Tana gama wayar Ainau ta tambayeta ko waye tace baban Amatullah ne. Ainau ta kurawa 'yar uwarta ido
"Yaya Asmau zaki iya yin sati a garin nan kuwa ko kawai mu bi Yaya Yassar mu koma Kano"
"Kada ki damu Ainau, irin wannan abubuwan nasan ban fara ganin komai ba ma. Idan ya faru ne yake taba min zuciya na dan lokaci har nayi kuka. Dama abinda ake gudu kenan, ba wai yin a lokaci daya ba, abinda zai je ya dawo bayan kayi. Kinga rana daya a rayuwata ta canja akalar komai nawa." Kuka suke yi duk su biyun Ainau tana bata hakuri
"Ku zan bawa hakuri ma da na janyo ake yiwa tarbiyar da Umma ta bamu kallon gazawa. Don Allah kada ku bari taji wannan labarin. Shima Yassar din zanyi masa magana"
Anti Bintu tana bakin kofar tana jinsu. Tausayin Asmau ta kara ji ta koma wurin maigidanta. Alfarmar kada su fadawa Yayarta tazo nema sai gashi Asmau tayi wannan tunanin.
Sun dauki lokaci a dakin suna magana kafin su dawo falo bisa umarnin Kawu Yusuf. Rokonsu yayi da suyi hakuri da halin tsufa irin na mahaifiyarsa kuma yana fata zasu sake a gidan bazasu takura kansu a daki ba.
Sai da suka yi sallah aka zauna cin abinci. Babu wata hirar kirki sai hayaniyar Amatullah. Kowa jikinsa a sanyaye yake. Ganin haka Asmau ta rinka dauko hira duk don ta nuna musu bata tare da damuwa.
Su Yassar sun dawo daga masallaci inda suka yi sallar la'asar yace zai kama hanyar komawa. Anti Bintu ta tsayar dashi ya jira a kawo sako da take son ya tafiwa da Umma dashi. Yana zaune a falon Col. Ishaq yayi masa waya yana tambayarsa kwatancen gidan da suke zai zo ganin Amatullah.
Yassar ya tashi tsaye cike da mamaki, sannan ya kwatanta masa inda zaije ya jirashi sai yazo ya kawo shi gidan. Anti Bintu ta tambayeshi ko lafiya ya sanar da ita bakon da zasuyi. Murmushi tayi "anya 'yar yazo gani ko uwar 'yar"
"Nima tunanin da nake yi kenan Anti. Mutumin ba karamin burgeni yake yi ba. Idan yace yana son Yaya Asmau ai ya gama min komai. Wallahi binsa zan rinka yi sau da kafa".
"To sarkin zumudi, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki" Anti Bintu ta fada amma itama tana fatan hakan ya tabbata. Dan ganin da tayi masa ranar da suka dawo da Asmau ta yaba dashi.
"Bari kiga naje bakin layin kada yazo yayi ta jirana"
"Ita yayar taku tasan da zuwansa?"
"Kai bana jin ta sani, kyaleta kawai Anti kada ta bata lamarin. Ba karamin aikinta bane ta tura masa Amatullah taki zuwa su gaisa. Kuma ai kinga bai dace ba mutum yayi tafiya irin wannan saboda danka"
Wannan karon dariya sosai ya bawa Anti Bintu. Lallai Yassar da yana da iko tuni zai bawa sojan nan auren yayarsa. Yana fita ta shiga ciki suna daki ana ta wanka saboda zafin gari. Ta tarar Asmau ta shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi shudiya ta yafa karamin mayafi fari a kanta. Anti Bintu tace ta taso ta tayata hadawa bako abinci don duk 'yan matan gidan suna Islamiyya.
Tashi tayi tabi bayanta ta bar Ainau da yaran. Da yake akwai sauran abincin rana salad kawai ta sake hadawa ita kuma Anti Bintu ta hada zobo mai sanyi.
Tray din abincin ta dauka ta shiga falo, ko tsakiyarsa bata kai ba taji sallamar Yassar da ta Jikamshi. Sai dai murya ta biyun ce tafi daukar hankalinta har ta daga kai suka hada ido. Sanye yake cikin kayan aikinsa da hularsa rike a hannu. Yayi kyau sosai. _Innalillahi wa inna ilaihi rajiun_ ta fada saboda tsabar kaduwar da tayi hannuwanta suna rawa tana neman sakin tray din a kasa.
Wani irin kallo ya bita dashi yana wani kashe ido. Sai kuma ya karasa gabanta ya karbi tray din da yake tangal-tangal ta kasa rike shi da kyau. Sai da ya ajiye shi a kan centre table din falon ya sake dagowa yana kallonta kamar wadda aka kafe a wurin yace
"Duk murnar ganina ce haka tasa kika kasa motsi?"
Juyawa tayi bayanta taga Anti Bintu tana murmushi,daga bakin kofa kuwa Yassar ne bakinsa ya kusa zuwa keya don dadi. Ji tayi kamar ta make shi.
Mamakin ganinsa ta yi sosai har ta kasa hada wata kalma a bakinta. Shi kuwa ba karamin dadi yaji ba da ya ganta.
"Kinyi tunanin wasa nake yi da nace zan zo? Gashi ko wurin zama baki bani ba sai aikin daukar miki tray daga shigowata"
Da sauri Yassar ya nuna masa kujera. Anti Bintu ta karaso ta zauna suka gaisa amma har lokacin idonsa na kan Asmau da ta tsaya kawai tana kallonsa. Bata taba kawowa da gaske zai zo ba kamar yadda ya fada a wayar. Ji tayi ya sake shiga ranta har abin yana bata tsoro.
"Yaya hanya? Yassar na shirin tafiya yace ka shigo gari"
Sai sannan ya maida hankalinsa ga Anti Bintu yana magana da alamar damuwa a fuskarsa
"Waya muka yi da Ummin Safina sai naji kamar tana kuka kuma taki fada min abinda ya sameta. Shine kawai nayi deciding na taho don ko na zauna bazan iya aikin ba"
_Subhanallah_ ta fada a zuci. Shi kuwa me yasa yake haka ne. Baya jin komai idan ya fadi magana a gaban mutane. Kallonta Anti Bintu tayi sai taji kunya. Kada tayi tunanin ko ta fada masa abinda ya faru ne. In'inar karfi da yaji ce ta kamata
"Uhmmm...dama...da.....lokacin...kai" ta rasa karyar da zata yi ma. Shi kuwa ya zuba mata ido kamar bai san da mutane a wurin ba.
Anti Bintu tayi gyaran murya don ta kula hankalinsa yayi gaba. Hasashensu ita da Yassar ya tabbata. Wannan kallo da yake yiwa Asmau indai ba na soyayya bane to bata san dame zata kwatanta shi ba. A iya saninta dai yasan komai game da Asmau shiyasa ta fada masa magana ce surikarta ta fada da batayi mata dadi ba shine dalilin kukan.
Bata so aka fada masa ba tana tsaye a inda take tun dazu ta soma hawayen da ta rasa dalilinsu. Karshe ciki ta shige kawai ta koma daki. Sai da yaga shigewarta yace "ita Asmau haka take ne da saurin kuka? Na zata a yadda taga rayuwa by now ta zama jaruma wadda zata iya daukar duk abinda yazo mata"
Yassar ya bi bayanta zai lallabata ta dawo wurin bakonsu don maganar komawarsa Kano yanzu kuma tabi iska.
Anti Bintu tace "tun da can Asmau mace ce mai raunin zuciya. Faruwar wadannan al'amuran sun sa ta kara samun rauni dole ne sai muna binta a hankali har Allah Yasa ta iya sakin jikinta kamar da. Dazu munyi mata nasiha sosai akan toshe kunnuwanta game da irin wadannan maganganun da zasuyi ta tasowa"
"Allah Ya kara rufa asiri. Kiyi hakuri I just can't help myself when it comes to Asmau"
Tayi dariya "babu komai, mu hakan muke so ma. Allah Ya tabbatar mana da alkhairi"
Da yake yasan bazata girmeshi sosai ba sai yayi murmushi "ko Yayata? Kada kice kin gano ni "
"Na nawa kuma" tayi dariya.
Sai ya rufe fuskarsa da hularsa "amma kuwa har naji kunya."
Anti Bintu me zatayi banda dariya ta tashi "haka kake da abin dariya"
Dan dakewa yayi shi a dole babu wasa "don dai kawai a gaban in-law nake. Amma ni serious mutum ne. Soja ai baya abin dariya"
"Uhmmm naga alama, sai dai ban rike sunan wannan sojan ba"
"Call me Ishaq"
"To Ishaq kanina Allah Ya bada sa'a. Bari na turo maka ita. Ga abinci nan don Allah ka ci"
Daga shi har ita dariya suke yiwa juna sannan yayi mata godiya ta tafi. Da taje dakin Yassar ta gani yana faman bawa Asmau dake kuka hakuri tana yi masa fadan me yasa ya kawo shi gidan.
Ta shiga dakin ta zauna a gefen gado "bana son shirme Asmau, meye abin kukan ma. Idan mutum ya nuna kina da mahimmanci a rayuwarsa bai cancanci wulakanci daga gareki ba. Dan gyara fuskarki kije ku gaisa."
Ta tashi zata shiga bandaki ta wanke fuskar Yassar yace "Antinmu kema kinyi mubaya'a ne. Naga kin shigo kina dariya"
Ta kalli Asmau da ta juyo tana kallonsu " ina wasa da kai ne. Tashi ka bani wuri kazo ka zauna a cikin mata" fita yayi yana dariya kawai.
Asmau ta wanko fuskarta ta fito "mubaya'ar me Yassar yake tambayarki?"
Ainau da tun dazu bata saka musu baki ba tace "nima abinda zan tambaya kenan"
"Ku kyale shi shashancia ne kawai" ta bagarar da zancen ta fita.
Ainau tace "ko dai baban Amatullah yana ciki ne"
"Kinga ki kiyayeni. Ya isheku daga ke har Yassar"
Tana jiyo dariyar Ainau har ta kai karshen korido din da zai kaita falon.
A zaune ta same shi yana waya ta zauna a wata kujerar daga can gefe. Yassar yana daga kusa dashi. Sai da ya gama yace "Yassar dan bamu wuri ina son siye zuciyar yayarka"
Ya tashi yana dariyar da ta soma bawa Asmau haushi ita kuwa ta bata rai. Ya dan mike kafafunsa
"yunwa nake ji"
Fuskarta babu wata fara'ar kirki tace "ba ga abinci nan a gabanka ba"
"Kince naci ne?"
"Au sai nace?"
Ya gyada kai yana murmushi wanda yasa ta dan saki fuska.
"To ga abinci nan kaci"
"Nagode" ruwa ya fara sha sannan ya bude plate din da aka hada masa abincin zai ci.
Asmau ta tashi "bari na baka wuri kaci abincin"
"No yi zamanki please"
Kasa kallonsa tayi yana cin abincin. Shima kadan yaci ya rufe plate din. Haka yake abinci bai dame shi ba.
"Asmau kalleni nan"
Dan kadan ta iya daga kanta ta dube shi
"Ina so ki zama jaruma mai hakuri da dukkan abinda zata ji ko ta gani a wurin mutane. Babu wani abu da bazai wuce ba a duniya saboda haka yawan zubar da hawaye akan magana ba naki bane. Ke uwa ce dole ki jajirce wurin zama macen da ba raguwa ba ko don kada 'yarki tayi koyi da hakan"
Yana magana ta soma hawaye har ya kai karshe. Girgiza kansa kawai yayi
"Don nace ki rinka barin kukanki kiyi a gabana shine zaki yi kuma. To share hawayen ko na share miki da kaina"
Habar mayafinta tasa ta goge hawayen da sauri
"Ko ke fa...yanzu ace nazo tun daga Kano amma fuskarki duk a kode"
Ta dan turo baki "don zaka zo sai nayi kwalliya?"
"Sosai ma kuwa, ko ba kya so ki kara samun karbuwa ne. Yanzu haka zan kama hanya har na koma gida kodaddiyar fuskar nan zanyi ta gani. Da na sani driver nasa ya kawoni"
Asmau tace "nifa..."
"Ke fa me? Kinga mu bar wannan zancen sai kin koma gida. Wai ina princess dina ne banganta ba"
"Sai yanzu ka tuna da ita? Tayi bacci"
Ya kwantar da kansa a saman kujera "duk laifinki ne. Kin wani kasheni da ido kinsa bana tunanin komai sai naki. Kije ki tasheta magriba ta kusa kada ki koya mata baccin yamman nan"
Asmau ta tashi tana tafiya tana waigensa. Duk juyawa sai yayi mata murmushi sai ta kawai da kai. A na ukun ta kusa karo da bango ya soma dariya "yi a hankali ba yanzu zan tafi ba sai kin koreni da kanki"
A kunyace ta shige tana mamakin yadda ya gama da zuciyarta cikin dan kankanin lokaci.
******
Bayan tahowarsu Mama Yalwa taje gidan Umma. Suna zaune harda Hajjo take fada musu yadda suka yi da Qasim a daren jiya kafin ya tafi da kuma amsar da Asmau ta bashi.
Hajjo tace "ki ji min yarinyar nan fa. Ita banda abinta ai ba saka mata ido zamuyi ba. Kuma yaron nan Qasimu ya cancanci yabo wallahi. Bari ta dawo muyi magana amma aure ai shine rufin asirinta."
Umma tace "nima na yaba da halayensa sosai. Nasan duk abubuwan da take tunani har yasa take tsoron yin aure. Amma ko kadan ba hujja bace. In sha Allah zamuyi mata magana. Ni kaina ban hango mata rufin asiri ba kamar a gidan Qasim. Allah Yayi masa albarka".
"Amin" Mama ta amsa. "Kar kiso kiga yadda naji dadin labarim nan. Yarinya ce mai biyayya nasan bazata watsa mana kasa a ido ba.
*****
Da yamma ne bayan tafiyar Mama Anti Bintu ta kira Umma tana bata labarin zuwan Col. Ishaq da hirar da suka yi. Cike da murna tace "Yaya Bara wallahi na yaba da yadda ya damu da Asmau. In Allah Yaso shine zai share mata hawayen dukkan damuwarta."
