"Haka na tattara kayana na hada da muhimman takardun makarantana da kuma hotunanmu da duk dai abunda nasan zai amfaneni ciki kuwa harda Atmcard dina. Mai taxi na samu bayan munyi cinikin inda zai kaini na shiga. Abu na farko da na soma yi shine,rubuta wasika na damk'awa maigadin gidansu Rilwan,nace ya bawa mahaifinsa a karshe nayi mishi sallama na hau taxi,muna cikin tafiya ina kuka,naji maganar mai taxi yana fadin"Kinga Hajiya idan babu damuwa ga wata can da alama itama tashar ta nufa ko zamu dauketa?"
Bance kala ba duk da nasan shatarsa nayi ina da ikon cewa aa saidai tashin hankalin dake gabana yafi gaban na bata lokacina anan. Ya tsaya ko kallon matar banyi ba,illai kuwa itama tashar dikkon ta nufa. Tana zama wani kamshi ya dokarmin hancina,duk da haka dai ban kalleta ba saidai na share hawayena sai numfarfashi nakeyi.
"Sannu ko? Nagode fa."
Tace dani, na dan kalleta,tabbas da ganin shigarta kasan tana hutawa kuma tafi kama da irin masu kud'in nan. Sanye take da wata atamfa yar ubansu tasha kwalliya ko yatsunta ka kalla kaga jerun zobbuna biyu na gwal sun wadatar dakai ka gane ba karamar Hajiya bace. Ita dinma ni take kallo fuskarta dauke da murmushi,wannan yasa na maida mata martani da murmushin da baikai zuci ba kafin na maida dubana ga gefen titi. Ina jinta tana waya kamar dai mota akayi niyyar aikomata don naji tana surfa ashariya tana fadin ita tafi karfin wulakanci,yasan yana. Tsoron matar tasa ya kwana da ita a hotel? Anan na fahimci lallai ba macen arziki bace. Har muka isa waya takeyi tun suna hayaniya har dai akarshe ta hau tuntsira dariya tana fadin babu komai ma zatabi motar kasuwa.
Da isarmu na sauka,zan biya mai taxi ta dakatar dani tace ai nayi mata alfarma don haka kada na damu itama yimin zatayi,ina kallo ta biya. Nayi godiya,ina shirin kinkimar akwatina ta zagayo ta dubeni
"Ina zaki ne?" Ganin da nayi mata na wacce ta fini shekaru yasa na amsa ba don naso ba don ta soma bani haushi ta soma takuramin.
"Kano." Tayi dariya"Nima nan na nufa,tsaya a sama mana mota."
Nidai bance uffan ba,abunda na soma tunani bai wuce ma ina zan nufa ba a Kanon? Waye zai amsheni da cikin shege??
Banyi mamaki sosai ba ganin Hajiyar nan ta dauki shatar karamar mota mai zuwa Kano guda daya. Tace nazo muje,wallahi Haris banji ko d'arr wai na rashin yarda da ita ba. Na sadakar idan ma yar yankar kai ce toh ta kaini a yankani na huta da bakar rayuwar da nake ciki. Koma dai menene alokacin ji nayi muje kawai.
Motar mu ta d'aga daga ni sai Hajiyar nan da direba,lokacin wajejan uku na rana. Daidai lokacin da muka soma tafiya wayata ta dauki kara,shaf na mance ban kasheta ba. Na duba,sunan wanda na gani yasa a fusace na kashe wayar na fiddo sim din na cusa dukansu a jakata. Me kuma rilwan zai min? Ina waigowa karaf muka hada ido da Hajiyar nan.
"Namiji ko?"
Mamaki ya kamani,tayi murmushi tana kashe ido na yan duniya "Ai bakin cikin mace bai wuce akan d'a namiji baiwar Allah. Tun ganina dake a farko na fahimci kina cikin matsanancin damuwa,idanunki kadai zasu tabbatarwa mutum kinci kuka kin koshi. Idan bazaki damu ba,zaki amince dani ko zaki sanar dani matsalarki? Ni kuma zanyi maki taimako daidai gwagwadon iyawata."
Na dubeta sai naji na aminta da ita. Hakanan na zayyane mata komai dangane dani da rayuwata. Ta jajinta min,na kara da cewa
"Babu abunda na tsana a yanzu kamar cikin nan Hajiya! Ki taimakamin don Allah ki kaini inda kikasan za'a ciremin shi."
Tayi murmushi ta rungumo kafadata
"Kinzo wajen share hawayenki BABY."
*****
Baby ta dubi Haris "Wannan itace Hajiya Hannatu Bariki wato MOMY. Itace ta sanyamin suna Baby wanda har ila yau ya bini, don wasu da yawa basu sanni da Tasleem. A gidanta na soma sauka inda kuma washegari ta kaini aka zubarmin da cikin jikina. Itace ta gogar dani a harkar bariki. Ita ta kasance tana nunamin hanyar da acewarta shi kadai ne jin dadin rayuwa babu wanda zai takura maka babu mai matsa maka. Tun ina tsoro har dai na bada kai bori ya hau,abun nufi dai ta shiga hadani da manyan alhazai wadanda cikin sa'a kowannensu rububina yakeyi. Komai Momi ita ta koyamin,Momi itace shugabarmu,yan mata da yawa da zauwarawa sanadinta suka rike kansu suka zama tantiran 'YAN BARIKI. Sai ya zamana nabar yayin dukkan manyan kayana,koda dai ba sosai daman nake sakasu ba nafi mu'amala da kananun. Saidai fa a lokacin ya k'aru sosai,Momi haka ta bada oda aka kawomin su kala kala daga Dubai. Haka nan babu kudina da ake tabawa,haka kawai jininmu ya hadu sosai da Momi tana ji dani kwarai da gaske. Duk da wasu kayan maye da Momi ke sha da sauran yan kungiya,bana shan komai sai taba,shima sai idan ina cikin matsanancin damuwa ko nishadi ban fiya sha sosai ba gaskiya."
Baby ta murmusa adaidai nan,da alama kuma abunda zata fadi,fari ne fat a wajenta.
"Daidai wannan lokacin ne,na shirya daukar fansa a wajen Usman. Ga Rilwan kuwa,Abbansa na zayyanewa komai a wasikar nan kuma inada tabbacin Abbansa mutum ne nagari da yasan ya kamata,kamar dai yadda nasan Rilwan da fadar gaskiya komai dacinta. Nasan bazai musa cewar shine yayimin wannan aika aikar ba. A yanda kuwa akayi na dauki fansar da taimakon Momi shine......."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(42)
Prince,dattijo ne mai kimanin shekaru arba'in,sunansa na gaskiya Alhaji Shitu Ibrahim. Shine na kusa kusa ga Momi,hakanan wani suka ne a gwamnati. Yana da yaransa ko kuma ince maka 'yan dabansa da yake sanyasu kashe dukkan wani rai dake kawomishi matsala a rayuwa. Daidai lokacin da muka sameshi da bukatarmu yayi dariya yace"Wannan abu ne mai sauki ai,yarana da suke kashe rai wannan karamin aiki ne a wajensu. Saidai kuma nima inaso a bani abunda na jima ina marari amma an tsaya yimin yanga." Ya karashe dadm dariyar 'yan duniya yana kallona. Murmushi nayi don a duniya ji nake alokacin ko me Prince ke so zan bashi saboda ya gama yimin komai da na bukata. Ba shiri na harhada kayana muka wuce dashi. Acan ya had'ani da babban yaronsa nayi mishi bayanin abunda nakeso ayi. Farko dai nayi mishi kwatancen inda babban shagon Usman yake domin alokacin yaci gaba har ma ya fito daga kwari ya bude babban shagon kaya wadanda yake sarowa daga Dubai. Nayi umarnin a k'onashi kafin nayi musu iznin nakastamin rayuwarshi ta hanyar yanke mishi dukkanin kafufuwansa."
Baby ta dakata a yayin data tuntsire da dariya cike da jin wani irin nishad'i,Haris kuwa mamaki kwarai yakeyi ashe daman zata iya aikata mugunta har haka? Tunaninsa ya tsaya cak sa'ilin da dariyar dake kan fuskarta ta dauke ta koma zubar hawaye. Kanta ta girgiza cike da takaici
"Saidai Haris, nasan ban dauki fansa ba. Domin babu yanda za'ayi na dawo da budurcina kuma mutuncina. Ya rigaya ya cuceni ya cuci rayuwata tun farko."
Baby ta fada kafin ta kara duban Haris
"Yanda kuwa na lissafa musu babu ko tangard'a hakan suka aikatamin. Ita kuwa Raliya itama saida suka tabbatar da fitowarta ita d'aya tana driving wataran suka tareta suka daure baki da idanunta. Ba wani abu sukayi mata mai yawa ba illah dai jibgarta dana sanya sukayi,yayinda a karshe dayansu ya kusanceta. Kafin su yi mota biyu da daddare daya yana jan nata,sauran kuma duk suna motar baya, wajejan sha biyun dare kenan. Daidai kofar gidan ya dire ta kafin ya koma motarsu suyi gaba ban kara bi takansu ba. Koda suka sanarmin sun cikamin aikina sai naji kuma na fashe da kuka kafin na saki dariya. Momy taso shima Abba a dan tab'ashi saidai naji bazan iya ba."
Baby ta dubi haris cikin hawaye tace
"Ban dauki fansa ba Haris,ban dauka ba. Saidai bana nadama ko kadan akan abunda nasa aka aikata musu a rayuwa. Haris tafiyata taci gaba kafin na samu na sayi gida wanda anan nake da zama yanzu. A hanya ne kuma na tab'a buge Manal da kullin kayanta,bayan na kaita asibiti naji likitan yana sanarmin wai tayi b'arin juna biyu. Koda ta farfado take bani labarin cewa marainiya ce,marikinta yayi mata ciki. Kaji silar haduwarmu da Manal. Dalal da Hibba a club muka hadu dasu, anan kuma kawancennu ya d'ore kafin daga baya nace subar gidan hayar da suke zaune su dawo nawa. Ni na hadasu da Momy,kaji yanda alakarmu tayi tafiya. Wannan shine labarina Haris."
