THIS PAGE IS DEDICATED TO MY FRIEND MAMAN HANANπππππ.
Kallonshi Dr,Shamsu yayi cike da mamakin abinda Anwar yafada mashi, sosai ya girgiza dajin abinda su Aunty suke shirin aikatawa. Anwar yace wlh ni kaina na girgiza da naji wannan magana.
Tabbas idan mutum be sonka babu abinda baze iya aikata maka ba. Hakika bantaba tunanin Aunty zata iya hararata ba, balle kuma acewai zata iya dukana.
Amma yau da kunnena naji zata iya kasheni, sannan bani kadai ba, Abbana ma bazata barshi ba. Hakika haduwata da Beelert alkhairi ne, domin da bamu hadu ba bazamu taba fahimtar asalin halin Aunty ba.
Abokina kasan me? Ina maka sha'awar auren Rayyana. Zaro ido Dr, Shamsu yayi yace wa? Haba, Allah ya kyauta, ai ko ta biyu bazan iya yi da ita ba, bare ta farko. Kada kamanta fa Ummanta itace tasamo gubar daza'a kashe ka.
Haka kake tunanin in auri diyarta? Kasanfa ana gadon bakin hali. Nikam kabarni idan bikinka yazo na nemi wata acikin kawayen Nabila nasan zan dace. Murmushi Anwar yayi yace ita wadda zaka neman kana tunanin halinta me kyau ne?
Bara kaji, wlh gara na auri macen datafi iyayenta kyan hali dana auri macen da iyayenta suka fita hali. Domin da ita zan zauna, kuma itace uwar nawa yaran, Kada kamanta kai abokina ne bazan taba zaba maka abinda ze cutar da kai ba.
Kuma bawai naki zabar Rayyana bane saboda halin Ummanta. Asalima bansan halinta ba seyanzu. Kawaide Beelert dana fara gani nafada sonta shine dalili. Amma fa shawarace nabaka.
Dr, Shamsu yace shikenan naji kuma nagode, tunda kace haka na amince, se muje karaka ni gurinta. Dariya Anwar yayi yace ana so ana kaiwa kasuwa. Dr, Shamsu yace yanzude ba wannan bane yakawo mu nan.
Naga kai abin kamar beda meka ba. Murmushi Anwar yayi yace to mezesa yadameni? Da ace banji bane shine abin damuwar, amma naji komai yanzu zuwa nayi kafada mani mafita.
Dr, Shamsu yace abokina wannan babban abune, idan kai kasan lokacin da za'a cutar da kai Abba be sani ba. Kuma bakada wata sheda dazaka iya gwadama Abba domin ya yarda cewar Aunty zata cutar daku.
Anwar yace karka damu, insha Allah Abba ze fahimci komai agame da ita, yanzude kabani shawara yanda zan kaucema fadawa tarkonsu, domin idan har nakicin abincin dole za'a samu wani yaci.
Idan kuma Beelert taci fa? Jinjina kai Dr, Shamsu yayi yace haka ne, amma inaganin meze hana katafi da leda kawai kajuyo abincin aciki, ko kuma kafadama Nabilar kaga seta saka ido kada azuba maganin.
Anwar yace nafiso tazuba maganin, domin su dauka shirinsu zeci, saboda zasu iya sake wani shirin idan basu samu damar aikata wannan ba, kuma kaga bansan lokacin dazasu kara hada wani ba.
Dr, Shamsu yace idan kuma sukaga bekama kaba fa? Anwar yace kawai kabari nasan yanda zanyi, kuma iname tabbatar maka kafin bikina se Abba yakori Aunty, kayarda dani. Bazan taba barin Abba ya cutu ba.
Dafashi Dr, Shamsu yayi yace nayarda da kai abokina, Allah yabada sa'a. Yaushe ne zamu je gurin Rayyanar? Dariya Anwar yayi yace mugu, to tashi mutafi yanzu, ammafa semun biya munci abinci agida kafin muwuce.
Da sallma Umman Rayyana tashigo, Umma ce ta amsa mata, murmushi tayi tace Umman Nabila aiki kike haka? Kallon mamaki tayi mata tace wlh kuwa. Zama tayi tace dan Allah kiyi hakuri da abinda nayi maku.
Hakika shedan yaso yayi wasa da zuciyata na ruguza farin cikin da muka dauki shekara da shekaru muna cikinshi. Naso inraba kan yaranmu amma Allah yasa nagane gaskiya, Yanzu haka daga gidan su Anwar nake Haj. Tace inbaku hakuri.
Umma tace bakomai komai yawuce, Allah yakara kyauta gaba. Umman Rayyan ta kwalama su Nabila kira, atare suka fito, gaban Nabila ne yafadi ganin Umman Rayyana tare da Ummanta.
Murmushi tayi tace zomana kika tsaya daga baya, kiyi hakuri da abinda namaki kinji, Allah yasanya alkhairi ita kuma kanwarki Allah yakawo mata nata. Kinga semusha biki gaba daya.
Murmushi Rayyana tayi suka rungume juna, Umma tace to ku karbi Umma itama ta huta, kuyi sauri kugama aikin. Daki suka shiga, sede jikin Umman nabila asanyaye yake, kawaide batasan meyafaru ba, amma tana jinjina tubar Umma.
Suna aiki suna fira, wayar Nabila ce tayi kara, Rayyana tace uhm su yayana babu sauki, dauka tayi tace ina wuni? Yace lafiya lau Beelert, ina kanwata? Tace gata nan muna aiki, yace yau kuma tare kuke aikin?
Murmushi tayi tace ai komai yawuce, murmushi yayi yace yayi kyau, kifada mata zamuzo zance. Nabila tace bangane ba. Yace yanzu ita nakeso. Dif Nabila takashe wayar. Jikinta gaba daya kamar an watsa wata ruwan sanyi.
Saurin dafata Rayyana tayi tace Yaya lafiya? Meyasamu Yaya Anwar din? Wayartace takara yin kara sede bata daga ba, Rayyana ce tadaga, Anwar yace kanwata kushirya gamunan zuwa nida abokina zanrakoshi wajenki.
Kashe wayar Rayyana tayi batace komai ba, kallon Nabila tayi tace dama wannan maganar Yaya yafada maki shine kika canza haka? Saurin kallonta tayi tace meya fada maki? Tabe baki tayi tace wai kinji ma Yaya, wai zerako abokinshi zance gurina.
Wata ajiyar zuciya Nabila tasaki batasan lokacin da murmushi ya kwace mata ba. Turo baki Rayyana tayi tace kai Yaya shine zaki kadamun hanji, shine hada wani canza fuska, to bazan fita ba kosunzo.
Wayar Nabilace tayi kara, tana dagawa Anwar yace ashede ana sona? Wannan kishi haka ko kara babu? Murmushi tayi batace komai ba. Yace to kufito muna waje.
Sauri kawai Sageer yakeyi yana shigowa ya sauke ajiyar zuciya ganin basu dawo ba. Bala yace harka dawo? Yace nadawo Baba inazuwa, office din yashiga yayi saurin bude dirowar yamaida takardun cikin files din ya kulle.
Fitowa yayi yana hamdala, zama yayi akusa da Bala yace wlh Baba nagaji dazama a wannan office din, shikanshi Yallabai baya zama sosai bare in rika karuwa da wani abun.
Nafara tunanin sake wajen aiki. Jinjina kai Bala yayi yace ai naga kokarinka daka iya neman aiki a wannan office din. Ko dayake bakasan abinda yake ciki ba shiyasa har kayarda kazo.
Ni kaina danake zaune dande banida yanda zanyi ne, amma da bazan zauna ina kallo ana cutar da talakawa ba. Gyara zama Sageer yayi dama abinda yakeson ji kenan yasa yakawo maganar. Kallonshi yayi yace wani abune yafaru Baba?
Bala yace Sageer tun ranar da kazo naji inasonka,kuma,nayarda da kai shiyasa zan iya fada maka sirrin wannna office din. Yallabai da kake ganinshi, bakaramin azzalumi bane.
Sam besan meye imani ba, shifa inde zaka bashi kudi ze iya yimaka duk abinda kakeso koda ace ze kashe rai ne, wannan bakar akidar dayake da ita yasa haryanzu yaki yarda abashi matsayin alkali, domin yasan kudin dayake samu sunfi karfin abinda alkali yake samu awata.
Sede yana da halin temakon mutane, hakan yasa halinshi marar kyau yaboye aciki, idan zakabi kaf maikatan gurin nan ka tamabyesu halayyar shi babu wanda ze iya aibatashi, domin azahiri yana da matukar kirki fiye da tunaninka.
Inajin kila takuce batazo daya ba shiyasa kake ganin baya maka kirki, kuma dama yana da wannan,abun, matukar jininshi be hadu dana mutum ba, haka zakaga yana mashi, daga karshema seyasan yanda yayi yakoreshi daga aikin.
Wlh Sageer, wani lokacin idan naji yanda masu kudi suke aje mashi ruwan kudi badan komai ba sedan ya maida karya takoma gaskiya ina mamaki. Acikin office dinnan yake gama komai.
Yanda kasan me lakani, da wuya kaga yafadi ashari'a duk shari'ar da kaga yafadi to gaskiya ba kananan shedu aka gabatar ba. Idan kaga abokinshi yazo wajen nan to tabbas zasu aikata wani babban abu, ko kuma sun aikata.
Shiyasa yau dana ganshi yazo seda na labe badan komai ba sedan inji dame yazo, wannan tambayr dakaji,namaka abinda najine yafada yasa nashiga rudani. A kullum banida addu'ar data wuce Allah yakowa wani me tausayin daze iya gogawa da yallabai.
Hakika zaluncin dasuke aikatawa yayi yawa, amma ayau naji abinda suka aikata ya girmama, dan Allah kafada mun abinda yake faruwa.
Ajiyar zuciya Sageer yayi yace lallai Baba kana kallon abun mamaki, kai kenan daka dade dashi, ni kaina dabamu dade ba, na fahimci halayyarshi sosai..........
Labarin duk abinda yafaru yafadama Bala, sede be fada mashi yadauki takardu ba. Sosai Bala yashiga tashin hankali. Domin duk iya mugunta ta yallabai betaba jin yayi irin haka ba, duk da yayi rashin adalici dayawa, amma nayau ya tsoratashi.
Bala yace hakika wannan mutum yakamata ace ansamu wanda ze iya tanka mashi, kuma bawani bane kaine Sageer, tabbas naga tausayi da kuma jajircewa agurinka, nasan idan harzaka samu komai zaka iya dawo da wannan case din sabo, badan komai ba sedan ka kwatoma iyayen Mannir hakkinsu.
shi kuma ka wankeshi daga zargin mutane, duk da baya raye nasan addu'ar da mutane zasuyi mashi se tafi yawa akan ace yana raye. Domin Allah yafimu sanin dalilin dayasa yadaukeshi tun kafin yasha wahalar duniya.
Idan suna tunanin sun cuceshi, Allah yafisu, kuma bazasu gane gata suka mashi ba se ranar da kowa ya tsaya agaban Allah domin karbar aikinsa. Tabbas Mannir yayi mutuwar da masu imani sukeso suyi, domin yau koda ace yanada wani mugun hali aka mashi wannan sharrin, kuma aka kashe shi yasamu kubuta.
Ina me tabbatr maka zangoya maka baya, daga yau har lokacin da zakayi nasara akansu, dan Allah kada kasaka tsoro, kasa Allah aranka nasan zete makeka. Sageer yace karka damu Baba koda zan rasa raina sena kwatoma Mannir hakkinshi.
Nasan banda komai, amma inada Allah, dashi nadogara nasan kuma ze temakeni. Daga yau zanfara bincike na insha Allah. Baba yace naji dadi kuma insha Allah seka daukaka adalilin wannan shari'a ta marigayi Mannir. Alkhairinsa zebika aduk inda kake, tayanda harka mutu bazaka manta dashi ba,domin zerika samun addu'a daga gareka aduk lokacin daka tuna dalilin daukakarka.
Kuma zanso kafara zuwa gidan yari, idan kaje kayi kokarin neman Baba yusha'u shine mutumin da duk wani wanda yayi zaman gidan yari zakaji yana yabonshi. Fatana de Allah yasa yana kan aiki lokacin da aka kai Mannir, idan har haka takasance tabbas zaka samu sauki. Sageer yace nagode Baba, bara inje inyi aiki.
Sosai mutuwar Mannir ta taba iyayenshi, mutane kuwa sun sami abun fada, mahaifinshi yashiga damuwa shida mamanshi, babu abinda take roko agurin mijinta se su saida gidansu sutashi daga garin, badan komai ba sedan surutun da jama'a sukeyi.
Duk da agidan gaisuwa ne amma haka zakaji ana magana kasa kasa. Baban Mannir yace kiyi hakuri ni bazen iya saida gidan dana ginashi da gumina ba kawai saboda tsoron maganar mutane, nasan sharri kawai akayima dana.
Kuma wata rana gaskiya zatayi halinta, domin bana bacci, akullum ina rokon Allah yatona asirin wadanda suka aikata wannan abun, kuma nasan Allah baya barci, kuma yana jina, wata rana ze amsa rokona. Domin wannan abun daya faru wata kaddara ce Allah yasaukar mana domin ya gwada imaninmu.
Domin babu wata rai dazata rayu batare da Allah ya jarabceta ba. Tunda har Allah ya jarabci annabawa da sahabbai to musuwaye dabaza'a jarabcemu ba? Dan haka kiyi hakuri musamu muci wannan jarabawar, nasan wata rana komai zewuce. Da haka ne yasamu ya shawo kanta suka cigaba da karbar gaisuwa.
Abu kamar wasa soyayya ta kullu tsakanin Dr, Shamsu da Rayyana, sosai Ummanta taji dadin samun mijin datayi koba komai bazata auri talaka ba, kuma gashi Nabila zata rasa Anwar se ayi bikinta ita kadai.
Lokacin da Aunty tasamu labarin itama taji dadi, hakan yasa tacema Umma kawai tashirya yanda zata bama Anwar guba ta abincin Nabila. Umma tace karki damu zansan yanda zanyi yazo shikadai dan kada suzo tare da mijin Rayyana kinga plan ze rushe.
Anwar ne suke waya da Abba yana fada mashi yasamu hutu na sati guda anjima zetaho, Anwar yace yauwa Abba dama inason kadawo wlh, murmushi Abba yayi yace akwai magana kenan ko Dr? Yace sosai ma, yace shikenan ai yanzu zan taho nasan baze wuce maganar Nabila ba. Dariya Anwar yayi yace kaide Abba sekazo.
Inspector Salis ne zaune a office dinshi ya daga kanshi sama kamar me bacci, ya dade ahaka kafin yayi saurin tashi alokacin daya tuno wani abu. Fita yayi ya nufi hanyar office din D.P.O
Masinjanshi Bukar yagani zaune abakin kofar yana jin redio, yana zuwa Bukar yatashi yasara mashi. Salis yace yauwa Bukar yallabai yana nan? Bukar yace a'a yafita kuma bansan inda yaje ba.
Salis yace ok biyoni office. Guri yabashi yazauna, kallonshi yayi yace Bukar nasan kai musulmi ne kuma Uba, nasan bazaka taba so ace wani abu yafaru da danka ko yarka ba. Domin kome yafaru dasu gurinka zedawo, kuma mutanan gari hada kai zasu rika zagi.
