A daren nan Qasim ya wuce Shanono. Abin duniya duk ya ishe shi. Dama wani lokacin baka sanin kana son abu sosai sai kaga alamun zaka rasa shi. Da gaske yake jin kaunar Asmau a ransa. Tunani yake har me ta gani a tattare da Col. Ishaq take sonsa haka. Yasan mutumin dai ya hadu amma ko babu komai shi Qasim ya fishi kuruciya. Duk da bai san komai game da Col. Ishaq ba amma yana da tabbacin da wuya idan bashi da mata daya ko sama da haka. Shi da yake da burin bata dukkan kulawa ta yadda babu wata mace mai suna kishiya da zata takura mata shine zata kai kanta cikin mutanen da basu dade da sanin juna ba. Yanzu idan ta aure shi danginsa suka wulakanta ta fa? Hawaye yaji yana neman zubo masa. Duk laifinsa ne da ya zama mugun aboki ga Abubakar. Ba don shawarar da ya bashi ba ai da haka bata faru ba. Ko Abubakar ya rasu ya tabbatar duk inda tayi aure zata tsira da mutunci da martabarta. Sai kuma tausayinsu da yaji. Asmau tayi masa halacci da har bata kalli tsabar idonsa ta nuna masa bata son shi ba. Yayi dan murmushi, dole yasan yadda zaiyi ya janyo ra'ayinta gareshi tare da nuna mata illolin da auren wanda basu gama sani ba zai iya jawo mata. Idan kuma hakan bai samu ba......kasa karasa tunanin yayi.
*****
Col. Ishaq yana zuwa gida ya kira Asmau. Jin wayar a kashe yayi dan murmushi. Ya fuskanci tana cikin matan da basa bawa waya mahimmanci. Yau ta kashe gobe tace wayar tana daki ne. Sai da yayi wanka yaci abinci sannan ya tafi dakin Hajiya.
A zaune ya sameta a kasa Bilkisu tana matsa mata kafafu. Ya zauna a gefenta ta dan janye jiki ita a dole ga dan fari. Dariya Bilkisu tayi ya rankwasheta a ka don yasan tsokanar Hajiya take yi, sannan ya fuskanci Hajiyar.
"ciwon kafar ne ya tashi,akwai maganin ko ya kare?
"Na sha ma bayan naci abinci dazu. Yau ina ka tsaya daga cewa zaka ganin abokinka"
"Asthma din Safina ce ta tashi suna asibiti an kwantar dasu."
Cikin tausayawa Haj Lubabatu tace "Allah sarki, ciwon yaro babu dadi bare ciwo irin wannan. Da ka fada mana tun dazu ai sai Sabo ya kawo mu kafin ya tafi gida. Ya kamata su hada mata da maganin gargajiya, zan tambayi Kawunku suna masana a bangaren. Kasan ciwon yana bukatar kulawa"
Yaji dadin yadda mahaifiyarsa ke nuna damuwarta akan abinda yake so duk da bata son fada. Bilkisu yasa ta tashi hado masa abinci ya samu ya sanar da Hajiyan duk abinda ya faru a yau bayan zuwansa asibiti. Haj Lubabatu ta kalle shi cikin damuwa
"Yanzu kai bazaka hakura da ita ba tunda iyayenta sun fi son wancan yaron?"
"Hajiya itama bata son sa. Kuma don ban gabatar da nawa magabanta bane da wuri. Kin sanar da su Kawun kuwa?"
Ta girgiza kai tana mamakin wannan soyayya da danta yake yiwa Asmau.
"Na fada musu don Yaya Auwalu ma yace zai kiraka kuyi maganar. Ni dai bana so azo a sami matsala daga iyayenta gara kawai tunda har an fara batun kawo kudi ka janye."
Dan murmushi kawai yayi "Hajiya idan kina kyamar aurena da Asmau ki fada min. Nasan hakan zai iya zuwa ranki saboda irin yanayin data tsinci kanta a baya. Kin sani duk yadda nake son abu bazanyi batare da izini da neman albarka daga gareki ba"
Akwai shi da iya tsara zance da ladabi shiyasa take sonsa.
"Ko kadan bana kyamar aurenku. Kuma ni wacece da zanki karbar kaddara. Ka sani babu wata uwa a duniyar nan musulma da zata ji farat daya hankalinta ya kwanta idan danta ya nemi auren macen da ta taba haihuwa a wajen aure. To amma kowa da abinda Allah Ya tsara masa. Yarinyar nan kana ganinta kasan ta fito daga gidan tarbiya sai gashi tsautsayi ya fada mata ta tsinci kanta a irin wannan yanayin. Bazan ki ta ba don da Allah Yaso da daya daga cikin nawa 'ya'yan za'a buga misali. Idan Asmau matarka ce fatana Allah Ya baku zaman lafiya da hakuri da juna"
A take fargabarsa na kin amincewarta ta gushe daga zuciyarsa. "Nagode Hajiya Allah Ya kara lafiya. In sha Allah zan nemi Kawu Auwalun idan ya bukaci naje Jikamshin sai naje. Ina so su zo da wuri ne."
Yanaa tashi Bilkisu ta shigo da abincin ta ajiye a gabansa tana murmushi "Uncle albishirinka"
"Goro maigadon zinare"
Ta danyi tsalle kamar karamar yarinya "gobe Mami zata zo"
Dena zuba lemon da yake yi yayi yace "da gaske" fuskarsa na nuna farincikinsa.
Hajiya tace "to sarkin surutu. Ke da tace kada ki fada masa sai da ya ganta kika fasa kwan saboda kina murna mamanki zata zo ko?"
Bilkisu ta turo baki "kai Hajiya nifa ba haka nake nufi ba"
Col. Ishaq yace "Hajiyar tawa kike turawa baki. To na mayar da goron albishir din banji abinda kika fada ba"
Tashi tayi ta bar dakin tana buga kafa yana mata dariya. Ya juya ga Hajiya cikin murna "gara tazo taga yayarta kuma kanwarta"
Mami ita ce 'yar Haj Lubabatu ta biyu. Shekara daya da rabi Col. Ishaq ya bata. Ba karamin shakuwa suka yi ba kamar ba sako da sako ba. Komai nasu tare suke yi. Hatta zancen Asmau ya fada mata ya sami wadda yake so amma sai tazo Kano ko shi yaje Jos din zasuyi maganar sosai. Ita kanta murna da doki ya isheta saboda ta matsu yayi aure. Tun bayan rabuwarsu da Badariyya bata kara jin yayi zancen mace ba sai yanzu.
******
Washegari litinin su Asmau sun kwana a asibiti. Da sassafe Umar yazo ya kai Mama gida ta yi wanka sai ya taho da Ainau ta taya Asmau zama. Ko goma bata yi ba suka ji sallamar Col. Ishaq. Asmau na jin muryarsa taji wani irin dadi a ranta. Soyayyarta da Jikamshi kullum jinta take sabuwa. Cikin khakinsa yake na sojoji yayi kyau ta bishi da ido a lokacin da yake shafa kan Amatullah dake kwance tana bacci. Ya amsa gaisuwar Ainau sannan ya juya yana kallon Asmau. Saurin sunkuyar da kai tayi tana jin kunyara tan cigaba da yiwa Husna dake hannunwa wasa. Bai dauke idonsa daga kanta ba yace
"Ainau dake ake shirin kai Matar Jikamshi gidan wani?"
Ainau ta zaro ido "wallahi babban yaya nima har kuka na tayaka. Ba don kada kuga wautata ba sai nace asthmar Amatullah tayi min daidai."
Wani wawan dundu Asmau ta kai mata harda harara. Ainau tace "ba fa har raina naso ciwon ba." Ta dan juya " kaga tana hararata ko"
Col. Ishaq ya karbi Husna daga hannun Asmau yana dariya "nima harararki nayi a zuciya. Ya zaki ce asthma tayi. Duk da dai na dauketa a matsayin tazo hanawa a raba Jikamshi da matarsa"
Irin kallon da yake yiwa Asmau yana wani lumshe ido yasa Ainau jin kunyar kasancewa a wurin. Sai murmushi suke yiwa juna. A ranta tace ba dole Yaya Asmau taso shi ba. Shi kuwa Yaya Qasim bata ga alamar ya iya nunawa mace soyayya ba. "Allah Ya baku hakuri to. zan fadawa Baba Amatullah ta warke ko gobe Yaya Qasim ya kawo kudi"
"Kinga kina jego shiyasa nake tausayinki. Idan aka aura mata wani ranar zaki kwana a guardroom don nasan adduarki ce taci" Col Ishaq ya fada suka yi dariya sannan ya yiwa Asmau alama da ta biyo shi.
Sai da suka je bakin motarsa yace "Matar Jikamshi kin tashi lafiya, ya jikin princess dina?"
Tana kallon kasa saboda kunyar tunowa da yadda jiya ta nuna masa tana sonsa tace "lafiya kalau Alhamdulillah"
"Yau 'yan kunyar sun zo ne zasu hana ace min I love you" ya karashe maganar yana kwaikwayonta.
Bata san lokacin da ta soma dariya ba yace "jiya duk bana cikin hayyacina ne sosai nima bance miki Matar Jikamshi ina sonki ba. Amma yanzu na fada. Zan wuce office sai an taso zan dawo ko kuma bayan magrib. Ki kular min da matata da 'yata"
"Allah Ya tsare Ya bada sa'a kuma Ya kareka daga dukkan sharri"
Kasa bude motar yayi ya kalleta "Matar Jikamshi"
"Naam Jikamshi _na_"
Yana murmushin jin dadi yace "komai naki ina sonsa, ki rinka yi min adduar nan kullum don Allah. Kuma idan zamu rabu ki kada ki rinka kirana Jikamshina. Sawa kike naji kamar kada na tafi"
Tayi dariya ta sake cewa "Jikamshina"
Ya dan marairaice mata "don Allah ki bari"
Ta sake bude baki zata maimaita tana dariya yace "kina fada zan wuce wurin Umma na fada mata irin kalaman da kike yi min wanda yasa nake so a daura mana aure a yau dinnan"
Ba shiri ta rufe bakinta. Ko dai bai fadi hakan ba tasan zai iya kwatantawa. Dan gefe ta matsa ya shiga motar ya dago mata hannu sannan yaja ya tafi.
Ciki ta koma Ainau tana yi mata tsiyar yadda duk su biyun yanzu basa iya boye sirrin zukatansu a gaban juna. Sai shabiyu su Umma suka zo ita da Hajjo da Mama. A nan suka yini don likita yace sallama sai gobe idan numfashin Amatullah ya daidaita yadda ake so"
*****
Daga wurin aiki gida Col. Ishaq ya wuce. Bazai iya zuwa wurin Asmau ba sai yayi wanka ya canza kaya. Idan Mami ta iso kuma su je da ita dasu Hajiya.
Tun a waje yaga motoci a cikin gidan na kannensa da wata da yake tunanin a cikinta aka kawo Mami. Hakan ya bashi tabbacin yau duk sun zo a tare. Mara motar dama daya ce mai bin auta. Dadi yaji saboda yawanci suna zuwa ne kafin ya taso aiki basu fiye haduwa ba. Ya shiga falon yaji shiru sai daga dakin Hajiya yaji ana magana ana daga murya. Karasawa yayi kofar dakin ya tsaya yana karewa 'yan uwansa kallo.
Mami ke binsa sai Ismail, Dahiru, Safiyya da auta Musaddiq.
Mami ce take magana cikin matsanancin bacin rai harda hawaye a idonta "wallahi tallahi Hajiya bazamu yarda Yaya ya bata mana suna ba."
Ismail yace "meye na rantsuwa Mami, kema kinsan babu mai zuwa cikin su Kawu nema masa aurenta. Idan basu san karuwa bace yarinyar ni...."
Tsawa mai karfi Col. Ishaq ya daka masa. Duk sai da suka razana don sun san halinsa sarai. Kirjinsa ke bugu da sauri da sauri saboda bacin rai "ko da wasa kada ka kara kuskuren kiranta da wannan sunan"
Safiyya tace "ayi hakuri Yaya, Sayyada zamu kirata ko ustaziyya?"
Dariya suka yi dukkansu banda Hajiya ta sha kunu "ban taraku a nan don ku zagi Asmau ba. Yarinyar nan kaddara ce ta fada mata wadda babu wanda ta wuce ta a cikinku. Kuma ni ba amincewarku na nema ba. Na dai fada muku tana da 'ya ne saboda bana son kananan zance nan gaba"
Musaddiq yace "haba Hajiya wannan ai ba zancen da ya kamata Yaya zo dashi bane ki karba. 'Yar shege da uwarta bazasu sami karbuwa ba a danginmu."
Col. Ishaq yayi kansa ya cakumi wuyansa yana huci. Musaddiq sai kakari yake yi don wahala. Hajiya tana ta cewa ya sake shi amma yaki. Cikin zafin rai yace "Musaddiq kada ka kaini bango. Dukkanku nan babu zaman wanda nake yi. Idan na aureta don Allah kada wanda yazo gidana."
"Dama waye zai zo" Safiyya ta fada cikin tsiwa. Ya juyo kama ya mareta.
Daga nan suka tararwa yayansu ana ta musayar magana. Hajiya taji babu dadi saboda yaranta akwai hadin kai. Yau daya sai fadawa juna magana suke yi akan Asmau. Ita da tayi laifi shekarun baya amma a yau sanadiyar wannan kuskuren 'yan uwa duka magidanta suna fada.
Col. Ishaq yace "an fada muku duk matar da ta haihu ko tayi ciki a waje karuwa ce jikinta ta sayar.?"
"Yaya ka fada mana gaskiya fyade aka mata ko me? Ni wallahi gara ka auri gurguwa da wannan yarinyar. Kila ma asiri tayi maka duk ka kasa fahimtar mu " cewar Mami
Yau duka 'yan uwan nasa haushinsu yake ji "ba fyade aka yi mata ba Mami. Idan su basu fahimce ni ba yakamata ace kin gane inda na dosa."
"Tausayinta kake ji?" Dahiru ya tambaya
"ina jin tausayin Asmau saboda irin wannan abubuwan naku ma tun farko taki amincewa da aure. Amma ba don tausayi zan aureta ba. Sonta nake yi so you all should better learn to live with that."
"Wai Yaya da kake maganar nan hala ka manta cewa baka *haihuwa* ?"
Ismail ne yayi maganar wadda tasa kowa yayi shiru. Hatta Col. Ishaq jikinsa yayi matukar sanyi. Hajiya ta taso rai a bace "Ismail wace irin magana ce wannan? Dan uwan naka kake fadawa magana haka" ta daga hannu zata mare shi
Col. Ishaq ya rike hannun idanunsa sun kada sunyi jawur. A sanyaye yake magana "Hajiya gaskiya ya fada. Lokaci daya na manta ina da lalura har nake tunanin yin aure."
Ya kalli kannensa daya bayan daya "in sha Allah daga yau na bar zancen auren Asmau. Ismail nagode da ka tuna min da waye Ishaq, ni mutum ne da Allah Ya tsarawa yin rayuwa ba tare da naga nawa dan ba. Alhamdulillah tunda duk kuna da yara bazan ce na rasa gabadaya ba. Allah Yayi musu albarka. Bari na shiga nayi wanka zafi nake ji"
Hankali a tashe Ismail yace "Yaya"
"Kada ka damu kasan gaskiya daci gareta. Na da dan lokaci idan tayi aure zan manta da ita in sha Allah. Fatana Allah Ya tabbatar da aurenta da Qasim ko wanda ya fishi alkhairi gareta."
Yana fita yaci karo da Bilkisu. Hawaye take yi sosai ga tray din abinci a hannunta. Tana jin shigowarsa taje ta hada masa abinci don tasan tunda su Mami suka zo bazai fito da wuri ba. Duk zantunkansu taji komai. Ganinsa baisa ta tsorata ta bar wurin ba. Shima baiyi mata magana ba ya wuce abinsa.
Tana nan tsaye taji Hajiya tace "kun bani kunya da mamaki. Ban taba zaton zaku iya juyawa dan uwanku baya ba. Ina cewa Asmau tana da 'ya kuka hau surutu babu wanda ya tambayi garin yaya tayi cikin kafin aure."
Cikin nutsuwa ta basu labarin Asmau kamar yadda taji kuma ta gani. Safiyya uwar tsiwa sai ta fara kuka
"Mun shiga uku. Hajiya kuji wata muguwar kaddara. Allah Sarki"
Mami kuwa cewa tayi "duk da haka Hajiya ai bamu tabbatar da cewa a garuruwan da ta zauna bata taba karuwanci ba. Nima ta bani tausayi amma a bar maganar auren tunda ya fasa shima. Kinsan shi baya magana biyu"
Suna ta magana akan halin da Asmau ta tsinci kanta wanda ya girgiza tunaninsu ya kuma basu tausayi. Ace har rubutun cikin waya ya isa ya sa mutum aikata zina. Abin da ban tsoro da firgici saboda babu wanda ya isa ya tserewa kaddara sai dai komai akwai sila. Hajiya Lubabatu tace tunda zata je dubo Amatullah tana so dukkansu suyi mata rakiya.
