Haka Rayyana ta wuni acikin dakin Ummanta se kuka takeyi sam takasa fitowa dan bataso Nabila ta tambayeta abinda yake damunta, saboda duk wanda yaganta yasan tasha kuka.
Nabila kuwa ganin bata dawo ba tadauka ko aikenta Ummansu tayi, haka ta kwanta tana me cike da farin ciki, tunanin Anwar kawai takeyi, jitake kamar tajawo dare kawai danta ganshi. Har lokacin islamiyya yayi Rayyana bata fito ba.
Hakan yasa da Nabila tashirya tashiga falon su Rayyana dan taji kota dawo, Ummanta tasamu azaune tana kallo, sallama tayi da kyar ta amsa, gaisheta tayi tace Umma ko kin aiki Rayyana ne?
Banza tayi da ita har seda ta maimata sannan ta kalleta cike da bacin rai tace idan na aiketa se akayi yaya? Nabila cike da mamaki tace bakomai dama makaranta zamuje shine banga tafito ba.
Tashi Umma tayi fuska adaure tace to bakar munafuka, ke yanzu ko kunya bakiji ba, kika iya anshema kanwarki saurayi? To bara kiji nafada maki, daga yau babu inda zaku kara fita keda Rayyana.
Dama shegen bakin jini gareki shiyasa kike like mata kuna fita, ranar badake na aiketa gidan su Anwar ba, amma saboda kinsan akwai namiji agidan shiyasa kika nace seda kika bita, kuma kina zuwa kikasan yanda kikayi kika yaudareshi harya fada tarkonki.
To wlh koma me zefaru se Rayyana ta auri Anwar, domin itace aka fara zaba mashi. Da gudu Nabila ta fita dakin tana kuka, a tsakar gida ta wuce Ummanta tana aiki, duk abinda sukeyi tana jinsu.
Bin Nabila tayi dakin tasameta tana kuka, zama tayi tana bata hakuri, sannan tace kinajina ko Nabila, kada wannan maganar ta tsorata ki, idan har kinason Anwar kada ki kuskura wannan maganar tasaki canza mashi.
Allah ne yahadaku babu wanda ya isa yarabaku, dan haka tashi ki wanke fuskarki kitafi makaranta, kuma bance kicanza ma Rayyana ba, sede idan itace tacanza maki, tashi kije Allah yayi maki albarka.
Tashi Nabila tayi ta wanke fuskarta ta tafi makaranta, koda taje ba komai take fahimta ba har aka tashi. Zarah ce take tambayarta abinda yake damunta.
Sanin basa boyema junansu komai yasa Nabila tafada mata duk abinda yake faruwa, sosai Zarah ta tausaya ma kawarta domin tasanta akwai hakuri. Zarah tace kinaji ko Nabila?
Kada kibari barazanar Umma tasaki hakura da Anwar, daga jin yanda kika bani labarin nasan kina sonshi, kuma shima yana matukar kaunarki, dan haka mucigaba da addu'a, idan har rabonki ne wlh sekin aureshi.
Kada ma kibari yasan akwai matsala,agidanku, sede idan shine ya tambayeki, kuma kada ki boye mashi domin yasan hakan ze faru, kima godema Allah da ba Ummanshi bace tayi mashi wannan zabin.
Nabila tace nagode Zarah, kuma insha Allah zanyi yanda kikace, nima har a raina naji bazan iya hakura da Yaya Anwar ba, so daya kawai mukayi wayar soyayya dashi amma jinake kamar munfi wata atare. Zarah tayi murmushi tace yauwa kawata, haka nakeso, nizan wuce senajiki.
^^^^^^^ ^^^^^^^
A gidansu Anwar kuwa duk yanda Abba yaso yashawo kan Aunty yakasa, lallashi babu irin wanda beyi mata ba, amma sam tasaka rigar rashin mutunci ajikinta.
A ranar ko abinci bata kawo mashi ba, sede yafita gurin Umman Anwar yaci, ganin zata bata mashi rai yasa shima ya shareta, dama yanayi ne, dan kada tace ba'a kyauta mata ba, kuma yafita hakkinta.
Gaba daya gidan seyayi masu babu dadi, Anwar kuwa se hakuri yake bama Abbansu, gani yake ta sanadiyarshi ansamu matsala akaro na farko acikin gidansu. Abba yadafashi yace kada kadamu Dr, dama duk inda kasamu ana zaman lafiya, dole ne wata rana asaba.
Dan haka kada kasa wannan abun aranka yadameka, komai ze wuce, so dayawa idan irin haka tafaru agida, daga karshe alkhairi ne yake biyowa baya, domin baka taba sanin zuciyar makiyinka se wani abu yahadoku, na bacin rai.
Shiyasa wani lokacin idan zaman lafiya yayi yawa mutum baya taba gano makiyinshi da kuma masoyinshi na gaskiya, wannan abun daya faru iname tabbatar maka nan gaba zaka gane abinda nake nufi, fatan mu de Allah ya takaita wannan fitina.
Anwar yace amin, kallon agogon ahannunshi yayi, murmushi Abba yayi yace Nabila ko? Dukar da kai kasa yayi yana murmushi. Abba yace to agaishemun da ita, tashi yayi yana sosa kai.
^^^^^^^^^ ^^^^^^^^^^
Nabila ce tafito daga dakinsu, se kamshi takeyi tace ma Ummansu zataje Yaya Anwar yazo, Umma tace to bari infada ma Babanku kada yafito yaganku bazeji dadi ba.
Falonshi tashiga yana zaune yagama cin abinci, zama tayi tana murmushi tace harka gama? Yace wlh kuwa, kallonta yayi yace kamar akwai magana abakinki ko? Kai tadaga tana murmushi.
Shima murmushi yayi yace kode munsami suriki ne agidan? Dariya tayi tace kamar kasani kuwa, Anwar dan gidan Alhaji Lamido Jaye ne yazo gurin Nabila, rannan sunje gidan ita da Rayyana yaganta yace yanaso, shine yazo yanzu, senace bara afada maka.
Dariya yayi yace lallai kam nasamu suriki, domin gidan Alh, Lamido gidane me tarbiyya, Allah yasanya alkhairi, kuma kifada mata idan yasamu lokaci inason ganinshi.
^^^^^^^^ ^^^^^^^^
Jingine yake jikin mota ya hade hannuwanshi guda 2 asaman kirjinshi, kofar gidan kawai ya tsurama ido, gyara tsayuwa yayi ganin tafito kanta akasa tana tafiya,
Tunkafin takaraso kamshinta ya doki hancinsa, da sallama ta isa gurinshi, kallonta yayi fuskarshi dauke da murmushi ya amsa, daga gefenshi ta tsaya itama ta jingina da motar.
Kallonshi tayi tace yaya ina wuni? Yace lafiya lau Beelert dita, inafatan nasameki lafiya? Tace lafiya lau yasu Laila da Umma? Yace duk suna lafiya Abba ma yace nagaisheki.
Murmushi tayi tace ina amsawa, yace ina kanwata nadauka zata rakoki ai? Dukar da kanta kasa tayi tace ai ta kwanta, kallonta yayi yace anya? Tace da gaske fa nakeyi.
Murmushi yayi yace Beelert bansanki da karya ba, yaune nafara zuwa gurinki, kuma Rayyana tana me farin ciki da wannan tarayya tamu, nasan yanda kuke ku biyu agidan nan, dole shakuwarku zatayi yawa.
Idan har da gaske babu abinda yafaru ni na tabbata kafin kifito dole Rayyana ce zata fara zuwa gurina, plssss Beelert banaso mu kulla wannan soyayyar tamu da haka, narigada nasan duk abinda yake faruwa akan soyayyarmu.
Dan haka bekamata ace murika boyema junanmu wani abu ba, domin fadin zeyi mana amfani, kuma musan yanda zamu bulloma matsalar. Dan haka kidaukeni amtsayin masoyinki, dan uwanki kuma abokin shawararki.
Dan Allah kifadamun abinda yake faruwa acikin gidanku, nima zan fada maki komai dan Allah🙏🏻🙏🏻. Kallonshi tayi cike da tausayi tafada mashi duk abinda Umman Rayyana tace mata, da kuma abinda Babansu yafada.
Murmushi yayi yace Allah sarki Beelert dita, kiyi hakuri da duk abinda aka maki, dama wanda za'a maki nan gaba, insha Allah komai ze wuce, kamar yanda Abbana yace baka taba gane makiyinka se bacin rai yashiga tsakaninku.
Saboda haka kawai kibar damun kanki, nasan ke macece kinada rauni, amma inaso kidaure kada kubari kibasu fuskar dazasu gane fushinki akansu. Haka Anwar yayita kwantar mata da hankali, harseda yaga tasake dashi.
Sosai suka kara fahimtar juna, duk abinda sukeyi Umman Rayyana tana lekensu, ganin dare yafara yine yayi mata sallama yamika mata wata leda daya siyo mata ice cream da snacks, godiya tayi mashi tashige gida.
Koda taje Ummanta taraba kayan biyu tabata tace takaimasu Rayyana, tana zuwa Umma ta jefota dasu, haka tafito tashige dakin Ummanta, dan Rayyana adakin Ummanta ta kwanta. Wanna shine karo na farko arayuwarsu dasuka fara kwana daban daban tun bayan girmansu.
^^^^^^^ ^^^^^^^^
Abdul ne ya daki kafadar Sageer, saurin kallonshi yayi, dariya Abdul yayi yace lafiyade abokina, tunda muka hadu da wanna kurmar naga hankalinka gaba daya yatashi, kode?
Ajiyar zuciya Sageer yayi yace wlh Abdul kamar kasani tunaninta nakeyi, arayuwata banaso inga nabatama mutum rai, dazun ma tsautsayi ne yasa nayi mata haka, atunanina irin matan nan ne masu zafin kai shiyasa namata haka.
Amma ganin kurmace ita gaba daya hankalina, yatashi, gashi sam nakasa bata hakuri har muka bar gurin, gaskiya dole inje inbata hakuri kozan samu kwanciyar hankali.
Dariya Abdul yayi yace ko kuma zaka samu soyayyarta ba, Sageer yace kaifa dan iska ne, yaushe nafada maka inasonta? Abdul yace yanzu mana, ai sede kafada ma wani bani ba Sageer, nasan halinka tamkar nina haifeka, saboda haka kawai kadena wani boye boye.
Murmushi Sageer yayi yace tonaji, sarkin sa ido, kai wlh dama kai ne lawyer ba niba, domin duk wanda ka ritse da tambaya dole ne yamika wuya.
Abdul yace nide yanzu abinda nakeso inji, da gaske kana sonta? Sageer yace sosai ma, kawai inaganin nayi matar aure nan ba da dadewa ba, zanfara shirin aure, tunda kai ka tsaya wasa.
Abdul yace enaji bakomai, ai garani inada yan mata kaifa? Se yau nefa kafara tunanin wata budurwa, Sageer yace nide dan Allah gobe da safe karakani muje wajenta. Abdul yace akan titi aka cemaka gidansu yake? Sageer yace dalla malam nafa ga gidan data shiga.
Abdul yace mugu, wato muna tafiya seda ka kura ido har kaga inda tashiga ko? Yace kwarai ma kuwa kuma na tabbata nan ne gidansu domin kayan miya tasiyo kaga kuwa dole gidansu zata kai.
