Kafin daddy su tafi saida aka qara musu nasiha sannan suka rakosu har mota da xasu tafi Amra ta fashe da kuka😭kan lallai tare da ita xa'a tafi dakyar aka lallashe ta sannan suka tafi.
Bayan tafiyarsu suna daidai bakin qofan shiga falonsu ya ja mata kunne Wanda saida tayi qara sannan ya sassauta ruqon tare da fadin Allah ya soki baki gaya musu ba da yau jikinki yy tsami yarinya kuma inaso in fada miki wallahi koda wasa wani ya kuma zuwa gidan bawai momy ko dady ba kika ce zaki bishi bawai kuka ba kawai zakiga abinda zan miki shasha kawai ya tureta yai dakins bai kula da kukan da take ba yai dakinsa yana tsaki.
Da asuba ta sheqa wankanta taje tayi sallah.har qarfe tara ta bata bude dakinta ba,bayan ta idar da sallar walha ne ta bude dakin dan xuwa ganin menene xata sanyawa cikinta.A falo ta tarar dashi kwance daga shi sai singlet da dogon wando yana kwance yana kallon wani Indian film a zee cinema Player.
Ta gabansa ta wuce ta shige kitchen ya bita da kallo yace lallai ma yarinyar nan.ta fito hannunta dauke da mug na tea tana juyawa sai da ta zauna sannan tace ina kwana yaya hara ya watsa mata gami da tsaki bata ce dashi uffan ba taci gaba da juya tea dinta .wani takaici yakara cikashi wato yari yar nan me ta maidani ke ya fada afusace tai saurin sauke kofin da take shirin kaiwa baki me kike nufi ne nanfa gida na ne nufinki ni zan shiga ingirka abinda xanci ko me kallonsa kawai tai gami da mikewa tai kitchen ruwan shayi ta hado masa hade da soyayyan chip agabansa ta dire yako watso mata shayin wato ga mahaukaci ko dan tsabar wula kanci bama xaki tsaya kiji abinda nake cewa ba balle samun matsayin kiji me zanci ko sa'arta daya akafa ruwan ya zubo mata yakuma dan huce hakan yasanya bata kone ba yi kofin ta dauke gami da durkusawa tana tsince dankalin tsaki yaja yai dakinsa sai da ta gama tsincewa ta goge ko ina sannan tai dakin data ga ya shiga da sallama ta shiga baya falon hakan yasata shiga ciki tsawar da ya daka mata ce tamugun firgita ta har batasan sa'adda tai hanyar fita ba ke dakata jikinta na kyarma ta tsaya me yajawo ki dakina daman daman ta fada tana rawar murya daman what daman tambayar ka zan me za'a dafa ma yaja tsaki inda abinda ke bata haushi be wuce tsakinnan ba banaso jeki kawai harta kai bakin kofa yace bakiji ba tai saurin juyowa ki hadan kunin gyada da kosai to tace tai waje.
Da yake mami ta aiko mata da gyada hakan yasanya komai yaxo mata da saumi yunwa takeji sosai dan haka kaskon farko na kosan ta cinyeshi kunu tai mai gardi da zafinsa ta zuba akula ta fido kenan da zummar kai masa daki ta ganshi yana waya har ya wuce taga alamar fita zaiyi tai saurin cewa yaya abinci zankiraki taji yace daga bisani yace love u too sweat heart sannan ya cilla wayar a'aljihu bai juyoba yace kibaima almajirai bai jira me zatace ba yai ficewarsa wani hawayen takaici ya gangaro mata.
Tunda ya zauna kamshin abincin ke kwakularsa dadinsa da yarinyar ta iya girki yana zaune ji yake kamar yaje yace ta kawo masa girman kai ya hanshi koda ta kawo masa cewa yai baya ci ya shiga kitchen danna tukunnyar ya maida yawunsa ya hado shayi yai dakinsa bata ko kalleshi ba ta cigaba abinda ya dameta.
