"Kiyi tunani,matan aure nawa kika dauki hakkinsu wajen nasarar dauke hankulan mazajensu a kansu? Allah bazai kyaleki ba,da rai da lafiyarki muddin baki tuba ba sai kinga sakayya."
Har zuwa yanzu da take kwance a gadon d'akin na hotel d'in,ita kad'ai. Wadannan kalaman ke yawo a kwakwalwarta. Damuwar da ta yawaita a zuciyarta ya hanata zuwa bangaren da ake fatin hibba,hakan yasa ta kama d'aki da zummar ta kwana da safe tayi gida. Batayi iya runtsawa ba kalaman Haris sun shigeta matuka. Ta tuno yanayin fuskarsa wanda ke nuni da tsantsar takaicinsa na halin da rayuwarta ke ciki. Bata taba cin karo da wanda ya nuna kyama a harkar rayuwarta ba kamar shi.
"Nan da kike ganinsa ustaz ne,ya fiye takura kansa baison ya more rayuwarsa."
Kalaman Kb akan Haris suka fad'o mata. Tabbas ta yarda da hakan,Haris kamilin mutum ne wanda bai sha'awar rayuwar da suke ganin itace ta arziki a garesu.
*****
Da zarar ya runtse ido,ita yake gani. Bai manta sa'adda ta dubeshi fuska dauke da ruwan hawaye wanda yasan na munafunci ne. Amma meyasa ta kasa b'acewa tunaninsa,bai manta sadda ta fice a motar ba jiki a sanyaye. Toh hakan yana nufin taji nasiharsa ne ko kuwa? Amma ai inda ace ta dauki zancensa,babu abunda zaisa ta shiga hotel d'in. Ya dafa goshinsa yana mai runtse ido,bayason ya dunga tunanin wacce bazata amfaneshi da komai ba. Hakan yasa ya mike tsam yayo alwala ya soma nafila duk domin kaucewa tunanin wacce ko sunanta bai sani ba.
******
"Gobe zan koma Abuja,inaso muyi wata magana ne."
Ya tsayar da rubuce rubucensa sannan ya dago fararen idanunsa ya saukesu akan Kb,fuska ba walwala.
"Na'am,ina sauraronka."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(16)
Kb ya numfasa yana mai sassauta muryarsa,ba tare daya yarda ya dubi kwayar idanun Haris ba ya soma magana
"Look Haris, nasan na aikata ba daidai ba. Nasan zuwa yanzu ka dauki zafi dani baka kaunar sanyani a idanuwanka ma,amma don Allah kayimin uzuri wallahi kaji na rantse maka babu macen da nake mu'amala da ita a waje idan ba Baby Tasleem ba."
"Baby Tasleem."
Haris ya nanata sunan a ransa,sai yau ma yasan sunanta. Kb ya cigaba da magana
"Nasan ban kyautawa Yasmeen ba kamar yanda ban kyautawa kaina ba. Gaskiyar magana rabuwa da Tasleem abune mai matukar wuya agareni,shiyasa na yanke shawarar zan aureta a matsayin matata ta sunna."
Wani mugun kallo da Haris ya watsa mishi ya sanyashi kauda kansa cikin jin nauyi,ya numfasa kafin ya cigaba
"Yes Haris, kabar yimin irin wannan duban,raya sunnah nakeson yi ba wai zina ba. Duk da dai zuwa yanzu Baby tak'i bani had'in kai,ta nunamin babu abunda ta tsana kamar aure,wannan shine hakikanin damuwata. A matsayinka na amini kuma d'an uwana don Allah ka taimakamin da shawara."
Ba tare da ya jira cewar Haris ba ya mike tsam ya nufi hanyar fita cikin jin nauyin amininsa. Saida yakai k'ofa sannan ya dakata ba tare da ya juyo ba
"Ba hakan dana fada yana nufin na rabu da soyayyar matata ba,a'a. Inason Yasmeen matuka saidai inason raya sunna. Idan har ka amince da bukatana,ka taimakeni kayi jihadi wajen shawomin kan Tasleem domin cetomu daga wannan rayuwa please Haris. Goodbye."
Ya fice cikin sauri ba tare da ya juyo ba ballantana ya lura da irin firgicin dake akan fuskar amininsa.
Rike kai yayi yana mai runtse ido,gabansa na duka da sauri da sauri. Aure?!! Tsakanin Kb da baby tasleem?!!
Ya nanata a zuciyarsa,kafin ya kwantar da kansa akan kujerar ya runtse ido. Toh menene matsalarsa? Me zaisa zancen nan ya dameshi? Amma kuma dole zai dameshi ai,ko babu komai,kanwarsa ce fa Kb ke shirin yiwa kishiya da karuwa! Dole yaji tsanar auren,dole ne ya taya 'yar uwarsa kishi. Kishi mai tsanani.
Ya bud'e ido,kafin ya hasko halittar Baby da wayewarta sannan ya dawo ga kanwarsa wacce baby bazata nunawa kyau ba saidai ta fita a halittar jiki da kuma barikanci. Ita d'in ta kasance saliha,domin ko a gida bata fiye magana mai tsawo ba,sam, bata da hayaniya tamkar Haris d'in take. Wannan yasa duk cikin kannensa yafi tausayinta yafi sonta tasu tafi zuwa d'aya. Anya kanwarsa zata iya kishi da gogaggiyar mace irin Tasleem?
"Idan har ka amince da bukatana,ka taimakeni kayi jihadi wajen shawomin kan Tasleem domin cetomu daga wannan rayuwa please Haris."
Ya tuno zancen Kb,wannan ya nuna kenan yayi kokarin shawo kan Tasleem domin ta amince da bukatarsa na suyi aure amma sam,tak'i aminta.
Haris ya girgiza kai cikin takaici da bacin rai
"Tabbas Kabir bashi da kunya."
Ya fad'a a fili. K'arar wayarsa ta katseshi,ya duba yaga sunan Daddy. Da sauri ya d'auka. Bayan sallama da gaisuwa ne Daddy ya sanar dashi ya shigo yazo ofishinsa yana nemansa. Ya amsa kafin ya tashi a hanzarce ya nufi ofishin director kuma uba a gareshi,Alhaji Idris.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(17)
Ya shiga da sallama. Daddy zaune akan kujerarsa sanye yake da riga 'yar ciki da wando ya rataye babbar rigar jikin (hanger). Idanunsa boye cikin farin gilashi. Ya bar danna laptop dinsa ya dago yana mai amsa sallamar d'ansa. Cike da girmamawa ya russuna ya gaida Daddy. Daddy ya amsa fuska a sake kafin yace
"Gaisuwarka bata k'arewa Harisu,ayi ta gida ayi ta ofis ko?"
Haris yayi murmushi mai bayyana hak'ora,baice komai ba ya zauna saman kujera bayan yayi kokarin d'an rage tsawo duk da hakan. Daddy yayi gyaran murya ya soma magana
"Haris,kwanaki sun shude sun zama watanni,ga watannin sun koma shekaru. Dan uwanka gashinan zaune da iyalinsa,a dukkan tsawon watannin nan mun barka ne akan ka nemi zab'inka gudun shiga rayuwarka. Saidai har kawo yanzu,shiru Harisu."
Daddy ya k'arashe cikin rarrauniyar murya mai russunar da zuciyar wanda ake yiwa. Haris baice komai ba yayi shiru yana sauraron Daddy
"Ga iyayenka nan girma yana k'ara hawan kanmu,wannan ya sanya naga tunda abun ya zama haka na baka zab'in zuwa can Kazaure,ka duba cikin 'yan uwanka dake can ko Allah zaisa ka sami wata cikinsu da zakaji nutsuwar zuciya akanta. Nidai fatana Allah Ya baka mace ta gari."
Haris yayi murmushi kad'an jin wannan batu da Daddy,a gefe kuma ya gama gaskata cewa ba k'aramin so Daddy da Hajiya sukeyi mishi ba,tamkar daga cikinsu ya fito. Ya tabbata gudun abunda zai b'ata ransa ne yasa Daddy b'ullowa ta wannan hanyar.
"Tashi ka koma ga aikinka Harisu,zan jiraka daga nan zuwa gobe duk abunda ka yanke toh,idan ma akwai wacce ka gani kake so toh Alhamdulillah. Wannan ma shi muka fi muradi. Allah Yayi jagora. Tashi ka tafi, ka turomin sakatare."
Cike da jin nauyi Haris ya mike yana mai amsawa da toh,ya fice jiki a sanyaye. Ya isar ga sak'on Daddy ga sakatare kafin ya koma ofis.
Kasa nutsuwa yayi,zancen Daddy yake ta juyawa. Toh wai ko zai koma ya sanar dashi cewar ya bashi zab'ine? Su zab'a mishi kawai mace tagari? Idan ba hakan ba ya zaiyi toh? Shi kam bai taba budurwa ba,a takaice ma basa gabansa. Allah Ya yishi mutum ba mai son magana sosai ba,baisan ta inda zai soma zuwa ga mace da zummar soyayya ba. Toh yace mata me? Ai shi kam matan ma bakin jini yake a gurinsu,bai mantawa dai da wata abokiyar karatunsa a Malaysia,Rahima. Babu irin bibiyar da batayi ba akan ya amince da soyayyarta amma sam bata samu fuska ba.
Bai mance ranar da Kb ya tursasashi akan sai ya saurareta ba. Suka shirya suka fita wajen shak'atawa inda tuni Kb ya yiwa Rahima maganar ta isa wajen zasu zo. Koda sukaje,nan suka hangeta zaune a kujera bakin swimmingpool na wajen. Kb ya daki kafadarsa yana dariyar mugunta
"Oya jeka,sannan don Allah kada ka bani kunya. Nasan wannan ne farkon tsayuwarka gaban mace a matsayin saurayinta,be a man!"
Harararsa yayi kafin yayi gaba cikin takunsa na nutsuwa,tana ganinshi ta mike tsaye domin girmamawa gareshi tana dariyar farin ciki.
"Sannu da zuwa Haris na."
Yayi dan murmushi kafin ya amsa ya zauna,hakan ya sanyata zama itama. Shiru ya ratso,ya zamana hirar ita keyi yayinda shi ya zama macen. Daga um,sai um um,ga murmushi da yakeyi baya ko dariya. Tun yana burge Rahima,har ya daina cikin yanayin damuwa tace
"Haris na yadai? Ko ka gaji da ganina ne? Na dameka?"
Ya duba agogo kafin ya kalleta yana murmushi
"No,ba haka bane saidai akwai wani uzuri dake gabana yanzu. Kiyi hakuri dai sai mun hadu a makaranta."
Daga haka ya mike da niyyar tafiya,tayi azamar dakatar dashi ta hanyar cewa
"Ya makomar soyayyarmu? Ka amince dani ne ko kuwa..."
"Yanzu kam karatu ne a gabana ba soyayya ba. Kiyi hakuri "
Yayi gaba,yayin da ya barta cike da bakin ciki da dana sanin zuwanta. Yana haduwa da kb wanda yake dubansu. Ya shiga dariyar mugunta har yana kwarewa. Daman yasan amininsa ba iya zancen yayi ba,saidai ta duri haushi. Abun ma bai bashi dariya ba saida Haris ya labarta mishi yanda sukayi shima yana dariyar. Kb ya bugi sitiyari
"Amma kai kam anyi d'an iska,wato baka soyayya sai karatu. Kalaman yayi yanayi dana mace."
Tun daga wannan ranar Rahima bata k'ara neman shiga harkarsa ba. Hakan ma sai yayi mishi dadi domin sam ba sonta yakeyi ba.
****
Haris yana kaiwa nan a tunaninsa yayi murmushi kafin ya watsar da komai ya cigaba da aikinsa.
****
Dalal,Manal da kuma Hibba,sai Baby. Zaune a falon.
Baby sanye da wando three quarter sai 'yar shimi,kwance take akan two sitter ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana (game) da iPad dinta,tana yi tana taunar cingam. Hankalinta kwance,jifa jifa take sanya baki a hirarsu na duniya. Manal ta dubesu tana murmushi
"Albishirinku."
Suka amsa da goro banda Baby dake sha'aninta saidai kuma hankalinta yana ga sauraron abunda zai fito daga bakin Manal.
