Saurin tashi Ammar yayi yasa kayanshi, abokinshi kuwa fita yayi da sauri dan besan abinda Mom zatayi mashi ba. Karasowa wajenta yayi har lokacin tana duke tana kuka, dukawa yayi yana kuka yadafa kafarta yace.
Mom dan Allah ki rufama mani asiri tsautsayine yasa muka ai kata hakan, kuma bamu taba ai katawa ba se yau, shima wani film muka kalla shine shedan ya rinjayemu har haka. Amma nayi maki alkawarin bazan kara ai kata haka ba.
Dago kai tayi ta share idonta tace Ammar kasan banason karya, duk wanda ya ganka yasan ba wannan ne karo nafarko daka fara ai kata wannan aikin ba. Dama wannan dalilin ne yasa sam baka kula kowace mace? Dama wannan dalilin ne yasa kullum kake zaune agida bakada aikinyi se kallon kwallo?
Lallai Ammar ka cutar da kanka, ka daukarma kanka muguwar rayuwar da Allah zeyi fushi da kai ba, kasan kuwa irin zunubin danaji ance masu ai kata wannan laifin suna dauka? Duk da banida ilimin addini me zurfi amma nasan aikata Zina da luwadi babban laifi ne.
Ammar dole masifa zata rika binka, ashe kai ne kake jawota da kanka, koyanzu ma bakasan masifar datake tunkaroka bane shiyasa har kasamu damar shiguwa daki har kana aikata wannan mugun abun.
Katashi muje Dadyn ka yana son ganinka. Saurin dagowa yayi yana kuka yarike hannunta yana kuka yace dan Allah Mom kirufa mani asiri, babu wanda yasan ina aikata wannan abun seke, dan Allah kada kibari Dad yaji nasan zeyi fushi dani.
Share idonta tayi tace shikenan, kaima kasan babu wata Uwa dazata iya tona ma danta asiri, shafa fuskarshi tayi tace kada kadamu babu wanda zan fadama mawa, tashi muje kada yaga mundade, goge idonshi yayi suka fita.
A zaune suka sameshi ya dafe kanshi, kusa dashi Ammar yaje yazauna tare da dora kanshi saman kafarshi. Runtse ido Dad dinshi yayi, hannu yasa yana shafa kanshi, lokaci guda wasu zafafan hawaye suka zubo mashi.
Hannu yasa yayi saurin gogewa, dago kai Ammar yayi yana fadin Dad lafiya de, naga kamar bakajin dadi ko? Murmushi yayi yace lafiyata kalau Ammar, kawaide akwai wata yar damuwa ne, dazu kotu ta aiko da takarda tana son ganinka. Saurin tashi tsaye Ammar yayi yana zare ido.
Kamoshi yayi yana fadin ka kwantar da hankalinka babu abinda ze sameka, koda zan karar da duka dukiyata zanyi kokarin kareka daga kowane bala'i daze sameka. Kuka Ammar yafara yana fadin dan Allah Dady kada kabari a kashe ni.
Rungumeshi Mom tayi tana kuka tace babu wanda ze kasheka Ammar, kana tare damu bazakaje ko ina ba, haka sukayi ta kuka, Dad ne yake kokarin lallashinsu. Sallama sukaji ta megadinsu, amsawa Dad yayi yana fadi shigo mana. Saurin mikewa sukayi ganin megadinsu tare da yan sanda.
Da sauri Ammar yakoma bayan Dad dinshi ya boye yana kuka, Salis ne yashigo yana fadin barka da dare Alh, kallonshi yayi bece komai ba. Salis yace Alh, nasan kasamu sako daga kotu, dan haka kamar yanda alkali ya bukata kafin jibi muzo mashi da Ammar, shine mukazo tafiya dashi domin mu ajeshi awajen mu tare da sauran wadan da alkali yace azo dasu.
Kallonshi Alh, yayi yace inspector idan bazaka damu ba inaso inroki wata alfarma awajenka. Salis yace inajinka. Dan Allah inaso kabar Ammar awajena, ni nayi maka alkawarin jibi tare zamuzo kotu, kasan ni kuma kasan gidana, idan har Ammar bezo kotu ba ni nayarda kazo ka kamani.
Shiru Salis yayi bece komai ba, Mom tace dan Allah kabarshi wallahi zamu kawoshi amma banaso akaishi office dinku. Jinjina kai Salis yayi yace shikenan, zan barshi dama munzo tafiya dashine saboda muna tunanin ze iya guduwa, amma tunda kace zaka akwoshi bakomai.
Godiya sukayi mashi Alh, yace dan Allah kozan iya ganin lawyer din da yake gabatar da shari'ar? Sails yace sunanshi Brr, Sageer. Alh yace idan bazaka damu ba kozaka fada mani unguwarsu inaso inganshi ne, murmushi Salis yayi dan yagane me yake nufi.
Salis yace badamuwa agida daya muke dashi, Alh, yace yauwa kamun kwatancen unguwar gobe da safe zan turo driver yadaukoshi. Salis yace badamuwa, zan kawoshi da kaina, domin Salis yana tsoron kada ya fada mashi yatura masu yan fashi. Alh, yace to,nagode, sallama sukayi masu sukatafi.
********** *********
Washe gari da safe, da misalin karfe 11:00 su Sageer suka isa gidan su Ammar, zaune suke afalon Alh. Bayan yashigo suka gaisa ya kalli Salis yace kozaka dan bamu waje? Salis yace badamuwa Sageer idan kungama ina waje. Bayan yatafi Alh, yakalli Sageer yace malan Sageer kayi hakuri na tadoka kana hutawarka.
Murmushi Sageer yayi yace bakomai. Alh, yace naji labarin kaine lawyer da kake tsayama wadan da suke karar Ammar ko? Sageer yace haka ne. Alh yadauko wani akwati, budeshi yayi sega kudi cike aciki.
Kallon Sageer yayi yace, wannan kadan ne daka cikin abinda zan iya mallaka maka matukar kayarda kabani duk wata shedar da kake da ita, kuma kasa alkali ya sallami wannan case din. Sageer zan mallaka maka dukiyar da har ka mutu bazakayi talauci ba, nide bukatata shine dana yacikaba da rayuwa cikin jin dadi da kwanciyar hankali.
Bandamu da kowa yayi farin ciki ba matukar dana zekasance acikinshi, dukiya awajena ba matsala bace, zan iya badata domin lafiyar dana kuma dama sabodashi nake tara ta. Kallonshi kawai Sageer yake cike da mamaki, besan lokacin da kwalla ta zubo mashi ba.
Tashi yayi bece mashi komai ba ya nufi hanyar fita. Saurin tashi Alh, yayi yace Sageer lafiya, ya ina maka magana zaka tashi bakace mun komai ba, kode kazone dan kayi recording duk abinda zance dan ka kara samun wata shedar akotu? Ashema kai ragon lawyer ne inde seta haka ne zaka hada shedunka.
Cak Sageer ya tsaya, dawowa yayi yana kallon Alh, hannu yasa ya goge idonshi, kallonshi yayi yace me kace? Nine zan ha'inceka domin insamu shedar dazata temaka mani akan wannan case din. To tsaya kaji, koda ace shedar ka ita kadaice zata sa nayi nasarar wannan case to wallahi gara na fadi.
Domin sheda daga bakin irinku asara ce, domin kai azzalumi ne, ma ha'inci, kuma me sabon Allah. Me ma kace dazu? Zaka iya bani dukiyar da har na mutu bazanyi talauci ba ko? To bara kaji, nasan cewar bakaje makaranta ba shiyasa har kake tunanin zaka iya azurta dan adam. To tsaya kaji, babu me iya azurtawa se Allah, kuma shikadai ne yake da ikon talautawa.
Kai waya fada maka zaka mutu cikin arziki? Wane tabbaci gareka nacigaba da rayuwar da har zaka iya azurta wani harya mutu beyi talauci ba? Kuma maganar farin cikin danka da kakeyi ina me tabbatar maka saura kwana daya ya kauracema fuskarshi.
Wato ta danka kawai kakeyi, su kuma wadan da suka rasa nasu basuda zuciyoyi ajikinsu ko? Ko kuma bacci suka kwanta suna tashi suka ga Allah yabasu 'ya'yan ko? Shiyasa kake tunanin danka kadai ne yasan farin ciki ko? To kajira zuwa jibi zaka san suma talakwa suna da 'yanci.
Tsaki yaja yafita. Zufa ce kawai take zuboma Alh, gabadaya hankalinshi yagama tashi, Mom ce tafito cike da damuwa tana fadin Alh, be amince ba ko? Zama yayi yadafe kanshi, zama tayi kusa dashi tace dan Allah kafada mani abinda yake faruwa.
Kallonta yayi yace be amince ba. Kuka tasa tana fadin shikenan yanzu zamu rasa Ammar kenan? Dan Allah kada kabari murasa farin cikinmu. Jawota yayi yana lallashinta, yace ki kwantar da hankalinki.
Ai se muna kasar za'a iya kamamu, yanzu zansa ayi mana komai, natafiya, tunda muna da visa nasan samun tafiya baze mana wuya ba. Kuma ta abuja zamu tashi, ayau dinnan zamu tafi zuwa dare nasan zamu iya tafiya.
Tashi tayi tana murmushi tace nagode Alh, kuma kana ganin koda mun dawo baza'a kamashi ba? Murmushi yayi yace ai idan har muka dauki kamar wata 5 bamu dawo ba, dole zasu hakura damu, kinsan kotu tana da aiyuka agabanta bazata iya tsayawa tana jiran wani case yarika bata mata lokaci ba. Jeki fara hada mana kaya mubar garin.
Zaune suke a office din Salis bayan Sageer yagama fada mashi duk abinda yafaru. Jinjina kai Salis yayi yace ai dama tunda naji yace yana nemanka nasan baze wuce ya rokeka ka bar wannan case din ba. Shiyasa nagama shirya duk wani abu dazesa nakamashi da hannuna domin banyarda da abinda yace mun ba wai zekawo Ammar kotu.
Bayan naje gidan, nafara tunanin matukar besamu hadin kanka ba dole yace subar kasar, kuma nasan dole ta abuja ne zasu tashi domin acan ne yake da hanya. Nasan ayanzu haka suna shirin tafiya abuja, shiyasa na shirya masu gadar zare, kuma ina me tabbatr maka yau din nan a cell zasu kwana, ko basu kwana su duka ba dole Ammar ya kwana awajenmu.
Ayanzu haka akwai wanda nasa ya kular mani da shige da fitansu, nasan dole cikin 2, suyi daya, kode sutafi ta jirgi, ko kuma sutafi da mota, shiyasa na baza yarana duk ta inda sukabi zasu kamasu. Sageer yace hakan yana da kyau, nima nafiso ace Ammar yana wajenku har zuwa gobe. Salis yace insha Allah yau ze shigo hannu.
Bayan Mom tagama hada masu kayansu suka rufe gidan, sallahu yabama megadi akan duk wanda yazo yace mashi sunje kano amma yau zasu dawo. Haka suka shiga mota Ammar se shigewa jikin Mom yakeyi kamar wani karamin yaro.
Yaron da Salis yasa ya duba mashi fitarsu ne yakira yasheda mashi sun tafi. Tafe suke amota Alh, yana ta lallashinsu yana kara karfafa masu guiwa, da yake bata jirgi zasu tafi ba.
Suna cikin tafiya kamar daga sama sukaga pilice, saurin taka burki Alh, yayi cike da tsoro suke kallonsu. Salis ne yafito hannunshi rike da bindiga. Murmushi yayi yace Alh, Abbas ina kuma zakuje? Fitowa yayi yana share zufa yace wallahi zamuje abuja ne, amma ayau zamu dawo.
Salis yace da kyau, zaku iya tafiya, sede zaku bamu Ammar yazauna awajenmu kasan yanzu karfe 2 ne, kafin ku kai abuja zakuyi dare, yaushe kukaje har kuka dawo muda zamu shiga kotu gobe? Hadiyar miyau Alh, yayi yana raba idanu.
Bude kofar motar Salis yayi yana fadin ku kamoshi mutafi, Mom ce tafito tana kuka tace dan Allah kuyi hakuri, wal........... Hannu Salis yadaga mata yana fadin idan kunason ganin danku sede ku fasa tafiyar, amma dole se muntafi dashi.
Bejira abinda zasu ce ba yafito da Ammar se rike Mom dinshi yake yana kuka, haka suka sa shi cikin motarsu suka tafi, zubewa Mom tayi tana kuka, shima Alhajin kukan yakeyi, da kyar ya lallashi Mom suka koma gida.