Kukan Bilkisu suka ji Hajiya ta tashi da kanta sai dai kafin ta fito Bilkisu ta koma dakinta tana kuka. Bata taba sanin wannan labarin ba. A iya tunaninta baban Amatullah ya rasu ne ko ya saki Asmau. Tsoro ne ya kamata saboda akwai wani saurayinta da suke chatting a facebook. A hankali ya fara sako mata zantukan banza tun bata amsawa har ta dan fara sakewa yanzu. Wai har ya iya tambayarta ta kwatanta masa kayan baccinta da daddare. Tayi saurin dafe kirji, yanzu idan da abin yayi nisa kila itama ta shiga sahun masu bawa samari jiki. Kuka take sosai tana tausayawa Asmau kuma har ranta tana fatan Uncle Ishaq ya aureta ko don ya rufawa rayuwarta asiri. Sabon saurayin da suke dan satar kallon juna dashi ta kira a waya tana sheshshekar kuka. Numbar ma a wayar Uncle ta dauka batare da saninsa ba. Da sallamarsa ya dauka cikin muryar da ta dashe da kuka tace "Yassar ne?"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽45
Batul Mamman💖
Mamaki ne ya kama Yassar, kamar ya san muryar amma bashi da tabbas.
"Da wa nake magana don Allah?"
"Bilkisu ce"
Tsorata yayi, shima yana neman numbarta amma yanzu da ta kirashi da alamun kuka sai yaji hankalinsa ya tashi.
"Bilkisu me ya faru?"
To me kuma zata ce masa? Tausayin kawunta take yi amma tana tsoron yi masa shishshigi. Uncle Ishaq yana da dadin sha'ani amma babu mai son ganin bacin ransa. Fasa maganar tayi na son ta roke shi ya lallaba yayarsa kada ta ki Uncle dinta tace "babu komai, anjima zamu zo duba Amatullah" tayi masa sallama ta ajiye wayar.
A ransa yasan don zasu zo ba shine dalilin kiran ba. Tashi yayi ya shirya ya tafi asibitin. Zai jira su zo ya sami damar tambayarta. Ko dai ta lura da yawan kallonta da yake yi ne? Yayi murmushi, tun zuwansa gidansu na farko ranar da kare ya biyo Asmau ya fara jin wani abu game da Bilkisu. Sai dai duk hayaniya ta Yassar bai taba yin budurwa ba. Ta nan bangaren tsoro ne dashi kamar farar kura.
*****
Col. Ishaq na shiga dakinsa ya fada kan gado ko takalmi bai tsaya cirewa ba. Kansa ne yake wani irin ciwo kamar ana buga masa kusa. Ga zuciyarsa ta gama tafasa da bacin rai. Wai yau shine kannensa har da Mussadiq dan karamin cikinsu suke fada masa magana son ransu. A gidansu akwai tsari na girmama na gaba sosai. Sun tashi da so da kaunar juna. Lalurar kowa tare suka haduwa suyi maganinta. 'Ya'yan Ismail biyar duka maza karamin ma bai shekara ba. Amma saboda yadda suke bashi girma duk shi yake sakawa yaran suna. Haka yaran Dahiru guda uku. Gidansu gwanin sha'awa baka ce babansu ya dade da rasuwa ba. Amma yau akan auren Asmau duk sun ture wani girmamawa da shakuwa kowa ya fadi son ransa. Da akanta kadai suka tsaya ya tabbatar da har yanzu yana dakin suna cacar baki. Sai gashi saboda irin rayuwar Asmau ta baya har gori Ismail yayi masa. Gori da abinda yafi so a rayuwarsa, haihuwa. Shi da kullum yake kwantarwa da yayansa hankali. Kafin rabuwarsa da Badariyya ma yaransa biyu manyan a wurinsa suke. Dumi yaji a idonsa yayi saurin mayar da hawayen dake neman zubo masa. Duniya ta Allah ce kuma ba wurin tabbatar bayi ba. Da ace babu lahira sai yace rayuwar Asmau ta wuce abinda ake gudu domin komai daren dadewa sai an ambaceta ko 'yarta a matsayin mazinaciya ko 'yar zina. Ya tabbatar ko shugabar malaman duniya Asmau ta zama sai kaji mutane suna cewa
"Wance kamar ba ita ce tayi cikin shege ba"
"Ji yadda take nuna mana ita ta Allah ce kamar bamu san tarihinta ba"
Amatullah kuwa ita ma bazata tsira ba. Komai kyawun rayuwarta sai an ce "kaga wance kamar ba shegiya mara uba ba" "wance fa da kuke gani babu aure aka haifeta"
Irin haka da maganganun da suka fisu zafi mutane zasu fada a kansu. Babu ruwan kowa da yaya tsakaninta yake da Allah. Shin ta tuba ko kuwa. Zina ta zama mugun tabo mara gogewa.
Tashi yayi ya zauna tare da daga hannuwansa sama. Hawayen da baya son yi ne suka zubo masa
"Ya Allah Ka karbi tuban baiwarKa Asmau da sauran al'umma da suke cikin hali irin nata. Allah Ka basu rayuwa mai albarka su ji dadin tuban da sukayi bisa laifukansu, Ya Allah Ka bata miji nagari wanda zai zame mata alkhairi kuma mai wanke mata bacin rai da bazata taba dena fuskanta ba a dalilin kuskurenta na baya. Ya Allah Ka karemu da sauran musulmi daga fadawa alfasha kowace iri ce. Amin"
Sai yanzu yaji saukin kuncin zuciyarsa ya tashi zaiyi wanka kafin a kira magariba. Abu daya ne a ransa yanzu, shine hakuri da Asmau da zaiyi. Ba karamin so yake mata ba amma dole ya barta ta auri wanda zata iya haihuwa dashi. Zafin soyayya ya rufe masa ido har ya manta yana da nakasa a rayuwarsa. Tunda baya haihuwa bazai cutar da kuruciyarta ba ta zauna da 'ya daya.
Wanka ya shiga ya fito ya sanya riga da wando na yadi mara nauyi. Ya saka hula kalar adon rigar ya sha turare sai gashi ya fito a Jikamshinsa. Idan ka ganshi bazaka ce yana da damuwa ba saboda tunda yayi adduar nan babu abinda yake sai tasbihi ga Allah. Wannan ne ya saukaka masa damuwarsa yaji kwarin gwiwar niyarsa ta rabuwa da Asmau idan suka koma gida. Kafin ya fito text dinta ya shigo wayarsa. Yaa budewa yaga ta rubuta _missing Jikamshina_. Wani sabon sonta yaji ya ratsa shi. Kasa yi mata reply yayi ya tura wayar a aljihu.
Yana fitowa ya tarar da kannensa jugum a falo domin kuwa Hajiya tana gama basu labarin Asmau tace su fice mata daga daki. Da ya fito duk da ransa babu dadi haka ya basar ya dubi mazan
"Kuzo mu wuce masallaci"
Suka tashi jiki a sanyaye. Mami tace "Yaya don girman Allah kayi hakuri da abinda Ismail ya fada. Wallahi duj don bama so ka auro wadda zata gurbata mana dangi ne"
Suma sauran suka soma bashi hakuri. Ismail kuwa ko kallon yayansa ya kasa yi. Murmushi yayi wanda dukkansu sun san irinsa yake idan ransa ya baci
"Magana ta wuce, bazan auri Asmau ba kamar yadda kuke so. *Amma ba don kun nuna rashin amincewarku bane, don baku isa ba*. Saboda kaddara ta fada mata ba zan ce sai na aureta ba duk da ni din bana haihuwa ko Ismail?"
Ismail ji yayi kamar yayi kuka. Idanunsa tuni sun canja launi. Yayansu yana da kirki matuka, bai san yaya akayi shaidan yaja shi yayi wannan katubarar ba.
"Yaya ka yafe min, wallahi Hajiya yau har zagina tayi bayan fitarka. Yanzu ma cewa tayi zamu rakata asibiti duba yarinyar Asma'un daga nan kowa ya fice mata daga gida. Hatta Mami Hajiya tayi rantsuwa bazata kwana a gidan nan ba."
Col. Ishaq ya kara murmusawa "to ai babu damuwa Mami ga kannenki nan sai kibi daya daga cikinsu ki kwana a gidansa"
Mami ta saki baki don batayi tunanin haka zai ce ba. Tayi zaton zaije ya bawa Hajiya hakuri. Duk sun san bacin ranta yafi karfi akan gorin haihuwar da aka yi masa ne.
"saboda Allah ya zaayi naje gidan kannena na kwana da girmana"
"To bari mu dawo daga masallaci sai na baki key din gidana. Babu datti sosai saboda karshen sati maigadi yana min shara. Sai ki tafi da taki 'yar Bilkisu ta tayaki kwana" yana gama magana yayi gaba kamar bashi ya fada ba. Sun san sun tabo soja yau sai yadda ta yiwu kuma. Bayan fitarsu masallaci Mami da Safiyya suka zauna suna ta magana akan lamarin auren Asmau da kuma karin laifin da Ismail ya janyo musu.
Bilkisu dai shiryawa tayi a daki ta fito ta zauna jiran zuwa asibiti don tasan dole aje da ita tunda mai aikinsu bata nan.
Tare suka dawo daga masallacin su Dahiru suna ta bashi hakuri ya nuna musu komai ya wuce. Wurin Hajiya ya je ta shirya ita ma tace motarsa zata shiga su tafi.
Suka fito falo Bilkisu tabi bayansu suma sauran suka fito. Bilkisu na gaban motarsa Hajiya a baya Safiyya tazo ta kama daya kofar zata bude ya juyo ya watsa mata harara ba shiri ta saki kofar.
"Ki koma kibi motar 'yan uwanki masu haihuwa. Ni Hajiya zan dauka da 'yata."
Tayi saroro tana kallonsa. Dahiru da yaji ya dan matso wurin motar "Yaya don Allah kayi hakuri ka manta da zancen nan. Kuma ka yarda ta biku ko Mami ta shigo. Kaga sai ayi saving din mai mu tafi da mota biyu"
Col. Ishaq ya wani kankance ido ya kalli Bilkisu "toshe kunnenki kinji mai gadon zinare" ta kuwa tura yatsu a kunne tare da sunkuyar da kanta.
Hajiya tasan karshenta wata maganar mara dadi zai yabawa kaninsa tace "a gaban 'yarku zaku nuna min hali ko, kai kuma Dahiru kusan yadda zakuyi ku taho"
Col. Ishaq ya mayar da kansa ciki albarkacin Hajiya suka ci. Dole mota biyu suka yi don daya zata matsesu saboda Dahiru da Safiyya duk akwai jiki.
Yana soma tuki Hajiya tace "kai"
"Naam"
"Kayi hakuri da abinda suka yi maka don Allah kada kuyi min gaba. Aure kuma da kaina zan sami kakar Asmau muyi magana in sha Allahu. Tun farko na fada maka dole zaka fuskanci kalubale ta ko'ina saboda wannan abu fa ba wanda ake iya saurin kawar da kai bane a kansa. Ni dai ina sonta kuma na baka goyon baya ka nemi aurenta. Allah mai yawan gafara ne da jinkai. Idan bama iya kawar da kai ga kuskuren mutane to bamu san da wane laifi mu kuma Allah zai kamamu ba"
Allah Sarki Hajuyarsa akwai zurfin tunani.
"Hajiya nagode sosai amma ki bar maganar auren. Asmau bata cancanci ta kare rayuwarta bata haihuwa ba. Nima daga yanzu bana fatan kara neman aure. Mu bari kawai tabi shawarar iyayenta a zauna lafiya."
Sosai Haj Lubabatu taji tausayin Ishaq. Duk sallah bata fasa yi masa adduar samun rabo saboda yadda yake son yara. Da suna kanana har goya masa kannensa tana yi saboda yadda yake mata nacin zaiyi raino. Sai ayi goyon ya zauna a falo ko baki tayi baya jin kunya.
"Dole kayi aure shine cikar dan Adam. Kayi addua kamar yadda nake maka. Allah Ya kawo maka mace tagari" ya amsa da amin amma ba don yana tunanin zai kara son wata bayan Asmau ba. Shi fa bashi da raayin auren da babu soyayya. Kuma soyayyarsa ta kare a wurin Matar Jikamshi.
Ya kai hannu kan giya zai canja yaji Bilkisu ta dora nata a saman nasa ta kankame. Ya dan kalleta ya kula kuka take yi a hankali. Yace "nine ko, nasa Maminki kuka"
Muryarta na rawa tace "a'a Uncle don Allah kada kaki auren Ummin Amatullah"
Murmushi kawai yayi yana kwanar shiga asibitin motar Musaddiq tana bayansa.
"Allah Yayi miki albarka kinji. Ki cire duk abinda kika ji dazu daga ranki.... Wai ma wa ya koya miki labe? Bari mu dawo yau sai kinyi tsallen kwado"
Da guntun hawayenta tayi murmushi. Hajiya ma murmushin tayi. Taji dadi da fushinsa bai shafi 'ya'ya ba.
Boot dinsa ya bude ya fito da ledoji biyu cike da tarkacen kayan kwadayi na yara sai katon din ziza. Yana tasowa daga office ya siyo kafin ya wuce gida. Bilkisu tazo taya shi dauka sai ga su Ismail da sauri kowa ya dauki abu daya cikin su mazan. Ya kawar da kansa gefe don yasan suna neman shiri ne. Abinda bazasu samu kenan a nan kusa ba.
*****
Shi da Hajiya ne a gaba sai Bilkisu da ta jero tare da Mami da Safiyya tana tambayar Mamin kannenta. Sun kusa zuwa dakin suka ga wata mace ta fito daga wani daki da hijab dinta har gwiwa tana kuka. Col. Ishaq bai san lokacin da ya isa gabanta ba da sauri ba hankali a tashe yace "Matar Jikamshi menene?"
Asmau kuka take yi kawai "Amatullah ce ta sake samun attack. Likita zan kira"
Shima a rude yake yace "koma wurinta bari na kira likitan"
Kasa komawa dakin tayi tabi bayanshi da gudu tana ta zubar da hawaye. Duk sunji tausayin Asmau da yadda ta gigice. Dakin da suka ga ta fito Hajiya tace "mu shiga mu jirasu"
Mami ta bude kofar suka shiga da sallama. Mama Yalwa ce a tsaye kan Amatullah tana ta kakari. Safiyya na jin yadda take kakarin ta matsa kusa da gadon da sauri tace "wannan ba attack din asthma bane. Ba kuji yadda take numfashin ba, majina ce a kirjinta"
Mama Yalwa tana jin haka ta saka bakinta a hancin Amatullah ko kyama babu ta rinka zuke mata tana tofarwa. Tana kaunar Safina fiye da sauran jikokinta sosai saboda yarinya ce mai tattare da tabo mai muni a rayuwarta. Bayan zina mace aka fi gani da nason zunubin duk da cewa dole idan anyi akwai namijin da suka yi tare. To amma namijin sai ya tsira daga aibatawar mutane saboda shi ba'a ganewa a jikinsa. Idan ya karyata babu yadda za'ayi dashi. Sharrin zuciya ya cutar da Abubakar wanda yayi sanadin cutar da Asmau. Gashi a karshe Safina ita ce abin ya kare a kanta. Mama ta dan share hawayenta sai ga Amatullah ta ware saboda hancinta ya bude.
Sai a lokacin suka gaisa dasu Haj Lubabatu. Mama tace "Hajiya duk wadannan yaranki ne? Masha Allah"
Hajiya ta dan murmusa "ya mai jikin?"
Mama tace " gata nan duk ta ruda mu." Ta kalli Safiyya "nagode miki kinji. Ya sunanki ne?"
Safiyya ta fadi sunanta kenan su Asmau suka shigo tare da likita. Ga mamakinsu a zaune Amatullah take ta jingina da pillow. Asmau taji wani sanyi a ranta sannan ta matsa kusa da Amatullah tana mata sannu. Likitan ya dubata ya tabbatar harda mura tayi mata mugun kamu. Magunguna yace zai turo nurse ta kawo musu.
Bayan fitar likitan Asmau ta gaishe da su Mami. Cikin su babu sa'anta duk sun girmeta. Sun amsa mata fuskokinsu babu yabo babu fallasa. Col. Ishaq yana tsaye daga wurin kofa. Idonsa kyam akan Asmau har 'yan uwansa suka fuskanci yadda suke jifan juna da kallo. Ita duk kunya ma take ji musamman saboda su Hajiya da Mama.