"Zanje zaman wata uku gidan Alhaji Ubale Kwangila."
Cikin rashin fahimta Dalal da Hibba suka yamutse fuska
"Bamu fahimceki ba."
Kafin ta basu amsa,Baby tayi dariya ba tare data dubesu ba
"Kudai kam baku saurin fahimtar mutum,kasuwanci na wata uku zataje yi gidan Alhaji Ubale. Don wannan baikai kimar da za'a kirashi da aure ba."
Dalal da Hibba suka buga shewa,Manal tana dariya tace
"Dad'ina dake saurin fahimta Baby,toh kun fahimta inace?"
Hibba tace
"Kwarai kuwa,amma fa yana da mata ko?"
Ta rausaya idanu
"Taci kaza kazanta(ashar),ke aure ne fa tun ana fama da shan miyar kuka a kauye. Babu abunda zata hanani,wai kin manta nafi kunama radadi?"
Ta buga hannuwanta
"Wata uku kacal,nayi na gama dashi na fito. Batun da nakeyi maku wahalallen ya kammala yimin gyaran gidansa na Abuja. Can zan lula mubar shegiyar a Kaduna. Magana ma ta isa kunnen Momi,aure nan da wata d'aya sai a soma shiri."
Sukayi dariya gaba daya har Baby,domin yanayin da Manal tayi furucin duka ya basu dariya.
"Kidai shiga da shirinki,kada a samu matsala ya gark'ameki. Me akeyi da aure?" Cewar Hibba.
Dalal tayi dariya
"Shegiya,kada ki manta shine ya haifeki,ko kin mance gyatumarki Sarai mai kosai na tuna maki?"
Dam! Kirjin Baby ya buga,jin furucin daya fito daga bakin Dalal......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(18)
Shewarsu ta katse mata tunani,hibba tace
"Allah Sarki uwata,hauka nakeyi zan mance da ita? Karki ganni anan, duk wata saina tura mata kud'i ta account kawata Balaraba. Ba don wannan mugun uban nawa ba ai da wataran saidai ta ganni naje ziyara. Kunsan dai duk iskancina bana manta MAHAIFIYA."
Baby tayi shiru,jikinta a sanyaye. Ita kam yaushe rabonta da tata uwar? Shekaru biyu kenan,gwara ma mahaifinta,tana da masaniya akansa,ta tsaneshi shima ya tsaneta,wannan dalilin ne yasa babu wanda ya taba yunkurin neman wani a cikinsu. Amma mahaifiyarta fa?
Dalal tace "Ai gwara a dungayi ana tuna asali,nikam saidai nace Allah Ya jik'an nawa iyayen. Ita kuwa Gwaggona da ita muke ci da sha. Ina yawan zuwa gidanta a Kano,kuma kun sani."
Ga mamaki sai sukaga Manal na hawaye tace
"Gwara ku, kuna da iyayen. Nikam idan baku manta ba tsintata akayi a bola,sai ya zamana wanda ya daukeni ya rikeni har girmana,shine mutumin farko daya soma aikata masha'a dani."
Tayi shiru tana sharar kwallah,kowannensu jiki yayi sanyi na tuno abubuwan daya shud'e a rayuwarsu. Baby daga kwance itama hankalinta taji ya tashi,babu wacce ta tsaya a ranta kamar mahaifiyarta. Taji gaba daya tanason taje duba lafiyarta. Manal ta share hawaye ta mike
"Yan iska zaku tunomin bakin labarin rayuwata,ku tashi muje shan ice cream. Yau jakata a cike take."
Sukayi murmushi don babu wacce keda kuzarin dariya,Manal ta dubi Baby.
"Zakije ne?"
Baby ta girgiza kai
"Banajin fita ne."
Sun lura jikinta yayi sanyi, tausayinta ya mamayesu musamman ma Manal wacce anan duniya ita kadai tasan wacece Baby Tasneem. Ita kadai tasan tarihin rayuwarta. Don kafin ta hadu da kowacce cikinsu,Baby tasleem ta soma haduwa da ita harma ta sauketa a gidanta. Haka suka fice suka barta a gidan. A ranar Baby taci kuka sosai,ba don komai ba sai don rashin sanin halin da mahaifiyarta ke ciki. Karshe ta mike ta shiga daki ta kwanta ba don tanajin bacci ba. Sai don kawai tunanin rayuwarta.
*****
KWANA HUDU BAYAN HAKA
Tafiya takeyi da baya da baya tana kallonta,yayinda ita kuwa ke kwance duk fuskarta ya baci da kuraje,hannu take miko mata alamun tsayar da ita tana ihun kuka
"Ya d'iyata,kada ki gujeni! Karki barni cikin wannan halin! Ki dawo gareni!"
Maimakon ta dawo,sai ta juya a guje zata tafi, karar da taji uwar tayi ya sanyata itama kwala ihu kafin tayi wuf ta fada wata rijiya a wajen."
A tsananin firgici Baby ta tashi sakamakon wannan mafarki mai rud'arwa,gumi ya wanke fuskarta duk da Ac dake a kunne. Sai haki takeyi tamkar wacce tayi gudu. Ta sanya hannu ta dafe kirjinta dake dukan uku uku. Can kuma tayi wuf ta sauko daga gadon. Wani d'an karamin akwati ta dauko ta bud'e. Hoto ne a cikin (envelope),nan da nan ta zaro tana duba. Dattijuwa ce tare da yarinya mai shekaru uku,sai dan saurayi mai kimanin shekaru goma sha daya a hoton. Dukkansu suna dariya.
Ta rungume hoton a kirjinta yayinda hawayenta suka karu. Tausayin kanta ya dabaibayeta,taji nan duniya bata sha'awar komai daya wuce na zuwa kauye ganin Mahaifiyarta. Tun hirar da sukayi tare dasu Manal,hankalinta yake a tashe. Ta amince bazata taba samun nutsuwa ba har sai ta dangana ga duba lafiyar mahaifiyarta.
******
Karfe goma na safiyar Asabar,ya shirya tsaf cikin kananun kaya ya feshe jikinsa da turaruka. Bai dauki komai ba sai karamin trolley dinsa inda ya shirya kayan sawarsa. Saida ya soma zuwa gidansu yayi sallama da Daddy,kafin yaje gidan Abba. Nan ma yayi musu sallama,mahaifiyarsa ta bashi sako a kaiwa uwarta,wato kakarsa. Daga haka ya kama hanya.
******
Zaune suke suna karyawa,basu ankara ba suka ganta ta fito tana jan akwati. Ba jan akwatin ne yafi basu mamaki ba,tunda sun saba tafiye tafiyensu. Shigar dake jikinta ne ya burgesu kuma ya basu mamaki. Doguwar rigar atamfa ce, anyi mata dogon hannu three quarter,maimakon ta dora dankwalin saita yafa karamin mayafin (pashmina) a kanta. Saida tazo kusa dasu sannan ta dubesu fuskarta babu wata kwalliya ta daukar ido sai hoda da jan baki mai kalar ruwan hoda(pink).
"Zanyi 'yar tafiya ne,amma in sha Allah bazata wuce kwana uku ba. Amanar gidana yana hannunki sister."
Ta dubi Manal. Murmushi manal tayi kafin tace
"Karki samu damuwa baby,shigarki tayi mana kyau,tamkar bake ba."
Tayi murmushi batace komai ba ta nufi waje. Babu wata wata,ta fada motarta ta shiga. Duk da dai bata taba karambanin tuk'i mai nisa ba,yau kam tanason yi. Dole taje ga mahaifiyarta ta duba lafiyarta. Tsananin kewarta yana neman hanata sukuni,ga fargabar abunda zata tarar sskamakon mafarkin da tayi a daren jiya......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(19)
Tafe take kawai saidai dukkan hankali da tunaninta yana ga zantukan karshe da tayi da mahaifiyarta kafin su rabu.
"Na sanki,yarinya kike mai basira da kula dakai. Kada ki sake ki bari shaidan yayi maki hud'uba Tasleem. Kibi matar ubanki sau da k'afa,kiyi biyayya ga mahaifinki kada ki sanya damuwar komai a ranki. Allah Yana tare dake."
Hawayenta suka k'aru,yayin data k'ara karfin gudunta.
"Fitarmin daga gida,yar iskar yarinya! Kin bata wayonki! Bazaki zo ki b'atamin tarbiyyar yarana ba! Shegiya! Kedai kam ina kwakwanto akanki! Anya nine ubanki?!"
A zuciye ta kuma k'ara karfin speed dinta,hawaye bai bar kwaranyo mata ba.
"Kin bani mamaki kanwata,kin bata wayonki. Har da kanki ki dunga kai kanki dakin namiji?!! Tirr da wannan d'abi'a taki. Toh wallahi ki barmin gidana,kuma kika kuskura kikaje ga mahaifiyarmu kika kashe aurenta,wallahi saikin raina kanki! Kije duniya ce! Daidai take da kowa!"
A fusace take tafiya,bata ankara ba,motar ta kufce mata, ta rasa yanda zatayi ta tsayar da ita. Taka burki takeyi saidai batasan dalilin cijewar burkin ba,haka tayita wala wala har ta k'umu da bishiya. Bata k'ara sanin duniyar da take ba.
******
Farkawa tayi ta ganta kwance a gadon da yafi kama dana asibiti,ta tsurawa rub'abb'en kwanon silin din ido tana duba,hannunta tayi kokarin d'agawa da niyyar tab'a goshinta wanda ke sarawa tamkar zai fad'o saidai wani irin azaba da hannunta yayi ya sanyata cije lebbanta tana 'yar k'ara kad'an.
Wannan ya jawo hankalinsa,yana zaune saman gadon dake fuskantarta yana danne wayarsa a kokarinsa na kiran gida domin kada a jishi shiru ayi tsammanin ko babu lafiya. Ya dubeta,nan da nan zuciyarsa tayi sanyi ya mike ya karaso wajen kanta
"Sannu,ya jikin?"
Ta waiwayo dakyar sakamakon ciwon kan da takeji ya addabeta,ido kawai ta zuba mishi ba tare da tace komai ba. A zuciyarta mamaki kawai takeyi,meyasa Allah Yake yawan kawo mata shi aduk lokacin da take da buk'atar taimako? Abun tambayar ma shine,ya akayi yazo nan?
Kafin ta kammala tunaninta tuni ya juya ya fita. Minti daya sai gashi da likita,likitan ya karaso yayi mata gwaje gwaje kafin ya dubeta yana murmushi
"Sannu fa madam,yanzu meke damunki bayan hannunki? Kina jin wani ciwo daban ne?"
Baby ta k'ak'alo murmushi kafin ta d'aga hannu ta dafe kanta.
"Oh sorry,bari na sanya nos ta k'ara baki magungunanki. A sannu zai daina. Saidai kafin nan..."
Ya juya yana dubansa
"A samo mata abunda zata ci don bana zaton taci wani abu a yau."
Ya dubi Baby wacce tayi tsai da ido tana kallonsa,fuskarta babu yabo ba fallasa kamar dai wani tunanin na daban takeyi. Ya dauke kansa ya maida ga likita yana mai gyada mishi kai.
Likitan yana fita yabi bayanshi ba tare da yace mata uffan ba. Ta bishi da kallo sannan ta kauda kanta tana tuna abunda ya janyo mata hatsarin. Hawaye suka gangaro saman kuncinta,ko kusa batayi yunkurin sharesu ba,saima ta barsu suka cigaba da shatata.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(20)
Haka har ya dawo ya sameta cikin wannan yanayin. Shigowar baisa ta sharesu ba,a zahiri ma sam batasan da wanzuwarsa ba. Lura da cewar ko kusa batasan da shigowarsa bane da kuma sallamarsa,yasa shi yin magana
"Tasleem."
Batasan lokacin data dubeshi ba,haka kawai sanyi ya ratsa zuciyarta domin tunda take bata tab'a jin wanda ya iya kiran sunanta ba kamarsa. Ya kauda kansa yana mai bude ledojin,fuskarsa a daure
"Tashi ki d'an ci wannan."
Ta mike dakyar ta zauna bayan ta sauke kafafuwanta dake ciwo kadan kadan a k'asa. Batace dashi komai ba ta mike tana dafe gado,band'aki ta zagaya. Can kuma sai gata ta fito.