Jinjina kai Bukar yayi yace haka ne. Salis yace ka saurareni zanbaka labarin shari'ar da akayi a kotu shekaranjiya, nasan bakaje ba. Inaso kasaka natsuwa ka fahimci abinda nake fada maka domin zan tambayeka idan nagama...........
Kaf abinda yafaru yafada mashi harzuwa mutuwar Mannir da abinda D.P.O yayi seda yafada mashi. Sosai Bukar yaji tausayin labarin. Kallonshi Salis yayi yace tambaya tafarko itace.
Kadauka kaine mahaifin Mannir haka tafaru da kai, shin zaka iya zama acikin garin nan? Bukar yace wlh yallabai ko sadakar 3 bazan iya bari ayiba, domin Allah yayi ni da tsoron abun kunya da surutun jama'a.
Murnushi Salis yayi yace idan kuma kasamu wanda zetemakeka bazakiyi kokarin zama ba? Bukar yace kai da wuya, saboda gano ainihin gaskiyar wannan case din se kwararran lawyer.
Murmushi Salis yayi yace kana tunanin shari'ar karya akayi kenan? Bukar yace e, na'am? Salis yace kaji abinda nafada ai. Sosa kai Bukar yayi yace nibance ba kawaide ina tunanin idan akace akwai karya acikin shari'ar ya za'ayi?
Salis yace a washe garin ranar da akayi kisan,abokin yallabai tare da wani matashi sunzo office din nan, kozaka iya fada mani mekaji alokacin daka labe? Zaro ido Bukar yayi yace wa, ni? Gaskiya ba ni bane.
Salis yace ai nadau keka a hoto domin in nuna ma yallabai cewar kana mashi labe, kaga seya koreka yakawo wani.
Bukar yace kawa Allah kada ka ruguje mani hanyar samun abinci na. Murmushi Salis yayi dama wasa yake soyake yafadi gaskiya domin tabbas aranar yaganshi sede bedauka wani abu bane yadauka ko soyake yabude kofar kuma ga files a hannunshi shiyasa ya wuceshi be mashi magana ba.
Salis yace to meyasa bazaka iya fadar gaskiya ba? Yanzun nan fa kace inda kaine Baban Mannir guduwa zakayi. Toshi Babanshi yanzu yayi me?
Nasan halinku sarai Masinjoji, babu wanda yafiku sanin sirrin megidanku, amma ina rokonka yau kadai katemakeni da wannan sirrin ko zansamu tundun dafawa. Ajiyar zuciya Bukar yayi..........
Duk abinda yaji aranar dasu Umar sukazo seda yafada mashi. Sosai Salis yayi mamaki. Godiya yayima Bukar yace zaka iya tafiya. Harya tashi yadawo yace bayan wannan kuma akwai abinda nasani akan Mannir da yallabai ta yanda akayi yasamu hoton hannunshi.
Salis yace meyafaru? Kwankwasa kofar da akayi ne yasa su yin shiru, wani Police ne yashigo yace Bukar kaje yallabai yana nemanka. Bukar yace zanje sena dawo. Sosai Salis yaji dadin labarin da Bukar yabashi, nan take yadauko takarda yafara rubutu.
Sosai Abdul yaji mutuwar Mannir alokacin da Sageer yake fada mashi, Abdul yace tabbas mutanan nan basu da imani, kuma babban marar imanin be wuce D.P.O ba, dan haka yazama,dole muje gidan yari kafara bincikenka tacan.
Sageer yace mubari segobe muje. Abdul yace ai yanzu zamu tafi domin aikinka na sirri ne, kaga kuwa dole seda dare zaka rika yinshi domin idan Brr, Yusuf yagane baka zuwa aiki dawuri ze iya bincikarka.
Kuma kada kamanta sh kwaro ne, yanada kwakwalwa dole sekayi ahankali dashi domin ze iya harbo jirginka idan kayi wasa. Sageer yace shikenan tashi muje.
Cikin sa'a suka iske wani tsoho zaune akan kujera acikin dakin masu gadi. Da sallama suka isa wajenshi. Bayan sungaisa sukace suna neman Baba Yusha'u ne. Kallonsu yayi yace kunci sa'a domin dashi kuke magana.
Wani benci yabasu suka zauna. Abdul ne yace Baba wani temako mukazo kayi mana, duk da baka sanmu ba, amma mu munsan kyawawan halinka hakan yasa muka taho gareka.
Baba yace inajinku, kuma inafatan bakuzo da cuta ba? Sageer yace wlh babu wata cuta damu kazo da ita. Jinjina kai yayi yace inajinku. Abdul yace akwai wani wanda aka kawo gidan nan shekaran jiya, anyanke mashi hukunci a babbar kotu na laifin kashe abokinshi da yayi.
Saurin dago kai Baba yayi yana kallonsu, shiru yayi can yace ya sunanshi? Sageer yace sunanshi Mannir, amma kuma ajiya akace yarasu. Baba yace mekuka sani akanshi? .......... Duk abinda yafaru seda Sageer ya warwarema Baba, da kuma son maido da shari'ar farko da yakeso yayi.
Runtse ido Baba yayi yana hamdala, saurin tashi yayi yace nan ba gurin zama bane, domin wani ze iyajin abinda zamu tattauna, kubiyoni zanje inkirawo wani yaro idan yaso semu samu wani guri domin mu tattauna. Tashi sukayi zuciyarsu cike da farin ciki, suna addua'ar Allah yasa su sami wani babban tudun da zasu fara dafawa.
Nima nace aminππ.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
Waiting for your comment. Thanks alot my fans for your concern to me. Luv u allππππ
[2/10, 2:10 PM] nabilalady5: π¨π»πKAFIN IN ZAMA LAWYERπ¨π»π π¨π»π π¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»π
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 70 π€ 75
Wannan shafin naki ne kawata kuma masoyiyata SURRAYYA BAUCHI, ALLAH YABAR KAUNAππππ»ππ»ππ».
Sosai Sageer ,Abdul da Baba sukayi mamakin labarin da Kamal yabasu wanda Mannir yafada mashi ana gobe ze rasu. Tashi yayi yaciro sarkar da Mannir yabashi yamika ma Sageer.
Amsa yayi yana kare mata kallo, Kamal yace koni banyarda wai Mannir kwayace ta kashe shi ba, tabbas akwai abinda Gali yabashi, domin lokacin dayana raba mana Koko ni nasan saboda Mannir ne yayi mana haka, tunda be taba daukar kofi yana mika mana ba.
Kuma lokacin da layin Mannir yazo akwai wasu kofuna guda 2 a hannunshi acikine yadauki daya yabashi. Baba yace tabbas Gali yanada sa hannu a mutuwar Mannir, kuma zansa yarona tunda dansanda ne yayi kokarin bincikar shi a sirrance.
Abdul yace Baba kawai sace shi zamuyi idan yaji wahala zefadi gaskiya. Sageer yace haka ne. Baba ya za'ayi muga Salis? Baba yace wannan ba matsala bane domin agida yake da kwana yau dan beda aikin dare.
Nima lokacin tashina yayi zamu iya tafiya amma fa kuyi sauri kufita kujirani abakin titi banaso Gali ya ganmu tare ze iya zargin wani abu. Godiya suka yima Kamal Abdul yaciro kudi yabashi, Kamal yace baze amsa ba shi dan Allah yayi.
Abdul yace nasani ai, nima ba lada na baka ba, kawaide kyautatawace. Karba yayi yana godiya yamasu sallama yatafi. Seda Gali yazo sannan Baba yatafi, yana zuwa suka tsaida adedeta suka tafi, tun kafin su isa yakira Salis yace yajirashi agida.
Bakaramin dadi Salis yajiba alokacin da yagama jin bayanin su Sageer, anan shima yafada masu duk abinda yasani da wanda yasamu agurin Bukar. Hamdala kawai Sageer yakeyi domin yasan acikin kashi dari yasamu 70.
Sageer yace duk da nakasance karamin lawyer wanda ko gwamnati batasan da zamana ba, amma zanyi kokarin neman takardar fara shari'a daga alkalin babbar kotu, insha Alah nasan zebani goyon baya tunda ana fadar gaskiyarshi da rikon amanarshi. Ance baya yanke hukunci seya tabbatar da manyan shedu.
Salis yace kwarai ma kuwa, kuma insha Allah nizanyi maka jagora har wajenshi domin adawo da wannan case farko. Sede zamuje musami mahaifin Mannir domin yashigar da kara akan mutuwar danshi.
Kaga dole za'a kira Gali, shugaban yari da kuma D.P.O, alokacin kuma kaine zaka tsaya masu kaga seka dauko shari'ar farko da akayi, dama kuma alkalin ne ya yanke hukunci. Abdul yace wannan magana haka take, nasan alokacin Brr, Yusuf da kai ne zaku fafata.
Sageer yace wlh zuciyata ta bushe, banajin tsoron shiga kotu duk da shine karona na farko dazan fafata da kwararran lawyer hakan baya damuna, zanyi kokari inga nima nazama kamarshi. Baba yace Allah yashige mana gaba, kuma yabaka ikon gabatar da aikin alkhairin da zaka fara.
Sukace amin. Salis yace yanzu zanyi kokarin jin sauran bayanin Bukar idan nagama hadasu zan baka, dama kuma nayi recording duk maganar da yayi, saboda kada mukirashi sheda akotu yafadi karya.
Sageer yace hakan ma yana da kyau, muzamu tafi, musayar number sukayi. Godiya sukayi masu suka tafi cike da farin ciki. Sageer yace abokina tunda dare beyi ba gaskiya zanje inga Baby ta, kwana 2 bamu hadu ba. Abdul yace aide ka bari muje muci abinci ko? Sageer yace kawai ka tafi idan nadawo zanci.
Washe gari tunda Abba da Anwar suka tafi masallaci basu shigo gida ba, zaune suke acikin mota. Abba ne ya kalli Anwar yace Dr, naga abin mamaki jiya agurin Auntyn ku dana dawo, sosai nayi mamakin abinda nagani wai hada bani hakuri kuma tace kaima tabaka hakuri ko?
Murmushi Anwar yayi yace haka ne, amma me kake tunani da hakan Abba? Jinjina kai yayi yace kasanni Dr, idan har abu be kwanta mun arai ba inajinshi ajikina. Babu yanda za'ayi yanda ta dauki zafi ace lokaci guda tasauko.
Gaskiya zuciyata tunjiya bata natsu da ita ba, da ace adakinta ma zan kwana wlh bazan iya bacci sosai ba, domin ina Abuja nayi wani irin mafarki da ita, wai ta biyoka da wuka kanata gudu, sede batasamu nasara akan ka ba.
Idan baka manta ba aranar da asuba nakira nake tambayarka lafiyar ka data gida. Anwar yace hakane, ni kaina akwai abinda nakeso infada maka, dan ko Umma ban fadamawa ba, saboda banaso hankalinta yatashi. Wlh Abba wannan tubar da Aunty tayi bawai ta gaskiya bace.........
Labarin duk abinda yaji suna fada ita da Umman Rayyana yabashi, sosai Abba ya girgiza da jin labarin. Kallon Anwar yayi yace tabbas bazance banyarda ba, domin zata iya aikata abinda yafi haka, saboda ni nafi kowa sanin halinta.
Dande nakasance mutum me boye sirrin wani, ko Ummanka batasan komai nagame da zamana da ita ba alokacin tana amarya, ganin nidin ba na wasa bane yasa ta saduda ashe akwai sauran kulli aranta. Ba zanso infada maka abinda tayi ba saboda muna da 'ya'ya da ita.
Amma idan har wannan karon abinda naji ya tabbata kuma nakara samun sheda da kaina, ina me tabbatar maka zamana da ita yazo karshe, domin bazan iya zama da makiyina ba.
A rayuwa daka zauna da makiyinka na boye gara ka zauna da makiyinka na bayyane, koba komai zakasan zaman da zakayi dashi.
Koda ace mun haifi yara dayawa da ita kuma ace ita kadaice matata wlh bazan cigaba da zama da ita ba. Inaso kuma kaje gidan, kasamu kataho da abincin nizansa likita yaduba manishi, matukar akasamu guba aciki to agaban kowa zan zo da result din kuma in yi bani.
Jinjina kai Anwar yayi yace nagode Abba, amma ada nashiga damuwa da tsoron kada ta cutar da kai. Abba yace kar ka damu Allah yana tare damu, kuma a yau ma zamuje neman aurenka. Anwar yace nagode Abba, kuma inaji tare ma za'ayi dana abokina Dr.
Murmushi Abba yayi yace shima yasamu? Anwar yace kanwar Nabila ce ai Abba, dariya yayi yace shikenan kun hada yan gida daya, inafatan itama tana da halin kirki? Anwar yace wlh Abba ba ruwanta, sam bata dauko halin Ummanta ba. Abba yace to Allah yasanya alkhairi.
Bayan Anwar yashiga gida Abba ya jingina da kujerar motar ya kulle idonshi kamar me bacci, tunanin abinda yafaru a baya yashigayi....... lokacin daya auri Aunty haka tarika yi mashi sata, duk abinda ya ajiye seta kasa biyu ta dauki rabi, koda kuwa adakin Umma yake badan komai ba sedan ta hadasu fada.
Da yake Abba yana da zurfin tunani tuni yagano itace take mashi sata, sede betaba yimata magana ba, aranar datayi mashi babbar sata aranar ne ya kamata dumu dumu. Wasu kudade ne da aka bashi ze kai office dinsu, kudi ne masu yawan gaske.
Yana fita sallar asuba Aunty ta tashi ta bude jakar kudin ta kwashi masu yawa, ashe dama be tafi ba ya labe yana kallonta. Seda yabari ta dau ka ta zuge jakar tadauki nata zata boye kawai yashigo ya kunna wuta.
Cike da tsoro ta zubar dasu tafara kuka, zama yayi yace tadauki kudin tamaida mashi, bayan ta mayar yadauki jakar yafita da ita, seda yadawo masallaci sannan yazaunar da ita, kallonta yayi yace Falmata nasan kece kike mun sata agidan nan dan haka tsaya kiji.
Wlh, daga yau bazan kara boye kudina ba, afili zan rika ajesu, duk ranar da naira 5 takara bacewa zakibar gidan nan kinji na rantse maki. Hakuri tayi ta bashi tana rokonshi ya rufa mata asiri kada kowa yaji, kallonta yayi yace dole infada masu saboda ki dena duk wani kilibibi da kikeyi masu wai ke amarya kuma suma surika adana kudinsu.
Tashi yayi yafita yabarta tana kuka, babu wanda yafada mawa kawai de yafada ne saboda tashiga hankalinta da abinda takema Umma na kilibibi saboda tana amarya. Tundaga lokacin tashiga hankalinta take girmama Umma harzuwa lokacin da suka bata.......
A jiyar zuciya Abba yayi yace lallai karshen zamana da ke yazo, saboda me hali baze taba barin halinshi ba, nan gaba zaki iya dauko mani yan fashi ma. Tashi yayi yafita yashiga gida.
Nabila ce zaune agaban Umman Rayyana, data kirata, kallonta tayi tace naji Rayyana tace anjima Anwar zezo shida Dr. Ko? Murmushi Nabila tayi tace e amma shikadai zezo Dr, yanada meeting. Murmushin jindadi tayi domin tana tunanin hanyar dazata bi kada suzo tare.
