A jiyar zuciya Bukar yasaki alokacin da aka cire mashi kyallen da aka rufe mashi fuska dashi, motsawa yayi amma yajishi daure a saman kujera, salati yafarayi domin yasan yafado hannun masu satar mutane.
Saurin runtse ido yayi alokacin da aka bude kofar dakin dayake ciki, haske ne ya gauraye dakin, dariyar dayaji ce tasa shi saurin bude ido. Cak numfashin shi ya tsaya nadan lokaci kadan sakamakon abinda idanuwanshi suka nuna mashi.
D.P.O ne yashigo yana dariya tare da wasu manyan maza. Kujera yajawo ya zauna, kallon Bukar yayi yace barka da war haka sarkin cin amana. A tunaninka nidin dakiki ne dazan kyaleka kana bibiyata ban dau mataki ba?.
Kawai nabarka ne saboda nafiso se dubunka tacika sannan na nuna maka asalin halina. Bukar kadade kana munafunta ta bayan ni kuma nayarda da kai, ashe dama zaman da kake a office dina kana yinshi ne domin kaga karshe na? Kuka Bukar yasa yana fadin dan Allah kayi hakuri wallahi daga yau nadena.
Murmushi yayi yace idan nayarda kadena, zaka iya fada mani iyakar mutanan daka fadama sirri na? Bukar yace ni babu wanda nataba fada ma sirrinka. Hada vedion daka daukeni a office? Hadiyar miyau Bukar yayi yana zare ido.
Matsowa D.P.O yayi yakama wuyanshi yana fadin wallahi zan iya kashe ka matukar baka fada mani wadan da katura ma wannan vedion ba. Bukar yace ni babu wanda natura mawa kuma tana nan awayata zaka iya dubawa ka goge.
Duk yanda D.P.O yayi amma Bukar yaki fada mashi wadan da yatura mawa, yaranshi yasa suka mashi dukan tsiya duk suka fasa mashi jiki amma yaki yafadi. D.P.O yace nasan dole ka nuna ma Sageer, inaso kafada mani sauran hakan zesa na kyaleka amma idan baka fada mani ba, bazan kashe ka cikin sauki ba.
Bukar yace yallabai ba karya na maka ba, babu wanda yasan da wannan maganar. Hada sajan Shehu? Wallahi yallabai bantaba maganarka ta sirri da Shehu ba kayarda dani. Amma ya akayi nasamu vedion dakayi mani awayarshi?
Shiru Bukar yayi yana tunani, can yace natuna wallahi rannan nabashi yatura film ina tunanin alokacin yaturashi. Wani daga cikin yaran yace Yallabai wannan mutumin yana bata mana lokaci fa, kuma kasan bamu da wani lokaci me yawa, kawai muje ga zabi nagaba.
Murmushi D.P.O yayi yace mikomun wannan karfen, zare ido Bukar yayi jin an fadi karfe, wani karfe ne me tsini aka miko mashi, yana amsa ya dorashi saman hannun Bukar wanda yake daure a jikin hannun kujera.
Inajinka fada mani? Yallabai kayarda dani gaskiya nake fada maka. Wani irin ihu Bukar yasaki alokacin da aka caka mashi karfen asaman hannunshi wanda seda tsinin ya nutse duk acikin hannunshi.
Cike da wahala yace zan fada wallahi zan fada. Inajinka, Sageer ne da abokinshi se Yallabai Salis su kadai ne sukasan da wannan maganar, kuma vedion tana wayar Sageer. Se kuma wa? Sukenan yallabai. Karya kakeyi kafada mani ko kuma incire maka yatsu.
Wallahi da gaske nake maka. Wata sabuwar wuka yadauko, babu tausayi yasata yacire mashi yatsu biyu. Ihu kawai Bukar yakeyi saboda tsananin azaba, jini duk ya bata wajen. Ina jinka kafada mani duk abinda kasan sun fada nasan dole kana wajen lokacin da sukaga vedion me sukace zasuyi da ita?
Shiru Bukar yayi saboda azaba, dayan hannunshi yakamo ze cire mashi wasu yatsun, Bukar yace dan Allah katsaya zan fada maka komai..................... Duk tattaunawar dasukayi agabanshi seda yafada, daga karshe yace amma duka shedun basa hannun Sageer ya kaima budurwarshi ajiya vedion ce kawai take hannunshi, dan Allah kayi hakuri kada ka kasheni iyalina zasu shiga damuwa.
Tashi D.P.O yayi yana huci, wayarshi ce tayi kara yana dagawa yaga Brr, Yusuf ne. Bayan sungama gaisawa Brr, yace akwai wani abu da aka asamu? D.P.O yace kwarai ma kuwa, abinda Bukar yafada mashi yafada masa. Brr, yace kutafi dashi ya nuna maku gidan yanzu idan yaso zuwa dare kasan yanda zakayi yaranka su karbo komai dayake wajenta.
Kuma shima kada ku sakeshi harse angama wannan case din. D.P.O yace angama yallabai. Yana kashe wayar yace ku kwanceshi kusashi mota, inaso kutafi dashi ya nuna maku gidansu yarinyar, sannan kumaido shi nan, inaso kusamashi tsoro sosai. Kai Bukar yasunan yarinyar? Shiru yayi can yace Saddika.
Murmushi yayi yace da kyau, kaga yanzu karasa yatsunka biyu, gobe ma idan akace karika daukar sirrin wanda ya amince maka se ka kara, kuma daga yau na koreka daga aiki. Fita yayi yana fadin idan kun kammala komai kufada mani ta waya.
A lokacin da Bala yaje shagon Abdul, duk abinda yaji suna fada seda yabasu labari, Bala yace wallahi Sageer mutanan nan basuda imani, basu dauki ran dan adam abakin komai ba. Sude idan zasu rayu basu damu kowama yamutu ba.
Abdul yace karabu dasu duk abinda suke dashi munfisu domin su shedan ne azuciyarsu mu kuma Allah mukasa acikin tamu. Dan haka kada kadamu Baba zanje gurinsu idan suka bukaci hakan, nasan zuwana zekara samoma abokina wata shedar.
Girgiza kai Sageer yayi yace banyarda kaje ba abokina, idan kuma suka canza wata shawarar fa? Gaskiya banyarda ba, zasu iya cutar da kai. Abdul yace wallahi senaje, kada kamanta yanda zaka iya bada ranka awannan case din nima haka yake awajena, dan haka kabarni koda ace wannan shedar dazan samo maka itace numfashina nakarshe senaje.
Matsowa Sageer yayi yakamashi yace Abdul dan Allah kada kaje, Bala yace Sageer tunda yace zeje kabarshi, addu'a itace abinda zamu bishi da ita. Katashi kabar shagon nan nasan yanzu zasuzo nemanshi banaso suganka awajen suna iya fasa abinda zasuyi kaga zaka rasa damar shedar dazaka samu.
Tashi Sageer yayi yana goge hawayen dasuka zubo mashi yana fadin shikenan Abdul kaje, Allah ya tsaremun kai, murmushi Abdul yayi yace amin abokina babu abunda ze sameni ma insha Allah. Tashi sukayi shida Bala suka tafi.
Suna fita motar su Umar tana tsayawa, tareda Brr, Yusuf suka shiga shagon Abdul, bayan sun gaisa Brr, Yusuf yace nasan ka shedani ko? Abdul yace kwarai kuwa nashedaka Brr, Yusuf. Murmushi yayi yace kwarai ma kuwa.
Abdul ko? Kai yadaga mashi, zama yayi yana fadin wata muhimmiyar magana nazo muyi da kai domin nasan kaine babban aminin Sageer, amma idan badamuwa muje cikin mota muyi magana saboda mutane.
Abdul yace badamuwa bara nayima wani yaro magana seya duba mani shagon. Fita yayi, murmushi Brr, yayi yace nasan zeyarda, kalli wannan marayan shagon nashi wanda gaba daya jarin ciki be wuce dubu 50 ba.
Zaune suke acikin mota, Abdul ne agaba se Umar yazauna baya, gaba daya glass din motar azuge yake. Tun kafin su shiga Abdul ya danna recording awayarshi yasata aljihu. Shiru Brr, yayi can kuma yace Abdul wannan shagon naka ne? Abdul yace kwarai kuwa nawane Brr, Yusuf.
Murmushi yayi yace sunan yana burgeka ne kake maimatashi haka? Murmushi yayi yace kwarai ma kuwa, shiko Abdul yayi hakane domin asan cewar dashine suke magana. Brr, yusuf yace da kyau. Shekararka nawa kana zaune ashagon nan? Abdul yace nakai shekara 3.
Brr, yace gidan da kake zaune naka ne ko haya kakeyi? Abdul yace haya nakeyi. Shin kana da mashin na kanka? Banida shi. Jinjina kai Brr, yayi yace shin kanajin dadin zaman da kake acikin talauci haka? Abdul yace inaji mana tunda halak dina nakeci.
Amma idan arziki yazo maka wanne zaka zaba atsakanin talauci dashi? Abdul yace ai bani ba, duk duniya babu wanda ze dauki talauci yabar arziki idan har yakasance na halak,ne. Brr, yace Abdul shin menene aikin halak?
Abdul yace duk wani aiki da mutum zeyi da karfinshi koda jikinshi kuma abiyashi wanda yakasance ba sata yayi ba hakkinshi ne aka bashi wannan shine aikin halak. Yanzu idan nabaka aiki kamun nakawo kudi nabaka na biyaka halak dinka?
Abdul yace idan aikin dazan maka naji bana sata bane zan iya yinshi kuma idan kabani kudina zan karba. Wato kaide Abdul sata kawai kafi tsana? A'a duk wani aiki inde na sabon Allah ne ina tsoronshi.
Haka ne, aini ba aikin sabon Allah zan saka ba, aiki ne zakamun inbiyaka makudan kudin dazasu fitar da kai daga wannan talaucin da kake ciki. Kudin dazasu sai maka gidan da kakeso, su saya maka mota, sannan su isheka ka bude babban shago. Inafatan zaka iya?
To Brr, ai baka fadi aikinba bare insan kozan iya. Bawani aiki bane natada hankali, kuma ba aikin karfi bane, aikine da zaka yishi acikin mintuna 5, kai kuma kasamu naira million 5. Murmushi Abdul yayi yace amma zanso inji wannan wane irin aiki ne haka me sauki.
Bawani aiki bane, inaso kadauko mani duk wata sheda da kasan abokinka Sageer yana da ita wadda zeshiga kotu da ita ajibi. Sannan akwai wata takarda daya dauko ta aoffice dina, idan ka duba zakaga takardar asibiti ce ta hoton sahun hannun wani da aka dauka na yatsunshi. Inaso ka taho mani da ita, sannan acikin wayarshi akwai wani vedio na D.P.O inaso ka gogeshi. Wannan shine kadai aikin da zakamun.
Jinjina kai Abdul yayi yace lallai Brr, Yusuf wannan aikin naka shine aikin danafi sani arayuwata wanda yafi komai wahala, aiko aikin fasa dutse arana be kaishi wahala ba,domin shi iyakar wahalar da mutum zesha kawai ta lokaci gudace, daya sha magani yayi wanka yayi bacci zata tafi.
Amma wannan aikin da kakeso nayi maka aikine na cin amana, ha'inci, zamba cikin aminci, yaudara da kuma zalunci. Kasan kuwa acikin wadan nan abubuwan akwai alamomin munafuki acikinsu? Dan haka kayi hakuri, nibazan iya goyon bayan zalunci ba, kaima kuma da ka kasance daya daga cikinsu ina me tabbatar maka a komawarku kotu ta karshe wallahi sekaji kunya agaban jama'ar da suka yarda da kai.
Bude marfin motar yayi yafita ko waiwayansu bekara yiba yashige shago. Wayarshi yadauko yayi saving abinda ya dauka ya sallami yaron yafito ya kulle shagon yatafi gida. Har ya bace suna binshi da kallo. Ajiyar zuciya suka saki gaba daya.
Umar ne yace munshiga 3, yanzu munkara tafka wani kuskuren. Brr, yace Umar ni bana kuskure, ka kyaleshi wannan taurin kan nashi zesa yarasa rayuwarshi, matukar muka barshi araye dagashi har Sageer dole zamushiga matsala.
Sede abinda nakeso inaso a dauko mani Abdul, kobamu kashe shi ba inaso mu boyeshi nasan batarshi zata tada ma Sageer hankali, har yakasa nutsuwa ya aiwatar da abinda yake gabanshi. Kuma dole mutura yaran D.P.O suje gidanshi su duba ko ina domin su dauko mana duk abinda Sageer yake takama dashi nazuwa kotu.
Waya yadauko yakira D.P.O, yana dagawa yafada mashi abinda yafaru, yace inaso acikin daren nan katura yaranka suje su sace Abdul, inaso su kaishi can gidan gona na, shikuma Sageer banaso kuyima budurwarshi da sauki harseta bada wadannan ajiyar daya bata.
Idan taki badawa kuma ku kashe ta, sannan yaranka suje gidansu su duba ko ina na gidan nasan zasu samu takardun. Sageer kuma idan sun sameshi agidan banaso su kasheshi domin za'a iya zarginmu, kawai suyi mashi dukan tsiya harseya fita hayyacinshi sannan. D.P.O yace angama.
Ya maganar kudin sallamar yarana fa? Brr, yace munyi waya da Alh, Abbas shima hankalinshi yatashi sosai, kuma yarokeni kada inabari asirin danshi ya tonu, bayaso yarashi, kuma ashirye yake daya bada konawa ne domin akashe case din. Yanzu haka yaturo mani million 20 domin afara aikin da ita, zanturo maka million 10 seka dauki naka ka sallami yaranka aciki.
Banaso kamasu sallama kadan, kasan ni banason harkar karanta, idan ma basu isheka ba zan kara maka. D.P.O yace karka damu zan basu kudin da ko iyayensu nace su kashe bazasuyi mana gardama ba. Sallama yayi mashi suka tafi.
Sageer kuwa suna tafiya daga shagon Abdul Salis yayi mashi waya akan yaje ya karbo ajiyar daya bama Saddika yabama Bala ajiyarsu kada ya karbesu idan Bala zeje kotu kawai yatafi dasu. Sageer yace akwai matsala ne? Salis yace kawai jikina ne be bani kabarsu waje daya ba, gara acanza masu guri.
Kaga babu wanda yasan kana tare da Bala, itako za'a iya bincikawa domin agano wacece budurwarka kaga za'a iya kamata kodan abaka tsoro kasan kuma mata da tsoro tana iya fada masu inda ajiyar take.
Sageer yace hakane, kaima kayi gaskiya, dama muna tare da Baban bara kawai mu wuce inkarba inbashi. Yana aje wayar yafadama Bala abinda yafaru. Bala yace wannan magana haka take, nima idan kabani ba agidana zan ajesu ba acan office dina zan kaisu kasan ance idan kayima kaya wawiyar ajiya sunfi kauda idon masu bincike, nasan babu wanda zeyi tunanin suna cikin office dina. Sageer yace haka ne.
