Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 90 🖤 95
THIS PAGE IS DEDICATED TO YOU AUNTY NICE💋💋.
Sosai Sageer yaji dadin labarin da Abdul yabashi, kallonshi Abdul yayi yace amma Sageer nikam inama Ammar kallon kamar yana cikin mazan da suke son jinsinsu. Sageer yace meka gani da kace haka?
Abdul yace kawai irin hotunan dana gani acikin wayarshi ne naji banyarda dasu ba. Sannan irin kallon dayake mani da yanda yake nuna kulawarshi akaina ne abun yamun yawa, daga haduwar farko? Harfa cewa yake wai inada kyau wai dimples dina suna burgeshi.
Dariya Sageer yayi yace lallai abokina kayi kasuwa, wato farin jinin naka yatashi daga masu talla ya koma kansu Ammar. Duka Abdul ya kai mashi yana fadin kai dan iska ne wlh, ina fada maka damuwata shine ka maida abun wasa.
Wayarshi ce tayi kara, Sageer ne ya duba, murmushi yayi yace dan halak, ga babynka yakiraka. Fisge wayar Abdul yayi yana hararrashi, Sageer yace dan Allah sata a hands free.
Dauka yayi yayi sallama, murmushi Ammar yayi ya amsa sallamar yana fadin friend ya yakake? Ina fatan kana lafiya? Abdul yace lafiya lau Ammar yaka koma gida?
Ammar yace lafiya lau ka ganni nan kwance adaki kawai na tunoka nace bara nakira inji muryarka. Hannu Sageer yasa yatoshe bakinshi saboda dariyar data taho mashi. Abdul yace lallai ka kyauta.
Ammar yace ai har Momy na fadama labarinka tace ingaisheka, itama taji dadin kirkin dakayi mani. Abdul yace haba ai bakomai. Shiru Ammar yayi can kuma yace amma de zaka zo ka gaisheta ko? Shiru Abdul yayi Sageer ne ya zungureshi hakan yasa yace insha Allah zanzo.
Murmushi Ammar yayi yace kai amma naji dadi wlh, zanzo anjima da dare intayaka fira. Abdul yace toshikenan sekazo, Ammar yace amma kaima gobe zanzo muje ka gaishe da Mom ko? Abdul yace Allah ya kaimu to. Ammar yace amin, nagode kamar kada murabu kanada kirki wlh.
Abdul yace kuma gashi anfara kiran magrib, Ammar yace haka ne, shikenan danayi isha'i zantaho, tsarabar me kake so? Harar wayar Abdul yayi yace haba de tsara ba sekace wani yaro, kabarshi kawai nagode.
Ammar yace nibazan bari ba idan nakawo maka sede kada kaci, Abdul yace to naji sekazo. Kashe wayar yayi ya wurgar da ita saman katifa ya ja tsaki. Dariya Sageer yake hada kwalla.
Abdul yace kacigaba idan ka bata mun rai zan mashi wulakanci kaga karasa damarka. Tashi Sageer yayi yace haba abokina kayi hakuri kaima kasan dole inyi dariya wai tsaraba, kuma beso kurabu. Nikam idan yazo fita zanyi dan zan iya kwafsa maka.
Abdul yace wlh ni tsoroma nakeji, Sageer yace haba karabu dashi, ai duk min iskancin mutum baya taba gwada maka halinshi daga farko, seya bari kun saba sannan ze fito maka da halinshi, kaga kafin kusaba mun samu abinda mukeso.
Abdul yace haka ne, garama muje gidan nasu gobe, insha Allah duk yanda zanyi a goben zanyi kokarin samun abinda ze tabbatar ma kotu wannan sarkar tashi ce. Sageer yace Allah yasa. Tashi mutafi masallaci kada murasa sallah.
A yau ne bayan sallar magriba yan gidan su Faisal suka kawo lefen Zaituna, kaya ne masu kyau da tsada, duk wanda yagansu yasan an kashe kudi. Bayan suntafi Umma ta kalli wata yar uwarta datazo tace Maman Yaseer gaskiya kaya sunyi.
Maman Yaseer tace kwarai kuwa, wannan kaya ko makiyi albarka, insha Allah kinga gobe idan Yaya Binta tazo semu kai na Anwar tunda angama komai, gara a kai masu da wuri suma sugama dinki da wuri.
Umma tace haka ne, dazu yake fadamun na Rayyana ma goben za'a kaisu. Maman Yaseer tace Allah de yasa wannan yarinya tana da nutsuwar Nabila, kinga shima Dr, Shamsu akwai hakuri. Umma tace ai gaskiya yan gidansu suna da tarbiyya, mahaifinsu babban mutum ne.
Maman Yaseer tace Aunty tayima kanta da yanzu da ita za'a rika hidimar bikin nan yanda takeson Anwar. Kuma haryanzu Alh, be fada maki abinda tayi mashi har ya saketa ba? Murmushi Umma tayi tace kinsan halin Alhaji akwai zurfin ciki.
Yace baze fadama kowa ba, shiyasa ma na kyaleshi. Maman Yaseer tace kinsan Allah da nice sena san yanda nayi yafada mani. Umma tace da ba kebace fa? Murmushi tayi tace shikenan, ai dama ke duk cikin mu halinki daban yake. Umma tace e naji, tashi kije kidubo tuwon can ya isa kwashewa ki kwashe.
Sageer ne da Saddika zaune asaman dakalin gidansu suna fira, mika mashi wayarta tayi, bayan ya amsa yaga ta rubuta wai yaushe zaka amshi wannan jakar daka kawo mani ajiya? Murmushi yayi ya maida mata da.
Kede ki ajeta nan bada wani lokaci ba zan amsa, inafatan kinboyeta da kyau ko? Rubuta mashi tayi mamana naba ta boye mani saboda karna aje adakina kannena su shiga su bincikota, kuma tace adakin Baba takai ta boye dan basa shiga can.
Sageer ya rubuta mata, baki jin kunya kika bama Mama ajiyata? Murmushi tayi ta rubuta mashi dole na boye abinda ka kasa ajeshi agurinka ka kawo mani shi, nasan yanada muhimmanci sosai, itama Mama haka tace shiyasa ta kai dakin Baba.
Sageer yace hakane, suna da muhimmanci sosai, zan fada maki komeye aciki amma sena gama amfani dasu. Murmushi tayi ta rubuta mashi zuwa yaushe kenan? Nan da sati 2 insha Allah nasan nagama komai.
Kinga daga ranar zamuzo neman aure wajen Baba, kuma baza'a sa ranar dayawa ba, wata 2 ma ya isa. Murmushi tayi ta rubuta mashi Allah ya kaimu. Haka sukayi ta fira cike da annashuwa se wajen 9 sannan yatafi dan Abdul yace da yaga flashing dinshi ya taho Ammar yatafi.
Ammar ne da Abdul suka fito daga cikin gidansu Abdul, kallon Abdul Ammar yayi yace wlh jinake kamar kada intafi, gaskiya ka iya fira me dadi, dama ace kullum muna tare karika mani firanka me dadi.
Abdul yace ai bakomai gobe ma muna tare. Ammar yace da anyi la'asar zanzo mutafi idan yaso seka bama wani tsaron shagonka ko? Abdul yace shikenan ai da mungaisa zan dawo. Hararshi Ammar yayi yace Allah banyarda ba, sekaci abincin dare agidanmu zan maidoka.
Idan kuma kanaso Mom tayi fushi to. Abdul yace toshikenan zanci, Ammar yace yauwa ko kaifa, kaga zamusha fira adakina muyi kallo harmu gaji ko? Abdul yace hakane, nagode da tsaraba, gashi ni kuma ban dafa abinci ba bare kaci.
Ammar yace bakomai, wata rana zanci ai. Har bakin mota Abdul ya rakashi, hannu yabashi sukayi musabaha yace ka gaida Mom, rike hannunshi Ammar yayi ya kura mashi ido yana murmushi. Zare hannunshi Abdul yayi yana fadin katafi kada Mom taga ka dade. Ammar yace to nagode, shiga motar yayi yatafi.
Tsaki Abdul yayi yajuya ze koma sega Sageer ya sauka a mashin. Jiranshi yayi harya karaso, Sageer yace abokina me kake awaje bacin tundazu kace yatafi? Tsaki Abdul yakara ja yace sefa yanzu yatafi kilama kaga motarshi.
Sageer yace to me ya tsaya yi? Abdul yace mun kusa minti 20 anan tsaye, yanda kasan yazo zance wajena, waishi beso yatafi😅 dariya Sageer yayi yace ai shiyasa nayi zamana wajen Baby dan nasan baze tafi da wuri ba.
Shiga ciki sukayi Sageer yana fadin me yakawo maka? Abdul yace ni na sani ma, gashi can aleda sede naji kamshi kila snacks ne, sekace yazo wajen budurwarshi. Sageer yace amma ya kyauta dama ahanya nake tunanin idan nadawo semunyi girki.
Bude ledar yayi sega gasassar kaza da taji kayan miya se kamshi takeyi, dayar ledar kuma hollandia ce manya guda 2 masu sanyi, se wata leda aciki ita kuma kayan zaki ne aciki.
Dariya Sageer yayi yace wato abokina idan kana raye zakaga abubuwan mamaki arayuwa, nine yakamata ace nakaima Baby irin wadannan kayan, amma gashi muna zaune Babynka yakawo mana😂.
Plate yadauko yazuba yace taho muci ko kana tsoro kada yasa maganin mallaka aciki? Zama Abdul yayi yadauki cinya yana fadin ai wlh sede ya mallakeni yanda ya cinyemun abincin cikina da surutunshi dole inci kaza, bismillah batabar komai ba ai.
Sageer yace gaskiya Ammar ya kyauta, dama na kwana biyu banci kaza ba, Abdul yace kana cimashi kaza kuma zaka makashi kotu ba. Sageer yace shiyasa ai bazan taba bari muhadu ba, kuma kaima kada kabari yasan muna tare. Kaga koya ganni akotu bazeji komai ba.
Abdul yace angama, wai Salis yaje sun kai takardar karar kuwa? Sageer yace a'a yade kai kaza😂 dariya Abdul yayi yace kai dan iska ne, wayace maka santi nakeyi? Sageer yace inba santi ba karasa lokacin yin tambayar se yanzu da kazar Babynka ta ratsaka. Abdul yace wlh bada wasa nake ba.
Sageer yace se gobe zasuje, kuma nasan kila mufara shiga kotu ranar Monday. Abdul yace to Allah yate maka, kaga nima kullum senaje kotu kodan inji da kunnena ba labari ba. Sageer yace kaga gobe ma inaso inje gidan yari ingaishe da Baba Yusha'u kuma in kaima Kamal ziyara. Abdul yace Allah ya kaimu.
********
Washe gari haka a gidansu Nabila aka tashi da shirye shiryen tarbar baki, abinci me rai da lafiya suka shirya masu da lemuka. Bayan sungama Nabila da Rayyana sukayi wanka suka tafi gidansu Zarah.
Da misalin karfe 1:30 suka iso, kusan atare sukazo dan Anwar yafadama Dr,Shamsu tafiyarsu hakan yasa sukaje kusan atare, sede yan gidansu Anwar sun rigasu zuwa.
Dayake kowa da cooler dinshi akayi, kuma bazama zasuyi ba, shiyasa aka kaima kowa nashi mota, suka bada tukuici, sosai sukaji dadin karamcin da akayi masu, haka suka tafi suna godiya.
Bayan suntafi Umman Rayyana takira Nabila tace kutaho gida suntafi. Duba kan suka farayi, Kaya sunyi kyau sosai, sede na Nabila sunfi na Rayyana da kadan, amma dukansu kowa akwatinan shi seti guda ne. An kashe kudi kam.
Umman Rayyana se murnata take tana kara godema Allah dayasa shirin da sukayi be tabbata ba, dayanzu kila itama Rayyanar bata samu miji haka ba. Gaba daya kayan dakin Umman Nabila aka ajesu.
Amma saboda kada yan tsegumi su hada fada yasa tace ma Umman Rayyana akaisu dakinsu Rayyana saboda idan kawayensu sunzo kada surika jin kunyar dagawa, da wannan shawarar yasa aka maidasu dakinsu Nabila.
