Who is Amra nace jin ya fadi haka yasata dan colling down tunda ta gano be santa ba maryam ta taba ta ki tashi karyai fushi ko bataxo bane tai saurin mikewa gani sir yadan kalleta au da kina ma gabana kikai min shiru koda yake ai naga tun daxu firar ku kawai kuke sorry sir tace any way u are deceiving ur self not me kinga ba ma wannan ba ya gijin ya fada tai saurin kallonsa Yayanki yaxo ya samemu yace baki da lpy nai test ki shirya gobe xan baki make up baiji ta cewarta ba yai ficewarsa dan daman ya gama lecture dinsa ana ficewa ta fada jikin maryan tana murna kai anman naji dadi da tuni co direct tai dariya mantawa nai ban fada miki ba ai tun randa bakixo ba yayanki me kawoki wataran yaxo ni nama kaishi office din Hod tai dariya aranta tace yah Ali kenan miji nane ta fada a hankula what maryam tace da ita ita kanta batasan sanda ta furta miji nane ba kunya duk ta rufeta.
✨✨✨✨✨✨✨
Maryam ta riketa da gaske kike kina da aure tai dariya eh zance ne be tada zance ba tun kanna shigo nakeda aure kuma da gaske shine mujinki ta daga mata kai alamar eh kai anman kinyi dace wallahi ko yai dace ba suka sa dariya Allah ki yadda dani samin sa a miji ba karamin dace bane kinga ni mubar batunsa awwo kishi kike ko tai dariya 😃 kawai.
✨✨✨✨✨✨✨
Waiko ina yayan nan naki Nasir tai dariya kwayi kwa gama ai tuni na ganoku kuna wani kunbiya kunbiya shima tunda ya kyallara ya ganki ya hanani sukuni ganin ta rafkota yasata sauya zancen da wani ke yar gata ce Amra ko ta fada eh mana ko ina kikai yayu na biye dake ga mijinki me sanki aranta ta kuma mai maitawa gamijina me sona tai dariya kawai.
✨✨✨✨✨✨✨
Koda ta koma gida ta kammala komai ta zauna dan kallo anman ina tunanin Yah aliyunta ya cikata shi kawai take ganowa yayin da yake goge mata jiki lokacin da bata da lpy ita kadai taketa sakin murmuahi musanman idan ta tuno lokacin da yake fada.
✨✨✨✨✨✨✨
Yana zaune yana kallo ta zo ta zauna a kujerar datake kusa dashi tace yah sannu da gida yaya yawwa yace batare da ya kalleta ba ya ciga ba da abinda yake can ya dago ko da wani abunne a'a daman cewa xanyi na gama abincin na kaima dinning ok nagode wani dadi ya cikata yau yace ya gode ji take kamar yai mata wata gaga ruwar kyautakyauta.
✨✨✨✨✨✨✨
Yana ci tana kallonsa jefi jefi tana sakin murmushi shiko gogon nata ko ajikinsa dan bema san tanai ba yadan jiyo jin ajikinsa kamar ana kallonsa tai saurin dauke kanta yaso fuskantar wani abu ya tabe baki gami da ci gaba da cin abincinsa dan baya gajiya da cin abincin yarinyar mami tai mata horo wajen iya girki ganin zai ganota yasata mikewa tai daki.
✨✨✨✨✨✨✨
Yadda suke zaune ba yabo ba fallasa fada dai yaki dewa yayinda ita kuma taki dena shagwaba abinda ke bashi haushi da ita dan ko ayau ta hadu da mami sai tayi abinda be saniba jikinta ya saba tana iya kokarinta wajen san ta dena.
✨✨✨✨✨✨✨
Kai Abbakar ka cika natsala daga can daya barin bataji me akace va taji dai yayan nata yace to shikenan sai kaganmu ya kashe wayar ganin goma tayi wato time din baccinta yasata mikewa da zummar yin daki ke ya ce taja ta tsaya gobe ki shirya zamu gidan Abbakar to yaya tace tai ciki.
