo"
Ta dan bata rai "saboda me"?
"Saboda na kamaki da kyau. Ina son sanin inda zaki kai min 'ya idan kin fita daga nan"
Cikin dakin ya koma ya cewa Amatullah zai je office ya dawo. Har da kukanta ita zata bishi. Asmau ta kalleta bayan ya fita a ranta tace ki gama ganinsa da kyau kafin ki dena ganinsa.
Da yamma Haj Lubabatu ta saje dawowa har take tambayar Asmau ina iyayenta. Tace mata yanzu suka tafi za'a kawo musu abincin dare. Hajiya tace "ai mun zama daya nasan zamu hadu ko ba yau ba".
A zuciyarta tana kokonton ko da gaske sun zo. Babu wani alamar kayan dubiya ga akwatunansu Asmau a gefe wanda ya kamata ace an tafi dasu gida. Da Ishaq ya koma gida da daddare sai da ta fada masa. Yace shima yana son bincike ne a kanta ko don yarinyar da take tare da ita.
*****
Sai wurin karfe tara na safe Col. Ishaq ya dawo washegari amma sau biyu yana aika musu da abinci har da kayan kwalama na yara. A lokacin aka basu takardar sallama da magani. Sauran kudin da ake binsu duk yaje ya biya mutumin da ya kawo musu abinci ya kinkimi akwatunanta.
Asmau ta dakatar dashi yace Yallabai ne ya saka shi. Dauka kawai yayi zai fita Ishaq ya shigo yace ya wuce dasu gidan Hajiya zasu biyosu a baya.
"Bangane ba" Asmau ta fada a tsorace. "Nima namu gidan zam wuce don Allah kace ya ajiye min kayana"
"Kinga ki wuce muje akwai tambayoyin da nake so nayi miki daga nan nayi alkawari zan kaiki gidanku da kaina."
"Ni bazan bika ba, haka kawai na sani ko....ko..."
Yayi murmushi "karasa mana. Ko satar mutane nake yi. Nima tsoron da nake ji kenan ko sato Safina kika yi".
Idonta har ya ciko da hawaye tace "wallahi 'yata ce, don Allah ka barmi mu tafi."
Fita taga zaiyi daga dakin tace cikin kuka "zanyi maka ihun barawo"
Col. Ishaq yayi dariya ya kalli Amatullah "Safina ina babanki?"
Ta sake lafewa a jikinsa "ga ka"
"To kinji, idan kina son 'yarki ki biyoni. Taimakonki nake son yi albarkacin wannan yarinyar"
"Bana son taimakon ka bani 'yata...." tafiyarsa taga yayi dole tabi bayansa tana dan gudu gudu saboda yadda ya soma yi mata nisa.
Gaban wata mota mai kyau suka tsaya baka ya bude gaba ya ajiye Amatullah wanda dadi ya isheta sannan ya zagaya ya zauna a wurin dreba. Babu yadda Asmau ta iya dole ta bude baya ta shiga. Suna hada ido ta mudubi ya kashe ido yana murmushi ita kuwa ta murguda masa baki.
Shi da Amatullah suke ta hira tana bashi labarin gidansu Umma Zulaiha. Gidan Hajiya ya wuce dasu zuciyar Asmau tana ta daridari.
Duk kunya ta dameta haka tabi bayansa suka shiga gidan. Haj Lubabatu ta tarbeta cikin fara'a aka kawo musu abinci. Col. Ishaq yace Bilkisu taje ta yiwa Amatullah wanka. Asmau tabi bayansu da ido yarinya sai murna takeyi ta sake dasu.
Hannunsa ya dan kada a gabanta ta dawo daga tunanin da take yi. Yace "Malama Asmau ina ganin ya kamata ki sanar damu ko ke wace ce. Hajiya ma ta fahimci akwai abinda kike boyewa shiyasa na kawoki nan ki fada mana a gabanta."