Salis ne yakira Sageer yafada mashi sun kai takardar karar kuma alkali yasa ranar shari'a Monday 29 ga wata, kuma yace zesa a aikama shugaban gidan yari da takaradar sammaci. Sageer yace yauwa abokina nagode.
Anjima idan bakada aikin dare muhadu a gidan yari zanje ingaishe da Baba, Salis yace shikenan babu damuwa senazo. Kallon Abdul yayi da yake zaune a shago yafada mashi abinda Salis yace.
Abdul yace lallai lokacin fara aiki yayi, kaga seka zuna kafin monday katsara yanda zaka gabatar da shedunka, kada kabari kafara gabatar da tasu D.P.O da brr, Yusuf harse lokacin hakan yayi.
Kaga ba zasuyi zarginka akan kana bibiyarsu tuntuni ba,kuma kada ka kira D.P.O shikadai amatsayin wanda zaka tambaya, ka hada da Salis kaga D.P.O baze musa ba, kuma baze canza likita ba tunda tare da Salis sukaje. Sageer yace haka ne, shiyasa nake sonka abokina, kana bani gudummuwa sosai a case din nan.
Kallon agogo Sageer yayi yace kaga saura minti 5 akira la'asar bara intafi nasan yanzu Babynka ze kira, ai kafin yagama magana wayar Abdul tayi kara. Dafe kai yayi yana fadin yau nashiga 3. Yana dagawa Ammar yace friend ganinan nataho idan nazo semuyi sallar anan.
Abdul yace to seka iso, kashe wayar yayi yana tsaki. Murmushi Sageer yayi yace to adawo lafiya, amma ka kula da duk abinda ze baka nasha, domin kasan halin mutum bakamar irinsu Ammar, nikaina ayanzu inajin tsoron zuwanka gidansu, bazanso wani abu yasameka ta dalilina ba Abdul.
Murmushi Abdul yayi yace kada kadamu abokina, wlh zan iya bada raina akan ka, matukar zaka tabbatar da gaskiya ni kuma zan shige maka gaba akan wannan case din, dan haka kadena damuwa zan kula da kaina insha Allah.
Sageer yace shikenan, Allah yatsaremun kai, zanje inyi sallah kabama wani ajiyar wajen idan kuka tafi se indawo, Abdul yace shikenan idan kaje ka gaishe da Baba da Salis, harma da Kamal, kace mashi ina nan ina kirga kwanakin da suka rage mashi, zamuzo tarbarshi. Fita Sageer yana fadin zasuji.
Yana tafiya sega Ammar yazo, bayan sunyi sallah suka tafi, Ammar bakinshi yaki rufuwa se murmushi yakeyi yana kallon Abdul, shikam jikinshi ne yafara sanyi ganin da gaske tafiyar zasuyi. Addu'a yafara karantowa aranshi dan ita kadaice mafita.
To su malam Abdul aci beta lafiya👍🏻😂.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[2/10, 2:10 PM] nabilalady5: 👨🏻🎓KAFIN IN ZAMA LAWYER👨🏻🎓 👨🏻🎓 👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 95 🖤 100
WANNAN SHAFIN NAKI NE KAWATA RALIYA YAHAIYA MALUMFASHI👭💋. ALLAH YABAR ZUMUNCI.
Bayan Abdul sun gaisa da Mom din Ammar suka shiga part din Ammar, sosai yayi mamakin irin karamcin da Mom din Amma ta nuna mashi, dan ita tana son duk wanda Ammar yakawo yace yayi mashi wani abun kirki.
Daga ita har Dad dinshi suna son shi saboda shikadai Allah yabasu, saboda son dasuke nuna mashi yasa haryanzu beyi aure ba,ya yawata kasashen waje da dama, kuma acan ya koyo harka da maza, domin shima yana da kyau.
Sam rashin aurenshi baya damun iyayenshi, domin Dad dinshi yace kozeyi aure sede yakawo matar cikin gidansu, akwai part din da aka gina mashi, sede haryanzu a cikin gidansu yake.
Duk barnar da yakeyi iyayenshi basu sani ba, duk yawan mazan dayake yawan kawowa gidan hankalinsu kwance domin sun dauka kallon kwallo suke zuwa kamar yanda yace. Shiyasa suke alfahari dashi, domin kafin kaganshi da mace da wuya.
Bayan sun zauna Ammar ya fita yadauko ma Abdul lemu da fruits din da Mom tasa me aikinsu ta yanka. Yana zuwa ya zauna kusa da Abdul yace friend kasaki jikinka mana, naga kamar kana tsoron gidan.
Murmushi Abdul yayi yace haba de tsoro, ai nima ya zama gidanmu domin naji dadin yanda Mom ta karbeni. Zuba mashi lemun yayi yace bara inbaka kada ka wahala ko? Murmushi Abdul yayi yace nizan fara baka idan kasha sena sha sauranka kaga abotar mu zatafi kara karko.
Wani dadi ne yakama Ammar jin abinda Abdul yafada, mika mashi yayi yace to ammafa ta inda nasha kaima tanan zaka sha, cup din yasamshi abaki, bayan yasha rabi sannan ya karba yace saura ni.
Abaki yabama Abdul seda ya shanye sannan ya aje cup din, ajiyar zuciya Abdul yayi, dama dabarar shi tayin haka kada yaje Ammar yasa mashi wani abun, amma tunda yaga yafara sha shiyasa hankalinshi ya kwanta.
Ayba Ammar yadauko yace to daga bakin, dan yau gurina kazo dan haka nine zanciyar da kai, Abdul yace banaso in wahalar da kai, kawo inci na hutar da kai. Murmushi yayi ya mika mashi yana fadin bara in kunna mana kallo.
Abdul kamar yasan irin film din dazesa masu yace idan kanada wrestling kasa mana ina matukar sonshi. Ammar yace shikenan da wani nigerian film zan samaka me kyau, amma tunda kace haka bara nasa maka anjima idan munyi magrib se mu kalli wancan.
Bayan yasa mashi yatashi ya bude wata jakarshi yaciro hotuna, dawowa yayi ya zauna ya jingina da Abdul yana fadin bara in nuna maka hotuna na na London inda nayi karatuna.
Abdul yace kacika son jiki kamar mage Ammar, murmushi Ammar yayi yasa hannunshi cikin dimple din Abdul yace wlh ina matukar son wannan abun naka. Kauda kai Abdul yayi yana fadin muga hotunan, mika mashi yayi yace zan fada maka koni da suwaye.
Haka yarika daga hotunan Ammar yana mashi bayani, harya wuce wani yayi saurin maidoshi, kura mashi ido yayi, yana sanye da farar riga da bakin wando, ya balle maballin rigar, wata sarka yagani bata da bambanci data gurin Sageer.
Ammar yace nayi kyau ko? Abdul yace sosai ma, Ammar yace ban kai ka kyau ba ai, murmushi Abdul yayi yacigaba da kallon hotunan, seda yagama ya lura da wannan hoton kusan guda 3 ne aciki.
Duk da bashi kadai bane yake da sarkar awuyanshi, amma yawancin sauran tadan boye cikin riga. Wayar Ammar ce tayi kara, yana dubawa yaga Mom ce, tashi yayi yana fadin sweet friend bara nazo Mom nakira na, ka kularmun da kanka fa kafin nadawo.
Tsaki Abdul yaja bayan yafita yace cigaba kenan, wai sweet friend. Saurin daukar daya daga cikin hotunan yayi yasakashi cikin aljihun gajeran wandonshi, komawa yayi yazauna yana fadin zakasan sweet friend.
Bayan sunyi sallar isha'i aka kawo masu abinci, Ammar se wani shigewa jikin Abdul yake yana mashi shagwaba, Abdul kuwa daurewa kawai yake dan yafara kaishi makurar bacin rai, kallonshi yayi yace idan bazaka tashi muci abinci ba nizan tafi.
Saurin tashi Ammar yayi yana fadin sorry muci, haka suka fara cin abincin Ammar yana bashi abaki, dande kar ya nuna wani abu yasa Abdul yake biye mashi. Bayan sungama Abdul yace muje nayima Mom sallama tafiya zanyi.
Ammar yace haba dan Allah, kabari se 10 mana, Abdul yace kada kadamu ai muna tare, wata rana ma kwana zanyi tunda kaga ni daya ne agidana ko? Murmushi Ammar yayi yace kai amma naji dadin wannan maganar.
Wallahi duk ranar da kazo kwana wajena zakaga yanda zanji da kai, bazaka so murabu ba. Abdul yace Allah yakaimu inzo insha gata. Tashi sukayi, Ammar yadauko mashi wani turare me kyau, daga ganinshi kasan yana da tsada, aleda yasa mashi suka fita yayima Mom sallama tana ta mashi godiya suka tafi.
Har kofar gida Ammar ya kaishi, suna zuwa Abdul yasa key ya bude kofar, juyowa yayi yace nagode Ammar ka gaida Mom. Kamo hannunshi Ammar yayi yasaka mashi ledar daya riko mashi.
Abdul yace nagode da kulawarka abokina, Ammar yace wannan ai bawani abu bane, kulawa tana gaba. Abdul yace nagode, kamar daga sama yaji Ammar ya rungumoshi yana fadin zanyi kewarka kafin gobe.
Cire jikinshi Abdul yayi yana fadin seda safe, har Abdul yashige Ammar yana kallonshi, seda yaga ya kulle kofar sannan ya cije lebenshi yashafi kanshi yana fadin zaka shigo hannu ne, motarshi yashiga yatafi.
Sosai Baba da Kamal sukaji dadin nasarar dasu Sageer suka fara samu, Baba yace in Allah ya yarda Sageer seka zamo abin alfahari acikin al'umma, wata rana seka daukaka, daga yau da izinin Allah talakawa bazasu kara kuka da rashin adalci ba.
Kuma insha Allah daga ranar monday har zuwa lokacin daza'a kammala wannan shari'a zan ziyarci kotu badan komai ba sedan inga yanda komai ze kasance. Sageer yace amin Baba, nima nagode da addu'ar ka.
Duk da kasancewar iyayena basa raye amma banyi maraicin addu'ar su ba domin Allah yabani kai, nagode kuma zancigaba da daukarka amatsayin mahaifi. Kamal yace gaskiya naji dadin wannan nasara da kuka fara samu.
Ina ma ace za'a barni danazo domin inyi kallon wannan shari'a. Salis yace ka kwantar da hankalinka, wannan shari'ar dole zaka ganta tun daga farko har kashe, domin kana cikin shedunmu, koda ace angama da kai bazan bari kadena zuwa ba harse an gama.
Kamal yace gaskiya danaji dadi, kuma ashirye nake infadi duk abinda nasani. Sageer yace Baba ina Gali fa? Baba yace yakoma aikin rana ai, nima gobe zan koma aikin safe, kada kadamu shima Allah ze tona mashi asiri.
Salis yace zamuzo mukoma, Allah yayi mana jagora, kudi Sageer yaciro yabama Kamal yana fadin Abdul yace ingaisheka kuma yana nan yana kirga kwanakinka tare zamuzo tarbarka. Murmushi Kamal yayi yace Allah yasa munada rabon gani. Godiya yayi masu suka mashi sallama suka tafi.
Sosai Sageer yasha dariya lokacin da Abdul yagama bashi labarin zuwanshi gidansu Ammar. Sageer yace gaskiya abokina yau kasha gata, katon Allah yabaka abinci abaki. Tsaki Abdul yaja yana fadin kaide bari.
Hada wani rungume ni kome yajima oho. Dariya Sageer yayi yace shiyasan meyaji tunda yasa wani abu aranshi. Abdul yace nikam daga yau mun rabu dashi, ko yakirani bazan dauka ba, idan yazo gurina bazan fita ba.
Sageer yace haba abokina yabamu samu komai daga gareshi ba kuma zaka datse abotar. Tashi Abdul yayi yaciro hoton daya saka agajeran wandonshi yana fadin niko nasamo maka sheda.