Anwar ne da Dr, Shamsu zaune a office, Anwar yace abokina ya shirin biki fa? Murmushi Dr, yayi yace kai za'a tambaya ai, Anwar yace wallahi jinake kamar injawo Sati 3 dasuka rage.
Dr, yace ai kamar gobe ne zakaga lokacin yazo. Wai kasan shari'ar da ake gabatarwa kuwa a babbar kotu? Anwar yace najide ana maganarta amma bantaba zuwa ba. Dr, yace nima haka amma gaskiya gobe kazo muje,domin ana fadin shari'ar, kasanfa har an yanke hukunci aka sake maidota.
Kuma wanda aka yanke mawa ma agidan yarin ya mutu, ashema sharri akayi mashi. Anwar yace lallai Allah yaso alkalin daya yanke hukuncin. Gaskiya dole inadauko su Ilham dasu Beelert mutafi dasu suma su kallema idonsu, kasan ance yawan zuwa kotu yanasa mutum yakara sanin rayuwa.
Dr, yace haka ne, Allah yasa gobe kada musamu patients se mutafi gaba daya. Anwar yace amin
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[2/11, 9:39 AM] nabilalady5: π¨π»πKAFIN IN ZAMA LAWYERπ¨π»π π¨π»π π¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»π
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Season 145 π€ 150
15th Sept, 2016.
WEDNESDAY
RETURN TO HIGH COURT
KATSINA STATE.
Kamar kullum, yauma harabar kotun cike take da jama'a, sede na yau sunfi na kullum yawa, haka suka fara shiga kowa yana neman wajen zama, sede mutane da yawa basu samu wajen zama ba.
Su Anwar kasancewar sunzo da wuri hakan yasa suka samu waje daga tsakiya suka zauna, gaba dayansu seda sukazo hada Ummar su Anwar dataji labarin tace itama zata je. Yan matan suna daga gefenta, su kuma su Anwar suna dayan gefen.
Bayan alkali yashigo kowa ya nutsu, haka aka shigo da masu laifin suka tsaya daga baya, Brr, Yusuf duk kunya tagama rufeshi jiyake kamar ya nutse kowa se kallonshi yakeyi.
Magatakarda ne yatashi domin karanto karar da za'a gabatar. A yau laraba 15 ga watan satumba shekara ta 2016. Wannan kotu zata cigaba da sauraron karar da akeyi akan marigayi Mannir, wadda ta daga shari'ar sakamakon rashin halartar wasu.
Mikama alkali takardar yayi yakoma ya zauna. Alkali yace ina fatan yan sanda sun kawo mutanan da kotu ta bada umarnin akawosu? Tashi Salis yayi yace yamegirma me shari'a munzo dasu.
Alkali yace Brr, Sageer zaka iya farawa. Tashi Sageer yayi cike da kwarin guiwa yafito tare da fadin inaso kotu tabani dama domin nayima daya daga cikin yaran D.P.O tambaya, wanda yakasance shine ogansu. Kotu tabaka dama.
Kotu zataso taji sunanka da kuma sana'ar ka? Sunana Ilu, kuma sana'ata fashi da makami. Malan Ilu ka dade kana aikata wannan aiki naka? Kwarai ma kuwa domin bazan iya cewa ga iyakar shekarun dana dauka ina sata ba.
Shin acikin satar da kakeyi ko kana kisa? Shiru yayi bece komai ba. Shin Ilu kasan D.P.O? Kallonshi yayi yana harararshi yace kwarai ma kuwa, nasanshi sama da shekara 2. Kana mashi aiki ne? Mundade nida yarana munayi mashi aiki.
Shin ko kasan abinda yafaru aranar litinin ta sati 2 data wuce agidan gonar Brr, Yusuf? Kai yadaga sama alamun tunanin, Sageer yace akwai wata yarinya kurma da aka kama aka kaita gidan gonar ko zaka iya ganeta?
Kasa yayi da kai, bece komai ba. Sageer yace muna sauraronka? Dago kai yayi suna hada ido da Brr, Yusuf yayi mashi alamu ta ido kawar da kanshi yayi yace nasanta, yarana ne ma suka daukota.
Jinjina kai Sageer yayi yace, wadannan sune takardun da likita yabamu na binciken da sukayi akanta, kuma ya tabbatar mana sanadiyar mutuwarta ta dalilin fyaden da mutane da yawa suka yimata ne, mezakace da hakan?
Kwarai kuwa, bazan boyema kotu komai ba, domin tunda aka kamani nasan cewa lallai asirina yagama tonuwa, domin malamina yace duk ranar da aka kamani daga ranar asirina yagama tonuwa.
Yau kusan shekarata 5 ina aikata manyan laifuka, kuma tunda nake ba'a taba kamani ba, babu sunana awajen yansanda, wannan kamawar da akayi mani ita ta tabbatar mani da asirina yatonu. Dan haka banga amfanin boyema kotu komai ba..............
Labarin duk yanda sukayi dasu D.P.O yabasu da kuma yanda suka aikatama Saddika har zuwa kisan da yayima Abdul. Runtse ido kawai Sageer yayi hawaye suna zubo mashi, mutane dayawa seda sukaji tausayinshi.
Haka kotu ta cika da hayaniya kowa da abinda yake fada, zuwa yanzu Brr, yusuf yagama sadakarwa beda madafa, domin ansamu mutum na biyu daya fadi hadashi acikin laifukan da ake zarginsu, duk da haryanzu ba'a samu wanda ya gabatar da shedar zahiri ba wadda zata nuna cewar yana da hannu ciki, amma yasan idan har Sageer yakirashi acikin wadan da ze tambaya dole kowama yagane hadashi.
Bubbuga tebur alkali yayi hakan yasa kowa ya nutsu. Share idonshi Sageer yayi yajuyo muryarshi tana rawa yace Ilu zaka iya fadama kotu ko suwaye ne suka saka wannan aikin? Kwarai ma kuwa, mutanan dasuka samu wannan aiki suna cikin kotun nan, duk da banida wata sheda dazata nuna sune suka sakani ta zahiri, amma sauran yarana zasu iya tabbatar ma kotu da haka.
Mungode Ilu zaka iya tafiya. Zanso kotu tabani dama domin nayima Gali wasu yan tambayoyi. Kotu tabaka dama. Haka Gali yafito kamar wanda aka tsamo daga ruwan zafi.
Gali kotu taji duk bayanin ka a wancen lokacin, kuma acikin bayaninka ka tabbatar ma kotu kaine ka samu kwayar da Mannir yasha acikin aljihunshi ko? Kame kame yafara duk arude yake domin yasan asirinshi yagama tunuwa tunda na uban gidanshi ya tonu.
Magana zakayi Gali. Dago kai yayi yana share zufa yace E nine rankai dade. Murmushi Sageer yayi yace kuma kace da kofin da yasha koko dashine ya jika kwayar aciki ko? Hakane.
To amma ya akayi aka samu kofin da yasha kokon a office dinku? Kuma lokacin da yan dakinsu sukaga gawarshi ya akayi su basuga kwayar da yasha ajikinshi ba? Bayansu ma akwai wasu masu gadin dasuka rigaka zuwa, su ma suka dauki gawar zuwa clinic ya akayi basu gani ba har se kaine dakazo daga baya sannan kayi tunanin aduba jikinshi?
Kwalla Gali yafara goge, domin gaba daya Sageer yagama kulleshi. Muna sauraronka? Dago kai yayi yace dan Allah kuyi mani hakuri wallahi sharrin shedan ne yasani na aikata haka, kuma ba laifina bane wallahi D.P.O ne yasani.
Zubewa kasa D.P.O yayi yasa kuka, tabbas shine aruwa, gashide atare suka aikata komai shida Brr,amma kowa yazo seyace shine yasashi, kuma gashi Brr, yafisu moriya da kudaden da yake samu. Tabbas seyanzu yasan ya aikata babban kuskure da ya yarda kowane aiki shine yake shigewa gaba. Lallai idan har hakane, wallahi seya tona Brr.
Bubbuga tebur alkali yayi kowa yayi shiru. Sageer yace munajinka Gali kafada mana gaskiyar abinda yafaru domin yanzu bakada sauran wata dama, abaya de Allah ya ara maka rana amma ayanzu bakada sauran wata hanya wadda tawuce kafadi gaskiyar abinda kasani? Dago kai yayi tare da goge kwallar idonshi yafara bayani...................
Duk yanda sukayi da D.P.O har zuwa lokacin da yasaka mashi kwayar a aljihu bayan ya mutu seda yafadama kotu. Sosai hankalin mutane yatashi dajin wannan rashin imani na Gali. Shugaban gidan yari kanshi seda hankalinshi yatashi.
Bayan kowa yayi shiru Sageer yace yanzu de kanaso kace Mannir baya shan komai kaine ka zuba mashi guba yasha, daga baya kuma kajika kwayar akofi kuma kasaka mashi wata a aljihu ko? Gali yace hakane, babu abinda Mannir yake sha, nine na aikata komai, amma nima D.P.O ne yasani kuma shine yabani gubar dazan zuba mashi yasha.
To saboda me sukayi kokarin kashe shi? Gali yace E to yace mun bayaso idan yadawo daga hayyacinshi yafadama wani gaskiyar abinda yafaru yasan koba yanzu ba za'a iya maido da shari'ar baya, wannan dalilin ne yasa yace in kashe shi. To dama kasaba aikata hakan acikin gidanku?
E to, gaskiya ban taba kashe kowa ba, sede nakasance ina yima mutane dayawa aiki aciki hada yaran gidan yari, nine dilarsu ta kowace irin kwaya da sukeso, kuma nine nake kawo masu duk wani rahoto dayake awaje, akwai mutane da dama dasuke aikata laifi bayan kuma suna kulle, wasuma nakan basu damar fita da dare suje suyi abinda sukaga dama da asuba sudawo. Wannan dalilin shine yasa nafi zabar aikin dare, daboda ba kananan kudi nake samu ba.
Salati kawai mutane sukeyi, kowa da abinda yake fada. Bayan kowa yayi shiru Sageer yace zaka iya tafiya mungode da bayaninka. Inaso kotu tabani dama domin nayima Brr, Yusuf wasu tambayoyi. Kotu tabaka.
Gaba daya mutane juyawa sukayi suna kallonshi. Gashi abun bakin cikin kayan aikine ajikinshi, jiyayi kamar kasa ta tsage yashige. Haka ya ratso mutane yafito. Yana shiga cikin akwatin tsayuwar seda yaji wasu kwalla sun taho mashi, hannu yasa yayi saurin gogesu. Wai yau shine acikin abinda mutane da yawa suke shiga yayin da shi kuma yana waje yana jifarsu da tambayoyi? Kuma wai yaron da ya raina shine mutumin dazeyi mashi tambaya.
Murmushi Sageer yayi yace kotu zataso taji sunanka da kuma aikinka? Daure fuska yayi yace kotu bata da bukatar sanin ko waye ni, domin nidin ba boyayye bane awajenta. Buga tebur alkali yayi yace Yusuf kashiga hankalinka, kada kamanta kana gaban kotu ne amatsayin me laifi, dan haka dole ka amsa duk wata tanbaya da Brr, Sageer yayi maka ko kuma ka fuskansi fushin kotu.
Gyara tsayuwa yayi cike da jinkunyar abinda aka mashi, dukar da kai kasa yayi yace Sunana Yusuf, kuma ni Barrister ne a wannan kotun. Shin kozaka iya fadama kotu abinda kasani agame da kazafin da akayima Mannir?
Babu abinda zan iya cewa domin, kotu da kanta ta karbi kwararan hujjojin da aka gabatar mata kuma ta yanke hukunci da kanta abisa dokar kasa. Amma baka ganin wannan hukuncin da kotu tayanke ta yanke shine abisa rashin sani? Gaskiya bana gani. Domin akoda yaushe kotu bata taba yanke hukunci akan abinda bata tabbatar ba, kuma wannan kotu itace babbar kotu da ake ji da ita, bana tunanin zata iya yanke wani hukunci batare da ta tabbatar da shedun da aka gabatar mata ba.
Shiru kowa yayi yana sauraron Brr, Yusuf, domin dagajin maganarshi kasan shidin kwararran lawyer ne, gyara zama alkali yayi domin yasan ko waye Brr, Yusuf, matukar Sageer beda wata kwakkwarar shedar dazata nuna yanada hannu acikin wannan laifin baze taba amsa laifinshi ba.