Abdul yace to Allah ya kaimu, ai gara kayi aure hakanan, Sageer yace muyi de. Abdul yace wai ni ranar monday ne za'a shiga kotu akan wanna case din ko? Sageer yace ni kaga wlh har namanta saboda tunanin baby ta.
Abdul yace haka ne fa, wato soyayya zata fara saka shiririta akan aikinka ko? To kada de kamanta, aduniya baka da burin daya wuce kazamo,babban lawyer me gaskiya da rikon amana, wanda ze iya kare hakkin talakawa.
Kaga kuwa ba'a zama jarumi afagen yaki se mutum yadage, idan har kabari soyayya tashiga gaban aikinka wlh bazaka taba aikata komai ba, kuma kada kamanta a inda ka ke aiki, ayanzu haka akwai wani abu agabanka wanda na tabba kanaso ace kaine kazamo wanda ze tabbatar da gaskiyar wanna case din nan gaba.
Idan har baka maida hankali ba, kanaji kana gani kasan gaskiya amma bazaka iya fadar taba, sede a yanke ma wanda beji ba be gani ba hukunci, saboda kawai son kai da kuma zalunci irin namasu kudi.
Jikin Sageer ne yayi sanyi lokacin da Abdul yagama maganarsa,kamo,hannunshi yayi yace hakika naso inshagala in manta da abinda yake gaba na, amma nayi maka alkawari bazan taba barin wannan case yatafi ahaka ba, koban samu nasara yan zuba, insha Allah wata rana nine da nasara. Abdul yace nasanka DAN MASANI Allah yayi maka jagora.
******** **********
Washe gari haka gidansu Anwar akayi shirin tarbar baki, bayan azahar suka iso, bayan sunci sun sha aka tsaida maganar aure akan nan da wata biyu, kudin neman aure suka bada sukace zasu aiko da kayan sa rana.
Sosai sukaji dadin yanda aka tarbesu, haka sukayi sallama suka tafi. Duk wannan bidiri da akeyi banda Aunty aciki, domin tunjiya bata kara fitowa babban falon gidan ba, duk wasu kayan aikinta dasuke babban kitchen tasa Laila ta dauko mata.
Dan aranar sede Umma tayi masu girki duk da aikinta ne, takoma kitchen dinta dayake part dinta, babu abinda yake hadasu shiyasa haryanzu basu ganta ba.
Seda akayi la'asar sannan Anwar yatafi raka Abbanshi air pot, ahanya ma nasiha kawai yake mashi, kuma yace daya dawo sati mezuwa zasuje neman auren Nabila. Sosai Anwar yaji dadi. Seda yaga tashin jirginsu sanna ya wuce asibiti.
^^^^^^ ^^^^^
A gidansu Nabila ma haka tafaru, domin sam Umman Rayyana ta canza ma kowa acikin gidan, dande tasan halin mijinsu itama da seta raba girkin gidan kowa yayi nashi, amma sanin hali yasa batayi ba.
Sede koda tagama girki tazubama Babansu Nabila itama ta dibar masu itada Rayyana tashige daki tabar masu Nabila nasu atukunya, wanda kuma ada ba haka sukeyi ba, ganin haka yasa Umaman Nabila tasa ta tadauko cooler tajuye masu nasu.
Da kyar Rayyana ta iya fitowa tashiga dakinsu, dan ita gaba daya kunyar Nabila takeji, akwance ta sameta suna waya da Anwar, zama tayi akusa da ita ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsunta.
Ganin haka yasa Nabila tace tana zuwa, kashe wayar tayi ta kalli Rayyana, kamo,hannunta tayi kamar tana jira tasaki kuka, saurin jawota tayi tana lallashinta, itama kukan takeyi.
Seda sukayi me isarsu sanna sukayi shiru, Rayyana tace dan Allah Yaya kiyi hakuri da abinda yafaru, dama wanda yake faruwa, wlh jinake kamar nabar gidan nan.
Bansan meyasa Umma zatayi haka ba, dani dake ai duk daya ne, duk wadda Yaya yazaba ai abin farin cikin gidan nan ne gaba daya ko? Meyasa zata bari Aunty ta canza mata hali?
Itafa Aunty da biyu take wannan abu, akwai kishi data keyi na rashin haihuwar namiji, na tabbata wanna shine dalilinta nason sena auri Yaya, kuma iname tabbatar maki bazan taba aurenshi ba.
Wallahi koda ace akwai aure tsakaninmu nidashi dake, bazan taba aurenshi ba, dan haka inaso ki kara hakuri da duk abinda Umma zatayi maki, insha Allah komai ze wuce, kuma ina tare dake dari bisa dari.
Jawota Nabila tayi ta rungumeta tace nagode Rayyana, hakika nasan nayi dace da 'yar uwa tagari, kema Allah ya fiddo maki da miji nagari, kuma insha Allah tare za'ayi bikinmu.
^^^^^ ^^^^^
Sageer ne da Abdul tsaye akofar gidan wanna yarinyar ta jiya, wani matashi suka gani yafito daga gidan dayake jikin nasu, sallama sukayi mashi, bayan sun gaisa, Abdul yace dan Allah muna tambayar wata budurwa datake gidan nan, wata fara haka me tsawo marar jiki, kuma kurma ce.
Murmushi saurayin yayi yace wai SADDIKA kuke nufi? Sageer yace inde bataji to itace, yace haka ne wannan ne gidansu, bara inshiga inkira maku ita, nimade sauri nakeyi zanje zaman gaisuwa nan baya.
Abdul yace Allah sarki rasuwa akayi? Yace wlh kuwa wani abokin mune akasamu wasu marassa imanin suka kashe shi da wuka, duka shekararshi daya da aure, kuma dayan abokin namu dasuke tare tunda abun yafaru ba' a ganshi ba.
Ammade gobe ne za'a fara shiga babbar kotu domin gabatar da shari'ar. Abdul yace wayyo Allah yaji kanshi, yace amin, bara nakira maku ita. Abdul yace kaji ko, na tabbata case din da megidanka ze gabatar agobe shine wanna yaron yake magana akanshi.
Amma meka fahimta da maganar bacewar abokin wanda aka kashe? Murmushi Sageer yayi yace ai ko ba'a fada ba nasan bewuce wannan abokin yallabai police din nan shine ze iya sawa a tsareshi, domin naji sunce shi kadai ne yagansu lokacin dasukayi kisan.
Fitowar saurayin itace ta tsaidasu, yace tana fitowa, godiya sukayi mashiya tafi, Abdul yace sede baka fada mana sunanka ba, dawowa yayi yace sunana Hassan, kuma wanna shine gidanmu.
Abdul yace idan badamuwa kabani,number dinka mana semurika gaisawa, amsar wayar yayi yasa mashi, Abdul yace nagode senakira. Fitowa tayi tana sanye da hijabi.
Tana ganinsu ta kalli Abdul tana murmushi tayi masa nuni da hannu alamun sune na jiya ko? Kai ya daga mata shima yana murmushi, gaishesu tayi ta sigar kurumta, matsowa Sageer yayi yana mata alamu datayi hakuri da abinda yayi mata jiya.
Murmushi tayi tace bakomai yawuce, Sageer yace abokina nifa ban iya maganar kurame sosai ba, Abdul yace ai seka koya tunda Allah ya hadaka da ita.
Sageer yace yauwa inazuwa, kallonta yayi, se kuma ya fiddo wayarshi ya rubuta yace sunanki Saddika ko? Mika mata wayar yayi ta amsa tana gani tadago kai ta kalleshi, murmushi tayi ta daga mashi kai.
Kafadar Abdul yadaka yace kagani ko, amsar wayar yayi yasake rubuta mata tana da waya kuma ta iya rubutu? Nan ma kai tadaga mashi, murmushi yayi yace ina wayarki? Mika mashi tayi tana ta murmushi.
Number dinshi yasa mata yakira wayarshi sega ta ta tashigo, saving sunanshi yayi awayarta sede My Luv yasa mata, rubuta mata yayi ga number dinshi nan yasa mata yayi saving, tana amsa ta duba, saurin kallonshi tayi.
Kai ya daga mata yana murmushi, fuska ta rufe tana murmushi tashige gida da gudu, Sageer yace Allah kuwa, seni Dan masani ake fada maka, to yakagani? Abdul yace babu abinda nagani, Allah de yasa wanna murmushin bana wani abu bane.
Sageer yace wlh Abdul zan rama ne, Abdul yace karama mana, kai kamanta iskancin dakamun afarkon haduwata da Amina? Allah ma yasoka taka kurmace, wlh da kaga iskanci. Sageer yace enaji, mutafi Abdul yace ammade chart zaku rikayi ko? Dan naga alamar za'ayi cacar kudi inde ta message za'ayi fira.
Duka Sageer ya kaimashi, Abdul yasa dariya ya ruga, Sageer yace wlh zan kamaka ne.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
Bunch of tnx to all my luvly and caring friends😘😘😘😘👍🏻👍🏻👍🏻
[2/10, 2:10 PM] nabilalady5: 👨🏻🎓KAFIN IN ZAMA LAWYER👨🏻🎓 👨🏻🎓 👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 45 🖤 50
Duk saurin da Sageer yakeyi kada yamakara amma a office ya iske su Umar da Brr, Yusuf. Hannu ya kai ze bude kofar amma abinda yaji yana fitowa daga office din yasa yafasa shiga.
Umar ne yace yallabai wannan file din da muka amso gurin D,P,O na wannan case din da zamuyi yanzu inje in konashi ko? Brr, Yusuf yace a'a kabarshi bana kona file nafiso sena tara kasan ni bana aiki da ka.
Duba kasan waccan dirowar zakaji wani mukilli, ka bude kasaka munshi aciki ka maida mukullin inda ka daukoshi. Wannan sirrina ne babu wanda yasan dashi sekai, kaima dan kana jini na shiyasa.
Bayan ya bude wasu files ne yagani haka yasaka ya kulle, kara kallonshi yayi yace kuma kana ganin D,P,O ze iya samun tambarin hannun wani amatsayin wanda yayi kisan?
Murmushi Brr, Yusuf yayi yace lallai Umar kai bakone a wannan harkar, nasan ko waye D,P,O mundade muna wannan aikin dashi, shiyasa sam bayason acireshi daga office dinshi domin yasan meyake samu, kamar yanda nake zaune anawa office din.
Kuma jiya naje gidan Alh, Abbas kusan awata 2 muna tare dashi da yaronshi Ammar, duk na fada mashi abinda zefada idan ankirashi agaban kotu, kasan mu lauyoyi munada wani abu, matukar mutum besan yanda ake amsa tambaya akotu ba, babu wuyar mu kadashi. To nasan baze bamu kunya ba dan naga beda tsoro.
Kasan wani abu? Munfi manyanmu samun kudi ahaka da kake ganinmu. Kuma duk yanda zeyi seya samu wannan tambarin hannun domin yasan kowaye ni, ni bana son kudi kamar yanda nake samunsu haka nima nake badawa domin amun aiki irin wanda nakeso.
Kaga million 5 ne asalin kudin danake rufe case din kisa, ina daukar million 3 inbashi 2, sannan ina sallamar mutane dayawa a wannan office namu, koda kuwa basuyi mani wani aiki ba.
Kawai suna dauka ina basu ne saboda kyawun halina, nayi nasara acase an bani kudin sallamata nima nake sam masu wani abu daga ciki. Shiyasa kaga ina zaune lafiya da kowa kuma suna girmama ni kamar me.