Karbar hoton Sageer yayi yana kallo, cike da farin ciki yace kai amma nagode abokina, wlh ga sarkar da Mannir yabama Kamal nan awuyanshi. Ya Allah kasa ita kadaice agurinshi kada mu kunyata a idon jama'a.
Zama Abdul yayi yana fadin insha Allah ita kadaice, kuma wannan hoton zetemaka mana sosai. Sageer yace yanzu abinda nakeso da kai, kada kace zaka ki daukar wayarshi, inaso idan yakiraka yafara maka magana kamar yanayi da mace kafara nuna mashi rashin dacewar hakan.
Idan kuma yace zezo kace kana aiki ashago, idan yace kabama wani ajiya kace a'a koda yace zejiraka kace mashi kai karatu zakaje dauka amasallaci bayan magriba kuma se anyi isha'i zaku gama. Idan yace zejiraka kace kana da abinyi agida zaka duba wasu littafan addini.
Ina me tabbatar maka matukar yaga kasa Allah agaba shida kanshi ze kyaleka, domin duk masu irin wannan harkar ko kuma wata harka ta sabon Allah basa son tarayya da wanda yake tsoron Allah kuma yake saurin fada masu gaskiya idan suna tare.
Abdul yace shikenan zanyi yanda kace, Allah yayi mana jagora. Sageer yace amin. Tashi yayi yadauko leda yasa hoton aciki yace wannan base na kaima Saddika ba, bara nayi mashi sakarar ajiya. Abdul yace ka ajeshi kawai gobe idan zamuje shago mutafi dashi ka ajeshi can tunda babu wanda yasan shagonka ne. Sageer yace haka ne, kaga jibi ne zamu shiga kotun. Abdul yace Allah yasa inada rabon gani. Murmushi Sageer yayi yace munada rabon gani de, Abdul yace haka ne.
*********
Washe gari takama lahadi tunda safe Anwar da Abba suka tafi makarantar su Ilham domin daukota, duk da tun juma'a suka gama amma dayake sun tsaya yin wasu programmes ranar asabar hakan yasa suka bari se ranar lahadi sannan sutafi.
Gate din F.G.C Bakori cike yake da manyan motoci kowa yazo daukar diyarshi, wasu kuma driver ne yazo daukarsu wasu kuma yayyansu. Da gudu Ilham ta rugo ta rungume Abbansu tana dariya, sakinshi tayi takoma kan Anwar.
Murmushi Abba yayi yana fadin Ilham haryanzu baki girma bane? Sakin Anwar tayi tana fadin Abba ai dole inyi murna daga yau nasamu 'yancin kaina, babu wani malami daze kara dukana.
Dariya Anwar yayi yana fadin ke kuma me tsoron duka ko? Gaishe su tayi, Abba yace Ilham ina tayaki murnar gama karatunki, murmushi tayi tace nagode Abba. Anwar yace congratulation my little sister, tace thank you my sweet Brother.
Juyawa tayi tana fadin bara indauko jakata mubar kofar makarantar nan duk ta isheni. Dariya suka sa. Har bakin mota kawayenta suka rakota bayan sun gaishe dasu, tayi masu sallama hada kukansu suka rabu.
A cikin mota se labari Ilham take basu suna dariya, Ilham tace yauwa Yaya mezaka bani amatsayin gift? Murmushi yayi yace nasaya maki irin wayar da kikacemun kinaso. Dariya tayi tana fadin amma Yayana nagode.
Abba kaifa? Murmushi yayi yace idan munje gida zaki gani, murmushi tayi tace dan Allah Abba, dariya yayi yace to nasaya maki laptop, ihun dadi tasa tana fadin kai wayyo ni yar gatan Abba da Yayana. Nagode Abba Allah yakara maka budi kaida Yaya, yace amin Ilham, kinga seki dage idan result dinku yafito kema kitafi makaranta kifara karatunki kuma banda wasa. Anwar yace kuma banda shiga group din banza a whatsapp, dariya sukasa, Ilham tace yauwa Yaya wai me yasa idan nakira wayar Aunty na tambayeta ya gida seta cemun yana can? Kallonta Anwar yayi yace Ilham surutu kizauna mu isa gidan.
Dariya tayi tace yauwa Yaya saura wata 1 bikinku kaida Yaya Zaituna ko? Uhm yace mata,tace ai munyi waya da ita tace gobe suma zasu gama. Yauwa Yaya amma de Aunty ce tazaba maka matar ko? Abba yace Ilham surutu, kibarshi yayi tuki mana. Bakinta takama tana dariya tace nayi shiru Abba.
Bayan sunje gida da gudu tafita tashige gida, sosai Anwar yaji tausayinta, kowane da yana murnar yadawo gida yaga mahaifiyarshi, amma ita bazata ganta agidan ba. Dafashi Abba yayi yace Dr, nasan abinda kake tunani, kacire wannan abun aranka, duk da nasan akwai ciwo agurinsu amma uwarsu taja masu, dan haka banason ina ganin irin haka agurinka daga yau. Anwar yace insha Allah Abba bazan kara ba.
Afalo tasamu Umma da gudu taje ta rungumeta tana dariya, itama Umman dariyar take tana fadin kaga yan Candy kai,sannu dazuwa su Ilham anzama yan mata. Dariya Ilham tayi tazauna tana fadin Umma ina kwana? Zama tayi tana fadin lafiya lau, Ilham ya makaranta ina fatan angama karatu lafiya? Ilham tace lafiya lau, nasameku lafiya Umma? Tace lafiya lau.
Tashi Ilham tayi tana fadin yanzu haka Aunty tana kitchen tunda najita shiru, bara inje inyimata bazata nasan bataji zuwanmu ba, hanyar part dinta tabi tana dariya. Tausayinta ne yakama Umma, tunda Aunty ta tafi bata taba jin tausayin yaranta ba kamar yau.
Shigowar su Abba ne ya katse mata tunanin data keyi, murmushi tasaki tana fadin sannuku da hanya, amma kunyi sauri. Zama Abba yayi yana fadin aikinsan Dr, akwai gudu da mota. Ina fatan anshirya mana abincin muzo muyi partyn Candy ina Ilham din?
A sanyaye Ilham tafito daga part din Aunty, kusa da Umma tazauna idonta tab da hawaye. Kasa Umma tayi da kai sam takasa kallonta. Juyawa Anwar yayi yashige part dinshi danshima idonshi yafara kawo ruwa.
A hankali Ilham tace Abba yanzu kam nagane dalilin dayasa Aunty take cemun gida yana can, ashe bata gidan nan, Share hawayen dasuka zubo mata tayi tana fadin base naji abinda yasa Abba ka saki Aunty ba, duk da takasance mahaifiyata nasan ba karamin abu tayi maka ba har ka iya sallamarta.
Bazanyi bakin ciki ba, tunda inada Umma, nasan zata maye mani gurbinta da ace halin Umma beda kyau tabbas nasan zanfi kowa bakin cikin tafiyar Aunty, amma Allah yasa hakan shine alkhairi. Kuka tasa tare da kifa kanta saman kafar Umma.
Itama Ummar kukan take, shikanshi Abba seda yaji zuciyarshi ta tsinke, kasa magana yayi kawai yatashi yashige daki. Lallashinta Umma tai tayi har ta hakura, tashi sukayi Umma tana fadin muje kiyi wanka kisa sabon dinkin danayi maki idan munyi salla semuci abinci.
Shugaban gidan yari ne zaune a office dinshi shida ma aikatanshi, kallonsu yayi yana jujjuya takardar datake a hannunshi, nasan zakuyi mamakin wannan kiran danayi maku, duk da ban cika zuwa office ranar lahadi ba.
Wani sako ne yasameni daga kotu aka aiko mani da takardar sammaci akan mutuwar wani yaro Mannir. Nasan bazaku manta da abinda yafaru a wannan gida namu cikin wannan watan ba? Hadiyar miyau Gali yayi har zufa tafara zubo mashi.
To shine iyayen yaron suka kai kara akan basu yarda cewa kwayace takashe masu da ba, domin baya shaye shaye. Alokacin da takardar ta sameni naje can office din nasamu wani abokina shine yake bani wannan
labarin.
Kallon Gali yayi yace malam Gali idan ban manta ba kaine wanda yake da aiki adaren da yaron ze rasu ko? Kuma har ya rasu kana kan aiki ko? Gyara zama Gali yayi yace e to haka ne, amma wallahi nima wasu masu gadi ne suka fadamun mutuwarshi.
Murmushi yayi yace malam Gali waya saka rantsuwa kuma? Ni kawai tambayarka nayi dan nasan alokacin da nazo wajen kaine kabani kwayar da aka samu a jikinshi.
Shiru Gali yayi yana zare ido, kafada yadaga yana fadin shikenan,dama nakiraku ne dan infadamaku akowane lokaci za'a iya kiranku akotu. Murmushi Baba Yusha'u yayi alokacin daya kalli Gali. Shugaban yace zaku iya tafiya, amma kusani gobe ne za'a fara shiga kotu. Godiya sukayi mashi suka fita.
Gali harda gudu yake hadawa yafita daga gidan, wani guri yasamu yakira D.P.O, bayan yadauka yace lafiya de Gali naji kana haki? Inafa lafiya yallabai, allurace zata tonu galma. Tashi tsaye D.P.O yayi yana fadin kamar ya?.........................
Labarin duk abinda yafaru yanzu yafada mashi, ai D.P.O hada kware wa yayi yana fadin gobe fa kace? Gali yace sosai ma, to wane lawyer ne ze tsaya masu? Gali yace wallahi nima bansani ba.D.P.O yace shikenan zanje wajen yallabai idan naje zamu nemeka komin dare, amma inaso ka kama bakinka. Kashe wayar yayi yana huci yakira Brr,Yusuf, yana dagawa yace ka kira Umar kuje office dinka ganinan zuwa zan taho da likita akwai matsala. Kashe wayar yayi yakira Dr.
Zuface kawai take zuboma D.P.O da Dr da Umar bayan sungama jin abinda yafaru.
Murmushi Brr, Yusuf yayi yace yanzu kai wannan abunne ya daga maka hankali? Kada kamanta kana tare da kwararran lawyer, kuma na tabbata Sageer ne ze tsaya masu domin yana takamar yayi nasara a wancan karamin case din.
Uhm, kubarshi dani yake magana, kuma nine wanda zantsaya ma shugaban gidan yari akotu, nasan za'a kiraka, inaso kada kadamu, mune zamu sake nasara, domin mune mukeda kayan aiki. Sageer besan komai a case din nan ba. Inaso ka kira Gali kaja kunnanshi sosai, ko kuma muje inganshi, ni nasan maganar dazan saka mashi abaki wadda zerike.
Dr, kaima kada kadamu wannan karon nine zanyi case din baza'a kara kada kaba. Kuma zankira Alh, Abbas infada mashi case zedawo sabo suma su shirya kawo kudi da kuma zuwa kotu. Allah yakaimu goben, zanji dashi zega ban bancin dayake tsakanina dashi.
BARRISTER SAGEER ALEE DAN MASANI YANZU ZAMU FARA BUGA WASAN👌🏻.

Facebook...Nabeela Ladeey
Season 100 🖤 105
11:00am @
HIGH COURT KATSINA STATE
🏨🏨🏨🏨🏨🏨🏨🏨🏨
Harabar babbar kotu cike take da jama'a, daya bayan daya suka fara shiga ciki har suka gama, Brr, Yusuf ne tare da wasu abokan aikinsu a tsaye suna tattaunawa, daya daga cikin abokanshi yace, wai ni Brr, wannan case din da za'a gabatar yanzu bashine wanda kayi kwanakin baya ba?
Murmushi Brr, Yusuf yayi yace shine, kasan mutane idan suna son kudi babu abinda bazasuyi ba, ina wannan karamin yaron da ya gabatar da shari'ar da akayi wancan satin akan fyade? Yauwa toshine wai yasa aka tado da shari'ar nan kasan be aikin komai yade gama karatunshi.