Suna zuwa yayi mata message tafito yana waje kuma ta taho mashi da jakarshi. Suna zaune asaman dakali segata tafito rungume da jaka, murmushi yayi yace Baba kaga amaryar tawa. Bala yace kai masha Allah sannu da fitowa diyata. Sageer yace ai Baba kurmace.
Bala yace Allah sarki, ai daka iya maganarsu babu wuya, domin kurame akwai dadin zama musamman idan kayi dace data kwarai. Har kasa ta duka tagaishe da Bala, bayan ya amsa, Sageer ya karbi jakar yamika ma Bala yace Baba gata.
Amsa yayi yace Allah yatayani riko, Sageer yace amin Baba, Bala yace nizan tafi gara inbarka kuyi firarku, Sageer yace to Baba semunyi waya. Bayan yatafi suka cigaba da firarsu gwanin sha'awa. Har akayi sallar magriba Sageer yace bara yayi sallah amsallacin unguwarsu.
Bayan yadawo tafito suka cigaba da firarsu har aka kira isha'i sannan yatashi yace zetafi, rubuta mashi tayi ita bataso yatafi. Murmushi yayi ya rubuta mata kiyi hakuri ai kin kusa zama mallakina, jibi zamu shiga kotu insha Allah damun gama wannan case din za'a dawo namu case din ni dake.
Dariya tayi lokacin data karanta abinda yarubuta, jigina yayi da bangon gidansu yana ta kallonta, itama shitake kallo, wayar Abdul ce ta dawo dashi hayyacinshi. Yana dagawa Abdul yace to sarkin yan soyayya ai seka dawo haka nan, tun dazu inajiranka amma kana can kana soyayya sekace itace zaka bada amatsayin sheda jibi. Dariya Sageer yayi yace yi hakuri abokina, ganinan tahowa itace tarikeni. Abdul yace to kayi sauri kasha labari.
Kallonta yayi yana murmushi ya rubuta mata Abdul yana jiranshi, murmushi tayi ta rubuta mashi to muje inraka ka bakin titi, haka suka tafi har bakin titi seda ya hau adedeta sannan tajuyo gida.
Tazo shiga kenan taji an riketa, mutsu mutsu tafarayi tana kaima wanda yariketa duka, cak yadagata yasata cikin motarsu sukabar kofar gidan. Dede lokacin kuma mahaifinta yashawo kwana, akan idonshi yaga ansata mota, aiko da gudu yataho sede kafin yakaraso sede kurar motar yatarar.
Da gudu yabisu amma tuni harsun bace, gida yashiga yana haki, matarshi tace lafiya megida naga kana haki? Kallonta yayi yace ina Saddika? Tace baka ganta anan waje ba ai Sageer ne yazo, kaima de ai kasan idan bashine yazo ba babu wanda yakesa tafita.
Zubewa kasa yayi yana salati, tace wai malan lafiya kafada mani abinda yake faruwa mana. Kallonta yayi yace wallahi nadawo daga masallaci kawai nahangi wasu suna kokowa da ita, kafin nakaraso harsun sakata mota suntafi.
Sallati mamar tasa tana fadin shikenan masu satar mutane suntafi da ita. Yayanta ne yashigo anan yaji labari marar dadi, babanta yace towai inashi Sageer din da kikace shine yazo? Mamar tace wallahi shine dan seda ma tace indauko mata ajiyarshi daya bata kuma har magriba anan yayi ta.
Yayanta yace tabbas Baba shine yazo domin nahadu dasu zanje shago suntaho tarakashi har seda muka gaisa dashi na wuce shago, kuma ina tsaye bakin shagon naganta tadawo daga rakiyarshi ta taho gida.
Baban yace yanzu yazamuyi? Yayanta yace kawai muje wajen yansanda. Baban yace idan kuma masu garkuwa da mutane ne fa? Kasande basaso a hadasu da yansanda ko? Muyi hakuri nasan zuwa anjima ko gobe da safe zasu kiramu, addu'ar dazamuyi Allah yasa kada su cutar da ita, mu kuma Allah yabamu dukiyar dazasu nema awajen mu domin,mu amsota.
Kuka kawai Saddika takeyi, babu yanda basuyi da ita ba akan tafada masu inda ajiyar da Sageer yabata take amma batayi magana ba, Ogansu ne ya kwasheta da mari hakan yasa tadago tana basu hakuri da hannuwanta.
Se yanzu suka fahimci kurmace, dariya ogan yayi yace oho, baki iya magana ko? Ammade ai kin iya rubutu tunda ga waya nan a hannuki. Amsar wayarta yayi ya rubuta mata abinda suke bukata. Bayan takaranta ta rubuta masu dazu dayazo tabashi kuma yatafi da ita.
Kara dauketa yayi da mari ya rubuta mata karya ne, rubuta mashi tayi wallahi da gaske takeyi. Tsaki yaja yakira D.P.O yafada mashi, D.P.O yace kada kuyarda da ita, itama munafuka ce bazata taba fada maku gaskiya ba domin masoyinta ne.
Na tabbata Sageer baze anshi ajiyar ayau ba, koze karbeta se ranar daza'a shiga kotu, idan bata fada maku ba ku yaga mata mutunci kumaidata kofar gidansu, anjima kuma kushiga gidan idan mutane sunyi bacci kuduba ko ina. Wallahi tunda yataboni bazan mashi da sauki ba, banaso kusa tausayi aranku domin wannan aikin kawai kuna million daya daya kafin agama kuma mukara maku.
Dariya Ogan yasa yana fadin nagode yallabai. Kama Saddika yayi yaturata wani daki, wani ya kalleshi yace Oga idan ka gama muna son sauran, dariya yayi yace tsunstu daga sama gasashshe ai rabon kowa ne.
Duk abinda sukeyi Bukar yana daure agefe yana jinsu, jin abinda sukace yana kuka yace kudubi girman Allah kada kuyi lalata da wannan baiwar Allah, kuma fa kunada kanne bazakuso ayi masu haka ba, wani wawan naushi da Ogan yasakar ma Bukar seda hakorinshi daya yafita, tsalla keshi yayi yashige dakin.
Kuka kawai Saddika takeyi kamar ranta zefita haka ya yaga mata rigar mutunci, bayan yagama yafito yana mika, haka suka rika shiga daya bayan daya, dama su shida ne, dukansu seda sukayi lalata da ita, na karshen ne bayan yagama yaga ko motsi batayi.
Saurin fitowa yayi yace Oga naga fa bata motsi, dariya yayi yace ba dole ba, taji maza ai dole taje hutun yan mintuna. Maida mata kayanta kadaukota mu mayar da ita kofar gidansu, can anjina cikin dare semuje mu aiwatar da abinda yallabai yace.
A bayan gidansu suka yardata wurga mata wayarta yayi suka tafi. Iyayenta suna zaune atsakar gida suna jiran tsammani sukaji hayani abayan gidansu, Babanta ne da Yayanta sukayi saurin tashi suka fita.
Cike da tashin hankali Baban ya duka kusa da ita yana kuka, wani ne yace wallahi na taho naga wata mota ta tsaya, kafin nakaraso naga sun fiddo wani abu sunyarda suntafi, inazuwa naga mace kwance kamar gawa ashe diyarka ce. Yayanta ne ya dauketa be tsaya jiran komai ba yanufi bakin titi da ita Baban yana binshi abaya.
Suna zuwa suka sami adedeta suka tafi asibiti.
Sosai Sageer yaji dadin shedar da Abdul ya samo mashi, Abdul yace wallahi abokina duniya mutane basa tsoron Allah, kuma wai dan rashin kunya su rasa wanda zasu nema yayi masu wannan aikin seni. Sageer yace ai Abdul yanzu duniyar ce tabaci, idan anaso acutar da kai cikin ruwan sanyi dole se anbiyo ta wanda yafi kusanci da kai sannan.
Kawai ina me karama Allah godiya daya bani aboki, dan uwa kuma amini nagari, wallahi iname tabbatar maka azamanin nan na yanzu yanda kowa yake neman kudi ta kowace hanya bakowa bane za'ayimashi wannan tayin kudin masu yawa yaki karba.
Kuma aikin da zeyi bawani me wahala bane. Abdul ayanzu fa saboda kudi danka ze iya cin amanarka, matarka zata iya cin amanarka, masu aikinka zasu iya cin amanarka. Kaga kuwa dan aboki marar imani ai abune mesauki.
Sede Abdul kaidin daban ne, banida kamar ka kuma bazan taba samun kamarka ba har abada. Fatana Allah yabani abinda zan saka maka da irin abubuwan da kake mani. Abdul yace amin abokina, kuma ni bana bukatar komai daga gareka, ko iya addu'arka kadai ta isheni.
Sageer yace wato Abdul idan nayi kudi zamu huta, bazan taba barin kayi nesa dani ba, abu nafarko dazan farayi shine insayi katon fili inyi mana gini iri daya, muyi aure musa matan mu aciki.
Dariya Abdul yayi yace kadeyi aurenka, nida ko budurwar kirki bani da ita. Sageer yace kai ko kake da babbar budurwa baga sweet Ammar ba. Duka Abdul ya kaimashi yana dariya yace dan iskan ba, ai tunda mukayi wannan wayar dashi ban kara jinshi ba kila yayi zuciya.
Sageer yace dade yafi mashi. Abinci Abdul yadauko masu suka faraci, Sageer yace gaskiya idan nayi aure zanyi missing girkinka medadi wallahi. Abdul yace haba ai Saddika seta fini iya girki. Sageer yace baiwar Allah yarinya salaha ba, wallahi dazu jinayi kamar karna taho.
Abdul yace gaskiya ai kayi dacen mata, koni ina yaba tarbiyarta sam batada kwadai, Sageer yace wallahi kuwa, tunda nake da ita bata taba cemun in siyamata wani abu ba, kai ko kati ne bata dashi nayi mata message bazata iya yimani call me ba, sede idan naji shiru ingane bata da kati intura mata.
Ai gaskiya idan nayi kudi ku biyun nan zakuji dadi sosai. Abdul yace dan rainin wayo da farko ai dukanta kasoyi bacin narike ka. Murmushi Sageer yayi yace ai Allah yasoni ban mareta ba, da har abada bazata kulani ba, kasan kurame akwai zuciya.
Hannu Abdul yasa yadauki wayar Sageer yana fadin bara intura mata recording din danayi dazu dana Ammar wanda kayi banaso ace awayata kadai yake kada tsautsayi yasa ya goge, amma idan yana wayarka kaga ko daya ya goge akwai wani.
Sageer yace hakane, dadina da kai akwai dogon tunani, bayan yagama tura mashi ya mika mashi, tashi yayi yana fadin gaskiya kwanciya zanyi nagaji kaina yana dan mani ciwo. Sageer yace sannu kasha magani to. Abdul yace. Barshi kawai nasan gajiya ce danayi bacci dasafe zanji dadi.
Haka suka kwanta sunata fira har bacci yadauke Abdul. Ganin yayi bacci yasa Sageer yadauko wayarshi yaturama Saddika message, alokacin wayar tana hanun Babansu dan lokacin da zasu tafi wani yaga wayar ya bashi .
Alokacin da sakon yashiga suna zaune gaban likita domin jin abinda ze fada masu bayan yagama binciken Saddika. Baban yana ganin sakon yakira Sageer, mamakine ya kamashi ganin takirashi, yana dauka yaji murayar Babanta cike da damuwa.
Bayan sun gaisa Baban yake fada mashi abinda yafaru da ita bayan tafiyarshi, afirgice yatashi zaune, tambayarshi yayi awane asibiti suke? Fada mashi yayi yace shikenan Baba ganinan zuwa zantaho da dansanda.
Kayanshi yasa harze tada Abdul yatuna yace kanshi yana ciwo, kallonshi yayi yanda yake ta baccinshi kawai seya fasa tadashi, kofar yabude ahankali yana fita ya kulleshi ta baya dan kada yabar kofar abude yana bacci wani yashigo yamasu sata.
Salis yakira yafada mashi abinda yake faruwa, Salis yace kawai muhadu asibitin. Yana zuwa ya iske tashin hankali, ashe tun sumar datayi ba suma bace mutuwa tayi, Sageer yana zuwa kofar office din yaji mummunan labari yana fitowa daga bakin Babanta yana fadin shikenan Saddika, ashe dama kasheki zasuyi shiyasa suka daukeki.
Karar faduwar abu sukaji abakin kofa, saurin fita sukayi, Sageer suka samu kwance akasa asume. Dede lokacin da Salis yakaraso. Da sauri suka kamashi suka nufi ciki dashi, hannu Salis yasa yadauki wayarshi data fadi lokacin daya fadi ya bisu.
Cikin bacci Abdul yaji kamar ana buga wani abu, tun yanaji kadan harya faraji da karfi, afirgice yatashi ya kunna wuta, dede lokacin suka samu damar balle kofar, cike da mamaki Abdul yabisu da kallo, sede fuskarsu a rufe take.
Kallon kusa dashi yayi amma bega Sageer ba, seya dauka ko yana bandaki ne. Tsawar da aka daka mashi ce ta maidoshi hankalinshi. Kusa dashi Ogan yazauna yace kai ina abokinka? Abdul yace bayanan. Karya kake ina zeje da wannan daren? Abdul yace inda kukaje.
Wankeshi da mari Ogan yayi yana fadin nizaka fadama baka? Kallon yaran yayi yace ku hargitse mani dakin inason ganin duka shedun da yake tarawa. Wani wawan naushi Abdul ya kaima Ogan, kafin kace me jini yafara zuba daga bakinshi.
Rufeshi da duka Abdul yayi, daya daga cikin yaran yadaga sandarshi ya bugama Abdul akai, wani irin kara Abdul yasaki yadafe kanshi, kafin yagama dawowa hankalinshi wani yakara mashi akai, tuni jini ya wanke mashi fuska.
Ogan yana dagowa yasoka mashi wuka aciki, nan take yazube kasa cikin jini. Haka suka hargitsa dakin amma basu samu komai ba, wayar Abdul suka dauka suka fita suka bar gawar Abdul anan. Suna tafiya wani makakocinsu dayaji zuwansu yayi saurin kiran wasu nakusa dasu suka shiga ciki.
Ganin wanda abun yafaru dashi yasa suka gane Sageer baya nan, wayarshi suka kira, Salis ne yadauka nan suka fada mashi abinda yake faruwa. Zubewa kasa Salis yayi jin mummunan labari, rokonshi yayi akan sukawoshi general hospital. Kashe wayar yayi lokaci guda yaji wasu zafafan hawaye suna sauko mashi, babu abinda yake tunawa se Sageer.
