Tasleem!!" Yaya abdullah ya fadi da k'arfi sannan ya dubi mutanen wajen gumi duk ya gama wankeshi hadi da hawaye kwance saman fuskarsa.
"Ku taimakamin don Allah."
Sai ga wata nos, tayi azamar kama tasleem ita da wata mace dake a layin ganin likita suka shiga ta kwantar da ita saman gado sannan ta kirayi likita. Nan suka soma kokarin ganin ta farfad'o.
Yana nan tsaye likitan dake tsaye kan mamma ya fito
"Alhamdulillah,ta farfado har ma tana nemanku. Kuna iya shiga,ina ita kanwartaka?"
Yaya abdullah ya numfasa yana hamdala kafin ya nunamishi d'akin da aka sanyata
"Ta suma ne amma likita yana tsaye a kanta."
Cikin damuwa likitan ya nufi dakin da baby take bayan ya damkawa abdullah takardar magungunan da za'a siyo ya kuma tabbatar mishi hawan jininta ne ya tashi amma da sauki,shi kuwa abdullah yayi azamar fad'awa d'akin da mamma take. Tana kwance ta kurawa silin ido,jin shigowar mutum yasa ta duban kofa kafin ta yunkura ta mike zaune,gaba daya tayi mugun sanyi ga hawaye na zubo mata. Abdullah ya zauna yana mai rike hannunta
"Sannu mamma."
Ta gyadamishi kanta kawai,kafin ta hau duban hanya, cikin rawar murya ta tambayeshi
"Ina tasleem?"
Ganin halin da take ciki yayi nufin rufeta,ta girgiza mishi kai
"Banda yau Abdullah,kabar k'ara b'oyemin komai ga rayuwarku. Idan ka boyemin taka,kada ka kara cutata da karemin damuwar diyata mace."
Hankalin abdullah ya tashi
"Ki gafarceni mamma,wallahi ban tab'a rufeki domin cutar rayuwar kanwata ba. Asalima bacin raine yasa na kori tasleem daga gidana wanda daga baya nayi muguwar dana sani bayan kuma da komai ya fito. Mahaifin rilwan ya sameni ya sanar dani batun wasikar,harma ya nemi a daura aurensu anan ne hankalinmu ya tashi."
Ya zame ya durkusa gwuiwoyinsa a k'asa yana hawaye jikinsa kuwa har kakkarwa yakeyi
"Ki gafarceni Mamma,bansan zan cuci rayuwar kanwata ba da ban aikata wannan mummunan laifin ba. Saidai ganinta da ciki ya rud'amin kwakwalwa har ma na kasa wani kwakkwaran tunani. Na tsoraci kada ta rusa aurenki ne,ganin da nazo nayi maki kina cikin kwanciyar hankali da walwalar dana jima ban riskeki cikinta ba mamma.
Bayan haka kuma ina...."
"Kiyi a hankali mana."
Jin muryar nos duk suka mayarda hankulansu ga kofar shigowar. Tasleem ce gaba dayanta a hargitse gashin kanta na usuli wanda bana k'ari ba duk ya barbazu a kafad'arta ko dankwalin babu. Ga bandaji da aka zagaye goshinta dashi sakamakon jinin dake fita daga goshin nata.Ta ja burki wanda ya janyo nos dinma tsayawa kafin kuma ta fita ta rufe musu kofa ganin kamar ba'a bukatarta a wajen. Kunya da nadama tsantsa suka kasa barin Tasleem k'arasawa ga mahaifiyarta. Meyasa alokacin data tashi yin wannan aika aikar na zina duk basu fad'omata ba? Babban tashin hankalin ma,mantawa da tayi da Mahaliccinta kuma alhamdulillah kullum cikin tuba take hakanan yanzu hakan ma haila takeyi. Zubewa tayi anan tana mai sanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana kuka kamar ranta zai fita.
"Astagfirullah! Astagfirullah."
Tayi ta maimaitawa har babu adadi,mamma kallo daya tayi gareta bata k'ara ba. Koda taji tausayin diyarta da kaddararran rayuwar da tayi a baya batajin zata iya saukowa a daidai wannan lokacin da bacin rai da tsoron tambayar da Allah zaiyi gareta akan amanar daya damk'a mata na d'iya babu abunda ke yawo a kwanyarta. Ta saki hannun abdullah bayan data dubeshi
"Maidani gidan mijina."
Wannan ya tsayar da tasle daga kukanta,a gaban idonta mamma ta kunce dankwalinta ta d'an rufawa jikinta tayi waje. Abdullah ya dauki takardar maganin ganin mamma na shirin fita tayi saurin rike kafarta
"Don Allah mamma ki yafemin. Nayi kuskure bazan kara maimaita irinsa ba."
Bata ko saurareta na ta janye kafarta tayi hanyar fita,da sauri abdullah ya ciro takalman kafarsa ya ajiye kusa da kafafunta
"Ki sanya Mamma,kada ki fita haka."
Ta sanya tana mai k'ara jin kaunar yaran nata a zuciyarta. Saidai kuma sunyi laifi gareta. Tabbas ta k'ara hakikancewa Dr. Khalid bashi da amana.
Suka fita, abdullah saida ya bari mamma tayi gaba ya bude mata motar ta shiga kafin yazo ya rarrashi baby itama ta mike tayi gaba sannan yaje ya share bill nasu,likitan yana kara jaddada mishi cewar a kula da abunda zai k'ara tab'a zuciyar mamma saboda blood pressure dinta kada yayi high.
A mota shiru,ba wanda ya cewa wani uffan tsakanin mamma da baby domin mamma zaune take a gidan gaba. Abdullah ya dawo
"Ki gafarceni mamma,na tsaya karb'o magani ne."
Batace uffan ba yaja sukayi gaba.
Suna zuwa gidan sukayi kicibus da Dad yayi ribas zai fito,ganinsu yasa shi komawa. Suka fito ya nufosu a gigice yana kama kafadun mamma.
"Maman nura lafiya dai? Maigadi ke sanarmin kuna asibiti dawowata kenan."
Ya dubi abdullah sannan Tasleem yayi mamakin halin da suke ciki.
"Ita kuwa d'iyata menene ya sami goshinta?"
Da sauri Mamma ta tare
"Lafiya,hawan jinina ne ya d'an motsa shiyasa suka kaini asibiti ba'a hayyacina ba. Bakaga yanda yaran naka suka rud'e ba?"
Baby ta amshe
"Dad buguwa nayi wajen sauko da mamma daga steps."
Ya danyi murmushi ya amince da hakan
"Wayyo sannunki diyata." Ya maida dubansa ga matarsa wacce kallonta ke mantar dashi komai
"Nagode Allah da ya ceci ran abar kaunata."
Daga haka yaja hannunta zuwa ciki yana sannu sannu ba iyaka. Baby ta daskare tana dubansa cike da sha'awa.
"Tell me now my sister,ta yaya zan bari matsala ta b'ullo tsakanin dad da mamma?'
Ta dubi yayan nata wanda ke magana cike da matsanancin damuwa hannunsa rike da ledar magunguna. Hawayenta suka cigaba da kwaranya tayi murmushi mai ciwo
"Babu."
Ya numfasa kafin yaja hannunta
"Inason mu zauna mu tattauna dake sosai."
Daga haka yaja hannunta suka mara musu baya.
Sam mamma tak'i bawa tasleem damar yin magana da ita a keb'ance. Tun magrib tayi sashen mijinta domin yace ta huta bayason ganinta a kicin. Shima can ya tare a wajenta. Abdullah yace mishi sai zuwa gobe zai koma.
Tana zaune ta idar da salla ta zubawa talabijin ido inda humaira ke kallon tashar Disney na cartoons zallah. Ta lula cikin tunanin wannan shariyar da mamma keyi mata,Abdullah ya zauna kusa da ita saman kujera yayinda take zaune kan darduma ta takure.
"Biyoni." Ta bishi babu musu har zuwa d'ayan falon dake jikin wanda suke. Bayan sun zauna ya dubeta......!
YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(54)
Saidai ya soma da bata hakuri laifin daya aikata gareta na korarta daga gida da kuma gargadinta da zuwa wajen mahaifiyarsu kafin yayi mata nasiha ya kuma nuna mata kurenta na rashin dacewar jefa kanta a karuwanci da tayi. Koda suka gangaro kan Mamma,ya shawarceta data koma gidan liman ta bari har zuwa sadda mamma zata sauko hakanan jininta ya daidaitu. Tasleem tayi na'am da wannan,saida ya kammala da wannan babin kafin ya kirayi sunanta wanda hakan ya sanyata dago kai ta dubeshi tana mai amsawa.
"Ya dace ki sassauta kiyayya ga mahaifinki."
Nan da nan ta daure fuska tamau,ya share kamar bai gani ba ya cigaba da magana.
"Mahaifinki a yanzu idan kika ganshi,kikaga yanda yake fama da ciwon sugar da hawan jini,zaki tausaya mishi saboda ramar da yayi tayi yawa,aikinsa tuni ya ajiyeshi gefe. Zakiyi mamaki idan nace maki kullum cikin zubar hawaye yake duk a dalilin rashin sanin takamaiman inda kike. Ban boyemishi dukkan abunda ya faru ba ya nunamin kurena,yace idan shi ya koreki ba'a hayyacinsa na meyasa zanyi wannan ta'asar? A karshe yace laifin nashi ne. Da ace bai koreki ba babu yanda za'ayi ki shiga wata rayuwa ta daban."
"Yaya bani labari mana game da abunda ya kawo chanjin Abba."