Haris ya numfasa kafin yace
"Kin tafka kura kurai da yawa a rayuwarki Tasleem,ciki kuwa babban shine fitowa da kikayi kika fada harkar bariki maimakon ki kame kanki da mutuncinki,a'a saima zuciya data kwasheki kika maida kanki karuwar gaske. Kinyi ganganci kin manta da dokokin addininki daya hanemu aikata zina. Kuskurenki na gaba kuma,daukar fansa da kikayi akan wadannan bayin Allah inda kika manta cewar Allah baya kyale wadanda suka zalunci bawanSa,kika manta da kalmar hakuri har kika ji a zuciyarki cewar lallai ke da kanki kin isa sakawa kanki batare da kinyi hakurin ganin Sakayyar Ubangijinki ba. Rayuwar da kikeyi Tasleem,rayuwa ce ta wofi wanda karshensa nadama. Na hakikance ba kwadayin abun duniya ne ya kawoki bariki ba illah kawai kuncin rayuwa. Haba Tasleem,a rayuwa akwai wadanda suka fiki shiga kunci da wahalar rayuwa. Ki godewa Allah ma a gefe kina da iyayenki da yan uwa, wasu fa basu da ko daya,wasu rayuwarsu har su mutu cikin kunci da bakin ciki sukayita amma basu fada karuwanci ba,basu nemi daukar fansa ba illah dai sun kasance masu tawakkali da mik'a zuciyoyinsu ga Allah."
Baby babu alamar jin haushin Haris a fuskarta saima kallo da take binsa dashi tana murmushi kafin daga bisani hawayenta su zubo. Ganin hawayen ya sanyashi tsayawa da maganarsa
"Ina fatan ban b'ata ranki ba Tasleem?"
Ta girgiza kai tana 'yar dariya
"Wallahi baka b'atamin ba Haris. Asalima burgeni kayi,dadi nakeji a kasan zuciyata. Tunda na soma harkar barikanci,babu wanda ya taba yunkurin gayamin gaskiya saikai. Tun farko haduwarmu saida na fahimci kai din daban kake. Ban kara sakankancewa da lamuranka ba saida na hadu dakai a karo na biyu. Tabbas Haris kai mutumin kirki ne wannan ne yasa nayi mamakin yanda ustaz ya iya aminta da mutum irin Kb."
Murmushi Haris yayi ya numfasa ya gyara zama kafin ya dubeta
"Muna iya tafiya gaida Mamma?"
Ta lumshe ido tana murmushi
"Da gudu ma."
Sukayi dariya kafin Haris ya mika mata ruwan roba daya siya zai sha
"Oya,ga wannan sauka ki wanke fuskar nan taki, ki d'anyi kwalliyar nan taki bebinsu."
Harararsa tayi a wasance,kafin ta narkar da fuska
"Au ba taka bace?"
Ya dubeta kafin ya basar da zancen ta hanyar fitowa ya bud'e b'angarenta ya amshi robar ruwan,yana kokarin budewa yace
"Juyo ki wanke fuskarki."
Ba musu ta gyara ta mika hannunta na hagu,yana zuba mata tana wankewa har fuskarnan tayi fayau,Baby ta gasken ta bayyana sannan ya zagayo ya bude boot ya dauko mata handbag dinta ya shigo motar kafin ya dire mata a cinya yana murmushi
"Ayi make up please."
Murmushin tayi kafin yayi addu'a ya daga gilasan ya kunna Ac,ya sanyamusu karatun al-kur'ani don kara nutsar da zuciyar Tasleem daga bisani yaja motar suka dauki hanyar Kazaure. Ita kuwa ta hau fente kyakkyawar fuskarta da kwalliya saidai bamai yawa ba. Bayan ta kammala ta dubeshi
"Baka sanar dani abunda zai kaika garinmu ba?"
Dam! Gaban Haris ya buga. Shaf ya mance da ainahin silar zuwansa Kazaure sai yanzu da Tasleem tayi tambayar. Ashe fa wai matar aure zaije zab'a.
"Kayu shiru??"
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(42)
Ya dan dubeta,ya rigaya ya gama tabbatarwa kansa cewar baby kyakkyawa ce ta gani a fada,tabbas baiga laifi ga KB dake makale mata ba domin kuwa idan zaka biyewa kyawun halitta da surarta,bakasan sadda zaka fada tarkonta ba. Yayi murmushi kafin yace "Garin iyayena ne."
Ta fiddo ido kadan fuskarta ta washe "Haba? Ashe kaima dan garinmu ne? No wonder na ganka da kyau kamar aljani."
Kallonta kawai yayi ya sakar mata murmushin da saida ta jishi har tsakar kanta. Tasan tun haduwarsu ta farko,tana jin wani al'amari bak'o game da Haris,saidai ita kanta tasan Haris yafi karfinta. Me zaiyi da 'YAR BARIKI? Ta maida kanta ta kwantar tana sauraron karatun Al-Kur'ani mai girma. Shi din ma kogin tunanin ya fad'a. Anya bai fada tarkon son 'YAR BARIKI ba? "A'a ban fada ba,just ina girmamata ne a matsayinta na wacce ke bukatar taimako. Ina kuma tausayawa rayuwarta."
Ya fadi a ransa.
*******
Hankalinsa a tashe,nutsuwa tak'i samun mazauni a kwakwalwarsa da jikinsa. Yana zaune sai afkin kiraye kirayen waya yake. Daga ya kira Manal,sai ya koma Dalal kafin a karshe yaji ta bakin Hibba. Momy ma ya kirata sau d'aya saidai ita kanta bata da labarin duniyar da Baby ta shiga. Zuciyarsa tayi bak'i har hasko Baby yakeyi kwance a kirjin wani da namijin. Kishi matsananci wanda har ya janyo sauyawar kalar kwayar idonsa.
Tun tsawon daren jiya take lura da mijin nata, hakanan ko lokacin daya fidda kunya ko shayi yake waya a gabanta duk tana sauraronsa,hankalinta ya tashi jin cewar mace ce ta rikita Kabir har haka. Ta soma sharar kwallah saidai gogan baisan tana yi ba,kwata kwata ma baisan da wanzuwarta ba sai sambatu yakeyi a fili
"Ina kikaje? Wane dan iskan kika samu har kika kashe wayoyinki Babyna?"
Ire iren abunda yake fadi kenan. Maganarta ta katseshi
"Wacece haka prince?"
Ya dubeta,gaba daya baisan da ita ba a falon. Tsaki yaja ya mike ya dauki wayoyinsa zai shiga d'aki
"Yanzu akan wata 'yar iska kake..."
Fisgota da yayi ne a fusace ya sanya sauran maganar makalewa a fatar bakinta. Ya hau jijjigata cikin tsawa yace
"Koda wasa kika kuskura kika k'ara kiran Babyna yar iska wallahi Yasmeen saikin raina kanki."
Ta fisge jikinta tana hawaye itama a fusace tace
"An fad'a d'in! Yar iska! Yar bariki..."
Tass! Ya kwasheta da mari,kafin ya hankadata ta bugi bango ya nunota da yatsa
"Wannan kadan kika gani! Wallahi akan Baby zan iya rabuwa dake Yasmeen! Sannan ki ajiye a ranki! Baby saita shigo gidan nan matsayin matata!"
Ya kwashi wayoyinsa da suka tarwatse a k'asa yayi daki ya buga kofar a fusace. Yasmeen ta tsorata ainun,mikewa tayi ta nufi dakinta. Mayafinta da fos na kudadenta ta dauka,ta sab'i diyarta Nasreen dake bacci tayi waje. Ta rantse yau bazata kwana Abuja ba kuma ma a gidan mutum irin Kb. Maigadi yana tambayarta ko lafiya ta dakamishi tsawa "Budemin kawai!" Yayi mamaki don baisan Hajiyar tasu da haka ba,akwai ta da girmama na gaba da ita komin kankantar matsayinsa. Mace mai hankali da tunani,ga fara'a da hakuri. Ba musu ya bude a hanzarce ta sanya kai ta fita tana zubar hawaye. Yau kam sai KANO......!
****
Karfe uku da mintuna na rana sai gasu a Kazaure. Gaba daya garin ya chanjawa Baby harma ta kasa sanin ta yanda zata soma kwatantawa Haris gidansu. Ga mamakinta taga yana ta shiga wurare bai tsaya ko'ina ba sai kofar gidan Liman. Tabbas gidan kakan nata ma yaso ya sauya mata sakamakon fenti da shukoki da aka k'ara mishi. Ta tsaya cak tana kallon tsohon dake zaune akan tabarma tare da makwaftansa suna hira,saidai suma hankalinsu ya dawo kan motar. Fitowar wata yarinya karama ce ta basu mamaki,tamkar an tsaga kara an karya ita da Baby saboda tsananin kamar da sukayi,tana wani yanga irin ta kananun yara masu iyayi ta isa ga tsoffinan ta zauna saman cinyar tsohon nan. Haris da Baby suka dubi juna,ganin hawaye a fuskar Baby da kuma murmushi yasa ya girgiza mata kai. Ta kwashesu da hannunta
"Haris kayimin abunda har abada bazan mance dakai ba. Ka samu babban gurbi cikin zuciyata. Ina jinka sosai a jinin jikina kana yawo akowane sassa na jikina. Wallahi banajin zan taba mancewa da abunda kayimin. Nagode sosai."
Yaji maganganunta har cikin k'ok'on ransa,ya kasa dauke idanunsa daga kanta. Ya rasa me yakeji game da ita,ji yakeyi tamkar kada su rabu. Inama zasu shekara a haka bayajin zai damu. Murmushin nan nata wanda yake tayar mishi da tsikar jiki ta k'ara yi mishi.
"Fito muje,gaskiya ka bari ka huta saika karasa gida."
Ya girgiza mata kai ya saki lallausan murmushi idanunsa a kanta
"No,ki bari zan shigo anjima kinsan gobe fa zan tafi. Zanzo mu gaisa sai na kaiki ku gaisa da Kakannina."
Ta marairaice fuska,kwalla ta ciko idonta
"Gobe zaka tafi ka barni Haris?"