Zaune yake yana rubutu taxo tazauna adan kai kaice ya kalleta tace sannu da gida yaya bece da ita kala ba tace daman yaya magana naxo muyi nanma bece kala ba kusan minti biyar ya mike zai bar gun tace yah nace xamuyi magana ina kunne ne keji dolene sainayi magana ai dan kar inyi kahauni da fada eyye wato inhauki da fada ko watakan ga mahaukaci ta turo baki gami da juyar da kayya eyye lallai yarinyar nan.
"Ki kiyayeni,wlh na kula baki sanni ba ko dan na lura mummy na tare miki fada shiyasa kk rainani?toh xaki san koni waye Aliyu very soon" yajuya zai shiga daki tako saki tsaki karaf akunnensa yako jiyo a fusace.
Finciko ta yayi,saida hannunta yayi qara ya matse bakinta sosai har saida idonta yayi ja,ya hankade ta.
.
kadan kk ka gani ki kuma yimin tsami agudannan sai na fasa bakin naki mara mutunci kawai. Hawayen takaici ya kara zubo mata.
Gaskiya yaya sulaiman nai fishi ace tunda aka kawoni sai yau zakaxo ganina yai dan murmushi kema kinsan kina raina abubuwa suka min yawa mun kusa fara final exam ne tasaki dariya kace mun kusa zama likitoci yai dariya ah kun kusa kam to Allah ya temaka ta mike bari na kawo maka abinci kai saidai ki xuban in tafi dashi axumi nake ta hade rai wato baxaka sha ruwa ananba yadanyi murmushi karkiji komai xanyi xuwa na musannan yini xanyi.
Yanxuma dady ne ya aikoni yace ki bada takardunki jibi kuma zai turo kamal ya kaiki xakiyi register ta jamb tai dariya kace har anfara yace eh shinema yace naxo infada dan yasan baku sani ba inba nai fishiba tunda ashema da dady be aiko kaba vaxakaxo ke dai kin fiye mita kinga maxa ni dauko min xan wuce ai suna can gida kace mami ta duba durowar da nake ajiyewa duk komai na ciki ban tawo dasuba ya mike se naxo din to yahya ka gaida mami yafice da flask din data xuva masa abincin.
Kwana Biyu bata sanya Aliyu a idonta ba,Sam abun bai taba damunta ba,ta tsaya tsayin daka ayi n ibadarta abu daya ke damunta tsoro dan baya shigowa sai dare ya tsala dabadan ma in ta tashi tanaganin kofa abude ba baxa ce agidan yake kwana ba.
Ranar da yamma tana xaune da yamma tana sauraran wani wa'axin Sheikh kabeer Haruna Gombe akan biyayyar mata ga maxajensu da irin axabar da Allah ya tanadarwa matan da bata biyayya ga mijinta koda kuwa wani irin miji ke gareta ko talaka,mai kudi,dan iska,mara mutunci kar kiyi la'akari da abinda ke tsakaninsa da mahallicinsa ne,yau idan mijinki dan fashine ko dan yankan kai ne ya xamo wajibi kiyi masa biyayya kamar yanda Allah da manzonsa sukayi umurni iyakacin abinda xakiyi kiyi qoqarin xakulo shi daga axabar Allah addu'ah domin yin haka tamkar jihadine sbd haka 'yan uwanmu mata ya kamata mu dage Allah yasa mu dace.
Amrah hankalinta ba qaramin tashi yayi ba dajin wannan bayanin domin tabbas ya xamo wajibi tayiwa Aliyu biyayya matuqar tana son saduwa da rahamar ubangiji...duk runtsi duk wuya.
Fargabar amra daya itace yadda yah Ali zai karbi maganar karatunta dan ta fiskanci yanxu salo salo na mugunta yake fito dasu duk dan ya bata haushi da maganar take kwana take tashi ta rasa yadda zata fada masa cewar yau zata register na jamb.