✨✨✨✨✨✨✨
Washe gari ta shirya tsaf tai kyau sosai ta fito baya falon tai dakinsa da alama alokacin ya fito daga wanka yana goge jikinsa kunya duk ta kamata ganinsa dagashi sai tawul tai niyar juyawa ya tsai da ita ina kuma xaki gani nai kana shiryawa yaja tsaki matsalarsa da yarinyat tafiye gida danci ok fadi me ya kawoki daman cema xanyi na shirya yadan kalleta ke na fuskance ki gabaki daya bakisan zaman gida wato danace zamu unguwa ai shikenan farin cikinki yaxo zaki shirya da wuri tasaki murmushi😃 kawai tai waje dan ta rasa me zatace ganewa ne beba ita ba unguwar takeso ba face fita dashi din dan ko bakomai in sunje gu baya shurun da yake mata agida zagewa yake ayi fira tare dashi ita ayanxu ba abinda takesan ji kamar muryarsa koda fadane shiyasa inta tarasa yadda zatai yai mgn take tsokanoshi yaita fada 😡tashige daki tai ta dariya.😂
✨✨✨✨✨✨✨
Yai kyau shima cikin shigar shaddarsa blue komai yaji inji matasan yanxu yai mata kyau a ido jitake kamar karta dena kallonsa tadai basar sai ayanxu yadan kalleta muje ko tai saurin yin gaba yaja ya tsaya ke me kike nufi ne tadan tsaya gami dabkallonsa kina nufin da wannan shigar zaki fita takalli kansa me tayi bansani ba jeki ki sauya matar aure ce fake yah naga kai zaka kaimu ka dawo damu ya daga mata kuma naga kinga ni atsarina matata hijab xata sa ta turo baki anman ko bakomai taji dadi tunda dai ya dauketa matarsa tai ciki.
Tafito sanye da hijab shi bega abinda ya sauya ba yaja tsaki suka tafi.
✨✨✨✨✨✨✨
Acan gidan Abbakar ansha fira da korafi kan Aliyun be kyauta ba ace tunda sukai aure ya kasa kai matar aagaisa mita kam yashata da yake sun saba da matar irin masu rahan nance tai tamasa tsiya eh kayi aure ka gujemu yace ke kuwa ba dole ba cewa nai ba huta da gori nima dai wane gori inkaga ka huta dashi sai kun aje mn babies kunya duk ta cika amra fuskantar hakan yasata janta zuwa ciki aiko tun tana sun sunkewa harta ware suka sha fira irinta gari dan Amra irin mutanannan ce da baka taba jin sirrinsu sai dare suka baro gida tare da jibgin alkairi daga Amina matar Abbakar.
✨✨✨✨✨✨✨
A hanya yake tambayar ta mene babu agidan tace aranta gida akwai komi saidai ginshikin gidanne babu afili tace akwai komi kifi da tumatir ne babu a jifato ya tsaya har ta fito da zummar binsa ko me ya tuna ohoo yace koma ki jirani.
✨✨✨✨✨✨✨
Da suka koma gida ta kaimasa tea dinsa tai dakinta wanka ta shiga tai wankanta gami da dauro alwala sunyi isha acan dan haka shafa'i da wuturi tai tafada gado dan tagaji sosai gashi gobe monday tanada lectute 8.
✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Ummusulym*
*F.A.Ya'u*
[1/7, 3:44 PM] Fadima A. Ya'u(F.A.Ya'u)😘: ⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
⚜
*Amratu*
*55-60*
*Na*
*Ummusulym*
*Da*
*F.A.Ya'u*
*In Dedication to Halima Dangado(Dangadoriasis)😘😘*
fayau9.blogspot.com
Fayau2626.wordpress.com
Da wurwuri ta tashi ta kammala komai dan tanasan yau tashiga sch da wuri karfe bakwai dai dai ta fito ga mamakinta Yah Alin bai nan tai dakins sai takar da ta gani kan gadon da alama ita ya barma ta dauka abinda ta gani shine _Nashiga baki tashi ba jiya ban fada miki ba anturamu kaduna a gun aiki yau zan dawo ki kijira nace wani agida yaxo ya kaiki sch_ har ga Allah har ranta taji ba dadi tace Allah ya dawo dakai lpy aranta tai falo ko karyawa ta kasayi sai a flask ta zuba tana jiran me zuwa kaitan.
