Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
πΎπ₯πΎπ₯
JUST FOR YOU MY FANS
HAPPY NEW YEAR
1st JANUARY, 2018.
ON MONDAY!!!!
Season 1 π€ 5
BISMILLAHIR
RAHMANIRRAHIM.
Alhamdulillah!! As i start my new novel today 1st JANUARY, 2018. I wish all my Family and Friends happy new year. May Allah protect us from any calamity of this year amin.
I also pray for Allah to help us in our life and forgive our past amin.
GODIYA.
Ina mika godiyata ga duk kanin masoyana, Allah yabar zumunci da kauna.
FIRST PAGE!!!
Wata bakar mota ce me tsadar gaske tashiga wani hadaddan gida, daga gani babu tambaya kasan gidan masu akwai ne.
A parking space ya aje motar ya fito, masu gadin gidan se mika gaisuwa sukeyi, yana daga masu hannu fuskarshi dauke da fara,a.
Alhaji Lamido Jaye kenan, babban dan siyasa me rike da matsayin Director Na house of assembly a Abuja.
Alh. Lamido babban mutum ne, yana zaune a garin katsina tare da matanshi guda 3, biyu suna zaune a garin katsina, amarya kuma suna tare dashi a Abuja.
Yana da matukar kula da iyalanshi, mutum ne wanda beda son kanshi, yana kokarin kwatanta adalci atsakanin yaranshi da matanshi.
Week end kawai yake zuwa katsina. Uwar gidanshi Haj. Maryam, mace ce me kirki da saukin kai. Diya ce ga Alh. Garba Mekaita, yar asalin garin Funtua ce.
Tana da yara 2 da mijinta, Babban danta shine ANWAR LAMIDO JAYE, yagama karatunshi a A,B,U Zariya inda ya karanci Dr. Yana aiki a Medical Center fannin yara.
Dr. Anwar yana da nutsuwa, duk da yanda mahaifinshi yake da kudi sam baya takama da su. Yana da son yara shiyasa ya bada duk kanin lokacinshi ga aikinshi.Beyi aure ba haryanzu.
Kanwarshi Zaituna, yanzu tana karatu a school of nursing katsina. Itama tana da hankali da nutsuwa.
Matarshi ta 2 itace Haj. Falmata, yar asalin garin kaduna ce, iyayenta suna da hali, yaranta 2, duka mata Laila da Ilham. Laila tana karatu a B,U,K kano. Ilham kuma tana S,S 3 a F,G,C, Bakori.
Haj. Falmata tana da son yaranta, batason abinda ze tabasu, sede kuma sam basa fitina ita da Haj. Maryam, suna zaune lafiya harda yaransu.
Amaryar Alh. Suhailat, yaronta daya AMMAR yana primary school a abuja, sam baruwanta da sauran kishiyoyinta, asalima babu abinda yake hadasu se idan sun hadu a hidimar mijinsu.
Ganin bata kulasu yasa suma suka fita harkarta, kowa yana hidimarshi. Sanin mijinsu baya son fitina yasa acikinsu babu wanda yake kawo wata damuwa acikin gidan.
Da sallama Alh. Lamido yashiga cikin falonshi, Umman Anwar da Aunty Mahaifiyarsu Ilham suna zaune suna kallo, tashi sukayi suna fadin sannu da zuwa Alh.
Umma ce ta amshi jakar hannunshi kasancewar itace keda girki. Zama yayi, Aunty tace ina wuni Alh, ya hanya? Murmushi yayi yace lafiya lau Auntyn yara, na sameku lafiya da yara?
Tace lafiya lau, suna ciki ma ba suji zuwanka ba. Tashi tayi ta wuce dakin yan mata domin ta kirasu. Umma ce tafito dauke da tire, bayan ta zuba mashi tazauna tana gaisheshi.
Hannunta ya kamo yana fadin lafiya lau Umman yara ya aiki ? Murmushi tayi tace lafiya lau, ya mutanan Abujan? Yace kalau suke suna gaisheku.
Hannunta tazame jin sallamar yan mata, amsawa Alh, yayi sannan yabasu izinin shigowa. Kasa suka zube suna gaishe shi, yace lafiya lau, ya makaranta Laila? Tace lafiya lau Abba,muna hutu ma.
Kallon Ilham yayi yace saura sati 1 ku koma ko? Tace E Abba kuma daga wannan hutun bazamu kara dawo wa ba se mungama. Dariya yayi yace ashe muna da yan Candy agidan nan.
Umma tace sosai ma, kinga se adena kukan komawa makaranta. Ilham tace kai Umma ai yanzu seniors ne mu babu sauran wahala kuma.
Abba yace to Allah yatemaka, seki dage kifito da result me kyau, kina ganin sauran yan uwanki babu wanda yasamu matsala da secondary result dinshi.
Kallon Umma yayi yace Zaituna batazo gida bane cikin week end din nan? Umma tace wai practical suke dashi gobe asabar. To Allah yatemaka, wannan karon baza tazo gida ba kenan.
Bakomai kafin intafi zanje makarantar tasu semu gaisa dan idan nakoma senayi 2 weeks banzo ba, akwai wani aiki da zamuyi.
Ina Dr. Fa? Murmushi Umma tayi tace ai kasan shi se dare ze dawo. Murmushi Abba yayi yace dan yasan be aje nauyi agidan ba shiyasa ya bada duka lokacin shi a asibiti, da yana da iyali ai dole yarika dawowa da wuri.
Shigowa Aunty tayi tana fadin kaima de kafada Alh, ina ganin semun samo mashi da kanmu sannan zeyi aure. Murmushi Umma tayi batace komai ba.
Abba yace rabu dashi, zezo yasameni, idan ma tsoron matan yake zan baki dama kinemo mashi wadda ta dace. Tashi yayi yana fadin bara inshiga ciki inyi wanka se nazo muci abincin. Ilham tace Abba afito lafiya.
Rayyana! Rayyana! Na,am Amma ganinan hijabita nake nema. To ai gara kiyi sauri kada yamma tayi kije kisiyo mani kayan miya indora abincin.
Fitowa Wadda aka kira da Rayyana tayi tana kokarin saka hijabinta. Amsar kudin tayi, Amma tace kisiyo mana kifi na 200 dan Allah kiyi sauri banaso Babanku yazo bangama ba.
Rayyana tace Amma bara induba idan Nabila tana nan tarakani. Amma tace kinsan data dawo nan zata shigo ai, amma leka kigani kota dawo dan Ummanku taleka makota.
Rayyana tace to bara intafi amma idan Nabila tashigo kice tabiyoni semu dawo tare. Amma tace naji maza kitafi, fita tayi tana fadin sena dawo Amma.
Rayyana da Nabila kenan su biyu Allah yabama mahaifinsu, Alh, Lawal me Hula, kusan kansu daya, yan watan nine tsakaninsu.
Alh, Lawal yana da mata 2, Karima da Saude, Karima itace uwargida, kuma itace mahaifiyar Nabila, tunda ta haifeta bata kara haihuwa ba, dama kuma seda ta shekara 5 bata samu ciki ba.
Ganin haka yasa Alh, Lawal yakara aure, cikin ikon Allah ana auren Karima tasamu ciki,alokacin da Alh, Lawal yasani bakaramun jin dadi yayi ba, haka suka zauna zaman lafiya ita da kishiryata Saude.
Alh. Lawal babban dan kasuwa ne, yana da kudi na rufin asiri, gidanshi yana kofar kwaya cikin garin katsina, sede sam beda sha,awar barin yaranshi su wuce gaba da secondary.
Yana kula da iyalinshi sosai, hakan yasa hankalinshi yake kwance a koda yaushe. Cikin Karima yanada wata 2, Itama Saude tasamu ciki, murna agurin Alh. Lawal ba,a magana.
Haka suka cigaba da renon cikinsu, har lokacin haihuwar Karima yayi ta haifi Mace, kyakkyawa fara tas da ita. Ranar suna aka samata Nabila.
Bayan wata 2 da haihuwar Karima Saude ta haihu itama mace, Alh. Lawal yaso ace namiji yasamu, amma ganin mace ce yasa yayima Allah godiya da addu,ar Allah yashiryar dasu.
Ranar suna akasama yarinya Rayyana. Haka suka cigaba da renon yaransu hankali kwance, kome suke so mijinsu yana yimasu.
Karima tana sana,ar saida kayan sanyi, irinsu zobo kunun aya, anan cikin gida take saidawa. Ganin Saude bata saida komai yasa tayima mijinsu magana akan yabama Saude jari seta rika saida aya, zobo, da sauran kayan hadinsu, ita kuma tana yi.
Sosai yaji dadin abinda Karima tayi, haka yaje yasiyo ma Saude duk abinda Karima tace yabata, godiya sosai tayi mata, haka suka cigaba da sana,arsu.
Sede tunda suka haihu so daya babu wadda takara haihuwa, Saude ce kawai tayi bari bayan haihuwar Rayyana tun suna damuwa har suka hakura ganin shi mijin nasu yabarma Allah komai.
Karima yar garin Mani ce, ita kuma Saude yar Kankiya ce. Zuwa yanzu yaransu suna da shekara 24, sungama secondary islamiya kawai suke zuwa, ajinsu guda, duk inda zasuje tare suke zuwa, wasu har dauka suke yan 2 ne, duk da basa kama sosai amma kusancinsu yasa ake ganin kamar yan 2 ne. Dan Nabila tafi Rayyana kyau, kuma ita fara ce.
Da Sallama suka shigo, Amma ce ta amsa tana fadin ai dama tunda naga baki dawo da wuri ba nasan kinhadu da Rayyana. Dariya Nabila tayi tace wlh kuwa Amma tana shawo kwana muka hadu shine na rakata.
Umma tadawo kuwa? A,a bata dawo ba, amma nasan yanzu zaki ganta. Ku dauki kayan miyan ku gyara daya kuma ta wanke kifin ta soya. To Amma yau mezaki dafa mana? Koma menene ai tare zamu dafa zaku gani, ku wuce muje, hijabinsu suka aje suka nufi kitchen.
Dan Masani lafiyarka naga kabuga tagumi, ko yau ma ba,a dace ba? Ajiyar zuciya wanda aka kira da Dan Masani yayi tare da cire hannunshi daga kumatunshi yace kaide bari Abdul.
Wlh har nafara cire rai da samun aikin nan. Wai ace yanzu mutum da takardunshi da komai amma samun aiki yayi mashi wahala. Tunda nake fita neman aikin nan babu ranar dana ji haushi kamar yau.
Wata babbar Chamber ce naje ta Babbar kotu, akwai wani babban lawyer kowa yasanshi agurin,ya iya aiki sosai, sede nayi sati 2 ina neman yanda zanyi inganshi.
Da kyar nasamu wani masinjanshi ya karbi number ta, ganin yanda nake zuwa bana samunshi, yace duk ranar dayazo zekirani. Kasan wani abun haushin? Wai ina zuwa na bashi takarduna.
Kasan meyace? Cewa yayi wai tunda banida experience akan Law sede yadaukeni amatsayin masinjanshi, amma tunda inada kwalin degree matsayina zefi na tsohon masinja kadan.
Kuma ma private aiki ne zanyi mashi. Wlh lokacin daya gama fada mani wani kululun bakin ciki ne ya tokareni. Kamar in karbe takarduna infito, haka de na tsaya yagama fada mani komai.
Wannan takardar yabani yace incike idan na amince zanyi aikin to inmaida mashi, nan da kwana 2, idan kuma ban amince ba, idan kwana 2 ya wuce beganni ba, ze bama wani aikina.
Ina fitowa kamar in yaga takardar dan haushi, haka de nasamu guri nazauna na kara karanta takardar, kasan ko nawa zerika bani? Dubu 15 fa, wai seyaga yanayin aikina sannan zekara mani.
Yanzu Abdul kasan irin yanda nasha wahala kafin in kammala wannan karatun nawa. Tunda nagama secondary iyayena suka rasu, kakata bawani karfi gareta ba, kana ganin saboda rashin kudi seda na bata shekara 1 kafin nasamu nashiga University.
Admission dina na farko sede asararshi nayi saboda rashin kudi. Har dako nayi, nine aikin karfi dan kawai insamu in kammala karatun dana sama raina. A kullum Kaka tanamun fada akan in hakura da wannan karatun, inkoma kasuwa tunda ba dole bane.
Haka na rufe idona nace mata a,a yanda nafara shan wahala ai bazan iya hakura ba. Kafin ingama itama tarasu. Haka nazamo maraya gaba da baya, Kawuna kadai yarage mani, kuma nayi alkawarin bazan ze in nemi wani abu na kudi agurinshi ba.
Domin shima bawani karfi gareshi ba. Haka nazauna acikin gidanmu ni kadai, amma saboda son Zuciya ace wai dubu 15 shine albashi na. Ai gara inje inkoya a wata private school nasan ko banza zasu bani dubu 20.
Amma yanzu nida ba abun hawa gare ni ba, ko a kudin abun hawa ai zasu tafi, yazanyi da sauran hidimomina? Hawayene suka sauko mashi. Dafashi Abdul yayi, cike da tausayi yace Sageer.
Inaso kabani hankalinka nan, sanin kanka ne baka da wani aboki koma ince dan uwan daya wuce ni. Yau munkwashe kusan shekaru 20 muna tare, babu abinda baka sani nawa ba.