Maganar ta shigeshi,yana kara jin zuciyarsa na shiga wani yanayi. Kwankwansa gilashin da akayi ne ya maido hankulansu ga wajen,Haris ya sauke gilas kasancewar gilasan daga wajenm akwai duhu. Dan saurayi ne,yana murmushi yace
"Malam tambaya kukeyi ne?"
Haris ya girgiza kai,baby ta sanya dariya
"Baharu." Ta fada kafin ta fito,da gudu gudu ta isa ga Kakanta wanda da alama shi kam ya ganeta. Domin gaba daya ya mike yana farin cikin ganinta sosai,ta rungumeshi kafin kuma su zauna ta saki kukan farin ciki. Zuciyar Haris tayi babu dadi,ba abunda ya tsana sama da kukan nan. Dolensa ya bude motar ya fito suka gaisa da wanda ta kira da Baharu.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(44)
"Tasleem,kukan na menene kuma? Me ya samu hannun naki?"
Ta share fuskarta ganin yanayin Haris shima kamar baiji dadin ganin hawayen nata ba,ta dubi hannun kafin tace
"Buguwa ce nayi Malam,amma yanzu da sauki sosai ma."
Tsohon ya kurawa Haris ido da murmushi wanda haka halittarsa take,da wuya kaga gushewarsa akan fuskarsa.
"Yaro kana yimin yanayi da aminina Hussein."
Furucin Malam yasa Baby zubawa Haris ido kasancewar tasan Baffa Hussein sosai jefi jefi takan lek'a gidansu a baya idan tazo domin har baffa Hussein ya santa yana nuna kauna agareta har takanyi mamakin irin soyayya da shakuwar dake tsakanin wadannan bayin Allah biyu. Haris cikin murmushi yace
"Lallai ma tsohon nan,tabbas idan na koma zan fadawa Baffa ka mance da autan jikansa,Haris."
Mamaki karara ya sauka akan fuskar Baby hade da dariyar nan nata mai burgewa,haris ya daga mata gira yana murmushi. Malam kuwa hakora ya washe ya rungumo kafadar Haris yana dariya sauran tsoffi uku suna tayashi.
"Allahu,daman kaine Harisu? Haka ka girma? Lallai Harisu baku da zumunci,da ace kun yo halin iyayenku da ba haka ba. Ina d'an wajen dan auta?(Alhaji idris)"
"Yana can Abuja da zama. Kayi hakuri dan tsoho ba rashin zumunci bane,ayyuka suke rikemu acan."
Malam ya jinjina kai,baby kam murmushi takeyi,yayinda ta kasa dauke fararen idanunta akan kyakkyawar fuskar Haris wanda samun namijin daya hada komai irinsa a fannin kyau na sura da halayya abune mai matukar wuya a zamanin nan. Ya kallota,tayi azamar mikewa tsaye tana basarwa da cewa
"Bari naga kishiyoyina,don Allah dan tsoho kada ku bari yayana ya gudu tun yanzu,kunga fa ko abinci bamu ci ba."
Haris ya hararota yana murmushi,tayi mishi gwalo kadan. Malam yayi dariya
"Ai babu inda zai tafi yanzu,Baharu shigar da yayan naka dakinku yayi alwala yazo muyi sallah sai yaci abinci ko?"
Suka mike,tuni Baby tayi gaba tana fadin zata turo yaro ya shigar mata da akwatin kayanta.
*****
Tun a hanyarta take ta kiran wayoyin yayan nata amma yana ringing bai dauka ba. Taci kuka har ta koshi,ganin baya kusa yasa tayimishi dogon text inda ta gutsura mishi halin da suke ciki da KB da kuma tahowarta Kano da tayi. Daga karshe ta kashe wayarta gaba daya.
Yasmeen kenan!!
*****
Murna da hira ta karade bayan tsakanin mutanen gidan bayan da Baby tayi wanka da sallah. Tana sanye da doguwar rigar kanti. Alokacin tana zaune tana cin abinci anata hira. Makwafta sai shigowa sukeyi,Gwaggo Hajara ma nan tazo da kwanonta. Kowa yaga bandejin hannun Baby sai ya tanka,tana rufesu da fadin buguwa ce tayi. Wayoyinta kuwa har lokacin a kashe suke ta jonasu a chaji. Sallamar da akayi ta maido hankulansu,Haris ne a gaba sai Yaya musty a baya. Ganin Yaya musty yasa Baby sakin ihu ta mike ta rukunkumeshi suna dariyar farin cikin ganin juna. Gaban Haris ya shiga dukan uku uku,haka kawai ya tsinci kansa da jin haushin wannan rungumar da Baby ta yiwa wani.
"Yaya mustyna,ashe da rabon rai ya k'ara ganin rai tsakaninmu?"
Sai kuma ta soma hawayen farin ciki.
"Yaya mustyna??" Ya maimaita a zuciyarsa,ashe har yanzu Yasmeen bata mance dashi ba?
Har lokacin hannuwansu harde cikin juna,Haris ya kauda kansa ya wucesu zuwa ga mutanen gidan suna gaisawa. Kasancewar gwaggo Hajara ta samu labarin kowanene a wajen Baharu wanda yakai mata tsegumin zuwan Tasleem yasa ta ganar dasu. Nan fa murna ta k'aru,suka shiga tambayarsa mutanen Kano yana amsawa. A karshe yayi musu sallama bayan ya dire musu rafar kudi 'yan dari dari guda biyu ya mike suna fadin ya barshi amma da azama ya nufi waje. Ganin haka tasleem tabar hirar bayan rabuwa da Musty tabi bayansa a da sauri. Ganin yana shirin wuce zaurensu ne yasa tayi azamar riko hannunsa wannan yasa shi juyowa ya watsa mata kallon da yayi kama dana farkon ganinta dashi. Ta saki hannun dayake kanta a waye yake ta nuna kamar bata gane yanayin fuskarsa ba ta hanyar marairaicewa da langabar da kanta
"Yanzu tafiya zakayi shine babu ko sallama?"
Ya dan tabe baki yana mai zura hannunsa cikin aljihun wandon jeans dinsa,ya daga kafada
"Gani nayi kina hira da yan uwanki banson katseki ne."
Murmushi tayi kawai,ta soma fahimtar wani abu kadan akan fuskar Haris, mai yiwuwa yana dauke da ciwon da itama take dauke dashi. Ya katse tunaninta
"Zan wuce."
Ga mamakinsa yaga ta durkusa har k'asa tana dubanshi
"Har na rasa manyan kalmomin da zanyi amfani dasu kuma wajen yin godiya agareka yayana,kayi jihadi babba wajen ceto rayuwata daga halaka. Daga yau na baka matsayi babba gareni. Zuwa yanzu bani da wanda yafimin.."
Ya katseta shima ta hanyar yin durkuson a gabanta,yana kafeta da wannan idanuwan nasa masu kara fama mata ciwon dake ranta. Saidai ita kanta tana raina kanta a gaban Haris,duk wani haduwarta ganinta takeyi tsumma a gabansa. Ita kanta ta riga tasan Babban Goro sai magogin karfe,me namiji irinsa zaiyi da 'YAR BARIKI? Ta kauda kanta daga dubansa ganin bashi da niyyar kauda nasa akanta. Wai daman akwai abunda take ko kuma zata tabajin kunya acikin mutane? Bata taba kawowa ba kuwa ko a kanta,ya katseta a karo na biyu ta hanyar mikewa
"Tashi Tasleem."
Ta mike tsaye,bai kara dubanta ba yace "Kina iya rubutamin lambar wayarki,watakil na leko gobe kafin na wuce."
Har ya soma tafiya sai kuma ya juyo dauke da murmushi saman fuskarsa wanda bata taba ganin irinsa ba a tattarr dashi. "Sannan ki sani,matsayin kanwata kike Tasleem. Bana bukatar ki yawaita godiya gareni. Ki cigaba da godewa Ubangijinki. Hakanan ya dace kiyi istibra'i. Sai Allah Ya kaddara saduwarmu Tasleem."
Ya soma tafiya da baya da baya, hawaye taji sun taho mata yayinda ya juya ya fita da sauri saurinsa. Ta tsaya cak tana binshi da kallo zuwa lokacin hawaye sun sauka saman fuskarta. A gaban idanunta yaja motarsa bai k'ara ko kallon kofar gidan nasu ba.
"Small."
Taji muryar Yaya Musty ya fadi ta bayanta,wannan ya fargar da ita a inda take tsaye.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(45)
Ta dubeshi tana murmushi,yayinda damuwa ta sauka saman fuskarsa shi kuma.
"Kin tsaya anan? Ko bakiso ya tafi bane?"
Abunka da wacce bata iya boye damuwarta ba tace
"Banso ba,ya tafi ya barni da damuwa marar misaltuwa saidai yace watakil kafin ya wuce ya biyomin muyi sallama."
Musty ya k'ura mata ido yana kallon kwayar idanunta. Akwai wani kwantaccen sirri game da Haris a cikinsu.
"Kanwata are you in love?"
Tayi tsai domin batayi mamakin jin wannan tambayar ba,inda takeson Yaya mustin nata kenan,nan da nan ya dago damuwarta ko wace iri ce. Ta basar ta hanyar dariya ta soma tafiya tana fadin
"Yaya mustyna kenan,ina Haris ina mace irina?"
Ya riko hannunta wanda yayi silar tsayuwarta,ya jawota baya kadan yana dubanta da idanunsa da suka bayyana bacin rai da damuwa karara a cikinsu,mamaki ya hana baby magana sai ya rigata da cewa
"Ya kike irin wannan maganar sisna,wa zaik'i mace kamarki? Ko kina da wani aibu ne?"
Ya karashe bayan ya saketa yana murmushi a sanyaye,bata yardarwa kanta hakan yayi niyyar fada ba sakamakon zafin da ya nuna a farko. Batace komai ba banda murmushi da "Uhm" daga haka tayi ciki.
Ya bita da kallo rai a bace,wai daman Tasleem ba sonshi takeyi ba kamar yanda ya jima yana yaudarar kansa? Yaya mustyna! Yaya mustyna! Me hakan ke nufi?!! Tsaki yaja bazai kuma iya komawa cikin gidan ba kawai sai yayi gaba zuwa gidansa rai babu dadi domin ya gama lura Haris ya samu gurbi a zuciyarta.