Batasan kuma shirin Anwar bane haka. Umma tace wai ku kamar ba yan matan zamani ba, ko ruwa ban taba ganin kin kaima Anwar ba idan yazo. Dan haka yau dole kushiga kitchen kuyi mashi girki, ai tun kuna waje ake kama mutum.
Shima zeji dadi idan ya dandana abincinki yaji dadi, kinga zeyi alfahari matar daze aura ta iya girki, kuma zeji dadi kin karramashi. Nabila tace to Umma zamuyi mashi. Umma tace yauwa koke fa, zanzo ingani.
Tashi tayi tafita, takira Rayyana domin su dora girki, sallamar Zarah ce ta katseta, da fara'arta tace shiyasa aka tashi da ruwa yau, ashe Zarah ce zatazo. Dariya tayi tace kefa kin cika tsokana, aide nazo ko.
Janta tayi suka shiga suka gaisa da Ummanta sannan suka shiga wajen Umman Rayyana. Suna fitowa suka shiga dakinsu. Gaisawa sukayi da Rayyana, Nabila tace dama kenake nema Umma tace muyima Yaya Girki.
Dariya Rayyana tayi tace yau wata rana, kodan de hada Abba za'azo shiyasa zamuyi mashi girki? Nabila tace wlh bawani, kuma ma ai su Abba seda dare zasu zo. Fita Rayyana tayi tana fadin bara in gyara kayan miyar kafin kizo.
Zarah tace ikon Allah, shiyasa akace idan kayi hakari arayuwa komai me wucewa ne, da ace Rayyana ta nuna bakin cikinta agame da ke, dayanzu itama bata samu Dr, ba. Amma gashi daga ita har Ummarta data dauki zafi yanzu ta sauko. Nabila tace shiyasa nake son Rayyana, babu ruwanta shiyasa ma nace ma Yaya ya hadata da abokinshi.
Zarah tace Allah de yasanya alkahiri, nima zuwa nayi infada maki jiya iyayen Najib sunzo, har antsaida rana nan da wata 4. Dariya Nabila tayi tace dan Allah? Kice anyi bikinmu da wata 2 zamusha naki. Amma naji dadin wannan maganar.
Zarah tace ke bara intafi nabaro aiki agida, Nabila tace semun hadu a islmaiyya semu kara tattaunawa. Bayan ta tafi suka cigaba da aikinsu. Basu dauki wani lokaci me tsawo ba suka gama fried rice din, tayi kyau sosai se kamshi takeyi.
Zobo suka hada sukashi a glass jug suka jefa kankara saboda babu wuta. Wata cooler me kyau madedeciya suka zuba ma Anwar suka hada komai akan tray, Rayyana tace muje muyi wanka ko, nasan se yayi sallar azahar zezo. Nabila tace to kifadama Umma mungama.
Nabila tashiga wanka Rayyana kuma tana gyara dakin Ummanta, fitowa tayi ta leka taga bakowa, hakan yasa tashiga kitchen ta bude cooler din tazuba maganin ta motse abincin ta gyara yanda baza'a gane ba tafita.
Sosai Bala yayi mamakin labarin da Sageer yabashi, Bala yace biri yayi kama da mutum, wlh kome kacemun Yallabai yayi ze aikata, saboda imaninshi ragaggene inde akan kudi ne. Ina maka addu'ar samun nasara, kuma inde akan ganin alkali ne nizan shige maka gaba.
Domin nasan duk wata hanya da zamubi domin ganinshi, kuma kada kadamu, ai kanada certificate dinka na school of law dakayi ko? Daga kai Sageer yayi, Bala yace zaka iya fara shari'a duk da ba karkashin gwamnati kake aiki ba. Amma akwai takardar da ake amsa kafin mutum yafara tsayawa shari'a akotu, amma insha Allah idan mukaje nasan alkali zeyi mana wannan alfarmar.
Amma zamuje wajen alkalin, kuma bazanso kabari Yallabai yaji wannan maganar ba, nasan ze iya korarka, kuma ze iya sawa ayi maka wani abun matukar yaji kanaso kaja dashi akan wannan case din. Saboda kada Mannir yatona masu asiri yasa suka kashe shi, kaima zasu iya kasheka.
Sageer yace insha Allah Baba zan kiyaye. Bala yace Allah yatemaka, dan haka kashirya anjima zamuje gurin alkalin, amma semun tashi daga aiki, nasan zamu sameshi a office dan baya tafitowa da wuri.
Tsayuwar motar Brr,Yusuf ce ta dau hankalinsu, yana yin parking wata sabuwar mota tashigo, da kallo suka bita harta tsaya, mamakin wanda yafito daga motar sukayi. Brr, Umar ne yafito yadau wanka, hatta da kayan dayasa sababbi ne.
Sosai yayi kyau, komai nashi black, rigar dayasa aciki ce kadai fara yadora coat baka, atare suka jero da Brr, Yusuf. Saurin tashi sukayi Sageer ya matsa ya karbi jakar Brr, Yusuf shi kuma Bala ya karbi ta Umar.
Murmushi Umar yayi yace Sageer katayani murna nasayi sabuwar mota. Murmushi Sageer yayi yace aikuwa tayi kyau, Allah yatsare. Bala yace gaskiya kashigo aiki da kafar dama, wannan irin cigaba haka?
Murmushi Umar yayi yace ai Bala masinja karabu da mutum idan akace maka ba dakiki bane, babu abinda baze iya ba, kaga kuwa har abada bazan kare a share office da karbar jaka ba. Murmushi Brr, Yusuf yayi yashige office.
Dafa kafadar Sageer Umar yayi yace nan gaba kadan zan bude tawa Chamber idan kanaso zan iya kara maka matsayi a office dina kadawo. Dauke hannunshi Sageer yayi yajuyo ya kalleshi fuskarshi dauke da murmushi yace.
Bakada damuwa Allah yatemaka, sede daukar jaka da share office sune matakin nasara araywata. Nan gaba kadan zasu zame mani abin alfahari ga rayuwata, alokacin kuma zanyi alfari da hakan. Ina tayaka murnar samun cigaba.
Bude office yayi yashiga. Bayan sun gaisa da Brr, Yusuf ya fito. Haduwa yayi da wasu mutane matasa su biyu daga ganinsu yaran masu kudi ne. Bayan sun gaisa suka tambayeshi office din Brr, Yusuf.
Sageer yace yasan da zuwanku ne? Girgiza kai sukayi alamun a'a yace to nan ne, kujira nasanar dashi. Kallonshi Brr, Yusuf yayi yace kace su shigo mana, dan suwa nake zaune anan? Tsaki yaja yace kai kullum ana nuna maka yanda ake aiki amma baka ganewa, sekace me kan jaki.
Fita Sageer yayi ranshi abace, sede fuskarshi murmshi ne asama, bude masu kofar yayi yace su shiga. Harze fita Umar yace kadawo kadauko masu ruwa mana koshima se an fada maka?. Dawowa yayi yadauko masu ruwa yafita.
Sede abakin kofar ya tsaya. Bayan sun gaisa sukace yallabai wata matsala ce muke da ita, shine mukaji labarin kwarewarka tasa mukazo wajenka kozaka temaka mana. Brr, Yusuf yayi murmushi yace me yake faruwa?
Dukar da kai dayan yayi se dayan ne yace nide sunana Jafar, wannan kuma abokina ne Salim. Tsautsayi ne yafada mashi ya fadama wata yarinya. Murmsuhi Brr, Yusuf yayi yace agaban Barrister kuke, kuma wanda kuke sa ran ze tsaya maku, dan haka bana son karya.
Jafar yace haka ne, agaskiya wata yarinya Salim yakeso ita kuma bata sonshi, shine yasa yaranshi suka dauko ta shine yayi raping dinta (fyade). To bayan yasa an maidata gida tafadama iyayenta. Kuma Babanta principal ne shine yashigar da kara, yanzu haka ranar monday za'aje kotun.
Gashi Dad din Salim baya nigeria shine Mom dinshi tabamu kudi akan munemo lawyer shine mukaji labarinka. Jinjina kai Brr, yayi yace wannan karamin case ne, awace kotu aka kai karan? High court ya kai domin alkalin shari'a court yayi tafiya.
Brr, yace abu me sauki ma kenan, bakuda damuwa. Umar nabar maka wannan case din kuyi ciniki subaka kudin. Washe baki Umar yayi yace nagode. Salim yace yallabai kana ganin ze iya? Brr, yace dana ne kada kudamu, babu abinda ze gagara.
Umar yace kashe case din kuke so ayi ko kuma korar karar gaba daya? Salim yace inde zeyuwu kawai kashe case din tayanda baza'a tadashi ba. Jinjina kai Umar yayi yace kubada million daya. Jafar yace zamu baka million daya da rabi. Umar yace angama.
Awace unguwa yarinyar take? Salim yace kofar sauri. Umar yace badamuwa zaku iya tafiya. Kudin suka aje mashi sukayi mashi godiya suka tashi. Da sauri Sageer yabar wajen.
Bayan sun tafi yadawo domin yajin abinda zasuce. Brr, Yusuf yace kada kadamu, kaje ka binciko waye saurayinta, shine ze dauki alhakin. idan anje kotu ka tabbatar ma kotu Salim beda lafiya a mazantakarshi. Zansa likita yayi mashi report na karya kuma zeje kotun amatsayin sheda.
Daga nan zuwa gobe zanje na nema maka takardar shedar zama cikakken lawyer wanda zefara shari'a. Kasan koda mutum yayi karatun law dole se kwamitin law tabashi lasisin daze iya fara aiki koda kuwa under private yake. Shiyasa nace maka seka riga Sageer daukaka domin shi beda hanyar samun haka sede idan gwamnati ce ta daukeshi ai. Umar yace nagode.
Girgiza kai Sageer yayi cike da tausayi ya koma office dinshi ya zauna. Bala ne yashigo yana fadin lafiya de Sageer ko wani abun kajiyo? Labarin abinda yaji yafada mashi. Bala yace wannan kuma sune zasu karama kansu zunubi, kaide ga aikin da yake gabanka.
Runtse ido Sageer yayi yace Baba inaso intemaka masu. Kallonshi Bala yayi yace wancan aikin naka fa? Sageer yace yana nan, nasan nan da sati 1 ma bazamu shiga kotu ba, amma shi wannan monday ne za'aje.
Bala yace yanzude anjima se muje wajen alkalin, idan yaso sekaje kafara binciken. Bazan hanaka aikata alkhairi ba, wata kila adalilin wannan alkhairin kaima kasamu biyan bukata awajen Allah. Kuma maganar lasisi kada kadamu kanka nasan alkali ze samar maka.
Zaune Anwar yake afalon baki suna fira shida Nabila, Rayyana ce tashigo da tray din abinci Anwar yace amma kanwata ban kyauta maki ba da banzo da abikina bako? Murmushi tayi tace ai bakomai shima zezo ya kyaleka.
Umman Rayyana ce tace to ai seku fito kubar dan nawa yaci abinci kun tsareshi da surutu. Murmushi Anwar yayi yace Umma abarmun kanwata muci tare mana. Kamar anjefota tashigo tana fadin kai de kaci abinka wata rana zakuci.
Kama hannunsu tayi tana fadin kutashi muje kuci naku kubarshi yaci anatse, kuma idan bakaci ba zamu bata sonake kacinyeshi duka tunda cooler karama ce bawani yawa ne dashi ba. Anwar yace ai Umma saboda inci abincin gidan nan yasa yau lipton kawai nasha da safe.
Fita sukayi tana fadin yauwa haka nakeso ai gaka itama Nabilar zataji dadi idan kacinye duka. Suna fita Anwar yayi murmushi aranshi yana fadin dafa beji abinda suka fada ba shikenan ajalinshi zeci ko? Hamdala yayi yasa hannu aljihunshi yaciro bakar leda.
Gaba daya abincin yajuye ya kulle ledar yadauko wata yasaka aciki, tsayawa yayi yana tunanin inda ze saka ledar, tashi yayi yaleka waje yaga bakowa yabude kofar waje yafita, dayake akwai kofa ta wajen gidan.
Mota yasaka abincin yadawo, ko zobon kasa sha yayi domin besani ba ko anzuba aciki, a cup yazuba yashiga bandakin cikin falon yazubar. Dawowa yayi yazauna yana karama Allah godiya.
A waya yakira Nabila tana zuwa ta bude cooler taga babu komai, murmushi tayi tace lallai kaci abinci. Anwar yace ba dole ba tunda ke kika dafa. Tashi yayi yana fadin zanje asibiti bana jin dadin jikina muje inma su Umma sallama.
Nabila tace meyasameka kuma? Anwar yace zamuyi waya kifada masu zantafi, shiga ciki tayi tafada masu zetafi, Umman Rayyana tace da wuri haka? Nabila tace yace asibiti zeje bayajin dadi. Tace yade ci abincin ko? Nabila tace duka ma yacinye.
Tace ai gara yayi sauri yatafi kada yakasa tuka motar, kinsan jiki da jini.shigowa yayi yamasu sallama bakin Umman Rayyana yakasa rufuwa, kudi yabama Rayyana yace tabasu. Godiya sukayi mashi yafita.
Direct asibiti yawuce acan yasamu Abba, abincin yabashi haka suka bama Dr, din aka shiga domin a aunashi, wani bera likitan yadauko, abincin yazuba mashi, yanaci yadauke yace mubashi minti 5.
Awonshi yacigaba, ai kafin minti 5 beran ya mutu. Sosai Anwar ya girgiza, Abba yadafe kai yana fadin yanzu wannan gubar itace zaka iya bama dan Adam yaci. Kai duniya ina zaki damu.
Likita yaciro result din daya gama, yazauna yana fadin ai Alhaji wannan kadan ma kagani, wlh mutane yanzu tsoron Allah yayi masu kadan azuciyarsu sede addu'a kawai, saukin ma da kuka iya gane makiyanku da wuri.
Karbar result din Abba yayi yana fadin nagode, seka jini, amma azubar da abincin nan inda wani baze ciba. Dr, yace badamuwa zansa shi a toilet ma. Tafiya sukayi suna mashi godiya.
Daga nan wajen kaninshi suka wuce domin suje gidansu Nabila, yayi niyar seda dare amma dan yanuna masu aikinsun beciba yasa Anwar yakira Nabila tafadama Babansu gasunan zuwa.
Sosai Anwar yaji dadi za'aje nema mashi auren Beelert dinshi. Abba yace kanaji na ko Dr? Kabani nan da kwana 1 zakaga irin hukuncin dazan yanke. Inaso ko Ummanka kada kafada mata komai. Anwar yace insha Allah.
Kafin su isa har Baba Nabila yadawo, alokacin Umman Rayyana bata nan tashiga makwabta. Umman Nabila yasa ta hado masu abinsha.
Bayan sunzo suka gaisa Kanin Abba yagabatar dasu, sosai Babansu Nabila yaji dadi, hakan yasa yace yabama Anwar Nabila. Godiya sukayi mashi, suka neme alfarmar hada bikin dana Zaituna kanwar Anwar dan ayi lokaci guda. Baban Nabila yace wannan badamuwa bane, ai duk sauki ne. Itama Rayyana kanwar Nabila mamanta tamun maganar wani abokin Anwar dayake sonta.
