YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(01)
Kayataccen hotel ne na shak'atawa. Mafi akasarin mutanen dake zaune a farfajiyar wajen matasa ne da yawansu kuma 'ya'yan masu hannu da shuni ne. Mutane ne daga kabilu iri iri,ya had'a da larabawa da turawa uwa uba hausawa da fulanawa. Kowanne sha'anin gabansa kawai yakeyi ba ruwan wani da wani.
Lokacin k'arfe bakwai na daren alhamis. Daidai lokacin ne wata matashiyar budurwa sanye da siket wanda ko cinyoyinta bai gama rufewa ba da wata shegiyar riga wanda dashi da babu duk d'aya domin rabin jikinta daga saman wuyanta da kuma cikinta duk a bayyane suke. Kanta yasha gashin doki,ta tufkeshi da manya manyan ribbons har uku,maimakon tufkar ya kasance a tsakiya sai ya zamana a gefen b'arin kanta na dama. Fuskarta sai shek'i takeyi gata sarauniyar kyau. Lebban sun sha jan baki. (Nayi kyam rik'e da alk'alamina ina duban irin takalmi mai tsinin dunduniya dake sanye a kafarta tare da mamakin yanda bata ko tsoron ya karya mata k'afa. Ganin zata b'acemin ya sanyani watsar da tunanina nabi bayanta a guje yayin dana bar Hanne cillare a bayana tana cillara k'afafuwanta wanda hakan ya tunomin da Kayan moh...(Hasken Idaniya..na tagwayen marubuta...lol).
Cikin takunta mai sanya zuciyar dukkan wani d'a namijin da yayi kicib'us da ita motsawa take tafiya bata tsaya ko'ina ba sai gaban teburin wasu 'yan mata su uku wadanda duk cikinsu suma babu mai shigar arziki.
"Sexy angel"
Cewar wani bature dake zaune a kusa dasu, ya lumshe ido saboda wani irin k'amshi da ya busoshi. Bata ko kalleshi ba saidai ta murmusa saboda ta karanci da ita yake. Tsinken sigari ta janyo ta sanya a bakinta kafin tayi amfani da lighter ta kunna.
"Baby wallahi mutuminki yayi fushi,munkai (30mins) zaune tare dashi yana jira yaga b'ullowarki amma...."
Wacce aka kira da sunan Baby,ta dakatar da ita ta hanyar watsa mata kallo da shanyayyun idanuwanta,kafin ta fesar da hayak'in sigarin. Cikin zazzak'ar muryarta tamkar sarewa marar tashi sosai
"Ya kamata by now ace kin fahimceni sosai Manal, banason a dunga yimin karan tsaye a sha'anina ok? Da nasan ya bar nan da babu abunda zaisa nazo ."
Tana gama fad'in haka ta mike da niyyar tafiya,baturen nan ya katse mata hanzari
"Excuse me."
Bata ko kalleshi ba tayi gaba tana karkada jiki. Manal ta dubi yan matan nan kafin taja tsaki
"Zaman me mukeyi kuma? Saiku tashi mu wuce tunda 'yar mulkin tayi halin nata. Ta sanya muzo mu jirata,tayi mana rashin arzikin."
'Yar bak'ar cikinsu ta bugi tebur daidai lokacin da baturen nan ya katsesu da tambayar lambar wacce suka kira Baby. Harararsa sukayi kafin su bar wajen. Akan hanya bak'ar ciki wato Dalal ta ja tsaki
"Guy dinnan baisan wacece Baby ba da baiyi gigin tambayarmu lambarta ba."
Manal ta tab'e baki
"Kowane gayu idan ya tashi baby,baby. Sai kace muma ba mata bane. Ji fa yanda guys din wajen nan suka bita da kallo tamkar ita kad'ai ce mai abun kallo a jiki. Naga muma dai muna da dirin jikin nan da kyawun fuska ko? Me tafi sauran mata ne?"
Hibba wacce tun soma maganarsu batace dasu uffan ba ta saki dariya a daidai lokacin da Manal ke kokarin bud'e mota. Wannan yasa duk suka kalleta da alamar tambaya na me kuma ya bata dariya haka?
Hibba ta cigaba da magana
"Kuna b'ata lokacinku wajen had'a kanku da Baby Tasleem. Wallahi tayi mana zarra,ku nifa tunda nake a rayuwata ban tab'a cin karo da gogaggiyar 'YAR BARIKI ba wacce komai nata daidai da fushinta ke burgeni ba kamar Tasleem. Ta cancanci a kirata baby domin wallahi ku kanku kun sani daidai da mayuka da turarukan da take amfani dasu abun kallo ne. Ai samun guy irin KB wanda zai tsaya maka akan komai wanda ko mijinka sai haka abu ne da mai matukar wuya. Abu na gaba da zai k'ara tabbatar maku ita d'in ta dabance,ba kowane shara take mu'amala dashi ba. Wallahi komai muk'ami da kud'in mutum idan har bai yiwa Tasleem ba toh koda yafi kare naci karan kanku ne kunsan ba kulashi zatayi ba. Wannan sai mu."
Ta k'arashe tana 'yar dariya,inda ta k'ara k'ular da Manal da Dalal. A fusace Manal ke tuk'in har suka haura titi suka fita daga hotel d'in na Tahir. Kwarai su ukun sun kasance amininan baby saidai suna matukar kishin yanda ta fisu da komai,ta k'etaresu a harkar bariki. Haka Hibba tayi ta dariya tana k'ara b'ata ransu.
*******
Baby Tasleem bata tsaya a ko'ina ba sai kofar gidan KB. Hon d'aya tayi,maigadin yayi azamar wangale mata k'ofa sanin ko wacece ita ga maigidan. Da gudu ta shiga harabar gidan ta faka motarta ta fito. Cike da yanga ta nufi cikin gidan kai tsaye.... ..!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(02)
Tangameman falo ne,yasha kayan k'awace k'awace,b'ata lokaci ne tsayawa kwatanta kyawu da tsaruwar falon. Daga can wata 'yar kusurwa kuwa, matattakala ne wanda zai sadaka da sauran sashen na dake cikin gidan.
Baby bata b'ata lokaci ba ta haye saman kanta tsaye bata dire a ko'ina ba sai a falon da ta hakik'ance zata tarar da Kb. Fitilun wajen a kashe,ta lalubi makunninsu ta kunna,saidai wayam babu shi. Tana shirin fad'awa d'akinsa ne taji an rungumota ta baya. Ta d'an rufe ido kafin ta bud'esu tana murmushi yayinda ta k'ara damk'e hannuwansa tana murmushi. Tana jinsa ya d'ora hab'arsa akan kafad'arta bata iya hanashi ba.
"Kina sane da laifin da kikayimin ko?"
Ya fad'a daidai saitin kunnenta yanda ita kad'aice zata ji. Ta lumshe ido,cikin muryarta mai sanyi tace
"Laifinka ne, meyasa bakayi calling dina ba kafin kabar wajen? Na biya nasha mai ne shine dalilin jimawata. Kaima kasan banason yin nesa dakai."
Matashin saurayin da bai wuce shekaru talatin ba,bak'i saidai bak'insa mai kyau kasancewarshi d'an hutu,yana da kyawunsa daidai misali. Da ganinshi kaga cikakken namiji. Shine dai wanda aka kira da KB(Kabir). Ya saki Baby yayi gaba zuwa bakin firij dinsa,kofi ya dauka a saman firij din yana tsiyaya lemun da baya rabo da shan shi(barasa). Sanye yake da kayan bacci na(pyjamas),sai lokacin ya k'arewa Baby data zauna saman kujera kallo tun daga sama har k'asa kafin ya saki murmushi mai burgeta. Ta kauda kanta daga dubansa tana mai lumshe ido
"Kallon nan yayimin yawa,a rage."
Yayi 'yar dariya kafin ya dawo ya zauna gefanta
"Mamaki kike bani aduk lokacin da kikace bakyason nesa dani Baby,alhalin nasha gayyatarki zuwa Abuja inda acan nafi jimawa nan kuwa sai weekend,ke ma kin sani. Baki tab'a amincewa da hakan ba Baby,(I don't know your reason.)"
Ta tab'e baki kad'an kafin ta sakar mishi wani shu'umin kallo,baisan lokacin daya saki baki yana kallonta ba cikin shauk'i matuk'a.
"Kanason maimaita magana KB,munyi maganar nan yafi sau goma. Na sanar dakai dalilina,bazan iya binka ba domin banason shiga tsakaninka da iyalinka. Aduk sa'ilin da kake garin nan,nikam taka ce, muddin ka cire k'afa ka koma Abuja,ka zama ikon Yasmeen. So please mubar zancen banaso,daga yau kada a k'ara maimaicinta."
Kb ya cigaba da kurb'ar barasarsa yana dubanta cike da mamaki,ya za'ayi wacce kw ikrarin tana matuk'ar sonshi amma har ace bata kishi da matarsa. Wannan wane irin so Tasleem keyi mishi ne?"
Ta katse mishi tunani da salonta mai rikirkita tunaninsa,babu shiri ya mance a duniyar da yake.
