Kasa karasa maganan sukayi sakamakon ganin junan su .. Godwin da karfin hali shine ma ya iya bude baki yayi magana "nxt tym in kina tafiya ki dinga duba hanya bawai ki dinga tafi anyhow bah" kallon shi kawai take yi sbd tsabar haushi "am nt in d mood" iya abinda tace kenan kawai ta fara tattare takardun bata sake kallon inda yake ba balle magana ta sake hada su.. Har ya duqa zai tayata kwashewa sai kuma ya fasa kawai yayi wuce war shi ko waigen ta be sake yi bah... "wannan wani irin mutum ne? Shi kullum haduwa dashi babu wani alkhairi? Gashi da shegen girman kai.. Me ya dauki kanshi" Mitchww ta ja tsaki haka tayi ta mita cikin ranta tana kwashe takardun.. Wasu mata da suke zaune a gefe suka zo suka fara tayata kwashe files din "baiwar Allah kiyi hakuri wasu haka suke sun san kirikiri suke da laifi amma basa daukan laifin su.. Shifa ya bige ki sbd yana tafe yana amsa waya amma ya daura miki laifin".. a haka har suka gama kwashe mata files din "muje mu raka ki dan naga files din sun miki yawa" "Nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairi" har kofan dakin theater suka raka ta ta shiga ciki ta ajiye na hannun ta sannan taje ta karbo na hannun su ta kara musu godiya "babu komai ki kara hakuri kinsan komai na duniya dan hakuri ne" "Allah ya biyaku" "Ameen" suka juya suka wuce ita kuma ta koma ciki..
Da kyar aka lalubo file dinta duk yayi kura sbd ta dade bata zo asibitin ba. Fada Dr. Magaji ya fara ma mijin ta "meyi haka? Tun yaushe ya kamata ace kun dawo asibitin nan baku dawo ba se yau kasan halin da take ciki kuwa? Se da nayi muku kashedi ku dawo akan lokaci amma baku ji bah. Na ja muku kunne har kai na kira na fada maka amma a banza. Baka damu da halin da take ciki kenan ba. Kasan sharrin fibroid kuwa? Har ya kai da tana bleeding" tabur ya buga yace "I will get back to u" office din shi ya wuce ya bar mijin matar a tsaya ko motsi ya kasa kamar ruwa ya cinye shi.. Dr. Magaji ya dawo cikin saurin sanye da kayan operation bayan yayi alwala a office din shi, hand gloves yake sawa ko kallon sashen mutumin be sake yi bah ya shige ciki.. Da sauri da sauri ya fara fiddo kayan aiki.
Dr. Magaji se sai specialist wanda ke hada alluran anesthesia sai kuma wata likita guda daya mai suna Dr. Salma sannan su Janan. Duk tsaye suke a gaban gadon matar bayan an canza mata kaya zuwa na operation kwata-kwata bata san inda kanta yake bah.. Dr. Salma ce ta fara sterilizing wukake da karafunan da za ayi amfani dashi.. Dr. Magaji ya karbi alluran anesthesia ya miqawa Janan yace "kiyi mata sbd kar muna cikin aiki ta farka tunda suma tayi zafin operation zai iya sa ta farka".. Jikin Janan ya fara rawa idon ta yayi raurau.. Ganin haka Dr. Magaji ya fasa bata ya miqa ma Aisha aiko ta karba tayi ma matan ita kuma Zee ta sa mata drip. Duk da likitoci basa ba nurses su sama patient drip ko suyi musu anesthesia amma shi ya basu sbd yaga they r very intelligent kuma suna da natsuwa.. Duk suna tsaye aka kunna fitulun operation nan da nan suka fara aiki Janan ta kasa jurewa sai kuka take yi.. Alama yayi mata da hannu taje waje sbd yanda hankalin ta ya tashi.. Kamar dama jira take yi ta fice da sauri.. A benci dake waje ta zauna tare da daura kanta a cinyar ta tai ta faman rusar kuka.. Ganin kuka bazai mata magani bah ta tashi ta wuce masallacin dake cikin asibitin..Nafila ta dinga jerowa tana roqon Allah ya tashi kafadun matar sannan Allah ya ba su Dr. Magaji sa'a bayan ta idar ta dakko Al'qur'ani mai girma ta fara karantawa a nan ne taji zuciyar ta tayi sauki.. Ta kai kusan awa 1 a cikin masallacin kafin ta koma wajen bencin da ta zauna dazu.. Wayar ta ce ta fara ringing tana dubawa taga _Nurulqalbee_ Imran kenan. Murmushi tadan yi sannan ta dauka "Amincin Allah ya tabbata a gareka Nurulqalbee (Hasken zucia ta)" bangaren Imran wani sanyi ne ya ratsa shi "Kema amincin Allah ya tabbata a gare ki Angel"
"Da fatan kana cikin qoshi lfy"
"Alhamdulillah Angel me ya faru dake naji muryan ki so dull kamar baki lfya ko kuka kika yi ne ban sani bah cuz naji muryan ki yana cracking"
"wata patient ce ta ta bani tausayi shine nayi kuka"
"haba Angel daga fara aiki yau se kuka? Ki kwantar da hankalin ki zaki saba kinji" saida ya tabbatar hankalin ta ya fara kwanciya sannan yace "angel na kosa in je neman izini wajen Abbiey in dinga zuwa wajen ki zance bana so in fara zuwa ba tare da izinin shi ba sbd bin ka'idar addinin musulunci" tayi farin ciki sosai da jin abinda ya fada tana kara jinjina hankali irin na Imran "Allah ya baka ikon zuwa"... Yace "Ameen" Haka suka yi ta waya har tsawon wani lokaci kafin sukayi sallama..
Dr. Magaji ya fito yana share gumi da hanky bayan sun share awanni biyar a dakin theater.. Da sauri mijin matar ya tashi ya je wajen Dr. Magaji "Likita ya take? Ancire mata? Likita mata ta ta farfado? "biyo ni office" iya abinda yace kenan ya wuce.. Da sauri mutumin ya bi bayan shi.....
*Rukky Bae*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も潱鉂b潱馃挄馃挄鉂b潱鉂p煉曗潱 *MATAR DOCTOR*鉂も潱鉂b潱鉂b潱鉂b潱鉂b潱
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
6鈨�3鈨�***************6鈨�4鈨�
Suna shiga office din Dr. Magaji ya zauna sannan ya ba mutumin waje yace ya zauna.. "likita Dan Allah kayi min bayani" se zufa yake yi yama cire hular kanshi sai fiffita yake duk da A.c da fankan dake cikin office din.. Remote Dr. Magaji ya dauka ya kara karfin A.c sannan yace "ka zauna tukunna se in maka bayani mana" jiki a salube ya zauna..
"Malam Adam gaskiya banji dadin abun da kuka yi kai da matar ka ba sbd ba karamar hatsari ta shiga bah domin fibroid din ya zama chronic amma munyi nasaran cire shi"
"Tor Dr. Yanzu ya take ta farfado?"
"bata yi regaining conscious nata ba sai nan da 2 hours zata farfado..Yanzu dai zaka bada ledan jini biyu mu samata cuz ta zubda jini dayawa amma b4 then kaje kayi clearing bills naka sannan muyi admitting dinta har se ta samu lfya. In an sallame ta bayan 6months zaku sake dawo wa a dubata" wani takarda Dr. ya mika mishi yace "ka kai lab in sun gani zasu gane"
"Nagode Dr. Nagode Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen amma Dan Allah nxt tym ku kiyaye kar haka ta sake faruwa"
"In shaa Allah hakan bazai sake faruwa ba likita"
Da sauri ya bar office din yana fita daidai nan su Janan na turo matar shi a gadon marasa lfya da wani abu a bakin ta kamar matacciya.. Da gudu ya fara bin su yana hawaye "Dan Allah ku tsaya inga lfyar matata"
"Kayi hakuri bazamu iya tsayawa anan ba sbd hayaniya da kuma mutane ka bari in ta farfado sai kazo ka ganta amma yanzu ka bimu kaga dakin da zamu kaita" haka yayi ta binsu yana hawaye gwanin ban tausayi seda yaga dakin da aka kaita sannan yaje yayi clearing bills ya wuce lab din dake asibiti ya nuna musu yar takardar da Dr. Magaji ya bashi. "ka sha madara ko malt sbd jiri"
ba musu yaje ya siyo malt da peak yasha sannan ya koma wajen nurse yace "na shirya" kadan nurse ta diba a sirinji tace ya jirata wajen wani machine ta nufa ta gudanar da test dan tabbatar da bashi da wata cuta sannan tace ya kwanta a wani karamin gado aka fara diban jinin.. Seda ya kai awa 2 kafin suka bashi izinin tafiya
"babu dai wani abu ko?? Kana jin jiri? Zaka iya tafi? Akwai inda yake maka ciwo"
"zan iya kuma bana jin komai babu inda yake min ciwo nagode"
Dakin da aka kwantar da ita ya nufa yana zuwa aka barshi ya shiga sbd babu kowa a wajen ta kuma any moment zata iya farkawa.. Ya kai kusan 10 mins kafin ta fara bude ido tare da turo abinda aka sa mata a baki.. Salati ta fara yi daganan kuma ta fara sambatu "wayyo likita ciki na yana ciwo karku kashe ni ciki na yana min ciwo bana so me nake yi a nan!! Haka tayi ta ihu.. Da sauri mijin ta yaje ya riqe mata hannu yana kuka "kiyi shiru kinji a asibiti muke basa san ana ihu anan"
"Ina ruwana da asibiti? Kai waye"
"nine mijin ki Adam sannu kinji"
"bana san ganin ka ka fita a dakin nan ko in kashe ka馃槼 hannun ta ta fizge kafin ya ankara har ta cire drip din da aka sa mata nan da nan jini ya fara zubowa.. Wani ihu ya sake "Nurse kuna ina jini! Jini yana zuba!!" da gudu su Janan suka shigo ganin matar sukayi a kwance tanata jijjiga tana bankarewa. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" abunda suka fada kenan Janan da Zee suka tafi wajen matar da gudu suka rirriqe ta ga jini se tartsowa yake yi duk fararen kayan Janan sun baci har fuskar ta sbd ita ke tsaye ta gefen da matar ta cire drip din gabaki daya ta fita a hayyacin ta.. Idanun matar suka fara qaqqafewa nan da nan suka sake rudewa gashi su ba sanin taimakon da zasuyi mata bah mijin na ganin haka ya saki wani razananne ihu ya tafi luuuuu ya fadi qasa....................