Idan shima yashirya kunga se ahade bikin lokaci guda kowama ya huta. Suka ce hakane, Abba yace zansa Anwar yayi mashi magana idan har da gaske yake to yaturo iyayenshi dan yanzu tsayawa wannan dogon zancen shine yake lalata mana yaranmu. Dan RAYUWAR MATA AYAU kawai suyi ta acikin gidan mazajensu. Sukace gaskiya ne
Anan suka bada kudin neman aure sukace zasu aiko da kayan sa rana. Godiya sukayi mashi suka tafi. Har suka tafi Umma bata dawo ba.
Salis, Bala da Sageer ne zaune a office din alkali. Bayan sun gaisa alkali yace mal. Bala kwana da yawa kaboye bana ganinka? Bala yace wlh abubuwan ne sukayi yawa. Ya aiki da fama da jama'a? alakali yace lafiya lau.
Lafiya de naganka da inspector Salis? Murmushi Salis yayi yace yallabai lafiya lau, alkali yace to dasauki ai nadauka koni akazo kamawa. Dariya sukayi Bala yace wlh yallabai wata babbar alfarma mukazo nema awajenka.
Alkali yace haba mal. Bala kafadi matsalarka inde bazata gagaraba ai ni meyi maka ne, ai mundade muna tare. Bala yace wannan sunanshi Sageer, yayi karatun lawyer yagama komai.
Gama takardunshi nan, karba alkali yayi yafara dubawa. Bala yace to yana aiki akarkashin megidana Brr, Yusuf, sede be dade da fara aikin ba. To akwai wata shari'a da akayi kuma kaine ma kayanje hukuncin, to akwai abinda yafaru shikuma yakeso ya tsayama iyayen yaron da aka yanke ma hukuncin.
Shine nace zan kawoshi wajenka munemi alfarma domin ya gabatar da wannan aiki. Jinjina kai alkali yayi yace wace shari'ar ce, kasan nayisu dayawa? ......... labarin sharia'ar daya gabatar sageer yatuna mashi, Sageer yace yallabai akwai alamun rashin gaskiya acikin shedun da aka gabatar. Alokacin gaskiya nasan ba haka abun yake ba. Sede banida wata kwakkwarar sheda da zan iya gabatarwa shiyasa banyi magana ba.
Amma ayanzu nasamu shedar dazan gabatar agaban kotu, kuma iname tabbatar maka zatayi anfani, shine muke rokon alfarma kabarni ingabatar da shedar. Jinjina kai alkali yayi yace natuna da shari'ar.
Hakika aranar dana yanke hukuncin da dare ina kwance nakasa samun nutsuwa, bantaba yanke hukuncin da zuciyata takasa nutsuwa ba kamar wannan, sede ban kawo komai arai naba nadauka kawai wani abu ne yake damuna.
Babu damuwa, tunda de kanada shedar zama lawyer kuma har kana da private offer babu damuwa zaka iya tsayuwa domin ka gabatar da shari'a. Dama abinda akeso daga gurin lawyer shine asamu takardar shadar zamanshi lawyer, abu daya ne baka dashi shine lasisin zama lawyer, shima kuma tunda kazo da mal. Bala insha Allah zante maka, domin munyi zaman mutunci dashi, ada shine megadina alokacin da yayi tafiya nasamu wani to bayan yadawo nasama mashi aiki a office din Brr, Yusuf
To Kada kayi mamakin kafi tsohon lawyer daya shakara 20 yana aiki hakaza, domin abun baiwa ne. Bakomai nayarda zan amshi kararku, kuje kusami mahaifin yaron yashigar d akara akan yanaso asake shari'ar, idan yaso se yaron yazo.
Bala yace yallabai ai yaron yarasu awashe garin ranar da aka kaishi. Runtse ido alkali yayi, cike da tausayi yace idan ko hakane, namaku alkawarin sena tabbatar da adalci idan har kuka gabatar da kwakkwarar sheda.
Banaso inji komai yanzu, kawai kuje ku dage inaso kuhada manyan shedun dazasu sa dani da ku bazamuji kunya ba, domin banason ace nayanke hukunci daga farko kuma amaidoshi baya azo kuma ace babu wata nasara.
Mahaifin yaron yashigar da kara akan mutuwar danshi. Idan yaso zansa ranar dazamu zauna sharia'a domin monday inada wata shari'a. Sageer yace mungode yallabai, kuma shari'ar monday ma itace nakeso zan fara gwada kwazona, domin inaso in tsayama wadan da aka zalunta.
Alkali yace hakan yana da kyau, gara kafara da ita saboda ka kara samun kwarewa kafin wannan. Allah yabada sa'a. Insha Allah kafin monday mal. Bala ze kawo maka lasisinka. Godiya sukayi mashi suka tashi suka fita cike da farin ciki.
Sageer yace Baba kaje kawai inaso zamuje gidan su yarinyar nan, nida Salis akwai abinda nakeso inbinciko. Baba yace shikenan Allah yatemaka senajika, tunda gobe babu aiki. Amma zan amsar maka.
Tafiya yayi su kuma suka wuce kofar sauri domin bincike akan shari'ar daze gabatar jibi.
FAFATAWA TSAKANIN BRR. UMAR DA BRR. SAGEER ALEE DAN MASANI. ALLAH YABA MERABO SA'A.
KUBIYONI DOMIN JIN SHARI'ARSU TA FARKOπ€·π»♀π€·π»♀ππ»♀ππ»♀.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[2/10, 2:10 PM] nabilalady5: π¨π»πKAFIN IN ZAMA LAWYERπ¨π»π π¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»π
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 75 π€ 80
This page is dedicated to my lovely sister's Farida, Maryam,Halima and Amina Rabi'u Zango. Luv u allππππ.
Zaune suke agaban mahaifin yarinyar da akayima fyade, shiru yayi alokacin daya gama jin bayanan su. Dago kai yayi yace da farko de nagode da kulawarku agaremu. Kuma naji dadin yanda kuka nememu badan komai ba sedan ku kwato mana hakkinmu.
Yanzu haka fitowar danayi gidan Brr, Yusuf zani domin dazu naso inje office dinshi bayan naje nashigar da kara. Se kuma akamun waya yarinyata ta farfado, domin bayan sun dawo da ita gida tafada mana abinda yafaru.
Mamanta ta kamata zasu shiga bandaki tafadi asume, shine muka kaita asibiti. To akwai wani abokina dayake fada mani irin kwarewar Brr, Yusuf shine nace zanje in sameshi domin ya tsaya mana.
Hakika naji dadin zuwanku, kunga da naje ma baze karbeni ba tunda anrigani, bakomai babu abinda zance sede ince nagode ma Allah, domin shine ya shiryo mani wannan abun. Ina maku fatan nasara, kuma nawa ne zan bada?
Sageer yace Baba bana bukatar komai daga gareka domin ba kudi bane ya kawoni wajenka, abinda naji ne yasani tausayin diyarka har na nemi gidanka badan komai ba sedan inkwato mata hakkinta.
Godiya Baba yayi masu yace ba damuwa zamu iya shiga domin kuyi mata tambayoyin. A kwance suka sameta kusa da mahaifiyarta. Bayan sun gaisa Sageer yace ya sunanki? Gyara zamanta tayi idanuwanta cike da hawaye tace Zubaida.
Sageer yace alokacin da wannan abun yafaru, babu wata sheda dazaki iya bamu wadda zata nuna cewar Salim shine yayi maki fyade? Shiru Zubaida tayi tana tunani, kallonshi tayi tace gaskiya banda wata sheda, sede abinda nasani alokacin muna kokowa dashi naji mashi ciwo gefen wuyanshi da yatsuna.
Kuma tabbas sun fasa shi dan harseda jini yafita alokacin dayaji zafi ne yake fadin ni zakijima ciwo? Shine ya wankeni da mari daga nan bankara sanin inda kaina yake ba.
Kallon Baba yayi yace alokacin da kukaje asibiti nasan likita yabaku result din awon da akayi mata ko? Baba yace kwarai ma kuwa suna nan. Sageer yace mungode insha Allah da wannan ma kadai zamu iya kamashi, sannan kuma zan samu likitan dazeyi mashi awon daze tabbatar ma kotu lafiyarshi kalau.
Shikuma surayainki zefita daga zargi insha Allah. Kuma inaso kada kiji tsoron komai agaban kotu kifadi duk abinda kika sani da yake tsakaninki dashi. Mamanta tace kai amma wannan yaron mungode, Allah yayi maka albarka.
Hakika da ace kowane lawyer haka yake da irin zuciyarka gaskiya da ansamu cigaba arayuwar nan. Mungode sosai. Sallama sukayi masu suka tafi.
Sageer yace nagode Salis, da abinda kake mani, hakika nasan Allah ne ya kawomun kai domin katemake ni, dan badan kai ba nasan zansha wuya sosai. Salis yace bakomai Sageer kada kadamu, nima inason insamu ladar da zaka samu.
Koba komai nima zance na aikata aikin alkhairi arayuwata, dan haka ashirye nake inbada rai na wajen gano gaskiyar wannan case din. Dan haka daga nan wajen Bukar zamu wuce domin mukarasa jin bayaninshi, saboda ina tsoron kada wani abu yafaru.
Sageer yace badamuwa mutafi kawai, gara mugama dashi. Salis yace shikenan nizan samo maka likitan dazeyi mana aiki tsakani da Allah, domin abokina ne. Sageer yace yauwa nagode.
Zaune suke sunsa Bukar a tsakiya domin jin abinda ze fada. Gyara zama yayi yace kamar yanda nafada maka, bayan yallabai yakawo Mannir ya kulle, awashe gari ina zaune naga yallabai da Mannir sun shiga office.
Kawai ni kuma senaji inason inji abinda ze fada mashi. Musamman danaji abinda sukace ayi mashi, hakan yasa naje ina leke. Wani glass cup naga yallabai ya mika ma Mannir yace ya zubo mashi ruwa a fridge din dayake office dinshi.
Sede daya mika mashi be amsa ba yace ya ajiye masa. Kallonshi yayi. Yace Mannir kada kadamu nizan fadama lawyer duk abinda kafada mani, nasan kuma za'a kwato ma abokinka hakkinsa, kuma agobe zaka fita daga nan.
Bayan yatafi naga yallabai yasa kyalle yadauki kofin yazubar da ruwan yasa aleda yafita. Wannan shine yanda yallabai yayi yasamu hoton hannunshi. Wannan wayar tawa akwai vedion dana dauki yallabai alokacin dayake zuba kwaya acikin ruwa.
Kuma wannan ruwan shine yabama Mannir yasha kafin sutafi kotu. Nide nasan bawai sheda zan kai ba. Amma hakanan narika bibiyar yallabai tun daga ranar danaji maganarsu, duk da ba wannan kadai bane laifin da nasan yallabai yana aikatawa ba.
Lokaci da yawa ina kamashi sede shi atunaninshi bazan fadama kowa ba, saboda yana daukata sakarai, shiyasa ni kuma nabarshi ahaka, bantaba tunanin zan iya fadama wani sirrin yallabai ba. Amma tunda mukayi magana da kai, na koma gida aranar banyi bacci ba.
Hakan yasa nayima Allah alkawarin koda zan rasa raina zan tsaya agaban kotu domin infadi duk mugun hali na yallabai. Wata kila nima Allah yayi mani rahama.
Jinjina kai sukayi, Salis yace mungode Allah yasaka da alkhairi kuma zamu nemeka idan lokacin yayi. Sede inaso kada kabari kowa yaji wannan maganar koda abokan aikin mune, kasan mutane basuda tabbas.
Karbar wayarshi Sageer yayi ya tura vedion suka mashi sallama suka tafi. Sageer yace ina ganin daga nan zamu rabu, Allah yabiyaka da ladarsa me yawa, semunyi magana. Salis yace amin, se anjima, amma ka tabbatar kaboye duk wasu muhimman takardunka, kada ka ajesu agida. Sageer yace insha Allah.
Washe gari da Anwar da Dr,shamsu da kansu suka kai kayan sa ranar Nabila bayan sun gaisa da Ummanta suka shiga ciki wajen umman Rayyana, lokacin data ganshi seda gabanta yafadi.
Domin tunjiya da sukayi waya da Aunty tace mata bedawo daga acibitin ba kila ko gubar batayi mashi lahanin daze mutu alokaci guda ba, shine tace amma tabari zuwa safe suga abinda zefaru. To har dare Aunty bata ga Anwar ba shiyasa bata gane ba.
Kuma da safe bataga Alh, ba shiyasa bata tambayeshi jikin Anwar ba. Umma tace yaushe aka sallameka Anwar? Zama sukayi yana murmushi yace Umma waya fada maki ankwantar dani?
Sosa kai tayi tace banaji jiya kace zakaje asibiti bakajin dadi ba? Murmushi yayi yace wasa nake ma Nabila kawai. Gaisheta sukayi amma gaba daya hankalinta baya jikinta. Anwar yace Umma dama iyayen Shamsu ne sukace afadama Baba zasuzo anjima.
Washe baki tayi tace to shikenan zan fada mashi,Allah yakawosu lafiya. Tashi sukayi zasu tafi suna fita Anwar yajuyo ya kalleta, wayarta yaga tadauko tashiga daki. Abbanshi yakira yace Abba kasa ido dakin Aunty nasan zakaji komai.
Aunty ce zaune afalo tana kallo, wayarta ce tayi kara dauka tayi, tunkafin sugaisa Umma tace munshiga 3, ashe yaron nan lafiyarshi lau, yanzu suka bar gidan nan shida Dr, sun kawo kayan sa rana.
Zumbur Aunty ta tashi tana fadin da gaske yakumbo? To kode baki zuba gubar ba? Amma kuma ai kince mun babbar guba ce idan mutum yacita baya wuce minti 5.
Shiru tayi tana saurarenta. Aunty tace ina, wlh baze yuwu ba, idan har ina raye se na kawar da Anwar da ubanshi. Kiji rani anjima zanzo wlh kota karfi ne se yabar duniyar nan kafin bikinshi. Kashe wayar tayi juyowar da zatayi taga Abba abakin kofa ya rungume hannu wanshi 2 a kirjinshi yana kallonta.
Sakin wayar tayi cike da tsoro, zama tayi tana fadin Abba yaushe kashigo? Amma de yanzu kashigo ko? Murmushi yayi yace lokacin da wayarki tayi kara kika dauka baki ganni ba?
Ai tunkafin lokacin nashigo. Dafe kirji tayi ta zube kasa tana fadin nashiga 3, yanzu duk kaji wayar danayi? Wayar hannunshi yadaga yana fadin duk abinda kika fada yana nan ciki, dan haka kisameni afalona.
Zaune suke afalon Abba Anwar yana daga gefenshi kusa da kafafuwanshi, Umma tana kujerar kusa dashi, kallon Abba tayi tace wai Abban Anwar lafiya de? Naga gaba daya fuskarka babu alamun walwala aciki, kuma katara mu kayi shiru.
Wayarshi yadauka yakira Aunty, tana dauka yace wlh idan kika kara minti 2 baki zoba zaki ganni da kaina. Tagumi Umma tayi tana kallon ikon Allah.
Aunty ce tafito da hijabi ajikinta se kuka takeyi, tana zuwa ta duka gaban Umma tana fadin dan Allah kiyi hakuri, kada kibari Alh, yakoreni.