Sageer yace kasan cewar kotu tana aiki da hujjojin da lawyoyi suka gabatar mata, baka tunanin wadannan shedun datayi amfani dasu wajen yanke hukuncin ko na karya ne? Murmushi Brr, Yusuf yayi yace E to bazan yi mamaki dan ka fadi haka ba, domin wannan itace shari'ar ka ta biyu, amma duk da haka zan baka amsarka.
Idan har kowace kotu tana amsar shedun karya ina me tabbatar maka babu wani dan adam daze kara kawo kara kotu, shiyasa nace maka wannan kotun tana amfani da shedar zahiri, kuma bayan shedun da aka gabatar mata ita da kanta ta tabbatar daga wajen wanda ya aikata laifin, kaga kuwa dole ta yanke hukuncin daya dace, sede kuma idan alkalin zaka karyata.
Dafe kai Sageer yayi dan Brr, Yusuf yafara caza mashi kai, gaba daya soyake ya rudashi. Murmushi Brr, Yusuf yayi yace ina fatan ka gamsu da bayanina? Dago kai Sageer yayi yace amma duk mutanan da suka zo sun tabbatar mana dacewa shedar karyace aka gabatar ma kotu.
Sunce kace ai, amma basu tabbatar ba, duk cikin mutanan dasu kazo kawai sun baka shedar bakine, wadan da suka bada ta zahiri kuma wadannan banida case dasu domin batawa suka bada ba, nine wanda na gabatar da case din da kake magana, kuma nine nabama kotu duk wata sheda, shin acikinsu akwai wanda yace maka yaga lokacin dana bada shedar karya?
Saurin kallonshi Sageer yayi yace babu, amma ni inada shedar dazata nuna ma kotu cewar kana da sa hannu acikin shedar daka gabatar ma kotu na karya. Brr, yace a shirye nake da na amsa laifina matukar ka gabatar ma kotu shedar dazata nuna mata inada sa hannu acinkin shedun karyar dakace angabatar mata.
Juyawa Sageer yayi yabude wata jakarshi, wata takarda yaciro yace inafatan zaka iya sanin wannan takardar? Amsa yayi yana dubawa, tabbas yasan itace wadda Umar ya ajiye a office dinshi, kuma original dince, amma saboda karfin hali yace ni kam bansan wannan takardar ba domin da alama daga asibiti ta fito kuma ni ba likita bane.
Juyawa Sageer yayi yace yame shari'a wannan takardar tana dauke ne da hoton tambarin yatsun wanda yakashe Qaseem, kuma likita ya same shine ajikin wukar da aka kashe Qaseem da ita, kuma nasamu wannan takardar ne acikin office din Brr, Yusuf cikin dirowarshi bayan da D.P.O ya karbota daga wajen likita ya kawomashi kuma akan kunne na naji yace da Umar ya aje mashi ita.
Tun daga ranar dana fara aiki a office dinshi na fahimci koshi waye, aranar da Alh, Abbas da abokinshi sukaje office dinshi akan aikin dazeyi masu na kisan da danshi yayi, akan kunne na naji komai, kuma nazo kotu naga yanda komai yakasance.
Bayan mundawo naji yabada ainihin takardar a aje mashi kafin daga baya ya konata, tun daga ranar nasama raina nima zanyi kokari domin inga an tabbatar da gaskiya, wannan dalilin ne yasa naje na dauko takardar nasaka masu photocopy aciki.
Murmushi Brr, Yusuf yayi yace lallai Sageer ka iya bada labari, be kamata ace aikin law ka karanta ba, yafi dacewa ace gidan redio kake aiki domin zakafi kyau da hakan. Buga tebur alkali yayi yace ka gyara kalamanka Yusuf domin agaban kotu kake. Ayi hakuri yame shari'a, naji Brr, yana bada wani labari ne wanda ni bansan dashi ba.
Sageer yace inaso kotu tabani dama intambayi likita wani abu. Kotu tabaka dama. Dr, kozaka iya tuna wannan takardar da kuma sa hannun dayake jiki domin takardar tafito ne daga asibitinku? Karba yayi yana dubawa.
Dago kai yayi suka hada ido da Brr, Yusuf, kauda kanshi yayi yace kwarai ma kuwa, wannan sa hannuna ne, kuma nine na badata ga D.P,O domin bayan naduba tambarin dayake jikin wukar abinda nasamu kenan shine nabashi.
Zaka iya tafiya mungode. Zanso akira mani D.P.O. kotu tabaka dama. D.P.O ko kasan wannan takardar? Kwarai kuwa na santa, itace likita yabani kuma nabama Brr, Yusuf ita. Zaka iya tafiya.
Juyowa wajen Brr, Yusuf yayi yace inafatan ka gamsu da duk abinda suka ce? A'a nadeji abinda sukace, domin wannan labari ne kawai suka bada. Cike da jin haushi Sageer yace ya kakeso karika yima kotu wasa da hankali bayan duk wadan da sukazo sukayi bayani kowa yasan tare kake dasu?
Murmushi Brr, Yusuf yayi yace haba Brr, nifa dan adam ne, kuma inada damar dazan kare kaina, shiyasa kotu ta tanadi wannan akwatin danake ciki, domin duk wanda yashiga cikinshi ya kare kanshi, shiyasa nace maka kotu bata aiki da ka, kamar yanda wasu dakikan lauyoyin sukeyi. Saboda haka dole zan kare kaina, kasani ko karya sukeyi ma?
Girgiza kai Sageer yayi yace shikenan, idan har baka yarda da wannan shedar ba na tabbata zaka iya yarda da wannan....... wayarshi yadauko ya kunna mashi recording da Abdul yayi lokacin da sukazo wajenshi. Ganin ba'aji sosai yasa ya dauko wata karamar speaker yahada da wayar ya kunna.
Gaba daya kotun tayi shiru tana sauraron firarsu. A nan nefa hankalin Brr, Yusuf yafara tashi, domin ga muryarshi nan tafito kuma ga sunanshi an fada. Zufa ce tafara zubo mashi se gogewa yakeyi, duk wata dabararshi takare mashi kasa kawai yayi da kanshi.
Bayan yakare ne Sageer yayi murmushi yace a tunaninka ka goge na wayar Abdul ko? Uhm! Hakika dakikin lawyer daka raina shine yake shirin saka goge zufa. Tabbas kai kwararre ne, kuma kayi wasa da hankulan mutane. Yanzu mezaka iya cewa da wannan shedar ko itama ta karya ce?
Dukar da kai kasa yayi bece komai ba. Sageer yace idan bakada abin cewa zaka iya tafiya mungode. Dago kai yayi ya kalli Sageer, shima kallonshi yake fuskarshi dauke da murmushi. Haka yasauka mutane sunata surutu kasa kasa.
Juyowa Sageer yayi yace zanso kotu tabani dama domin ingabatar da tambaya ta karshe, zanso akira mani Ammar Abbas. Iyayen shi dasuke zaune jisukayi kamar an watsa masu ruwan zafi. Mom kuwa kuka takara sakawa, Ammar kuwa jiyayi kamar ya ruga cikinshi se kara yakeyi.
Ammar kamar yanda kafadama kotu a wancan karon cewar aranar da aka kashe Qaseem kana gida babu inda kaje ko? E hakane. Shin wannan hotonka ne? Karbar hoton yayi yace kwarai kuwa nine.
Bakayi mamakin yanda akayi yazo waje na ba? Gaskiya nayi mamaki. Ko kataba bama wani shi? A'a bantaba bama kowa hotona ba. Amma de idan ka kai abokanka gidanku kana basu hotuna suna gani ko? E ina basu.
Baka tunanin acikinsu ne wani yadaukar maka? E ze iya yuwuwa. Shin wannan sarkar datake wuyanka ta jikin hoton nan kozaka iya nuna mani ita? Ammar yace ta dade da faduwa.
Shin ko kasan inda ka yarda ta? Gaskiya bazan iya tunawa ba, nide na nemeta banganta ba. Dama awuyanka take? E tunda nadawo daga waje nasata kuma bantaba cire taba.
Yaushe rabon daka ganta? Shiru Ammar yayi bece komai ba. Sageer yace ina nufin ka kai kwana nawa rabon daka ganta awuyanka tunda kace baka taba cire ta ba? Shafa kanshi yayi yace gaskiya bazan iya tunawa ba ammade an kusa sati 3.
Zanso kotu tabani dama inyima Kamal tambaya. Kotu tabaka dama. Kamal kozaka iya fadama kotu abinda Mannir ya fada maka ana gobe ze rasu? Kwarai ma kuwa.............. Bayan yagama basu labarin abinda Mannir yafada mashi na game da mutuwar abokinshi da maganar da D.P.O ya fada mashi, seya ciro sarka daga aljihunshi yace.
Wannan sarkar itace Mannir yabani kuma ya sheda mani ya sameta ne a hannun Qaseem lokacin da yarasu. Karbar sarkar Sageer yayi yace zaka iya tafiya mungode. Kallon Ammar yayi yamika mashi sarkar yace amma kamar wannan sarkar tana kama da tajikin hoton nan ko? Dukar da kanshi kasa yayi zufa tana fito mashi, domin yatuna bayan sun dawo gida abokinshi yake tambayarshi sarkarshi yake fada mashi yaji lokacin da Qaseem ya cireta daga wuyanshi. Sam basuyi tunanin za'a iya gane sarkar shi bace.
Murmushi Sageer yayi yace shin ko kasan Abdul me shago akasuwa? Ammar yace E na sanshi. Shin akwai abinda yataba hadaku dashi kona fada haka? Babu abinda yataba hadani fada dashi.
Dama kasanshi ne ko kuma baku dade da haduwa ba? A gurin aski muka hadu kuma bamufi kwana 3 bama muka rabu. Amma yataba zuwa gidanku ko? E yataba zuwa so daya. Tome yahadaku har kuka rabu? Kawaide haka nan naga ba tsarana bane shiyasa muka rabu.
Kode ka nemi wani abu daga wajenshi yaki baka shiyasa kukayi fada? Saurin dago kai Ammar yayi yana zare ido yace wallahi ni babu abinda nataba nema awajenshi, talaka nefa mezan nema awajenshi.
Dauko wayarshi yayi yajona da speaker yace dan tsaya kaji wannan firar ko zaka iya sanin me muryar. Kunnawa yayi kowa ya nutsu domin sauraron abinda ake fada. Kuka Ammar yafara jin abinda ake fada. Tabbas ayau yasan asirinshi yagama tonuwa.
Sageer kam runtse idonshi yayi, jin muryar Abdul se mutuwarshi tadawo mashi sabuwa, hawayene kawai suke fita daga idonshi. Hakika yayi rashin aboki. Alkali kanshi seda ya tausaya ma Sageer, domin kobe fada ba yasan jin muryar Abdul ne tasashi shiga wannan halin.
Bayan ya kare ne, Sageer ya juyo domin cigaba damashi tambaya, sede kuka yaci karfinshi, duk yanda yaso yadena kukan kasawa yayi, daya daga baki zeyi magana se kuka yataho mashi. Seda yasa mutane da yawa kuka, musamman wadan da sukasan Abdul abokinshi ne kuma yarasu.
Ganin yakasa magana ne yasa alkali yace kotu zataje hutu na minti 15. Tashi yayi yashiga office dinshi, wasu kuma suka fita domin su huta yayin da wasu suka cigaba dazama acikin kotun. Ammar kuwa dukewa kasa yayi yana kuka. Da sauri Mom dinshi tazo ta rungumeshi itama tana kuka, haka Dad dinshi.
Lallashin shi suka rikayi, Mom tace Ammar kada kafadi komai wallahi kasheka zasuyi. Dago kai Ammar yayi yace Mom dole infada, karyata takare, kotu tariga data gano nine na kashe Qaseem, banida sauran mafita. Dad dinshi yace ina me tabbatar maka kida an yanke maka hukunci nizan daga kara, bazan taba bari a kulleka har bayan ranka ba, ai akwai kungiya masu nemar ma mutane hakkinsu, kosu zasu iya kwatar maka hakkinka.
Salis da su Baba ne suka ja Sageer zuwa wani office dayake cikin kotun. Lallashin shi sukayi suna kara karfafa mashi guiwa, ruwa Salis yadauko yabashi, bayan yasha yayi ajiyar zuciya haka sukarika bashi baki har yasamu yayi shiru.