Yazeji idan yafarka yakarajin wani babban al'amarin? Rushewa da kuka Salis yayi kamar karamin yaro, tsoro yakeji kada Sageer yasamu tabin hankali, shin yazeji idan yafarka?😭
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
Am really sorry my fans for d lost of Abdul and Saddika, may there souls rest in peace ameen.😭😭🙏🏻🙏🏻That is how life it's, only God can make a perfect decision, am sorry for my decision. that is how Sageer's destiny is, and nobody can pass his or her destiny
And today is exactly 2 years that i lost my father, may his gentle soul continue to rest in perfect peace amin😭😭🙏🏻🙏🏻
[2/10, 2:10 PM] nabilalady5: 👨🏻🎓KAFIN IN ZAMA LAWYER👨🏻🎓 👨🏻🎓 👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Season 115 🖤 120
NAGODE DA ADDU'ARKU🙏🏻🙏🏻
Sosai hankalin Salis yatashi ganin yanda aka kawo Abdul jina jina, haka aka turashi zuwa daki likitoci suka nufi kanshi. Komawa yayi wajen Sageer wanda yake kwance haryanzu be farfado ba ansa mashi ruwa.
Fitowa yayi yana kuka sega Yayan Saddika yadawo daga samo motar dazata dauki gawarta. Tare suka nufi dakin da take, mahaifinta yana saman gawarta, kallonsu yayi yace yallabai yajikin Sageer din?
Goge kwallan data zubo mashi yayi yace ai Baba sede addu'a kawai, domin wani iftila'i yasamu Sageer, ina tunanin mutanan dasuka aikatama Saddika wannan abun sune sukaje domin su illata Sageer, sede basu sameshi ba se abokinshi.
Yanzu haka yana wajen likitoci suna dubashi, shima bana tunanin yana da rai, domin sun caka mashi wuka aciki kuma kanshi yaji duka duk jini yabata mashi fuska. Sosai suka tausayama Sageer.
Baban Saddika yace towai meyafaru haka? Salis yace kawai saboda yana son tabbatar da gaskiyar wannan yaron na unguwarku da akace abokinshi ne ya kasheshi kuma ashe ba gaskiya bane. Kuma Sageer ya bama Saddika wata ajiya ina tunanin ita sukazo amsa basusan kuma ya amsa ba.
Baba yace amma na tausayama Sageer, Allah yabashi lafiya, ke kuma Saddika Allah yajikanki yakuma saka maki akan zalincin da aka yimaki. Yayanta yace Baba muje nasamo motar dazata daukemu. Salis yace nima zan tsaya wajen Su Sageer
Baba yace haba bakomai, amma dan Allah kasan yanda zaka fada mashi kada yasamu wata matsalar. Salis yace insha Allah, kuma zan karbi duka awon da akayima Saddika domin idan zamuje kotu dasu zamuje. Baba yace mungode Allah yabada sa'a.
Haka suka dauki gawar Saddika suka nufi da ita gida, tunkafin suje suka fadama mamanta, kasancewar dare yayi yasa sukabarta se gobe arufeta. Sosai Mamanta take kuka, da wasu makotansu dasu kazo. Kallonta kawai Babanta yake, shikenanfa yanzu sun rabu kenan har abada. Innalillahi Wainna Ilaihirraji'un. Shine abinda kawai yake fada.
MUTUWA KENAN, CIKIN LOKACI KANKANI TAKE ZUWA, KAFIN WANI LOKACIN KAZAMA TARIHI DOMIN BA'A AWA GUDA BATARE DA ANKAIKA MAKWANCINKA BA. DAGA LOKACIN SEDE ARIKA KIRANKA DA MARIGAYI. YA ALLAH KA KYAUTATA KARSHENMU, KASA MUTUWA TAZAMO HUTU AGAREMU, ALLAH KAJIKAN WADANDA SUKA RIGAYEMU, KA SAUKA KA MANA AZABAR FITAR RAI ALLAH KA KAREMU DAGA AZABAR KABARI😭. Amin.
Wani likita ne yafito daga dakin da aka shigar da Abdul, dasauri Salis yabishi office, bayan ya wanke hannunshi yazauna tare da cire glass din idonshi. Kallon Salis yayi yace kaine ka kawo wanda aka caka ma wuka ko? Salis yace e nine, ID card dinshi yaciro ya nuna mashi.
Jinjina kai Dr, yayi yace to gaskiya sede kuyi hakuri domin tun kafin akawoshi Allah yayi mashi rasuwa, domin bayan wukar da aka caka mashi dukan da akayi mashi akai ma yayi sanadiyar da jini yashigar mashi kwakwalwa, wanda shine yayi sanadiyar mutuwarshi.
Runtse ido Salis yayi hawaye suna zubo mashi. Dr, yace duk wani abinda zaku bukata nasa adauka yanzu idan suka kawo zan hada inbaka. Kuma zaku iya tafiya dashi, ga wannan takardar kasa hannu.
Kuka kawai Salis yakeyi, haka yasa hannu a takardar, yadago yace dan Allah kozaku iya aje mani gawar domin dan uwanshi yana nan akwance tunda akace budurwashi ta rasu ya suma haryanzu be farfado ba.
Da sauri Dr, ya kalleshi yace wai wannan wanda aka sama ruwa shine dan uwan wannan? E shine, girgiza kai Dr, yayi cike da tausayi yace lallai wannan bawan Allah an hada mashi zafi 2.
Itama fa sanadiyar fyaden da maza da yawa sukayi mata shine yayi sanadiyar mutuwarta. Salis yace ina me tabbatar maka duk mutane daya ne sukayi wannan aikin, kuma shine akaso kashewa da ba'a sameshi ba suka kashe Abdul.
Dr, yace towai saboda me?.............Labarin duk abinda yafaru Salis yabashi, sosai yaji tausayinshi, idanuwanshi sun kada sunyi ja saboda tausayi. Dr, yace wallahi mutane basa tsoron Allah, gaskiya dole ayi hikima wajen fadama Sageer mutuwar Abdul, domin Allah ne kadai ze iya dakar mashi da zuciya.
Ba komai zamu aje gawar anan idan yafarka ka kirani ninasan yanda zan fada mashi. Godiya Salis yayi mashi yatashi ya koma wajen Sageer.
Tsaye suke agaban su Brr, Yusuf agidan gonarshi, se raba ido sukeyi. Kallonsu D.P.O yayi yace yanzu shikenan duk aikin da kukayi baku samu komai agidan ba? Ogan yace yallabai babu inda bamu duba ba amma bamu samu komai ba.
To ina wayar Sageer din da nace ku dauko mani? Yallabai ai bamu sameshi ba, sede wata waya da muka dauko kila ta abokinshi ce. Amsar wayar Umar yayi, Brr, Yusuf yace kashiga ko ina kaduba har wajen record list duk kaduba.
Kallonsu yayi yace yallabai nasamu wani recording guda 2. D.P.O yace kunnasu muji. Yana kunna na farkon sukaji maganar da sukayi da Abdul ce, har karshe sukaji. Bayan takare ya kunna ta biyun.
Har suka gamaji basu fahimci abinda ake nufi da maganar ba. Umar yace to waye kuma Ammar? Shiru sukayi can Brr, Yusuf yace shiga contact dinshi kaga number da akasa Ammar ka bani ita.
Wayarshi ya dauka yakira Alh, Abbas, yana dagawa yace dan Allah Alh, katuro mani number din Ammar. Alh, yace inafatan de lafiya? Brr, yace lafiya lau wani abune zanduba. Yace toshikenan gatanan zan turo maka.
Umar yace gashi ansamu. Brr, yace jira inazuwa. Wayarshi ce tayi kara alamun sako yashigo. Yana dubawa yaga number Ammar ce aka turo, amsar wayar Abdul yayi yasaka number, yana dialing sega sunan Ammar yafito. Murmushi yayi yajira domin adauka.
Ammar yana dauka yace haba sweet dear nah, ai dama nasan zaka nemeni, kawai da kaga bankiraka ba dama nadaga maka kafa ne bawai na hakura da kai bane, tunda nake bantaba haduwa da gayen da yashiga zuciyata kamar ka ba. Wallahi Abdul ina sonka kabani dama injiya maka dadi, amma kaki.
Nafada maka idan har na furta inason mutum matukar be amince dani ba to tabbas yana fuskantar hukunci me tsanani, kai zan iya kashe mutum wallahi, kamar yanda wasu suka fuskance shi. Kit Brr, Yusuf yakashe wayar.
Jingina yayi da kurjerar da yake akai tare da rufe idonshi. Ya dade ahaka babu wanda yayi mashi magana, can ya bude ido yace tabbas ayanzu nagane ko waye Ammar, kuma nagane meye amfanin wanna recording din da sukayi.
Uhmm Sageer yanada kwakwalwa, tabbas na sara mashi, sede kuma yazo wajen da aka fishi fasaha, hakika kun kyauta da kuka kawo mani wannan wayar, domin nasan tana cikin daya daga makaman Sageer.
Hakika nasan zeyi amfani da maganar Ammar kuma ya bukaceshi a kotu domin ya daureshi da tambayoyinshi. D.P.O kasan kowaye Ammar? Kai ya girgiza yana fadin seka fada. Tabbas Ammar yana daya daga cikin mazan da suke son jinsinsu. Kuma Sageer ya hada Abdul da Ammar ne dan yagano wani abu.
Kuma gashi yasamu sede ayanzu zan gogeshi, kaga yarasa sheda. Kallon sauran mutanan yayi yace yanzu inashi Abdul din danace ku kamo? Ogan yace yallabai sede kuyi hakuri, domin yayi mani abinda ba'a taba mani ba shiyasa kawai nakara mashi iska.
Labarin abinda yafaru yafada masu. Murmushi Brr, yayi yace kunyi dede, zuwa yanzu nasan Sageer yana cikin tashin hankali, ga abokinshi ya mutu, kuma ga budurwashi tazama sauran maza. Dariya suka gaba dayansu. Wani yace ai kila itama ta mutu dan banji tana numfashi ba. Brr, yace wannan kuma damuwarsu.
Brr, yace iname tabbatar maku baza'ayi shari'a gobe ba, domin nida kaina zanje nasamu alkali nafada mashi tashin hankalin da abokin aikina yake ciki, nasan dole adaga shari'ar, wanda babu wanda yasan lokacin daza'a sata, kuma kunga alkali zetafi hutu, idan lokacin tafiyarshi yayi dole yatafi kuma kusan wata 2 zeyi kunga kafin yadawo mun batar da Sageer.
Sosai sukaji dadin wannan magana ta Brr. D.P.O yace shiyasa nakeson aiki da kai, kanada kaifin basira. Toyanzu yazamuyi da Bukar? Brr, Yace kada asakeshi yanzu abari se alkali yatafi hutu sannan.
Gobe zanje insamu alkalin, sauran kudin sallamarku kuma idan komai yayi dede za'a baku. Tashi yayi yace Umar mutafi. D.P.O yace ku kuma kujira inbaku kudinku.
Adede lokacin da suke maganar shi kuma Bukar yana can adaure, cikin ikon Allah yasamu ya kwance daga daurin da akayi mashi, zuwa yanzu hannunshi ya kumbura sosai, ta tagar dakin yasamu ya fita, yana dirkawa yaganshi awajen gidan, da gudu ya haura katangar yafita can waje.
Gudu kawai yakeyi har yafita bakin titi, da kyar yasamu wani me adedeta ya daukeshi, be nufi gidanshi ba domin yasan zasu iya binshi can. Kai tsaye yace ma me adedetar ya kaishi kofar durbi wato unguwar su Bala, domin yasan gidanshi.
Lokacin dayaje wajen karfe 12:30 na dare, kwankwasa kofar gidan yayi, ya dade yana kwankwasawa kafin aka bude, yana budewa Bukar yace Baba nine Bukar, haskashi Bala yayi cike da mamaki, Bukar yace bani dari 200 na sallami me adedeta.
Bayan sunshigo ciki Bala yakawo mashi ruwa da tuwo, haka Bukar yazauna yaci yakoshi, se alokacin yadan dawo hayyacinshi. Bala yace wai meyake faruwa Bukar? Jingina yayi yace Baba ina cikin matsala.................
Duk abinda yafaru yafada mashi, cike da firgici Bala yace innalillahi wainna ilaihirraji'un. Yanzu ina Saddikar? Bukar yace Allah kadai yasan halin datake ciki, domin lokacin dasuka fita ko motsi batayi. Bala yace yanzu dare yayi bare inkira Sageer inji wane hali shiyake ciki, nasan dole se sunje wajensu.
Yanzu abinda za'ayi bara indauko maka magani kasha nasan ze rage maka zafin da kakeji, ka kwanta zuwa gobe musan abinda zamuyi. Bukar yace nagode Baba.
*******
Washe gari Salis yana shigowa dakin da Sageer yake kwance yadawo daga masallaci, dede lokacin Sageer ya farka afirgice, babu abinda yafito daga bakinshi se sunan Abdul. Da sauri Salis yakarasa wajenshi, kamashi yayi yana fadin kayi ahankali Sageer. Kallonshi yayi hawaye suna zuba daga idonshi yace ina Abdul?
Meyafaru dashi? Ka fada mani naga wasu mutane suna kokowa dashi dan Allah kafada mani. Kuka yasa kamar karamin yaro, shima Salis hawaye ne suka cika idonshi, gashi da yayi magana zasu zubo.
Dago kai Sageer yayi yace Salis da gaske Saddikata ta tafi ko? Hawayen dayake boyewa ne suka zubo mashi, dafashi yayi yace kayi hakuri Sageer duk me rai mamaci ne. Jingina yayi ya runtse ido hawaye suna zubo mashi. Dago kai yayi yace ina wayata inkira Abdul nasan yanzu yatashi daga baccin.
Salis yace wayarka data fadi nabama wani Dr ya aje maka kuma yanzu gari be idasa wayewa ba bezo ba. Kallonshi yayi yace Salis kafada mani wani abu yafaru da Abdul ko? Salis yace bakomai ba'a gida kabaroshi ba? Sageer yace e bacci yakeyi. Amma mafarkin danayi fa? Salis yace Sageer mafarki ba gaskiya bane.
Tashi Sageer yazoyi da sauri Salis yarikeshi yana fadin kazauna likita yazo sannan. Sageer yace nasan ba'a rufe Saddika ba, inaso insamu jana'izarta dan Allah. Salis yace kabari Dr,yazo sannan.
Kallonshi yayi yace to bani wayarka inkira Abdul infada mashi nasan yana can yatashi beganni ba kuma yakira wayata akashe, duk inda yake yanzu hankalinshi yafara tashi domin jiya ban fada mashi zanzo nan ba. Kasan Abdul bayaso yatashi beganni ba.
Saurin juyawa Salis yayi yafita domin wani kuka ne yataho mashi jin abinda Sageer yake fadi. Tsayawa Sageer yayi yana kallonshi. Tabbas yasan akwai abinda yake boye mashi, yama za'ayi yadauki wayarshi yabama wani likita ya aje mashi? Kai ya girgiza kawai yasauko.
Drip din hannunshi yacire yanufi kofa, yana budewa yaga Salis yana goge idonshi, Sageer yace Salis mutuwar Saddika ce tasaka yin wannan kukan haka? Juyowa yayi zeyi mashi magana sega Dr,yazo dasauri yakaraso wajensu yana fadin yana ganku awaje kuma?