*Qarfe sha Biyu*
Taji knocking a qofa taje ta bude was xata gani class mate dinta ne a secondary school su Zainab I Tukur,Ruqayya Abdullah, Nafeesa Shehu Lawal,Zee yabour,Hussy suka shugo tana mmki tace sannun da xuwanku Xee harda ke tace hmmmm ai wlh Amrah bamu taba sanin xaman da mukeyi dake kenan a skul ba ace auranki ya tashi bb gayyata kawai ji mukayi daga sama Hussy tace ke kuyi shuru ai Amrah ni nayi niyyan inxo in xaxxaga Miki nawa masifanne ace duk kirana mummy da kk yi wai daughter xata yi aure ban sani ba wannan ai abun kunyane kinason mutane suyi mana dariya koh daughter😡tayi mgnan cikin rashin jindadi.
Amrah tace kuyi hqr abunne ba'ayi tsammani ba sannan tayi musu bayani sun jinjina lamarin tare dayin musu Allah sanya alkhair ya bada xaman lfy da qasantar daki tace ameen tagode tana jinjina kaman qaxantar daki a ranta wato 'ya'ya ta amsa ameen ne domin kar su San akwai wani matsala tattare da ita sannan kuma a ranta tayi alqawarin xama da Yaya Aliyu koda kan kullum xai dinga yanka
naman jikinta yana ci.
Sunyi hira sosai na tsakanin qawaye domin sai qarfe shida suka yi mata sallama kan cewan xasu tafi gida da xasu tafi kamar kada su rabu haka nan suka bata gift dinsu kan cewan suna tare kuma xasu yi xumunci ta rakasu suka tafi kowa da kewan dan uwansa
Zaune yake yana hira da mukli dan duda sunyi aure da Amra ya kasa rabuwa da muklinsa kullun suna tare a waya danma bata kasar shiyasa nake sanki wallahi Amra dake tsaye tace yah yadago mata hannu alamar ina xuwa I will call u back sweat heart ya kashe wayar afusace ya kalleta ke lpy tace yah magana zamuyi shine xakixo ki damen ke bakisan mutun in yana waya ba yi hakuri tace sai afkin ki cuci mutun ki bashi hakuri me zaki cemun daman jiya yah sulaiman yaxo yace gobe yah kamal zaizo yakaini danyin register din jamb afusace ya kalleta kina nufin karatu xakiyi ba zaman aureba gabanta ya fadi cikin kin kina tace dady ne ya aikoshi to ni atsarina mata ta baxatai karatun jami'a ba kin gane to kawai tace tai daki tana kuka.
Koda yah kamal yaxo tace masa ai ita ina yanxu bata sha'awar karatu yadda ya ganta yai tunanin da wata akasa yadda yasan kanwar tasu da dan banxan san karatu rana daya tace ta fasa koda yakoma gida ya fadama dady mami tace ina ai tasan Ali ne xai hanata hakan yasa dady kiransa ya ci masa mutunci dole ya hakura ya barta.
Amra tai sa'a jamb tayi kyau dan taci maki sosai aiko murna bakama hannun yaro kasantuwar an soke post UTME yasa tunda akai jamb din akaga taci dady ke ta cuku cuku har saida yaga tasamu admission randa kuwa aka kawo mata admission ko bacci batai cikakkeba minti kadan sai ta juya ta dauki admission letter din takalla ta saki murmushi gani take kamar ma burinta ya gama cika.
Amra yau xa'a fara daukan lectures a class da doki ta shirya cikin jin dadi yau an xama yan university😜ta gama shiryawa ta fito falo dan jiran Yaya Aliyu ya shirya ya kaita sbd yace matanshi ba xata yi driving ba taji shuru×2.kamar tayi kuka ta dai daure domin xuwa dakin shi taga lfy xuwanta ta tarar da yana bacci tayi turus ynxun kada in tashi masifaffe ya fara man fada ta kai batasan sanda ta shagala da kallonsa ba sai yau ta taba yima yayan nata kallon tsaf baccinsa yake cikin kwanciyar hankali sai yau ta yadda da su bilki da suke cemata yayanta me kyaune tsawar da ya daka mata ce ta dawo da ita daga hankalinta lpy kika wani xuban idanu cikin jin kunya tace daman yaya lokacin sch yayi naga baka tashi ba xan makara se akai yaya kuma kace baxan tuki ba ok jeki yanxu xan fito yah nafa makara nace kije ko tai waje yafi minti shida sannan ya fito dinning ya kalla me kike nufi ina abinci na yah nafa cema na makara ke kikaga xaki iya karatu ni auro ki nayi inkinga kin bar gidannan kin dafan abinci rai abace taje ta ta daba masa tsaye ta ganshi xuban a flask har bakin mota ta kaimai ta bude xata shiga yace na makara ki kirawo sulaiman ko wani a babban gida su kaiki bai jira amsarta ba yaja motarsa yai waje hawayen takaici ya xubo mata dan tana san makarantar ne da wallahi baxata ba haka ta kira yah nasir ya kaita sun sha hira nanma yake fada mata kwanaki mami bataji dadi ba tai ta mita tace xata je ko da daddare ne.