✨✨✨✨✨✨✨
Tadan russuna ta gaidashi Yah nasir ina kwana yaki amsawa shima yafan russuna kanwarmu ina kwana ta turo baki kai yaya nafa ce bana so nima nace ki dena gaishe ni kinki kefa matar yaya na ce Allah zanyi fishi dakai to ayi hakuri baxan kuma kaso ka makara yai murmushi bansan da zuwanba seda naga yaya sulaiman zaixo yace zaizo kai kine nace yabarshi na kaiki tai dariya kaji dashi dai yadan kalleta me xanji dashi tai darita ni muje ina makara.
✨✨✨✨✨✨✨
Ahanya yake mata maganar maryam tasa dariya ahaf ai nasani me kika sani ohoo gashi data fara wari mun faraji kinga ni bafa wasa nake ba pls ya za'ai ko number dinta ki ban tadan daga kai alamar tunani any way zanyi tunani haba aunty Amra ta tsuke fuska to wallahi zaka sanya infasa to nadena kanwarmu ta bude motar gami da lekawa inkaje ka gaida mami dan Allah kace wanda zaizo dauka na yaxo da wuri to yace tanxu number dinfa kabari zan tambayeta to shikenan se najiki.
✨✨✨✨✨✨✨
Bayan sun fito daga lecture Aisha taxo pls maryam yunwa nameji zoki rakani village Amra tace af kinga na mance naxo da abinci inxaki ci me zai hana yadda nakejin kudinnan nawa suka saka dariya dayake abincin da dan yawa tare suka ci su ukun Aisha sarkin jama'a ta mike ina zuwa tai gun dataga wasu na fira.
✨✨✨✨✨✨✨
Amra ta kalli maryam ban fada miki ba inajinki ai yau mutumin naki ne ya kawo ni tsaf ta gane wa take nufi ta basar wa kenan tadan kalleta ana so ana kaiwa kasu pls wa kike nufi ban gane ba waye inbanda Yaya Nasir tadan ja tsaki yaushe ta zama mutumina ohooo kya tambayeni kinga daman cewa yai inbashi contact dinki nace ai ankusa bikinki ta fadi haka ne dan ganin yadda zatai what inji uban...tai saurin rufe baki haba Amra yazaki min haka ke kika kusa bikin nawa aiko ankusa nasamu kama Nasir butsewa zanyi kaji yar newa to cewa nai zanmaki mgn abinda kika ce ynx zance ya kwantar da hankalinsa kema kina ciki haba ke kuma karki bada ni mana bama haka suka sa dariya vaki daya.
✨✨✨✨✨✨✨
Koda aka tashi Nasir ne yazo daukan Amrar sai da ya takura mata ta kira masa maryam dan ita tayi faculty din History dan dauko kanwarta da yake ita take driving aiko awayar tasha tsiya takusa minti goma bataxoba ta koma gefe dan kar yajita ke banfa san wulakanci yaysn nawa ma sai anja masa aji tai dariya yi hakuri ganinan.
✨✨✨✨✨✨✨
Anya kuwa kin kirata wallahi na kirata yaya tace kanwar tata ce bata fito ba ok ban wayar na kirata kan tace wani abu ya faketa ya kwace wayar yasa number din awayar tasa yana kokarin kira ta karaso Amra na kallonsu sai wani shassharewa Maryam take kasa kasa take musu dariya dan kar yagano wani abu.
✨✨✨✨✨✨✨
A gida gabaki daya ta kasa bacci duda bata iya wuce 10 sai gata har 11 idonta tan gararas sai 12 ya shigo gidan ga mamakinsa tana zaune ta rafka ta gumi bakuma kallo take ba dan ita din ba gwanar sa bace yazauna wash ya fada duda yai sallama bataji ba wash din data ji ne ya firgita ta tai saurin dagowa atsorace yasaki murmushi matsora ciya kawai tai dariya lah yaya sannu da zuwa yawwa ya fada ban ruwa ta mike jiki na rawa tai gun fridge yakar ba yasha tai dinning area ta hado masa abinci sai da ya fara ci ta mike gami da gada masa ruwa nakai maka toilet tadago yana murmushi me ya hanaki bacci kamar tacd rashinka ta daure tsoro to ynx na dawo jeki ki kwanta gobe da sch nagode Allah yai albarka amin ta fada gami dayin dakinta har bacci ya dauketa tana tunawa da dagowar dayai cike da murmushi fuskarsa maganarsa ke mata yawo aka to ynx na dawo jeki ki kwanta Allah yayi albarka.