Kama Sageer yayi suka shiga ciki yana fadin muje kaida jikinka babu kwari meyasa kataso?. Bayan sun zauna Sageer yace yauwa Dr, bani wayata. Dr, yace ai bata wajena. Saurin kallon Salis yayi yace kaji ko? Kai baze yuwu ba, wallahi akwai abinda kuke boyemun.
Na rokeku da girman Allah kufada mani, idan kuma bazaku fada mani ba kubarni inje inraka Saddika gidanta na gaskiya, inje wajen Abdul dan Allah. Juyawa Salis yayi yacigaba da kuka. Tashi Sageer yazoyi Dr, yarikeshi yana fadin zauna infada maka abinda yafaru.
Shiru Dr, yayi nawani lokacin kafin yadafa kafadar Sageer yace da farko de inaso kasaka Allah aranka kuma kayi tawakkali da dukan abinda zan fada maka, kamar yanda karasa iyayenka ka hakura nasan duk wanda karasa arayuwarka zaka iya dangana.
A jiya karasa masoyiyarka kuma gashi kasa dangana aranka, dan haka inaso kasani duk wanda Allah yadauka bawai dan bayason shi bane, haka kuma mu daya bari bawai soyayya bace tasa yabarmu. Sede kowane bawa Allah yadibar mashi iya kwanakin dazeyi aduniya.......................
Labarin duk abinda yafaru tun daga kan Saddika har zuwa bayan tahowarshi yabashi. Yace kayi hakuri Sageer, hakika kayi babban rashi, kuma inaso kadauka Allah yana jarabtar bawansa akowane lokaci, kaima kila taka jarabawar kenan.
Kallon Sageer yayi ze cigaba da mashi nasiha sede a firgice yatashi ganin halin da yake ciki, kamashi yayi yana jijjigashi, amma ina Sageer idanuwanshi ne kawai a bude hawaye suna zuba daga ciki, amma ko numfashi bayayi. Salis ne yakarso da sauri yana kiran sunanshi.
Dr, yace ina zuwa Salis yace ko inbashi ruwa? Dr, yace kada kabashi komai inazuwa, dasauri yafita yanufi office, be jima ba yadawo dauke da wani karamin akwati, wata allura yaciro zuka yayi yayi ma Sageer. Kwantar dashi sukayi sede haryanzu baya numfashi.
Wani drip yaciro yasa mashi Salis se kuka yakeyi, Dr, yace kada kadamu insha Allah ze samu sauki wannan allurar danayi mashi zata daukeshi kamar awa 3 kafin yatashi zuwa lokacin insha Allah bugun zuciyarshi ze dedeta, kuma numfashinshi zedawo dede.
Kasan haka tana faruwa ga mutumin daya samu wani mummunan labari ko wani mugun tsoro, bugun zuciyarsu yana tsayawa nawani lokaci, to allurar tana temakonsu, kuma wannan baccin dazeyi shine ze temaka mashi, domin idan yana afarke zuciyarshi zata iya bugawa.
A jiyar zuciya Salis ya saki tare da goge idonshi yace amma Dr, kana ganin babu wata matsala? Dr, yace babu abinda ze sameshi insha Allah, kawai addu'a yafi bukata. Salis yace shikenan bara inje gida idan nashirya zanje wajen aiki infadi uzurina kafin nan nasan yafarka se inzo musan yanda za'ayi domin akai Abdul makwancinshi shima yahuta.
Dr, yace babu damuwa zansa akula dashi, Salis yace nagode amma dan Allah ka kula dashi dan yanzu rayuwarshi tana cikin hadari. Dr, yace bakada damuwa amma kaje wajen alkali kafada masa abinda yafaru kaga se adaga shari'ar zuwa wani lokaci ko? Salis yace zanje insha Allah.
Wayarshi ce tayi kara yana dagawa yaga Bala ne, bayan sungaisa yake fada mashi abinda yafaru da Bukar kuma yana gidanshi. Runtse ido Salis yayi shima yafada masu abinda yake faruwa. Sosai Bala yashiga tashin hankali jin abinda yake faruwa.
Salis yace abinda za'ayi Baba kadauko Bukar ka kawoshi asibiti, idan kazo kanemi office din Dr. Malik shi zeyi mashi komai, kuma ze ajiyeshi awajenshi kada kabari kowa yasan yana asibiti sannan asamu afadama iyalanshi amma kafada masu kada subari kowa yasan yana raye idan ma wasu sunje tambayarsu shi suce suma tunjiya ya bace basu ganshi ba, kuma kayi masu jagora suje wajen D.P.O sukai korafi akan batarshi.
Baba yace shiekanan zanyi yanda kace, shikuma Abdul Allah yajikanshi, Allah kuma yabama Sageer lafiya da hakurin jure rashinsu. Bayan ya kashe wayar yafadama Dr, abinda yake faruwa. Dafe kai Dr, Yayi yana fadin ikon Allah, wai meyake damun wadannan mutanan ne? Bakomai kaje kawai insha Allah nima zan bada tawa gudun muwar akan wannan case din. Sallama yayi mashi yatafi.
Kowa yagan Salis yasan yaci kuka, yana cikin tafiya ne D.P.O yakirashi, yana dauka yace Salis inafatan lafiya ba kazo wajen aiki ba haryanzu, dan Shehu yakirani yace bakaje ba? Salis yace yallabai inada marasa lafiya a asibiti ne, yanzu haka daga asibitin nake fitowa acan na kwana, amma yanzu zanzo dama infada maka. Waye beda lafiya? Wani dan uwana ne. To Allah yabashi lafiya, bakomai base kazo ba kawai katafi can. Godiya yayi mashi yakashe wayar.
A gidan su Saddika kuwa tuni har an rufeta andawo anata zaman makoki. Duk wanda yaga iyayenta seya tausaya masu, kuma duk wanda yaji yanda akayi ta mutu seya tausaya mata, domin kowa yana shedar Saddika, yarinyace da babu ruwanta, batada hayaniya bare abokiyar fada. Tasamu sheda me kyau, kuma tayi jama'a sede muce Allah yajikanta.
Baba Yusha'u ne mahaifin Salis zaune yana goge hawayen dasuka zubo mashi alokacin da Salis yagama bashi labarin abinda yafaru. Baba yace kai amma gaskiya na tausaya ma Sageer, shine abun tausayi saboda su tasu takare, lallai wadannan mutane sunyi mashi illar da harya mutu baze taba mantawa dasu ba.
Hakika Allah baze barsu ba, ina me tabbatar maka se sunyi mutuwar wulakanci, tun aduniya se Allah yafara wulakantasu kafin suje lahira, akwai mutane marasa imani dayawa dauniya, sede bantaba haduwa da wadan da suka fi wadan nan ba. Bakomai Allah shine wanda ya dorama Sageer wannan iftila'in kuma shine ze saka mashi dangana.
Kasan Allah yana daukar ran uwar jaririn dayazo duniya kuma ya sama mashi uwar reno, kamar yanda yake halittar makaho kuma ya halitta mashi dan jagora. Ina me tabbatar maka suna ganin kamar sun na kasa Sageer ta yanda baze iya kara tsayawa yayi sharia ba ko? To kajira zakasha mamakin yanda Allah ze saka mashi kwarin guiwa kuma ya gabatar da shari'ar yanda yakamata.
Katashi kayi wanka kaci abinci katafi wajen alkali kafada mashi duk abinda yafaru. Shi kuma Bukar Allah yabashi lafiya.
Brr. Yusuf ne zaune a office din alkali dan yau da wuri yafito hakan yasa yayi sa'ar samunshi. Bayan sun gaisa alkali yace Brr, ya aiki? Yace lafiya lau yallabai, dama nazo ne akan maganar shari'ar da mukeyi, wadda agobe ne za'a koma kotu.
Wato wani iftila'i ne yasamu abokin shari'ar tawa, kuma nasan baze iya gabatar da shari'ar ba shiyasa nace bara inzo infada maka ko za'a dagata zuwa wani lokaci? Gyara zama alkali yayi yace meyake faruwa ne?
Brr. Yusuf yace wato matar daze aura ce Allah yayi mata rasuwa jiya, kuma damashi maraya ne, yana zaune shida wani babban abokinshi shima ajiyan wasu barayi suka shigar masu gida suka bubbugeshi suka caka mashi wuka aciki,sede basu samu Sageer din agida ba. Kuma haryanzu ban sani ba shima ko yarasu ammade inaji ankaishi asibiti.
To gaskiya Sageer yashiga tashin hankali sosai, shiyasa nace zanzo infada maka domin abashi dan lokaci yagama jinyar wannan rashi. Zare glass din idonshi alkali yayi cike da tausayi yace lallai Sageer ya hadu da jarabawa. Bakomai, duk da inaso ingama wannan shari'ar kafin intafi hutu, amma tunda wannan abun ya ratso dole adaga shari'ar domin mutuwa ba wasa bace.
Brr. Yusuf yace gaskiya kam, nagode yallabai nizan koma. Alkali yace bakomai zansa asheda ma mahaifin yaron dayake kara andaga shari'ar zuwa wani lokaci, kuma gobe ma idan mutane sunzo za'a fada masu. Sallama yayi mashi ytafi.
Yana tafiya babu jimawa Salis ya iso, bayan masinjan alkali yasheda mashi aka bashi izinin shiga. Bayan sun gaisa Salis yafadama alakali duk abinda yake faruwa, sosai alkali yayi mamakin wannan rashin imani, kuma ya tausaya ma Sageer sosai.
Alkali yace yanzu ina shi Bukar din? Salis yace yana asibiti shima. Alkali yace kayi kokari wajen bashi kariya domin shine ze zamo maku sheda akan abinda aka yima Saddikan da kuma abinda yaji suna fada akan shi Abdul da Sageer din.
Gaskiya na tausaya ma Sageer, kuma idan har suna tunanin abinda suka mashi shine zesa wannan shari'ar ta lalace to sunyi shirme, domin ina me tabbatar maka koda zata shiga cikin huta na sena gabatar da ita kafin natafi.
Hakika nagode ma Allah da yasa Sageer ya dawo da wannan case din, domin nayanke hukunci abisa kuskure, kuma zanyi amfani da wannan damar domin na gyara kure na. Allah yabashi lafiya, su kuma Allah yajikansu, kabani wayarka domin idan yafarka kafada mani inaso in halarci jana'izar Abdul, kuma inaso muyi magana da Sageer din.
Godiya yayi mashi ya rubuta mashi number dinshi yayi mashi sallama yace ze koma asibitin yaga koya farfado. Bayan yatafi alkali ya dauki takarda yayi rubutu sannan yatashi yafita.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
Nagode da addu'arku kuma nasamu sauki Allah yabar zumunci🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Season 120 🖤 125
Seda akayima Bukar allurar kashe zafi sannan aka fara mashi dressing, hannun ya kumbura sosai, seda aka sa wani karfe na wuta aka kone inda suka cire mashi yatsun saboda tsoron kada cuta tashiga.
Sun dade suna mashi aiki kafin sugama, wani daki na musamman Dr, Malik yabashi ruwa ya daura mashi wanda aka zuba wasu allurai domin kare lafiyarshi. Ganin yana bacci Bala yacema Dr, suje ko Sageer ya farka gara akai Abdul makwancinshi da ayita ajeshi.
Suna kan hanyar zuwa dakin suka hadu da Salis, atare suka shiga ciki. A kwance suka sami Sageer sede idonshi biyu kanshi yana kallon sama hawaye ne kawai suke zuba daga idonshi. Dr, ne yaje ya cire mashi ruwan dayake hannunshi, har lokacin be kalli kowa acikinsu ba.
Bala ne ya dafashi yana fadin Sageer inaso kabani aron hankalinka, nasan kai musulmi ne, kuma kasan cewar imanin mutum baya cika har seya yarda da kowace kaddara idan tazo mashi, me kyauce, ko kuma akasin haka.
Ka rasa wadan da suka kawoka duniyar baki daya, kuma gashi har yanzu kana raye babu abinda ya sameka, nasan ance sabo shi akeyima kuka, akwai wanda ze iya rasa abokinshi ya shiga damuwar da kila kota iyayenshi idan yarasa baze shiga haka ba.
Badan baya son su ba, sede dan shakuwar da take tsakainsu. Hakika duk wanda yaji labarinka dole ya tausaya maka, kuma duk wanda yasanka yasan irin yanda kuka shaku kaida Abdul. Sede inaso kasani babu wata soyayya da zaka nuna ma Abdul wadda tafi katashi ka rakashi gidanshi na gaskiya.
Domin manzon Allah yana cewa mutanan kirki idan suka mutu babu abinda suke so kamar a gaggauta kaisu makwancinsu. Wannan shine babban gatan da zakayi mashi. Abu na biyu kuma addu'a itace tafi akan kazauna kana mashi kuka, domin mamaci bayason ana zubar mashi da hawaye.
Duk da kukan yana saka sauki acikin zuciyar meyinshi, amma hakuri shine yafi cancanta agareka. Kana gani masoyiyarka bata samu rakiyar ka ba, ga abokinka shima akwance, idan har bazaka iya zuwa rakiyarshi ba, gara muje mukaishi kodan shima ya huta.
Gashi acikinmu babu wanda yasan wani nashi da tun dazu munje mun sanar dasu kaga idan sukazo dole su daukeshi su kaishi makwancinshi koda kuwa baka farka ba. Inaso kadubi girman Allah, ka saukaka ma kanka kayi hakuri katashi muje afadama yan uwanshi azo akaishi kabarinsa.
A jiyar zuciya Sageer yasaki me karfin gaske tare da runtse ido wasu hawaye masu zafi suka gangaro mashi. Salis yana gefe shima kukan yakeyi, hatta da Dr, seda ya zubar mashi da kwalla.
Kokarin tashi ya farayi da sauri Bala yakamashi yatashi zaune. Hannu yasa ya goge idonshi yana fadin shikenan Baba, zanyi yanda kace. Hakika nasan na rasa Abdul da Saddika, kuma mutuwa ba karya bace, har abada nasan bazasu dawo ba.
Allah yajikan ku ya gafarta maku, wadan da suka aikata maku haka kuma Allah shi kadai yasan yanda zeyi dasu. Tabbas nayi rashin masoyi babba, sede kuma ina godiya ga Allah, alokacin da yasan ze rabani da masoyana se yakara hadani da wasu.
Wannan ba karamin gata bane Allah yayi mani, da yaso seya barni nikadai, kuma yadauke wadan da yaso, Baba koda narasa Abdul Allah yabani ku, ajiya ma seda yakaramun da Dr, gashinan, wannan wata falalace daga rabissamawati.
Nayarda da abinda kace, ina fatan Allah ya saka mani dauriya, kuma yabani ikon jure rashin da nayi. Kuka yake sosai wanda yake karya zuciyar duk wani me sauraronshi. Dago kai yayi yace Salis ina wayata in bugama Kawun Abdul nasan beda labarin abinda yafaru domin bada safe Abdul yake zuwa gaisheshi ba bare yaga shiru beje ba.