*****
Mutanen gidan sunyi farin cikin ganinsa sosai. Nan aka shiga hidima dashi,sai abinci ake ajiyewa agabansa. Hankalin Haris ko kusa baya kan yan matan da suka had'e cikin kwalliya sunata shawagi a falon wajen kawo mishi abinci,ya tabbata an riga an basu labarin abunda ya kawoshi. Sai hirarsu sukeyi da kakarsa,Hajja. Koda ya kammala mikewa yayi ya nufi sashen kishiyoyinta suka gaisa kafin ya nufi bangaren kakansa,Malam Hussein.
Nan ma suna hira yake sanar dashi tare sukazo da Tasleem diyar gwaggo maryama 'yar amininsa Liman. Ai sai Malam Hussein ya tashi zaune fuskarsa a sake sosai. "Jikar Abdulmalik ce? Ikon Allah,daman kunsan juna ne acan Kano?"
Haris ya rasa amsar da zai bashi a karshe yace "Eh munsan juna,tare mukayi makaranta saidai banma san 'yar gwaggo maryama bace saida muka hadu itama zata zo nan take bani labari." Kakan nasa yayi dariya,cike da mamaki yace
"Wai kuwa d'an tsoho wane irin aminta ke tsakaninka da Liman? Na lura kuna kaunar junanku fiye da tsammani."
Jin tambayar ya k'ara sanya Malam dariyar farin ciki
"Bazaka gane ba Harisu,kaunar da muke yiwa junanmu ta samo asali tun daga iyayenmu da suka rasu,saboda karfin zumuncin ne,yasa mahaifina sanyamin sunan mahaifin liman din,wato Hussein yayinda shima yaci sunan nawa mahaifin Abdulmalik. Bayan haka,Allah Ya riga ya sanya mana kaunar junanmu fin tsammani Harisu. Wanda muke burin wataran mu kulla zumuncin da zai d'orar. Saidai kasan a zamanin nan ba'a yiwa yara dole,amma har gobe bamu bar burin wasu cikin jikokinmu ba su share mana wannan hawayen."
Haris yayi murmushi,baffa ya katse tunaninsa
"Ina fatan kayi abunda akace ya kawoka?"
Haris ya hade fuska
"Na rasa wacce zan zab'a domin na lura jikokin naka akwai yanga. Duk kama sukeyimin da juna ma."
Sukayi dariya,Baffa yace
"Ja'iri,ko kanawan dabo ba zasu nunawa mutanen Kazaure kyawawan yan mata ba shiyasa har zuwa yau ka kasa zab'en matar aure. Kada ka damu ka nutsu ka zab'a bazan bari Aliyu yayi maka dole ba."
Daga haka suka tab'a hirarsu ta zumunci kafin Haris yayi mishi sallama ya fice zuwa d'akinsa. Hankalinsa yakai ga wayoyinsa wanda ya barsu suna chaji,ya dauko yana dubawa. Missedcalls har fin goma,shida kuwa na kanwarsa ne. Yayinda daya na Abba sai kuma daddy daya kira sau uku. Hankalinsa yafi raja'a ga na kanwarsa. Yana shirin kira ya hangi sak'onta. Tun soma karantawarsa ransa yayi mummunan b'aci,jikinsa har rawa yakeyi. Wai Kb wane irin d'an akuya ne? Meyasa baya shakkar b'ata ran mutane? Ya lalubi layin Yasmeen ta daga tana kuka alokacin tana kwance a gadon mami(Maman kb wacce ta gama fusata).
Cikin kuka tace "Yayana kaga text dina? Yayana ka ceci rayuwata bazan iya yinta ba saida Kabir. Na shiga uku."
Ya runtse ido yanajin bakin ciki har ransa
"Wacece yarinyar?" Shine kawai abunda ya nemi sani.
"Baby yake yawan ambato."
Tuni idanun Haris suka bud'e,Baby?!! Akanta Kb yake cin zarafin kanwarsa? Kawai sai ya kashe wayar a fili ya furta
"Na rantse da Allah Kabir bazaka tab'a aurar Tasleem ba. Daga kai har ita zan nuna maku ni Haris na isa."
A fusace yasa kai,bai zarce ko'ina sai d'akin BAFFA......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(46)
"Ya wajen yayan naki? Ai farko mun damu da rashin samunki a waya. Wancan zuwan da sukayi na karshe yace min kin koma makaranta da zama anan Kano kuma ya hanaki yawan amfani da waya a dalilinsa nason ganin kin mayarda hankali ga karatu, har ina fad'a ina cewa me zaisa a wannan zamanin baligar mace tabar gaban mahaifanta ta koma jami'a da zama. Haba Tasleem,shi Khalid(Abba waziri,mahaifinta) din baiga kuskuren yin hakan ma? Koda dai na yarda da tarbiyyar da kika samu wajen maryamu amma hankalina bai kwanta ba Tasleem,nafison ganinki a d'akin mijinki."
Baby dake sauraron dogon bayanin kakarta,a gefe idanunta yana kan wannan 'yar budurwar mai matukar kama da ita tunaninta kuwa ya raja'a akan zuk'i tamallen da Yaya Abdullah ya shararo ya gaya musu. Kenan cewa yayi tana makaranta? Ikon Allah kenan. Ta numfasa ta kauda maganar
"A ko'ina Allah kan tsare bayinSa inna,kubar damuwa. Wai wacece wannan duplicate din tawa?"
Inna ta dubi yarinyar duk da bata gane turancin ba saidai ta fahimci baby bata ganeta ba.
"Lallai ma 'yar nan,keda har aike kikayi na sutura a kawowa kanwar taki tana jaririya? Aisha humaira ce fa,taci sunan aminiyar uwar taki. Lallai baki kyauta ba tasleem."
Tasleem idonta ya cika da kwalla,inna ta katseta da cewa
"Ai kusan sa'annine da takwararki,ko wannan zuwan nasu na karshe karkiso kiga har tasleem karama ta kusa kamota a tsayi."
"Wacece mai sunana?"
Anan kuma inna ta tsaya cak tana dubanta,wannan karon mamakinta da shakku sunfi na koyaushe domin kuwa tun zuwan Tasleem take lura da yanda ta chanja duk da tasan yanga da nuna aji halinta ne saidai zuwa yanzu ta soma zargin kodai Tasleem bata wani zumunci da yayan nata.
"Kinga abunda yasa banason makarantar kwana ko? Kada dai kicemin bayan mu da kika daina zumunci damu,yayan naki ma bakya zuwar mishi hutu kamar yanda ya fadamana ne? Nayi mamakin jin cewar kin manta da d'iyarsa."
Sai lokacin Baby ta farga da kuskurenta,ta wayance ta hanyar dariya duk da har lokacin tana fushi da yayan nata hakan baisa ta karyatashi ba.
"Kai inna,karatu fa yayi zafi duka duka munkai wata bamu hadu ba,inada matsalar yawan mantuwa ni ki gayawa liman ma ya nemar mini maganinsa."
Inna tace "Assha,naga alamun hakan kuwa. Tabbas dole ki nemi magani da kuruciyarki da komai wannan cuta ce babba. Saiki bar yin fitsari a inda kike wanka,domin shima yakan jawo larurar yawan mantuwa. Zan kuwa gayamishi."
Tasleem ta janyo hannun humaira wacce ta kammala cin tuwon dare,ta rungumeta kafin ta sumbaci goshinta.
"Ni yayarki ce, kina sona?"
Humaira tana dariya tace "Eh."
Ta kara rungumeta tana kokarin danne hawayenta,burinta gari ya waye taje ga mahaifiyarta.
Daren bata iya bacci ba,sai kuka da taci k'asa k'asa tunanowa da gurb'atacciyar rayuwar datayi a baya, gashi tana kunyar yan uwanta su samu labarin. Batasan yayanta yana mugun sonta ba sai a lokacin,tunda har ya iya sanyawa 'yarsa sunanta ayanzu kam bata da burin daya wuce ta sanya yarinyar a idonta. Har zuwa lokacin bata da niyyar bud'e wayarta domin batason amsa wayar mutanenta agaban mutan gidan.
******
Baffa ya dubeshi ya ajiye littafin karatunsa
"Lafiyarka kuwa Harisu?"
Harisu ya zauna kansa a kasa
"NA SAMU MATAR AURE BAFFA.....!"
"Alhamdulillah! Wacece?"
Ya gyara zama har lokacin ransa a matukar b'ace yake.....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(47)
Yayi kokari sosai wajen danne mugun tsanarta dake taso mishi aduk sadda ya tuna cewar ita ke haddasa rashin zaman lafiya a gidan kanwarsa.
"TASLEEM."
Ya karashe cikin d'acin zuciya,yayinda idanunsa suka kara kad'awa.
Ji yayi Baffan ya rungumoshi cikin matsanancin farin ciki wanda sanin amintar bayin Allahn a yanzu yasa ko kusa baiyi wani mamaki ba yanzun.
"Allah Ya albarkaceka a gaba daya rayuwarka Harisu,kamar kasan addu'ar dana gama yi kenan akan Allah Yasa kace kanason jikar aminina. Allah Yayi ni Husseini ban mutu ba zanga aure ya kullu tsakanin zuri'ata dana Abdulmalik? Allah na gode maKa daka amsamin addu'ata nan take. Saidai kuma harisu bazan baka auren jikata ba har sai ta amince zata aureka don haka ka tashi ka tafi zuwa gobe sai na tuntub'eta. Allah Ya tashemu lafiya."