"Tun bayan tafiyarki da watanni uku, mummunan iftila'i ya fad'awa Usman na konewar babban shagon da baiyi ko wata biyar da bud'ewa ba,hakanan wasu b'arayin sun tareshi a hanya sun mishi duka har suka nakastashi suka kwace wayoyi da kudadensa. Abun mamaki kuma sati ba'a rufa na itama marigayi raliya akayi hada mata jini da majina a karshe aka watsar da ita a kofar gida. Jinyar da tayi kamar bazata tashi ba,gashi kuma wata kaddarar komai na Abba ya soma ja da baya Tasleem. Kamar wanda aka sanyawa hannu fitar ma da yake zuwa asibitinsa ya gaza. Hakanan raliya ta matsa mishi akan sai an fidda d'anta waje anyi mishi aiki saboda tuni matarsa tace bazata iya zama da nakasashshe ba ta ajiye mishi 'yar sa ta tafi. Akan dole Abba ya kashe makudan kudade wajen aikin kafar Usman ta hanyar fitar dashi waje saidai aiki baiyi ba wai a niyyarsu a sanyamishi kafafun roba saidai garin haka mutuwa ta riskeshi acan. Nan raliya ta hau ihu da zage zage,abun ne ya zame mata wajen goma ba. A gefe ga d'iyarta ta tsunduma kanta a harkar bin maza itama. Can kuwa nura ne ya kara lalacewa da bin mata. Matarsa ma ta gujeshi,hamza kuwa ya zamo mijin tace a wajen matarsa. Ke rayuwa fa tayi mata zafi ga mutuwar Usman,haka ta dawo ta rungumi jikokinta da suke a wajenta. Bata isa ta sanya Hamida da Hamid aiki ba suyi,kamar wata sa'arsu haka zakiga sunayi mata tsawa. Duk cikinsu,hindatu kadai ta fita daban,babu ruwanta ke sai kice ma ba daga jikin raliya ta fito ba. Nazo jana'izar Usman sannan na tattara na koma Abuja ina mai cike da dumbin mamakin ramar da Abba yayi sannan gaba daya duk yayi sanyi kamar bashi ba.
Wata biyu rabona dashi saidai nakan kokarta kiranshi na gaisheshi,wataranar juma'a ina zaune na dawo daga masallaci na amsa kiransa inda ya nemi nazo na sameshi da sauri. Ba shiri washegari na tafi a mota. Kuka sosai na samu Abba yana yi,cike da fargaba nikam na karasa wajenshi don gani nakeyi kamar zai yimin magana cikin fada fada kamar yanda ya saba. Ga mamakina naga ya rungumeni yana neman gafarata,yace a baya yakan damu idan yayimana wani abun ashe ba'a son ransa yakeyi ba Tasleem. Yace min ya iske raliya tana waya da bokanta inda takeso tazo ayi mata aikin da za'a kasheshi suci ragowar kudinsa saboda ta fahimci ya soma talaucewa ita kam bata tab'a ganin jinin sarauta mai bak'in jini kamar Khalid ba. Kowa gudunsa yakeyi yan uwan duk sun juyamishi baya saboda ganin shi kadai ne ba uwa ba uba.(Ta manta itace ta janyomishi tsanar,don akwai randa yayansa waziri yana son ganinsa yace bai zuwa. Kusan sati shiru har da kanshi wazirin yazo gidan,ganin babban mutum yasa maigadin budemishi dakin bak'i,yayita zaman jira amma raliya ta rike abba ta hanashi fitowa a karshe waziri ya fusata yabar gidan da alkawarin bazai kara shiga harkar Khalid na tunda bashi da bukatarsu hakanan ya gargadi dukkam zuri'arsu kada wanda ya k'ara lek'awa gidansa. Wannan labarin nima baba Maigadi ke bani,hankalina ya tashi don har gidan waziri naje na bashi hakuri ya sakarmin fuska sosai ya nunamin ai mu d'in nasu ne. Yace kuma zai sanya ayi addu'a sosai gareshi don bai amince da yanayinsa ba. Shima ya d'agawa mahaifinmu kafa ne har zuwa wani lokacin.
Abba ya cigaba da labartamin,yace tun sadda yaji wannan zancen yaji kamar bashi ba,komai na rayuwarsa ya daidaita,kirjinsa yabar nauyi. A ranar kuwa ya yiwa raliya abunda bai tab'a yinsa ba sakamakon tsanarta da yaji,duka yayi mata sosai sannan ya saketa. Tace wallahi bazata bar gidan ba,saida ya hado da jami'an tsaro har jikokinta yace duk ta tattara ta tafi dasu shi kam baisan menene ya kwasheshi ya auro wannan kaddarar ba. Hakanan ya kori nura wanda har ya nemi ya zageshi. Hindatu kam tasha kuka,ta hau rokonsa ya barta a wajensa itama ta tsani uwarta. Haka dai ya hakura yabar yaransa. Washegarin faruwar al'amarin ne yayi kirana yake sanar dani. Nayi godiya ga Allah da baisa zan mutu kafin wannan rana ba. Nan Abba ya tambayeni game da mamma,na bashi labarin komai har zuwa gidana da kikayi da sauransu. Anan ne nadama tsantsa ya kamashi. Tun dai daga lokacin ya kamu da rashin lafiya,karshe yasa na kaishi wajen waziri. Muna shiga waziri yana zaune a fada,yana ganin Abba cikin yanayin zubar hawaye yana nufoshi,tsam ya mike har na tsoraci ko marinsa zaiyi kawai sai ya rungumeshi wanda hakan ya bawa abba kuka sosai a jikinsa. Ya jashi inda fadawan suka mike suna zuba kirari,sukayi ciki. Kinji yanda aka sasanta,Abba ya tsanantawa su Hamid ya hanasu fita ko'ina ya santa ido sosai a kansu,ganin batanci da rashin maida hankalin Hamid a karatu zaiyi yawa yasa shi turashi makarantar horo. Hamida kuwa kasancewar tana tsoron abba alokacin ganin irin korar da yayiwa mamanta sannan taje taga muhallin da raliya take babu wani kayan morewa rayuwa dolenta ta nutsu,Abba yace ya bata sari ta fiddo miji ko kuma ya aurar da ita ga wanda yaso. Har nan kazaure na rakoshi ya roki gafararsu kafin ya koma kuma rashin lafiya ta hau shi. Yayimin fadan dalilina na boyewa iyayen mamma inda kike karshe abba ya hau yawaita addua da tsayuwar dare da kuma zubar hawaye duk saboda rashinki da alhakin daya dauka namu. Raliya kuwa gobara sukayi a gidan babu wanda ya tsira daidai da nura,sakamakon jonin wuta direct da Nura yayo musu acewarsa bazai iya rayuwa ba wutar lantarki ba ya gama zage mahaifiyarsu tas akan bakin cikin data janyomusu suna cikin daula. Karshensu kenan. Yanzu haka hamida tayi aure ga wani alhaji mai mata biyu har ta haihu,duk da wulakancin da take sha hakanan take zaman hakuri. Hindatu kuwa tana nan tare dani a Abuja ta soma karatunta a jami'a, hakanan Abba da nake jinyarsa saidai yanzun jikinsa da sauki sosai. Waziri ma ya matsamin na maidoshi gabansa inajin hakan zaiyi tunda shima Abban yace ya gaji da zama gidana saboda kunyar hasina. Duk da dai yanzu gidane na kashin kaina."
Tasleem tayi shiru,tabbas rayuwa abar tsoro ce. A sanyaye ta kara tambayarsa
"Ina labarin Ridwan kuma?"
Murmushi Abdullah yayi
"Allah Sarki,abbansa fa ya jima yana fushi dashi har korarsa yaso yi na hana. Amma yanzu yayi aure yana zaune acan London wajen uncle dinsa da matarsa Jidda. Yaransu biyu ma,daya taci sunanki dayar kuwa sunan mamansa."
Tayi murmushi kawai.
*****
Washegari yaya abdullah yana tafiya,itama ta shirya koda ta yiwa mamma sallamar komawa wajensu inna bata ko kalleta ba. Haka nan ta wuce a sanyaye.
Da la'asar Liman ya tura ayi kiranta.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar
(55)
Bata kawo komai ba ta mike ta yafa mayafinta ta nufi dakin Liman jikinta akwai yanayin sanyi wanda tun dawowarta daga gidan mamma take cikinsa. Koda inna ta tambayeta ta amsa da babu komai.
Yana zaune yana duba wani littafi na hadisai yaji sallamarta wanda hakan yasa shi ajiye littafin a gefe yana mai amsawa fuska a sake. Ta shigo tana yamutsa fuska kadan kafin ta soma kokarin zama tana fad'in
"Nidai wannan tsohon kana neman matsamin fa,yanzu kuma menayi aka d'agoni bama a tarbeni da 'yar shila ba."
Yayi dariya
"Shak'iyiya,wanda kika ci bai isheki bane a k'aro maki gobe? Nutsu don magana zamuyi."
Ya soma da yi mata doguwar nasiha akan muhimmancin aure wanda tun daga haka tasha jinin jikinta,kirjinta kuma bai bar bugu da sauri da sauri ba. Saida ya kammala sannan ya bijiro mata da bukatarsa na neman amincewarta kan batun aurenta da Haris.
Cikin tsananin mamaki da fargaba ta dubeshi
"Shi Haris dinne yace yana sona baffa?"
Jin dadi game da amsar da zai bata yasa Liman yin wata 'yar dariya
"Shakka babu,harisu ne yazo da batun kamar yasan fatanmu kenan ni da aminina. Kuma munyi na'am da batunsa nasan bazaki watsa mana k'asa a ido ba kasancewarki yarinya mai biyayya."
Tayi k'asa da kanta,nan da nan abokan hirarta suka ziyarci fuskarta(hawaye). Ina ita ina Haris wai? Haris yasan abunda yake kuwa? Me zaiyi da sauran maza? Sam bazata bari ta cuci mai niyyar taimakonta ba,kai ta kasa gaskata da gasken shine yayi tayin auren nata.
"Kuyi hakuri bafamfa,bazan iya aurensa ba!"
Nan take annurin dake saman fuskarsa ya dauke,tamkar bai taba dariya ba ya koma Abdulmaleek Hussein dinsa sak!
"Nufinki zaki bani kunya ne Tasleem? Toh bari na fadamaki wallahi tunda nake da Aminina tun zamanin kuruciyarmu dayanmu bai taba zuwar wa dayanmu da bukata ba munyi watsi da ita. Baki isa ba Tasleem! Ko uwarki k'arya takeyi na nemi bukata awajenta tak'iyi,na takaice maki ma aminina shine ya wuce gaba wajen aurenta da Ubanki tun a farko domin a baya banso tayi nesa har haka ba. Ki tashi ki barmin d'akina,aure kuwa keda Harisu saidai idan anyishi ki mutu."
Daga haka ya maida fuskarsa gefe babu wata walwala a samanta.
A sanyaye tasleem ta mike tana k'ara mannewa da abokin hirarta harda sheshshek'a.
Kallo daya tayi mata kafin tabar murza robb a hancinta
"Lafiya kuwa?"