*Rukky Bae*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も潱鉂p煉曗潱鉂b潱鉂b潱鉂b潱 *_MATAR DOCTOR_*鉂b潱鉂p煉曫煉曫煉曗潱鉂b潱
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
*_((2016))_*
6鈨�5鈨�**************6鈨�6鈨�
"Innalillahi wa innailaihirrajiun" ana wata ga wata!! Ga mata ga miji.. Sun rasa yadda za suyi ga Aisha taje siyo musu abinci sbd tun breakfast basuci komai bah
"Zee dawo ta nan ki danne mun wajen dake fidda jinin nan ina zuwa" ba musu Zainab ta saki hannun matar ya tafi sharaf! Ya fadi kan gado.. Kallon juna sukayi ita da Janan cike da tsoro a gurguje ta koma side din da Janan take ita kuma Janan ta fita da gudu ko takan jinin dake jikin ta bata bi ba.. Ko knocking kofar bata yi ba ta shiga da sallama kamar an hankado ta "lfya Janan kika shigo haka duk jikin ki jini?
"Baba patient! Patient da mijin ta! "me ya faru da patient? Calm down nd talk to me" da sauri da sauri tayi mishi bayani.. Ko secs 2 be kara ba ya fita cikin hanzari daga office Janan na binshi a baya ya nufi dakin da matar take suna shiga yaga halin da suke ciki ita da mijin ta "Janan taimaka min mu turo gadon ta zuwa emergency room ke kuma Zainab ki yayyafa mishi ruwa yanzu zan turo wani Dr. yaga halin da yake ciki"
Gudu gudu sauri sauri haka suka nufi dakin emergency.. Oxygen aka fara sa mata domin numfashin ta yayi sama yana barazanar daukewa.. "Daughter kije ki gyara jikin ki in kin gama ki tafi gida sbd kayan ki ya baci da yawa kuma ki dena yawan kuka ke nurse ce be kamata zuciyar ki ta dinga yawan karaya haka bah"... Jiki a salube ta fito daga emergency room din daidai ta fito shima Dr. Godwin ya fito daga office din shi bata lura da shi ba.. Gefe ya koma yana kallon ta a ranshi yana fadi "ita kuma wannan meke damun ta haka duk jini a jikin ta? Ganin tayi hanyar sauka daga steps yayi sauri ya sha gaban ta "Ke! Miye haka? Jikin ki duk jini kina kokarin shiga cikin mutane kamar baki san aikin ki bah" ko kallon shi bata yi bah tace "excuse me" ganin beda niyyar matsawa ta kauce zata bi dayan gefen da sauri ya sake tare ta haka suka dinga yi har wajen sau 3 gajiya yayi da draman da suke yi ya fizgo hannun ta ya fara janta sai kokarin kwace hannun ta take amma ta kasa "miye haka wai! Ka sake ni! Ka sake ni!..be tanka ta ba kuma be seke mata hannun bah seda suka zo daidai bakin kofar office dinshi yasa key ya bude har lokacin be sake mata hannu bah.. Bayi straight ya wuce da ita sannan ya ciro hanky fari sol daga aljihun wandon shi ya fara goge mata jinin kan fuskar ta wanda har ya soma bushe wa. Be damu da yanda take ture mishi hannu bah se da ya gama goge mata fuskar tas sannan ya jawo hannun ta ya daura mata hankyn akan tafin hannun nata "goge ki fito" ya juya ya fita da harara ta rakashi sannan ta tara hannun ta a pampo ta matso hand wash ta dinga wanke hannun tana istigfari "shi wannan besan haramun bane namiji ya taba macen daba muharramar shi bace! Koda yake ba musulmi bane shiyasa yake abunda yaga dama" haka taita dirje hannun har hand wash din ya kusa karewa sannan ta barshi. A hankali ta dan goggoge jikin ta sbd kar kayan ya jike sannan ta wanke fuskar ta.. "a bayin zaki kwana ne? Seda ta murguda baki kamar yana ganin ta kafin ta bude bayin ta fito yana tsaye ya jingina da bango yayi crossing kafafun shi hannayen shi duka biyu ya zurasu cikin aljihun wandon shi yana facing kofar bayin. Dan nesa dashi ta tsaya amma bata dago bah ganin be tanka bah yasa tayi hanyan waje "Ke! Ya kirata.. Cak ta tsaya ita batayi gaba ba kuma batayi baya bah. A hankali ya tako yazo daidai gaban ta ya tsaya kanshin turaren shi na _Fresh guy_ yana dukan hancin ta. Ganin batada niyyar dago kai ya sunkuyo da kanshi daidai fuskarta yace "baki iya godia bane"
"tnx" tace a takaice ta cigaba da dosan bakin kofa. Tana daura hannu kan handle din kofan ya "ban baki izinin tafiya bah karki sake ki kara koda 1 step forward ne" fadi take a ranta "ikon Allah mutum sekace ubana se wani bani orders yake yi kamar a karkashin shi nake aiki gaskiya ya iya rainin wayau" katse mata zancen zuci yayi ta hanyar daura mata lab coat akan kafadar ta. ''wear this nd follow me" kamar kar tasa se kuma tayi tunanin gwara tasa kawai tunda batada wani zabin.. Tana cire hannu daga jikin handle din shi kuma ya bude ya fita.. Haka taita bin shi ba tare da sanin ina za su bah.. Wayar shi ce ta fara ringing yana dubawa ya Dr. Magaji da sauri ya dauka "Hello Dr."
"Surgeon G kana ina ne?
"Gani zan fita me ya faru"
"kazo emergency room yanzu pls"! Ya fada demandingly.
"OK, ok gani nan zuwa" kudi ya ciro a aljihun shi ya ya miqa mata "gashi ki hau taxi Dr. Magaji ya kira ni"
Mamaki ne ya cika ta a zuciyar ta tace "O! Dama shi a nufin shi gida ze kai ni? Tab! Allah ya kyauta in bishi ko in karba kudin hannun shi"
"ki karba kina wasting min tym" firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta fada "no! Nagode inada kudin transport"
"OK, ya miki kadan koh! Let me add more 4 u" wasu kudin ya sake kara mata a kai "take"
qin karba tayi ya miqa hannu zai riqe mata hannu tayi saurin maida su baya... Ya fahimci kwata kwata bata so ya tabata wani killer smile ya mata wanda shi kadai yasan nufin shi.. Da sauri ta juya ta fara tafiya shima cikin sauri ya sake miqa hannun zai janyo ta baya wayar shi ta fara ringing dauka yayi cikin azama ya fara sauri "am on my way" ya katse wayan. Yana waigawa yaga Janan har ta bace mishi daga gani.."zaki zo hannu"
Da sauri ya karasa emergency room din ya shige.. Cikin sauri Dr. Magaji yace "stitches din da aka mata ya kwance sbd jijjigan da tayi yanzu haka wajen bleeding yake jinin ta se karewa yake yi she is suffering" ya dafe goshin shi hannun daya..
Se da Dr. Godwin ya dubata yace "aiki ya dawo baya yanzu se mun koma dakin theater" da sauri aka turata dakin theater.. Shi kuma ya canza kaya. A waya aka kira lab attendant ta kawo jinin mijin tare da wani leda biyu zuwa dakin theater da sauri ta kawo aka jona ma matar ga oxygen a hancin ta aka fara mata aikin....
_Best of luck_
Wajen su Zee ta koma amma bata basu lbrin abunda ya faru bah se dai tace musu ta bar matar a emergency room. Rakata suka yi inda aka kwantar da mijin matar wanda ya farfado amma an bashi gado ya huta..