Amatullah ce ta kurawa Ismail ido tace "kai da Babana iyinku daya. Kaima sunanka Jikamshina?" saboda irin kamaninsa da Ishaq.
Ya Salam, Asmau ji tayi kamar kasa ta tsage ta shige. Allah Ya taimaketa ma Amatullah bata ce irin yadda Ummia ke fada ba. Don kadan daga aikinta ne yin hakan.Col. Ishaq kansa yau yaji kunya karo na farko a rayuwarsa game da fadin magana a gaban kowaye batare da yaji komai ba.
Su Musaddiq sai kallon kallon kallo ana dan murmushi. Ismail kuwa yace mata "nima babanki ne 'yan mata" ya karasa wurin gadon da murmushinsa.
Ta kalli Col Ishaq tayi masa gwalo " Babana kaga nayi sabon baba ko. Ni yanzu na dena yin baba da kai"
Yace "subhanallahi me nayiwa princess dina haka. Kai Ismail tashi ka bani wuri mu sasanta ni da 'yata"
'Yar dramarsu tasa mutanen dakin dariya. Amatullah tayi saurin rike hannun Ismail tace "yanzu baka wasa dani sosai sai da Ummi na. Nima ga sabon Baba nayi"
Asmau ta rasa abin cewa. Tsiyar yaro mai surutu fa kenan. Yau Amatullah ta gama bata kunya.
Safiyya tace "amma da baban nan naki da Ummi basu kyauta ba. Yanzu ga sabo nan mun baki. Amma kiyi hakuri Babanki so yake ku koma gidansa sai ku rinka wasan tare kullum shiyasa yake yi da Umminki"
Kana gani kasan Amatullah taji dadin wannan zancen tace "Ummi kuje kuyi wasa da Babana to idan kun gama mu koma gidansa."
Yau kam ta kai karshen jin kunya, shi kuma Col. Ishaq saboda shawarar da ya yanke ta rabuwa da ita shiyasa yau bai bada amsar da zata karasa bata kunya ba.
Hajiya da Mama Yalwa sai sunkiyar da kai suke. Ita Mama harda mamakin dama son Asmau sojan nan yake bata sani ba.
Ismail ji yayi ta shiga ransa. Dama yana son 'ya mace gashi duk maza gareshi.
"Ki kyale wancan Baban kawai kinga a gidana zan siyo miki kayan wasa da alawa"
Tace "ai Ummi ma tana siya min. Ta hanani kwadayi. Kuma bana yi sai tace min Allah Yayi miki albayka"
Yarinya karama sai basu sha'awa take yi. Mami kallon Asmau take yi. Yanzu mace mai kamannin kamala irin haka ace a waje ta haihu. Kai wannan duniya mai rudin bayin Allah.
Amatullah ta sake cewa "sabon Babana in kayanta maka Allahu?"
Dahiru yace mata "karatu ake cewa ba kayatu ba"
Tuni ta bata rai "kayatu fa nace ba kayatu ba"
Daki ya kaure da dariya. Col. Ishaq yana kallon yadda 'yan uwansa duk suka mayar da hankali gareta. Murmushi yayi yana fatan ko nan gaba idan ya roki alfarmar a bari tazo gidansu ta yini wurin Hajiya bazasu yi mata gori ba. Ido suka hada da Asmau tayi murmushi sai taga ya dan sunkuya kamar zai duba waya. Bata kawo komai a ranta ba.
Ismail ya samu shiga wurin Amatullah yace "karanta min a kunnena ni kadai kada su ji"
Ta fito da ido da mamaki "Ummi fa tace mai yada mai yada dan wuta, mai ji mai ji kafiyi." Nan dariya aka yi suka ce to sai ya kiyaye yarinya tasan rada babu kyau.
Daga kai yayi ya kalli Asmau ta danyi murmushin jin kunyarsa. Su Mami suma mamakinta suke yi. Ga dai ta yadda ta haifi 'yar nan amma ga dukkan alamu tana da tarbiya sosai. Tunda ta bude baki ta fara karanto sunayen Allah gudu biyar da tsallake. Musaddiq ji yayi inama 'yarsa ce. Ga muryarta akwai dadi tana yi kamar da addu'a
"YA RAHMANU YA ALLAH-AMIN
YA RAHIMU YA ALLAH-AMIN
YA MALIKU YA ALLAH-AMIN...."
Haka tayi ta yi har karshe. Mami ta y kurawa Asmau ido, yarinyar bata da makusa sai abinda tayi a baya. Idan har aurenta zai sa dan uwanta ya dawo mata kamar da, to zata amince da auren nan. Sai dai fa dole su shirya da jin surutu da gorin 'yan uwa da sauran mutane.
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
ABINDA AKE GUDU🙆🏽46
Batul Mamman💖
Surutun Amatullah ke tashi a dakin da masu biye mata. Tsakani da Allah ta shiga zuciyar Ismail. A ransa ji yake ina ma yarinyar nan ta cika 'ya kamar kowa. Ta tashi har karshen rayuwarta bazata taba jin wata magana mai muni game da haihuwarta ba. Col. Ishaq kuwa Asmau har ta gaji da kallon inda yake tsaye. Duk iya yinta ta kasa yin sa'ar kallonsa a daidai lokacin da yake kallonta. Shi kuma yana sane yake dauke kansa daga gareta idan yaga ta dago nata kan. Duk son da yake mata dole ya rabu da ita indai tsakaninsa da Allah yana son farincikinta. Duk wani tanadi da yake yi mata da Amatullah maganar Ismail ta rusa komai. Zaiyi kokarin taimakonta ta kowane fanni na rayuwa musamman karatu da tace tana son komawa. A shirye yake ya dauki nauyin hakan idan bazai kawo matsala tsakaninta da wanda ta aura ba. Ko kawai ya hada kudi ya bata a matsayin gudunmawar aure. Shi kadai yake ta tunaninsa har su Umma suka shigo ita da Anti Bintu da Shemau.
Ba haka su Mami suka tsammaci ganin dangin Asmau ba. Gashi dai suna da rufin asiri sannan ga hadin kai. Wani abin mamaki wai harda babar wanda yayiwa Asmau ciki ake jinyar Amatullah. Mamakinsu bai karu ba sai da Alh Adamu ya shigo. Mutum mai fara'a jan mutane a jiki. Ya gaisa da kowa sannan ya zauna yana tsokanar Amatullah. Lokacin dakin ya cika sosai shiyasa Haj Lubabatu tace su tashi su tafi.
Tun daga kan Mami har Musaddiq sun yaba da 'yan uwan Asmau. Kaddara kam babu inda bata giftawa. Kuma idan ta ratso kamata yayi dukkan musulmin kwarai ya karbeta hannu bibbiyu. Ashe ba daidai bane idan 'yar mutum tayi ciki ko zina a kyamaceta a koreta. Hakan ba komai zai kara musu ba sai bushewar zuciya idan basuyi sa'a kamar ta Asmau ba. Ba'ace a nuna musu sunfi kowa ba ko a shafe girman laifinsu a mayar dasu kamar komai bai faru ba. Amma a jasu a jiki ta hanyar nuna musu kuskurensu da wajibcin tuba da nesanta daga aikin dana sani. Asmau ta zama babban misali. Duk da iyayenta sun yafe mata kuma ta tuba amma fa har abada da gaban abada idan akwai baza'a taba mantawa ba. Ita da ta manta da haka a rayuwarta sai ranar da taji ance *shiga aljannah cikin aminci*. Ya Allah Kasa mu dace.
Ita da Anti Bintu suka fito rakiya. Sai a lokacin suka hango Bilkisu da Yassar a wurin wani benci. Kusan kowa ya manta dasu ma.
Duk abinda taji daga bakin iyayenta da kakarta ta tambayi Yassar ya tabbatar mata da haka ne. Bilkisu tayi kuka sosai taji tausayin Asmau. Ta fada masa shawarar da kawunta ya yanke na rabuwa da Asmau saboda matsalarsa. Nan fa hankalin Yassar ya tashi. Bai ga wanda ya dace da yayarsa ba kamar Col. Ishaq. Suna wannan tattaunawar ne suka hango fitowar su Ismail. Bilkisu ta rasa inda zata saka kanta don kunya. Kada ayi zaton ko Yassar saurayinta ne duk da kuwa hakan take fata. Amma bata riga ta faru ba. Yanzu kokarin daidaita Kawunta da yayarsa suke yi.
Allah Yasa hankalinsu baya wajen. Asmau da Anti Bintu ne suka gansu. Anti Bintu sai ta tsaya wurin Col. Ishaq saboda dama tana son ganinsa. Sauri zatayi suyi magana kafin Hajiya ta fito don Alh Adamu dasu Umma sun dan tsaya hira da ita. Ita kuma Asmau ta karasa wurin su Bilkisu.
Suna hangota suka tashi sai dai ta kula da hawayen da Bilkisu ke gogewa da sauri. Tsorota tayi ko Yassar yayi mata wani mugun abin. Tsaresu tayi da ido tana kallonsu daya bayan daya
"Me kuke yi a nan tun dazu?"
Yassar ya dan sosa kai yana murmushi "babu komai Ummin Amatullah"
Tayi dan tsaki "Bilkisu fada min kinji. Me yayi miki kike kuka?"
Itama murmushi tayi "Allah babu komai, abu ne ya shigar min ido"
Ko kusa bata yarda dasu ba. Daga ganin yanayinsu tasan basu da gaskiya.
"Tunda bazaku fada min ba bari na kira babanki, shi nasan zaku fada masa"
Zata juya Yassar ya riko hannunta da sauri "don Allah kada ma ki fara. Bari su tafi wallahi zan fada miki duk abinda kike son ji.
Suna kallo motocin su Ismail da Dahiru suka fita daga asibitin. Bilkisu tace "bari naje, Anti Asmau sai da safe."
Asmau ta dan bata rai cikin wasa "bazan amsa ba sai naji bayani."
Murmushi kawai Bilkisu tayi ta kama hanyar motar Col. Ishaq.
******
Tana karasawa taji Anti Bintu cikin tashin hankali tana cewa "wace irin magana ce wannan Ishaq? Haihuwa ta Allah ce. Yanzu saboda wannan zaka ce ka fasa. Wallahi baka ga yadda na shiga damuwa ba da naji zancen Qasim"
Rabin hankalinsa yana kan Asmau da yake hangowa suna magana da Yassar. Ba a nan inda 'yarta ke kwance tana jinya yake so taji zancen ba. Bilkisu ya kalla babu fara'a a fuskarsa.
"Kin gama kai gulmar? To kije ki fada masa nace kada ya kuskura ya fada mata komai yanzu"
Hanjin cikinta har wani kullewa yayi don tsoro ta koma wurinsu da sauri sosai. Ya mayar da hankalinsa ga Anti Bintu.
"Rashin haihuwa ba karamar matsala bace. Ke shaida ce ina sonta amma yaushe zan tauye mata hakkinta ta zauna dani babu haihuwa"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Asmau tana ganin jarabawa kala kala a rayuwarta. Tunda ta dawo gida ban taba ganin farincikinta ba kamar idan tana tare da kai. Ishaq wallahi tana sonka. Kada kayi mata haka. Yarinyar nan taga taskun rayuwa. Yanzu kuma zata rasa masoyi" Anti Bintu tana magana ita kanta kamar zata yi kuka.
Ji yayi zuciyarsa har wani zafi take masa. A jiya ya yanke shawarar ko me zai faru bazai rabu da ita ba. Amma magana daya tasa ya tuno da rashin dacewarsa da ita.
*****
Kafin Bilkisu ta isa wurinsu Asmau tayo gaba. Yassar yayi mata alkawarin sai sun koma gida zai fada mata komai, ita duk tunaninta ma ko soyayya sukeyi a boye. Bata matsa masa ba tace shikenan. Cikin nutsuwa ta taho wurin da Jikamshi yake tsaye da Anti Bintu. Ita dai Anti Bintun tana ganinta ta bar wurin zuciyarta tana kara karaya. Bata san halin da Asmau zata shiga ba idan taji abinda Ishaq yake tafe dashi. Gashi lamari na haihuwa ba'a daukarsa da wasa. Ita bata isa tace dole ayi auren ba tunda da kansa ya fada mata aurensa na fari shekarunsu goma shadaya da matar. Gashi suna rabuwa ta haihu.
Da zata bar wurin suka hada ido da Asmau tayi saurin sunkuyar da kai a kunyace. Shima ba dadewa zatayi a wurinsa ba saboda kada Hajiya ta fito.
Yaji dadin ganinta amma yanayin da zuciyarsa take ciki ya hana ya bayyana mata duk kokarinsa na boyewa. Da murmushi a saman fuskarta ta gaishe shi.
"Matar Jikamshi"
"Uhmm"
"Yau nafi sonki akan kullum, ji nake kamar yau na fara sonki ma" yadda yake furta kalamansa a hankali yasa taji wani dadi a ranta.
Mukullin motar yake dan kadawa yace "baki amsa min ba."
A zuciyarta tace zai fara sakata jin kunyar da ya saba. Kasa take kallo tace "to me zan ce?"
"Au baki ma sani ba, to bari na fada miki tunda ni nake son jin amsar. Ina ji idan baki fadi abinda nake so ba bazan iya kaimu gida ba." jikinsa duk a sanyaye yake. Daga yau baya jin zai kara furta mata kalmar so. Kallo kuwa tamkar ya cinyeta da idonsa. Jin soyayyarta yake sabuwa a zuciyarsa.
Dago kai tayi "don Allah ka dena fadin haka bana so"
"Nine bakya so ko maganar da nayi"
Kwabe masa fuska tayi tana shirin kuka yaji ta kara shiga ransa"kasan me nake nufi. Ka dena cewa bazaka iya zuwa gida ba"
Yayi dariyar karfin hali "to bani amsar da ta dace"
Rufe fuskarta tayi da mayafi sannan tace "I love you Jikamshina" da sauri ta juya zata gudu ya dakatar da ita ta tsaya amma bata juyo ba.
"Matar Jikamshi ki rike mijinki da gaskiya kinji ko. Allah Ya albarkaci rayuwarki"
Duk ya kashe mata jiki da kalamansa amma ko kadan bata kawo komai a ranta ba. Ita a zatonta shi yake nufi a matsayin mijin nata shiyasa tace
"Amin" sannan ta shige cikin asibitin.
Allah Ya taimaketa domin kuwa a hanya ta hadu da Umma da Mama sun rako Haj Lubabatu. Gashi babu damar canja hanya haka tayi mata sallama ta wuce su kuma suka rakata har mota.
Har su Umma suka zo tafiya Anti Bintu bata ga wani sauyi a tare da Asmau ba. Wannan ya sa tayi tunanin Ishaq bai riga ya fada mata ba. Duk su biyun tausayi suke bata, zata saka su a addua don ita bata san wace shawara zata basu ba.
*****
Bayan kwana biyu aka sallami Amatullah. Duk kwanakin da Mami tayi a Kano a gidan Col. Ishaq tayi su don kuwa da gaske Haj Lubabatu ta hanata kwana a gidanta. Ranar da zata tafi suka taru ita da kanneta suka sake bawa Hajiyan hakuri. Shi Col. Ishaq tuni ya ware dasu. Fushin bazai kaishi ko'ina ba yanzu tunda akwai gaskiya a maganarsu. Mami ta tafi akan duk shawarar da ya yanke su duka zasu bashi goyon baya.
A wannan lokacin ya rage kiran Asmau. Idan ta kira sai taji wayar a kashe. Nambobinsa biyu gareta duk bata samunsa sosai sai idan shi ya kirata. Shima din hirarsa tafi yawa da Amatullah. Idan ta karbi wayar daga gaisuwa sai yace mata zaiyi aiki ko zai kwanta. Tun bata dauki abin komai ba har dai ta fara tunanin akwai wata a kasa.
A bangaren Qasim ya matsa mata sosai da waya yanzu. Yazo sau daya ya koma bakin aikinsa. Nunawa yayi bai san da maganar Col. Ishaq ba. Ita kuma taki sakar masa jiki tana jira taji daga bakin Jikamshi tukunna.
*****
Haka tayi sati daya duk abubuwa sun cakude mata. Jafar ya karbi takardunta na SSCE zai sake nema mata admission. Amatullah tunda taji sauki Abdulhalim ya zo wata litinin da safe ya tafi da ita makarantar da yaransa suke yi. Makaranta ce mai tsada sosai domin kuwa ana arabiya da boko tun bakwai da rabi sai hudu da rabi ake tashin yara.