Yana zaune yana cin abinci ta zauna kusa dashi baiko dago ba balle yasan da ita tace yah lpy yace daman yah Nasir yace mun mami bataji dadi ba shi ne nace dan Allah ko xaka temaka ka kaini daga nan inasan inje sabuwar kofa wato asalin gidan iyayenta ce miki akai ni direbanki ne eyyi tai shuru to ba inda zan kaiki bakuma xakije ba batace uffanba sai hawaye kawai da take yafi minti uku yana kallonta yaja tsaki shirya muje tasaki murmushi nagode yaya tai daki.
Tayi shigarta dingin bingil material ce pink ta amsheta sosai,ta fito falo sai kamshi take yi shi har ya saba da cin abinci mai dadi da kallon kwalliyar kallo daya yai mata ya dauke idonsa yana gaba tana biye da shi.
A can gidan mami hira suka sha ita da yan uwanta ji take kamar karsu tafi jin zata gida yasa mami hada mata tsara sosai dan kai musu.
Acan sabuwar kofa ma dai sun taba fira dayake in kadauke shakuwa irinta jini basu wani saba ba kannenta ma bakuwa suke daukanta mamanta tace ina dai kuna zaman lpy tai dariya eh mama to Allah ya dawwamar bata ce uffan ba dan kunya yawwa inasan fada miki nasani Hajiya Aisha uwa ce agunki anman kisani Aliyu danta ne dole saikinyi hankula da kai mata kararsa ko sukarsa kinji ko diyata tai dariya to mama tare ma muke dashi babanta dake kan tabarma yna cin tuwo yace jaji ja'ira bakya bakya cewa yashigo wallahi baba nace yashigo yaki ya mike hara haje yana ganinsa ya durkusa yana gaisheshi haba Ali se kace wani bako yai dariya to muje mama na ganinsa tace dan nema wato surukuta kame damu kenan ai da kanka tsaye kake shigowa yai dariya yana sosa keya ananma sun sha fira sai goma suka koma goda.....
✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Ummusulym*
*F.A.Ya'u*
Dan ci gaba duba b
fayau9.blogspot. Com
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
*AMRATU*
*page 45➰50*
*Na*
*Ummulsulaym*
*Da*
*F.A Ya'u*
fayau9blogspot.com
fayau26.wordpress.com
*Short and brief story*
*We Dedicated this page to Xee Yabour,Husnarh(my hussy)Miss Xoxo,Miss Mjay,Miss Gorgeous, Memxiey,Tuartah Aberdah(Taurah😜),Also Noor Luv you so much kwando-kwando😜😘😘😘*
Suna komawa gida lkcin ta gaji sosai da yake sun cika cikin su bata wani kalla kitchen ba tayi shigewata can bacci ya fara daukanta taji rankwsmashi ta tsakiyar kanta wani azababben zafi ya ratsata cikin magagin bacci tace haba wannan wane irin wulaqancine mutun yana cikin bacci sa aso a tasheshi...bata qarisa ba taji a murda bakinta tare da jan mata kunne keh tashi ai da sauri ta mitsika ido data tuna abinda tace batasan sanda gumi ya keto mata ba a ranta tana cewan lallai kashina ya bushe,yaci gama keh ni kk wa rashin kunya tabb yau jiki xaiyi tsami yaja mata kunne Wanda saida ta durqushe qasa ya qara jah da qarfi sannan yace dan wulaqanci ke na sane da kullum da daddare kafin in kwanta sai nasha ruwan Lipton Amman yau tunda kin rainani kk yi shigewarki gani dan iska kinyi shigewarki ba xaki dafa ba ko inyi duk abinda xanyi yana mgn ne hannunsa riqe da kunnanta cikin kuka tashe Allah Yaya Aliyu baccine bansan sanda ya kamani ba kawai gajiyane nayi yace "eyye wato kinma gaji ni kike cewa kin gaji ni nace ki kirkiro tafiyar ina seda nace bazaki ba kika sakan kuka ?" Tayi shuru toh ynxun muje ki hada maxa ki kawo minti biyar in ya wuce double punishment 😡aikam har kitchen ya rakata sannan ya sakar mata kunne ya tunkudata.