Cikin kukan dai ta labarta mata yanda sukayi da Liman,inna taja tsaki gami da fadin
"Allah Ya kyauta,ina goyon bayan Liman,wannan hukuncin yayi. Domin kuwa samun yaron mutunci irin Harisu a zamanin nan akwai wuya. Nikam dari bisa dari na amince kuma banga aibu da aurenku ba. Budurwa sharab dake,ai wallahi sai yanda kikayi dashi ta hanyar biyayya da kissar d'iya mace."
Ji tayi tamkar magana take yab'a mata,da sauri ta mike ra shuri takalmanta batayi wata wata ba ta fada gidan gwaggo Hajara bazata kwana a gidan ba. Meyasa Haris zaiyiwa rayuwarsa haka? Duk a zatonta jihadi yake niyyar yi don tausayinta batasan kudurin da Haris ke shirin yi ba. Gwaggo Hajara ma yabo da hamdala ta shiga yi,ai ita kam tun farkon ganinta da Haris takeso aure ya kullu tsakaninsu sai gashi Allah Ya amsa. Nan tayita lallashin tasleem gami dayi mata nuni akan illar bijirewa umarnin babba.
******
"Nayi zaton ai da Zahra za'a hadashi?"
Murmushi Malam yayi kafin ya bata amsa
"Ya kike wata magana kubra? Da Zahra da Tasleem basu da wani bambanci a wajena. Tunda yaro ya nuna yanason Tasleem sai a bisu da addu'a inajin hakan zaifi."
Ba haka taso ba sanin da tayi Zahra ita kadai take iya gayawa sirrinta,kuma ta tabbatar mata cewar tana son Haris. Bata hakura na dai ta k'ara muskutawa
"Malam fadamaka ne banyi ba amma hakikanin gaskiya Zahra banda alkunya ya hanata magana tana son Haris kwarai dagaske,mezai hana a had'a mishi su biyu duka a aura mishi na tabbata Harisu bazai watsa mana k'asa a ido ba."
Malam ya dubi hajja kubra a mamakince
"Harisun ya gayamaki yana da ra'ayin mata biyu da wurwuri haka ne?"
Ta girgiza kai,zatayi magana ya dakatar da ita
"Bazan hanaki abunda kikaga zaifi ba,saidai ni da kaina bazan tunkari Harisu da zancen ba. Ki tuntub'eshi da kanki idan yaga zai iya toh nawa bai wuce daura aure ba."
Ranta ya d'anyi sanyi jin hakan. Tana matukar kaunar Zahra,bata tab'a tsayawa kula samari ba sai gashi rana tsaka ta kamu da son Haris wanda har ta kasa b'oye mata ita kuwa mezaisa ta kasa yin wannan kokarin gareta?
"Shikenan Malam,Allah Ya zab'a abunda yafi alheri. Zan gwada hakan."
"Ameen." Kawai yace mata kafin ya nemi ta kawomishi furarsa.
******
Momi tayi wani murmushi kafin ta rausaya idanuwa
"Ka kwantar da hankalinka Kb,na tabbatar maka baby zata dawo. Bata komai saida shawarata. Koda ya tabbata auren zatayi na tabbatar maka da cewar zata nemeni bada jimawa ba. Nima ban sameta a waya ba,saidai nasan wacece baby tunda har ta furta maka tabar wannan harkar tabbas da gaske takeyi. Mu kuwa a sharuddan kungiyar,lallai idan mace zata bar harka sai ta tattaro mana dukkan kadarar data mallaka cikin harka idan kuwa ba haka ba zamu hanata auren gaba daya muyi sanadiyyar gurb'acewar dukkanin rayuwarta wanda nake da yak'inin Baby bazata iya ba. Yanzu kawai mu jirayi dawowarta."
Kabir ya jefa hannu aljihu ya zaro bandiran kudi 'yan dari bibbiyu har uku ya dire a kusa da Momy yana murmushi
"Ga wannan asha ruwa,burina ta dawo na ganta."
Tana taunar cingam gami da wani irin murmushi na duniyanci ta dauki kudin a wulakance tana juyawa kafin ta watsa mishi kallo tana fari da ido
"Bukatarka zata biya da zarar Baby ta dawo. Zanbi kowacce hanya don ganin ta amince da aurenka."
Ya shafi suma yana dariya kafin ya jinjinawa Momy
"Dakyau momynmu,anjima zanbi jirgi zuwa Abuja,sai naji wayarki."
Daga haka yasa kai ya fice yayinda Momy ta bishi da murmushi na musamman.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(56)
Kwance yake akan restingchair a farfajiyar gidansa daga can poolside. Idanunsa a lumshe fuskarsa ma'abociyar kyau da kwarjini sai shek'i takeyi. Yammacin juma'a ne,garin yayi luf luf sai wani ni'imantaccen iska ke busowa da kamshin k'asa kasancewar da safiyar yau din anyi ruwa sosai. Sanye yake da jar t-shirt,da wando wanda da kad'an ya rufe gwuiwoyinsa.
Sallamar isah mai gadinsa ne ya sanyashi bude idanunsa yana mai amsawa bayan yayi kokarin danne damuwar dake shimfide kasan ransa.
"Yallabai kayi bak'o yace a sanar dakai cewa Deen Bukar ne."
Jin sunan wanda ya jima baiji daga gareshi ba ya dago yana murmushi
"Kayi mishi iznin shigowa isah."
Matsakaicin saurayi ne,mai d'an kiba. Yana sanye da kananun kaya shima,kallo d'aya zakayiwa bak'ar fatarsa ka fahimci yana hutawa sakamakon lukui lukui da tayi. Ganinsa yasa Haris mikewa tsaye yana bayyana hakoransa a waje cike da farin cikin ganin oldclassmate dinsa na Malaysia. Deen Bukar. Rungume juna sukayi suna masu dariya kafin su cafke.
"Shegen sama,deen kana hutawarka,irin wannan k'iba kamar ba soja ba?"
Deen yayi dariya yana nunoshi da yatsa
"Zaka fara ko Gent? Toh ai kaine za'ace baka aikin komai. Ka ganka kuwa?"
Sukayi dariya kafin Haris ya dauki wayoyinsa da tab
"Bismillah."
Suna tafe suna hira har suka shiga falon Haris wanda ya k'ayatu iya k'ayatuwa. Haris yayi kiran kuku dinsa,Henry. Ya sanyashi ya kawowa bak'onshi abun motsa baki. Bayan tafiyar henry ya dubi deen
"Sai fa hakuri kasan abunka da gwauro."
Deen yayi dariya
"Kai ka sowa kanka,ya dace ka nemo mana mata musha biki. Gashi dai twins dinka(yaran deen) suna k'ara girma. Kb fa,ya labarinsa?"
Haris yayi dariyar yak'e
"Yana nan da bebinsa d'aya,Nasreen."
Deen ya jinjina kai lokacin Henry ya iso ya soma zuba mishi juice a kofi.
"Banji dadin rashin aurenka Gent,ko still now tsoron matan kakeyi?"
Haris yayi murmushi
"Aure lokaci ne Deen, sannan idan nace ma ina tsoron matan na yanzu ai ba laifi bane."
"Magana ta fito,kacemin kawai tsoronsu kakeyi."
Murmushin dai Haris ya k'ara yi kawai,shi kadai yasan matsalarsa. Duk sadda ya tunano da tafiyarsu kazaure a gobe damuwa kadai ke dabaibaye zuciyarsa.
"Last two months ai,inajin 5th of may ne,na hadu da wani kamar KB naka a Ni'ima hotel da wata baby. Naso nayi mishi magana duk da dai ina kokwanton ko shi d'inne tunda kaga bazan kawo har yanzu KB yana yayin wasu bebs din ba tunda he's married. Kafin ma nakai wajensu sunyi gaba,na rako oganmu ne wajen wani abokinsa. Saidai yanzu kace yana ina ma?"
Haris ya kara zuciya da lamuran KB, yana kara jin kwarin gwuiwar auren Baby don ya fahimci ita kadai ce yake tarayya da ita yanzu. A zahiri ya murmusa
"Hum, bana zaton shi ka gani dai,mutumin dake zaune a Abuja ba."
Deen ya tabe baki yana mai daga kafada kadan
"Zai iya yiwuwa."
Daga nan suka share zancen,zuwan Deen shi ya mantar da Haris damuwarsa sukayita hira yana bashi labarin yanda wasu rundunarsu ke fama da matsalar boko haram,bai bar gidan ba saida sukaci girkin henry. Bayan magriba ya wuce.
*****
Abdullah kuwa,koda ya koma Abuja bai rufewa Abbansa komai dangane da halin da Tasleem ta shiga ba. Abba yayi kuka kamar me a karshe yayi nadamar watsi da rayuwar yaransa da yayi wanda sanadin hakan gashi har karuwanci diyarsa wacce ta samu kyakkyawar tarbiyya tayi. Abdullah kuma ya sanarmishi da zancen aurenta da za'ayi da Haris din kamar dai yanda Baffa ya sanarmishi kafin barinsa Kazaure. Abba yaji dadi matuka musamman jin cewar Haris din da kansa ya amince zai rufawa diyarsa asiri yana sonta ba tare da kowa ya tilasta mishi ba. Sannan kuma ya d'okantu da ganin tasleem ko don ya nemi gafararta,amma Abdullah yace mishi ya saurara dai tunda can gidan basu san komai ba. Ya hadashi a waya da baffa ya nuna amincewarsa dari bisa dari ya kuma nunawa Baffa ai tasleem ikonsa ce. Baffa yaji dadi matuka,bayan hakan ne ma ya nemi tasleem yayi maganar gareta.
Wannan kenan!!
*****
RANAR ASABAR!!!!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(57)
Kabir yana zaune a falonshi bayan ya kirayi wayar
Momy har zuwa lokacin babu kwakkwarar
magana ta inda Baby take. Ya damu kwarai,har
abun yana neman shafar walwalarsa. Daidai
lokacin Yasmewn ta zauna tana amsa waya cikin
dariya ta karashe maganar data soma tun kafin
shigowarta da cewa
"Aa yayana,mudai kam kada a tsawaita mana
lokaci munason shan biki da wuri."
Ta danyi shiru a nishadance tana sauraron amsar
da Haris ke bata,yayinda KB ya mike zaune yana
zuba mata ido cike da dumbin mamaki.
"Toh Allah Ya tsare hanya,agaishemana dasu
Malam."
Daganan ta katse wayar ta ajiye.