Haris ya mike jiki babu kwari ya fice zuwa d'akin da aka tanadar masa. Kwanciya yayi akan makekan katifar sakamakon kansa da yaji yana sarawa. Anya bai kwari kansa ba kuwa?!! No! Bazai yiwu kuma yabar rayuwar Yasmeem cikin garari ba. Tabbas rayuwarta da farin cikinta sun dogara ne da Kb,burinta a duniya bai wuce Kb ba. A yau aka wayi gari Kb ya auri Tasleem,wulakanci da bakin ciki sune abunda zai biyo bayan auren ga Yasmeen. Shikam ya gwammace yayi wannan jihadin,alhalin ma a yanzu koda kud'i yana da yak'inin Baby bazata k'ara waiwayar karuwanci ba. Yana jin tsanarta a wani sashen zuciyarsa yayinda wani sashen kuma yakejin sassauci game da ita. Ya rantse sai ya rabata da Kb hanyar data dace,kb bai isa ya nemeta ba idan ta zama matarsa. Bai isa koda wasa ma ya tunkareta ba,ba wai don kishinta yakeyi ba(a fad'arsa kenan!!),sai don samawa kanwarsa 'yanci da kuma farin cikin gidan aure. Wanda bazai tabbata ba sai yayi nasarar raba wad'annan shaid'anun biyu..!
*****
Da sassafe ya kammala komai ko karyawa baiyi ba ya fito da shirinsa na komawa garin Kano domin bashi da bukatar k'ara yin tozali da Baby hakazalika hankalinsa ya tafi gaba d'aya ga kanwartasa.
Ya shiga ya samu Baffansa yana lazumi,ganinsa cikin shiri yasa Baffa watso mishi tambaya
"Harisu tafiyar ce?"
Haris ya danyi murmushi kai da ganin idanunsa kasan bai samu wadataccen bacci ba
"Tafiyarce Baffa,akwai ayyuka masu yawa da zanyi a yau in sha Allah."
"Toh madallah,game da zancen da kazo dashi kuma fa?"
Yaji ransa ya b'aci tunawa da batun aurensa da Baby wanda ya k'ak'abawa kansa,
"Baffa na baku nan da karshen sati,duk abunda kuka yanke in sha Allah zan dawo sai naji."
Ya jinjina kansa
"Ai shikenan,lallai kuma ka gayawa iyayenka maza ina bukatar ganinsu idan zaku dawo ku dawo tare. Allah Ya tsare hanya. Ka shiga kuyi sallama da aminin nawa ko?"
"Amin." Daga haka Haris ya fice batare da yayi na'am da zancen baffa na karshe ba,bayan ya yiwa mutan gidan sallama ya fita,yan matan da bai zab'a ba kenan!
Yana sane ya share batun zuwa gidan liman,ya tayar da motarsa wacce tun jiya da yamma yasa aka wanke mishi tayi k'al. Ya zauna kenan yana kokarin daura seat belt ya hango wata sark'a a k'asan mazaunin kusa da direba. Hannu yasa ya dauka,ba shakka sark'a ce da baby ke ado da ita a k'afarta. Zuciyarsa ta d'an sosu,ji yayi kuma yana kewar rashin abokiyar hira a kusa dashi. Saidai tunawa da yayi da kanwarsa da halin da take ciki yasa yayi azamar ajiye sark'ar a saman kujera ya kunna karatun kur'ani mai girma yayi ribas ya d'auki hanya...sai Kanon Dabo.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(49)
"Ya akayi Kabir?"
Ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya cikin jin dadin muryar daya jima yana kewarta.
"Idan da abunda yafi tashin hankali da matsanancin damuwa tsanani,toh kin sanyani a ciki Babyna. Nayi mugun kewarki har na zama tamkar zararre wanda hakan ke nema ta shafi mu'amalata da kowa da kuma aikina. Where have you been for so long? Kinsan irin halin da na shiga?"
Ta numfasa cike da takaicinsa,ita kam yanzu haushi ma yake bata,ta dan ja karamin tsaki
"Banson takura ne Kabir,na d'anyi tafiya bana zaton dawowata nan kusa ma."
"What?!!"
Ya fad'a da k'arfi yana mikewa zaune daga kishingid'ar da yayi a daya daga cikin kujerun na babban airport dake birnin tarayyar Abuja,alokacin yana shirin zuwa Kano ne domin amsa kiran iyayensa duk akan matar da sai daga baya ya gane rashin kyautatawarsa gareta. Yayi kokarin saita kansa ganin yanda mutanen wajen suka zubomishi ido gaba daya. Cikin tattausar murya yace
"Meyasa kikeson tayarmin da hankali babyna? Jikina ya bani kina tare da wani shegen shiyasa kika chanjamin. Wai me yake baki? Me kuma yake maki da bana iya kokarina wajen yi maki?"
Hawaye suka surnano daga idanuwan Baby,ba wai na wani abu bane sai jin tsanar kanta da kanta. Wai har itace yau ake gayawa haka? Karuwa ta gaske ake daukarta. A fusace tace
"Nabar wannan rayuwar kabir! Bana tunanin daga yau zaka kara ganina ballantana akai ga kaji muryata! Bakai ba,kowanene nabarshi har abada na gane wannan rayuwar ba rayuwa ce..."
Dariyar daya sanya kamar wani zautacce yasa Baby tsayawa cak, hakazalika mutanen dake zaune tare dashi suka zubamishi ido domin zuwa lokacin baiko damu dasu ba.
"Karya kikeyi?! You can never live without me baby! Ke d'in tawa ce, baki isa kiyimin YANKAR KAUNA ba! Dani dake babu mai rabamu,kuma ki sani, ina nan ina jiranki. Ki ajiye a ranki baki da miji sai ni! Saina aureki kota halin k'ak'a sai na cigaba da gabatar da rayuwa dake!"
Ta katse wayar gaba daya a fusace ta fiddo sim ta tauneshi ta furzar. Kawai sai ta durkushe ta fashe da kuka.
"Adda menene?"
Maganar Humaira ya ankarar da ita a inda suke, ta share hawayenta ta mike tana kokarun kakalo murmurshi
"Bakomai kanwata,muje."
Tafiya takeyi saidai komai na kalaman kabir yana dawo mata,taji ta tsani kanta. Inama za'a maido hannun agogo baya,inama inama zai zamana wannan kaddarar zata shafe a tarihin rayuwarta. Kai inama ace Abbanta bai auri Raliya ba har ma hakan yayi sanadin fad'awarsu ha'ula'i. Haka tayi ta tunane tunane jikinta babu laka har suka iso gidan auren Mamma. Baki ta saki ganin makeken gidan wanda bata taba zaton anan Kazaure za'a samu gida mai kyawun fasali kamar na turawa ba. Humaira ta katseta tana jan hannunta
"Nan ne gidan fa Adda."
Wata yarinya suka soma cin karo da ita tasha d'amara,ta cika eyeshadow a saman idonta,ga kuma jan baki data maka. Lukuta ce ta gaske,tana tsallenta kamar ba budurwa ba tana b'alla rake. Ganinsu yasa tayi d'if tana bazo ido. Kafin ta washe baki ganin Humaira
":Yar Humeme,wacece wannan kamar baturiya?"
Baby murmushi kawai takeyi ganin yarinyar,kamar dai tana da matsalar yarinta amma irin wannan kwalliyar ai an bar yayinsu.
"Addana ce, daga birni."
Yarinyar ta cuno baki. Wani saurayi mai shekaru sha takwas ya iso wajensu yace
"Kedai kam Safiya bazaki bar shiririta ba,inace anti tace ki tafi gidanku kibar fitowa idan kaka tana bacci? Wannan yar birni ce,kinga ma yanda ake kwalliya ba irin naki ba."
Ya karashe suna dariya har baby wacce abun ya bata dariya,wacce aka kira da Safiya ta murguda baki ta k'ara b'antalar rake
"Oho dai,Ali nuhu ma kansa yace mata suna kauye."
"Yauwa d'an k'arasa mana."
Ta harareshi tayi gaba tana tsalle tsallenta tace
"Akwai wanka."
Ta fice, saurayin ya dubi baby sukayi dariya. Ya dan russuna ya gaisheta gami da tambayar wanda take nema. Kafin ta bashi amsa humaira ta cafe
"Yaya Nura,addana ce ta Kano."
Ya kalli humaira ya kalleta,tabbaa yaga kama ya kara washe baki
"Yaya tasleem,right?"
Ta lumshe ido hadi da jinjina mishi kai lokaci daya. Ai sai ya sheka da gudu
"Kai ka kai,amma yau ni zan soma kaiwa antinmu albishir."
Jin haka Humaira ma tabi bayansa a guje. Dariya baby tayi ta mara musu baya tana mai zumudin yin tozali da mahaifiyarta....
******
Haris cike da mamaki ya dubi Yasmeen bayan sun keb'e a farfajiyar gidan inda tayo mishi rakiya zai koma ofis lokacin karfe ukun rana.
"Ashe kina da hankali har haka little? Kwarai banyi tsammanin zaki iya b'oyewa iyayenmu ainahin abunda ya had'aku da KB ba."
Yasmeen tayi murmushi mai ciwo
"Bari kawai yayana,wallahi inason Yaya kabir kai kanka shaida ne. Gani nayi a yanda kawai Daddy ya dauki zafi jin cewar yace na dawo ba tare da wani dalili ba(kamar yanda ta fad'a musu kenan don kare mijinta),kar kaso kaga yanda ya fusata sai faman bud'e wuta yakeyi. Ya kake tunanin idan sunji har marina yayi akan karuwarsa? Ba yanda za'ayi nayi gangancin da za'a rabani dashi. Kaima ina rok'onka don Allah kada ka nunamishi kasan zancen."
Ya kara tsintar kansa da kauna da matsanancin tausayin kanwar tasa, shi kuwa ya za'ayi yayi gangancin barin Tasleem ta ruguza farincikinta? Bazai yiwu ba. Ya numfasa
"Baki da matsala dani little,saidai ina rok'onki da ki rage son d'a namiji har haka kada ya zame maki babbar matsala fiye da yanzu. Ki cigaba da addu'a Allah Yayi mana magani. Bari na tafi, Abba yana jirana."
Ta tareshi
"Af,baka sanarmin wacce ka zab'o mana matsayin antin tawa ba? Kodai zatona ya zama gaskiya,Zahra ce?"
Yayi murmushin dole
"No.. Baki canka ba."
Ta dan nuna damuwarta,ganin ta bude baki zata k'ara magana ya bude motarsa ya fad'a
"Ke kyaleni kinji ko? Sai mun dawo da yamma."