Kasan kananan lauyoyi idan suka shigo gari jisuke kamar sunfi kowa, ga rashin aikinyi ga rashin kudi, inaji ganin yayi nasara akan wancan case din yasa yake tunanin zekarayi a wannan karon, shiyasa yasa suka kawo kara kaga ai dole subiyashi.
Dariya suka sa wani yace habade, ai wancan karon da tsaranshi yakara, bakaga yanda kowa shari'ar tabashi dariya ba, amma wannan karon da shugaban lauyoyi ze kara kaga kuwa dole yasha kashi.
Dariya suka kara sawa hada kashewa. Sageer ne da Abdul suka zo wucewa jin ana dariya yasa suka juya, suna ganinsu suka kara kwashewa da dariya suna nunashi. Hannunshi Abdul yaja yace mutafi.
Sageer Alee Dan Masani!! Abinda yaji an fada daga bayansu kenan, tsayawa yayi sede be juya ba, takowa Brr, Yusuf yayi har inda yake, kafadarshi yadafa yana murmushi yace ba fada meyakawo gaba?
Ai ni da alkhairi na zauna da kai, amma yazaka maidani abokin gabarka? Inaji ko aikin kwasar kashi na baka bekamata ka watsar dani haka ba. Bare kuma na baka aiki me rai da lafiya amma se in nemeka inrasa.
Murmushi yayi yace haba Sageer, ai idan mutum zebar aiki magana yakeyi kaga se a sallameshi bawai katafi kabar mani bashinka akai na ba. Koba komai ai kayi mani aiki na wasu kwanaki.
Kodayake ance idan kaga bako ya tafi babu sallama to ya aikata rashin gaskiya, to kode abinda yafaru da kai kenan? Kara hade fuska Sageer yayi amma beyi magana ba. Brr, Yusuf yace koda yake yanzu ka girma kafara cin gashin kanka har kana tunanin hada kafada dani dole zaka bar office dina.
Naji ance kaine zamu goga da kai ayau ko? Uhm, Sageer kaji tsoron wasa da maciji domin wata rana shine ajalinka. Zakasan ban banci tsakanin cikekken lawyer da kuma Dakikin lawyer. Nabarka lafiya.
Tsaki Sageer yaja yakama hannun Abdul suka wuce, Abdul yace dan allah abokina kada wannan abun yadameka har yasa ka kasa gabatar da aikinka, na tabbata yayi haka ne domin yakada maka ciki, ka daukeshi tamkar dalibinka, hakan zesa ka fafata dashi babu tsoro aciki.
Murmushi Sageer yayi yace kada kadamu, banji komai ba, kuma zan nuna mashi dakikin lawyer da suka raina shine ze sasu cikin tashin hankali, ina me tabbatar maka daga yanzu kafin afara shari'ar nan Brr, Yusuf shida mutananshi sundena bacci medadi, haka zalika bazasu kara dariyar farin ciki ba. Abdul yace haka nakeson ji abokina.
Wayar Abdul ce tayi kara, yana dubawa yaga Ammar ne, tsaki yaja yana fadin baka hakura ba kenan, yana dauka Ammar yace haba Friend, wai meyasa kakemun haka? Idan kasan zakamun haka meyasa zaka fara bani fuska yanzu kuma karika raina mun hankali?
Wallahi Abdul baka sanni bane, idan har nanuna inason mutum saukinshi yabini, domin banida mutunci da kake ganina haka,saurin amsar wayar Sageer yayi ya danna recording.
To bara kaji Abdul, ni Ammar nafi karfin wulakanci domin ni ba'a wulakanta ni, duk wanda na nuna inaso yakawo mun rainin hankali nasan yanda zanyi maganinshi, na kara da mutane da dama kuma nine nayi nasara akansu.
Dan haka ka kula da kanka, tun jiya ina binka amma kana mun wulakanci dan kaga ina sonka, to wallahi komin son danake maka baze hana in hukuntaka ba, garama kabini asannu muyi rabuwar arziki.
Kashe wayar Abdul yayi yaja tsaki, kallon Sageer yayi yace kai kuma ya zakamun recording muryar wannan banzan manemin maza? Murmushi Sageer yayi yace saboda gaba, kasan yanzu acikin nema nake, to sheda komun kankantar ta bana rainata.
Lokacin da yafara maka wannan maganar kawai wani abu yafado mani arai, hakan yasa na danna recording, idan mun koma gida zan kara nazari akan maganganunshi. Abdul yace shikenan, muje naga kowa yashiga.
Bayan alkali yashigo kowa yazauna magatakarda yatashi domin karanto shari'ar da za'a gabatar.
A yau litinin 30 ga watan agusta shekara ta 2016, zamu saurari karar da iyayen marigayi Mannir suka kawo akan mutuwar dansu wanda aka yanke ma hukuncin kisa daurin rai da rai agidan yari, wanda kuma wannan kotun ce ta yanke wannan hukunci.
Sede a washe garin ranar da aka kaishi gidan yari da safe yarasu, wanda abinciken da shugaban gidan yari yasa akayi akan mutuwarshi an gano cewar yarasu ne asanadiyar muguwar kwayar dayake yawan sha.
Hakan ne yasa mahaifanshi sukace basu yarda da wannan shedar ba domin sun tabbata dansu baya shaye shaye. Mikama alkali takardar yayi yakoma yazauna. Surutu aka farayi acikin kotun, kowa da abinda yake fada.
Bubbuga tebur alkali yayi kowa yayi shiru, kallon barin da lauyoyi suke zaune yayi yace ina lauyoyin dazasu gabatar da wannan shari'ar? Tashi Sageer yayi ya gyara rigarshi yace.
Sunana Brr, Sageer Alee Dan Masani lawyer mezaman kanshi, kuma nine wanda zan kare wadan da suka kawo kara.
Cike da izza Brr, Yusuf yatashi, gyara glass din idonshi yayi yace sunana Brr, Yusuf lawyer me zaman kanshi, nine wanda ze kare bangaren shugaban gidan yari, nagode.
Jinjina kai alkali yayi yace lawyer daze fara bismilla. Kintashi Sageer yayi domin yasan yanda kwararrun lawyers suke, basu taba bari sufara gabatar da shari'a sede su fito akaro na 2, domin yaga yanda suka gabatar da shari'ar farko.
Brr, Yusuf ganin Sageer yaki tashi yadauka tsoro ne ya kamashi, murmushi yayi yatashi yana gyara riga. Yame girma meshari'a zanso kotu ta gayyato mani shugaban gidan yari domin nafara mashi wasu yan tambayoyi. Kotu tabaka dama.
Kotu zataso taji sunanka da kuma aikinka? Ni sunana. Naziru Isah, kuma nine shugaban gidan babbar yari.
Shin kozaka iya fada mana abinda kasani agame da mutuwar daya daga cikin yaran dasuke gidanka wanda aka kawo da laifin kashe abokinshi?
E to, agaskiya ranar da aka kawoshi bana gurin aiki, kuma ba nine aka bama shi ba, sun sami daya daga cikin ma aikatan gurin suka bashi, sede bayan nazo abincikena danayi na file dinshi. Ya nuna mana lokacin da aka kawoshi ma baya cikin hayyacinshi.
Saboda yasha wata kwaya datafi karfinshi, hakan yasa ba'a bashi daki agidan ba, domin mazan gidan karsu cutar dashi yasa aka barshi a cikin dakin masu kula da masu laifi. Bayan nakara duba file dinshi naga wannan takardar, kuma takarda ce wadda tafito daga gurin likita wanda alamu sun nuna kamar shine likitanshi.
Takardar ta nuna mana yawan shan kwayar dayakeyi yasa ta taba mashi zuciya, domin abinciken da yayi mashi ya nuna cewar idan har ya kuskura ya cigaba da shan irin muguwar kwayar dayake sha zata zamo barazana ga rayuwarshi.
Bayan nagama duba file dinshi naje wajen mutumin dayake da aiki alokacin, sede koda naje har lokacin be farfado daga baccin buguwar dayake ba, hakan yasa nabar ma wanda yake kula dashi sallahu akan ya kula dashi harzuwa lokacin daze tashi, kuma ya kaishi dakin dayasan baza'a cutar dashi ba har yagama dawowa hankalinshi, shine na aje file dinshi anan dan idan yatashi yafada masu komai nashi su rubuta aciki.
To washe gari da safe ina gida na samu waya daga wani ma aikacin da shine yayi aikin kwana alokacin, shine yake fadamun inyi sauri inzo babu lafiya daya daga cikin yarana yarasu. Jin hakan yasa nayi saurin tahowa.
Ina zuwa nasamu gawarshi a clinic dayake cikin gidan, malam Gali shine wanda ya kwana akan aiki, kuma shine yakirani awaya. Alokacin ne yamiko mani wata kwaya atakarda yake sheda mani yasameta ne acikin aljihun mamacin.
Kuma ansami wata takardar kwayar daya bare yazuba acikin ruwa yasha, lokacin da yan dakinsu sukaje suka sami gawarshi sune suka iske sauran ruwan dayasha tare da takardar kwayar agurin.
Wannan dalilin ne yasa nace kwayar da yasha itace tayi silar mutuwarshi, amma duk da haka nace akira yansanda domin muje akaishi asibiti a aunashi akara tabbatar da dalilin mutuwarshi.
Alokacin se D.P.O yace mun shine yake kula da case din yaron, dan haka mubashi shi sukaishi asibiti domin adubashi, shine nace masa idan sunje sukawo mana copy na result din da akasamu domin mu aje a cikin file dinshi, wannan itace takardar da suka kawo.
Amsar duka takardun biyu Brr, yayi yabada aka mikama alkali. Jinjina kai yayi yace malam Naziru, idan na fahimceka kaima ka tabbatar da cewar yaron da aka kawo maka yana Shaye shaye, kuma dalilin shan wannan kwaya shine yayi silar mutuwarshi?
Kwarai ma kuwa domin duk wata sheda dazata nuna mana kwayace tayi silar mutuwarshi munsameta agurinshi. Murmushi Brr, yayi yace amma kuma amatsayinka na shugaba, meyasa ba kusa dokar hana yaranku shaye shaye acikin gidan yari ba?
Saurin kallonshi Sageer yayi, domin tambayar dayake shirin yimashi kenan idan yakirashi amma segashi Brr, Yusuf yayi mashi ita, shikanshi alkali seda ya jinjinama wannan tambaya ta Brr, Yusuf, domin duk wanda yaji yanda yake tafiyar da aikinshi yasan ba karamin lawyer bane. Idan kashigo kotun daga baya ma bazaka iya tantace wane bangare yake karewa ba.
Munajinka malam Naziru? To yallabai kasan yau ko kaine ka haifi mutum duk yanda kaso kabashi kariya sede idan be matsa daga kusa da kai ba, koda ace yau tare kuke kwana kuke yini, bazakataba shedar mutum ba.
Domin babu me iyawa da dan Adam se Allah,shiyasa arayuwa bazaka iya shedar kowa ba, koda kanka ne, domin akowane lokaci mutum yana iya canza hali. To muma haka yake agurinmu, muna iyakar kokarinmu akan yaran da nauyinsu yarataya akanmu, sede komin dabarar mu zaka iske sunfi dabara.
Duk yanda mukaso muhana abu zaka iske abun ya faskara, domin yanda kasan masu aiki da aljanu haka suke, ni har mamakin inda suke samun kayan maye nakeyi, sede gaskiya bantaba samun wanda yasha kwayar datayi sanadin mutuwarshi kamar wannan ba.
Jinjina kai kowa na cikin kotun yayi, gaba daya kan Sageer ya daure, jiyake kamar basirarshi ce Brr, Yusuf yake aiki da ita. Runtse ido kawai yayi yana karanto addu'oi.
Brr, Yusuf yace maganar ka haka take malam Naziru, wato duk yanda kaso kare dan adam bazaka iya ba, domin azamanin nan nayanzu danka ma yafika dabara, ko baka bane?
Haka ne yallabai. Mungode da wannan bayani naka malam Naziru, domin bayanine me cike da ilimi acikinsa, na tabbata mutane dayawa zasu karu kuma zasu fahimtu da wannan bayani naka. Zaka iya tafiya.