"Sorry prince,abinci saura kad'an."
"Wane yayan naki ne zaiyi aure?"
Tayi mamakin tambayarsa,bata dauka koda wasa
baisan da zancen ba kuma ganin agabansa aka
danyi maganar tafiya kazauren a kano duk da dai
ba'a fadada zancen yanda zai fahimta
"Baka da labarin sanya ranar auren Yayana
za'aje yi Kazaure?"
Ransa ya baci jin tambayt daya kalleta matsayin
rainin hankali
"Da ina da labarin zan tambayeki ne?"
Ganin ransa ya baci yasa ta sanyaya murya
domin yanzu batason batamishi ko kusa
"Kayi hakuri,ganin yanda kuke dashi shiyasa nayi
zaton bazaka rasa sanin komai ba. Ni kaina
bansan cikakken zancen ba. Amma Daddy ne ya
turashi Kazaure zab'ar matar aure cikin yan
uwanmu. Kuma yanzu ya zab'a shiyasa Malam
ya nemi ganinsu gaba daya harma dasu Daddy
din."
Kb jikinsa yayi sanyi, me ya yiwa Haris da zafi
har haka? Duk irin shakuwarsa amma ya kasa
sanar dashi labarin aurensa? Ya jinjina kai kawai
baice uffan ba.
"Hadomin Coffee."
Ta mike ta fita itama din dai ta lura yayan nata
saboda abunda KB yayi gareta ne ya kullaceshi
wanda ba halinsa bane(wato kullata).
Shi kuwa KB wayarsa ya dauka ya kira Haris
dake shirin tayarda mota zuwa gidansu Daddy
don tafiya. Kamar bazai dauka ba sai kuma ya
dauka da sallama.
Kb ya amsa yana yar fara'a kafin yace
"Wani tsastsauran laifi nayi da har dan uwana
kuma aminina ya kasa sanarmin da batun
aurensa har haka? Inda aminci kamata yayi ma
ace a bakina Princess(yasmeen) zata soma ji ba
bakinka ba. Haba Haris,abun har yakai haka?
Allah ma munayin laifi gareShi ya gafarta mana
ballantana dan adam?"
Ya karashe a sanyaye gwanin tausayi domin
hakikanin gaskiya KB yana kaunar Haris kwarai
dagaske,kauna ce mai tsafta tun suna yara suke
yiwa juna. Jin yanda ya narke murya yasa Haris
sauka daga fushinsa,shima cikin sanyin murya
yace
"Dan uwan nawa ne ya kasa saita rayuwarsa,ya
kasa fahimtar hatsarurrukan dake cikin sab'awa
Ubangiji. Banda wannan babu wani abu dake
had'ani dashi."
"Oh come on my friend,tuni na watsar da wannan
hanyar wallahi. Just ita ke wahaldani ga kuma
fama da rashin sanin inda take amma daman
banda ita komai na watsar. Ka tayani addu'a."
Murmushi Haris yayi na mugunta
"Bakomai,itama zaka mantata har abada in sha
Allah. Zan tayaka addu'a. Barni hakanan,Daddy
suna jirana."
"Toh ango,yaya sunan matar.."
Kafin ya karasa Haris ya katse kiran yana
murmushi
"Da sauran lokaci Kb,bazan amince ka rusamin
komai ba."
Daganan yayi ribas ya fita kasancewar tun
shigarsa mota isah ya wangale gate din.
*****
Rashin samun wadataccen bacci da kuma
matsanancin kukan da baby tasha a daren ya
janyo mata ciwon kai matsananci da zazzabi
wanda ya sanyata lafkewa saman darduma tun
bayan sallatar Asubahi da tayi. Gwaggo Hajara
tayi shigowa dakin wajen sau biyar amma bata
tashi na gashi har rana tayi sosai domin lokacin
wajejan karfe sha daya na rana. Ganin bata da
niyyar motsawa ne,yasa Gwaggo tashinta
"Wai lafiyarki kuwa 'yar nan? Wane irin bacci
kikeyi hakane?"
Jin muryar Gwaggo yasa baby bude ido kadan,
ganin yanayin baby yasa ta taba wuyanta
"Ikon Allah wannan bandejin kuma fa na kanki?
Jiya dankwalin kanki bai barni na lura ba,ga
jikinki da zafi ashe masassara kikeyi baki fada an
nema maki magani ba? Bari na aika kemis din
Abdulaziz a amso maki magani. Kokarta ki tashi
ki sanya ko kunu a cikin naki."
Ta karashe tana kokarin mik'ar da Tasleem
zaune,dakyar ta mike tayi azamar rike kanta
sakamakon sarawar da yakeyi.
Ta daure ta wanko bakinta ta dawo tasha kunun
kadan,saidai fa tuni cikinta ya hau murd'awa
saida ta ruga bandaki ta amayar dashi tas!
Gwaggo na mata sannu. Bayan ta kamota sun
fito take fadin
"Haba jama'a,ana kokarin yi maki gata amma
kina facali da damarki? Harisu yaron arziki ai ba
abun gudu bane."
Ita dai tasleem batace uffan ba,da gwaggo zata ji
labarinta da bata amince da aurawa namiji irin
Haris 'Yar Bariki ba. Dakyae ta iya hadiyar
magungunan ta sha ruwa sai kuma bacci ya
dauketa a saman gadon bayan ta ja bargo ta
kudundune jikinta saboda sanyin da takeji yana
damunta duk da kasancewar rana ake kwalawa.
******
"Kace ashe harisun sun iso kenan?"
Tambayar da taji Gwaggo na yiwa wanda batasan
ko wanene ba. Tashinta daga bacci kenan,ba laifi
zazzabin ya d'an sauka saidai ciwon kan.
Batasam takamaiman karfe nawa ba saida taji
muryar Baharu na fadin
"Ya iso gwaggo,shiyasa Baffa yace nazo nayi
kiranta su gaisa."
"Toh ai shikenan,bari na gani ko jikin nata yayi
sauki."
Jin gwaggo na kokarin shigowa tayi saurin
mayarda idanunta ta rufe gabanta na bugu fat
fat......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(58)
Ta taba goshinta taji sanyi radau wanda ya
tabbatar mata da saukar zazzab'in. A nutse
gwaggo ta hau bubbuga kafarta
"Tasleem,tasleem."
Ta bude ido sannu sannu kamar mai baccin
gaske.
"Na'am gwaggo."
"Sannu ko? Ya jikin naki?"
"Alhamdulillah."
"Haka nakeson ji,maza daure ki tashi,Baffa ya
aiko kiranki ku gaisa da bak'i."
Kamar zatayi kuka tace
"Banjin dadi fa gwaggo."
Gwaggo ta hau lallab'ata
"Haba d'iyata,meyasa bazaki kasance mai hakuri
a rayuwa ba? Babu amfanin bijirewa maganar
manya. Ki tashi kije ai ba auren kikaga anyi ba.
Mu dage da addu'ar zab'in Allah."
Haka tayita kashe mata jiki da maganganu,Baby
ta mike ba don taso ba.
"Toh nidai ki sanya a daukomin akwatina sai nayi
wanka."
Gwaggo tayi dariya
"Ai shikenan babu komai d'iyata ta kaina. Shiga
kiyi abinki don ma kayana bazasuyi maki ba ai da
shi zan baki."
Murmushi baby tayi kafin ta soma kwab'e kayan
jikinta.
****
Ta fito wanka sai kuma ta rasa suturar sanyawa.
Manyan kayan daman kala biyar ne. Uku
atamfa,biyu kuma shaddoji suma kyautarsu akayi
mata. A karshe dole ta dauki daya cikin shaddojin
nan ta sanya ba don taso ba. Shaddar brown
ce,tasha surfani anyi mata riga fitet hakanan skirt
din yayi d'as a jikinta saidai hakan bai boye 'yar
ramar da tayi ba. Ta sanya dankwalinta tayi
dauri wanda ya rufe bandejin kanta,ta kudurta
suna tafiya zataje kemis a fidda mata.
Kai kuzo kuga baby acikin hadaddiyar shaddar
nan. Batayi kwalliya ba kwata kwata,toh auren da
bata murna da yinsa kuma ma me zata nunawa
Haris bayan shi d'in daban ne a komai. Ta fesa
turaruka masu fisgar hankali wanda har gwaggo
dake waje saida tayi mata magana
"Kai tasleem,turaren nan kodai na maza ne? Kibar
amfani da turare mai k'arfi haka kina mace."
Batace komai ba ta maida ta ajiye,ita kam anya
zata iya daina shafa turare? Da kamar wuya don
ma'abociyar son kamshi ce. Ta zura takalminta
sai kuma ta rasa mayafi. Kawai saita janyo na
mamma da tun zuwanta take yafawa ta yafashi.
Gwaggo Hajara ta dubeta tana zabga murmushi
sadda ta fito
"Ko babu kwalliya kina da kyawunki diyata ta
kaina saidai muje na baki wani mayafi ki sanya
wannan ya tsufa da yawa."
Murmushi kawai baby tayi gabanta bai bar bugu
ba,taji kwallah ta taho mata saidai tayi azamar
maidasu. Baharu ya shigo karo na biyu yana
sallama ta amsa. Baki ya washe
"Antina wallahi kamar bake ba. Kullum k'ara kyau
kike."
Ta d'an harareshi ya kyalkyale da dariya
"Kamar kinsan kuwa surukan naki ne ya
tambayeki shine nace bari na turo masa ke."
Surukanta? Ta nanata a ranta,ita fa jikinta yana
k'ara yin sanyi. Mamaki takeyi ace wai Haris ke
sonta,haka kawai tsoronsa yayi mata dirar
mikiya. Tunaninta ya katse sa'ilin da gwaggo ta
fito rike da wani mayafi kalar ruwan madara(wato
surfanin dake jikin shaddar)
"Fiddo wannan ki yafa wannan."
"Kai gwaggo ashe kinsan kalar gayu." Cewar
Baharu. Baby dai kamar kurma ko don bata fiye
son yawan magana bane? Oho. Amma batace
musu uffan sai murmushi na dole.
Suka jera Baharu yana bata labarin yanda
surukan suka yaba da wannan auren ji sukeyi
tamkar a daura auren ma a yau.
"Wallahi anti angon nan naki burgeni yakeyi kana
ganinsa kaga dan boko kuma wayayye amma ko
kusa bashi da wulakanci ko girman kai. Kunyi
bala'in dacewa dashi wallahi."