Umma bata iya bata amsar kirki ba saboda tunani da ta shiga yi akan maneman 'yarta.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽36
Batul Mamman💖
Ba karamin damunsa rashin daukar wayarsa da Asmau take yi yayi ba. Sai dai kuma ya kuduri niyyar bazai barta ba. Murmushi yayi....yana son mace mai jan aji, amma bazai bari ta ja masa aji da yawa ba saboda yadda yake ji da ita a zuciyarsa. Har mamakin kansa yake yi. Bai yarda sonta yake yi har haka ba sai bayan 'yar hirarsu ta dazu. Yana son muryarta, kunyarta, yanayinta....ya dan shafa kansa yana murmushi ya tura mata da text
"Asmau Ummin Safina ki shirya, don Jikamshi da gaske yake. Kiran wayarki kuma yanzu na fara. Gudnyt"
*****
Hannunta har rawa ya soma bayan ta karanta text din. Wani abu taji ya ratsa jikinta gabadaya don dadi. Bayan Abubakar bata taba tunanin sake jin wani abu makamancin wannan akan kowane da namiji ba sai akan Col I.M Jikamshi. Sai dai kuma wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Yaudarar kai ne ma ta yarda wani abu yayi nisa tsakaninsu. Tafi kowa sanin ko ita wacece, bata cikin mata da zasu sami rabon aure a wannan duniyar. Dadin dadawa Jikamshi ba karamin mutum bane. Yana da wata kima ta daban a idonta, sam bazata so suyi rabuwa mara dadi ba. Gara tun ba'a soma ba kada a fara. Tana wannan tunanin ne bacci ya kwasheta.
Washegari Umma ke fada mata su fara shiri nan da kwana biyu zasu tafi Zaria da Aina'u. Sati daya zasu yi daga nan zata zo ta same su su wuce Wushishi. Jin zata je Zaria wurin Anti Bintu yasa ta farinciki har ta dan manta da tunanin da ta kwana ta tashi dashi.
Shirye shirye suke yi daga ita har Aina'u sun hada kayansu da komai. Yassar ne zai kaisu ya dawo washegari.
Da yamma ne ta tafi gidan Jafar saboda yace yana son ganinta tace ya bari zata zo da kanta. A gida ta bar Amatullah tana bacci. Sun dan taba hira da Sabira ta tashi ta basu wuri. Ba wani dogon abu bane maganar karatu yayi mata wanda yace sunyi shawara ne da Shemau zasu hada kudi su biya mata ta koma makaranta. Kuka take yi sosai kamar yasan abinda take son yi kenan.
"Yaya Jafar Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai, nima abinda yake raina kenan don bana son nayi ta zaman haka."
"Kada ki damu Asmau. Ina so ki manta da rayuwar baya kiyi kokarin gina rayuwa mai kyau daga yanzu. Kada ki manta ko ke wacece a duk inda kike. A yanzu da kika dawo gida inda mutane suka sanki suka san labarin rayuwarki ki zauna da shiri na fuskantar kalubale kala kala. Dole duk inda kika shiga kiji maganganu marasa dadi daga bakin mutane daban daban. Abinda nake bukata daga gareki bai wuce ki toshe kunnuwanki ba. Komai yayi farko yana da karshe. Ki mayarda dukkan lamarinki ga Allah sai kiga kinyi nasara."
Tayi murmushin takaici "hakane, kuma nagode da shawararka. Dole ne nayi hakuri da dukkan abinda mutane zasu ce game dani da Amatullah. Irin labarinmu dai da wuya yake zama tarihi. Duk wanda ya sanmu duk sanda muka hadu sai sun tuna. Wannan kaddara har jikoki idan da rabo nasan za'a goranta musu wata rana" ta kare maganar da kuka.
Tausayin kanwarsa yaji sosai. Ya dade da sanin cewa illar zina tana bibiyar mutum duk inda yaje. Musamman idan akwai haihuwa tsakani. Fatanmu kawai Allah Ya tsare mana imaninmu Ya karemu daga fadawa sharrin shaidan da mukarrabansa.
"Ki tsarkake zuciyarki Asmau, daga nan ki barwa Allah komai. Rayuwa ce kowa da irin tasa. Babban abin dubawa dama shine tuba da komawa ga Allah. Idan kika yi haka to babu ruwanki da zancen mutane. Duk wanda ya fiye bibiyar kuskuren dan uwansa don tonon asiri to Allah na kallonsa kuma Shine Yasan yadda zaiyi da bayinSa."
Godiya ta sake yi masa har ta kira Shemau tace zata je har gida tayi mata godiya. Dan uwa rabin jiki inji bahaushe...banga mai kamarka ba. Abinda suka aikata ita da Abubakar ba su kadai yake bi ba domin kuwa tasan za'a nuna iyayensu da 'yan uwansu idan dalili ya kawo suma a goranta musu. Kai zina laifi ce mai muni, kazanta ce mai kaskantar da mai daraja. Ya Allah Kasa mufi karfin zukatanmu. Masu neman aure maza da mata Allah Ka basu abokan rayuwa nagari. Mu kuma Ka bamu zaman lafiya da wadanda Ka hadamu dasu.
*****
ASP Qasim zaune gaban mahaifiyarsa ya gabatar mata da zancen Asmau wanda ta dade da sanin kudurinsa akai.
"Baba ni bazan hanaka aurenta ba. Babanku ma yace ya amince da auren. Abu daya nake so da kai shine ka tuna dukkan abubuwan da suka faru. Naso kwarai kayi aure kafin yanzu ta yadda ko ka auri Asmaun zaka hadata da wata matar"
"Inna kenan, kina gudun ita kadai ta kasance surika a gareki saboda tana da 'ya kafin tayi aure?"
"Dan nan yau da gobe sai Allah. Mutane da bakinsu bazasu fasa surutu ba"
"Amma Inna nasha fada miki ina gudun zamansu da kishiya yaki dadi saboda gori. Da bata dawo ba kamar yadda kika bukata a shekarar nan zan nemi aure. Ku cigaba da yi mana addua."
Ta kada kai "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi. Haj Yalwa tace zata zo dasu su gaishe da Malam. Allah Ya kiyaye hanya"
Qasim ya tashi ya leka dakin mahaifinsa har lokacin bacci yake yi. Shiryawa yayi cikin wani yadi mara nauyi ruwan toka yayi kyau sosai ya kama hanyar Kano daga Shanono.
Ana magariba ya iso. Gidan Mama ya fara zuwa suka gaisa sannan ya kira Asmau ya fada mata zai zo idan an idar da sallar isha. Umma taje ta sanarwa.
"Allah Sarki Qasim, gaskiya ya rike amana. Ji yadda yake kokarin kula daku duk da ba a garin nan yake aiki ba. Allah Ya biya shi da mafificin alkhairi."
Asmau ta amsa da amin tana gyara goyon Husna da tayi.
Suna cikin hira Qasim yayi sallama Umma tayi masa izini ya shigo. Cike da ladabi ya gaisheta ta amsa fuska a sake. Daga nan ta tashi ta bar falon ta koma dakin Hajjo. A nan ta sanar da Amatullah zuwan Qasim daya baban nata ta fito gaishe shi.
Qasim ya ajiye kofin lemon dake hannunsa yana maida hankalinsa Asmau.
"Asmau magana nazo muyi, ina fata zaki saurare kuma ki fahimceni."
"Ina jinka Yaya Qasim"
"Asmau kinsan irin shakuwa da abotar dake tsakanina da marigayi Abubakar"
Ta gyada kai tana tuno masoyin da bazata taba mantawa ba a tarihin rayuwarta.
"Duk abinda ya gudana a rayuwarku na sani na kuma san nima akwai sa hannuna a ciki. Bazan gaji da rokon gafararki ba saboda ance karfe daya baya amo. Kamar yadda kawa ta ribaceki haka nima nayiwa Abubakar, ga kuma sakamakon hakan duniya ta gani. Asmau tun kafin ki dawo na yanke shawarar aurenki ko a wane yanayi na sameki. Cikin ikon Allah yanzu na tsinci kaina da tsananin kaunarki"
A razane ta dago kai ta kalleshi ta mayar da kanta kasa. Yayi sassanyar dariya
"Nasan dole kiyi mamaki sai dai kuma ki sani burina ba wai na maye gurbin Abubakar bane. Ina so ki bani dama a matsayin masoyi na sami kaunarki na kuma zama uba ga 'yata Amatullah."
Wannan shine ana wata ga wata. Ita fa ko kadan bata son maganar aure ma yanzu. Qasim wani babban jigo ne a rayuwarta saboda yadda ya damu da lamarinta da na Amatullah. Ya rike amanar Abubakar ba da wasa ba.
"Yaya Qasim bani da abinda zance maka sai godiya da fatan alkhairi amma don Allah ka janye maganar aure a tsakaninmu. Maganar aure ba ta mace irina bace. Duk yadda zan so bani da wani mutumci da kima da zan kai gidan aure. Amatullah ko naki ko naso 'yarka ce amma don Allah mu bar maganar aure."
Dama yasan da wuya ta amince kai tsaye.
"Ba cewa nayi ki bani amsa yanzun nan ba. Zan baki lokaci kiyi tunani. Amma ki sani kamar yadda aure yake zama garkuwa ga kowace mace kema shine mutumcinki. Zamanki a haka shine zai janyo miki duk abinda kike gudu wato surutun mutane."
"Ni dai....."
Hannu ya daga mata alamun tayi shiru ya tashi tsaye "kiyi tunani nace kuma kiyi shawara da duk wanda kika san zai baki shawara tagari"
Rasa abin fada tayi kawai ta sanar dashi batun tafiyarsu a washegari yayi mata addua sannan yace zai zo idan ta dawo yasan lokacin tayi duk wani tunani da zata yi.
Bayan tafiyarsa Asmau ta shiga tashin hankali. Ko zata yi aure ba dai da Qasim ba. Idan ta amince tamkar taci amanar Abubakar ne. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa ta tafi daki da niyar kwanciya wayarta ta soma kara.
Sai da gabanta ya fadi da taga sunan mai kiran. Kwana biyu tun ranar da taki amsa wayarsa bai kara kiranta ba sai yau. Zuciyarta ce ta rinka bugu da sauri da sauri amma ta kasa amsa kiran. Text taga ya turo mata
_Idan Safina batayi bacci ba ki hadani da ita. Taki muryar ma ina son ji amma ba a waya ba, so wayar ba taki bace._
Wani dan murmushi ne ya subuce mata. Sai kuma ta dan dake tana yiwa zuciyarta tuni da cewar ta manta da maganar aure. Babu wani namiji da zai aureta a yanayin da take ciki komai tsahon lokaci ace wata rana bai goranta mata irin rayuwar da tayi a baya ba.
Dakin Umma taje ta bawa Amatullah dake aikin wasa da Husna wayar da ya sake kira. Kusan minti ashirin tana ta yi masa hira sannan mikawa Asmau. Da ta karba sakawa tayi a kunnenta tayi shiru tana so taji ko ya ajiye.
Yanayin yadda take saukar da numfashi ne ya tabbatar masa ta karbi wayar. Murmushi yayi kamar tana kallonsa yace
"Ana so ana kaiwa kasuwa"
Da sauri Asmau ta kashe wayar tana dariya. Me ya kaita saka wayar a kunnenta ne. Umma tace "ke lafiyarki kuwa?"
Tayi saurin daidaita kanta. Yanzu fa ta gama cewa babu zancen aure a sauran rayuwarta. Me yasa take jin wani daban idan al'amarin ya shafi Jikamshi.
*****
Col. Ishaq yana zaune ya saka abinci a gaba bai ci ba ya soma wayar. Dariyar da yake yiwa Asmau ce tasa Hajiya kallonsa.
"Yaya dai kake dariya kai kadai? Kwana biyu na fuskanci wani nishadi kake ji."
"Hajiyata babu komai" abincin yaci dan kadan ya sa Bilkisu ta kwashe kwanukan. Wai shine tunanin mace ya mayar haka. Abin da mamaki, duk dakiya irin ta soja yanzu baya jimawa sai Asmau ta fado masa.
******
Da wuri suka tashi aka karasa shiri saboda Yassar yana son dawowa a ranar. Kafin karfe goma na safe sun hau hanya bayan sun biya gidan Mama sunyi mata sallama.
Aina'u tana gaba Asmau na zaune a baya da baby Husna da Amatullah. Sunyi nisa Qasim ya kirata. Har kunya taji saboda yace ta kirashi kafin su fito taki kira, a cewarta kada ta sa masa rai yayi zaton zata amince nan gaba. Adduar neman tsari yayi musu sannan ya gaisa da Amatullah. Ba dadewa kuma Col. Ishaq yayi mata text. Lokacin bai dade da shiga office dinsa ba.
_Zan kira ki yanzu ki fara dauka kafin ki hadani da princess dina._
Ya zata yi ne da Jikamshi. Duk irin wannan abubuwan da yake yi mata kara kashe mata jiki yake yi. A daya bangaren kuma tana ganin gangancinta da har ta bari yake tasiri a zuciyarta haka. Idan har aure ya zama dole a kanta ma bashi ya kamata ta aura ba. Qasim yafi kusanci da ita, yafi sanin dukkan matsalarta. Amma Jikamshi shine a ranki zuciyarta ta tuna mata kafin wayar ta fara ringing.
A kasalance ta daga wayar ta kara a kunnenta kamar tana jin tsoron amsawa.
Shi kadai ya sauke ajiyar zuciya da yaji ta dauka.
"Just wanted to let you know how much I miss you."
Muryarsa da komai nasa daban take jinsa. Ga wani girmansa da take gani a kullum. Lumshe ido tayi batare da tayi koda gyaran murya ba.
"Idan kin janye yajin aikin yi min magana ki fada min zan zo na ganki. Ina Princess dina?"