Aranta tace Allah yah Ali mugune dan dai ruwan tea tunda nai bacci ai ya dafa ahaka tana tsaye har ya tafasa kanta ke mata wani irin ciwo sakamakon tsoratar datai da ya rankwasheta haka ta daure ta kai masa.
✨✨✨✨✨✨✨
Yana sana'ar tasa wato danne dannen laptop ta kawo saida yaja aji sannan ya daka mata tsawa tare da cewan da yake kin rainani koh dole ki yi mini tsaye akai saina amsa tunda ga sa'anki yana mgn jiki na rawa ta ijiye sannan sum sum ta tafi daki ta haye gado saida tayi kukanta 😭ma ishi sannan barci ya kwasheta.
✨✨✨✨✨✨✨
Da safe da xaxxabi ta tashi sbd a daddafe tayi sallah subhi sannan ta koma ta kwanta sbd jin kanta wani irin sarawa da yake yi
✨✨✨✨✨✨✨
Safiya lkcin tashi bacci yy domin Six take tashi tayi aiki da girki sannan ta shirya xuwa makaranta Aliyu ya kaita yau yajita shuru baiji alamun ana girki a kitchen ko wani alamun movement dinta yace "Ah lallai yarinyar nan wuya yy qwari amman xanyi mgninta sbd wulakanci sai munyi latti"
Ya dai xauna shuru shuru bb alamun ta ya tashi da niyyar yaje yaci mutuncin ta yana qiyasta abinda xaiyi mata a ransa yana xuwa yy turus ya tsaya dalilin hangota da yy can quryar gado da qaton blanket sai rawan sanyi takeyi
*Tuartah yar sa ido👁bata bari ya qariso ganin me ya samu Amrah ba har tayi saurin sako kai nai saurin turata baya to yar sa'ido ina ruwank 😜*
✨✨✨✨✨✨✨
A fusace ya yaye blanket din da niyar fara fadan da yasaba yadda ya ganta a dunkule tana rawar dari yasa shi fadin subhanallah ya dagota tai saurin janye jikinta yaja tsaki ke tun yaushe ne baki da lpy tai shuru koda yake ma ace mutun bashi da sana'a sai kuka ba dole jikinsa ya gaza ya fara cuta ba ya mike gami da ficewa.
✨✨✨✨✨✨✨
Ita dai tana kwance yadda ya barta ko motsawa ta kasa yi ya shigo rike da tea mai kauri da ya hada mata gefe guda kuma yana rike da magani ya dagota ahankula yake bata harta shanye ya bata maganin saida yai jan ido sannan ta iya sha aikuwa tana sha tayo amansa ajikinsa takaici ya kamashi ya mike gami dayin waje da tsumma ya shigo ya goge gun tas itama ya goge mata jikinta data bata sannan ya dauko mop ya goge gun ya kamata zuwa toilet da zunmar wanke mata jikinta data bata aiko yana kokarin xuba ruwan taga dai dagaske yake ta noke zan wanke ya tabe baki gami dayin waje.