Nabila kuwa kamar itace yar uwar Sageer, duk da basu san takan abinda yafaru ba, amma ganin Sageer yana kuka yasa itama tafara, Zaituna ma kukan takeyi, har Umna seda tayi kuka. Anwar yace haba kuyi shiru mana kada wani abun yasameku. Dr. Shamsu yace ai abunne akwai tausayi, naji na bayanmu suna cewa abokinshi ne Abdul din kuma shine wanda su D.P.O suka kashe. Anwar yace wallahi dana san da wannan shari'ar da tun farko munzo. Amma bakomai zamuji komai daga karshe.
Daga bangaren su D.P.O kuwa fada ne yafara tashi, D.P.O yana fadin wallahi da bakina sena tona komai, ashe dama munafuntarmu kakeyi Brr? Duk irin wahalar danayi taka amma daga karshe seka koma kana kare kanka? Lallai dan adam butulu ne. Brr, yace ai dole in kare kaina, domin dan adam bayada tabbas. Haka suka rika rigama harseda yansanda suka tsawatar masu.
AFTER 15 MINUTES.
Gaba daya kotun tayi shiru, bayan alkali yazauna yace Brr, Sageer zaka iya cigaba da aikinka. Tasowa yayi idanuwanshi duk sunyi ja, yace Ammar muna sauraronka, kace baku taba fada da Abdul ba, kuma gashi yanzu kowa yaji abinda kafada mashi ta waya ko ba kayarda muryarka bace?
Ammar yace tabbas muryatace, amma ai abinda nafada bada gaske nake ba kawai nafa mashi. Idan na fahimceka, kanemi Abdul da lalata, shikuma be baka goyon baya ba shiyasa ka kirashi har kafada mashi wannan maganar ko? Dukar da kanshi yayi kasa bece komai ba.
Kamar yanda kace duk wanda ka nuna kanaso be amince ba kana daukar mataki akanshi. Kuma hakan ne tafaru tsakaninka da Qaseem, da be amince da bukatar kaba shine ka kashe shi ko? Saurin dago kai Ammar yayi idanuwanshi suna zubar da kwalla yace ina kuma kasan labarina nida Qaseem?
Murmushi Sageer yayi yace Abdul abokina ne,kuma dan uwana, shine wanda kaji ance an kashe, duk abubuwan dasuka faru tsakaninku babu wanda bansani ba, wani abun nine nake nuna mashi yanda zeyi maka.
Hatta da haduwarku nine nasashi yazama abokinka domin musamu shedar dazata nunama kotu wannan sarkar takace. Bayan yasamu hoton kuma seka bullo mashi da asalin halinka, faruwar haka ne yasani nayi nazari akan halayyarka, kuma shine nagano wannan dalilin ne yasa ka kashe Qaseem.
Domin babu wani abu daze hadoka dashi har kayi fada dashi inba wannan ba, asalima ba unguwarku daya ba, shiyasa nayi tunanin haka.
Ammar bakada sauran mafita, na dade ina so insamu labarinka domin insheda ma kotu. Amma yanzu da bakinka nakeso kafadama kotu waye kai? Kuma menene yahadaka da Qaseem har ka kashe shi?
Ammar kada kamanta duk wannan mutanan da suke gurin nan basu kai yawan mutanan dasuke garin nan ba, bare kuma ace sunkai yawan mutanan kasarnan, bare kuma ace sunkai yawan mutanan duniya. Banga dalilin dazesa kaji kunyarsu ba, domin akwai ranar dazaka tsaya agaban kowa kuma gaban Allah domin kafadi laifukan dakayi.
A ranar da baki baya magana domin harshe makaryacine, gabobi sune zasuyi magana, aranar da za'a haskoma koma irin laifin dakayi. Ranar hisabi kenan, ranar da ko iyayenka bazasu kalle kaba, idan da rabin cokali na lada zerage maka kasamu kashiga aljanna idan kaje nema awajen iyayenka babu wanda ze iya baka.
Ashe idan har iyayenka bazasu iya yima alfarma ranar tashin kiyama ba kenan basuda wata hujja dazasu iya kareka a duniya domin suna tsoron rabuwa da kai. Ammar yau koda ba'a yanke maka hukunci ba, iname tabbatar maka wata rana dole seka iriski laifinka.
Domin masu iya magana suna cewa, IDAN KA KASA SAMUN ADALCI A KOTUN DUNIYA, KA DAGA KARARKA ZUWA TA LAHIRA DOMIN ARANAR MALA'IKU SUNE MASU SHEDA, ALLAH KUMA SHINE MEYANKE HUKUNCI.
Ashe bazakaso ayanke maka naka hukuncin tun aduniya ba? Kafiso se ranar da babu me cetonka? Ammar bawai ina maka wannan jawabin bane dan ka amsa laifinka, iname tabbatar maka wadannan shedun dana gabatar ma kotu kadai sun isa su tabbatar mata kana da hannu akisan Qaseem, kuma akwai sheda daya data rage ban gabatar ba, kasan kuwa itace tabbatacciya, domin munada hoton tambarin yatsun wanda yayi kisan, kuma kasan zamu iya daukar naka agwada, banida shakku akan zasuyi dede. Amma idan har baka bude baki kafadama kotu gaskiya ba to zamu gano da kanmu.
Kuka kawai Ammar yakeyi, gaba daya jikinshi yagama yin sanyi da jawabin da Sageer yayi, duk da beyi nisa a akaratun addini ba, amma tabbas yasan babu karya acikin maganar Sageer. Dago kai yayi ya kalli iyayenshi, suma kukan sukeyi, dukar da kanshi kasa yayi, tabbas yasan duk wani gata da iyayenshi zasu nuna mashi dan yana raye ne.
Daze mutu bazasu taba kara mashi ko kwana daya bane saboda suna tsoron kada yayi masu wari. Hannu yasa ya goge idonshi, yadago kanshi yace hakika Brr, kazo mani da maganganu masu kashe jiki, bantaba tsayawa nayi irin wannan tunanin ba, amma ayau nakara fahimtar meye rayuwa.
Tabbas na cuci kaina, fitar danayi waje karatu babu abinda ta haifar mani se illah, domin acan ne nakoyo abubuwan da suka bata mani rayuwa. Kaicona dana kasance da marar tarbiya, kuma mane min maza yan uwanshi. Hakika ayau ne zan bama kowa labarin haduwata da Qaseem domin hakan yazama ishara ga yan baya.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[2/13, 12:44 PM] nabilalady5: π¨π»πKAFIN IN ZAMA LAWYERπ¨π»π π¨π»π π¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»π
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Season 150 π€ 155
HIGH COURT
KATSINA STATE.
Kamar yanda kuka sani sunana Ammar Abbas, tunda nataso agaban iyayena ni kadai ne dansu, kasancewar iyayena masu hali ne, hakan yasa nasamu gata me tarin yawa.
Bansan meye bacin rai ba, haka zalika bansan babu ba, mahaifana suna matukar sona, bayan nagama karatun secondary mahaifina yaturani waje domin nayi karatuna acan.
Kasancewar cikin turawa nake hakan yabani damar yin rayuwa ta 'yanci irin tasu, Allah yayi ni da kyau shiyasa nasamu masoya maza da mata. Sede alokacin dana fara shiga harkar neman maza yan uwana, tun daga lokacin soyayyar mace ta fitar mani arai.
Tun ina tsoron harkar harna kware acikinta. Sam mace bata burgeni, wannan dalili ne yasa haryanzu banyi aure ba. A tunanin iyaye na bana kula mata shiyasa bansamu wadda nakeso ba, kuma hakan ne yayi masu dadi, domin dama sunce konayi aure sede muzauna a gidanmu saboda basaso inyi masu nisa.
Bayan nadawo gida sena bude harkar neman maza agidanmu, amma sena kaudama iyayena hankali da sunan bude kallon kwallo a dakina dan banason yawo. Hakan danayi ba karamin dadi yayi masu ba.
Shiyasa akoda yaushe suke alfahari dani dan bana irin yawon nan da yaran masu kudi sukeyi. Dady na da kanshi ya hada mana komai na kallon kwallo, ni kuma nayi amfani da wannan damar ina kawo maza cikin dakina batare da kowa ya fahimci abinda muke aikatawa ba.
Wata rana nafito sena hadu da Qaseem, yana tsaye shida abokinshi Mannir, harna wuce da mota na dawo baya, tsayawa nayi ina kallonshi yanda suke fira suna dariya. Allah yasani Qaseem yana da kyau, da ace dan gidan masu kudi ne hakika kyanshi seyafi haka.
Sosai Qaseem ya burgeni, na dade awajen ina kallonshi har suka bar wajen. Haka natafi gida cike da tunaninshi. A ranar kasa bacci nayi domin zuciyata ta kwadaita da Qaseem matuka.
Washe gari da abokina yazo nafada mashi halin danake ciki, shine yarakani inda naganshi jiya, sede koda naje banganshi ba. Haka muka rika zarya wajen amma seda muka dauki sati guda bamu sameshi ba.
Nashiga damuwa, hatta da harkar da nakeyi seda na dena saboda damuwa, arana ta 8 da muka koma naci sa'ar ganinshi kuma shi kadai. Bayan naje wajenshi muka gaisa nace mashi dan Allah ya sunanka? Yace mun sunanshi Qaseem.
Gyara tsayuwa nayi nace Qaseem dama tun rannan zan wuce naganka kaida abokinka kuna zaune anan hannunku kamar da littattafai kuna fira shine naga kun burgeni a wannan zamani a samu matasa kamarku amma kuna zuwa makaranta, shine kuka burgeni nace zanzo mugaisa.
Murmushi Qaseem yayi yace bakomai, bama makaranta mukaje ba mune malan dasuke koyama dalibansu. Jin haka yasa wata dabara tafado mani. Zama nayi nace mashi na dade inaso insamu wanda zerika koyamun karatun addini amma ban samu ba.
Kuma awaje nayi karatuna bansamu damar karatun Qur'ani ba. Bayan nafada mashi haka senaga fuskarshi tacika da annashuwa, a nan ne nagane yaji dadin abinda nace. Hannuna yakama yana murmushi yace amma gaskiya naji dafin abinda kafada.
Da za'a samu yaran masu kudi matasa irinku suna son karatun addini da ancigaba dayawa. Kallona yayi yace ya sunanka? Nace mashi Ammar. Jinjina kai yayi yace bakomai Ammar, insha Allah zanyi kokarin ganin na koyar da kai abinda nasani. Kuma idan kanaso zaka rika zuwa masallacin da muke daukar karatu bayan magriba sekarika dauka kaima.
Murmushi nayi nace mashi kasan halin iyayenmu basuso murika nisa dasu, kuma bazasu yarda narika zuwa karatu ba, ni kuma inaso amma bansan yanda zanyi ba, gashi kai kuma nasan bazaka iya jihadi ba wajen temakona da karika zuwa gidanmu muna karatu ni zan dauki nauyin daukoka da kuma maidoka.
Kallona yayi ganin yanda nayi kalar tausayi yace kada kadamu Ammar, inde har zaka tsaya ka koyi duk abinda zan koya maka ni kuma zanyi iya kokarina domin intemakeka domin irinku ba'a kyaleku. Nayarda zan sama maka lokaci kazo kadaukeni.
Murmushi nayi nace tunda kace bayan magrib kuna tsayawa karatu meze hana musa karatun karfe 8:30 zuwa 9:00 ina ganin ya isa haka kada intakura maka. Qaseem yace shikenan hakan ma yayi. Number wayata nabashi shima yabani tashi, haka mukayi sallama akan gobe za'a fara karatun.
Kamar da gaske Qaseem yafara mani karatu ni kuma ina kokari wajen ganin narike abinda yake koya mani, sosai muka saba dashi, yayin da akasan zuciyata sonshi yake kara yawa, soda yawa inamashi abubuwa sede shi bekawo komai aranshi ba, ya dauka kawai ina bashi girmanshi ne.
Bayan munyi sati 2 muna karatu nakasa daurewa, kawai se bayan na kaishi gida se inkirashi awaya muyita fira ina fada mashi kalamai masu dadi, tun yana daukar abinda nake mashi da wasa har abun yafara fin karfinshi.
Tun daga ranar dana nuna mashi inasonshi da aikata lalata yadena zuwa koya mani karatu, idan nakirashi baya dauka, hankalina yatashi sosai, naso ace koda ta kwayace nasa mashi nabiya bukatata ko so daya ne zanji dadi.