"Ko zaka taimakamin da brush da maclean please?"
Ya mike ya fita, sai gashi ya dawo dauke dasu sabbi. Saida ta tabbatar da tsaftar bakinta sannan ta fito. Maimakon ta iskeshi saita iske nos. Da taimakonta ta ci abincin kadan ta sha yoghurt din da yawa kafin daga bisani tasha magungunan. Bayan nan tayi mata godiya,nos din tana shirin fita ta tsaidata
"Don Allah karfe nawa ne? Inason gabatar da sallar dake kaina."
Ta bata amsa
"Ai Hajiya yanzu haka ma isha'i ta kusa."
Cikin mamaki Baby ta mike tayo alwala ta fito, rarraba idanuwa ta tsaya yi ganin babu wani darduma ko abunda zata rufe jikinta dashi. Turo k'ofar da akayi ta sanyata waigawa. Sukayi ido hud'u dashi,ta sakar mishi murmushi ya kauda kai.
"Sannu HARIS,don Allah inason yin sallah ne."
Wani irin kallo yayi mata,ta kauda kanta. Ya jinjina kai baice uffan ba ya fita. Sai gashi dauke da akwatin kayanta da kuma dardumar dake cikin motarsa. Ajiyewa yayi kawai ya koma gefe ya tsaya domin son ganin ikon Allah. Ga mamakinsa sai yaga ta fiddo Hijab zunb'ulele ta sanya. Baki ya saki har lokacin bai bar jifanta da kallon mamaki ba. Ta lura da hakan,murmushin dai ta k'ara yi mishi a karo na ba adadi. Batace komai ba ta soma kokarin shimfid'a dardumar da hannunta na hagu wanda baya ciwo,saidai ta kasa. Ba zato taga hannuwansa sun kama mata. Ta dubeshi,bai ko kalleta ba. Yana gama shimfid'a mata ya kauce.
"Nagode."
Ta furta a sanyaye. Salloli uku dake kanta ta rama,kafin ta zauna ta kwararo addu'o'i tana hawaye. A karshe ta shafa. Tana shirin mikewa,aka soma kiraye kirayen sallar Isha'i,wannan yasa Haris ficewa zuwa masallaci.
Itama ta gabatar da sallar isha,ta had'a da shafa'i da wutri. Nan ma addu'ar tayi ta shafa duk da irin radadin da hannunta keyi bata k'i d'agashi ba yayin addu'a.
Anan kan darduman ta zauna,kafafuwanta a mik'e tana mai jingina kanta da bango. Bata fi mintuna ba,Haris ya dawo da sallamarsa. Bakinta ya motsa alamun amsawa. Ya zauna a gefen gadon kafin ya soma magana
"Nayi iyakar taimakon da nake ga ya dace nayi gareki a matsayinki na 'yar uwa a musulunci dana sameki rai a hannun Allah na kawoki asibiti. Alhamdulillah,tunda har sauki ya soma samuwa zan tafi. Ga wayoyinki nan..."
Ya sanya hannu a aljihu ya fiddo mata su gami da ajiyewa a gefenta.
"Kina iya kiran d'aya cikin abokan harkarki,anan babban asibitin kauyen danbatta kike. Batun motarki kuma,gaskiya ta samu matsala,amma tana nan a police station na nan gefen asibitin(inji ni.. Lol)idan yaso idan kun tashi saiku janyeta ku koma. Na barki lafiya."
Ya sanya hannu ya fiddo bandirin kud'i na 'yan d'ari biyar biyar ya ajiye mata. Caraf ta riko hannunsa,da sauri ya dubeta. Hawayen da yaga tana fitarwa ne ya sanyaya mishi jiki. Ta narkar da fuskarta tana mai marairaice murya
"Kada ka gujeni a wannan yanayin da nake ciki don Allah Haris. Babu wanda zai taimakeni kamar kai,babu mai bani kulawar daka bani. Da ace kasan inda na nufa yanzu,da bazaka barni ba har sai kayi kokarin sadani da muradina."
Ya dauke hannunsa ya koma ya zauna yana dubanta baice uffan ba.
"Duk tsawon rayuwata a Bariki,ban tab'a cin karo da mutumin da yayi kokarin yimin fad'a akan wani abu na daga bakar rayuwar dana zab'arwa kaina ba,sai kai Haris. Ban taba fahimtar kuskuren da nakeyi ga rayuwata ba sai a wannan lokacin dana kusan mutuwa ba tare dana kai ga neman gafarar Ubangijina ba game da b'arnar dana jima ina aikatawa ba."
Ta tsagaita gami da sanya hannunta marar ciwo ta share hawayenta kafin ta dubi Haris wanda ya zuba mata ido kawai yana sauraronta,auna maganganunta kawai yakeyi a zuciyarsa. Wai gaskiyarta take fad'a mishi ko kuwa dai barikancin ne ya dawo kanshi?
"Da wuya ka aminta da zancena,saidai don Allah ina neman alfarma agareka,ka taimakeni kada ka barni anan. Ka amince na taso mu tafi?"
Ta karashe tana karya wuyanta gefe idanunta a kansa. Ya tabe baki kafin ya girgiza kansa
"Ni ba d'an BARIKI bane,saidai na karanci halayyarku. Ki sani, Allah ba abin wasa bane. Yanzu idan kikace zakiyi karya da sunanSa,zai iya hukuntaki. Ba don ni zaki tsorace shi ba Tasneem. Ban hanaki aikata masha'arki ba. Saidai wannan hatsari daya sameki ya kamata ya zamto izna gareki,da ace mutuwa ta riskeki a daidai wannan lokacin,wane guzuri kika tanada da har kike ganin zai tseratar dake daga azabar Allah?"
Ya k'ara girgiza kansa,bakin ciki karara da kuma tsana ya bayyana saman fuskarsa.
"Kuna ganin cinyewa ce ga diya mace ta fad'a yawon barikanci! Kuna kallon lamarin a matsayin wayewa,alhalin babu abunda zaku tsinta ciki nan gaba sai bakin ciki idan kuwa har mutuwa ta riskeku ba tare da kun tuba ba,hakika zakuyi nadama irin wacce baku tab'a yinta ba a duniya. Babbar DARAJAR DIYA MACE,shine ta kasance a d'akin mijinta. Babu mutunci a zamowarta tamkar wata kasuwa da kowane kara da kiyashi zai shiga."
Ya dakata sakamakon sheshshekar kukan Baby Tasneem daya cika d'akin. Gaba daya a rayuwarsa ya tsani kuka,musamman ma na d'iya mace. Yanzu yanzu ne zaiji zuciyarsa ta karaya,wannan ya sanyashi mikewa da sauri ya nufi hanyar fita.
"(No Haris, please don't leave me alone,please!)."
Baiko juyo ba ya fice daga d'akin. Kuka sosai Baby takeyi,babu abunda take tunanowa sai rayuwarta. Ji takeyi tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta a gaban mahaifiyarta kwance a jikinta. Dakyar ta share hawayenta.
Kasancewar cikin magungunan da nos ta bata harda na bacci,ya sanya ta soma hamma. Tun tana korewa har dai ya dauketa anan kan dardumar ba tare data shirya masa ba........!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(21)
Sanyin asuba ne ya farkar da baby. Duk shaidanci irin na Baby,bata wasa da sallah. Ta mike tana mutsistsika ido. Sai lokacin ta tuno abunda ya afku. Tausayinta kanta ya mamayeta,ta mike ta zagaya bandaki.
Ta jima tana addu'o'inta kafin ta mike ta dauki wayoyinta ta hau kan gado. A sannu ta shiga sarrafata tamkar bataso. Missedcalls din Kb har shida a Mtn dinta dinta,hakanan a Airtel dinma missedcalls har goma. Text message kashi kashi harda na whatsapp,duk tambayar tana ina. Ta samu missed calls daga Momi ma da kuma kawayen nata. Wato su Manal. Sai sauran wadanda ta daukesu matsayin tarkace. Murmushi tayi kafin ta kashe wayar gaba dayanta. Ta kurawa silin ido bata da niyyar bacci. Tunanin Haris ya fado mata, yanzu dagaske shikenan ya tafi ya barta? Hawaye suka kwaranyo mata, haka tayi ta tunane tunane kafin bacci na ba zato ya saceta.
**** BAKWAI DA MINTUNA(7:00AM)
Turo kofar da akayi gami da sallama ne ya farkar da ita daga baccin da takeyinsa ba don dad'i ba sai don kawai yana fisgarta. Idanuwa ciki ciki take dubansa,daman ya lumsassun idanuwanta suke a farke ballantana kuma akwai bacci cikinsu. Ta k'ara lumshesu tana murmushi duk a zatonta mafarki takeyi ba gaske bane. Saida ta k'ara jin sautin ajiye leda a kusa da 'yar dirowar gefanta,tayi firgigit ta bud'e ido ta zuba mishi.
Fuskarsa a daure tamau babu alamun dariya,kallo daya yayi mata ya dauke kansa,baice da ita komai ba ya fice. Bayansa tabi da kallo tana murmushi kafin ta cije lebbanta.
Tabbas Haris yana da tausayi,mutumin kirki ne sannan Ustaz ne na hakika kuwa kamar yanda Kb ya shaida mata. Bata tab'a tsammatar yana nan asibitin ba bai tafi ba sai a yanzu daya shigo. Ta mike ta janyo ledar,murmushi tayi ganin jug dauke da ruwan shayi da batasan daga inda yazo ba,saidai yayi mata kama da sabo. Sai kayan shayin. Mikewa tayi a sannu,zuwa lokacin banda hannunta da take fama dashi babu kuma sauran wani ciwon dake addabarta. Wanka ta soma yi kafin tayi daura kirji ta fito. Kayanta ta dauka a akwati ta koma bandakin ta kimtsa cikin riga da siket 'yan kanti,bakak'e anyi musu kwalliya da fari da bulu. Ta yafa mayafin (pashmina) a kanta,saboda dukkan kayanta bata da wadataccen mayafi kwata kwata. Tana shirin ninke wanda ta cire ne nos ta shigo. Suka sakarwa juna murmushi,kafin nos ta ajiye kayan aikinta akan gadon.
"Sannu madam,bari na taimaka maki. Ai yanzu kada kice zaki dunga wahalar da hannun nan naki,ki bishi a sannu har ya warke."
Ba musu baby ta zauna tana dubanta yayinda take linke mata kayan. Cikin siririyar muryarta ta jefo mata tambaya
"Don Allah na tambayeki mana."
Nos ta juyo tana dubanta
"Inajinki madam."
"Wannan yayan nawa daya kawoni yana nan har yanzu?"
Ta danyi dariya
"Yana nan madam,ai bazai iya tafiya ya barki a wannan halin ba. A masallaci ya kwana yanzu haka ya sanya a wanke mishi motarsa da alama dai yau zaku wuce don likita yace zai iya baku sallama a yau."
Baby ta gyada kanta,ita kanta ta k'agu tabar wajen nan,don ma dai babu laifi,suna kula da tsaftar asibitin nasu. Tana kallo nos dinnan ta k'ara yi mata dressing na hannunta tare da yin allura,sannan ta fice bayan ta gargadeta akan tasha magungunanta.
Ta hada shayin kad'an tana tunanin ko Haris ya karya? Ta daure ta ci ta sha.
Daidai lokacin da take b'allar magungunanta zata sha,ya shigo da sallama likita yana biye dashi. Duk iyakar kokarinta na ganin sun had'a ido bai yarda ba,gashi sai faman d'ad'd'aure fuska yakeyi. Hakan duk ya sanyayar da jikinta.
"Sannu ko? Ya jikin?"
Ta maida dubanta ga likitan,wanda ba shine wanda ya dubata da farko ba. Dakyar ta iya amsa mishi
"Alhamdulillah."
Ya aunata kafin ya duba takardunta sannan ya dubeta
"Akwai inda keyi maki ciwo?"
Girgiza mishi kai kawai tayi domin a zahiri hankalinta yana ga Haris dake danne danne a waya. Batasan dalilin daya janyo bata gajiya da dubansa ba. Haka kawai ya zame mata tamkar farin wata,wani irin kyau da kwarjini ya k'ara yi mata. Zancen likita ya katse tunaninta a inda ya dubi Haris
"Alhamdulillah,zamu iya bata sallama yanzu. Jikinta yayi sauki sosai. Saidai ta kula da shan magunguna hakanan kada ta takurawa hannunta da aiyuka."