Asmau ta soma hawaye "naso ace yadda muka hadu cikin mutumci mun rabu a haka batare da na tonawa kaina asiri a duk inda na tsinci kaina ba"
Hajiya tace "kada kiga kamar mun takuraki, rayuwar Safinatu muke dubawa shiyasa. Idan har baki da wurin zuwa ga yarinya mai lalura lallai kina bukatar taimako"
"Ina da iyaye da 'yan uwa. Kuma a garin nan muke"
Col Ishaq yace "to me ya rabaki da gida har kika kasa fada musu kuna asibiti"?
Asmau tayi ajiyar zuciya sannan ta basu labarin rayuwarta. Tun Haj Lubabatu tana kada kai ha[truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽33
Batul Mamman💖
Gidan suna dai ya koma wurin zuwa kallon Asmau da 'yarta. Bayan anyi sallar la'asar ne ta tuna da Col. Ishaq da ya kawo su. Dafe kai tayi saboda tasan bata kyauta ba. Ganin su Umma yasa ta manta da kowa. Shema'u ta fadawa cewa dan matar da suka zo tare shi ya kawosu kuma yana waje. Haj Lubabatu tana jinsu sai dai kunya ta dan fari ta sanya taki tuna mata dashi. Kuma tasan yau rana ce mai matukar mahimmanci a wurin Asmau. Ta hadu da iyayenta da 'yan uwa bayan tsahon lokaci. Shema'u ta sanar da Umma. Nan da nan aka samu food flasks aka hada masa duk wani na'uin abinci na gidan sunan. Jafar aka kira akan su wuce gidansa domin bako ya samu yaci abinci ya huta.
Jafar da Sabira suka fito dauke da kayan abincin tare da Asmau dake binsu a baya rike da hannun Amatullah. Zaune yake a gaba ya kwantar da kansa a saman kujera yana sauraron karatun Al'Qur'ani kira'ar Shiek Mishary Rashid. Tausayinsa Asmau taji saboda kunyar abinda tayi masa. Babban mutum kamarsa sun shanya shi a kofar gida. Kuma ta tabbatar baici abinci ba kafin su taho. Yana dawowa daga masallaci ko zama baiyi ba yace su taho kawai.
Amatullah ta tafi da gudu ta fada jikinsa. Hakan yasa shi saurin bude ido yana murmushi. Jafar ya karasa gaban motar ya mika masa hannu suka gaisa.
"Kayi hakuri don Allah an barka a waje tun dazu. Duk laifin Idon kuka ne da bata fada mana tare kuke ba"
Col. Ishaq yace "Idon kuka kuma?"
Dariya Jafar yayi kana ganinsa kasan yana cikin farinciki, ya nuna Asmau "ai sunanta kenan."
Kyakkyawan murmushi Col. Ishaq yayi yana kada kai "sunan ya dace da ita"
Duk akayi dariya sannan Jafar ya fada masa yana son ya biyo shi gidansa domin yaci abinci. Da farko Ishaq ya nuna baya jin yunwa sai da Asmau ta bashi hakuri tare da rokonsa. Yayi yar dariya
"Haba Idon kuka, bayan ko introducing dina a wurin yayanki baki ba?"
Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Jafar ya sake mika masa hannu murmushinsa yana kara fadada "nima da laifina, sunana Jafar ni Asmau take bi,wannan matata ce Sabira. Idan kaci abinci zamu shiga ciki ka gaisa da duk 'yan uwa."
Col. Ishaq ya dafa kan Amatullah "ni kuma sunana Baban Safina"
Sabira ta kalli Asmau "kice kawai biki zamu sha kwanan nan"
Da sauri Asmau ta daga hannuwa "ba haka bane, Ama ce kawai take kiransa babanta. Sunansa...."
Shiru tayi duk suka zuba mata ido. Kunya taji ta kasa fadin sunan sai ta wayance tace ya kamata su tafi saboda kada abincin ya huce. Col. Ishaq ya nuna su shiga motarsa.