Amma nagama wahala abanza bansamu abinda nakeso ba. Babu irin zuwan da banyi ba amma yaki saurarata, daga karshe yace mani idan nakara zuwa wajenshi seya fadama duniya halin danake ciki, kuma yace ko abokinshi besan da maganar ba, amma idan nakara takura mashi wallahi zeje gidan redio yafadi komai.
Duk da abinda yafada mani ban tsorata ba, sede nadena zuwa inda yake amma ina kiranshi awaya, aranar dana kirashi narika rokonshi akan ya temakeni koso daya ne, zan kyaleshi, aranar yamun rantsuwar seyaje yafada agidan redio kuma yayi recording duk maganar danayi.
A wannan dare ne na fadama abokina halin da ake ciki shine muka fita nemanshi, cikin sa'a muka hadu dasu kuma wajen babu kowa, babu bata lokaci naje na cakumeshi muka fara kokawa, abokina shine yadauke wayarshi duk kokarin da yayi na kada na kasheshi tunda ya karbi wayar banji ba, seda na caka mashi wuka, anan ne yasamu yacire sarkata, shi kuma abokinshi ya ruga domin fadama yansanda.
Bayan muntafi na bude inda yayi recording nagoge komai na fasa wayar muka yarda ta. Alokacin dana fadama mahaifina sosai ya firgita, sede ban fada mashi gaskiyar abinda yafaru ba, nace mashi kawai muna zaune muna cin abinci yazo yana zagin masu kudi shine ni kuma nakasa hakura muka fara fada har tsautsayi ya fada na kashe shi.
Kasancewar iyaye na suna matukar sona haka suka shige mani gaba harseda aka maida laifin kisan akan wanda beji ba kuma be gani ba, duk da basune suka sa ayi mashi kazafin kisan ba amma sune suka bada kudi domin arufe case dina, shi kuma Brr, Yusuf yayi nashi aikin.
Tabbas kowane Uba zeso ace yarayu da danshi, amma kuyi hakuri abinda kukeso baze taba kasancewa ba, domin nima inaso ranar lahira insamu sassauci daga wajen ubangijina. Mahaifiyata kinyi kokari sosai, duk duniya bayan wadan da nake aikata masha'a dasu babu wanda yasan halin danake ciki se ke, kema ajiyane kika kamani ina aikatawa, amma duk da haka kika rufa mani asiri.
Hakika kunaso ku rayu dani sede kuma duk son da kuke mani bazaku iya temakona aranar dazamu tashi gaban Allah ba. A yanzu bani da wani buri da yawuce nima akashe ni kozan samu in samu sauki arayuwata.
Hakika maganar Brr, gaskiya ce, gara mutum yaji kunyar duniya dayaji ta lahira, haka zalika mutanan dazasu san abinda na aikata kadan ne akan na ranar lahira. A yanzu banajin kunyar komai, na mika wuya ayi mani duk hukuncin daya dace dani ashirye nake dana kar beshi.
Kuka yasa me tsuma zuciya, mutane dayawa seda yabasu tausayi duk da irin abun da ya aikata amma duk wanda yaga yanda yake kuka seda zuciyarshi ta tabu, wasuma seda sukayi kuka. Kowa da abinda yake fada gaba daya kotun ta cika da hayaniya.
Iyayenshi kamar ransu zefita saboda kuka, Dadynshi yayi matukar mamakin jin wannan bala'i da danshi yake aikatawa agidanshi amma beda labari. Hakika seyanzu yayi dana sanin kaishi waje yayi karatu, gashi nan yanzu yajawo abinda duniya zata zagesu kuma su rasa dan da suke dashi shi kadai.
Bubbuga tebur alkali yayi kafin kowa yayi shiru. Sageer ne ya matso kusa da Ammar yana fadin, hakika Ammar kayi kokari wajen iya yaudarar Qaseem sede abinda baka sani ba, duk yanda kaso dakayi lalata dashi tunda har Allah ya tsareshi babu abinda zakayi mashi kasamu biyan bukatarka.
Hakika akwai mutanan da Allah ya haramtama shedan kusantarsu bare har ya rinjayesu zuwa ga sabon Allah, tabbas Allah yakare Qaseem daga fadawa tarkonka. Kuma daga karshe se yayi mutuwar shahada domin duk wanda aka kashe Allah yana daukar dukan laifukanshi ya dorasu akan wanda yayi kisan.
Yanzu kam Ammar bakada sauran wani lokaci daya rage maka najin dadi, kazamo me laifi biyu awajen Allah, na farko ka aikata laifin da Allah ya tsinema masu aikatashi shine luwadi, saboda irin wannan bala'in ne Allah ya halakar da mutanan Annabi ludu.
Sannan kuma kazo ka aikata laifin kisan kai. Hakika abinda yarage maka shine ka koma zuwa ga Allah ka nemi tuba daga gareshi domin babu wanda ya isa yace Allah baze yafe maka ba, kofar tuba akoda yaushe a bude take, idan kuma mutum yatuba zuwa ga Allah, toshi gafurur rahim ne, ze iya gafarta ma bawansa.
Juyowa yayi yace yame girma me shari'a, a nan nakawo karshen tambayoyinda zanyima kowa, kuma ina fatan wannan kotu me adalci zatayi duba zuwaga kwararan shedun dana gabatar mata wajen yanke ma wadannan azzalumai dasuka aikata laifi hukunci.
Kuma ina rokon wannan kotu data wanke marigayi Mannir duk da baya raye, amma haryanzu jama'a suna mashi kallo amatsayin mashayi kuma wanda yakashe abokinshi.
A bisa shedun dana gabatar ina fatan wannan kotu me adalci zata gamsu da cewar Brr, Yusuf, D.P.O, Umar da Gali sune suka tsara komai na mutuwar Mannir da kuma laka mashi sharrin shaye shaye.
Kuma sune suke da alhakin kisan da akayima Saddika tare da Abdul bisa ga temakon yaransu, wadan da suka aikata laifin fyade ga yarinyar da bataji ba kuma bata gani ba, wanda shine yayi sanadiyar mutuwarta.
Ina fata kuma kotu zata hukunta Dr, wanda shine yabada hadin kai wajen tabbatar da shedar karya domin yazama kashedi ga sauran likitoci. Se mutum na karshe wanda shima yabada gudummu warshi domin a yaki gaskiya da kuma karya dokar aiki shine Sajan Shehu.
Ina fatan kotu zata hukuntashi dede da laifinshi domin sauran yan uwanshi sudauki darasi. Kuma inaso kotu ta bima Bukar hakkinsa na zaluncin da sukayi mashi har D.P.O yacire mashi yatsu 2.
Daga karshe inaso inbama Brr, Yusuf amsar tambayarshi dayace DAKIKIN LAWYER baya aiki da hankalinshi wajen aiwatar da aikinshi.Takawa yayi har wajen su Brr, Yusuf ya kalleshi yace Brr, ayanzu kam ka gane banbancin dake tsakanin Dakikin lawyer da kuma fasihin lawyer ko? Dukar da kai yayi kasa yana zare ido. Murmushi Sageer yayi yace D.P.O Bello Saulawa, hakika seka kula da wanda kake tare dashi, dominshi dodo ne, idan har da kudi ze iya kashe duk wanda suke tare.
Juyowa yayi yana fadin nagode, yame shari'a, daga karshe ina rokama mutane biyu wadanda sukeda matukar muhimmanci arayuwata, wadan da suka rasa ransu badan komai ba sedan su ga nayi nasarar wannan case din, segashi ayanzu nayi nasara sede kasa ta rufe masu idanuwansu babu damar sukalli aikin dana fara dasu.
Hannu yasa ya goge kwallar data zubo mashi yace ina rokon Allah ya kai haske kabarinsu, kuma yatadasu ranar gobe kiyama tare da amincinshi. Kuka me tsuma zuciyar me sauraro yasaka haka Salis yakamashi yazaunar dashi.
Duk wanda yakeda tausayi seda ya zubarma da Sageer Kwalla, a wannan karon hatta da alkali kasa daurewa yayi seda kwalla dazubo mashi, sede dayake akwai glass a idonshi ba ko wane zegane ba.
Hakika Sageer ya burge kowa daya halarcin kotun, yan jarida suna daga gefe suna daukar abinda yafaru, mutane se tafi suke mashi suna gode mashi. Iyayen Qaseem dana Mannir kuka kawai sukeyi, hakika basuda abinda zasu sakama Sageer dashi. Koba komai ya wanke masu yaransu daga sharrin da akayi masu na shaye shaye.
Yansanda ne suka maido da masu laifin gaban kotu, gaba dayansu sun kasa daga idonsu su kalli mutane. Cikin dabara alkali ya goge idonshi ya bubbuga tebur kowa yayi shiru. Dago kai yayi yana kallon dumbin jama'ar dasuke cikin kotun.
Hakika yayi shari'a da yawa amma be taba samun sarkakiyar shari'a irin wannan ba, hakika ya jinjina ma Sageer, a da yasan babu wanda ya isa yayi irin wannan case din kamar Brr, Yusuf, amma ayanzu yasan Sageer yafishi baiwa da kuma basira.
Murmushi yayi tare da hade hannuwanshi biyu, gyaran murya yayi tare da fadin, hakika dole na mika godiyata ga Allah, wanda shine yabani ikon gyara kuskuren dana aikata abaya, kuma yabarni da raina har gashi yanzu zan sake yanke hukuncin dana yanke a sati 3 da suka gabata, wanda na yankeshi abisa rashin sani.
Duk da kotu tana amfani da hujjojin da aka gabatar mata sede a wannan karon nasamu shedun karya, wanda kuma nakara tabbatarwa daga wajen wanda ake zargi sakamakon munafuntarshi da akayi, dasu nayi amfani nayanke hukuncin dabe dace ba.
Tabbas kowane alkali yana fuskantar kalubale arayuwarshi, yawan files da muke dasu na shari'a yafi karfin yawan da muke dashi. Shiyasa seka samu alkali daya ze gabatar da shari'a dayawa, saboda karancin alkalai.
Duk alkalai irinmu basu son irin wannan shari'ar, bare kuma wanda ba aikinshi ba. Amma kuma koyanzu kasamu mutane suna fada, cike da kwarin guiwa zakaji ko wannansu yana fadama dan uwanshi zamu hadu akotu.
To meyasa? Saboda kowa yanada yakinin acan ne kadai zesamu adalci. Kuma yakinin dasuke dashi, idan har gwamnati da jami'an tsaro basu yimasu adalci ba, to sun san kotu zatayi masu. Kuma wannan maganar haka take.
Haka kuwa duk wanda yataba zama saman wannan kujerar tawa to hakika hakki ya rataya awuyanshi na kare amanar da Allah yabashi. Shiyasa kowane alkali yake kokarin tabbatar da gaskiya, badan komai ba, sedan yana tsoron ranar daze tsaya agaban Allah domin ya amsa tambayoyin aikin da yayi.
Dan haka kotu zata fara yanke hukunci daga kananan masu laifi. Abisa kwararan shedu da aka gabatar ma kotu, kuma wadan da ake zargi da aikata laifin sun amsa da bakinsu. Wannan kotu bisa duba ga kundin tsarin mulki nakasa, kotu ta yanke ma Dr, hukuncin daurin shekara 5 agidan yari, tare da soke lasisinshi na aiki, domin kotu tasameshi da ha'intar aikin gwamnati da kuma cin zalin mutane.
Saboda acire baragurbi daga cikin azzaluman likitoci da muke dasu, shiyasa kotu tayanke mashi wannan hukunci, tare da tarar daze bama iyayen Mannir na bacin suna da yayima dansu na naira dubu dari biyar.
Sannan wannan kotu ta yankema Sajan Shehu hukuncin sallama daga aiki, domin yatemaka ma azzalumai wajen dakushe shedar gaskiya.
Sannan abisa kwararan shedu da aka gabatar ma kotu da kuma hujjoji sun tabbatar da Ammar Abbas shine ya kashe Qaseem, abisa dalilin daya fadama kotu. Haka kuma, Gali, D.P.O, Yusuf da kuma Umar sune suka hada baki wajen kashe Mannir. Da kuma yaran D.P.O da suka kashe Saddika tare da Abdul.
Saboda haka, wannan kotu me adalci, abisa tsarin kundun mulki na kasa tayanke ma Ammar da Yusuf tare da jama'arshi, a karkashin PENAL CODE Sashe na 302, da 201, da 180, da 340 sashen kisa, amfani da makami ko wani abu,tare da wulakantar da shedu, cin zarafi, yaudarar kotu tare da gabatar da shedun da kotu ta tabbatar na karya ne.