Wayan Ya Saleem ta kira yana dauka yace "black sisi ya akayi ne"
"Ya Saleem pls kazo ka dauke ni a asibiti bazan iya dawowa da kaina ba jinin wata patient ya bata mun kaya"
"jini kuma? Bari in juyo dama yanzu na wuce asibitin ku naje refilling gas kawai ki fito bakin gate" sallama tama su Zee sannan ta wuce.
Tana fita ta ganshi.. A mota ta bashi lbrin duk abunda ya faru da matar.. Ba karamin tausayawa matar yayi bah. A haka har suka kai gida. Tana shiga daki ta wuce tayi wanka ta sa dogon riga mara nauyi tayi sallah. Dakin Ummiey ta leqa taga tana barci. Kitchen ta koma ta deba abinci taci tasha ruwa seda ta bari abincin yadan fada mata ta koma dakin ta ta kwanta dan huce gajiya.
****
Da dare bayan sun gama cin abinci Abbiey ke tambayar ta ya aikin. Nan ta labarta musu komai suma dai duk sun tausayawa matar addu'a sosai suka mata Allah ya bata lfya.. Daga nan kowa yaje ya kwanta............
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も潱鉂b潱馃挄鉂b潱鉂b潱馃挄馃挄 *_MATAR DOCTOR_*鉂も潱鉂p煉曫煉曫煉曗潱鉂も潳
(( *_2016_*))
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
6鈨�7鈨�****************6鈨�8鈨�
Alhamdulillah! Anyi operation lfya kuma sun fito lfya.
A hankali matar ta fara samun sauki.. Kullum likitoci da Nurses suna duba ta.
Tun daga lokacin Dr. Magaji ya dau nauyin ciyar dasu Janan kullum daga gidan shi ake kawo musu abinci.. Yana jin dadin aiki dasu suma suna jin dadin aiki a karkashin sa..
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. Inda yanzu Janan ta fara sabawa da yima patients alluran anesthesia da kuma sa musu drip. Tunda suka fara aiki da Dr. Magaji kullum 2:30pm yake sallaman su sbd Islamiyan da suke zuwa har yana cema Janan da Aisha "lallai lallai idan saukan ya rage 2 weeks ku fada min kar in manta"
suka ce "in shaa Allah za mu fada maka".....
Gefe guda kuma ita da Imran soyayya na kara karfi inda yayi mata alkawarin yana dawowa daga seminar daya je a London ze zo wajen Abbiey neman izini...
Ashirin da biyar ga wata aka biya su albashi. Ba karamin farinciki suka yi bah. A ranan Janan ta shiga kasuwa bayan sun tashi daga aiki ta siyo ma Ummiey atampa karamar _Sheraton_ ta saima Abbiey agogunan fata guda 2 baki se kuma light brown Ya Saleem da Ya Khaleel ta siyo musu takalma na maza se kuma Nurulqal dinta tasai mai turaren _Gentle guy_... Har ta fito se ta hango wani shagon Arabian perfumes karasawa tayi ta siya guda 2 _Ameer oud da Alharamain Madina_ tana gama siyayya ta tsare adaidaita ya kaita gida...
***Da dare bayan sun gama cin abinci taje ta dakko kayan data siyo tare da canjin daya rage seda ta ba kowa nashi suna ta murna hade da yaba hankali irin na Janan cuz she is jaz 18yrs zata shiga 19 amma tayi abunda wasu 'yan 25yrs baza su iyi bah Ummiey da Abbiey sun samata albarka sosai Ya Khaleel da Ya Saleem se godia suke mata murmushi tayi sannan tace "kun cancanci fiye da haka"... Canjin daya rage ta ajiye a gaban iyayen ta tace "Ummiey,, Abbiey ga sauran canjin daya rage kuyi anfani da shi.. Kanta Abbiey ya shafa yace "Muhibbaty babu abinda za muyi dasu kinga ki ajiye a wajen ki sbd in bukata ta taso miki kinji! Ummiey tace "kwarai kuwa ki riqe ai naki ne Mamana Allah dai yayi miki albarka tare da yayyin ki baki daya" "Ameen" suka amsa.. Janan bata ji dadin haka ba amma bata san yin jayayya da iyayen nata haka ta hakura.. Hira suka dan yi kafin kowa ya wuce makwancin sa.. Tana shiga ta dauki turaren da ta siyo ma Imran ta shaqa tare da lumshe idon sannan ta bude drawer ta ajiye da niyyar in ya dawo ta bashi as a gift.. Har ta sa kayan bacci ta kwanta wayar ta ta fara ringing ko bata duba ba tasan Imran ne sbd wakar _Aashiqui_ ta sa mai.. Sunyi hiran soyayya sosai har yake fada mata nxt week ze dawo kuma cikin week din zai zo wajen Abbiey.. Tayi murna ba kadan bah se da ta fara hamma sannan yace "gwara in barki ki kwanta kar ki fara min sambatu" murmushi tayi kamar yana ganin tace gudnyt nd swt drmz" shi kuma yace "gudnyt nd chocolate drmz I luv u" da sauri tace "bye" ta katse wayan sbd tasan halin Imran yanzu se yace itama sai tace tana son shi.....
~A week later~
Imran ya dawo Nigeria cike da farin ciki ji yake kamar ya tafi gidan su Janan ya ganta sbd ba karamin missing dinta yayi bah amma se ya fasa yafi son se an bashi izini sannan ze je wajen ta su hadu... Bayan ya koma gida ya kirata ya fada mata ya dawo tayi murna sosai tare da mai Allah huta gajiya...
Ranar Thursday da yamma Imran ne tare da Faisal yayan Zee wanda suke kusan sa'annin juna shirye su cikin kaftan harda hula suka zo gidan su Janan se da ya kirata ya tambayeta Abbiey nanan ta tabbatar mai da ya nanan.. Bayan sunyi sallama Abbiey ya fito suka gaisa sannan ya kai su parlon baki yace "Bismillah ku zauna a kujera"
cikin jin kunya suka ce "aa Abbiey kasa ma yayi" bayan sun zazzauna Abbiey ya tashi ya bude fridge ya dakko ruwa da drinks hade da glass cups guda 2 ya aza kan tray ya ajiye musu... Faisal yayi gyaran murya ya farama Abbiey bayanin dalla dalla yana sauraren shi se da ya gama sannan Abbiey yayi ma Imran yan tambayoyi shi kuma ya bashi amsa Abbiey ya kara da "Alhamdulillah nayi farinciki da nuna soyayyar ka ga 'ya ta da kuma izini na daka zo nema kuma ka tabbatar min da auren ta zakayi ba wai da wasa kazo bah.. Tor na amince ka dinga zuwa sau 2 a sati ku kara fahimtar juna kafin magabata su shiga cikin maganar"
"mun gode mun gode Abbiey Allah ya kara girma"
Haka suka bar gidan Imran baki yaki rufuwa dan murna suna shiga mota ya kira Janan ya fada mata yanda sukayi da Abbiey sosai taji dadi har suka kusa gidan su Faisal Imran na waya da Janan seda sukayi parking a kofar gidan sannan sukayi sallama..
Abbiey na shiga gida ya fadawa Ummiey komai ita ma tayi farin ciki jin yanda Abbiey ya yaba da hankalin Imran.. Yace "ina so in kara bincike a kanshi kin san rayuwar yanzu se a hankali" "gaskiya ne" inji Ummiey sannan ta cigaba "Uhum kaga ikon Allah ko? Bakin ka ya bi 'yarka da kake kiranta *MATAR DOCTOR* gashi likita yazo neman auren ta" yace "kedai bari Allah mai iko Allah yasa abokan rayuwa ne su"
"Ameen thumma ameen" Ummiey ta amsa...
_Shawara ga iyaye.. Ya nada kyau iyaye su dinga yiwa 'ya'yansu fata nagari ba wai su dinga binsu da mugun fata ba domin bakin iyaye ba karamin tasiri yakeyi ba akan 'ya'yan su_ ...
_Allah yasa mu dace ameen_
*******
Yau ta kama Friday su Janan na zuwa aka ce list ya fito na Nurses domin za a canza su daga office din da suke zuwa wani.. Addu'a kawai su Janan suke yi sbd basa son a canza su daga office din Dr. Magaji....
Suna dubawa suka ga Aisha zata dinga aiki tare da Dr. Salma ita kuma Zee an barta da Dr. Magaji Janan kuma an hadata da Dr. Godwin... Ba karamin haushi suka ji da aka raba su kuma ranan Monday za su fara aiki da sabbin likitocin da aka hada su... Ita dai Janan ta kasa magana gabadaya bata san ganin Dr. Godwin balle har tayi aiki karkashin gashi kuma babu daman a canza sbd tun daga ministry of health aka tsara list din kuma an aika ooffice din ko wanni Doctor.. Haka suka ta jimami shi kanshi Dr. Magaji be ji dadin abunda ya faru bah amma babu yanda ze yi... Gaba daya ranan sun kare shi cikin rashin walwala Janan kamar tayi kuka dan bakin ciki...