Mika mata wayar tayi ta fara bashi labarin tun dazu suke cikin mota suna ta tafiya. Ina zasu je da safen nan ya tambayi kansa. Sai kuma ya tambayeta waye yake tuka motar tace Uncle Yassay ne. Yana son jin inda zasu je amma kuma baya son tilasta Asmau tayi masa magana. Karshe yace tace masa ya kirashu idan sun tsaya. Bata ajiye wayar ba ta fadi sakon. Yassar yasa Ainau ta danna speaker a wayar. Gaisawa suka yi ya fada masa inda zasu je. Col. Ishaq yace to a kula masa da 'yarsa.
Sai da ya ajiye wayar ya hau tunanin ko kwana nawa zasuyi. Kwana biyun da baiji murya ko yaga Asmau ba baya jindadi.
*****
A gidan Anti Bintu yau tun safe suke kitchen ita da 'ya'yanta. Yadda kasan bata ga Asmau ba bayan dawowarta haka take ji. Maman mijinta Kawu Yuduf tana gidan ana gyara a nata gidan. Tun da taga suna aikin nam take tabe baki tana kananan surutai. Bata tashi yin magana sosai ba sai da taji tsayuwar mota taga duk sun fita tarbarsu Asmau. Suna shigowa ta ganeta don dama ta santa. Yar tsohuwa tace
"Yanzu duk wannan doki da murnar na ganin shegiya ne da uwarta, banda lalacecar zamani yaushe 'ya zatayi zina sannan a rinka rawar jiki don ta dawo kamar wadda tayi wani abin arziki"
Anti Bintu ta rasa me zata ce don tsabar kunya. Asmau kuwa tuni ta soma zubar da hawaye. Babbar 'yar Anti Bintu da ake shirin aurarwa bata rai tace "haba Gwaggo"
"Wane irin haba, barni nayi magana son raina. Ba 'yar zinar bace ko kuwa uwarta bata bar mata abin kunya ba na 'ya'ya da jikoki?"
Ba Asmau ba hatta Aina'u sai da tayi kuka. Allah Ya rufa musu asiri ma Kawu Yusuf yana gidan ya fito daidai sanda babarsa ke yabawa Asmau maganganu.
"Gwaggo me ya kawo wannan maganar kuma. Kaddara ce wacce bata wuce kan kowa"
"A'a wallahi irin wannan kaddarar sai 'ya'yan da basu da tsayayye a kansu. Nawa jikokin Allah Ya tsare min su. Kowacce zata kai budurcinta gidan miji"
Kuka wiwi Asmau take yi. Kukan nata ba don abinda Gwaggo ta fada bane ai duk abinda tace gaskiya ne. Gaskiya kuwa akwaita da daci. Lallai sun tafka babban kuskure a rayuwarsu kuma muddin tana numfashi tasan wannan abu bazai taba gogewa daga zukatan mutane ba. Mutumci madara ne idan ya zube ba'a taba iya kwashe shi gabadaya.
Anti Bintu ta kaisu dakinta tana ta rarrashi da bata baki. Yassar ya kasa zama ya fice ya koma mota rai a bace. Allah Kadai muke yiwa laifi yafe mana baki daya amma indai dan adam ne to a kowane lokaci ya sami dama sai ya tuna mana da laifinmu ko da bisa kuskure ne. Hakika shaidan dole yayi murna idan yaci galaba ya sanya mutane suka aikata zina domin tabonta baya taba kankaruwa a duniyar mutane dai.
Yassar na zaune ransa sai suya yake. Ko kadan abinda aka fadawa yayarsa baiyi masa dadi ba. Mutane basu san laifi indai Allah akayiwa kuma aka tuba Shi mai yawan gafara ne da jinkai. Yamadidi da mai laifi bashi daga cikin kyawawan halayen musulmi. Tsaki yayi ya dauki wayarsa ya kira Col. Ishaq dama ya karbi numbar a wurin Asmau. Ya sanar dashi sun iso lafiya sai dai tuni ya gano akwai abinda yake damun Yassar din. Yayi ta tambayarsa me ya faru ya dage babu komai. Hankalinsa ne ya tashi ya kira Asmau.
A lokacin Anti Bintu har da mijinta sun gama bata baki sun fita akan sai tayi hakuri domin zata yi ta cin karo da irin haka.
Tana ganin wayar batayi tunani komai ba ta dauka.
Wannan muryar mai dadi taji yace "Ummin Safina"
Fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya wanda ya sashi saurin tashi daga zaman da yayi.
"Asmau me ya ya sameki?"
Shasshekar kukanta ya cigaba da ji ya sake kiran sunanta har lokacin bata amsa ba. Hankalinsa a tashe yace "Asmau please ki amsa mana"
"Naam" ta fada cikin muryar kuka.
To me aka yi mata haka?duk yadda akayi abin ya shafi 'yan uwanta tunda yaji Yassar ma ransa a bace.
"Kina son ganin Jikamshin ki?" Ya fada cikin wata irin murya.
"Naam" ta sake fada da alamar tambaya duk da kukan da take yi.
"Kinji me nace fa ni bana son gulma. In zo ki ganni ki fada min damuwarki?"
Sake kankame wayar tayi tana jindadin maganarsa harda dan murmushi.
"Kinyi shiru ko ba kya son gani na?"
"Eh" sai tayi saurin cewa "a'a" tun kafin ya sake magana.
"Ban san abinda ya saka min ke kuka ba amma ki rinka jira sai ina wuri kiyi kuka don na rarrasheki. I will see you soon in sha Allah"
Bai jira tayi magana ba ya katse wayar ya tashi ya tafi office din abokinsa.
SADAUKARWA GAREKU
*MATAN KWARAI NA SAMI SAKON GAISUWA
*UMMUL DIHYAH, HASSANA, USAINA, AMINA DA RUQAYYA.
SAURA MASU GAISUWA DUK BAN MANTA DAKU BA. NAGODE
ABINDA AKE GUDU🙆🏽38
Batul Mamman💖
Har karfe tara na dare ta wuce Col. Ishaq bashi da niyar tafiya. Hira suke yi da Anti Bintu da Kawu Yusuf kamar sun dade da sani juna. Sai ko Amatullah da ta tare a falon tana jikinsa tun bayan tashinta daga bacci. Hatta masallaci da ita suka je da Yassar. Maman Kawu Yusuf kuwa tana daga daki tuni tayi bacci bata san wainar da ake toyawa ba.
Asmau tana tare da 'yan uwanta suna tasu hirar amma tana tunanin yaushe Jikamshi zai tafi ne. Gashi a dalilin zuwansa Yassar yayi biris da zancen komawa Kano. Ainau ta dauki waya zata kira babbar Yaya wato Shemau ta tsegumta mata abinda ke faruwa a Zaria Asmau ta hanata.
"Naga alama sai da ya tofeku tas ya shigo gidan nan. Kowa sai wani kokarin kyautata masa yakeyi"
Ainau tayi dariya "ki ce hakan baya miki dadi duk sai mu daure fuska"
"Yaya Asmau mu dai kada ki cucemu ki hanamu zuwa bikin sojoji. Kinsan babu abinda ke bani sha'awa kamar su hada takubba amarya da ango su wuce ta tsakiya." Dijah ta fada tana hango ranar bikin.
Daga nan suka shiga tsara biki harda irin kayan da zasu saka. Tun Asmau na hanasu har ta koma sakin baki tana jin yadda suke bayani kamar gobe ne daurin aure. Da ta gaji tace "to amarori sai kuyi hakuri zan bata muku show amma ni bani da niyar aure, dadin abin ma ba cewa yayi yana sona ba kuke ta rawar kai"
Ainau tace "jiran *I love you*kike sai kace wata matar da. Yanzu ai alama kawai ta isheki. Dazu fa da na fito falo ba karamar kunya naji ba yadda yake yi miki ga Anti Bintu a wurin."
Bata da abin cewa da zai hanasu abinda suke yi sai kawai ta kyalesu.
*****
A falon Col. Ishaq yace zai nemi wurin kwana gobe da sassafe ya kama hanyar Kano don ba da niyar kwana yazo ba. Yassar yaso binsa masaukin da zai nema sai dai yadda Anti Bintu ke kallonsa ya gane rashin dacewar hakan ko don kada ya dora masa nauyi. Tace ya daure ya biyo ta gidan yayi breakfast sannan ya wuce. Ya tashi yana yi musu godiyar irin karramawar da suka yi masa, suma suna masa godiyar ziyarar da ya kawo musu.
A waje ya tsaya da Amatullah wurin motarsa ya tura Yassar ya kirawo masa Asmau. Daga shiga sallar magriba bata sake fitowa ba. Gabadaya kewarta ta dameshi. Don kada aga rashin kunyarsa tayi yawa ne da tuni ya nemeta saboda ziyarar ma don ita yayi.
Tasha tsokana a dakin kafin ta fito. Yassar ne mai yi musu jan ido su dena damun matar ubangidansa. Yana fadin haka ta dage ta kai masa dundu a baya tana cewa duk sun raina ta amma zatayi maganinsu.
Tana sakkowa daga matattakalar kofar wajen yana ta kallonta har sai da ta kusa faduwa saboda yadda kafarta ke hardewa. Yayi saurin zuwa inda take yana mata sannu ta dan daure fuska. Yayi murmushi
"ashe dai kema kina jin yadda nake ji Asmau."
"Nake jin me?"
"Dazu garin kallona kika kusa bugewa da bango, yanzu kuma gashi kina neman faduwa" yayi mata murmushi "idan muka yi aure anya zaki bari na rinka zuwa aiki?"
Tafa hannu tayi tana girgiza kai sannan tace "ni bansan me zan ce maka ba ma."
"Babu abin fada ne tunda kinsan gaskiya"
Ya bawa Amatullah ledar alawa yace ta shiga ciki yana zuwa. Sai da ta nunawa Asmau tayi masa godiya sannan ta shiga ciki.
Yace "gara ta koma cikin gida kada ki koya mata soyayya tun yanzu"
Dan cije lebenta tayi tana murmushi. Har kasan zuciyarta ta amince tana son Col. Ishaq. Bata san lokacin da ta kira sunansa ba a can ciki tana mai jan sunan.
_Jikamshi_"
Wani irin sonta yaji yana kara shigarsa. Bai taba damuwa da sunan garinsu ba amma saboda dashi Asmau take kiransa har wani dadi yake ji na daban.
"Yes dear"
Ta sunkuyar da kanta kasa "wai so...so"
"Ki fadi abinda zaki fada bana son jan rai. Ko don kinga ina son muryarki. Hmmm? Sai ki rinka kara hargitsani da ita."
Murmushi ta sake yi shima yayi. Yana jindadi idan yaga ta saki jikinta tana fara'a kamar kowa. Tace
"Wai soyayya muke yi"?
"A'a a filin yakin duniya na uku muke" ya bata amsa yana daga gira.
"Kina so nayi miki gwari gwari ne sai ki fi fahimta?"
Ta kawar da kanta gefe cike da kunya da fargaba. Muryarsa taji yace "Ina sonki Asmau Ummin Safina. Babban burina yanzu bai wuce na aurenki ba da kasancewa tare daku har karshen rayuwata. Kuma zuciyata tana bani kema abinda ke taki zuciyar kenan. Right?"
Hawaye taji sun taho mata. Wannan mutumi da ya santa cikin kankanin lokaci kuma yasan sirri mafi muni a rayuwarta shine yake fada mata kalaman so har yake batun aure. Dole taji sonsa yana kara shigarta sai dai kuma bata manta alkawarin da tayiwa kanta ba. Duk irin son da take yiwa Jikamshi bazata iya aurensa ko waninsa ba. Tana kuka tace
"Nagode Jikamshi, kaine mutum na farko da ya fara sona da gaskiya tun bayan kaddarar da ta sameni. Ka kyautata min kuma ka kyautatawa Amatullah. Allah Ya saka maka da alkhairi. Amma kayi hakuri da maganar aure. Kasan komai game da rayuwata me zai sa ka...."
Bai nuna damuwa ba ba fuskarsa sai ma murmushi da yake yi mata a yayin da take zubar da hawaye.
"Asmau, Asma'u na. Kina ganin idan nace na janye zaki ji dadi?"
Sai da taji faduwar gaba sannan ta gyada masa kai.
"Hmmm kamar gaske. Ina so kisan cewa bazan taba janyewa ba. Ni ba karamin yaro bane. At the age of 42 nasan meye so ko kishiyarsa. Kuma a naki idon so nake gani....infact kamar ki hadiye ni"
"Lahhhhh" ta iya fada hawaye na sintiri a idonta. Wallahi tana son Col I.M Jikamshi amma dole ta hakura indai ba so take ta daukarwa kanta dala ba gammo ba. Tana da yakinin ko Hajiyarsa bazata lamunce danta ya aureta ba.
"Rufe bakin mana"
Ta kuwa hade bakinta kamar yadda yace.
Dan kara matsowa yayi amma da sauran tazara a tsakaninsu.
"Kafin haduwarmu na ajiye batun aure a gefe tun bayan rabuwarmu da matata ta shekara kusan shadaya. Yanzu da na hadu dake sai nake jin rayuwata bazata kara min dadi ba idan babu ku. Ki manta da komai na bacin rai ki rungumi mai sonki. Ni fa nake nufi"
Murmushi ne yazo mata babu shiri. Sannan tace
"Kasan dalilina na gudun aure. Gori nake gudu ko a ni ko Amatullah. Sannan kaima duk inda kaje za'a nuna ka"
Hamma yayi alamun baya son maganar "duk kin tsareni da zance kin hanani na tafi na kwanta."
"Maganar fa tana da mahimmanci"
"Bacci na ma yana da mahimmanci. Ina fatan haduwa da Asmau ne muyi hirar arziki batare da tayi min kuka ba."
Jikinta ya kula yayi sanyi. Duk abinda take gudu ya riga ya hangosu amma ko da aure ko babu abinda ya faru ya riga ya faru a baya. Wucewarsa sai a hankali idan Allah Yaso. Indai ya sami amincewar Hajiya wanda baya tunanin zata ki to duk abinda mutane zasu fada sun dade basu fada ba.
"Zan baki lokaci daga nan har ki gama zamanki. Yassar ya fada min zaku je Niger so duk zan baki damar yin tunani kiji ko zaki iya zama batare da kina ganina ba. Ranar da kika dawo a ranar zanzo naji amsarki. Kada kiyi tunanin gujemin Asmau."