Jafar ya shiga gaba, Sabira na baya sai Amatullah da ta dage zata bi babanta. Asmau tana tsaye suka ja mota suka tafi ta koma ciki.
Hira aka dora daga inda aka tsaya. Shema'u tana goye da Abid din Sabira sai jijjiga shi take kafin Sabirar ta dawo.
*****
Mata kamar kara turo su akeyi gidan ana ta zuwa kallon Asmau. Hajjo duk ta matsu su firfita don su samu ayi hira yadda ya kamata da Asmau. Duk dakin da ta shiga mata ne harda wadanda ma basu zo ba da farko. Su Umma ma dai kara kawai suke yi amma duk a matse suke da a basu fili suyi hira da 'yarsu. Da suka ga abu yaki karewa Hajjo da kanta ta shiga falo rai a bace tana mita yadda masu hankali zasu fahimta
"Kai jama'a ace anzo taron suna anci tatsotse dinnan anci salak, anci tuwo anci wannan anci wancan amma mata sai tururuwa suke yi. Fisabilillahi ko irin karar nan ta a fita a bamu waje da jikarmu muyi hirar yaushe gamo ya gagara".
Wasu nan suka fara jin kunya suka fara hada kayansu suna fita. Sauran da suka yi biris kuwa Hajjo ta rufe idonta ta sallamesu. Umma da Mama dai sunji kunya to amma halinmu na mata wurin saka ido da bin kwaf ya janyo musu.
Basu samu gidan yayi daidai ba sai bayan karfe tara. A falo suka zazzauna. Duk 'yan uwan Asmau makusanta suna wurin har da Kawu Garzali ga kuma Haj Lubabatu da danta. A nan aka shiga bada labarin abubuwan da suka gabata. Kowa jikinsa yayi sanyi musamman da suka ga Asmau tana ta kuka da rokon a yafe mata. Suka yi ta kukan wannan kaddara da ta riga fata.
Mama Yalwa tace "ai wannan bala'i na waya sai an dage da addua sosai. Akwai alkhairi tattare da ita amma sharrinta a bayyane yake. Kuma kullum kara samar da sabuwa akeyi mai saurin hada mutane da barna."
"Haka ne" Haj Lubabatu ta amsa mata. " Sai kiga yara kanana sun yini da waya a hannu ki rasa me suke tattaunawa. Wani lokacin a haka ake haduwa da mutane babu sanayya idan kika yi rashin sa'a ba nagari bane sai su bata maka tarbiya ba tare da ka lura ba. Kwanakin baya jikata dake karatu a nan wurina Bilkisu na fuskanci ta soma nacewa waya fiye da yadda ta saba. Kullum suna hira da wata yarinya da suka hadu a irin group dinnan na waya. Kunsan yanzu tsakanin mace da mace ko maza ma babu abinda ba'ayi. Na kula kawancen ya soma yawa bata da zance sai nata. Abun ya fara bani tsoro. Shabiyun dare sai kiji suna waya sai da nayi mata tas akan hakan."
Hajjo tace "ni idan babu hali ba sai a hakura da wayar ba. An fara abu da gaisuwa da sada zumunci a hankali waya ta zama tamkar kana dauke da duniya a tafin hannu. Idan kaki bawa danka waya ma zai fita ya gani a ta wasu."
Tattaunawa suka yi ta yi a game da tasirin waya ga al'umma yanzu. Babu babba babu yaro kowa yana da ita kuma ya iya amfani da ita. Jankunne sosai manyan suka yi garesu akan su dubi yadda rayuwar Asmau ta kasance su kula da kawunansu da na yaransu. Kasancewarsu masu aure duk bashi bane domin yanzu hatta mata da mazan aure suna fadawa tarkon waya. Daga group sai kaga matar aure tana mu'amala da 'yar uwarta mace ko namiji mai aure ko mara shi wanda a da ba halinta bane.