Jinjina kai Umar yayi yace lallai kai babba ne, Allah yabani ikon kamo koda rabin kane, dariya Brr, Yusuf yayi yace idan kana tare dani har seka fini matukar kana maida hankali. Dauko mani jakata mutafi kada lokaci ya kure mana. Kaima idan muka dawo zan baka million 2.
Zaro ido Umar yayi yace million 2? Kai yadaga mashi yana murmushi, Umar yace aiko wlh mota zansiya, Brr, yace kanada damar yin komai, inde irin wannan kudin ne ka dunga samunsu, amma ka kula banaso kabari Sageer yafika sanin yanda nake aiki.
Jikin Sageer ne yayi sanyi sosai, lallai mutanan nan basa tsoron Allah, ace da saninka ka dorama wani laifin kisa kawai dan kasamu kudi? Lallai idan haka ne, dole zeyi kokari kodan ganin yatemaki duk wanda za'a dorama wannan laifi.
Dadin daya keji ma daya ne, ba shari'a court za'a kai case din ba, yasan Babbar kotu ba'a kashe mutum sede amashi daurin rai da rai, yana fatan kafin lokacin yagano gaskiya yatemaki wanda aka kulle.
Kwankwasa kofar yayi, akace yashigo, da sallama yashiga, bayan sun gaisa Brr, Yusuf yace yau kam ka makara ina fatande ba jikin bane? Sageer yace ai naji sauki kawaide na biya asibiti ne. Umar yace Allah yasawake.
Brr, Yusuf yace idan bazaka iya zuwa ba, kawai kayi zamanka muje akwai wani case dazan gabatar a kotu. Sageer yace zan iya ai naji sauki, bata fuska Umar yayi ba haka yaso ba, Brr, yace shikenan, mutafi, amma ina fatan kana sane da abinda nafada maka?
Babu ruwanka da abinda be shafeka ba. Sageer yace ban manta ba yallabai. Brr, Yusuf yace da kyau, karbi jakar hannun Umar mutafi, kuma idan kaje kasamu guri kazauna kawai ka kalli yanda ake komai Umar ze miko mani duk abinda nake bukata.
^^^^^^^^^ ^^^^^^^^^^^
Kasancewar da yaron babban mutum za'ayi shari'ar hakan yasa kotun tacika da manyan mutane da sauran jama'a masu kallo. Alhaji Abbas da shida mutananshi aguri guda suka zauna.
Se matarshi itama da nata mutanan, shikuwa dan gwal din yana gefen mahaifinshi, tare da abokinshi hankalinshi kwance dan mahaifinshi ya tabbatar mashi sune zasuyi nasara.
Bayan alkali yashigowa kowa ya zauna alkali ya bukaci da magatakarda yakaranto shari'ar daza'a gabatar.
Tashi magatakarda yayi yace ayau litinin 15 ga watan january 2018. Zamu saurari kara daga bangarori guda biyu, inda iyalan malam Adamu suke karar Ammar dan gidan Alhaji Abbas me dala, akan tuhumarshi dasukeyi na kashe masu dansu Qaseem Adam adaran ranar alhamis da wuka, wanda akayi a unguwar kwado.
Mikama alkali takardar yayi ya koma yazauna. Alkali yace ina lauyoyi masu gabatar da wannan shari'a? Tashi daya daga cikinsu yayi yace ni sunana Brr, Naseer lauyen gwamnati, kuma nine nake kare wadan da suke kara.
Sunana Brr, Yusuf lawyer me zaman kanshi, kuma nine nake kare wanda ake kara.
Alkali yace wanda ze fara bismillah. Tashi Brr, Naseer yayi yace yamegirma me shari'a zanso ganin Ammar, wanda ake zargi da aikata wannan kisa domin inyi masa wasu tambayoyi. Alkali yace kotu tabaka dama, Ammar Abbas yafito gaban kotu.
Brr, Naseer....... Ko zaka iya fadama kotu sunanka?
Sunana Ammar Abbas.
Brr, Naseer........Ammar zaka iya fada mana kana ina aranar alhamis 11 ga wata da misalin karfe 10 na dare?
Ammar....... alokacin muna tare da abokina Sanee agidanmu cikin dakina muna buga game.
Brr, Naseer........ Amma ya akayi ka hadu da Qaseem abayan layinsu har rigima tahadaku har ka iya daukar wuka ka caka mashi aciki, alokacin yana tare da abokinshi?
Tashi Brr, Yusuf yayi yace inada ja ya meshari'a, lawyer yana kokarin dorama Ammar laifin da besan ya aikatashi ba, idan be manta ba, amaganarshi ta farko cewa yayi yanason ganin Ammar wanda ake zargi.
Dan haka bekamata ba yarinka jingina mashi laifin kisa ba. Nagode yame shari'a. Alkali yace Brr, Naseer ka gyara tambayarka.
Brr, Naseer yace shin Ammar ko kuntaba rigima kaida marigayi Qaseem kafin faruwar wannan abun?
Ammar....... gaskiya ni bantaba ganinshi bama, asalima ni anguwarsu ba gurin zuwana bane, domin banida alaka da ita, zan iya cewa tunda nake bantaba zuwa unguwar kwado ba, domin ni gaba daya rayuwata banyita anan garin ba, kai akasar ma baki daya.
Asali ma banfi sati daya da dawowa daga London ba, shiyasa ban ma fara fita ba, sede nazauna agida mu buga game nida abokina, amma kawai senaji wai ana zargina da abinda bansan ta ina yafaru ba.
Jinjina kai alkali yayi ya duka yayi rubutu, Brr, Naseer yace zaka iya tafiya. Zanso kotu tabani dama domin nagayyato D,P,O. Alkali yace kotu tabaka dama.
Brr, Naseer yace kozaka iya fadama kotu asalin sunanka da kuma aikinka?
Sunana Bello saulawa, kuma ni D,P,O ne, nine wanda case din kisan Qaseem yake hannuna.
Brr, Naseer.......shin malam Bello kozaka iya fada ma kotu abinda yafaru alokacin da kuka je wajen da aka kashe Qaseem?
Kwarai ma kuwa, domin aranar alhamis da dare da misalin karfe 10 ina kokarin fitowa daga office domin intafi gida, nazo shiga mota sega wani matashi yazo gurina da gudu yana haki,
Daga ganinshi ba acikin hayyacinshi yake ba, tambayarshi nayi meyake faruwa, tun kafin yabani amsa naga jini ajikinshi da hannunshi.
Gashi se warin kayan maye yakeyi, yana daga baki zemun magana yakasa alamun acikin maye yake, hakan yasa nakamashi muka shiga mota.
Kara tambayarshi nayi babu abinda yake fada se cewa yake shikenan ya mutu, wlh ba haka naso ba, dade naga yakasa fadamun abinda yake faruwa sena wanka mashi mari.
Anan yadawo hankalinshi, nace meyafaru? Shine yake fadamun wai wani yaro dan gidan Alh, Abbas me dala ya kashe mashi aboki. Ganin muna bata lokaci yasa na kira wani dansanda Salisu nace yabiyoni muje wani guri.
Muna zuwa muka iske mutum kwance cikin jini ga wuka a cikinshi, Salisu nasa yacire wukar muka kamashi muka nufi babban asibiti dashi.
Abinda na lura dashi agurin abokinshi jikinshi se rawa yakeyi yakasa zama guri daya. Bayan munje likitoci sukayi duk wani bincike, suka tabbatar mana da cewar Qaseem ya rasu.
Alokacin da aka fada mana, ashe shi abokin nashi yafita yakira yan gidansu yafada masu Ammar yakashe Qaseem. Bayan na karbi duk wasu bayanai daga gurin likita harda hoton tambarin hannun dayake jikin wukar.
Ina fadama abokin Qaseem nadauki hoton hannun wanda yayi kisan dan haka bazeyi wuyar kamawa ba, anan ma senaga hankalinshi yakara tashi, ganin haka yasa nayi masa dabara nace kozamu fara gwadawa da hannunka?
Lokaci guda hankalinshi yakara tashi, murmushi nayi nace wasa nake masa, haka muka fito, nasashi yarakani har gidansu Qaseem, bayan naga gidan yace shi anan zesauka, alamun dana gani narashin gaskiya yasa zuciyata bata amince dashi ba, hakan yasa nace baze tafi ba.
Haka muka wuce dashi office domin bazan iya barinshi ba, nasan yana iya guduwa, bayan na kulleshi wanda haryanzu babu wanda yasan yana wajena, atunanin mutane ko Ammar ne yasa aka kamashi.
Shine naje nafada ma iyayen Qaseem, sede ban fada masu ina zargin abokinshi ba, shine su kuma suka dage akan lallai Ammar ne yakashe masu yaro, hakan ne yasa suka kawo kararshi.
Gaba daya kotun tadauki hayaniya, kowa da abinda yake fada. Murmushi Brr, Yusuf yayi jin yanda D,P,O ya shirya manakisa.
Bubuga tebur alkali yayi hakan yasa kowa yayi shiru.
Runtse ido Brr, Naseer yayi domin duk wani kwarin guiwa dayake dashi yakare, domin dan sandan da case din yake hannunshi ya fadi komai.
Saurin tashi Brr, Yusuf yayi yace yamegirma meshari'a zanso inyima D,P,O wasu yan tambayoyi. Alkali yace Brr, Naseer ko,kanada sauran tambayar dazakayi ma wani? Babu yame shari'a. Alkali yace kotu tabaka dama Brr,Yusuf.
Matsawa yayi cike da izza, domin shi sam tsayawa gaban mutane baya bashi tsoro, domin yasaba da hakan.
Malam Bello ko zaka iya gabatar mana da takardun da ka amsa daga hannun likita? D,P,O yace kwarai ma kuwa.
Wannan shine takardar shedar mutuwar Qaseem, wannan kuma takardar shedace da likita yabani, abinciken da yayi yagano cewar kafin Qaseem ya mutu yasha wani abu na maye, hakan ya tabbatar mana da cewar dashi da abokinshi duk seda suka bugu kafin sufara fada.
Wannan kuma takardar shedar sahun hannun wanda yayi kisan ne, kuma shine yayi dede da sahun dayake jikin wukar da aka kashe Qaseem da ita.
Kuma ba sahun hannun kowa bane sena abokinshi Mannir. Nagano hakan ne ta daukar sahun hannun Mannir danayi na kaima likita ya duba kuma yabamu dede.
Tashi mahaifiyar Mannir tayi tana kuka tace wlh karya ne, sharri ne, kawai irin na yan sanda, ai dama tunda naga yarona bedawo gida ba, nasan ankulla wani munafuncin. Wlh dana be taba cin koda goro ba, bare sigari bare kuma yasha wani abu da ze iya kawar mashi da hankali har ya iya kashe mutum, kuma babban abokinshi.
Tebur alkali ya buga, yana fadin baiwar Allah ki kama bakinki, nan kotu ce ba kasuwa ba, saboda haka kizauna. Jawota mahaifin Qaseem yayi tazauna suna ta kuka.
Brr, Yusuf yace kozaka iya gabatar ma kotu da Mannir? D,P,O yace zan iya idan kotu tabani dama, alkali yace kotu tabaka dama.
Wata kofa aka bude kowa yabita da ido, yan sanda ne suka kamo Mannir da kyar yake tafiya domin jikinshi babu kwari, kuma ba dukanshi akayi ba, koda aka sashi inda ze tsaya da kyar ya iya tsayuwa.