Ta dubi Baharu zatayi magana ta fasa
sakamakon ido hudu da sukayi da Haris ya fito
yana amsa waya. Sanye da manyan kaya amma
babu babbar riga, kansa sanye da hula. Sai taga
yayi mata kyau da kwarjini sosai,shi kansa
Baharu saida yaga yayi mishi kwarjinin. Ya daure
fuska yana mai kauda kansa yana mai juya musu
baya ya cigaba da wayarsa da alama dai da
kanwarsa yakeyi. Ta sunkuyar da kanta yayinda
kwallah suka cika mata idanuwa. Daman tasan
ba sonta yakeyi ba. Har suka is a daf dashi bai
bar wayar ba hakan yasa tayi cikin gidan,zata
karasa can wajensu inna,Baharu ya dakatar da ita
da cewa
"Ki soma shiga suna nan d'akin fa anti."
Ta gyada kai kawai,gabanta na faduwa tayi
sallama. Dukkansu suka amsa kafin ta shiga
kanta yana k'asa. Su kuwa su Abba ganin
surukar tasu nan da nan fara'arsu ta k'aru bare
ma Malam Hussein wanda yaji tamkar diyarsa ce.
Ta gaishesu a ladabce,suka amsa kafin ta
tambayesu hanya. A karshe Malam Hussein ya
kara jin ta bakinta sannan yazo mata da batun
cewar ba ita kadai Harisu zai aura ba(kamar
yanda suka zauna sukayi zancen da yaransa
abba da daddy da hajja kubra,Haris ya amince da
hakan ga mamakinsu. Itama Zahra tayi na'am
tana mai farinciki saboda son da takeyiwa Haris
mai girma ne.),hankalinta ya tashi jin wannan
zancen. Saidai ta daure tunawa da nasihar
gwaggo tace ta amince da bakinta. A karshe suka
sanya mata albarka ta mike ta fito kanta na
k'asa suna zubar hawaye. Jikinta kuwa rawa
yakeyi gabanta na dukan tara tara sakamakon
tunanin daya darsu a zuciyarta na cewar lallai
d'osanawa Haris ita akayi,daman Zahra yakeso.
Tana kokarin sanya takalminta amma jikinta rawa
yakeyi,ta dunguro zata fad'i tayi azamar kai
hannu da niyyar dafe bango saidai taji ta dafa
hannun mutum. Da sauri ta dago idanunta ya
sauka akan kyakkyawar fuskarsa,taja baya bayan
ta sakeshi.
"Sorry." Ta furta murya na rawa,ya matso saitin
kunnenta ya soma magana
"Kina tsammanin sonki yasa na amince zan
aureki ne Tasleem? No! Lik'amin ke akayi,ni
kuma babu yanda na iya na kaucewa maganar
magabatana. Zahra itace zab'ina! Abar kaunata!
Zan aureki bisa kaddara kawai!"
Ta juyo da sauri, ganin numfashinsu na gogar
juna tayi azamar ja da baya tana kallon
fuskarsa,murmushin mugunta kawai yakeyi mata
a zahirin gaskiya kuwa daurewa kawai yayi domin
cin zarafin dan adam baya daga d'abi'arsa. Ya
daga mata gira yana murmushi
"Idan kinga zaki iya,muje zuwa toh..."
Daga haka ya wuceta ya fita ya fasa shiga dakin
ma. Kawai tayi ciki a guje takalmin da bata
sanyaba kenan...!!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(60)
Takai mintuna biyar kafin ta kammala saidai kuma jin yanda hayaniya da shewar murna ta cika dakin inna ya hana Tasleem fitowa yayin data kifa goshinta jikin kofar bandakin tana rusar kuka. Ta tabbata an daura aurenta da Haris akan sadaki dubu hamsin. Shikenan Haris ya samu damar wulakantata da cin zarafinta. Yan uwanta sun kasa fahimtar Haris ba kaunarta yakeyi ba. Ta bandakin tana jiyo muryar Baharu yana labarta musu cewar ai Haris ne ya nemi a daura auren a yanzu,Abba(alhaji Aliyu,mahaifinsa) yana fadan wane irin gaggawa ne haka? Liman yace hakan shine daidai tunda gashi an hadu domin har mijin Mamma,Dad yana wajen wanda shine ya zama wakilin tasleem aka daura auren kawai. Zahra ma an daura saidai an bar tarewar sai nan da wata daya bayan an kammala shirye shirye. Nan dakin ya dauki kabbara cike da sowar farin cikin jin wannan labari. Tana jin sadda d'iyar Dada(dada matar kanin Liman daya rasu take zaune gidan) wacce take zawarci sakamakon mijinta daya rasu da jimawa,wato Hafsa ta tahowa tana buga kofar tana fadin
"Fito kin kunshe kanki a bandaki,komin abunki fa sai mun murjeki da lalle." Aka kwashe da dariya kafin dai kowa ya tattara ya fice. Saida taji shiru sannan ta fito, ji tayi an rukunkumeta ana dariya
"Ja'ira,ai daman nace sai na ga fuskarki." Cewar Hafsat. Tasleem tana kuka tace
"Anti Hafsa kina kallo aka auramin wanda baya kaunata baya sona? Anya ba'a kwareni ba?"
Jikin Hafsa yayi sanyi,ta ja hannunta suka zauna bakin gado
"Haba Tasleem,kinga yanda yake rawar kafa da wasa da dariya kuwa? Anya zan amince baya sonki? Kodai kece bakya sonshi ne?"
Tasleem tayi shiru da kukan,toh tana da bakin cewa batason mutumin da tun zuwanta Kazaure dashi take kwana take tashi a zuciyarta? Tabbas tana son Haris. Banda Rilwan bata taba son wani d'a namiji ba da zuciya daya sai shi.
"Kinyi shiru?"
Inna dake jinsu tace
"Ki rabu da wannan sakaryar wacce batasan abunda ya dace gareta ba. Nikam takaicinta ma yana sanyani jin kamar na kwasheta da mari."
Hafsa taja hannun Tasleem sukayi hanyar fita zuwa dakinta tana fadin
"Ayi hakuri innarmu,kinsan sabon shiga."
Inna ta tabe baki suka nufi dakin Hafsat. Ita dinma rarrashi da ban baki gami da gwada mata hanyoyin kissosi da zata bi domin mallakar zuciyar Haris cikin sauki. Tasleem dai sauraronta kawai takeyi,wannan ba matsalarta bace,babu wani abu na fannin kissa da bata kware dashi ba saidai Hafsa ta gaza fahimtar matsalarta. Ita fa kalaman da Haris keyi mata ne yake daukar hankalinta.
"Nan zuwa sati biyu za'a kawo lefenku. Aurensa dake aka soma d'aurawa sannan kuma da Zahra. Kinga kenan matsayinki ta babba dole saikinyi hakuri kin rike girmanki koda dai Zahra bata da raini yarinyar akwai hankali da nutsuwa ba kamar su Atika ba. Duk da haka sai kin dage."
Haka dai sukayita hirarsu har Hafsat take bata labarin zaman hakurin da tayi da facalolinta wanda yasa Tasleem sakewa sosai. Sallamar Musty ta katsesu. Ya shigo suka hada ido da Tasleem yayi mata murmushi a sanyaye
"Babana ya akayi?" Cewar anti Hafsa kasancewar sunan kanin Liman yaci kuma mahaifi gareta. Hakanan mustapha jikan Dada ne mahaifiyarta sannan shi din maraya ne gaba da baya a hannun Dada ya girma har zuwa aurensa da Farida.
Ya zauna saman hannun kujera yana yamutsa fuska
"Ina fa lafiya kuna ji kuna gani an kwacemin matata." Duk suka dubeshi Tasleem kuwa saita dauki abun wasa ashe Antin ma wasa ta dauka jin tayi dariya tace
"Me zatayi dakai yarinya yar birni.?"
Ta fice daga dakin,Tasleem ta gaidashi yak'i amsawa
"Small ashe zaki iya auren wani ba ni ba?"
A mamakince ta yamutsa fuska kadan kamar bazatayi magana ba sai kuma tayita tamkar bataso
"Wai daman kana sona ne yaya?"
Musty ya ciji lebbansa cike da takaici
"Tun kina secondary nake dawainiya da sonki. Allah bai kaddaro ke zam fara aure ba sai Farida. Yanzu kuma gashi ina murnar dama tazo min sai kawai na tsinci labarin aurenki da wannan gayen."
Ya danyi shiru itama tausayinsa takeji,
"Haka Allah Ya kaddaromin. Allah Ya baki zaman lafiya da mijinki. Saidai ina fushi har yau gashi satinki daya cif a garin nan baki tako kinga matata ba shiyasa nima duk da dokin ganinki da takeyi domin ina yawan bata labarin sister dita mai sona amma na hanata zuwa."
Ya karashe a wasance,itama ta share wancan zancen watakila dai ya tuna a yanzun matar aure ce,
"Kayi hakuri dai yaya mustyna,zan shigo."
"Ai na mantaa yanzun saida iznin oganki ko?"
Gabanta ya fadi,ashe yanzu komai zatayi saida iznin Haris? Tab ai kuwa ta gwammace tayi ta zaman gidan gashi tana matukar son komawa wajen mahaifiyarta domin ta kara neman afuwarta.
"Bari na wuce."
Ya maidota daga kogin tunanin data shiga,ta dubeshi har yakai kofa
"Toh yaya saida safe." Itama ta mike ta koma dakin inna. Sallar isha'i kawai tayi kafin tayi zaman hira da inna. Sai ga Liman ya aiko kiranta. Ta iskeshi babu kowa a dakin sai shi. Nan yayi mata doguwar nasiha akan aure da nuna mata ita din yanzu fa karkashin ikon Haris take sannan ya gargadeta data dunga mutunta shigarta. A karshe ya damka mata sadakinta tace ita yanzu bata da abunda zatayi dashi,ya adana mata. Yace shikenan. Ta mike ta fita, zatayi ciki taji muryar Baharu a bayanta yana kiranta dole ta tsaya ta dubeshi ta lura dai d'asawa yakeyi da Haris sosai. Leda ya mik'omata yana dariya
"Gashi inji maigidanki."
Ita kam duk sadda aka dangantata da Haris sai gabanta ya fadi,tasa hannu ta karba babu ko godiya tayi ciki.