Zanso kotu tabani dama inyima mutumin da yakarbi Mannir alokacin da yansanda suka kaishi gidan yari tambaya. Kotu tabaka dama.
Baba kotu zataso taji sunanka da kuma aikinka? Sunana mal. Yusha'u, kuma ni Gandiroba ne. Shin kaine kake kan aiki alokacin da aka kawo Mannir? E nine.
Shin da aka kawoshi kasa mashi kayan gidan yari? A'a bansa mashi ba. To meyasa? Saboda yana cikin yanayin maye, kuma kafin wani lokaci yayi bacci. Da misalin karfe nawa ne yafarka?
Wajen karfe tara ne na dare. Da misalin karfe nawa aka kawoshi to? Kafin azahar. Kenan yadauki awonni dayawa yana bacci? E. Amma kai atunaninka meyasa shi yin irin wannan dogon baccin wanda kai kanka kasan bana lafiya bane?
E to idan mutum yakasance baya cikin hankalinshi dole ze iya yin fiye da irin wannan baccin, kuma alamu sun nuna ba'a hayyacinshi yake ba tun kafin ayanke mashi hukunci domin da alamu abunda yasha yadan dauki lokaci ajikinshi kafin yasashi bacci.
Kallonshi Brr, Yusuf yayi jin irin amsar daya bashi, ajiyar zuciya yayi domin acikin amsar daya bashi takusa tona masu asiri, hakan yasa yayi saurin canza tambaya. Shiko Sageer acikin bayanin da Baba yayi ne yakara samun wani abu, hakan yasa yayi saurun rubutawa.
Shin Baba lokacin daya farka kabashi riga yasa meyasa baka cajeshi ba? E to banyi tunanin za'a samu wani abu marar kyau ajikin mutumin da naji ance kwananshi kusan 2 agurin yansanda ba. Kuma daga wajensu kotu suka kaishi, kuma ana yanke mashi hukunci sune suka kawoshi nan.
Hakan yasa banyi tunanin cajeshi ba. Sosai wannan amsar da Baba yabada tayi tasiri azuciyar mutane da yawa, domin hatta da alkali seda ya duka yayi rubutu. Murmushi sageer yayi shima ya duka yayi rubutunshi.
Tsarguwa Brr, Yusuf yayi ganin yanda kowa yake kallonsu, amma dayake kwararrene, hakan yasa yayi murmushi yace, amma Baba zaka iya fada mana tayaya mutanan dasuke tsare agidan yari suke iya samun sigari?
E to bazan iya saniba, sede idan wasu ne suke kawo masu. To ashe Mannir ze iya samun kwaya a ko ina? Gaskiya bazance nasan wannan ba, tunda batare dashi muka kwana ba, bayan yatashi nakaishi dakinshi natafi.
To Baba baka hadashi kuma da kowa ba tunda naji shuganbanku yace akaishi dakin da baza'a cutar dashi ba kafin ya karasa warware wa? Na hadashi da wani yaro mesuna Kamal.
To meyasa kayi tunanin hadashi dashi? Saboda nasan baze cutar dashi ba. Da kyau, mungode da amsoshinka, zaka iya tafiya.
Zanso kotu tabani dama domin nayima Kamal wanda aka hadashi da Mannir wasu yan tambayoyi. Idan Kamal yana nan yafito gaban kotu. Tashi shugaban gidan yari yayi yace yallabai bamuzo da yaranmu wajen nan ba, sede zamu iya turawa adaukoshi.
Brr, Yusuf kajega tambaya ta gaba kafin akwo Kamal idan kana da ita. Ina da ita, yame shari'a. Zanso kotu tabani dama domin yima mutumin dayake aiki alokacin da Mannir yarasu. Kotu tabaka dama.
Kotu zataso taji sunanka da aikinka agidan yari? Sunana Gali, kuma ni gandiroba ne. Kaine wanda akace kayi aikin kwana ko? E nine. Kafin asamu gawar Mannir anbasu abincin safe?
E ambasu. Lokacin da suka karba kozaka iya gane fuskarshi tunda yakasance bako awajenku? Kwarai ma kuwa, domin nine ma nabashi abincin da kaina,to dayake dama inaso inje innemi dakin da aka kaishi domin nakirashi yazo yafadi address dinshi da shekarunshi domin ashigar acikin file dinshi, saboda lokacin da yazo baya cikin hayyacinshi.
Hakan yasa dana bashi nace yabiyoni office. To bayan kungama ina yatafi ko tare sukaje da wanda aka hadasu? A'a shikadai yazo domin sauran yaran sunagama amsar abinci idan sunci gurin aiki suke tafiya.
To bayan mungama muka fito nace mashi yatafi can wajen aikinsu idan yaje yace ma megadin wajen nine na tsaidashi, ni kuma na koma office domin inhada file din in maidama yallabai dama shine yamaidoshi ajiyan.
Kenan kaima bakasan inda Mannir yaje ba daga gurinka? Gaskiya ban sani ba, domin nayi mamaki lokacin da akace mani wai yarasu kuma adaki aka sameshi akwance. Kenan beje wajen aikin ba? Gaskiya beje ba.
Meyasa kayi tunanin duba jikinshi alokacin da akace ya mutu? Dafe kai Sageer yayi jin irin abinda Brr, Yusuf yake mashi. Tamkar yana shiga cikin kwakwalwarshi haka yakeji, seyaji dama ace shine yafara gabatar da shari'ar.
Saboda ansami kwayar da yasha adaki, shiyasa naduba jikinshi domin asamu sheda. Murmushi Brr, yayi yace kozaka fadama kotu a inda kasamu kwayar ajikinshi? E to gaskiya nayi mamakin inda nasamu kwayar, domin bakowa bane ze iya gane akwaita sede idan a injin caje mutum aka sashi sannan ze iya ganoshi.
Bayan na gama duba ko ina ajikinshi ban samu komai ba, shine naduba gajeran wondanshi anan ma bansamu komai ba, shine nacire gajeran wondon senaga wani zare daure a jikin mararshi, ina jawoshi naga wata karamar jaka, ina dubawa ciki nasamu wata takarda, bayan nacirota naduba aciki nasamu kwayar dana bama yallabai.
To dama kana tunanin samun wani abu ajikinshi da har ka iya bin har cikin jikinshi domin samo sheda? Gyara zama alkali yayi yana kallon Brr, Yusuf, duk da ba yau ne yafara shari'a ba, amma ayau yazo dawani salo wanda ze burge duk me sauraro. Shari'a yakeyi amma kamar shine yake kare masu kara.
A'a sede sabo da caje masu laifi yasa muka san duk wata ma'ajiya tasu, hakan yasa na duba ko ina ajikinshi. Jinjina kai yayi yace da kyau, mungode da amsarka, zaka iya tafiya.
Haryanzu de idan Kamal be iso ba zanso kotu tabani dama domin nayima magaifin Mannir tambaya. Kamal be iso ba, kotu tabaka dama.
Kozaka iya fadama kotu sunanka? Sunana mal. Tukur, kuma nine mahaifin marigayi Mannir. Kamar yanda kace baka yarda danka yana shaye shaye ba, kuma gashi mutane da dama sun sheda kwaya ce tayi silar mutuwar danka. Shin haryanzu kana akan maganarka ta cewar danka baya shaye shaye?
Kwarai ma kuwa. To meyasa kace haka? Saboda nine nafi kowa sanin halinshi, duk inda yake muna tare shiyasa. Mal. Tukur idan na fahimceka kanaso kace babu abinda yake rabaka da danka ko? E kusan hakan.
Kenan ba koda yaushe ne kuke tare ba? E hakane, amma rabin lokacinshi duk atare dani yakeyinshi. Kenan bazaka iya shedar komai na rayuwarshi ba? Gaskiya zan iya shedar yarona domin nabashi tarbiya me kyau.
Shin yan matan danka nawa? Tashi Sageer yayi yace inada ja yameshari'a, bekamata barrister yarika kawo mana maganar da bata da alaka da case dinmu ba. Murmushi Brr, yusuf yayi yace idan har wannan tambayar danakeyi batada alaka da wannan case din nayarda zan aje aikina.
Domin nafi karfin shekaru 20 ina wannan aikin, kuma niba dakikin lawyer bane daxan rika kawo maganar da bata cikin case dan in kawar da wata maganar. Hayaniyace tafara tashi hakan yasa alkali ya buga tebur, bayan kowa yayi shiru ne alkali yace Brr, Sageer korafi be karbu ba, cigaba da bayaninka Brr, yusuf.
Murmushi yayi yace inajinka. To gaskiya wannan bansani ba.
Kuma kace zaka iya shedar danka? E haka ne. Uhm, bazaka iya shedarshi ba matukar bazaka iya sanin komai dayake tafiya na rayuwarshi ba.
Idan har mutum ze iya shedar wani to tabbas seya san komai nashi ta yanda babu abinda za'a iya tambayarka wanda bazaka iya bada amsarshi ba. To wai ma karfe nawa yaronka yake dawowa gida da dare? Gaskiya baya wuce karfe 9 awaje.
Karfe nawa kuke rabuwa dashi kenan? E to damun tashi daga shago karfe 6 saura mukaje masallaci mukayi sallar magrib, muna tsayawa daukar karatu tare da abokinshi Qaseem har zuwa isha'i, to da munfito suke tafiya wajen firarsu.
Ko kasan inda suke zuwa fira? To tayaya ni zan sani kasan idan akace mutum ya mallaki hankalinshi baze yuwu ace kana bin diddikinshi duk inda yaje ba, wata kila akwai inda suke zuwa ko zance.
Ashe mal. Tukur maganata tafarko tana kan hanya, akan bazaka iya shedar danka ba? Shiru yayi be bashi amsa ba. Tambayarka nake ko ba haka bane? E to haka ne, a wannan bangaren bazan iya shedarshi ba, amma inde akan maganar shaye shaye ne gaskiya baya shan komai.
Shin ko zaka iya fada mana lokacin da danka ze sha lemu? To meyasa zan rika bincikar duk abinda yasha ai nasan yana da kudin siye. Da kyau, idan har bazaka iya sanin lokacin da danka yasha lemu ba, kenan bazaka iya sanin lokacin da zeje ya dauki kayen maye yasha ba. Domin akwai kimanin tsawon awanni 3 atsakaninku da kuke kasancewa ba tare ba.
Idan ko haka ne, baka da ikon cewar ga abinda danka yaci ko yasha ba a tsawon wannan awannin, idan har bazaka iya shedar shi a wannan lokacin da kukayi baku tare ba kenan bakada wata hujja dazaka iya kawoma kotu nacewar ba kwaya bace tayi sanadiyar mutuwar danka ba. Idan kuma kana da wata hujja kwakkwara kotu tanaso taganta.
Hujjata dayace wadda zata nunama kotu dana baya shaye shaye,mutum daya ne wanda yafini sanin halin Mannir domin shine wanda suke tare akoda yaushe, bacci ne kawai yake rabasu. To wanene wannan mutumin? Shine abokinshi wanda aka laka mashi sharrin cewar yakashe shi.
Mal. Tukur kotu tana amfanine kawai da shedar zahiri, amma bata amfani da abinda bata gani ba, kuma nasan da kai aka fara wannan shari'ar nasan kaji kuma kaga duk shedun da aka gabatar, dan haka abinda kotu tagani dashi zatayi amfani.
Idan kuma kanada wata shedar ka kawo. Banida wata sheda. Da kyau, Mungode da amsarka zaka iya tafiya.
Idan Kamal ya iso zanso nagabatar da tambayata takarshe yame shari'a? Munsami labarin zuwanshi, yana hanya dan haka kafin Brr, Sageer yafara nashi tambayoyin kotu tanaso zataje hutu na rabin awa domin wani dalili. Kottt!!
Haka kowa yatashi yafita yaname jinjinama kokari irin na Brr, Yusuf da iya kwarewar aikinshi. Fita su Sageer sukayi, wani guri suka samu suka zauna. Dafe kai Sageer yayi, lokaci guda yaji wasu zafafan hawaye suna sauko mashi.