Abba yace kiyi mana shiru muyi abinda yatara mu anan, domin banason ganinki cikin gidan nan,zaro ido Umma tayi sede batayi magana ba.
Gyara zama Abba yayi yace Alhamdulillahi ina godiya awajen Allah daya kawo mana wannan rana,wadda insha Allah itace rana ta karshe da gidan nan ze rabu da tashin hankali da kuma annobar datake cikinshi.
Hakika Falmata kinyi faduwar toto a ruwa, kin bani mamaki yanda kika bari shedan yashiga zuciyarki har ya iya busar da ita haka saboda kawai kwadin duniya.
Gashi ayau base gobe ba zaki kwashi laifinki da hannunki, albarkacin yaran damuke dasu kawai zesa bazan kaiki kotu ba, amma da sekin yi zaman gidan yari wlh. Kinso ki cutar damu Allah be baki dama ba.
Ashe dama duk son da kike nuna mana bana gaskiya bane? Idan baki sani ba, aranar da kuka shirya komai keda yar uwarki a falonki to a kunnan Dr, kukayi komai.
Tabbas gubar da kuka zuba mashi taci, sede ba'a kanshi taci ba, kinsan ko waye yaci? Bera shine wanda yacita, kuma kamar yanda kuka fada kafin minti biyar duk wanda yacita ze mutu, hakan ne tafaru shima ya mutu.
Wannan itace takardar shedar da likita yabani daya gano irin muguwar gubar da kuke so Dr, yaci. Allah ya tsare bawansa amma har kike ikirarin wai kota halin yaya ne se nida Dr, munbar duniya.
Kunna wayar yayi, anan kowa yaji duk maganar da tayi, sosai Umma tashiga tashin hankali, hakika Allah yatsare mata danta, da yanzu yajima da rasuwa.
Matsawa tayi daga wajen ta kamar taga wani mugun abu, kuka kawai Umma takeyi, Aunty tace dan Allah kuyi hakuri wlh ba laifina bane, kuma daga yau natuba bazan kara ba.
Abba yace ai sede ki koma gidanku kicigaba da tubar amma ba'a gidana ba. Wannan takardar sakin kice, duk da ba'a son ayi saki 3, amma babu yanda na iya, idan anayin 100 ma zan iya maki badan komai ba sedan inyanke duk wata alaka dazata kara hadani dake.
Ihu Aunty tasa tana fadin ya zakamun haka,Anwar dan Allah kasa baki wlh nayi nadama. Tashi Abba yayi yace na gama magana, kitashi nabaki minti 30 mota tana jiranki awaje ki hada kayanki, idan kuma lokaci yacika wlh bazan jira kidauki komai ba.
Motar ma nayi maki adalci ne nasa Dr, yakawota saboda nasan ba garin nan kike ba. Idan kuma kina da abinyi acikin gari zansa sutafi. Kudi ya dora mata akan cinyarta dubu hamshin yace ga wannan ki rike.
Kuka sosai Aunty takeyi tana baUmma hakuri, Abba ne yadawo ya kama hannun Umma suka shige ciki. Ganin an barta ita daya yasa ta dauki kudinta tashiga daki, kayanta tafara hadawa tana kuka.
Kaf ta hada kayanta ta leka tafadama Anwar tagama, magana yayi masu suka shigo suka cire gadon da sif din suka fara fiddawa, duk yanda Anwar yakejin haushinta seda yaji tausayinta.
Kudi yaciro yakara mata, godiya tayi mashi tana ta bashi hakuri, kallonshi tayi tace dan Allah Anwar ka kula mun dasu Ilham, nasan Umma bazata taba cutar su ba, idan tadawo kace tayafe mani, tana murnar zata gama makaranta seta dawo ta iske abinda nayi.
Anwar yace karki damu, muje kada Abba yafito. Aunty tace dan Allah zanje gidan yakumbo kafada masu subiya dani ba dadewa zanyi ba. Yace to.
Har dakin Umma taje tana kuka tana bata hakuri, itama Umman kukan take, sosai ta bata tausayi, rungume juna sukayi suna kuka, haka tafita tana kuka, shi kanshi Anwar seda yaji idonshi yacika da kwalla, saurin juyawa yayi yakoma dakinshi.
Kafin su karasa cikin unguwarsu Nabila tace su tsaya, fita tayi dama itace agaban motar kayan, da sallama tashiga bakowa atsakar gidan, ganin akwai mutane afalon baki yasa tashige dakin Yakumbo.
Tana shiga ta rungumeta tana kuka, Umma cike da tashin hankali tace lafiya, meyake faruwa kuma? Kuka kawai Aunty takeyi tana fadin shikenan nashiga 3 yakumbo.
Baban su Nabila ne yafito domin kiran Umman Rayyana akan tasa akawo masu abinci domin iyayen Dr, Shamsu ne sukazo suna falo,yazo shiga falon kenan yaji ana kuka, tsayawa yayi afalon domin suna cikin daki.
Labarin duk abinda yafaru Aunty tabama Umma, cikin kuka tace shikenanYakumbo ni ban ci dukiya ba an koreni, nayi 2 babu yanzu idan nakoma gida kema kinsan irin zaman dazanyi da matan gidanmu.
Gashi ni bawani kudi nake tarawa ba bare inja jari, ba aiki nakeyi ba, haka zan,koma inacin abincin gandu, kinsan halin Baba sarai baze goya mani baya ba seya kira ya tambayi abinda yafaru.
Nide Yakumbo kin cuceni, meyasa ma kika kawo mani gubar daza'a sama Anwar? Da kin bari kila da babu wanda zeji da barata. Umma tace hakama zakice? Aunty tace toyanzu meye abunyi, tunda kema bawani abu kike karuwa dashi agidan nan ba, kawai kisa ya sakeki kinga semuje mukama haya agarin nan muzauna tunda ga kudi nan.
Kinga muna cikin gari yaranmu zasu rika temakon mu. Saurin tashi Umma tayi tana mata wani irin kallo, murmushi tayi tace lallai falmata inaji kanki ya motsu, kina tunanin zan iya kashe aure na inbar gidana na aure in koma gidan haya? Uhm to bara kiji shi MUHALLI DAKIKE GANINSHI KOMIN KAN KANTARSHI DARAJA GARESHI.
Kuma duk wanda yarasashi yayi babbar asara, me ake da gidan haya? Ai gara kiyi hakuri ki koma gidanku ko ba komai kinsan nakune, kuma mahaifinki baze taba korarki ba.
Amma ki ma dena wannan maganar, babu abinda zan yima Allah se godiya, Allah yasoni da rahamarshi da be bari Anwar yaci abincin nan ba, da yanzu nikeda alhakin kisan kuma daga karshe kece da dukiyar sede kirika samma ni.
Hakika na godema Allah daya kareni daga sharrin shadan, kuma insha Allah daga yanzu base anjima ba natuba daga aikata duk wani mugun abu, Allah ya yafe mani, kuma zansamu duk wanda na cuta innemi yafiya daga garesu.
Babu ruwana dake, kawai kitafi kaduna, idan nazo marika gaisawa. Tashi Aunty tayi tana fadin wlh sena tona maki asiri, kema sekin bar gidanki kamar yanda nabarshi. Fita tayi Umma tabiyota.
Cak suka tsaya ganin Baba afalo, zubewa kasa Umma tayi tasaki kuka, murmushi Aunty tayi tace sekin taho ni nayi gaba, wuce shi tayi ta fita. Girgiza kai yayi bece mata komai ba, yace kibama Nabila abincin baki takawo masu. Fita yayi kawai, zuciyarshi cike da bacin rai.
Saurin tashi Umma tayi ta goge idonta cike da fargabar abinda ze biyo baya tafita domin hada masu abincin.
Jinjina kai Abdul yayi yace gaskiya naji dadin wannan labari,alkalin nan yana da kirki inba dan shiba ina zaka samu wannan lasisin? Sageer yace wlh kuwa, ai na Allah basa karewa.
Yanzu ni ina zan aje wannan takardun,domin Salis yace kada na aje su agida? Shiru Abdul yayi can kuma yace meze hana bazaka sasu acikun karamar jaka ba ka kaima Saddika ta aje maka, amma kada kafada mata ko menene aciki, nasan acan zasufi zama dede, domin babu wanda zesan kabata ajiya, asalima bakowa bane yasan kuna tare.
Sageer yace haka ne, wannan ma shawara ce. Yanzu yakake ganin yanda zamu hadu da Ammar har na iya bincike akan wannan sarkar, domin kona nunata amatsayin sheda idan yace besanta ba bani da abin cewa.
Abdul yace haka ne, amma ka bari zanyi kokarin yimaka binciken yanda za'ayi, insha Allah zamu samu wani abu daze tabbatar ma kotu sarkarshi ce. Sageer yace yauwa abokina nagode, Allah yabani abinda zan iya saka maka dashi. Murmushi Abdul yayi yace amin abokina. Haka suka cigaba da hada shedun da Sageer ze gabatar a kotu ranar monday.
Bangaran Umar ma Brr, Yusuf yagama hada mashi komai hatta da lasisin shi yakarbo mashi, duk yanda zeyi idan yaje kotu ya nuna mashi.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
Godiya agareku masoyanaππ»ππ»ππ»ππ»π€π»π€π»

Season 80 π€ 85
WANNAN SHAFIN NAKA,NE DAN KANINA, UMAR RABI'U ZANGO.π΄π»π΄π»
Gaba daya hankalin Umman Rayyana ya kasa kwanciya, gashide tun jiya Babansu Nabila bece mata komai ba, tunda yashigo bekara kallonta ba, ko kudin auren Rayyana da aka bashi Umman Nabila yabamawa.
Duk da adakinta yake amma aranar bedawo gida da wuri ba seda ya tabbatar kowa ya kwanta sannan yashigo shima dakinshi yashige. Haka ya kwanta yana cike da tunanin abinda yaji afalon Umma.
Sosai yayi mamakin wannan abu da suke shirin aikatawa amma shi beda labari, tunanin irin hukuncin da yakamata ya yanke akan Umma yakeyi. Ganin yakasa samun mafita kuma bacci yaki daukarshi hakan yasa yatashi yayi alwala yafara nafila.
Washe gari haka yafita beci abincin Umma ba, kowa agidan yasan akwai abinda yake damun Umma, domin da kyar ta fito ta hada masu abincin safe, Umman Nabila taso tayi mata magana sede bataso tashiga abinda be shafeta ba, dan tana tunanin ita da megidan ne.
Da azahar bayan yadawo gida yana falonshi wayarshi ya dauka yakira Anwar, bayan sun gaisa Baba yace Anwar naji duk abinda yake faruwa jiya bayan Auntyn ku tazo gidan nan.
Da farko de ina baka hakuri kuma shima Alhajin zan kirasa inbashi hakuri bisa abinda medakina tayi maku. Kasan halin mata, sede ina rokonka wata alfarma guda daya, kuma inaso shima Baban naka kafada mashi.
Dan Allah yanda akayi maganar nan tawuce to abarta, kada abari yara suji abinda yariga yawuce, ina ganin hakan shine zefi domin tada fitina beda wani amfani arayuwa. Anwar yace insha Allah Baba komai yawuce, kuma zan fadama Abban.
Bayan sungama wayar yakira Umman Nabila,bayan tazo ya kalleta yace daga yau inaso ki cigaba da girki dan inaso in cire Saude daga cikin iyalina daga yau.
Saurin kallonshi tayi cike da firgici tace dan Allah malan kada kayanke wannan hukuncin. Idan ma kayanke dan Allah kamayar da ita, duk da bansan abinda tayi maka ba,amma kadubi girman Allah kayi hakuri.
Kasan Allah ma muna mashi laifi kuma mune mi afuwarshi kuma yayi mana, kadubi zuri'ar da take tsakaninku da shakuwar datake tsakninmu wlh bazanji dadin zaman gidan nan ba idan akace Saude zata barshi.
Shiru yayi yana jinjina kyan hali irin na Karima, hakika ba kowace mace bace zata iya abinda Karima tayi, kallonta yayi yace shikenan ya isa. Nagode da Allah yabani mata irinki me zurfin tunani, gashi de nafada maki zan rabu da Saude, amma bakiso kiji abinda tayi mani ba.
Nima kuma dama nayi alkawarin bazan fadama kowa abinda tayi ba, duk da bani tayi mawa ba, sede nayafe mata tunda har kin roka mata hakan, dama kuma ban ri ga da nasaketa ba. Nagode Allah yayi maki albarka.
Ki kira mani ita. Cike da fargaba Umma tazauna kamar zata ruga haka ta zauna a dosane, shiru yayi yana kallonta, duk seta kara tsarguwa, Saude! Saurin dago kai tayi tana kallonshi.
Duk naji abinda yafaru ajiya tsakaninki da yar uwarki. Hakika kin bani mamaki, wai ace kamar ke zaki iya daukar guba kizuba ma dan uwanki musulmi kawai saboda son zuciya.
Tsoron Allah yayi karanci azuciyarku har kuke tunanin kawar da wani dan kuzauna aduniyar kuji dadi saboda ance ku bazaku mutu ba. To wlh kiji tsoron Allah. Abu daya ne yasa bazan kore ki daga gidan nan ba.
Na farko tun ajiyan naji alamun nadama daga gareki, sannan na biyu kuma saboda Karima, hakika kinyi dacen abokiyar zama, dan haka ki kara riketa tsakaninki da Allah, domin har abada bazaki taba samun kamarta ba. Ba dan ita ba babu abinda ze hanani baki takardarki yau.
Umma tace dan Allah kayi hakuri, wlh nayi nadamar abinda na aikata, insha Allah bazan kara aikata hakan ba, kuma ina rokonka alfarma karufa mani asiri kada wani yaji wannan maganar, duk da nasan kafadama Karima amma nasan bazata iya fadama kowa ba.
Kallonta yayi yace shikenan komai yawuce Allah ya yafe mana gaba daya, kuma itama Karimar ban fada mata komai ba,zaki iya tafiya, godiya tayi tamasa tana kuka.
Agidan su Anwar kuwa sosai Umma taji kewar rashin Aunty, duk da tana cike dajin haushinta amma hakan be hanata jin kewarta ba, domin ance komin rashin dadin mutum idan baya kusa da kai sekaji kewarshi.
Jitayi duk gidan yayi mata shiru, dan ma Abba yana nan, Anwar ne yashigo, bayan ya gaisheta Abba yafito daga daki yana fadin Dr, kashigo kenan? Yace wlh kuwa Abba, kallon Umma yayi yace dazu munyi waya da Zaituna take fadamun an rage masu kwanakin su, sati mezuwa zasu dawo, gobe zasu fara jarabawa ma.
Umma tace Allah sarki, dama yanzu naga miss call dinta na kecewa bari kashigo ince kasiyo mani kati inkirata, ashema kunyi waya. Abba yace haba Umma babba dake kike zama babu kudi awayarki?
Umma tace wlh jiya nacinyesu, Abba yace to bara namaki transfer. Anwar yace yauwa Abba dama Baban Nabila yabani sako infada maku...... Anan yafada masu abinda yafada mashi.
Abba yace bakomai ai komai yawuce, dama banyi niyar fadama yaran nan abinda yafaru ba, sede idan itace tafada masu, amma nayi niyar dama in fada maku koda sun dawo kada wanda yafada masu abinda yafaru, duk wanda ya tamabayi ba'asi kuma kuce ya tambayeni.