Sun jima suna hira har shadayan dare tayi basu kula ba sannan Haj Lubabatu da Col. Ishaq suka tashi tafiya. Sun sha godiya a wajen dangin Asmau sosai tare da neman a cigaba da zumunci don yanzu sun zama daya.
Fitowa suka yi har bakin mota rakiya Amatullah na makale jikin Col. Ishaq tana bacci. Tashin da yayi zasu fito yasa ta farka ta soma rigimar binsa. Shi kan shi baya son rabuwa da ita. Ana ta lallabata taki yin shiru sai da Asmau ta karbeta ta karfi tana mata fada. Hakura tayi amma bata dena kukan ba. Col. Ishaq ya bata rai sosai saboda fadan da tayiwa Amatullah. Kallon da yake mata ya nuna rashin jindadinsa sai kawai ta sunkuyar da kanta.
Bayan tafiyarsu Umar ya tafi kai Mama Yalwa gida shi kuma Abdulhalim ya dauki matarsa da yara suka wuce. Dakin Umma suka koma Amatullah tana ta kuka har sai da Asmau ta goyata duk girmanta don taki yarda da kowa. Daga nan aka soma wata sabuwar hirar har aka zo kan Kawu Rabe Asmau tace shi kadai ne bata gani ba . Shema'u tace "hmmm Asmau mutum babu kyau. Ashe duk tsahon lokacin nan Kawu Rabe wurin wani malami yake zuwa ana rufe bakin Hajjo da su Yaya Abu. Bayan tafiyarki Hajjo tazo ta nemi gafarar Umma har ta bukaci lallai ta dawo gidannan dasu Aina'u idan har ta yafe mata. Shi kuma tace ya soma gyara musu gidan kofar mazugal su koma. A nan aka ji ashe ya dade da siyar da gidan. Ya kuma dage wannan nasa ne. Sai ga ainihin takardun gida Hajjo ta fito dasu, ke magana har za'a shiga kotu don duk su Kawu Garzali sun ce sai ya biyasu kudin gidansu da ya sayar. Wurin aikinsu ma suka kore shi yaci kudin kamfani bai biya ba. Sai da yaga abu ya kure masa ya roki gafarar Umma suka tashi. Yanzu haka yana kauyen Dakasoye can ainihin kauyen babansu Anti Sagira. A nan baban nata ya bashi gona da gida suka zauna tunda bashi da wurin zama. Yanzu da wuya yazo cikin Kano. Zahra dai tayi aure tana Jigawa"
Asmau tace "har ya bani tausayi. Da ma Umma ta barshu kawai a nan din"
Aina'u tace "tabdi, ko yanzu fa ba wani rissina yayi ba. Tsoron hukuma yaji don da gaske su Yaya Abu sunso a kama shi sai ya biyasu kudin shiyasa ya bada hakuri ya tattara yayi gaba"
"To Allah Ya kyauta" duk suka ce Amin.
Kan katon gadon Umma suka kwanta su uku sannan aka shimfide yaran akan bargunan banda baby Asmau wadda suke kira Husna.
Sai wurin daya da rabi na dare Umma ta baro dakin Hajjo inda su Anti Lami suke. Su ma sum gama tasu hirar. Wani hawaye taji yazo mata da taga 'ya'yanta mata kwance su uku a wuri daya sun takure alamun daya gefen nata ne. Kasa kuma ga yaransu duk sunyi bacci. Maimakon ta kwanta alwala ta dauro tazo tayi sallah tana mai mika godiyarta ga Allah tare da adduar dadin shiriya ga zuri'arta da sauran musulmi.
*****
Col. Ishaq yana kwance amma ya kasa bacci. Ya rasa abinda yasa yake ta tunanin Asmau. Can kasan zuciyarsa yace tausayinta ne kawai da kuma son Amatullah. Sai dai kuma ko rufe ido yayi murmushin da tayi bayan komawarta gida yake tunawa sai kawai ya tsinci kansa da yin murmushin shima.