Dan haka zan baka shawara guda 1, wadda idan har ka dauketa zakaji dadinta, kuma ko bayan rai na insha Allah nasan zakayi alfahari dani, amatsayina na wanda yabaka shawara da kabi har ka samu biyan bukata. Goge idonshi Sageer yayi yace ina jinka, kuma nayi maka alkawarin zan dauki duk shawarar dazaka bani matukar bazata sabama Allah ba.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[2/10, 2:10 PM] nabilalady5: π¨π»πKAFIN IN ZAMA LAWYERπ¨π»π π¨π»π π¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»π
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 5 π€ 10
Sageer Alee inaso kasani duk wani dan Adam na duniya daka gani da arziki to seda yasha wahala kafin ya tarashi. Kai yau ko mutum harkar tsafi yakeyi dole seya sha wahala kafin yatara kudi.
A kwai masu kudi da yawa da zasu fada maka ta yanda akayi suka zama yanda suke ayanzu wlh se kayi matukar mamaki.
Kai sekaji ai kai baka sha wahalar komai ba. A binda akeso mutum yarike arayuwarshi shine hakuri, idan karike hakuri babu abinda bazaka samu ba.
Hakuri yanada matukar wahala, amma daga karshe babu abinda ya kai shi dadi. Kai ko mutuwa kayi batare da kaci ribar hakurin da kayi ba, tabbas ranar gobe kiyama Allah ze linka maka akan hakurin dakayi a duniya.
Koshi wannan Barrister da kake fada shima na tabbata seda yabiyo ta irin matsayin daya baka, kai kilama naka yafi nashi daraja, ai ni agurina, duk abinda zan samu arayuwa nafiso nasha wahala kafin insame shi.
Koba komai nasan zanfi rikeshi da daraja, kuma bazan taba bari nayi wasa da damar dana samu ba. Dan haka ina baka shawara akan kada kayi la,akari da yawan kudin daza,a baka.
Ka kalli muhimmancin aikin ka.
Kudi komin yawansu suna karewa, amma kima da daraja basa taba gushewa koda bayan ranka, wata kila katara dukiya, wadanda katara dominsu kila surika amfani da ita ta hanyar banza.
Amma idan ka tsaya kayi aikinka tsakani da Allah, ko mutuwa kayi aikinka da addu,ar jama,a zasu bika har kabarinka, koda baka aje kowa ba.
A binda nakeso ka cike wannan takardar kuma kamaida mashi ita, kasa aranka zakayi wannan aiki da zuciya daya, koda wata zezo ba,a biyaka kudinka ba, kada kayi saurin fushi.
Ni nasan abinda zaka samu agurin da wanda zaka karu dashi yafi kudi. Kuma shima yanada gaskiya, yanzu idan aka dauki shari,a aka baka, nasan bazaka taba sanin yanda zaka tafiyar da ita ba.
Saboda abinda aka koya maka amakaranta daban, duk da kasamu experience a school of law amma baze kai wanda zaka samu agurinshi ba, kai da kanka kacemun Babban lawyer ne.
Kaga kenan yasan aikinshi, kada ka koyi abinda yakeyi, kawai kadauki abinda yakoya maka, kasan kamar malamin addini ne, da ake cewa kayi aiki da abinda malaminka ya koya maka, amma kada kayi aiki da abinda yakeyi.
Wannan maganace me harshen damo, ba kowane me hankali bane ze iya fahimtar abinda ake nufi, kasan da yawa akwai wasu malaman da zasu koyama dalibansu abu, amma idan ka kallesu sekaga su basa amfani da abinda suka koya.
To kaima haka nakeso ka kasance, Sageer tun muna makaranta kake da ra,ayin kazama lawyer, wannan dalilin ne yasa muke kiranka da DAN MASANI.
Gashi haryanzu wannan suna yabika, kana da gaskiya, acikinmu kafi kowa riko da gaskiya da amana, hakan yasa akoda yaushe nake fada maka kaine kadace ka karanci Law acikin mu.
Dan Allah kada kabari wasu su canza maka ra,ayi, kasan irin wannan aikin naku, babu abinda kudi besawa ayi inde a harkar shari,a ne, babu wahala wajen maida karya tazama gaskiya, kamar yanda ake iya maida gaskiya tazama karya.
Nasan duk wanda yace zeyi riko da gaskiya a fannin aikinku to ko acikin abokan aikinshi beda wani tasiri, bare kuma gurin wasu mutanan, musamman masu kudi.
Karike Allah, ze te makeka, kayi gaskiya Allah ze kareka, ina me tabbatar maka ko bana raye wata rana se kazama babban mutum a wannan harkar. Nide fatana kayi amfani da shawarar dana baka.
Kuma seka kwantar da kai ne zaka iya fahimtar abinda kakeso ka koya, duk wani aiki na duniya dole zaka samu akwai wanda yafika iyawa. Yanzu misali, mutane nawa ne kasani wadanda suke aikin kanikanci, ayanzu sunzama manyan kansu?
Amma da zaka tambayesu wlh nasan akwai wanda zece maka daga mika sifana yafara koyon aikin, wani ma aikinshi mikama ogansu abinci ko ruwa. Amma da sukayi hakuri daga karshe me suka zama.
Akwai wanda zakaga idan ya kware a aikin ma seyafi oganshi iyawa, shima ze bude gurinshi kuma yasamu yaran daze koya masu, ahaka suma zasu iya harsu koyama wasu.
Kaima idan kayi hakuri wata rana seka bude taka Chamber wadan da mutane zasu zauna akarkashinka. Dan haka kayi hakuri dan Allah Sageer.
Hannu Sageer yasa ya goge kwallar da take zubo mashi tun lokacin da Abdul yafara bayani. Gaba daya jikinshi yayi sanyi da maganganun da Abdul yafada.
Tabbas ada yamanta da alkawarin daya daukarma kanshi zeyi aiki ko badan kudi ba, ko dan ya temaki talakawa, wadan da ake danne masu hakkinsu saboda kawai talaucinsu.
Kallon Abdul yayi, ya kamo hannunshi yace nagode Abdul, hakika banida wani dan uwa daya wuce ka a duk duniyar nan, bayan iyayena banida wanda ze fadamun farar gaskiya babu son zuciya a cikinta kamar kai.
Tabbas kayi mani tuni akan abinda namanta, kuma ka kara mani wani ilimi wanda bansanshi ba na rayuwa. Ina maka albishir da cewa insha Allah zanyi wannan aikin kamar yanda kace.
Kuma zanyi amfani da abinda kafada mani, idan ma akwai kari tozan kara akan hakan, bazan kara kallon abinda za,a bani ba. Fatana Allah yashige mani gaba a wannan aikin.
Murmushi Abdul yayi yace amma gaskiya naji dadin maganarka, Allah yabamu sa,a gaba daya. Tashi muje kaga ankusa kiran magriba.
Dr. Anwar ne yafito harabar asibitinsu hannunshi rike da jaka, haduwa sukayi da abokinshi Dr. Shamsuddeen, hannu yabashi suka gaisa yana fadin bade har katashi ba?
Murmushi Dr. Anwar yayi yace kasan yau Abba yake dawowa, kuma harma ya iso, dazu Umma takirani take fada mani. Dr. Shamsu yace hakane, shikenan se Allah ya kaimu, nasan gobe bazaka fito da wuri ba tunda Boss yana gida.
Dr. Anwar yace ya danganta, idan aka kawo patients urgent ai dole nafito, amma de zamuyi magana da Abba, hannu Dr. Shamsu yabama Dr. Anwar sukayi sallama ya wuce gida.
Seda ya tsaya suka gaisa da masu aikin gidan, sannan yawuce ciki, haka al,adarshi take, shiyasa kowa agidan yake yabonshi, sam bashida girman kai.
Da sallama yashiga fuskarshi dauke da fara,a zaune yasamesu asaman table suna cin abinci. Kusa da Abbansu yaje ya duka har kasa yana fadin sannu da zuwa Abba.
Hannu yamika mashi suka gaisa, yace Dr, na sameku lafiya? Tashi yayi yana fadin lafiya lau, Abba ya hanya da gajiya? Alhamdulillahi gajiya tabi lafiya.
Kallon iyayenshi yayi yace sannunku da gida, sukace yauwa Dr, ya aikin. Su Ilham sukace Yaya sannu da dawowa. Yace yauwa yan mata na ya aikin gida ina fatan baku kyalesu Aunty na da aiki ba.
Murmushi Aunty tayi tace a,a ai basa laifi, sun tayamu aiki. Zauna ga abincinka nan in zuba maka. Murmushi yayi yace Aunty zanshiga ciki in danyi wanka, idan nafito zanci.
Bayan kowa yagama cin abinci suka koma falo domin fira, dan aka,idar Alh, Lamido baya ganin baki aranar daya dawo, sede washe garin ranar, shiyasa iyalenshi suke samun lokacin shi.
Kallon Dr. Anwar yayi yace Dr. Wai ya maganar mu ne, haryanzu naji shiru, ko semun kebe? Dariya suka saka Anwar ya dukar da kai yana murmushi. Aunty tace a,a Alh, nace kabar komai a hannuna yaron nawa kunya gareshi baya son magana agaban yara.
Alh, yace a,a nikam hakurina yakare, shekarar ka 35 fa, amma ace haryanzu kana zuwa cin abinci agidanku. Haba Dr. Kayima kanka fada mana, kaifa likitan yara ne, na tabbata saboda kanason yara yasa ka karanci wannan fannin.
Meyasa bazakayi ma kanka fada ba, kaima kayi kokarin samun naka yaran. Dan haka nagaji, ayau dinnan ba gobe ba, senaji wata magana dazan tafi da ita me dadi.
Inaso kafin indawo ace matar dazaka aura kawai zangani. Aunty tace shikenan insha Allah kafin kadawo zakaji waya medadi. Kallon Anwar tayi tace Dr, akwai wadda kakeso ne ko ka bamu zabi?
Murmushi yayi yace Aunty kunfini sanin mata, kawai kuzaba mani wadda kuka ga zata dace dani. Amma fa wadda ta iya girki kuma me tsafta. Bandamu da kyawunta ba, inde tafito daga gidan mutunci, tana da tarbiya.
Kuma akwai ilimin addini ni babu ruwana da talaucinta ko kudinta, wadan nan abubuwan nafiso, domin mu kudi ba damuwar mu bace, to banga abinda yar masu kudi zata nuna mani ba.
Dariya suka saka, Laila tace ah! haba Yaya, shima kyau ai yana cikin abubuwan da annabi yace a auri mace danshi. Anwar yace amma daga karshe me yace? Ilham tace addininta.
Anwar yace yauwa yar gari, Aunty kawai kizaba mani irin wadda nace. Aunty tace to idan takasance gidansu suna da kudi kuma tana da abubuwan da kakeso yaza,ayi?
Murmushi yayi yace, aidama nace baruwana da kudinta, kawai asamu me wadannan abubuwan. Tace angama, ammafa gaskiya bazan zabo maka mummuna ba, koda tana da fin abinda kace.
Dariya suka saka gaba daya, Anwar yace dama Aunty saisa saisa zaki nemo. Aunty tace angama, kallon Umma tayi tace Umma kawo mana taki mufara zaba.
Dariya tayi tace a,a wannan maganarku ce, mude addu,a itace tamu, munbaki wuka da nama, keda danki. Laila tace Umma nizan kawo yan makarantar mu guda 4 se azaba.
Anwar yace waike waya fada maki zaben mata kamar zaben kayan sawa ne? Dariya tayi tace emana, ai nasan halinsu. Yace to nide bansaki ba, kije kizabo naki, tukunna, dariya sukayi, Alh, yace to nide nabada zabi, kafin indawo inji labari medadi.
Kwance Nabila da Rayyana suke adakinsu kowa yayi shirin kwanciya bacci. Rayyana tana ta charting, tana dariya. Fige wayar Nabila tayi tana fadin wlh shiyasa banaso azo kwanciya babu wuta, kawai seki damu mutane da dariya.
Da akwai wuta nima se in kunna kallo in kyaleki. Dariya Rayyana tayi tace wayace kema kibama kawarki aron wayarki kawai dan tace maki zataje biki kuma kibata aron waya.
Wlh ni bazan iya kwana 1 batare da waya ba, bare kuma kwana 3. Nabila tace enaji ba komai, ai mutunci kesa ayi komai, kuma kinfi kowa sanin yanda muke da Zarah, ba waya ba, abinda yafi waya ma zan iya bata.
Itama ai tana da ita kawai lalacewa tayi, kuma kinsan kowa yanaso yaje biki da babbar waya ko? Rayyana tace to naji, sarkin tsara magana, yanzude bani wayata.
Duka Nabila ta kai mata tana dariya tace wlh yarinyar nan kinrainani, kinsande na girmeki ko? Rayyana tace da wata 2, ko? Oho koma da second daya ne, aide narigaki shakar iskan duniya.
Rayyana tace tonaji dan Allah kibani haba yar yayata ko sokike aganni online kuma bana maida amsa? Kallon wayar tayi, tace bara inga abinda yake baki dariya to.
Rayyana tace babu kyau fa kallon sirri, Nabila tace sena gani, wayar tafara kallo, murmushi tayi tace kice sabon saurayi kikayi shine baki fada mani ba.