Kanta a kasa har ya shiga mota yana tausaya mata. Ba don kaddara ba ace tana son abu amma wani kuskure da ya riga ya wuce yasa tana gudunsa. Bata dago kanta ba har ya saita motar zai tafi sannan suka hada ido. A hankali ta karanta lebensa ta gane abinda ya fada wanda ba'a ji sai motsin bakinsa kawai.
_Love you_
******
Bayan tafiyarsa gida ta shiga tana ta juyayin zancensa. Dakin Anti Bintu ta nufa tayi sa'a bata dade da fitowa daga wanka ba. Cike da damuwa ta zayyana mata yadda suka yi da Jikamshi.
"Ko baki fada ba Asmau idanuwanmu sun gane mana. Ki godewa Allah da Ya dubeki da rahma Ya kawo miki mai share miki hawaye"
"Anti ba kya ganin rashin dacewarmu. Karshenta danginsa bazasu amince ba. Kuma ina tsoron wulakanci da gori nan gaba duk da ni na janyowa kaina." Ta fashe da kuka
"Haba Asmau. Har yaushe za'ayi ta maimaita abu daya. To bari kiji in fada miki. Indai bakiyi aure ba wallahi sa ido sai yafi a kanki. Ko takalmi kika canza sai an sami masu yi miki muguwar fassara. Gara kiyi aure ki samu garkuwa da rufin asirin da kowace mace take nema."
Tasan gaskiya ake fada mata amma gaba take ji. Ranar da miji zai goranta mata. Ranar da zai nuna mata alfarma yayi mata da ya aureta. Anti Bintu tana ta nuna mata ta karbi kyautar Allah hannu bibbiyu ta fada mata yadda suka yi da Qasim.
"Ikon Allah, wannan yanke shawara ba zai yiwu da gaggawa ba. Duk mun shaida irin neman da Qasim ya rinka yi miki. Amma banyi zaton abin zai kare a soyayya ba. Ga kuma Ishaq da kuka hadu lokaci guda ya kamu da sonki da na Amatulllah. Kuma kema nasan shi din kike so. Ki bari ku koma Kano nima sai nazo ayi magana da su Hajjo da Yaya Abu. A yanzu dai ki dage da neman zabin Allah. Amma ki sani aure shine gatanki. Kada na kara jin kince bazaki yi ba"
*****
Sati dayan da suka yi sunji dadin zaman garin idan ka cire maman kawu Yusuf. Soyayyar Jikamshi kuwa kullum karuwa takeyi a ranta. Duk da basa waya don yace zai bata lokaci tayi tunani batare da ya dagula mata lissafi ba. Ga Qasim kullum yana waya amma baya mata zancen soyayya. Shima yace sai ta dawo zasuyi shawara.
Al'amura duk sun cakude mata. Ranar da suka cika sati Umma, Yassar da Jafar suka iso harda Sabira. Mota biyu suka yi. A ranar suka wuce Wushishi. 'Yan uwa da abokan arziki sunyi musu tarba mai kyau. A gidan Kawun su Umma aka yi musu masauki. Mutane suna ta zuwa ganin Asmau da 'yarta. Kowa da abinda zai fada. Wasu su fadi mai dadi wasu kuma sai dai a kawar da kai idan sunyi magana. A nan ma sati guda sukayi suna zaga dangi sannan suka kamo hanyar Kano.
Tun a hanya Qasim ya sanar da ita zai zo washegari da daddare idan sun huta saboda jin amsarta. To kawai tace tana tunanin abinda zata fada masa. Gashi Umma tace sai sun dawo Kano zasuyi maganar sosai don duk su biyun babu na yarwa amma dai zukatansu sunfi karkata ga Qasim da suka sani tuntuni.
*****
Kamar yadda yayi alkawari a gidan Isha tayi masa ma. Bayan sun gaisa da Umma suka fito waje da Asmau suka zauna kan wasu kujeru daga gefe.
Bayan fitarsu Col. Ishaq ya rinka kiran wayarta. Yasan jiya tace zasu dawo saboda haka lokacin jin amsarta yayi. Da yaji shiru saboda tun kafin magariba ta jona chaji ta barta a daki sai kawai ya shirya ya taho.
******
Suna zama Qasim yace "Ya naga kamar kin rame ne? Ko duk rashin hutu ne kuna ta ziyara."
"Kai kuma kayi kiba Yaya Qasim kamar ba dansanda ba. Anya zaka iya bin barawo da gudu kuwa yanzu?"
Tare suka soma dariya yana kallonta yana jindadi. A daidai wannan lokacin Col. Ishaq ya shigo gidan da motarsa. Bisa rashin sani ya haskosu suna dariya ransa yayi matukar baci saboda kishi.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽39
Batul Mamman💖
Tsabar bacin rai yasa yayi wani irin cin taya sannan yayi parking din motar. Duk jikinsa tsuma yake yi, zai iya rantsewa bai taba jin kishi makamancin wannan ba duk tsahon rayuwarsa.
Asmau ma tuni ta hadiye dariyarta gabanta na faduwa. Duk da bata ganshi ba amma ta gane motar. Sai taji ta tsani kanta da har tayi abinda zai bata masa rai. Amma laifinsa ne don ranar da suka dawo yace zai zo shiyasa yau ta fito wurin Qasim da kwarin gwiwarta. So take yi ta fara sallamarsa sannan shima wanda yayi nasarar samun soyayyar tata ta nemi su rabu. Duk iya tunaninta karatu ne kawai mafita garesu ita da Amatullah.
Qasim bawan Allah ya kula da yadda ta canja lokaci guda har ya fara tunanin waye a motar. Motar ya rinka kallo da Asmau.
******
Kamar ya juya haka ya rinka ji sai dai kuma hakan ba girmansa bane tunda har ya shigo gidan. A zuci ya karanta *Hasbunallahu wa ni'imal wakeel*har yaji bacin ran ya ragu sannan ya fito yana zuba _kamshi_. Taku yake daidai har ya iso kusa dasu. Kamshin turarensa da yake sanya Asmau nishadi ne ya fara ziyartar ta. Taji bugun zuciyarta ya tsananta. A iya saninta da Jikamshi baya boye magana ko gaban waye. Bata san me zai ce a gaban Qasim ba, mutumin da bai cancanci wulakanci ko kadan ba daga gareta.
Yana karasowa ya saki fuska duk da ta ciki na ciki ya mikawa Qasim hannu yayi masa sallama.
Qasim ya karbi hannun shima cikin fara'a ya tashi suka gaisa. Sai kuma suka kalli Asmau suna jira ta gabatar dasu. Tsuru tayi da ido kamar wadda tayiwa sarki karya.
Da kyar ta saita kanta tace "Yaya Qasim ga baban Amatullah da nake fada maka. Col. I M Jikamshi."
Sake kama hannunsa Qasim yayi yana murmushi "naso ace har gida nazo na sameka domin kara mika godiya bisa taimakon da kayi mana. Allah Ya saka da alkhairi Ya bada lada. Ashe manyanmu ne masu tsaron kasa. Bari na baka girmanka yallabai."
Gyara tsayuwa Qasim yayi ya daidaita kafafunsa sannan yayi saluting Jikamshi. Shima murmushi yayi ya tsaya a attention ya mayar masa da salute din duk suka yi dariya banda Asmau.
Col. Ishaq yace "ka kirani Ishaq kawai. Asmau bata iya kiran sunana kai tsaye ne shiyasa kaji tana maka kwana kwana ko" ya fada yana mata kallon da ke kara kashe mata zuciya. Ta sunkuyar da kanta kawai. Abinda take gudu kenan ya bata kunya a gaban Qasim.
Ta daure tace "ga Yaya Qasim shi dan sanda ne"
"Allah Sarki, its a pleasure meeting you. Ai ta bani labarinka. Kune manyan ai muna bayanku. Baka ji ana cewa abokin kowa dan sanda" Col Ishaq ya fada yana kara kallonsa zuciyarsa fal kishi yana ta kokarin dannewa.
"Nima ta fada min yadda ta hadu daku. Muna kara godiya."
"Kada ka damu ai yiwa kai ne. Amma me kuke yi a waje haka ga kura? Ina tsammanin damuna ta kusa tsayawa dai" yadda yayi maganar Asmau ce ta fahimci da biyu yake yi.
Shi kuwa Qasim ya dan sosa kai yana dariya. Ko babu komai Jikamshi ya girme shi "Yallabai kenan. A tayamu addua dai muna nema ne"
Wani abu ne ya tokarewa Col Ishaq makoshi yaki sauka kasa. Wai ya taya shi addua. A zuciyarsa yace (Allah Yasa kada ta taba yi maka soyayya irin ta mace da namiji.). Abu daya ke yi masa yawo a ka shine kada Asmau ta juya masa baya. Wannan Qasim din wani sanyi ne gareshi mai sa mutum yaji dadin mu'amala dashi.
A fili kuwa murmushin yake yayi "ah to bari naje naga Amatullah sai na tafi. Dama ita nazo gani kewarta ta isheni" daga nan gefe ya matsa ya kira Yassar. Bai dade ba ya fito ya shigar dashi ciki. Ransa a bace da ya hango Asmau da Qasim yana taya Jikamshi kishi.
Bayan sun shiga ciki Qasim yayi ta yabon saukin kai irin na Col. Ishaq "kamar ba babban soja ba, ji yadda yake jana kamar ya dade da sanina"
"Uhmm" kawai Asmau tace a sanyaye.
"Asmau wace shawara kika yanke mana?"
Ta dago kai a hankali "Yaya Qasim ni dai da mun bar maganar nan"
"Kinga Asmau duk abinda kike gudu baki da tabbas a kansa. Yana iya faruwa ko kuma kiga bai faru ba. Haka nan ma masu aure na fuskantar matsaloli musamman mata daga dangin miji. Bance komai zai tafi mana daidai ba amma nayi alkawarin tsaya miki har karshen rayuwata"
Tausayinsa ta kara ji. Banda tsoronta na aure ko kadan bata jin son Qasim sai tausayinsa saboda yadda yake mata.
"Ka dan kara min lokaci, ban samu nayi maganar da Umma ba"
"To babu komai, shi garaje ai bashi da alkhairi. Duk yadda kuka yi ki sanar dani. Sannan zan kiraki idan na koma gida in sha Allah. Akwai keke da na siyowa Amatullah bari na dauko yana bayan mota"
"Nagode"
"Wai kin gode, mutum da 'yarsa? Shiga ciki bari na dauko"
Da sauri sauri tayi shige.
*****
Daga kallon kofa sai agogo Col. Ishaq yake yi tunda ya zauna hankalinsa baya tare dashi. Ji yake kamar ya koma wajen ya hana zancen. Hajjo ce take kokarin janshi da hira sai Amatullah tana bashi labarin Wushishi. Yassar kuwa kamar yaje ya dauko Asmau yake ji. Da ta shigo Jikamshi ya kafe ta yayi da ido ta kasa kallon inda yake kawai sai ta shige dakin Umma inda suke ta hada kaya ita da Ainau zata koma gidanta washegari.
Qasim ya shigo da keke mai kyau na yara. Amatullah sai tsalle da murna. Tana ta cewa ta gode kamar yadda Umminta ta koya mata. Hajjo ta dubi Col Ishaq "da kai da Qasim kuna shagwaba yarinyar nan da yawa. To ni ina nawa keken?"
Suna dariya Yassar yace "kada ki damu ni zan siyo miki irin mai katuwar tayar gaban nan na zamaninku"
Umma ta fito tayi godiya sannan Qasim yayi musu sallama ya fita. Sai da suka ji tashin motarsa Col Ishaq shima ya tashi yace da Amatullah ta kira Umminta su gaisa. Umma ta jinjina kai tunda ya shigo dazu ta kula ransa a bace yake yana dannewa. Gaskiya akwai matsala nan gaba sai dai fatan Allah Ya zabawa Asmau mafi alkhairi cikinsu.
*****
Tana kwance akan gado har wani zazzabi ke neman kamata saboda tunani Amatullah ta fada mata sakon babanta. Ta dan zaro ido "Baba Qasim ya tafi?"
"Eh ya tafi kuma ya kawo min keke mai kyau"
"Kinyi masa godiya ko"
"Nayi masa Ummi"
"Muje kiyi wasa kafin lokacin bacci yayi"
******
Baya falo da ta fito sai ta saka takalmi ta fita waje.
Tsaye yake a jingine da motarsa yana danna waya ta hasko fuskarsa. Kamar mai taka kwai haka Asmau ta karasa gabansa.
"Ina wuni"
Muryarta tana masa dadi, wani irin sonta yake kara ji yana shigarsa. Sai dai kishi yasa ya kasa amsa gaisuwar.
"Asmau wallahi ina da kishi sosai. Kada ki bari na kara ganinki a yanayi irin na yau. I can't take it"
Ta kara sunkuyar da kai da jin furucinsa.
"Kinga ki dago kanki ki kalleni magana zamuyi"
Mayafinta tasa ta rufe fuskarta gabadaya. kunyarsa take ji.
"Kina so na bude fuskar ne da kaina?"
Ta girgiza kai da sauri
"To ki bude da kanki kafin hakurina ya kare"
Hannu tasa ta bude fuskar tare da dagowa a hankali. Fuskarshi ta bata tsoro saboda babu digon wasa
"Jiranki da nayi a falo dazu yana cikin lokutan da bazan manta ba a rayuwata. Zuciyata bazata juri ki hadani da wani ba"
"Don Allah kayi hakuri" tace idonta na kawo ruwa.
"Ki fada min ni dashi waye ya fara nuna miki so"
"Kai ne" ta amsa masa jiki a sanyaye. Bata son bata masa rai ko kadan saboda yadda take sonsa.
"Alhamdulillah, da ya rigani zan ci girma na bar masa ke don bazan iya tarayya da wani akanki ba. Ina da kishi mai zafi wanda ban taba sanin kaina dashi ba sai yau. Amma tunda na riga shi sai dai shi ya hakura. Ina sonki kuma bana jin zan iya hakura dake."