*****
Washegari karfe takwas na safe sai ga Jafar da Sabira dauke da kwanunkan abinci. Dankali ta suya da plantain da kwai. Duk da tasan dai a gidan ma za'ayi. Umma ta nuna jindadinta sosai. Shiyasa take son Sabira, barta dai da surutu amma mace ce mai ladabi da sanin ya kamata. Sauran matan masu jini a jika irin su Shemau da Rashida suna kitchen ana ta soye soye. Aina'u ma ta tashi duk da hanata aikin komai ita da Zubaida mai ciki. Asmau kuwa kamar wadda aka saukarwa bacci tana yin sallar asuba ta koma. Ji takeyi rabonta da bacci mai dadi cikim kwanciyar hankali har ta manta.
Amatullah ce ta tasheta tana kiran Babanta. Cikin bacci Asmau ta janyota jikinta ta soma rarrashi
"Ama nan ne gidanmu fa, na rasa inda kika koyi rigima. Amma idan kika cigaba zan mayar dake wurin Zinaru"
Shiru tayi ta kwanta a jikin Asmau daga baya tace "Ummi to zaki kaini naga Babana sai mu dawo?"
Asmau ta shafa kanta tana murmushi "in sha Allah zan kaiki kinji. Tashi muje muyi brush a gaishe da su Hajjo"
Suna fitowa falo suka tarar da kowa a zaune har su Jafar. Rike take da hannun Amatullah sai suka basu sha'awa. Ita kuwa kallon da suke mata yasa taji kunya ta saki hannunta. Yanzu tunda anzi gida sai ta koyi kara kada ace bata da kunya. Suna zama suka gaishe da kowa Anti Bintu ta cikawa kowannensu plate da abinci. Amatullah ta ware ido sai ta tashi taje tayiwa Asmau rada a kunne. Duk ana kallonta sai suka ga tana share hawaye. Hankalinsu ya tashi Umma tace me ya faru.
Kunya tasa Asmau ta kasa fada da wayo Umma tace "Safina zo ki fada min abinda kika fadawa Ummi. Kinga gashi har kin sakata kuka"
Duk aka zuba mata ido ita kuwa tace "Ummi in fada?"
Murmushi kawai Asmau tayi tace "tambayata tayi taci ko kuwa"
Amatullah ta cafe "idan naci Ummi zata ce nayi kwadayi. A gidan Babana ma sai tace naci. Mu a gidan Zinayu koko da kosai muke ci, ko byodi da tea, ko tuwon safe ko Ummi"
Kasa cin abincin Asmau tayi ta fashe da kuka. Sunga rayuwa ita da Amatullah. Dan kudin da take samu a kudin makaranta yake tafiya. Abinci kuwa sai dai aci garau garau. Su Umma suma kukan suke tayata. Abinda tafi karfi a da shine yanzu yafi karfinta. Anti Bintu tazo ta rungumeta "komai ya wuce Asmau. Kuka bazai dauke shekarun baya ba sai dai ya tuna miki da bacin rai."
Hajjo tace "haka ne ki dena kukan haka. Rayuwace kowa da irin tasa duk da dai komai yana da sanadi. Naji dadi da kika koyawa yarinyar nan tarbiya mai kyau."
A haka suka ci abincin ana taba 'yar hira har Asmau ta sake. Kafin su tashi Amatullah ta sake cewa "Ummi daga yau a nan zamu zauna ne?"
"Eh mana ai kun dawo gida kenan" inji Shemau
Tare duk suka tashi aka kwashe kwanukan suka fara layin wanka.