Rufe fuska Rayyana tayi tace kai Yaya duka fa jiya muka hadu dashi, dana fita, nafiso sena gama saninshi sannan infada maki. Nabila tace to kide kula, kinsan halin samarin yanzu,
Yanzu zakiga yafara fadin kitura mashi hotunanki, daga nan kuma se abinda yayi gaba. Rayyana tace insha Allah ma bazan biye mashi ba.
Nabila tace anshi wayarki ga wannan mararjin kawar taki nan tayi maki magana, ni banga abinda kika gani agurin Hidaya ba harkike kawance da ita.
Yarinyar da tafiki komai, ita a university ma take, kawai dan tana dan zuwa islamiya shima ba sosai ba, amma kin wani like mata. Dariya Rayyana tayi tace kai Yaya banga dalilin dayasa kika tsani Hidaya ba.
Kalli yanda take girmamaki amma ke bakya gani, e bana ganin nide kawai jinina be hadu da nata ba. Rayyana ta anshi wayarta tana fadin dama hakane.
Wani zakaga jininku behadu dashi ba, nima ai jinina be hadu da Zarah ba. Nabila tace ammade kinsan Zarah tafi Hidaya kyan hali ko?
Rayyana tace yanzu de abar maganar, kowa ya kwanta. Nabila tace to kema ki kashe wayarki mu kwanta. Rayyana tace kinsan wani abu Yaya? Nabila tace sekin fada.
Wlh na kagara inga nayi aure kodan inga wai agidana nake zaune, komai nacikin gidan nawa ne, inci abinda nakeso, babu wanda ze hanani.
Dariya Nabila tayi tace lallai Rayyana da alama wannan sabon saurayin naki yazo maki da wani sabon salo, inafatan de shima ya isa aure ko?
Rayyana tace karatufa yakeyi kuma duka wannan shekarar yafara. Nabila tace bakida magana, kawai kirabu dashi, dan wlh irinsu babu abinda suke sa mutum se son aure.
Kinsan samarin jami,a akwai iya kalamai, yanzu zasu canza maka akida, ga soyayyarsu akwai tsayawa arai, tunkafin kuyi nisa kirabu dashi mucigaba da addu,a Allah yakawo mana mazaje nagari.
Rayyana tace amin, amma bazan rabudashi yanzu ba, kinga koba komai zerika debe mani kewa. Murmushi Nabila tayi tace to Allah yasa mudace, amma ki kula. Kwanciya tayi tana fadin seda safe.
A yau ne Sageer Alee ya koma office din babban brr. Yusuf. Seda yayi jiranshi na kusan awa daya kafin yazo, masinjanshi ya karbi takardar yabishi da ita.
Bayan yagama abinda zeyi ya amshi takardar ya duba, kallon masinjan yayi yace kace mashi yashigo. Bayan sun gaisa yace Sageer Alee ina tayaka murnar fara aiki dani, zan fada maka dokokina idan kaji kuma zaka iya binsu, daga gobe zaka fara zuwa aiki. Dan haka kabude kunnuwanka kaji abinda zan fada maka.

Season 10 π€ 15
Dago kai Sageer yayi yana kallonshi, Brr. Yusuf ya cire glass dinshi ya ajiye yace Sageer ko? Kai Sageer yadaga mashi zuciyarshi har tafara tafasa ganin irin rainin hankalin da yake mashi.
Murmushi Brr. Yusuf yayi yace ina tayaka murnar fara aiki dani, sede akwai wasu abubuwa dana keso nafada maka, kuma idan kabisu zakaji dadin aiki dani.
Da farko de bana son karika shiga abinda be shafeka ba, kuma banaso ka aiwatar da komai seda izinina, kasande wajen nan gurin karbar karar jama,a ce, to banaso wani yazo yakawo case dinshi ka karba batare da na baka damar hakan ba.
Sannan bana son saka ido akan duk wani abu da nakeyi, idan zaka iya kallo to ka kalla kuma kaja bakinka kayi shiru, ni kwararran Lawyer ne, nafi karfin shekara 20 ina wannan aiki,
Ganin damata ne yasa nake zaune anan haryanzu, amma danaso da tuni na dade dazama alkali, amma sanin irin kudin danake samu anan yasa nayi zamana.
Dan haka banaso kazo ka kawo mani wani sabon salo, nayi aiki da kananan lauyoyi irinka, wasu sun wuce, wasu kuma halinsu yasa nakoresu, dan haka ina fatan kaima zaka bani goyon baya.
Ajiyar zuciya Sageer yayi, yace insha Allah zanyi maka aiki da gaskiya da amana, bazanyi wani abu daze saba ma shari,a ba, kuma zanbi duk wata doka daka saka mani matukar bata sabama Allah ba. Fatana Allah yata yani riko.
Amin, Sageer, dan haka wancan office din shine naka shi Bala masinja yana waje, tunda kai da karatunka shiyasa na ajeka anan, ammafa kada kadamu zakaga kayi degree amma kana amatsayin karamin ma aikaci.
Kowama da haka yafara, saboda haka iyakacin kwarewarka a aiki iyakacin karin matsayinka, zaka iya tafiya, akwai file akan tebur kadubashi zakaga komai. Godiya Sageer yayi mashi yafita.
Auntyn su Ilham ce zaune ita da Laila domin Ilham takoma makaranta, Laila tace Aunty wai ya maganar samoma Yaya mata, haryanzu naji shiru bakice komai ba ko baki samu ba?
Murmushi Aunty tayi tace nasamu mana, aikema kinsan gida be koshi ba baza,a kaima waje ba, sanin kanki ne yanda nasan Anwar bazan bari ya auri wata bare ba se dangina.
Domin yaro ne me hankali, ga kudi, sannan mahaifinku yana da kudi, taya zan bari yanda banida namiji agidan nan sannan inbari wannan damar ta wuce ni.
Laila tace to Aunty wacece kika samomashi? Aunty tace, ina tunanin inhadashi da Rayyana yar wajen Yakumbo Saude, saboda yarinyar tanada hankali, inason gidansu domin akwai tarbiya.
Bazanso inzabama Anwar matar dazeyi kuka da ita ba, duk da mijinsu yanada rufin asiri amma ina matukar tausayinta domin, duk cikin danginmu ita kadaice Mamanta ta auri marar karfi.
Kuma dan nan katsina ne, bayan an haifeta mahaifiyarta tarasu, a hannun kishiyar Mamanta ta tashi, alokacin da zatayi aure danginmu sunso abasu ita dan tayi aurenta acan kaduna, amma mahaifinta yace tasamu miji anan.
Babu yanda suka iya haka nan suka hakura, damma Allah yahadata da miji nagari kuma kishiyarta tanada hali me kyau, amma duk da haka ina tausayinta.
Kinsan da mahaifiyarta da Ummata mamansu daya babansu daya, shiyasa nakeso inhada wannan zumuncin, duk da banice na haifi Anwar ba, amma zanji dadi idan ya auri dangina.
Laila tace hakane Aunty, amma fa Rayyana batayi karatu sosai ba, meze hana kibashi Humaira yargidan Baffan kaduna, kinga tagama karatunta kuma itama tanada hankali.
Aunty tace a,a kema kinsan halin Humaira, sam batada wani ilimin addini sosai, sannan bata girmama manyanta, mahaifiyarta ta sangarta ta dayawa, kede kibarni nafiso inbama Anwar yarinyar da mahaifiyarta ta kasance itace dangina ba mahaifinta ba.
Kinsan halinmu na mata, duk yanda kuke da mace matukar baku hada komai ba, wata rana seta juya maki baya, musamman idan akace auratayya tashiga tsakaninku.
Laila tace toshikenan Allah yasanya alkhairi, to yaushe zakisashi yaje? Aunty tace a,a inaso mufara magana da Yakumbo ne, zansa ta turota nafiso yaganta agabana inga yanda zeyi, mikomun wayata ma inkirata.
Zaune Umman Rayyana take adaki tana gyara kayanta, wayar ta ce tayi kara, bayan sungama gaisawa, Umma tace haba Hajiya Falmata, ai da nayi fushi, yanzu kinrage zumunci.
Dariya Aunty tayi tace wlh ba haka bane, kwana 2, idan nakira wayarki bata shiga, kuma naso inzo se Alhaji yazo shiyasa ayi hakuri Yakumbo.
Umma tace haka ne, wayar tasamu matsala ne, jiya aka amsota daga gurin gyara, to yakuke ya yara suma karatu ya boyesu. Aunty tace wlh kuwa. Duk suna lafiya.
Bayan sungama gaisawa Aunty tafada mata duk abinda yake faruwa na maganar auran Anwar, sosai Umma taji dadin abinda Aunty tace, dama tana matukar son taga Rayyana tayi aure da wuri dan tasan idan itace tafara aure Alh, zekashe mata kudi akan ace se Nabila tarigata aure.
Godiya tayi mata kuma tace insha Allah gobe zata turo Rayyana ita kadai ma zatazo, amma bazata fada mata komai ba, kawai idan tazo taji daga bakinshi. Aunty tace yauwa yakumbo kada kifada mata, nafiso su dedeta kansu taji maganar daga bakinshi. Sallama sukayi Umma tana cike da farinciki.
Zaune Sageer yake shida Bala masinja suna shan rake, Bala yace wato Sageer inafada maka, tunda Allah yashigo da kai wannan Chamber tamu kaima zakasha kallo harka gaji.
Kaganni nan, shekarata 10 ina aiki da megida agurin nan, babu abinda bansani ba, nagame da shari,ar dayakeyi, wato Sageer idan kana raye zakasha kallo, inafada maka wlh masu kudi suna yin yanda sukeso akasar nan.
Yanzun nan zakaga ankawo Case na kisan kai, amma iname tabbatar maka inde yallabai aka bama case din, wlh baya kwana 3, yagamashi, Allah yabashi basira, shiyasa dawuya kaga yakare masu hakki, sede yakare yaran masu kudi,
Shifa shari,arshi hawa hawa ce, kowace tanada kudinta, shiyasa yaki yarda yatashi daga wajen nan, idan har yadaukeka aiki, matukar yaga zaka kawo mashi gyara a aikinshi yanzu ze koreka, danshi yafison aiki da mutum,kamarshi.
Jinjina kai Sageer yayi yace yanzu kuma Baba, kana gani bazaka iya fada mashi gaskiya ba, murmushi Bala yayi yace lallai yaro yarone, ni ina ruwana, nide aikina shine masinja,
Babu ruwana da aikinshi, idan nace zanyi magana to nasan zan iya rasa aikina, kuma wannan aikin shine rufin asirina da iyalina, idan narasashi bansan yazanyi ba.
Kasan ance idan kaga zakayi gyara inda baze karbuba, to abinda yafi kawai kaja bakinka kayi shiru, wata rana Allah zekamashi. Sageer yace haka ne, Allah yayi mana jagora
Rayyana ce kwance tana ta waya da saurayinta, Nabila ce tashigo tazauna da abinci a hannunta, hannu tasa takaima Rayyana duka tana fadin seki aje wayar kitaso muci abinci.
Sallama sukayi ta tashi tana murmushi tace kai Yaya wlh, kin katse mana jindadinmu,Nabila tace lallai kam wannan yaron yayi nasarar kwace zuciyarki.
Rayyana tace kede bari Yaya wlh ya iya kalamai masu dadi, shiyasa idan ina waya dashi banaso indena, Nabila tace kide yi ahankali, kinga ba aure zakuyi ba,
Kada kizo kisakashi aranki kuma kisamu mijin aure ki kasa fiddashi aranki, kinsan yanda soyayya take da yara. Rayyana tace haba de Yaya sede idan bansamu dan gayu ba, da gudu zan cireshi inkama wancan.
Nabila tace to Allah yayi mana zabi nagari, amin Yaya, yauwa kinsan wani abu kuwa Rayyana? A,a sekin fada, gobe da safe inaso zanje gidansu Zara, dan tadawo zanyi mata sannu da zuwa,
Idan kuma zakije kishirya. Rayyana tace uhm kemade kinsan bazan jeba, gashi inaso inbiki amma tunda gidansu Zara zakije bazanje ba, kawai kitafi amma kidawo dawuri dan Allah.
Nabila tace a,a wuni zanyi mata, kinsan kwana 2 bamu haduba, dole akwai labari, gashi gobe babu islamiyya. Rayyana tace to naji, sekindawo, murmushi Nabila tayi tace to kema kije gidansu Hidaya mana.
Rayyana tace bazanje ba, kawai zan zauna muyi fira da Saif, zefi mani dadi ma. Dariya Nabila tayi tace toshikenan, hakan ma yayi.
Washe gari bayan Anwar yagama shirinsa yafita yagaida iyayanshi yaci abinci Aunty tace yauwa Anwar inaso yau ka gajarta aikinka domin zankiraka anjima kazo kaga wani abu.
Murmushi yayi yace to Aunty, insha Allah zanyi kokarin takaita aikina, idan ma bangama ba, zan iya barma Dr. Shamsu yakarasa, Umma tace wani abude ake boye mana ba,aso muji ko.
Idan tafasu ai zamuji. Aunty tace e Umma nafiso seta fasu sannan kuji, shima kanshi yarona bazan fada mashi ba, Umma tace toshikenan Allah ya nuna mana.