Waya ce da chajinta da komai,sai kwalinta da alama harda sim. Blackberry ce. Sai kayan ciye ciye, nan inna ta hau duddubasu tana fadin oh,abun dadi basu karewa a duniya. Wayar tayi k'arar shigowar sak'o. Ta bude ganin lamba.
"Ga waya nan,ban amince ki bawa kowane namiji damar mallakarta ba ke daidai da dan uwanki banda Abdullah banason ganin lambar kowaye!
"Harith"
Ta tabe baki ai shi d'inma bazaici darajar saving number nasa ba a wayar. Ta ajiye wayar ta mike domin watsawa kanta ruwa haka dai inna ta dauka tayita kalle kallenta tana fadin yanda wayar ta burgeta kwarai.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(59)
Cikin fushi inna ta ture tasleem daga jikinta
"Ke ni matsamin kibani wuri shashashar banza kawai! Aure hauka ne? Don za'ayi maki gata ke kuma kin kasa fahimta? Toh wallahi ba baki zanyi maki ba Tasleem,amma matukar kika bari batun auren nan naku ya rushe da yaron nan zaiyi wuya ki samu madadinsa. Ke kamar wata yarinya karama,a hakan ake cewa kinyi degree? Amma tabbas bakiyi kama da matan jami'a ba sam sam baki da wayewa. Mts. (Hhhh kuji fa! Baby ake fadawa duniya..cewar Rufaidarh)
Ta dago ta dubi inna dake faman zazzaga masifa
"Shi da bakinsa fa yace baya sona lik'a mi.."
"Kina nufin Liman k'arya yayi maki?"
Ita dai batace uffan ba,ai sai fadan inna ya k'aru karshe tace bazata iya ba saita had'ata da mamma. Sai kuma tayi shiru kafin ta kara cewa
"Allah Ya kyauta,namanta ashe ita dinma daren jiya tazo tana surutanta wai don me za'a yiwa Harisu haka? Saida na zageta tsaf na nuna mata kurenta sannan tace shikenan. Haka kawai kunbi kun tsani yaro na arziki ma."
Haka dai inna ta mike ta fice bayan ta dauki furar data kammala damunsa zata bayar a mik'awa bak'i.
Baby ringingine ta kwanta ta lumshe ido yayinda kwakwalwarta ke k'ara tunano mata bakaken maganganun Haris daya jefa mata. Zarginta ya tabbata kenan ba sonta yakeyi ba? Zahra,Zahra? Wacece ma hakan?
'Yar farar yarinyar nan dai siririya mai siririyar fuska. Kallo daya zakayi musu ita da Haris ka tabbatar da cewar jini d'aya suke saboda matukar d'ibar kamar da sukeyi da juna. Bata da mazauna sosai hakanan kirjinta baida cika sosai.
Tabbas ta tuno Zahra, itace dai wacce tayi mata rakiya gidansu KB. Murmushi kawai tasleem tayi tunawa da sanyin halinta. Babu ruwanta watakila shine dalilin da yasa Haris ke sonta. Kaico da rayuwarta,ita kam ba abun ta samu su Baffa ba tace bata kaunar auren nan.
"Taso kije Harisu ya aiko kiranki."
Ta bude idanuwanta sosai jin muryar inna. A sanyaye ta mike,ita fa batasan dalilin da yasa take shakkar Haris ba,kai bata taba kawowa bama zataji tsoron wani d'a namiji ba sai Haris.
"Don Allah ki mutuntashi babu kyau wulakanta mutum."
Murmushi tayi mai ciwo,ta mike ta dauki mayafinta ta fita bayan ta zura silifas. Ta nufi zauren saidai bayanan,ta karasa waje gabanta na dukan tara tara. Hon da taji ya tabbatar mata cikin motarsa yake, hakan yasa ta karasa kafin ta bude ta shiga. Bazata mance motar nan ba a tarihin rayuwarta,motar data fayyacewa Haris komai na sirrin rayuwarta?
"Baki iya gaisuwa bane ko kuwa dai rashin tarbiyya zaki gwadamin?"
Ta kalleshi
"Haris wai menayi maka hakane? Haris ka chanja ba haka...."
Kallon daya watsa mata shi ya sanyata yin shiru.
"Ba wannan na tambayeki malama."
"Barka da yamma."
Ya tabe baki kadan
"Rike abinki tunda rok'a nayi. Abunda nakeson sani shine,kinga period naki?"
Ta kauda kanta ga barin kallonsa
"Da asuba nayi wanka."
"Kina iya tafiya."
Shiru na mintuna,ganin bata da niyyar motsawa yasa shi saurin fita ya rabu da ita a motar. Tana kallonsa ya koma ciki,hawayenta suka kara kwaranyowa karo na ba adadi,toh zaman me takeyi kuma? Kawai saita bude ta fito itama.
*****
"Ayyiriri yiriri! Kai Alhamdulillah. Harda na Zahra?"
Batasan lokacin da cikinta ya murd'a ba,me kunnuwanta ke shirin ji mata ne? Innalillahi wa inna ilaihiraaji'un!
Da azama ta nufi bandaki domin rage cikinta......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar
(61)
Washegari wajejan uku na rana,mutan gidan basunan sunje gaisuwa acan k'asa gidan wani almajirin Liman wanda ya rasu sakamakon hatsari. Tasleem ce zaune a tsakar gidan cike da tunanin kawayenta. Tunani takeyi ko Manal tayi aure? Toh Dalal da Hibba fa ya suke? Tunanin neman layin Hibba ya fadomata. Bata mantawa saboda saukin lambar wayar Hibba ta haddaceta a kwanyarta har akwai ranar data taba karantowa sukayita mamaki har hibbar domin ko ita bata da haddar lambarta aka. Da azama ta mike tayi daki,wayar dai data tsana ita ta dauko ta dawo ta zauna. Ta duba akwai kud'i har dubu daya a ciki. Baki ta tab'e wannan kam a wurinta karamin kudi ne bazai burgeta ba. Batason wulakanci a rayuwa. A nutse ta jera lambar ta kira. Akayi sa'a ta hau ringing.
Hibba alokacin tana zaune a gefan ruwan Tiga Dam ita fa sabon saurayinya,HAYAT. Tunda ta soma bariki bata taba tsintar kanta dumu dumu cikin soyayyar wani d'a namiji ba illah Hayat. Matashi mai ji da naira da hutu. Ganin unknown number yasa ta jan tsaki ta ajiye wayar. Hayat ya dafa cinyarta yana kasheta da kallon kauna
"Lafiya dai my beb."
"Wata number ce da bansan da zamanta ba."
Acan kuwa baby tsaki taja sai lokacin ta tuna ko ita akayi kira da unknown no.a wayarta bata fiye dauka ba. Ta yanke shawarar tura sak'o.
"Hibba,it's me Baby. Pick d call."
Tana shirin turawa yayi sallama ya sanyo kai. Ta amsa bayan tayi saurin ajiye wayar a gefe. Hankalinsa yayi kan wayar cike da zargi kafin ya basar ta hanyar fad'in
"Ina mutan gidan?"
Itama fuskarta ba yabo ba fallasa saidai kirjinta sai bugu yakeyi.
"Basunan sunje gidan gaisuwa."
Bata ankara ba taga yasa hannu ya dauki wayar yayi tsai yana karanta sak'on....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(62)
Fuskarta a tamke baisan sadda ya daga wayar ya bugata da bango ba kafin ya fisgo Tasleem wacce ta mike tsaye ganin yanda ya yiwa wayar. Murde hannunta tayi ya komar dashi ta bayanta,har suna shakar numfashin juna ita kam na tsoro ne. Tayi ta murza hannun saidai fa iyaka yatsunta ne don kuwa ba rikon wasa ta samu daga wajen maza ba.
Cikin kakkausar muryar da batasan Haris da ita ba yace
"Menene gaminki da ita a karo na biyu?! Me kike shirin yimin? Daga yau ki sani cewa banason mu'amalarki da kowace abokiyar shaidancinki ta baya! Wannan shine gargadina a gareki na karshe."
Daga haka ya saki hannunta,tayi saurin ja baya tana zubar hawaye. Ta dubeshi ido cikin ido kallon nan na alamar tambaya(Kaine kuwa?..lol). Ya kauda fuskarsa,har ya juya zai fita kuma ya dawo baya ya dauki wayar wacce tuni screenface dinta ya tsage,sim d'in ya fidda kafin ya cilla wayar jikinta daga haka yayi gaba cikin takunsa kamar wani basarake.
Ta dubi hannunta wanda har yatsun Haris sun bayyana jikinsa,kafin ta lumshe ido ta zauna d'abas akan sumintin tsakar gidan tana kuka. Karshe dai mikewa tayi ta dauki wayar tayi daki. Jimawa kadan taji sallamar Baharu,bata ko fito ba har ya shigo ya miko mata simcard sabo.
"Gashi inji angonki,yanzun nan suka wuce. Yace ki sanya a wayarki zai kiraki."
Bata ko kalleshi ba ballantana yasa ran zata karb'a,ganin shiru ya ajiye ya fita yana mai jin haushin yanda antin nan tasa ta kasa gano kaunar da Haris keyi mata.
*****
Tsaye yake a farfajiyar hotel din na Nicon dake birnin tarayyar Abuja yayinda yake cike da farin ciki da walwala na ganin wacce bai taba tsammatar ganinta ba a wannan lokacin. Ta karaso bayan ta cewa wacce suke tare tayi jiranta minti biyu. Ta wulka ido irin na kwararrun 'YAR BARIKI kafin ta sakar mishi murmushi wanda ya kara fiddo zahirin kyawunta na asalinta na buzuwa.
"KB manya daman ana ganinku?"
Kb yayi yar dariya
"Gaisheki DALAL,kun b'ata b'at a garin ta dabo. Ashe kina nan kina holewarki."
Dalal tayi dariya
"Kai haba,mu a suwa? Kaine dai gakanan sai fresh kakeyi,nikam tunda mun hadu yau bazan bari ka gudu ba saika kaini na gaisa da k'awarmu. Wallahi just one week kenan da bamu ganta ba amma kewarta ta cikamu."
Cikin rashin fahimta yace
"Wai Dalal kuna zaton Baby tana tare dani ne?"
Tayi k'as k'as da cingam tana kallonsa shek'ek'e
"Bangane manufarka ba KB? Wai bakwa tare da Baby? Toh ina take?"