✨✨✨✨✨✨✨
Karnin da yaji dakin nayi yasashi feshe shi da turare nan da nan kamshi ya bai baye ko ina data fito yace bara na kira doctor tace yah kabar na warke hararar da ya watsa mata yasata yin shuru kan doctor yaxo ya kammala girki dayake tun yana gida ya iya komai dan mami dan sun kasance maxa hakan besata kasa sanyasu aikin gida ba.
Koda doctor yaxo yace ai gajiya ce kawai ba wani abu ba ta dan huta ya rubuta mata magani gami da tafiya aranar yini Ali yai yana mata hidima komai na gidan shi yai ita dai binsa kawai take da ido.
✨✨✨✨✨✨✨
Yah na shirya ta fada ya dan kalleta harta fada yace kin shirya me sch mana ya cigaba da abinda yake bai ce mata komi ba ta kuma daurewa yah nafa shirya zan makara adan fusace ya dago ke wai bakisan ciwon kanki bane na fuskanci zaman gidanne bakiso inba haka ba mutun bai da lpy yace sai yaje makaranta tace cikin raunanniyar murya wallahi yaya na warke kuma ganinai banyi reporting ba kar ayi attendance ko test eh kice karatu yafi lpyar ki to ba inda zaki tai rau rau da fuska zata sa kuka yace karki fara nafada miki batun yauba inda abinda yafi ban haushi dake to wannan kukanne ki koma daki ki kwanta kuma nashigo naga kina kuka Allah nida kene.
✨✨✨✨✨✨✨
Sai da tai bacci ta tashi ta tuna da maryam kawarta da sauri ta dauki wayarta dan kiranta ta fada mata bata da lpy ko dan ta sanar sai dai wayar bata shiga gashi number dinta kawai take da dan da ita kawai suka saba sosai taja tsaki itama dai maryam matsala ce wallahi ta fada gami da saukowa daga gadon toilet din dakin tashiga tai wanka gami da dauro alwala dan lokacin azahar yayi sai da tai sallah sannan ta fito da niyar dafa abinci.
✨✨✨✨✨✨✨
Ga mamakinta yauma kamar kullun tana fitowa falo komai tas kamshi kawai ke tashi wato yah Ali ya gyare gidan tas tai kitchen da zummar dora abinci ta akan tukunyar taga ya dora takarda da rubutu kamar haka _your breakfast in the dinning_ tai murmushi gami dayin waje komai yayi tana ci tana murmushi lokaci lokaci tana tubawa da yanayin Yayan nata.
✨✨✨✨✨✨
Jikinta yai sauki batajin komai dan yanxu tana riga yah Alin tashi ta kammala komai anman taga alamar har yanxu bai ga damar barinta taje sch ba hakan yasa yau tai niyar zuwa ta sameshi yana zaune yana kallo tazo ta zauna ko kallon inda take bai ba tace yah sannu da gida bai amsaba ta riga ta saba da halinsa tace yah dan Allah kaga fa na warke gobe ka barni naje sch pls yadda tai maganar yaso bashi dariya ya daure kije zanyi tunani pls yah to shikenan ki shirya tunda naga kin dena kuka tai murmushi gami da far da ido nagode yaya tai ciki.
✨✨✨✨✨✨✨
Ai kuwa a sch tasha ciwon baki bataxo ba kwana biyu anyi test hankalinta ya tashi dataji malamin dayai dan shi inbaka da test co direct aikuwa akan maryan ta hakke ita dai maryam hakuri ta dinga bata tace network ne ita wayarta kullun akunne take ita ce ma ankirata akashe.
✨✨✨✨✨✨
Dan Allah maryam in mungama lecture dinnan zaki rakani muje inroki malaminnan ko zai min test din ke nifa tsoronsa nakeji inji maryam pls kawas zainab dake gabansu tadan juyo kunsanfa halinsa kudena surutu karku jaza mn masifa kan tai shuru sukaji yace Amra Muhd Nasir stand up pls Amra ta kwalalo ido nashiga uku ina wannan mutumin yasanni Maryam tace ki tashi watakil yaga surutun da muke cikin Amra ya turu ruwa........
✨✨✨✨✨✨
0 comments:
Post a Comment