Umman Rayyana ce take kwalama Rayyana kira, shigowa tayi tana fadin Umma gani ina bandaki ne shiyasa ban amsa ba. Murmushi tayi tace yauwa Rayyana ta, tunda kinyi wanka, jekiyo kwalliya me kyau, wadda baki taba yin irinta ba,
Kidauko kaya masu kyau, kizo zan aikeki gidan Ummanki Falmata, bata fuska Rayyana tayi tace ni Allah Umma banason zuwa gidan nan, idan naje Yaya Laila bata mani fara,a sosai.
Umma tace inde Laila ce ai haka take, miskila ce amma ai Ilham ba haka takeyi maki ba ko? Rayyana tace emana, amma ai yanzu bata nan ta koma makaranta, Umma tace nide kitashi kishirya, kuma kedaya nakeso kitafi, banaso kija Nabila.
Rayyana tace Umma saboda me? Saboda aiken sirri ne, kuma yar'uwata ce, kinga itama idan Mamanta zata aiketa gurin danginta ai bata tafiya dake ko, Rayyana tace tonaji, itama bata nan, ta tafi gidan kawarta. umma tace yauwa tashi maza kitafi, amma fa bance kidawo da wuri ba.
Bayan tagama shiryawa Ummanta tabata kudin adedeta da kuka da kubewa da barkono tace ta kaimata, kuma ta gaisheta, Rayyana tace to umma ina aiken sirrin? Umma tace wasa nake maki ai, maza kije kiyima Mamanku sallama kitafi.
Fita tayi tashiga dakin Maman Nabila tayi mata sallama, mama tace wai yau lafiyarku, kowa ta fita ita kadai? Rayyana tace lafiya lau, taje yima kawarta sannu da zuwa ne, kinga ni kuma bama shiri da ita shiyasa banje ba.
Yanzu ma Ummace ta aikeni gidan Aunty Falmata. Mama tace to sekin dawo, kigaisheta, bara inbaki daddawa ki kaimata da yaji ko, Amsa tayi tafita, tana fita takira Nabila awaya,
bayan tadauka tace Yaya kishirya ganinan zuwa Umma ta aikemu gidan Aunty Falmata, kuma tare tace muje shiyasa zanbiyo mutafi. Nabila tace tosekin zo, dariya Rayyana tayi takashe wayar tana fadin nasan idan bance maki haka ba bazakije ba, adedeta tasamu tanufi unguwarsu Zarah.

Season 15 π€ 20
A dede kofar gidansu Zarah Rayyana ta tsaya, shiga ciki tayi suka gaisa da mamansu Zarah, Nabila tace amma kinyi sauri, Zarah tace Rayyana manya, shine kika ki biyo kawata kuzo ko?
Murmushi Rayyana tayi tace aiki nataya Umma kuma zata aikemu shiyasa nazauna, kindawo lafia? Zarah tace lafiya lau ga tsarabarki nan nabama Nabila takawo maki.
Rayyana tace kai amma nagode. Yaya tashi muje me adedeta yana jiranmu, Tashi Nabila tayi tana fadin to kawata sekinzo dan firar bata kare ba akwai saura,
Zarah tace shikenan zanzo ko kuma idan muka hadu a islamiyya se mucigaba, Nabila tace wlh baki isa ba, kema sekinzo, tashi tayi tana dariya tace tonaji.
Sallama sukayi ma mamansu Zarah suka tafi, acikin mota Nabila tace wai aiken me Umma tayi mana? Dariya Rayyana tayi tace bakomai kawai cewa tayi muje mugaishesu.
Duka Nabila ta kaimata tana fadin ai dama wlh nasan karya kikeyi kawai dan injene kikace aikenmu akayi, nasan kuma ke kadai ta aika ko?
Rayyana tace ai nasan idan bance maki haka ba, bazaki baro gidan su Zarah dawuri ba, kuma kinsan banason zuwa gidan Yakumbo ni kadai duk senaji nagaji dazaman.
A kofar gidan su Ilham suka tsaya, kudinshi suka bashi suka shiga ciki, Nabila tace anya Rayyana ba suriki zamu samu ba, naga wannan kwalliya kamar ta sallah? Murmushi Rayyana tayi tace wlh bawani suriki kawaide inajin yin kwallaiyar ne.
Gidan nan ma wazakayi ma kwalliya, Yaya Anwar ai yafi karfina, kuma se inyi fin wata banganshi ba, kina ganin ko Umma sede su gaisa awaya, kinsanshi da son aikinshi.
Gaisawa sukayi da megadin, suka shiga ciki, afalo suka samesu zaune suna fira, da sallama suka shiga, Amsawa akayi, Laila tace a,a su Yaya Nabila ne da Yaya Rayyana agidanmu.
Rayyana tace wlh kuwa mune, tunda ku kun boye, Aunty tace sannunku dazuwa, har kasa suka duka suka gaishesu, Umma tace lafiya lau yan matan Umma, ya kuka barosu?
Rayyana tace lafiya lau suna gaisheku, tashi Laila tayi ta kawo masu ruwa da lemu, bayan sun sha, Laila tace kutashi muje ciki, bayanta sukabi suka shiga part dinsu.
Aunty sam ba haka taso ba, tashi tayi taje kitchen takira Umman Rayyana, bayan sun gaisa tace Yakumbo ya naga haka, tace meyafaru kuma?
Tace Rayyana nagani tazo ita da Nabila, bayan kuma kince ita kadai zatazo, Umma tace amma yarinyar nan batajin magana, ita kadai fa tafito daga gida,
Aunty tace ai kuwa su biyu sukazo, kinsan Rayyana da nacin yar uwarta, Umma tace nide duk yanda zakiyi kada kibari kuyi maganar agabanta.
Idan ma Anwar din yazo kisa Laila ta tafi da Nabila dakinta. Aunty tace shikenan angama, sallama sukayi Aunty tadaga wayarta takira Anwar, yace to Aunty ganinan zuwa. Dakinta tawuce tana me cike da murna.
Kamar kullum Sageer yana zaune a karamin Office dinshi yana duba wasu takardu, Barr. Yusuf ne yashigo tare da wani matashi wanda shekarunsa bazasu wuce na Sageer ba.
Dasauri Sageer yatashi ya karbi jakar Barr. Yusuf yana mashi sannu dazuwa, yace yauwa sannu Sageer yau se kai kadai, Bala bayanan ko? Sageer yace wlh kuwa yaje kauye.
Bayan sun zauna Barr. Yusuf yace yauwa Sageer miko ma bakona ruwa, sunanshi Barr. Umar, shima yazo nan domin yafara aiki dani, kuma dan uwana ne, dan kanin mahaifina ne.
Hannu Sageer yabashi suka gaisa yana mashi sannu dazuwa, murmushi Brr. Umar yayi yace sannu Sageer ya aiki? Yace lafiya lau, juyawa Sageer yayi zekoma office dinshi Brr. Yusuf yace a,a dawo Sageer.
Kujera ya nuna mashi yace yazauna, kallonshi yayi yace kamar yanda nafada maka Umar ze fara aiki a office din nan, kuma wancan office din nakusa da nawa shine nashi, daga yanzu shine PA na,
Ina fatan zaka girmamashi kamar yanda kake mani, kuma kamar yanda nafada maka ka tsaya inda na ajeka banaso kashiga abinda babu ruwanka.
Sageer yace insha Allah, zan kiyaye, Allah yabamu zaman lafiya, kuma Brr. Umar ina tayaka murna, Allah yasa kafara aikin nan a sa,a. Yace amin nagode, Brr. Yusuf yace zaka iya tafiya.
Yazo fita suka hadu da wasu manyan mutane daga ganinsu kasan masu fada ajine, baya yadawo yabasu hanya suka wuce, tare da gaishesu.
Da fara,a Brr. Yusuf ya tarbesu, gurin zama yabasu a kujerun dasuke cikin office din, dawowa Sageer yayi ya dauko masu ruwa da lemu yakawo masu.
Daya daga cikinsu yace lallai Brr. Kana jin dadinka, naga office din naka yakara cika, har sabon masinja kasake? Dariya Brr. Yusuf yayi yace ito amma bawai masinja bane, shima karamin lawyer ne.
Dayan Alhajin yace e lallai kam, to sannu yaro, zaka iya tafiya mungode, juyawa Sageer yayi yafita zuciyarshi tana masa zafi, wai da kwalinshi amma arika kiranshi masinja.
Tashi Brr. Umar yayi da niyar fita, Brr. Yusuf yace a,a kayi zamanka Umar,ai kai nawane, kuma inaso kafi wancan iya sanin makamar aiki shiyasa.
Kallonsu yayi yace Alh. Abbas yau kune a office dina kaida aminin naka Alh. Bashir? Alh. Abbas yace wlh kuwa, wata babbar matsala ce ta taso mani shiyasa kaganni nazo babu ko waya.
Sageer dayafita yazauna a waje hakanan kawai yaji zuciyarshi tanaso taji dame wadannan mutanan sukazo, dan tunda yafara aiki a office din betaba ganin wasu sunzo ba, shiyasa yakeso yaji abinda yakawosu.
Komawa yayi ya tsaya yanda zejiyosu. Brr. Yusuf yace Alh. Inajinku mece damuwarku, kunsan zan iya yimaku komai arayuwa. Alh yace wlh brr. Kasan idan akace kanada yara abubuwa kala kala zaka rika ganinsu.
Kasan akwai babban yarona daya dawo daga London Ammar, to wlh jiya yaje gurin wani abokinshi bayan yarakoshi suka hadu da wani saurayi shine yayi masu rashin kunya.
Kasan Ammar da zuciya shine kawai ya caka mashi wuka aciki, nan take yaron ya mutu, kuma yaron tare suke dawani abokinshi yaga yanda abun yafaru, shine su Ammar suka gudu.
Brr. Yace yanzu wane officer ne aka bama case din? Alh, yace yana hannun D,P,O Tahir. Dariya Brr. Yayi yace bakuda matsala mutumi nane. Alh, yace ammafa brr. Wukar da yayi kisan da ita tana hannunsu
Ina tsoron kada lawyer da zasu dauka yayi amfani da sahun hannun Ammar. Brr, Yace Alh, bakada damuwa, yaufa shekarata 20 ina wannan aikin.
Nayi case sama da 50 aciki kadanne banyi nasara ba, komin wahalar case baya damuna inde za,a sakar mani kudi.
Alh, dan in maida karya tazamo gaskiya agurina bawani abu bane,dan haka ku kwantar da hankalinku, kamar yanda muka saba daku, yanzun ma haka za,ayi.
Alh, yace karka damu Brr. Inde kudine zan iya kashe ko nawane akan Ammar, wlh bazan taba barin ayanke ma Ammar hukuncin kisa ba, dan haka zan baka naira million goma, inaso case din nan ya mutu gaba daya.
Wani irin murmushin farin ciki brr. Yayi, domin yasan inde akashe case din kisa ne farashin da yake karba million 5 ne, idan yaci case din yadauka duka, idan kuma ya fadi a case din to ze dauki rabi yamaida masu rabi.
Hannu brr, yamika masu yace badamuwa nagode Alh, insha Allah komai zeyi dede, yaushe ne za,a shiga kotun? Alh, yace ranar monday ne kuma a high court za,ayi shari,ar.
Brr, yace babban kuskuren da sukayi kenan dama banaso ace Shari'a court za'ayi shari'ar, dan haka badamuwa zanje inga D,P,O. Hannu Alh, yasa aljihu yaciro check na million 10 yabama Brr.
Godiya yayi mashi sukayi masu sallama suka fita. Dasauri Sageer yabar gurin idonshi cike da kwalla bakaramin tausayin iyayen wanda aka kashe yayi ba,aranshi yana fadin inama ace yanada iko.
Aunty nashiga falo tacema Laila kuje dakinki keda Nabila zansa Rayyana wani aiki kada abarta ita kadai. Laila tace tashi muje Yaya Nabila in gwada maki ma wani abu,
Rayyana tace banda son kaide, murmushi Nabila tayi tace anyi son kan, fita sukayi, harsun kai bakin kofa Aunty takira Laila, kitchen tabita Nabila kuma tafita dan tajirata.
Aunty tace yauwa kinaji na ko, kada kibarta tafito harsena kiraki awaya, nakira Anwar yace gashinan zuwa nafiso yaga Rayyanata ita kadai shiyasa naso tazo ita kadai.
Murmushi Nabila tayi, sam bataji dadin maganar dataji ba, datasan hakane wlh bazata biyo Rayyana ba, amma tasan kila itama batasan da maganar ba, Laila tana zuwa tajata suka wuce dakinta, gaba daya Nabila jitake kamar tabar gidan.

Season 20 π€ 25
Laila tace bara nashiga bandaki infito, Nabila tace to sekinfito, kallon dakin Nabila ta rikayi, sosai tsarin dakin ya burgeta, ganin ta gaji da zaman yasa ta kwanta saman gadon ta rufe idonta kamar me bacci.
Da sallama Anwar yashigo part din Ummanshi, amsawa tayi tana fadin har kadawo Anwar? Kai ya sosa yace wlh Aunty ce takirani shiyasa nadawo dawuri.
Murmushi Umma tayi tace to jeka kila de sirukata tazo dan naga yan matan Umman Rayyana sunzo, dukar da kai yayi yace nide bansani ba.