Hannu Abdul yasa ya goge mashi yana fadin haba abokina, meyasa zakayi saurin karaya tun ba'ayi nisa ba? Kada kamanta kaine kake da sheda insha Allah kaine zakayi nasara. Girgiza kai Sageer yayi yace wallahi Abdul nayi loosing hope.
Naji matukar dadi lokacin da alkali yace za'a tafi hutun rabin awa da bansan yanda zanyi ba idan akace infito alakocin. Wallahi nafarajin tsoron kada inkasa cika ma Baba da Maman Mannir alkawarin dana daukar masu, inajin tsoro Abdul.
Kuka yasa kamar karamin yaro. Dafashi Abdul yayi yace zaka iya Sageer, kada kamanta munyi ma mutane dayawa alkawarin kwato masu hakkinsu, dan haka ni nasan zakayi nasara Sageer, zakayi nasara, Ko bana raye karike wannan aranka da izinin Allah kaine zakayi nasara. A wannan karon, inaso kadauki duk wata sheda da Brr, Yusuf ya gabatar amatsayin makami.
Duk abinda yafada nasan karubuta, kayi amfani dashi wajen juya duk tambayar da yayi. Ina me tabbatar maka kafin kagama tambayar mutanan daya tambaya seka girgiza tunaninshi, kuma iname tabbatar maka shine wanda ze nemi kotu tadaga wannan shari'ar. Jinjina kai Sageer yayi cike da gamsuwa , yace nagode abokina kuma namaka alakwarin bazan kara sarewa ba.
Dariya su Brr, Yusuf kawai sukeyi acikin office din wani abokinshi, D.P.O yace gaskiya abokina katafi da zuciyoyin mutane dayawa, kai hatta da alkali seda naga alamun jin dadi afuskarshi. Brr, Yusuf yace nafada maku ai, niba Dakikin,lawyer bane dazan gabatar da kowace irin tambaya da duk wani lawyer yake farawa da ita ba.
Dan haka kucigaba da bina zakuga yanda zan watse wannan shari'ar.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
Waiting for your comments👂🏻💋👄

Season 105 🖤 110
RETURN @ 1:15pm
HIGH COURT KATSINA STATE.
🏨 🏨 🏨 🏨 🏨
Shiru ne ya ziyarci kotun alokacin da alkali yashigo, bayan yazauna yace idan Kamal ya iso kotu tana son ganinshi. Fitowa Kamal yayi yana sanye da kayan gidan yari ajikinshi.
Tashi Brr, Yusuf yayi ya isa gurinshi. Kotu zataso taji sunanka. Sunana Kamal.
Shin kaine Baba Yusha'u ya hada da marigayi Mannir? E nine.
Bayan daya kawoshi wajenka,me kafahimta agareshi a tsawon zaman da kukayi dashi daga dare zuwa safiya? Babu abinda na fahimta daga gareshi se gaskiya da tsoron Allah, domin azaman da mukayi da Mannir na fahimci akwai zalinci a shari'ar da aka yi mashi.
Murmushi Brr, Yusuf yayi yace idan na fahimceka kana nufin kaima baka yarda Mannir yana shaye shaye ba ko? Kwarai ma kuwa.
Mecece shedarka? Ni banida wata sheda, sede ko makaho ya tsaya ya dubi Mannir yasan baya cinkin sahun mutanan banza, kuma shida kanshi yamun rantsuwa akan ko goro bayaci. Abu na biyu kuma dayasa nakara yarda dashi tunda aka kawoshi wajena duk inda zeje tare muke zuwa.
Lokacin da yazo ma dare yayi dazeje bandaki yayi alwala nine narakashi, bayan yagama muka dawo tare bekara fita ba seda akayi kiran asuba shima tare muka fita, muna tare dashi yana karatun Qur'ani har gari ya waye muka tafi karbar abinci wanda daga lokacin ne Gali yatafi dashi muna dawowa sede gawarshi na iske.
Shin alokacin da yashiga bandaki tare kuka shiga? A'a shikadai yashiga.
To ya akayi har ka iya shedar shi akan bakaga alamun wani abu atare dashi ba, kada kamanta wanda yasamu kwaya ajikinshi ya duba besamu ba, seda yaduba sosai sannan ya iya ganota meyasa kai kace baka yarda ba?
E to saboda bashine mutum na farko da nazauna dashi acikin gidan yari ba, matukar akace mutum yana shaye shaye to baze taba iya hakura dede na minti 30 batare da yasha ba bare kuma ace har tsawon dare guda, musamman idan akace mutum yana cikin bacin rai.
Amma banga hakan awajen Mannir ba, asalima dayatashi da asuba karatun Qur'ani ya tsayayi abinshi taya mutumin kirki kamar wannan za'ace wai yana shan muguwar kwaya wadda har tazamo mashi jiki ta yanda yawan shanta har ya jaza mashi matsala acikin jikinshi?.
Wallahi ko alkur'ani zan iya dafawa akan tabbatar ma da mutane Mannir ba mutumin banza bane, duk da bansanshi ba, haduwata dashi ta lokaci kadan ne, amma ahaka na fahimci kowaye shi.
Idan wanda ya kasa hakuri agaban yansanda yasha kwaya bayan yasan zeje yabada shedar wadan da suka kashe abokinshi kamar yanda D.P.O yace mashi. Ashe kenan baze ji tsoron shan kwaya wajen dayasan yawancin mutanan gurin suna shan abubuwa na kauda hankali ba.
Toni gaskiya banga wani lokaci da Mannir ya kebe shikadai ba bare kuma ace ya sha wani abu. Kuma idan har alokacin kwayar tana jikinshi babu dalilin daze hanashi dauka yasha domin babu wani wanda ze iya hanashi alokacin, kuma babu wanda yake kallonshi. Ina me rokon wannan kotu me alfarma data kara tsananta bincike akan laifin da aka yanke ma Mannir hukunci akanshi.
Bazance kotu batayi dede ba, domin nasan kotu tana yanke hukunci da abinda aka gabatar mata, sede iname rokon kotu data sake bincikar shedun da aka gabatar mata akan Mannir. Nagode.
Gaba daya kotun tadauki hayaniya, kowa da abinda yake fada, shikanshi Brr, Yusuf rasa abin fada yayi, domin gaba daya maganar da Kamal yayi abin dubawa ne agurin kowa, amma dayake bayaso ya nuna gazawarshi hakan yasa yayi kokarin sake ma Kamal wata tambayar.
Bayan kowa yayi shiru Brr, Yusuf ya kalli Kamal yace. Amma ko kana da shedar dazaka nunama kotu na cewar Mannir ba kwaya yasha ba alokacin da kukaje kuka samu gawarshi adaki? Gaskiya banida ita, domin bama tare alokacin.
Idan ko hakane bekamata ace ka shede shi ba, domin mutanan banza ba dole seta fuska kota halayya ake iya ganesu ba, zaman da kayi da Mannir na dare daya ne. Zaka iya zama da mutum harna tsawon shekara 10 batare da ka gama gane waye shiba.
Idan har mahaifan mutum bazasu iya tsawa su bada shedar mutum ba, ina tunanin duk duniya babu wanda yafi cancanta daya bada shedar shi, sede idan yanada mata. Dan haka ba abun mamaki bane wai dan kayi zama da Mannir na dare daya kuma be nuna maka yana shan wani abu ba.
Idan kuma kana da wata shedar dazata nuna ma kotu wannan kwayar da aka samu acikin ruwan da ya aje agabanshi ba ita bace ya sha har tazamo ajalinsa kafada. Haka zalika idan kana da shedar dazata nunama kotu wannan kwayar da aka samu ajikinshi wanine yasa mashi to ka kawo. Haka zalika idan kana da wata kwakkwarar sheda dazata nuna ma kotu takardar da likita ya rubuta akan binciken da yayi akan gawar Mannir to ka kawo. Kana da ita? Shiru Kamal yayi bece komai ba.
Malam Kamal muna sauraronka? A'a banida ita. Mungode zaka iya tafiya.
Yame girma me shari'a anan nakawo karshen tambayoyin da zanyi. Ina fatan wannan kotu me alfarma da adalci zatayi adalci akan wanda iyayen Mannir suke kara akan mutuwar dansu akarkashin mulkinshi.
Kuma ina fatan kotu zatayi duba abisa wadannan kwararan shedu dana gabatar akan cewa lallai Mannir me laifine, haka zalika muguwar kwayar daya dade yana sha itace tayi mashi illa har daga karshe tazamo ajalinsa. Daga karshe iname neman lafarmar da kotu ta wanke malam Naziru daga zargin da iyayen Mannir sukema wajen aikinshi. Nagode yame shari'a.
Komawa yayi yazauna abokanshi se bashi hannu suke suna gaisawa, mutane dayawa Brr, Yusuf yakara birgesu ganin yanda yatafiyar da aikinshi.
Bayan alkali yagama rubutunshi yace Brr, da yake kare wadan da suke kara ko kanada tambayar dazaka gabatar? Tashi Sageer yayi yace ina da ita yame shari'a.
Fitowa yayi addu'a dauke abakinshi, bayan yafito yace ina so kotu tabani dama domin nayima mal. Naziru tambaya. Kotu tabaka dama.
Mal. Naziru kamar yanda kace lokacin da aka kawo Mannir baka wajen, kuma dakazo kaduba file dinshi kaga cewar baya cikin hayyacinshi alokacin da aka kawoshi. Shin tunda kuke karbar me laifi, kataba karbar wanda akace ya aikata laifin kisan kai, kuma daga wajen yansanda aka kaishi kotu, sannan a kotu ma har aka yanke mashi hukunci baya cikin hankalinshi aka gama kuma aka kawo maku shi?
E to agaskiya banyi mamakin hakan ba, domin akwai wanda ake kawo mana ma sume, wasu kuma abuge, sede shi wannan nashi daban yake, domin kwayar dayasha da alama tana daukarshi har zuwa wani lokaci kafin tafara bugar dashi.
Amma meyasa amatsayinka na shugaba lokacin da akace za'a tafi da gawar Mannir asibiti domin gwaji baka bada daya daga cikin gandirobobinka ba suka bisu idan kai bazaka iya zuwa ba? Saboda naga case din yana bukatar yan sanda shiyasa da sukazo nabasu shi.mungode da amsarka zaka iya tafiya.
Zanso kotu tabani dama domin nayima Baba Yusha'u tambaya. Kotu tabaka dama.
Baba alokacin da Mannir ya farka daga baccin da yakeyi, bayan yadawo hayyacinshi kafin ka kaishi dakinshi kozaka iya fadama kotu wani abu daka fahimta daga gareshi, ina nufin ko akwai maganar da kayi dashi?
Kwarai ma kuwa, alokacin daya farka yatashi ne da salati abakinshi, alokacin ina zaune akusa dashi, sede abinda yabani mamaki yanda yake bin dakin da kallo, hakan yasa nace mashi yatashi yayi kokarin rama sallolin da ake binshi kafin nakaishi dakinshi. Kallona yayi yace dan Allah meyake faruwa dashi kuma inane nan?
Alokacin ne nafada mashi cewar yasha kwaya ya bugu har aka yanke mashi hukunci kuma yakasa musa abinda alkali yatambayeshi hakan yasa aka yanke mashi hukuncin daurin rai da rai agidan yari sanadiyar kashe abokinshi dayayi. Lokacin danake fada mashi haka naga firgici a idanunshi.
Kuma ya tabbatar mani dashi be kashe abokinshi ba, yasan de yaje yafadama yanda wani yakashe mashi aboki kuma D.P.O ya ajeshi a wajensu daniyar kada wanda yakashe abokinshi shima yazo kasheshi tunda yace shikadai ne yagansu.
.................................................
Labarin duk abinda Mannir yafada mashi akan yanda sukayi da D.P.O yabasu. Bayan yagama bani wannan labarin nace mashi amma meyasa yasha kwaya bayan yasan zeje kotu yabada sheda akan abokinshi? Shine yacemun wallahi tunda yake ko goro betaba ci ba bare sigari har azo ga maganar kwaya. Shide abu daya yasani kafin sutafi yaci abinci kuma yasha ruwan da D.P.O yabashi, tundaga lokacin bekara sanin me akeba se yanzu daya farka.