Ga karatun Qur'ani ba kama hannun yaro. Ita dai Asmau sai son barka. Kowa na kokarin kyautata musu. Shemau taso ace a makarantar da nata yaran suke zuwa aka saka Amatullah. Da yake saura sati daya hutun makaranta gwaji kawai aka yi mata suka bata aji, kayan makaranta da litattafai. Karatu sai an dawo zata fara sosai. Abdulhalim ya biya kudin komai. Alh Adamu ya kara masa kudi don kada ya shiga matsi tunda yana da nasa yaran. Amma yaki karba Amatullah 'yarsa ce baya bukatar taimakon kowa.
Da ya dawo da ita gida kuwa an sha labarin sabuwar makaranta. Tana ta zuba zance akwai lilo da wurin computer irinta Uncle Yassar. Hajjo da Umma kadai ke amsa mata. Asmau na rike da waya a hannu tana ta kiran Jikamshi ta kasa samu. Bata jima da ajiye wayar Qasim ba yace mata iyayensa suna so a sake basu ranar da zasu dawo.
Umma ce ta lura da yadda take ta tsaki ga waya a hannu tana ta dannawa.
"Asmau wa kike nema ne haka? Kinsan dai wani lokacin network sai yaki dadi amma duk kinsa abin a ranki sai tsaki kike faman yi."
Amatullah tayi caraf tace "kuma ni ta hana ni yi, wai tsaka ce yake yi"
Ran Asmau yayi mugun baci ta kai mata duka ta sameta a gefen fuska "ban hanaki idan manya na magana ki saka baki ba. Tashi ki bar wurin nan kafin na kara miki"
Kuka sosai Amatullah take yi don har dankunnenta sai da yayi tsalle. Umma da Hajjo har suna rige rigen janyota jikinsu. Umma itama ta harzuka tace "wane irin rashin hankali ne wannan Asmau. Daga tayi magana sai duka."
Hajjo tace "kuma dukan ma a fuska, tayi kuskure don ba'a so a koyawa yara saka baki a zancen manya. Amma ya zaki mata hukunci irin wannan. Ji yadda dankunne ya karce ta"
Suna kokarin jan Amatullah amma taki tsayawa. Da Hajjo ta saketa jikin Asmaun ta koma tana kuka "Ummi kiyi hakuyi na dena"
Kuka Asmau ta saka, tasan bata kyauta ba don fushinta ta saukewa Amatullah. Ga zuciyarta dama ta gama rauni. Bata samun Jikamshi shima baya kira sosai sannan Qasim yana jiran amsarta na ranar da zasu dawo. Amatullah ta sake cewa "Ummina kin hakuya?"
Cikin kuka ta rungumeta sosai a jikinta "na hakura Ama"
"To ki dena kuka nima na dena"Amatullah ta fada tana share hawayenta.
Wannan ya kara karyarwa Asmau zuciya ta cigaba da kukanta bilhaqqi. Umma da Hajjo suka tsaya kallon ikon Allah. Sai da tayi mai isarta ta dauki Amatullah suka shiga ciki.
Suna tafiya Hajjo ta rike baki "Bara'atu anya yarinyar nan bata da mutanen boye? 'yan kwanakin nan na lura tana cikin damuwa. Wannan kukan ma da biyu ko uku ma zance take yinsa."
"Nima haka nagani, bari naje naji ko menene"
*****
Dariyarsu Umma ta fara ji Asmau tana bin Amatullah tana cewa zata shafa mata dettol a wurin da dankunne ya karceta ita kuma tana zagaye gado da gudu. Umma ta rike baki kawai. Asmau da Safinanta sai Allah. Tare suka ga wahalar rayuwa shiyasa shakuwarsu take bawa mutane sha'awa.
Sakin fuska tayi ta shiga ta daga Amatullah.
"Gudu wurin Hajjo kinji yarinyar kirki."
Ta fice kuwa a guje tana dariya. Asmau kunya ta kamata ta ce "Umma kiyi hakuri don Allah".
"Bakiyi min komai ba Asmau. So nake ki fada min abinda yake damunki. Ba'a so damuwa tasa iyaye su rinka hucewa akan 'ya'yansu. Amatullah bata kyauta ba da tayi magana amma ba da haka zaki tsawatar mata ba. Ko don gaba ki kiyaye"
"In sha Allah Umma. Nagode"
Wuri Umma ta samu ta zauna tace "zauna Asmau, magana zamuyi"
Murmushi ta kirkiro "babu komai fa Umma, haushi ta bani ne"
"To na tashi kenan tunda kina da wanda zaki fadawa matsalarki bayan ni"
Daga magana kamar ance fara kuka kawai ta kwantar da kanta a cinyar Umma ta soma kuka. Tausayi ta bawa Umman ta fara rarrashinta "komai yayi tsanani maganinsa Allah. Yakamata ace kece mai fadawa wani hakan. Wa kike nema a waya har abin ya bata miki rai haka"
Muryarta har ta dan shake tace " idan mutum ya dena nemanka a waya sosai alama ce ta ya hakura da kai ko, ko kayi masa laifi"
Duk da Umma tasan wa Asmau ke so sai tace "waye baya kiranki a waya"
Rufe bakinta tayi da sauri. Maganar ce take cinta amma bata yi niyar fada ba.
Dan murmushi Umma tayi. Tun ranar da suka hadu da su Hajiya a asibiti kafin Anti Bintu ta koma Zariya ta fada mata yadda suka yi da Col. Ishaq. Ta sauke ajiyar zuciya
"Ishaq ne baya kiranki?"
Sake sunkuyar da kai tayi ta kasa amsawa. Umma tace "ki yawaita addua da neman zabin Allah nima zan tayaki."
Abinda yake ta cin ranta ta kasa boyewa "cewa yayi zaiyi magana da Hajiya, ina jin saboda Amatullah bata amince ba. *Umma nayi kuskure ne da ban zubar da cikin ba na haifeta*?
Wannan karon Umma ma sai hawaye "ko kadan Asmau. Haihuwarta shine maslaha gareki damu baki daya. Mun so bin son zuciya da muka dage sai kin zubar da cikinta. Ki duba ki gani yadda Allah Yayita mai kokari da ladabi. Kema kinsan ba iyawarki bace kawai tasa kike da yarinya mai tarbiya kamarta. Mata da yawa da iyayensu sukan gujewa kunyar duniya su zubar da ciki ko a yar da jariri. Sai anje lahira kuma ido ya raina fata. Ga laifin zina ga na zubar da ciki ko kashe jinjiri. Ko ki sami miji ko kada ki samu ki sani cewa rayuwarki ibada ce. Hakuri da tawakkali shine ginshikin farincikin dan adam. Batun Ishaq kuma kada ki damu zai nemeki da kansa ku kare magana. Da shi da Qasim wanda duk Allah Ya zaba miki ko waninsu sai mu ce Alhamdulillah.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽47
Batul Mamman💖
*Maman Farida mai Hanyar Ruwa. Ina gaisuwa da fatan alkhairi. Ga naki shafin yar uwa*
*Amina Yau, Jikamshi yana gaisheki da kyau.*
*Shafaatu mai masaukin baki a gidan Batul ina godiya*
*Masu sakonnin gaisuwa bazan taba mantawa daku ba. Allah Yayi mana jagora*
Sai yanzu Asmau ta dan sami nutsuwa a ranta. Tun da Jikamshi ya dena kiranta sosai ta fara tunanin ko Hajiyarsa ce bata amince ba. Amma yanzu Umma ta kwantar mata da hankali. Zata sake nemansa daga yau zuwa gobe. Idan taji shiru to zata bar komai ga iyayenta. A yanzu dai Umma da Mama Yalwa sun riga sun san da maganar Col. Ishaq. Mama har fada tayi da basu fada da wuri ba sai a asibiti ta ganewa idonta. Asmau ta san bazata bar maganar ba dole ta fadawa Baba.
Bayan fitar Umma tashi tayi ta dauko Al-Qur'ani tana karantawa. Neman sauki kawai take a zuciyarta da ke kitsa mata abubuwa da yawa. Adduarta bata wuce idan Jikamshi bazai aureta ba zata mayar da hankali ga karatu, idan kuma iyayenta sun zaba mata Qasim duk da a yanzu sun san bata son shi to bazata yi musu ba. Fatanta bai wuce ta sami juriya wurin karbar duk wata jarabawa da tazo mata ba.
*****
Washegari Umma ta gama shirin zuwa gidan Mama suyi magana ta karshe da Alh Adamu sai ga Garzali ya shigo yana ta fara'a suka hadu a bakin kofa. Umma tace "kanina mijin 'yata irin wannan fara'a haka. Ko dai Zubaida ta haihu"
Yana murmushi yace "yanzu daga asibitin nake. Ko awa daya bata yi ba. An sami namiji."
Umma sai murna ta koma ciki tana mita akan me bai fada musu ba tun lokacin da suka tafi asibitin. Sai da suka je dakin Hajjo bayan ta fada mata kyakkyawan labari tace "ina kuka kai su Walid?"
"Kai Yaya Bara'atu sai faman fada kike yi. Tsakar dare fa ta fara nakudar. A makota na ajiyesu muka tafi."
Asmau ce ta shigo dakin daga kitchen bayan taji muryar Kawu Garzali. Tayi murna sosai tace bari ta dora ruwan zafi sannan ta hada abinci. Kawu Garzali yace ta barshi makociyarsu duk tayi wannan. Yana jin bazata dade ba za'ayi sallama. Tace to bari tayi wanka sai su tafi. Tana tafiya Umma ta soma fada masa halin da suke ciki ga Qasim kuma da yake jira a sake basu lokaci. Hajjo tace
"Allah mai iko, wallahi idan aka ce min yarinyar nan zata sami manemin aure sai in karyata. Gashi yanzu an samu har an rasa na zabe. Ni dai shawarata kada ayi mata dole. Yaron nan Qasim dan mutumci ne gaba da baya amma bana son ayi auren dana sani. Asmau ba kankanuwar yarinya bace da zaa ce bata san me take yi ba. Kai Garzali mu zamu je asibitin. Kaje ka sami Alhaji kuyi magana. Idan za'aji ta bakin Ishaq din ne ya kamata a hanzarta. Idan kuma da Qasim din ne ma duk yadda akayi babu matsala."
Umma ta dan sassauta murya tace "Bintu fa ta fada min shi Ishaq din yace ya janye saboda baya haihuwa."
"Baya haihuwa?" Hajjo ta fada tana daga murya.
Umma tace "Asmau bata sani ba. Yace zai fada mata da kansa. Nima ban nuna mata na san wani abu ba"
Kawu Garzali ya shiga jimami. Zubaida ta fada masa irin yadda ta ga Col. Ishaq da Asmau suna son juna ranar da taje yini a gidan. Anya akwai ranar da Asmau zata ga haske a rayuwarta kuwa. Daga wannan matsalar sai wannan.
"Wai ya taba aure ne ko tuzuru ne shi Ishaq din"
"Kaima dai Garzali in bai taba aure ba yaushe zai san da matsalar rashin haihuwar. Shekararsa shadaya da matarsa ta farko"
Gefen gado Hajjo ta samu ta zauna "ni dai kaina duk ya kulle. Haihuwa ba abin wasa bace duk da mutum baya bawa kansa amma kowa yana so. Muje dai wurin maijegon, kai kuma duk yadda kuka yi da Alhajin ka fada mana. Ai ita shawara tana da dadi. Bana son azo ana cizon yatsa nan gaba shiyasa cikinsu babu wanda zan ce lallai sai ta zabe shi."
*****
A nan suka bar zancen su Umma suka wuce asibiti daukar Zubaida. Kawu Garzali ya tafi gidan Alh Adamu.
Bayan sun gaisa ne Alhajin yace "ina Hajiya Bara'atun? Tace zata zo. Ashe tare ma kuke"
"Ni kadai ne Alhaji. Sun tafi asibiti mai dakina ta sauka dazu bayan asuba"
Barka Alh Adamu yayi masa sannan suka fara tattauna abinda yake gabansu. Zancen Col. Ishaq ma sai da Alh Adamu yayi ya ce Mama ce ta fada masa. Ashe shiyasa yaga shi da mahaifiyarsa da 'yan uwansa sun zo duba Amatullah. Daga Shanono kuma jiya ya sami waya suna bukatar a sake basu lokaci.
"Alhaji wannan abu duk mai sauki ne. Yanzu nake ji cewa shi Ishaq din yace zai janye saboda yana da lalura ta rashin haihuwa. Idan haka ne kaga Qasim ya kamata ta aura"
"Banki taka ba Garzali. Duk abinda aka riga aka sani yafi sauki idan za'a tunkare shi. Amma menene tabbacinmu na cewa shi Qasim yana haihuwa ko ita Asmau zata sake haihuwa? A zahiri nafi sonta da Qasim saboda kusancinsa da Abubakar. Gani zanyi kamar dana ne ya aureta. Sai dai kuma bana son mu saka son zuciya a cikin al'amarin nan. Tana gida ne yanzu?"
"A'a tare suka fita dasu Hajjo" Garzali ya bashi amsa.
"Idan ta dawo kace ina nemanta jibi bayan azahar in sha Allah. Zan je daurin aure ne gobe Gashua. Tambayarta zanyi don kada abin yazo da daukar alhaki. Wanda ta zaba sai mu duba mu kuma muga dacewar hakan. Aure ai ba'a yi masa garaje. Rashin karasa karbar kudin wancan karon ma daga Allah ne."
"Shikenan Alhaji, Allah Ya zaba mata mafi alkhairi." Daga nan suka yi sallama Kawu Garzali ya tashi ya tafi.
*****
Inna mahaifiyar Qasim ce ta saka shi a gaba suna magana akan aurensa.
"Baffanka yace sunyi magana da Alhaji Adamu yace a dan kara musu lokaci zasu sanar da ranar da za'aje kai kudi"
"Eh munyi maganar. Dama Asmau nace ta fada musu da farko to ashe ma Baffa ya kira shi"
Rai a bace Inna tace "yanzu ita Asmaun har sai an bukaci lokaci kafin ace an yarda a kai kudin? Naga dai ita ce ma me abin bincike a kanta. Yarinyar da ta bar gidansu tsahon shekara biyar."
Murmushi kawai yayi. Inna bata son auren nan nasa duk irin yadda zaiyi mata bayani tace su rayuwarsu ba irin ta birni bace. A nan duk wanda yaji Asmau tana da 'ya sai ya tambaya mijinta rasuwa yayi ko sakinta yayi. Wasu ma suyi ta cewa mai zai sa Qasim ya fara da auren bazawara. Babu yadda za'ayi su boye gaskiyar lamari. Wasu ma sun dade da sanin rasuwar abokin Qasim da cikin da yayiwa budurwarsa. Gulma da kananan maganganu sai yawo suke. Ko kadan Inna bata jin dadin hakan duk da tana kokarin yiwa Malam biyayya ta nuna ta amince da auren.
"Sai anyi magana kayi ta murmushi kamar wani bazawari. Ya dai kamata kafin komai ya kankama kuje ayi mata gwajin 'yan cututtukan nan na zamani musamman kanjamau"
"Inna ba fa karuwanci taje tayi ba. Aikin asibiti tayi duk tsahon lokacin nan"
Tabe baki tayi "haka dai ta fada muku ku kuma kuka hau kuka zauna. Mace babu mai kwabarta ai sai ta mike kafa. Ni dai ba wani abu nace ba. Ayi mata gwaji ko don taka lafiyar. Gurbacewa ce dai ka gama gurbata mana dangi. Ko me kuka haifa nan gaba sai ance yayarsu shegiya ce"
Har ransa Qasim baiji dadi ba. Innarsa ta lura da yadda ya hade rai tayi murmushi "Baba kenan, kada ka daukeni muguwar uwa wadda bata son danta yayi aikin neman lada. Duk wata uwa komai shedancin danta tana son ya auri mace tagari. Abubuwan da kaga suna ta faruwa da yarinyar nab kadan ne daga *abinda ake gudu* a zina. Bana muku fata amma wata rana idan kunyi aure zata iya yin abu da zuciya daya amma saboda sanin da kayi na rayuwarta ta baya kawai sai shaidan ya kitsa maka zargi ka hau kai ka zauna. Karuwai da yawa sun yi aure. Wasu ma a gidan mijin suke sheke ayarsu. An sani amma da yake aure rai gareshi sai kaga ba'a sake su ba. Kasan halina bana boye abinda yake raina. Idan ka auri Asmau kayi mata halacci kuma ka rike amanar abokinka. Ka gyara abinda ya bata. Sai dai bazan fasa nanata maka ba ina so ka kara aure a gaba."
Duk maganar Inna yasan gaskiya ne. Idan Asmau zata taba mantawa da juyin da rayuwarta ta samu sai dai idan an goge wannan bakar ranar da tayi sanadiyar tarwatsa mata rayuwa.