Umma tace to ai zanji koma mene kaida Auntyn taka, Allah de yasa adace, juyawa yayi zefita tace yauwa kaduba dakin Laila nasan tana can tana baccinta na gado, tunda taga Aunty tayi baki kasanta da miskilanci, ka tadomun ita tazo mushiga kitchen. Anwar yace to Umma.
Kai tsaye dakin Laila yawuce, sallama yayi dan baya shiga dakinsu se sunbashi izini, so 2 yana sallama amma yaji shiru hakan yasa yashiga yasan kila bata jishi bane, kusa da gadon yaje yace ke Laila kitashi Umma nakira zakuyi aiki.
Nabila da bacci yafara daukarta batasan abinda akeyi ba, seda yakara kiranta harso biyu amma bata motsa ba, hakan yasa ya kai hannunshi abayanta yasakar mata duka mezafi.
A firgice Nabila ta tashi harda yar kararta saboda dukan yashigeta, cak Anwar ya tsaya, mutuwar tsaye yayi ganin abin kunyar da yayi, Nabila kuwa kallonshi take idanuwanta harsun fara fitar da kwalla.
Hannunta daya yana bayanta ta dafe inda aka daketa, shima kallonta yake ido cikin ido, yarasa meze cemata, haka suka rika kallon juna. Laila kuwa jin ihun Nabila yasa tafito dasauri.
Karar bude kofar ne yasa Nabila tayi saurin juyawa tana kallonta, Laila tace Yaya Nabila lafiya me yasameki? Nabila batasan lokacin da wani sabon kuka yataho mata ba.
Ita duk daukarta wulakanci ne yayi mata saboda tahau gadon kanwarshi, dama tundazu ranta abace yake ganin irin abinda Aunty tayi mata, yanzu kuma gashi harda duka.
Matsowa Laila tayi takamata tana fadin dan Allah kiyi shiru kifada mani meyafaru? Kallon Anwar tayi tace yaya lafiya ko wani abun kayi mata?
Da kyar yace dan Allah Laila kibata hakuri, wlh nadauka kece akwance, Umma tace nazo nakiraki, ganin nayi sallama baki amsa ba, nadauka kina bacci, nashigo naga mutum kwance asanina kedayace agidan nan.
Shiyasa nafara kiranki, ganin baki amsa ba yasa nakai maki duka abaya ashe bake bace dan Allah Nabila kiyi hakuri. Laila tace shikenan kaje ganinan zuwa zan bata hakuri.
Juyawa yayi yafita yana waigen Nabila datake kuka, sam beji dadin abinda yayi ba. Kamata Laila tayi suka zauna tace kiyi hakuri kinji, kinga besan ke bace. Nabila tace shikenan yawuce, Laila tace yauwa bara inje Umma na kirana.
Sallama Anwar yayi yashiga falon Aunty, amsawa tayi fuskarta dauke da fara'a tace yauwa yarona harka iso? Yace wlh kuwa.
Zama yayi saman kujera Rayyana da take zaune tayi saurin dukawa tana fadin Yaya ina wuni. Murmushi yayi yace lafiya lau, wai Aunty bade Rayyana bace? Aunty tace itace mana.
Kaga tazama yan mata ko? Yace gaskiya kam, ai na kwana 2 banje nakagaishe da Ummanta ba. Aunty tace Rayyana dauko mashi ruwa, tashi tayi tafita.
Aunty tace kaganta nan itama haryanzu bata fitar da miji ba, Anwar yace ai komai lokaci ne, Aunty tace shiyasa nace bara inzaba maka ita nasan zakaji dadinta domin kasan gidansu akwai tarbiyya.
Amma ban fada mata ba, nafiso kafada mata da bakinka, shiru Anwar yayi, danshi hankalinshi gaba daya yana gurin Nabila, idanuwanta kawai yake gani suna zubar da kwalla.
Aunty tace inafatan tayi maka? Anwar yace babu damuwa Aunty zan duba ingani, tace yauwa yarona. Shigowa Rayyana tayi da sallama.
Zuba mashi ruwan tayi tamika mashi, amsa yayi yace yauwa yar kanwata nagode.
Yana gama sha yace Aunty shikenan zan iya tafiya nabaro aiki a office? Tace shikenan sede kafin kadawo ta tafi, Anwar yamika mata wayarshi yace yauwa kanwata samun number dinki ki gaishe dasu Umman.
Wani dadi ne yakama Aunty, mika mashi wayar tayi yace yauwa ga wannan kihau mota ko, amsa tayi tana masa godiya, itama Auntyn godiya tayi mashi yafita.
Yaso yakara komawa dakin Laila, amma ganin Aunty tabiyo bayanshi yasa kawai yawuce, dan dama yasan zata iya biyo bayanshi shiyasa ya anshi number Rayyana yasan zefi saurin samun Nabila.
Sallama yayi ma Umma yatafi yana me cike da tunanin Nabila dan haryanzu fuskarta takasa bace mashi. A waya Aunty takira Laila, gabanta ne yafadi kada ace yaya Anwar yafada mata yaga Nabila har yayi mata laifi.
Dan ita batayi niyar fada mata abinda yafaru ba, dauka tayi Aunty tace kidawo da ita yatafi, ajiyar zuciya tayi tace to Aunty.
Komawa dakin tayi tace yaya Nabila muje, suna zuwa Rayyana tace Yaya meyasameki? Nabila tace bakomai bacci nayi shiyasa.
Nabila tace Rayyana mutafi ko? Laila tace habade kubari agama abinci kuci mana, Nabila tace ai babu komai zamu dawo wani lokacin. Laila zatayi magana Aunty tace kibarsu zasu dawo kila ita Nabila tanada wani uzurin ko?
Rayyana tace wlh bawani uzuri, Aunty tayi murmushi tace a,a kede baki sani ba, banaso atakura mata, wani lokacin zaku dawo. Rayyana tace shikenan mungode bara mutafi.
Aunty tamika ma Nabila leda tace gashi wannan turare ne keda Rayyana.
Nabila tace mungode Allah yasaka da alkhairi, wata ledar tamikama Rayyana tace ke kuma rike maku wannan ku kaima su Ummanku, kuce masu mungode.
Tare suka fito, part din Umma suka shiga sukayi mata sallama, Umma tace habade har zaku tafi kubari kuci abinci mana, ai nadauka yini zakuyi mana ma.
Aunty tace ai Nabila ce takeda wani uzuri shiyasa, Umma tace to ina zuwa, daki tashiga tafito da wata leda tace gashi ku kaima ummanku, wannan kuma takuce.
Godiya sukayi mata Laila tarakasu, juyawa dakinta Aunty tayi dama bataso su zauna kada Anwar yadawo yasamesu. Seda suka samu a dedeta sannan Laila tadawo zuciyarta cike da tausayin abinda akayima Nabila, jitake dama itace Yaya ze zaba.
Saboda tsabar damuwa sam Sageer yakasa zama, hakan yasa yaje gurin brr, yace kanshi yana ciwo yanaso yaje gida. Brr, yace badamuwa nima fita zanyi zanje wani guri nida Umar zaka iya tafiya Allah yasawake.
Yana tafiya suma suka fito suka nufi police station gurin abokinshi D,P,O domin tsara case din dazeje ranar monday.
Kai tsaye Sageer dakin Abdul ya wuce, sede besameshi ba, hakan yasa ya kwanta yana jiranshi yadawo bayason yakirashi yasan yana iya katse duk abinda yakeyi yataho. Kwanciya yayi yana kara tunanin wanda aka kashe.
Da sallama Anwar yashiga office din Dr. Shamsu, kujera yaja yazauna yana jiranshi ya sallami wata patient. Bayan sungama Dr. Shamsu yace abokina harka dawo?
Anwar yace wlh kuwa nadawo, kasan halin iyayenmu, waisu sunaso nafitar da mata ni kuma kasan halina haryanzu banga macen danake so ba, amma ayau.
Murmushi Dr. Shamsu yayi yace ayau me? Kasamu wata ko? Anwar yace ni bance ba, kawaide wani abu nayi wanda banji dadinshi ba. Labarin abinda yafaru shida Nabila da kuma abunda Aunty tafada mashi yabashi.
Jinjina kai Dr, Shamsu yayi yace amma ai kai kace tazaba maka, ni dama tunda kacemun kabama Auntynku zabin mata arai na naji ban amince da shawararka ba.
Kasanfa halin mata Dr. Yanzu na tabbata zabinta beyi maka ba, kaga kuma idan kace bakaso ita bazataji dadi ba, dama ace Ummanka ce tayi maka zabe kace bakaso bazataji komai ba.
Anwar yace nide gaskiya yarinyar batayi mani ba, amma nace ma Aunty zanduba ingani. Yanzude ba wannan ba sonake inkara bama Nabila hakuri wlh tundazu fuskarta nake gani a idona.
Dariya Dr, Shamsu yayi yace kaide abokina fadi gaskiya anya ba Nabilar bace? Gira yadaga mashi. Murmushi Anwar yayi yace kai dan iskane wlh, bara inkira Rayyana inji ko sun koma gida. Dr, Shamsu yace kawai kace ta turo maka number Nabila nasan da biyu ka anshi number Rayyana. Dariya Anwar yayi yatashi yafita.
Da sallama su Rayyana suka shiga gida, a tsakar gida suka iske su Ummansu, sannu da aiki sukayi masu suka basu kayan da su Aunty suka bada akawo masu, suka nuna masu nasu.
Godiya sukayi Nabila tashige daki, dan tunda suka taho ranta yake abace, tun Rayyana tana mata magana hartagaji tayi shiru, da kallo Ummanta tabita, tacema Rayyana meyasamu yayar taki kuma?.
Rayyana tace wlh nima bansani ba tunda mukaje gidansu Aunty suka tafi dakin Laila to tana dawowa naga gaba daya tacanza, shine tace wai mutaho.
Umma tace kila kanta ke ciwo kin san halin Nabila idan kanta yana ciwo batason yawan magana. Umman Rayyana ta tabe baki aranta tana fadin bakin ciki ne kawai yake damunta Rayyana tayi miji.
Abdul ne yashigo dakinshi, yana ganinshi abude yagane Sageer yadawo danshi kadai yakeda key din kofar, harya aje kayanshi amma Sageer besan yashigo ba.
Zama yayi yadaki kafadarshi yace Dan masani lafiyarka kuwa wannan dogon tunani? Tashi zaune Sageer yayi yace uhm, kaide kawai Abdul ayi sha'ani, idan mutum yana duniya baze gama kallon abun mamaki ba.
Abdul yayi murmushi yace babu kamarku lauyoyi, shiyasa akullum nake kashe kunne idan naganka domin inji labari, kasan ku labari baya katse maku, yanzude kafadamun abunda yafaru dan naganka cikin damuwa.
Labarin abinda yaji kaf yafadama Abdul. Sosai Abdul ya girgiza dajin labarin Sageer, cike da tausayi Abdul yace Allah sarki, gaskiya na tausayama iyayen wannan yaro.
Babban abun tashin hankalin ma, kada su dorama wani laifin kisan, kasanfa wasu masu kudin basuda tausayi. Sageer yace shiyasa nazo gareka, meye abunyi Abdul?

Season 25 π€ 30
Numfasawa Abdul yayi yace babu wani abu da zakayi da yawuce ka kara kwantar da kai, kada kabari su fahimci kanaso kasan abinda suke ciki, aduk lokacin da kaga zasuyi wata magana idan kana gurin kayi kokarin barin wajen.
Amma karika bibiyarsu aboye hakan zesa ka kara fahimtar yanayin aikinka, kuma kasamu duk wani abinda kakeso. Amma tabbas Sageer har cikin zuciyata naji inaso atemaki wannan bawan Allah.
Kuma na tabbata sune zasuyi nasara domin babban lawyer ne kuma wanda yasan makamin aiki, kayi kokari kasamu wani abu, bance kabada sheda ba, amma ina me tabbatar maka idan kasamu wani abu daga shari'ar nan tozatayi maka ammafi wata rana.
A jiyar zuciya Sageer yayi yace shikenan abokina nagode, a kullum bana damuwa da duk wani abu daze shigemun duhu saboda nasan ina da kai, hakika zurfin ilimi bashine nasara ba.
Mutum yakasance me zurfin tunanin shine nasara arayuwa, Abdul kai jigone arayuwata Allah yabarmu tare kuma yayi maka sakayya da gidan aljanna. Abdul yace amin abokina, tashi muyi sallah muci abinci.
Rayyana tana zaune bayan tagama sallah wayarta tafara kara, saurin tashi tayi, ta dauka saurayinta ne, sede kuma sabuwar number ta gani, dauka tayi tare da sallama.
Murmushi Anwar yayi yace kai kanwata ko kina tsoron asaceki ne? Dariya Rayyana tayi domin tagane me magana, gaishe shi tayi yace lafiya lau ya kuka isa gida? Tace lafiya lau, su Umma suna maka godiya.
Yace haba ai bakomai, ina Yayarki? Rayyana tayi murmushi tace wlh tunda muka dawo tashige daki wai kanta yana ciwo, da alama akwai abinda yabata mata rai adakin Laila.
Domin tun bayan fitowarta daga dakin naga ranta yabaci, bayan kuma ba haka muka shigo ba, kuma nasan halin Yaya Nabila bakomai bane yake bata mata rai ba.