******
Baby bata bar gidan KB ba sai washegari da yamma bayan ya cikata da kud'i. Nan ma da yayo mata rakiya kamar kada su rabu. Suna tsaye a wajen fakin,yana rike da ita a jikinsa inda yayi mata iznin zab'ar mota d'aya cikin tsadaddun motocinsa dake k'asan rumfar ajiye motoci. Saida ta kammala duban kowaccensu kafin ta zab'i
bak'ar (Mercedes Benz C300). Ya yafito direbansa da hannu,yayi mishi nuni da motar ba tare da yace uffan ba. Direban ya gyada kanshi cike da ladabi kafin ya fice. Can ya dawo d'auke da mukullin ya mik'awa ogansa,KB ya karb'a ya damk'awa Baby suka sakarwa juna murmushin kafin ta had'a mukullin da hannunsa ta sumbata.
"Thank you my soul,sai had'uwa na gaba."
Ta k'arashe tana mai kanne mishi ido d'aya. Baisan lokacin daya d'aga mata yatsunshi ba saboda duk lokacin da yake gaban Tasleem,mantawa yakeyk da komai sai ita. A gaban idonshi tayi ribas taja motar. Maigadi ya bud'e mata ta fita.
Akan hanyarta tasha kwanar shiga sultanroad taji anayi mata hon babu kakkautawa. Da fari ta dauka bada ita ake ba,saida ta rage sautin kid'an dake tashi ta k'ara duba side mirrow dinta,tabbas Honda civic dinnan ita take bi,a yanda ta lura da yacce fitilunta ke kawowa su dauke a lokaci guda tasan ita d'in akewa magana. Baki ta tab'e ba tare da tayi niyyar tsayuwar ba ta k'ara k'aimi wajen gudun da takeyi. Saidai me? Rikitaccen hon d'in da mai motar nan ke cigaba da danno mata ya fusatar da ita. Ala dole ta taka burki a ta tsaya,wannan ya sanyawa mai motar dake biye da ita taka burkinsa babu shiri gudun kada ya goga mata. Bata da niyyar koda fitowa daga cikin motar balle kuma mai shi ya samu damar cewa wani abu. Tana karkad'a yatsunta jikin sitiyari idanunta naga madubi tana duban motar ta bayanta. Bakin ciki ya turnuketa ganin an tsayar da ita sannan ba'a da niyyar fitowa balle kuma ayi magana. Takaici bai gama cika Tasleem ba saida taga motar nan tayi ribas tayi U turn ta koma baya. Wani wawan zuciya
daya taso mata batasan sadda ta juya ba itama ta bi motar. Gudu mai motar yakeyi,itama gudu take. Saidai abun bakin cikin suna zuwa danja ya b'ace mata domin kuwa yana ficewa kafin ta karaso aka dakatar dasu. Ta bugi sitiyari don bakin ciki,hakanan ta koma hanyar da ta nufa cike da bakin cikin yanda mai motar da batasan ko wanene ba ya raina mata wayo har haka.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(03)
A fusace ta wuce su ta fada kan kujera tana huci kafin ta janyo kwalin sigarin dake ajiye saman center table din,wanda da wuya ka rasa shi a wajen. Ta zari d'aya ta soma zuk'a.
Manal,Hibba da sauran abokan watsewarsu maza da mata duk suka bita da kallo cikin rashin sanin tak'amaiman dalilin fushinta.
"Baby ke da wa?"
Cikin murya irin na wacce ta sha kwaya,Hibba ta tambayeta. Ta kauda kai tana fesar da hayak'i,kafin ta sanya hannu ta cire tufkar da ta yiwa kitsonta na gashin doki,ya zubo har kafad'unta.
"Uban waye ne? Ina zan sake samun damar cin karo da mai motar nan?"
Hibba ta dubi Manal wacce tayi filo da cinyar abokin watsewarta,Manal ta tabe baki inda ta juyar da kanta gefe don kuwa zuwa yanzu kishin Baby fal cike a zuciyarta. Wani d'an karambanin aka samu ya kai hannu da niyyar tab'a fuskar Baby,batayi wata wata ba ta mik'e ta wankeshi da mari gami da nunashi da yatsa.
"Ba kowane tsami ne yake da damar tab'a jikina ba! Daga yau ina mai gargad'inka ka nisantar da kanka daga gareni if not..."
Tayi kwafa ba tare data k'arasa ba ta dauki mukullin mota da jakarta ta haye sama.
Dariya gayun suka sanya mishi,wani dake can gefe yana kokarin jona socket jikin TV ya d'ago mishi hannu
"Sorry Baaba,wannan fa babban goro kake gani sai magogin k'arfe. Ka kiyaye a zauna lafiya."
Wanda aka kira da baaba ya shafa kumatunsa yana murmushin takaicin marin da Baby tayimishi kafin yayi kissing hannunshi
"Me takeji dashi? Kud'i ko kyau?"
"Babu wanda bata ji dashi,kasan babu abunda zaka nuna mata don ubanka.Da kud'inka tsohonka kake tutiya,ita kuwa harkarta har da sa'annin ubanka da gayu irinmu da suka dame tsoffinmu a kud'i da komai Baby gogayya take dasu."
Baaba ya jinjina kanshi yana murmushin da shi kad'ai yasan manufarsa kafin yayi wuf yabar wajen. Suka k'ara sanya dariya,banda Manal wacce takeji tamkar ta tashi da kifawa Musty mari yanda yake ta kod'a Baby. A fusace ta mike zaune zatayi magana saidai ta fasa sakamakon kid'an da ya cika ko'ina na gidan. Nan wasu suka mik'e suka hau casu alhalin ga kiran sallah can na magrib yana tashi a masallatan unguwa.(Allah Ya shiryemu,amin.)
Baby tasleem kuwa tana shiga d'akinta wanka tayi na musamman ta fito ta k'ara mulke jikinta da mayuka da turarukanta tsadaddu kafin ta shirya cikin wata gown mai tsaga a gefe gefenta,tun daga gwuiwa har k'asa. Ta k'ara gyara gashinta,ta fesheshi da Hairsprays kala kala. Kafin tayi zaman shafa jan farce a yatsunta kalar skyblue(wato kalar gown dinta). Ta kwashi awa kusan uku gaba daya yayin wankan da komai nata na shiri. A lokacin da take jiran bushewar faratan nata ne,Dalal ta turo k'ofa ta shigo. Itama ta had'e cikin riga da wando matsastsu masu bin jiki. Sai taunar cingam takeyi na yan bariki ta rike k'ugu tana duban Tasleem wacce kallo d'aya tayi mata ta madubi bata k'ara dubanta ba.
"Zaki gidan Momi ne ko muyi gaba?"
Kamar bazatayi magana ba,har ta k'ular da Dalal.
"Kuje,zan biyoku. Hibba ta jirani mu wuce tare."
Harararta Dalal tayi kafin tayi gaba tana jan tsaki yanda Baby bazata jiyota ba. Ta iske Hibba cikin shiri zaune a saman mota
"Hakimar tace kiyi jiranta ku taho tare. Munyi gaba,kinsan Momi batason a b'ata lokaci."
Hibba tayi murmushi domin tasan yanda Momi ke ji da Baby ko don masu gidan ranar da take kai mata a kowane sati,domin nata kyautar ga Momi yafi na dukkansu yawa.
"Kada ku damu kuyi gaba."
Manal ta bud'e wutar hon,da azama Dalal ta shiga suka tafi. Basuyi mintuna da barin gidan ba,Baby ta fito cikin takunta na jin ita d'in ta isa tana tafe ko'inanta yana rawa,tana amsa waya tamkar bataso. Hibba dai kallon ikon Allah takeyi,har ta soma zargin kodai Baby 'yar wata basaraken ce? Haka tayi ta kallonta ita kuwa batasan ma tana yi ba,mota ta bud'e ta shiga ba tare da ta cewa Hibba uffan ba. Don kanta itama ta bud'e gidan gaba ta shiga. Minti uku da soma tafiyarsu,Hibba ta fahimci da shahararren mai kud'in nan Baby take waya, wato Alhaji Ridwan Naira. Gudu takeyi kasancewar dare ne,hakan yasa tafiyar mintuna talatin,sai gashi minti goma sha biyar ya kawosu gidan MOMI......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(04)
Falo ne babba,cike yake da matasan mata da manyansu. Kowacce tana ji da kanta da ganin tafi 'yar uwarta. Wacce aka kira fa Momi tana hakimce a saman kujera mai zaman mutum biyu ta kishingid'a tana cin tuffa. Kallonsu takeyi d'aya bayan d'aya fuskarta dauke da murmushi. Kowaccensu tasha shiga ta alfarma,saika rantse wani shagalin akeyi. Daidai lokacin Baby ta sanyo kai,a bayanta Hibba. Matasa da yawa dake mutanenta ne,suka hau jinjina da ihu
"Shegiya Baby,manya a baku naku daban."
Ta sakar musu murmushi mai bayyana hak'ora tare da mimmik'a musu hannu suna cafkewa. Manyan kuwa gaisheshu tayi kafin ta isa ga Momi wacce ta zuba mata ido tana murmushi. Hannu ta dunkule,alamun jinjina
"Na gaida uwata,ranki ya dade tuba nake."
Momi ta ja hannunta ta zauna da ita gefanta tana dariya ga hakoran Makkah farare a hakoranta biyu na gefe da gefe.
"Bakya laifi gareni baby."