"Akwai wadda kike so na aura ne? Da niyata bazan kara aure ba bayanta."
"Yo dan nan kasan me gobe zata haifar ne da zaka ce haka? Zabin wata matar yana daga gareka don kada ma a sami matsala nan gaba kace nice na zabo matar. Bari na shiga wurin Malam naga la'asar ta kusa"
Da Inna ta tashi Qasim dogon tunani ya zauna yi game da auren Asmau da ya takurawa kansa lallai sai yayi. Burinsa ya kyautata rayuwarta ba ya zama sanadiyar kunci da bacin ranta ba. A yadda ya fahimci hirarta da Col. Ishaq kwanakin baya ba karamin so suke yiwa juna ba. Addua ya rinka karantowa a zuciyarsa
"Ya Allah, na sani ina daga cikin mutanen da suka batawa Asmau da Abubakar rayuwa. Allah Ka yafe mana baki daya. Ka zaba mata miji nagari tsakanina da Ishaq. Idan aurenta ba alkhairi bane garemu Ka kaita gidan da za'a so ta dominKa."
Tashi yayi yayi shirin masallaci. Yana ganin janyewa kawai zaiyi amma zai tsaya mata sosai idan ta tashi aure. Dole mijin da zata aura ya kasance mutum da za'a iya yarda dashi. Mai amana. Shi kadai yayi murmushi da ya tuno irin kalaman da Col.Ishaq yake fadawa Asmau. Hmmm dole ta so shi ma. Shi kam ya manta rabonsa da tsara mace irin haka. Tun zamanin yana Qasim mai shafe 'yan mata. Rasuwar Abubakar tasa duk tunanin soyayya ya fice masa a rai. Kila harda rashin wannan yasa Asmau bata sauraron shi sosai. Mata da son soyayya kuma....
*****
Haj Lubabatu ke faman fifita an dauke wuta saboda hadarin da ya hado. Ta kira Bilkisu da ke zaune wurin taga tana ganin haske tana karanta littafinta na makaranta saboda test da zatayi washegari.
"Bilkisu ina babanki ne? Na zata ya dawo amma naji shi shiru tun dazu."
"Ya dawo Hajiya, na kai masa abinci ma"
"Duba min kiga me yake yi a ciki tun dazu. Kwanakin nan sai kace wata amarya bashi da aiki sai zaman daki"
Dariya Bilkisu tayi "Hajiya ita amarya zaman daki take yi?"
"Ban sani ba. Wuce ki duba ga magariba ta kawo kai."
Da sallama Bilkisu ta shiga dakin. Duhu ta gani duk labulayen a sauke ga zafi. Daga kan gadon ta hango shi a kwance ya rike kansa. Saurin karasawa tayi bakin gadon
"Uncle Ishaq" ta kira shi a hankali.
Da kyar Col. Ishaq ya iya bude idanunsa. Kansa ke masa wani azababben ciwo kamar zai tsage. Kwana uku kenan yana fama amma na yau yafi tsanani.
"Uncle baka da lafiya ne, bari na fadawa Hajiya."
Ta tashi zata fita wayarsa tayi ringing. Bata yi niyar dauka ba sai da yace "dauki wayar nan Safiyya ce take kira tun dazu. Idan kin amsa ki kasheta kawai. Ga dayar can a kusa da tv itama ki kashe"
Muryarsa da kyar take fita. Hankalin Bilkisu a tashe ta dauki wayar ta fita. Karawa tayi a kunnenta tace "Anti Safiyya bashi da lafiya Uncle din. Kamar ciwon kan nan da yake na bari..."
Gaban Asmau ne yayi mugun faduwa. Baki na rawa tace "Bilkisu nice Asmau. Tun yaushe ne bashi da lafiyar?"
Dan sauke wayar Bilkisu tayi daga kunnenta ta duba sunan. MJ ta gani wanda ta gane yana nufin Matar Jikamshi saboda ta taba ji Uncle din nata ya fada.
"Anti Asmau yi hakuri ban san kece ba. Yanzu na shiga dakinsa na ganshi a kwance. Zan fadawa Hajiya ne ko za'a kai shi asibiti. Dama yana yi idan baya samun hutu sosai."
Idanunta har sun ciko da kwalla , duk abinda tayi niyar fada masa na bacin rai tuni ta manta. Sake rike wayar tayi da kyau tace " Bilkisu don Allah ki kai masa wayar kinji."
Ta san baya son komai idan yana wannan ciwon musamman surutu. Amma kuma bazata iya cewa Asmau a'a ba. Juyawa tayi ta koma dakin. Yana nan inda ta barshi a kwance ta dan kara masa wayar a kunnensa tayi saurin fita kafin yayi mata fada.
Asmau ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta tare dashi. Allah sarki Jikamshinta. Ashe bashi da lafiya shiyasa kwana biyu ta dena jinsa. Haushin kanta taji da har da tayi niyar nuna masa fushinta saboda baya kiranta kuma baije gidansu ba.
Yanayin canjin numfashin da take iya ji yasa ta gane an bashi wayar. Mamakin karfin halin Bilkisu yake da ta kawo masa a halin da yake ciki. Bari ya warke zata fada musu. Rashin Asmau yasa shi shiga damuwa sai yayi ta dadewa wurin aiki. Hakan ya tayar masa da ciwon kai. Sai kuma ga text da tayi tana fada masa yadda suka yi da Qasim akan zasu sake turowa. Tsabar kishi ne da rashin sanin me ya kamata yayi ya kara kwantar dashi. Kamar ba soja ba ya kasa daurewa zuciyarsa yaje ya fada mata ya janye. Dena kiranta a waya din ma ba karamin juriya yayi ba.
Muryarta mai sanyi yaji tace "Jikamshina me ya sameka?"
Bugawa zuciyarsa tayi da karfi da yaji muryarta babu zato babu tsammani. Ba karamin dadi yaji ba ya ratsa shi har ya dan manta da ciwon kan na 'yan dakiku. Bai iya ce mata komai ba sai manna wayar da ya sake yi a kunnensa. Ita kuma ta sake rudewa ko ciwon yayi tsanani ne
"Jikamshina nice, matarka ce, kayi min magana don Allah."
Shiru da ta cigaba da ji ne ya sakata kuka. Dama kullum haka take kamar tana jiran kiris.
Kukan nata murmushi ya saka shi babu shiru. Idon kuka kenan ya fada a ransa kamar yadda yaji a gidansu.
"Its ok ki dena kukan"
Cikin shagwaba tace "Kaji sauki? Ina da ina ke yi maka ciwo? Me yasa baka fada min ba kawai naji ka shiru"
Ta so saka shi dariya yadda yake jin muryarta a hankali amma tana rawa alamun kukan nata bai kare ba
"I miss you too" taji yace a wahale saboda ciwo.
"Uhmm?"
"Duk wannan tambayoyin nan nasan abinda kike son cewa kenan. Kinyi missing dina. But I miss you more Matar Jikamshi. Kin hana Ishaq sukuni."
Jin kanta take kamar anyi mata wani babban albishir da taji muryarsa har ya fara tsokana yadda ya saba. Ta kara kashe murya
"Nima ka hana ni. Har dan wuya nayi. Kasa naji ina kara ....uhmm....na fasa fada"
Sautin dariyarsa taji. Dama Asmau ce ciwon kuma ita ce maganin. Ajiyar zuciya yayi yana gyara kwanciya
"Yanzu ina kwance babu lafiya ma sai kinja min rai. Ki tausayawa patient."
"Kasha magani ne?"
"No, muryarki kadai ta isheni magani. Yau ki shirya zamuyi ta waya har sai kunnenki ya gaji"
Kamar yana gabanta tayi dan fari da ido "bana fatan gajiya da kai Jikamshina. Baban Ama _da kannenta_"
Yaji dadin furucinta amma kalmar karshe ta dawo masa da tunanin da yake addabar zuciyarsa.
"Matar Jikamshi ina son ganinki. Akwai magana mai mahimmanci da zamuyi kinji"
Tunanin maganar aurensu ne yazo mata tace "to Allah Ya kaimu. Ka bari sai kaji sauki sosai. Dama duk na damu ne da naji ka shiru."
"Ki kular min da kanki." Ya iya cewa zuciyarsa babu dadi ya ajiye wayar.
Motsi yaji a wurin kofa ya juya. Hajiya ce a tsaye bai san tun yaushe take a wurin ba. Abin mamaki sai yaji 'yar kunya kadan ba da yawa ba. Itama basarwa tayi ta shigo ciki kamar bata ji komai ba.
"Zaka je asibitin ko kaji sauki? Ni a yadda Bilkisu ta fada min na zata ciwon sosai ya kamaka"
"Sosai ne mana Hajiya. Kamar kan zai tsage haka nake ji"
Tayi dan murmushi kawai "ai naga kamar ka sami magani."
Dariya ta bashi ya tashi zaiyi alwala. Fita tayi tace idan anyi magriba lallai yaje asibiti don tasan ciwon kan baya masa da wasa.
*****
Bayan isha Asmau da Amatullah suna gwada sabon dinkinsu da Yassar ya karbo musu taji waya. Ringtone din Jikamshi daban yake shiyasa ta gane shi. Da fara'a ta dauka don tun wayarsu ta dazu hatta su Umma sun ga canji a tare da ita. Kafin tayi magana yace "fito ina jiranki"
Har wani faduwar gaba taji. Tayi kewarsa sosai amma tana jin kunyar hada ido dashi kuma. A waya ta iya nuna masa soyayya sai an hadu bakin ya mutu. Ga mamakin zuwansa shi da bashi da lafiya. Amatullah ta tura wurin Yassar tace ta fada masa suje babanta ya zo. Ita kuma ta zauna ta gyara fuskarta ta sami mayafi ta yafa sannan taje ta fadawa Umma. Addua tayi mata tace ta gaishe shi. Da ta fita Umma tace ashe ga dalilin sauyin da ta gani a tare da ita. Allah Yayi mata zabi mafi alkhairi. Mai son naka dole ka so shi.
Tunda ta fito daga cikin gidan yake kallonta. Samun kansa yayi da yin godiya ga Allah da ya hada jininsa da Asmau. Yarinyar akwai nutsuwa da kamala. Tana bukatar miji nagari saboda samin ingantacciyar rayuwa da nutsuwar zuciya idan aka yi laakari da kaddarar da ta fada mata. Kuma tana burge shi saboda ta karbi jarabawarta hannu biyu. Har ta iso wurin da yake zaune a gefen mota shi da Yassar da Amatullah kanta na kasa tana murmushi.
Da sallama ta karaso ta dan rissina ta gaishe shi. Ya amsa yana kare mata kallo. Tayi kyau sosai. Shi kuma ta lura ya dan fada.
"Yassar ka shigo dashi falo"
Yace "kiji min mata, ni gurgu ne?"
Ita da Yassar suka yi dariya sannan suka koma falon. Da kyar Yassar ya yiwa Amatullah wayo suka shige ciki.
Daga inda take zaune Asmau ta dan dago kai suka hada ido da Jikamshi. Karuwa sonta yake a zuciyarsa amma dole yayi abinda ya kawo shi. Tattaro duk nutsuwarsa yayi yace......
ABINDA AKE GUDU🙆🏽48
Batul Mamman💖
Ta kagu sosai taji abinda zai fada shi kuma nauyin maganar yake ji. Idan ya fada shikenan yayi musu katanga daga wannan lokacin. Ganin babu amfani yayi ta jan abin yasa yace
"Banda sunan sunan matata ta fari baki san komai game da ita ba ko"?
Asmau ta dan turo baki kishi na cinta duk da bata san matar ba.
"Ni sunan nata ma na manta. Kawai kazo bayan sama da sati daya ka fara min da hirarta"
Yadda take hade rai ya bashi dariya. Ya gyada kai "kishi gareki haka, mun dade da rabuwa fa har ma tayi aure".
"To ai kaine sai ka rasa hirar da zaka yi sai tata"
Ya gyara zama tare da harde kafafunsa "saboda abinda zan fada miki yana da alaka da ita. Ina so ki saurareni da kyau ki fahimci abinda zan fada miki."
Hankalin Asmau ya fara tashi. Wani abu ne ya darsu a zuciyarta ta soma hawaye babu shiri tace cikin murya mai nuna rauni "ba ma sai kace komai ba na gane abinda kake son fada. Aurenta ya mutu zaka mayar da ita ko. Babu komai zan iya zama da kishiya. Don Allah Ka kwatanta adalci a tsakaninmu" ta kare tana jan hanci.
Col. Ishaq bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Ita kuwa Asmau tayi kicin kicin da fuska. Hankici ya dauko daga aljihun wandonsa ya bata "kinci sunanki Idon kuka. Daga fara magana ji yadda fuskarki ta kumbura. Ai dai kya bari na fadi abinda ya kawoni kafin ki soma zubar da hawaye. Mata na gidan mijinta zaki kashe mata aure da baki"
Dan sanyi taji a ranta kila ba abinda zai fada ba kenan. Har tayi murmushi sai kuma wani tunanin yazo mata "maganar aurenmu ne?"
Ya daga kai yana kallonta. Tausayinta yake ji sosai a ransa.
Murmushi tayi mai ciwo "Hajiya bata amince ka aureni ba ko? Dama nayi tunanin haka zata faru. Ba kowace uwa bace zata iya daure zuciyarta ta bari danta ya auri mace irina. Ko nice kila nayi sama da haka ma. Abinda kayi mana na kyautatawa Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai wallahi. Ko a haka ma nagodewa Allah da Ya hadani da kai har ka nuna min so ka zama cikin masu nuna min na kara hakuri da kaddarar rayuwa"
Hawaye ke zubo mata tana magana bata ko tunanin tare shi. Dago kansa yayi daga cikin kujerar ya dan matso gaba.
"Ya Salaam, Matar Jikamshi haka kike? Lokaci daya duk kin rikita kanki. Kada ki dauki alhakin Hajiyata wallahi ta amince da aurenmu"
Jikinta duk da haka a sanyaye yake tace "sauran 'yan uwanka ne basu amince ba?"
"A duniyar nan Hajiya ce kadai zata hanani aurenki na hanu. Banda ita babu wanda ya isa. Yara kanana akeyiwa haka ba ni ba. Kamata kowa yasan ina da hankalin da zan san abinda ya dace da rayuwata. Ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada. Kamar yadda na fara magana kafin ki katseni da dan bakin nan naki mai bani shaawa..." ya fada yana kashe mata ido.
Kunya taji sosai harda rufe fuska da hannuwanta. Yayi murmushi ya cigaba da magana "na taba aure, shekarunmu shadaya da Badar babu haihuwa. Munje asibitoci da dama ana cewa bamu da matsala. Har maganin gargajiya mun sha. Daga karshe mahaifiyarta tasa na saketa kuma cikin ikon Allah a shekarar da tayi aure ta haihu"
Asmau ta dan girgiza kanta "Allah sarki, dama haihuwa ta Allah ce. Wani baya haihuwar dan wani"
Kallonta yake da mamaki kamar bata fuskanci inda ya dosa ba
"haihuwar Badar ya tabbatar min da inda matsalar take. *Matar Jikamshi, bana haihuwa*. Saboda haka kiyi hakuri da na bata miki lokaci amma na _janye maganar aure a tsakaninmu_."
Tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi haka taji saukar maganarsa ta karshe. Shiru tayi na dan lokaci yana ta kallonta yana jiran ta fara kuka sai yaga idanunta ko alamar hawaye babu banda wanda ta zubar dazu. Shirunta tsorata shi yayi yace "kice wani abu mana."
Murmushi take yi kamar bata ji abinda ya fada ba ma.
"Jikamshina"
Jiran amsarta yake na nuna masa bacin rai da bai fada mata tun da wuri ba.
"Lokacin da ka fara sona tausayina kake ji ko kuwa sona kake fisabilillah"
"I love you Asmauna, and I will always do"
Tayi sassanyar ajiyar zuciya "duk macen arziki bata da burin da ya wuce idan zatayi aure ta kai budurcinta gidan miji. Jikamshina na rasa wannan damar har abada. Na fada tarkon shaidan har ya zamana ina da shaidar da duk wanda ya kalleta bazai manta da cewa Asmau ta taba bayar da jikinta ga mutumin da babu aure a tsakaninsu ba. Ni abar gudu ce da kyama a cikin mutanenmu. Bani da sauran daraja da kima a idon jama'a sai dai kawai ayi min kara. Da wannan ciwon nake kwana nake tashi kuma dashi zan koma ga Mahaliccina. Idan aka kallemu sai an sake. Ga wadda tayi cikin shege nan. Amma duk da wannan nakasar ta rayuwata kake sona saboda Allah. Ka rike 'yar da bata da uba na aure a matsayin taka. Ka nuna min ina da sauran darajar da zaka iya zama dani. Shine yanzu zaka ce zaka barni saboda rashin haihuwa.?"