Hayaniya ce tacika kotun, cikin D.P.O banda kara babu abinda yakeyi shikanshi Brr, Yusuf seda yaji wata zufa tafara zubo mashi, amma sanin kotu bata amsar shedar baki yasa hankalinshi yadan kwanta.
Sageer yace kenan kaima Baba baka yarda Mannir ze iya shan wani abuba? Gaskiya banyarda ba, domin ko yaro na dana haifa bazan iya shedarshi kamar yanda zan iya tsayawa agaban kotu zan iya dafa Kur'ani ma akan cewar Mannir baya daya daga cikin irin mutanan dana saba zama dasu wajen aikina masu shan irin wadan nan mugayen abubuwan ba. Jinjina kai Sageer yayi yace mungode zaka iya tafiya.
A message Brr, Yusuf ya turama D.P.O cewar yatashi yabar kotun yasan akowane lokaci Sageer ze iya kiranshi kuma basu shiryama hakan ba, ya tafi idan an nemeshi yasan mezece. Sajan Shehu kuwa tunda Baba yabada labari yake kallon D.P.O yana kallon lokacin da yashiga damuwa, kuma akan idonshi yaga yatashi yafita wanda bakowa ne ya lura da hakan ba. Murmushi yayi yajuya yacigaba da sauraron Sageer.
Inaso kotu tabani dama domin nayima Gali wasu yan tambayoyi. Kotu tabaka dama.
Mal. Gali amatsayinka na tsohon ma aikaci agidan yari, meyasa lokacin da ka gama karbar bayanan Mannir baka rakashi wajen dasuke aikin ba? ko kuma kasamu wani yarakashi wajen ba tunda kasan sabon zuwa ne besan ko ina ba?
Hadiyar miyau Gali yayi yace na'am? Sageer yace nasan kaji abinda nace ai. Sosa kai yafara yana yan mazurai, dafe kai Brr, Yusuf yayi ganin yanda Gali yakeyi, sam yamanta be fada mashi abinda yakamata yace idan Sageer ya kirashi ba, wannan karyar dayayi dazu ita kadai ya fada mashi domin yasan kotu da mutane zasu gamsu da abinda yafada.
Muna sauraronka Mal. Gali? To wallahi kasan dayake lokacin tashina yakusa, kuma da muka fito duk yaran suntafi can wajen aiki shiyasa nace mashi yatafi wajen aikin.
Shin da kace mashi yatafi wajen aiki ko kayi mashi kwatancen wajen? E to wallahi mantawa nayi shiyasa banyi mashi kwatance ba kawai nace yatafi wajen aiki.
Mal. Gali lokacin da Mannir yaje office dinka da kofin kokon da aka bashi, acan yashanyeshi ne? Kwarai kuwa acan yasha hadama biredi na bashi ganin kamar yanajin yunwa. Kenan acan yabar kofin yatafi? E acan yabarshi dan bayan nadawo naganshi nace idan sun dawo zansa abokin aikina ya kai mashi.
To da wane kofi aka samu ruwa me dauke da kwaya adakinsu? Ai inajin wannan kofin da yasha koko shine yadauraye yazuba ruwan aciki. Surutu ne yafara tashi kasa kasa acikin kotun jin abinda Gali yace.
Murmushi Sageer yayi yace amma ya akayi kuma kofin da aka barshi a office aka iya samunshi adaki? Yauwa, mantawa nayi, ashe dana koma naga yabarshi shine nayi saurin kiranshi nabashi abinshi. Sosai abinda Gali yafada yakusa bama mutane dariya.
Saurin tashi Brr, Yusuf yayi yace yame shari'a inaso lawyer ya gyara tambayarshi domin acikin tambayarshi yana rudar da wanda yake tambaya kuma hakan baya cikin tsarin doka. Sageer yace yame shari'a abinda na tabbatar ne kuma nagani shine abinda nake tambaya.
Korafi be karbu ba, cigaba da tambayarka Brr, Sageer. Komawa Brr, Yusuf yayi jiki asanyaye yazauna, zuwa yanzu kanshi yafara daukar zafi, domin yanda yadauki shari'ar ba ahaka tazo mashi ba, yana rai nata se kuma gashi tanaso ta dawo masu da hannun agogo baya.
Mungode Mal. Gali zaka iya tafiya. Zanso kotu tabani dama domin nayima Kamal tambaya. Kotu tabaka dama.
Kamal shin acikin dakinku ko akwai irin kofin da aka samu ruwan kwayar da akace Mannir yasha? Gaskiya bamuda irin wannan kofin, asalima kowa da kofinshi yatafi wajen aiki bayan mun karbi abinci, kuma wannan kofin da aka samu adakinmu ba irin wanda aka zubama Mannir Koko bane, ni ban ma ga kofin daya tafi dashi ba.
Mungode zaka iya tafiya. Zanso kotu tabani dama insake yima Baba Yusha'u wata tambaya guda daya. Kotu tabaka dama.
Baba alokacin daka anshi aiki da safe, shin me kasamu acikin office dinku? Nasamu biredi akan tebur da kuma kofi wanda aka sha koko aciki. Mungode zaka iya tafiya.
Zanso kotu tabani dama domin inyima inspector Salis tambaya. Kotu tabaka dama.
Inspector Salis ko kana cikin yansandan da sukaje daukar gawar Mannir domin akaishi asibiti gwaji? E ina cikinsu.
A wane asibiti kukaje? A general hospital ne. Lokacin da kukaje gurin wane likita kuka kaishi? Alokacin da mukaje yallabai yace babu wanda ze dubashi ajira yakira likitan daya saba dubashi yana zuwa.
Bayan yazo shin da kai aka shiga? A'a. To meyasa baka shiga ba amatsayinka na babban dan sanda acikin wadan da kukaje? Saboda yallabai ne yace bayaso kowa yashigo mujirashi awaje.
Shin bayan anshiga dashi office din likita kuna tsaye abakin kofar har aka gama komai? Kwarai kuwa ina zaune akujerar datake kallon kofar tayanda duk wanda zeshiga koze fita sena ganshi.
Bayan sun shiga babu wanda yafito ko zuwa wani waje? E to naga likita yafito yaje motarshi yadauko wata takarda, kuma yana komawa D.P.O yafito muka tafi.
Takardar shedar awon da aka mashi typing dinta akayi ko kuma da biro likita ya rubuta bayanin? A'a typing dinta akayi.
Duk kuna zaune a wajen akayi typing dinta har akayi printing? E muna wajen sede bamu dade muna jiransu ba suka fito angama komai. Mungode zaka iya tafiya.
Zanso kotu tabani dama inyima likitan daya duba gawar Mannir tambaya. Kotu tabaka dama.
Cikin likita ne yafara kara, sam beyi tunanin za'a nemeshi ba, shi kanshi Brr, Yusuf seda yadan tsorata da kiran likita. Umar kuwa yagama sarewa da asirinsu yakusa tonuwa.
Dr, kaine ka auna gawar Mannir ko? E nine. Dama aka idar asibiti idan aka kawo gawa likita daya ne yake aunata? E to yadanganta idan yakasance likitan shine akan aiki ze iya dubata idan har anzo da yan sanda.
Lokacin da aka kawo gawar Mannir, kana cikin asibitin? A'a inade kan hanyar zuwa. Kuma babu kowane likita a asibitin? To wallahi ban sani ba, ina tunanin saboda nine likitanshi shiyasa suka jirani.
Ka kai shekara nawa kana duba lafiyar Mannir? Bamu dade ina dubashi ba, lokacin da aka kawoshi gurin yansanda dana duba tambarin hannunshi shine D.P.O yace yana shan kwaya dan abuge yazo wajenshi shine ni kuma naduba lafiyarshi.
Dama kawai ana duba lafiyar mutum batare da shine ya so hakan ba? Tashi Brr, Yusuf yayi yace yame shari'a kada lawyer ya manta shi likita yana bin umarnin dan sanda ne kawai, domin shine ya kai mashi Mannir domin yayi bincike akanshi.
Sageer yace ai ba bincike aka kai Mannir ba, asalima D.P.O yasheda ma kotu shine yasamu yadauki hoton tambarin hannaun Mannir kuma ya kaima likita ya auna amshi. Acikin bayanin da D.P.O yayi babu inda ya nuna cewar yaje da Mannir wajen likita kafin yakawoshi kotu.
Korafi be karbuba, cigaba da tambayarka Brr. Cike da tashin hankali Brr, Yusuf yazauna, sede dayake kwararran lawyer ne, babu wanda ze iya fassara abinda yake kan fuskarshi.
Muna jinka Dr? Shiru yayi bece komai ba. Kenan baka taba duba Mannir ba se akan gawarshi? Hannu yasa ya goge zufar datake zubo mashi yace haka ne.
Amma a ina aka samu report din da akace daga wajenka yafito amatsayinka na likitanshi wanda kabada aka saka acikin file dinshi na gidan yari ko bakai bane ka rubutashi? Nine. Amma alokacin da D.P.O yake fada mani yana shan muguwar kwaya domin har yana gurinshi ba'a cikin hayyacinshi yake ba, shine narubuta wannan takardar domin abashi kila tazamo abun tsoratarwa awajenshi yadena shanta.
Kenan da ka rubuta report din baka aunashi ba? E haka ne, amma ai temakon musulunci nayi, wanda musulunci ya yarda kayi karya dan ka kare wani daga shiga halaka.
Da kyau, gaskiya Dr, kayi kokari kuma kayi temako. Amma kana da printer a office dinka? A'a banda ita sede idan nayi typing ayo mani printing.
To dama idan kuka duba mutum dole se kunyi typing sannan kuke bashi result? Ba dole bane. Amma ya akayi takardar shedar abinda yayi sanadiyar mutuwar Mannir takasance wadda akayi typing ce?
Saboda D.P.O yace mani za'a kai gidan yari asa cikin file dinshi shiyasa. To dawane lokaci kabada akayi maka printing dinta bayan kuma inspector Salis yace suna zaune awajen babu wanda yaje wani guri se kai daka dauko takarda amota? Shiru yayi bece komai ba.
Muna jinka Dr, ya akayi haka tafaru? Kasa yayi da kanshi yakasa magana. Murmushi Sageer yayi yace mungode zaka iya tafiya. Zanso kotu tabani dama inyima D.P.O tambaya. Kotu tabaka dama.
Tashi Brr, Yusuf yayi yace yame girma meshari'a D.P.O dashi aka fara wannan shari'ar, sede yana cikin sauraran shari'ar ne yasamu waya daga iyalanshi cewar an kai medakinshi asibiti zata haihu kuma aiki za'ayi mata ana bukatar sa hannunshi shine yayi gaggawar tafiya.
Ina neman alfarmar wannan kotu me albarka data daga wannan shari'a zuwa wani lokaci nagode. Rubutu alkali yayi yace wannan kotu ta daga sauraron wannan shari'a zuwa ranar alhamis 2 ga watan satumba shekara ta 2016. Tebur yabuga akace kotttt!!!.
Abdul ne yazo ya rungume Sageer yana dariya, yana fadin dama nafada maka zaka iya abokina, kana da Allah, kuma kamika al'amuranka agareshi nasan zetemakeka kafisu sheda insha Allah kaine zakayi nasara akan wannan case din.
Dariya Sageer yayi yana fadin haka ne abokina, naji nutsuwa ayanzu, zan iya gogawa da kowa, maganarka ta tabbata, na karyar mashi da zuciya, nasashi neman daga shari'a, nafara sasu guduwa domin tsoron tambayata, zamuyi nasara abokina.
Dariya suka sa Salis yabashi hannu suka gaisa suka fita.Haka mutane da yawa suka rika taya Sageer murna. Brr, yusuf dashi da jama'arshi kuwa babu wanda ya tsaya jiran wani abu haka suka fita kowa da abinda yake sakawa.
*********
Gidansu Anwar cike yake da murna saboda dawowar Zaituna bayan ta kammala karatunta na school of nursing, duk da itama bataji dadin abinda yafaru ba, amma tasan dalilin dayasa Abbansu ya saki Aunty, hakan yasa ta aje damuwarta agefe domin samun farin cikinsu.