Brr, Yusuf yace Mannir shin zaka iya fada mana inda kukaje kaida abokinka Qaseem aranar da yarasu? Dago kai yayi bece komai ba, kara maimata tambayar yayi, da kyar ya iya bude bakinshi yace kawai daga cikin gari muke.
Kwallace ta zuboma Sageer, ganin yanda ake gabatar da shari'ar rashin gaskiya, sede yanda akeyi babu wanda zece karyane sede wanda yasan gaskiyar maganar. Saurin goge idonshi yayi dan bayason aganshi, duk da bezauna akusa ba. Cigaba yayi da rubutunshi, domin tunda aka fara yake daukar wasu muhimman abubuwa.
Brr, Yusuf yace amma aranar meya hadaku kaida abokinka har kukayi fada? Kallonshi Mannir yayi yace nibanyi fada dashi ba. Brr, Yusuf yace to amma meyasa ka caka mashi wuka?
Shiru yayi bece komai ba, kara maimata tambayar yayi amma Mannir bece komai ba. Duk yanda yaso yayi magana beyi magana ba.
Juyowa Brr, Yusuf yayi yace yame girma me shari'a da wannan ne nakawo karshen tambayata, inafatan wadannan shedun da aka gabatarma kotu zasu tabbatar da cewar Mannir shine wanda ya kashe abokinshi Qaseem sakamakon fadan dasukayi
Hakan ne yasa Mannir ya kashe Qaseem. Daga karshe inafatan kotu zata yankema Mannir hukuncin daya dace dashi, domin hakan yazama darasi ga yan baya.
Komawa yayi yazauna, gaba daya kotun tayi shiru, kowa da abinda yake tunani, Alh, Abbas kuwa se murmushi yakeyi, shida Ammar.
Bayan alkali yagama rubutunshi yadago yace Brr, Naseer ko kana da sauran ja akan wannan shedun da aka gabatar? Tashi yayi yace babu yame shari'a.
Domin shi dama andau koshine dan yagano masu wanda yakashe masu da, tunda yaji bayani me gamsarwa yasan beda abun cewa.
Jinjina kai alkali yayi yace Mannir ko kana da ja akan wannan laifi da ake tuhumar ka dashi? Shin kayarda kaine ka kashe abokinka Qaseem?
Shiru Mannir yayi bece komai ba,alkali yakara maimaita tambayarshi amma Mannir yayi shiru, sede kawai ya dukar da kanshi, dan baya son yin magana, gashi bakomai yake fahimta a kotunba, hakan yasa yakeyin shiru.
Alkali yace, abisa kwararan hujjojin da aka gabatar ma kotu, bisa nazari da wannan kotu tayi, kotu tagano cewar Mannir ne yayi amfani da wuka wajen kashe abokinshi bisa wani dalili nashi.
Kuma yakasa musawa akan zargin da ake mashi. A bisa wannan dalilin ne kotu tayanke ma Mannir hukuncin kisa daurin rai da rai agidan yari. Buga tebur yayi akace kottttt.
Haka kowa yarika mikama Alh. Abbas hannu suna tayashi murna, hannu Brr, Yusuf ya mika ma Brr, Naseer suka gaisa.
Kuka kawai iyayen Mannir sukeyi, mahaifan Qaseem kuwa mamaki ne yakamasu ganin irin abinda yafaru, sosai sukayi mamakin wai Mannir ne yakashe Qaseem, duk yanda suke tare.
Sede mahaifin Qaseem yana matukar mamakin yanda akace wai su Qaseem suna shaye shaye, bayan kuma lokacin da yayi mashi wanka shi beji warin komai ba. Amma kuma dan yau ba'a shedar shi
Haka yansanda suka tasa Mannir duk abinda akeyi bin kowa da kallo yakeyi domin shikadai yasan yanda yakeji ajikinshi, sam babu kwari, idanuwanshi ma da kyar yake dagasu. Sema yan sanda ne suka rikeshi.
Ko wajen iyayenshi beje ba sede sune suka karaso gurinshi. Kamashi mahaifinshi yayi yana kuka yana fadin Mannir meyasa haka? Yaushe ka canza hali ban sani ba? Bin mahaifinshi kawai yake da kallo.
Mamanshi ta rungumeshi tana kuka, takasa fadin komai, se kuka kawai takeyi, mahaifinshi yace bakomai Mannir, ni nasan sharri akayi maka, idan har kana da gaskiya da izinin Allah wata rana se gaskiya ta bayyana.
Nayafe maka duniya da lahira, zancigaba da addu'a Allah zekare ka, kuma seya bayyana gaskiya da izininshi.
Haka yan sanda suka wuce dashi, mutane dayawa sun tausaya ma iyayenshi. Mahaifan Qaseem kuwa har gaban su Alh, Abbas sukaje suka basu hakuri akan sharrin da sukayima dansu.
Alh, Abbas yace ai bakomai, kuma ba laifinku bane,abokinshi ne daya fada maku, kuma kosuwaye dole su dauki irin matakin da kuka dauka matukar suna son dansu.
Shiyasa akoda yaushe akeson idan ansamu sabani aje kotu, saboda anan ne kadai za'a iya kwatarma kowa hakkinsa, kunga yanzu anyi walkiya ta haska kowa yagane me gaskiya.
Ina maku ta'aziyar rasuwar danku, Allah yajikanshi. Kuma insha Allah idan nakoma gida zan aiko da tawa sadakar. Sosai sukaji dadi nan sukayi masu sallama suka tafi.
Girgiza kai Sageer yayi, domin duk abinda akeyi yana tsaye agurin yanaji, idanuwanshi harsunyi ja saboda damuwa. Sam yamanta tare suka zo dasu Umar, kawai tafiya yayi yasamu wani guri daga can baya yazauna.
Kuka yakeyi sosai kamar karamin yaro, dama tundazu yakeson yi dande kawai kada aganshi da kayan lawyer a kotu kuma yana kuka. Yafi minti 20 ahaka yana kuka.
Goge idonshi yayi, seyanzu yaji dadin zuciyarshi, littafin dayayi rubutu dashi dazu yadauko,Biro yasa yafara rubutu.
KISAN KAI ALHAMIS,
11/1/2018.
UNGUWAR KWADO.
AMMAR ABBAS ME DALA
/ /
D,P,O. Brr, YUSUF
/ /
SALISU. DR.?
MANNIR!!!
Ajiyar zuciya yayi daya gama rubutu, rufe littafin yayi ya kulle idonshi yana tunanin yaushene zefara wanna binciken??? Wane Dr, ne ya duba gawar Qaseem? Saurin bude ido yayi, afili ya furta inspector salisu. Tabbas shine zebani amsata.
Dariya yajiyo daga can gefenshi, yana juyawa ya hango su D,P,O dasu Brr, Yusuf. Hannu yabashi suka gaisa, Brr, Yusuf yace wai abokina meyafaru haka? Kai nafa ya kulle.
Dariya D,P,O yayi yace ai wannna karon na kure fasaha ta, nima nace sena baka mamaki, domin ka farantamun sosai. Muje mu huta zakaji komai.
Nikam nace ko menene?🤔🤔 muje zuwa
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
Thanks for ur prayer. Waiting for ur comment😘😘😘

Season 50 🖤 55
Da kyar Sageer ya isa gida dan har wani duhu yake gani saboda ciwon da kanshi yakeyi, yana zuwa besamu Abdul ba hakan yasa yasha magani ya kwanta, babu abinda yakeyi se tunanin abinda yafaru.
Shikenan fa yanzu an yanke ma Mannir hukuncin kisa ko? Haka rayuwarshi zata kare a gidan yari, iyayenshi basuda karfin dazasu iya daga kara ko? To idan ma sun daga karar kowace kotu taji irin hujjojin da aka gabatar a babbar kotu dole zata amince da ita.
Innalillahi wa Innailaihirraji'un. Shine abinda Sageer yarika fada azuciyarshi hawaye suna sauka daga idonshi, da haka har bacci yadaukeshi.
^^^^^^^^ ^^^^^^^^^
Zaune suke a office din Brr, yusuf banda dariya babu abinda sukeyi, sun kulle kofa babu wanda kejin abinda suke fada sede kajiyo dariyarsu. D,P,O ne yafara basu labarin yanda ya shirya komai. Duk yanda naso inji abinda yake fada nakasa domin kofar a kulle take kuma yayi kasa da muryarshi.
Bayan sungama suka fito, har bakin mota Brr, Yusuf yarako D,P,O shida Umar. Bayan yashiga mota Brr, Yusuf yace amma abokina kana ganin nan gaba wannan yaron baze kawo mana matsala ba?
Kasanfa manyan mutane suna yawaita ziyartar gidan yari, kuma ana binciken files na masu laifi. Tunda nake shari'a banta ba yin wadda naji zuciyata bata kwanta da ita ba se wannan. Duk da nayi wadda tafi ta hatsari.
Amma awannan karon nakasa samun nutsuwa, ina tsoron kada Mannir yadawo hankalinshi. Jinjina kai D,P,O yayi yace gaskiya ne, kaima ka kawo magana me amfani. Amma meze hana mu taikaita mashi shan wahalar gidan maza.
Kallonshi yayi yace kamar ya? Ina nufin yabi abokinshi inda yatafi, domin duk ranar da asirinmu yatonu wlh alkali baze yankema Alh, Abbas hukuncin daze yanke mana ba. Kaga kuwa dole musan yanda zamuyi mukare kanmu.
Kasande munsaba da wannan harkar. Brr, Yusuf yace haka ne, kaima ka kawo shawara, amma taya ya zamu aikata hakan, bayan yana tsare? Murmushi D,P,O yayi yace haba abokina, Kada kamanta nifa tsohon dan sanda ne, kabar komai a hannuna.
Bade kowa yasheda dan shaye shaye bane? Ta wannan hanyar zamubi mugama dashi, kuma aikin baze wuce daga yau zuwa gobe ba, domin ta haka ne kawai baza'a zargi kowa ba. Hannu yabashi suka tafa yace shiyasa nakeson aiki da kai.
Wannan dabara tayi, kuma kana da karin dubu dari biyar, nasan kila akwai wanda zakasa yayi aikin. Godiya D,P,O yayi mashi yace shikenan seka jini. Bayan yatafi Brr, Yusuf yabama Umar kudi yaraba kananan ma aikatan gurin.
^^^^^^^^ ^^^^^^^^^^
A gidan su Anwar kuwa zaman lafiya ya kare, gaba daya Aunty tacanza halinta, bata kula kowa agidan, abincinta daban takeyi, store din gidan taje taraba abincin tadauki nata, hatta da Laila tahana ta zuwa part din Ummansu Anwar. Shiyasa ta tattara kayanta tace makaranta zata koma, duk da saura sati daya hutun yakare, amma ganin abinda Auntynsu takeyi yasa taji gidan ya isheta.
Ko dakin Umma Sede idan Aunty bata nan take zuwa, duk abinda Aunty takeyi labari yana iske Abba, amma sede yabama Umma hakuri, ita tun tana damuwa har tadena. Sede zaman kadaicin dayake damunta, domin bata samun kowa Anwar ne kuma baya dawowa gida da wuri.
Shikam Anwar soyayya kawai sukeyi shida Nabila, ko a office yana kiranta suyi fira, abokinshi Dr, Shamsu se tsokanarshi yakeyi.
^^^^^^^^ ^^^^^^^^^
A gidansu Nabila ma haka abin yake, duk yanda Umman Rayyana taso tasa diyarta tajanyo hankalin Anwar abin ya faskara, gashi bakin cikinta daya adaki daya suke kwana da Nabila, shiyasa take fushi da Rayyana.