Shiru tayi tana kallon kasa. Tun bayan rasuwar Abubakar ta cire rai da sake samun soyayyar wani da namiji sai gashi yanzu har mutum biyu ne suke sonta. Mutum biyun da take matukar son daya, dayan kuma take ganin girmansa. Duk su biyun kuma tana jin kunyar nuna musu bata sonsu a yadda take ganin ba karamin darajata suka yi ba da suke sonta da aure.
Col Ishaq yana kallo yadda ta shiga rudani. Kamar yadda ya fada mata da ace Qasim ya rigashi to zai hakura ne indai ya tabbatar da gaske yake sonta. A yanzu kuwa yana da yakinin shi Asmau take so kuma ya riga saboda haka yana nan daram sai yaga abinda ya turewa buzu nadi. Shi kishin kara masa so da kaunarta yayi ma.
"Kamar kwana nawa kike bukata na baki ki sallame shi"
Ji karfin hali ta ayyana a ranta. A fili tace "bangane ba"
"Kin gane, karin bayani kike nema dai. Bansan iya matakin da kuka kai ba ke dashi shiyasa zan baki lokaci kuyi rabuwar arziki. Shima don na fahimci kamar yana da halin kirki ne."
"Ya kake so nayi? Kaima na fada maka babu zancen aure a raina shima kuma hakan na sanar dashi"
"Idan babu zancen aure a ranki kin tanadi yadda zakiyi da soyayyata wadda yanzu ma na fara nuna miki ita. Idan bakiyi wasa ba nan gaba kadan saboda yadda zan rinka yakin neman sonki da kanki zaki ce gobe a daura mana aure"
Dariya tayi, shi a komai sai ya saka wasa tace"kai Jikamshi"
"Allah kuwa Asmau" shima ya mayar mata da murmushi.
"Ni da ban taba cewa ina sonka ba. Amma kana da confidence a kaina"
Kansa ya shafa yana kallonta. Baya gajiya da kallon Asmau ko kadan.
"Asmau kina sona. Nima ina sonki. So bana bukatar sai kinyi ta maimaitawa da baki. Akwai lokacin da zaki rinka fada da kanki"
Ita kam Jikamshi yana bata mamaki. Sai ya fadi magana ya kuma dake abinsa.
"Ki shiga ciki bana son kina shakar kurar nan. Kada ki manta da abinda nace. Idan kin sallame shi zan turo iyayena a fara maganar aurenmu"
Magana taso yi ya sanya yatsansa akan lebensa alamun tayi shiru.
"Idan rokona zakiyi akan Qasim kada ki bata bakinki. Nan da sati biyu idan baki sanar dani yadda kuka yi ba ki zaki ga magabatana sunzo. Ki kula min da kanki da princess dina. Yau duk kin rikita min lissafi na kasa bata kulawa yadda ya kamata"
"Ni babu ruwana."
"Harda tsakinki. Sai da safe"
"Allah Ya bamu alkhairi"
Tana kallo ya shiga mota ya zauna sannan itama ta juya.
"Matar Jikamshi"
Cak ta tsaya amma bata juyo ba sai murmushi da take yi.
"I love you"
Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cike da kunya tayi hanyar gida a kunyace.
******
Daurewa kawai Col. Ishaq yayi har suka karashe hirar cikin wasa. Da ya rage shi kadai yana tuki tunani yake kada iyayen Asmau su bawa Qasim ita saboda sunfi sanin shi sannan abokin Abubakar ne. Saurin kawar da tunanin yayi daga ransa. A zatonsa ya gama soyayya akan Badar sai gashi lokaci guda Asmau ta wargaza masa tunani.
Yana zuwa gida dakin Hajiya ya wuce. Bayan sun dan taba hira ya sanar da ita zancen Asmau. Tayi mamaki sosai don bata taba hasko hakan ba. Bilkisu da tayi niyar fada mata kuma ranar tun a hanya yaja mata kunne. Shiru tayi na dan lokaci kafi tace
"Kai yanzu kana tunanin sai ka aureta ne kawai zaka iya kyautata rayuwarta da ta Safina?"
"Hajiya nifa ba don in kyautata musu kawai nake son aurenta ba. Ina sonta ne tsakani da Allah"
Ko kunyar yace yana son mace baiyi a gabanta. Tayi iya kokarinta wurin nuna masa kunyar dan fari amma duk baya biye mata. Yanzu me ya kawo zancen soyayya a gabanta.
"Bazan zama irin iyaye marasa karbar kaddara ba musamman da na san komai game da ita. Kai ba yaro bane da zan ce baka san abinda ya kamata ba. Amma ka jira nayi shawara da 'yan uwana dana mahaifinka. Kasan zancen duniya baya buya. Gara su sani tun kafin ayi auren sabo gudun gutsiri tsoma"
Murmushi yayi ya nuna mata tsantsar farincikinsa. "Hajiya nagode da kika fahimce ni. Ina fata ko sun nuna rashin amincewa don Allah kada ki hanani aurenta don wallahi bakiji yadda nake jinta a zuciyata ba"
Haj Lubabatu ta kawar da kanta gefe a kunyace. Ya cigaba da cewa "idan tayi murmushi ji nake kamar...."
"Kai tashi ka bani wuri zancen ya isa haka" ta fada amma kafin ya tashi ita tayi gaba. Dariya yayi dama tsokanarta yaso yi.
Sai da ya gama shirin bacci ya dauko wayarsa zai kira Asmau yaga missed calls da bakuwar number har uku. Ya kira numbar ga mamakinsa sai yaji muryar Qasim. Sun sake gaisawa yace ya karbi numbarsa a wurin Yassar ne don su rinka gaisawa. Hira suka dan taba cikin mutunta juna. Suna yin sallama ya kira Asmau.
Ta dauka kafin tayi magana yace cikin muryar shagwaba "Matar Jikamshi kin cuce ni"
Gyara zama tayi a dan tsorace." Me nayi kuma"?
"Wannan dan sandan saurayin naki wallahi yana da mutumci. I feel guilty nace ki rabu dashi gashi har yana min waya."
Ta dan murmusa "to ko na barshi kai ka janye"
"Ba haka nake nufi ba fa. Kawai dai naji babu dadi ne. Da kin sani wani dan caburus kika nemo wanda zanji kwarin gwiwar yiwa rashin....." ya dan toshe baki "wai shekarunki nawa ne? Kinsan dole na kula da abinda zan fada a gabanki saboda kada na bata yarinya"
"Nice ma yarinyar. Shekarata ashirin da takwas fa"
"Kai, kai ,kai...kada azo a kamani ina soyayya da 'yar yarinya"
Asmau sai dariya take yi tana juyi akan gado, Ainau daga gefe tace "love in Tokyo"
Pillow ta jefeta dashi ta cigaba da dariyarta saboda yadda Jikamshi yake mata shagwaba yau "shiyasa nace ka hakura ka janye kawai ka barwa yaro"
"Ai baki isa ba yarinya. Bayan duk kin gama kashe min jiki da wadannan idanuwan naki. Na dai fada miki ina tausayinsa ne amma bance ki tausaya masa ba. Ki gaggauta sallamarsa kada ya janyo zuciyarki da kirkinsa"
"Jikamshi"
Sai da ya gyara kwanciya ya amsa mata "mene ne?"
"Babu komai, sunan kawai nake son fada"
"Shi mai sunan ba kya son shi?"
"Ina so"
Da sauri ta tashi zaune da ta gane abinda ta fada. Ta rasa dalilin da yasa idan tana tare dashi take manta komai tayi ta sakin baki. Ko dai ta fara zama irinsa ne???
*****
Washegari Malam Musa ya zaunar da iyalinsa ya fada musu cewa nan da sati mai zuwa zai tura masu wakiltarsa a nemawa Qasim auren Asmau. Ya gaji da ganin dan nasa gwuaro. Da Qasim yace basu gama shawara sa Asmau ba, Mal Musa yace babu komai sunyi magana da Alh Adamu yace zaije ya sami Umma da Kawu Garzali a tsayar da magana ayi aure kowa ya huta. Murmushi Qasim yayi na jindadi don yasan Asmau bazata bijerewa iyayensu ba.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽40
Batul Mamman💖
Washegari su Asmau basu sami zaman gida ba. Sun hadu da Shemau, Sabira da su Nasiba an sake gyara gidan Ainau kamar masu shirin kai amarya. Da yamma Umar yaje ya daukota. Kana ganinsa kasan yau yana cikin farinciki. Kusan wata uku bata gida don tun kafin ta haihu aka bata bedrest shine Mama tace ya kaita gida zata fi hutawa.
Ranar Jikamshi ya kirata yafi sau shida kuma sai anyi hira akalla ta rabin awa. Yana kira sai ya tambayeta ko Qasim ya kira kuma wayar minti nawa suka yi. Sai da ta gama dariya sannan ta zolaye shi tace
"baya ajiye waya sai wata wayar ta shigo min."
Shima dariyar yayi mata kawai yace "ba zan damu ba don nasan tawa hirar ce kawai take burgeki koda kuwa ta minti daya ce. Amma zancen gaskiya ki dena kashe masa murya yadda kike yi min. Kara sonki kawai zaiyi ni kuma ba hakura zanyi na bar masa ba"
Tayi dariya sosai hakan ya sanya shi nishadi.
"Haba Yaya Ishaq, kai fa Yayana ne kuma Yayan Qasim. Kaci girma kawai"
Kamar tana gabanshi ya dan daure fuska cikin wasa "ki kiyaye ni fa matar Jikamshi. Ni ba yayanki bane na fada miki. Kina magana da baban Safina mijin Asmau in Sha Allah"
Ta danyi shiru tana jin inama hakan ya tabbata.
"Baki ce amin ba"
"Amin" ta amsa ba don yana tunanin ganin ranar aurensu a gaba ba. Addua zata yi masa Allah Ya bashi mace ta gari. Amma tasan bazata je komai ba a bikin.
Daga haka suka yi sallama kowannensu yana kara jin son dan uwansa.
*****
Bayan sati daya kullum Col. Ishaq da Qasim sai sun kirata a waya kowanne yana kara jaddada mata irin son da yake mata. A wannan kwanakin da Jikamshi bai zo ba ita kanta abin ba karamin damunta yayi ba. Har mamaki take yi da take masa so irin wannan duk da tana kokarin dannewa. Ranar alhamis ta kira Zubaida ta sanar da ita zata zo yini washegari. Zubaida sai murna don tun dawowarta sau daya ta samu taje gidan, basu zauna sunyi hira yadda suke so ba. Ita kuma Zubaida saboda cikinta ya tsufa babu batun fita.
Kafin shabiyun rana washegarin Asmau ta gama girkin rana tayiwa Amatullah wanka sannan itama ta shiga. Tana fitowa taga Umma ta dawo duk da ranar aiki ne. Har daki ta bita tana tambayar ko lafiya.
"Babu komai yau dai na gaji ne. Kinsan kwana biyu bamu huta ba. Kema da kin hakura da zuwa gidan Zubaidan sai wani satin. Yarinyar nan kina ta yawo da ita 'yan kwanakin nan"
"Umma Yaya Jafar yace zai kaini ba adaidaita zan hau ba."
"To kiyi maza ki karasa shiri kinsan baya son jira."
Asmau ta tashi ta koma daki ta karasa shiryawa sannan ta zauna jiran Jafar. Ko rabin awa ba ayi ba ya iso. Suna shirin fita taga Kawu Garzali shima ya shigo. Gaisawa suka yi yace mata Zubaida tun asuba take jiranta. Yanzu Kawun nasu kamar wani kaka haka yake musu wasa. Shima dai tayi mamakin ganinsa don ance mata Umma ce ta sama masa aiki a inda take wato MTN office.
*****
Suna fita Umma tayi ajiyar zuciya ta tafi dakin Hajjo ta sanar da ita wayar da suka yi da Mama tun tana wurin aiki. Shine ma dalilin dawowarta gida da wuri da zuwan Kawu Garzali. Alh Adamu ne yake son ganinsu don yace gidan zai zo idan ta taso aiki. Kasa hakura tayi saboda Mama tace mata batun auren Asmau da Qasim ne zai kawo shi. Shiyasa ta fada Garzalin suka dawo gida kawai. A cikin satin da tayi magana da Asmau akan manemanta biyun ta nuna mata ita karatu kawai zatayi duk zata sallamesu batare da bacin rai ba. Sai dai kuma tuni Umma ta gano inda zuciyar 'yarta tafi karkata. Matsalar dai bai wuce abinda itama Asmau take jiyewa tsoro ba na dangane da gori ko rashin amincewa daga dangin mazan.
Bayan ta gama bayaninta Hajjo tace "yaron nan da gaske yake da rike amanar amininsa. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Ta danyi shiru kamar mai tunani sannan tace
"Amma idan banyi kuskuren fahimta ba sai naga Ishaq shima kamar fa sonta yake yi. Kinsan mu idonmu idon soyayya. Muna ganinta muke ganewa"
Umma tayi dariya sannan ta fada mata wayarsu da Anti Bintu da kuma yadda suka yi da Asmau
"Bazamu zuba mata ido ba duk da muna jin tsoron surutun mutane auren shine rufin asirinmu. Duka su biyun ni bana kin kowa amma Hajjo kinga Qasim muka fi sani kuma gashi har maganarsa ta kai kunnen manya. Garzali ma ya shigo ina tsammanin a falo ya tsaya. Shine namiji dole ayi komai dashi "
"Kinga wancan mutumin banzan shi ya kamata ace zaiyi komai akan lamarin yaran nan amma kafin a ganshi ma aiki ne"
Umma ta fahimci da Kawu Rabe take. Murmushi kawai tayi "kada ki damu Hajjo, Garzalin ma ai babanta ne kuma na fadawa su Yaya Abu don su san me ake ciki. Saura kuma sai yazo munji"
Kawu Garzali sallama zai shigo dakin yaji Hajjo tace "Kinsan Allah Bara'atu kada ku yarda kuce kun amince ba tare da munji ta bakin Asmau ba, bazan yarda kuyi mata auren dole ba. Idan bata so ya hakura kawai"
Umma tace "Hajjo mu har mun isa muce bama so? Kada ki manta duk abinda ya faru da Asmau. Yanzu duk wanda yazo neman aurenta ai alfarma yayi mana"
Hajjo ta danyi shiru tana tausayawa jikarta "kuma fa haka ne. Allah Ya rabamu da mummunar kaddara"
Tashi Umma tayi "dama yanzun ma ina jin shawara ce dai yake son bamu a matsayinsa na uba gareta."