Daga haka Momi ta juya don soma abunda ya tarasu. Magana ce aka cigabansu a harkokinsa. Ta kara gargad'insu akan su kiyaye kada su bari ciki ya shiga jikinsu koda wasa. A karshe ta dubesu sosai
"Maganata ta karshe ku sani, babu aure a tsarinmu. Nasha sanar maku koda ya kasance zakuyi auren,toh fa baifi na wata uku ba kin fito. Auren ba talaka ba,mai hannu da shuni,ki tabbatar kin tatso mana mai yawa kafin ki datse igiyar auren naki. Wannan shine jawabina. Batun balance kuma,ina jiranku babu wacce batasan acc.no. dina ba."
Haka suka jima suna tattaunawa kafin taro ya watse,Momi ta dubi Baby wacce tayi haramar tafiya. Lokacin karfe sha biyu da mintoci
"Baby baby,kodayaushe tauraruwarki kara haskawa takeyi. Ba daga kananun ba,daidai da manyan suna son mu'amala dake. Ina kuma ga an lek'a ga Hajiyoyinmu duk da dai kin nuna wannan baya kanki yanzu."
Baby tayi murmushi ta girgiza kanta
"Momina kenan,me zanyi da jinsi irin nawa? Wannan babbar kazanta ce, wannan dinma da nakeyi fatana nan gaba na daina."
Momi ta kyalkyale da dariya tana mai dafa kafad'ar Baby
"Babu ranar da wannan fatan naki zai tabbata kuwa,zan maki uzuri da alama bakisan alfanun jinsi ba sai nan gaba."
Baby tayi murmushi mai had'e da jan numfashi
"Ba halina bane,baya daga abunda nake sha'awar aikatawa. So,in sha Allah bazan tab'a bin wannan hanyar ba."
"Ja'irar kaya,ashe har yanzu kinsan da sunan Allah? Toh ba laifi muje zuwa."
Abun sai ya bawa baby dariya,ta d'an dara kafin ta mik'e tayi hanyar fita
"Momi kenan,na barki lafiya."
******
Mutum ne matsakaici,mai dogon fuska,yana da matsakaicin hanci saidai akwai magana(idanu). Girarsa a cike kuma bak'i wuluk,kamar dai yanda sajensa da gashin kansa yake. Fari sol,zubin Fulani.
Zaune yake a ofis yana aiki akan Laptop. Hankalinsa gaba d'aya ya tafi ga aikinsa,kallo d'aya zakayi mishi kasan yana hutawa. Daidai lokacin aka bud'e kofar gami da yin sallama. Ba tare daya kalli mai sallamar ba ya amsa ciki ciki kasancewar ransa a b'ace yake dashi. Ya k'araso da fara'a ya zauna
"An gaida mutumina,ba fad'a mai ya kawo gaba kuma? Ace har ka iso garin nan saidai don rashin mutunci ko waya bakayi domin sanar dani ba sai a bakin kanwarka na tsinci labarin."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(05)
Har ya gama maganarsa baice mishi komai ba. Ganin haka ya buga tebur wannan yasa shi watsa mishi wani irin kallo kafin ya karkato yayi juyi da kujerarsa yana fuskantarshi. Fuska a daure yace
"Kana da kunyar takowa ofishina bayan wulakancin kayimin?"
Cikin rashin fahimta,KB ya zuba mishi ido kafin ya tambayeshi
"Me kake nufi wai Haris? Nifa bansan takamaiman laifin dana aikata ba."
Ya dubeshi kadan kafin ya girgiza kai
"Jiya,(around 6:00pm),na had'u dakai anan wajejan sultan road. Saidai abun mamaki nayita hon baka tsaya ba saida kyar,karshe ma don rainin hankali kak'i fitowa daga motar. Saidai a yanda ka nuna yanzu ya tabbatar min ba kaine cikin motar ba saidai tabbas lambar motarka ce. Na soma tunanin direbanka ne,toh a gaskiya ka chanja direba,domin bakayi dace ba wallahi da zan ganshi zai sha mari ne...."
Kb ya katseshi
"Tsaya don Allah,gayamin menene ya faru?"
Haris ya labarta mishi,ya k'arashe da cewa
"Mercedes Benz dinka ce, kada kaso kaga gudun da direbanka ke...."
KB ya katseshi a kunyace
"Oh,Baby ce a ciki fa."
Haris ya yamutsa fuska
"Who the hell is Baby?"
Kb yayi murmushin basarwa
"Wata cousin d'in Mamina ce,ta ari motata ne tun kusan (last two days.)"
Haris ba don ya yarda ba,sai don kawai bai fiye bin kwakkwafin abunda bai shafeshi bane,ya gyada kanshi
"Ok."
Daga haka suka bar zancen suka fad'a hirarsu.
*****
Kabir Idris Babangida da Haris Aliyu Kazaure. Aminan juna ne,wadanda amintarsu ta samo asali tun daga iyayensu maza wadanda suma a baya can makwaftaka ta had'asu tun suna kauyensu na Kazaure kafin Allah Ya azurtasu a garin Kano. Kowannensu yayi gini na gani na fad'a ya dawo birnin Kano da zama.
Makaranta d'aya Haris da Kabir sukayi. Har ya zamana sun karanci course d'aya,wato business.
Kabir shi kad'ai ne d'a a wajen mahaifinsa Alhaji Idris. Shi kuwa Haris,su biyar ne. Saboda zumunta dake tsakanin iyayensu wadda bata wasa ba,ya sanya Alhaji Aliyu daukar Haris tun yana d'an shekara biyu ya damk'awa Alhaji Idris da matarsa Hajiya Jamila. Sunyi murna matuk'a domin Allah Ya sani,tun Haris na jariri suna matukar kaunarsa,kai bama su kad'ai ba. Mutane da yawa suna kaunar Haris saboda kyawu da farin jinin da Allah Ya bashi. Hajiya Aisha kuwa,mahaifiyar Haris mace ce mai alkunya wannan yasa ko kusa bata nuna damuwarta akan wannan kyautar ba tunda ga YASMEEN da sauran yaranta uku a gabanta.
Haka Kabir da Haris suka taso cikin kaunar juna da tsananin gatan da ake nuna musu. Rayuwarsu saita burgeka na yanda suka shak'u.
A fannin halayya kuwa,nan suka bambanta domin Kb mutum ne mai matukar son 'yan mata,karshe ma ya fad'a harkar nemansu. Abun bai k'ara gaba ba saida sukaje Malaysia karatu.
Duk abunda yakeyi yakanyi kaffa kaffa gudun kada Haris ya sani saidai kuma ba'aje ko'ina ba ya ganeshi. Yasha fama dashi kwarai dagaske domin har k'ararsa yakai wajen Alhaji Aliyu. Nan ya kirashi yayi mishi tas kafin daga bisani Kb ya daukar mishi alk'awarin ya dauka,nan ma ya daukarwa abokinsa alk'awarin dainawa. Hakan kuma bata canza zani ba,domin da abun ya bunk'asa sai ya zamana ma hatta da shaye shaye,KB yana gwada aikatawa.
Haka dai har suka kammala karatu suka dawo,saidai fa tun dawowarsu KB ya dora ido akan Yasmeen yaga yanda ta koma cikakkiyar budurwa. Nan ya shiga tura kanshi gareta. Ga Yasmeen kuwa,tuni itama ta mato akan kaunar Yaya KB. Wannan ya sanya ta bashi kai,soyayyarsu ta k'arfafa. A karshe iyayensu sukaji daga bakin Kb,ran Haris baiso 'yar uwarsa ta auri Kb ba. Ba wai don bai kaunarsa ba saidai tsoron halayensa a ganinsa tamkar bazai fasa ba.
A haka dai iyaye sukayi na'am,aka sanya ranar aure da zarar Yasmeen ta kammala secondary,idan yaso ta k'arasa a dakinta. Kafin auren ya iso,tuni Kb fa Haris kowanne ya kama aikinsa. Inda Alhaji Aliyu ya d'ora KB a matsayin manajan babban kamfaninsa dake a garin Abuja. Wannan mukamin da Alhaji Aliyu ya bawa Kb,ya bawa dukkan yan uwan Alhaji Idris mamaki,karshe suka k'ara ganin girma da kimar Alhaji Aliyu. Shima Abba yace baza'a barshi a baya ba,nan ya d'ora Haris a manajan kamfaninsa a Kano. A cewarsa baza'a yiwa danshi wannan son kan ba. Ba karamin karfi hakan ya sanya zumuncinsu ya k'ara yi ba. Shakuwa sosai da fahimtar juna. Ya zamana Kb baya dawowa garin Kano sai weekend. A haka har Allah Ya daukakasu.
Bayan aurensa da Yasmeen da shekara daya ya siya gidansa na kansa a garin Kano. A cewarsa nan iyalinsa zasu dinga sauka ba sai sunje gida ba. Shima Haris yana da hadadden gidansa mallakinsa a garin Kano.
Babbar damuwar iyayen,auren da Haris bashi da niyyar yinsa. Wannan ba karamin daga musu hankali ba musamman ma ga mahaifiyarsa wacce tafi damuwa ainun. Ganin ya nuna shi kam baiga matar aure ba saidai ko nan gaba wannan ya tsoratasu,suka tashi da addu a zatonsu aljana ce ta auri d'ansu.
*****
HADUWAR BABY DA KB NA FARKO........