Ganin Rayyana tana cikin damuwa yasa Nabila tace kinsan wani abu Rayyana? Girgiza kai tayi tana hawaye, Nabila tace kinsan kome iyayenmu zasuyi mana bazamu taba canzasu ba, dan haka inaso kiyima Umma biyayya akan abinda takeso.
Kinga bataso tarika ganinmu tare muna fira, dan Allah daga yau kada ki kara zama acikin dakin nan, da kintashi daga bacci kirika tafiya dakinta, idan kuma zaki kwanta kirika bari se dare yayi, yanda zata dauka dakinzo bacci zakiyi.
Kinga zamu iya fira anan, kuma ga islamiyya acan ma zamuyi fira, sannan idan kina dakinta zamurika yin charting, kinga de zataji dadi kinbi umarninta.
Rayyana tashare hawaye tace yanzu shikenan Yaya saboda son zuciya se araba mu? Kuma da kike cewa haka, idan nabi umarninta ai ba haka takeso ba, tafiso lallai sena janyo hankalin yaya Anwar.
Wlh Yaya bazan iya ba, koda ace saurayin kawata ne bazan iya kwace mata ba, bare kuma wanda 'yar uwata ta jini zata aura. Amma bakomai zanyi yadda kikace kodan in kareki daga duk wani abu dasu Umma zasuyi maki.
Zama agurinta zesa na kara fahimtar duk wani shiri daza suyi akanki ita da Aunty, dan natabbata akwai wani abu dasuke shiryawa, ni kuma nayi alkawarin kareki bazan taba bada goyon baya acutar dake ba.
Rungumeta Nabila tayi itama tana kuka, tace nagode kanwata Allah yabarmu tare, insha Allah kema zaki samu wanda kikeso. Idan kuma da dan saurayinki na jami'a zamuyi shikenan. Dariya suka sa gabadaya.
^^^^^^^^^^ ^^^^^^^^^^
Abdul ne yashiga dakinshi, Sageer yasamu yagama sallah yana latsa waya, zama yayi yana fadin koda Saddika ake fira ne? Murmushi Sageer yayi yace kamar kasani, gaskiya yarinyar nan akwai saurin shiga rai.
Jinake kamar munyi shekara da ita. Abdul yace naga alama ai, tunda jiya kusan raba dare kukayi kuna fira, wlh kada ka hurema diyar mutane kunne, kilama ko saurayi bata dashi amma kazo zaka rudata da zazzafar soyayyarka.
Dariya Sageer yayi yace bawani muna koyama juna de, Abdul yace ai sekayi mata sallama muci abinci. Suna cikin cin abincin, Abdul yace wai ya maganar shari'ar da akayi ayau?
Girgiza kai Sageer yayi yace wlh abokina da kana gurin nan ayau sekayi kuka sede idan kana da da kakkiyar zuciya. Abdul yace ai daga ganinka kasha kuka, ina fatan ba'a kotun karika masu kukan ba? Sageer yace haba de, ai se su zargeni.
Amma duk da haka seda idona yarika cika da kwalla kawai gogewa nakeyi, ana fitowa nasamu guri nazauna naci kuka na kamar wanda aka aikoma da mutuwa. Dariya Abdul yayi yace ai nasanka mutumina akwai tausayi. Meyafaru?
Duk abinda yafaru seda Sageer yafada mashi, yana gamawa ya dauko mashi littafin da yayi rubutu aciki yabashi. Bayan yagama karantawa Abdul yadago kai cike da tausayi yace anya mutane suna tsoron Allah kuwa?
Yanzu shikenan an yankema Mannir hukuncin kisa? Sageer yace wlh ni kaina abinda yake damuna kenan,amma insha Allah sena fito dashi. Ni babban abinda yafi damuna yanda akayi akace wai suna shaye shaye kuma da aka kawoshi acikin maye yake.
Murmushi Abdul yayi yace tabbas D,P,O shine wanda yabashi abinda ze kawar mashi da hankali, domin yasan idan yakawoshi lafiya lau, dole Mannir ze musa akan zargin da ake masa, kuma ai shirinsu akan su Qaseem suna cikin maye lokacin da akayi kisa yake.
Kaga dole zesan yanda zeyi Mannir yazo cikin maye. Babban abinda za'a kalla anan shine, mutumin da yake kulle harna tsawon kwanaki 3 tayaya yasamu abinda ze iya kawar mashi da hankali?
Idan kuma yace lokacin daya kamashi yana cikin maye ai yakamata ace acikin kwana 3 dayayi koma menene yasha yasakeshi. Lallai wannan kadai abin dubawa ne.
Rungume Abdul Sageer yayi yana dariya yace kai abokina, hakika kai bango ne agare, abin jingina, tundazu tunanina bekawo mani haka ba, amma kana zuwa harka gano komai, hakika inajin dadin tarayya da kai.
Idan kuma ina tare da kai nasan wannan case din baze taba bani wahala ba. Biro yadauka ya rubuta abinda Abdul yace. Kallonshi yayi yace yanzu ta ina kake ganin zan fara wannan binciken?
Abdul yace da farko dole semun gano wane likita ne yaduba Qaseem, na biyu kuma dole ka kulla abota da inspector Salis, kuma kada kabari yasan kudirinka akanshi harsekaji dakanshi yafara sukar megidanshi.
Hanya ta 3 kuma, duk yanda zakayi kasamu kadauko wannan file din, idan yaso sekayi photo copy ka aje masu acikin dirowa din kai kuma kadauke original din. Hanya takarshe itace Mannir.
Zaka kaimashi ziyara amatsayinka na abokinshi, amma kabari senan da kwana 2, nasan zuwa lokacin ya koma dede, agurinshi ne zaka samu duk wani bayani gam sashshe.
Idan karike wadan nan mutanan insha Allah zasu temakeka, koda bana raye zakayi alfahari da abinda nafada maka watarana. Sageer yace wai kai se ana magana karika sako mutuwa.
Abdul yace ammade kasan dole zamu mutu ko? Sageer yace nasani, amma nide kadena fadar haka. Murmushi Abdul yayi yace shikenan nadena. Yanzu ni kwanciya zanyi dan danayi la'asar zan koma shago. Sageer yace nima gurin Baby na zani.
^^^^^^^^^ ^^^^^^^^^^
9:00pm agidan yari.
Mannir ne zaune yahada kanshi da guiwa yana ta kuka, dan tunda aka kawoshi dazu yake bacci, yansandan dasuka kawoshi ma seda sukayi ma masu gadinsu bayani akan subarshi yahuta.
Lokacin daya farka haka abubuwa suka rika dawo mashi tamkar amafarki, tun yana ganin,ba gaskiya bane, har ya bude idonshi yaganshi sanye da kayan gidan yari, saurin runtse ido yayi babu abinda yafara dawo mashi se lokacin dazasu tafi kotu.
D,P,O yashigo da kanshi yakawo mashi abinci, yana ta lallashinshi akan yaci, kada yadamu kanshi kotu wajen adalci ne, idan har akaje beda laifi za'a sakeshi, dafashi yayi yace. Mannir kasan dalilin dayasa nace a ajeka anan?
Girgiza mashi kai yayi, murmushi yayi yace nasan kaga wadan da suka kashe Qaseem ko? Yace E, kasande yaron babban mutum ne, nasan ze iya binka duk inda kake kaima yakashe ka domin kai kadai ne kagansu alokacin da abun yafaru.
Shiyasa nace zan ajeka agurina kuma haryanzu babu wanda yasan kana nan, nide abinda nake bukata daga wajenka shine shedarka akotu, shiyasa tunda kazo nan babu wanda yatabaka.
Dan haka karka damu idan munje kotu kasaki jikinka kafadi duk abinda yafaru, alokacin babu wanda ya isa yayi maka wani abu kaji ko? Jinjina kai Mannir yayi yace nagode yallabai.
Abinci ya mika mashi da ruwa akofi yace yisauri kaci mutafi kada ajiramu, nan take yadauki abincin yafaraci, seda yacinye duka yadauki ruwan yashanye duka.
Yana gamasha yaji kanshi ya sara mashi, haka yaji dakin yana juya mashi idanuwanshi suna lumshewa. Tundaga nan bekara sanin inda kanshi yake ba se yanzu daya farka.
Wani kukane yakara taho mashi, yanzu shikenan an rufe abokinshi ko jana'izarshi ba'a bari yaje ba? Ashe dama duk abinda D,P,O yake mashi munfuntarshi yakeyi? Towai ma ta yaya yazo gidan yari shida bashine yayi kisan ba?
Maganar wani megadi yaji yana fadin yan samari idan katashi kafito kaci abinci tundazu kana ta baccin asara ko sallah bakayi ba, kaje kasha abinda yafi karfinka har aka gama yanke maka hukunci ma bakasan me ake yiba.
Kafito kadauki abincinka, shima tausayinka naji yasa naje nakarbo maka da bazaka samu ba. Idan kagama muje in kaika dakinku dan nan wajen mune an ajekane saboda yanayin da aka kawoka aciki kada kaje maza suyimaka illa.
Kallon mutumin da yake maganar yayi, wani dattijo ne, akalla shekarushi zasu kai 50, wani sabon kuka Mannir yasaki domin jin abinda mutumin yafada. Yanzu waye ze amsa mashi tambayoyin dasuke kanshi?
Tasowa mutumin yayi yashigo dakin da abincin, zama yayi yadafa Mannir yace kayi hakuri yaro, ita kaddara babu abinda bata jawowa, shiyasa ba'ason kuna wannan shaye shayen banzan domin zasu saka mutum ya aikata aikin dana sani kamar yanda akace kayi.
Goge idonshi yayi ya kalli mutumin yace Baba, nasan kai babban mutum ne, ka dade aduniya, kuma kayi zama da mutane kala kala, wanda ayanzu ma kana cikin mutane marasa jin magana.
Na tabbata zaka iya fahimtar kowa da kuma yanayinshi. Baba kai muslumi ne, idan nayimaka rantsuwa da Allah zaka iya yarda? Kai Baba yadaga mashi jikinshi asanyaye.
Mannir yace na rantse da Allah, wallahi tunda nake arayuwata ko goro bantaba cibba bare ajega sigari ko kuma wani abu da ze iya kauda hankalina. Ni kaina bansan meyake faruwa ba, yanda kaganni anan nima haka naganni.
Abu daya nasani.............. labarin abinda yafaru yafada mashi harzuwa abinda D,P,O yafada mashi da kuma abinda yabashi. Shikanshi Baban seda kwalla tazubo mashi saboda tausayi.
Lallashin shi yafarayi yace lallai yaro kanacikin matsala babba domin wannan abu da dan sanda yayi maka bakomai bane se sharri irin nasu, kuma yayi amfani da kai domin su cima wani buri nasu.
Hakika bakada sauran dabara sede kamika al'amuranka ga Allah. Idan bakada hakki wata rana zaka fita. Alokacin da aka kawoka akwai wani dana acikin yan sandan da suka kawoka.
Sunanshi Salisu, shine yake fada mani abinda yafaru yace wai ansamu hoton hannunka ajikin wukar da aka kashe abokinka, kuma alkali dakanshi ya tambayeka amma ka kasa musawa akan zargin da ake maka.
Kuma anga rashin gaskiya atare da kai lokacin da kaje office dinsu, sannan kafin akashe abokinka ku dukanku acikin maye kuke. Bisa wadannan hujjoji da aka samu yasa kotu tayanke maka wannan hukuncin na daurin rai da rai.