_Har na kosa in fara ganin drama tsakanin Dr. Godwin da Janan.. Kuma nasan kun kosa masoya na_馃槣
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/5, 8:08 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: 鉂b殰 *MATAR DOCTOR*鈿溾潱鉂b潱鉂b殰鈿溾潳鉂b潱鈿溾殰鉂b潳鉂b潳鉂も潱鈿溾殰鈿溾潱鉂も潱鈿溾殰鈿溾殰鉂も潳
*Rukky Bae*馃槒馃槒馃槒
6鈨�9鈨b€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�7鈨�0鈨�
*Sunday*
Zaune suke gaba ki dayan su a parlor Abbiey yayi gyaran murya ya fada musu komai game da zuwan su Imran sannan ya kara da cewa "Muhibbaty na yaba da hankalin yaron nan sbd ya fada min yanda kuka hadu sannan kuna waya amma be taba zuwa kuyi hira ba sbd be tambayi izini na bah.. Hakan kuma da yayi ya kara mishi kima da daraja a waje na.. Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhayrin dake ciki" duk suka amsa da ''Ameen" amma banda Janan wacce take ji kamar ta nutse a wajen dan kunya gaba daya ma ta kasa dago ido ta kalle su se wasa take da yatsun kafar ta.. Abbiey yace
"zaki iya komawa dakin ki dan naga duk kin takure waje daya" ai kamar jira take yi ko rufe baki be gama yi ba ta tashi a guje ta wuce daki... Murmushi yayi tare da girgiza kai sannan suka cigaba da magana anan yake cewa Khaleel da Saleem "ku bazaku fito da mataye ba ko? So kuke in bar duniya ba tare danaga jikoki na ba kenan kai Khaleel yanzu ka doshi shekaru 29 kai kuma Saleem yanzu kana 26 lokaci fa yana kurewa duk da dai aure lokaci ne amma har da niyyar mutum Dan Allah ku yima kanku fada" duk suka yi shiru sbd sun san gaskiya Abbiey ya fada Khaleel yace "Abbiey kayi hakuri in shaa Allah nan bada dadewa ba zamu yi aure ku taya mu da addu'a"
Ummiey da bata ce komai ba tunda suka fara magana tace "Allah ya baku mataye nagari sannan kuma ku kara qaimi wajen yin addu'a.. Allah ya zaba muku mafi alkayri" duk suka amsa da "Ameen" sannan Abbiey yace "Allah yayi muku albarka ku tashi ku tafi".. A tare suka tashi suna amsawa da Ameen sannan duk suka fice ......
Janan na zaune a daki tana duba wasu takardu har yanzu zuciyar ta babu dadi sbd maidata office din 'surgeon G' da akayi amma dai yanzu tadan ji sanyi a ranta sakamakon yabon da Abbiey yayi wa Imran.. Tana cikin tunani wayar ta tafara ringing ko ba a fada ba Imran ne. Da sauri ta dauka bayan sun gaisa ya ce "Luvly Angel yau In shaa Allah zan zo bayan magrib hope u r free"... Shiru tayi ta kasa bashi amsa "Angel r u there?
"yeah ina ji amma dan ban 2 mins I will call u bck"
ding! ta katse wayan. Da sauri taje dakin Ummiey tayi sallama aka amsa mata sannan ta shiga ta same ta kwance a kan gado amma ba barci take yi bah. Gefen gadon Janan ta zauna tana wasa da hannun ta ta kasa magana.
"Hulwaty akwai magana ne? Naga kin yi shiru kin kasa magana"
"em.. em.. dama.. dama" tashi tayi daga kwanciyar da tayi sannan ta dafa kafadan ta tace "Hulwaty feel free nd talk to me kin san dai babu wacce ta fini a wajen ki ba ma wannan ba ko kin manta we r frnds ke fa da bakin ki kika ce am ur bestie?
"ban manta ba Ummiey u r my best nd u will always be"
"so tell me am all ears"
"Ummiey dama em...em ya kira ni wai if am less busy after magrib ze zo shine na zo in fada miki sbd ban san ko akwai abinda zan yi miki bah kuma ban san ko tym din yayi daidai ba nd I hv to ask 4 ur permission b4 I can make any decision"
Tunda ta fara magana Ummiey ke kallon ta kafin ta nisa tace "ke ta daban ce Angel" da sauri ta dago tana kallon Ummiey sbd tayi mamakin sunan da ta kirata dashi cuz Imran kawai ta taba ji yake kiran ta da sunan.. Ummiey ce ta tsamota daga duniyar tunanin data fada ta hanyar kamo hannayen ta tana murzawa kafin ta cigaba "babu abin da za kiyi min koma akwai na yafe kuma tym din it's okay se dai ina so in kara tunatar dake duk da nasan kin sani amma wajibi na ne in sake fada miki a matsayi na na mahaifiyar ki..ki riqe mutuncin ki a duk inda kike ki sani duk abinda za kiyi Allah yana kallon ki kuma shedan babu abinda bazai iya ba domin a cikin wani hadisin mazon Allah (SAW) yana cewa: _"a duk lokacin da baliga mace da baligi namiji su kebe a wani waje su biyu to lallai ne shedan ze kasance cikon na ukun su"_
A cikin wani hadisin ma mazon Allah (SAW) ya kara cewa:
_"kada dayan ku ya kebe da mace face a tare da ita akwai muharramin ta_ Hulwaty ki kula da kyau domin yanzu zamani ya canza shedan yana matukar yin tasiri akan mutane especially masoya sbd haka u hv 2 b very careful"
Rungume Ummiey tayi tare da fadin "Jazakillah khairan Ummiey u like no other"
"oya tashi kije daki ki kira shi ki fada mishi ze iya zuwa" fuska ta rufe cike da jin kunya kafin ta miqe ta fita..
Daki ta koma sannan ta kira shi ta fada mishi.. Yayi murna sosai sannan yace "at long last zan zo in sake ganin cute face din luvly Angel dinta".. Kin san miye? "aa sai ka fada"
"kin fi ko wace mace kyau a duniya komai naki is unique nd special no words to describe how beautiful u r Angel"
"Hmm Nurulqalb akwai ka da iya tsara zance ur words r cool kai kanka u r so cool in short komai naka is cool.. Yanzu dai mu bar wannan maganan se anjima in ka zo"
"OK luv se kin ganni take care of ur self 4 me"
"bye banda over speeding kayi driving a hankali"
"as u wish my lady"
鉂も潱鉂も潱鉂も潱鉂も潱鉂�
鉂b潱
*Rukky Bae*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/6, 12:41 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: 鉂� *_MATAR DOCTOR_*鉂b殰鈿溾潳鉂b潳鈿溾潱鈿溾殰鉂も潱鈿溾殰鉂も潱鈿溾潳鉂b殰鉂も潱鈿溾潳鉂b殰鉂�
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
7鈨�1鈨�
4:00pm Malam Ahmad yazo yi ma Janan lesson bayan ya dawo daga garin su. Ba bata lokaci ta fita tayi mishi ya gajiyan hanya anan take fada mishi saura 2 months ya rage ayi saukan su.. Yayi farin ciki sosai.. Nan yake tambayan ya mutanen gida?
Tace "kowa lfya lau sun ce a gaishe ka"
"Ma shaa Allah ina amsawa nima kafin in tafi zan leqa mu gaisa"
Karatun baya yace ta karanto mishi. Bayan ta karanta tace "Malam na kara amma ban san fassaran ba"
"karanto inji se in kara miki tare da fassaran"
Tiryan tiryan ta karanto mishi har se da ta kai inda ta tsaya.
"gaskiya kin yi kokari kuma kin kyauta da kika kara sbd baki tsaya tunanin bananan ba ki ajiye kice se na dawo Allah ya albarkaci ilimin ki"
"Ameen Malam"
Kari yayi mata sannan ya fassara mata duka se wajajen 6:00pm suka gama karatun. Bayan ta ninke tarduman har ta wuce ya kira ta ya miqa mata wata bakar leda yace "gashi ki ba Ummiey tsaraban kauye ne kema na kawo miki ridi da kwakumeti duk suna ciki kuma ki mata iso ina so mu gaisa"
"Allah ya saka da alkhayri Malam mun gode"
Tana shiga gida ta fada ma Ummiey Malam yace su gaisa ga kuma tsaraba ya kawo a baki.. Hijjab Ummiey ta saka sannan ta fita.. Bayan su gaisa ne take mishi godian tsaraban daya kawo musu.
"a haba babu komai ai ba ma shida yawa...
"aa me yawan kenan mun gode sosai"
Sallama suka yi ta koma ciki shi kuma ya wuce..