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(06)
Haduwarsu ta farko a Nightclub ne. Kb yana zaune da abokinsa,Nas. Bai jima da isowa wajen ba,ya hau kallon gayun wajen domin ganin ta inda zai samu wacce tayi mishi. Shi kam a farko ya raina matan kano,ganinsa basu da wani wayewa na azo a gani. Wannan yasa yafi yin shegantakarsa a Abuja.
Maza da mata ne,kowannensu babu mai shigar kirki,ga kid'an dake tashi tamkar zai fasa wajen. Rawa sukeyi marar kyawun gani,a gefe kuwa wasunsu zaune suna iskance iskancensu basu ko damu da idanun mutune ba. Cikin nishadi ya tsiyaya barasa da niyyar kwankwad'a,yana niyyar kaiwa bakinsa ne ya hangota zaune cikin shigar kananun kaya kamar sauran matan wajen. Taci ado har ta gaji da had'uwa,shisha take sha hankalinta kwance. Tamkar bafulatana saboda hasken fatarta mai kama da madara,ga wani dan iskan rigar dake jikinta wanda bai rufe komai nata ba kasancewarsa shara shara.
Nas ya lura da hankalin abokinsa bai tare dashi,hakan yasa shi juyawa don ganin abunda yake kallo. Murmushi yayi kafin ya juyo ya taimaka wajen tura kofin hannunsa bakin KB,sai lokacin KB yasan ya lula tunani. Nas ya gyada mishi kai hadi da daga gira
"Baby tasleem sunanta,kaf bebs dake nan gurin babu wacce zata nuna mata komai na halitta. Ina gayamaka tana ji da kanta,gata da class. Ba kowane guy take mu'amala dashi ba. Kada ka kuskura ka tunkareta domin ba karamin aikinta bane ta disga ka a gaban kowa ba wajen nan."
Kb yayi murmushinsa,ya sanya hannu ya k'ara kwantar da sumar kanshi.
"Dats my girl,haka nakeson mace. Sha kuruminka kayi kallo."
Nas yana kokarin dakatar dashi saidai tuni shi kuma ya mik'e ya nufi inda baby ke zaune. Wannan yasa Nas tsayawa kallon ikon Allah tare da fargabar irin wulakancin da za'a yiwa abokinsa.
*****
Kb yana zuwa ya nemi kujerar dake fuskantar baby ya zauna. Baice da ita komai ba,sai kallonta da yakeyi itama ta kalleshi sau d'aya ta maida kanta ga abunda takeyi. Murmushi yayi kafin ya rik'o shishar hade da hannunta. Wannan ya sanyata dagowa a fusace tana dubanshi,saidai tunda baby take a rayuwarta bata taba cin karo da wanda dubansa ya sanyaya jikinta ba sai Kb. Tayi makwas bata iya hanashi abunda yake niyyar aiwatarwa ba. Rike da hannunta ya zuki shishar kafin ya d'ago ya dubeta. Ta kauda fuskarta,bazaka fahimci yanayinta ba sakamakon bata daure fuska ba kuma bata saki ba. Ta janye hannunta,ta mike tayi hanyar fita. A sannu take tafiya har ta kawo titi,saidai wayam ba motoci,gashinan manal bata gama shagalinta ba balle saurayinta ya maidasu gida. Hon taji ana yi mata,bata ko kalli motar ba,saida ya iso daf da ita ya faka ya fito. Ta saci kallonsa,shine dai. Ya bude mata mazaunin kusa da direba yana mai mata nuni a ladabce cikin murmushi
"Ba girmanki bane ranki ya dade,a ganki war haka a tsakiyar titi kin rasa abun hawa. Idan babu damuwa kizo ki shiga motata duk da nasan matsayinki ya wuce ki hau jagwal dita."
Ta dubi motar.babbar harka ce kwarai,range rover. Saima ya bata dariya,wannan ya sanyata murmusawa.
Lahaula! Tuni ta k'ara kashe Kb,ya sanya hannunsa akan murfin motar yana dubanta cike da murmushi,jinsa yake duk babu laka a jikinsa. Har ya fidda rai bazata shiga ba saidai ga mamakinsa yaga ta shiga ta zauna,cikin jin dadi ya rufe motar ya shiga ya zauna. Sai lokacin ya dubeta bayan ya matso daf da ita,murya kasa kasa yace
"Fatan zan samu rakiya gidana?"
Ta juyo ta dubeshi,numfashinsu na bugun juna,ta kauda kanta tana murmushi wannan ya bashi tabbacin amincewarta. Da gudu yaja motar, bakajin komai sai kid'a dake tashi ga sanyin Ac.
*****
Tun daga wannan ranar Kb da Baby suka dinke,dinkewa kuwa bata wasa ba. Su kansu su manal sunyi mamakin inda baby ta samo hadadden guy har haka. Karshe har gida ya sanya aka gyara musu,kudin kuwa da yake aikawa baby abun yaso ya baci. Ga sauran manyan da take harka dasu suma ba'a barsu a baya ba wajen cika mata account. Karshe Kb ya hanata mu'amala da kowa,acewarsa shi kadai ya isa dauke mata nauyin komai. Baby murmushi kawai tayi ta bishi a hakan,saidai kuma abunda bai sani ba,duk sadda yasa kafa ya koma Abuja babu irin tsiyar da bata shukawa da manemanta. Mota kyauta ya bata,wasu lokutan idan taga dama koda baya gari,zataje gidansa ta huta ta fita da motar da takeso. Babu wanda yake cewa uffan cikin ma'aikatan sanin matsayinta a wajen ogansu. Saidai suyita gulmammakinsu tare da rok'awa maigidansu shiriyar Allah.
******
Ta gama komai na tarar mijinta,ta gyara gidanta da jikinta. Jiran dawowarsa kawai takeyi.
Tana cikin sanyawa diyarsu,Nasreen,ribbon a jelar kitsonta,taji shigowar motar mai gidan. Nasreen ta kwace kanta daga wajen maminta tayi waje a guje.
"Daddy oyoyo,daddy oyoyo."
Haka tayita fad'i har takai ga jikin motarsa. Ya fito ya daga diyarsa cak yana sumbatar kumatu da goshinta cike da farin ciki ganinta.
"Bebin daddy oyoyo,I miss you soo much."
Tana ta dariya haka suka shiga ciki. Ya ajiye nasreen,daidai lokacin Yasmeen ta karaso tana duban mijinta cike da so da kauna saidai fa a sanyaye take sanin da tayi waccan zuwan nashi bai wani saki jikinsa da ita ba. Abu kadan da baikai ya kawo ba zai soma gayamata magana.
"Sannu da zuwa."
Ga mamakinta taga ya amsa tare da rungumeta. Ta saki ajiyar zuciya gami da hamdala a ranta.....!
Rufy: 'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(07)
Ya dagota yana mai riko kafad'unta
"Ya dai na ganki haka a sanyaye? Ko bakiyi murna da zuwana ba na juya?"
Ya saki kafadunta ya soma tafiya da baya, da hanzari ta riko hannunshi tana dariyar farin ciki
"Wace ni na guji prince dina? Barka da zuwa."
Ta ja hannunshi suna murmushi har zuwa d'aki,Nasreen tana biye dasu.
Yasmeen mace mai biyayya,ta taimaka mishi ya gyara jikinsa ya sanya kayan shan iska. Sannan suka fito ta zuba mishi abinci yaci.
Ranar kam sun farantawa juna saidai ko kusa zuwa yanzu bayajin dadin mu amala da kowacce mace sai Baby. Yau dinma tausayin matar tashi ne ganin yakan jima bai kusanceta bane.
*******
JUMA'A,5:00pm
Baby ce tafe cikin motarta,tuki takeyi cikin kwarewa. Kallo daya zakayi mata kasan tana cikin nishad'i. Dawowarta kenan daga gidan gonar Alhaji Ridwan Naira,wanda kusan sati yayi yana magiya da rokonta akan don Allah tazo gareshi. Sai a yau baby taga damar amsa kokensa bayan ta jera satuttuka tana lashe kud'ad'ensa.
Kai tsaye gidan Kb ta nufa duk da cewar tasan bazai shigo Kano wannan satin ba gudun kaucewa zargin iyayensa da matarsa. Yau kam a gidansa take sha'awar kwana don tasan koda ta koma bazata samu su Dalal a gidan ba. Manal tana Kaduna,yayinda Hibba da Dalal ke tare da mutanansu a gidajen shak'atawarsu.
Tayita hon saidai maigadin yayi nisan kiwo,wani maigadin ne daga makwafta yazo ya bud'e mata ta shiga. Ta fiddo 'yar bigmama dinta da wayoyinta ta rufe motar ta shiga ciki. Bata da matsalar mukullaye kasancewar tana da safayar kowanne mukulli na gidan a wajenta duk saboda mukamin data samu a wajen Kb. Wanka kawai ta fad'a sakamakon gajiyar data kwaso.
Daidai lokacin ya shigo layin,duk a zatonsa aminin nashi ya shigo gari kamar yanda ya sanar mishi a waya cewar watakila ya shigo. Hon yayi har sau uku,maigadin har lokacin bai kusa. Wanda ya bude kyauren da farko shine dai ya k'ara zuwa,Haris ya sauke gilashi ya yafitoshi da hannu. Yazo cike da ladabi ya kwashi gaisuwa,haris ya amsa gami da tambayar
"Mai gidan yana nan?"