Bisa la'akari da wannan sashe na PENAL CODE. Kotu tayanke masu hukuncin daurin rai da rai. Sannan dukansu zasu biya diya ga iyalan mamatan. Haka kuma D.P.O ze bama Bukar tarar dubu dari 4, abisa yatsunshi daya cire mashi.
Kuma kotu ta soke lasisin Brr, Yusuf domin ya wulakantar da aikin law, kuma kotu ta baku dama zaku iya daukaka kara daga nan zuwa wata daya, idan har yacika baku daga ba hukunci ya tabbata. Kotttt!!!! Gaba daya mutane suka tashi suna tafi, Sageer kuwa kamar an bude mashi famfon kuka, jiyake inama ace Abdul yana kusa dashi, yasan seyafi kowa farin cikin wannan nasara tashi.
Dadyn Ammar saboda kaduwa yana mikewa yafadi awajen, kumfa yana fita daga bakinshi alamun barin jikinshi ya shanye, kuka Mom takara saki ganin halin da megidanta yake ciki. Ammar ma da gudu ya nufi wajenshi yana kuka.
Haka mutane suka temaka masu aka fita dashi, yayin da yansanda suka tasa keyar su Ammar suka nufi waje dasu. Babu shiri Brr, Yusuf yacire rigar aikinshi π€£ Umar se kuka yakeyi, Dr, ma kuka yakeyi dadin da yakeji iyalanshi basuzo wajen ba.
Mutane se zuwa suke suna yima Sageer murna akan nasarar da yayi, iyayen Mannir da Qaseem se addu'a sukeyi mashi, shikam har lokacin hawayenshi sun kasa tsayawa, dukawa kasa yayi yayima Allah sujadar godiya.(Sujudushshukur)
Yan jarida se so suke suyi mashi tambaya, amma ganin yanda yake kuka yasa suka fasa, Salis ne yakamashi suka fita waje. Sunzo wuce su D.P.O ya dago kai ya kallesu, murmushi yayi ya goge idonshi yamatsa wajensu.
D.P.O ya kalla yace ayau ina cike da farin ciki marar misaltuwa, domin fatana baya wuce Allah yakawo karshen azzalumai irinku, ayau kam bana bakin cikin mutuwarsu Abdul, koba komai iya yawan bakin mutanan dasu kayi masu addua'a ayau kadai ya isa rahama takai kabarinsu.
Naso ace a Shari'a court aka yanke maku hukunci domin mutane sukalli yanda za'a ratayeku a wulakance, amma ko yanzu ina me farin ciki domin zakuje ku iske mutanan da kune kukayi silar zuwan wasu gidan yari, kuma dole kuzamo akasansu, zaku bautu da aiki me tsanani.
Na tabbata sekun gwammace mutuwarku da rayuwarku, inama ace bawa yana rokama wani addu'ar tsawon rai. Da babu abinda ze hana ban roka maku ba, kodan kuga duniya, sannan abinda kuka tara na zalunci bakuda ikon amfani dashi.
Matanku, 'ya'yanku sune zasurika facaka dasu, se kunci sa'a surika kawo maku ziyara. Yusuf ina kaga karshenka? Kayi tunanin ni dakikine se gashi nidin, nine nayi silar shigarka gidan yari, koyanzu aka barka kaji kunya, agaban mutanan dasuka yarda da kai.
Lallai jahilci yana dawainiya da kai, da har ka iya tunanin irin aikinka shine babbar nasara arayuwa. Kuma aikin law yanzu nafarashi, domin zalunci yadena yaduwa acikin wannan kotu me albarka.
Kuma baza'a dena fadar gaskiya ba, domin makaryata basa so sujita, idan aka dena fadarta makaryata zasu cigaba da aikin da suka saba. Ina tayaku murnar shiga sabuwar rayuwa. Kafadar Yusuf yadafa yana murmushi tare da goge kwallar data zubo mashi.
Da kallo kawai suka bishi domin basuda bakin magana ayanzu. Jinjina kai Yusuf yayi yana share kwallar data zubo mashi tare da dafa kafadar Sageer yana fadin gaskiya ne Brr, Sageer, kayi nasara ni kuma na fadi. Kai ne mutum na farko daya taba sani zubar da kwalla, hakika naso nasaka kayi dana sanin shiga aikin law, sede daga karshe nine nake dana sanin zama lawyer. Na jinjina maka, kuma kaine asama dani yanzu. Nagode. Murmushi Sageer yayi tare da fadin Allah me iko.
Hannu Anwar yasa ya goge kwallar data zubo mashi, tunda Sageer yafito yake bin bayanshi, kuma duk maganar da yayi akan kunnanshi, sosai Sageer ya burgeshi, kuma yabashi tausayi.
Dafashi Dr, shamsu yayi yace muje gasu Umma can suma suna nasu kukan. Murmushi Anwar yayi yace bantaba ganin lawyer daya burgeni kamar Brr. Sageer ba. Hakika shidin gwarzo ne, kuma jarumi. Yana da tarin baiwar da Allah yabashi wanda shikanshi besan yana da ita ba. Dr, yace gaskiya koni ya burgeni, Allah ya daukakashi ya kuma kareshi daga sharrin mahassada.
Haka kowa yatafi gida cike da al'ajabin abinda yafaru. Har su Sageer zasu shiga mota alkali yakira Salis yace suzo yana son ganinsu. Zaune suke a office dinshi, alkali ya kalli Sageer yace bansan da wane baki zanyi maka godiya ba. Hakika katemaka mani wajen gyara kuskuren dana aikata wanda nayishi abisa rashin sani.
Idan Allah ya kaimu ranar litinin zankiraka domin zanmika takardunka da kuma bayananka ga shuwagaban ninmu. Kuma nasan labarinka ze isar masu ayau tunda yan jarida sun dauki komai.
Gaskiya Sageer kayi namijin kokari, domin ba kowane karamin lawyer bane ze iya abinda kayi, na jinjina maka, domin ka goga da kwararran lawyer wanda gwamnati take jidashi, wanda lauyoyi da yawa sun kasa kureshi segashi cikin lokaci kankani ka bude bakin bargon daya rufa dashi kowa yaga asalin halinshi.
Insha Allah Sageer seka daukaka arayuwarka, kuma zan cigaba da aiki da kai,domin irinku akwai rike amana da gaskiya. Allah yajikan wadan da suka gabacemu, mukuma Allah ya kyautata karshenmu. Kayi hakuri Sageer, kacigaba dayimasu addu'a, kada kabari damuwa tayi maka yawa.
Kallon Salis yayi yace ina rokonka alfarma daya, kucigaba da zama da Sageer harzuwa wani lokaci kafin ya warware, domin ayanzu yana bukatar mutane akusa dashi, idan kadaici yayi mashi yawa ze iya shiga wani halin.
Idan kuma akwai damuwa ni inaso yadawo gidana da zama. Murmushi Salis yayi yace yallabai wallahi babu komai, nadauki Sageer tamkar kanina, uwa daya uba daya, zamu zauna dashi har se idan shine yaso yatashi. Alkali yace naji dadin hakan, Allah yashige mana gaba.
Yan jarida ne suka shigo suna fadin yallabai idan bazaka damu ba zamuso mudan yima Brr, Sageer yan tambayoyi? Alkali yace Sageer kaje kudan gana kasan yin hakan zekara daukaka ka. Tashi yayi yafita.
Brr. Sageer Alee Dan Masani, wane irin farin ciki kakeyi ayau na samun nasarar da kayi akan wannan shari'ar?
Hakika ina godiya ga Allah, domin shine ya shige mani gaba akan wannan shari'a. Dan ba wayau na ko dabarata bane suka bani sa'ar wannan shari'a. To babu abinda zance se godiya ga Allah, kuma ina cikin farin ciki marar misaltuwa.
Bawai dan nayi nasara ba, sedan Allah yatemakeni nakawo karshen zaluncin da aka dade ana yima talakawa marasa galihu, wannan ba karamin abun alfahari bane, domin insha Allah daga yau babu wani lawyer daze kara danne hakkin wasu talakawa.
Brr. Sageer wannan shari'ar dakayi itace ta farko?
A'a ba ita bace, nayi ta farko kuma nine nayi nasarar cinyeta, sede wannan daban take domin na kara da mutumin da kowa yakasa kureshi, kuma wanda yakasance shine babban azzalumi a wannan kotun.
Shin Brr, ya kakeji na rashin abokinka akusa da kai wanda ba haka kaso ba, kaso ace yana raye kayi wannan nasara?
Bazan iya kwatanta damuwar danake ciki ba akan rashin Abdul akusa dani yau ba, domin nafi kowa son ace yana gefena na kammala wannan shari'a, domin koni se yafini farinciki.
Amma a bangare guda bana bakinciki, domin Allah yafini sonshi, kuma shine yadauke kayanshi, addu'ar danake mashi dashi da Saddika, Allah yasa suna cikin aminci.
Kuma ina godema Allah daya bani sauyi akan Abdul, domin bazanyi maraici sosai ba, Allah yabani inspector Salis, wanda shine ya maye mani gurbin Abdul wajen kammaluwar wannan case din.
Hakika Abdul yataka rawar gani akan wannan case din nawa, seda yakasance tamkar shine lawyer ni kuma dan koranshi, badanshi ba da tuni na dade da canza aiki, domin farkon fara aikina a karkashin Yusuf nasha wahala.
Amma saboda kwarin guiwar da Abdul yake bani, da kuma te makon dayake mani shine ya kaini ga wannan mataki na yau. Allah yajikansu, domin sun rasa ransu ta dalilina. Goge kwallar data zubo mashi yayi.
Brr, wane sako zaka bada zuwa ga masoyanka, da kuma sauran talakawa da suke cikin fargaba akan rashin adalcin da ake masu idan wani abu ya hadosu da shari'a?
Babu abinda zancema masoyana se fatan alkhairi, kuma naji dadi matuka yanda suka nuna mani so da kauna. Sauran talakawa kuma ina masu albishir da tabbatuwar gaskiya, in Allah ya yarda babu wanda ze kara kuka saboda rashin adalci.
Mungode Brr,Sageer, muma muna maka fatan alkhairi.
Haka suka tafi gida cike da farin ciki, hakika yau Sageer yanajin dadi azuciyarshi, jiyake duk wani kunci yatafi. Kafin kace wani abu gaba daya garin katsina harma da makotan ta labari yagama bazuwa.
Gidan TV, dana redio babu labarin da akeyi sena Shari'ar da aka gabatar da kuma nasarar da Sageer Alee yayi.
A washe garin ranar da abin yafaru a jaridar farko hoton Sageer ne dana su Brr, Yusuf ajiki, labarin abinda yafaru ne jiya aka buga, duk wanda ka gani to labarin yake karantawa.
Alkali ya kai maganar Sageer babban office dinsu, harma da wajen gwamnati, kuma suma sun kalli irin gwazon da yayi kuma sun karbi takardunshi domin bashi gurbi a aikin lawyer karkashin gwamnati.
Sannan sun saka ranar litinin amatsayin ranar da zasu karrama Sageer, tare da mika mashi sandar girma da jinjina, kuma sun sa abuga cewar zasu karramashi ranar litinin.
Ba karamin dadi alkali yaji ba, haka yakira Sageer yafada mashi, su Baba da Salis da Bala se farin ciki suke tayashi, alkali yace ze aiko mashi da kayan dazesa idan zezo taron. Godiya yayi mashi. Bala yace lallai nima zan halarci wajen domin naga yanda za'a karrama dana. Dariya sukayi tare da fadin Allah ya kaimu.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
GAYYATA!!ππ»
ππππ Wannan sakon gayyata ne na karramawar daza'ayi ma masoyinku aranar litinin, BRR. SAGEER ALEE DAN MASANI. Allah yakawoku lafiya amin.
[2/13, 1:00 PM] nabilalady5: π¨π»πKAFIN IN ZAMA LAWYERπ¨π»π π¨π»π π¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»ππ¨π»π
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Season 155 π€ 160
LAST PAGE!!!
This page is for you AISHA SULEJAπ
Babban dakin taro ne wanda ake karrama duk wani wanda yayi abin azo agani na jarumta, cike yake da manyan mutane, tun daga governor na Katsina har zuwa manyan alkalai da manyan yan siyasa da sauran jama'a masu fada aji.
Jami'an tsaro ne kewaye da wajen, kowa yana aikinshi, domin ba kowa ake bari yashiga wajen ba. Harabar wajen daga nesa kuwa sauran jama'ar garine tsaye suna kallon abinda ke faruwa. Yan jarida sunfi a kirga wadan da suka halarci wajen.