Yayi wani d'an malalacin murmushi kafin ya zura hannu aljihun wandon jeans nasa. 'Yan dubu dubu ne da baisan ko nawa bane ya zaro da d'an kaurinsu ya mik'a mata
"Idan basu isheki ba kiyi magana na k'ara maki Dalal,fatana da burina bai wuce ki taimaka wajen lalubomin inda kawarku take ba. Ko kuma idan kinsan wani labari game da rayuwarta please ki sanarmin sauran binciken zanyi da kaina."
Ta shinshina kud'in,ita kam ai kud'i koyaushe basu tsufa awajenta sabbi ne. Ta tura a jakarta bayan ta tuno da Manal data tab'a tabbatar mata cewar ita kadai tasan wacece baby da kuma garinsu saidai bisa amana ta gayamata ita kam bazata fadawa kowa ba.
"Aikinka zai cika muddin zaka saki kud'i Hajy KB."
Shima kallo yakeyi mata na kwararren 'Dan Bariki,kafin ya shafi sumarsa yana dariya
"Ba abune mai wuya ba,kina iya bani acc.no dinki hade da phone.no."
Ya amsa kafin suyi sallama ya shige don gabatar da abunda ya kawoshi cike da matsanancin farin ciki....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(63)
A gajiye ta k'arasa kujerar tangameman falon wanda yaji kayan alatu ta zauna tana fadin wash! Manal ta zube gefanta suna dariya
"Shegiya Dalal,kina cin karenki babu babbaka nikam ina nan kamar kullin kayan wanki. Ke a yanda na lura anya kuwa Alhaji Ubalen nan idan munyi aure zai barni na fita wani wajen? Mahaukacin kishi gareshi,ji fa dai daga maganar aure har ya killaceni gidansa,babu wata harka wai yana bukatar nayi istibra'i,mts."
Dalal ta mike zaune tana dubanta bayan ta kyalkyale da dariya
"Kefa baki fahimci wannan d'an fulanin naki ba,toh wallahi dagaske yakeyi sonki yakeyi da gasken gaske."
Ta tabe baki
"Barshi dai yayita haukansa,wani sa'in ni kaina ina jin kauna da tausayinsa wallahi ya iya lallab'a mace ne. Ke nasa fa an bincikamin asalin aurensa da matarsa,ashe dole yabi umarnin mahaifinsa ya aureta har yanzu da suke da yara biyar bai taba sonta ba. Kinsan fa ba wani shekaru ne dashi ba,arba'in da wani abu yake."
"Yara biyar? Kuma ace ba soyayya? A ruwa tasha?"
Manal ta harareta da alama maganar ta bata ranta,Dalal kam murmushi tayi gami da jin tsoron auren wata uku ya koma na har abada....
"Wai kuwa kina samun Baby a waya? Nasha nemanta naji switched off."
Jin an ambaci Baby ya tunasar da Dalal abunda ya kawota. Ta zabura ta matso kusa da Manal har tana firgitata.
"Ke nima bansan inda ta lulluk'a ba,anya ba garinsu ta koma ba?"
Manal tayi shiru tana tunani,daman tun sadda baby ta fito da shigar hausawa jikinta ya bata cewar Kazaure zataje.
"Gayamin sunan garinsu mana,kinga sai na gano mana ko lafiya?"
Cewar Dalal,Manal ta numfasa
"Banason karya alk'awarin dana daukarwa baby na cewar bazan sanarwa kowa ba game da garinta ko asalinta,wannan shine..."
"Haba Manal, bamusan halin da take ciki ba,idan ance ma tana bukatar taimako babu k'arya a ciki. Idan kin fadamin wa zan gayawa,just give me full address ni kuma zan binciko mana lafiyarta koda a b'oye ne. Kinga idan bata garin sai mu sanya cigiyarta ko kuma mu bi abokan harkarta gaba daya tunda ba wani yawa garesu ba muji ko suna tare."
Manal tace "KB fa?"
"Basu tare da KB,domin kuwa Momy tace min yazo nemanta wajenta amma bai sameta ba."
Dalal tayita siyasance Manal har saida ta samu ta shawo kanta tayi na'am da hakan batare data bata ko sisin naira biyar ba. Duk da dai Manal bata da tabbacin baby can tayi amma bata zaton zata je gidan yayanta da mahaifinta domin a yanda ta nunawa Manal ba karamin tsana tayi musu ba,mammanta ce ma take son sanyata ido wataran.
Ta gayamata ta rubuta.
"Idan kinje Kazaure ki nemi gidan babban limamin garin, nan ne gidan da nasan watakila ki samu labarin Baby."
Bayan ta gama rubutawa,Dalal ta tuntsire da dariya
"Amma Baby anyi shegiyar yarinya. Don ubanta ita daman d'iyar Liman ce take bura uba haka?"
Manal ma dariyar tayi,saidai tsoron kada Baby ta kamata da cin amanarta yasa bata gayawa Dalal cewar gidan kakannin baby ne ba ta wajen mahaifiyarta. Da zataji waye uban baby,zata fahimci cewar lallai Baby ta ketaresu kota ina tunda ba kudi ne ya fiddota bariki ba.
******
Kishingide yake a kujera mai zaman mutum uku,Yasmeen tana gefe tana mammatsa mishi kafafuwa yayinda ya maida hankalinsa ga kallon Ball. Wayarsa tayi k'arar shigowar sak'o
"Mikomin wayata."
Ya fada ba tare daya dauke idanunsa daga kallon ba. Ta dauki wayar ta mik'a masa. Ganin sak'on daga Dalal ne,ya sanyashi mikewa zaune.
"Kazaure gidan babban Liman,duk wanda ka tambaya za'a kaika. Idan kaje babu nasara zan k'ara bincika mana."
"Wuuu!"
Shine ihun murnar da KB ya saki. Yasmeen ta iso gareshi
"Lafiya prince?"
Ya mike ya dagata sama yana juyi da ita suna dariya. Babu kamar Yasmeen wacce take jin mamakinsa da kuma farin ciki. Yaushr rabon daya kula da lamarinta haka? Kai a ranar dai ya faranta mata fiye da tsammaninta. Shi kuwa Allah Allah yakeyi weekend yayi yaje ga Baby shi koda bai ganta bama ya samu shiga wajen liman. Domin kuwa yasan kwarai wanene Liman saidai bai taba kawowa shine uban tasleem ba. Har ya soma mamakin abunda zaisa Tasleem wacce ta fito gidan manya haka ta b'ata rayuwarta da barikanci. Meyayi zafi haka toh?
******
Karshen sati nayi,ya yiwa matarsa sallama da sunan zaije Kazaure gaida kakanninsu. Taso ya tafi da ita saidai koda ta matsa da magiya ya bata rai a dolenta ta hakura tana ji tana gani yayi mata sallama ya wuce airport domin hawa jirgin zuwa Kano.
Tunawa da tayi cewar tun angoncewar yayanta bai nemeta a waya ba yasa tayi kiransa. Yana dauka ta soma shagwaba murya
"Haba yayana ashe daman akwai sadda zaka share lamurana? Nikam har na soma fushi da yayyuna nasan waya dasu ya janyo ka shareni."
Haris dake kwance akan gado kawai yana hutawa domin ya jima da tashi daga bacci,darem jiya sun sha waya da Zahra wacce babu laifi ta samu gurbi sosai a zuciyarsa duk da dai karfin hirar itace shi kam yakan rasa abun cewa saidai ta jefo mishi tambaya.
"Kiyi hakuri small,ban manta dake ba. Ai babu matar da zata mantar dani ke. Ya kuke? Ya dotana?"
Yasmeen tayi dariya
"Gatanan tana tsalle tsallenta,babanta ma yanzu ya tafi Airport zai wuce Kazaure idan ya sauka anan Kano. Wallahi naso ya taho dani naga amare amma yak'i."
Tunda Haris yaji wai KB ya taho Kano zaije Kazaure yaji bacin rai matuka ya dirar masa. Bazai fa amince da wannan sakarcin ba,ya dace tun yanzu ya sanyawa lamarin burki.
"Hello." Cewar Yasmeen jin yayi shiru.
"Small,bani mintuna." Ya katse kiran ya mike zaune yana mai zuro kafafunsa k'asa. Dabara ce ta fadomishi na kiran Mamma. Matar da tunda ta ganshi ta nuna mishi kauna hakanan sun jima a falonta su biyu suna tattaunawa game da Tasleem sannan ya nuna mata komai dangane da lamarinta ya sani. Har kwallah tayi don farin cikin jin cewar yaji ya gani yana son diyarta zai iya aura. Bayan sun gaisa yace yanason Nura yaje ya dauko Tasleem a mota harda kayanta ta zauna a wajenta. Mamma ta tambaya ko lafiya. Bai sanar mata ba saidai yace akwai 'yar matsala ne. Tace bakomai zatayi hakan.
Tasleem tayi mamakin ganin Nura yazo wai Mamma da kanta ta nemi komawarta gidanta. Har inna tana fada wai Mamma babu ko kara,bata tambayi ko da iznin Haris ba ko Aa saboda taji Nura yace shine yayi kira. Hakanan ta hau mota,Nura yaja suka nufi gidan Mamma sai tambaya takeyi Mamma da fara'a tayi maganar zuwanta ko a'a shidai Nura tun yana amsawa har tambayoyin sukayita bashi dariya ma.
******
KB yana dira a Kano,direbansa ya kaishi gida. A gaggauce yaci abinci yayi wanka sannan ya saka kananun kaya. Jakar kayansa ya dauka ya saka a mota. Jeep dinsa ya dauki yayi hon Maigadi ya bude.. Sai Kazaure......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(64)
Hankalin Haris bai kwanta ba har saidai ya lalubi layin baby saidai baiyi mamakin jinsa a kashe ba yasan tayi fushi tak'i sanyawa ne. Wannan yasa ya k'ara nemanta ta hanyar layin Mamma. Ya sanarwa Mamma yanason magana da baby. Ta mik'awa Tasleem lokacin tana zaune anan gefen Mamma suna 'yar hira don babu laifi ta sakarmata.
"Sai ki tashi ki shiga daga ciki mijinki ne."
Ta mike ba don taso ba wayar na hannunta. Saida ta zauna gefen gado sannan tayi mishi sallama. Ya amsa ciki ciki
"Kina jina ko? Kb yana hanyarsa ta Kazaure."