"Ok."
Daga haka suka fice tare da Doctor din.
Kafin tayi wani yunkuri,wayarta ta soma k'ara. Ta duba,Kb ne. Dauka tayi tana mai karawa a kunnenta batace uffan ba.
"Hello,hello babyna. Kina jina? Don Allah kiyimin magana kafin na fita a hayyacina."
"Na'am,ina sauraronka Ka..."
Ta gaza k'arasawa sakamakon shigowar Haris. Ya dubeta ta dubeshi kafin ya dauke kai ganin yanda tayi yanayi da marar gaskiya. Akwatinta kawai taga ya bude zif dinsa,ya dauki kudaden daya bata ya sanya mata ciki. Sannan ya dauke dardumarsa yayi gaba tare da akwatin. Ranta yayi sanyi.
"Hello,me kike cewa ne?"
Sai sannan ta tuno da ashe fa waya takeyi
"Look kabir,yanzu ba lokacin magana bane. Zan nemeka."
Ta kashe wayar gaba dayanta. Tana shirin mikewa ya dawo,ledojin magungunanta ya dauka sannan ya ajiye mata silifas dake a hannunsa sabbi fil. Har yakai k'ofa yayi magana tamkar bayaso
"Kina iya tasowa."
Ya ficewarsa,ta mike ta sanya silifas din tana murmushi. Komai na Haris burgeta yake, a tun ranar data soma ganinsa.
*****
A harabar asibitin ta hangoshi yana kokarin mikawa wani kud'i da alama dai shine wanda yayi mishi wankin mota. Kallonta da yayi ne ya sanyata soma tafiyar nan nata mai kama da yanga ta nufeshi bayan ta dauke idanunanta a kansa. Zagayawa yayi ya shiga motar, itama ta zagaya ta shiga gidan gaba. Ribas yayi ya fita daga asibiti
"Barka da asuba Haris."
"Barka. Ya jikin?"
Ya fad'i tamkar dole akayi masa,
"Alhamdulillah,na samu sauki sosai."
Baice uffan ba,kai tsaye police station dinnan ya nufa. Anan baby taga motarta a ajiye.
"Ina zuwa."
Ya fice, magana taga sunyi da wani sanye da kayan 'yan sanda kafin ya fiddo kud'i ya bashi. Sai kuma taga sun zaro waya,Haris na magana mutumin yana kwafa hakan ya fahimtar da ita cewar lamba ya bashi. Tayi tsai tana dubansa,ta tsani yawan kallo,batayi hakanan batason ayi mata. Amma menene da Haris wanda ke daukar hankalinta ga kallonsa.
"Kefa banza ce, keda ake ganin kin fita daban ko cikin kawayenki da sauran hadaddun 'yan barikin da kuke tare. Menene na yawaita kallon wanda a kyau babu abunda zai gwada maki?"
Zuciyarta ta kwab'eta,wannan yasa ta gyara zamanta ta maida dubanta ga gabanta. Saidai kamar jan idanunta akeyi,sai gashi suna komawa ta gefe gefe suna duban Ustaz Haris. Ganin ya taho yasa ta daure ta sunkuyar da kanta har ya bud'e motar ya zauna. Sai anan ya dubeta....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(22)
"Zan mik'a ki tasha. Idan yaso saiki hau mota ya k'arasa dake. Nima naje ga abunda ya kawoni."
Bai saurari cewarta ba yaja motarsa ya soma tafiya.
"Nagode da taimakonka gareni,fatana Allah Yasa zumuncinmu ya..."
Kallon daya watso mata ne hanata k'arasawa. Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta murmusa
"Wai har yanzu ba'a bar fushi dani ba? Ya dace kayimin uzuri,tunda kaji nace maka nayi na damar ayyukan da nake aikatawa wanda daman tilastani akayi,toh iyakar gaskiyata na fad'a maka. Ban iya rantse rantse ba,nafiso mutum ya yarda dani. Banga wanda zan yiwa karya ba Haris, ba halina bane."
Ta kauda kanta gefe tana wani d'an tunani,shi kuwa nanata maganarta yakeyi. Tilasta ta akayi tayi karuwancin kamar ya? Haka yayita juya maganar,zuwa yanzu zai so yaji tarihinta saidai bayason yiwa mutum shishshigi a sha'anin rayuwarsa.
"Baka tambayeni inda zanje ba?"
Ta jefo mishi tambayar tana dubansa da wannan shu'uman idanuwan nata. Ya dan kalleta babu laifi ya dan saki fuska kad'an.
"Mahaifiyata zanje gani."
Baisan sadda yayi mata duban mamaki ba,tana murmushi yayinda hawaye suka kwaranyo mata ta gyada mishi kai
"Eh Haris,mahaifiyata zanje gani. A yau bana bukatar komai sai ita. Rabona da ita shekaru uku kenan."
Ya shanye mamakinsa yana maida dubansa ga titi
"A wane gari kenan?"
"KAZAURE."
Ya gangara ya sauka gefen titi,bayan mamaki daya bayyana a saman fuskarsa har da d'an murmushi. Haka kawai yaji dadin kasancewarsu 'yan gari guda. Ita kam kamar a mafarki haka take ganin murmushin da yakeyi gareta. Wannan yasa ta dan lumshe ido ta budesu domin tabbatarwar,saidai har zuwa lokacin basu gushe ba.
"Menene ya baka mamaki na kasancewata 'yar Kazaure?"
Yabar kallonta,fuska a sake yace
"Kasancewata d'an Kazaure shiyasa nayi mamaki."
Itama baby ta d'an bude ido cike da mamaki kafin ta langab'ar da kai tana marairaice murya
"Daman garinmu d'aya amma kake kyamatana?"
Yayi tsai yana dubanta,ita kam wayewar har tana neman yi mata yawa. Yanayinta ne a haka ko kuwa dai tsabar kwarewa a bariki ne?
Ya kauda wannan tunanin ta hanyar fad'in
"Ban tsanar dan uwana musulmi saidai na tsani wani hali nasa. Me kikayimin da har zan tsaneki Tasleem? Hakikanin gaskiya gurb'atacciyar rayuwa irin wacce kikeyi ne na tsana,bana kaunar dukkan mabiyanta. Babu wani burgewa a cikinta face tsantsar nadama a karshe wanda wasunku ma alokacin komai ya k'are maku babu damar tuba. Ki godewa Allah da akwai sauran numfashinki,yaci ace kinyiwa kanki fad'a da karatun ta nutsu. Kisa misali idan da ace ya zamto mutuwa ce ta riskeki yayinda kikayi hatsarin nan,wani guzuri zaki tafiyarwa Ubangijinki dashi da kikejin ya isheki kufcewa azabobinSa?"
Ta share hawayen da tun soma maganarsa suke ambaliya,idanunta yana ga kallon titi tace
"Nasani dukkan abunda ka fad'a babu k'arya aciki. Hakika rayuwar dana zab'arwa kaina ba rayuwa ce ta abun tutiya da tak'ama ba. Rayuwa ce tamkar ta dabbobi,inda mutum yake da damar yin kowane kalar sab'o ba tare da tunanin makomarmu ba. Na tafka kuskure a rayuwata Haris,saidai kamar yanda na fad'amaka,tursasani akayi."
Tun soma maganarta idanunsa ke kanta,maganarta ta karshe ta chanja yanayin duban da yake mata zuwa na rashin fahimta.
"Har ila yau,bangane manufarki ba Tasleem. Daman akan tursasa mutum ya sab'awa umarnin UbangijinSa shi kuma ya amince yabi?"
Tayi murmushi mai ciwo,ta jinjina kanta
"Bacin rai da bakin cikin kazafi da akayiwa mutum bada hakkinsa ba,ya sanyani fad'awa wannan yanayin. Abun bakin cikine ace makusantanka sune basu yarda dakai ba,har suke gaskata sharrin makiyanka. Meyasa wannan bazai dameni ba? A halitta irin tawa,na kasance mai saurin fushi da zuciya. Duk da cewar inada saurin sauka kamar yanda wasu suka fad'a,saidai na rasa yanda akayi na kasa barin abunda ya faru ya wuce a rayuwata. Babu wanda na tsana tamkar mahaifina,duk duniya babu wanda yafi bani mamaki kamar d'an uwana da muka fito ciki d'aya dashi."
Ta tsagaita ta dubi Haris wanda shima idanunsa ke kanta cikin rashin sanin inda ta dosa da maganganunta.
"Kada kayi mamaki idan kaji cewar mahaifina sananne ne a fad'in jahar Kano ba b'oyayye ba."
Ai sai ya kasa dauke ido a kanta,yayinda ta cigaba da yi mishi murmushin nan wanda ke k'ona zuciyarta. Haris ya numfasa
"Idan kinga babu damuwa,ko zaki iya bayyanamin labarinki Tasleem?"
Ta d'anyi shiru tamkar bazatace komai ba,can kuma ta karkato jikinta sosai tana mai lankwasar da kafafuwanta a saman kujera. Idanuwanta suna duban na Haris, yayin da fuskarta ta chanja kala zuwa ja. Murmushi ta k'ak'alo ta jefamishi
"Zakaji tarihina,zakaji wacece ni Haris. Na yarda dakai dari bisa dari."
Ta jingina kanta jikin kujera ta tsurawa sitiyari ido kafin ta bud'i bakinta ta soma magana...
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(23)
"Mahaifina Doctor Abba Waziri,d'a a wajen marigayi Wazirin Kano,Alhaji Ma'aruf Waziri.(ahuwan kanawa..lol)."
Haris ya fiddo ido kadan yana dubanta cikin razana,Doctor Abba Waziri? Shi kuwa ya za'ayi ya kasa saninsa? Babban likita kuma kwararre a fannin k'ashi. Dukkan fad'in garin kano harma da yawa daga sauran garuruwa ansan da zamansa. Ko marigayi mahaifinsa,Alhaji Ma'aruf Wazirin kano,baiyi sunan da d'an nasa yayi ba. Wajen taimakon mutane da kiyaye lafiyarsu.
Baby ta cigaba da zancenta bata ko damu da razanar data sauka a saman fuskarsa ba.
"Mahaifiyata kuwa,Hajiya Maryam Abdulmalik,haifaffiyar Kazaure ce. D'iya a wajen babban limamin masallacin juma'a na Kazaure,Malam Abdulmalik Hussein."
Ai sai Haris ya k'ara sarewa,Malam Abdulmalik Hussein,babban aminin kakansa ne na wajen uba. A iyakar saninsa,gidansa ya zamto na mahaddata Al-k'ur'ani. Suna da nutsuwa yaransa hakanan kowannensu suna zaune ne a gabansa. Duk shine ya aurar da yaransa. Kenan Gwaggo Maryama itace mahaifiyar Tasleem? Unbelievable!
Sai lokacin ne ma idanuwansa suka soma hasko masa kamannin Gwaggo maryama a fuskar Tasleem.
Hawaye akan fuskarta
"Wad'annan bayin Allah biyun,sune sukayi silar samuwata a duniya da ikon Allah.
Mahaifana sunyi rayuwa cike da jin dadi a matsayinsu na ma'aurata kafin Allah Ya albarkacesu da samun d'a namiji,Abdullah. Yaya abdullah yana da shekara d'aya a duniya,kakanmu Alhaji Ma'aruf ya rasu aka nad'a Yayan mahaifina,Alhaji Nasir akan karagar mulki.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(25)
Mamma tana nan zaune har na kusan mintuna sai gasu sun fito suna dariya. Abba yayi shirinsa na tafiya asibiti yayinda briefcase dinsa ke a hannun Raliya tana takowa da murmushi dauke saman fuskarta. Mamma duk da haushinta da takeji ta kasa cewa uffan akan wannan al'amari,saidai ta daure fuska. Wai ma duk a banza,Abba baisan tana yi ba. Har ya nufo teburin sai Raliya tayi saurin magana,wai me yake nufi ne? Bazaici wainar da tayi mishi ba? Ga mamakin Mamma sai ya juya ya dubeta ya bata hakuri cewar zaije yaci wainar Raliya kada tayi fushi. Mamma kai kawai ta gyada mishi,ta kasa cewa uffan har suka fice.
