Shirin tafiya sosai suke yi. Umma ta nemi Shemau da Jafar su kawo abinda ya sauwaka wanda zasu kaiwa mutanen Azare da Jos tsaraba. Duk da bata san Zulaiha ba amma ta yaba da taimakon da tayiwa Asmau. Sune suka rufawa 'yarta asiri ba don haka ba Allah kadai Yasan irin rayuwar da zata tsinci kanta a ciki yanzu.
Shemau dai katan din taliya hudu ta kawo da maggi. Shi kuma Jafar galan din mai da katan din macaroni bibbiyu. Suna zaune a falo ana ganin kayan tana saka musu albarka. Idon kuka sai da tayi sana'ar tata kafin tayi godiya. 'Yan uwanta sun rufa mata asiri. Bata san mata nawa bane irinta a duniya wadanda kyama da hantara ta dangi ta kara tura su ga aikata sabo. Umma tace "na bawa Yassar ya siyo min buhun shinkafa biyu sai a bawa su Rashida daya ita ma Zulaiha daya."
Asmau ta kara yi musu godiya "nima zan duba cikin kayan da kuka bani wanda ban dinka ba na daukar musu."
"Hakan yayi kyau" inji Hajjo "kai Yassar ina naka ne? Ka zauna sai washe baki kake yi ban ga wani abu daga gareka ba"
"Hajjo ni da ban fara aiki ba ina ni ina gudummawa. Ai ma na kyauta tunda zan tuka mota." Sai ya kara fadada murmushinsa "ashe da Yayanmu za'ayi tafiyar."
Shemau tace "haka Umma ta fada min. Ni fa har kunyar Qasim nake wallahi. Nutsuwarsa tayi yawa. Gashi dai bashi zata aura ba amma ko kadan bai bari hakan ya zama sanadiyar bacin zumunci ba"
Yassar ya dan tabe baki "au shima zuwa zaiyi? Ni da mutumina nake yallabai baban Amatullah"
Umma ta rike haba "oh ni Bara'atu, nagode Allah a namiji kazo Yassar da ina tsammanin sai kunyi fada da yayarka. A take takenka da gani zaka iya kwacen saurayi. Idan Ishaq yazo gidan nan aka yi rashin sa'a kana nan kayi ta rawar kafa kenan. Jiya ina jin ku kana mita wai Asmau taki fitowa da wuri"
Dariya suka yi, Yassar ya sosa keya "wallahi Umma burgeni yake yi. Nifa gaskiya idan an gama bikin nan zan nemi short service nima na zama soja. Baki ga ba idan yana tafiya ko magana....kai"
Hajjo tace "anya Bara'atu kin tabbatar yaron nan namiji ne ba mata maza ba?"
Su Jafar sai dariya Yassar ya tashi yana tura baki. Shi ba'a kyauta masa ba. Yabonsa fa kawai yayi saboda ya burge Asmau. Da taga anyi masa taron dangi sai ta koma bayansa tana kare masa. Yace "rabo dasu sai sun ga matar da zan aura ma sis. Kowa sai ya yaba harda tsohuwa mai ce min mata maza" aka sake dariya.
******
Lokacin da Col. Ishaq ya fadawa Hajiya zaiyi tafiyar nan dasu Asmau ta dage itama sai taje.
"Ke da kike fama da kafa Hajiya"
"Kada kaga laifina. Ba wai na karyata abubuwan da Asmau ta fada mana bane amma ance gani ya kori ji. Kai sonta kake da aure ni kuwa son 'ya nake mata. Ina so idona ya gane min inda ta rayu kafin haduwarku. Ina son samun hujja ga mutanen da tuni suka fara kawo min sukar auren nan. Da yawa cewa suke karuwanci tayi lokacin da ta bar gidansu. Bazan tura kowa a dangi ba bare a sami na gutsiri tsoma. Kai dai kawai ka hadani da dreba idan motarka ta cika"
Ji yayi jikinsa yayi sanyi. Mutum ba'a iya masa. Mahaifiyarsa kuma da gaskiyarta. Da yana da yayye kila su zata wakilta tasan bazasu yi mata karya ba. Kuma gara taje din akan ta tura wani.
"Shikenan Hajiya Allah Ya kaimu. Bilkisu sai ta koma gidan Safiyya ko su Dahiru"
"Tare zamu je kasan rabonta da gida tun haduwarmu da Asmau. Ita ma gara taje ta kwana biyu kafin bikin tunda ta gama jarabawa"
Da ya kira Asmau ya fada mata ko kadan bata nuna damuwa ba. Har zuciyarta dadi taji ko babu komai idan akwai wani zargi da yake ransu zasu ganewa idanunsu cewa ba karya tayi ba.
Ranar da zasu tafi sammako suka yi. Yaran Shemau duka ta kawosu gidan Umma zasu zauna da Amatullah da Hajjo. Asmau da ita taso tafiya Shemau tace gara ta barta ta fara sabawa da rashin ganinta saboda idan anyi biki sai kamar bayan sati biyu ko uku za'a kawo mata ita. Ta dai amince don babu yadda zatayi ne. Basu saba rabuwa da juna ba. Wani abin ma sai sunje kwanciya ta mayar da kanta yarinya ta biyewa Amatullah suyi ta hira tana sauraron shirmenta. Burinta ta dasawa kanta babban matsayi a zuciyar Amatullah yadda nan gaba yarinyar bazata nuna mata kyama ba idan taji tarihin haihuwarta. Soyayya kuwa zata nuna mata hadda wadda take tunanin da Abubakar yana raye shima zaiyiwa 'yarsa. Allah Sarki bai ma san da cikin ba bare haihuwarta.
Sun gama loda kayansu a motoci aka fara shiga. Asmau, Bilkisu da Zubaida suna motar Jafar da yaran Zubaidan. A motar Umma kuma kawu Garzali ne a gaba Yassar zai tuka. Baya ita da Mama ne. Shi kuma Col.Ishaq drebansa ne zai tuka su. Yana gaba a baya kuma Hajiyarsa da Shemau.
Tun zuwansu gidan ya samu Asmau ta dan fito kafin a fara shiga mota "yanzu ina kallo zamu je wuri daya amma ba motarmu daya ba? Wannan tsarin baiyi ba gaskiya ki dawo motarmu Shemau ta koma ta Jafar. Wa zan rinka satar kallo ta madubi"
Zaro ido tayi "sai na zauna kusa da Hajiya don rashin kunya kai kuma kana kallona?"
Yace "to meye a ciki? Naga auren danta zakiyi karewa."
Ta kawar da kai tana murmushi "ni dai kayi hakuri don Allah kada a fito ka fara cewa na dawo motarku. Kada ka sani jin kunyar da ban shirya ba".
"Dama kina da kunyar ne? Ana shirin tafiya kin kasa hakuri kin fito ki ganni"
Asmau ta rasa me zata ce sai bude baki kawai da tayi cikin mamaki. Shine fa yayi mata waya yana magiyar ta zo ya ganta.
Dariya yake mata don yasan ya kureta "rufe bakin kada ya makale a haka"
Ta dan juya ido "gara ya makale kowa ya huta"
"Tuba nake Matar Jikamshi, shi bakin nan naki da kike gani ba karamin mahimmanci gareshi ba. Idan ya makale an cuce ni."
Ta soma dariya ganin yadda ya kara marairaice fuska "meye amfanin bakin banda cin tuwo. Idan ya zauna a haka kaga na dena shan wahalar bude shi"
Yace "da gaske kina so na fada miki kadan daga cikin mahimmancin bakin Matar Jikamshi"
Wani jan zancen yake yana kallonta kasa kasa. Ko baa fada ba tasan ko me zai fada karshenta sai taji kunya shiyasa ta saka hannuwanta biyu ta toshe kunnenta tana ja da baya.
"Ka barshi kawai na yafe. Wani ilimin ba sai na sani ba"
Yayi murmushi mai kyau "kaji min yarinya. To ba abinda kike tunani zan ce ba. Shiyasa nace kinfi karfina dama"
Sosai Asmau taji kunya ta koma ciki da sauri tana jiyo dariyarsa.
Yanzu da suka shiga motocinsu zasu tafi ji yake ina ma motarsu daya. Ko yaya suka juya su kama juna suna kallon junansu.
*****
A titin Zaria road suka hadu da Abdulhalim da Qasim a motar Qasim din. Daga nan suka mika sai Azare.
Tun fitowarsu Zubaida ana ta hira a mota amma jikinta yayi mugun sanyi. Ba don Umma tayi mata nasiha sosai ba ita ko kadan bata son tuna asalinta. Yanzu duk mutanen nan kowa sai ya ga a irin kazantar da ta tashi. Addua take Allah Yasa kada su je su tarar da irin tsofaffin yan tashan nan da basa tsoron Allah masu zuwa wajen Uwargida a dakin. Sai su zo suce wai banda tsufa ya fara zuwar mata duk tafi yaranta iya aiki. Wani sa'in ma idan taji kudi sosai komai kuruciyar mutum bata jin komai take bashi dama. Koda yake ina wata kunya ga mace irin wannan.
Motarsu ce a gaba Zubaida tayiwa Jafar kwatance. Su Asmau ma jiki ya mutu suka dena hirar saboda ganin yadda yanayinta ya canja. Asmau tana zancen zuci tace kada Allah Ya kawo ranar da Amatullah zata kyamaceta irin yadda Zubaida take yi a yanzu.
Gidan yana nan yadda yake ko fenti ba'a canja ba. 'Yan bakin kasuwa suna kallon abin mamaki. Motoci irin wadannan a kofar gidan Uwargida. Kuma gashi harda mata bare ace wasu kadangarun barikin ne suka zo neman 'yan matan gidan.
Asmau da Zubaida aka rasa me fara shiga. Ita Zubaida ma hawaye take yi har Kawu Garzali ya gani. Da sauri yazo ya karbi baby dinta mai suna Shuaibu suna kiransa Aiman sannan ya rike hannunta suka fara shiga. Zuciyar Asmau ta tsinke, yanzu haka Jikamshi zai shiga gidannan. Allah Yasa kada shi ko Hajiya wani yace a fasa auren.
Zuga guda suka shiga da sallamarsu. Matan a gaba maza a bayansu. Kaya ne tarkace kala kala a tsakar gidan. Wasu matan na wanki wasu suna girki. Kowacce da sabgar gabanta. Kadan a ciki Asmau ta gane. Duk barin abinda suke yo suka yi kallo ya dawo kan baki. Daga kofar dakin Uwargida Bulayi ya fito. Mutumin da ya fara kawota gidan nan. Dama can a dattijo ta san shi. Yanzu kuwa tsufa ya kara bayyana a tattare dashi. Yana kokarin zura takalmansa ne idonsa ya sauka akan Zubaida. Fuskarsa ba karamin mamaki ta nuna ba yace "Zuby???"
Ranta a dagule yake dama ta harare shi "Zubyn uwarka" a duniya yana cikin mutanen da ta tsana. Duk yarinyar da aka kawo gidan sai yayi amfani da ita kafin kasuwarta ta bude.
Maimakon ta ga bacin rai a fuskarsa sai ya washe baki cike da fara'a yace
"Shegiya ita ce kuwa, kina nan da bakinki kamar reza"
Cikin dakin ya koma da sauri har yana tuntube. Suna jin muryarsa yana kiran Uwargida tazo ga Zuby ta dawo. Zubaida ta ji muryar mahaifiyarta tana cewa "Bulayi kada kayi min wasan da zai tayar min da hawan jini"
"Yasin da gaske nake, bari na kamaki muje wajen"
Kunya ta kara kama Zubaida, yanzu haka zasu fito hannu da hannu kamar wasu mata da miji a gaban mutanen nan masu daraja a idonta. Dukkansu kallon kofar suke zasu ga wannan Uwargidan ga wadanda basu taba ganinta ba. Bulayi ne ya fara fitowa hannunsa rike da sanda yana cewa "yi hankali da matattakalar kofar"
Rike da sanda ta fito wacce Bulayi ya daga mata daga waje yana mata jagora. Tana nan da tsayinta fuskar nan tayi wani irin dabbara dabbara saboda mayukan bleaching da taji a baya. Sanye take da tubarau baki wuluk irin na makafi. Tana mika hannu cikin iska alamar lalube tace
"Zuby kina ina?"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Zubaida bata san lokacin da ta saki hannun Kawu Garzali ba ta tafi wurin babarta tana kuka
"Mama makancewa kika yi? Wayyo Allah na, kinga ni fa jikokinki na kawo miki nayi aure. 'Ya'yana hudu. Mama ki bude ido ki gansu don Allah"
Uwargida tayi dan murmushi tana rungume da 'yarta. Hawaye ya zubo mata tana ta shafa fuskar Zubaida tace "Ashe zamu gana kafin na mutu Zubaida. Allah nagode Maka. Ina yaran? Wane dan albarkan ne ya rufa min asiri ya aureki? Kinga yadda Allah Ya mayar dani ko. Karyar karuwanci ta kare bani da wani mataimaki sai Allah sai Bulayi da bai gujeni ba"
Zubaida ta kalle shi sai taji kunyar zagin da tayi masa. A yadda taga mahaifiyarta ta kara tsufa da yankwanewa sai ta godewa Allah da Umma ta dage lallai sai tazo. Bulayi ne yace "Uwargida tare da baki take fa. Ina jin surukanta ne mu shiga daga ciki ko kuma ina zuwa dai" dakin ya koma ya dauko tabarmi gudu uku. Kamar hadin baki Qasim da Col. Ishaq suka ki zama. In da sabo tsayuwa ba komai bace wurin soja da dan sanda. Sai akayi dace kyamarsu tazo daya basa son zama a tabarmar da ta fito daga dakin matar.