Sosai Mannir yake kuka, idanuwanshi har sun kumbura, Baba yace kayi hakuri, kaci abinci yanzu za'azo a karbeni dan banine zanyi aikin kwana ba. Kuma wanda zezo beda imani ko kadan, gara muje na kaika dakin danasan ba zakasha wahala ba.
Akwai wani yaro dazan hadaku dashi, duk da shi laifinshi ba irin naka bane, amma shima tsautsayine ya fada mashi, shiyasa aka kawoshi nan, sede yakusa fita dan befi wata 5 ba yafita.
Mannir yace wlh Baba nagaji da wannan rayuwar, inama ace Allah ze dauki raina danafi kowa farin ciki duk da bani da tabbas akan abinda zan iske acan. Baba yace kadena fadar haka, kaifa musulmi ne.
Dauki abincin kaci mutafi,Mannir yace Baba bazan iya cin komai ba, kawai bani ruwa insha. Bayan yasha ruwan suka tafi domin yakaishi dakinshi.
Seda yahadasu da yaron sannan yayi masu sallama yace se yazo gobe. Jan hannun Mannir yaron yayi suka shiga ciki.
Baba yazo shiga dakinsu yaga abokin aikinshi wanda ze karbeshi yafito daga motar D,P,O. Sosai yayi mamaki dan yasan inde kaga D,P,O yazo to akwai wani abu dazefaru. Duk da ansan haka tana faruwa amma babu wanda yake tsayawa yayi bincike. Addu'a Baba yayi akan Allah yakare duk wanda zasu cutar.
To amin Baba🙏🏻😭.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
Ina mika godiyata ga dukkanin masoyana Allah yabar kauna👍🏻

Season 55 🖤 60
Wannan shafin nakine Momy na Aunty Salima, jinjina agare Allah yashirya maki yaranki damu baki daya💋😘😘
Bayan Baba yagama kallonsu yawuce dakinshi ya hado kayanshi yana fitowa suka hadu da abokin canjinshi. Hannu yabashi suka gaisa yace Baba har kafito? Baba yace wlh kuwa, tunda kazo ai se intafi.
Amma kamar motar D.P.O nagani ko Gali? Sosa kai yayi yace e itace yakawo mani sako ne dazu yaje kauyenmu. Baba yace toshikenan nizan tafi. Gali yace yauwa Baba ina aka kai wannan sabon me laifin?
Baba yace ai masu laifin sunada yawa basan wanda kake nufi ba. Shiru Gali yayi dan bayaso Baba ya ganoshi. Tafiya Baba yayi yana fadin seda safe. Bayan yatafi Gali yadauko littafin da ake rubuta sunayen wadan da aka kawo.
Sunan Mannir yafara dubawa yana zuwa kan sunan yayi murmushi, sede Baba yamanta be rubuta sunan dakin daya kaishi ba. Gali yace nasanka da tausayi Baba, baze wuce ka kaishi dakin masu hakuri ba, dan can kasaba kai masu laifi inde kaine ka basu daki.
^^^^^^^^ ^^^^^^^^
Bayan sun shiga ciki wanda Baba ya hadashi da Mannir me suna Kamal ya raka Mannir bandaki yayi alwala, bayan ya rama sallolin da ake binshi Kamal yace kaci abinci kuwa Mannir?
Goge hawayen dasuka zubo mashi yayi yace banajin zan iya cin komai Kamal. Ina tausaya ma kaina da iyaye na, nine gatansu ni kadai na rage masu acikin yayan dasuka haifa.
Mahaifina zeshiga damuwa ta rashina, domin tare muke zama dashi akullum, domin baya barina inje ko ina, shiyasa daya bude shago yace tare zamu rika zama, abokina da akace na kashe, shima tare muke zama dashi ashagon Babana.
Duk inda ka ganni dole kaga Qaseem, bacci ne kawai yake rabamu amma duk da haka wai ace nine na kashe shi. Kuka yasa me tsuma zuciya wanda hatta da Kamal seda zuciyarshi ta tsinke.
Dafashi yayi yace kayi hakuri Mannir, amma zanso inji labarinka? Dago kai Mannir yayi yafara bashi labarin abinda yafaru............
Sosai Kamal ya girgiza dajin labarin, shima seda yayi kuka. Mannir yace shikenan saboda bamuda kudi haka rayuwata zata kare anan har mutuwa tadaukeni.
Wlh babu abinda yafi bakanta mani rai yanda aka laka mana sharri wai muna shaye shaye. Kamal yace kayi hakuri Mannir, ai ko makaho ya laluba yasan baka yi kama da yan iska ba.
Haka duniyar ta gada, yanzu masu kudi sune sukeyin abinda sukaga dama suda yaransu, mukam yaran talakawa sede hakuri kawai. Amma Mannir alokacin da abun yafaru baka samu wata sheda ba wadda zata iya nuna Ammar shine yakashe Qaseem?
Shiru Mannir yayi yana tunani can yayi saurin tashi yasa hannunshi acikin gajeran wondonshi na ciki, wata sarka ce irin wadda maza yan duniya suke sawa yaciro. Zama yayi yana fadin na tuna.
Kamal kaga wannan sarkar, wlh awuyan Ammar Qaseem yacireta alokacin daya caka mashi wuka, lokacin da abokinshi yajashi suka gudu ni kuma nakama Qaseem, shine yabani sarkar alokacin ko magana baya iya yi.
Lokacin dazan tafi wajen yansanda nasakata cikin aljihu, nayi niyar inba dan sandan da muka taho tare, amma senace bara nabari se anzo bincike. Lokacin daya kaini office dinsu ya kulle, ni kuma senayi tunanin za'a bincikeni shine nasakata cikin gajeran wando na.
Kamal yace tabbas idan nafita daga gidan nan nayi maka alkawarin se ansake dauka ka kara, insha Allah seka fito daga gidan nan. Mannir yace nagode Kamal, anshi wannan sarkar ka ajeta agurinka idan kafita itace zata zamo mana sheda.
Karba Kamal yayi yace nima bara nasata cikin gajeran wando na, kasan agidan nan baka da gurin ajiya daya wuce nan domin akwai barayi na fitar hankali.
Mannir yace amma kai mekayi har aka kawoka nan? Murmushi Kamal yayi yace nikam tsautsayi ne ya hauni da kaddara, asalima nine nasa aka kawo ni nan badan komai ba sedan ina tsoron hukuncin da Allah zeyimani aranar kiyama idan har ban bari an yanke mun hukuncin daya tanadar ma masu laifi irinmu aduniya ba.
Mahaifiyata ta rasu, kawai se mahaifinmu ya auro wata yarinya wadda yayi mata tsufa kawaide budurwar zuciyace irin tashi yasa ya aure ta, saboda tana diyar abokinshi.
Shi kuma Babanta baya son yabata wanda takeso, hakan yasa da Babanmu yaganta yafada mashi yana sonta kawai yace yabashi ita. Yarinyar gaba daya shekarunta bazasu wuce 20 ba, kaga koni nabata shekara 10.
Amma haka Babanmu ya aurota duk da bata sonshi. Alokacin bakaramin haushi naji ba, wai Babanmu yayi aure, auren ma na yarinya. Haka muka cigaba da zama da ita, tun lokacin data ganni tafara sona, haka tashiga yimani abubuwa kala kala.
Nagane abinda take nufi, ni kuma sena fara canza mata fuska, abincina har daki take kawo mani, kuma ko awane yanayi nake ba ruwanta dayin sallama haka zata shigo.
Ganin tana niyar zarce gona da iri yasa nayi mata kashedi, amma duk da haka bata dena ba. Danace zan fadama Babanmu se tace ai gara infada mashi, tasan idan yaji sakinta zeyi.
Kawai sena kyaleta. Wata rana Babanmu bayanan yayi tafiyar kwana daya, da dare ina kwance ina kallon wani najeri'an film kasansu basu da kunya, alokacin jinake dama ace ina da aure, haka nacigaba da kallona.
Ganin hankalina yafara tashi yasa natashi na kashe, sam na manta ban kulle kofata ba, gashi marata tafara mani ciwo, haka na kwanta bacci ya kauracemani.
Ina cikin haka banji shigowarta ba se kawai naji mutum yafado mani.
Saurin tashi nayi na kunna hasken wayata, saurin kashewa nayi domin yanda naganta bana fatan,nakara kallonta, tureta nayi yace baki da hankali ne? Kara matsowa tayi tafara shafani tana fadin dan Allah katemaka mani.
Wlh banajin dadin Babanku kawai hakuri nakeyi. Zanyi magana kawai ta hade bakina da nata, abinka da wanda yake cikin hali, ga shedan agefe bansan lokacin dana biye mata ba. Haka muka kusa kwana muna abu daya da ita sekace mayya.
Seda komai yalafa nadawo hankalina kawai senaji kamar amafarki, bansan lokacin da hawayen bakin ciki suka fara sauko mani ba. Zuciyata lokaci guda tacika da kunci, memakon inji nishadi se sabanin haka naji.
Kuka kawai nakeyi, sabanin ita wadda take kwance tana kokarin jawoni, tashi nayi na wanke ta da mari, haka najata na wurgata waje nadawo daki, wanka nayi nafara sallah ina neman tuba.
Wlh Mannir dayake muna tsayawa karatu amasallaci bayan magriba, aranar da abin ze faru akan Zina malam yayi mana karatu, duk hukuncin da Allah yasaukar seda yafada mana segashi adaren na aikata babban laifin da bantaba aikatawa ba.
Washe gari tazo tana bani hakuri, babu abinda yafito daga bakina, nace mata wlh, tunda har tasa muka aikata Zina dole semun fuskanci hukunci koda za'a tara mana mutanan duniya hakan bazesa inji kunya ba.
Kallonta nayi cike da tsana nace kuma bari kiji, idan kina tunanin kin cuceni to kanki kika cuta, domin ni inada sauran lokacin rayuwa, kefa? Matar aure ce ke, hukuncinki kisa ne. Dukewa tayi tafara kuka tana rokona.
Ganin zata bata mani lokaci yasa na kulleta adaki damma kada ta gudu, kai tsaye kotun musulunci naje, inazuwa nafada masu abinda muka aikata, kuma nace inaso ayanke mana hukunci.
Nan alkali ya hadani da yan agaji muka je, muna zuwa na iskeBabanmu yadawo, bamu tsaya bata lokaci ba, suka fada mashi dalilin zuwansu. Sosai yashiga tashin hankali. Haka suka kamota tana ta kuka muka tafi.
Kafin kace wani abu har labari ya cika gari, nan da nan kotu tacika da jama'a. Babanmu kuwa kasa zuwa kotun yayi, haka na maimata abinda yafaru kowa seda yatausaya mani, abokanaina se kuka sukeyi.
Hatta da malaminmu seda yazo, shima seda yayi kuka, nan alkali ya tambayeta takasa musawa, nan take aka yanke mana hukunci. A kamun bulala da daurin shekara daya, ita kuma hukuncin kisa ta hanyar jefewa.
Iyayenta se kuka sukeyi, mahaifinta sosai yayi da nasanin hanata auren wanda takeso yayi, alkali ma seda yakara jawo hankalin iyaye akan auren dole da sukeyi, haka yakara jama samari kunne akan yawan kallon film din batsa.