A ranar kuma,da daddare tana zaune a falonta,Abba yayi kiran wayarta yana nemanta. Ba musu ta tafi da tsohon ciki,ta nufi sashensa. Turus tayi ganin matasan da basu wuce ashirin da wani abu ba,zaune saman kujera tare dasu Abba da Raliya sai hira akeyi da dariya. Abba ya ankara da shigowarta,ya dubeta kafin yayi mata iznin shigowa. Ta karasa ta zauna a gefensa. Abba ya dubi samarin
"Banji kun gaisheta ba?"
Sai lokacin dukkansu suka hau kwasar gaisuwa,Mamma ta amsa. Bayan ya kira sunanta,ya shaida mata yaran Raliya ne,da Hamza,Nura da kuma Usman. Anan gidan zasu cigaba da rayuwarsu kasancewarsu marayun da ubansu ya rasu. Zai dauki nauyin karatunsu da komai ma na rayuwarsu. Maganar ta daki Mamma,sai lokacin ta k'ara gaskata magana gwaggo sarai. Ta boye mamakinta tayi mishi fatan alheri akan niyyarsa sannan tayi mishi alk'awarin itama zata daukesu tamkar Abdullah d'anta. Bazata bambantasu ba kamar yanda ya nema. Abba yaji dadi,yace su bata girmanta a matsayinta na matarsa. Suma kamar gaske sukayi na'am. Daga haka ta tashi ta koma.
Zamanta da Raliya kuwa zama ne ba yabo ba fallasa,Raliya aikinta bai wuce jaye jayen fad'a ba duk da ba sashe d'aya suke ba. Tsakaninta da Abba ma ya chanja,ya zamana mukullan motar gidan a hannunta suke,acewarsa itace babba don ta girmeta. Mamma batace komai ba ta bisu hakanan.
Babbar matsalar data soma tayarwa Mamma hankali,bai wuce kwananta da yake kaiwa ga Raliya ba. Ya chanja mata kullum cikin daure dauren fuska. Abdullah bashi da damar sakewa da Abba kamar a baya,ya zamana bai fiye janshi da wasa ba.
Cikin wannan yanayin na rashin samun kulawar miji,abunda bai kai ya kawo ba zai hau ta da fad'a marar dalili koda a gaban 'yan aiki ne. Nakuda ya kamata,gatanan ita d'aya a d'aki. Da abun yaci tura ta lalubo wayarta ta kira Abba. Cikin magagin bacci ya amsa,jin cewar tana nakuda ne ya wartsakar dashi domin har lokacin akwai burbushin sonta a ransa. Haka ya taso Raliya na biye dashi."
Baby ta dakata tayi dariyar takaici gami da kwafa
"Ta hana akai uwata asibiti,shegiyar taso ta kasheni Allah Yayi zan fito duniya na zame mata annoba."
Haris dai kallon Baby yakeyi,murmushi kawai yayi jin abunda ta fad'a kafin ta cigaba.....
Sorinku...bana gida ne...sai zuwa dare in sha Allah.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(24)
"Mamma,wato mahaifiyata. Sunan da muke kiranta dashi kenan,tana dauke da cikina ne babu zato Abba ya soma shirye shiryen aure. Sam,Mamma bata tayar da hankalinta ba kasancewarta mace tagari,wacce take da ilimin addini kuma take aiki dashi. Ta bashi goyon baya sosai har kuma a yanda ta labartamin yazo yana jin kunyarta ba kuma ya fasa batun auren nasa ba.
Hankalin Mamma bai tashi ba har saida labari ya risketa ta hanyar kanwar Abba,Gwaggo Sarai akan wacce Abba zai aura ba yarinya bace. Asalima a girme ta girmeshi nesa ba kusa ba sannan tana da manyan 'ya'ya maza har su uku sai kuma mace d'aya dake gidan mijinta. A yanda Gwaggo Sarai ta ji harda yaran Abba yayi na'am zai rike mata su tunda dai marayune mahaifinsu ya rasu gashinan su d'in basu kasance masu kudi ba. Wannan babban taimako ne zaiyi. Tun alokacin ma ya zamana shine komai na karatunsu,domin kuwa sun kusan yin watanni uku suna tare da Abba kafin ya sanarwa Mamma halin da suke ciki. Wannan shine ya d'agawa Mamma hankali saidai ta nunawa Gwaggo Sarai hakan ba damuwa bace tunda a irin girma na gidan Abba da kuma tazara dake tsakanin sasunan guda uku sai mutum yayi abunda zaiyi babu wanda yaga wani tsakaninsu. Sai bayan tafiyar Gwaggo Sarai ne hankalin Mamma ya tashi,ta nemi yin shawara da aminiyarta wacce bani da masaniyar ko har yanzu suna tare,wato Hajiya Aisha,itama 'yar Kazaure ce kamar yanda Mamma ta gayamin. Ta sanar da ita halin da take ciki,Hajiya Aisha ta bata shawara akan ta dage da addu'a domin dai idan ta d'aga hankalinta babu ribar da zata tsinta a ciki. Haka dai Mamma ta nutsu ta zubawa sarautar Allah ido. Lokacin kuwa Abdullah babu inda baya yawonsa ya soma wayo.
Akayi shagalin biki tamkar na wata budurwa da saurayi harda dinnerparty. Koda Mamma ta nunawa Abba rashin alfanu ayin wani party sai ya hau fad'a acewarsa tunda ita Hajiya Raliya haka tafiso toh bazai hanata ba,idan Mamma taga zata amsa gayyatarta toh,idan kuwa bazata je ba nanma matsalarta.
Tun lokacin Mamma ta soma shan jinin jikinta,ace tun kafin ta Raliya ta shigo har ta soma ganin chanji daga Abba?"
Baby ta dakata da tabe baki tana girgiza kai cikin tsana
"Hum,Haris yawancinku maza baku da kunya. Baku kunyar nuna rashin adalci k'arara a bayyane."
Ta numfasa kafin ta d'ora
"Saida Mamma ta toshe kunnuwanta ta kauda kanta. Ga tsohon ciki da take fama dashi ga kuma wannan damuwa na auren da Abba zaiyi data sanya a ranta. Ta gwammace ace Abba ya samu matashiya daidai ita ya aura akan dai ya auro mata babbar mace wacce ta doshi arba'in. Don alokacin Mamma bata wuce talatin ba,gwara ma Abba ya girmeta don zai kai talatin da takwas. Haka Mamma ta rame,ta zamana Abba hankalinsa kacokam ya koma ga Raliya tamkar wanda ya auri budurwa,kai a yanda Mamma ta misaltamin cewa tayi koda budurwar ya aura sai haka.
Bayan Raliya ta tare ne,Abba ya sami Mamma a daki a niyyarsa ta wucewa dakin Raliya. Anan ya tambayeta game da kwana nawa ta bashi,takaici ya sanya tace mishi sati biyu. Ta dauka zai nuna wata alama ta damuwa saidai walwala data k'aru a fuskarsa,yayi mata godiya ya ajiye mata leda ya fice.
A wannan sati biyun kuwa,Mamma sai ta wuni cur bata sanya Abba a idanunta ba duk da tasan yanayin aikin likitanci,wani sa'in da daddare yake fita amma abun yayi mata ciwo. Ko irin ma a kawo maka amarya ku gaisa baiyi ba.
Saida yayi kwana uku kafin ya lekota,anan ne tayi mishi tambayar ko bazai kawo mata matarsa su gaisa bane. Sai cewa yayi,a girme fa Raliya ta girme mata don haka ita ya dace ta taka taje su gaisa. Domin shi kanshi yana bata girma a matsayinta na wacce ta fishi shekaru. Mamma shiru kawai tayi don mamaki,don alokacin idan Abba yana wani furucin saika rantse baida ilimin addini. Ta rasa dalilin juyamata baya da yayi. Abun sai ya kasance tun tana ganinsa da wasa har dai ta daina,don koda girki ya dawo hannun Mamma sai ya chanja mata. Komai tayi na burgewa sai ya gwatsale yace baiyi mishi ba. Batun Raliya kuwa,Mamma bata ganta ba sai a safiyar da take da girki. Tana cikin shiryawa Abba kayan karin kumallo akan tebur,Raliya ta shigo. Mamma ta kalleta a d'an firgice saboda rashin jin sallamar da batayi ba. Kyakkyawan harara ta watsawa Mamma tana yiwa cingam wani d'an iskan tauna.
Raliya gajeriyar mace ce,mai k'iba. Fuskarta sai godiyar Allah,domin kuwa bata daga layin kyawawa da kuma tsaka tsaki. Kallo d'aya zakayi mata kasan an gwabza a duniya. Ta k'araso ta watsawa Mamma duba na raini a karo na biyu,gaban Mamma ya bada sautin dam! Haka kawai taji matar tana bata tsoro,tayi saurin sunkuyar da kanta ba tare da tasan dalilin dayasa take tsoron Raliya ba daga haduwa da ita a farko.
"Mijina na biyo."
Ga mamaki sai ga Mamma ta d'aga yatsa tana nuna mata hanyar d'akin Abba,muryarta na rawa tace
"Yana ciki,ki shiga."
Malalacin murmushi Raliya ta sakar mata sannan ta karasa ciki. Sai fa a lokacin ne Mamma taji tamkar ta jawota ta shak'eta alhalin a farko bata iya tab'uka komai ba....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(26)
"Ta sanya Abba ya fice daga dakin tace mishi babu komai ai ta iya karb'ar haihuwa. Abba ya fita. A haka Raliya ta zauna tana duban Mamma tana faman salati. Bata yi wani yunkurin komai ba,cikin ikon Ubangiji kuma ta haifeni,jin nayi kuka Abba yana shirin fadowa dakin tayi azamar mikewa ta isa ga Mamma. Anan ta tambayeta inda ta ajiye kayan haihuwar,Mamma tayi mata nuni da hannu,nan ta sami reza ta yanke cibiyar domin dai ta iya d'in tsabagen mugunta ce ya hanata taimakawa Mamma koda da sannu ne. Daga haka ta wanke hannunta ta fito ta dubi Abba tace yayi kiran yar aikin mamma. Yaje ya kira kulu,itama tayi mamakin nakudar da Mamma tayi a daren kuma sam bataji ba. Nan ta shiga ta tsaftacemu ta gyara wajen.
Haka washegari mutane sukayita tururuwar zuwa ganina. Ranar suna aka sanyamin Tasleem.
Rayuwa tana tafiya har nayi shekaru biyu a duniya da dadi da rashinsa babu kalar wanda Mammana da yayana Abdullah basu gani. Daidai da 'ya'yan Raliya basu kyaleta ba,sun raina Mamma,rashin kunya babu irin wacce basuyi mata. Wani sa'in idan suka fita yawon darensu basu shigowa gidan sai washegari. Mamma tana lura da komai nasu, har dai rannan ta kasa daurewa a matsayinta na matar gida mai kokari wajen kiyaye dokokin Allah,ta yiwa Abba maganar akan ya dunga sanya ido kan 'ya'yan daya kira amana gareshi. Ta fada mishi yanda suke tafiyar da rayuwarsu wannan ya sanya Abba zuwa sashen Raliya ya tarar dasu yayi musu tambaya game da hakan. Nan suka k'aryata,sukace su kam idan sunyi dare toh basu wuce majalisarsu. Raliya tayita bambamin fad'a har da tashi taje sashen Mamma wai don ba yaranta bane shiyasa takeyi musu sharri da yawon banza. Haka dai tayi ta fada mamma mai hakuri batace komai ba. A karshe ta fice, shima Abba ya bawa Raliya hakuri,ita kuwa ta tubure wai idan har ya kasance mai daukar magana ba tare da bincike ba toh lallai bazasu daidaita dashi ba zata dauki mataki kan hakan. Abba ya lallab'ata kafin ya juya ga Mamma ya hau yi mata fad'a akan tana neman shiga tsakaninsa da matarsa.
Tun daga wannan ranar ne kuma,yaran Raliya suka daina ganin girman Mamma,acewarsu ta sanya musu ido. Sai ta wuce su wuce amma ko gaisheta basuyi.