Sauran dai sun zauna sannan Zubaida ta fara yi mata bayanin kowa. Yaranta kuwa sai da Uwargida tabi tana shafasu tana binsu da kiss a fuska. Manyan biyu mace da namiji dai kyankyaminsu suke. Tana yi suna gogewa duk ta yaba musu yawu. Da Zubaida tace tare suke da Asmau Uwargida ta mika hannu zata kamata. Balayi yace "Yar dabas kin canja Yasin. Jikinki duk ya murje kinyi fresh. Dama naso naga kama to kuma sai naga ta yanzu tafi ta da kyau da daukar ido."
Wani mugun kallo Col. Ishaq ya sakar masa wanda ya girgiza har hanjin cikinsa. Ba arziki yayi shiru. Asmau ta dan matsa gaba Uwargida ta kama hannunta.
"Nayi sanadiyar lalacewar 'ya'yan mutane da yawa Yar dabas, iyayenki har nan sun zo nemanki. Nagodewa Allah da baki kama sa'a kamar yadda naso ba. Hakkin wadancan shegun kadai ya isheni. Ni shaida ce akanki har kika bar gidannan namiji bai taba zuwa kofar dakinki ba. Ke kam kinji dadi 'yan uwa basu kyamaceki ba har Allah Yasa rayuwarki ta koma kan layi. Me kika haifa?
Tausayi Uwargida ta rinka basu. Asmau ta soma kuka saboda yadda ta tuna Uwargida da iya gayu duk girmanta. Yanzu kuwa sai da dauriya zaka iya zama kusa da ita saboda warin jiki. Su Umma sun gama gaisawa da Uwargida sai Haj Lubabatu ta dan yunkura zata tashi. Col. Ishaq yace "Hajiya kafar ce?"
Bata bashi amsa ba sai matsawa da tayi gaban Uwargida ta zauna kusa da Zubaida tana kare mata kallo. Kuka sosai ya kwace mata tace "Habiba"
Uwargida ta fara mika hannu inda taji kira. Rabonta da amsa wannan sunan tun ranar da ta baro garinsu. Hannunta har rawa yake tana ta mika shi ko zata kama mai kiran tace "wace ce don Allah, babu wanda yasan sunana sai 'yan garinmu"
Hajiya sai kuka ta kara shigewa kusa da Uwargida. Col. Ishaq ji yake kamar ya janyota. Me ya hadata da wannan matar. Hannuwanta duka biyu ta rike
"Lubabatu ce, Luban gidan Sarkin dorin Jikamshi"
Salati sosai Uwargida ta saka kafin ta rungume Hajiya. Babu kyama Hajiya ta rungumeta itama suka barke da kuka. Kowa sai kallosu yake. Matan gidan sun fito ganin kwaf Qasim ya daka musu tsawar da ta kidimasu suka bar wurin suna karo da juna.
Uwargida ta share majina da kasan zaninta tace "Allah mai iko, ashe zan sake ganin na gida. Luba ina Baba da Inna, ina 'yan uwana?"
Cikin kuka Hajiya tace "Liman da Inna sun dade da rasuwa. Yayarki Indo ma babu ita. Sauran 'yan uwanki duk suna nan an tara 'ya'ya da jikoki"
"Allahu Akbar, Allah Ya jikanku Baba, Allah Yasa sun yafe min kafin su rasu"
Tana kuka ta labarta musu yadda almajirin Liman yayi mata ciki ashe ma fyade ne yayi mata kuma ya gargadeta kada ta fada har ciki ya bullo. Babu uzuri ko neman ba'asi iyayenta suka tsine mata. Wannan kuskure ne babba. Yana da matukar amfani jurewa wajen kula da yara idan sunyi kuskure domin a toshe kofar gaba. Tunda ta fiti take aikatau da ayyukan wahala domin taci abinci. A haka cikin ya bare tana yawo a gari. A wani gidan aikinta ne a Bauchi maigidan ya kuma yi mata fyade da ta fada matarsa tayi mata duka duk da lokacin shekarunta sunyi gaba don da jima tana rayuwar kunci da wahala. Maigida ya karyata kamar yadda aka saba ji. Shine da ta fito ta sami uwardaki. Bata zubar da cikin ba ta haifi Zubaida. Da girmanta ta fara sana'ar karuwanci kuma tace ta gwada rashin imani kamar yadda mutane suka gwada mata. Sai shekaru biyu da suka wuce da ta kamu da lalurar ido tayu nadamar rayuwarta. Duk matan gidan sun dena bata kudin haya ga rashin abinci. Ta kare da bawa mutane shawara da su rinka taimakawa masu raunin imani da wadanda ke cikin matsanancin hali don gujewa samuwar karin mugayen dabi'u a cikin jamaa.
Su Mama duk anyi kukan tausayin labarin Uwargida da kuma dadin handala da Asmau tayi dacen haduwa da mutane nagari. Wannan kuma zamu iya cewa harda adduar da suke yi mata ba tsinuwa ko zagi ba. A gidan aka bar Zubaida da Kawu Garzali. Sun yanke shawarar idan zasu koma Kano a tafi da ita sai a kaita Jikamshi taga 'yan uwanta ko da basa maraba da dawowarta.
*****
Daga nan gidan Rashida suka wuce. Dama tasan da zuwansu. Sada ma yana gida yana jira ga su Abba duk an zama samari. Cikin gidan aka yi musu shimfida mazan kuma suna dakin nan da Asmau ta taba zama. Tana shiga gidan sai kuka da ta tuna lokacin da ta zauna ga ciki ga rashin iyaye a kusa. A falo taga Sada ya kalleta fuskarsa dauke da murmushi yace
"Asmau kece kuwa?"
Tana kuka ta durkusa har kasa ta gaishe shi. Sada ne mutum na farko da ya fara taimakonta a rayuwa sosai bayan Zubaida mai bata shawarar kada ta zabi gurbatacciyar rayuwa. Wurinsu Abdulhalim yaje inda aka ajiye musu kayan abinci. Sai da suka yi sallah suka ci abincin.
A ciki suma matan sallar suka yi aka ci abinci. Nan hira ta barke ana tuna baya ana kuka da dariya. Rashida tace "yakamata watarana muje kiga Yaya Tagwai fa"
Asmau tayi murmushi, Yaya Tagwai ai ta janyo mata kara shiga garari. Cikin yaran kuwa babu wanda ya tuna ta sai Abba. Sai da suka yi laasar a ranar dai suka kama hanyar Jos. Rashida da Sada sai lokacin biki zasu taho Kano.
Sun sha tafiya jiki kuma ya fada saboda zaman mota. Duka matan a gidan Mami akayi musu masauki sai gari ya waye zasu gidan Zulaiha. Asmau ta damu sosai da ita saboda dena samunta da tayi a waya. Col. Ishaq ne ya samarwa mazan masauki a cikin barikinsu na sojoji dake garin. Shi da Matarsa sai dare suka sami damar yin waya aka biya bashin soyayyar da ba'a yi ba a ranar.
Mami da yaranta sunyi kokarin karrama bakin Kano. Bilkisu sai murna anzo gida. Da safe wurin shadaya suka gama shiri aka dunguma zuwa gidan Zulaiha. Motarsu na tsayawa Asmau ta hango Humaira da karuwar roba a kanta cike da ruwa. Da sauri ta fito ta kira sunanta. Ai tuni Humaira ta saki robar ruwan ya kware a jikinta ta rugo da gudu ta dafe jikin Asmau. Sai ga kannenta suma duk ruwan suka. Yara sai murna suke suna tambayarta ina Ama. Kusan janta cikin gidan suka yi tawagarsu Umma suka biyo baya suna mamakin yadda yaran ke murna haka.
A durkushe bakin murhu tayi tozali da Zulaiha tana ta hura wuta tana tari. Tsaye a gefenta kuma Zinaru ce ta harde kafa tana masifa "malalaciyar banza, tun dazu hada wuta ya gagareki. Yanzu idan suka fito da me zasuyi wanka. Kinsan Gidado baya son ruwan sanyi...."
Zulaiha tace "Zinaru kiyi hakuri itacen ne mai danshi"
Tun a bakin kofar Asmau ta soma hawaye. Rayuwarta ta gyara ga Zulaiha cikin matsanancin kunci har yau. Duk ta kara figewa sai dan wuya kamar kazar mayu. Cikin sauri ta karasa shigowa tace "Zulaiha"
Tashi Zulaiha tayi da sauri itama ta nufo Asmau cike da murna da mamaki. Rungumar juna sukayi suna kukan yaushe gamo. Zinaru babu bakin magana saboda yadda gidan ya cika da mutanen da Asmau tazo dasu. Borin kunya ta soma da taga su Shemau na binta da mugun kallo.
"Haka ake tarbar baki kin tsareta a hanya kuna kuka. Ke Humaira maza shimfida tabarmar nan a rumfar babanku. Kai kuma Ali jeka ka taso babanku. Yau Asmaun da yake ta jira ta dawo"
Wata mace ce wadda da kadan zata girmi Humaira ta fito tana yatsina fuska.
"Hayaniyar me nake ji haka? Zinaru wannan banzar ta dafa min ruwan wankan ko kuwa?".
Zinaru ta galla mata harara zata bata musu harka. A yadda taga mutanen da shigar Asmau tasan akwai maiko. Har ta fara nadamar barin Gidado da tayi ya auro 'yar mutumin da ya bashi shago a kasuwa.
Zulaiha sai murna take ta shimfida musu tabarma da zannuwanta wankakku biyu don babu abinda zata basu su zauna. Basu zauna ba sai tausayinta da suka rinka ji. Zulaiha tana cikin mawuyacin hali. Yaranta kaf babu mai zuwa makaranta yanzu. Duk abinda ya rage mata dashi Gidado yayi aure. Watarana ya sha giya ya bugu yayi mata duka cikin jikinta ya bare. A yanzu haka babu irin wukakancin da basa gani ita da 'ya'yanta a wurin Zinaru da amaryar Gidado. Yi sukayi kamar basa ganin su Zinaru suka shiga hirarsu da Asmau da yan uwanta.
Col. Ishaq ba karamin haushinsa yaji ba bare da ya fito yana tangadi alamun mayen jiya bai sake shi ba. Ya dubi Zulaiha da take gaishe da su Umma. Wahala ta mayar da ita wata iri. Idan za'a bashi dama daga Gidadon har uwarsa sai ya kullesu.
Zulaiha tace "Ummi kinji dadi iyayenki sun yafe miki. Ji yadda kika koma nayi miki murna"
Hajiya ce ta ce "kema in sha Allah bazamu tafi ba sai mun hadaki da naki iyayen. Asmau ta fada mana komai game da rayuwarki"
Zibaru ta cafe "to tace muku tana bukatar taimako ne? Yarinya tana zaman auren soyayya da mijinta zaku shiga tsakani"
Qasim ya taso mata "idan baki kiyaye bakinki ba wallahi idan nasa aka rufeki babu wanda ya isa ya fito dake"
"Kaiiiiii, babar tawa kake yiwa tsawa" Gidado ya fada.
Darajar 'ya'yansa tasa duk mazan nan su Jafar, Yassar, Abdulhalim ga soja da dan sanda basu rufeshi da duka ba.
Zulaiha tana kuka tace "nasam bazasu yafe min ba. Shekarun da yawa. Kara na kaisu na zabi wannan rayuwar akan su"
Asmau tayi ta bata baki ta amince da shawararsu ta zuwa gida. Zinaru tace "idan kika fita a bakin aurenki"
Yau da Zulaiha ta sami masu tsaya mata bata ji maganar Zinaru ba tayi gaba 'ya'yanta na binta. Tana ji Zinaru tace Gidado ya sake ta. Dama me ya rage mata a auren nasa. Suna kallo duk suka fita. Zinaru tasan sun gama yawo domin kuwa korarsu zaayi daga gidan.