Wayarshi yamika mashi, yana kira ya dauka, shiru Sageer yayi yana kuka marar sauti, yakasa magana, Kawun yana ta sallama amma babu amsa, ganin haka yasa Bala ya amshi wayar. Bayan sun gaisa yayi mashi bayanin abinda yake faruwa, kuma yafada mashi gasunan zasu taho da gawarshi.
Sosai Kawu ya firgita dajin wannan labari, yana kashe wayar yafara kiran sauran yan uwan Abdul domin suzo ayimashi sutura. Da temakon Dr, aka hada komai ambulance ta asibiti ya karba masu aka saka gawar Abdul aciki.
Sageer kuwa seda Salis yarikeshi sannan ya iya tafiya, wayarshi yadauko yakira alkali yayi mashi kwatancen inda za'ayi jana'izar Abdul. Bayan sun zauna Sageer ya rubuta message yaturama sauran abokan kasuwancin Abdul tare da fada masu inda za'ayi jana 'izarsa. Haka suka tafi Sageer yana kusa da Abdul ya daga fuskarshi yana ta kallo.
Kafin wani lokaci kofar gidan Kawun Abdul ta cika da jama'a, wasu ma basu sanshi ba amma da sunji yanda abun yafaru suke zuwa domin rakashi makwancinshi. Tabbas Abdul yayi jama'a, daga bangaren alkali kawai wadan da sukazo suna da yawa, dan yan office dinsu sunzo dayawa, hada wasu da suka kasance abokan alkali,ne seda yafada masu yanada jana'iza haka kuma suka halarci wajen.
Idan kaga jama'ar da Abdul yatara zaka dauka wani babban mutum ne yarasu. Brr, Yusuf da Umar ma sun halarci wajen domin Brr, yace gara suje dan sufita zargin jama'a. Bayan angama mashi wanka aka fiddo dashi domin ayi mashi sallah.
Gaba daya kan layinsu seda yacika da mutane, hatta kan titin unguwar seda aka tsaida masu abin hawa. Sageer yana sahun gaba haka suka sallaceshi. Bayan angama haka,mutane suka jera aka tafi rufeshi.
Gaskiya jama'a rahama ne ga mamaci, domin manzon Allah yace da za'a samu mutane arba'in su sallaci gawarka, babu wanda yataba shirka acikinsu tabbas Allah ze gafarta maka kurakurenka, kuma ze saka ka aljannarshi.
Allah kabamu ikon cikawa da karshe me kyau, kuma kabamu baiwar samun mutanan kirki domin su tsaya akan gawarmu amin. Alokacin da za'a saka Abdul kabari Sageer kasa matsawa wajen yayi, dama Salis yana rike dashi har sukaje wajen.
Yana kallo aka kama gawar Abdul aka saka cikin kabari, alokacin kasa tsayuwa yayi sede yaduke saboda gaba daya kafafuwanshi rawa sukeyi, haka ya duka yana wani irin kuka sede ahankali yakeyi, amma duk wanda yaganshi yasan irin kukan nan ne me cin rai.
Umar da tunda akazo wajen hankalinshi yafara tashi, komawa yayi gefe guda yana kallon yanda aka saka Abdul rami aka fara rufeshi, duk inda aka ga wata kofa se an tosheta. Besan lokacin da hawaye suka fara zubo mashi ba, gaba daya jikinshi rawa ya farayi.
Bayan an gama rufeshi aka yimashi addu'a. Baba Yusha'u ne yatashi domin ya gabatar da dan wa'azin da aka saba yi aduk lokacin da aka binne mamaci. To jama'a, kowa de yaga yanda aka rufe wannan bawan Allah. Ina me kara jan hankalin mutane dasuji tsoron Allah.
Wallahi wannan dan karamin ramin da kowa yake gani babu wata rai dazata tsira batare data shiga cikinshi ba. Komin kudin ka, komin mulkinka wata rana dole wannan karamin ramin yazamo gidanka.
Wadan da suka aikata wannan mummunan abu ga wannan bawan Allah, to su sani beyi sauri ba. Haka zalika su dasuka rage aduniya basu makara ba, domin wata rana suma zasuzo inda yazo.
Mazon Allah (s,a.w) yana cewa, babu wata rai dazata zo ranar tashin kiyama face seta dan dani zafin mutuwa. Kuma babu wata rai dazata halarci filin hisabi face seta bi takan siradi. Jama'a kunsan ya siradi yake? Fadinshi be kai silin gashin kai ba. Haka kaifinshi yafi kaifin sabuwa takobi.
Sannan atsakiya yake, kasan shi kuma wutar jahannama ce, sannan wasu sarkoki na wuta da kugiya suna yawo atsakanin ta. Wallahi babu wani bawa daze wuce lafiya se wanda yakasance ya aikata abin kirki aduniya.
Dan haka ina mana nasiha da muji tsoron Allah, kada rudin duniya da abinda yake cikinta ya rudemu mu manta da wannan gidan namu dayake jiranmu. Kuna gani babu komai cikinshi kome mutum yasamu aciki to shine ya kawoshi.
Karami ne ga mutanan dasuka kasance azzalumai, fasikai, mazinata da kuma kafirai. Duk wanda yashiga cikinshi batare da guziri me kyau ba, hakika ze matseshi, harse hakarkarinshi na dama yashiga cikin na hagu. Wa iyazubillah. Muji tsoron Allah. Allah yajikan wadan da suka rigayemu, mu kuma Allah ya kyautata namu karshen. Da wannan nasihar nakawo karshen maganta.
Gaba daya mutanan dasuke wajen seda jikinsu yakara yin sanyi, mutane dayawa sun zubar da kwalla saboda wannan nasiha da akayi masu. Brr. yusuf jiyake kamar anjefashi cikin ruwan kankara. Gaba daya jikinshi yayi sanyi.
Haka kowa yakama hanya domin komawa gidan makoki.Umar da Brr, daga makabartar gida suka wuce, babu wanda ya iya cewa komai, kowa da abinda yake sakawa.
Haka aka cigaba da zaman makoki, duk wanda yaga Sageer yasan yafita hayyacinshi, gefe guda yazauna atakure, Salis yana kusa dashi, mutane se zuwa suke suna yimashi gaisuwa, wasu kuma suna kawo kayan abinci da kayan sadaka.
Bayan an dan lafa ne Bala yace ma Salis yakama Sageer sutafi gidansu yasamu yayi wanka yabashi wani abu me ruwa yasa acikinshi. Bayan sun tafi Sageer yace dan Allah Salis muje muyima yan gidan su Saddika gaisuwa. Salis yace haba Sageer, kaima fa mutuwa akayi maka, sannan bakada wani kwari ajikinka bekamata muje wani guri ba.
Kuka Sageer yasa mashi yana gadin dan Allah kabari muje, wallahi inaso inje wajen Baba inyi mashi gaisuwa, kasande ta dalilina suka rasa diyarsu. Salis yace shikenan ya isa haka kadena wanna kukan dan Allah.
Tun kafin su karasa kofar gidan Sageer yafashe da kuka ganin jama'a zaune akofar gidan su Saddika, kuma wai zaman makokinta akeyi? Lallashinshi kawai Salis yakeyi. Da kyar yakamashi suka tafi zuwa kofar gidan.
Baban Saddika yana ganinshi shima wani sabon kuka yazo mashi. Haka suka rikayima mutane gaisuwa, har suka iso wajen yayanta, bayan sunyi mashi gaisuwa yatambayi Salis yame jikin da aka kawo? Salis yace ai shima ajiyan yarasu.
Sosai ya tausayama sageer, gaisuwa yayi mashi ya matsa wajen Baba, shima ya tausayama Sageer, haka suka yima juna gaisauwa, sannan suka shiga ciki sukayima Mamanta gaisuwa.
Sosai ta yi kukan ganin Sageer, domin yatuna mata da rabuwarta ta karshe da Saddika. Kuma itama ta tausaya mashi jin abinda yafaru dashi, mutane da yawa sukayi mashi gaisuwa, haka suka fito yana ta kuka sukayi masu sallama suka tafi gidansu Salis domin yasamu yayi wanka yaci abinci duk da bayajin ze iya cin komai.
Tunda su Umar suka dawo daga makabarta haryanzu bedawo dede ba, shi kanshi Brr, Yusuf haryanzu zuciyarshi a cunkushe take, yarasa abinda yake mashi dadi. D.P.O ne yashigo office dinsu hade da sallama. Bayan sun gaisa, yace wai ina kuka jene haka?
Brr, yace wallahi munje anyi ta'aziyar abokin Sageer ne, kasan mutane suna iya zarginmu shiyasa kawai nace muje. Kasan wani abun mamaki kuwa? Hada alkali nagani yaje, bakaga yanda abokanshi suka halarci wajen ba, kai kace dan uwanshi ne yarasu.
D.P.O yace kode shidin dan uwanshi ne bamu sani ba? Brr, yace gaskiya kamar da wuya,ina ganin dan de Sageer yakasance lawyer shiyasa alkali yaje mashi kasan ai naje nafada mashi halin da Sageer yake ciki shiyasa yazo.
D.P.O yace Umar meyafaru naganka kamar baka lafiya, kuma ga idonka ya dan kumbura? Brr, yace wallahi tunda muka dawo daga makabarta yake kuka. Hakuri zakayi kada wannan abun yatada maka hankali, nasan kana tsoron kada asirinmu ya tonu.
Ajiyar zuciya Umar yayi yace ba haka bane, kawai de bana jin dadin zuciyata ne. Brr, yace kada kadamu, hannu yasa aljihu yaciro dubu hamsin ya mika mashi yana fadin karbi wannan kaje kasayi abinda kakeso kafin naciro wasu kudin sena kara maka kayi hidimarka.
Murmushi Umar yasaki ya karba yana fadin nagode, bara inje dama zamuje shopping. Brr, yayi murmushi yace kode kaida surukata? Dariya Umar yayi yana fadin itace.D.P.O yace ai da mun gama wannan case din zamu fara maganar bikinka gara kaima kashigo sahun manya.
Godiya yayi masu yafita yanajin dadi harya manta da yanayin daya shiga na tsoron Allah. SHEGIYA NAIRA, MESA MUTUM YA MANTA DA KOMAI, MUSAMMAN MASU KARANCIN IMANI. ALLAH YAYI MANA TSARI DA SHARRIN ZUCIYA,AMIN.
Yana fita D.P.O yace da alama Umar yashiga damuwa. Brr, yace naga alama shiyasa nabashi kudi ai, kasan sune kadai zasu iya sanya mutum fara'ar dole. Dariya suka saka. D.P.O yace wai ni yakaga Sageer? Murmushi Brr, yayi yace ai ina tabbatar maka Sageer baze iya cigaba da wannan shari'ar ba. Kuma nan da wani lokaci alkali zetafi hutu, kafin ya dawo komai ya wuce, kaga mune keda nasara.
Dama nafada maka sena maida Sageer abin tausayi, sena saka mashi tsanar aikin law arayuwarshi. Dani yake magana.

Season 125 🖤 130
Haka aka cigaba da zaman makokin Abdul da Saddika, tunda Sageer yabar gidansu bekara komawa ba, sede Salis ne yaje yadauko mashi jakar kayanshi da sauran kayan amfaninshi ya kulle gidan.
Duk wata kulawa Salis da Babanshi suna bama Sageer, ya rame sosai, kullum cikin tunani yake, abinci ma da kyar yake iyaci shima se Salis yayi da gaske idan kuma yakici se Baba ya matsa mashi da kanshi.
Bayan anyi sadakar bakwai kowa ya tafi, Sageer ne da Salis sukaje wajen Kawun Abdul domin ya bashi duk wasu kayanshi. Kawu yace to Sageer ina kara baka hakuri akan wannan rashi da mukayi gaba daya.
Hakika kai abokine nagari, nasan yanda kukayi zama kaida marigayi, babu abinda zance sede inyi maka godiya, kuma inafatan kada wannan zumuncin ya yanke. Goge idonshi Sageer yayi yace bakomai Kawu insha Allah zancigaba da daukar ka tamkar mahaifina.
Kuma kayan shagon Abdul zan saidasu se asaki shagon tunda dama na haya ne, gidan ma zan sakeshi in kama wani bazan iya cigaba da zama acikinshi ba, domin kullum zan rika ganin kamar zanka Abdul aciki.
Sauran kayan sawarshi da kayan amfaninshi duk za'a kawo se a rabama masu gadonshi. Allah yajikan Abdul. Kuka yasa me ban tausayi, har seda yasa su kuka. Godiya Kawu yayi masu haka sukayi mashi sallama suka tafi.
Shirye shiryen biki ya kan kama agidajen biyu,biki yarage saura sati 3, duk wani gyara atare akema su Nabila da Rayyana, domin yanzu Umman Rayyana ta saduda, komai se abinda Umman Nabila tace, kuma bata banbanta tsakanin Nabila da Rayyana.
Sosai Babansu yayi kokari, yayi masu kayan daki masu kyau, haka kowa mamanshi tayi mashi siyayya dede karfinta. Umman Rayyana da kanta takira Aunty tanemi yafiyarta, Aunty tace bakomai Yakumbo, nayafe maki.
Umma tace wallahi nayi dana sanin kawo maki wannan shawarar, gashi yanzu nayi sanadiyar barinki gidan mijinki ni kuma ina zaune lafiya. Dan Allah kiyi hakuri. Aunty tace bakomai Yakumbo, komai kaddarace nima tawa kaddarar kenan, kuma nagode ma Allah dayasa haka tafaru, da asirina be tonu ba da yanzu nazama me aikata laifin kisa.
Kuma gashi sanadiyar tonon asirina yazamo mani darasi, inaganin Allah yakara bani wata damar dazen iya gyara rayuwata , kuma Alhamdulillah ayanzu kam nasan nagane kuskurena, kuma bana fatan Allah yasa nasake maimaita makamancin laifin da nayi.
A yanzu haka dana gama iddah ta bazan tsaya bata lokaci ba duk wanda yafito yana son ya aure ni idan har na kirki ne, zan bashi dama domin inje inkara gyara rayuwata. Umma tace nima zan tayaki da addu'a Allah yakawo maki miji nagari.
Ina fatan zakizo bikin su Nabila ko? Aunty tace gaskiya bazan boye maki ba, wallahi bazan iya zuwa ba. Yau ko bikin Laila akeyi sede inyi nawa taron anan amma banajin zan iya zuwa Katsina ayanzu bare kuma ace wai inje tsohon gidan aure na. Kinsan koda wani be ya damun magana ba dole wani yayi kinga kuma ni na kawo kaina.
Umma tace haka ne, bakomai wata rana zakizo ai, amma inaso kicire komai aranki kema kisamu kiyi kiba dan yanzu nasan kin rame sosai. Aunty tace wallahi Yakumbo yanzu na hakura, nasama raina salama neman lahirata kawai nakeyi amma nacire komai araina. Godiya Umma tayi mata sukayi sallama.