✨✨✨✨✨✨✨
Da safe da wuri ta tashi ta gama komai tai makaranta A sch maryam ke mitar wallahi Amra baki da mutunci jiyafa kinso badani tai dariya tunda ban badake dinda ai shi kenan Allah da gaske nake inkina dariyar nan sai inna kalloki se inji nima kamar in sheke da darita kai dan Allah me yasa baki sheqe dinba mtseeew taja tsaki gami dayin gaba.
✨✨✨✨✨✨✨
Amra tabi bayanta ayi hakuri haba sis bafa ma haka dake ni ki kyaleni dole tasata dariya harta tsaya baki fadan ya kukai ba tadan tsuke fuska sirrinmu ne aha lallai masoya haka zaki ce eh haka zance to dai kiyi ahankula se inki baki shi ko sannu babarsa tasa dariya.
✨✨✨✨✨✨✨
Toma wai ke banda abinki Amratu ai ke zaki girmamani yayanki nake aute hoooo maryam Allah ya shiryeki wato ma harkin daura muku aure ahtoo ya ranki fari tas tace to bari yazo zaki sha mamaki tai aji tana dariya maryam tabita da sauri me zaki ce masa ah ohoo ki bari inyazo kyaji tai tai tafada mata taki.
✨✨✨✨✨✨✨
Agida suna zaune suna cin abinci ita abincin ma bawani ci takeba shi kawai take kallo wayarsa dake can kan kujera ta hau ruri yace mikon wayar can ta mike da hanzari bata duba wake kiranba dan kar kiran ya tsinke ta kawo masa yadan kalli screen din waya yawani saki murmushi kafin ta kara akunnensa taji yace Aminci agareki yake masoyita wani tukikin bakin ciki yazo mata wuya bataji me akace ba daga daya barin sai murmushi dataga yasaki tare da kara narke murya tare da naki afusa ce ta tashi tabar gun hartana faduwa dan ita kadai tasan me takeji aranta ya juyo ya kalleta ya tabe baki alamar i don't care yaci gaba da wayarsa......
✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Ummusulym*
*F.A.Ya'u*
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜
⚜
*Amratu*
*60-65*
*Na*
*Ummusulym*
*Da*
*F.A.Ya'u*
fayau9.blogspot.com
Fayau26.wordpress.com
Daki ta shige ta bugo kofar da karfi tana shiga kuka ya kwace mata ta jingina ajikin kofar kuka take maras sauti tun tana tsaye harta kai kas saida tai mai isarta sannan taje ta wanke fuskarta bata koma takan abinci ba ta hau gado danyin bacci anman bacci yace shi bai shirya ba.
✨✨✨✨✨✨
Zaune ta tashi to ma wai mene naki na damuwa dan yayi waya da wata zuciyarta ta fada mata wani barin yace mata kardai fa kin kamu dasansa ina ta fada baso bane afili can ta mike tahau zirga zirga inba so bane to mene kishi ta kada kai wata zuciyar tace ai mijinki dole kiyu kishinsa alwala tadauro ta dauko alkur'ani dan karantawa ko taji dadi aranta.
✨✨✨✨✨✨✨
Washe ruwan shayi kawai ta dafa sai kwai data soya ko dakinsa bataje ba bslle yasamu matsayin gaidashi shikansa yai mamaki be kawo komai ransa ba ya fito tana zaune akujera tadan kalleshi fuskarta adaure ina kwana tace ya amsa batare da tunanin komai ba yaje dan karyawa.
✨✨✨✨✨✨✨
Bai ce komi ba ya ci abincinsa ya mike muje ko tabi bayansa ko amota tunda ta sunkuyar da kanta bata dago va sai da yace zaki iya fita ta fice batare da tace kala ba ya kada kai kawai ya tafi aransa yana cewa yau yan shaga bar suka motsa dan yaga babu abinda tai agidan yadda ya kwanta yabarshi haka ya tashi yaganshi.
✨✨✨✨✨✨✨
Sakawa take tana war warewa ta rasa me zatayi a sch ma a sabule ta wuni har aka tashi maryam nata tambayarta me yasameta sai dai tace batajin dadi ne jitake kamar taje ta fasa wayar tasa.