Domin babu abinda yake jawowa se fitina. A nan akamun bulalata, kafin agama na suma, seda na kwanta asibiti na tsawon sati 2 kafin a kaini yari,ita kuwa kwana daya kawai aka kara mata domin tayi sallama da yan uwanta. Washe gari aka jefeta.
Nikam ina zuwa Allah ya hadani da wannan Baba me kirki, shine yakawoni wannan dakin, kuma yana temakona sosai. Kaji dalilin dayasa aka kawoni gidan nan, yanzu saura wata 5 infita.
Sosai Mannir ya tausayama Kamal. Kallonshi yayi yace lallai Kamal kai kaga illar kallon film din batsa, Kamal yace wlh kuwa, shiyasa banida abinyi agidan nan se neman gafara, azumi ma dande kawai muna shan wahala yasa banayi, amma dana koma gida zan rikayi.
Haka sukayita fira har wajen 2 kafin suka kwanta.
Shikam Gali be kwanta ba seda yagano dakin da Mannir yake.
******* ********
Washe gari da safe bayan sun gama aiki suka tafi karbar abinci, kofi Gali yasamu yasaka guba aciki, haka ya koma kan layinsu Mannir, duk wanda aka zuba ma koko shine yake mika mashi.
Ana zuwa kan Mannir yamika mashi wanna kofin, yana amsa yace yauwa kaine aka kawo jiya ko? Mannir yace e nine, Gali yace muje office akwai abinda ba'a rubuta naka ba, saboda kana baccin shan kwayar datafi karfinka.
Kowa agurin seda ya kalleshi. Gali yace kana saurayinka amma kana shan abinda yafi karfinka. Allah yasoka amma likita cewa yayi idan ka kara shanta zaka iya rasa ranka domin zuciyarka zata iya bugawa.
Mamaki ne ya hana Mannir magana, gashi kowa se kallonshi yakeyi ana dariya, kama hannunshi Gali yayi yace muje ni kana batamun lokaci gida zantafi. Kamal da ranshi yagama baci yace kawo kofin inrike maka mutafi.
Wani kallo Gali yayi mashi hakan yasa yakoma domin yasan rashin mutuncin Gali.
Suna zuwa office Gali yace zauna, file ya bude yace sunanka da shekarunka? Da kyar Mannir yafada mashi, dago kai Gali yayi yace naga ranka ya baci, ko ba gaskiya bane abinda nafada, dannima fadamun akayi.
Sede kuma banga alamun haka daga gareka ba.Mannir yace wlh sharri akamun, bantaba shan komai ba. Gali yace Allah sarki, dan Allah kayafe mani, nayi maka mummunar fahimta.
Hakika kabani tausayi, shanye kokon ka ga biredi ma kahada dashi nasan bakaci komai ba tun jiya. Idan kagama zamuje gurin mutane na wanke ka agurinsu idan ba haka ba, kasan gidan maza, wlh kabani.
Godiya Mannir yayi mashi, yaji dadin wankeshin dazeyi agaban mutanan daze zauna dasu har abada, dan yasan ahaka zasuyita kallonshi. Kamal ne kawai yasan gaskiyar labarinshi,kuma yakusa tafiya.
Daukar kofin yayi yafara sha,ko takan biredin be biba dan seyanzu yasan yanajin yunwa. Gali yace kaci biredin mana. Mannir yace nakoshi dama abu me ruwa ruwa nafiso. Ruwa yamika mashi wanda yasa wata muguwar kwaya da D.P.O yabashi.
Bayan yagama sha yaji kanshi yasara , tashi Gali yayi yace muje ko, nasan ma yanzu suna wajen aiki. Suna fitowa Mannir yafarajin cikinshi yana murdawa, dafe ciki yayi Gali yace ko bazaka iya zuwa wajen aikinba? Mannir yace wlh cikina ke murdawa.
Gali yace bakomai muje inraka ka daki kafin wasu masu gadin suganka dan bazasu kyaleka ba. Haka suka nufi dakinsu, babu kowa saboda suntafi aiki, yana zuwa ya kwanta yafara juyi, zufa duk tajikashi.
Haka Gali ya tsaya babu imani yana kallon Mannir yadena motsi, murmushi yayi yadauko wani kofi yazuba ruwa yajefa kwayoyi aciki ya aje akusa da Mannir, wata leda yaciro yasa kata cikin gajeran wandon Mannir yafita.
Babu wanda ya ganshi, dariya yayi ya dauko waya yakira D.P.O yana dauka yace aiki ya kammalu yallabai, ka saurari kiran waya. Dariya D,P,O yasa yace sauran kudinka zasu shigo.

Season 60 🖤 65
A FUWAN, NASAMU MISTAKE A DATE DIN DANA SAKA NA SHARI'AR DA AKA GABATAR, NASA 15TH JAN, 2018. KUMA ABUN YAFARU NE A 15TH AUGUST, 2016. SABODA MUNA BADA LABARIN SAGEER
WANDA YARIGA YA WUCE.
NAGODE.
Tun da Kamal yake aiki gabanshi yake faduwa, gashi shiru har lokacin Mannir bezoba, da kyar yabari suka gama kowa yakama gabanshi, kai tsaye dakinsu ya wuce domin yacire kaya yaje office din su Gali yadubo Mannir.
Turus ya tsaya alokacin daya shiga dakin, wasu da suke binshi abaya sukace yade Kamal? Hannu yasa ya nuna masu inda Mannir yake kwance, dariya wani yayi yace da alama wannan yaron da hutu ne.
To waya fada mashi ana bacci agidan Maza. Jikin Kamal a sanyaye ya matsa kusa da Mannir, fara bubbugashi yayi amma shiru, kunnanshi ya kai saman kirjinshi, da sauri ya dago.
Ganin abinda yake faruwa yasa sauran ma suka matso, wani ne ya daga hannun Mannir, amma yadawo, zaro ido yayi yace kai, da alama fa kamar baya da rai. Wasu zafafan hawaye ne suka sauko ma Kamal.
Fadawa yayi samanshi yana kuka yana jijjigashi, fadi yake dan Allah Mannir katashi, bana so ka mutu harse an tabbatar da kai me gaskiya ne. Kafin kace me, dakin yacika da jama'a.
Kowa da abinda yake fada wasu suna fadin kode kwayar yakara sha. Wani babba acikinsu ne ya duka yadauki kofin dayake kusa da Mannir, yana dagawa sega takardar kwayar da Gali yabude ya zuba acikin ruwa.
Dariya yayi yace lallai wannan yaron kayi wasa da rayuwarka, ai koni bazan iya shan wannan kwayar ba, gaskiya ka cuci kanka. Saurin dagowa Kamal yayi ganin abinda ake nunawa yasa yace wlh karya ne.
Mannir baya shan komai sede idan sharri aka masa, ai dama tunda naga Gali yatafi dashi jikina be bani ba. Dafashi wani yayi yace haba abokina, kada kamanta fa nan gidan maza ne, abinda yafi haka ma ze iya yi, kawai kabishi da addu'a.
Masu gadin wajen ne suka shigo da sauri, ganin abinda yake faruwa yasa suka dauki gawar Mannir suka tafi da ita clinic din dayake gidan. Kafin kace me har shugaban wajen yazo tare da yan sanda.
D.P.O shine gaba tare da inspector Salis. Gali ne ya fadama shugaban abinda yafaru, ansamu wata muguwar kwaya adakinshi, kuma aruwa yasata yasha ansamu sauran ruwan akofi.
Wata farar takarda ya mika mashi yace wannan sauran kwayar ce an sameta ne acikin gajeran wandonshi. Sosai mutane sukayi mamakin Mannir.
Shugaban yace za'a tafi dashi asibiti domin agano asalin abinda yayi sanadiyar mutuwarshi. D.P.O ne yayi saurin matsowa yace yallabai dama wannan yaron case dinshi a hannuna yake, kuma jiya muka kawoshi, dama abige yazo.
Dan haka zamu tafi dashi ayi mashi duk wani awo daya kamata kafin mu mikashi wajen mahaifansa. Jinjina kai shugaban yayi yace shikenan, zaku iya tafiya, amma akawo mana copy na report din da likita yabada domin musa a file dinshi. Godiya sukayi mashi aka dauki gawar Mannir,Kamal se kuka yakeyi.
Sunzo fita kenan Baba ya iso, Salis yana ganinshi yaje ya gaisheshi, gaisawa sukayi da D.P.O ya koma gefe shida danshi. Kallonshi yayi yace Salisu meyake faruwa haka kuma? Salis yace wlh Baba wannan yaron ne da muka kawo jiya yarasu.
Wai ance wata muguwar kwaya yasha, kuma ansamu saura ma a wandonshi. Innalillahi wainna ilaihirraji'un, shine abinda Baba yafada. Goge hawayen dasuka zubo mashi yayi, yace ai dama nasan bazasu barshi ba.
Wlh tunjiya dana tafi gabana yake faduwa, sam banyarda da zuwan D.P.O wajen Gali ba, Salis yace hakika nima ina zargin wani abu, amma tunda haka tafaru, insha Allah zanyi kokarin saka ido awajen Oga.
Baba yace Salisu kamun alkawarin zakayi kokarin gano gaskiyar abinda yafaru, nasan insha Allah za'a samu wani lawyer wanda ze kwatoma iyayen yaron nan hakkinsu.
Salisu yace na maka alkawari Baba zanyi iyakar kokarina. Baba yace shikenan, zanga yaron dana hadasu zanji komeye yafaru, kaje kada su zargi wani abu. Haka suka tafi da gawar Baba se kuka yakeyi, yashiga ciki domin yaga Kamal.
Duk abinda yafaru seda Kamal yafada mashi, Baba yace nasan za'ayi haka, wlh banyarda wai kwaya ce takashe Mannir ba, tabbas akwai wani makirci dasuka shirya, kuma insha Allah asirinsu seya tonu. Kada kabari kowa yaji wannan maganar abakinka, duk lokacin da mukasamu wanda ze tsaya mashi zan nemeka.
D.P.O beyarda ankaishi gurin kowane likita ba, shine da kanshi yasamu likitan da yayi mashi awon hoton hannanun Mannir domin yakara yimashi report na karya, babu bata lokaci yayi mashi komai, ya rubuta silar mutuwarshi akan kwayar dayake yawon shane.
Dubu dari 1 ya bayashi, sukayi mashi sallama suka tafi gidansu Mannir. Shide Salis kallonshi kawai yakeyi, amma tunda yaga yahana abama kowane likita ya dubashi seda yakira wannan yasan akwai matsala.
Haka kuma yahansu shiga yace sujira awaje, tundaga nan yafara tunanin abubuwa da dama da suka wuce. Mahaifin Mannir yafito zetafi kasuwa yaga motar yansanda, gabanshi ne yafadi.
D.P.O ne yafara fitowa, bayan sun gaisa yace Baba sede kuyi hakuri. A sanadiyar kwayar da yaronku yakesha, tayi ma zuciyarshi illa, wanda har likita seda yace idan har yacigaba da sha ze iya rasa ranshi.
To kasan masu shaye shaye akwai zuciya, kila wani abunne yabata mashi rai, shine yazubata acikin ruwa yasha, wanda hakan ne yayi sanadiya bugawar zuciyarshi harta kaishi ga mutuwa.
Runtse ido Baba yayi yana salati a zuciyarshi, tare da karanto addu'oi. Ya dade haka kafin yabude idonshi, sunyi jawur kamar anzuba mashi barkono, yama kasa yin kukan.