Maigadin ya dubi gidan kafin ya dubeshi
"Eh toh,inaga dai yana nan don Hajiya bata jima da dawowa ba ni na bude mata kofa."
Haris ya dauka kanwarsa Yasmeen ce, yaji dadi domin yayi kewarta sun kwana biyu basu hadu ba saidai gaisuwa ta waya. Ya jinjina kanshi
"Taimaka ka bud'emin mana."
Da azama ya bud'e mishi ya shiga ciki yayi fakin. Bayan ya fito ya tsurawa motar da baisan da zamanta ba a gidan ido,cike da mamakin mamallakin motar ya dubi gidan kafin kuma ya tunkari cikinsa.
Fitowarta kenan daga wanka,tana shirin goge jikinta taji sallama a falon gidan. Farin cikin ya k'aru,ashe daman zai zo gari shine bai sanar da ita ba duk da wayar da sukayi? Cikin sauri sauri ta nufi hanya ta fita.......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(08)
Tana fitowa falon,wayam! Hakan ya tabbatar mata daga falon k'asa ne. Sai ta soma shakku akan anya kuwa Kb ne? Don bai tab'a tsayawa k'asa ba sai ya k'araso falon sama.
Haris jin da yayi sallamar ba'a amsa ba,kawai ya tunkari falon sama yana fadin
"Little,ina kika shiga ne?"
Baby ta tsaya cak daga bakin matattakalar,kafin takai ga yunkurin kaucewa har ya nufo benen. Ido hud'u sukayi,duk da batasan ko waye ba saida ta d'an tsorata. A gefen Haris kuwa,kallonta yayi tun daga k'asa har sama,bai k'ara marmarin kallonta ba. A fusace ya juya kanshi yana mai kokarin korar shaidan daga zuciyarsa. Cikin kakkausar murya yace
"Who are you?"
Cike da mamakin yanda gayen ya juya baya daga barin kallonta,baby ta kalli jikinta. Tawul ne ko cinyoyinta bai gama rufewa ba. Ita kam bata taba ganin namijin daya ganta haka ba harma ya iya juya mata baya ba sai a yau.
"I said who are you?!!! Mekikeyi a gidan nan?!!"
Ta razana matuka,tunda take wallahi ba'a taba yi mata tsawa har irin haka ba a rayuwarta. Ta tsaya kyam tana dubansa bata ko iya bud'e bakinta ba. Jin tayi shiru ne yasa shi juyowa a fusace ya karasa hawa matattakalar baiyi wata wata ba ya d'aga hannu da niyyar marinta,sai lokacin ta iya karfin halin rike hannunshi. Kallon juna sukeyi ido cikin ido,wani kwarjini yakeyi mata wanda ya hanata yin magana cikin tsiwa. Ta saki hannunshi ta kauda idanuwanta fuskarta a daure
"Ganganci ne tab'a lafiyata,gaba ka kiyaye."
Ta ja baya ta janye kafafuwanta daga matattakalar zuwa sama. Ya zamana matattakala uku ce tsakaninsu,ta tsuke baki kafin ta kad'a idanuwa ta k'ara dubanshi,har lokacin kallonta yakeyi saidai cike yake da mamakin karfin halinta,ganin yanda ta iya rike hannunsa da nufin dakatar dashi.
"Game da tambayar da kayi,ka tambayi kb. Inaga shine yafi cancanta ya baka wannan amsar ko?"
Ta k'arashe tana mai murmusawa,daga haka ta juya ta tafi. Haris na tsaye har saida ta b'acewa ganinsa,ransa idan yayi dubu toh ya b'aci. Ashe har yanzu Kabir bai bar neman mata ba? Ya rasa irin wannan akuyanci na Kb,menene amfanin auren nasa toh? Tsananin tausayin Yasmeen ya turnukeshi. Saidai ya rantse bazai tafi ya bar tsinanniyar karuwar nan a gidanta na sunnah ba,dole ta fice yanzu kuwa!
Gama tunaninsa keda wuya ya nufi hanyar data bi a fusace,saidai kuma tunanin da yayi na watakila a wannan lokacin tana shiryawa ne,ya sanyashi tsayawa a falon gami da samun waje ya zauna. Layin wayar Kb ya shiga nema......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(10)
"Assalamu alaikum warahmatullahu wabarakatuhu."
Cikikkayiyar sallamar da a yau ta fito daga bakin Kb kenan,wanda ya k'ara nuna tsantsar rashin gaskiyarsa. Tunda dai a sanin da Haris ya yiwa aminin nashi,baya taba cika sallama haka tun suna k'ananu sai idan yana cikin firgici.
Dariya taso kubcewa Amadu maigadi,yayi saurin tosheta. Harara kb ya watsa mishi da sauri ya sauke jakar ya fice.
Haris ya amsa ciki ciki,har kb ya iso ya zauna kallonshi kawai yakeyi cike da tsabar bakin ciki. Tun kafin Kb yakai ga cewa komai ya tareshi
"Ka bani mamaki Kb,abune da koda ace za'a tareni acemin baka bar aikatawa ba zance karya akeyi. Karuwa fa!! A gidan da kake raya sunnar ma'aiki?!!! Da sunan kana da aure? Ka gayamin wane jin dadi ne a bibiyar kazaman matan nan da har yau ka kasa russuna?! Ya kake tsammanin su Daddy zasu dauki wannan zancen?"
Haris ya dakata,kallo d'aya zakayi mishi ka gane yana cikin tsananin bacin rai,wannan farin fatar tashi ta fuska ta chanja launi zuwa ja,hakanan kwayar idanunsa. Ya numfasa
"A ture maganar iyayenmu,me zaka cewa Mahaliccinka akan wannan d'anyen aikin da kakeyi na aikata zina? Baka tsoron mutuwa ta riskeka a wannan yanayin Kabir? Inace Ubangiji Ya halatta mana auren mata hud'u idan har zamuyu adalci? Why not ka nemi wata ka aura tunda mace daya bazata iya kashe maka kishirwarka ba. Amma wannan(yayi nuni da matattakala) ba alheri bace gareka face halakarka.!!"
Kb wanda tsananin kunyar Haris ta mamayeshi,yana ganin tamkar Yasmeen ce a gabanshi. Ya runtse ido kafin ya bude cikin sassanyar murya na rashin gaskiya
"Hakane,nasan ban kyauta ba. In sha Allah daga yau bazaka k'ara kamani da laifi makamancin wannan ba. Na amsa laifina,babu shakka bakayi karya ba duk abunda ka fad'a na aikatashi. Kayi hakuri,don Allah ka rufamin asiri a matsayinka na dan uwana kuma amini...."
"Its ok,baka da matsala dani Kabir,fatana ka gyara tsakaninka da Ubangijinka. Abu na gaba,yarinyar nan tazo ta fice yanzu yanzun please."
Kai da kaga yanayin fuskar Haris kasan yana tsananin kyamarta. Kyakkyawar matashiyar budurwa saidai fa kyawun dan maciji ne.
Shi kuwa Kb,mikewa yayi ya nufi saman gami da jin dadin cewa Baby batayi fushi tabar gidansa ba.
Tana zaune taga mutum tsaye a kanta,ganin kb ya sanyata mikewa tana murmushin jin dadin ganinshi,bai ankara ba har takai ga rungumeshi. Kamshin jikinta da taushin fatarta,ya mantar da kb dukkan wasu nasihu na Haris. Sai yaji sam bazai iya rabuwa da Baby ba,tun haduwarsa da Baby,baya iya hada shimfida da kowace Yar Bariki sai ita. Yasmeen ma,gudun kada takai korafi ga iyayensu ya sanya yake mu'amala da ita. Ta dago ta sumbaci lebbansa har lokacin da murmushi dauke a fatar bakinta. Baisan lokacin da shima ya sakar mata murmushin ba. Ta fidda earpiece daga kunnenta,ta zuba mishi shanyayyun idanuwanta kafin daddad'an sautin muryarta ya ratsa cikin kunnuwansa
"Welcome back my dear."
Ya riko hannuwanta cikin nashi salon kallon,ji yakeyi nan duniya bashi da farin ciki sama da Baby. A shirye yake ya aureta idan har hakan zaisa ya dauwama tare da ita bata haramtacciyar hanyar da za'a gani a rabasu ba.
"Thank you my baby,hankalina a tashe yake."
Ta janye jikinta tana murmushi kafin ta nufi hanyar sauka k'asa
"Daukomin handbag dina, kada ka damu na fahimci matsalar."
Yayi mamakin yanda akayi ta fahimceshi sosai har haka. Cikin jin dadi ya shige dakin,ya dauki harda mukullin motarta.
Haris dake zaune yana jiran fitowarsu,suka dubi juna,ta sakarmishi murmushinta mai burgewa saidai ko kad'an bata burge Haris ba. Ta zagaya ta bayan kujerar da yake,daidai saitin kunnenshi ta furta
"Sai had'uwa ta biyu."