Zulaiha ke kwatance har suka iso bakin gate din wani makeken gida. Gida ne babba na gani a fada. Asmau tace cikin tsantsar mamaki "nan ne gidaku?"
"Nan ne Asmau" su Humaira ma duk mamaki suke wai daga nan mahaifiyarsu ta fito amma suke ganin kuncin rayuwa. Daga bakin gate kenan ma. Maigadi yayi musu iso akan cewa bakin mamanta ne. Jikinta a sanyaye suka shiga. Gidan ya kara fadi gashi ya dace da zamani. A wurin ajiye motoci ta hango kaninta da Alhajinsu. Zuciyarta tana dar dar Alhaji na hangota ya taho wurin da suke yana kallon Zulaiha. Shekarunta sha bakwai rabonta da gida. Ana jiran aji da wacce zai tarbi yarsa.
A hankali yace "sai yau uwata? Sai yau kika iya tunawa kina da iyaye?"
Abin tausayi Zulaiha ta fada jikin mahaifinta. Saboda yadda ta kode sai ka zata wa da kanwa ne ba uba da 'ya ba. Farinciki yake ji mara misaltuwa. Allah Ya karbi adduarsa 'yarsa ta dawo. Ba karamin fushi yayi da ita ba a da amma daga baya ya hakura sai dai yayi alkawarin babu mai zuwa gareta idan bata kawo kanta gida ba. A ciki ma wurin Innarta sai murna da kukan farinciki. Ga 'ya'yanta duk aka taru ana kallonsu. Duk 'yan uwanta suka taru ana murna. Alhajinsu yayi ta godiya ga su Umma da suka dawo da ita gida. Zama suka yi ana jajanta irin wannan hali da yara ke jefa kansu a dalilin soyayya sun yarda su rabu da kowa.
Asmau da Zulaiha sun zauna suna ta mayar da zancen halin da suka tsinci kawunansu a ciki. Ta yanke shawarar nema takardarta a wurin Gidado. Ita da aure kuma sai a aljanna. Asmau tayi dariya tace "zaki yi ne tunda na sami miji kema zaki samu in sha Allah" ta bata labarin Jikamshinta da bikinsu da za'a fara nan da sati biyu. Zulaiha tace biki kam da ita za'ayi komai in sha Allah. Ranar ma a gidan Mami suka kwana washegari sai Kano ta Dabo tumbin giwa. Biki ya gabato ana ta rabon kati
ABINDA AKE GUDU🙆🏽52
Batul Mamman💖
Daga 'yan uwan Asmau har na Col. Ishaq kowa shirin biki yake yi sosai. Ita har mamaki suke bata. Hala sun manta wace ce ita suke son yi mata biki irin wannan. Mutanen da zasu zo karshenta duk 'yan kallo ne wadanda zasu tafi da ita a baki. Sake yiwa Jikamshi korafi tayi akan haka yace shi bai taba damuwa da biki ba sai yanzu. Idan suka yi abin shiru shiru a gida shine mutane zasu sami na magana ace dama ansan dole ayi abin kamar na marasa gaskiya. Yanzu kuwa biki zasuyi su nunawa duniya farincikinsu da ni'imar Allah garesu. Dama tasan tuni yabi zugar su Shemau da Ainau shiyasa batayi mamakin amsarsa ba. Kwanansu biyu da dawowa Walida tazo gidansu har ta rakata karbo dinkunanta na fitar biki. Kokari suke su ajiye komai su mayar da kawancensu na da. Bata da niyar gayyatar sauran kawayen makaranta don basu nemeta ba a baya kuma dama bata dasu da yawa. Yanzu ma bata san ina yawancinsu suke ba. Duk wadda tazo bazai wuce bawa ido hakkinsa ba. Dinkuna sunyi kyau sosai. Kayan Amatullah ma ba'a magana. Musamman da yake kayan yara akwai daukar ido. Ita da su Mimin Shemau da Nanan Kawu Garzali mai sunan Hajjo duk anko akayi musu.
A bangaren gyaran jiki da abinda ya shafi lalle kuwa takanas Nasiba yayar Abubakar tayiwa aminiyarta ta Nijar magana. Massouda kenan, matar da a Nijar din ma ji suke da ita. Taji labarin Asmau kaf a wurin kawarta kuma ta tausaya mata shiyasa tayi mata hadin kayansu masu kyau da tsada sosai don tace Asmau dole a gyarata a saya mata kima a wurin mijinta. Shi kanshi mijin wani girmansa take gani. Duk mutumin da zai iya auren mace kamar Asmau lallai ya cancanci yabo da jinjina. Dole a taya shi da adduar Allah Ya saka masa da alkhairi bisa wannan kyakkyawan aiki da yayi. A wannan lokacin idan kaga Asmau zaka so sake kallonta. Duk da dama can ita bata sahun farare amma fatarta ta kara kyau sosai tayi haske. Kuma duk wahalar nan ta baya da tasa ta rame yanzu cima ta canja ga kwanciyar hankali. Shiyasa jikinta ya dan dawo ta ciko. Idan Umma ta kalleta sai dai tayi godiya ga Allah. Bata ma so tayi tunanin halin da Asmau zata fada da bata hadu da mutanen kirki ba ko ta dawo gida.
A dan tsukun lokacin Col. Ishaq ya damu sosai da rashin ganin Matarsa. Massoudan Nijar ta saba da irin wannan aikin na gyaran amare ta taho har gida ta murjeki da kyau. Saboda haka gidan Umma akayi mata masauki. Safe, rana, dare daga wannan turaren sai shafa wancan abin. Sau uku yana zuwa ana ce masa bazata iya fitowa ba. Ransa a bace a karo na hudu yace da Yassar idan bata fito ba wallahi bazai tafi ba komai dare.
Yassar yayi murmushi wannan soyayya tana daukar hankalinsa sosai "ka bani dan lokaci zan fito da ita. Umma da matar da Anti Nasiba ta kawo ne basa bari ta fita. Yau kwana biyar ko kafar gidan nan bata fito ba"
Fuskarsa sam babu walwala yace "Ka fadawa matar zan kara mata kudi amma gobe tayi shirin komawa garinsu aikin ya isa haka"
Yassar ya kalli yadda yake magana kamar bashi yayi ba ya wani hade rai. Shi dai ya sosa keya ya tafi. To Col. Ishaq ba irin wanda zaiyiwa tsiya bane da ya sha tsokana.
Yana komawa dakin Anti Bintu tace "Allah sarki bawan Allah, ya tafi kuwa?"
"Ya ce komai dare zai jira a gama"
Umma ta dan sha kunu "kaje kace ina wurin ka kasa fadin sakon, haba yayi hakuri mana. Nan da kwana hudu za'a fara bikin sai ya ganta. Kema da laifinki da baki fada masa lokutan da kuke farawa ba"
Asmau ta rufe ido kawai. Ba karamin kewarsa take yi ba ita kanta. Gashi tasan abubuwa sunyi masa yawa tunda bikin ya matso amma kullum kokarinsa ya ganta ko yaji dadi. Sai ake rashin sa'a idan yazo an fara shafe shafe ko turara mata jiki. Da daga ita sai Massouda ne kawai yadda suke wasa da matar ficewa zatayi ba'a sani ba. Amma kullum ba'a rasa babba da take jin kunya.
Har Yassar ya juya Hajjo ta dakatar dashi. Tace a goge jikin ta fita "gyaran nan ai saboda shi ake yi ko. Kwana nawa kullum yazo amsa daya ai babu dadi, sai kun sa ta fita a ransa. Ko dai ku barta ta fita ko kuma naje na kawo shi har dakin nan muga karshen gyara"
Umma kunya ta kamata ta fice daga dakin su Anti Bintu suna dariya. Auduga ake tsomawa cikin ruwan wani humra mai bala'in kamshi ana goge mata jiki. Sai da aka gama tas ta zura dogon hijab akan rigar jikinta ta fita don ko kwalliya an hanata sai ranar kamu.
*****
Tayi zaton yana waje sai ta ganshi a falo yana waya ga Yassar da Amatullah suma suna zaune. Cikin nutsuwa ta shigo falon Yassar ya dauki Amatullah a wuyansa suka fice.
Col. Ishaq ko sallama baiyi ba a wayar ya kashe yana kallonta. Ya ciri tuta a iya kallo mai kashe mata jiki. Ashe ita ma tayi missing dinsa sosai. Sai yanzu da ta ganshi taji sauki a ranta. Ko hoda babu a fuskarta kuma iya abinda yake iya gani kenan amma tayi masa kyau. Ga wani kamshi mai sanyi da bai san da yadda zai fasalta shi ba yana fitowa daga jikinta.
Kujeru biyu ne tsakanin wadda ta zauna da tashi ta gaishe shi amma da kai ya iya amsawa babu magana. Shirun nasa ya dameta tace "Jikamshina yaya, ko kayi fushi ne?"
Yayi sassanyar ajiyar zuciya "Matar Jikamshi harda muryarki ma gyarata ake yi? Tunanin nawa zan karawa matar da take gyara min ke nake. I just love the way you look. Matsalata daya ce hanani ganinki da ake yi"
Tayi murmushi "to kayi hakuri kaji _Jikamshina_ .
"Na fada miki idan zan tafi ki dena kirana da sunan nan amma kinki ji ko?"
Wani kalar tausayi yake mata tayi dariya sannan ta fara magana da shagwaba "haba Jikamshina yanzu fa na fito. Ko rabin ganinka banyi ba kake zancen tafiya"
"Kina wasa dani yarinyar nan. Nace ki dena kin cigaba. Kada kice banyi warning dinki ba dai. Bari na tafi, da na sani ban matsa sai na ganki ba yau"
Gabanta taji ya fadi ko dai yayi fushi da gaske ne. Tana ganin ya tashi itama ta mike tsaye jiki a sanyaye tace
"Me yasa kace haka"
Kallon da yake mata na ido cikin ido ne yasa tayi saurin kawar da kanta. Rage muryarsa yayi yadda itama bata jinsa sosai batare da ya bar kallonta ba yace "zan fada miki nan gaba. I love you. Sai da safe"
Kasa amsa masa tayi tana kallonsa ya fita. Ta koma ciki duk tana jin babu dadi. To me tayi masa haka da ko minti shabiyar batayi ba da fitowa ya tafi. Ko dai yayi fushi ne da gaske? Bazata iya jurewa hakan ba kwanaki kadan kafin aurensu. Dakinsu ta koma ta dauko wayarta zata tura masa text don bata son kira yana tuki. Hakuri zata bashi idan ma tayi laifi ne. Tana dauko wayar ta ga sakonni a whatsap dinta. Idan ba 'yan gidansu dasu Rashidan Azare ba babu wanda take chatting dashi sai Jikamshinta. Budewa tayi zata tura masa text sai taga nashi ne a sama alamun yanzu ya turo sakon.
_Allah Ya kaimu ranar aurenmu Matar Jikamshi. Ranar zaki san irin matsayin da Allah Ya baki a zuciyar Ishaq. Kada ki fassara tafiyata da komai, idan na dade tare dake *kamshin matar jikamshi zaiyiwa jikamshinta illah* Ji nayi kamar na tafi dake._
Asmau ta karanta sakon yafi a kirga tana murmushi ita kadai. Ko a yanzu ace zaiyi mata kishiya ta tabbatar zuciyarta zata iya bugawa. Duk wannan kalaman nasa da iya nuna kulawa ace ya nunawa wata matar bata san inda kishi zaiyi da ita ba. Adduar son kai tayi a zuciyarta. Allah Yasa Jikamshi nata ne ita kadai....
*****
Washegari da azahar sai ga Zulaiha a Kano ita da su Humaira, Muhsin da sauran 'ya'yanta. A bakin kofa suka rungume juna suna tsalle kamar wasu yara ita da Asmau. Yara na murnar ganin Amatullah. Gida mai dadi ba Zulaiha ba hatta yaranta sun dan murmure. Kayan jikinsu kuwa ya isa ya fada maka cewa babanta wani ne. Don ko gidan Mama da Asmau take yiwa kallon arziki sosai bai kai na mahaifin Zulaiha ba. Kaddara da rabon 'ya'ya ya kaita auren Gidado. Dreba mahaifinta yasa ya kawosu tare da kanwarta itama sunanta Asmau suna kiranta Ma'u.
A tsarin bikin ranar Juma'a za'ayi Kamu da walima wanda gidan amarya ne suka dauki nauyi. Washegari asabar a daura aure sannan bayan magriba ayi Sword Crossing sai kuma ranar lahadi ayi yini a kai amarya.