Gaba daya jiyayi beji dadi ba, shiru yayi can yace Allah sarki, kinga na manta ban anshi number dinta ba, kituromun in dubata, Rayyana tace toyanzu zanturo maka, godiya yayi mata yakashe wayar.
Jingina yayi da kujerarshi ya lumshe idonshi, babu abinda yakeson kara kallo kamar fuskarta, hakika betaba tsintar kanshi cikin soyayya ba amma ayau kadai ya fahimci yafada tarkonta.
Wayarshi tayi kara alamun kira, saurin dauka yayi ganin kanwarshi ce take kira, bayan sun gaisa ya tambayeta ya karatu? Tace yaya lafiya lau ai munkusa gamawa saura 1 month.
Yace lallai ashe muna da babban party. Dariya tayi tace Yaya dama Faisal ne yake so iyayenshi su zo. Ganin nakusa gama karatuna shine nace yabari nafada maka seka fadama Abba.
Dariya yayi yace lallai yarinyar nan, wato kin gama rayuwarki amakaranta, yanzu zaki gama amma bazaki bari kizauna damu ba harzaki fara maganar aure ko? Turo baki tayi tace kai Yaya!
Kafiso nima Abba yafaramun magana kamar yanda yake maka? Kuma fa bada nagama za'ayi auren ba, bayanma ko rana ba'a saba. Anwar yace naji kuma zan fada ma Abba bama seya dawo ba tunda de kanwar tawa tagirma.
Nadauka ma zaki jira Laila ai? Dariya tayi tace Yaya kasanfa bata gama karatun taba, yace hakane, Allah yasa alkhairi tace amin. Can tace yauwa Yaya dazu munyi waya da Umma take fada mun wai Aunty tazaba maka mata ko?
Daure fuska yayi kamar tana kallonshi yace wasa take maki, dariya tayi tace yaya fadamun batayi maka ba ko? Murmushi yayi yashafi fuskarshi yace gaskiya ne.
Tace ammade Yaya dagaji yau kana cikin farin ciki, da alama akwai magana abakinka fadamun. Murmushi yayi me sauti yace kanwata kawaide na mata laifi ne, hartayi kuka yanzu haka tana kwance kanta yana ciwo.
Jiran Rayyana nake ta turomun number dinta inkirata inkara bata hakuri kuma inji ya jikinta. Dariya sosai tayi tace Nabila ko? Murmushi yayi bece komai ba, tace tabbas itace, wayyo Allah na dadi kasheni yau Yayana yafada soyayya.
Kai amma naji dadi sosai, harna kosa indawo domin inga salon soyayyarka, zangani shin zaka iya shiga damuwa idan Nabila tana cikin fushi? Zaka kasa bacci dan bakaji muryarta ba?
Zaka iya bata kadan daga cikin lokacin aikinka da baka iya bama kowa? Shin zaka iya kwana 2, batare daka sata idonka ba? Uhm Yaya yanzu ne zaka gane abinda mukeyi ba shirme bane.
Domin ita soyayyar gaskiya bata boyuwa. Ajiyar zuciya yayi ya lumshe idonshi yanajin wani dadi da farin ciki suna saukar mashi, ahankali yace kanwata kicigaba da tayani addu'a nasan zan bata da Aunty domin kinsan yanda suke da Umman Rayyana.
Na tabbata saboda kada muhadu da Nabila yasa tace Laila ta kaita dakinta. Labarin duk abinda yafaru yafada mata. Sosai ta tausaya ma Yayanta. Hakika tun lokacin da Ummansu tace wai Aunty ce zata zabama yayansu mata tasan dole seta so kanta.
Tace kada kadamu Yaya, kaifa namiji ne, ko Umma da Abba bazasu iya zaba maka mata ba, bare kuma Aunty, duk da kaine kabata damar hakan, amma kaima kana da ikon zabar ra'ayinka.
Dan haka kawai kasameta kace Nabila kakeso, idan har da gaske tanason abinda kake so, kuma zabin tsakani da Allah tayi maka zata bi zabinka, domin dukansu daga gida daya suka fito idan ma tarbiyar ta keyimawa.
Anwar yace nagode kanwata, kuma zanyi abinda kikace, tabbas nasan soyayyar Nabila tashigeni cikin lokaci kankani, kuma bazan bari ta kwace mani ba, gashinan ta turo mani number dinta bara inkirata zan fada maki yanda mukayi da ita. Tace nagode yaya Allah yabada sa'a.
Daukar number dinta yayi kawai yashiga kira, seda ta katse bata dauka ba, kara kira yayi harta kusa katsewa ta dauka, ajiyar zuciya yayi, sallama tayi muryarta kasa kasa dan bacci takeyi.
Lumshe ido yayi lokacin da sallamarta tashiga cikin kunnuwanshi, da kyar ya amsa, yace Nabila ya kuka koma gida? Gyara kwanciyarta tayi jin muryar Yaya Anwar.
Daure fuska tayi tace lafiya lau, yajikinki naji Rayyana tace kanki yana ciwo ko? Uhm tace tayi shiru. Murmushi yayi dan ya lura haryanzu bata huce ba. A hankali kamar meyin rada yakira sunanta.
Saurin lumshe ido tayi dan seda tsigar jikinta ta tashi, wani abu taji ya ratsata tundaga kanta har kafarta. Kasa amsawa tayi, kara kiran sunanta yayi da kyar ta amsa.
Yace Nabila dan Allah kiyi hakuri da abinda yafaru dazu, wlh banji dadi ba, kiyafemun dan Allah. Murmushi tayi yanda taji yana marairai cewa kamar wata mace.
Sautin murmushinta yaji yace Nabila dariya kike mani ko? Tace a'a babu abinda nayi. Karka damu komai yawuce, tunda nafahimci bada gangan kayi mani ba komai yawuce.
Dan haka nayafe maka. Murmushi yayi yace nagode sosai, kuma inafatan zakiyi saving numberta murika gaisawa? Nabila tace ai dole inyi saving number mijin kanwata.
Jiyayi kamar tasara mashi adda, shiru yayi kamar ruwa yacishi, cigaba tayi da fadin Allah yasa muna da rai, musha biki, kaga yanzu ka kara zama..... cikin tsawa yace mata ya isa haka Nabila.
Kada kikara fada mani irin wannan maganar, nibansan da wata maganar aure tsakanina da Rayyana ba, dan haka bazan yafe maki ba idan har Rayyana tafara jin wannan maganar daga bakinki.
Babu wanda ya isa ya zabamun mata, dan haka ki iya bakinki. Cike da tsoro Nabila tace dan Allah Yaya kayi hakuri, wlh bansan haka maganar take ba, da banyi maka ita ba, amma bazan karaba.
Tausayinta yaji dan muryarta har rawa takeyi, kwantar da murya yayi kamar merada yace kiyi hakuri Nabila bazan kara maki tsawa ba, ki kwanta kihuta zankiraki anjima inji yanda kika tashi kinji Nabilata.
Kashe wayar yayi, yabarta da sakin baki, jitayi maganar tana mata yawo wai Nabilata? Anya ba kunnanta bane beji da kyau ba? Lumshe ido tayi tana kara tunanin abinda Aunty tace.
Tabbas tasan itace takeson hada Rayyana da Yaya Anwar. Amma da alama Rayyana batasan da maganar ba, domin bazata boye mata komai ba, amma bakomai zatabi asannu taji komai.
Anwar kuwa jiyayi kamar ansashi aljanna, rufe ido yayi soyayyar Nabila tana kara shigarshi, dariya yaji anyi tare da tafa hannu, hakan yasa yayi saurin bude idonshi.
Dr. Shamsu yagani, tsaki yaja yace amma wlh kai dan sa ido ne,ashe dama kana labe kanajin abinda nake fada ko? Dr. Shamsu yace bawani sa ido, kawai kace kafada soyayya.
Anwar yace wlh kuwa, abokina ina cikin matsala, ta kowane bangare akwai damuwa, domin nasan zansha wahala kafin Nabila ta amince dani, domin tasan da maganar hadina da Rayyana.
Kuma suna son junansu sosai, ni har tsoron fada mata abinda yake raina nake. Sannan adayan barin ga Aunty, nasan wannan maganar kila itace silar rashin jituwata da ita, dan Allah abokina kabani shawara.
Tura kofar office din sukayi domin yariga yasan da zuwansu. Saurin tashi D,P,O yayi yana fara'a yace sannunku da zuwa Brr. Yusuf, bismillah kuzauna.
Bayan sungama gaisawa D,P,O yace ai tunda naganka nasan harkar samuwace, domin ganinka alkhairi ne, shiyasa nake farin ciki da ganinka.
Murmushi brr, yayi yace hakane D,P,O. Nasan kaine wanda aka bama case din kisan kan da yaron gidan Alhaji Abbas me Dala yayi, wanda za'a shiga kotu aranar litinin, kuma nine lawyer dazan tsaya masu.
Dariya D,P,O yayi yace kwarai kuwa nine wanda aka bama case din, kuma sanin ko waye Alh. Abbas me Dala yasa ban bari kowa ya fahimci yaya case din yake ba.
Domin nasan kaine wanda zasu dauka ka tsaya masu, sanin amintakarmu yasa na hana kowa bibiyar case din, kuma yaro daya ne wanda akayi abun agabanshi, kuma abokin wanda aka kashe ne.
Sede duk wata sheda ta asibiti dasuka bani tundaga tambarin hannun wanda yayi kisan da sauran shedunsu duk kagansu nan. Murmushi Brr, yayi yace shiyasa nakeson aiki da kai, domin baka bani ciwon kai.
Yanzu inaso kabani file din gaba daya, sannan inaso ka hada wani file na karya tare da sauran shedun asibiti, inaso kazo dasu kotu ranar litinin. Kudinka naira million 3 ne.
Zaro ido D,P,O yayi tare da hadiyar miyau, washe baki yayi yana godiya, yace angama rankai dade. Amma batun tambarin hannun jikin wukar nawa yakamata asamu?
Brr. Umar yace kaifa babban dan sanda ne, kowa yasan yanda kuka kware da iya sharri, bekamata kayi mana wannan tambayar ba. Kodayake, kasan akwai bambanci tsakaninmu da ku.
Domin aiki da tunani yafi aiki da zuciya, to haka ne bambancin dake tsakaninmu daku.
Badamuwa zan baka satar amsa. Shi abokin nashi da yaga lokacin da akayi kisan, meye amfanin tambarin hannunshi?
Saurin kallonshi sukayi su duka, gira daya ya daga ma D,P,O rungumeshi Brr. Yusuf yayi suka sa dariya gaba daya.

Season 30 π€ 35
Tsagaita dariyar sukayi, Brr. Yusuf ya dafa kafadar Brr, Umar yace da kyau Umar, haka akeso shiyasa naji dadin zuwanka Office dina. Na tabbata wancan yaron baze taba bani goyon baya haka ba.
Nima kuma bazan taba nuna mashi asalin halina ba, bare yasamu damar zargina, dan ni banason harka da bare. Karbar account number din D,P,O yayi yamashi transfer din million 2, yace dayar se angama shari'a.
Kwankwasa kofar office din akayi, gaba daya seda suka zabura, turo kofar akayi, Masinjan shine yashigo dauke da wasu takardu. Gaishesu yayi yamikama D,P,O takardun.
Amsa yayi jikinshi asanyaye, yace amma Bukar dama kana bakin kofar nan? Saurin girgiza kai yayi yace ina can bakin kofar waje shine yallabai Salisu yakirani office dinshi yabani wadannan takardun yace nakawo maka.
Ajiyar zuciya yayi yace shikenan zaka iya tafiya, ka koma inda kake zankiraka, yace to nagode. Yana fita Brr. Umar yayi murmushi yace Yallabai ina ganinka kamar me dabara ashe baka da ita.
Tabbas bazakayi wuyar kamawa a kotu ba, haka zalika da ace kai lawyer ne bazaka taba yin nasara ba. A duk lokacin da kake cikin aikata wani abu na sirri.
Duk wanda yashigo kada kataba nuna alamar tsarguwa, domin zaka kama kanka, dan haka ka kara kula. Jinjina kai Brr, Yusuf yayi jinbayanin Umar. Godiya D,P,O yayi mashi sukayi masa sallama suka fita.
Rayyana ce tashigo dakinsu, Nabila tasamu tafito daga wanka, zama tayi tace yaya harkin tashi? Juyowa tayi tana murmushi tace natashi, Rayyana tace ya kan naki? Tace ai tunda nasamu nayi bacci shikenan ya warke.
Rayyana tayi murmushi tazo ta rungumeta ta baya tace harnaji dadi, wlh tundazu nadamu nadauka Laila ce tabata maki rai. Murmushi Nabila tayi tace wlh babu ruwanta.
Zama Rayyana tayi tace yauwa Yaya Anwar yakiraki? Seda gaban Nabila yafadi, tace e yakirani yadubani da jiki. Rayyana tayi dariya tace ai nice nafada mashi bakida lafiya, kuma natura mashi number dinki.
Rayyana tace ai Yaya Anwar yanada kirki duk yafi yangidansu dagashi se Yaya Zaituna kodan dakinsu daya? Nabila tace gaskiya sunada kirki. Rayyana tace kishirya muje muci abinci.
Gyara zama Dr. Shamsu yayi yace kasan mezakayi abokina? Tunda de kace haryanzu Rayyana batasan da maganar ba, kawai kabiyo tawajenta hakan zefiyimaka sauki.