Daga haka ya fice, taso taji kowace mai sa'ar ce tayi nasarar samun namiji irin Haris? Da ace KB yana da kyawawan halaye irin na Haris da ta bugi kirji ta kira kanta mai sa'a. Saidai abun takaici ya zamana bashi da hali.....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(48)
Fuskarta ta bayyana tsananin damuwa da mamakin jin cewar wai
Haris da take zaman jira su karb'i lambar juna ya koma Kano.
Menene haka Haris yayi mata kodai mantuwa ce yayi? Inna dake
lura da ita tace
"Kin shirya zuwa gaida malam husseini daga can ki wuce gidan
mahaifiyarki,kuma kin cire mayafi kinyi zaman dirshan daga samun
labarin tafiyar Harisu. Kina nufin bazaki ba saboda shi?"
Baby ta kalli kanwarta humaira wacce duk ta shanye janbakin data
shafa mata a lebba kafin a sanyaye kuma ta janyo mayafi
wadatacce wanda ta dauka cikin kayan mamma data barsu a dakin.
"Banji dadi bane daya wuce batare da munyi sallama dashi ba.
Amma ba hakan na nufin bazanje ba. Taso muje Humaira."
Ta dauki wayoyinta fuskarnan ta baby babu walwala ta zura
takalminta mai tsini wanda sanyasu har sun zame mata jiki. Inna
dai takalmin take kallo cike da mamaki kodayake ta lura duk
takalma uku data zo dasu haka suke da tsinin dunduniya. Ta kasa
dai hakuri ta tofa
"Wai Tasleem baki tsoron wadannan takalman su karya maki
k'afa?"(Kamar dai yanda kawata Ummu Abdool ta sanya ta fad'i
cikin taron mutane koda yake farkon zuwanta birni ne👌)
Baby tayi murmushi
"Inna ai na rigaya na saba,inajin dadinsu sosai."
Inna ta tabe baki
"Oh,duk wannan tsawon naki neman k'ari kikeyi. Toh Allah Ya
tsare,sai kun dawo."
Ta amsa kafin ta fita rike da hannun Humaira wacce ta rigaya ta
mamaye zuciyarta.
Tayi mamakin samun Malam Hussein din tare da Liman a falonsa.
Ashe ma yana gidan? Suna ganinta fara'arsu ta k'aru inda Liman
yace "Ga jikar taka ai."
Cike da ladabi ta gaishesu suka amsa,Malam Hussein ya sanya
mata albarka kafin ta mike tayi musu sallama ta fita.
Duk da hakan saida ta nufi gidan ko Allah zaisa ta hadu da wanda
zai bata lambar Haris.
******
Alhaji Aliyu Hussein(mahaifin Haris, su shida iyayensu suka haifa.
Shine d'a na farko namiji,sai mace mai bi masa ta rasu, sannan
Kawu Usman,Kawu Bilal da autarsu Hajiya Barira dake aure a garin
Maradi,jamhuriyar Nijar da kuma Hajiya Mariya(mami,mahaifiyar
Kb)
Gaba dayansu mazan idan an cire Abba dake kano,suna zaune ne
anan gidan kowanne da bangarensa.
Fa'iza,Habiba 'ya'ya mata ne ga Kawu Usman,manyan mazan su
uku ne. Yasir,Abdulmalik(Babban yaya) da Faisal
Rahina,Badiyya da Atika 'ya'ya matane ga Kawu Bilal,rahina tayi
aure sauran Badiyya da atika wadanda sukayi candy. Bashi da d'a
namiji.
Sai kuma babbar diyar Hajiya barira ta fari kafin tayi aure na biyu ta
koma Nijar da zama,Zahra. Wacce ke a hannun kakarsu uwargida
kuma amaryar Malam husseini,Hajja Kubra.
Kyawawan yan mata saidai na wata tafi na wata,hakan bai hanasu
sakin baki wajen kallon wacce suka tabbatar ta ketaresu a komai
ba,wacce kamshinta mai sanyi ya soma ziyartar hancinsu kafin
kyakkyawar surarta ta bayyana a gabansu gami da zazzak'ar
muryarta wacce tayi musu sallama da ita.
Gaba daya kuwa yan matan sun had'u suna masu jimamin tafiyar
Haris wanda bai zab'i d'ayansu ba. Kada ma Zahra taji
labari,yarinya mai tsananin kunya da kawaici saidai a k'asan ranta
ba k'aramin so take yiwa Haris ba. Abunda batasani ba,daman Haris
a farko kafin yazo ya kudurtawa ransa matukar anyimishi dole ya
fito da mata cikinsu toh hakika yafi ganin dacewar zab'ar Zahra. Ya
lura akwai nutsuwa da tarbiyya tattare da ita duk da dai sauran ma
akwai saidai basu da kawaici kamarta. Ko jiya da suke shawagin
nan bai ganta ba saida yasa aka kirata suka gaisa. Wannan ba
karamin dadi ya yiwa Hajja Kubra ba ganin matukar dacen data
hanga tsakanin Haris da Zahra. Hakan yasa ta kudurta yiwa Malam
zancen.
Bayan gaisuwa ta sanar dasu itace tasleem. Zahra ta tareta da
murmushi
"Wow,kece d'iyar gwaggo maryama ta Kano ko? Duk sadda naje
gidanta bamu da hira sai taki. Tabbas kinyi kama sosai da
Humeme."
Kasancewar haka take kiranta,sukayi dariya gaba daya. Bayan
gama gaisuwarsu ta nemi gaisawa da Hajja Kubra,har cikin dakinta
Zahra ta jagorance ta,itama ta nuna murnar ganin Tasleem a karshe
sukayi sallama. Ta sanya Zahra yi mata rakiya sauran sashen kafin
ta dubeta har lokacin tana murmushi haka kawai taji Zahra ta
burgeta.
"Nagode 'yar uwata,bari na karasa gidan Mamma."
"Lah bazaki shiga gidan Malam Ibrahim ba?"
Cikin rashin sani tace "Waye hakan?"
Zahra tayi dariya "Mahaifin amininin Kawu Abba ne dake garin
Kano. Kawu Abba kuma mahaifin Yaya Haris ne."
Jin wannan bayanin,Tasleem ta jinjina kanta,ta hakikance gidan
kakannin KB kenan. Gidan yana kallon juna dana kakannin Haris
suka shiga.
*****
Matansa biyu,Hajja Badi'atu da Hajja Atine. Yaransa tara cif. Hajja
badi'atu tana da biyar yayinda Hajja Atine keda hudu.
Alhaji Idris(Babangida),mahaifin Kb shine babba. Sai Safinatu,
Aisha(mahaifiyar Haris),Bello,Abdulmalik(Baba karami). Ya'yan
Hajja Badi'atu kenan. Matan duka suna gidan mazajensu. Mazan
kuwa idan an cire Daddy suna nan agidan da matansu da yaransu.
Hajja Atine kuwa,Garba,Fatima,Hafsa da Zakari. Suma duk sunyi
aure sun hayayyafa.
******
Babu inda Zahra bata shigar da tasleem ba,a inda Tasleem ta rasa
ma da wanda Kb ke kama tsakanin iyayensa. Idan ta hangi
kamanninsa da Hajja badi'atu saita hango da Malam ibrahim.
Karshe Tasleem ta yiwa Zahra godiya suka kama hanya da
kanwarta wacce tayi wayon sanin gidan mahaifiyarta."
Sai lokacin ta kunna wayarta,da kamar mintuna biyar kiran Kb ya
shigo. Wannan yasa dole ta dakata a gefen wata bishiya domin
amsa kiran nasa....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(50)
Hankalinsa idan yayi dubu ya tashi,Allah Allah yakeyi jirginsu ya tashi yaje ya nemi inda baby take ya dauketa koda ta halin k'ak'a ne. Shaf ya manta da dalilin zuwansa Kano akan matarsa ce,ana kiran masu tafiya Kano yayi zumbur ya mike yayi gaba.
Baby tana neman rainamishi hankali,shi kam bayajin zai iya rabuwa da ita a yanzu. Ko me za'ayi saidai iyayensa su amince su aura masa ita koda na watanni ukun ne yanda kungiyarsu tace idan yaso daga baya zai san yanda zai fiddata cikin shaid'anin kungiyar nan.
******
Da gudu ta isa ga Mamma wacce ke tsaye tana sauraron maganar Nura da humaira duk bata gama yarda dasu ba. Jin tasleem a jikinta tana kuka yasa ta tsaya cak,itama hawayen ne suka cika idanunta. Sallamar dattijon ta katsesu,duk suka waiga suna amsawa. Yayi tsai ganin bakuwar fuska,kafin ya jefo tambaya,nura ya amsata
"Adda tasleem ce fa Dad,'yar anti ta birni."
Fara'arsa ta k'aru,fari fari ne da silkin bak'i,dogo ne yana da jiki. Ganin Mamma ta nufeshi gami da amsar ledar hannunsa a ladabce ya fahimtar da baby lallai shine mijin Mammanta. Murmushinta ya fad'ad'u itama had'e da hawayen farin cikin ganin irin sauyin da Allah ya yiwa mammanta. Tun kafin yakai ga k'araso kusa da ita ta zube gwuiwoyinta k'asa ta gaisheshi
"Ina kwana Kawu."
Ya mikar da ita ta hanyar riko hannunta yana 'yar dariya
"Ashe bazaki bani matsayin uba ba tasleem? Toh ni kuma na daukeki matsayin d'iyata tun kafin na sakaki a kwayar idona. Kiyi kirana da Dad kema amma banjin dadin uncle dinnan."
Mamaki ya kamata tana dariyar farin ciki,kawai saita fashe da kuka,ashe wataran zata samu wannan soyayya irinta uba? Alhamdulillah.
Dad ya katseta ta hanyar duban Mamma fuskarsa ta cika da farin ciki
"Yau duk abunda za'ayi a gidan nan na fannin girke girke da shaye shaye ya zamana yazo daidai da ra'ayin d'iyata kada ayi abunda bataso."
Daga haka ya dubeni
"Menene abun kuka my daughter? Sai kisa naji kamar bakyayin uban dani."
Tayi azamar share hawayenta ta dubi mamma wacce murmushi kawai takeyi tana kallonta kafin ta maida dubanta ga Dad
"Ba haka bane Dad,kukan murna nakeyi."