Umma tace hakan ma yayi dede, kaga duk wanda ya tsananta bincike shize tonoma kanshi. Abba yace itama Ilham ai karshen watan nan zasu gama, damma sun sami jinkiri awajen jarabawarsu ai da tun cikin July zasu gama.
Umma tace kai amma naji dadi wlh, dama zaman kadaicin ya isheni, kaga idan tadawo ma dakina zata sauka. Abba yace idan ma zaki saba gara kisaba domin itama karatu zata tafi, idan kuma tasamu miji aure zatayi. Sede idan kishiya kikeso akawo maki ita kadaice zaku zauna tare?
Dariya Anwar yayi yace kaji Abba da son wasa, ai kaida aure sede kayima wasu. Umma tace ka barshi yakawota, ai bana tsoro, Abba yace kede fadi gaskiya, lokacin danayi maganar meyasa bakice komai ba? Seda fa numfashinki yadan dauke na yan mintuna sannan yadawo. Dariya suka sa gaba daya.
MONDAY
22ND AUGUST, 2016.
Brr, Yusuf ne da Umar a office suke hada takardun da zasu tafi dasu dan yau sakko sukayi. Turo kofar akayi tare da sallama, amsawa sukayi Sageer ne yashigo, bayan sun gaisa Brr, Yusuf yace Sageer kataya abokinka murna yau zefara shiga kotu domin gabatar da wata shari'a. Kuma yasamu lasisin fara aiki.
Murmushi Sageer yayi yace amma na tayaka murna Umar, Allah yasanya alkhairi. Umar yace amin nagode. Bayan yagama saka takardun cikin jaka ya mikama Sageer yace ansa karikemun kaima kadan samu wani abu.
Idan munje seka kara tsayawa domin ka koyi yanda akeyi, kaga wannan karon seka zauna a mazaunina kada ka koma baya kamar wani dan kallo. Kodayake ba laifinka bane, haka yawancin dakikan lauyoyi sukeyi.Amsar jakar Sageer yayi yana murmushi yace to nagode.
Fita yayi ya kai mashi jakar mota yadawo wajen Bala, bayan sun fito Umar yace muje narage maka hanya amotata dama baka taba danawa ba. Sageer yace kuje kawai akwai wanda nake jira zantaho.
Bayan suntafi Bala yayi murmushi yace dole inkulle office din nan kodan inje inga yanda za'a kare. Dariya Sageer yayi yace Baba nasan daga yau nagama zuwa office din nan, dama kuma haka nakeso.
Nafiso nayi shari'ata hankali kwance, kasan kuwa inde nayi nasara ayau dole yallabai ya koreni, nasan zece ban fada mashi nasamu lasisi ba. Bala yace dan Allah kada kadamu da wannan, ni nasan dan ya koreka bazaka rasa madafa ba. Allah de yabaka sa'ar wannan case din da dayan.
Mutane dayawa sun halarci cikin kotun, kowa yana jiran alkali, Salim da Jafar suna zaune guri guda, gaba daya hankalin Salim atashe yake, Jafar se lallashinshi yakeyi. Umar ne yaje kusa dashi.
Dafashi yayi yana fadin, haba Salim, kaifa namiji ne, bekamata ace duk wanda ya kalleka yagane akwai tashin hankali a fuskar ka ba. Idan baka natsu ba idan kafito gaban kotu domin amsa tambayoyi dole ayi saurin kadamu. Jinjina kai Salim yayi yace shikenan zan dake.
Shigowar alkali ce tasa kowa ya nutsu, bayan yazauna kotu tayi shiru, magatakarda yatashi yakaranto karar da za'a gabatar.
Ayau litinin 22 ga watan agusta shekara da 2016. Kotu zata saurari karar da mal. Nazifi yakawo ta Salim Me Wada akan yayima diyarshi Zubaida fyade aranar 18 ga wannan watan.
Mika ma alkali takardar yayi ya koma yazauna, alkali yace ina lauyoyi masu gabatar da wannan shari'ar? Tashi Umar yayi ya gyara rigarshi da glass din idonshi.
Ni sunana Brr, Umar Farouk lawyer mezaman kanshi kuma nayi karatuna awaje, sannan nazagaya kasa she kamar.... Alkali yace barrister ka takaita maganarka. Taboshi Brr, Yusuf yayi, hakan yasa yace ina neman afuwa yame shari'a.
Nine wanda zan kare wanda ake kara, Nagode. Alkali yace ina lawyer masu kara? Tashi Sageer yayi tare da addu'a yafito gaban kotu. Cike da mamaki Umar da Brr, Yusuf suka bishi da kallo, sosai sukayi mamakin hakan.
Ni sunana Brr, Sageer Alee Dan Masani, lawyer me zaman kanshi, nine zan kare wandan da suka kawo kara. Komawa yayi yazauna. Alkali yace lawyer daze fara bismillah.
Saurin tashi Umar yayi yace yame girma me shari'a, zanso kotu tabani dama domin inyima Zubaida wasu yan tambayoyi. Alkali yace kotu tana son ganin Zubaida.
Kozaki iya fadama kotu sunanki? Sunana Zubaida Nazifi.
Zubaida samarinki nawa? Ni saurayina daya ne, kuma shima agidan mu asan dashi, shinema zan aura.
To amma a ina kikasan Salim? Kallon inda Salim yake tayi, dukar da kanta kasa tayi hawaye suna zuba daga idonta. Muna jinki malama Zubaida?
Ni ban sanshi ba shine de yake bibiyata. Kamar ya kenan? Taya za'ayi kice yana sonki amma kuma kice ke baki sanshi ba? E ai shine yake sona ni kuma bana sonshi shine yasa yaranshi suka kamoni.
Shin zaki iya fadama kotu a inda kuka hadu da Salim? Gaskiya ni bansan inda muka haduba, kawai de rannan nazo shiga gida naganshi yafito daga mota, shine yace inzo.
Bayan naje yake fadamun wai yana sona, shine nace masa yayi hakuri anyi mani miji, amma seyace shi babu ruwanshi tunda ba aure aka daura mana ba, ganin yadameni yasa nashige gida nabarshi.
Tun daga lokacin yake bibiyata, shine wata rana da yamma wanda zan aura yazo narakashi bayan nadawo kawai wasu sukazo amota suka daukeni, shine suka kaini wani gida shine shine.... Kuka tasa.
Murmushi Umar yayi yace kema kin kasa karasawa ko?. Yame girma meshari'a, Salim yakasance beda lafiya tunda aka haifeshi yasamu matsala a mazankutarshi, hakan yasa kwata kwata baya kula yan mata.
Domin yasan koya kulasu baze iya aure ba, shiyasa ya maida hankali wajen karatunshi. Wannan itace takardar shedarshi wadda nasamu awajen likitan dayake dubashi.
Karbar takardar magatakarda yayi ya mikama alkali. Umar yacigaba idan kotu zata bani dama inaso inyima mahaifiyar Salim tambaya. Kotu tabaka dama.
Komawa Zubaida tayi tana kuka, mamanta ta riketa tana lallashinta. Hajiya kozaki iya fadama kotu menene asalin matsalar Salim? Kallon alkali tayi tace lokacin yana dan shekara 7 mukayi hadari tun daga lokacin yasamu nakasa mun kaishi manyan asibitoci harda nakasar waje amma sun gagara bashi maganin daze warke.
Daga karshe se suka ce sede muyi hakuri haka Allah yaso dashi, haka yatashi ma sam beda sha'awar maganar mace, idan kaganshi da mace to yar uwarshi ce, har abokinshi nake tambaya wanda sukayi karatu tare ko Salim yana da budurwa.
Shine yake fadamun baya kula kowa, haka yataso kuma haryanzu bashida wata wadda suke tare. Umar yace Haj. Zaki iya tafiya. Murmushi Brr, Yusuf yayi jin bayanin da Haj, tayi sak irin wanda ya rubuta mata yaba Umar ya kai mata ne.
Har yanzu de zanso kotu tabani dama inyima Jafar wanda yakasance aminin Salim tambaya. Kotu tabaka dama. Jafar zamuso muji shekararka nawa da Salim?
A gaskiya mun kai shekara 20 muna tare, beda wani aboki daya wuce ni, duk inda kaganshi zaka ganni bacci ne kawai yake rabamu, hatta da gurin aikinmu daya ne, mutane dayawa suna son Salim sede sanin baze iya aure ba yasa baya basu dama.
Shiyasa nayi mamaki da akace wai Salim yayima wata fyade aranar alhamis, wanda ko aranar ma da safe seda mukaje likita yakara aunashi ya tabbatar mana haryanzu maganar daya ce, sede yabashi wasu magunguna yayi mafani dasu.
Hannu yasa a aljihu yaciro wata bakar leda ya mikama Umar yace wannan sune magungunan da likita yabashi, katin ma yana ciki. Amsa yayi yabada aka mikama alkali.Jinjina kai alkali yayi daya gama karanta katin da magungunan.
Umar yace tambayata ta karshe zanyita ne akan saurayin Zubaida wato Waleed, zanso kotu tabani dama. Kotu tabaka dama.
Duk abinda ake Sageer yakasa kunne yana sauraransu, idan kuma abun rubutawa ne yana rubutawa, ahaka yakara samun duk abinda yakeso.
Kotu zataso taji sunanka da kuma dangantakar datake tsakaninka da Zubaida? Ni sunana Waleed Sulaiman, kuma nine wanda ze auri Zubaida.
Aranar da kuka fita kaida ita, tace kazo wajenta ne taraka ka, dama haka kuka saba idan kazo wajenta seta raka ka, duk da gidansu abikin titi yake? Waleed yace a'a kawai de ranar ne nace zanje can kasan layinsu wajen wani abokina, shine tace zata rakani.
Ni kuma nace a'a, shine tace ai ba wajenshi zata rakani ba kawai da munyi rabi zata dawo, shine muka tafi. Murmushi Umar yayi yace haba malam Waleed, taya kake tunanin zaka iya rainama kotu hankali.
Dakin abokinka fa kace zakaje, ita kuma tace zata raka ka, bayan ta raka ka shine kajata kuka shiga kukayi abinda kukeso bayan tadawo gida kuma tanemi ta rainama iyayenta wayo ko? Tashi Sageer yayi yace yameshari'a yakamata Brr, Umar ya gyara maganarshi, domin yana kokarin saka ma Waleed magana abaki.
Brr, Umar ka gyara kalamanka. To yame shari'a. Inajinka mal. Waleed meyasa tunda kuke tare baka taba cewa taraka ka wani waje ba se aranar? To ai banine nace taraka ni ba, itace tace zataje, kuma ko kusa da gidan abokin nawa bamuje ba ta koma gida.
Shikenan zaka iya tafiya. Dafe kai Brr, Yusuf yayi sam Umar yamanta abinda yace ya tambayi Waleed. Kallon alkali Umar yayi yace yame girma me shari'a wadan nan sune hujjojin da muka samu ina fatan wannan kotu me adalci zata gamsu da cewar Salim bashine yayima Zubaida fyade.
Saboda sam beda lafiyar daze iya tarawa da wata diya mace bare har ya iya aikata fyade ba. kuma ina fatan kotu zatayi duba abisa maganar da Waleed yayi na tafiya dasu kayi shida Zubaida domin tarakashi wajen abokinshi. Nagode yame shari'a.
Rubutu alkali yayi sannan yace lawyer me kare wadan da suke kara ko kanada ja akan wadannan hujjoji da Brr, Umar ya gabatar? Tashi Sageer yayi yace inadashi yame shari'a.
Zanso kotu takira mani Mahaifiyar Salim domin inyi mata tambayoyi. Mahifiyar Salim ta fito. Cike da fargaba tafito.
Hajiya acikin bayananki kince har kasashen waje kun kai Salim ko? E mun kaishi. Jinjina kai yayi yace na tabbata likitan daya dubashi yabaku sakamakon awon da sukayi mashi ko?
Shiru tayi tana yan kame kame, tashi Umar yayi yace yame girma me shari'a muna magana ne akan result da aka bama Salim na last awo da akayi mashi, kuma ai gashi nan sun kawo, amma Brr, Sageer yana kokarin maida magana akan abinda yafaru shekara da shekaru.
Korafi be karbuba Brr, Umar. Brr, Sageer cigaba da tambayarka. Sageer yace nagode yame shari'a. Kotu tana sauraronki Hajiya, ina takardar awon da akayi mashi?
E to gaskiya daya ke abun yadan dade bazan iya gano inda suke ba, kilama na barosu acan kasar da mukaje. Murmushi Sageer yayi yace idan na fahimceki kinmanta asalin indama suke?
E haka ne. Amma nasan zaki iya bani wanda aka mashi na wata 3 da suka wuce tunda kunce yana zuwa awo ko? E e haka ne, sede ba nice nake ajesu ba, Dad dinshi ne kuma baya kasar.
Shikenan Hajiya zaki iya tafiya amma kafin kitafi inaso kibani dama domin inkira nawa likitan yakara duba maki danki kila adace ta dalilinshi? Tashi Umar yazoyi Brr, Yusuf yayi saurin rikoshi.
Zufa ce tafara zuboma Hajiya, Sageer yace kin bani dama ? Daga mashi kai tayi yace nagode zaki iya tafiya. Zanso kotu tabani dama domin nayima likitan daya auna Salim wasu yan tambayoyi. Kotu tabaka.
Likita zanso kafada ma kotu shekara nawa kayi kana duba Salim tunda sunce kai ne likitanshi? Zan kai tsawon shekaru 10. Shin ko zaka iya bamu file dinshi wanda yake awajenka?
Shiru likita yayi yana zare ido, sam basuyi tunanin za'a tambayi file ba, shiyasa kawai suka hada takardar karya. Kotu tana sauraronka likita?
E to gaskiya dayake anyi mani gyara na hargitse office din idan nace zan dubo file din zansha wahala. Murmushi Sageer yayi yace shikenan babu matsala. Amma Jafar yace aranar alhamis da safe sunje wajenka kayima Salim awo?
Likita yace e gaskiya ne gama result din nan nakawo. Jinjina kai Sageer yayi yace amma aranar alhamis baka fito daga gidanka ba se karfe 1, ya akayi kamashi awo da safe? Domin na tabbatar da hakan ne bayan binciken danayi agidanka da kuma wajen aikinka?
Kame kame yafara yi, can kuma yace e mantawa sukayi wajen karfe 2 ne sukazo office dina nayi mashi awon. Sageer yace da kyau, zaka iya tafiya. Zanso kotu tabani dama domin inyima Salim wasu tambayoyi. Kotu tabaka.
Salim kace ba kasan Zubaida ba ko? Kwarai ma kuwa bansanta ba, asalima ban taba ganinta ba. Sageer yace da kyau, amma kasan wannan? Wani matashi ne inspector Salis yashigo dashi.
Salim yace gaskiya ni bansanshi ba. Sageer yace ma yaron yamatso, kallonshi yayi yace ya sunanka? Karkace baki yayi yace sunana Kaura. Shin kasan wannan? Niban sanshi ba, ko awajen yan sanda nafada masu basanshi ba amma sun dage akan nasanshi.
Sageer yace shikenan zaka iya tafiya, kallon Salim yayi yace duk da ance kaje wajen likitoci dayawa, kuma sunyi maka awo, haryanzu baka samu sauki ba, shin zaka iya bamu dama muyi maka namu awon?