Kawu Garzali ya gaishe da Hajjo sannan tace su fito falo Alh Adamu yazo.
*****
Sun zazzauna an gaisa da Alh Adamu da Mama Yalwa da bata dade da shigowa ba itama.
Yayi dan gyaran murya wanda ya janyo suka fuskance shi "Nasan Yalwa ta fara sanar dake dalilin zuwan nan. Mal Musa ya kirani a waya ya sanar dani yadda suka yi da Qasim akan auren Asmau. To shi a son ransa nan da lahadi su zo ayi magana ta iyaye a tsayar da lokaci. Shine ya bukaci lallai in fara sanar daku domin ayi shawara"
Hajjo ce ta soma magana "hakika Alhaji kai uba ne ga dukkan 'ya'yan Bara'atu. Ka rikesu tsakani da Allah tun lokacin da mu da suke dolenmu muka wofantar dasu. Duk shawarar da ka yanke akan yarinyar nan muna da tabbacin bazata cutar da ita."
"Duk da haka Hajjo me kuka gani? A basu dama su zo ko akwai wani tanadi da kuka yi mata".
Kawu Garzali yayi saurin cewa "haba haba Alhaji akwai wani tanadi ne da ya wuce aure. Amma Haj Bara'atu me kika gani?"
Idanu suka koma kan Umma. Daga yadda Alh Adamu yake magana ta tabbatar yana so su amince tunda har ya zo gidan da da kansa. Mutumin nan yayi musu gata fiye da tunanin mutane. Ta dauke shi tamkar dan uwanta bazata iya bijere masa ba balle kuma Asmau.
"Nima dai bani da zabi sai abinda kuka yanke. Wannan aure idan ya yiwu ba karamin dago mata martaba zaiyi ba a idon jama'a sai dai muyi fatan alkhairi. Shi kuma Abubakar Allah Ya gafarta masa" ta kare da guntun hawaye. Da yana raye duk wannan abin bazai taso ba.
Mama ma sai ta soma kuka duk kuma zukatansu suka raunana. Alh Adamu yace "zaku fara ko?"
Da yaga sun nutsu ya ce "tsakani da Allah ni naso nasa Abdulhalim ya nemi aurenta domin kare martabarmu gabadaya. Sai na bari ta dan kara kwana biyu ashe rabon Qasim ce. Zan sanar dashi su zo jibin. Idan yaso sai mu kira dangi na kusa azo ayi komai da wuri. Iyalin Mal Musa sunyi mana abinda bazamu manta ba tunda suka bari dansu ya nemi auren tamu 'yar."
Sunyi ta tattaunawa akan maganar karshe mazan suka yi shirin zuwa masallaci. Aka bar su Mama suna kara shawara akan kamar yaushe ya kamata asa auren idan dangin Qasin sun nemi asa rana da wuri.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽41
Batul Mamman💖
Asmau tana can gidan Zubaida suna hirarsu bata san wainar da ake toyawa a gidansu ba. A cikin hirar ne ta fada mata zancen Qasim da Col. Ishaq.
Zubaida taji dadi sosai "kinga yadda Allah ke juya lamarinSa ko. Shawarar zan baki ki yarda kiyi aure amma ki zabi wanda zuciyarki tafi so. Ni shaida ce akan irin abinda Qasim yayi da kika bata to amma nafi danganta hakan da rike amanar Abubakar da yayi. Bansan gaskiyar lamari akan menene a zuciyarsa ba yanzu. Ma'ana soyayya ce ko tausayi. Shi kuwa sojan nan dole na yaba masa. Duka duka yaushe ya sanki amma yake sonki da aure"
"Ba kya tunanin nan gaba matsala ta taso ko a kaina ko akan Amatullah"
"Hmmm Asmau kenan, ke kike da goben da har kike tunanin matsala? Yadda Allah Ya daidaita miki lamura yanzu, idan har wani abin ya taso a gaba Shi din dai zai mana magani. Kada ki manta nima ba 'yar aure bace amma Allah Ya hadani daku gashi babu wanda ya taba yi mim gori. Auren ma Hajjo ce ta hada. Zamana nake lafiya na manta da kazantar da na taso cikinta. Yadda na hadu daku da yardar Allah itama zata hadu da mutane nagari a rayuwarta"
Asmau ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na taho mata. Duk matar da tayi zina ta gama cutar abinda ta haifa. Sai dai idan an hadu da mutane na kwarai. Kuma duk da haka haifewar itace tafi akan zubar da ciki wanda yake daidai da kisa idan an busawa jaririn rai. Mace sai ta sami rahmar Allah idan ta rungumi kaddararta ta bawa abinda ta haifa tarbiyar da ta dace da addininmu.
"Ki kara hakuri da rayuwa Asmau. Haka Allah Ya tsara miki. Ke kika zama ishara ga masu hankali wadanda idan sunji labarinki zasu san cewa biyewa sharrin yanar gizo da son zuciya halaka ne. Uwa uba babu wani alkhairi da yake tattare da shiga groups din nan na whatsapp ko facebook masu yada alfasha."
"Nagode Antina ta kaina. Allah Ya raba lafiya mu sha suna"
Dadi Zubaida taji da taga Asmau ta dan sake. Amatullah tana tsakar gida suna wasa da yaran Zubaidan.
"Tashi mu soya wainar fulawa"
Asmau ta zaro ido "yaushe muka gama cin abinci?"
Cikinta ta shafa "bani nake so ba kaninki ne ko kanwa"
"To kala masa sharri saboda bashi da baki. Ina fulawar take na hada?" Ta fada tana tashi.
Ranar dai sun wuni suna hira kuma taji dadin shawarar da Zubaida ta bata. Duniya kenan, Zubaida da ta tashi a matsayin 'yar magajiyar karuwai gashi Allah Ya sauya mata rayuwa. Sai bayan magariba Asmau tayi shirin tafiya. Dama Jafar yace zai dawo daukarta sai ya kira yace ayyuka sun masa yawa. Nan kuwa bata san suna can gidansu ana maganar aurenta bane.
Zubaida ta sake yi mata tuni akan lallai kada ta bari dama ta kubuce mata. Ta amince tayi aure
"Ni na kula sojan nan ba dai iya nuna kulawa ba. Zuwanki nan kunyi waya sau uku."
Murmushin Asmau ya tabbatar mata da zarginta na cewa shi take so. Har kofar gida ta rakata suka tafi titi suka shiga adaidaita sahu ita da Amatullah suka tafi gida..
Abin mamaki tana zuwa ta tarar da Anti Bintu tazo da yaranta wai zasuyi weekend. Tayi murna sosai. Amatullah ma ta ganesu saboda haka ta saki jiki ana hira. Umma tace idan ta huta tazo dakin Hajjo tana son ganinta. Anti Bintu Asmau ta kalla tana dan murmushi, ko dai ta fadawa Umma zuwan Jikamshi Zaria ne. Karshenta maganar aure ce. Ta riga ta kudiri niyar bin shawarar Zubaida. Zata tsananta addua ta amince da Col. I M Jikamshi.
*****
Ko kayanta bata cire ba da ta shiga daki Jikamshi ya kirata kamar yasan tunaninsa take yi a wannan lokacin.
Daukar wayar tayi tare da yin sallama.
Shima lokacin yana gida ya tasa laptop a gaba yana kallon wasu hotuna da ya dauki Amatullah. Yana son yarinyar nan, ko babu komai ta dauke shi uba sannan gashi tayi sanadiyar hadashi da Umminta. Safinansa akwai shiga rai.
Sallamar Asmau ce ta katse masa tunani ya amsa mata cikin daddadar muryarsa.
"Matar Jikamshi kun dawo gida lafiya?"
"Lafiya kalau"
"I miss you so much"
"Duk wayar da muke yi tun safe?"
Yayi yar dariya "yanzu ke hirar waya ta isheki. Ni nafi son na ganki a gabana. By the way lokacin da na baki fa yayi. Anyi sati daya ya kuka yi da Qasim?"
Shiru tayi domin kuwa bata sami biyan bukata ba. Tayi kokarin nuna masa ya hakura da zancen aure sai ya rinka danganta abin da ko tana gudun aurensa saboda tunanin Abubakar ne. Karshe yace mata ta jira nan da lahadi komai zai zo karshe.
Col Ishaq yace "ya kika yu shiru? Kada kice min bakiyi komai ba."
Sautin muryarsa kamar baiji dadi ba tace "ka kara hakuri yace na jira zuwa ranar lahadi idan yazo kamai zai zo karshe"
"Ban fahimceki ba, komai zaizo karshe kamar yaya?"
Asmau kanta bata gane abinda Qasim yake nufi ba "nima dai haka yace min"
Col. Ishaq ya tashi daga kashingidar da yayi "look Matar Jikamshi, ni mutum ne kaifi daya. Idan kina jin nauyin fada masa saboda kusancin families dinku ni zan fada masa da kaina. Tunda naga ya cigaba da yi min text da waya nasan bai san alakarmu ba. Kinga kashe wayar kawai bari na kira shi na fada masa Ishaq da Asmau suna son juna don Allah ka nemi wata"
Bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba "yanzu don Allah sai ka fada masa haka"?
"Kin dauka wasa nake yi, yara ne suke da lokacin wasa da soyayya."
Tace "kayi hakuri zuwa lahadin please"
Yadda take magana duk ya kashe masa jiki. Zai iya hakuri amma zuwa sunday kawai. Daga nan kuwa to sai dai ayita ta kare. Shi ba don yana ganin mutuncin Qasim din ba tun ranar da ya gansu da Asmau da a lokacin zai fada masa.
"Yarinya dake duk kin rikita min lissafi. Amma zan rama ne, sai kin shigo gidanki"
"Nima fa ka rikita min"
"Me kika ce?"
Zancen zuci ne ya fito fili tayi saurin toshe bakinta. Ta rasa inda zata sa kanta don kunya. Tana ji yana mata dariya don yasan bata so yaji abinda ta fada ba.
"I love you Matar Jikamshi. Nasan bazan kara samun nutsuwa ba idan ba aurenki nayi ba. Na riga na fadawa Hajiya amsarki nake jira a fadawa iyayena maza. Idan kika zabi Qasim zan tayar da yaki a zuciyarki"
Wani dadi ne taji yana ratsata. Ashe tana da rabon samun farinciki a rayuwarta. Ita ma tana son shi kuma ta shiryawa duk wani nau'i na gori da zai iya zuwa daga danginsa. Abinda ake gudu ya riga ya faru sai dai a kiyayi gaba.
" 'yarka da Yassar ma bazasu barni ba idan na zabi wani ba kai ba. Da ka tashi sai ka hada da zuciyata data Amatullah kuma harda ta kanina."
Da tasan irin yadda yake ji a ransa da ta rage yi masa magana ko don ta sassauta masa. Ajiyar zuciya yayi har tana jin sautin
"Say you love me please" ya fada cikin sanyin murya.
Yau daya zata sakaya kunyarta ta farantawa mai faranta mata "I do love you _Jikamshina_"
Kafin ya kara magana ta kashe wayar gabadaya don tasan zai sake kira. Kwanciya tayi akan gado tana juyi ita kadai zuciyarta kamar an wanke mata.
Shi kuwa rike yake da wayar a hannu yana murmushi. Hmmm bari dai ace an daura musu aure. Ranar Asmau zata san tana da masoyi. Zaiyi iya kokarinsa wurin nuna mata soyayya da cewar itama har yanzu tana da darajarta a cikin mata. Abinda ya wuce a baya sai ayi ta addua da fatan Allah Ya yafewa musulmi kurakuransu.
*****
Tana ta maimaita hirarsu a kwakwalwarta tana dariya Amatullah ta shigo
"Ummina Umma tana kiyanki"
Ai da sauri ta sauko daga kan gadon. Shaf ta manta Umma tace tana son ganinta.
Saurin da take yi yasa Amatullah tace "Ummi guduwa zamuyi ne? Me nene akan gadon?"
Asmau tayiwa kanta dariya sannan ta dauki Amatullah tana juyi da ita. Soyayyar Jikamshi ta zame mata wani bangare mai mahimmanci a rayuwarta. Tana juyin tana dariya.
Amatullah tana tayata duk da bata san dalilin murnar Ummin ta ba
"Ummi abin dadi ne ya fayu?"
"Shine zai faru in sha Allah Ama, muma Allah zai bamu rayuwa mai tsafta kamar kowa"
"In ce Alhamdulillah?" Amatullah ta tambaya
"Fadi kinji Aman Ummi"
Sai da ta gama murnarta ta kama hannun Amatullah suka fito. A falo ta barta ta karasa dakin Hajjo. Kafin ta shiga taji muryar Anti Bintu tana magana sama sama da ji kasan ranta a bace yake
"Yaya Bara wallahi Asmau tana son Ishaq. Don ta fada miki zata sallamesu duk su biyun kawaici ne kawai. Ita a tunaninta bata da wata kimar da namiji zai aureta. Don Allah kada ku shiga tsakaninsu. Hajjo kiyi mata magana "
Hajjo tace "Bintu nima ba wai naki Ishaq bane. Ki tuna wacece Asmau, tana da tabon da babu ruwan da zai wanke shi duk duniya. Qasim da iyayensa sun san komai game da ita kuma dazu muke ji ashe saboda ita yaki aure tuntuni wai kada kishiya tayi mata gori ko habaici"
Anti Bintu tace "to duk abinda yayi ai ba wai sunyi da ita zata aure shi bane. A yadda na kula da irin son da Ishaq yake mata ba zai hakura kai tsaye ba."
Umma kanta tasan wanda Asmau take so amma bazata iya yiwa Alh Adamu musu ba kamar yadda shima yaji nauyin Mal Musa. Idan ta biyewa Bintu jan zancen kawai za'ayi ta yi azo zumunci ya sami rauni.