Kwanan Bukar 8 a asibiti aka sallameshi kuma hannunshi yayi sauki sosai, sede haryanzu be koma gidanshi da zama ba, sede yaje da dare yadawo gidan Bala ya kwana anan.
Duk irin neman da yaran D.P.O sukayi mashi basu ganshi ba, kuma gashi matarshi taje har wajen D.P.O sun kai korafi akan batanshi. Sosai D.P.O ya nuna damuwarshi, kuma yayi masu alkawarin sa yaranshi su nemoshi aduk inda yake.
So biyu Salis yana sa Matar Bukar tana zuwa wajen D.P.O domin takara yimashi tuni akan batan mijinta. Wannan dalilin ne yasa hankalinsu be kai suje gidanshi su duba ba. Kullum D.P.O sede yabasu hakuri. A nan Matar tace zata koma gida tacigaba da addu'a idan yadawo zatazo tafada mashi, anan ne yaji dadin abinda tace, dama yafara gajiya da zuwan data keyi.
Baban Salis ne da Bala, Bukar dasu Salis zaune agidansu. Sageer yana zaune daga gefe yayi shiru kamar kullum. Kallonshi Bala yayi yace Sageer iname kara maka ta'aziya akan wannan rashi da kayi.
Nasan haryanzu kana cikin alhinin mutuwar da akayimaka, sede inaso kasa hakuri aranka kuma kadaure kada kabari makiyanka suyi nasara akanka. Tabbas nasan wannan abun da akayi maka anyishi ne dan a hanaka aiwatar da aikin alkhairin da kayi niyar aikatawa, ni nasani babu wanda yayi maka wannan abun se abokan takararka akan wannna case din.
Dan Allah Sageer kada kabari suyi nasara akanka, kada kabari suyi maka dariya aduk lokacin dasuka ganka, kada kabari suyi nasarar saka maka tsanar wannan aiki naka kamar yanda sukeso. Inaso ka nunama duniya wanene Brr, Yusuf.
Kai kadai ne zaka iya gogawa dashi, kuma kai kadai ne zaka iya gabatar da wannan case din, kamar yanda kayima Baban Mannir alkawari inaso kacika mashi alkawarinshi. Kasan ance mutuwar wani tashin wani, Abdul de yarasu, idan ma sun kasheshi ne dansu ci ribar abinda suka sa gaba to basu sani ba yanzu ne Abdul yasamu nasara akansu.
Domin yasamu gatan da bazasu taba samu ba, yasamu jama'a sosai hada wadan da betaba tunanin haduwa dasu arayuwarshi ba segashi sunzo sun tsaya akan gawarshi kuma sun sallaceshi. Kaga wannan kadai babbar rahama ce agareshi. Dan haka kacire komai aranka ka fuskanci makiyanka domin kadaukarma Abdul da Saddika fansar abinda akayi masu.
Wannan abun da zakayi masu shikadai ne sauran gatan dazakayi masu. Kuma kaga zaka cikama Abdul burinshi, domin Abdul beda wani buri daya wuce yaga kayi nasara a wannan case din. Ka kalli irin baiwar da Allah yayi maka ta jama'a, lokacin tafiya hutun alkali yayi amma saboda yanaso ya tabbatar da gaskiya yasa yakara daga tafiyarshi hutu badan kowa ba se dan kai.
Dan Allah Sageer kadaure ka bari asaka ranar da za'a koma kotu kodan hankalin Bukar ya kwanta, kana ganin saboda kai yayi nisa da iyalinshi, beda ikon kwana agidanshi, badan kowa yake wannan abun ba sedan kasamu kayi nasara akan wannan case din. Baba yace maganarka gaskiya ce, dan Allah Sageer kasaka dauriya aranka nasan zaka iya kodan ayanke wannan hukuncin kowa yasamu nutsuwa azuciyarshi.
A jiyar zuciya Sageer yayi tare da goge idonshi domin tunda Bala yafara magana yake kuka. Kallonsu yayi yace nagode da irin kaunar da kuke nuna mani. Hakika nasamu mutane nagari arayuwata, kuma kamar yanda nayi alkawari insha Allah sena karasa wannan shari'ar kamar yanda na farata. Fatana Allah yabani ikon yinta cikin nasara.
Gaba dayansu sukace amin. Salis yace ai duk wasu shedarka suna wajenka ko? Sageer yace suna nan. Allah sarki Abdul, kamar yasan haka zata faru aranar da dare muna zaune ya dauki wayata ya tura mani duk recording din da yayi awayarshi. Hakika nayi rashin Abdul, tsakanina dashi sede addu'a. Salis yace zanje wajen alkali seya sake samana lokacin da za'ayi shari'ar.
Gaba daya hankulansu atashe yake jin labari marar dadi da Brr, Yusuf yazo masu dashi akan maganar komawa kotu. D.P.O yace towai shi Sageer din harya dawo hayyacinshi daza'a koma kotun? Brr, yace nima nayi mamakin abinda alkali yace mun, kumafa lokacin hutunshi yayi ban san dalilinshi nakin tafiya ba.
Kuma sanin da nayima alkali babu abinda yake hanashi tafiya hutu idan har yadauka. Amma abun mamaki saboda wannan shari'ar gashi yadaga lokacin tafiyarshi hutu. Umar yace yanzu Yallabi kana ganin Sageer ze iya nuna wata sheda wadda zata gamsar da alkali harya yarda da abinda yace? D.P.O yace mutum daya ne ze iya kokarin tona mana asiri ko kuma yabama Sageer shedar daze iya gabatarwa a kotu.
Brr, Yusuf yace wakake ganin ze iya haka? Dr, mana. Sanin kanka ne Dr yafita daga cikinmu, kuma akowane lokaci ze iya fadar duk abinda muka aikata. Murmushi Brr, yayi yace ai kotu bata amfani da maganar fatar baki, akullum kotu tafi aiki da shedar data gani da ido, ko kuma me laifi ya amsa laifin da yayi da kanshi.
Dr, beda wata sheda daze iya nunama kotu wadda zata nuna muna da hannu akan mutuwar Mannir. Dan haka ku kwantar da hankalinku Dr, baze kara zuwa kotu ba sede idan an nemeshi.
Amma idan har kuna tsoron kada yatona mana asiri zan kirashi in gargadeshi idan har yasake yayi magana marar dadi a koti wallahi iyalanshi zasu shiga cikin tashin hankali, kasanshi da tsoro baze yarda ya aikata komai ba.
D.P.O yace yanzu idan Bukar ya bayyana yazamuyi? Sosa kai Brr, yayi yace to wai kai mekakeyi da haryanzu baka gano inda yaje ba? D.P.O yace wallahi babu inda yarana basu duba ba, amma haryanzu basu ganshi ba, Matarshi tazo wajena harta gaji amma babu labari.
Umar yace kuma ba mutuwa yayi ba? D.P.O yace amma ai da anga gawarshi. Brr, yace kana tunanin bugun da sukayi,mashi ze iya barunshi yacigaba da rayuwa? Gaskiya bana tunanin ze iya rayuwa, domin yaji bugu bana wasa ba,ko hannunshi kadai ka kalla zakasan baze iya doguwar rayuwa ba domin nacire mashi yatsu biyu, kuma kaga ba'a samashi magani ba, kilama cuta tashigar mashi hannu ko ita zata iya sanadiyar mutuwarshi. Brr, yace nima haka jikina yake bani ya mutu shiyasa bandamu sosai ba da kace ya gudu, kila daya gudu yafada wani wajen inda baza'a iya ganin gawarshi ba, karshema sede karnuka su cinyeshi.
Murnushi D.P.O yayi yace tabbas Bukar ya mutu, da yana raye kodan iyalinshi daya dawo, kuma Sageer beda sauran shedar daze nunama kotu, idan ma kuna tunanin wannan takardar daya dauka anan ne, nasan bazatayi mashi amfanin komai,ba domin ayanzu babu wukar da akayi kisan bare ace akara daukar wani result din.
Kuma vedion da Bukar yadauka na gogeta, ta wayar Shehu ma ka goge, abubuwan dasuke wayar Abdul ma gaba daya nagogesu, dan haka Sageer beda sauran madogara.
Brr, yace Umar inaso ka kwantar da hankalinka, idan har kana tare dani asirinmu baze taba tunuwa ba, nashiga gaban Sageer nafi karfinshi har abada baze taba yin nasara akai na ba. Allah ya kaimu monday din zakuga abinda zefaru a kotun.

Season 130 🖤 135
13TH SEPT, 2016.
MONDAY
HIGH COURT KATSINA STATE.
A yau kam harabar kotun tafi koyaushe cika, domin mutane da dama sun sami labarin shari'ar da ake gabatarwa a wannan kotu, da kuma yanda abubuwa suka kasance. Kowa yanaso yaji yanda shari'ar zata kasance hakan yasa mutane da dama suka halarci kotun.
Motar gidan yari ce ta tsaya, wasu masu aikin gidan ne suka fito tare da Kamal, acikinsu hada Baba Yusha'u da Gali. Su Brr, yusuf ne da mutananshi suka fito daga mota fuskarsu dauke da murmushi.
D.P.O yace kasan Allah sam banajin tsoron shari'ar nan ta yau, domin nasan kariga da kagama da Sageer. Brr, yace ai dama nafada maka, babu wanda ze iya jadani a wajen shari'a, nayi case yafi akirga kafin kaga nafadi da wuya, shiyasa ayanzu banajin komai dan zamuyi shari'a da yaron dana koyar.
Sageer ne da Salis suka jero daka ganshi kasan a kasalance yake tafiya, gaba daya yarame, haryanzu idanuwanshi akumbure suke. Sunzo wucewa ta gabansu, D.P.O yace malan Sageer ya karin hakuri kuma?
Kallonshi yayi amma bece mashi komai, murmushi yayi yace kayi hakuri bansamu nazo maka gaisuwa ba, naje wani bikin karramawa ne shiyasa, ashe hada matar da zaka aura aka kashe ta hanyar fyade ko? Kash! na tausaya maka, dama bata mutu ba nasan zaka iya maleji da ita haka.
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo ma Sageer, hannunshi Salis yakama yana fadin mungode yallabai, janshi yayi suka wuce. Dariya suka sa gaba dayansu. Brr, Yusuf yace gaskiya kai dan iska ne ya mutum zeshiga kotu zaka fada mashi abinda ze birkita mashi tunani, haka nan yaje ya manta abubuwan daya shiryo.
Dariya D.P.O yayi yace ai gara in karasa rushe tunaninshi koba komai narage mashi sauran karfin dayake dashi. Brr, yace dani yake magana, muje ga alkali can ya iso.
Kotu tacika har wasu basuda wajen zama, shigowar alkali yasa kowa yayi shiru. Bayan yazauna magatakarda yamike domin karanto karar daza'a gabatar.
A yau 13 ga watan satumba shekara ta 2016. Kotu zata cigaba da sauraron karar da aka farayi a 30 ga watan Agusta, wanda aka daga shari'ar domin rashin halartar wanda za'a tambaya a kotu. Komawa yayi ya zauna.
Dago kai alkali yayi yace Brr, Sageer kotu zataso taji sauran tambayar da zakayima D.P.O idan yana nan. Tashi Sageer yayi jiki asanyaye, haryanzu idonshi akwai sauran kwalla aciki. Tashin da yayi ne yakara tuno mashi da Abdul a waccen shari'ar.
Yana zaune abayanshi lokacin daze tashi seda yayi mashi addu'a a kunne kafin yamike, amma yanzu gashi baya wajen. Tissue yasa ya goge kwallar data zubo mashi, duk wanda yasan halin da yake ciki seda yaji tausayinshi, alkali kanshi seda yaji zuciyarshi tayi ba dadi, sosai yake tausayin Sageer.
Bayan yafito murya a sanyaye yace inaso kotu tabani dama domin inyima D.P.O wasu yan tambayoyi. Kotu tabaka dama. Cikin D.P.O ne yayi kara jin ta kanshi za'a fara shari'a.
Mal. Bello saulawa, alokacin da nake tambayar Dr, wancan karon nasan kana wajen baka kai da tafiya ba. Ina fatan kaji duk bayanin da yayi kuma yace kaine ka umarceshi daya yi haka? Hadiyar miyau yayi yace E to wallahi da yake hankalina baya wajen ina tunanin iyalina shiyasa ban fahimci abinda yake fada ba.
Oh! Ashefa haihuwa akayi maka ko? E hakane. Da kyau Allah yaraya, amin.
To a cikin bayanin da kayi kace Dr, shine likitan Mannir, kuma ka kaishi ya aunashi harya gano yawan shan kwayar da yakeyi ta haddasa mashi ciwo a zuciyarshi, wanda hakan yasa likita ya rubuta report yabaka domin asaka cikin file dinshi na gidan yari.
Segashi Dr, da bakinshi yace baka kai Mannir wajenshi ba, kawaide kace ya rubuta maka report yabaka domin ka kai. Ina fatan yanzu ka gane abinda yake nufi?
Sosa kai yayi yace to ai alokacin baya cikin hayyacinshi bare in daukeshi muje asibiti, shine naje nafadama Dr, yanayin dayake ciki shine yace ze rubuta report yabani domin asashi ya tsorata yadena shan abinda yake sha.
A ranar da Mannir yazo wajenka domin yafada maka mutuwar abokinshi kace acikin maye yake ko? Kwarai ma kuwa, domin jikinshi warin kayan maye kawai yakeyi da kyar ma yake magana.
Amma kuma yaronka Salis da kuka tafi tare dashi yace bega alamun maye atare dashi ba. Gaskiya be gani da kyau ba, nine wanda yafara ganinshi kuma nine nasan halin dayake ciki.
Tun bayan daka aje Mannir wajenka akwai wanda ka bama damar zuwa wajenshi acikin yaranka? Shiru yayi yana zare ido. Muna sauraronka? Babu.
Kenan kaine kake bashi abinci acikin kwana biyun da yayi awajenka? E nine.
Idan kabashi kana tafiya ne ko kuwa agabanka yakeci katafi da kayan? Ba inda nake zuwa harseya gama ci nake tafiya da kayan. Dafe kai Brr, Yusuf yayi jin banzar amsar da yabashi.
Kenan duk kwana biyun da yayi awajenka bacikin hayyacinshi yake ba? A'a yadawo hayyacinshi. A ranar da zakuzo kotu da kabashi abinci agabanka yaci? E agabana yaci.
Bayan yagama tare kuka fito ko kuma seda kafita ka dawo? Tare muka fito dashi ya tsaya a wajen yansanda domin sune suka rikeshi lokacin da yadan fara layi.
Yaci abinci agabanka, kuma kunfito tare, to dayaushe yasha kwayar data kawar mashi da hankali kafin kuzo kotu? Saurin zaro ido yayi jin abinda Sageer yace, sam ya manta da yace agabanshi yaci komai.
Muna jinka? E to kasan wanda yasaba da shaye shaye kila lokacin da aka sakashi cikin mota kafin azo kotu yasha, kasan ko ba ruwa suna iya shan abunsu.