Kayan kadi ya kawo musu harda daddawa Ummiey tayi murna sosai tace "a lallai zamu sha miyar kuka kenan"
Janan tace "ai fa! nasan Abbiey ze yi murna idan yaga anyi miyar kuka"
Suna zaune suna cin ridin har aka fara kiraye kirayen sallan Magrib duk suka miqe dan gabatar da sallah
Ummiey ce ta shigo ta tarar da Janan kan sallaya tace "Huwalty ki tashi ki shirya kafin ya karaso"
"toh Ummiey na"
Fita Ummiey tayi ita kuma Janan ta shiga bayi tadan watsa ruwa. Tana fitowa ta bude wardrobe riga da skirt na atampa purple nd white tasa... Body spray kawai ta fesa ta shafa mai bata shafa komai a fuskar ta ba dama ita ba ma'abociyar kwalliya bace.. Ribbon ta dakko tayi parking kalban da Ummiey tayi mata wayar ta ta fara ringing da sauri ta karasa kan gado ta dauka "Assalamu alaikum"
"Wa'alaikumussalam my Angel gani a kofar gidan ku"
"OK ur highness gani na fitowa in a jiffy"
"pls kiyi sauri kin san na kosa in ga cute face dinki"
Tace "Toh" da sauri ta dauki purple hijjab din ta me hannu ta saka flat shoes purple ta saka sannan ta fito. Jin motsin Ummiey a kitchen yasa ta nufi can, ganin ta tayi tana daura wani glass bowl akan tray tace "Ummiey ga shinan ya karaso"
"tor je ki shigo dashi ki kai shi parlon baki"..
Tana fita ta tarar dashi jingine a jikin mota yayi folding hannayen shi a kirji yana sanye da ash caftan..
Da sallam ta kara wajen shi sannan suka karasa parlon bakin.. Kujera me facing juna suka zauna sannan suka gaisa..
"Ina zuwa" tace mishi
Da sauri ta shiga kitchen ta daura drink da glass cup akan tray ta fito.. Tana fitowa suka ci karo da Ummiey.. "Huwalty koma kitchen din zaki ga peppered chicken a cikin glass bowl tare da plate nd fork sannan ki dakko babban tray ki kawo nan"
Kitchen din ta koma ta dakko sannan ta fito. "Ummiey gashi nan na dakko"
"tor yi maza ki kai mishi"
Baki bude take kallon Ummiey tace "Ummiey yaushe kika yi wannan?
"dazu ne da zan yi girkin dare naga ya kamata ayiwa bako wani abun"
"Ummiey ke uwace wacce babu kamar ki"
"ni dai wuce ki kai mishi kin barshi yana jiran ki"
Peck ta manna mata a kumatu sannan ta koma wajen Imran.. Hiran soyayya suka yi sosai se da aka fara kiran sallan isha'i yace "Luvly Angle zan tafi badan na gaji bah se dan lokacin salla ya shigo.. Nxt Week in shaa Allah zan dawo amma kafin nan ina so in shiga mu gaisa da Ummiey kafin in tafi"
Komawa ciki tayi ta sanar da Ummiey sannan ta dawo tace mishi "zaka iya shigowa"
A kujera ya tarar da Ummiey zaune. Kasa ya zauna sannan ya gaishe ta. Ita kuma Janan daki ta wuce dan dakko turaren da ta siyan mishi. Tana kokarin fitowa Ummiey ta kirata. Da sauri ta fito Ummiey tace "kije kuyi sallama ya fita"
Sanda ta karasa har ya shiga cikin mota amma be kulle kofar ba.. Ledan turaren ta miqa mishi tace "a gift frm my hrt"
Murmushi yayi sannan ya karba yace "tnx Angel".. Sallama suka yi har ta juya zata wuce ya kirata.. Dawowa tayi sannan shima ya miqa mata wata yar madaidaiciyar leda yace "ga tsarabar London kiyi hakuri naso in siyo miki abubuwa da yawa amma ban samu chance na shiga kasuwa ba se ana gobe zan dawo sbd aiki yayi min yawa"
"nagode Nurulqalbee wannan ma yayi kuma nayi farin ciki sosai"
Hannu suka daga ma juna sannan ta koma gida se da yaga shigan ta gida yayi ajiyar zuciya sannan ya tada motar shi ya wuce... Tana shiga ciki ta miqa ma Ummiey ledan da Imran ya bata. Suna budewa suka ga wasu hadaddun flat shoes guda biyu baki se kuma brown.. "kin gode in Abbiey ya dawo se ki nuna mishi"
Bayan dawowar Abbiey ta nuna mishi sannan ta dauki abincin ta ta wuce daki kwata kwata yau taki yarda taci abinci da su sbd kunya.
Kafin ta kwanta seda suka yi waya da Imran..
鈿溾潱鈿溾潱鈿溾潱鈿溾潱鈿�
*_Monday 7:00am_*
Dr. Godwin ne ya shigo asibitin cikin shigar black suit nd white sleeve se bakin tie, black cover shoes da bakin sunglasses yayi kyau matuqa.. Hanyar office din shi ya nufa ba tare da ya kula nurses din dake gaishe shi bah. Yana dosan kofar office din shi yaga tarin patients suna jiran shi murda handle din kofar yayi ya shiga ciki to his greatest surprise be ga Janan ba se Jessica da Ruth kawai zaune cikin office din suna ganin shi suka miqe tare da fadin "morning sir"
Be kula su ba seda ya zauna akan kujerar shi sannan yace "morning" a taqaice.. Files din dake kan teburin shi ya fara dubawa sannan ya kira me kawo files yace "ina office patients za su iya fara shigo wa"
*_7:45am_*
Janan kwance a kan gado tana bacci hankali kwance Ummiey ta shigo tana bubbuga kafar ta tana fadin "Hulwaty! Hulwaty!!"
"uhumm Ummiey pls let me sleep a little" ta fada cikin muryan bacci
"ki tashi fifteen minutes to 8 fa! Kin san dai kinyi latti ko?
Wani irin zabura tayi hade da salati tana murza idanu lokaci guda ta dire kafafun ta a kasa da sauri ta wuce bayi tayi wanka tana fitowa a gurguje ta shirya..
8:05am ta gama shiri ta dakko jakan ta ta fito.. Ummiey ta gani tana fitowa daga kitchen da cooler a hannu
"Ummiey ina kwana"
"lfya lau Hulwaty ga plantain nan kizo ki karya"
"aa Ummiey wallahi nayi latti sosai"
"tor tsaya in sa miki a karamar cooler se ki tafi dashi kya ci a can"
"Ummiey karki damu zan siya abu in ci idan na karasa asibitin"
"Allah ya bada saa se kin dawo ga 500 akan center table ki dauka"... Da sauri ta dauka ta fita... Kwata kwata bata samu adaidaita ba haka ta fara tafiya da qafa gashi akwai nisa zuwa bakin titi daga gidan su.. Se da tayi tafiya sosai sannan ta samu Napep da sauri ta shiga.
8:25am suka karasa asibitin biyan me adadaita tayi sannan ta kara asibitin se faman sauri take yi..
_8:30 am_ tana tsaye a bakin office din Dr. Godwin.... Agogon hannun ta ta duba sannan tace "Ya Rabbi help me! Wani dogon numfashi ta ja sannan tayi knocking kofar..
"yes" taji muryan Dr. Godwin daga ciki..
Dummmmmm!!!! Gaban ta ya fadi. Jiki na rawa tasa hannu ta murda hannun kofar sannan ta sa kafar ta daya cikin office din hade da yin sallama.........
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/12, 5:48 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: [11/11, 4:44 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: 鉂b殰 _*MATAR DOCTOR*_鉂b殰鈿溾殰鉂b潱鈿溾潱鈿溾潱鈿溾潱鈿溾殰鉂b殰鉂b殰鉂b殰鉂b殰鉂b殰鈿溾殰鉂b潱鉂�
_*Rukky Bae*_馃槒馃槒馃槒
7鈨�2鈨�
Kafar ta daya ta sa cikin office din hade da sallama babu wanda ya amsa mata cikin su sbd duk ba musulumai bane.. A hankali ta karasa shigo ta ajiye jakan ta kan kujera sannan taje gaban taburin shi yana duba wani file.. muryanta na rawa tace "Go...od...mo..rning sir"
Bai dago ba balle taga yanayin shi ya amsa mata da "morning"
Wani dogon ajiyan zucia tayi wanda har Dr.Godwin din yaji amma duk da haka bai dago ba.. Kujeran da jakan ta ke kai ta koma ta zauna tana me jin dadin be mata fada bah...
Haka patients sukayi ta shigowa yana basu appointment sbd yau bazai yi ma kowa operation bah..
Lokacin sallah nayi ta tambayi permission din shi sannan ta fita.. Tana idarwa ta fita wajen asibitin.. Wani shagon snacks da drinks taje ta siyo meat pie da hollandia milk sannan ta dawo office din.. Tana shiga taga duk basa nan. Wani sanyi taji a ranta sbd sauri ko kofar bata rufe ba... Wajen zaman ta ta koma sannan ta dakko meat pie din ta bude hade da yin Bismillah a hankali ta fara ci tana sipping hollandian ta ji take kamar ba a cikin duniyar nan take ba sbd dadin abunda take ci har wani lumshe ido..