"Bintu don Allah ki bar zancen nan. Komai ya kure tunda ranar lahadu zasu zo kawo kudi. Itama sai tayi hakuri ta karbi kaddara"
A fusace Anti Bintu ta mike "ni bazan zuba ido ina kallo a cuci yarinyar nan ba. Ba kwa tunanin kada *abinda ake gudu* ya sake faruwa? Don kaddara ta fada mata shikenan kuma bata da damar zabar wanda take so"
"Abinda ake gudu ya riga ya faru kumq shine yasa dole duk muyi hakuri. Kina jin da hakan bata faru da rayuwarta ba zan amince da auren nan ne? Yanzu kuwa bamu da bakin magana tunda mu za'a taimakawa. Ki dena bata bakinki akan maganar nan. An gama yanke shawara tun dazu"
Hajjo ta rasa yadda zatayi da su biyun. Kowacce ta kafe har suna neman yin fada "don Allah kuyi hakuri. Bintu kece karama, mu taru kawai mu tayata addua."
Hawayene kamar an kunna famfo yake saukowa daga idanun Asmau. Dama shiyasa Qasim yace ta jira zuwan lahadi? Yanzu shikenan tun ba'aje ko'ina ba an datse mata samun farinciki daga wurin Jikamshi. Duk maganar su Umma kuma gaskiya suke fada. Ita din tana da tabo a rayuwarta. Wannan yasa a komai shawararta zata zamo ta karshe. Iyaye zasuyi ta ganin kamar komai suka yanke shine alkhairi gareta.
A sanyaye ta shiga dakin ta zauna a kasa.
"Umma indai auren Qasim kuke gani shi yafi dacewa dani na amince"
Anti Bintu ta taso ta tayar da ita tsaye.
"Asmau wace irin magana ce wannan. Ishaq kike so kuma na shaida yana matukar sonki. In Allah Ya yarda shine mijinki"
Umma taji tausayin Asmau har ranta amma yadda abin yazo musu ne basu da yadda zasuyi "Bintu na dauka mun gama maganar Ishaq dinnan"
"Yaya Bara'atu bazan bar maganar ba sai naji daga bakin Ishaq ko shi din ya hakura"
Cikin kuka Asmau tace "Anti Bintu ki bar maganar kawai. Allah Yasa hakan shine mafi alkhairi"
Tashi tayi ta fita jikinta duk babu kwari. Gobe in Allah Ya yarda zata kira Jikamshi ta bashi hakuri. Bata san wace irin rayuwa kuma zatayi da Qasim ba. Mutumin da bata taba jin sonsa ko kadan a ranta ba.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽42
Batul Mamman💖
Sallar isha kawai tayi ta kwanta sai kuka. Ganin bazai fishsheta ba yasa ta tashi ta dauro alwala ta soma nafila. Yi take tana kuka tana kara istigfari. Rokon Allah take Ya yafe musu kuskuren da suka aikata wanda har yau yake bibiyar komai na rayuwarsu. Daga nan tayi adduar fatan samun nutsuwa da dukkan wanda Allah Ya kaddara zata aura. Tana sallar Anti Bintu ta shigo da niyyar sake bata baki ta tarar tana sallah. Gefen gado ta samu ta zauna tana jiran ta idar. Tunanin wannan al'amari ne ya rinka damunta. Idan akace *abinda ake gudu*to ba faruwar laifin ake ji ba. Abubuwan da zasu iya biyo bayansa. Asmau ta dade tana ganin tasirin hakan a rayuwarta tun ranar da Abubakar ya rasu. Miji ya rasu ranar daurin aure sannan a sami amarya da ciki. Ai ko a iya nan aka barta ta kafa tarihi a rayuwa wanda duk mutumin da ya santa idan suka hadu sai ya tuna. Ga 'ya ta haifa itama nan gaba tana kara wayo zata iya bukatar jin waye ainihin babanta. Idan kuma marasa tausayi cikin mutane suka goranta mata yanayin haihuwarta ko na sakan daya ne sai ta tsani mahaifiyar da ta sha wahalar rayuwa don ta haifeta. Babu dan da yake son jin shi shege ne. Sannan ga soyayyar wani Allah Ya dora mata amma saboda abinda ya faru a baya idan tace zata bijire ma kallon mara kunya kuma mara godiyar Allah za'ayi mata. Allah Sarki Asmau da matan da suka sami kawunansu a yanayi shigen nata. Tuba da tawakkali shine kawai kwanciyar hankali garesu.
Anti Bintu tana ta tunani har bacci ya kwasheta a zaune Asmau bata idar da sallah ba. Itama sai gabanin asuba ta soma baccin. Ana kiran assalatu ta tashi dama baiyi nisa ba. Ta shi Anti Bintu da 'yan matan da suka shigo dakin kwanciya tun tana sallah. Sai wurin bakwai na safe bacci mai nauyi ya dauketa.
*****
A kitchen Umma ta rabawa kowa aikinsa na taron gobe. Gidan Mama zasuyi meatpie da doughnut. Nan kuma cake zasuyi da pepper chicken sai lemuka da za'a siyo. Har dakin Yassar taje ta bashi kudin abubuwan da zai siyo a fara aikin yace mata da zazzabi ya kwana. Yassar da bashi da kyuyar aike yau kirikiri ya nuna mata bazashi ba. Dama tun jiya ta kula yana wani cin magani ta rasa dalili. Bata san Col. Ishaq yake tayawa kishi ba tun kafin ya fara nasa. Dayake Shemau zata zo sai kawai ta kirata a waya ta fada mata abubuwan da zata taho dasu.
Ta fito tana mitar tasan Yassar kalau yake Anti Bintu tayi dariya.
"Indai Yassar ne ranar daurin auren ma yana iya kirkiro ciwo. Don baki san irin shakuwarsu da Ishaq bane."
"Ke kuma naga alama abin yayi miki dadi. Ni duk a yaushe ya tara masoya a gidan nan ne ban sani ba?"
"duk abinsa ai dole yaji kunyarki. Don baki ga yadda mukayi dashi a Zaria ba. Hatta babansu Dijah sun sha hira sosai. Tamkar 'yan uwansa haka ya dauke mu. Gashi yanzu kun zo kun raba"
Umma ta rike haba tana kallon kanwarta. Da gaske Bintu ta zama 'yar kamfen "kun mayar dani wata boss dai. Gani kuke yi kamar bana son Asmau. Bari ayi auren ku gani idan suka fara zaman lafiya. Yau fa ko gaisheni bata fito tayi ba."
Anti Bintu tace "bacci take yi, jiya kwana tayi tana sallah da kuka"
Hajjo dake tsaye a bakin kofa tana musu dariya tace "ta kwana sallah kika ce, to ni dai babu ruwana Bara'atu da Garzali ne suka yanke shawarar. Allah Yasa dai bata ambaci sunana a adduar ba. Ko dai na tasheta na tambayeta ne. Kunsan addua ba abin wasa bace"
Duk su biyun dariya suka yi. Daga falo suka ji shigowar Zubaida da Sabira. Har kitchen din suka zo aka gaisa suna yiwa Zubaiba fadan dalilin zuwanta tace "Umma jiya banyi bacci ba tunda ya fada min gobe za'a kawo kudin Asmau. Mu dan shiga ciki akwai wani sirri da nake tsammanin bata fada miki ba"
Anti Bintu tace "fadi a nan kawai, ba zancen Ishaq bane"
Zubaida tace "wannan sojan ko. Ashe kun sani, to meyasa za'a hadata da Qasim?"
Hajjo tace "kinga matar auta, jeki ki bawa 'yar uwarki baki kawai. Maganar nan an gamata tun jiya. Allah Ya sanya mana alkhairi"
Jikin Zubaida duk sai yayi sanyi. Mata nawa ta gani a gidan Uwargida wadanda suka ce auren dole ne ya fito dasu daga gidan iyayensu. Allah Yasa Asmau ta iya hakuri dai.
Ko sau daya Asmau bata fito daga daki ba. Abinci ma Dijah ce ta kai mata. Amatullah da bata iya komai idan Umminta bata walwala itama a dakin ta zauna. Har su Shemau suka zo yara sun cika gidan amma taki fita sai nanikar jikin Asmau take yi. Col. Ishaq yayi ta kiranta ta daure ta dauka tace masa baki ne a gidan yau duk ya cika. Har su Anti Bintu sun zo.
"To bazan takuraki ba kije kuyi hira zuwa dare sai muyi magana. Ki gaishe min da Yayata Bintu"
Tana ajiye wayar sai kuka. Yanzu da tasan za'ayi mata katanga dashi tafi jin sonsa ma a zuciyarta. Duk bayan dan lokaci kadan sai tayi mata text mai cike da kalamai masu ratsa zuciya. Shemau tazo tayi ta rarrashinta akan ta hakura ta karbi wanda Allah Ya zaba mata. Gudun kada su dameta yasa ta dan sake tana amsa musu idan an sakota a hira.
Sunyi aikinsu sun gama zuwa yamma. Washegari kawai ake jira mutanen Shanono su iso. A daren ranar Ainau da bata sami zuwa tayasu aiki ba ta kirata harda kukanta. Ta kira Umma tana rokon kada a hana yayarta wanda take so. Umma dai ta rasa yadda zata yi. Duk sun hade mata kai. Jafar ne ma bai nuna ga wanda ransa tafi so da Asmau ba.
Uban gayya ASP Qasim shima sai dare ya kira Asmau. Kana jinsa kasan yana cikin farinciki yace
"Asmau kinga ikon Allah ko. Ina sanar da su Baba maganarmu suka ce kawai azo ayi komai. Ina fatan hakan zai karan kwantar miki da hankali kisan cewa komai ya wuce."
Zuciyarta har wani zafi take yi don bacin rai ta daure tace "babu komai Yaya Qasim, Allah Ya tabbatar mana da alkhairi"
Yaji dadin furucinta "Amin Asmau, goben zanzo nima. Idan sum gama nasu sai mu fara tsara bikin. Sai da safe ko gimbiyata"
Ta kakalo murmushi tayi "to sai da safe" ta ajiye wayar ido na cikowa da kwalla.
*****
Washegari da wuri gidan ya cika kamar masu shirin biki. Yaya Abu da Anti Lami sun zo, Mama da 'ya'yanta mata harda matar Abdulhalim. Sai Aina'u da Shemau da Sabira. Falon aka share aka tura kujerun baya aka shinfida wani kafet din ko da wurin zaman zaiyi kadan. A bangaren maza ma akwai masu zuwa ta bangaren Hajjo da maigidanta sai Kawu Garzali da abokansa biyu. Ga mazansu Anti Lami da na Anti Bintu. Banda kuma gayyar Alh Adamu. So suke su nunawa dangin Qasim suna son 'yarsu kuma ita din 'yar dangi ce.
Tun safe Asmau ta kashe wayarta don bata san me zata cewa Jikamshi ba idan ya kirata. Adduarta kada yazo ana tsakar taron. Yau ma a daki ta zauna sai dai 'yan uwanta su shigo tayata hira.
*****
Ana la'asar mutanen Shanono suka iso gidan Alh Adamu. Daga nan suka dunguma zuwa gidansu Asmau. Mota biyu suka ciko da nasu 'yan uwan. Qasim dama ya rigasu zuwa ya sai zauna a cikin gidan idan taro ya watse zaije ganin Asmau gimbiyarsa.
Kafin su iso Umma tace Asmau ta tafi gidan Jafar tare da wasu cikin 'yan matan tace kanta na ciwo bazata iya fita ba. Umma tayi murmushi kawai ta rabu da ita.
Sauran suka tashi aka jera komai a falon sannan suka koma ciki suna hira a dakin Hajjo saboda yafi fadi.
Asmau na kwance zazzabin dole ya rufeta taji hannuwan Amatullah sun rike mata wuya ta baya. Tun jiya taki sakewa itama. Idan ta korata tayi wasa bata dadewa take dawowa wurin Umminta. Murmushi tayi tana kokarin cire hannunwan don rikon ya danyi karfi
"Ama sake min wuya mana"
Jin tayi shiru yasa ta juyawa sosai. Amatullah ta gani tana kokarin numfashi bakinta a bude.
"Subhanallah" ta fada a rude tana dagata.
"Ama ki rufa min asiri, wayyo Allah"
Gabadaya ta manta da inhaler din da aka basu a asibiti ta dauketa sai dakin Hajjo. Kuka take yi sosai tun kafin ta shiga su Umma suka fara fitowa saboda muryarta da suke ji.
Ganin Amatullah na numfashi da kyar Shemau ta karbeta Sabira kuma ta kira Jafar a waya. Lokacin Umma har ta dauko mukullin tata motar. Yassar baya gidan shi tun safe ya fice.
Sabira na fadawa Jafar ya tashi da sauri. Lokacin an gama gaisawa da dangin Qasim kenan. Abdulhalim ya tambayeshi abinda ya faru ya fada musu.
Kowa sai salati suka tashi don ta nan su Umma zasu wuce.
Kafin kace meye wannan suna mota Asmau ta cire dankwali sai hijabinta kawai tana yiwa Amatullah fifita. A can gidansu kuma Alh Adamu ya gama gigicewa. Yana matukar son jikarsa shiyasa hankalinsa ya tashi. Karshe yace don Allah suyi hakuri zai bisu asibitin. Idan komai ya lafa sai su karasa abinda ya tara su. Duk da wasu basu ji dadi ba to amma lafiya tafi komai. Haka suma aka samu wasu cikinsu suka bi bayansu aka tafi asibiti.
Ainau ce ta kira Yassar ta fada masa. Kafin ya karasa asibitin ya kira Col. Ishaq ya sanar dashi da kuma sunan asibitin. Shima hankalinsa a tashe ya tafi. Dama yayi ta kiran wayar Asmau yau baya samu. Niyarsa bayan magariba yaje gidan.
*****
Emergency suka kaita nan da nan likitoci suka fara aikinsu. Sun tabbatar musu ba abin damuwa bane asthma dinta ce ta tashi amma abin baiyi tsanani ba.
Ana ta rarrashin Asmau ta kasa shiru. Dama can hankalinta ba a kwance yake ba. Suna nan aka canza mata daki lokacin numfashin ta daidaita ta sami bacci. Qasim ya shigo dakin aka gaisa ya duba Amatullah ya fita. Bai dade da fita ba Jafar yace taje waje Qasim na kiranta.