Domin idan har tariga tasan maganar aurenku dole zata fadama Nabila, kaga ita kuma bazata taba yarda taci amanar kanwarta ba, amma idan Rayyana tasan kariga fadin kanason Nabila to idan Ummansu tayi mata magana itama bazata amince ba.
Murmushi Anwar yayi yace kai abokina, shiyasa nake sonka, kanka yanaja sosai wlh. Dan haka yanzu base anjima ba zankira Rayyana kasan ance abari yahuce shike jawo rabon wani.
Bugu biyu Rayyana tadauka, bayan sun gaisa yace yauwa kanwata inafatan ke daya ce? Tace a'a, yace to inaso kitashi kibar wajen zamuyi wata magana.
Kallon Nabila tayi wadda suke cin abinci, tashi tayi Nabila tace gulmamma yanzu haka wannan yaron ne.
Bayan tazauna tace inajinka Yaya. Yace yauwa kanwata, wani abu nagani agidanku, shine nace bara nayima kanwata magana kozata iya tayani nemanshi.
Shiru Rayyana tayi cikin rashin fahimta tace bangane ba Yaya? Murmushi yayi yace nasande kanwata zata iya bani duk abinda nakeso, naga Yayarki kuma naji inasonta shine nace bara nayima kanwata magana danni kunya nakeji nasan zaki shige mani gaba.
Dariya Rayyana tayi tace kai amma naji dadi sosai Yaya, wlh kamar kasani Yaya Nabila sam bata kula samari, amma naji dadi, kuma zanyi mata magana nasan zata amince da kai.
Lumshe ido yayi, sosai yaji dadin abinda Rayyana tafada, yace nagode kanwata dole inbaki tukuicin wannan magana da kikayi, nabaki nan da anjima zankiraki inji idan kin fada mata.
Tace kada kadamu zanfada mata yanzu ma. Sallama sukayi ta tashi cike da farin ciki tafita. Dariya yayi yamika ma Dr. Shamsu hannu suka gaisa.
Yace gaskiya abokina shawararka tayi, kaga ni kuma se indage domin cusa ma Nabila soyayyata, nasan zansha wahala amma bakomai, dama duk wani abu na alkhairi ba'a samunshi tasauki. Dr. Shamsu yace yanzu kam seka tashi muje round ko. Dariya sukayi suka fita.
Aunty ce takira Umman Rayyana awaya, bayan sun gaisa tace ina fatan Rayyana ta fada maki labari medadi, dan naga Anwar ya amshi number dinta? Mirmushi Umma tayi tace inaji be kirata ba, kila yana aiki.
Aunty tace hakane, kinsan dan nawa akwai bama aiki muhimmanci, amma nasan zuwa dare zasuyi waya. Umma tace wlh naji dadin wannan hadin, shiyasa akace kobakayi arziki ba inde ka haifi mace to kagama arziki.
Aunty tace ai su sun dauka wannan soyayyar dana ke gwada mashi ta gaskiya ce, ashema bana kinshin kaina, su duka matan Alh, suna da yara maza, ni kuma mata gareni.
Ai,kema kinsan bazan bari ashani banza ba. Dariya Umma tayi tace ai dama seda nayi wannan tunanin, nasanki Falmata bakida kyau, Aunty tace aikede kawai kizuba ido.
Ni kadai nasan abinda nake kullawa, wlh bazan bari nasha wahalar banza ba, shima Alhajin ina zuwa kanshi, nafiso nagama da danshi, dole ne yakarbi zabina, idan kuma ba haka ba. Uhm.
Umma tace ai aurenshi da Rayyana yazama dole, dan haka ki kwantar da hankalinki, ba fa daga karkara muke ba, bazamu zauna a nuna mana komai ba. Aunty tace shikenan sena jiki, zuwa gobe.
Suna gama waya takira Abbansu Ilham bayan sun gama gaisawa yace waini lafiya naji bakinki yaki rufuwa, kode wani albishir za'a fada mani? Dariya Aunty tayi tace sosai ma kuwa.
Amma dole abani goron albishir, yace to fada mani inji, tace to yaude inaso kayima Allah godiya domin ka kusa zama Kaka. Yace kamar ya? Kina nufin kinsamo ma Dr, matar? Tace emana.
Kuma auren gida zanmashi, kasan yanzu kafin kabari danka yadauko maka wata bare, gara kabashi wadda kayarda da tarbiyarta, kuma kasan gidanmu gidan tarbiyane, bazanso akawo wata wadda zata shigo ta bata mana tarbiyar gida ba.
Rayyana diyar Yakumbota itace nazaba mashi, kasan mahaifinsu yanada kula da yaranshi, dan ko Jami'a be barsu suntafi ba, kuma haryanzu suna zuwa islamiya kasan kuwa sunada tarbiya.
Murmushi Abba yayi yace kai amma naji dadin wanna labari, kinga se a hada da bikin Zaituna tunda tasamu miji, dan munyi waya da Dr, dazu yake fada mani iyayen saurayinta Faisal zasuzo.
Jitayi kamar ya watsa mata ruwan zafi, cike da tashin hankali tace yaushe akayi wanna maganar bamu sani ba? Kuma kamanta kace kozasuyi aure se sungama karatu? Yace ina sane, ko kin manta saura wata 1 tagama makarantar ta?
Ajiyar zuciya tayi tace amma ai nadauka tare za'a hadasu ita da Laila tunda itama befi wata 5 tagama ba. Yace ita Lailan tanada tsayayye ne? Tace bazata rasa ba, ammade nafiso ace anyi bikin dana shikadai musha biki tunda shi namiji ne.
Abba yace a'a tunda sun samu atare kawai tare zanyi masu, idan yaso idan ita tagama se ayi nata daga baya, kinsan ni banason jan biki dayawa, idan sunzo ma kawai zansa shi wata 2 ne, kinga tagama da wata 1.
Amma kome kenan zanzo gidan gobe asabar, dan lahadi zasuzo banyi niyar zuwa wannan satin ba, amma dole inzo. Ki gaishe da mutanan gidan, zankira Umman yara infada mata, kyautarki kuma senazo.
Kashe wayar tayi zuciyarta cike da bakin ciki, wato yaranta za,a bari agida kenan? Lallai kam akwai matsala bazata bari Zaituna tayi aure tabar Laila ba.
Cike da farin ciki Abba yakira Anwar, yana dauka suka gaisa Abba yace Dr, shine dazu baka fadamun nima zanje neman aure ba? Murmushi yayi yace auren wa kuma Abba?
Yace naka da Rayyana mana. Anwar yace wace Rayyana kuma? Aini Nabila nakeso. Cike da mamaki Abba yace kamar ya? Ba kaine kabata zabi ba, kuma yanzu tayi maka zabi sekace bakaso.
Anwar yace hakane Abba, amma kasan zuciya akwai abinda takeso, gaskiya ansamu akasi, domin nide naga Nabila Yayar Rayyana kuma naji ina sonta sede ban fadama Aunty ba, inaso inafara fadama Nabilar sannan.
Abba yace bangane ba? Labarin komai yabashi, kamar zeyi kuka, sosai Abba yatausaya mashi, daga jin yanda yake magana yasan yaronshi yakamu da soyayya. Lallashin shi yayi yace kayi hkr gobe zanzo gidan.
Idan yaso zamuyi magana, ai bawani abu bane itade fatan ta kasamu me tarbiya, to tunda daga gida daya suka fito ai babu damuwa, kuma kace ita Rayyanar batasan da maganar ba.
Kaga abin zezo dasauki, kada kadamu kanka,yace nagode Abba sekazo Allah ya kiyaye hanya.
Bata fuska Nabila tayi jin abinda Rayyana tafada tana dariya. Nabila tace naga alama kin maidani abokiyar wasanki. Rayyana tace wlh ba wasa nakeyi ba kinsan Allah Yaya yakamu da sonki.
Tunda har ya iya kirana yafada mani to bakaramin so yake maki ba. Kawai ki amince mashi tunda bakida wani saurayi, kinga semusha biki. Nabila tace, ke ki aureshi mana.
Dariya tayi tace ammade ai kinsan inada wanda nakeso ko? Nabila tace toni bana sonshi, Rayyana ta kwantar da murya tace wlh banyarda ba, kawaide jan aji zakiyi, amma babu macen dazataga Yaya Anwar tace bemata ba.
Nabila tace hada ke ko? Shiru Rayyana tayi tace ammade aibani yace yanaso ba. Nabila tace idan kuma akace keze aura yazakiyi? Rayyana tace kibar wannan maganar Yaya, bama zefaru ba, nide dan Allah ki amince.
Tashi Nabila tayi tace nace maki banaso ko. Daki tashige tabarta. Dariya Rayyana tayi tace zama ki sauko nasan Yayartawa ai.
Da dare bayan Anwar ya kwanta yajawo wayarshi domin kiran Nabila, seda tayi ringing 2 bata dauka ba, Rayyana tace haba Yaya dan Allah kidauka kinsan fa babu kyau wulakanci, kuma atunani na Yaya yafi karfin wulakanci agurinki, sede idan akwai wata matsala da kike boye mani.
Saurin daukar wayar tayi dan bataso Rayyana ta fahimci wani abu, ajiyar zuciya yayi yace haba Beelert, har kinsa zazzabi yafara saukar mani na rashin daukar wayarki.
Jitayi tsigar jikinta ta tashi, shiru tayi batace komai ba. Murmushi yayi yace kiyi hakuri natasheki bacci ko? Ina fatan kinsamu sakona awajen kanwata?
Nabila tace yaya dan Allah inrokeka wani abu? Yace idan har bacewa zakiyi in kyaleki ba, ni kuma zanyi abinda kikeso. Runtse ido tayi batace komai ba. Cigaba yayi da fadin wlh, Beelert bantaba fadawa aoyayya ba se akanki.
Ki tausaya mani kada kice baki sona saboda abinda su Aunty sukace, nasan zamu fuskanci matsala, amma idan mukayi hakuri komai ze wuce, inasonki, son da bantaba yima wata ba.
Idan kika barni Allah kadai yasan halin dazan shiga, kinga ni liktan yarane, idan har bansamu kulawarki ba, mutane dayawa zasu rasa natsuwata, wanda yin hakan hatsari ne, ga lafiyar yara.
Beelert dan Allah ki amsa rokona. Hawaye ne suka sauko daga idanuwan Nabila, tabbas tasan karya take idan tace batason Anwar, sede tayi alkawarin ko sonshi ze kasheta bazata amince dashi ba.
Domin Rayyana akeso ya aura ba itaba, idan har ta amince tasan zata hura wutar kiyayya atsakanin gida biyu, wanda tunda ta taso ko musayar yawu bata taba ganin iyayensu sunyi ba.
Kayi hakuri Yaya Anwar, shine abinda ta iya fada tayi saurin kashe wayarta. Koda yakira akashe yajita, hakan yasa yakoma ya kwanta, beyi aune ba, yaji kwalla tana zuba daga idonshi.

Season 35 π€ 40
INA MIKA GODIYATA GA DUKKANIN MASOYANA. NAGODE DA ADDU'AR KU AGARE NI. ALLAH YABAR ZUMUNCI.
WANNAN SHAFIN NAKU NE, MASOYANA NA NABEELERT LADY NOVELS 1 & 2ππππ
Washe gari haka Anwar da Nabila suka tashi gaba dayansu jikinsu a sanyaye, bakamar Anwar, domin ko dakinshi yakasa fitowa.
Duk da yakasance asabar ce, amma yana zuwa asibiti kuma da wuri, sede yau har 10 tayi befito ba, kuma ba bacci yake ba. Gaba daya tunanin Nabila yakeyi.
Sonta da kaunarta sunkara shiga zuciyarshi, gashi haryanzu taki bude wayarta, kuma bayaso yakira Rayyana kada Ummanta ta fahimci wani abu.
^^^^^^ ^^^^^^
Zaune suke afalo suna fira, Aunty tace wai ni yau dana ko sakko yayi ne banjishi ba tundazu? Umma tace wlh nima haka, nadauka ma ko daga masallaci yawuce asibiti amma kuma dana duba kofa naganta akulle alamun be je masallaci ba.
Aunty tace gaskiya inaji ba lafiya ba, bara na duba, amma mutumin da 10 a asibiti takeyi mashi gashi har 11 takusa amma befito ba.
Kwankwasa kofar tayi alokacin yana bandaki, jin be amsa ba, yasa tashiga, karar ruwan dataji tagane wanka yakeyi, fita tayi tajawo mashi kofar. Komawa tayi tafada masu yana wanka.
^^^^^^ ^^^^^^
Umman Nabila ta kalleta tace meyasa bakije islamiyya yau ba? Shiru tayi batace komai ba. Umma tace magana nake maki fa, ko haryanzu baki warke ba? Daga mata kai tayi.
Umma tace amma dana tambayi Rayyana cewa tayi kince bazakije ba, sede ita kadai ta tafi, kina tsammanin idan Babanku yaji yau bakije makarantar safe ba baze maki fada ba?
Dukar ta kai kasa Nabila tayi tace Allah Umma banajin dadin jikina, kuma nasan konaje bazanji dadin karatun ba, kuma ma yau ba hadda za'a amsa ba kari ne za'ayi kuma na iya wajen.