Ya dafe kanta cikin murmushin yace
"Ya isa hakanan kada yayi yawa kuma. Bari na shiga ciki."
Ya mike ya nufi sama. Baby ta zauna saman kujera tana dariya tace
"Mamma nayi maki murna."
Ta harareta kadan,nura yaja hannun humaira yana fad'in
"Yar kanwata zo mu amso alawa wajen Dad."
Suka haye saman tare,Mamma da Baby suma saman suka nufa d'akin Mamma.
Ta dubi hannun diyarta
"Ya naga kamar hannun naki a kumbure?"
Ta d'an dubi hannun,ashe fa dazu da zatayi wanka ta fidda bandage din,ta dan tabe baki kadan
"Buguwa nayi kuma har yanzu yanamin zafi kadan kadan. Amma da sauki,mamma ya sunan dad din nawa? Ke daya ce a wajensa ne? Waye wannan nuran shima d'anki ne?"
Mamma tayi dariya
"Tambaya uku lokaci d'aya?"
Baby tayi dariya itama
"Allah kuwa mamma ke d'ince duk kin chanja kin k'ara kyau kamar baki da kishiya."
Ta fada don a zatonta wannan katon gidan bazai yiwu ace mata daya ciki ba. Kuma daman a baya gwaggo Hajara ta fadamata yana da iyali.
"Kema kinyi chanjawar data bani mamaki tasleem,kamar ba 'yar makaranta ba anya kina karatun ma?"
Mamma ta fada tana binta da kallon zargi. Tasleem ta diririce sai kuma ta basar da sakin 'yar dariya,mamma tayi tagumi ganin d'iyartata harda b'ulin hanci haka kawai jikinta yayi sanyi duk da tasan kwalliya ce.
"Kai mamma,muda muke karatu. Kuma fa shekara nawa rabonmu da juna kinga dole fa na chanja maki. Don Allah gayamin mamma."
Mamma ta sauke ajiyar zuciya
"Alhaji Kamal Hassan sunansa,kafin ya aureni yana da mace guda daya,Hajiya Aisha. Tana da yaranta manyan maza biyu,suna karatu a turai,sai budurwa d'aya,tana aure a Minna. Sai kuma nura wanda a wajen haihuwarsa Allah Ya dauki ranta. Tun bayan rasuwarta Alhaji yak'i aure har Allah Ya kawo mutuwar aurena ya amince zai aureni bayan da yazo gaida Liman ya ganni yace yana so. Humaira sunan matarsa taci muke kiranta hakan. Kinji tambayarki. Inaso kema ki amsamin tawa tambayar. Menene ainahin abunda ke faruwa? Jikina yana bani akwai abunda keda Abdullah kuke b'oyemin,hakanan nayi mamaki don ko d'azu munyi waya dashi bai bani labarin zuwanki Kazaure ba. Ya cemin mahaifinki na kwance tsawon watanni biyu baijin dadi shine ke d'awainiya dashi,duk sadda na tambayeshi ko kinzo dubashi daga makaranta sai ya hau yimin kame kame. Tasleem ko bakwa jituwa da yayan naki ne?"
Zufa ta karyowa Tasleem,gabanta ya hau dukan uku uku. Shigowar Nura da sallama itace ta ceceta
"Anti kizo inji dad."
Mamma tayi azamar mikewa
"Ina zuwa."
Tayi gaba wanda hakan yasa tasleem sauke ajiyar zuciya. Amma rashin gaskiya ma baiyi ba.
Hawayenta suka kwaranyo,wannan wane irin bala'i ne haka? Ita kam ko za'a kasheta bazata fadi komai ba ko don gargadin yayan nata ala barshi shi da bakinsa ya fad'a d'in. Waya ce ta soma k'ara,ta duba taga mai kiran. "Abdullah1"
Bata d'aga ma ta ajiye. Har yayi ya katse. Haka ya jera kira har uku shiru sannan ya hakura. Tana nan zaune tana tunane tunane har Mamma ta k'ara shigowa tare da Humaira. Ganin wayarta na blinking ya fahimtar da ita anyi kiranta ne. Ta dauka ta duba,murmushi tayi mai ma'anoni tana duban Tasleem wacce ganinta yasa ta d'agowa daga kwanciyar da tayi idanunta bai bar fidda ruwan hawayen ba.
"Ko yanzu kadai maganata ta fito."
Ta zauna tana mai daure fuskarta tamau ta zauna kan gadon
"Humaira tafi wajen gwaggo kuyi hira."
Ba musu yarinyar ta fice a guje,tasleem kallo daya ta yiwa mahaifiyarta tasan babu wasa a tattare da ita
"Baki da wacce ta fini duk duniyar nan,baki da wacce zaki kaiwa kukanta a duniya ta baki shawara wacce ni bazan iya baki ba. Tun rabuwata daku bana bacci mai dadi tasleem. Ga yawan mafarkai da nakeyi da lamuranki,haka kawai hankalina bai kwanta ba akan irin rufeni da Abdullah ke yawan yi idan na tambayeki. Ki fito ki gayamin hakikanin halin da rayuwarki ke ciki,naso na dauko ki alokacin da RALIYA ta rasu saidai kuma hakan bai samu ba sakamakon Abdullah daya cemin karatu kikeyi nima kuma alokacin Allah baiyi zanje gaisuwar ba. Wai menene ainahin abunda ke tafiya dangane dake?"
"Raliya ta rasu?!! Ta maimaita a fili cike da tsananin mamaki. Tuni hawaye sun wanke fuskar Mamma
"Baki kyautamin ba keda yayanki Tasleem,tambayarki ta kara fad'armin da gabana. Mutuwar Raliya baki da masaniya akai,rashin lafiyar abbanki baki sani ba,haihuwar yayanki da takwarar daya samar maki nan ba baki da labarinsa. Wannan wane irin al'amari ne mai d'aure kai? Tasleem ko guduwa kikayi daga gidan mahaifinki kika kasa hakuri har komai ya wuce??"
Kawai sai baby ta fashe da kuka,toh ya ta iya? Mahaifiyarta ce fa.
"Bazakiji komai daga bakina ba wallahi sai kinyi kiran yaya abdullah garin nan. Sai mun hadu mu uku sannan zanyi maganar dake bakina."
Mamma tayi shiru tana kallonta har na tsawon mintuna kafin tayi azamar daukar wayarta tayi kiran Abdullah. Ya dauka ya soma gaisheta gami da tambayar ko lafiya ya kira ba'a d'aga ba?
"Bana dakin,kanwarka ce a ciki."
Bai taba kawo tasleem take nufi ba,a zatonsa ma Humaira ce. Mamma ta katseshi
"Duk abunda kakeyi inaso ka ajiyeshi abdullah,gobe kazo kazaure inason ganinka."
Yayi tsai kamar mai tunani sai kuma a sanyaye yace
"Lafiya dai mamma?"
"Lafiya lau,kazo dai nace."
"Shikenan,in sha Allah ina nan tafe goben."
Sukayi sallama. Mamma ta mike bata kara cewa komai ba ta fita. Ranar basuyi wata hirar arziki da diyarta ba kamar a farko ba itace ke d'okin ganinta ba......
*****
Gaba daya sun hadu a babban falon Daddy ciki kuwa harda Kb.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(51)
Abba ne ya soma magana cikin nutsuwa
"Kabir."
Cikin sussunne kai ya amsa
"Na'am Abba."
"Jiya yarinyar nan muka ganta kwatsam ta dawo a motar kasuwa,koda muka tambayeta tace kaine kace ta dawo ba tare da ita kanta tasan dalilinka ba,gashi mun taru munason jin hakikanin matsalar data had'aku. Me tayi maka da zafi har haka?"
Kabir ya saci kallon Yasmeen wacce akaci sa'a ita d'inma kallonsa takeyi. Kauda kai tayi gefe,jikinsa ya k'ara sanyi, ga kunya data dabaibayeshi. Toh me zaice? Lallai Yasmeen ta barshi a tsaka.
"Wai bakaji ne ana magana sakaran banza da wofi!"
Cewar Daddy cikin fusata. Yasmeen cikin kuka ta tare
"Wallahi Daddy laifina ne,fad'a yayimin ni kuma nayi fushi nayi tahowa wata. Don Allah kayi hakuri Yaya kabir,ka gafarceni bazan k'ara ba don Allah."
Haris ya runtse ido kansa a k'asa idanunsa sunyi jazur kirjinsa har d'agawa yakeyi saboda bacin rai. Ya saci kallon Kabir,duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a fuskarsa.
"Daman nasan kece marar gaskiya Yasmeen. Ni nasan d'ana bazai wulakantaki ba.." Cewar Abba.
"Kada kayi saurin shaidar mutum mana Aliyu,idan anbi ta b'arawo abi ta mabi sahu. Alamun wannan shashashan sun nuna bashi da gaskiya. Idan ba haka ba kayi magana mana."
Kabir ya daure kansa a k'asa yace
"Gaskiyane Daddy,laifi tayimin nayi mata fad'a saidai banyi tsammanin zai mata ciwo har haka ba ta taho Kano bada sanina ba. Na yafemaki kema kuma ina fatan komai daya faru ya wuce,kuskure ne."
Haris ya wurga mishi kallon raini,saidai baice komai ba.
Abba yace komai ya wuce,nan ya k'ara yi musu fad'a akan hakuri da juna daga karshe yace su bari zuwa gobe su juya Abuja.
"Na dawo kanka kai kuma,ya zancenka ya kwana?" Cewar Daddy.
Haris ya k'ara russunar da kansa
"Kamar yanda na fad'awa Daddy ne,Malam yace muje daku karshem sati yanason ganinmu ne."
Daddy da Abba suka dubi juna,kafin Abba ya jinjina kai
"Shikenan,Allah Ya kaimu asabar d'in."
Aka amsa da amin kafin su sallamesu.
Da sassarfa ya nufi wajen motarsa
"Haris!!"
Muryar KB ta dakatar dashi. Kamar bazai tsaya ba sai kuma ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Ya karaso ya jingina da motar yana fuskantar Haris.
"Nasan koda yasmeen ta boyewa kowa abunda ya had'amu,toh bazata boyemaka ba. Nayi laifi,please ka tayani bata hakuri."