Shekara biyu ne tsakani da Yaya Abdullah,shekara kuwa na zagayowa,aka sanyashi a makaranta yana da shekaru uku a duniya. Duk da alokacin yayana baida wani girma saidai Allah Ya bashi baiwa ta hankali ga wayo. Yakan zauna ya fashe da kuka idan yaga Mamma ta zauna tana yi,hakan ne ya janyo tabar yin kuka a gabansa saidai ta kulle kanta a d'aki idan abun yayi mata yawa tasha kukanta ta share hawayenta. Ita kadai tasan wuyar da Abba ya gasa mata kafin na girma nayi hankalin sanin abunda ke wakana.
Duk fa wani arziki da mace zata rayu cikinsa idan har mijinta bai bata kulawar daya sabar mata dashi ko kuma ma ace baya bata gaba d'aya,toh fa bata da wani jin dadi a rayuwa idan har tasan ciwon kanta. Menene amfanin rayuwa namiji yana wulakantaka alhalin karkashinsa kake?
Ko Hajiya Aisha bata da masaniyar halin da Mamma ke ciki don macece mai zurfin ciki,ni kaina sai bayan dana ziyarceta bayan mutuwar aurenta nakejin wannan d'an labarin daban sani ba a bakinta duk da a rufe ta bani ba komai take bud'emin ba.
Raliya bata rufa shekaru biyu ba a gidan,Allah Ya azurtata da haihuwa 'yan biyu,mace da namiji. Kar kaso kaga dukiyar da aka kashe,Abba kuwa sai kace ba'a tab'a yi mishi haihuwa ba. Haka ran suna sai gidan Waziri akaje akayi taro. Nan ma anyi shagali,Mamma ko a kanta saidai fa tayi mamaki kwarai na yanda wasu cikin yan uwan Abba suka bar shiga sha'aninta saima suyi zuwa biyu gidan Abba amma saidai ya samu labarin ko daga yar aikinta kulu na ta ga fitarsu ko sunce a gaisheta. Aka sanyawa yara suna,Hamid da Hamida.
Rayuwa ta cigaba da tafiya a haka,'yan biyu suna da shekara daya ta kara haihuwar mace aka sanya mata Hindatu. Mamma kuwa tun daga kaina sai cikin ikon Allah haihuwarta ya tsaya abun yana damunta saidai hakanan ta barwa Allah.
Yan biyu suna da shekaru shida a duniya,hakanan suna aji daya a primary,yayinda Hindatu ke a Nursery 2. Yaya Abdullah kuwa lokacin yana (primary 6) ne,akayi auren Hamza,ni kuwa lokacin shekaruna takwas a duniya ina aji na uku a firamare. Ranar da Yaya hamza ya tare a gidan aurensa,har 'yar walima nayi da k'awayena a ajinmu bayan mun fito break saboda tsabar murna. Na wahala sosai a zaman Yaya hamza a gidan nan duk da cewar banda wani wayo amma alkawari ne duk sadda muka hadu sai ya murdemin kunnena. Gashi sam bashi da fara'a,akwai sadda ya aikeni nak'i zuwa domin mamma ta hanani shiga b'angarensu shi kuwa yace naje na dauko masa canvas dinsa,ba tsoro nace mishi ban zuwa Mamma ta hanani shiga dakinsu. Ranar saida na gwammace kid'a da karatu. Haka ya kamani ya zaro belt ya jibga tamkar ya samu wata babbar mace. Saboda azaba ko tashi ban iya yi daga wajen ba saida Maigadi ya daukeni cak ya kaiwa Mamma. A can ma mamma saida ta bubbuge bakin nawa sakamakon Allah Ya isan da nayita jero mishi. Tun daga ranar ko yaya na yiwa Hamza laifi,kai koda ace banyi bama toh fa sai ya kamani ya mora da duka. A lokacin kuma,Nura da Usman basu k'asar,Abba ya biyamusu sun fita London karatu. Tun ina Nursery,amma har nayi wayo na shiga Primary basu dawo ba. Allah kadai yasan abunda suke shukawa. Koda ace twins sunyimin laifi,nakan kamasu na jibga a hanyar zuwa makarantarmu domin makaranta daya ake kaimu. Haka zan horasu a mota,koda Malam Nasir yayimin magana saidai na zumbura baki nace ya rabu dani tunda baisan abunda sukeyimin ba. Haka kuwa idan muka dawo zasu sanar da uwarsu,har nan gaban Mamma take zuwa koda ina kuryar daki,shiga takeyi ta jawoni ta jibga wataran kuwa Yaya hamza take sanyawa ya kamani ya jibga.
Yaya abdullah ya tsani wannan rashin ji nawa,domin haka Allah Ya yini,bani yarda a taka uwata. A gabansa a mota zan jibgi yan biyu bai isa ya hanani ba don koda ya hana banaji. Sannan baison taba lafiyata tun ma muna yaran,haka zaiyita lallab'ani saboda yasan na fisu gaskiya ni ce sama dasu basu bani girma. Allah Ya yini mace mai son girma tun ma kafin na zama wata cikakkiyar budurwa.
Tun ina da kankanin shekarun nan na soma tsanar Abba ganin yanda yake budewa Mamma wuta ba tare da tayi mishi wani kwakkwaran laifi ba.
Yasha cewa wai yaranta basu da tarbiyya ta k'ara gyara tarbiyyarmu tunda har a matsayina na babba bana tausayin kannena nakan kamasu na duka. Mamma taji ciwon furucin Abba saidai kawai ta bashi hakuri akan bazai kara faruwa ba.......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(27)
Auren da Hamza yayi shine ya kawomin kwanciyar hankali kad'an a gidan. Domin duk sadda yazo idan har zamu had'u ban tsira ba.
A wannan lokacin ne Abba da Raliya suka tashi tafiya Saudiya domin aikin umrah aka shirya tafiya harda yaranta. A lokacin ne nayita kuka ina korafin Abba bai taba zuwa dani ba. Nan ta Mamma ta hau yimin fad'a na rufe bakina,domin ko yayana abdullah bai taba ketarawa zuwa Saudia ba ballantana kuma akai ga ni. Haka nayita fushi,a karshe naje batare da sanin Mamma ba na iske Abba a falonsa shi kadai. Rok'onsa na shiga yi akan a tafi dani saidai hakuri daya bani kan cewar nima zanje wataran. Duk da kankancin shekaruna nayi bakin ciki kan haka. Ga twins masu aikin yi mini gwalo. Babu yanda na iya haka suka fice akan idanunmu.
Saida sukayi sati biyu sannan sukayo waya zasu dawo. Mamma bata damu ba ta shirya abinci ta jera akan dinningtable na sashen Abba bayan an gyara komai na sashensa. Na kalli jerun kulolin da aka ajiye naja tsaki cike da bakin cikin wannan rashin damuwa da Mamma batayi akan irin cin kashin da kuma bambanci da ake nuna mata. Dabara ta fadomin,a guje na koma sashenmu,jakar Yaya abdullah na bude na fiddo office pins guda hud'u kafin na koma a guje sashen Abba. Mamma na kwalamin kira tana tambayar inda na nufa saidai ban ko saurareta ba. Haka nace na samu kujerun da Raliya da yaranta suka mayar kamar na gado, na caccaka kafin na kwashe da dariya. Ina hanyata ta fita dakin mukaci karo da Abdullah. Harara ya watsamin kafin ya tambayeni abunda nayi da officepins dinsa,a zatona bai ganni ba saidai fa yana daga falo alokacin,ganin na fito daga dakinsa yasa shi shiga kuma ya taras na zubda wasu a k'asa. Na nuna mishi banyi komai ba yace karya nakeyi,wannan yasa na fashe da kukan karya sanin da nayi baison ganin hawayena.
Nan fa ya hau rarrashina ya ja hannuna muka koma dakinsa ya bani alawa. A zuciyata banda Allah Allah da nakeyi na dawowarsu bana komai. Ai fa wajen magrib sai gasu sun shigo. Nan yan uwan Raliya da sukazo tararsu suka kacame da ihu da murna cikinsu kuwa harda hamza da matarsa Zakkiyya. Sai wajen bayan isha'i kowa ya watse. Yan biyu da kuma Hindu sun kara murjewa abinsu,da ace sun fini kyau dana sha haushi alokacin don har kalloni sukeyi suna gwalo. Na tabbatar sai sun dunga mamakin yanda nake murmushi ga wani ladabi dana soma yiwa Raliya. Ni ce harda zuwa sashenta na durkusa ina yi mata sannu da zuwa. Ita kanta tayi mamaki,saidai ta amsa tana dariyar mugunta. Nima ficewata nayi da dariyar ta mugunta.
Misalin tara na dare akayi zaman cin abinci,saida na tabbatar da kujerun da ban sanya alluran nan ba,ba nan mamma da abdullah suka zauna ba,haka nan Abba baya chanja wajen zama,waje daya ne kadai nashi. Nima naja na zauna don nafi kowa zumudin azo aci. Abba ya dubeni
"Tasleem tashi maza kije ki kirawo Maman.."
Bai karasa ba sai gasunan sun iso,Raliya sai shan kamshi takeyi ala dole an zama Hajiya. Abunda yafimin dadi lokacin bai wuce na itace ta soma zama ba,sai ta sanya k'ara ta mike tsaye tana sosa mazaunanta. Abba da Mamma suna cikin tambayarta ko lafiya,suma yan biyu suka zauna har da Hindu. Ai kuwa Hindu ta canyara ihun kuka,yan biyu ma haka. Raliya ta fusata ta hau duba kujerun,ai kuwa nan ta fiddo alluran,ta ajiyesu kan teburin. Dukkaninmu muka kalla,ciki harda ni,bansan ya akayi ba sai ji nayi na saki dariya. Abba ya buga tebur a fusace
"Waye da wannan aikin? Ke kuma yar iskar yarinya shine kike dariya?!"
Mamma a sanyaye tace
"Wallahi bansani ba doctor,Tasleem kodai kece?"
Ta jefomin tambaya,Yaya abdullah kawai hararata yakeyi,
"Bani bace nima.."
"Kinci kaza kazanki! Munafuncin da uwarki ta koyamaki kenan na ki raina matata ko? Toh yau zaki gane shayi ruwa ne! Amma kuwa Maryam kin bani mamaki,sai kace wata jahila har kike tiwa yaranki tarbiyya b'atacciya! Me kikeso ki koyarwa yarana ne?!"
Bansan lokacin dana mike ba
"Abba ba laifin Mamma bane! Ka daina yi mata fad'a."
Mari naji,nan kuma Raliya ta rufeni da duka,Abba cewa yakeyi
"Kinga irin tarbiyyar ko? Wallahi kedai Maryam kin cuceni."
Mamma mikewa tayi a fusace tabar falon na tabbata haushina taji,Yaya abdullah ma fita yayi. Raliya ta dauki allurar nan tayi ta tsikaramin ina ihun kuka. Saida ta gaji da jibgata sannan ta sakeni,Abba baice komai ba. Haka na fice ina kuka. Saidai kuwa ina shiga falon Mamma na tarar da ita zaune tana kuka wannan ne silar shanye nawa kukan. Na karasa na durkusa a gefe,
"Ya zanyi dake Tasleem? A shekarunki da ko tara baki cika ba kinsan kiyi wannan muguntar me zaki zama a yayinda girma ya tasa ki? Ashe haka zaki cigaba da janyomin magana da cin mutunci?"
Gaba daya hankalina ya tashi,mukayita bawa Mamma hakuri,anan ta gargadeni da kada na kuma. Saida mukayi yini cur Yaya Abdullah bayamin magana don tsabar bakin ciki,hakanan a karshe ya sauko.
Na sanya a raina sai nasa an jibgi twins a makaranta. Na fidda homeworks dinsu a jaka na cusa a nawa jakar dayake antinsu muguwa ce. Ai kuwa a ranar saida ta zanesu don har muka baro makaranta suna kuka da Allah Ya isa. Banda kyakyata dariya dana dunga yi a motar bance uffan ba. Saida mukazo gida na fiddo na basu abinsu. Ai kuwa kai tsaye wajen Mamma sukaje suka gayamata. Mamma bata taba dukana ba sai a ranar,Kulu ce ta kwaceni daga hannunta.
Bayan dana cika shekaru goma sha biyu a duniya.............