Umma tace shikenan, ni nasan akwai abinda yake damunki tunda kuka dawo daga gidan Haj. Falmata kika canza, kawaide bakiso ki fada mani ne, kuma ba haka nasanki ba.
Kwallace ta cicciko a idanuwanta, tashi tayi tashige dakin Ummanta domin atsakar gida suke. Ganin haka yasa itama Umma tabita, domin tasan idan tanason fada mata wani abu dakinta take shiga.
Zaune tasameta tana share hawaye, zama tayi tace fadamun damuwarki Nabila, kinsan tunda muke dake bana boye maki komai, kuma kema haka, duk duniyar nan ni kadaice zaki fadamun damuwarki nabaki shawara tagari babu son zuciya acikinta.
Dago kai tayi tafada mata duk abinda yake faruwa, tun daga zuwansu gidansu Anwar, da maganar dataji Aunty tanayi da Laila, da abinda Anwar yayi mata, da kuma maganar soyayyar da yayi mata.
Ajiyar zuciya Umma tayi Nabila kuma tacigaba da kuka. Dafata Umma tayi tace kiyi hakuri inaso kisani duk wani abu da kika ga yafaru da bawa Allah ne ya shirya mashi.
Kuma duk abinda Allah yaso ya faru seya faru, babban misali kalli yanda suka so kada Anwar ya ganki, amma duk da haka kece ma yafara gani. Aini dama tunda naga Ummanku tasaka Rayyana tayi kwalliya zata aiketa gidan jikina yabani wani abu.
Dan haka inaso daga yau kirage bacci, idan bazaki iya tashi tsakiyar dare ba, kitashi kamar 4:30 kiyi sallah ki kai kukanki gurin Allah, kibashi zabi, domin Allah yana sakkowa dede wannan lokacin domin yaga bayinsa masu neman kusanci agareshi, kuma yana karbar addu'arsu.
Kada ki gajiya, kibarma Allah zabi shikadai yasan alkhairin dayake cikin wannan al'amarin, danni banji wata damuwa ba, sede ina rokon Allah ya takaita fitinar dazata taso agidan nan, domin nasan halin Ummanku.
Saboda haka inaso kisaki jikinki, kuma banaso kirika wulakanta Anwar domin wulakanci beda dadi, saboda ko be aureki ba zerika jin haushin irin wulakancin da kikayi masa. Allah yayi maki zabin alkhairi, tashi kije kiyi wanka.
^^^^^^ ^^^^^^^
Sageer ne shida Abdul a adedeta zasuje shagon Abdul. Domin yau asabar babu aiki. Tafe suke suna fira, sun shiga kwana kenan me adedetar yayi saurin taka burki.
Gaba dayansu seda suka kusa bigewa, wata budurwace sanye da hijabi tsugunne tana kwashe kayan miyar data siyo tazo tsallaka titin unguwarsu ledar ta tsinke.
Horn me adedetar yake yimata amma ko motsawa batayi ba, tsintar kayanta kawai takeyi, cikin bacin rai Sageer yafita, yana zuwa yasa hannu ya fincikota ya jata gefe guda.
Saurin saukowa Abdul yayi yana fadin haba Sageer kayi mata ahankali mana, baka ganin cikin layi ne ba babban titi ba, kuma ai bari tayi take kwashewa ko. Kallonta Sageer yayi itako duk a tsorace take binshi da ido.
Sageer yace ke bakiji ne ana maki horn amma kinyi zamanki kamar kina cikin gidanku, yanzu idan aka bigeki kuma kijamana kashe kudi ko? Kallonshi kawai take tana bin bakinshi da ido.
Abdul ya mika mata ledar daya gama kwashe mata kayan miyar, amsa tayi tamashi alamar godiya cikin sigar kurumta. Nuni Abdul yayi mata yana tambayarta batajine? Kai tadaga mashi alamun e.
Jikin Sageer ne yayi sanyi, tausayinta duk yakamashi,sam beji dadin abinda yayi mata ba, karbar ledar tayi ta kalli Sageer tasakar mashi murmushi tawuce.
Hannunshi Abdul yakama suka hau adedetar, Abdul yace Allah sarki ashema kurma ce, shiyasa bataji karar horn ba. Me adedetar yace wayyo har naji tausayinta. Sageer kuwa bema san abinda suke fada ba, ita kawai yake kallo har tashige wani gida, da alama shine gidansu.
^^^^^^ ^^^^^^
Bayan Anwar yaci abinci suna zaune afalo, Aunty tanason tayi mashi maganar Rayyana amma bataso Umma taga kamar itace takeson abun. Karar horn sukaji, Laila tace kai amma Abba yayi sauri.
Tashi Anwar yayi yafita domin tarboshi. Bayan yayi parking yafito Anwar yaje da sauri ya karbi jakarshi yana fadin sannu da zuwa Abba. Hannu ya mikashi suka gaisa yana murmushi yace nasameku lafiya ko Dr? Yace lafiya lau.
Bayan yashiga ciki suka gaisa ya wuce dakinshi shida Aunty domin ranar girkinta ne, seda yayi wanka yaci abinci sannan ya kwanta ya huta kafin azahar.
^^^^^^ ^^^^^^^
Zaune suke afalo bayan sungama cin abinci, Abba yace kamar yanda nafada maku gobe iyayen yaron da yake neman Zaituna zasu zo, Alhamdulillahi tunda shima Dr, yasamu wadda yakeso kawai se a tsaida rana lokaci guda.
Murmushi Aunty tasaki tana fadin gaskiya ai muna da hidima babba agidan nan, Umma tace Allah yasanya alkhairi, Abba yace amin. Naso ace inje neman auren buduwar Dr, zuwa gobe, amma yacemun inbari se wani satin tunda gobe muna da baki kuma agoben zan koma.
Aunty tace ai bakomai inde dan Rayyana ce ni kaina na isa in nema mashi aurenta tunda diyata ce. Murmushi Abba yayi yace Rayyana ko kuma Nabila?
Aunty tace Rayyana de, ai ita yagani kuma itace nazaba mashi. Abba yace Dr, acikinsu wacece kake so? Anwar yace Abba ni Nabila nakeso domin itace nafara gani kuma ita naji ta kwanta mani.
Saurin tashi Aunty tayi tace Anwar wace irin Nabila kuma? Amma de ai Rayyana nafada maka nazaba maka yaushe ma kaga wata Nabila da har zakace ita kafara gani?
Anwar yace Aunty adakin Laila naganta kuma ma ko banganta ba sedaga baya ai so daya ne, nide wlh ita nakeso. Aunty tace kam bala'in nan, wlh inde ina da rai Rayyana zaka aura.
Inaso inzaba maka yarinya yar gidan mutunci me tarbiya amma zaka watsa mani kasa a ido, ko kunyar idona bakaji ba kace bakason diyata.
Abba yace ya isa haka Auntyn Yara, zauna, banason tashin hankali kema kinsani zama tayi tana huci. Umma kuwa tazama yar kallo, domin batasan da bayanin wadda aka zaba ma Anwar ba. Duk da dama tasan baze wuce Rayyana ba, tunda itace yar uwarta.
Abba ya kalli Aunty yace yanzu ke wace irin yarinya kikeso danki ya aura? Aunty tace nafison wadda tafito dga gidan mutunci me tarbiya. Murmushi Abba yayi yace da Rayyana da Nabila ai duk gidansu daya ko?
Kai tadaga mashi, yace yauwa, kuma duk tarbiya daya suka samu, dan haka ina ganin babu wata matsala dan yace Nabila yakeso, ai duk daya ne. Aunty tace wlh ba daya bane domin kowa nonon uwarshi yasha, kuma ni nasan ko wacece Yakumbo, nasan asalinta amma bansan wacece Umman Nabila ba.
Ganin zataja magana da tsawo yasa Abba ya daure fuska ya kalli Anwar yace Dr, wa kakeso fada mani? Yace Abba Nabila nakeso, ina matukar sonta, wlh zan iya shiga matsala idan har narasa Nabila.
Sosai Abba da Umma Sukaji tausayinshi, ganin yanda idanuwanshi suka canza lokaci guda. Dafashi Abba yayi yace kwantar da hankalinka Dr, duk abinda kakeso shizanyi maka, koda zan rasa dukiyata zan sama maka farin ciki.
Rungumeshi Anwar yayi yana murmushi, tashi Aunty tayi tabar wajen zuciyarta kamar zata fashe saboda bakin ciki. Da kallo suka bita, Umma tace gaskiya banji dadin abinda yafaru ba, kabata dama tayi maka zabi kuma daga baya kace bakaso.
Abba yace kada kidamu zan fahimtar da ita, yanzu tana cikin fushi bazataji lallashi ba. Kuma duk abinda kikaga yafaru Allah ne yashirya abinsa, dan haka banaso kiyi jayayya da hukuncin ubangiji domin shine yafimu sanin dede.
Addu'a ita tafi kamata kiyi mashi amatsayinki na mahaifiyarshi. Umma tace shikenan Allah yayi mashi zabi mafi alkhairi. Abba yace yauwa ko kefa, amin.
Laila ta tsunkulo kafar Anwar tana murmushi kallonta yayi shima yayi murmushi yatashi ya nufi dakinshi, yana zuwa ya fada saman gadonshi yana cike da farin ciki, wayarshi yajawo yana addu'ar Allah yasa ta kunna wayar.
^^^^^ ^^^^^
Zaune suke adakinsu suna fira Rayyana tace namanta kawarki tana gaisheki, Nabila tace baki fada mata banda lafiya ba? Rayyana tace meya sameki? Harararta Nabila tayi tace bansani ba
Dariya Rayyana tayi tace kawai kice ciwon soyayya kikeyi kawai malama, amma bawai ciwo ba, Nabila tace Allah kin rai nani sosai Rayyana, dawa nake soyayya? Karan wayarta ne yasa sukayi shiru.
Kallon wayar Nabila tayi bata dauka ba, dariya Rayyana tayi tace ga maganinki nan yakira kidauka, turo kofar dakinsu akayi harseda suka tsorata. Umman Rayyana ce tashigo ranta abace.
Kallon Rayyana tayi tace inata kiranki kina nan kina zuba kamar wata Jakadiya, dalla ni taso kibiyoni daki ina son ganinki. Cike da mamaki Nabila take kallonta,
Jiki asanyaye Rayyana tabi bayanta, kirane yakara shigowa wayarta hannu tasa tadauki wayar, ajiyar zuciya Anwar yayi yace haba Beelert, duk kinsa bawan Allah yashiga damuwa.
Yau itace ranar farko dana ki zuwa asibiti saboda damuwa, kuma duk saboda kece yasa banje ba, wlh nashiga damuwa saboda rashinki, bazan iya jurar rasaki arayuwata ba.
Dan Allah kisoni kada kiyi la'akari da maganar Rayyana kidauka Allah ne ya hadamu kawai,lumshe ido Nabila tayi duk tausayinshi yakamata jin yanda lokaci guda yakamu da soyayyarta.
A hankali tace kayi hakuri Yaya Anwar idan nabata maka rai, bazan kara ba, cike dajin dadi yace kina nufin kin amince da soyayyata? Zaki aure ni? Murmushi tayi batace komai ba.
Anwar yace nagode Beelert Allah yayi maki albarka ya kuma tabbatar mana da abinda yafi zama alkhairi, wlh dande kada intakura maki da yanzu zaki ganni gidanku, amma anjima zanzo da dare, inafatan kina maraba dani?
Kai tadaga mashi kamar yana kallonta, yace magana zakimun inji dadi Beelert, plsss kice kina sona inji dadi dan Allah, Nabila tace kai Yaya gaskiya bayanzu ba, yace dan Allah fa nace. Runtse idonta tayi tace inasonka Yaya na.
Dif takashe wayar ta cusa kanta cikin pillow tana murmushi jitake kamar zata nutse saboda kunya. Shikam Anwar pillow dinshi ya rungume yana dariya.
^^^^^ ^^^^^
A tsaye ta iske Ummanta tana zagayen daki fuskarta sam babu alamun wasa aciki, zama tayi tace gani Umma, itama zaman tayi cike da bacin rai tace Rayyana meke tsakanin Anwar da Nabila?
Murmushi tayi tace uhm Umma mun kusa shan biki agidan nan fa, wlh yaya Anwar son Yaya Nabila yakeyi, kuma ni yafada mawa na fada mata ma.
Umma tace saboda ke kuma kina sakarya ba, kin wani saki baki kina fadamun wai sonta yakeyi, bakisan komai ba shiyasa har kika iya goya mashi baya........... Labarin dalilin dayasa ta aiketa gidansu Anwar da abinda suke kullawa da Aunty ta bata.
Sannan tace dan haka inaso ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada maki, kozanyi yawo tsirara sekin auri Anwar, domin kece aka zaba mashi tun farko.
Dan haka daga yau kidaura dammarar kwatar Anwar idan har kinaso incigaba da kiranki diyata. Base nabaki shawarar yanda zaki jawo hankalinshi ba, domin,kema macece.
Tana gama fadin haka tashige daki. Zubewa kasa Rayyana tayi tasaki wani kuka, hannu ta dora akai tace nashiga ukku ni Rayyana wace irin fitina ce haka?
π€·π»♀π€·π»♀π€·π»♀ Nima nace bansani ba!!!!

0 comments:
Post a Comment