Zaro ido Salima yayi yace to dan me? Duka yau kwana 4 danayi awo kuma ai gashinan ankawo maku, amma kuma yanzu se ace za'a sake mani wani. Sageer yace haba Salim, kwantar da hankalinka.
Bafa naman jikinka za'a yanka ba, bare kace kai ka gaji, kawai awo za'ayi maka, kasani ma ko adace agano kawarke? A'a wlh ni ban warke ba, saboda magungunan da likita yabani ma ban fara shan ko daya ba taya za'a ce na warke daga alhamis zuwa yau.
Sageer yace amma acikin magungunan da aka kawo anduba aciki babu na kwana 4, kaga kenan alamu sun nuna kayi amfani dasu. Kara kallon magungunan alkali yayi yaga babu na kwana 4. Jinjina kai yayi yacigaba da sauraron Sageer cike da birgewa.
Shikam Sageer tun,lokacin da aka mikama alkali magungunan lokacin yana dubawa ya hango an balli guda 4. Hakan yasa yayi saurin rubutawa.
Salim yace e mantawa nayi amma gaskiya ban wani,warke ba. Juyawa Sageer yayi yace yame girma me shari'a zanso kotu tabani dama domin likita yasake auna Salim, kuma munaso agaban kotu yazo da sakamakon anunama kowa.
Tashi Umar yayi yace agaskiya bamu yarda da wannan maganar ba, domin likitanka zaka kawo babu wanda yasan ko nawa kabashi ze iya yimaka result na karya dan haka bamu yarda ba, sede kotu takawo nata likitan. Rufe fuska Brr, Yusuf yayi, da alama wannan karon ma Umar yakara kwafsawa.π€£.
Hayaniya ce tadan fara tashi acikin kotun, bubbuga tebur alkali yayi yace ya isa, kotu ta gamsu da korafin Brr, Umar, dan haka zankira likitan daze auna Salim bayan yagama kuma likitan Brr, Umar dana Brr, Sageer dama karin wani likitan duk zasu aunashi, kuma kowa ze kawo,mana sakamakon daya samu.
Kotu ta tafi hutu na awa daya da rabi, kuma kotu tana bukatar yan sanda su taho da Salim da sauran likitocin domin awo. Buga tebur yayi akace kotttt.
Da gudu Abdul yazo ya rungume Sageer yana dariya, yana fadin gaskiya abokina kayi matukar kokari, ka ganka kamar wani babban lawyer. Zo muje insiyamaka abu me sanyi ka jika makoshinka kafin adawo.
Juyawa yayi ya kalli kujerar su Umar,murmushi yasakar mashi ganin yanda duk yajike da zufa kamar wanda yafada ruwa, kallon Brr, Yusuf yayi wanda yake magana dawasu abokanshi.
Takawa yayi yaje wajen Umar, dafa kafadarshi yayi yana fadin kwararran lawyer da kanshi yake zufa? Yanzufa wasan yafara, Yau ne shari'ar ka tafarko amma har kanka yafara caji? Kanemi ruwa me sanyi kasha kada makoshinka ya tsage. Inafatan yanzu kafara ganin irin aikin dakikin lawyer wanda yayi karatu a nigeria? Yakamata ka koma turai kafadamasu nan gaba idan zasu sallami dalibansu surika koyamasu yanda ake fara magana akotu.Semun dawo.
Wuceshi Yayi yana murmushi yakama hannun Abdul suka fita. Cike da bakin ciki da tsana Umar yabishi da kallo, yanzu shikenan idan beyi nasara ba seya maida kudin da ya karba? Wannan itace tambayar daya juyo ya fara mani.
π€·π»♀π€·π»♀Nima nace bansani ba, sekajira kaga idan bakayi nasara ba. Kuma ai Dakikin lawyer ai shine yake maida kudi.π€ππ€£.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
Waiting for your comments. Luv u allππππ

Season 85 π€ 90
WANNAN SHAFIN NAKI NE KAWATA ZARAH B_B. ALLAH YABAR ZUMUNCIπ
Kowa yasamu waje ya zauna saboda lokacin da alkali ya bayar yacika. Kotun takara cika hatta da wadanda bandasu aka fara yanzu sunzo, kowa yanaso yaga yanda shari'ar zata kasance.
Alkali ne yashigo, bayan ya zauna sega yan sanda da Salim tare da likitoci guda 4 da suka aunashi kowa da takardarshi a hannu. Da kaga Salim da likitanshi zaka ga tashin hankali kwance akan fuskarsu.
Alkali ne yace Brr, Sageer mundawo, zaka iya kiran kowane likita domin yafada mana sakamakon daya samu. Tashi Sageer yayi yakira likitan da alkali ya kawo domin yafara.
Yana zuwa yafara bayani, a sakamakon binciken da nayima Salim, babu abinda yake damunshi, lafiyarshi kalau kuma bema taba haduwa da wannan lalurar ba, koyanzu ya kwanta da mace idan da rabo zata iya daukar ciki.
Runtse ido Mom din Salim tayi hawaye suka fara zubo mata, gaba daya kotun ta hargitse da hayaniya, Salim kuwa kamar ya ruga haka yakeji. Bubbuga tebur alkali yayi hakan yasa kowa ya nutsu.
Dayan likitan ne yazo shima amsar daya ce, likitan su Sageer ne yazo, shima amsar daya ce. Likitan karshe shine likitan Salim. Kowa ido yazuba mashi domin yaji abinda zece.
Gaba daya zufa ta rufeshi, babban tashin hankalinshi kada ta sanadiyar wannan shari'ar yarasa aikinshi. Gashi de yasan abinda kowa ya gano shima haka ya gano, amma yana jin kunya ace ya canza magana.
Kai muke saurare kana bata mana lokaci, Sageer ne ya katseshi. Dago kai yayi yace hakika magungunan dana bashi masu karfi ne, gashi acikin kwana 4, Allah me iko yabashi lafiyar da iyayenshi suka fidda rai da ita.
Gaba daya kotun ta kara daukar hayaniya, alkali kanshi seda yayi murmushi jin rashin kunya irin ta likita. Bubbuga tebur yayi kowa yayi shiru. Brr, Yusuf saura kadan dariya ta kwace mashi hakan yasa yayi saurin tashi ya fita.
Murmushi Sageer yayi yace gaskiya ne babban likita, shiyasa ai nace gara akara yimashi awo kila yasamu lafiya, gashi kuma an dace. Amma likita kana tunanin acikin kwana 3 yasamu sauki kenan?
Likita ce kwarai ma kuwa, samun saukinshi ze iya farawa daga ranar juma'a. Jinjina kai Sageer yayi yace lallai Allah shine abin godiya. Zaka iya tafiya. Tambayata ta karshe zanyita ne akan Zubaida.
Zanso kotu tabani dama. Kotu tabaka dama Brr, Sageer. Malama Zubaida, kamar yanda kikace Salim ne yayi maki fyade, shin da wane lokaci ne abin yafaru? Da yamma ne.
Kinga fuskarshi ko baki gani ba? Naganta domin seda mukayi magana dashi kafin faruwar hakan, kuma wannan yaron da dan sanda yashigo dashi dazu yana daya daga cikin wadan da suka kamo ni.
Sageer yace shin ko kina da wata kwakkwarar sheda dazata iya nunama kotu cewar Salim shine yayi maki fyade? Ina da shedu guda biyu, duk da nasan dayar shedar kotu bata amfani da ita, ta farko Allah shine shedata.
Ta biyu kuma inaso Salim ya bude wuyanshi, idan har ba'a ga sahun yakushi ajiki ba, ni nayarda bashine yayi mani wannan fyaden ba, domin na tabbata lokacin muna kokowa dashi naji mashi ciwo da yatsuna har seda jini yafito.
Ai Salim kamar wanda aka zabura saurin shafa wuyanshi yayi, yana jin alamun ciwon da yasan tabbas itace taji mashi,haka ya zunduma da gudu ya nufi kofar fita. Da sauri yan sanda suka rikoshi.
Duk yanda mutane basu so suyi dariya a wannan karon seda suka dara, shikan shi alkali seda yasaki wani murmushi, Brr, Umar kanshi seda abin yabashi dariya, sede fargabar dayake ciki itace ta hanashi darawa.
Gaba daya kotun hayaniya tayi yawa, bubbuga tebur alkali yayi hakan yasa kowa ya nutsu. A cikin akwatin da ake tsayawa aka saka Salim, kasa yayi da kanshi hawayene kawai suke fita daga idonshi.
Hakika tunda yake arayuwarshi beta ba jin kunya irin ta yau ba, haka zalika duk abubuwan dayake aikatawa betaba dana sani ba se yau, duk da ba wannan karon bane yafara aikata zina, koda yayi karatunshi awaje yana aikatawa.
Haka daya dawo gidama yanayi shida yan matanshi. Sede tunda yake betaba aikata fyade ba se akan Zubaida, itama tun lokacin daya ganta sonta yashigar mashi zuciya, duk yanda yaso ta kulashi taki bashi hadin kai.
Hakan yasa abokinshi Jafar yabashi wannan shawarar shiyasa ya aikata hakan akanta. Alkali ne yace malam Salim kotu zatso taga wuyanka domin a tabbatar da abinda Zubaida tace.
Dago kai yayi, hannu yasa ya goge idonshi yace a'a ya isa haka, tabbas nasan akwai tabon yatsun Zubaida a wuya na, kuma hakika nine nayi mata fyade abisa temakon bin shawarar abokina Jafar.
Domin shine yayi mani hudubar aikata hakan, kuma wannan shine karona na farko dana taba yima wata yarinya fyade arayuwata. Bazan boyema kotu komai ba, ina harkar neman mata. Amma wlh bantaba yima wata fyade ba se Zubaida.
Hakika nayi nadamar aikata wadan nan munanan aiyukan arayuwata, kuma nagode ma Allah da wannan abun yafaru dani, ni nasan insha Allah shine silar shiryuwata.
Ina rokon wannan kotu me albarka data sassauta mani hukuncin dazata yi mani..... kuka yasa me tsuma zuciya, gaba daya kotun shiru tayi, mutane da yawa seda sukaji tausayinshi. Mom dinshi kam kuka hada majina.
Yan sanda ne suka shigo da sauran yaran da Salim yasa suka dauko Zubaida. Bayan alkali yagama rubutunshi. Sageer yace yame girma me shari'a anan nakawo karshen tambayoyin da zanyima Kowa.
Ina fatan wannan kotu me alfarma zatayi duba da wadannan shedu dana gabatar domin ta yanke ma Salim hukuncin daya dace. Nagode.
Dago kai alkali yayi, sosai Sageer ya burgeshi, duk da wannan ce shari'ar shi ta farko, amma babu wanda ze iya gane hakan se wanda yasani. Yanayin yanda yake tafiyar da aikinshi tamkar wani kwararran lawyer.
Gyara glass din idonshi yayi yace, abisa kwararan shedun da aka gabatar, da kuma amsa laifin da wanda ake kara yayi. Abisa tsarin doka ta kasa, laifi akan fyade, Kotu tayanke ma Salim Me Wada hukuncin daurin shekara daya agidan yari.
Sannan ze biya tarar million daya da zebama Zubaida. Sannan idan har ciki yashiga jikinta shine yakeda alhakin ciyar da ita harta yaye abinda zata haifa, kuma idan tanaso zata iya maida mashi danshi ko yarshi.
Yaranshi kuma kotu tayanke masu hukuncin daurin wata 3 agidan yari tare da abokinshi Jafar, domin hakan yazama jan kunne ga yan baya.
Bisa goyon baya da likita yabada wajen aikata zalinci ya samar da takardar karya, kotu ta dakatar dashi akan aikinshi har na tsawon wata 5. Haka zalika Brr, Umar wanda ya gabatar da shedun karya ga kotu, shima kotu ta dakatar dashi na tsawon wata 5. Kottttt!!!!
Gaba daya kotun tacika da hayaniya, kowa yana taya Sageer murnar nasarar daya samu, Abdul kuwa baki yaki rufuwa, lokacin daya kai dubanshi a kujerar Brr, Yusuf beganshi ba, tuni ya sulale.
Haka Umar ya tattara kayanshi yafita be tsaya kallon kowa ba. Iyayen Zubaida ne suka karaso wajen Sageer, godiya sukayi mashi. Sageer yace bakomai Baba,yima kai ne.
Hannu Waleed yamika ma Sageer yana murmushi yace nagode yallabai, Allah ya biyaka kamar yanda kayi mana. Sageer yace bakomai abokina kaine zan bama hakuri abisa abinda akayi maka.
Waleed yace ai yayima kanshi, koda ace Zubaida tasamu ciki zan iya hakuri harta yaye abinda ta haifa adaura mana aure, domin babu abinda yaragu na son dana ke mata. Idan kuma bata samu ciki ba, ina me tabbatar maka bikinmu yana nan.
Murmushi Sageer yayi yace lallai kacika dan halak, Allah yabiyaka kaima da abinda kayi, musayar number sukayi suka masu sallama suka nufi office din alkali.
Murmushi yayi alokacin da yaga Sageer, Bala yace yallabai sannu da aiki. Alkali yace yauwa malan Bala, ai Sageer shine za'a yima sannu. A gaskiya Sageer ka burgeni. Bantaba ganin lawyern daya burgeni ba kamar ka.
Kayi matukar kokari, kuma irinku al'umma suke so da gwamnati,ina maka fatan alkhairi a shari'ar da zaka gabatar ta gaba. Sageer yace nagode yallabai, kuma zamuje musamu mahaifin Mannir domin yashigar da kara.
Alkali yace babu damuwa, zanyi kokarin sama ku ranar dazan gabatar da shari'ar nan kusa domin nakusa tafiya hutu, amma sena gama da shari' arku. Godiya sukayi mashi suka tafi.
A office Umar yasamu Brr, Yusuf domin tun yana hanya yayi mashi waya akan yasame shi can, zaune yasamesu su 3, da likita da D.P.O, haka yashiga jikinshi duk a sanyaye.
Kamashi Brr, Yusuf yayi ya zaunar dashi yana fadin kayi hakuri Umar, ai kayi kokari sosai, dama kuma haka shari'a ta gada, kode kafadi ko kuma kayi nasara, kuma dama gaba daya duniyar haka ta gada.
Babban abinda ya bani haushi ba faduwarka bace tabani haushi, Sageer shine mutumin daya bani haushi, kuma daga yau mun daura damarar yaki dashi, har ni ze munafunta. Ko dayake dama haka dan Adam yake, shiyasa tunda na daukeshi aiki naji zuciyata bata sonshi.
Allah de besa zan koreshi da wuri ba kamar yanda nakeyima duk,mutumin da zuciyata batayi na'am dashi ba. Hakika yazama makiyina, domin banida makiyi kamar wanda zeso yaruguza nasarata.
D.P.O yace kadena bata ranka haka nan, damu yake zan can, wlh tunda yashigo gonarmu baze fita tasauki ba, ai mune gidan sharri, wanda beyi mana ba muna dora mashi bare kuma shi daya kawo kanshi.
Dr, kayi hakuri wannan banzan yaron yasa karasa aikinka, kuma yabata maka suna, amma kada kadamu muna tare da kai. Likita yace dole indamu saboda yasani jin kunyar jama'a, iyalina dawane ido zan kallesu?