Wurin shadayan safe Asmau na saka kaya don kuwa Mama Yalwa tace yau a gidanta zasu yini taji wayarta na ringing. Ko da ta dauka bakuwar number ta gani har tayi zaton ko Zulaiha ce tace "tuba nake maman 'yan biyu ban samu na kiraki ba"
Shiru taji daga daya bangaren tace "Zulaiha ko kinyi fushi ne. Ni da ke fa ba'a ji kanmu ba"
"Ashe kin iya hira Idon kuka" ji tayi gabanta ya fadi. Muryar da ko cikin bacci yanzu tasan zata gane taji. Kamar yana gabanta ta dan russuna a kunyace ta gaishe shi.
"Har kin gane mai magana, ko kuwa dai wayancewa kika yi?"
Tana murmushi tace "Na gane"
Col. Ishaq ya gyara kwanciyarsa. Shi bai ma san dalilin da yasa yayi mata waya da safe haka ba.
"To waye?"
"Baban Amatullah"
"Uhmm uhmm, a wurinta kadai nake baba. It seems ko sunana baki sani ba. Shiyasa jiya kika kasa fadawa yayanki"
Asmau taji muryarsa kamar baiji dadin hakan ba tace "na sani kuma na fada masa ma"
Magana yake kamar maganar aiki ce mai zaman kanta yace "me kika ce masa? I am sure ba Baban Safina kika ce ba".
Ita fa kunyarsa take ji. Ganinsa take yi babban mutum mai matukar kwarjini da cika ido shiyasa bata tsawaita hira dashi. Sake maimaita tambayar yayi tace "Col I. M Jikamshi"
Wani iri yaji yadda ta fadi sunan a hankali kamar bata so yaji.
"I. M Jikamshi yana rokon alfarmar ayi saving din numbarsa saboda kada ki sake kirana Zulaiha. By the way ina princess dina?
"Ana yi mata wanka"
"To zan sake kira anjima ki hadani da ita. Ina fata kinji request dina. Idan kika sake kirana da sunan mata zamu kulleki ni da Safina. Ki gaida da Umma."
Amsa masa tayi da to...tana 'yar dariya ta ajiye wayar.
Mimi babbar 'yar Shemau ce ta shigo tana kiranta Umma tace tazo falo. Hijab ta saka ta fito daidai lokacin da Qasim ya dago kansa. Suna hada ido nata ya ciko da hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai.
Ya kura mata ido yana kallonta "Asmau ke ce?"
Ta fashe da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. A da Abubakar ya fushi kumari. Gashi duk ya canja alamun yana da sukuni.
Kusa da Umma ta zauna a kasa ta gaishe shi tana dan murmushi ga hawaye
"Yaya Qasim ai bazan ganeka ba"
Yau da Asmau namiji ce babu abinda zai hanashi rungumeta don ya nuna mata tsantsar farincikinsa da ya ganta. Jiya da ta tsaya a Shanono su Inna suka ce dare yayi ya bari gari ya waye ya karaso Kano ji yayi inama bai biya ya sanar dasu ba. Yau dai burinsa ya cika Asmy din Abubakar ta dawo gaban iyayenta.
Amatullah ce ta shigo falon tana kira Asmau. Duk da ta sake da mutanen gidan amma haka halinta yake da an dan jima sai ta nemi Umminta. Tana ganinta kuwa zata kama wata sabgar.
Gaban Qasim har faduwa yayi da ya ganta. Baya bukatar wani karin bayani ya tabbatar wannan 'yarsu ce wadda rabon haihuwarta ya jefa iyayenta da su kansu cikin rudani. Tashi yayi ya durkusa a gabanta yana shafa fuskarta, muryarsa na dan rawa yace "yaya sunanki"?
Tayi masa murmushi irin wanda yake tunawa Asmau da Abubakar idan tayi shi "Safinatu Amatullah Abubakay"
Rungumeta yayi kawai hawayen farinciki na fito masa. Muddin yana raye yayi alkawarin kula da ita har karshen rayuwarta. Yana shafa kanta yace
"Safinatu nine babanki"
Ta dago kanta tana kallon Asmau "Ummi ni babana biyu ne"?
0 comments:
Post a Comment