Kenan Mannir yana cikin hayyacinshi lokacin da kuka fito daga office? E haka ne. Amma ya akayi a wancan karon kace da kotu tunkafin ku taho daga office Mannir baya cikin hayyacinshi? Gaskiya mantawa nayi ammade tabbas kafin mu iso yasha kwayar.
A ranar da aka kai Mannir gidan yari, me ya kaika gidan yarin da dare wajen Gali? Na'am? Kaji abinda nace ai, hannu yasa yafara share zufar data zubo mashi.
Tashi Brr, Yusuf yayi yace yame shari'a yakamata Brr, ya gyara tambayarshi, idan baku manta ba D.P.O babban dansanda ne, babu dalilin dazesa arika tambayarshi dalilin daya kaishi gidan yari, domin yana da ikon zuwa duk inda yakeso batare da wani yaji dalili ba.
Brr, Sageer ka gyara tambayarka. Komawa Brr, Yusuf yayi ya zauna yana murmushi. Gyara tsayuwa Sageer yayi yace report din da ka kawoma shugaban gidan yari wanda akayi typing ne, kuma Dr, yace kaine kace yayi typing dinshi yabaka ko?
E nine nace yayi typing dinshi saboda acikin file dinshi za'a sa. Kenan kafin ya mutu aka rubutashi? Shiru yayi yana kallon kasa. Sageer yace inajinka.
A'a alokacin dana kaishi yayi typing dinshi. Kenan yana da computer din yin typing a office dinshi? E yana dashi, amma ya akayi ya iya rubutun cikin lokacin kankani domin Inspector Salis da kukaje tare yace baku dade a office din ba?
To ai kasan kowa da irin yanayin rubutunshi, akwai wanda ze iya maka typing me yawa acikin mintuna kadan. A bayanin da Dr, yayi mana wancan karon yafada ma kotu office dinshi beda printer aciki, kuma yace ba alokacin yayi rubutun ba, mezakace da hakan?
Shiru yayi bece komai ba. Sageer yace ko bakada abincewa? Kara dukar da kai yayi beyi magana ba. Brr, Yusuf jiyayi kamar ya shako Sageer, sam beyi tunanin Sageer ze iya samun kwarin guiwar yin irin wannan tambayoyin ba.
Idan na fahimceka kafin Mannir ya rasu aka rubuta report din da ka kaima can gidan yari ko? Shiru yayi bece komai ba, Sageer yace shirunka ze iya bama kotu amsar E, daga wajenka.
Dago kai D.P.O yayi idanuwanshi harsun kada saboda tashin hankali, Sageer yace yanzu kam kotu ta fahimci ba gaskiya bane report din da aka samu na cewar kwaya ce tayi sanadiyar mutuwar Mannir, ko ba haka bane?
Ba haka bane, domin ai ansamu takardar kwayar da yasha adakinshi, kuma ansamu sauran ajikinshi, kaga kuwa dole itace zata kashe shi. To ya akayi kasan cewar itace tayi silar mutuwarshi tunda babu wanda ya aunashi? Saboda itace abu na karshe daya sha.
Amma baka tunani ko saboda damuwa zuciyarshi zata iya bugawa har tayi silar mutuwarshi tunda ansamu kofin daya zuba kwayar aciki akwai ruwa kamar besha bama?
Kwarai ma kuwa, ai kasan idan damuwa tayima mutum yawa zuciyarshi tana iya bugawa lokaci guda, tabbas maganarka haka take, bugawar zuciyarshi zata iya zamowa silar mutuwarshi.
Surutu ne ya fara tashi acikin kotun jin abinda D.P.O yace, wasuma dariya sukeyi kasa kasa, hatta da alkali seda yadanyi murmushi. Brr, Yusuf kuwa rigarshi tagama jikewa da zufa,gaba daya D.P.O yagama bata mashi duk wani shirinshi, bema san abinda ze ceba. Umar kuwa jiyake kamar zeyi gudawa saboda fargaba.
Bubbuga tebur alkali yayi sannan akayi shiru. Sageer yace amma meyasa alokacin bakayi wannan tunanin ba kuma baka bari likita yayi aikinshi ba, domin duk wata gawa daza'a kaima likitoci abu na farko dasuke farayi shine auna bugun zuciyar mutum, meyasa baka bari likita ya auna bugun zuciyarshi ba, idan har kana tunanin bugun zuciya yana kawo mutuwa?
To ai kasan duk abinda aka fara nuna ma mutum dashi yake amfani, da ace ba'a samu kwaya ajikinshi ba, kuma ba'aga alamun yashata ba to dole zamu fara duba wani abun daban.
Jinjina kai Sageer yayi yace mungode zaka iya tafiya. Ajiyar zuciya D.P.O yasaki yashare zufa yakoma mazauninshi.
Zanso kotu tabani dama domin nayima Bukar masinjan D.P.O tambayoyi. Kamar an tsinkulesu haka sukayi, D.P.O zumbur yamike tsaye saboda firgici, hankalin kowa ya koma kanshi, ganin ana kallonshi yasa Brr, Yusuf yayi saurin kamoshi yazauna.
Fitowar Bukar bakaramin dagama su hankali tayi ba, ashe dama Salis yasan inda yake amma yarika nuna mashi besan komai ba? Kenan shima Salis yana bayansu? Wannan tunanin D.P.O shikadai yakeyinshi. Umar kuwa tuni hawaye sun fara zubomashi saboda tsabar tsoro.
Kotu zataso taji sunanka da kuma aikinka? Sunana Abubakar amma anfi sanina da Bukar, kuma ni masinjan D.P.O Bello Saulawa ne.
Shekararka nawa kana aiki a karkashinsa? Zan kai shekara 5. Shin wane irin sani ko sheda zaka iya yima megidanka? A gaskiya babu wata sheda me kyau dazan iya yimashi, domin nida nake zaune dashi nafi kowa sanin halinshi.
Duk wata munakisa dayakeyi akan idona yakeyinta,atunaninshi saboda ina kasan shi bazan iya yin komai ba. Hakika nasan na dade ina ganin yallabai yana abubuwa marassa kyau, sede alokacin yana kyautata mani shiyasa ni kuma son kudi yahana ni fadama wani.
Banta ba tunanin tona mashi asiri ba se a wannan karon, shima ada banyi niyar fadar komai ba duk da nakasance ina da babbar shedar dazata nunama kotu wanda ake zargi da aikata kisan abokinshi bashine yayi ba. Amma naki nunawa dan nasan bawani abu hakan zata haifar ba.
Duk da Yallabai besan ina bibiyarshi ba haka kawai yake bani kudi badan komai ba sedan kara rufe mun baki. Yallabai Salis shine mutumin farko daya fada mani gaskiya kuma ya nuna mani muhimman cintemakon da zanyi.
Zufa tamkar an zuba ma D.P.O da Brr, Yusuf ruwa haka tarika zuba daga jikinsu. Ta message Brr, Yusuf yaturama D.P.O cewa koda asirinshi ya tonu kada ya fadi gaskiya ya bari yasan yanda zeyi ya fitar dashi. D.P.O yace wallahi tsoro nakeji idan kuma baka fitar dani ba fa? Brr, yace kayarda dani kaji.
Sageer yace Bukar ko zaka iya fadama kotu irin abinda kagani awajen megidanka har kayi kokarin fadin gaskiya? Kwarai ma kuwa.
A ranar da Mannir yazo wajenshi domin yakawo kara akan wasu sun kashe abokinshi, yana gama fada mashi naga yallabai yasashi mota yace sutafi, kuma alokacin da yazo babu wani alamu na maye atare dashi, kawaide tsoro ne da firgici.
Bayan kamar awa guda ina zaune bantafi ba senaga sundawo, wani daki ne wanda se mutum yanada matsayi ake ajeshi awajen, can naga yallabai ya kai Mannir. Bayan sun shiga ya rufo kofar hakan yasa ni kuma naje na labe dan inji abinda zasuce.
Inaji yallabai yana fada mashi ya kwantar da hankalinshi yayi mashi hakane saboda kada akasheshi, domin wadan da sukayi kisan sun san shikadai ne yagansu. Shine yace ze ajeshi a nan har zuwa lokacin daza'a tafi kotu seya kaishi kuma ze tsaya mashi yafadi gaskiyar abinda yasani.
Bayan kwana daya ina zaune da safe senaga Brr, Yusuf shida Brr, Umar sunzo wajenshi, abinda nasani duk lokacin da Brr, Yusuf yazo wajen yallabai tabbas samuwace, domin shikadai ne dansandan da Brr, ya yarda dashi, kuma dashi kadai suke harka...............................
Anan yafada masu abinda yaji suna fada lokacin dasu kazo office din D.P.O da kuma shawarar da Umar yabada akan adauki tambarin hannun Mannir ace shiyayi kisan.
Gaba daya kotu tacika da hayaniya, tashi Brr, Yusuf yayi yace yameshari'a wannan maganar ba gaskiya bace, kawai Brr, Sageer yadauko Bukar ne yabiyashi dan yazo ya tozartani, dama kuma ai yafada mani tunda nakoreshi aiki yace seyaga bayana.
Bubbuga tebur alkali yayi yana fadin ya isa. Korafi be karbu ba. Bukar zaka iya cigaba da bayaninka. Komawa yayi yazauna yana share zufa.
Bukar yacigaba da fadin, alokacin danaji wannan magana sam banji komai ba, domin nasaba jin abinda yafi haka agurinsu, kawai nayi tafiyata, sede zuciyata takasa nutsuwa hakan yasa daga ranar nafara bibiyar yallabai domin inga yanda abun ze kasance, bawai dan inzo infadi gaskiya ba.
Aranar da dare yallabai yakira Mannir akan yazo office dinshi, ina kallo yasa shi yadauko mashi ruwa a glass cup, sede be karba ba, yasa shi ya aje, bayan yatafi yasa kyalle yadauki kofin yafita dashi. Da safe naji suna waya akan angama hada takardar hoton yatsun Mannir kuma gashi yasa a file.
Haka na cigaba da binshi, aranar daza'a kawo Mannir kotu tunda safe yallabai yazo, abinci yakawo mashi se kuma yashiga office dinshi domin yadauko mashi ruwa, ina kallon lokacin daya zuba wani abu acikin ruwa ya kawoma Mannir. Yana gama cin abincin yasha ruwan kawai naga yadafe kanshi.
Tashi Brr, Yusuf yayi yace yame shari'a inada ja akan wannan magana ta Bukar, kotu bata amfani da maganar baki, idan har gaskiya yake fadi yakamata yabada kwakkwarar shedar da kotu zata gani bawai ya ajemu yana bamu labari ba.
Bukar yace inada sheda yame shari'a. Murmushi Brr, Yusuf yayi yace ai seka nuna mana ita idan har kana da ita. Bukar yace zan nunata yanzu, atunaninku kun kashe maciji ko? Sede kun manta baku sare kanshi ba.
Nasan kana tunanin kun goge abinda nake dashi. To yanzu kowa zega asalin abinda yafaru. Yame shari'a alokacin da yallabai yake zuba maganin da yabama Mannir nadauka da wayata, kuma yallabai Salis shine mutumin daya tunasar dani mahimmancin fadin gaskiya shiyasa nayi alkawarin koda zan rasa raina zan tsaya harsenaga an bima Mannir hakkinsa.
Ayanzu haka vedion dana dauka tana cikin wayar Brr, Sageer, duk da sun goge tawa sede abinda basu sani ba naturamashi. Kuma sajan Shehu shine mutumin daya ga vedion awayata yaturata domin ya kai masu kuma yabasu har suka sallameshi da kudi masu tsoka.
Alkali yace yana bukatar projecter domin a haska kowa yagani. Cikin mintuna kadan aka hada komai. D.P.O kuwa dukewa kasa yayi yana hawaye domin yasan asirinshi yagama tonuwa, aranshi yana fadin idan har asirinshi ya tonu na kowama seya tonu.
Cike da mamaki mutane suka rika kallon abinda D.P.O yake aikatawa, kowa da abinda yake fadi, alkali kam cire glass din idonshi yayi saboda tsananin mamaki, aranshi yana kara godema Allah dayasa aka dawo da wannan case din da yanzu shikenan ya yanke hukunci akan kuskure.
Bubbuga tebur alkali yayi hakan yasa kowa yayi shiru, kallon Bukar Sageer yayi yace bayan Sajan Shehu ya kai masu vedion kozaka fadama kotu abinda yafaru?.............................................
Duk abinda sukayi mashi da irin azabar dasukayi mashi seda yafada ma kotu, harzuwa lokacin da suka kamo Saddika da abinda sukasa yaransu sukayi mata da abinda yaran sukayima Abdul seda yafada.
A lokacin Sageer kasa daurewa yayi haka yarika kuka kamar karamin yaro, sam yamanta agaban kotu ma yake, domin lokacin da Bukar yake bada labarin gani yake kamar agabanshi ake aikatawa, runtse ido kawai yayi yana kuka, seda yasa mutane dayawa nacikin kotun kuka sosai aka tausaya mashi.
Salis ne yazo yakamashi yazaunar dashi domin yaga jikinshi yafara rawa, alkali kanshi seda idonshi yacika da kwalla, kotun tadade ahaka kafin alkali ya buga tebur akayi shiru. Sanin Sageer baze iya cigaba da shari'ar ba yasa yace kotu zata daga wannan shari'ar zuwa jibi.
Kafin nan kotu tabada umarnin yansanda sukama D.P.O, Brr, Yusuf, Umar, Sajan Shehu da kuma Dr, a tsaresu harzuwa jibi sannan azoma kotu dasu. Kuma kotu tanaso yansanda suyi kokarin kamo yaran dasuka aikatama Saddika da Abdul wannan abu kafin jibi. Haka zalika Kotu tanason azo mata da Ammar dan gidan Alh, Abbas zuwa jibi. Kotttt!!!!!
Brr, Yusuf jiyayi kamar kasa ta tsage yashige saboda kunya, Umar kuwa kukan ma ya kare se tsabar tsoro, D.P.O kuwa yamakasa kallon kowa, haka Salis da sauran yaranshi suka tasa keyarsu zuwa police station.
Bala da Baba sune suka kama Sageer suka tafi dashi domin kuka kawai yakeyi. Haka kowa yatafi yana jimamin abinda yafaru, kowa yana fatan zuwan jibi domin suji wannan shari'a me sarkakiya.
Nima nace Allah ya kaimu lafiya😎.

Season 135 🖤 140
Umar ne ya kalli Brr, Yusuf da idanuwanshi da sukayi ja saboda kuka yace wallahi bantaba danasanin saninka ba se yau, gaka dan uwan Abbana amma karasa irin turbar dazaka dorani akai se wannan bakar turbar wadda daga karshe babu inda takaini sega halaka.
Ko auren fari banyi ba, alokacin da nakeji da kuruciyata ka jefani cikin fitina, yanzu shikenan rayuwata haka zata kare, wallahi gara ma ace a kotun musulunci za'a yanke mani hukunci nasan bazan kara dadewa a duniya ba.