Yadda su Shemau suka ci burin kawata kamun ayi biki mai kayatarwa wasu mata suka dauko masu shirya biki da duk wani abu na bikin kamar abinci da harkar decoration. Ya da kanwa ne Aisha da Zainab Maiturare. Tunda suka ji sunan ango har ragin kudi suka yi musu sun ce ai su kannensa ne wannan biki na yayansu ne saboda haka zasu zage damtse wurin yin abinda za'a yaba.
Rashida tazo itama da yaranta da kanwarta Harira. Yaya Tagwai ma ba'a barta a baya ba. Da ta shigo gidan harda kukata tana bawa Asmau hakuri da bata tausaya mata ba ta koreta. Sai a lokacin suka daidaita da Hajjo. Mutanen Wushishi da amarya Dijah wadda ta kafawa mijinta naci duk sun zo. Gida kam yayi albarka don ya cika da 'yan uwa da abokan arziki. Asmau gidan Jafar ta koma ita da Zulaiha. Rashida tana tare da Zubaida a nata gidan inda take kula da Uwargida. Sai bayan biki zasu je Jikamshi.
Sabira ce ta kai Asmau wani salon aka gyara mata kai gashin nan yana ta kyalli sannan aka gyara kafa da hannu. Ta kalli Sabira tace "yanzu banda iyayi har hannu ma ana gyara shi. Na zata sai masu saka farce ake yiwa"
"Ummin Amatullah yanzu gyara ai ko'ina ake yiwa. Matan da ake cewa suna kwacen miji a waje ba wata tsiya suka fimu ba sai gyaran da rashin kunya. Mu kuma Hausawa komai sai mu ce Allah Ya sauwake nayi kaza bayan kuma gidan mijinki kike"
"Kuma fa gaskiya ne, shiyasa naga Yaya Jafar indai abu ya shafeki wallahi baya kyashi ko kadan. Ashe gyara ne da sauran sirrikan da zanzo ki bani. Muma Allah Yasa mu dace"
Suka yi dariya, Sabira tace "ai dacewa dai kin gama. Wallahi ki rike baban Amatullah tsakani da Allah. Irin yadda yake sonki kadai ya isa ya nuna miki cewa Allah Yana jin adduar bayinSa. Abinda ya rage kawai ki bi duk wata hanyar kyautata masa yasan cewa shima ya auri mai sonsa."
Ummy mai salon tana mata gyara tana nade shawarar da Sabira ke bata itama zata gwada a nata gidan.
*****
Ranar da daddare Col. Ishaq ya dawo gida a gajiye saboda ya tsaya karasa wasu ayyuka kafin hutunsa na aure ya fara washegari. Har wani aiki za'a turo shi Liberia ya samu aka bawa wani. Suna magana da Mami da ta iso a ranar ne yaji waya. A zatonsa Asmau ce don yau aiki yasha masa kai tun wayar safe bai kara kiranta ba. Da ta kira ma bai ji ba sai daga baya ya gani ya aika mata da text.
Bakuwar numba ce ya dauka tare da sallama. Muryar da yaji ko bata fadi sunanta ba bazai taba mantawa da ita ba.
Badariyya...
Ko aurenta ya mutu ne????
ABINDA AKE GUDU🙆🏽53
Batul Mamman💖
Amsa sallamar tasa tayi suka gaisa a mutunce. Shiru ya biyo baya ya katse shi ta hanyar tambayarta ya maigidanta da danta Nabil. Dan gyaran murya tayi tace
"Uhmm Ishaq dama dazu naje yini gida ne aka bani katin bikinka. Ashe aure zakayi babu labari"
"Badar kenan, kina gidan mijinki ai bai kamata na kiraki nace zanyi aure ba. Dama Hajiya tace zata aika cards nasan zaki ji labari"
Rayuwa kenan, mutumin da suke matukar son juna gashi yanzu akwai katanga mai karfi tsakaninsu. Tayi dan murmushi. Wayar ma sai da ta nemi izinin mijinta dama ta kira saboda kare hakkin aure. Zancen ba'a son ranta akayi auren ba tuni ya wuce da ta sami ciki.
"Allah Ya sanya alkhairi na bugu inyi maka dama. Sai dai naji wani labari a gida da ya tada min hankali...."
Katseta yayi wayar ta fara isarsa. Abokai da mutanen da bai ba sani ba duk sun ishe shi da irin wannan maganar. Ga kiran Asmau yana ta shiga call waiting.
"Cewa Asmau tana da 'yar da ta haifa babu aure ko? Haka ne abu daya kawai zakiyi min shine adduar da kika yi ta Allah Ya sanya alkhairi ki cigaba da yi"
Maganarsa batayi mata dadi ba "idan saboda rashin haihuwa ne don Allah ka nemi wata mai 'ya'yan. Me zakayi da wadda ta gama yawonta a gari?"
Runtse ido yayi ransa na kara baci. Haka ce zata yi ta faruwa kenan ko bayan aurensu. Albakarcin zaman tare da son da yayi mata a baya ya hana shi fada mata maganar da zata dade tana mata ciwo a rai.
"Kema kinsan bazanyi aure irin wannan ba. Ina son Asmau da zuciya daya. Anyway nagode da wayar taki. Ki gaida mijinki"
Ya katse wayar Mami tace "kayi hakuri Yaya. Nasan bazai wuce irin maganar da mukayi ba ita ma shi tayi. Sai an sami mai zurfin tunani ne zai nemi jin ainihin labarin Asmau kafin ya yanke muku hukunci."
"Gaskiya ne, Allah Ya kyauta. Babu mai iyawa mutane sai Ubangijin da Ya haliccemu. Komai kayi a wurin mutane baka iya ba a wurin wasu."
Dakinsa ya tafi ya kira Asmaunsa yana bata hakurin rashin jinsa da tayi. Dayake tasan yana aiki tace babu damuwa. Sunyi hira wadda duk akan abinda ya shafi biki ce sannan ta kwanta.
*****
Ranar Jumaa gidan Umma tun safe ya cika da jama'a duk da a katin an rubuta ba a gidan za'ayi kamun ba. Mutane sun rasa daga inda wasu ma suke zuwa. Abin mamaki sai ga Sagira matar Rabe da 'ya'yansu matan. Duk ta yamushe rayuwar kauye babu dadi. Umma batayi zaton zasu zo ba ganin da Asmau ta dawo an aika musu. Hajjo ce ma ta hana Asmaun zuwa Dakasoyen ta gaishe da Kawu Raben saboda shima ya dauke musu kafa. Gashi dai shine da laifi amma yafi kowa fushi.
Su Anti Lami da Yaya Abu duk sun iso da safe da yaransu har na gidan miji. Abu yayi kyau ko babu komai dai dangi ba'a canza su.
Lalle aka zauna yi mata ja da baki wanda aka bata lokaci wurin yinsa. Tasha zama kuwa don 'yan uwanta sun dage bazata cire da wuri ba sai ya fito sosai yadda za'a jima ana cin amarci.
Ana idar da sallar jumaa aka fara wanka don gidan Umma, Mama da na Jafar duk babu masaka tsinke. Itama Asmau kafin a kira la'asar tayi wankanta mai kwalliya Najah tazo ya fara aikinta. Fuska ta dauka don Naja ba daga nan ba. Kwalliyar ta nutsuwa ce ba'ayi mugun fentin nan na foundation ba da fuskar mutum take canzawa gabadayanta. Ana gamawa ta tashi tayi sallah aka sake gyarawa sannan ta saka kaya. Idan ka ganta a lokacin bazaka ce Asmau mai wankin bandaki bace a asibitin Jos. Tayi kyau ba kadan ba. A lokacin yawancin matan dake gidan sun tafi venue din. Yaya Abu ce ta kira Zubaida akan lallai su taho da amarya da wuri mutane sun soma cika a wurin. Ita har mamaki take yi wasu daga ina suka zo.
Wata mota ango Ishaq ya turo mai kyau ta daukar amarya zuwa wurin biki. Da suka isa ita da Walida da Zulaiha ne a motar. Safiyya tazo tace ta zauna domin ango yana hanya sai ya iso zata fito. Ta saki wani murmushin jindadi bayan Safiyya ta tafi. Zulaiha ta ce
"Hmm Asmau amare na dan kuka rana irin ta yau sai fara'a kike yi."
Allah Yasa dreban motar ya fita sai AC da aka ware musu. Walida tace "baki ga komai ba ita da Col. Ishaq nasu salon daban yake"
Asmau tayi fari da ido kawai tana murmushi. Motar tasu mai tint ce ta waje ba'a ganinsu sun jiyo kida daga wurin bikin yana tashi ga mata suna ta shige da fice. Wurin cike yake da sojoji masu gadi. Da farko ma taron ba'ayi niyar yi da maza ba. Sai Mami ta roka akan cewa ango zai zo da abokansa suyi hoto da amarya ya tafi. Shima da kyar ya yarda da zuwan. Shemau ce ta fada mata kalar kayan da amarya zata saka suka yi gaggawar nemawa ango wanda zai dace.
Bugu zuciyar Asmau ne ya karu da ta hango motar Jikamshinta. Wurin motoci bakwai ne suka shigo tare. Wai bikin da akace babu maza kenan. 'Yan kashe kwarkwarar ido da abokan arziki duk sun biyo shi.
Saitin motar da take Dahiru da ya tuko motarsa ya daidaita tasu yadda zasu fito tare. Ya hakimce a baya yana waya. Sai da ya gama ya fito ko'ina ya dauki kamshi.
Kofar inda take zaune yaje ya bude suka hada ido. Babu karya ya yarda yana son Matar Jikamshi. Duk abinda kake so kuwa dole kaga kyaunsa. Indai haka ne Jikamshi da Asmau sunyi kyau a yau ranar kamunsu. Wani hadadden lace ne peach a jikinta da ta samu tela yayi mata dinki na gani a fada. Doguwar riga ce amma tayi kyau sosai mai dogon hannu. Dankwalin rigar aka hada da wani yadi mai kyalkyali purple mara turowa akayi mata dauri. Sai tasa mayafi irin yadin aka makale mata shi daga tsakiyar daurin nata da pin. Takalminta mai tsini da jaka duk kalar mayafin ne. Ango ma shaddarsa irin mayafin nata ce amma fa ba mai kyalli ba. Ga hula har wani dan karkacewa tayi. Asmau tana gama fitowa aka fara daukar hotuna kamar me. Safiyya da Shemau ne masu tsari suka jera su MC din taro S.Kilishi ita ce ta sanar da shigowar ango da amarya. Suka taho suna taku daidai. Wuri ya kaure da sowa.
_Qamshi qamshi yana tashi, 'yan mata zamu kamun amarya_
_Yaune muke shirin kamu...amarya_
_Asmau amarya zo gamu...amarya_
_Ki hakuri da zancenmu, kinsan aure yana kanmu_
Kafin mai wakar ta karaso gaban ango da amarya tuni 'yan mata sun fito ana ta rausayawa. Jajimaji kenan, idan ta bude baki ko Sangandali sai dai taja baya. Haka ta cigaba da waka har amarya da ango suka zauna.
Bayan Hajiya YBK ta bude taro da addua aka shiga biki da gaske. Su Bilkisu da tawagar gidan Hajiya Lubabatu da 'yan Jikamshi ankonsu iri daya ne da nasu Ainau. Ga su Amatullah yau anyi kwalliya itama ta fito sosai. Yaran su Shemau da nasu Sadiya 'yan uwan Abubakar kowa fa yayi kyau.
An bukaci dangin ango su fito fesawa amarya turare sai gasu mata biyar ne harda Mami kowacce da tsadadden turare a hannunta suka zo a rinka fesawa. Biki yayi biki mata sun sha rawa. A cikin taron mata 'yan taya ango da amarya murna sun gwangwaje. Saboda yawansu ba sunan kowa zaka iya kamawa ba. Akwai su Maman Afrah, Tash, Jatma, Zahida, Mrs G, Sadiya Jegal, Ibtihal, Shukriya, Ummu Rauda, Maman Sadiq, Ummu Aslam, Mrs Ambursa, Hauwa Ag, Mum Little, Farha, Jammu, Mardiya, Shafa, Ruqayya, Tafeesu, Ummi BK, Didi, Mjay, Zahra BB, Biebie Isah, Temseey, Khadija Candy.....(wai abin da yawa ni mai rubutu naji hannuna zai tsinke nace wallahi sauran ma duk ina sonku har raina).
Taro kam ya kayatar. Anci an sha an kuma rausaya. Ana cikin daukar hotuna ne Mama Yalwa tazo zasu dauka ita da Asmau da ango. Suna hada ido da Asmau suka tuna abu daya suka fara kuka lokaci guda. Duk wanda yasan wadannan matan yasan kukan me suke yi. Allah Ya jikan Abubakar, mutuwarsa ce tasa har aka zo rana irin wannan. Suna yi ana tayasu har su Umma. Suwaiba karamar kanwarsa ce ta iya daurewa tana basu baki. Col. Ishaq duk kishi irin nasa ya dauke kai a yau. Abubakar wani bangare ne na rayuwar Asmau da bazai gogu ba.