Sageer ne tare da alkali zaune a gefe guda, yayi kyau cikin shiga ta alfarma, idan ka ganshi seka dauka wani babban mutum ne. Lokacin daya daga idonshi yaga irin manyan mutanan da suka taru awajen badan kowa ba sedanshi seda kwalla tacika mashi ido.
Bayan an gama gabatar da bayanai tare da yima jama'ar da suka halarci wajen sannu da zuwa, megirma gwamna yatashi yayi jawabinshi tare da mika jinjina ga Sageer Alee. Bayan ya zauna aka kira alkali domin shima yayi nashi jawabin.
Sosai ya yabama Sageer abisa namijin kokarin da yayi, kuma ya bama jama'ar wajen takaitaccen tarihin Sageer da irin kalubalen daya fuskatan tundaga farkon fara aikinshi, tare da fada masu yanda komai ya kasance.
Vedion shari'ar aka kunna dede inda Sageer yakema Yusuf tambayoyi. Tafi mutanan wajen sukayi alokacin da akazo wajen da Yusuf ya kasa amsa tambayar karshe sema ya sauko. Sosai Sageer ya burge mutanan wajen.
Bayan wadan da zasuyi jawabi sunyi aka kira me girma gwamna domin ya mika ma Sageer kyautar girmamawar da aka mashi. Hawaye ne kawai suke zuba daga idon Sageer, se gogewa yakeyi, ahaka ya amsa ana ta daukarshi hoto.
Bayan nan aka kira babban alkalai domin yabashi offer dinshi tare da karanta mashi rules na law. Bayan ya karba, wanda ze karanto mashi rantsuwa yazo, haka yarika karanta mashi yana maimaitawa har suka gama.
Daga karshe aka bashi guri domin yayi jawabi. Duk yanda Sageer yaso yarike kukanshi kasawa yayi, koda yafara jawabinshi yanayi yana goge kwallar datake zubo mashi. Sosai yabama mutanan wajen tausayi, kuma ya burgesu.
Bayan yagama yasauko haka aka dauki tafi. A nan manyan mutane suka rika mashi kyauta tundaga ta kudi har zuwa mota seda yasamu. Me girma gwamna kuwa kyautar wani gida yayi mashi wanda yake a Goruba road.
Sosai Sageer yasamu kyaututtuka, yasamu kudade masu yawan gaske, cash da check babu abunda besamu ba. Haka aka tashi taron kowa yana tayashi murna. Sageer yama rasa wane irin farin ciki zeyi. Haka su Salis sukazo suka tafi dashi.
Tun bayan da aka kai su Brr, Yusuf gidan yari bayan an basu kaya sun saka aka kaisu dakinsu. Tunda sukaje wani gungun maza suke bin D.P.O da Brr,yusuf da kallo. Daya daga cikinsu yace kai abokina wancan ba wannan lawyer din bane tare da D.P.O? Murmushi dayan yayi yace sune mana, aini tun jiya nasamu labarin zuwansu. Dara taci gida.
Shafa gefen fuskarshi yayi yace wallahi sena rama dukan da wancan D.P.O yasa akayi mani. Wancan Brr, kuma shine yayi sanadiyar zuwa na nan. Wani yace wallahi nima shine yayi sanadiyar zuwa na nan, kuma laifin da aka yanke mani hukunci akanshi ba asalin wanda nayi bane.
Dariya Ogansu yayi yace tabbas na ganesu, kuma suma sunzo gidanmu zasu dandani kurensu. Sauran yaran D.P.O kuwa suna zuwa suka shige cikin wadan da suka sani suka cigaba da harkarsu.
Amma Dr, Da Umar gefe guda suka koma dan sunde na bin su Yusuf, sukuma aka barsu su biyu. Haka suka zauna kamar munafukai, ganin haka Umar yace ma Dr, yatashi su koma dayan dakin tunda ance mutum 2 su taho.
Haka suka bar su Yusuf a dakin manyan gagararrun maza, su kuma suka koma dayan dakin. Koda dare yayi seda sukayima su D.P.O dukan tsiya hadasu tsallan kwado seda suka sasu, bayan sun gama Ogansu yabasu wanki haka suka fita suna kuka sukayi masu wankin sanna suka dawo, amma hanasu kwanciya saman katifa sukayi sede suka kwanta kasa.
Washe gari tunda asuba sukaji ruwa ajikinsu, haka suka tashi aka aje masu bokatai suje su debo ruwa. Babu irin wahalar da basu basu ba, kwana daya amma sun sha jiki, kuka suke da idonsu, seda sukaje karbar abincin ma, dasun shiga layi ake turesu, haka suka koma baya sune na karshe.
Zaune suke suna cin abinci da kyar, kuka kawai Brr, Yusuf yake yana saka loma abaki, jiyake kamar zeyi amai, D.P.O ya kalleshi yace hakuri zamuyi, duka yaune mukayi kwana daya acikin kwanakin da zamuyi arayuwarmu. Saboda haka gara musa hakuri kawai kuma mudage wajen koyon zama da mutanan gurin nan, domin bazamu taba fita daga wajen nan ba sede afitar da gawarmu.
Kallonshi Brr, yayi yace yanzu shikenan ahaka zamu kare? Matsayina, dukiyata, iyalina gabadaya sun haramta agareni? Wannan abincin shine zanrika sama cikina harna mutu? Faskare, fasa dutse, gina rami da sauran aiyukan wahala sune abinda zan rikayi har na mutu? A gaskiya bazan iya cigaba da rayuwa haka ba, wallahi gara nakashe kaina na huta.
D.P.O yace haba Yusuf, yada guntun iliminka zaka rika fadin haka? Ka manta wanda yakashe kanshi da gangan ya mutu kafiri? Ai yanzu ne yakamata mudage munemi yafiyar Allah, kaga idan Allah ya yafe mana yarage tsakaninmu da wadan da muka zalunta tunda Allah baya yafe laifin wani akan wani.
Share idonshi yayi yace haka ne, kaima kafadi gaskiya, bakomai Allah yabamu ikon jure duk abinda za'ayi mana. Amma wallahi wajen nan cike yake da yaran da mune mukayi silar zuwansu wajen nan. Tsoro nake kada sudauki mataki akanmu.
Kode muje mukai kara domin ayi mana katanga dasu? Murmushi D.P.O yayi yace lallai kana daukar gidan nan da wasa, bakaji me akace ba? Gidan maza, duk wanda yashigo wajen nan to dole ya iya zama da kowa.
Naga alamar kana tsoronsu, amma zakaga yanda zan dage duk wanda yakara kawo mani raini zan fidda iya karfin danake dashi mu daku, duk da suna yan shaye shaye amma nasan nima zan bigi wani abu ajikinsu.
Brr. Yusuf yace kaga fa kotu tabamu damar daga kara, kode mu daukaka karar mu zuwa appeal court? Dafa kafadarshi D.P.O yayi yace wato abokina har yanzu kana son zaman duniyar kenan? Banyi tunanin yanda ka fini ilimi wannan maganar zata fito daga bakinka ba.
Ko dayake ilimin boko kawai ka fini. Kana tunanin da a shari'a court aka yanke mana hukunci da tuni ba'a rataye mu ba? Kaga munyi mutuwar wulakanci batare da mun kara aikata wani aiki na lada ba. Amma yanzu fa? Muna da sauran lokaci, zamu iya tuba.
Kuma kaifa babban tsohon lawyer neπ kana tunanin ko mun daukaka kara irin wadan nan mayun shedu da Brr, Sageer yagabatar ma kotu zasu kyale mune? Inaji ko kotun amerika itace de kasar 'yanci ko? To ko acan aka samu wadan nan shedun semun fuskanci hukunci.
Dan haka kawai malan kayi hakuri mu rungumi kaddara idan kuma kaine zaka daukaka karar to ina jiranka anan kadawo. Amma wallahi tunda Brr, Sageer yayima Ammar wannan bayanin naji na gwammace in dauki hukuncin duniya akan inje lahira.
Domin kuskuren duniya ana iya gyarashi, amma na lahira wallahi baya taba gyaruwa. Dan haka nide babu inda zanje. Jinkin Brr, Yusuf duk yayi sanyi. Kallon D.P.O yayi yace shikenan nagode da bayaninka. D.P.O yace yauwa ko kai fa. Brr, yace shine zaka cemun wani tsohon lawyer ko? π€£ dariya D.P.O yayi yace to ai sunanka kenan daga yau.
Brr, yace yauwa mudawo maganar dukan dakace zakayima wadan can, nide ina tsoro kasan ance sarkin yawa yafi sarkin karfi ko? Nide zanje insamu shugaban wajen in kaimashi korafi. Dariya D.P.O yayi yace ai sekaje. Wani ma aikacin wajen ne yazo yace kai kutashi kutafi wajen aiki.
Brr, ze mashi son iyawa ya buga mashi wata katuwar sanda datake hannunshi yana fadin dalla kutashi nan ba office dinku bane da kuka saba zalunci aciki, kara Brr, yasaki yadafe kafarshi domin yaji zafi sosai. Haka suka tashi suka nufi wajen aiki.
Bayan sati 2, aka sha bikin Anwar da Nabila, Dr,Shamsu da Rayyana, Faisal Da Zaituna. Sosai bikin ya kawatu, ansha taron jama'a anci kuma an sha. Party daya sukayi kuma gaba dayansu sukayi.
Amare sun sha kyau. Bayan an daura aure aka kai kowa gidanta, sede muce Allah yabada zaman lafiya da zuri'a tagari.
Bayan wata daya, Sageer ya warware yayi kyau, kudi sun fara zauna mashi, kuma har lokacin be koma gidanshi da zama ba. Salis ya samu karin matsayi shi akaba D.P.O yayinda aka bama Bukar matsayin sajan Shehu.
Sosai police station din ta gyaru, duk wasu wadan da basa aikin gaskiya Salis ya ganosu kuma yabasu kashedi na karshe, domin yace duk wanda aka kama da laifin zalunci ko cin amanar aiki za'a koreshi.
Office din Sageer kuwa babban office ne, kuma Bala shine ya dauka a matsayin masinjanshi dan yace shi kadai ne ya yarda dashi. Sosai mutane suke bashi girma, kuma yana zaune da kowa lafiya. Ya maida alkali megidanshi kuma Uba agareshi.
Kudaden da yasamu sune ya budema Saddika islamiya kuma da sunanta ya bude amatsayin sadakatujjariya da fatan Allah yakai ladan kabarinta. Abdul kuwa masallaci ya gina amatsayin sadaka agareshi.
Sosai yake kyautata tama iyayen Saddika da Kawun Abdul, dan duk juma'a yana kai masu ziyara. Sam dukiya bata dameshi ba, yana yawan yimasu Abdul sadaka duk juma'a kuma yana masu addu'a.
Bayan sati biyu suka sha bikin Salis inda aka kai mashi amaryarshi asabon gidan da yayi. Wannan dalilin ne yasa shima Sageer yatafi yakoma sabon gidan da aka bashi kyauta, sede yana zuwa yana duba Baban Salis.
Bayan Aunty tagama iddarta Allah ya hadata da wani wanda matarshi tarasu amma basu haihu ba, babu bata lokaci ta amince mashi aka sha biki, inda aka kaita zariya, mutumin lecturer ne a F,C,E zariya, kuma yana da hali.
Zaune take dashi tsakaninta da Allah, sosai take mashi biyayya, sam baruwanta da kawaye. Ummansu Anwar ta roki Abbansu daya bada driver yakaisu zariya domin su kaimata ziyara.
Haka suka shirya ita da su Ilham suka tafi. Sosai Aunty tayi murnar ganinsu, abinci ta shiryamasu. Bayan sun gamaci suka shiga daki ita da Umma. Kallonta tayi tana murmushi tace wallahi Umma kunyarki nakeji haryanzu.
Umma tace haba ai komai ya wuce, kima dena tunashi dan Allah. Aunty tace wallahi ban taba tunanin Allah ze bani miji inyi aure da wuri haka ba, idan ma zanyi auren nadauka zan auri me mata 2 ko 3 kuma marar hali, segashi cikin ikon Allah nasamu wannan.
Umma tace kinsan shi Allah me gafara ne ga duk bawan daya koma gareshi yana me neman gafararshi tare da alkawarin baze kara aikata abinda yayi ba. Wasu suna dauka idan kayima Allah laifi dole se rayuwarka ta wulakanta ne zaka gane kuskuranka.