Daga haka tayi gaba cikin takunta na jin ta isa. Mamaki ya sanya Haris binta da kallo. Amma ta tabbata Baby tsohuwar 'YAR BARIKI ce, ya kauda kansa yana takaicin yanda mace kyakkyawa har haka ta b'ata wayonta. Son duniya ya sanya tana siyarda jikinta ga wanda ya isa da wanda baima isan ba. Tunaninsa ya tsaya sa'ilin da abokin nashi ya taho da sauri rike da jaka da mukullin mota. Ya zuba mishi ido yana duban ikon Allah,Kb ya tsuke fuska
"Mantuwa tayi,banason komai nata ya rage a gidana domin daga yau na barta kenan."
Shi dai Haris baice komai ba,fuska a daure. Kb ya fita a fusace wanda zaka rantse zancensa har zuci ne.
Yayi ta hangen inda Baby ta shiga, hon yaji. Ya juya ga daya daga cikin motocinsa,hantar cikinsa ta kad'a. Wannan ma fa wata matsalar ce, ta yaya zata shiga motarsa? Ya dubi hanyar gidansa,Haris bai fito ba,da gudu gudu ya isa bakin motar. Fuskarta a daure kai ka rantse bata tab'a dariya ba.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(09)
Ringing uku ana hud'u,Kb ya d'aga.
"Yadai mutumin? Kana ina ne kazo ka daukeni a airport. Allah Yayi zuwana bisa neman da Abbana(Alhaji Aliyu) ke yimin akan harkokinmu."
Haris ya runtse ido cikin jin haushin Kb,dakyar ya iya dannewa yace
"Banajin zan iya zuwa,ina gidan naka yanzu haka tare da matarka wacce bamu da masaniyar sadda kuka kullawa junanku aure. Kana iya shigowa taxi kazo ka samemu."
Daga haka ya kashe wayar,a bangaren Kb kuwa,hankalinsa idan yakai dubu toh fa ya gama tashi. Kada dai baby ce? Ya salam! Yanzu menene abunyi?"
Ya lalubi lambar Baby ya danna kira.
Ta kammala shiryawa cikin riga da wando gajera marasa nauyi,ta kunna karan sigari ta soma zuk'a hankali kwance kafin ta sanya earpiece a kunnenta tana shirin danno wak'a ne kiran Kb ya shigo wayarta. Murmushi ta saki kafin ta d'aga alokacin data nufi falo.
Kafin takai ga cewa wani abu,Kb ya soma magana
"Babyna kina ina?"
Daidai lokacin ta fito falon,lokaci d'aya suka dubi juna dashi,ta dauke kanta ta nufi kicin.
"Ina gidanka,wani abu?"
Ya zaro ido,hantar cikinsa ta kad'a
"Baki ga wani bak'o ba da yazo?"
Daidai lokacin ta fito dauke da glasscup tayi hanyar firij,
"Gashinan zaune,da alama baisan wacece ni gareka ba ko?"
Kb ya dafa goshi,ya rasa ta inda zai b'ullo. Ashe a gaban Haris take magana dashi?
"Look,he's my bestfriend. Please kada ki sanar mishi komai dangane da relationship dinmu dake kin fahimta? Gani a airport,na iso Kano. Yanzu zan zo gidan."
Ta tab'e baki,daidai lokacin ya kashe wayar. Ita kuwa freshmilk ta tsiyaya ta koma ta zauna a kujerar dake kallon Haris. Kurb'a takeyi tana duban fuskarsa yanda duk yabi yayi kicin kicin tamkar ya tashi ya rufeta da duka. Saida tayi kurba uku kafin ta ajiye ta cire earpiece dake kunnenta.
"Nice meeting you."
Ta fad'i a tausashe. Bakin ciki ya sanyashi watsa mata kallon da taga ya k'ara fiddo kyawunsa zallah. Murmushi ta sakar mishi kafin ta d'ora tafin k'afa d'aya akan kujerar da take zaune
"Fuskarka ya nuna baka son ganina."
Ta tabe baki inda ta k'ara zuk'ar sigari ta fesar da hayak'in.
"Abun mamaki,bamu tab'a had'uwa ba sai yau. Ban fiye kaunar naga mutum yana kuntata rayuwarsa ba musamman akan abunda ba matsalarsa...."
Tashin da yayi ya hanata k'arasa zancenta. Dubanta yayi cike da tsana,ya soma tafiya saidai ya tsaya cak ya juyo
"Da gaskiyarki,ban sanki ba,asalima yau na tab'a ganinki a inda bai cancanci ace kina nan ba. A matsayinki kuma na kilaki. So,as you said,bake zaki bani amsar kowacce tambayata ba. Ke kuma kiyi hankali da kazantacciyar rayuwar da kike ciki,na lura baki da damuwa ko kuma d'igon bakin cikin wannan rayuwa taki. Saidai fa..."
Ya dubeta,sai lokacin ya sakar mata murmushi wanda daga gani kasan na yak'e ne
"Akwai ranar k'in dillanci."
Daga haka ya sauka zuwa falon k'asa domin jiran aminin nashi.
Ta maido dubanta ga falon,ta lumshe ido tana murmushi
"He's very handsome,saidai ba wayewa."
Ta furta cikin zazzak'ar muryarta,bata ko damu da kalamansa ba ta maida earpiece dinta ta kunna wak'a abinta tana kurb'ar lemo,a gefe kuma zuk'ar taba.
*******
Taxi yana tsayawa,kb ya biyashi ya fito. Da azama Maigadinsa ya iso a guje yana kokarin karb'ar akwatin hannunsa. Kyakkyawan mari yayi mishi a kunci,kafin ya soma magana a fusace
"Don ubanka wace doka na sanya maka?!!! Bance maka idan bana gari ba,banda baby kada kabar kowa ya shigomin gida ba?!!"
Matashin maigadi wanda yaci suna Amadu,yana rike da fuskarsa ya russuna cike da girmamawa
"Kayi hakuri yallabai,wallahi ina fama da ciwon ciki shine na lek'a kemis bansan da zuwan Madam ba."
"Mts!"
Kb yaja tsaki yayi gaba,da azama Amadu ya ciccib'i akwatinsa jiki yana rawa yabi bayanshi bayan ya watsawa Ado maigadin makwaftansu kallon baka kyautamin ba.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(11)
"Babyna wannan motar kuma?"
Ta dubeshi
"Nufinka na sauka na baka abarka?"
Yayi azamar dakatar da ita
"No,bance ba. Saidai kinga Haris zai iya d'ago..."
Ta soma kiciniyar bud'e mota, yayi saurin dakatar da ita.
"Haba babyna,please ni bance ki sauka ba. Ga handbag dinki,daga baya zanzo gidan please. Kada kiyi fushi dani."
Sai lokacin ta sakar mishi murmushi na gefen kumatu
"Ko kaifa."
Daga haka ya matsa tayi ribas,tuni Amadu ya bud'e mata k'ofa ta fice.
Kb ya dawo da hankalinsa akan motar Baby,dabara ta fad'o mishi,ya sami k'usa ya sace taya d'aya kafin ya mike. Ido hudu sukayi da Haris wanda fitowarsa kenan,ya dubi motar kafin ya nufi tasa a fusace ya hau kokarin budewa. Kb ya isa da sauri ya riko hannunsa
"Don Allah kada kayimin gurguwar fahimta mana,tayar motarta d'aya ne ya sace shine dalilin daukar tawa da tayi. Amma idan an gyara zan aika mata sai a karb'omin tawa. Kada.."
"Ya isa Kabir,gyara kuma ya rage tsakaninka da Mahaliccinka. Shi yafi cancanta ka tsorata ba kowa ba. Kayi tunani da ka haihu,baka gudun ace yau diyarka ce cikin wannan..."
"Haris please! Banason wannan irin zantukan! Ya wuce,na fadamaka kaddara ce yasa nake kula wannan d'inma amma nayi maka alk'awarin daga yau ta k'are. Don Allah ka rufamin asiri."
Ya tabe baki gami da daga kafad'a
"Ka tsaya mana muyi sallah,nasan ko magrib bakayi ba. Gashi kafin ka kai gida nasan anyi isha'i."
Sanin da yayi haka dinne,ya sanyashi dakatawa. Sukayi sallah,sannan ya wuce.
******
Tun komawarsa gidansa,tunani da matsanancin tausayin kanwarsa Yasmeen sun hanashi sakat. Har lokacin surar yarinyar ya kasa b'aceqa daga idanuwansa,ba don komai ba saboda tsanarta da yakeji tare da mamakin karfin hali irin na karuwan mata masu maida gidan wani nasu. Kodayake dai babban laifin yana ga Kb wanda har ya iya bata wannan fuskar. Zina fa!! Wai ma menene abun dadi da tunkaho a cikinta?!! Me Kb yakeji idan ya tafka irin wannan sab'on? A gefe d'aya ga Yasmeen,a yanda yasan kanwarsa,yarinya ce mai hakuri da halayen mijinta. Tabbas bata boyemishi dukkan sirrukanta tun tana budurwa ma. Dukkan abunda hankali zai dauka na neman shawara,daidai da wanda ya dace ya sani takan sanarmishi ta waya. Ko kuma idan yaje su kwashi fin awa suna hira. Duk da ba gida d'aya suka taso da Yasmeen ba,sun shaku sosai dashi.
Idanunsa suka kad'a sukayi jazur,hakikanin gaskiya,ko kusa kanwarsa batayi sa'ar miji ba. Manemin mata wanda har yake zargin yana shaye shaye. Duk da har zuwa yanzu bai taba kamashi dumu dumu cikin mayen ba saidai ganin yanda neman matan nasa yayi yawa yasa ya soma gaskata komai akace kb yayi zai aminta da haka.