✨✨✨✨✨✨✨
Koda ta koma gida indomi ta dafa ko ci batai ba ta ajiye masa a dinning tai dakinta da ya dawo yai mamakin rashin ganinta a falo be kawo wani abu ba yaci abincinsa sannan har ya kwanta ya mike dan zuwa yaga me yasa bata fito ba dan hankalinsa ya kasa kwanciya.
✨✨✨✨✨✨✨
Tana jiyo bude kofar tai saurin kwanciya alamar bacci take batasan ya ganta va tace au dankin dafa indomi shine zaki koma yar buya dani ta bude idonta dayai jawur sabida kuka tace kaina ke ciwo sub hanallahi kinsha magani tace eh Allah ya sawwake ya fada gami dayin waje.
✨✨✨✨✨✨✨
Yanayin waje hawaye ya zubo mata wato shi bemasan me take ma fishi ba shi yadauka shirmenta kawai take kaico na ta fada.
✨✨✨✨✨✨✨
Dasafe ta fara wucewa tai dakinsa yana wanka wayarsa ta gani kan bed side drawer nan hankalinta ya bata ta dauka da sauri ta dauka number din mukli ta nemo tai niyar gogewa se ta fasa tasa ta black list ta shiga watsap tai blocking dinta tai ficewar ta dan ta fuskanci ita take kiransa shi kuma na biye mata.
✨✨✨✨✨✨✨
Fes tajejin ranta dan ji take kamar ta rabasu tunda inta kira bata shigoba ta turo message be shigo ba intana da tunani ta hakura shi kansa yai mamakin yadda ta sauya cikin fara'a suka gaisa abuncin a flask ya tafi dashi suka fuce.
✨✨✨✨✨✨✨
Yau gidan a cike yake dan kannenta na sabuwar kofa ne suka zo dadi ya cikata sai nan nan take dasu tun safe sukazo sai dare zasu tafi koda Aliyu ya dawo dashi sukai ta fira dan sunma fi sabawa dashi kan yayar tasu.
✨✨✨✨✨✨✨
Da zasu tafi ta basu turarurruka Aliyu yadauke su dan maidasu sai da ya biya ta Sahad yai musu tsaraba sannan ya wuce dasu gida acan gida mama take ta mita ku yanxu daga ziyara sai wahala yai dariya ina wahalar take mama au haka zaka ce to kuwa zasu dena zuwa ayi hakuri yazauna suka taba fira ya wuce gida.
✨✨✨✨✨✨✨
Allah maryam nayi fushi ta kalleta me kuma nayi ace baki taba zuwa gidana ba ko sau daya ayi hakuri kimin uxiri tadan harareta uxiri fa kika ce haba Amra tarefa muke karatunnan dake kina kallo a sch muke wuni da kefa taushe fa baje gida natafi yawo au zuwa gidan nawa ne yawo ba komai ta kada kai tai dariya ayi hakuri ba haka bake nufu ba zaki ganni tsulum kedai ki tanadi kayan dadi yaushe to sai randa Allah yayi taja tsaki kice kawai bazaki xo tai dariya nidai bance ba.
✨✨✨✨✨✨✨
Yaya mezan dafa yadanyi shuru kiyi kome ma kika ga yadace to yaya tace tai kitchen da yake yau ba aiki suna gida dan shi ba gwanin yawo bane innyaje gida ma mami cewa take ya dawo gidan matarsa koda ba fira sukeba anman sun saba zaman guri daya duda kowa kowa da abinda yake.
✨✨✨✨✨✨✨
Bawani abinci me wuya taiba danbun kuskus tai sai dan lemo tana jerawa a dinning taji kamar ana taba kofa ta basar dantaji kamar iska ce kawai ta cigaba da abinda take tsaf take tai kyau cikin pink din diguwar riga alamar dai bugun da gaske ne har Aliyu ya mike zai bude ta wuce shi bari na duba.
✨✨✨✨✨✨✨
Wa zata gani muklisa wato
tsohuwar budurwar Alin ce gabanta yai
mugun faduwa ta daure Aunty mukli kece eh bakiyi tsan mani ba ko tadanyi murmushi ba haka bane ok me gidan yana ciki kamar tace a'a tace eh basu jira karashen amsar ba sukai ciki tabi bayansu da kallo tana sake saken abu buwa da dama.....
0 comments:
Post a Comment