Tunda ta fara cin meat pie din Dr.Godwin ke tsaye a bakin kofa ya harde hannun shi yana kallon yanda take cin abincin.. Hannun shi yasa a aljihun ya ciro wayar shi ya seta ta daidai sanda ta saki wani murmushi ya kashe mata hoto sai da ya mayar da wayan aljihu sannan yayi gyaran murya daidai ta na cinye last bite da sauri ta dago tana kallon shi cike da tsarguwa ganin ya kafe ta da Ido da kyar ta hadiye na bakin ta har tana kokarin kwarewa.. Ciki ciki ta fara magana "ji yanda ya kafe ni da idanun shi gashi nan na kusa kwarewa"
Wajen ta ya karaso yace "me naji kina cewa"
"Am.. am.. Ni banyi magana da kai ba"
"Toh da wa kike magana in ba dani bah
"Ni bada kowa nake yi bah"
"Dago ki kalli cikin idona kice bani kike yi bah"
Gamgam ta runtse idon ta dan bazata iya kallon shi ba
Ido ya kafa mata yana kallon yanda ta runtse ido kamar taga abun tsoro ga eyelashes din ta sun sakko har ya bude baki zai sake magana kenan su Jessica suka shigo cikin office din.. Cak suka tsaya suna kallon su jin alaman an shigo yasa Dr.Godwin saurin kallon kofa ganin su Jessica ne yasa shi bata rai hade da galla musu harara sannan ya koma wajen zaman shi se da ya zauna sannan yace "baku iya knocking bane zaku shigo min cikin office anyhow?
"Sorry sir! But mun yi...
"Shhhhh surutun ku ya ishe ni haka bana san jin komai"
Wajen zaman su suka koma cike da jin haushi..
Ita kuma Janan dadi taji atleast shigowan su ya mata anfani...
_2:25pm_ nayi Janan ta fara tattara kayanta dan dama ta saba lokacin da suke office din Dr. Magaji karfe 2:30 suke barin office... wajen table din shi ta nufa dan signing out tana daukan littafin yace "hey miss! what r trying to do?
"Uhum uhumm... ina so inyi signing ne cuz it's almost 2:30pm
"U came late nd u wanna leave early huh!
Shiru tayi ta kasa magana
Ya cigaba da cewa "ba yanzu zaki tafi ba"
"Dr. Pls let me go zan je islamiya kuma bana so inyi latti"
"I said no! Ki koma ki zauna cuz babu inda zaki baki so kiyi latti shine kuma kika zo latti"
"But sir..
Be bari ta kai karshen maganan ta ba katse ta "no but! kawai ki koma ki zauna sai tym din da naga dama zan barki ki tafi kuma karki sake cewa komai as u can see na gaji da magana kin gane ko"
Jiki babu kwari ta koma ta zauna idon ta duk ya cika da kwalla dolenta ta hadiye hawayen ta dan kar ya raina nata... Wayar ta ta ciro dan buga game unlock button ta danna amma taga be kawo ba sai a lokacin ta tuna bata da chargy a waya dan jiya basu kwana da wuta bah gashi bata zo da charger ba na Dr.Godwin ne kawai manne a jikin socket kuma ita asara take ji ta tambaye shi ya bata aro ta gwammace ta zauna a haka.. gaba daya haushi ya cika ta haka tayi ta zama bata aikin komai..
Bangaren Dr.Godwin yaji dadin abun da yayi mata dan ko ba komai yasan taji haushi dama haka yake so.
_3:00pm_ Ruth da Jessica suka yi signing tare da wuce nan fa Janan haushi ya kara kamata ga tsoro kuma duk ita kadai sbd bata san zama daga ita sai Dr.Godwin.. jira kawai take lokacin sallah yayi ta fita daga nan ta wuce gida abun ta... ganin ta kawo ma kanta mafita yasa ta dan murmusa...
_3:55pm_ nayi tayi saurin mikewa dama komai nata a hade yake tace "sir lokacin sallah yayi fa"
Be dago ya kalleta ba gaba daya ma ya maida hankalin shi kan laptop din dake gaban shi kamar yasan plan dinta yace "kije ki zauna bazaki fita ba har sai tym din danayi niyya"
Ido ta zaro waje tace "sir sallah ne fa!
"Yeah ai naji abun da kika ce but zan iya miki favour guda daya ki shiga cikin toilet din nan kiyi abun da zakiyi sai ki shinfida dankwalin ki kiyi a kai"
Zata sake magana ya daga mata hannu "bana san yawan surutu".. Bata da wani option daya wuce tayi haka dan bata san lokacin da zata koma gida ba kuma lokacin sallan zai iya wucewa... haka ta shiga tayo alwala ta shinfida dankwalin ta a kasa ta fara sallah.. tunda ta fara sallah Dr.Godwin yayi tagumi yana kallon yanda take sallan a nutse duk se yaji ta kara burge shi.. ya shagala da kallon ta har ta idar tana juyowa suka hada ido da sauri ta kauda kanta gefe...
_6:15_ hadari ya taso garin yayi bakinkirin ganin haka yasa Janan ta kara rudewa dan bata kaunar ruwa ya taba ta sbd babu wuya mura ta kamata..
Ganin yanda hadari ya taso yasa Dr.Godwin dago da kanshi cike da mugun ta yace "u can go nw"
Wani kallo tayi mishi ji take kamar ta fasa ihu da sauri ta dau jakarta ta fita ko kala bata ce ba..
Da sauri da sauri ta fita daga harban asibitin tana fitowa aka fara yayyafi gashi ta rasa abun hawa dan duk adaidaitan da yake zuwa acike yake duk tabi ta qagara ta ganta a gida haka tayi ta tsayuwa har ta dan fara jikewa sai faman tsaki take yi sbd haushi.. kusan minti 4 tayi a wajen sanna dan adaidaita ya tsaya da wani saurayi aciki ta fada mishi idan zai kaita gashi yayyafin ya fara karfi saurayin yace " Dallah Malam ba kudin drop na baka bah kuma inada in da zani ka tsaya a nan kana bata min lokaci"
Mai napep yace "haba dan saurayi baka ga ta fara jikewa bane? Naga kuma duk kusan hanya daya zamu bi in na kai ka sai in je in ajiye ta"
"Ni ina ruwana to! Kaga in zaka ja mu tafi gwara mu tafi in kuma ka nace sai ka dauke saidai ka bani kudina"
Hannu yasa a aljihu zai ciro kudin ya bashi Janan tayi saurin cewa "aa malam jeka kawai bari in jira wani bana so shiga hakkin kowa"
Cike da jin tausayin ta mai adaidaita ya burga abinshi ya wuce yana Allah wadar da hali irin na saurayin nan shiko saurayin ko a jikin shi..
Haka tayi ta tsayuwa amma ta kasa samun abun hawa cikin lokaci kadan har ta fara rawan sanyi gashi ruwa yayi karfi wani dakali ta hanga sbd babu inda zata fake da sauri ta nufa dakalin ta zauna tare da tusa kanta cikin cinyoyin ta ruwa na dukan bayan ta so take tayi kuka amma ta kasa.. Tana zaune a haka taji horn din mota kin dagowa tayi dan yanda zuciyar ta ke zafi... A hankali ya bude motar tare da fitowa riqe da lema a hannun shi har ya iso gaban ta tare da durkusawa jin an sa mata lema ruwa ya dena dukan ta ga kuma kamshin turaren shi yasa ta dago suka hada ido ya sakar mata wani murmushi mai sanyi.......
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/15, 10:10 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂� *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潱鉂b潳鈿溾潳鉂も潱鉂も殰鉂b潱鉂b殰鉂b潱鉂b殰鈿溾潱鉂b殰鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潱鈿溾潱鈿溾殰鉂も潱
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
*_wannan page din na sadaukar dashi ga duk daukacin masoya na nagode da soyayyar ku agareni da kuma kwarin gwiwan da kuke bani Allah ya bar zumunci.. soyayyar da kuke nuna ma wannan littafin shi ke kara bani courage wajen cigaba da rubuta muku shi_*
*_Jazakumullah bi khayr_*
*_i luv u lodi lodi_*
馃槝馃槝馃槝馃槝馃槝馃槝馃槝馃槝馃槝
7鈨�3鈨�
Hada ido suka yi ya sakar mata da wani murmushi mai sanyi wani kallo ta watsa mishi tare da kauda kanta gefe haka yasa jikin shi yayi sanyi ga ruwa na jika shi white sleeve din shi ya jike har singlet dinshi na nunawa haka gashin kanshi ya jike sajen shi ya kwanta lub a gafen fuskar shi.. ganin bata sake kallon shi ba yayi gyaran murya sannan yace "hey! Ki tashi in rage miki hanya danna ga baki samu abin hawa ba in kuma bazaki ba gud nd fyn dan ni bana taimako balle tausayi kema ba wai ina tausayin ki bane kawai naga dama ne"..
Yi tayi kamar bada ita yake yi ganin yanda ruwa ke jika shi yasa tadan ji dadi ita ma ko ba komai shima ya dandana yaji..
Sake magana yayi yace "baki ga ruwa na jika ni bane? Ki tashi in kuma baki so inyi tafiyata"
Tasan sarai in ya tafi bazata samu abun hawa ba amma ita gani take bazata iya bishin ba dama gashi shi yaja mata har ruwa ya jika ta.. ganin bata da niyyar mishi magana yasa yayi tunanin bari ya fada mata magana hala taji haushi ta bishi yace "kina wani pretending kamar baki so ki bini bayan can karkashin zuciyan ki kina jiran irin wannan opportunity kuma karki manta opportunity comes but only once sbd haka ni zan wuce mota na baki minti daya tak ki gama gulman ki sai ki shigo mu tafi" da sauri ya miqe tsaye dan baya san ta samu damar yin magana sannan ya jingine mata leman yanda ruwa bazai jika ta ba ya juya ya fara tafiya wajen mota ruwa na kara jika shi...