Ilham kuwa tuni tadena damuwa domin tana samun kulawa sosai agurin Umma, duk wata kulawar da bata samu agurin Aunty itace Umma take kokarin nuna mata, hakan ne yayi tasiri azuciyarta har tasamu zaman farin ciki agidan.
So daya Anwar ya kaita kaduna wajen Aunty, kwananta 2 acan, sosai Ilham taji tausayin Auntynsu, ganin yanda takoma duk da gidansu ba talakawa bane amma rashin kwanciyar hankali da tunani sune suka sa ta canzawa.
Sosai Aunty tayi nadamar abubuwan tada aikata. Duk yanda Ilham taso tafada mata dalilin dayasa Abba yasaketa amma sam taki bata amsa, daga karshe ma Aunty ta kalleta tace Ilham, idan nafada maki wata magana zaki amince da ita? Kai tadaga mata.
Ilham nasan kina da ilimin addini, kuma kinsan ba'a son tsananta bincike akan komai, idan har kinyarda dani inaso daga yau kirufe wannan maganar, banaso ko bayan yayarki tazo hutu ki tambayeta komai, kuma banaso ki kara tambayar kowa akan wannan dalilin inaso kibar wannan maganar akan Allah ne yakawo karshen zamana da Abbanku.
Goge kwallar data zubo mata tayi tace shikenan Aunty ina me tabbatar maki daga yau nadena wannan maganar kuma ina rokon Allah yakawo maki ranar da farin cikinki ze dawo gareki wannan shine fatana. Rungumeta tayi suna kuka.
Bayan tayi kwana 2 Anwar yazo daukarta shima seda yakawo mata kayayyaki sosai tayi murna da zasu tafi yakawo kudi masu yawa yabata, haka suka tafi Ilham tana ta kuka, shima Anwar seda yaji idanuwanshi sun kawo ruwa haka suka tafi.
Zaune suke a office din Brr, Yusuf gaba dayansu hankalinsu atashe yake, D.P.O ne ya kalli Brr, yusuf yana goge zufa yace yallabai gaba daya hankalina yatashi, wallahi ina tsoron ranar da za'a koma kotu, ina tsoron tambayoyin yaron nan masu firgitarwa.
Likita yace dole kaji tsoron haduwarka da Sageer, wallahi idan na kalli idonshi tsorone da firgici suke kamani, a duk lokacin da yayi mani tambaya jinake gaba daya basirata ta bace, dan Allah yallabai kada kabari yaron nan yakara halartar kotun nan dan Allah.
Tashi Brr, Yusuf yayi yana zagaye yana fadin tabbas sena nunama Sageer koni waye, hakika seyayi dana sanin shigarshi aikin lawyer, sena jefashi cikin tashin hankalin da tunda Uwarshi ta haifeshi betaba fadawa ciki ba.
Wallahi! wallahi! wallahi se Sageer yaji yatsani aikin lawyer. Umar dauko mani wannan file din dana baka ka saka mani cikin drower domin mu konashi kada ma shari'a tabiyo takanshi dan yanzu nadena yarda da Sageer domin alokacin da mukayi wannan case din muna tare dashi, Allah kadai yasan abubuwan dayasamu daga garemu, duk da bana aiki dashi alokacin amma dole musashi cikin zargi kodan mukare kanmu.
Tashi Umar yayi yanufi drowar da yasaka file din, bayan yadauko D.P.O yace yauwa jeka yanzu base anjima ba ka konashi. Brr, Yusuf yace miko munshi nan, koda yakasance nine nabaka ka ajeshi dole naduba saboda na dasa zargin Sageer azuciyata dan haka bazan kara yarda da komai na cikin office din nan ba.
Cike da tashin hankali Brr, Yusuf yace D.P.O menake gani haka? Dama photocopy ka kawo mana? Saurin tashi sukayi Suna fadin photocopy kuma? Kwarai ma kuwa gashi nan kugani. D.P.O yace wallahi ta gaskiyar ce nabaka kuma kaima ai kagani tunda seda ka karanta ko.
Jinjina kai Brr, Yusuf yayi yace ai dama nafada, Sageer ya dade yana bibiyarmu, haka zalika seda yashirya sannan ya tado wannan case din, babu wani mahaifin Mannir daya tadoshi, shine ya tsara komai.
Dan haka dole kafin alhamis dole musan duk yanda zamuyi musamo duk wata sheda da Sageer ze gabatar da ita akotu, inaso musa shi yaji kunya agaban jama'a, inaso kotu ta soke lasisin shi, inaso mutane suyi masa tsana da har abada baze kara marmarin komowa aikin lawyer ba.
D.P.O acikin yaranka akwai inspector Salis dan gidan ma aikacin prison, tabbas zuciyata tana bani yana tare da Sageer domin amsoshin daya bayar akotu sun tabbatar yana bayan Sageer, hakika dole kasa ido akanshi ina jin tsoron kada yasamu wasu bayanan sirri daga gareka yabama Sageer.
Gaba dayansu sun rude, hankalinsu yatashi Umar kuwa kuka kawai yake domin yasan idan har asirinsu yatonu gaba dayan su suna da hakki akan kisan Mannir tunda sune suka tsara hakan.
Brr, Yusuf yace inaso ku kwantar da hankalinku, yanzu ba lokacin damuwa bane, lokaci ne daya kamata muzauna muyi tunanin mafita, idan har munaso mucigaba da rayuwa cikin farin ciki dole mu kawar da duk wata matsala dazata zefamu cikin damuwa kai koda takama mukashe sageer wallahi ashirye nake.
Tunda nake aiki bantaba samun karamin lawyer daya caza mani kwakwalwata lokaci guda ba kamar Sageer. Akwai abokinshi Abdul, duk duniya shi kadai ne abokinshi dayafi yarda dashi, kuma nasan shine kadai yasan inda ya aje duk wasu shedunshi, kuma agida daya suke zaune dashi kunga dole semun samu kan Abdul zamu iya komai cikin sauki.
A duniya babu abinda mutum baze iya aikatawa saboda kudi ba, idan har za'a iya samun mutumin daya kashe mahaifinshi badan komai ba sedan ya mallaki dukiyarshi, ashe kuwa kowa ze iya komai dan yasamu kudi.
Haka zalika idan har kanaso kasamu sauki akan makiyinka, dole seka samu najikinshi shine kadai ze iya yimaka aiki cikin sauki, dan haka inaso Alh, Abbas yasamu labarin za'a maido shari'ar da danshi yayi kisa aranar alhamis, kunga dole yakawo kudi matukar yanaso danshi ya kubuta, da wadan nan kudin ne zamuyi amfani domin mu mallaka ma Abdul duka, nasan shidin talaka ne, ganin kudi masu yawa zesa yabamu goyon baya.
Sosai suka gamsu da shawarar shi, likita zeyi magana sukaji ana kwankwasa kofa. Hankalinsu ne yatashi kada ace wanine yake labe yana jinsu. Umar ne ya bude kofar domin ganin ko waye. Sajan Shehu ne tsaye abakin kofar.
Da sauri D.P.O yataho yana fadin bakada hankali ne zaka biyoni har nan? Idan nemana akeyi bazaka iya kirana awaya ba? Sara mashi yayi yana fadin kayi hakuri yallabai, wani abune nake tafe dashi me muhimmanci, yadade awajena alokacin banyi tunanin sanar da kai ba,amma ayau danaje kotu nagane kome abun yake nufi.
Brr, Yusuf ne yace yashigo,kallon Umar yayi yace kaleka idan Bala yana nan kace yatafi gida, kuma kada kadawo harse kaga tafiyarshi, domin shima banyarda dashi ba. Fita Umar yayi yasamu Bala a office dinshi yace yallabai yace katafi gida.
Cike da tashin hankali Bala yace inafatan de ba sallamata yayi ba? Umar yace a'a kawai yace katafi gobe kadawo, ajiyar zuciya Bala yayi, ba haka yaso ba, yaso ya karasa jin abinda suke fada, musamman da yaga wani dan sanda yazo yanzu kuma yashiga ciki. Tashi yayi yahada kayanshi yatafi domin ya kaima Sageer sabon rahoto,seda Umar yaga barinshi wajen gaba daya sannan yakoma.
Lokacin daya koma ya iske tashin hankali karara afuskarsu kuma ga waya a hannunsu suna kallo, matsawa yayi domin shima yaga abinda suke kallo. Shehu yace wallahi yallabai tunda naga wannan abun babu wanda na nuna mawa, kuma ganin Bukar yana munafuntarka yasa nayi alkawarin fada maka domin kayarda dashi sosai.
Tashin hankali wanda ba'a samashi rana, D.P.O gaba daya rigarshi tajike da zufa, sam yakasa magana ma, Brr, Yusuf ne yayi karfin halin fadin mungode maka, kuma iname tabbatar maka da zaka samu kyauta me tsoka saboda wannan abun dakayi, hannu yasa ya goge vedion yace ka tabbata wannan ce kadai vedion baka turama kowa ba?
Shehu yace wallahi babu wanda natura mawa. Bude dirowa Brr, yayi yadauko kudi kusan dubu hamsin yamika ma Shehu yana fadin karbi kafara rike wannan, idan komai ya kammala zakaga babban sako, hatta da matsayi se ka kara samu. Kuma inaso kada kafada ma kowa wannan maganar, zaka iya tafiya. Godiya yayi masu yafita cike da murna domin yasamu abinda yake tunani dan yasan shima Bukar kila yayi ne dan ya nunama Yallabai yasamu kudi ta hakan shiyasa yarigashi.
Kuka D.P.O ya farayi kamar karamin yaro, murmushi Brr, yayi yana fadin haba abokina kada kabada ni mana,ai wuyar abun ace bamu samu wannan labarin ba, kaga kuwa yanzu tunda munsameshi dole musan abinyi.
Inaso kasa a kamo maka Bukar,ka tambayeshi iya mutanan daya turama wannan vedio, idan yaki fadi ayi mashi azaba mezafi wadda zata sashi dole yafada, duk wanda yasan wannan sirrin dole ya fuskanci hukunci koda kuwa yakama na mutuwa ne.
Tashi likita yayi cike da damuwa yace haba yallabai, wai wace irin zuciya gareka haka? Bakajin tsoron Allah ne? Rayukan mutane fa kake cewa akashe, baka tunanin kaima zaka mutu? Wallahi nayi danasanin haduwata da ku,kuma iname tabbatar maku idan har naje kotu zan fidda kaina, nasan hukuncina karami ne domin bantaba bada goyon baya wajen kashe wani ba.
Murmushi Brr, yayi yace Dr, kaine kasan wani abu waishi tausayi, arayuwata idan har zan samu kudi ban damuwa da kowa, idan ta kama nakashe kodan intsira da mutuncina da kuma dukiyata, bandamu da wani ya mutu ba idan harni zan rayu.
Dan haka ka kula da kanka, nibazan kashe kaba, amma tabbas idan har kaje kotu kafadi wata magana wallahi sena karar da iyalanka, kuma kasan zan iya, kaga koda an daureka kafito bazaka cigaba da zama da iyalanka ba. Katashi kafita banason kara ganin kafarka.
Tashi Dr, Yayi cike da tsoro yafita. Umar yace amma yallabai baka ganin ze iya tona mana asiri? Murmushi yayi yace nasan halin Dr, yanada matukar tsoro ina nan dakai baze kara zuwa kotu ba sede idan ance ana nemanshi, kuma koyaje baze iya fadar komai ba.
Dafa kafadar D.P.O yayi yace ka kwantar da hankalinka, bazan taba karaya a wannan shari'ar ba, tare muka fara wanna aikin kuma tare zamu tsira. Daga yau kada mukara haduwa anan, domin yan sa ido suna dayawa, akwai gidan gonata acan zamu rika haduwa, kuma inaso ayau kasa akamo Bukar.
Shi kuma Abdul zanji dashi, ayau zan samu kudin dazan bashi. Kai kuma Sageer kajirani inazuwa kanka.😡

0 comments:
Post a Comment