Kallanshi yayi yace shikenan,Allah yajikanshi yasa ya huta, Allah yasa lahirarshi tafiye masa nan. Kutemaka kushigo mana dashi. Wasu hawayen tausayi ne suka zubo ma Salisu, sauran yan sandan ma seda suka tausayama Baba.
Haka Baba yashiga ciki yafada ma matarshi da yan uwanta wadan da suka zo mata jaje akan su gyara za' shigo da gawar Mannir. Tashin hankalin da Mamanshi tashiga baya faduwa, riketa sukayi saboda tunda yafada masu tayi shiru takasa koda motsi.
Haka suka aje masu gawar suka tafi, D.P.O yace su wuce office shizeje wani guri yadawo, kallon tuhuma kawai Salis yake mashi.
Abinka da mutuwa kafin kace me har gidan yacika da jama'a kowa yatausaya ma iyayen Mannir. Babu bata lokaci aka yimashi wanka aka sallaceshi , haka aka tafi dashi gidanshi na gaskiya😭😭. Allah yasa mucika da Imani.
Duk wannan abun da akeyi Sageer beda labari, tafe yake a hanya domin yau ya makara, yana tafiya suna fira da Saddika awaya, har me adedeta ya kawoshi besan ankawo ba hankalinshi yana kan wayarshi yana typing.
Yana sauka Saddika ta rubuto mashi wannan wanda yakashe abokinshi dan unguwarsu shima yarasu, dayake hankalinshi yayi gaba yasa be karanta ba, domin ya hango D.P.O yafito daga office dinsu.
Yana zuwa suka hadu da Bala Masinja, dariya Sageer yayi yace A'a Baba kadawo kenan? Murmushi yayi yace nadawo Sageer ai tunjiya nadawo da yamma shiya banshigo ba.
Bayan sun gaisa Bala yace ya aiki, ina fatan de babu wata matsala yanzu? Sageer yace bakomai Baba ina gane komai, Bala yace haka akeso, naga office din ma yakara samun karuwa.
Sageer yace wlh kuwa, ya kabarosu? Yace lafiya lau, jeka dawo kazo ka karbi tsarabar kauye, murmushi Sageer yayi yace toshikenan Baba. Da sallama yashiga office din, bayan sun gaisa Brr,Yusuf yace naga alama kafara saka shiririta a aikinka Sageer.
Kana karamin ma aikaci amma ace nine zan rigaka zuwa office, da Bala masinja bedawo ba nine zan share maka office din in goge ko? Sageer yace ayi hakuri yallabai bazan kara ba. Brr, yace shikenan dauki wadannan files din kashirya mani su.
Umar kabashi kudinshi kuwa? Umar yace a'a ai jiya bedawo ta nan ba, kila ko shari'ar ce ta girgizashi, dannaga yanda yakoma can baya ya rakube kamar meshirin guduwa. Dariya suka sa gaba daya.
Brr, Yusuf yace ammade Umar baka rabuwa da abin dariya, sosai maganar ta batama Sageer rai, amma seyayi murmushi yace haka ne Umar, ai duk wanda ya kalli shari'ar jiya dole yaji tsoronta, domin abune akayi shi wanda idan har ba kwararran lawyer irin yallabai ba, a sati guda ma baza'a gamata ba.
Murmushin jin dadi Brr, Yusuf yayi yace ai inde nine kadan ma kagani, karbi kudinka salalace dana saba bama ma aikatan gurin nan acikin irin kudin danake samu idan nayi nasara a shari'a.
Kamar baze amsa ba, amma ganin kada sukawo wani abu aransu yasa yakarba, sede yayi niyar daya fita ze badasu dan bazeci haramba, dubu biyar ce aka bashi. Godiya yayi mashi yadauki files din yafara shiryawa. Mukulli Brr, Yusuf yadauka yace Umar muje, Sageer zamuje wani guri duk wanda yazo nemana kace yadawo nan da awa 1.
Sageer yace se kadawo. Umar yace nifa? Dafashi yayi yace kabi ahankali naga bakason bani girman da akace karika bani, kada kamanta niba dakikin lawyer bane danayi karatu a nageria ba. Sakinshi yayi yafice yana murmushi.
Murmushi Sageer yayi yace dani kake wasan, zaka gane dakikin lawyer. Awa daya? Yes dama tasamu harzan dauka indawo in maida basu dawo ba. Yana gama gyaran yafita. Zaune suke shida Bala yana cin aya da gyadar da Bala yakawo mashi.
Gyaran murya Bala yayi yace wai Sageer da bana nan akwai abinda yafaru ne? Sageer yace me kagani? Kawai de wata magana naji, sede ban fahimci inda ta dosa ba. D.P.O yace anbashi guba yasha, sede ansaka mashi kwaya ance ita yasha.
Yanzu haka daga gidansu nake mun kai gawar. Wannan shine report din da likita ya rubuta zan kai can gidan yari. Kaji abinda naji yafada kuma senaji suna dariya. Shin wai me hakan yake nufi?
Zufa ce tafara ketoma Sageer, wayarshi yaji tayi kara alamun shigowar sako, yana dubawa yaga kamfanine, harze maida yaga sakon Saddika. Budewa yayi. Saurin tashi tsaye yayi ganin abinda ta rubuta.
Jiyake kamar ze fadi da gaske Mannir yarasu? Guba? Kwaya? Office yashige yana fadin ina zuwa yallabai ya aikeni yanzu zandawo.
Kai tsaye kasan dirowar nan yanufa, yanasa hannunshi yaji mukullin. Budewa yayi cikin sa'a yaga file din takardun yadauka yasa aljihu ya kulle yafita, addu'a kawai yake kada suri gashi dawowa.
Umman Anwar ce zaune afalo tayi shiru tana tuna rashin mutuncin daUmman Rayyana tayi mata daga shigowarta. Ita tsoroma takeji kada su hada kai suyima Anwar wani abu.
Daga shigowarta tasameta afalo, harzata wuce Umma tagaisheta, shinefa tarufeta da bala'i, haka tashige part din Aunty. Sosai Umma ta tsorata da ita, sam bataji dadin wannan zabi da Anwar yabama Aunty ba gashinan yazamo masu masifa agida.
Da sallama Anwar yashigo amma harya zauna batasan yashigo ba. Dafata yayi, yana fadin haba Umma, meyasa kikeson damun kanki akan abinda be kai yakawo ba? Ajiyar zuciya tayi tace dole indamu.
Yanzu kana ganin duk soyayyar da Auntynku take nuna maka yanzu takoma kiyayya, yanzu ko gaisheta fa bakayi kuma kasan hakan bedace ba ko Anwar? Sosa kai yayi yace haba Umma konaje gaisheta bazata amasa ba shiyasa bana zuwa.
Kuma dama can basona take ba, da tana sona bazataki abinda nakeso ba, haka zalika bazata canza soyayyata zuwa kiyayya ba. Dan haka kawai kibarta, kila Allah ne ya bude mana abunda yake cikin duhu, kamar yanda Abba yace, baka gane makiyinka se wani abu yahadoku.
Umma tace naji, katashi kaje ka gaisheta, Umman Rayyana ma tazo itama ku gaisa. Anwar yace dan Allah Umma.... hannu tadaga mashi tace umarni nake baka, Abbanku bazetaba jin dadi ba idan har yasamu labarin nice nake goya maka baya kana raina mashi mata. Dan haka katashi inde kanason farin cikina.
Tashi yayi kamar zeyi kuka, yasan idan yaje bakinciki kawai ze kwaso, dama ace ita daya ce dasauki. Haka nufi part dinta ranshi abace, yazo shiga falonta yaji maganar data girgizashi.
Wlh yakumbo hakurina yakare, mutanan nan bazasu taba bin zabina ba, dan haka dole mubiyo masu tabayan gida, shiyasa nakiraki domin kizo, nasan acan bazamu samu gurin sirri ba shiyasa banje ba.
Dago kai Umma tayi tace abu dayane zakiyi Haj Falmata ki kwaci yancinki keda yaranki agidan nan, kuma hakan zesa kiwuce abokiayar zamanki koda Alhaji yatafi.
Domin tafiki arabon gado tunda ita tana da namiji, ita kuwa waccan kima dena maganarta, domin dede take dake, saboda danta daya kuma gadon namiji daya dede yake dana mata 2, kinga kuwa dede kuke da ita.
Tunda har tsarinmu na auren Anwar da Rayyana ya rushe, kawai mubar zancan, inaso idan Alh, yadawo kisamesu kibasu hakuri, kuma ki gwada kina farin ciki da auren kinyarda dama sharrin shedan ne, kinga kin kawar masu da hankalinsu.
Saboda haka kafin ayi auren mufara kawar da Anwar, kinga kowa yarasa,daga ita har Nabilar, kinga daga baya se mudawo kan Alh, domin babu abinda zaki tsaya jira agidan nan, baki karuwa da komai saboda yanzu bata kanku yake ba.
Ta amaryarshi yake shiyasa bayasan dawowa, kinga idan kika samu gadonki zaki zauna keda yaranki acikin gidan nan kuci karenku babu babbaka.
Aunty tayi murmushi tace amma gaskiya naji dadin wannan shawara, nadade ina kunsa wannan abun arai na, amma nakasa samun dama, Allah sarki dan uwa me dadi, Yakumbo nayi maki alkawarin matukar komai yayi dede kema sekin shana,
Har gida sena sai maki nabaki jari, domin ke bakalar mijinki bace, kawai kaddara ce tahadaku, kinga kema seki fito kiyi zaman 'yanci. Yanzu ya kikeso ayi?
Gyara zama tayi tace, kinga wannan, guba ce kuma babu bata lokaci kafin akai mutum asibiti ya mutu domin bata wuce minti 2 zuwa 5 tagama aiki.
Aunty tace Yakumbo idan nabashi guba kinsan dole likita yagane, kuma za'ayi binciken inda yaci abinci. Dariya Umma tayi tace, nifa bana aiki da ka.
Kamar yanda za'a kashe shi, dole itama tabishi domin hukuncin wanda yakashe, shima akashe shi. Aunty tace kamar ya? Umma tace nima dole zan koma ma yan gidanmu kamar da, zan basu hakuri dama kuma megidan besan munayin fada ba.
Kinga zansa Nabila tayima Anwar girki da kanta, kuma takaimashi idan yazo, agabanta zeci sede bazan bari ita taci ba, zan kula idan zefaraci inkirata, kafin tadawo yaci. Kinga dole ace ita takashe shi, domin acikin abincin gubar take.
Kinga hukuncin kisa yahauta. Dariya suka sa hada kashewa. Aunty tace angama, inason abun yafaru nan da kwana 3, kinga kafin lokacin mun koma dede. Umma tace bakuda damuwa, shiga kidauko mun kudin, kidebomun hada kayan abinci.
Wata irin juwa Anwar yagani harseda yadafa bango, da kyar yaja kafa yafita, yadade kafin yakoma falon Ummanshi, samu yayi ya dedeta kanshi, yana zuwa yace Umma zanje ankira ni yanzu daga asibiti.
Umma tace inafatan basuyi maka komai ba? Murmushi yayi yace bara indawo kisha labari, Aunty ta sakko, hada hakuri tabani kuma tace tayarda da zabina. Fita yayi yabar Umma a duhu. Yana fita yakira Dr,Shamsu yace gashinan zuwa akwai maganar dazasuyi.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
Inajiran comment dinku domin samun kwarin guiwar cigaba, senaga commen zakuji ni gobe😉😉😉😘😘

0 comments:
Post a Comment