Sai da yayi tunanin haka zata iya faruwa. Ba yanzu yake jiye musu ba. Kada ayi aure hakurinta ya kare musamman da yake tana da kuruciya.
"Matar Jikamshi, haihuwa ba abin wasa bace nakasa ce mai girma. rashinta ya kashe aure da yawa. Ya bata soyayyar shekaru da dama. Ya hana zaman lafiya tsakanin kishoyoyi"
Innalillahi wa inna ilahi rajiun take karantawa tun da ya fadi maganar don ta sami kwarin gwiwar magana. Kada tayi kuka ya tursasa mata amincewa da bukatarsa.
"Sayar da jiki a waje ko haihuwa babu aure shine babbar nakasa a rayuwar musulmi. Amma rashin haihuwa ta sunna ba nakasa bace. Jarabawa ce daga Allah Madaukakin sarki. Shi kadai Yasan ladan da Ya tanadarwa masu hakuri da rashi. Ita fa aba ce da duk kudin duniya bazai siyeta ba kuma marasa ita su kadai suka san halin da zukatansu ke ciki sai Allah. Amma mutuncina da ba fin karfi akayi min ba wurin rabani dashi kaga bani da uzuri. Taka jarabawar kenan, hakuri da ita sai yasa Allah Ya yafe maka dukkan zubunanka Ya baka aljannah. Ni kuwa fa? Ni na jawowa kaina. Bani da masaniya Allah Ya yafe min ko kuwa...."
Sai yanzu ta soma kuka mai cin rai. Wayyo Allah son zuciya. Babu wanda yayi musu dole ita da Abubakar suka biyewa shaidan. A rayuwa bazata taba manta groups da ake hira ko litattafan da ake rubutawa ba masu sanya mace budurwa taji bukatar namiji, mai aure idan mijinta na nesa taji ta kasa hakuri. Duk su biyun idan shaidan na kusa ga kaddara sai su fada ga halaka. 'Yan mata nawa ne a sanadiyar karamce karance irin wannan suke burin samarinsu su dan taba wani bangare na jikinsu ko don su rage musu shaawa? Da yawansu sun koshi da tarbiya kuma suna kokarin kamewa. Rana daya tsautsayi zai sa suci karo da irin wadannan masu yada alfashar shikenan komai nasu sai ya lalace.
Col. Ishaq ji yake kamar ya tayata kuka. Tausayi tare da son Asmau ke karuwa a zuciyarsa. Bude baki yayi zaiyi mata magana ta riga shi
"Jikamshina idan kaki aurena saboda rashin haihuwarka ka cutar dani kuma ka raina son da nake maka. Idan so kake ka rabu dani saboda Allah zanyi hakuri. Amma idan wannan ne dalilinka to ka sani *wallahi* bazan taba rabuwa da kai ba. Har zaka iya son auren mace irina sai nice kake tunanin zan gujeka"
Dafe kansa yayi saboda ta daure shi da zantukanta. Ya kara yarda Asmau mace ce tagari wadda kaddara ta gifta mata. Yana jin kukanta har ransa. Saukowa yayi daga kan kujerar da yake ya zauna a kasa dan nesa kadan da ita.
"Look at me please"
Babu musu ta dago kanta. Wannan idan su Umma suka ganta sai a zata wani mugun abin yayi mata ai.
"Har mamaki nake yadda kika shiga zuciyata Matar Jikamshi. Ban taba jin zafin so da tsoron rabuwa kamar akanki ba. Ina tsoron muyi aure ki kasa hakuri da lalura ta. Kada son da muke wa juna ya koma zaman hakuri kawai a nan gaba. Kada kiga kamar saboda abinda ya wuce a baya dolenki ki zauna dani duk yadda nake. Kiyi tunani sosai, bani da niyar cutar dake."
Idonta cikin nasa abinda bata yi ko bisa kuskure suka hada ido tana saurin dauke nata.
"Gobe Baba yace yana son ganina kuma nasan so yake yaji wa na zaba cikinku. In sha Allah sunanka zan fada masa. Idan kaki amincewa zan hakura nasan Allah bai kaddari aurenmu ba. Amma bazanyi aure ba har abada. Bazan yarda na kara son wani ba balle na kara haduwa da irin ciwon da nake ji a zuciyata yanzu."
Tana gama magana ta tashi tayi hanyar da yasan zata kaita cikin gidan sosai. Kasa motsin kirki yayi sai daga baya ya tashi duk jikinsa babu kwari. Wannan ciwon kan ne ya sake dawo masa ya tashi jiri na dibarsa. Yana son Asmau amma yana tsoron kada Allah Ya kamashi da tauye mata hakki. Da kyar ya iya zuwa bakin motarsa. Duhu duhun da yake gani yasa ya dauko wayarsa ya kira Yassar.
Bai dade ba ya fito ya tsorata da halin da yaga Col. Ishaq. Mukullin motar ya bashi yace don Allah Ya kaishi asibiti daga nan ya ajiye shi a gida amma kada ya fadawa su Umma balle Asmau. A rude Yassar yaje yace da Umma zai raka Col. Ishaq unguwa tace to sai sun dawo.
Asmau kuwa daki ta wuce ta fada kan gado tana kuka. Bata da abinda zata sakawa Jikamshi dashi sai aure da yi masa tsantsar biyayya. Zata aure shi ta nuna masa haihuwa ba ita kadai bace aure. Ita dai tana karawa maaurata jindadi ne. Amma idan Allah Ya hanaka to bai hanaka saurin jindadin rayuwa ba. Bai hanaka lafiya da arzikin ibada ba. Ko yanzu kukanta na tsoron kada yaki amincewa ne.
Da Umma taji shiru bata fito ba tace karshenta tana can tana kuka Ishaq ya gaya mata ya fasa.
*****
Da Yassar ya kaishi gida yaso tambayarsa abinda ya faru amma ya kasa saboda yanayin da yake ciki. Sunyi sallama ya bashi kudin mota yaki karba ya tafi gida da wasiwasi.
*****
Washegari Asmau tayi wanka da wuri tana jiran zuwan Shemau da Jafar. Tun bayan asuba ta tura musu text tana rokon su zo kafin taje gidan Baba. Umma dai addua take yi mata a zuci da fatan Allah Ya kawo mafita cikin sauki. Tayi mamakin ganinsu Shemau suka ce Asmau ce ta neme su. Suma hankalinsu ya tashi.
Hajjo na bacci lokacin suka shiga dakin Umma bayan ta hada Amatullah da kayan wasa don kada ta dame su. Duk yadda sukayi da Col Ishaq ta fada musu. Babu wanda yayi mamaki domin kuwa duk sunji komai a wurin Umma. Maganarta ta karshe ce ta dauki hankalinsu da tace shi zata cewa Baba ta amince ta aura.
Shemau tace "Asmau baki da hankali ne. Rashin haihuwa da kuruciyarki ba abu bane da ya kamata ki bari soyayya ta rufe miki ido a kai."
"Yaya Shemau ki tuna shi fa da 'yata ya ganni kuma yace yaji ya gani. A irin rayuwata ko 'ya'ya yazo dasu yanzu ai dole na hakura na aureshi tunda nima ina da ita. Duk yarinyar da ta tafka kuskure irin nawa wallahi zabinta ya zama ragagge a rayuwa. Dole idan tana son jindadi ta hakura da wasu abubuwan. Sharrin zina kenan. Yanzu ko auren mai duka nayi indai ina son rufawa kaina asiri dole na hakura na zauna dashi ko na fito duniya ta zageni ace kila ma halin da nayi a baya ya sake kamani dashi."
Umma tace "yanzu ke kina ganin zaki iya zama dashi a hakan. Bai fiye miki ba ki amincewa Qasim."
"Umma ba karamar alfarma yayi mana ba da yace yana sona. Babu wata alaqa da ta hadamu fa. Rana tsaka ya ganni kuma yace yaji ya gani duk da abinda ya faru dani. Sai nake ganin bai dace ba naki shi saboda rashin haihuwa. Abinda bashi yayiwa kansa ba. Yaya Qasim kuwa nafi alakanta da tausayinmu yake ji "
Jafar ji yayi Asmau ta burgeshi ba kadan ba. Kanwarsa ta ga rayuwa ta kuma hankalta da ita. A yanzu tasan so ba shine samu ba. Duk yadda ake son haihuwa a aure indai tana son kanta da arziki dole ne ta ajiye son ranta ta karbi abinda Allah Ya azurta dashi
"Umma ni dai ina ganin indai tana sonsa kuma ta amince da lalurarsa a barta ta aureshi. Wallahi shi da Qasim bazamu manta dasu ba har abada. Duk da sun san komai game da ita suke son aurenta. Umma mu akayiwa alfarma ba mune zamuyi musu ba. A matsayina na yayan Asmau na bawa Col. Ishaq ita har abada" ya fada da murmushi.
Shemau ma ta fahimci kanwarta yanzu ta kai masa duka a baya "to sannu waliyyin Asmau. Ai dai akwai manya gaba da kai"
Nasiha mai ratsa jiki Umma tayi mata tare da bata goyon baya. A karshe tace "bamu ba wasu ma zasu hankalta idan suka ji labarin rayuwarki Asmau. Auren Ishaq zai iya rage miki gori da surutan mutane saboda wasu zasu ga kema kinyi masa hallaci. Shi Qasim sai a bashi hakuri tare da godiya domin ba karamin mutuntamu yayi ba. Allah Yayi muku albarka. Allah Ya kara kare mana zuria daga fadawa ga tarkon shaidan Ya yafe mana kurakuranmu baki daya."
"Amin" suka amsa su uku. Bayan azahar kuwa da Asmau taje gidan Baba bata yi nauyin baki ba ta sanar dashi wanda ta amince wa. Sai da yayi ta tambayarta zata iya zama dashi babu haihuwa. Amsarta ko sau daya bata canja ba tace eh. Addua yayi mata shima da fatan alkhairi. Da rayuwarta bata zama yadda take yanzu ba bazasu yarda da wannan aure ba. To amma yanzu sun san cewa ba karamin arziki Allah Yayi musu ba da ya bata manemi kamar Col. Ishaq Muhammad Jikamshi. Zai rufa mata asiri itama ta rufa masa. Allah Mai hikima ne kuma Masani akan komai. Zuwa Shanono ya kama shi dole zai je yasan irin dabarun da zaiyi a warware maganar Qasim batare da zumunci ya sami rauni ba.
*****
Su Asmau na zaune a tsakar gidan Kawu Garzali suna hira ta dauki waya ta turawa Jikamshi text.
_Na zabi Jikamshina a matsayin miji. Na yarda na bashi amanar sauran rayuwata. Na amince babu wanda nake so sai shi kadai. Ina fata zaka amince ka karbi soyayyata. Kuma ina so ka sani cewa ba tausayinka nake ji ko auren alfarma nake nema ba. So ne kawai, Matar Jikamshi sai da Jikamshinta_
*****
Zaune yake gaban Hajiya tana yi masa nasiha saboda damuwa da tayi masa yawa yaji shigowar text din. Yana karantawa ya dago kai ya kalli Hajiyarsa yana murmushi mai burgewa "Hajiya ki fadawa su Kawu su shirya zuwa nema min auren Asmau"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽49
Batul Mamman💖
Bayan tayi text din duk da hira suke mintuna kadan sai ta duba wayar ko ya aiko mata da reply. Ganin babu bai sa taji komai ba. Naci zata kafa masa har sai ya amince don dole. Wannan shine abinda ta yankewa kanta zata yi masa. Haka kawai bazata bari Jikamshinta ya kasance cikin bacin rai da sadaukarwa ba shi kadai saboda wata lalura da bai isa ya yayewa kansa ba. Wani guntun murmushi tayi ta sake daukan waya. Kafin ta fara rubuta text din taji an kwashe mata da dariya. Shemau da su Sabira ne a wurin. Asmau ta dago kai tana kallonsu. Maijego Zubaida da Ainau shayar da yaransu suke amma suna tayawa wurin yi mata dariya. Ta dan ware ido
"Me aka yi?"
Sabira tace "me kuwa akayi banda kallonki da muke yi. Gaskiya wannan sojan ya cancanci a kira shi da gwarzon namiji."
Ainau ta amshe "ai baku ga komai ba ma. Sai suna tare wallahi, abin sai ya baki shaawa. Shiyasa tuni na canja takuna wurin Yaya Umar. Muma mun zama Laila Majnu"
"Lallai yaran nan kun koshi, a gaban nawa ko" Shemau ta fada amma fuskarta a sake.
Sai yanzu Asmau ta gano wai da ita suke dariyar. Ta murmusa "to me nayi yanzu"
Wannan karon Zubaida ce tayi magana "ke kadai kike ta kallon waya kina murmushi kamar yana kusa dake. Don Allah a bawa Qasim hakuri idan ya rabaku karshenta ku kamu da ciwon zuciya."
Aka sake yin dariya. Shemau tace "da dai Asmau akwai kunya amma yanzu sai a hankali. Akan _Jikamshinta_bata gane su waye a kusa. Allah Ya kaimu lokacin buki a kaiki tun asuba kafin mu laluba muji amarya ta kai kanta.
Suna dariya Asmau ta turo baki "amma kun gama dani wallahi. Kuma har yanzu da kunyata fa. Daga yau na dena magana ma"
Sabira tace "Yi abinki Asmau, idan mutum na sonka kaima ka nuna masa baka da tamkarsa. Bari nima na kira Abban Abid mu dan taba hira. Yau tunda muka fito banji muryarsa ba" sai da ta gama magana ta tuna da Shemau. Tashi tayi da gudu ta shige daki. Tsakar gidan kuwa sai dariyar su Asmau.
Sai yamma suka tashi tafiya gida. Hankalinta kwance kamar an cire mata dutse a zuciyarta. Duk da bata ga amsarsa ba ta gama yanke shawarar jurewa har sai ta shawo kansa ya amince. Ainau da Shemau tare suka tafi. Ita kuma ta bi Jafar da yazo daukar Sabira suka ajiyeta a gida.
A bayan motar tana zaune da waya a hannu Amatullah tana wasa da Abid. Text din da bata sami damar yi ba dazu ta rubuta ta tura masa.
_Don Allah kace kana sona....zanyi kuka fa._
Daga bakin gate suka sauka don lokacin har anyi magariba suna hanya. Tana tura gate din ta ga wata bakuwar mota a kusa da ta Umma. Bata damu da sanin mai motar ba ta shiga ciki tana sauri taje tayi sallah. Amatullah tace "Ummina muyi yige yigen shiga falo"
Ta bi 'yarta da murmushi "idan na riga me zaki bani?"
"Zan siya miki mota idan na giyma. Kuma zan kaiki Makkah da Madina"
"Idan kuma kika rigani me kike so?"
Amatullah tayi dariya harda alamar tunani "zaki goyani yau har nayi bacci."
"Kin girma fa Ama ga nauyi"
"to bazan ci abinci daye ba. Don Allah Ummi ki goyani" ta karashe da buga kafa.
Asmau tace "naji shirya 1, 2....." kafin ta kai 3 Amatullah ta kwasa a guje. Dariya tayi kawai tabi bayanta. Yarinya sai son goyo bata san ta girma ba. Kyaleta tayi sai da ta kusa shiga sannan ta bita da gudu. Tana sane ta bari ta rigata.
Da dariyarsu shiga falon Amatullah tana cewa ta riga. Asmau ma ta shigo da dariya sai tayi turus daga bakin kofa. Kamshin turarensa ta fara ji kafin idanunta su sauka akan Jikamshi. Shadda ce ruwan kasa a jikinsa ga hula tayi masa kyau. Ganinsa tayi kamar an kara masa girma, ya gyara sajensa da gashin baki. Shima din ita yake kallo sai da suka hada ido tayi saurin sauke kanta a kunyace. Ko kadan bata yi tsammanin ganinsa a gidansu ba. Balle da taji shiru bai amsa sakonninta ta hanyar waya ko text ba.
Dan gyaran murya taji sannan aka ce "muna kusa fa" ta kalli wurin da sautin ya fito. Subhanallah...
Umma, Hajjo da Ismail ne zaune a wurin. Daburcewa tayi gabadaya tace "uhmm sauri nake banyi sallar magariba ba."
Bata jira amsar kowa ba ta shige ciki gabanta na tsananta bugu. Tana jiyo dariyar Ismail din yana tsokanar yayansa.