Ba karamin haushi maganan ya bata ba amma ta daure dan bata so ya gane taji haushi ko kallon shi bata yi bah.. shikuma a tunanin shi tunda ya gaya mata magana kuma ya juya zai shiga mota hala tayi saurin biyoshi har ya bude motar se ya juya ga mamakin san ko motsi bata yi ba sai ma lemar shi daya gani a kasa ta wurgar
Murmushi yayi sannan yace a ranshi "komai tayi yana mata kyau when she gets angry she looks cute in tayi murmushi she looks more cute... zan so in ganta in tana kuka nasa zeyi fitting dinta" a hankali ya kara komawa inda take amma beyi mata magana ba se dai ya tsaya a gaban ta yana kallon ta yafi minti 2 a haka yaga alaman bata da niyyar tashi balle tayi magana hakan yasa shi yinkurin riko hannun ta dan ya daga ta da sauri ta sake dukunkune kanta abun yaso ya bashi daria se ya dake yace "ki tashi nifa na gaji in kuma baki tashi ba i swear with my life sai na dauke ki kamar baby na saki a mota if u think am joking ki tsaya ki gani" hannun sleeve dinshi ya fara rolling sama ganin da gaske yake yi yasa tayi saurin mike wa tana turo baki amma bata tafi ba ya sake cewa "ohh bazaki iya tafiya ba ko? Shikenan lemme carry u" dayan hannun rigan ya sake nadewa sama ai bata jira komai ba tayi saurin wucewa jikin ta sai digan ruwa yake... gwalo yayi mata sanna ya bita shima sai diga yake yi abun ka da dagon mutum har ya wuce ta ya bude mata kofar gaba a hankali ta shiga cikin motar wani sanyi da kamshi suka doki hancin ta bata san sanda ta lumshe ido bah.. zagayawa dayan side din yayi ya shigo ganin tana rawan sanyi yasa shi kashe A.c sannan ya miqa hannun shi bayan seat din ya dakko suit dinshi daya yi hanging ya sa mata da sauri ta kankame suit din duk yana kallon ta amma beyi magana bah.... Kunna motar yayi suka fara tafiya se sharara gudu yake yi babu me cewa wani uffan shi be tambayeta ina ne gidan su bah itama bata fada mishi hanyar bah jin shirun yayi yawa yasa shi kunna wakar _patoranking na my woman my everything_ lokaci zuwa lokaci yana bin wakar haka sukayi ta tafiya.. agogon motar ta kalla taga 7:30pm ido ta zaro amma kuma ita bata so tayi mishi magana ga ruwa ya kara karfi ganin ya dau hanyar Zaria yasata yin saurin cewa "ba nan bane hanyar gidan mu fa"
"Aww ashe kina kallo se yanzu kika ga daman yin magana? Na riga na dau hanya duk inda na kai ki nan zan ajiye ki"
Baki ta tabe amma can kasar zuciyar ta tsoro ne fal daurewa tayi tace "Hmm ko dai kidnapping dina zakayi ne shiyasa ka bi hanyar nan?......
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂b潱鈿溾殰鉂b殰鉂も潳鈿溾殰鈿� *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潱鉂b潳鈿溾潳鈿溾潳鈿溾潳鉂b殰鈿溾潳鉂も殰鉂�
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
7鈨�4鈨�
[11/16, 7:04 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫:
Wani irin daria ya fashe dashi wanda shi kanshi be san ya iya irin ta ba sannan yace "akan wani dalili zanyi kidnapping dinki? After all ni bama san ganin fuskar ki nake ba da ace dai sonki nake yi watakila da nayi kidnapping dinki yanzu dai ban san in sake cewa komai sbd tun dazu kike ta sani surutu kuma ze iya sani rashin lfya ki dinga kwatan ta mun gidan ku kuma bance ki nuna min hanya da hannu ba da baki zakiyi magana sbd ki biya ni maganan da nake tayi tuntuni har sai na kaiki kofar gidan ku in kuma kika ki gida na zan wuce dake in kuma kina tantama ki gwada"
Ido ta zaro waje cike da tsoro a ranta tace "nasan zai iya gwara kawai in mishi kwatancen" da wannan shawaran ta ce "a wurno rd muke"
Yace "Ban san gurin ba sbd haka aikin ki yafara yanzu"
Haka tai tayi mishi kwatance har suka kai kofar gidan.. ko gama parking be yi ba ta murda hannun kofar ta fita da sauri ta shige gate din gidan su ko waigowa batayi bah.. girgiza kai kawai yayi tare da cewa "zamu hadu gobe ai zaki sani ne" sannan ya wuce gida shima..
Tana shiga tsakar gidan su ta tuno da suit din shi a jikin ta da sauri ta fita amma bata ganshi ba haka ta dawo ciki ta cire suit din ta nade shi ta sa cikin jakan ta sannan ta bude kofar parlor'n da sallama ta shiga ganin su Ummiey tayi a tsaitsaye sai kai komo Ya Khaleel ke yi da waya a hannun shi.. jin sallamanta yasa su juyowa da sauri suna tambayan ina ta tsaya har karfe 8:00pm kuma wayar ta a kashe?
Lbr ta basu na rasa abun hawa amma bata fada musu komai ba game da Dr.Godwin.... se a lokacin hankalin su ya dan kwanta..
Daki ta wuce tasa wayar ta a chargy sannan ta shige bayi tayi wanka da ruwa mai zafi hade da wanke suit din Dr.Godwin da kayan ta ta shaya a bayin tana fitowa tasa kayan bacci ta fito daga dakin ta wuce kitchen ta debo abinci ta ci tana gamawa Abbiey yace ta je tayi bacci sbd karta makara ga kuma gajiyan yau...
Sallama tayi musu sanna ta shiga daki.. Imran ne yazo ranta da sauri ta kunna wayar nan taga text msgs daga Imran iri iri wanda yake nuna yanda yayi missing dinta da kuma rashin samun ta a waya.. Murmushi tayi a fili tace "Allah sarki Nurulqalbee nima nayi missing dinka" dialing numb din shi tayi taji number busy tana kashewa ya kirata nan tace "naji number busy ne"
"Ke nake kira ai kin san tun yaushe nake trying layin ki ne"
Hakuri ta bashi tare da fada mishi wayar ce babu chargy.. sosai suka sha hira sannan yace "yau ni zan miki addu'a se ki shafa ki kwanta kinji Angel"
"Yawwa Nurqalbee ina jinka"
Adduo'i sosai yayi mata sannan ta shafa daga bisani sukayi sallama ta juya ta kwanta cike da nishadi....
鉂b殰鉂も殰鉂b潳鈿溾潱
Dr.Godwin na koma gida ya wuce dakin shi towel ya dauka sannan ya shiga bayi ya hada ruwa mai zafin gaske ya dade kafin ya fito ya shirya cikin yellow pyjamas.. dining ya wuce yaci abinci yana gamawa ya koma kan kujera ya kalli kwallo sai wajen 10:00pm ya koma daki nan ma seda ya gama danne dannen shi a laptop yana rufewa yaji kanshi ya fara ciwo nan ya tuno yau through out be sha maganin shi bah da sauri ya ballo yasha har yaja bargo ya kwanta ya tuno da hotan da yayiwa Janan zumbur ya tashi ya dakko wayar shi ya zubawa hoton ido yanda tayi murmushi yasa shi shafa screen din wayar a haka bacci ya kwashe shi....
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/22, 5:38 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: [11/21, 6:43 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂� *_MATAR DOCTOR_*鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂も殰鉂も殰鉂も殰鉂も潳鈿溾殰鉂も潱鈿溾潳鈿溾潳鈿溾潳鉂�
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
_Dedicated this page to_
_Hadiza berrish_
_Pheenerh fulani_
_and all the members of Hauwa Slim Small group_
7鈨�5鈨�
*~_washe gari_~*
Da asuba Janan na farkawa taji hancinta ya toshe alamar mura kenan dama tayi tunanin haka... bayi ta shiga tayi alwala sannan tayi sallah bayan ta idar tayi daily adhkar dinta se wajen shida saura sannan ta shiga bayi ta dakko suit din Dr.Godwin ta goge har lokacin kamshin turaren shi na jiki kamar be dade da fesawa wa ba a ranta tace "gaskiya wannan ya iya cika turare na wanke riga amma har yanzu kamshin yana nan"
Tana gama gogewa ta wuce kitchen dankali ta soya musu da kwai sannan ta dafa ruwan shayi me kayan kamshi da na'a na'a ta zuba a babban flask se karamin flask kuma wanda zata tafi dashi asibiti sbd mura 6:30am ta gama hada komai na breakfast sannan ta koma dakin ta tayi wanka ta shirya tana dawowa parlor taga duk basu fito karya wa ba a gurguje ta dan tsakuri dankalin sbd bata da appetite ta dau jakar ta zata fita kenan Ummiey ta fito tace "har kin shirya ne 'yar albarka"
Janan tace "eh Ummiey bana so in kara yin latti ne ga breakfast nan na hada muku se na dawo"
Ummiey tace naji kamar muryarki ta canza ko mura kike yi ne?