Amma wannan kotun tsarin dokar kasa suke bi bazata kashe mu ba sede ayita ajiyarmu agidan yari har karshen rayuwarmu. Gidan da babu dadin zama, yan iska kala kala zaka hadu dasu, ga aikin wahala wanda tunda uwata ta haifeni bantaba yin irinshi ba.
Lallai na biyema rudun duniya da kuma sharrin ka, wallahi gara ace wani bare ne yasani wannan hanyar da ace wai jinina ne ya koya mun duk wannan bala'in. Kaico na da wannan aiki dana samu akarkashinka.
Saukar marin da yaji ne tasashi yin shiru yacigaba da kuka, Brr, Yusuf cike da bacin rai yace kai har kana da bakin da zakamun irin wannan maganar? Wato kamanta duk irin halarcin danayi maka har zaka fadi haka ko? To meyasa alokacin dana fara jiya maka dadi baka fadi haka ba?
Uhmm lallai kai yaro ne, to wallahi ku tsaya kowa yaji abinda zan fada mashi, duk wanda ya kuskura yakara fada mani wata mafanar banza wallahi senayi maganinshi. Saboda acikinku babu wanda nayima dole, kowa da yaga kudi se ya haukace.
Acikinku akwai wanda yataba tunanin yimani wa'azi ko so daya ne? Babu, domin kowa yana tunanin idan yafada mani zan dena bashi abinda nake bashi. Haka duk wani dan Adama yake fada alokacin da asirinshi ya tonu.
Nima inajin abinda nakeji, kada wanda yakara kawo mani ciwon kai, abinda yakamata muyi neman mafita bawai mutsaya muna cewa wannan ne yasamu ko ya bata muba. Kallon Dr, yayi wanda yaketa kuka, murmushi yayi yace Dr, kadena wannan kukan domin kai kana da sauran rayuwa, babu wanda ka kashe.
Mune yakamata muyi kuka, sede kuma ni bana saurin karaya, domin mahaukaci shine yake dukan jaki, amma me hankali shiyasan yanda yake bidashi. Bantaba gazawa arayuwata ba, kuma haryanzu bazan gaza ba. Wannan yakinin daga zuciyata yake.
Murmushi D.P.O yayi yace lallai abokina kanada karfin hali, wato duk irin shedun da aka gabatar ma kotu dama wasu wanda zasuzo daga baya basu isa su saka ka saduda ba ko? Nikam nasan ko iyakar vedion da aka gani kadai ta isheni a yanke mani hukunci.
Brr, Yusuf yace kaine aka nuna shedar ka, kuma kaine sukeda shedar da kotu zata gani, domin kotu da shedar zahiri take amfani bata badini ba, nikam nasan basu da wata shedar dazata nuna ma kotu inada laifi acikin case dinnan, sede kawai kowa yafadi tabakinshi kuma nasan bazata bada ma'ana ba.
Sajan Shehu da Dr, babu abinda sukeyi se kallonsu, gaba dayansu kuka sukeyi, Shehu sosai yayi nadamar abinda ya aikata gashi tun begama more kudinshi ba asirinshi ya tonu.
Zaune suke agidansu Salis sunata lallashin Sageer, Bala yace ai kayi kokari Sageer, kuma kabama Brr, Yusuf mamaki, domin naga tsananin tashin hankali a idonshi, kuma ko ayanzu yasan cewar kafishi basira. Dan haka kayi hakuri insha Allah lokacin farin cikinka yakusa zuwa.
Baba yace haka ne, basuyi zaton zaka kawo shedu kamar haka ba, sam basuda shirin tonuwar asirinsu, segashi abun yazo masu daga sama. Inaso kabani wannan sarkar da Kamal yabaka, inaso in bashi yarike awajenshi idan an koma kotu ka kirashi domin ya bada sarkar da kanshi.
Salis yace wannan haka ne, kuma insha Allah wannan komawar da za'ayi itace ta karshe, kuma zanyi iya kokarina inga yaran yallabai sun shigo hannuna ayau din nan. Bukar yace ina tunanin bazasu wuce wajen gidan gonar Brr, Yusuf ba, domin acan wajen naji yace suke.
Salis yace bakomai zamu fita ayau zamu kamosu. Shi kuma Ammar nasan za'a aika ma Babanshi da takardar sammaci. Bala yace amma baka tunanin ze iya guduwa yabar kasar tunda sunada kudi baze rasa biza ba?
Salis yace wannan haka yake,zanyi kokarin kamoshi, gara shima mu tsareshi kada yaja mana wata dagawar shari'ar, nafiso ace zuwa jibi an kammala komai domin hankalinmu ya kwanta musan abunda zamuyi ma arayuwarmu ta gaba.
Sageer ya goge idonshi yace Allah ya biyaku da mafificin alkhairin abinda kuke mani. Nima nakosa agama wannan shari'ar nima nahuta, ina ganin daga wannan shari'ar zan bar aikina, domin yafitar mani arai, sam bana son incigaba da wannan aikin.
Adalilinshi narasa mutane guda 2 masu mahimmanci arayuwata, banaso incigaba da aikin kuma wani abun yazo yafaru da wadan da nake tare. Dafashi Baba yayi yace Sageer kataba ganin wanda Allah yanufa da wata kaddara ya kauce mata?
Ko kana wannan aikin kobaka yinshi dole se wannan abu yafaru dasu, babu wanda yake wuce kaddararshi. Idan kuma kace zaka aje aikinka to me kakeso kayi? Ashe bazakaso ka mutu ta dalilin daukaka gaskiya ba?
Idan magabata basuji tsoron mutuwa saboda fadin gaskiya ba, bana tunanin mu zamu tsorata, domin su afagen yaki ake kashe su, suna sara ana sararsu amma ahaka suke kokarin tabbatar da gaskiya.
Dede da rana daya basu taba gazawa akan abinda sukeyi ba, idan baka manta ba, wasu daga cikinsu suna wa'azi ana jifarsu ana zaginsu, amma duk da haka basu taba sarewa ba. Kai fa? Kana cikin rufin asirinka, kawai wani aiki ne zakayi dan kadan, babu wata wahala, babu zufa babu ciwon jiki.
Kawai zakayi amfani da baiwar da Allah yabaka ne wajen ceton talakawa marassa karfi daga danne masu hakkinsu da akeyi. Kuma kowa ya sani azamanin nan na yanzu masu kudi sune sukeda karfi a ko ina.
Duk inda ka kaisu sune suke nasara badan komai ba sedan sun ruga da sun saye mutane da dukiyarsu. Idan za'a rasa irinka a wannan aikin naku, to tabbas azzalumai irinsu Yusuf zasu daukaka aduniya.
Ni na tabbata acikin masu irin aikinku akwai wadan da suke son su tabbatar da gaskiya amma saboda tsoro da rashin wadatar zuci yasa sukayi shiru, domin kowa yadauki wannan aikin naku tamkar sana'a, duk yanda ake bama mutum albashi baya godewa yafiso ya karbi karar masu hali.
Badan komai ba sedan sun san zasu samu dukiya me yawa, shiyasa akoda yaushe talakawa sune suke faduwa akotu, domin basuda karfin dazasu iya ja da masu kudi. Idan har za'a samu irinka kamar 2, tabbas sekun dakushe azzaluman lauyoyi masu karbar cin hanci suna danne gaskiya.
Kamar yanda kace kadaukeni amatsayin mahaifi, ina rokonka da girman Allah kacire duk wani shakku azuciyarka, kasama ranka wannan aikin naka tamakar jihadi ne, ko mutuwa ma zaka iyayi akanshi, kada kace zaka barshi, domin zaka rusa farin cikin talakawa da yawa,na tabbata awannan shari'ar talakwa da dama zasuyi farin ciki, domin ansamu wanda zerika tsaya masu.
Jinjina kai Sageer yayi yace shikenan Baba, insha Allah zancigaba da aikina, kamar yanda kace, sede kila zuwa gaba na canza aiki amma bazan barshi duka ba, fatana Allah ya ciremun son zuciya ya kuma kareni daga sharrin shedan kada na kasa cika alkawarin dana dauka. Sosai Sageer ya burgesu sukace amin.
Zaune yaran D.P.O suke a bayan gidan gonar Brr, Yusuf suna kasa wasu kudi da suka sato a wani gida, bayan sun gama ne wani yace wai Oga haryanzu fa yallabai be kara waiwayarmu ba, kuma kaji yace idan komai ya kammala ze kara mana wani abu.
Ogan yace nima tunanin da nakeyi kenan,kadafa ya raina mana hankali, yau kusan sati guda kenan bekara kirana ba, kuma nasan Alh, Abbas ba karamin me kudi bane, ze iya basu ko nawa ne inde zasu rufe case din danshi. Kuma da alama har anyi case din sun karbe kudin sun barmu haka nan.
Amma kabarsu,basu san kowaye ni ba............. Saukar bindigar dayaji asaman kanshi ne yasashi yin shiru, kafin su ankara yan sanda sun zagayesu, cike da firgici suka fara kokarin tashi. Salis ne yace duk wanda ya motsa sede uwarshi takara haifo wani. Jin haka yasa kowa ya nutsu. Haka suka tasa keyarsu da kayansu suka nufi police station dasu.
Zirga zirga kawai yakeyi afalonshi hannunshi rike da takardar da megadinshi ya kawo mashi yanzu ta sammaci daka kotu. Mom din Ammar ce tashigo tana fadin Alh, lafiya naganka atsaye? Juyowa yayi idanuwanshi har sunyi ja.
Zama yayi yana fadin inafa lafiya. Ina Ammar yake? Mom tace ai kasan yana dakinshi suna kallon kwallon dasuka saba, tsaki yaja yana fadin wato shi har lokacin kallon kwallo gareshi ma. Duk wannan tashin hankalin da nake ciki waye yasani inba shiba.
Duk fadi tashin da nakeyi na neman kudi badan kowa nakeyi ba sedanshi, amma gashinan yaje yajawo ma kanshi abinda ze hanashi cin moriyar dukiyar dana tara mashi. Dafe kirji Mom tayi tace mekake nufi Alh?
Takardar hannunshi ya nuna mata yana fadin fitinar da yaje yajawo mana kwanakin baya, wadda muke tunanin mun kashe ta to yanzu itace ta dawo. Yanzu aka aiko mani da sammaci daga kotu ana neman Ammar ranar laraba.
Mikewa tsaye tayi cike da tashin hankali tace dan Allah Alh, kada kabari su kashe mani Ammar, wallahi bazan iya rayuwa ba idan wani abu yasa meshi. Kabasu duk wata dukiyarka nide subar mani yarona.
Kallonta yayi yace bansan meyake faruwa ba, Brr, Yusuf yace inbashi kudi wancan satin domin an maido da shari'ar Ammar baya, kuma natura mashi kudade masu yawan gaske, kuma da bakinshi yayi mani alkawarin ze kashe case din.
Da naji shiru ma nadauka komai yawuce shiyasa ban fada maki ba, amma segashi yanzu an aiko mani da sako. Kuma nakirashi wayarshi kashe shiyasa nakejin tsoro, dan babu wani lawyer wanda ze iya tsaya mana kamarshi. Cikin kuka Mom tace to wai wane lawyer ne ya maido da case din? Alh, yace nima shine abinda nakeso insani.
Saurin daukar wayarshi yayi yace ina zuwa bara inkira wani yaro da yake aiki a babbar kotun, nasanshi zanji komai ai. Bugu 2 aka dauki wayar, bayan sun gaisa Alh, yake tambayarshi abinda yake faruwa................
Duk abinda yafaru a kotun seda yafada mashi, hada kullesu Brr, Yusuf da akayi. Godiya yayi mashi cike da tashin hankali ya kashe wayar. Kallon Mom yayi yafada mata abinda yake faruwa. Kuka tasa tana fadin shikenan munshiga 3, yanzu kashe Ammar za'ayi ko? Hakuri yafara bata yace kibari gobe zansa akira mani lawyer din daya tsaya masu.
Koda ze karbi duka dukiyata wallahi zan iya bashi matukar zesa arufe case din, kuma ze bani duka shedun da yake dasu in konasu da kaina. Mom tace kana ganin ze yarda? Murmushi yayi yace bakiji menace ba? Kudi, babu wani dan adam dabaya son kudi, zan bashi kudin dazasu gigitashi harse yamanta da wata gaskiya.
Zansa gobe driver ya dauko manishi, zansa a binciko mani unguwar dayake ayau din nan. Jeki kira mani Ammar yazo ya san halin da ake ciki, dole yazo yabar kasar nan zuwa gobe idan har wannan lawyer beyarda da bukata ta ba. Mom tace amma idan yatafi kai zasu kama fa.
Alh, yace zema yarda insha Allah babu wanda za'a kama, sede inaso idan case din ya mutu gaba dayanmu zamu tafi waje muyi hutu kona wata 2 ne domin musamu nutsuwa dan na dade banshiga tashin hankali irin wannan ba. Shiyasa ake cewa dan kuka mejama uwarshi jifa.
Bansan meyasa Ammar ya aikata wannan babban aiki ba. Mom tace to kasan yaran talakawa da hassada yanzu haka shine yafara janshi kasan kuma Ammar beda hakuri kuma bayason raini shi kuma ya bigeshi har zuciya tajashi ya caka mashi wuka.
Tsaki Alh, yaja yace wallahi shiyasa banso yadawo kasar nan ba, naso ace ya zauna acan sede yazo mana hutu ya koma, kawai kece kika nuna kinaso yadawo. Amma me akeyi da talaka, arayuwar talaka babu abinda ya tsana kamar yaga mekudi ya wuce cikin babbar mota, ya gina katon gida, yasaka kaya masu tsada yanzu sekaji hassada tafara tashi yana fadin kila tsafi yake yana samun kudin.
Shiyasa sam,banason kulla alaka da talaka, domin beda wata rana arayuwata. Mom tace ai dole yabar kasar nan, bara na kirawoshi. Tafiya tayi domin takirashi. Alokacin kuwa Ammar da abokinshi suna kwance haihuwar uwarsu suna aikata abinda suka saba.
Sam sun manta basu rufe kofar ba, domin yasan babu meshigo mashi daki, ko nemanshi Mom takeyi sede takirashi awaya. Suna tsaka da jin dadinsu Mom ta tura kofar falon. Jin shiru yasa ta nufi dakinshi.
Tsoro ne yafara kamata saboda wani irin nishi da take jiyowa acikin dakin, gashi wutar dakin akashe take, tunani tayi ko Ammar ne beda lafiya shiyasa tayi saurin shiga, tana zuwa ta kunna wutar dakin. Mutuwar tsaye Mom tayi domin abinda tagani bakaramin tsoratata yayi ba.
A zabure suka tashi suna neman abinda zasu rufe jikinsu dashi. Da sauri abokin Ammar yadauki kayanshi yashige toilet, Ammar kuwa bargo yaja ya rufe jikinshi. Dukewa Mom tayi tana kuka kamar ranta ze fita.

0 comments:
Post a Comment