*****
Bandaki ta fada ta watsa ruwa da sauri tayi alwala. Sai da tayi sallah sannan ta koma gaban madubi ta shafa mai da gyara fuska. Ba kwalliya ta tsananta ba amma tayi kyau. Ta rasa kayan da zata saka kada su Umma suce kwalliya tayi saboda ganin Jikamshi. Sannan kuma bata son mayar da na jikinta don a gaskiya tayi suyar nama dasu. Karshe wata jallabiya ta dauko baka mai adon duwatsu pink. Tana son rigar sosai, Anti Bintu ce ta siya mata da taje Zaria. Mayafin rigar tasa tayi nadi sannan ta sami wuri ta zauna tana tunanin yadda zatayi ta fita.
Umma da kanta ta shigo ta danyi murmushi ganin Asmau na kallon kasa. Allah mai iko, sai Ya sanya musu son juna duk da lalaurar dake tattare da kowanensu. Wannan ma kadai ya ishi bawa aya. "Asmau kije ku gaisa mana kin barmu da baki kuma kinsan naki ne"
A kunyace tace "ni bansan zasu zo ba."
"Bari na sallame su to. Ina jin gaishemu suka zo gara su tafi tunda mun gaisa."
Dago kai tayi da sauri amma bata ce komai ba. Umma tayi murmushi kawai ta godewa Allah. Cikin ikonSa 'yarta ta sami farinciki a rayuwarta. "Gulma to tashi kada waccan akun ta cika su da surutu"
Sai da Asmau ta jira Umma ta bar dakin sannan ta fito falon. Da sallama ta shiga. Ai kuwa Amatullah ta gani tana ta zuba zance tana bawa Ismail labari yana biye mata suna dariya. Hajjo kuma da Jikamshi suke tasu hirar.
Tana shiga Ismail yace "yauwa ga amaryar tamu. Hajjo ke fa an sallameki. Daga yanzu duk abinda zaki fada ba ganewa zaiyi ba"
Wayyo Allah, ji tayi kamar ta juya da gudu. Ismail na tsokanarta shi kuma gogan ya wani zubo mata idanu yana kallonta yana lumshe ido kamar mai jin bacci.
"Babu inda zani, ni har akwai masu nuna min soyayya ne. Allah Ya jikan Malam amma muma a zamaninmu fa ba'a cewa komai"
Ismail yace "Allah Hajjo?"
"Hmmm kaidai bari dannan." Ta fada tana jinjina kai. Yau fa tunda ta tuno Malam to wanda bai sanshi ba zai sha labari. Allah Sarki Malam Yahya. Hajjo baki shi kuma shiru shiru. Shiyasa akayi zaman lafiya duk da rigimarta.
Daurewa Asmau tayi ta gaishe su. Ismail ne kawai ya amsa, Jikamshi tashi yayi yana dubanta. "Muje na baki amsa ko"
Hajjo tace "'yan nema kuyi a gabana mana."
Da muryarar nan tasa me sa Asmau jin tafi kowa dace yace "ga Ismail nan ya fini iya hira da tsofaffi. Ni ga tawa nan." Ya nuna Asmau.
Amatullah ta taso tana kumburi "Babana kace fa yau da ni zaka yi wasa banda Ummi"
"Duk yau taki ce. Yanzu ma sako zan bata kinji princess. Zauna a wurin sabon Baba kafin na dawo"
Asmau na kallonsa ya fita. Ismail yayi mata alama da hannu tabi bayansa. Sai da tayi dariya a hankali sannan ta fita. Hajjo tace "oh, yaran zamani baku da ta ido. Wannan yayan naka Sama'ila yana wani mici mici da ido sai kafirin iya saye zuciya."
Ismail sai dariya "ko dai za'a koma da ne ki zabe shi ki bar Malam"
"A'a fa, Malam yafi kowa. Wannan alakoro ne Asmau ta samu. Ni kuwa nawa shine gangariya"
*****
Wurin motar Ismail da suka zo da ita ya kaita. Barin dreba ya bude ya nuna mata kujerar yace "zauna"
Zata tambaye shi ina zai zauna ta ga ya tafi hanyar kofa inda wasu kujerun roba suke farare ya dauko daya. Sai a lokacin ta zauna kafafunta a waje shi kuma ya dasa kujerar daga gabanta ya zauna kafarsa daya kan daya.
Ji tayi kamar wadda aka rufe a cikin keji duk ya cike wurin. Ta kasa kwakkwaran motsi.
Wayarsa taga ya dan turo gabanta ta karanta abinda ke rubuce a ciki. Text dinta ne na biyun da ta tura masa kafin su iso gida.
"Ina sonki Matar Jikamshi, don Allah kada kiyi kuka. Hawayenki yana da tsada. Ba a gaban kowa zaki zubar dashi ba. Amsar ta gamsar dake ko na kara wata?"
Murmushin da yake so daga gareta take yi amma ta kasa dago kanta. Kunyarsa ke karuwa sosai a zuciyarta. Ga wani nishadi da take ji kamshin turaren Jikamshinta ya baibaye wurin gabadaya.
Dama yasan irin wannan kalamai sai a text. Tana ganinsa take komawa bebiya. Ranakun da take ajiye kunyarta kuwa sai taga alamun zata rasa shi ne.
"Dago kanki na baki amsar sakonki na farko. Shine babban dalilin zuwana"
Dan kadan ta iya daga kan tana sauraronsa.
"Matar Jikamshi Allah Yayi miki albarka. Bani da wata kalma da zan iya nuna miki matsayinki a zuciyata. Sakonki ya shigo a lokacin da komai ya rikice min. Haduwata dake zuwa yau hadi ne daga Allah. Har abada nasan cewa kinyi min abinda mata da yawa bazasu yi ba. Ni kuma saboda son kai na amince maimakon na dage na rabu dake ki auri wanda zaki haihu dashi..."
Bude baki tayi zata yi magana ya sanya yatsansa a saman lebensa "shhhh, kada kiyi magana. Text dinki yace komai. Ki barni nima na fadi nawa. Banyi miki alkawarin cewa idan munyi aure shikenan duk wani bacin rai da damuwar da kike dasu zasu kau dari bisa dari ba. Amma Matar Jikamshi zanyi kokari naga na kare hakkinki kuma na kyautata rayuwarki har karshen rayuwata. Abinda kike gudu tun farkon da na gabatar miki da soyayyata bance bazai taba faruwa ba. Kowane mutum yana da damar fadin son ransa duk da kiyaye bakin shi yafi akan fadar magana mara alkhairi. Ki sani a dangina ko naki, makota ko abokan arziki dole watarana sai anyi miki gori a gabanki ko bayan idonki wannan bani da haufi akansa. To ina so duk lokacin da aka fada miki maganar da ta shafi rayuwarki ta baya kuma bana wurin bare na kare miki ki sani cewa Ishaq yana son Asmau. Ki sakawa ranki akwai wanda zaki zo kiyi kuka a gabansa ya rarrasheki, akwai wanda yake kaunarki saboda Allah yake fatan kasancewa abokin rayuwarki har a aljannah."
Ba sai na fada ba Asmau kuka take yi sosai saboda yadda kalaman Jikamshi ke ratsata. Shi kanshi a raunane yake idan ya tuna cewa duk su biyun suna da abin fada a rayuwarsu.
"Abu na karshe Matar Jikamshi ina so don Allah kiyi hakurin zama dani. A duk lokacin da kika ji anyi haihuwa zuciyarki ta kwadaitu da son ina ma kece maijegon to ki tuna cewa samu da rashi na Allah ne. Da kudi na bayar da haihuwa da wasunmu sun sayar da komai nasu don suji kukan jariri a gidajensu. Ki godewa Allah kina da wadda zaki kalla a matsayin tsatsonki. Ni bani da wannan kuma na yarda na karbi kaddarata. Ina fatan hakurin da nake da wanda zaki zo ki tayani muyi ya zama silar samun rahmarmu a wajen Allah"
Da gaske Asmau take kuka. Abinda ake gudu ya riga ya faru. Allah Ya kara kare sauran 'yan uwa musulmi. Ji take duk duniya idan ba da Jikamshi ba bazata taba iya rayuwar aure da wani ba. Shi kanshi idonsa yayi ja amma sai ya daure yace "kinsan dai ba'a daura mana aure ba don Allah ki dena kukan nan. Nafi so ki tara shi sai ranar da idan kinyi zan daukeki na...."
Da kukan nata da jikakkiyar fuska ta dago kanta tana murmushi tare da dora hannunta irin yadda yayi a lebenta "shhhhh Jikamshina kada ka karasa ko na gudu"
Yayi murmushi "ina sane na turaki cikin motar don kada kice zaki gudu. Share hawayenki kinji Matar Jikamshi. Kada Umma ta hanani aurenki, kullum nazo sai kinyi kuka."
Tissue din gaban motar ta zara tana goge hawayen yana fada mata wuraren da kwalli ya bata. Tace zata duba madubin motar yaki yarda. Haka ta goge suna kallon juna suna dariya.
Sun danyi hira yake ce mata sunyi magana da Umma yana ganin nan da wata uku za'a saka musu rana. Umma tace akwai bikin Dijan Anti Bintu wata biyu masu zuwa wanda shima lokacin yaso ayi aurensu. Yasan kafin nan ya gama gyaran gidansa.
"yanzu da Umma kayi zancen saka rana?"
"Na lura kin mayar dani mara kunyan karshen zamani. To Ismail ne ya fada musu. Ni shiru nayi ina ta sunkuyar da kai irin yadda kike yi"
Dariya take yi wanda hakan yake sanyaya masa zuciya. Yana jindadin ganin ya faranta mata. Sun fi awa daya a wurin batare da sun san lokaci ya wuce ba. Ismail ne ya fito da Amatullah a bayansa. Haka nan Allah Ya dora masa son yarinyar nan. Shi bai ki ba wallahi Asmau tace ta bar masa ita.
Suna zuwa gaban motar Amatullah tace "Ummi kinga sabon Baba ya goyani."
Col. Ishaq ya tashi tsaye ya sauko da ita daga bayan Ismail sannan ya dorata a cinyarsa.
"Idan banyi da gaske ba naga alama zaka yi min kwacen 'ya"
"Colonel ai na gama da kai. Ka taho nan sace zuciyar Umminta da dadadan kalamai ni kuma ina nawa yakin a kanta da kayan kwadayi. A takaice dai yanzu nine baban"
Asmau ta rufe ido tace "Yaya Ismail kada muyi haka da kai"
Jikamshi yace "gara ki kira Musaddiq yaya da wannan. Shifa bai san ya girma ba. 'ya'ya biyar amma idan yana barkwanci kamar mara iyali."
"Kada ka zubar min da girma mana soja. Yanzu dai gaskiya Madam ta damu ban koma gida ba tun fitar safe. Ummin Amatullah taimaka ki sallame shi mu tafi. Don ma na fada mata Yayanta na rako zance yau da an hanani tuwon dare"
Ta fuskanci da gaske Ismail mutum ne mai barkwanci. Jikamshi ya katse mata tunani da cewa "haka suke daga shi har matar tasa. Gidansu kamar gidan wasan yara"
"Allah Sarki kace ina gaisheta"
"Fada mata da kanki dai" Ismail ya ciro wayarsa ya kira Aisha matarsa. Da gaskiyar Jikamshi kuwa don da gaske Aisha tayi ta janta da hira da wasa kamar ta santa. Karshe tayi ta jaddada mata ta rike amanar yayansu. Ita dai Asmau sai dariya kawai. Bayan sun gama wayar sukayi sallama dasu. Jikamshi kamar kada ya tafi. Ba don dare yayi ba kuma dai yakamata Ismail ya tafi gida yau da Umma sai ta koreshi da kanta.
A hanya ne ya dubi kaninsa yace "nagode Ismail da yadda kake yiwa Asmau da Amatullah "
Idonsa na kan titi yace "Colonel nine da godiya da ka yafe min maganar da nayi maka rannan. Duk da bana ganinsa amma na tabbatar shaidan ne irin masu hada fada tsakanin 'yan uwa ya murde min harshe na fadi abinda banyi niyya ba"
Murmushi dan uwan nasa yayi "zaka fara ko, kada ka damu komai ya wuce a wurina in sha Allah. Ka fadawa su Dahiru idan zasu sami lokaci karshen sati sai muje Jikamshi ayi magana dasu Kawu"
*****
Ranar Juma'a da yawancin ma'aikata ke tashi da wuri Col. Ishaq da kannensa maza suka tafi garinsu, Jikamshi a Katsina garin Dikko...Katsinawa kunya gareku ba tsoro ba. Kafin tafiyarsu dama Hajiya ta riga ta fadawa Yayanta da kuma kanin mijinta komai game da Asmau a waya. Kamar yadda yayi tsammani bai sami goyon baya sosai daga garesu ba. Wani kawunsa ma cewa yayi indai saboda rashin haihuwa ne yasa zai auri karuwa, karuwar ma mai 'ya to akwai zawarawa a gari masu yara ya zaba a cikinsu don Allah Ya aura amma kada ya gurbata musu dangi. Su da suka je yin kwana biyu basu sami dawowa ba sai litinin. Col. Ishaq sai da ya taba rashin kunya aka sami daidaito tsakaninsa da Kawunan nasa da manyan Gwaggoninsu. Daga karshe ma dai harda wa'azi da nasiha ya hada. To anyi sa'a da yake ana ganin girmanshi gashi kuma da dan abin hannunsa sai suka gama fadansu suka amince zasu taho Kano nan da sati biyu. Kamar yadda ya saba ya hadasu da alkhairi kafin ya tafi. Wannan karon harda kari don kada su bashi kunya ma.
*****
A bangaren su Asmau kuma washegarin da Jikamshi yaje gidansu Qasim yazo. Ya nuna mata ya janye batun aurensu kuma yana mata fatan alkairi a zamansu da Col. Ishaq. Taji kunya sosai tace "Yaya Qasim kayi hakuri da hukuncin da na yanke a matsayin zabin Allah. Bazan taba mantawa da abinda kayi mana ba. Duk da kaine babban abokin Yaya Abubakar amma hakan ba shine yake nufin sauran su gujemu ba. Tun ranar da ya rasu ban kara jin duriyar kowa ba sai taka. Nagode Allah Ya baka mace tagari kamilalliya."
Yayi mata murmushi "babu wata godiya mata zaki nemo min kawai."
Itama tayi murmshin ga dan hawayenta "to In sha Allahu zan nema maka kuwa"
"Kada ki dauka wannan abin zai shafi zumuncinmu Asmau. I am always here for you. Ki daukeni dan uwanki wanda zaki iya fadawa matsalolinki. Shi kuma soja tunda yayi min fin karfi ki fada masa aure bazai yiwu ba sai ya kama kafa dani."
"An gama ranka ya dade" ta fada zuciyarta wasai. Alhamdulillah dama bata so su rabu ana jin haushin juna.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽50
Batul Mamman💖
Tun daga wannan lokacin tsakanin Matar Jikamshi da Jikamshinta wata sabuwar soyayya ke tashi da shakuwa. Duk wani labarin rayuwarsu da basu sani ba a da yanzu sun fayyacewa juna. Komai nasu abin shaawa sannan suna soyayya a tsaftace. Irin hirar nan da zata jawo budurwa da saurayi su fara sakin layi har a kai ga jin sha'awar kusantar juna sun nesanta kansu da ita. Kuma duk da haka idan kaga yadda suke sai sun burgeka. Wannan ita ce soyayya ta gaskiya. Duk wata hira mai tado sha'awa sunanta batsa kuma tana cikin jerin abubuwan da suka kusanci zina indai ba ga ma'aurata ba wanda Allah SWT Ya umarcemu da mu nisanta kawunanmu da ita. Allah Ya kara shige mana gaba.
*****
Bayan sati biyu kamar yadda suka yi alkawari kawunnan Col. Ishaq suka zo daga Jikamshi. Haj Lubabatu ta shirya musu tarba mai kyau sai da suka ci suka koshi sannan sauran kannensa maza suka yi musu jagora zuwa gidan Umma. A nan din ma tun safe ake shirin zuwan nasu. 'Yan uwa da abokan arziki sun taro. Alh Adamu ma da tasa gayyar duk don a taru a rufawa juna asiri. Baki kam sun ga karamci kuma sun yaba. Matsalar dai itace haihuwar Asmau kafin aure. Amma tunda dan nasu yace yaji ya gani dole su bi yarima su sha kida. Dubu dari suka bada wanda yasa su Baba nuna a rage. Wani cikinsu dan tsoho yace ko kwandala bazasu rage ba. Dansu yace lallai abinda zaa bayar kenan ko sama da haka. Kawu Garzali sai murna yake. Allah Yayi Asmau zatayi aure kuma zata auri wanda yake matukar sonta. Adduarsu Allah Yasa soyayyar ta zarce har gidan aure. Taro ya tashi cikin mutunta juna aka yi sallama suka tafi.