Tabe baki tayi,ai daman tasan ko ba dade ko ba jima sai KB ya samu labarin inda take tunda har yasha alwashin nemanta ruwa a jallo.
"Ya akayi yasan da zamanki a Kazaure?"
(Ya fadi hakan da niyyar bugar cikinta duk da bashi da tabbacin saboda ita Kb zaije Kzu.)
Cikin rashin fahimta tace
"Kana zargina ne da gayawa KB inda nake Haris? Ko ka mance garinsu ne?"
Ya lumshe ido ya kara gyara zaman towel din dake daure a kugunsa,fitowarsa kenan daga wanka. Zak'in muryarta daban ce,hakika zai iya rantsewa bai taba sauraron muryar mace a fili ko waya ba, da yayi mishi dadi irin na Tasleem.
"Nidai ina mai gargadinki,stay away from him. Kada koda wasa na samu labarin kun hadu har maganar fatar baki ta shiga tsakaninku. OK?"
Ta rausayar da ido tana tsuke baki cikin jin haushin Haris. Banda abunsa ma,kare ne ya cijeta da zata k'ara waiwayar BARIKI. Don KB barikin ne ma gaba daya a rayuwarta.
"Kin rasa baki ne?"
"Naji zan kiyaye."
"Good,had'ani da Mammana."
"Ko a ina ta zama taka?" Ta fadi a zuci,a fili kuwa da toh ta amsa kafin ta mike ta fita zuwa falon.
Mamma ta karbi wayar,sunyi magana wacce Tasleem batasan abunda yace mata ba saidai ta lura da hararar da Mamma ta dafko mata kafin ta amsawa Haris da cewa
"Kada ka damu d'ana,baza'a samu wata matsala ba."
Daga haka ta kashe wayar ta mike tayi dakinta a fusace. Wannan ya sanyayarwa da Taslewm da jiki ta mike ta rufa mata baya. Kuka sosai ta tarar Mamma nayi. Ganin ta shigo ta zauna Mamma ta ja majina
"Kin cuceni Tasleem. Idan na tuno kinyi karuwanci raina baci yakeyi naji ke kanki ina jin haushinki. Wallahi koda wasa naji kin sab'awa mijinki babu ni babu ke. Ba don Liman ne da kansa yazomin da batun aurenki da yaron mutuncin nan ba wallahi ban yarda a cuci rayuwarsa a aura mishi ke."
Jin haka itama Baby ta fashe da kuka sosai ta durkusa gaban Mamma
"Wannan ya nuna har wannan lokacin baki yafemin ba Mamma. Ya kikeso nayi,Mamma idan bada sanya albarkarki gareni ba komai na rayuwata bazata tafi a daidai ba. Please Mamma kada kiyimin bakin da zan kasa zaman aure."
Jin wannan furucin ne ya tashi hankalin Mamma,ta rungumo diyarta tana fadin
"Na yafemaki Tasleem,bazaki fi haka lalacewa ba. Har abada in sha Allah kin shiryu kenan,bana fiddaki a addu'ata."
Farin ciki yasa Tasleem dariya. Mamma ta kara dubanta bayan ta saketa
"Kabiru da Harisu sun taba ganinki cikin waccan rayuwar,hakan yasa Harisu rokona akan kada na bari ki hadu dashi."
Ranta idan yayi dubu ya baci,Haris yafison kare sirrin abokinsa akan nata??
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(65)
Bata cewa Mamma komai ba banda toh.
******
Yaran gida sai ihun murna sukeyi da ganin Kabir. Hajiya Atine ce a
tsakar gidan zaune kan tabarma suna hira da mai musu hidimar
girki yayinda take kwasar tuwo. Ganin dagaske jikan nasu ne ta
hangame baki tana dariya
"Ashe da gaskiyar yaran nan. Lale marhabin da mijin."
Kabir yayi dariya suka gaisa suka taba barkwanci kafin ya shige
wajen kakarsa Hajiya Badi'at. Itama karatun Kur'ani takeyi,sanye da
gilashinta na ciwon ido,ganin Kabir ta karashe aya tayi addu'a kafin
ta shafa.
"Ashe zakazo nan kusa? Ai da bamu ganka tare dasu Harisu ba nayi
zaton kaida zuwa nan sai biki kuma?"
Ya kai hannu ya bude firij ya dauki robar ruwan Faro,yana kokarin
budewa yayi dariya
"Haba dai? Ai dole nazo ganin amaren namu. Ko Haris din baisan da
zuwana ba so nakeyi dai na bashi mamaki. Wai ma naga kokarin
Haris,naji don karfin hali mata biyu ya aura? Yayi kokari."
Ya karashe yana mai daga robar ruwan ya soma kwankwada. Hajiya
badi'at tayi dariya
"Kai don bakaga zuk'ak'an matan da ya zab'a ba. Zahra da
Tasleem,....."
Tuni ya maido ruwan bakinsa ya fesar har yana b'ata jikin Hajiya
Badi'at. Ya cigana da tari saboda ba karamin kwarewa yayi ba.
"Baka da hankali ne? Kana shan ruwa kamar wani karamin yaro? Ji
yanda ka b'atamu?"
Hankalinsa baya tattare da ita,gabansa na bugu da sauri da sauri.
Ganin yanda gaba daya ya chanja yasa Hajiya Badi'at dakatawa
tana k'ara cillaro mishi idanuwanta wadanda tsufa ya soma
tab'awa.
"Kai Kabiru lafiya kake?"
"Hajiya wacece Tasleem da Haris ya aure ne?"
Ta d'an tabe baki
"Kai amma Allah Ya kyauta,ai na dauka wani abun ne wallahi. 'Yar
wajen maryama ce ta gidan Liman."
"What?!!"
Ya fada cikin tsawa wanda ya tsorata 'yar tsohuwa Hajiya. Ya mike
tsaye,duk jikinsa rawa yake. Nan da nan idanunsa suka kad'a wai
kodai wata ce daban?
Da sauri ya fito daga dakin ya zura takalmansa,yana ji Hajiya na
kwala mishi kira amma baijin yana cikin hayyacin da zai samu ya
tsaya. Bai dire ko'ina ba sai gidan Liman. Tsayawa yayi ya rasa ya
zaiyi,gashi ba wani sabo yayi da mutanen gidan ba saidai ko ta halin
k'ak'a yau sai yaga Tasleem matar Haris. Yana nan tsaye yana
shawarar shiga ko tsayawa anan,saiga Baharu ya sauka saman
mashin dinsa yana kokarin tsayar dashi. Kb ya karasa wajenshi
sukayi musabaha,cikin sakin fuska kasancewar Baharu yasan Kb.
"Yaya kabir saukar yaushe?"
Kabir yayi murmushi wanda iyakarsa lebbansa
"Dazun nan na sauka. Ina amaryarmu?"
Baharu ya washe baki yana dariya
"Anti Tasleem tana nan mun b'oye maku ita har sai ranar."
Kb ya share wannan don ba shine a gabansa ba.
"Kana iya yimin magana da ita? Sak'o angon nata ya bani."
"Kash,ai kuwa tana gidan Mammanta."
"Ko zan samu rakiyarka gidan?"
Ba musu suka hau mashin din Baharu suka tafi. KB burinsa yaga
wacece Tasleem matar Haris,baya fatan ta kasance bebinsa.
Haka har suka iso kofar tangameman gidan. Kb yabi gidan da kallo
kafin ya tabe baki
"Not bad." Ya fadi a zuci.
"Bismillah shigo."
Ya bi bayan Baharu suka shiga. A nan tsakar gidan suka iske
Humaira gwaggo mai aikin Mamma tana turata a saman kekenta.
Kuri KB yayi mata da ido yana karajin gaskiyar zatonsa tana
bayyana. Wannan inda ace Baby bata wuce sa'arta ba sai yace itace
saboda matukar kamar da sukayi da juna.
"No Haris! Kada kayimin haka."
Ya fadi a fili kasa kasa,zuciyarsa na tafasa sosai. Suka shige ciki ba
tare daya amsa koda gaisuwar da gwaggo keyi mishi ba. Sukaci
karo da Mamma ta fito daga kicin. Ta amsa sallamarsu cikin jin
dadin rashin ganin Tasleem a falon kamar yanda ta haneta fitowa
daga daki har zuwa sadda Kabir zai ba Kzu.
"Mahaifiyar Baby kenan." Ya fada a ransa.
"A'a yau kuma wa muka samu haka kamar ma ba bakuwar fuska ba
a wajena?"
Ta fara maganar da duban KB,yayin data karashe tana kallon
Baharu.
Baharu yayi dariya
"Yaya Kabiru ne da,jikan Hajiya kuma aminin surukinki."
Magana ta fito! Tasleem da Haris! Wai wanene maci amanata a
cikinsu ne?
Dakyar suka gaisa da Mamma,baharu ya tambayi Tasleem Mamma
kuwa tace bacci takeyi. Kabir murmushi kawai yayi kafin a karshe
ya mike yace zai wuce.
"Haba dai ko ruwa baka sha ba?"
"Bama wannan ba,yace sak'o aka bashi ya bata fa."
Cewar Mamma da Baharu. Kabir tuni yayi kofa,ganin haka Baharu
ya mara mishi baya. Tuni yakai gate wajen mashin din. Baharu yana
zuwa yayi azamar fiddo wayarsa ya bud'o bangaren hotunan
tasleem wadanda ma'adanarsu daban ce a wayarsa,dakyar ya
lalubo wanda take zaune a falo sanye da doguwar rigar abaya tana
dariya ya dauketa domin shi kadai ne mai mutuncin a ciki.
Kafadar Baharu ya rike cikin dusashshiyar murya yace
"Duba dakyau,itace wannan?"
Baharu wanda ya tsorata da yanayin KB yayi saurin duba hoton.
"Itace ai amaryar taku."
Ya watsawa Baharu mahaukacin kallo kafin ya maida jajayen
idanunsa ga gidan. Ashe Tasleem da Haris zasu iya cin amanarsa?
Bar maganar Tasleem,yafi mamakin yanda Haris ya munafunceshi
ya auri wacce yafi so cikin mata. Ya rantse sai ya dauki mataki koda
hakan zaikai ga rabuwarsa da Yasmeen,rabuwar zumuncin iyayensu
hakanan da rabuwar wannan amintar tasu da Haris na shekara da
shekaru,duk akan 'YAR BARIKI.......!!!!!
KARSHEN NA DAYA....!
0 comments:
Post a Comment