Haka aka kare taron kowa ya tafi gida cikin farinciki da annashuwa. 'Yan gulma basu sami abin fada ba sai san barka domin taro ya burge kowa.
*****
Washegari sai shabiyun rana zaa daura aure. Asmau tun dare ta kasa baccin kirki. Yaushe zata manta ranar aurenta na farko da ango ya rasu. Ji tayi gabadaya bata da kuzari har gari ya waye.
Col. Ishaq kuwa jin kansa yake kamar anyi masa wani albishir mai kyau. Farar shadda ya saka harda babbar riga. Anyi mata aiki da zare ruwan goro saboda haka hularsa da takalmi harda agogon hannunsa ruwan goron ne. Masallacin Hotoro ya dauki jama'a wadanda suke son shaida wannan babbar rana. Su Jafar da Yassar suna kan gaba, ga Kawu Garzali da wani abin mamaki Kawu Rabe yazo yana ta ra6e ra6e. Bisa amincewar Hajjo da sauran 'yan uwansu Alh Adamu Matawalle shine waliyin amarya. ASP Qasim ma gayya guda yazo da ita daga abokan aiki zuwa makusantansa a Shanono. Ga su Sada suma ba'a barsu a baya ba.
Ango sai faraa yake yana gaisawa da jama'a. Har hoto suka yi da Qasim suka gaisa a mutunce. Shabiyu nayi Liman ya bukaci wakilin angon da waliyin amarya. An daura auren Col. Ishaq Muhammad Jikamshi da Asmau Shu'aib Yahya akan sadaki dubu sittin.
*****
Asmau na zaune kowa yayi wanka ana ta shirin tafiya gidan Umma inda zasu zauna saboda baki masu son ganin amarya. Tamkar wadda aka zarewa laka haka take jin jikinta. Ga faduwar gaba da ta kwana dashi. Tana kwance text ya shigo wayarta ta dauka a firgice. Kalma daya ta gani daga Jikamshi wadda ta saka ta kuka sosai.
*Alhamdulillah.*
Su Sabira suka zuba mata ido har dakin ya fara cika da su Ainau da Zulaiha suna ta tambayarta me aka yi mata. Shemau rai a bace tace "ku kyaleta tayi kukan nan. Tun daren jiya take neman yinsa. Ni nayi mamaki ma da kika jira sai yanzu. Ace mutum bashi da sana'a sai ta zubar da hawaye."
Tana kukan tace "Anti Shemau an daura fa"
La'ila ha ilallah....shine abinda Shemau ke fada tana tafa hannuwa.
"Amaryar zamani da kanta take sanar da aurenta"
Wani hawayen ne ya zubowa Asmau bata ji haushin yayarta ba tace "na zata shima mutuwa zaiyi, tun jiya gabana ke faduwa"
Jikin Shemau yayi sanyi bata san abinda ke ran kanwarta ta ba kenan taje ta rungumeta. Ainau ma ta matso ta rungumeta suka soma kuka. Sabira da Zulaiha aka bari da rarrashinsu.
Sai da suka saka Asmau yin nafila godewa Allah sannan tayi wanka ta shirya suka tafi. Shigarsu gidan ke da wuya Yassar ya shigo yace ga ango a waje zasu dauki hoto da amarya. Umma tana cikin mutane ta girgiza kai tana murmushi. Wannan ango bashi da dama. Bare an daura aure ai shikenan kuma.
Dakin da suke zaune da su Rashida Mimi taje ta kirawota. Yawanci sallah masu rakata sukeyi sai ta nemi takwararta Ma'u ta rakata. Mayafi tasa ta rufe fuska haka suka fito. Ashe tawaga guda ce domin harda su Jafar da Qasim. Ita dai duk kunya ta isheta haka akayi hotunan ta kasa sakewa. Shima bai matsa mata ba. Ko don idon mutane ya raga mata.
Qasim tun fitowarsu idanunsa suka fada kan Ma'u. Yarinya ce kyakkyawa suna kama da Zulaiha sosai. Itama ta kula da kallon da yake mata sai ta sunkuyar da kanta cike da kunya. A take yaji wani abu a ransa game da ita. Sun gaisa da Asmau zata shiga ciki ya kalli Col. Ishaq. "Ango don Allah a bani dama zan roki amarya alfarma. Ta dan daga kai suka hada ido da Jikamshi yace "bari na matsa ga mutane can zamu gaisa. Idan kun gama sai kuyi mana jagora mu dauka dasu Hajjo"
"Godiya nake yallabai, idan tarkona ya kama zan fada maka don kune masu nema"
Col. Ishaq na matsawa Qasim ya tambayi Asmau game da Ma'u. Tayi murna sosai ta masa bayani game da ita harda bashi numbar waya. Tana tafiya wurinta ta fada mata. Ma'u tayi murmushi kawai. Asmau tace alamun nasara kenan.
Har cikin falo aka shigo da angwaye aka dauki hotuna da iyaye da kakanni sannan suka tafi.
*****
Bayan magariba aka shirya tafiya Meena event centre inda za'ayi Sword Crossing. Wasu sun saba yi ido na ganin ido amma wannan karon tsarin na dare ne. Fili suka kama ba hall ba saboda shi zai dace da irin abinda suka shirya.
Kayan Asmau na yau har sunfi na jiya. Wannan ango da kansa ya aiko mata dashi dinki kawai ta kai. Material ne light green sosai. Riga da siket aka yi mata. A bisa umarnin ango ita da Amatullah suka dinka kayan. Wani irin dauri Najah mai kwalliya tayi mata da sauran material din wanda ba'ayiwa shafi ba. Kowa sai cewa yake tafi jiya yin kyau. Komai da ta saka ya dace da kayan sai daukar ido take. Amatullah ma Najah sai da tayi mata kwalliya kada da ta dace da yara aka daukesu hoto da Umminta. Ana fara tafiya ango yazo daukar amaryarsa. Drebansa ke jan motar sai wani abokinsa a gaba. Ko kadan ba haka yaso ba amma wannan tsarin na Mami ne. Kasa dena kallon Asmau yayi tunda ta zauna. Itama yayi mata kyau sosai domin kuwa korayen kayan sojoji ne irin wanda suke sawa lokutan taro a jikinsa. Sai yau ta kara jin soja yayi. Fuskar nan tasa ya gyara saje ya kara haske da kyau. Ji yayi inama daga wurin dinner sai gidansu. Ya mika hannu mai sanye da farar safar hannu mai santsi zai riko nata da yasha lalle suka ji kukan Amatullah. Kuka harda ajiyar zuciya wai Umminta da Babanta zasu tafi su barta. Ana ta rarrashinta akan suma can zasu je yarinya taki amincewa. Col. Ishaq yace a miko masa ita. A tsakiyarsu ta zauna ta hana ruwa gudu don har suka isa wurin surutu kawai take yi. Gata a tsakiyar iyayenta duniya tayi mata dadi.
Da suka je wurin ya fara cika. Duk masu cewa zasu sword crossing dinnan kowacce ta je. Gashi dai card admit ne amma haka wurin ya cika sai san barka.
Iyaye ma ba'a barsu a baya ba. Hajjo da Yaya tagwai ma duk tsufansu sunce basu taba ganin bikin sojoji ba dole ne ayi dasu.
Tare da sauran yara aka hada Amatullah sannan MC ya sanar kowa ya zauna ango da amarya zasu shigo. Yace a zauna ne saboda a tsaye dogaye zasu karewa marasa tsaho. Duk sojojin wurin cikin uniform din occassion suke. Dole su burge mutane. Sannan babu hargitsi don biki ne na manyan kasa da kowa baya son tsokano su.
Layi ne sojoji suka yi hagu da dama mutum goma goma. Kowanne ya rike hularsa a hannu daya sannan suka hada takubbansu ta sama inda amarya da angi zasu wuce. Kida ne mai taushi yake tashi aka umarci amarya da ango da su taho su wuce. Babu masu daukar hoto ta waya don ance kowa ya zauna. Masu daukar hoto biyu ne kawai wadanda aka hayo su suke binsu. Sun zo inda zasu shiga karkashin takubban hularsa na makale a hannunsa ya lankwasa hannun damansa yayi mata alama da ta rike. Duk da tana jin kunya haka ta zura hannunta ta cikin nasa suka fara tafiya. Jama'a kuwa sai tafi har suka wuce suka zauna.
Duk taron da akayi da tsari dole ya bada sha'awa. Irin wannan taron akayi a bikin Ishaq da Asmau. Tana daga mazauninta ta hango Qasim table dinsu daya da Ma'u suna ta hira. Ta nunawa Jikamshinta yayi murmushi "Allah Yasa shima tashi Asmaun mace ce tagari kamar tawa"
"Amin" ta amsa tana 'yar dariya masu hoto suka sami na yi.
Yaya Tagwai tace da Hajjo "wai ku a bikin Kano tsufaffi basa takawa ne? Tunda muka zo kidin yara ake sakawa suna ta rawa."
Hajjo tayi dariya sosai sannan ta yafito Yassar da hannu tace aje a saka wakar da zasu iya takawa kuma a fada filin nasu ne tsufaffi. Ango da amarya dole su sauko.
Yassar ya rinka dariya yaje ya fadi sako amma don shakiyanci wakar da yace a saka bata dace da Yaya Tagwai da Hajjo ba da sauran irinsu masu kashin kafa yayi laushi.
Sai da suka fito tsakiyar fili ga ango da amarya kawai aka soma wakar Uban Duma ta Ali Dawayya. Hajjo ta karkace itama Yaya Tagwai ta gotar da kafa daya zasu fara taku suka ji sautin yafi karfinsu. Kunnen Yassar ta jawo yace "wallahi Hajjo tsohuwar waka nace ya saka kuma ita ya saka."
'Yan taro suna ta dariya Yaya Tagwai ta gwangwaje abinta. Ango ma sai gashi yana juyi da abokai. Asmau dai kunya ta hanata rawa sai dariyar tsufaffi dake cikinta.
Iyaye ma sunyi tasu da amarya da ango asa ta turanci asa ta hausa. Da taro yazo karewa su Hajjo sunyi hanyar fita aka saka Mata ku dau turame. Dafa juna sukayi ita da Yaya Tagwai suka koma fili suka sha rawa. Su Ainau sun sha dariya kamar cikinsu zai kulle. Hajjo tace ita ba don amarya tayi ba. Dole ta taka idan aka ambaci sarki.
Sai wuraren shadaya da rabi wurin yayi saukin mutane anata tafiya gida. Col. Ishaq ya dubi Asmau wadda duk ta gama gajiya. Ga tsinin takalmi. Drebansa yace ya bashi key din mota ya bi wasu ya tafi gida. Abokinsa da suka zo tare yana wurin yace "ango duk tsiyarka fa tare zamu tafi. Naga kana sallamar dreba nasan ni zan biyo baya. Kasan Mami...."
"Mamo ba Mami ba. Ka fita idona Captain. Wai Baraka ba tazo ba. Don Allah ka dauketa ku tafi dare yayi"
Saluting dinsa yayi yana kyakyata dariya. "Na barku lafiya angon Asmau."
A can gefe daya kuma su Mami ke neman Bilkisu a tafi gida an rasa inda tayi. Tana can ita da Yassar a wurin wasu kujeru. Abinci yake ci yunwa ta dame shi yaji sallamarta. Har kusan kwarewa yayi don baiyi zaton ganinta ba. Tayi murmushi ta zauna a kujerar dake kallon tasa. Yassar ya ajiye cokalin yana kallonta. Tace "ci abincinka mana"
"Bazan iya ba. Ni bana iya cin abinci a gaban mutane shiyasa ma kika ganni a nan yanzu"
"Ni kuma kaga so nake kullum ka rinka ci a gabana"
Sauran abincin bakinsa ne yasa shi kwarewar da yake gudu da yaji abinda tace. Tayi masa sannu amma tarin yaki tsayawa. Da tayi magana sai ya sake yin tari.
Bilkisu ta dan harare shi "dama saboda ni kake tarin? To aiki ya sameka don bazan dena yi maka magana ba"
Yassar ya rasa me zai ce mata. Haka yake da kunyar mata tuntuni. Babu wanda zaice ga budurwarsa. Ta dan sassauta kallonsa tace "ni na gaji da kallon kallo da muke yi fa, sai yaushe zaka ce kana sona?"