Bata son nunawa mutane rashin son auren shiyasa ta fita ta same shi. Kokarin kwantar mata da hankali yayi tace ta gode. Suna nan tsaye Col. Ishaq ya iso. Tunda idonsa ya gano masa Asmau da Qasim yaji wani bacin rai sai dai jikin Amatullah ne a gabansa. Daya karaso suka gaisa da Qasim. Itama ta gaisheshi sai ya shareta kawai. Tana kallo Yassar ya fito ya kaishi dakin ya duba Amatullah.
Kasa nutsuwa yayi ya fito ya dawo inda suke. Gaban Asmau sai faduwa yake yi. Yana zuwa yace
"Naga dakin a ciki da mutane da yawa. Tun yaushe ta fara ciwon ban sani ba?"
Qasim ne ya bashi amsa "ko awa daya ba'ayi ba. Mutanen ciki 'yan uwana ne dana Asmau. Kayi hakuri naso sanar da kai ma abin ne yazo a kurarren lokaci."
Idon Col. Ishaq akan Asmau yace "wane abu kenan?"
Da dan murmushi Qasim yace "kawo kudi aka zo sai ciwon Amatullah ya tashi"
Guntuwar fara'ar fuskar Col. Ishaq tuni ta bace "kudin aure??? Na wa?"
Kirjin Asmau sai bugu yake da karfi don tsoro. Gashi yq tsareta da ido.
Qasim yace "kin barni ina ta magana ni kadai ko, wallahi daga fadawa iyayena kawai sai suka yanke shawarar gara ayi komai lokaci guda. kudin *aurenmu* aka zo kawowa."
Sabanin bacin ran da tayi tunanin gani a fuskar Jikamshi sai taga yayi dan murmushi
"Kasan mata da kawaici da kunya. Musamman ma dai _Matar Jikamshi_. Asma'una baki fada masa muna soyayya bane?"
Qasim ne yaji kamar an sauke masa guduma a kansa. Sai ya kalli Asmau da tayi mutuwar tsaye sannan ya kalli Col. Ishaq wanda yake binta da kallo mai nuni da tsantsar soyayya kamar ya sanyata a jikinsa.
Daga bayansu Yassar ne yazo kiran Asmau ya fada mata Amatullah ta farka. Jin abinda Col. Ishaq ya fada yasa shi daka tsalle ba shiri.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽43
Batul Mamman💖
Shiru suka yi gaba dayansu sai Col. Ishaq da yake murmushi kamar bai san abinda yayi ba. Shi kuwa Qasim nema yake maganar da yaji ta gama shiga kwakwalwarsa. Ihun tsallen Yassar ne yasa duk suka kallo inda yake. Baiyi wani dogon tunani ba don kada a gano shi ya durkusa kasa tare da rike kafarsa ta hagu
"Wayyo Allah wani abu ne ya cije ni"
Asmau tayi kansa da sauri dama neman hanyar da zata bar wurin take yi don ji take kamar idan ta kara minti daya itama sai dai a bata gado kusa da Amatullah saboda irin bugun da zuciyarta take yi.
"Mu gani a ina ne?"
Ya dago kansa yana kallonta, duk sai ta bashi tausayi. Karyar kafar ma saboda ita yayi
"Barshi kawai bari na cire takalmin. Kije Amatullah ta tashi tana kuka"
Kamar an harba walkiya haka ta bar wurin ko waigowa baya bata yi ba. Qasim da Col Ishaq suka dawo kusa dashi suna tambayarsa abinda ya sami kafar.
"Ji nayi kamar abu ya cije ni. Ku shiga ciki Amatullah ta tashi."
Qasim ya dawo hayyacinsa daga abinda Col. Ishaq ya fada har ya yiwa Yassar sannu harda kokarin cire masa takalmin zai taya shi duba kafar. Yassar yayi saurin jan kafar yana mai jin kunyar karyar da yayi "ya dena ciwon, zan karasa motar Umma ina da silifas a ciki ina jin cinnaka ne ya shiga."
Daga haka ya samu Qasim ya shige. Kafin ya mike tsaye yaji an kama wuyan rigarsa an tayar dashi. Ba don yasan wanda ya rike shi ba sai yayi ihun gaske. Col. Ishaq yayi 'yar dariya yana kallonsa "ka kyauta da ka taimakawa yayarka don sauran kadan ta suma a wurin nan. Har na fara tunanin me zan fadawa su Umma"
Shima Yassar dariyar yayi yana murza wuyansa "haka kawai kun sata a tsakiya. Ga soja ga dan sanda da wanne zata ji"
"Laifinta ne da tasa duk muka kamu da sonta. Allah Yasa kada ta kwaso mana lauya ko alkali kuma."
Murmushi Yassar yayi tare da jin kunyar amsar da aka bashi. Shi dai komai na Col. Ishaq yana burge shi. Ina ma ace shi zai aureta. Ba kuma don baya son Qasim ba sai dai wannan maganar aure ce.
*****
Asmau na shiga dakin Amatullah ta dena kuka. Kan gadon taje ta zauna tana yi mata fadan dalilin kukan don bata ganta ba kamar bata san sauran mutanen wurin ba.
Mama tace "kiyi mata a hankali Asmau. Yarinyar nan taji jiki. Haka muka sha fama da Abubakar da yana yaro. Idan ta kara wayo zata san yadda zatayi ta rinka kiyayewa sai kiga attacks din basa zuwa sosai."
'Yan uwan Qasim suka ce zasu tafi sai dai su dawo wani satin. Alh Adamu yayi ta basu hakuri yace tunda Amatullah taji sauki suna iya komawa a karasa. Hakan ya razana Asmau sosai ta shiga rarraba idanu taji me Jikamshi zai ce. Sai tayi sa'a yayi kamar baya jinsu. Su din ma sun nuna babu damuwa tunda yamma tayi zasu sake saka rana.
Ita dai Asmau ko kallon Qasim din ta kasa. To da wane idon zata kalle shi bayan abinda Jikamshi ya fada masa. Shi a rayuwarsa ta kula baya jin shakkar fadin magana ko a gaban waye indai yana tunanin akan gaskiyarsa ne. Gashi yau ya fadi maganar da tasan dole Qasim ya kullaceta a ransa.
Shima a nasa bangaren gani yayi gara ya kyaleta saboda asibiti ba muhallin maganar bane. Sannan ga Amatullah babu lafiya yanzu ko me zata fada masa zai zamto babu nutsuwa a tare da ita. Tare da su Alh Adamu suka fita raka 'yan uwansa zasu biya gidan Umma su dauko sauran. Kayan ciye ciye da aka tanadar musu Umma tasa Sabira da Shemau su bi bayansu sai su hada a basu su tafi dashi.
*****
Suna zaune har akayi magariba sannan su Umma suka tafi aka bar Hajjo da Asmau. Kayan kwana za'a hadu musu sai Mama ta dawo su kwana tare. Col. Ishaq yana dakin amma shima yaki kallon inda Asmau take, shima bata da abin fada masa. Ba don ciwon Amatullah ba da yanzu an gama magana tsakaninta da Qasim sai batun saka rana. Biyewa Amatullah yayi tana ta shagwaba son ranta, sai Hajjo dake dan yi masa hira itan ma kunyarsa take ji tunda tasan komai. Duk yadda Asmau taso su hada ido yaki. So take ta bashi hakuri tunda tasan yanzu bata da sauran mafita. Karshenta kafin sati ya zagayo ma mutanen Shanono su sake dawowa.
Shigowar Jafar da Qasim yasa shi tashi yayi musu sallama ya fita.
Damarta kenan ta bashi hakuri a yau tunda wayarta tana gida. Bai dade da fita ba tace zata je tambayar likita ko zata iya bawa Amatullah abinci. Jafar yace ta bari yaje ta wayance "barshi Yaya Jafar so nake na dan fita na gaji da zaman wuri daya"
Shi kuwa Qasim tuni ya gane inda take son zuwa sai kawai ya dauke kansa. Yana kallo ta fita cikin sauri don kada ya bar asibitin kafin ta karasa wajen.
Tana fitowa ko alamunsa babu ta kara sauri harda dan gudunta. Tsoronta bai wuce kila daga yau yaki dawowa ba. Garin sauri tabi wata hanyar da zata kaita wurin ajiye motoci ta kusa karo da mutum har sai da taji tsoro saboda rashin wadatar haske a wurin. Tsaye yake ya sanya hannuwansa a aljihun wando yana kallonta. Kallo ne na tuhuma wanda har ranta sai da taji babu dadi don bata kyauta masa ba. Bai motsa daga inda yake ba yace "me yasa kika wahalar da kanki da yin gudu bayan kinsan dole zan jira fitowarki. You have alot of explaining to do"
Fuskarsa yau babu fara'ar nan da take kara saka mata sonsa. Yau a sojansa ya fito sai ta daburce ta rasa ta ina zata fara bayani.
"Kinyi shiru, na tafi ne?"
"A'a don Allah kayi hakuri" sai ta soma kuka.
"Matar Jikamshi" sai yanzu ta danji sanyi a ranta saboda yadda ya kirata. A hankali ta dago ido ta kalle shi.
"Why?" Ya tambaya shima duk dakewarsa yana jin babu dadi. Idan ya rasa Asmau gani yake bazai taba samun madadinta ba. Yana mamakin irin wannan so da yake mata wanda ya shige shi lokaci daya.
Idanunta cike da hawaye ta soma fada masa yadda abin ya faru." Kayi hakuri da ban sanar da kai ba. Babu yadda zanyi ne tunda duk iyaye sun amince"
Ya gyara tsayuwarsa yana fuskantar ta "ki dena kukan nan kinji ko. Idan nace miki everything is ok nayi karya because it is not. Kinji kunyar sanar da Qasim da wuri kinga abinda hakan ya janyo. Magana kuma tunda ta hada da iyaye zan hakura kamar yadda kike so. Dazu ma naga ya kamata ya sani ne shiyasa na fada masa."
Wani kukan ne yazo mata sai zubar da hawaye take. Tana sonsa fiye da yadda take tsammani a baya.
"Jikamshi to yaya zanyi?"
Tausayi ta bashi. Asmau ta fuskanci abubuwa da dama a cikin 'yan shekaru.
"Da ace babu ni a cikin manemanki sai na baki shawara. Amma tunda ina ciki bana so a zargeni da son kai. Shawara tana gareki Asma'una. Idan Allah Yayi Qasim ne mijinki alfarma daya nake nema kada ku rabani da Safina. Atleast ko school fees dinta ku bari ya zama responsibility dina."
Meyasa Qasim bai sanar da ita iyayensa zasu zo da wuri ba. Ji tayi gabadaya auren ya fice mata a rai. Kuka kawai take yi mai ciwo. Muryarta a shake tace "To yanzu shikenan?"
Murmushi yayi mata, sai da taji shi har ranta. "Shikenan Matar Jikamshi. Maybe daga yau bazan kara kiranki da wannan sunan ba. Ki rike duk abinda Allah Ya kaddara miki da hannu biyu. Qasim mutumin kirki ne a yadda na fahimce shi. Ban taba ganin mutum mai kokarin rike amana kamarsa ba"
"Na sani wallahi, shiyasa na kasa fada masa gaskiyar abinda ke zuciyata. Ina gudun bata masa rai saboda nasan duk abinda yake yi don ya kyautata mana ne."
"Kada kiyi ja in ja da iyaye akansa. Idan shine alkhairin rayuwarki bamu da zabi da ya wuce karbar kaddara."
Juya mata baya yayi zai tafi. Yana jin sautin kukanta ya karu. Yasan yana sonta ba da wasa ba, amma duk abinda aka ce iyaye sun shiga ciki a matsayinsa na babba bai kamata ya nuna mata bijerewa alkhairi bane. Duk da kuwa yana ji a ransa kamar gobe ya turo nasa iyayen. Asmau ta wuce a kirata wani bangare na jikinsa. Shine ita, itace shi. Da haka kawai zai iya kwatanta kaunar da yake mata.
A sanyaye yaji muryarta yadda bata zaton zai ji tace "Jikamshi ina sonka" a hankali
Wannan kalmar ta tsaya masa sosai a zuciya har ya fasa tafiya. Sake juyowa yayi ya ganta durkushe tana kuka. Shima durkusawa yayi a gabanta suna fuskantar juna "Matar Jikamshi kina so na hakura dake"?
Girgiza kai tayi tana fitar da hawaye mai dumi.
"To bazan hakura ba. Jikamshi yana son matarsa. Ki tashi ki koma ciki. Gobe in sha Allah zanyi magana ta fahimta da Hajjo tunda ita ce babba. Zan fada mata bazaki iya rayuwa da kowa ba sai Ishaq. Nima da ke kadai nake son karashe rayuwata. Duk shawarar da ta bayar da ita zanyi amfani."
Tana hawayen amma murmushi take yi tana kallonsa. Yayi dariya "to dena kallona haka kada ki cinyeni kafin a daura auren"
Ta sunkuyar da kanta kasa cikin kunya. "Ba fa kallonka nake yi ba."
"Kallo na nawa kuma, a ciki ma ko kunyar Hajjo baki ji ba kika rinka satar kallona. Anya yarinyar nan baki fi karfina ba. Da ina yi miki kallon saliha amma yanzu ajinki daban ne"
Murmushi kawai tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannuwanta tace "zama da kai ne"
"Indai nine baki ga komai ba. Kinga koma kada a fara cigiyarki. An saba maza ke zuwa zance amma yau kin kasa hakuri kin biyo ni. "
Sai da ya rakata har kusa da dakin sannan ya dawo. A daidai inda suka gama magana yaga kamar alamar mutum. Ya dan juya yaji shiru sai kawai ya tafi.
Qasim ne a wurin kuma duk yaji maganganunsu. Tun bayan fitowar Asmau ya biyo bayanta a zatonsa Col. Ishaq ya riga ya tafi. Rasa inda zaisa kansa yayi saboda a yau ya tabbatar ko kadan bata yi masa soyayya irin wadda yake fata. Duk wani tunaninsa ya kulle a yanzu shiyasa kawai ya shiga motarsa ya bar asibitin.
0 comments:
Post a Comment