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(29)
Ina nan zaune tare da Gwaggo Hajara naji sallamar Yaya abdullah. Harara ya soma makomin kafin kuma ya kama kunnena ya murd'a. Tunda nake da yayana bai taba yimin abunda naji zafi ba sai yau. Ihu nakeyi,wanda hakan ya shigo da gwaggo Hajara dake dakinta. Ta dakamishi tsawa kafin ya hankad'ani nayi baya ina kuka.
"Menene haka Abdullah? Metayi maka?"
Yana huci yace
"Duk wata matsala da mamma ke shiga,Tasleem tana da kamasho a ciki. Yanzu kin janyo Malam yayi fushi yace ta zauna har sai ya nemi Abbanmu yaji abunda ke faruwa anyi zaman sulhu. Ga mamma na kuka,nikam ban taba ganin yarinya irinki ba. Duk da irin kwab'ar.."
"Kai dakata,menene ya faru da Adda Maryam din?"
Gwaggo Hajara tayi tambayar da batasani ba. Abdullah baice komai ba ya fice. Sai ni na labarta mata komai ina kuka. Na kara da cewa indai Mamma bazata koma ba toh nima babu inda zanje anan wajenta zan cigaba da rayuwata
Gwaggo Hajara dai batace mini komai ba sai jinjina halin zurfin ciki irin na Mamma takeyi. Ba don ma dai so GAMON JINI bane,manyan mutane nawa ne a kauyen nan da suka nemi auren Maryama basu samu ba,Allah Yayi sai tayi zaman birnin Kano.
Muna ganin abun da wasa sai gashi kuwa hutunmu yana k'arewa na sati daya da zamuyi a Kazaure. Direbanmu yazo,nan Malam yace babu inda Mamma zataje sai Abba ya tako yazo anyi magana. Ko a jikina,don da a sona ne nima bazan koma va saida Mamma ta budemin wuta daman cike take da haushin na tona sirrinta da take rike dashi. "
Baby ta numfasa ta dubi kwayar idanun Haris
"Ban taba ganin mace mai matukar son mijinta ba kamar Mamma. Duk da wannan wahalar da take sha wajen Abba bai sanya ta tsaneshi ba. Kullum cikin fatan su dawo daidai takeyi."
"Haka muka koma muka barta,Abba kuwa har mukayi kwana uku baisan ba tare da Mamma muka dawo ba. Kwananmu uku da dawowa kuma yabar garin zuwa Minna don yin wani aiki daya shafi likitanci. Wannan abu ya konamana rai. Kullum sai munyi waya da Mamma. Har na soma damuwa,nayi danasanin zamanta a gida. Kulu ita zatayi ta rarrashina da ban baki. Ita ta zame mana madadin Mamma. Ita ke mana girki da komai na gyare gyare. Dattijuwa ce sosai da zatakai shekaru arba'in. Yaya abdullah yafini kewar Mamma,saboda tsananin shakuwar da yayi da ita. Don kuwa Mamma alokacin data haifi Abdullah ta dauki son duniya ta doramishi musamman ma da taga ta shafe shekaru uku bata haihu ba saita dauka shi kadai ne rabonta. Sau da yawa sai su kashe su binne ina can ina harkata bansan sunayi ba. Wataran ma saidai ina gefe ina assignment na jiyo dariyarsu.
Ranar wata asabar ina zaune cikin garden dinmu ina game da wayata da Mamma ta siyamin. Allah Ya yini mace mai son game a rayuwa hakanan ban fiyeson kaya masu nauyi ba gaskiya. Lokacinma sanye nake da riga da wando marasa nauyi 'yan kanti. Shekaruna sha uku alokacin,kaga kenan ban zama wata cikakkiyar budurwa ta azo a gani ba. Hankalina gaba daya ya raja'a akan wayata,banyi zato ba naji hannu yana shafani. A firgice na wurgar da wayar ina mikewa zaune daga kwanciyar da nayi akan lilon. Tsananin tsoro da mamaki da kuma rawar jikin da nakeyi yasa na kasa cewa komai. Ba kowa bane illa Usman. Kallo daya ya tabbatarmin a bugensa yake. Yana dariya irin ta maye yace
"Hey you girl,mene kike ja da baya? Ke kanwa kike gareni menene ciki?"
Ya fada yana k'ara nufoni,na suri wayata na arce a guje. Ina zuwa falo nayi arba da yaya abdullah wanda ke shirin fita hannunsa rike da ruwan swan. Na rukunkumeshi ina rawar jiki.
Ya dagoni a tsorace yana fiddo ido
"Ke! Menene haka?"
Na hadiyi miyau ban iya cewa komai ba. Ya dakamin tsawa
"Bakyajina?! Me akayi maki?"
Na tsorata da yanayinsa duk da kankantar shekarun yaya abdullah,wato sha shida. Babba ne a kaina. Ga mamakina sai na kasa fada mishi na girgiza kai
"Kadangare ya biyoni."
Tsaki yaja kafin ya tureni yana fadin
"Banza kawai."
Ya ficewarsa. Ranar haka na yini sukuku,bansan usman cikakken dan iska bane sai ranar. Duk wani kuzari bani dashi,abunda nakeji a bakin kawayena suke cewa iskancine sai ma'aurata keyi yau gashi a kaina. Haka dai na dunga kiyayewa ban kara bari munyi arba da usman ba balle Nura.
Kwanan Abba uku muka ganshi ya dawo. Washegari da safe ya fice bamusan inda ya nufa ba.
Cikin ikon Allah washegarin ranar da muka ganshi yayi fitar safe,sai ga Mamma ta dawo da Gwaggo Hajara da tayo mata rakiya. Ihun murna muka hau yi da tsalle. Mamma ita kanta farin cikin ganinmu takeyi.
Babu laifi Abba ya chanja don har girki Mamma tana karb'a. Wannan ya dagawa Raliya hankali sosai,ashe sanyin da tayi mana a baya ganin Abba yabar shiga harkarmu ne. Abba yanzu da taga har girki ya bawa Mamma sai hankalinta ya tashi. Nan kuma ta dawo da masifarta. Sai ta kintaci Mamma ta shirya fita da mota, zata hana mukulli tace motocin gidan babu mai,hakanan Mamma ke hakura ta koma don sau daya ta taba zuciya ta hau mashin saboda alokacin ba'asan da adaidaita ba, Abba ya ganta. Ranar saura kiris ya saketa Allah Ya tak'aita.
*******
Bayan shekara biyar,inada shekaru sha bakwai a duniya. Na zama cikakkiyar budurwa kuma alhamdulillah sai Allah Ya bani wani irin farin jini. Maza da mata a makarantarmu suna kaunata. A gida kuwa,har doka Mamma ta sanyamin akan babu ruwana da shiga sashen matan Nura da Usman,don kuwa anan suka tare kowannensu da matarsa su dinma matan irin gogaggun nan ne kamarsu. Hakanan ta sanyamin dokar fita da hijabi ko kuma sanya abayoyi tunda ta kula mayyar kananun kaya ce ni, duka duka manyan kayana irinsu atamfa da leshi yawanci sai anko ko kuma na dinka don sha'awa na ajiye. Yaya abdullah baya garin gaba daya, a can k'asar waje yake karatunsa,shekararsa uku acan ya zamana baifi mishi sauran shekara daya da rabi ba ya takarkare karatunsa fannin bussiness. Twins suma sun girma,fad'a tsakanina da Hamida na cacar baki wataran ma har da duka babu abunda aka fasa. Dama dama Hindu ce bana tunanin zata dauki d'abi'un uwarta duk ta fisu hakuri sannan ta kasance marar hayaniya. A makaranta ina ganin sharholiyar da Hamida keyi dukkan abunda ya hada na raye raye da kula kulan maza ba wanda bata cusa kanta ciki. Hamid ne dai ya wuce boarding school wannan ne bazance ga halinshi ba."
Baby ta gyara zama tana yamutsa fuska saboda gajiyar da hannunta ya soma yi
"Sorry."
Haris ya furta cike da kulawa,abunda bai taba yi bane. Hakan ya sanyata murmusawa shima ya mayarda martani yana mai basarwa ta hanyar shafa sumarsa.
Ta cije lebbanta na kasa mai nuni da abunda zata fada akwai ciwo(lol)
"A wannan lokacin ne,Allah Ya kawo karshen zaman Mamma da Abba,Yaya abdullah yana can wata duniya baisan abunda ke wakana ba...."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(28)
Alokacin ina jss1,yayana ss1. Twins kuwa suna primary 4,Hindu kuma 3. Na soma hankali da fahimtar abubuwa,a fannin islamiyya ma tuni Yaya abdullah yayi haddar Al-kur'ani,sai hadisai da sauran litattafai da akeyi mishi. Nikam sauka nakeyi don ko haddar ban soma ba alokacin. Twins ne abinsu sai a hankali,don uwar tasu cikin yawon biki da suna da gaisuwar mutuwa take. Koyaushe bata fiye zama gida ba duk fitarta da yaranta take tafiya(note! Ban taba rayuwar kowa ba!). Wannan ya janyo wala wala a karatunsu na addini,malaman har korafi sukeyi don har Abba sun samu sunyi magana dashi ya nuna za'a kiyaye saidai fa bata canza zani ba.
Wataranar juma'a da yamma na dawo daga gidan Waziri inda nakai ziyara ga aminiyata Juwairiyya,misalin karfe biyar da mintuna ne,direba ya faka. Na fito ina duban wasu matasa biyu tare da Hamza anan kusa da motar Hamza suna hira da kyakyata dariya. D'aya gajere ne,bak'i saidai kalar fatar ta haskaku tamkar dai na yan gidan hutu. Bashi da wani kyau na azo a gani yayinda d'ayan kuwa ya kasance dogo yana da d'an haske. Sannan yayi kama matuka da Raliya. Bazasu wuce talatin da wani abu ba,kansu wani dan iskan aski ne na yan duniya. Gashi duk sun matse cikin kananun kaya masu wanduna iyaka gwuiwa. Na dauke kaina kamar ban gansu ba zan shige gida. Tsawar da Hamza ya dakamin ce ta rud'a tunanina,na dubeshi. Jajayen idanunsa ya shiga zaremin,yace naje. Ba musu ta isa jiki yana rawa.
"Don ubanki baki iya gaisar da mutane ba? Ko bakiga Nura da Usman bane? Kina daukarsu bare ne? Toh don ubanki sun fiki matsayi a gidan nan."
Jin abunda yace na zumburo baki,a ganina rainin hankali ne ace wani can ya fika alhalin gidan ubanka ne. Naji an kaimin hauri da k'afa a bakin. Nura ne,gajeran ciki. Ya zaromin ido
"Barta Yaya hamza,ashe har wannan lokacin wannan yar iskar yarinyar bata nutsu ba. Tun tana 'yar ficikarta take tsula tsiya a gidan nan. Toh don ubanki tunda muka dawo garin nan keda gyatumar taki zaku magantu. Tashi kibar nan!"
Ya dakamin tsawa,ai da gudu gudu nayi ciki cikin ihun kuka. A falo na zube inata bori,Kulu da Mamma suka fito suna tambayar ko lafiya? Yaya abdullah kuwa bai nan yana tare da abokansa na unguwa suna ball. Na shaida musu abunda ya faru,Mamma taja tsaki
"Allah Ya kyauta."
Daga haka tayi gaba bata ko damu da wankemin jinin dake d'iga daga bakina ba. Kulu ta kamani mukayi bandakina ta wankemin bakin tsaf sannan ta sanyani na chanja kayan kasancewar sun b'aci da jini.