Wannan karon da ya fara tari har sai da ya sauko daga kan kujera. Yana dafe da kirji tana yi masa sannu yace "ke haka danginku suke ne, basa jin kunyar magana"
Turo masa baki tayi "to ba wani bane a cikin 'yan biki yace yana sona ba. Kuma har cewa yayi zaiyiwa Uncle magana shima soja ne a karkashinsa yake"
Yassar ya ware ya koma ya zauna yana kallonta babu zancen wasa "don Allah kada ki amsa masa. Nima zanyi sojan nan har Yaya Ishaq ya karbo min takarda zanyi short service"
"Uncle Ishaq nake ce masa fa" tana magana kamar zata yi masa kuka
Duk ya rude da tayi zancen wani soja yace "to nima Uncle Ishaq kinji"
Ta juya masa ido "to kana sona kenan na sallami wancan"
Kai ya sunkuyar kasa da gaske kunyarta yake ji ya gyada kai a hankali.
"Ni da baki zaka fada"
"Kiyi hakuri zanyi miki text ko na kiraki"
Shan kunu tayi "zan cewa wancan ya turo kawai"
Yassar ya sake rudewa "me yayi zafi kiyi hakuri. Ina sonki mana ai ko ban fada ba kin sani"
Sai yanzu yaga alamu taji kunya ta rufe kuskarta da mayafi ta tashi "bari naje nasan ana jirana. Don Allah ka kirani fa"
Yayi murmushi "in sha Allah ina zuwa gida zaki ji wayata"
Sai da ta soma tafiya ta dan daga murya yadda zaiji tace "Yassar"
Ya juyo yana kallonta "dama karya nake yi, so nake kawai kace kana sona" daga haka ta tafi. Ya zauna yana sosa keya. Yana tunanin ko dai soyayya a jinin dangin Jikamshi take. Tasha fada kuwa a wurin Mami. To bukatarta ta biya ko kadan ranta bai baci ba.
******
'Yan uwan Asmau sunyi gaba da harda yi mata tayin ko zata bi motar Umar tunda Ainau ce kawai a ciki. Col. Ishaq ya jefi Shemau da kallo harda harara ta kwashe da dariya. Dama tsokanarsa tazo yi. Sai da yayi sallama da abokansa sannan yazo ya sameta a inda yace ta jira shi. Jikinta yayi sanyi tunda taga ya sallami 'yan motar tasu. Har wani dan tsoronsa take ji. Ya kula da canjin yanayinta a ransa yace baki ga komai ba.
Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar yaki sakin hannun. Wani iri take ji daban don bata saba ba. Idan ba bisa lalura ba tana iya rantsuwa banda Abubakar babu wani namiji da ba muharraminta ba da ya taba mata hannu. Shima jin hakan yake har ransa. Ya dade yana jiran ranar da Asmau zata halatta gareshi ya tabata batare da tsoron zunubi ba. Sai ma lada da zai biyo baya.
Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna wurin dreba. Ya tayar da motar sannan ya kamo hannunta ya dora akan giyar. A haka ya saka giyar ya soma tuki cikin nutsuwa. Zuciyar Asmau ta kusa ballo kirjinta don tsoro.
"Tunanin me kike yi ne"
Ta dan rufe idonta ta bude "babu komai" muryar nan a salihance take fita.
"Are you sure, har tunanin abinda zan iya yi miki daga nan zuwa na kaiki gida bai zo kanki ba?"
Ta shiga kifta idanu kamar mara gaskiya. Saboda dare ne kuma titin babu motoci sai tsiraru shiyasa yake iya kallon bangaren da take.
"Kinyi shiru, bari na fada miki abinda naji zuciyarki tana cewa"
Kallonsa tayi tana jiran taji abinda zai ce. Shima sai da ya dan juyo sannan ya mayar da ido sa ga titi.
"Zuciyarki tace yau dai gani ga Jikamshina a matsayin maya da miji. Daga nan zuwa ya kaini gida zanyi kokari ko kiss ne nayi masa"
"La'ila ha ilallahu, ni banyi wannan tunanin ba..." Asmau ta fada tare da cukwikuye kanta cikin mayafinta. Kunya taji har bazata iya misalta ta ba.
Shi kuwa dariya yake mata. Yana son wannan kunya ta Asmau.
" ko kwana daya bamuyi da aure ba har kin fara karyata ni?"
Ta dan dago kanta daga kan cinyarta da ta rufe "ba haka nace ba fa"
Nishadi kawai yake ji gashi ga Asmai a matsayin maaurata. Ya daga gira daya "to yaya, kin amince kinyi wannan tunanin?"
Ta soma girgiza kai sai taga ya bata fuska. Tayi saurin cewa "Allah Sarki banyi ba amma dai naji nayi tunda haka kake so nace"
"Good girl, that means I will get one kafin mu rabu yau."
Ta turo baki don ta san idan ta sake magana wani abin zai kuma fada. A hakan ma bata tsira ba ya kalli dan bakin ya sha janbaki
"Mayar da lips din mana, ai ba yanzu za'ayi ba sai mun isa gida. Naga alama kin fini zumudi".
Kwafa tayi tana tunanin me zatayi masa, tukinsa yake hankali kwance. Tace "Jikamshina"
"Yes sweetheart. Kinsan fa yanzu duk wani suna da ake kiran masoyi a duniya zan kiraki dashi"
"Zan rama ne."
Yayi dariya "dama haka nake so. In ce wani abu ki rama yanzu?"
Ta gyada kai "I want to hug you"
Ta bata fuska a shagwabe "wallahi zan maka kuka"
Ya sami abinda yake so. Tana jinsa yana dariya ta ja mayafi ta rufe fuska har suka isa gidan Jafar. Yaron makota da yake masa gadi ya bude ga motarsa nan alamun sun dawo.
Ta kama kofa zata bude taji ta a rufe. Yace mata
"Kiyi hakuri kiyi min magana please"
Ta noke kafada, ya ce "to shikenan ina zuwa. Umarni na baki kada ki bude kofar nan"
Itama nata salon ramawar kenan yau duk abinsa bazata yi masa magana ba har ya tafi. Tana kallo ya bude ya fita ya zagayo ta gefenta ya bude mata. Sai da ta ziro kafafunta waje kawai ya durkusa a gabanta ya kafa kafar ya cire mata takalma yana bin yatsun kafar yana matsawa. Kasa magana tayi saboda bata yi zaton abinda zaiyi mata ba kenan. Ga kunya kamar tayi ihu. Har fargaba take kada wani ya fito ya gansu. Ta dan ja kafar ya rike sosai ya cigaba da matsawa yana magana a hankali.
"Tun dazu kike dingishi kina tunanin zan bari ki shiga ciki ne kice wata tayi miki tausa a kafa?"
"Don Allah ka dena kada yaya Jafar ya fito" tana magana idonta na kan kofa.
"Matsoraciya bari kiga wani abu" bata ankara ba taji yayi mata daukar jarirai. Abinka da dogon soja tashi yayi ya nufi hanyar kofar gidan da ita.
Asmau ta gama tsurewa ga tsoro tasa hannuwanta biyu ta kankame masa wuya "Ji...Jikamshi don Allah ka saukeni"
"Anki din, ki sassauta rikon nan kin shake ni"
Ta dan marairaice "idan aka fito aka ganmu fa"
"Zaki sa na shiga dake har dakin da kike kwana idan bakiyi shiru ba"
Shirun tayi don kada ta kara tunzura shi. Kanta a wurin kafadarsa ya cigaba da tafiya ta lumshe idanu. Komai nasa daban yake mata. Aure dadi aure lada yau ba tsoron fada take yi ba idan da wani zai fito ya gansu. Ko waye sai dai taji kunyarsa sabanin da wani namijin ne kawai da babu aure a tsakaninsu. Taji tsoron a kamasu sannan ta hada da lodin zunubi. Allah Ya kara karemu daga soyayyar tabe tabe babu aure wadda wasu suke yiwa kallon burgewa.
Tunaninta ya katse da taji ya ajiyeta a bakin kofa sannan ya bata takakmanta. Ya daidaita fuskarsa da tata ta hanyar rankwafowa ya rage tsaho suna jin numfashin juna. Idonta a rufe don fargaba.
"Ina jin na cancanci wannan kiss din da kika yi tunani dazu"
Bata bude idon ba taji ya hada bakinsa da nata. Alhamdulillah cikakken farinciki yana tare da aure. Da da yanzu ta kwatanta sai taji yanzu duk da tana jinta kamar akan kaya kada wani ya fito kuma shima tana jin kunyarsa amma yanzu ne hankalinta ya kwanta. Yanzu ne taji nutsuwar kasancewa da namiji-mijinta.
Ya dan dago kansa yana karewa fuskarta kallo kamar kada ya barta yace "saura ladan nauyi da na sha"
.
Tar ta bude idon "gaskiya bani da nauyi"
"Ba kiji yadda zuciyata ke bugu bane da na daukeki." Ya dora hannuta daidai kirjinsa ya sake kissing dinta.
"Ke dai ba na nauyinki bane, tsabar dadin kasancewa dake ne. Ba don ina jin kunyar Umma ba sai dai a biyoki da kayanki gobe"
Kunya tasa ta kasa kallonsa. Ya rungumeta sosai a kirjinsa zukatansu na kara son juna "yau zanyi bacci mai dadi Matar Jikamshi. Ina fata kema zakiyi. Sai gobe idan mun hadu a dakinki" a goshinta yayi mata wani kiss din ya tafi ya barta a tsaye tana numfashi da kyar.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽54
Batul Mamman💖
_Gaisuwa da fatan alkhairi gareki Maman Iman da Asim. Nagode Allah Ya saka da alkhairi._
Har motarsa ta fita daga gidan Asmau ta kasa motsi kamar an kafeta a wurin. Daga ciki taji kamar ana taba kofa tayi saurin bude kofar ta shiga da sanda ga takalma a hannu. Tayi sa'a masu kwanan falo wasu sunyi bacci. Na ido biyun kuma ba 'yan tsirku bane.
Dakin Sabira ta lallaba ta shiga suma suna kwance. A ranta tace wai sun dade ne da Jikamshi a waje? Ita fa gani tayi kamar bai jima ba. Tana dukawa ta ajiye takalmanta taji ance
"Sai yanzu"
Ba karamin tsorata tayi ba harda dan tsalle. Ta juya suka hada ido da Zulaiha tana murmushi.
"Meye haka kika firgice kamar an kama barawo. Kinga bakinki kuwa?"
Asmau tayi saurin dora hannu akan lebenta tana rufewa don a tunaninta ana ganin abinda Jikamshi yayi mata a bakin. Ko kafin ta shigo ji take kamar a lokacin yayi. Ido a waje tace "me...me kika gani a bakin nawa?"
Zulaiha sai dariya tace "amma dai kina da matsala. Kowa ya ganki sai yasan baki da gaskiya. Yanzu yanzu kin tonawa bawan Allah asiri har na gano abinda baki son na gane"
"Da gaske ana gani? Na shiga uku. Shiyasa a falo suka bini da kallo ashe." sai kuma ta sake rufe baki da ta gane sake tonawa kanta asiri take ta shige toilet da gudu tana jin dariyar Zulaiha.
Ita Zulaiha kwanciya ta gyara tana dariya tace "dama wannan angon naki ai banga alamar wasa ba tare dashi. Goben ma gara a kaiki da wuri kada muji dirar sojoji a gidan nan".
*****
Wanka Asmau tayi ta dauro alwala ta fito. Dakin dai shiru Zulaiha ma ta gyangyada. Ta dafe kirjinta oh Allah Yasa sauran basu gane ba. Amma Jikamshi ya janyo mata jin kunya sosai.
Ko mai bata shafa ba ta saka kayan bacci ta kwanta saboda gajiya. Ji tayi tana son kiransa taji ko yaje gida lafiya. Gashi har daya ta wuce idonta ya soye kamar ba wadda ta gaji ba. Tana ta tantamar kiran nasa taji wayarsa ta shigo. Saurin dauka tayi saboda kada ringing din ya tashi masu bacci.
Zaune yake akan gado ya jingina da pillow. Shima tunda yayi wanka bacci ya kaurace masa. Matarsa yake tunani da yadda yaji dadin hirarsu ta dazu. Tana dauka yace "me ya hanaki bacci"
Wannan murya ta Jikamshinta ita kadai tasan dadin da take mata. Sai taji kamar kada ya dena magana. Rufe ido tayi taki magana
"Ni ne ko? Na biya miki sabon karatu na tafi na barki da bugun zuciya"
Sake runtse ido tayi kamar yana gabanta tana jin kunyar kalamansa "ban ce ba fa"
"Ai ni nace. Kada ki manta ban dade da jin bugun zuciyarki ba a kirjina, kinsan shi baya karya. Nasan dai nawa yafi naki. Tsoronki yasa baki nutsu ba kinji zuciyar da take bugu da kaunarki. Burina na farko ya cika. Na aureki, na biyun ma in sha Allah zai cika. Shine mu sami zaman lafiya da fahimtar juna"
Tayi dan murmushi tace "Amin Jikamshina"
Kwanciya ya gyara yace "Kinsan tun yaushe nake son daukar ki? Tun ranar da kare ya biyoki. Daga ranar kika tashi daga matsayin Ummin Safina a wurina kika koma Matar Jikamshi."