Ba kowane laifi bane Allah yake jarabtar mutum da rayuwa me muni ba. Bawa ze iya yima Allah laifi kuma idan yanemi yafiyar Allah seya saka mashi da abinda betaba tunani ba. Abinda akeso wannan bawan yayi a wannan lokacin, seya kara riba aikin daya keyi na lada sama da wanda yakeyi abaya.
Kada kidamu Aunty, Allah yayi maki ni'ima me yawa, ke de kidaure kada shedan yakara samun waje azuciyarki. Aunty tace ai insha Allah bazan kara maimaita kuskuren danayi ba, koda ace acikin kishiyoyi nake bazan kara aikata komai ba.
Shiyasa ma nashiga islamiya domin inaso inzama malamar addini. Murmushi Umma tayi tace gaskiya kin kyauta. Allah yakara karemu daga sharrin shedan da kuma zuciyoyinmu. Kuma Allah yabar zumuncin dayake tsakaninmu. Abbansu Anwar yace kuma infada maki ya yafe maki. Rungumeta Aunty tayi tana mata godiya.
Bayan wasu watanni. Wata tamfatsetsiyar mota ce naga tayi parking akofar gidan yari. Kamal ne nagani yafito daga gidan yari yana kara kallon gari. Fitowa wanda yake cikin motar yayi. Ba kowa bane se Brr. Sageer Alee Dan Masani.
Yakara zama babban mutum kuma attajiri, sam kamal be ganeshi ba, seda yayi mashi magana yamatso wajenshi yana dariya. Kamal yace yallabai kaine anan? Kamo hannunshi Sageer yayi yana fadin katuna alkawarin da Abdul yayi maka?
Shine nazo domin incika mashi alkawarinshi na zuwa daukarka a duk lokacin da ka gama zamanka. Rungumeshi Kamal yayi suna kuka, dagowa yayi yana fadin hakika kai abokine nagari, ban taba tunanin zaka kara zuwa wajena ba. Salis ne yafito daga dayar kofar yana murmushi yace.
Ai dan halak shiyasan muhimmancin alkawari, dan haka kada kadamu muna tare da kai, kushiga mutafi. Haka suka tafi cike da farin ciki, kai tsaye gidan Sageer sukaje seda yayi wanka yabashi sababbin kaya yasa yaci abinci sannan ya kaishi gidansu.
Kasancewar Kamal yayi karatun N,C,E yasa Sageer yasama mashi aiki tare da temakon alkali, kuma yabashi jari ya bude babban provison store, wanda Kamal shima ya rubuta sunan Abdul a saman shagon. Hakan da yayi bakaramin dadi Sageer yaji ba. Sosai Kamal yake jin dadin Sageer.
Sede duk yanda su Baba sukaso Sageer yayi aure yace masu bayanzu ba, domin sam bayason maganar soyayya takara shiga tsakaninshi da kowa, duk lokacin da sukayi mashi maganar ma kuka yake sa masu, ganin haka ne, Baba Yusha'u yace su barshi zuwa wani lokaci ze manta komai.
A yanzu kam ansamu zaman lafiya a kotu, duk wanda yayi laifi ana yanke mashi hukunci dede da laifinshi, lauyoyi da dama sanadiyar abinda yafaru sun shiryu daga aikata laifun da sukeyi.
Sageer yayi cases da dama kuma duk wanda yayi shine yake nasara, kuma shi be cika karbar karar masu kudi ba, se idan ya bincika yaji sune keda gaskiya sannan yake karba, haka zalika inde me kudi ne ya daukeshi to yana karbar biyan dasuke mashi.
Sede baya amfanin kanshi dasu, sede ya kai gidan marayu amatsayin sadaka ga iyayenshi da kuma su Abdul. Amma idan har talakawa ne suka kaimashi kara to baya karbar komai daga garesu.Iya albashin da ake bashi dashi yake amfani.
Bayan shekara 1, agidan yari, Brr, Yusuf ne zaune shida D.P.O, duk sun rame sun kara tsufa, idan ba sune suka fada maka ba bazaka iya ganesu ba. Brr, Yusuf ya kalli hannunshi daya wanda ayanzu yazama gundulmi.
Sanadiyar fadan da sukayi da wani wanda yake jin haushinshi domin shine silar kawoshi gidan yari, suna cikin fadan ne yasa adda yacire mashi hannun hagunshi tun daga guiwar hannu.
Kwalla ce tazubo mashi wadda inda sabo yasaba da yinta, gogewa yayi yace abokina yanzu shikenan an sare mun hannu kuma anci banza ko? D.P.O yace to me kake so ayi? A kalla ankusa shekara dayin wannan abu haryanzu ba'a dauki wani mataki ba ai kawai ka manta.
Muda muka raba wasu daga duniyar ma gaba daya. Brr, yace kasan abinda yake yawan sani kuka? Ka duba tunda aka kawomu gidan nan so biyu iyalai na suka kawo mani ziyara, kaduba irin kyautatawar danake ma mata ta, amma har nan tazo tasani nabata takardar sakinta.
Yarana suna can suna facaka da dukiyata, dama nasani koda iyayen Mannir sukace sun yafe diyar na kwasheta duka nabasu sadaka. D.P.O yace ai garama kai, nifa? So daya iyalina sukazo.
Murmushi Brr, yayi yace shikam Umar ya huta, Allah yadauki ranshi yatafi yabarmu anan. Ga Dr shima saura shekara 4. Yabar gidan nan. Mu ko yaushe zamu mutu? D.P.O yace Allah shine masani, amma ai mu mukaga rayuwa.
Kalli yanda Ammar ya koma, wallahi duk yafi bani tausayi, duk ya lalace kamar me cutar kanjamau. Brr, yace wama yasani ko itace. Ai kasan abinda yake aikatawa kila wata cuta ce tasamshi.
Gashi yanzu kullum yana clinic akwance kowa yagaji dashi, ai garama muturwashi tafi. D.P.O yace ato shiyasani duk ba ta dalilinshi muke zaune anan ba. Dariya Brr, yayi yace daka gama cinyema Babanshi kudi ko.
Wai ni ina mutuminka Gali? Dariya suka sa yace kasan yafimu laifi awajen mutanan gidan nan, wallahi dariya yake bani , bakamar idan mukaje karbar abinci. Brr, yace wallahi kai mugu ne. Allah de yasa mudace, amma tabbas muna ganin rayuwa.
Brr, Sageer ya zama hamshakin me kudi, zuwa yanzu ya bude chamber tashi ta kanshi, kuma mutane dayawa suna aiki a karkashinshi. Ya karo karatu na wata 9, beda sauran matsala arayuwarshi sede har yanzu beyi aure ba.
Shida Salis zumuncinsu yazama tamkar na yan uwa. Zaune suke afalon Baba Yusha'u, domin yau juma'a sunzo mashi barka da juma'a. Bayan sun gama cin abinci. Baba ya kalli Sageer yace yakamata ace yanzu kaima ka aje iyali, koba komai zaka fita daga zargin mutane.
Domin Allah ya baka komai, idan bakayi aure ba jama'a zasu fara zarginka, abinda yafaru yariga ya wuce, yakamata kamanta dashi idan har ba fushi kake da hukuncin Allah ba? Dukar da kai Sageer yayi yace insha Allah Baba nan bada dadewa ba zanyi aure.
Murmushi Baba yayi yace yauwa ko kaifa, ai gara kayi auren koma samu Abdul ko Saddika. Dariya suka sa gaba dayansu. Salis yace ai nasan dole yasa wadannan sunaye. Sageer yace kamar kashiga raina, bazan taba mantawa da wadan nan mutanan biyu ba.
Baba yace Allah yajikansu da rahama, sukace amin.
CIGABA DA LABARIN RAYUWAR MATA AYAU. IDAN BAKU MANTA BA SAGEER YANA BAMA SU MANSOOR SADDIK LABARIN RAYUWARSHI.
Ajiyar zuciya Sageer yayi tare da goge hawayen dasuka zubo mashi ya kalli mutanan dasuke cikin falon yana fadin wannan shine asalin labarina na KAFIN. IN ZAMA LAWYER. Gaba daya jama'ar dasuke falon seda sukayi kuka, sosai suka tausaya ma Sageer, Ayyama sarkin kuka ita da Farida kamar ransu ze fita haka suke kuka.
Share hawayenshi Mansoor yayi yace lallai abokina ka fuskanci kalubale arayuwarka naji tausayin wannan labarin,rabon danayi kuka haka tunda Yaseer ya rasu. Dole kace zaka aje aiki, domin ba ko wane ze iya daurewa abisa kaddarar da Allah yadora maka ba. Allah yajikansu Abdul, kai kuma Allah yabaka ladar aikin da kakeyi.
Sageer yace amin. Kallon Ayyama yayi yace haba matata kibar kukan haka mana. Kamo hannunta yayi yana fadin inaso kema kisani idan Allah yabani yara Su Abdul da Saddika sune mutanan farko dazan fara sama yarana sunansu.
Goge idonta tayi tace bakomai, wannan ba wani abu bane, Allah yajikansu da rahama.
Mansoor yace to Brr, πau, ashefa yanzu da alkali nake magana. Dariya sukasa baki daya, Sageer yace kajika ko? Mansoor yace ai gaskiya na fada, domin yanzu kawuce Brr. Yusuf, zanso inje gidan yari in kai mashi ziyara. Dariya sukayi Sageer yana fadin har abada babu wanda banaso naga fuskarshi kamar Yusuf da D.P.O.
Mansoor yace haka ne, Allah yayi mana tsari da mutane azzalumai masu son abin duniya da kuma son zuciyar su. Sageer yace amin. Mansoor yace ai gaskiya duk wanda yataka dokar shari'ar dole shari'a tayi aiki akanshi. Sageer yace ai ba dokar shari'a kadai ba. KOWA YATAKA DOKAR ALLAH BAZEGA DEDE BA.
ALHAMDULILLAH!!!!!!!
A nan nakawo karshen littafina mesuna KAFIN IN ZAMA LAWYER, HADE DA RAYUWAR MATA AYAU.
Ina mika godiyata ga Allah daya bani ikon kammalasu lafiya. Kuskuren da yake ciki Allah ya yafe mani. Darasin dayake ciki kuma Allah yabani ladarshi ga duk wanda yakaranta kuma yayi amfani dashi.
Godiya ta musamman ga dukkanin masoyana, wadan da nasani dama wadan da bansani ba. Hakika nagode da irin yabon da kuke mani. Allah yabar zumunci amin.
Se mun hadu a sabon littafina me suna KOWA YATAKA DOKAR ALLAH??????.
Kadan daga labarin KOWA YATAKA DOKAR ALLAH........
Matasa ne maza guda 3 da yan mata 3 suka fito daga wani daji wanda sukaje yin party na birthday din budurwar daya daga cikinsu. Gudu suke sosai, sun kure kara suna shan sauti.
Alokacin da misalin karfe 1 na dare ne. Motar su ta lalace kafin su fito daga cikin dajin, gashi sune karshen tasowa daga wajen, abokan tafiyarsu duk sun tsere masu.
Wasu mutane ne suka fito daga cikin dajin dauke da makamai, babu bata lokaci suka kamasu su duk suka nufi cikin dajin dasu.
Ihun daya daga cikin matan sukaji, alokacin da aka dauketa aka kaima Ogansu, bayan yagama abinda zeyi da ita yabama sauran yaranshi, suma suka shana.
Jefota sukayi da alamun babu rai ajikinta, domin ba karamin illa sukayi mata ba.
Wata datti jiwar matace take kwance cikin wani daki, banda wari babu abinda dakin yakeyi, ta yamutse, se kuka takeyi wani ruwan kyama yana fita daga jikinta.
Aminiyarta ce kadai awajenta, itama daurewa tayi tazo dubata. Kuka take tana fadin Lami, na cuci kaina da Alh, nasan DOKAR ALLAH da muka taka itace takawoni wannan matsayin da nake ciki.
Ke kam haryanzu bakiga komai ba, nide tawa takare mani. Dana abin sona yaguje, inaso inganshi domin nabashi labarin rayuwata. Banaso na mutu ban nemi yafiyar Alhaji ba.
Duk wata takama da Nabil yake da kudin ubanshi besan ainihin sirrin dayake boye ba. Dan Allah kitemaka mani kada na mutu banga Nabil ba.
KADA KUBARI ABAKU LABARI,
SUNAN LITTAFIN KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH. YANA NAN TAFE!!!!
UR'S.

0 comments:
Post a Comment