K'arar wayarsa ce ta katse mishi tunani,dakyar ya lalubota ya duba mai kiran. Yasmeen dince. Murmushi ya saki wanda yafi kuka ciwo,kafin ya daga. Tun kan yace wani abu,ta soma magana cikin farin ciki
"Yayana kasan wani abun mamaki kuwa? Au,Assalamu alaikum,yayana barka da dare."
Nan da nan ransa ya danyi sanyi jin cewar kanwarsa tana cikin farin ciki. Cikin tattausar muryarsa ya amsa sallamar ya d'ora da fad'in
"Fadamin da sauri little,bazan iya jira na wani lokaci ba."
Tayi dariya mai nuni da tana cikin farin ciki
"Wallahi yayana wannan zuwan naga chanji sosai a wajen Prince..."
"Me yayi maki?!! Gayamin ko menene?!!!"
Ta danyi shiru kad'an jin ya fusato,a sanyaye tace
"Cool down yayana,bafa wani abu yayimin na bacin rai ba. Kawai dai umm...mun dawo tamkar new couples."
Ta karashe tana dariya kasa kasa,ya lumshe ido yana mai sauke ajiyar zuciya.
"Alhamdulillah little, burina na ganki cikin kwanciyar hankali. Ina diyata?"
"Allah Sarki yayana,nima farin cikinka shine nawa. Ai bansan ya zanyi ba idan aurenka yazo don murna."
Murmushi yayi wanda bai shirya mishi ba,ita kam Yasmeen bata gajiya da tunasar dashi batun aure sai kace wani karamin yaro. Ya shafi sumar fuskarsa
"Zanyi,lokaci ne baiyi ba little. Ki tayani addu'a. Baki amsamin tambayata ba."
"Oh,nasreen tayi bacci. Ai yanzu muka gama waya da babanta yace min ma Monday zai juyo da safe."
"Kabir kenan."
Ya fad'a a zuci,don ya fahimci ba karamin razana yayi ba yau.
A fili kuwa ya amsa da ok.
"Bari na kyaleka kaji da gajiyar ofis. Bye."
Sukayi sallama ya ajiye wayar. Tausayin kanwarsa ya k'aru a zuciyarsa,tabbas har yanzu batasan waye Kb ba,kuma baya fatan tasan wannan boyayyen al'amarin,daidai da iyayensu baiso zancen yaje wurinsu. Shi kam,sai inda karfinsa ya k'are akan ganin rayuwar amininsa kuma dan uwansa ya daidaita.....!
*****
Misalin (1:00am) na dare......
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(12)
Kwance suke a dakinta kan makeken gadonta,tayi
matashi da cinyarsa.
"Babyna."
Ba tare data amsa ba ta dago idanuwanta
lumsassu ta dubeshi,ya sanya hannu yana wasa
da girarta kafin yace
"Inason muyi wata magana ne."
Batace komai ba,sai kallo da take binsa
dashi,wannan ya bawa Kb damar cigaba da
zancensa.
"Kinga dai a yanzu babu damar haduwa a gidan
ko? Sannan yanzu idanun Haris a kaina yake na
tabbatar bai gamsu cewar na rabu dake da gaske
ba."
Ya danyi shiru kamar mai nazari,kafin ya riko
hannunta yana cigaba da duban kwayar idanunta
masu k'ara dulmiyar dashi kogin kaunarta.
"Abu ne da bazan taba iya aikatawa ba,saidai
zuwa yanzu ina tsoron kada Haris yakai k'arata
wajen iyayenmu....."
"Menene dangantakarku da guy dinnan ne? Na
lura ka bashi matsayi da yawa a rayuwarka KB."
Baby ta katseshi ta hanyar jefo mishi wannan
tambayar. Murmushi yayi ya shafi gashin dokin
dake kanta wanda sai yace shi dai tunda yasan
baby bai taba ganin iyakar jelar gashinta
ba,baisani ba tana da yawan gashin ko babu.
"Haris Aliyu kenan,iyayenmu aminan juna
ne,wannan yasa mukayi sabo dashi sosai fiye da
tunanin mai tunani. Ya kasance dan uwana
wanda bama boyewa juna sirri. Nan da kike
ganinsa ustaz ne,ya fiye takura kansa baison ya
more rayuwarsa."
Kb ya dan tabe baki kafin ya cigaba
"Abunda zai baki mamaki ma,har yau bai taba
sanin diya mace ba sannan har zuwa yanzu yak'i
aure a cewarsa gareni,baiga wacce tayi mishi
bane."
Baby ta lumshe ido kafin ta muskuta ta juyawa
Kb baya
"Karancin wayewa ke damunsa,saidai kasan wani
abu? Da ace nice kai babu wanda ya isa hanani
yin abunda nake ra'ayinsa. Kaban mamaki KB,
akan wannan guy din saika rabu dani."
"No baby,ni wanene da zan bar mace irinki?
Wannan karya ne. Shiyasa na samo mana
mafita,kawai ki nutsu ki saurareni please."
Har lokacin idanuwanta a rufe suke,haka kawai
take tsintar kanta da tunano kyakkyawar halittar
fuskar HARIS,
"Ina sauraronka."
"Zaki aureni Tasleem?"
Cikin matukar razana ta bude idanuwanta,kafin ta
mike zaune tana duban kwayar idanuwan
Kabir,kwarai babu alamun wasa a abunda yace.
Gabanta ya shiga faduwa haka kawai,yayi azamar
matsowa ya riko hab'anta
"Wallahi Tasleem zan iya aurenki,babu kyankyami
ko wani abu. Sonki nakeyi,bazaki gane yanda na
shaku da soyayyarki..."
Ta cire hannunshi ta juya mishi baya gami da
sauke kafarta akan gadon,har lokacin bugun
zuciyarta bai daidaita ba
"Na gayamaka tun a farkon mu'amalarmu kafin
muyi nisa haka. Kamar yanda ka taba zuwarmin
da batu irin wannan a yanzun ma amsar d'aya
ce,bazan iya aurenka ba."
Kb hankalinshi ya tashi,kaunarta na kara karfi a
zuciyarsa. Zuwa yanzu ya amincewa kansa lallai
ba sha'awa kawai yake yiwa Baby tasleem
ba,harda soyayya. Hannunta cikin nasa,yayinda
kalar kwayar idanunsa suka sauya launi saboda
tsabar tashin hankali na jin maganar dake dake
fitowa a bakin baby.
"Me kikeso a rayuwa wanda har yanzu baki samu
ba? Wallahi ki fad'amin ko menene shi zan
mallaka maki Tasleem dan har zaki yarda na
killaceki a gidana ya zamana ni kadai nake da
hakki akanki. Ya zamana kinbar mu'amala da
kowa. Wallahi tasleem zan iya mallaka maki
dukkanin dukiyata matukar hakan zaisa ki amince
dani matsayin mijinki. Please ki....."
Ta mike a fusace
"Ya isheni Kb!!!!"
Ta dakatar dashi kafin ta watsa mishi duban da
tunda suke tare bata taba yi mishi ba. Duba ne na
raini da wulakanci,
"Bazaka taba samun biyan bukatar nan ba. Na
tsani aure! Bazan taba yinshi ba!! Babu komai a
rayuwar aure sai tozarci da wulakanci! Wannan
ikrarin da kakeyi na kana sona,zai tafi da zarar na
kasance matarka."
Kb ya nufeta da niyyar rikowa tayi azamar
dakatar dashi ta hanyar daga mishi hannu. Daga
haka ta fice da gudu tabar dakin. Bata shige
ko'ina ba sai d'akin Dalal ta sanya mukulli jikin
kofar ta rufe. Kuka takeyi sosai wanda ya tada
hankalin kb dake tsaye daga waje yana jiyo
sautin kukan nata.
"Please baby i'm sorry,indai maganar aure ne
bazan k'ara yi maki ba."
Ita kuwa baby,ita kadai tasan me me kalmar aure
yake tunano mata.
Daren babu wanda yayi kwanan farin ciki a
cikinsu.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(13)
Kukan da Baby tasha a wannan daren ne ya sanya ta tashi da matsanancin ciwon kai. Bata fito daga d'akin nan ba saida tayo sallar asubahi ta kara kwanciya bacci,a takaice dai saida rana ta fito. Ta bud'e kofa ta fito,falon babu kowa kamar yanda tayi zato,Kb ya tafi. Ko a kanta bata damu ba,ita kam idan har zancen aure ne bazai tab'a samun goyon bayanta ba. Tabbas saidai alak'arsu ta yanke anan.
Kai tsaye dakinta ta nufa,tsayawa tayi cak,ganin Kb kwance yana bacci bayan ya rungume hotonta dake ajiye gefen gadon. A hankali ta karasa ta durkusa saitin fuskarsa tana duba,murmushi dauke akan fuskarta. Lallai ba karamin so Kb yake yi mata ba,duk da cewar nata zuciyar ba wani sonshi takeyi ba sosai. Tafi daukarshi a matsayin mai biya bukatarta. A hankali ta mike ba tare da tayi yunkurin tashinsa ba. Wanka kawai ta fad'a. Bayan ta fito ta iske har lokacin kb bai farka ba,mamaki ya kamata. Kodai baiyi bacci bane daren jiya. A sannu isa gefen gadon ta zauna kafin ta jijjiga gashinta,ruwa ya fallatsar mishi a fuska. Sannu sannu ya bude ido,kafin yakai ga cewa wani abu ta mike da sauri ta koma gaban madubi
"Ya kamata ka tafi gida kafin ustaz din naka ya nemeka."