*****
Asmau kuwa da wuri ta fita amma ta bar Amatullah a gida. Hankalinta a kwance wannan karon kana ganinta zaka san amarya ce mai murna da dokin lokacin aurenta. Da kwatance saboda sababbin gine gine ta isa gidansu Walida tsohuwar aminiyarta. Har kofar gidan adaidaita ya kawota. Tana sauka a kofar gidan Walida ta fito daga makotansu. Hada ido suka yi sai suka tsaya kallon kallo kowacce tana zubar da hawaye. Duk su biyun abubuwa da dama suke tunawa wanda suka wargaza musu rayuwa. Asmau ce ta fara yunkurawa kafin ta karasa itama Walida ta taho cikin sauri suka rungume juna. A bakin kofar gidan suka fashe da kuka sosai suka rike da juna. Mutane kuwa sai kallonsu suke yi. Sai da suka dan nutsu Walida ta ja hannunta suka shiga ciki. Antin Walida matar babansu na zaune tana yankan farce suka shigo. Murna ganin juna suke sosai. A firgice ta tashi tana nuna Asmau.
"Wa nake gani kamar Asmau?"
Walida tace "ita ce Anti"
Ta karewa Asmau kallo sannan ta tabe baki "to ina abinda kika haifa. Ai na jima da jin labarin kin dawo Kano da dane ko 'ya ni ban rike ba. An gama yawon ta zubar an dawo gida."
Murmushi Asmau tayi, irin wadannan maganganun 'yan uwa da yawa da Jikamshinta sun fada mata dole ko taki ko taso sai tayi hakuri dasu. Kuma sanin halin Antin na kwarewa wurin rashin mutunci yasa bata dauki abin da zafi ba. Walida ma da a da tasan cewa bata shiru, idan matar nan tayi mata ramawa take suyi ta cacar baki kamar kishiyoyi shiru Asmau taga tayi. Ta kama hannunta suka shiga dakinta. Kan wata kujera suka zauna Walida tace
"Ashe rai kan ga rai 'yar uwa? Na fidda rai da sake haduwa dake wallahi"
"Kiyi hakuri Walida. Na dan jima da dawowa amma na rasa me zamu cewa juna idan muka hadu. Har ga Allah abinda ya faru dani shekarun baya kika gujeni yasa ban kara nemanki ba"
Walida ta share kwalla "ki yafe min Asmau, na cutar dake da na zama sanadiyar koya miki dabi'un da ba naki ba. Ba haka kawai na gujeki ba amma..."
Asmau tace "kada ki damu. Yaya Qasim ya fada min kema duk abinda ya faru dake. Mu kuma haka Allah Ya rubutu mana tama jarabawar" da kuka ta karashe maganar. Suka taru su biyu suna yi babu mai rarrashi. Asmau na tuna rasuwar Abubakar da cikin da aka gane tare da ita a ranar da ya rasu. Ita kuma Walida tana tuno ranar da mahaifinta ya kamata da saurayi ya zura hannuwansa cikin rigarta. Wa'iyazu billah wadannan 'yan mata bazasu manta da sharrin social media ba.
Da suka gama kukan ne suka bawa juna labarin irin gwagwarmayar da suka sha. Walida tayi murna da jin zancen auren Asmau sannan tayi ta kallon hotunan Amatullah a waya tana mita ba'a zo mata da ita ba. Itama ta bawa Asmau labarin irin takunkunmin da babanta ya saka mata saboda jin labarin cikin Asmau. Karshe ma ko karatun jami'ar bai bari ta kammala ba yace sai tayi aure. To gashi shekaru shida babu auren babu karatun sai zaman gida da zuwa islamiyya. Matar gidan ta sami yadda take so wurin fadawa Walida maganganu sai dai ta dena ramawa saboda yanzu babanta bai damu da lamarinta ba. Indai ba aure tayi ba shi baiga amfaninta ba. A wannan zaman gidan kannenta biyu 'ya'yan Anti sunyi aure har sun haihu. Bata yawo daga islamiyya sai gida sai kuma abinda ya zama dole. Samari kuwa kamar anyi ruwa an dauke. Babu mai zuwa yanzu.
Asmau tace "dukkanmu munga irin abinda ake gudu a waya da social media. Allah kara rufa mana asiri duniya da lahira."
"Amin Asmau, amma ai kinfini ganin tashin hankali. Kullum ina miki addua Allah Yasa kada rayuwarki ta lalace da kika bar gida. Da farko a social media na fara watsa hotunanki cigiya kafin Baba ya karbe wayar. Rabona da wayar arziki na manta"
Yini suka yi suna hira sai bayan laasar lokacin da Asmau ta tabbatar an gama taron gidansu tayi haramar tafiya. Jikamshi yayi mata waya yace to ta fara shiri sauran kadan fa ta karasa zama matarsa yana fatan za tayi shiri mai kyau kafin zuwan lokacin. Yaso zuwa daukarta ma da kansa amma kamar yadda suka faro da bin komai yadda ya kamata sai ya hakura. Wani lokacin ko babu social media idan budurwa da saurayi suka kebe su kadai a mota sanyin AC yana dan ratsasu sai shaidan ya fara kawo musu hari. Ko kadan babu burgewa kice wai duk inda zaki saurayinki shine yake kaiki ya dauko ki. Ki duba da kyau kiyiwa kanki adalci watarana ko dan yaya sai anyi abinda bai dace ba ko da kuwa taba hannu ne. Yau da gobe ai tafi karfin wasa.
******
A cikin wata daya Col. Ishaq ya dage sosai ana ta gyaran gidansa. Duk inda yake bukatar canji kamar kayan cikin toilet irinsu baho da sink an canza an saka komai sabo. Haka ma a kitchen da su kofa. Ga fenti sai da ya kira Asmau ta fadi irin kalar da take so. A bangarensu ma Umma ta tashi tsaye sosai. Daga Asmau yanzu babu kowa a gabanta sai Yassar. Su Shemau ne suka je suka gano gidan aka zo aka fara siyayya. Dole ita ma ta dage ta fito da 'yarta ta. Gado ma ready made ta siya guda biyu tare da sauran kayan gida. Shemau, Jafar, Kawu Garzali da gidan Mama duk ba'a barsu a baya ba. Kowa akwai abinda ya dauki nauyi don ganin cewa Asmau ta sami nutsuwa a rayuwarta. Ita kam sai son barka da yi musu addua.
Saura kwanaki biyar su tafi Zaria bikin Dijah. Umma da Anti Bintu basa zama kullum sai an fita siyayya saboda ana gama na Dijah da sati hudu za'ayi na Asmau.
Jikamshi yazo yiwa Asmau sallama tafiya ta kamashi Warri zaiyi sati uku. Zaune yake ya dora hannuwansa akan cinyarsa sannan ya tallabi fuskarsa dasu yana kallon Asmau. Kallon ya takurata tace "Jikamshina zan tashi fa idan baka dena kallona na ba"
"Tashi ki tafi ban hanaki ba. Amma ki sani zan je na sami 'yan matan Warri na kalla son raina"
A shagwabe tace "don Allah ko da wasa ka dena fadin haka. Kada kasa na kasa bacci yau"
"Shine kike son hanani baccin? Daga gobe fa zanyi sati uku ban sakaki a ido ba. Ji nake kamar a daura auren nan na tafi dake. Idan mun dawo sai ayi bikin, kada kice wani abu nasan kema haka kike so ko Matar Jikamshi" wannan lumshe idon yake mata. Ita kuwa ta soma dariya.
"Wane irin aure ne amarya da ango zasuyi tafiya bayan an dawo ayi biki."
Yace "to kawai idan mun dawo mu wuce gidanmu ko. Tsayawa bikin duk bata lokaci ne."
Dariya Asmau take yi kawai. Jikamshinta yau sai wani marairaicewa yake.
"Kada ka damu ni dama ba wani biki nake so ba. Zuwa za'ayi ayi ta kallona. Na fadawa Umma ayi komai a rana daya. Bayan daurin aure mata kadan su zo a kaini."
Col. Ishaq ya gane sarai dalilinta na yin haka. Yadda mata ke son biki amma tace bazatayi komai ba saboda surutun jamaa. Dena wasan yayi yace "Matar Jikamshi ko me kika yi na fada miki dole za'a sami masu magana. Bakiji ance Dan Adam mai wuyar gane hali ba. Idan kinyi biki ace baki da kunya ko makamancin haka, idan kin ki biki ace ko dan bikin nan batayi ba don kada mutane su je. A wurin Dan Adam bazaka taba fita ba. Saboda haka biki da akeyi abu na lokaci daya zukatan masoya suji dadi na makiya su fashe...."
Da har ta fara kwalla sai yanzu tayi dariya. Shima biye mata yayi.
"I am a soldier Matar Jikamshi. Dole nayi aure irin na sojoji. Su Safiyya suna can suna tsare tsare kamar yadda su Ainau suke yi. Zamuyi aure da biki kamar kowa kinji ko. Duk wanda ya fada miki mara dadi ki rinka tuna ranar asabar din da zaki tare a gidana. Ranar da Jikamshinki zai nuna miki matsayinki a rayuwarsa. Wannan ya isheki maganin duk wani bacin rai. Look forward to being Mrs Jikamshi a zahiri." Gyara zama yayi bayan ya gama maganar yana son ganin yanayinta. Kasa take kallo tana wannan murmushin da ta saba idan tana jin kunyarsa. Bai barta haka ba sai da ya tabbatar mata lallai bikinsu za'ayi taro kamar na kowa. Masu farinciki da 'yan saka ido kowa ana gayyatarsa. Addua zasu cigaba Allah Ya kare duk wani tashin hankali da abin ki har ayi a gama lafiya.
Da zai tafi Asmau harda kuka. Tana ta cika masa baki sati uku ba komai bane zata iya jurewa ko basu hadu ba akwai waya. Hoto ya rinka daukarta fuska a kumbure saboda kuka. Da ya shiga mota ya tayar tace "Jikamshina don Allah kada ka kalli kowace mace. Ai ni kadai na isheka ko?"
Ya murmusa "anya kuwa? A haka kinsan bazan tabbatar ba sai nan gaba. Idan rabon na hadu da kishiyar matar jikamshi ne a can sai ki tayani addua"
Ranta a bace ta zamo dankwalinta ta kasan mayafin da ta lullube kanta ta jefe shi dashi. Dariya yayi mata ya dauki dankwalin ya dora akan fuskarsa tare da rufe idanu. Muryarsa can kasa yace
"Ina son kamshinki"
Kunya taji ta mika masa hannu "don Allah ka bani"
"Haba yarinya, dama ba roka nayi ba kika bani. Yanzu kuma yazo kenan. In sha Allah ke dashi sai a gidanki. Love you, kiyi min adduar tafiya"
Tana kallo ya rataya dankwalin a wuyansa yaja mota kamar baya jin magiyar da take masa. Dafe kai tayi tana tunanin me zata ce idan aka tambayeta dankwalin. Tayi sa'a babu wanda ya kula. Kafin ta kwanta ya turo mata hotunansa ya ware dankwalin akan fuskarsa ya rungume da hannuwansa. Ranar har tayi bacci shi take tunani.
Da sassafe ta kira shi bayan sun gaisa tayi ta jero masa addu'o'in neman tsari da sa'ar tafiya. Dadi kamar me haka ya rinka ji yana saka mata albarka. Haka suka yi ta waya yana hanya har suka isa.
*****
Kwanci tashi sun je Zaria an sha biki lafiya. 'Yan uwansu na Wushishi sun zo sosai suna cewa saura zuwa Kano bikin Asmau. Bayan an kai amarya Kaduna da suka dawo da daddare kafin su kwanta Anti Bintu ta kirata dakinta. Ita dama bata je kai amarya ba kamar yadda al'adar bahaushe take. Wata jarka karama ta dauko ta bawa Asmau.
"Ga wannan zuma ce da aka yi mata hadi mai kyau. Kullum a kalla kisha cokali biyu. Kada ki sakata a gaba kiyi ta sha da yawa. A hankali zata ratsaki." Ta hado mata da wasu kullin magani duk na sha ne. Tace da kanta ta hadasu kayan amfanin jiki ne.
Tunda ta fara bayani kan Asmau a kasa. Da farko kunya take ji daga baya sai hawaye. Anti Bintu ta rude "menene kuma Asmau?"
"Anti yanzu a matsayin budurwa fa zanyi aure amma ....."
Fadawa tayi jikin Anti Bintu ta rungumeta tana kuka. Itama ta biye mata tana kukan tana rarrashi. Umma dake bakin kofa tana jinsu itama da nata hawayen. Babu wani abu a duniya da zasu bawa Asmau ya dawo mata da budurcinta. Shi kam idan ya tafi ya tafi kenan. Shiyasa ake so mata mu kiyaye. Kada ki sayar dashi a waje wasu suci kudinki da sunan zai dawo. Halittar Allah da 'yan dabaru na mutane basa taba zama daya.
"Ki dena kuka Asmau. Shima Ishaq din yasan komai ba yaudararsa kika yi ba. Amma dole ki gyara jikinki saboda rayuwar aure zakiyi yanzu. Ki cire yawan tunani don Allah. Bashi da fa'ida. Yawan kukan nan tamkar baki godewa Allah ba da ya ni'imtaki da samun masoyi. 'Yan mata da zawarawa nawa ke kwadayin irin wannan sai gashi ke Allah Ya kawo miki don Ya saukaka miki matsalolinki na baya."
Haka ta dauki jakar da magungunan jiki a sabule. Yadda 'yan mata ke rawar kafar shan magani idan bikinsu yazo sai gashi ita jin abin take kawai wani iri. Yanzu haka za'a daura auren budurwa mai 'ya. Allah abin godiya.
*****
Sun fi sati da dawowa Kano sannan Col. Ishaq ya dawo. Yana zuwa gida wanka kawai yayi tunda yayi sallah ko abinci ya kasa nutsuwa yaci ya fice. Hajiya ta girgiza kai, Allah Ya kara hada kawunansu su zauna lafiya.
Asmau ta zauna ta hada abinci mai rai da lafiya wanda ya dace da tarbar bako. Bata taba yi masa abinci ba. Idan yazo lemo kawai take bashi da snacks saboda tana kunyar irin wannan. Yau ma Umma ce ta bawa Yassar kudi akan a siyo abubuwa na abinci yau kwadayi take ji. Tasan yau Ishaq zai dawo amma saboda kunya Asmau bazata yi yunkurin yi masa wani abu daban ba. Itama kuma hakan yafi mata. Bata taba bawa 'ya'yanta kofar idan saurayi zai zo ayi ta girke girke kamar maigida ba. Sai kaga 'ya'ya basa kunyar iyayensu. Bayan ta gama Umma tace "ki dibarwa Ishaq mana kinsan matafiyi kila yayi sha'awa." A kunyace ta diba ta ajiye masa nasa.
Da ya iso Amatullah ta dafe shi tana ta murnar ganinsa. Yayi musu tsaraba ta doya da sauran abubuwan kudancin kasarmu. Idonsa kyam a bakin kofa har Asmau ta fito. Ji yake inama dai anyi auren. Yayi kewarta sosai, ga wani haske da kyau da ta kara saboda mayuka da sabulun gyara jiki da Zubaida ta hada mata da kanta. Itama ganinsa ba karamin dadi yayi mata ba. Tana zama yace
"Yi a hankali kada na narke da wannan kallon da kike yi min"
Sam ta kasa boye murnarta shiyasa yake ta tsokanarta. Da ta gaji da kunyar ta soma ramawa. Yaci abinci ya kuma yaba da iya girkinta. Daga nan ne suka dasa hira har ta fada masa cewa ita dasu Umma zasu je Azare da Jos nan da sati daya.
"Wannan tafiyar dani za'ayi in sha Allah. Dole naje har gida na godewa mutanen da suka taimaka wurin kare min martabar iyali."
"Kuma har gidan Uwargida zamu je. Umma tace dole Zubaida ta ga mahaifiyarta"
"Tabbas uwa komai munin halinta ba'a canja mata suna. Kila kiga rabon shiriyarta ne idan taga 'yarta tayi aure har da 'ya'ya. Ki fada min da wuri ranar da aka yanke yin tafiyar sai na shirya da wuri."
Ta danyi ajiyar zuciya "Yaya Qasim ma yace zashi"
Murmushi Jikamshinta yayi "Matar Jikamshi bazan taba rabaki da Qasim ba. Ina son halayensa kuma nasan mutum ne nagari. Ko jiya munyi waya dashi. Yasan Asmau matar Jikamshi ce wannan ya isheni kwanciyar hankali. Ke dai Allah Ya kaimu muje mu dawo a fara biki "
ABINDA AKE GUDU🙆🏽51
0 comments:
Post a Comment