Result din Nura da Usman ba wani kyau sukayi ba,tun dawowarsu ma banda yawo da suka sanya a gaba basu da wani aiki. Ga yan mata da suke yiwa b'arin naira. Bayan bautar kasarsu Raliya ta sanya Abba ya nema musu aikin yi saidai babu wanda akayi dacen samarwa. A karshe tace ya basu jari. Nan ya basu kudade da yawa don suyi sana'a koda kasuwanci ne. Saidai ba wanda ya yunk'ura,karshe ma mota suka saya kowanne da tasa. Rayuwarsu ta baya sai abunda ya k'aru,neman mata kamar me don hatta da shaye shaye sukan d'an tab'a. Mamma tasha gargad'ina akan kar na kuskura koda wasa na dunga shiga sashensu. Baruwana dasu, naji gargadinta sosai duk da inajin haushinsu. A duniya babu wadanda na tsana bayan Abba sai su. Tsakanin Mamma da Abba kuwa,har ta manta rabon da Abba ya zauna sukayi hirarsu cikin nishadi har ma ya nemi shawararta akan wani aiki nasa, ko kuma ya sanar da ita abunda yake niyyar yi ko kuma yayi. Zuwa lokacin ma Mamma bata damuwa,idan da sabo yaci ace ta saba domin kuwa abun gaba yakeyi. Na takaice maka saida ya zamana Abba ko girkin Mamma bayaci,sam Mamma bata da kwana a gidan. Kiyayyarsa gareta tamkar an k'ara ne. Domin hana kawo abinci sashensa yayi,yace tayi zamanta a nata sashen idan yana da bukata ai yasan inda take amma anan ita ya lura bata da aiki sai korafi akan abunda baikai ya kawo ba. Tun ina zuwa sashen Abba da kaina duk da kwab'ar Mamma har nazo na daina domin ko kallo ban isheshi ba. Zafi ya hadewa Mamma,gashi ita ba suruka ba balle takai k'ara don tun Abba yan karami mahaifiyarsa ta rasu. Shi kadai ne a wajen mahaifiyarsa,a hannun mahaifiyar Alhaji Nasir,uwargida a wajen marigayi Waziri Ma'aruf wato mahaifinsu Abba,ya tashi. Itace komai nasa kafin itama ciwon sugar yayi ajalinta. Mahaifiyar Gwaggo sarai ita kadaice tsohuwar data rage a matan Waziri,sai yaransa su goma sha biyar cif. 'Ya'ya goman duk na uwargidan ne,sai Abba cikon na sha daya sannan ya yan amaryar waziri,uwar Gwaggo sarai,itace mai yara hudu.
Kwarai dukkansu matan sun watsar da Mamma,hatta da Gwaggo Sarai mai kawo mata tsegumin auren da Abba zaiyi a farko. Matar Waziri mai ci a yanzu,Alhaji Nasir,Hajiya Hajara. Itace suke mutunci sosai da Mamma don shekarunta bai wuce na Mamma ba. Itace kuma k'arama ta uku a matansa. Ita ta kasance mahaifiyar Juwairiyya.
Wannan kenan!!!
Mamma ta rame ta rasa meke mata dadi,Abdullah shine mai rarrashinta. Akwai sadda naji yana bata shawarar kodai zataje Kazaure ta sanarwa Malam? Don lokacin bai zama limamin juma'a ba,marigayi Malam Abubakar ne Limamin. Mamma tak'i. Yaya abdullah shine abokin shawararta wasu lokutan yanda ta suka shak'u ko ni da nake mace ba muyi wannan shak'uwar ba.
Rayuwa na tafiya da dadi babu dadi. Saida muka samu hutun watanni uku na makarantar boko,ina shirin shiga jss2 Yaya abdullah kuwa zai shiga Ss2,mukaje Kazaure ziyaran kakannina. Yan uwan mamma babu wanda bai firgita da ganin yanda ta koma ba. Sukayita tambaya tana cewa babu komai. Har Malam ma haka ta fada mishi. A karshe ta sanyamu a d'aki ni da abdullah ta k'ara kwab'armu akan kada mu sake mu gayamusu halin da take ciki. Ai kuwa bayan ta fita ziyarar yar uwarta. Naje na samu Malam,ina kuka na zayyane mishi komai na yanda Mamma ke rayuwa a gidan nan don har yan aikin Raliya sun fita muhimmanci a wajen Abba. Ga rashin kunya da yaran Raliya sukeyi mata,babu mai ganin girmanta musamman ma manyan. Malam ya fusata ainun,yace nabar kukan bari ta dawo. Ai kuwa Mamma tana dawowa nabar gidan da zummar lekawa gidan kanwar Mamma,Gwaggo Nusaiba......
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(30)
"Maganar da nakeyi maka har ila yau,bansan takamaiman silar rabuwar iyayena. Abunda zan iya tunawa shine. Adaidai wannan lokacin da sakin ke daf da faruwa,Mamma ta shiga wani irin yanayi na yawan tunani da kuka. Nasha kamata a daki tana kuka,tambayar duniya nayi mata tak'i sanar dani. Ga Abba ma bai shiga sha'aninta,na fahimci ran girkinta saidai tayi mishi abinci takai ta juyo bata zuwa inda yake. Ta rame gaba daya, zuwa lokacin nayi hankali nasan menene ya kamata hakan yasa ban sanarwa Yaya abdullah ba duk kuwa da cewa muna yawan chatting dashi yayita bani labarin wata budurwarsa da yake fatan aurarta,Hidaya. Itama 'yar Kano ce karatu ya kaita London. Na gaji da ganin halin da Mamma ke ciki wannan yasa na tambayi kulu ko tana da masaniya saidai ta tabbatar min babu abunda Mamma ta gayamata,itama ta tambayeta amma ta nuna mata bakomai.
Wataranar alhamis na dawo daga makaranta ina mai murnar kammala paper dina na jarabawar karshe da mukeyi. Karab mukayi ido hudu da Yaya Usman tsaye a bakin motarsa sanye da kananun kaya tana shirin fita. Naja tsaki ganin yanda yake sakar mini murmushi,a fili nayi magana
"An girma ba'asan an girma ba."
"Tasleem."
Sunana daya kira yasa na tsaya don kuwa bai taba ambaton sunana ba saidai yace "ke."
"Zo nan."
Na nufi inda yake cikin tsabar takaici domin a rayuwa na tsani 'ya'yan Raliya gaba dayansu musamman ma wadannan agololin da suke mana karfin hali a gidan uba. Na isa na tsaya kerere gami da hard'e hannuwana a kirji fuska ba walwala don a yanzu sam bana tsoron ta kwab'e mana dasu. Inajin zan iya karawa da duk shegen da zai hanani taka rawata da tsalle a gidan mahaifina.
"Gani."
Na dauka zanji babu dadi sai ga mamakina cikin maganarsa mai sauri yace
"Inye,au yanzu an daina ganin girmana ko? Ba laifinki bane,kin isa ne don a yanzu kin zama biggurl."
Furucinsa yasa na dubeshi,ya dagamin gira hakora a washe, na tsuke baki gabana yana faduwa nadai daure nace
"Ina sauri ne,nagaji."
"Kada ki damu,nima saurin nakeyi zan fita. Tambayar da zanyi maki daman meyasa bakya shiga sashena? Kodai baki daukeni yayanki ba? Kin daukeni bare?"
Na kauda kaina don a zahiri ban fiyeson kallo ba. Banayi banso kuma a tsawaita yimin,saidai yanda na kula Usman mayen kallo ne. Muddin waje da mata baya saurarawa,yan matan dake gidan Waziri nasha jinsu suna korafin yawan kallonsa da son kulasu da yakeyi acewarsu haushin zuwansa sukeji saidai kuma abokin yayansu ne,Bukhari ba yanda zasuyi.
"Daman ai ba wani zumuncin mukeyi a tsakaninmu ba ballantana har na dunga ziyartar gidajenku. Babu laifi idan mun hadu sai adunga gaisawa."
Yayi mamakin maganata,har yayi dariya. Nikam wani lokacin ma mamaki yake bani,mutum mai zuciya da ashariya shine yake bina har haka?
"Gaskiyane Tasleem,komai ya wuce. Ke dince akwai rashin kunya sadda kina da kuruciya,amma yanzu tunda kin nutsu ai shikenan."
Na d'an tabe baki kafin naja kafata nayi gaba
"Ban sallameki bafa."
Ko kallonsa ban k'arayi ba domin na tsani rainin hankali. Ya tsayar dani da surutan banza. Da sallama na shiga saidai babu kowa a falon,na karasa dakin Mamma,kafin nakai na tsaya cak saboda maganar Mamma da naji cikin kuka.
"Kulu don Allah ki rikemin sirrina,nayi iyakar kokarin ganin na gyara zamantakewata da Abban Abdullah,saidai tamkar tunzurashi nakeyi. Bansan takamaiman abunda nayi mishi ba ya tsaneni. Kada ki sanarwa Tasleem komai dangane da abunda na fadamaki. Ayau zan koma garinmu,na bar maki amanar yarana Kulu. Bada son raina ba na rabu dasu. Haka Allah Ya kaddaro zamana da Abbansu bazaije ko'ina ba. Bari na tafi domin banason Tasleem ta iskeni....."
Shigar da nayi ba a hayyaci bane yasa sukayi turus gaba daya. Mamma ce rike da akwatin kaya sai jakar hannu,sanye cikin hijabi fuskarta tayi jazur ga hawayen da take fitarwa daya yana bin wani. A durkushe kuma Kulu ce ke kuka sosai.
Tsananin tashin hankali yasa naji kafafuwana sun kasa rikeni,kawai sai na zube a k'asa kafin nasa tafukan hannuwana na rufe idanuna ina kuka sosai. Mamma ta karaso ta ja hannuna na fisge naja baya ina kuka
"Ki rabu dani nace! Ba kin riga kin shirya guduwa ki barmu a wannan bak'in gidan ba? Kin shirya barinmu wajen azzalumin uban.."
Ta toshemin bakina da sauri
"Kina da hankali kuwa? Kada ki k'ara zaginsa,kada ki kara zagarmin...."
Na fisge hannunta
"Wa?! Waye naki? Mamma ki farka ya rigaya ya sakeki! Baya kaunarmu tunda bayason mahaifiyarmu. Shekaru nawa yana nunamana kiyayya? Babu wata shakuwa tsakaninmu dashi a matsayinsa na ubanmu,tunda nake da wayona ban taba ganin Abba ya tako zuwa sashenki domin duba lafiyarki daga kowace irin cuta data sameki ba! Mamma wallahi bazaki tafi ki barni ba! Nima bana sonsa bana kaunarsa! I hate me so..."
Marin data sakarmin ya dakatar dani, saidai ban fasa fad'i ba na mike naja baya ina kuka da karfin murya nace
"Saidai ki kasheni Mamma! Amma na tsani Abba! Na tsani Raliya! Har abada bazan taba son makiyin uwata ba kowanene!"
Na fice a guje,kayana na soma hadawa a akwati,kulu ta shigo ta sameni. Duk yanda taso ta hanani amma nak'i hanuwa. Na fito saidai Mamma tuni ta fice. Banyi wata wata ba nima na mara mata baya. Kulu na bina tana kwalamin kira saidai ko waigowa banyi ba.
*****
Ga wanda baisani ba,sai yace tare muka isa Kazaure da Mamma domin shigarta da mintuna nima na shigo. Malam na soma cin karo dashi yayi niyyar tafiya masallaci gabatar da sallar la'asar.
"A'a,matata daman tare kuke?"
Kawai saina sanya kuka,wannan ya fiddo mutan gidan. Ba karamin mamaki nagani akan fuskar Mamma ba,saidai batace komai ba ta juya ta koma ciki. Malam ya rikeni
"Lafiya kuwa? Meke faruwa ne?"
Cikin kuka na sanar dashi sakin da Abba ya yiwa Mamma. Matan suka hau salallami,Malam banda innalillahi wa inna ilaihir raaji'un babu abunda yake maimaitawa. Kafin ya numfasa yace
"Shiga kiyi sallah Tasleem,bari har na dawo daga masallaci."
Daga haka naja akwatina,ban yarda na shiga dakinsu Mamma ba,sai nayi zamana dakin Gwaggo Fatsima,matar kanin Malam, Yunus. A zatona Mamma zata shigo ta rufeni da duka,wanda na riga na kudurta a raina ko kasheni zatayi bazan koma ba saidai ko alamunta banji ba.
Malam sai bayan isha'i ya nemi Mamma. Sun jima suna magana kafin yayi kirana. Nan ya lallabani akan nayi hakuri na koma ga mahaifina na tubure mishi karshe na sanya kuka ina fadin sun tsaneni suma. Jin haka Malam yace Mamma ta barni na zauna. Mamma zatayi magana ya hanata yace na tashi na tafi. Bansan me suka tattauna ba,nidai burina ya cika tunda Mamma bata kara matsamin ba akan batun kome na daga ranar.....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
0 comments:
Post a Comment