Idan nakoma aikina shikenan banida wata power a asibitin, duk wanda yaganni yaga marar gaskiya. Nikam nayi nadamar aikata wannan abubuwan danayi, hakika nayi dana sanin haduwata daku.
Daga mashi hannu Brr, Yusuf yayi yace dakata dan Allah, ya muna cikin damuwa zaka kara mana taka? Lokacin da aka kawo maka aikin meyahana bakace bazakayi ba? Wato saboda alokacin kaga kudi shiyasa kanka be caza maka wata rana hakan zata faru ba ko?
To inaso kasani, duk wanda yake da hankali idan har yana aikata abu marar kyau dole akansan ranshi seya aje irin wannan ranar zata iya zomashi, sede idan mutum,yana da dabara ze iya samun riga kafin abun.
Bakaji dramar da za'ayi da shedan ranar gobe kiyama ba? Kodayake babu mamaki bakayi zurfi acikin addininka ba, domin aturai ka kararar da lokacinka. To idan baka sani ba bara nafada maka, idan kuma ka manta zan tuna maka.
Ka koma cikin suratul Ibrahim ayata 21 zakaji abinda ayar take magana akan shedan da jama'arshi. Alokacin suna tuhumarshi da laifin daya sasu suka aikata aduniya.
Kasan meyace dasu aranar? Cewa yayi kada su zargeshi su zargi kawunansu, domin shi baze iya kubutar dasu ba, kamar yanda suma bazasu iya kubutar dashi ba.
To haka duniyar ta gada, kayi kokarin samun,mafita akowane abu da kake aikatawa. Nafada maka haka ne domin ka gane niba Dakikin lawyer bane kamar yanda kake tunani.
Dan haka ka kula da kanka, kada kayi tunanin zaka iya takani yanda kakeso saboda kawai kayi mani aiki, idan kuma ka isa kaje kasamu alkali ko,jama'a ka sheda masu irin abubuwan damuke aikatawa da kai.
Tashi likita yayi yadafa shi yace dan Allah kayi hakuri, wlh rai nane yabaci, nima nasan kunyi mani rana, kayi hakuri abokina komai yawuce. D.P.O yace shikenan komai yawuce Allah ya tsare gaba. Kai kuma Umar ka kwantar da hankalinka kana tare da yallabai komai ze wuce.Tashi sukayi suka fita
Zaune su Sageer, Salis, Abdul da Bukar suke agaban mahaifin Mannir. Jinjina kai yayi alokacin daya gama jin bayaninsu, kallonsu yayi yace yallabai banki taku ba.
Amma yanda Mannir yabar duniyar nan muka hakura inaso abar maganar nan, domin mutanan nan sunfimu karfi fiye da yanda baku zato, saboda haka banaso a tono abinda yawuce saboda mahaifiyar yaron nan tafara samun sauki akan rashin Mannir.
Banaso akara dawo mata da abinda kuka san bazakuyi nasara akanshi ba. Kuma inde nine ubanshi na hakura da wannan shari'a nabarma Allah, domin WATA SHARI'AR SE A LAHIRA.
Tashi yayi yana fadin nagode da kulawarku amma dan Allah kada ku kara zuwa wajena da wannan maganar dan Allah. Tashi Salis yayi yace Baba dan girman Allah kazauna mu nuna maka shedun da muke dasu, idan har baka gamsu dasu ba ina me tabbatar maka wlh munbar wannan maganar har abada.
Zama yayi yace ina sauraronku. Wayar Bukar Salis ya amsa ya kunnomashi vedion da ya dauka, bayan yagama gani Salis yace Baba bayan wannan shedar muna da sarkar yaron daya kashe maka danka, wanda shine yabama wani Kamal aranar da aka kaishi yari.
Bayan wannan muna da wasu shedu dayawa wanda ina me tabbatar maka da izinin Allah zamuyi nasara, domin bamuzo wajen nan ba seda muka nemo izini daga wajen alkalin daya yanke wannan hukuncin.
Yanzu haka hutu ze tafi amma saboda munje mashi da wannan maganar yace shima tunda ya yanke hukuncin beda nutsuwa, zeso yakara bin case din ko Allah zesa agano gaskiya shima yasamu nutsuwa.
Ka dubi girman Allah Baba kada kace bazaka amince da muba. Shiru Baba yayi yana nazarin maganarsu, muryar matarshi sukaji tana fadin, hakika yanzu nasan Allah ya amshi addu'ata.
A kullum,banida wani lokaci sena rokon Allah yatabbatar da gaskiya kafin nakoma gareshi, hakika zuwanku ya tabbatar mani da cewar Allah ya karbi rokona. Ina me goyon bayanku dari bisa dari. Kuma zan cigaba da tayaku addu'a akan Allah yabaku sa'a.
Jinjina kai Baba yayi yace shikenan, nayarda daku inamaku fatan nasara akan wannan case din. Allah yayi maku jagora akan wannan tafiya. Mungode da kulawarku.
Ajiyar zuciya Sageer yayi yace muma mungode Baba daka bamu damar samun wannan ladar da muke hange zamu samu. Takarda Salis yabama Baba yace gashi zaka rubuta kana karar shugaban gidan yari akan mutuwar danka domin,baka yarda kwaya ce ta kashe shi ba, domin yaronka baya shaye shaye.
Kaga idan aka je kotun acan za'a tono komai. Baba yace shikenan nagode kuma zan aikata hakan, Salis yace mungode kuma zanzo in kaika can inda zaka kai takardar. Sallama sukayi masu suka tafi suna ta godiya.
Bukar yace Allah sarki, gaskiya na tausaya ma wadan nan bayin Allah, hakika sunga tashin hankali, se yanzu nake dana sanin rashin zuwa kotu na bada wannan shedar dana dauka. Salis yace bakomai Bukar, yanzu zatayi mana amfani,kila da ka kai alokacin bazatayi amfani sosai ba.
Bukar yace yauwa dama inaso in tambayeku, ya akayi ba'a yima Salim bulala 80 ba kafin a kaishi yari, tunda ai betaba aure ba? Sageer yace ai sa'ar dasukaci alkalin kotun musulunci yayi tafiya, dan can sukaso su kai karar.
Dama kuma ban bancin dayake tsakanin kotun musulunci da High court kenan. Domin a dokar kasa bata yarda a kashe wani ba, ko kuma adukeshi sede amashi daurin rai da rai agidan yari,ko kuma yayi shekaru idan ba laifin kisa yayi ba.
Sede idan mutum yana tsoron Allah seya kai kanshi kotun musulunci ayi mashi hukuncin da Allah yace. Bukar yace tab, Allah ya kyauta.
Salis yace yauwa Sageer ina fatan ka tattara duka shedun dasuke wajenka ka daukesu daga gidanka ko? Sageer yace ai tun ranar daka fada mani na hadasu na kaima Saddika ta aje mani, domin ita kadaice zan iya bama ajiya, tunda Abdul muna tare dashi.
Salis yace lallai ka iya bada ajiya, kasan babu wanda ya iya ajiya kamar masoyi. Abdul yace kaima kafadi haka, wannan soyayya ta Sageer da Saddika tana burgeni, yanzu haka badan yagaji ba kila anan zamu barshi.
Salis yace anan unguwar take ne? Abdul yace anan take kaga gidansu can. Dariya suka saka gaba daya Sageer yace wlh Abdul kai dan tonon asiri ne, Bukar yace yallabai komuje adan gaisa? Sageer yace wlh bayanzu ba, sede wani lokacin dan nagaji, idan kuma ka iya mafanar kurame to.
Salis yace Allah sarki kurma ce ashe? Abdul yace wlh kuwa, amma ahakan yana gane duk abinda tace. Bukar yace ai soyayya ba ruwanta da nakasa. Allah ya nuna mana lokaci musha biki. Abdul yace ai insha Allah damun gama wannan case din zamuje neman aurenta.
Salis yace Allah yasa. Haka suka isa bakin titi Sageer yace to Salis zamu wuce zanshigo domin musan yanda zamu fara takan Ammar. Salis yace badamuwa ai ga Abdul ma, tunda yafimu shiga gari nasan zefimu saurin samo mana wata hanya. Sallama sukayi masu suka tafi.
Tun daga ranar Sageer yabar aiki a office din Brr, Yusuf haka ya koma bin Abdul shagonshi domin kada yazauna shikadai agida. Acikin kwanakin da suke wucewa babu abinda Sageer yakeyi se hada duk wata seda daze gabatar a kotu.
A bangaren su Anwar da abokinshi dasu Nabila kuwa soyayyarsu kawai sukeyi hade da shirin biki, haryanzu su Nbila basu san abinda yafaru ba, saboda yanzu Umman Rayyana tadan saki jikinta agidan, duk da haryanzu tana yin dari dari dasu.
Har bataso ace su Anwar zasu shigo gaishe su. Sosai takejin kunyarsu, shi kam Anwar nunawa yake kamar babu abinda yafaru.
Aunty kuwa tunda ta koma gida haka takoma shiru shiru, dama mamanta tarasu kuma ita kadaice agurinta, hakan yasa ta bude dakinta tasa kayanta ta zauna aciki.
Babu irin tambayar da Babanta beyi mata ba amma bata fada mashi abinda yahadasu da mijinta ba. Har waya yakira Abba amma shima hakuri yabashi yace yabar maganar kawai auren ne yakare. Babanta yace nasan duk abinda yasa ka iya sakin Falmata har saki 3 bakaramin abu bane.
Domin ko yaji bata taba yiba. Nagode da irin kulawar da kabani, kuma ka rufama 'yata asiri, domin na tabbata itace keda laifi. Bakomai, insha Allah daga yau nima bazan kara tambayar kowa abinda yafaru ba. Domin Allah yahana tsananta bincike.
Tundaga lokaci yadena tambayarta, sede yace dole tafito tarika taya matan gidan aiki, bazata zauna subata taci ba. Haka take shiga kitchen tana tayasu aiki, cikin lokaci kadan harta rame.
Sosai takara nadamar abinda ta aikata, batada aikinyi se neman gafara agurin Allah da kuma rokonshi ya kawo mata wani mijin tayi aure tabar gidan haka nan.
Abdul ne yafito daga wani shagon aski, wayarshi ce tayi kara yana kokarin dauka yaji ya bige mutum, saurin dago kai yayi domin yaga wanda yabuge. Cike da mamaki ya kara kallonshi, bakowa bane se Ammar.
Duk da bawani saninshi yayi ba, amma baze iya manta fuskarshi ba lokacin da Sageer ya taba nuna mashi shi wata rana bayan angama case dinsu. Dukawa yayi yadauko mashi key din motarshi daya fadi, hannu yasa ze goge mashi kafarshi daya taka. Da sauri Ammar yadagoshi yana fadin haba abokina meye zakayi haka kuma?
Murmushi Abdul yayi yace dan Allah kayi hakuri wlh banganka ba har na bigeka. Kara kallonshi Ammar yayi domin,ya burgeshi gashi yana da kyau, shi kuma yanason mutum me kyau. Hannunshi yakama yana fadin karka damu bakomai.
Key din ya mikamashi, amsa Ammar yayi yana fadin aski kazo ne? Abdul yace wlh kuwa harma nagama zantafi. Ammar yace kash!! Gashi ni kuma yanzu nazo, kozaka jira ayi mani se mutafi tare idan ban takura maka ba? Murmushi Abdul yayi yace bakomai muje kawai.
Shiga ciki sukayi bayan sun zauna Ammar yace sunana Ammar, kaifa? Abdul. Murmushi Ammar yayi yace suna medadi. Abdul yace ai be kai naka ba. Ammar yace ai komai naka me kyau ne, kafin asamu namiji da dimple da wuya, amma kai gashi gaba daya kana dashi a kumatunka.
Abdul yace nagode, Ammar yace gaskiya ka burgeni, sam baka da zafin kai, kozaka iya zama abokina? Abdul yace zakayi abokan taka da talaka ko? Ammar yace banason haka, ni da kai duk ba mutane bane? Abdul yace haka ne, to nayarda.
Wayarshi yabashi yace yasa mashi number dinshi, bayan yasa yayi mashi flashing yayi saving. Me askin ne yace yallabai nagama kataho, mikama Abdul wayarshi yayi yace ajemun abokina.
Kawo inbude maka kayi kallon hotuna kafin agama mani, mika mashi yayi yatafi wajen aski. Haka Abdul yazauna yana ta kallon hotunan yan mata dana Ammar, sede yawanci na maza sunfi yawa kuma duk wanda ze gani haka zega sun rungume juna kamar yasamu mace.
Wayarshi yadauko yayima Sageer message akan yasamu Ammar yanzu haka suna tre, idan yazo zeji komai. Sosai Sageer yaji dadin labarin da Abdul yafada mashi.
Bayan angama ma Ammar aski suka fito, Ammar yace amashin kazo ne? Abdul yace a adedeta nazo, Ammar yace to muje in ajeka ko? Abdul yace badamuwa muje nagode.
Bukar ne zaune a office dinsu shida yansanda suna zaune a kanta suna cin gyada suna fira. Wani Sajan Shehu ne yace wai ni Bukar waye yayi nasara a shari'ar dakace zakaje kallo?
Dariya Bukar yayi yace kai ai kallo yabarku baya, naso ace kunje domin shari'ar da akayi tabama kowa dariya musamman lokacin da wanda ake kara yaruga da dugu. Dariya sukasa Shehu yace bamu labari mana.
Labarin yanda akayi yafada masu, sosai suke dariya har da faduwa kasa. Har D.P.O yashigo basu sani ba. Bukar ne yafara ganinshi hakan yasa yayi saurin tashi, sauran ma duk tashi sukayi tare da kamewa suka sara mashi.
Kallonsu yayi yace kalleku, kamar ba yansanda ba zakurika irin wannan dariyar. Kai kuma dama gulmace ta kaika kotun da zakazo kana basu labari.
Tsaki yaja yawuce yana fadin kazo ni zan aikeka. Tabe baki Bukar yayi yace to semu kiyin dariya. Juyawa yayi zetafi Shehu yace yauwa Bukar bani wayarka intura film. Cire pass word din yayi ya mika mashi yana fadin idan kanada wani sabo nima katuramun.
Bayan yatafi Shehu yashiga vedios domin tura film, ya tura na farko ze tura nabiyu ya danna vedion da Bukar yayima D.P.O be sani ba, bayan yagama shiga yacigaba da turawa, bayan yagama yabude na wayarshi domin yaga nawa ya tura.
Harze goge wanda yatura daya ga ba film bane se kuma yace bara ya bude yagani, sosai yayi mamakin abinda yagani, saurin kashewa yayi yana kallon abokanshi. Wani yace kai kuma lafiyarka kamar wani marar gaskiya?
Tashi yayi yana fadin lafiyata kalau, fitsari nakeji ne ga wayar Bukar nan idan yafito kubashi, wani yace yauwa nima bani intura film, Shehu yace ai tashiga key sede idan yazo.
Fita Shehu yayi yasamu wani guri yazauna ya gama kallon abinda yafara gani,sosai yayi mamaki ahankali yace dama yallabai shine wanda yabama Mannir kwaya? Lallai Bukar munafikine, yallabai ya yarda dashi amma yana munfuntarshi.
Murmushi yayi yace da kyau, Bukar kayi kokari. Dariya yayi ya girgiza kai yakoma ciki.

0 comments:
Post a Comment