"Wannan karen naka bai kyauta min ba"
"Ni kuwa yayi min komai. Ya bude kofar zuciyar Asmaun Ishaq. Ya kamata ki kwanta haka kafin gobe"
Hamma take yi amma kuma bata so ya ajiye wayar.
"Bana jin bacci. Gobe nayi idan an gama hidimar nan"
Tashi yayi zaune yana kallon wayar da mamaki kamar ita ce Asmau sannan ya mayar kunnensa "ba dai a gidana ba ko?"
Asmau tace "to a ina zanyi. Kasan nan yini za'ayi babu lokacin bacci"
"Kinga Allah Ya bamu alkhairi, ki kwanta kawai ko babu baccin ki rufe idonki ki huta. Wai bacci! Matar Jikamshi anya kina sona kuwa, a ina kika taba jin anyi bacci ranar da aka kai amarya idan ba auren dole ba?" magana yake da gasken sa ya ma za'ayi ta fadi magana irin wannan.
Sai da tayi dariya tace
"To bazan tambayeka me ya kamata ayi ba nasan halinka. Yanzu sai kasa na gwammace banyi magana ba, ka fi karfina"
"Muka fi karfin juna dai. Dama yaushe zaki tambaya bayan kin san abinda nake nufi."
Dariyarta yaji sannan tace "uhmm bari naje falo neman pillow din kujera na dakin sun kare ni kuma bana jin dadin bacci haka."
"Kice dai kawai kina so kiyi pillow da kirjin mijinki. Daga gobe ne fa Matar Jikamshi. Har kin fini....."
Ya Salaam, bata kara magana ba ta kashe wayar ta fita neman pillow tana dariya. Haka ta dawo ta kwanta don bata samu ba. Shima dariyar kunyar da yasan taji ya gama ya gyara kwanciya yana tuno dan lokacinsu na dazu zuciyarsa na kara nutsuwa da zabin da Allah Yayi masa.
*****
Da safe sai da suka yi breakfast kowa ya shirya aka fara komawa gidan Umma wurin yini. Yau atampa ta saka anyi mata dinkin half-gown da plain zani. Ta kashe dauri ta yafa mayafi irin na kayan. Da ta fito falo guda aka saka amarya da farinjini.
Kujeru aka jera a waje da tabarmi da kafet. Sai ga Ado Gwanja ya iso da tawagarsa. Wannan aikin Sally ne 'yar Yaya Abu da Ab Kura kamar yadda suka saba kiran babbar 'yar Anti Lami. Sun dage sai sun gwangwaje suma a bikin nan. Tun kafin dawowar Asmau zumuncin 'yan uwan ya karu bayan tafiyar Kawu Rabe. 'Yan mata kuwa da su Shemau aka shiga filin rawa. Amarya dai sai janta akeyi amma ko da can bata iya sakin jiki tayi rawa balle yanzu da tun jiya Jikamshinta ya rada mata baya son rawar nan. Idan zatayi ta jira sai su kadai.
Ana ciye ciye biki na ta tafiya aka kira Sabira a waya sai ta fita da gudu tana murna. Anti Bintu tace "ke lafiyarki kuwa"
Sauri take ta karasa waje ta taro bakin tace "Anti Bintu 'ya'yan yayyen Mama ne daga Maiduguri. Mota ce tayi musu tsiya tun shekaranjiya suka so zuwa."
Ta fita ta taro 'yan uwanta tazo ta gabatar dasu wurin amarya Asmau.
"Wannan sunanta Fatima Goni ga kuma Amalus sai Halima Wasagu da Feey. Cousins dina da nace miki suna son zuwa biki"
Asmau fuska a sake ta gaisa dasu tana godiya da suka sami damar zuwa. Daga nan aka cigaba da taro har yamma.
Sai da magariba ta gabato aka sallami mai waka iyaye suka kira Asmau cikin dakin Hajjo. Jikinta ya gama sanyi ta shiga dakin suna zazzaune. Hajjo ce a tsakiya ga Mama Yalwa, Umma, Anti Bintu, Yaya Abu da Anti Lami don kara irin tasu harda Yaya Tagwai da Uwargida basu nuna mata kyama ba.
Nasiha ce suke mata wadda tasa ta kuka kamar an bude famfo. Hakuri ne kowacce take mata nuni dashi domin shine jigo a zaman aure duk son da kuke yiwa juna da miji to sai an kai zuciya nesa. Zama ne ake fatan yi har karshen rayuwa. Suka dora mata da ta jure ta kawar da kai ga dukkan maganar da zata ji musamman daga dangin miji. Haka Allah Ya kaddara mata dole ne kuma sai an sami masu yi mata wannan gorin. Hakuri, ladabi, biyayya, tsafta da iya girki kuma sai ta dage. Ishaq yayi mata karamci da yake sonta a haka ya aureta. Ta zage damtse ta kyautata masa.
Kowa ya fadi nasa Asmau tayi kukanta son rai. Bayan ta fita daga dakin ba jimawa Zubaida tazo ta kirata dakin Yassar. Abin mamaki Uwargida ce a dakin Zubaida ta rufe kofar. Sake bawa Asmau hakuri tayi da taso bata mata rayuwa
"idan naje muka gana da 'yan uwana zan koma Azare ne. Gidan nan ba zan barshi a cigaba da sabon Allah ba. Da kika ganni babana Limami ne. Da kuruciya muke sauka. Ina da ilimi na daidai gwargwado. Zanyi amfani dashi wurin bawa matan dake gidan shawara da koyar dasu sannan su koma gaban iyayensu. Ba ido gareni ba kada ayi abinda bazan gani ba. Za'a raya gidan da bautar Allah in sha Allah"
Asmau taji dadi sosai haka ma Zubaida. Uwargida tace "Asmau ina so ku saurareni da kyau. Nasan sana'ata ba mai kyau bace kuma ina ta rokon Allah gafara. Amma ina son sanar daku wasu 'yan sirrikan rike miji da muke amfani dasu a da muna raba mata da mazansu muna aikata haram. Wannan abin idan kunyi a gidan miji riba zaku samu da lada. Ku zama marasa kunya amma ba tsiwa da fitsara ba. Duk abinda miji yake so kiyi masa kada yaje nema a waje. Wani kinkime jiki da hijabi a dakin miji sai a sallah ko kunyi baki. Ku zauna da kayan da zasu ganku da kyau suji suna sha'awarku."
Zubaida da Asmau sai kunya aka fara sunkuyar da kai. Uwargida da taji sunyi shiru tace "kunga ni babarku ce. A bariki nayi amfani da wannan banga riba ba saboda aikin haramci ne. Amma ku gwada a gidan aure wallahi miji sai ya yaba muku. Da ajiye kunya mu kyautata musu muke raba auren soyayya. Matan hausawa kamar munfi kowa kunya. Muyi a waje sannan a gidan auren ma miji yana binki kina nokewa wai ke kin girma. Ai kullum ku nuna musu kamar yau kuka fara kasancewa tare. Sunayen soyayya na zamani samo ki kira abinki. Wani maigida ko baban wane an wuce wurin. Idan miji bai zo da kansa ba ke ki nemo shi. Hanyoyi gasu nan barkatai. Ku dan matso kada aji daga waje ace Uwargida zata bata ku. Allah Ya gani sharrin irinmu nake guje muku. "
Ai kuwa su Asmau sunji batu a bakin Uwargida. To dama kunya a wurin irinsu sai a hankali. Baro zance kawai take Zubaida ta gama jin kunya. Ko da ta gama bayani sai dai su kalli juna suyi murmushi.
*****
Wanka Asmau tayi saboda ance masu daukar amarya suna hanya. Amatullah kamar tasan ba da ita za'a tafi ba yau ta like mata. Da kyar da dabara Shemau ta hadata da yaranta tasa Yassar yayi saurin kai mata su gidanta. Nan da sati biyu sai a dawo da ita lokacin itama Asmau ta saba. Ana fita da ita kuwa Asmau tasa kuka. An rabata da Ama ji take gara kawai a bata ita su tafi tare. Da kyar tayi shiru ta shirya cikin wani material mara nauyi riga da skirt. Fuska tasha kwalliya sosai ga katon mayafi har ka ta lulluba. Jammu cikin kawayen Shemau ita ta matso kusa da Asmau ta damka mata wani abu kamar zuma kadan a kofi. Asmau ta dan dago kai ta kalleta.
"Nasan kin sha abubuwa da yawa shiyasa na zuba miki kadan. Kinsan yadda muke da Shemau kanwa na daukeki. Na bata sauran za'a ajiye a gidanki."
Wannan kayan idan batayi da gaske ba cikinta sai ya baci. Kowa da nasa kuma duk abu daya ne. Suna son daga darajarta a wurin miji. Kafa kai tayi ta shanye tsumin. Jammu tayi dan murmushin jindadi. Tasan nan gaba Asmau sai ta nemeta da kanta. Sirrinsu ne na Sokoto.
******
Dirar motoci aka ji wanda yayi daidai da faduwar gaban Asmau. Shikenan ta zama matar aure. Auren da ta fitar da rai ashe tana da rabonsa. Gashi zata bar Umma ta kama rayuwar ibada.
Su Mami ne suka zo daukar amarya da wasu 'yan uwansu manya. Da aka tashi fita da kyar aka bambare Asmau daga jikin Umma, ita ma Umma kukan take. Su Anti Bintu ma da Mama Yalwa sunyi nasu kukan. Motoci sunfi goma daga bangaren ango banda na dangin amarya masu motar gida da ta haya. Mata ne kawai suka cika gidan. Biki yayi albarka. Mutan Jikamshi sun dauki amaryarsu Asmau.
A motarsu daga wanda yake ja wani soja ne abokin aikin Col. Ishaq sai Walida a gaba. A baya kuma Yaya Abu ce da Mama Yalwa suka saka Asmau a tsakiya.
Gida ne flat mai kyau tun daga waje ga filawoyi sun fito ta saman katanga. Gate din a bude yake da yake bazai dauki motoci sama da uku ba dole aka bar wurin da za'a shigo da motar amarya. Tun a nan zaka san anzo gidan amarya saboda kamshin dake tasowa daga ciki. Wannan aikin su Shemau, ne da Rashida, Sabira da Suwaiba. Mata sai son barka ake gida yayi kyau sosai. A cikin falon aka kai Asmau wurin wasu mata iyaye ga Col. Ishaq ta bangaren Hajiya da babansu. Anyi barkwanci suka kare da nasiha. Babu mai iya tanka Asmau domin sun sha gargadi a wajen iyaye maza. Col. Ishaq yana da kwarjini basa son bata masa, ihsani ya sami tangarda.
Daga nan aka wuce da ita dakinta wanda Umma tayi namijin kokari wurin sayan kayan kawata shi. kanta a rufe yake tana hawaye har aka zaunar da ita a bakin gado. Wata da tace gidanta na jikin na Asmau mai suna Husna tazo ta dan bude fuskar amarya tana murmushi
"Masha Allah amarya Allah Ya bada zaman lafiya. Idan kina da matsala ki rinka nemana. In kina so ma ni kullum sai na shigo na taimaka miki."
Ainau dake gefe tayi dariya, Husna baki san wannan angon ba.
Sai da aka hada da magiya aka samu matan suka fara fita. Gidan ba babba bane sosai. Daidai mata da miji da 'ya'yansu. Gida ya watse sai makusantan Asmau. Har lokacin bata bude fuskarta ba.
Walida tace "kinga ki tashi kiyi sallar isha in da hali kiyi wanka ki canza kaya. Kinsan saboda mutane dakin yayi zafi gaki a kunshe cikin mayafi"
"Nima abinda zan fada mata kenan. An taho da kayanki sai ki sami 'yar rigar bacci mai kyau ki saka"
Asmau bata san lokacin da ta bude lullubin tana kallon Zulaiha ba harda harara. Dariya suke mata sosai Zulaiha tace "meye na hararata, ki tashi ko na tonaki wallahi"
Zubaida tace "don Allah tona" sauran suka rinka naci ita kuma Zulaiha tana ta ja musu rai. Da yake yau bakin yayi lakwas Asmau bata ce komai ba ta shiga inda aka nuna mata bandakin dake cikin dakinta. Sai hamdala take, ko a toilet ba karamin kashe kudi aka yi ba. Duk kayan toilet Abdulhalim ne yayi mata su. Wanka tayi da alwala ta mayar da rigarta akan tawul din. Tana fitowa duk an ragu sai yayarta Shemau. Za'ayi sirri na 'yan uwa ta nuna mata inda ta ajiye kayan gyaran da aka bata a wata drawer
"Don Allah kada ki rinka yi musu shan koshi. Komai sama sama yafi ko don kada ki sha wanda zai illata ki. Ga wannan kuma ki saka"
Asmau ta karbi kunshin ledar da Shemau ta bata. Doguwar riga ce abaya amma ruwan madara. Rigar ta tsaru karshe da mayafinta. Bude baki tayi zata fara godiya da dan hawayenta Shemau tace "indai tayi miki kyau shikenan. kiyi sauri ki shirya kiyi sallah kada ango yazo kina daure da tawul. Mu zamu tafi ga Zulaiha nan da Walida sune kawayen naki dama. Sabira da mijinta bai kamata ta zauna ba."