Haris yayi mai wani irin duba yana d'aga girarsa kadan
"Ka kwantar da hankalinka dan uwana,yanda kaima ka shaidi Yasmeen da nuna maka soyayya tsantsa wacce ba algus hakika bazaka samu wata mishkila ba daga gareta..."
Jin taku a d'an nesa dasu ya sanya Haris juyawa kafin ya dubi Kabir yana murmushi wanda tuni KB ya fahimci can k'asan nurmushin nan bacin rai da haushinsa ne tsantsa.
"As i said,bazatayi fushi dakai ba koda kuwa zata kamaku turmi da tab'arya,ita d'in mai rufa asirinka ce. Sai kayi hattara KB,ba'a cutar irin wadannan matan a zauna lafiya."
Daga haka ya kama handle na motarsa zai bud'e,KB fuska daure ya matsa,daidai lokacin Yasmeen ta k'araso.
"Yayana tafiyarce?"
Haris wanda ke kokarin sanya key ya dubeta yana murmushi cike yake da tausayinta
"Tafiyarce kanwata,kada ki damu zan b'ullo kafin ku wuce. Hope bada wuri zaku tafi ba?"
Ya maida akalar tambayar zuwa ga KB,KB ya d'an tab'e baki
"Banajin da wuri zamu tafi, watakil ma sai zuwa jibi.."
"Meyasa? Kaga fa ban taho da wasu kaya ba sosai,kuma Abba yace lallai gobe mu wuce."
Ya watsa mata kallo kamar yayi magana sai kuma ya fasa, shi fa so yake ya nemi inda baby take. Ganin kallon da yayi mata yasa ta tsoraci fad'ansa tayi azamar cewa
"Yayana saida safen."
Tayi gaba da sauri saurinta,Haris ya dubeta kafin ya watsawa Kb kallo a wulakance,tuni idanunsa sun sauya
"Baby ce ke neman shiga rayuwar aurenka kb,right?"
Kb ya dubeshi a sanyaye,ya numfasa
"Hakane Haris, saidai wallahi bansan meyasa na tsinci kaina da mugun kaunar yarinyar nan ba ni kaina bazance maka ga...."
Figar motar da Haris yayi ne ya sanya Kb ja baya da sauri hakanan hon ya shigayi da karfinsa har Maigadi ya kammala bud'ewa ya fita. Yayi daidai da zuwan Abba da daddy. Abba ne zai shiga gidansa.
Ganin yanda Haris ya fita,Abba yace
"Kai Kabiru,menene ya faru?"
Kb wanda tunani da mamakin yanda akan yasmeen amintarsa da dan uwansa ke neman samun mishkila duk ta hanashi motsi,jin maganar Abba ne yasa ya juyo.
"Bansani ba Abba."
"Allah Ya tsare hanya toh. Matarka nace ta shirya kuje can gidanka idan yaso zuwa gobe saiku wuce Abujan."
Baiji dadin wannan hukuncin ba,saidai yasmeen ta biyashi data boye sirrinsa,tabbas idan yayi mata wani rashin adalcin bai kyauta ba. Ya amsa da toh kawai. Jimawa kadan ta fito suka wuce a mota sai janta yakeyi da hira ta basar dashi bisa hud'ubar mami da ta nuna mata ya dace ta d'an ja ajinta.
****
Da sallama ya shigo gidan,humaira aguje ta rukunkumeshi tana ihu
"Ga yaya! Ga Yaya!!"
Wannan yayi sanadin tashin tasleem dake bacci a falon sakamakon damuwa ta haneta bacci daren jiya da kuma shariyar da Mamma tayi mata tabar wani d'okin ganinta gaba daya ma ta chanja mata fuska.
Cak ya tsaya ita kuwa ta daure fuskarta tamau tayi azamar mikewa zata nufi falon sama,a guje yasha gabanta. Bakinsa na rawa,ya kasa gaskata cewar ita d'ince tsaye a gaban idonsa. Dakyar ya iya tab'a hannunta jin cewar ita d'ince yasa ya riko hannun hawaye sun wanke fuskarsa. Kawai sai ta soma kukan itama kafin ta warce hannunta tayi sama a guje har zuwa d'akin mamma da batanan tana dakin mijinta. Gadonta ta fad'a tana kukan tunowa da yanda yayan nata yayi mata korar kare daga gidansa. Muryarsa taji cikin kuka a kusa da ita
"Na rasa kalar godiyar da zan yiwa Ubangiji,da ace kin kara shekara baki dawo ba wallahi mutuwa zanyi ko nima a nemeni a rasa. Tasleem kin jefa yayanki cikin tashin hankali,nayi magana cikin fushi na zartar da hukunci ban tab'a zaton zakiyimin haka ba. Tasleem ina kika shiga? Ya za'ayi ni Abdullah na yankewa kanwata abar kaunata wannan hukunci mai tsauri. Ina sunan 'yan uwantakanmu? Wallahi kusan zaucewa nayi dana wayi gari naga da gaske kin gujeni...."
Mamma ya gani tsaye ta harde hannuwanta a saman kirjinta,hakanan ta zuba musu ido. Jin da tasleem tayi Abdullah yayi shiru yasa ta dago kai,taji k'arar rufe k'ofa wannan yasa itama ta dubi k'ofar. Mukulli mamma ta saka daman mijinta ya fita zuwa aiki,humaira tayi umarni ga gwaggo mai aikinta ta mik'ata gidan liman. Nura kuwa makaranta yake zuwa baya dawowa sai yamma sakamakon shirin jarabawar karshe na sakandire da yakeyi.
Gidan ya zamana daga Mamma sai yaranta mafi soyuwa azuciyarta. Fuska a daure ta zauna yayin data dubesu
"Ku zauna sosai."
Tasleem ta mike zaune daga kwanciyar da tayi,shima abdullah ya zauna gefenta a saman gadon,yayinda mamma taja kujerar gaban madubinta ta zauna idanunta a kansu. Ta dubi tasleem
"Kince sai yayanki yazo zaki fadamin abunda ya afku a rayuwarki ko? Yau kuma gani gaki,gashi muna sauraronki duka."
''YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(52)
Yau ba ranar boye boye bace, ita kam koda zata boyewa kowa matsalarta toh banda mahaifiyarta. Don haka ta russunar da kanta ta labartawa mamma halin data tsinci kanta tun rabuwarsu. Da kuma fyaden da Usman yayi mata wanda ya sanya mamma fashewa da kuka,Yaya Abdullah kuwa tsananin mamakin yanda akayi kanwarsa bata sanar dashi bane ya cikashi.
"Haba Tasleem,meyasa kiks boyemin magana har haka?"
Tayi murmushi duk da ruwan hawayen da take fitarwa
"Yaya baka nemi hakan daga gareni ba. A karshe ma saika kama maganar su Raliya ka yarda cewa na bawa wani budurcina. Haba yaya, wane talauci ne zaisa nayi haka?"
Ta ja majina kafin ta dora,haka har ta gangaro kan rayuwarta a hannun yayanta da kuma rud'in shaidan da yasa ta bawa rilwan jikinta da cikin data samu yayanta ya koreta. Haduwarta da Momi harma da barikancin data fad'a har zuwa taimakon da haris yayi mata bayan tayi hatsari da zuwansu nan. Hakanan bata b'oyemusu ko wanene haris ba saidai bata tonawa kb asiri ba.
Salatin da Mamma ta doka ne ya maido hankalinsu gareta,tuni kuma ta kife a k'asa sumammiya. Ihu tasleem ta fasa,Yaya abdullah kuwa yayi yunkurin fadawa bandaki ya debo ruwa. Baiyi wani jinkiri ba ya yayyafawa mamma amma ina bata motsa ba. Tasleem tana ihun kiran sunanta tana fadin "Mamma kimin aikin gafara,wallahi mamma ni ba 'YAR BARIKI bace yanzu. Mamma mutuwarki mutuwata ce..."
"B'udemin kofar nan da sauri."
Yaya abdullah ya fada lokacin da yake kokarin daukar mamma. Da gudu tasleem ta bude kofar,tuni yayo waje yana fadin
"Ki biyoni da hijabin mamma."
Ta wulk'a idonta,ta kasa gane hijabin ma kawai saita janyo farin abu dake rataye jikin hanger. Yaya abdullah ya ajiye mamma a baya jikinsa a sake yana kuka.
Ganin haka tasleem tayi azamar zagayawa ta shiga mazaunin direba ta tada motar. Da gudu maigadin dake kallonsu ya bude kofar ta fita shaf batajin radadin hannunta tama manta tana da ciwo saboda tsabar Firgicin da take ciki.
"Yaya ina ne asibitin,ka gayamin kada ka janyo mu rasa mamma."
Yayi ta maza ya dunga gwada mata hanya har suka iso. Da gaggawa aka amshesu akayi ciki da mamma. Tasleem kawai ta zube a bakin kofar ta hada kai da gwuiwa tana kuka sosai. Yayanta ya iso ya zauna kujerar dake gefanta,hakan ya bata damar kwantar da kai a cinyarsa
"Yayana na halaka!"
Ya dafa kanta ya shiga girgiza kai saidai ya kasa magana. Ta dago ta dubeshi
"Idan mamma ta mutu wallahi nima mutuwa zanyi. Rayuwata bata da amfani,dana sani da nadama sun dabaibayeni fin tsammaninka yayana,meya rud'eni da bariki? Menene shi? Mena d'and'ana cikinsa? Wallahi yaya abdullah rayuwata bata da amfani,wani wanda baida uwa da uban ya fini. Amma yayana kaima kasan bani da laifi ko? Khalid Ma'aruf waziri shine ya watsar dani. Bayasona,bai damu da sauke hakkin daya rataya a wuyansa a kaina ba. Wallahi bana sonshi,na tsaneshi nima. Bayamin fad'a,bayamin nasiha,ya kasa aurar dani. Na tsaneshi!!!"
Sai ta mike tana ihu kafin ta hau buga kanta da bango,yaya abdullah ya damk'eta a gigice,mutanen wajen ma sai salati sukeyi suna kiran lafiya kuwa? Kawai saita suma jikin yayan nata......!
''YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
0 comments:
Post a Comment