Ta karashe tana murmushi,kb ya taso ya janyota ta mike tsaye suna fuskantar juna. A karshe ya zaunar da ita gefen gado shima ya zauna. Yanda ya karanceta ko kusa bata da fushi sosai,tana da saurin hucewa,(hum).
"Na bata ranki Babyna,amma daga yau nabar zancen nan tunda har bakiso,kinji?"
Tayi murmushi kafin ta sauya salon zancen nasu. KB bai bar gidan ba sai wajen goman safe,ya k'ara tabbatarwa kansa bazai iya rabuwa da Baby ba. Ta musamman ce. Cike da nishadi ya koma gidansa.
*****
Dattijai ne guda biyu masu kimanin shekaru Sittin da d'oriya,suna zaune a kayataccen falon gidan. Kowannensu ya sha babbar riga suna hira cikin nishad'i. Lokaci guda kuma fuskar Alhaji Idris ta sauya zuwa yanayin damuwa. Wannan yasa Alhaji Aliyu tsagaita dariya ya dubeshi
"Lafiya kuwa?"
Alhaji Idris ya sauke ajiyar zuciya
"Wallahi lamarin Harisu ya soma tsoratani Alhaji. Ace yaro yak'i zancen aure,har rana mai kama da yau ya kasa kawo mana zancen da zai sanyamu farin ciki? Babu ranar da bana rokon Allah,daidai da liman saida na sanarwa domin a taimaka mana da addu'a. Kaga fa har rukiyya anyi mishi a zatonmu aljanu ne saidai ko gezau babu. Anya tafiya zata yiwu haka?"
Alhaji Aliyu yayi murmushi
"Ka gafarceni Alhaji idris,zuwa yanzu na daina ganin laifin yaron nan nafi ganin laifinku na iyayensa."
Daddy ya dubi Abba da alamun rashin fahimtar maganarsa. Abba ya jinjina mishi kai
"Kwarai ma kuwa Alhaji Idris,wannan laifin bana d'anku bane,naku ne. Kada ka manta fa,yaron nan ba shine ya haifeku ba! Akan wane dalili ne zaku zuba mishi ido sai yanda yakeso za'ayi? Ga yan uwansa nan mata a Kazaure,wadanda sukayi karatun na addini dana zamanin don me bazaku samar mishi wata a can ba? Haba jama'a,yaron nan fa ba fin karfinmu yayi ba. Yau ga dan uwansa nan har ya soma tara zuri'a shi ya zauna jiran autar mata? A'a fa,gaskiya laifi yana wajenka Alhaji."
Daddy yayi murmushi
"Gadanga kenan,zamanin nan da kake gani ba'a yiwa yara auren dole,ba irin zamanin mu bane wanda ko fuskar matanmu bamu gani ba sai bayan an mik'o mana su gidajenmu. Wannan zamanin za'a kuntata rayuwar yaro ne kawai."
"Nima bance kuyi mishi dolen ba idi(ya fada cikin zolaya kasancewar sunan da yake kiranshi kenan a baya da kuma wasu lokutan na yanzu),ku turashi kuce yaje ya zab'a idan yaso sai ya sanar maku wacce ta kwanya mishi ko kuwa?"
Daddy yayi dariya
"Gaskiyane,sai ayi hakan toh. Fatanmu Allah Yasa mu dace."
Abba ya amsa da amin. Daga haka hira ta mik'a.......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar
(14)
Misalin karfe sha biyu da rabi na dare,baby tafe akan hanyarta na zuwa birthdayparty na Hibba da saurayinta ya had'a mata. Taci kwalliya har ta gaji da had'uwa. Kid'a ke tashi kawai a motar,saidai cak motar ta soma kokarin tsayawa. Karshe ta tsaya cak akan titin daya kasance shiru tamkar babu mutane sai tsilli tsillin motoci suke wucewa. Ta buga sitiyari da k'arfi ganin mai ne ya k'are mata. Shaf ta mance cewar Dalal ta ari motar taje kasuwa da ita dazu,gashi babu alamun masu siyarda mai a kusa. Wayarta ta dauko,ta kira lambar Hibba,yana ta ringing bata dauka ba. Hakanan Manal da Dalal. Ta tabbatar dukkansu hankulansu yana wajen party. Taja karamin tsaki kafin ta soma duban hanya taga ko zata samu mai taimakonta.
Tafe yake a hanyarsa ta komawa gida daga meeting da yayi (attending) na aikinsu. A gajiye yake saboda ya mance rabon da yakai war haka baiyi bacci ba. Hannu ya gani an sanya mishi ana tsayar dashi. Ya duba dakyau,mace ce,kuma da alama motarta ce ta sami matsala. Ba tare daya lura da ko wacece ba,ya samu waje ya faka domin shi ya dauka ma kabila ce duba da yanayin suturar dake jikinta na gown marar hannu ga kuma gashi a waje.
"Sannu,please ko..."
Sauran maganar ya makale a fatar bakinta ganin Haris. Shi kanshi baisan ita bace saida ya fito daga cikin motarsa suka nufo juna.
Zallar kyawun fuskarsa ta k'ara fitowa a lokacin daya tamketa,ya juya da niyyar komawa motarsa ya tafi. Tayi azamar tarar gabanshi,cikin marairaicewa tace
"Domin Allah ka tausayamin mana bestfriend,wallahi ka tafi ka barni anan za'a saceni ne. Man motata ya k'are ne."
Sai lokacin ya lura ashe harda hudin hanci gareta,ta maka barima fara akan hancin. Ganin yanda ta marairaice ne ya sanyashi kauda kansa,baice komai ba ya gifta ya shige motarsa. Har ta fidda ran cewa zai taimaketa taji yana mata hon. Cikin sauri ta dauki wayoyinta da fos dinta. Ta rufe gilasan motar ta kulleta ruf sannan ta nufi motar tasa. Sai lokacin hankalinta yakai ga lambar motar,nan da nan ta tunano inda ta santa. Ashe shine ya taba binta a guje sadda ta tuk'o motar Kb. Murmushi ta danyi kafin ta zagaya ta bud'e gaban motar ta shiga. Nan da nan kamshinsu ya mamaye motar, har suka rasa fahimtar na wanda yafi tashi.
"Nagode bestfriend."
"Haris sunana."
Ya fada cikin fusata. Ta dubeshi ganin yanda yayi kicin kicin,ta kad'a idanuwanta
"Ok,Haris."
"Ina zan kaiki?"
"Tahir."
Baisan sadda ya dubeta ba,itama har lokacin idanuwanta na kansa. Saidai baice komai ba ya fisgi motar a fusace,gudu yakeyi kamar zai tashi sama,baby kuwa ko a jikinta. To yau ya soma sanin gudu a mota ne? Kallonsa kawai takeyi cike da mamakin irin kyawu na Haris. Bayan haka ma,tafi mamakin yanda duk haduwarta ko kallo bata isheshi ba. Toh ita kuwa iyakar zamanta a rayuwa bata taba ganin namijin daya ganta bai kara kallo ba saboda zubin da halittar da Allah Yayi gareta.
Taka burki da yayi,ya maidota hayyacinta. Wannan ya sanyata kauda kanta daga barin kallonsa. Ta duba,kwarai sun iso kofar hotel din.
"Rayuwar da kika zab'awa kanki ina mai tabbatar maki akwai ranar k'in dillanci. Sam,wannan bai dace da musulma ba. Kin maida kanki kasuwar da kowa yake da damar shiga. Kin zubda k'imarki ta d'iya mace akan son duniya wanda bazai kwatoki daga azabar Allah da kwanciyar kabari ba. Kiyi tunani,matan aure nawa kika dauki hakkinsu wajen nasarar dauke hankulan mazajensu a kansu? Allah bazai kyaleki ba,da rai da lafiyarki muddin baki tuba ba sai kinga sakayya. Idan zina abun yi ce kije kiyi tayi,ke da karya baku da bambanci."
Yayi shiru yana mai duban titi,murya a kausashe ya kara magana
"Get out."
Kamar wacce aka daskarar,gaba daya ta gaza motsi. Bata ce mishi uffan ba. Jin tayi shiru ya sanyashi juyowa da niyyar fad'a,abun mamaki hawaye ya gani suna zuba daga kwayar idanun Baby. Tayi azamar sharesu,murmushi ta k'ak'alo ta jefeshi dashi
"Nagode da taimakon da kayi gareni,Allah Ya kaika gida lafiya."
Daga haka tayi saurin ficewa tayi ciki,saidai kana dubanta zaka fahimci a sanyaye take ko daga yanayin tafiyarta. Ko kadan bata bashi tausayi ba,saidai har ya tafi yana mamakin yanda akayi kalamansa suka sanyata hawaye. Karshe dai ya watsar a cewarsa,munafunci ne. Wanda yayi nisa bazai tab'a jin kira ba....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
0 comments:
Post a Comment