Shemau bata fita ba sai da Asmau tayi sallah ta shirya. Wani turare mai maiko ta bata ta fara shafawa kafin aje ga sauran. Kamshi ne zai tarar da Jikamshi.
Bayan tafiyarsu daga ita sai su Walida suka dawo falo don ba'a son wannan zuwa har uwar daki da abokan ango. Alamun bude gate ya sa hankalin Asmau tashi. Mayafinta ta gyara kafin su shigo. Su hudu ne harda angon. Biyu abokansa da kaninsa Ismail. Bata iya ganin kowa sai muryoyi da take ji. Ba wasa suka tsaya yi ba nasiha ce dai da addua. Sai a lokacin taji muryar maigidan nata yace Amin. Daga nan suka tashi yace akwai dreba zai ajiye su Zulaiha. Abokin nasa mai dauko amarya yace shi zai je. Ashe Walida ce ta dauke masa hankali.
Tana ji ya fita rakiya ta kasa bude mayafin bare ta tashi. Lokacin da ya rufe kofar gidan kuwa zuciyarta ba karamin harbawa take ba. Anyi an gama yau ga Asmau a matsayin matar Ishaq.
Motsi da kamshinsa taji a kusa da ita ta sake kankame mayafin. Shiru bata ji ya zauna ko yayi magana ba. A hankali taji an bude gaban mayafinta ya shigo da kansa ciki. Ashe a gaban kafafunta ya durkusa. Zatayi baya yasa hannu ya zagayeta ga mayafinta ya rufe su sai kamshin turaruka da numfashinsu. Babu abinda zata iya yi sai kawai ta rufe idonta cike da kunya.
A hankali yake mata magana "Kinyi kyau Matar Jikamshi, yau so nake kamshinki ya rikita ni shiyasa zanyi ta like miki"
Sake runtse ido tayi tana jin wata irin kunyarsa tana karuwa a zuciyarta. Ya dago kanta tare da matso da bakinsa kusa da nata ga hancinsu yana gugar juna
"Ko na daukeki ne?"
A nutse ta bude ido suka sauka cikin nasa. Murmushi tayi masa yaji gabadaya ta hargitsa masa lissafi. Irin wannan farincikin a karkashin inuwar aure halattaccen zama kawai Allah Yake sako shi. Bai dena kallonta ba ya rike mata hannu suka tashi. Mayafin ya cire ya ajiye a kan kujerar ya karewa rigarta kallo. Shemau ta iya zabe. Sai a lokacin ita ma ta kula da kayansa. Yau ma harda babbar riga a shaddarsa ruwan madara kamar kayan jikinta. Hular kuwa a kasa ta ganta kusa da inda take zaune. Yana rike da ita har suka je dakinta.
"Shiga ki jirani naje nayi wanka. Kunyarki nake ji da nace ki rakani. Amma kiyi alwala kafin na dawo" Yana kashe ido tana sunkuyar da kai. Sai da ta shiga ya wuce yana murmushi.
*****
Da abin sallah ya shigo harda mayafinta na falo sanye da kayan bacci riga da wando. Ya shimfida musu abin sallar tana kallonsa sannan ya nuna mata alamun ta tsaya suyi sallah. Kira'ar Jikamshinta ta tafi da ita don nutsuwa da bawa harufa hakki. Raka'a biyu suka yi sai shafai da wutri sannan ya shiga jero addua da larabci kamar bazai dena ba. Bayan ya kai karshe suka shafa ya dawo gabanta ya dafa kanta ya sake wata sannan ya tashi zai nade abin sallar. Karatun Uwargida ta tuna ta dan matsa a kunyace ta karba ta ninke. Ya ji dadin hakan kuwa sosai.
Fita yayi daga dakin ya dawo yace ta biyo shi. Falo suka koma ya ajiye mata snacks, nama, juice da youghurt.
"Wanne kika so"
Jikinta duk ya fara sanyi ta ce ta koshi. Yayi murmushi wannan salihancin duk zatayi ta gama ne.
"Ni zanci kinga ya kamata ki zauna a kusa dani har na koshi ko"
Tace "uhmm" kamar wadda ta tauna flagyl bisa kuskure. Centre table din na gabansa ta zagayo zata zauna a kusa dashi kawai ya janyota kan cinyarsa tare da yi mata rikon da bazata iya gudu ba.
"kada kice min kunyata kike ji kin san ni dai bani da ita indai a kanki ne. Kema kuma haka nake so ki zama."
Ta rausayar da kai gefe guda tana kokarin zillewa.
"Idan ba kya so muci abincin sai mu koma inda muka fito ni bani da matsala."
Tace "To bari na matso da plate din ni ina jin yunwa"
Hancinta yaja yana dariya "ace sai da dabara zan samu kici abinci."
Bayan sun gama ta kwashe komai ta kai kitchen din da bata gaji da gani ba tun da su Walida suka nuna mata. Da ta dawo ya kashe duk kayan wuta suka shiga ciki. Dakinta zata shiga yace "muje namu dakin ki saka masa albarka"
"Brush zanyi"
"Can ma akwai duk abinda zaki bukata" hannunta ya kama suka tafi. Ni'imtaccen kamshi da sanyi ne suka doki hancinta. Komai na dakin sabo ne. Dama dakuna hudu ne a gidan. Aka saka mata gado a biyu dayan aka mayar mata karamin falo. Nasa dakin ya dauki hankalinta. Ya shiga bandaki ta tsaya dube dube. Wani bakin abu mai santsi ta gani akan gadonsa ta dauka. Baki ta bude da ta gane ko meye. Rigar bacci ce mai kyau da ta dace da amare.
Tana jin zai fito ta ajiye sai dai ya ganta. Ya zo ya rungumeta ta baya "rigar tayi miki kyau ko? Hmmm nifa ban ganewa kamshin nan naki ba. Ji nake kamar na mayar dake jikina"
Asmau ta janye jikinta kai a kasa. Rigar ya mika mata yace taje ta shirya yana jiranta don yaga taki sakewa a nan. Idan ta wuce minti goma zai biyo baya. Dakinta ta koma tana mayar da numfashi kamar wadda tayi tsere. Sai juya rigar take yi a hannu. Karshe dai ta sake shiri ta saka ta dora zani ta fito.
Daga bakin kofa ya tareta ya dagata sai kan gado. Sai dai kuma yana ajiyeta ta soma hawaye. Zuciyarta tayi mata nauyi sosai. A take ya rude yana tambayarta ko me ya sameta. Duk yadda zaiyi Asmau taki magana sai kuka har yaji babu dadi a ransa. A sanyaye yace
"Kin tuna Abubakar ne? Addua ya kamata kiyi masa ba kuka ba"
Tayi saurin girgiza kai. Idan ya tabata kuma jikinta rawa yake sosai. Ganin taki magana sannan kamar tana tsoronsa sai kawi ya kwantar da ita yaja bargo ya lullubeta tare da yi mata kiss a goshi "kiyi hakuri idan nayi miki abinda bakya so ne. Just sleep bazan dameki ba"
Daya gefen ya koma ya zauna yana kallonta. Asmau ta juya baya tana kuka mai tsuma zuciya da tada hankalin mai saurare. Dole tayi kuka a wannan rana ko taji sauki a ranta. Yana gefe yana jin kukan har ransa amma ya rasa me take so.
Sai da tayi mai isarta yaji tana ajiyar zuciya. A zaune ma yake jingine da pillow yana kallonta ya rage hasken dakin sai fitilar gefen gado.
Baiyi fushi ba ya matso kusa da ita ya sanyata cikin jikinsa. Fuskarta duk hawaye ta matsa kusa dashi itama don kokari harda zagaye hannuwanta a jikinsa ta kwantar da kanta a kafadarsa tana mayar da numfashi.
Hankalinsa ya dan kwanta da yaji ta a jikinsa ya shafa mata kai "kukan me kika yi, dama akwai abinda zai saka ki kuka ki zabi yinsa ke kadai ki kasa fada min?"
Saukar hawaye mai dumi yaji a kirjinsa tace "Jikamshina don Allah da gaske kana sona?"
"Kinfi kowa sanin amsar tambayarki"
Ta dago kanta tana fuskantarsa kunya sosai a tare da ita. Muryarta ce take nuni da rauni da ciwon dake cikin ranta "a yau na kara tsanar kaina da biyewa zuciya, nayi aure a matsayin budurwa amma na dade da rasa wannan darajar. Ban san na gama cutar kaina ba sai yanzu, lokacin da duk wata mace take jin ta isa a wurin mijinta idan ya sameta cikakkiyar budurwa. Na rasa wannan damar, bazan taba yi maka tinkaho da abinda bani dashi ba. Ina jin kunyarka ina jin kamar na cuceka ma...."
Allah Sarki, tausayinta yaji ya kama shi sosai har tasa zuciyar ta raunana ya hanata karasa maganar ta hanyar da yasan dole tayi shiru. Sai da ya gama kissing dinta ya sanya yatsansa a saman bakinta. Tana kallonsa da fuskarta mai hawaye "ba karya kika yi min ba game da rayuwarki. Nasan komai kuma duk da haka Allah Ya sanya min sonki a zuciyata. ASMAU yarda da kaddara shine cikar musulunci. Abinda kika rasa bazai taba dawowa ba. Tunda kinsan baki da iko akansa babban abinda zaki yiwa kanki gata dashi shine hakuri da dangana. Mata da yawa suna aure a irin wannan yanayin kuma wasu sai kiga asirinsu ya rufu. Ke da naki ya fito fili kin zama misali ne ga sauran mata. Kinyi nadama kin tuba, kuma wannan ake nema daga dukkan musulmin kwarai. Allah Ya kara kare sauran mata daga haduwa da fadawa irin wannan sharrin."
Wani kukan mai karfi yazo mata tace "wallahi sau daya ne...sau daya tsautsayi ya fada mana. Ka yafe min don Allah."
Rungumarta yayi sosai a jikinsa duk dauriya irin tasa sai da yaji hawaye ya zubo daga idonsa. Ya Allah Ka nesanta mu daga tarkon zina. Mai zubar da kimar mai kima, ta zubar da girman babba, ta wulakanta mai daraja. Idan aka yita Allah zai iya yafewa wanda ya tuba amma wallahi tayi tambari kenan a rayuwar wanda yayi.
A daidai kunnenta yace "Ashe duk yadda nake fada miki ina sonki baki taba yarda ba tunda har kike kokwonto a yau. Ban taba karyata zancenki ba. Da kinso tun ranar farko zaki iya cewa Safina ba 'yarki bace kuma zan yarda. Fatana Matar Jikamshi shine mu kasance ma'aurata har a aljannah." Ya kwantar da ita akan pillow yana kallon fuskarta
"A daren yau nake so na goge miki duk wata damuwa da kika tsinci kanki a baya. Ina so na zama farincikinki. Ina so tarihin Asmau da Ishaq ya fara. A yau nake son rubuta kaina a zuciyarki. Ki yarda cewa kema abar so ce kuma da yardar Allah zakiyi rayuwar aure cikin jindadi kamar kowace mace. Abu daya kawai nake bukata yanzu daga gareki"
Maganganunsa sun sanyaya mata zuciya. Tsoron da take ji na zata wayi gari taga canji daga gareshi saboda rashin cikarta yasa ta kuka.
"me kake so"
"Kice kina son mijinki"
Sai da ta kalle shi tayi murmushi sosai sannan tace "I love you Ishaq, I love you Jikamshina. Ina sonka mijina"
Ya riko fuskata a tafin hannuwansa ya matso da ita daidai da tasa yana mata wani irin kallo.
"Lokacina da kika cinye kina kuka zaki fara biya yanzu"
Kokarin guduwa tayi ya janyota ya danne tare da rufa musu bargo.
Amarya da ango....asuba ta gari.
_Mrs Othman Maman Jannah gaisuwa mai tarin yawa gareki_
0 comments:
Post a Comment