"Eh Ummiey ruwan daya dake ni jiya ne amma ga ruwan shayi nan zan tafi dashi asibiti"
"Torm Allah ya tsare a dawo lfya"
Da sauri ta fita karfe 7 daidai me napep ya sauke ta a bakin asibitin tana shiga Dr.Godwin ya shigo da motar shi yi tayi kamar bata ganshi ba tayi wuce warta yana kallo ta kauda kai parking lot ya nufa inda aka tanadarwa likitoci ya ajiye motar sannan ya fito yana sanye da riga me gajeren hannu na versace da black pencil trousers da bakin hightop shoes ba karamin kyau yayi ba da sauri ya dau brief case dinshi yabi bayan ta duk saurin ta seda ya kamota daidai wajen hawa steps yace "kina ta sauri gashi na kamoki kuma idan kika bari na riga ki shiga office yau ma latti zaki tafi gida" ya kashe mata ido daya
Zata yi magana kenan wani atishawa me karfi yazo mata harda guntun hawaye... ta bashi tausayi amma ya basar yace "karki sa mun mura kin san dai communicable disease ne koh?
Baki ta murguda mishi sanna tayi saurin wuce wa..
Murmushi yayi yace "ji dan bakin har ta iya murguda shi" da sauri da sauri ya hau steps din daga nesa ya hangota ta tsaye tana magana da wasu mutane guda biyu da alama kwatance take musu kara sauri yayi ya raba ta dayan gefen ya wuce batama lura dashi ba tana gama musu kwatance kawai ta hangi Dr.Godwin har ya shige salati tayi dan ta san dole se ya aikata abun da yace... jiki a salube ta bude kofar ta shiga kanta a kasa a hankali ta karasa wajen shi tace "Good morning"
Yace "se yanzu kika ganni da zaki gaishe ni? Torm hv a seat dan yau keda tafiya se 7pm kuma ko kin riqo ni bazan yi changing mind dina ba"
wani irin zaro ido tayi hade da toshe bakin ta ji take kamar ta fashe da kuka amma a ranta tace "wallahi bazan roke ka ba in ya gaji dole ka barni in tafi kuma nasan abin da zan maka" da wannan tunanin ta samu guri ta zauna... messenger na shigowa Dr.Godwin yace "yau patients 4 kawai zan duba sbd zan shiga theater room karfe 9......
yana cikin duba patient din farko Ruth da Jessica suka shigo tare da gaishe shi ko kallon su be yi ba bare ya amsa musu.. Janan ta kawo iya wuya wato ita ya raina su da suka zo latti be ce musu komai ba tana dagowa suka hada ido da shi kasa tayi da idon ta hade da hararan shi yanda ba zai gani bah..
ya duba mutane uku saura na karshe.. mata da miji ne suka shigo tare da yarinyar da bazata fi 5yrs ba tunda Janan taga yarinyar taji ta shiga ranta se kallon ta take yi a ranta tace "very cute baby" itama yarinyar tunda suka shigo take kallon Janan gani kawai suka yi ta kwace hannun ta tafi wajen Janan da gudu kallon juna sukayi ita da mijin ta sannan suka karasa wajen Dr.Godwin.. wajen zama ya nuna musu suka zauna sannan suka fara mishi bayani kamar haka "yarinyar mu kullum tana complain cewa kirjin ta yana ciwo jiya daya tashin mata se take nuna mana daidai setin zuciar ta mu kuma bamu san me hakan yake nufi ba shiyasa muka kawo ta nan"
Dr.Godwin ya kalli setin su Janan yaga se hira suke yi da yarinyar yana kallo Janan na barewa yarinyar chocolate da kanshi ya tashi yaje wajen su hannun shi a aljihu yace "cutie zo muje"
Kafada ta maqe alaman bazata ba ganin ya miqo hannu ze dauke ta ta kankame Janan tana fadin "Anty kin gan shi ze dauke ni kuma allura ze min ni dai bazani ba"
Maman ta ce ta zo tace "Baby Hanayya kizo ba allura ze miki ba"
"No Mummy nidai bazan je ba"
Baban ta ma yace "babu abinda ze miki kuma in kika je zan saya miki chocolate kinji"
Yarinyar tace "aa Daddy nidai ina jin tsoro kuma gashi Anty ma ta bani chocolate" ganin taki yarda ne yasa Janan tace "my baby baki so in zama frnd dinki ko?
Tace "pls Anty ina"
"Torm in dai kina so in zama ki tashi Doctor ya duba ki kuma bazai miki allura ba in kuma yayi miki zan rama miki"
''Yawwa my Anty promise! Ta miko mata hannu alamar su kulla alkawari Janan ta miqa mata suka kulla sannan Janan ta riqe mata hannu suka karasa gaban gadon
Sosai Dr.Godwin ya duba ta yace ma Janan "ki kai ta dakin x-ray a duba ta kuma kiyi sauri cuz yanzu 20mins to 9... suna zuwa dakin x-ray akwai mutane wajen wata nurse ta nufa tayi mata bayani tunda urgent ne yasa nurse din ta ba mutanen hakuri akayiwa Hanayya.... basufi minti 10 ba aka gama komai suka koma office din Dr.Godwin suna zuwa ya duba result din sanna ya ce musu "yarinyar ku tana fama da cardiovascular disease"
Mijin ne yayi saurin cewa "Doctor pls kayi mana bayani yanda zamu fahimta bamu san me kake nufi ba"
Tunanin yanda zasu dauki abun yayi sannan ya nunfasa yace.......
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/26, 6:42 AM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂も殰鉂b殰鉂� *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潱鈿溾潱
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
*_Dedicated this page to all the group members of_*
馃啈馃叞 *_SSIC LADIES_*
7鈨�6鈨�
Dr.Godwin yace "abun da nake nufi da 'yar ku tana fama da cardiovascular disease shine tana fama da ciwon zucia"
A tare iyayen suka hada baki wajen cewa "ciwon zucia kuma Doctor! Innalillahi wainna ilaihirraji'un" ita kanta Janan abun ya girgiza ta sbd bata taba ji ance karamin yaro ko yarinya na ciwon zucia...
Ganin sun shiga rudani yasa Dr.Godwin cewa "cool down ba wani abun tada hankali bane domin shi ciwon zucia yana cikin jerin ciwukan da ake inheriting dinshi watakila wani a cikin family'n ku yana fama da same sickness amma in dai zaku kiyaye rules nd regulations tor komai ze dawo normal but in dai baku kiyaye ba dole ne se an mata operation domin bugun zuciar ta ya daidaita...
Baban yace "tor Doctor mene ne rules nd regulations din?
Dr.Godwin yace "firstly! a guji duk abun da ze bata mata rai sannan duk abun da take so a bata in kuma babu se ayi mata dabara tunda yarinyace a bata wani abun kuma ku lura da duk abun da take ci zan muku prescribing drugs kuje pharmacy ku siya ku tabbatar kun bi ka'idan magungunan ina tabbatar muku da cewa ur baby will be healthy kar kuyi skipping bata drugs din ko da once ne sbd in kuka tsallake za a iya samun matsala.... a nan ya sake basu appointment nan da 1 month su dawo a sake duba ta.........
Bayan ya gama musu bayani suka mishi godia sannan suka fito domin tafiya har a lokacin Baby Hanayya tana tare da Janan har bakin mota ta raka su da kyar da wayau Hanayya ta yarda ta shiga mota bayan Janan ta hada ta da chocolates masu yawa.... se da sukayi exchanging digit da Maman Hanayya sannan Janan ta daga musu hannu har suka wuce....
Tana komawa office din taga baya zaune a kujerar shi se su Jessica da suke ta lbr kasakasa ita da Ruth waje itama ta samu ta zauna se ga Dr.Godwin ya fito daga inner room na cikin office din sanye da kayan shiga theater yana gyara hand gloves dinshi.. gaba dayan su duk suka miqe suna shirin binshi theater room da sauri ya dakatar dasu ta hanyar daga musu hannu kuma yayi haka ne sbd Janan dake fama da mura dan baya so ta wahala sannan baya so su Ruth su tayashi aiki domin rawan kansu yayi yawa.. ko waigowa be sake yi ba ya bar office din..
Janan taji dadin hakan jakarta ta bude ta dakko karamin flask dinta ta zuba ruwan tea tama su Jessica tayi suka ce basu sha a hankali take shan abunta su kuma su Ruth suna hira tana kammalawa ta dauki wayar ta ta fara buga game din _My Talking Tom_ a cikin hiran su Ruth ne taji sun sanyo maganan Dr.Godwin inda Jessica ke cewa "hmm Ruth kin san yanda nake son _young surgeon_ din nan? Ba karamin burge ni yake ba he is unique nd different ya iya daukan wanka kuma gashi so charming i luv his style kin san me yafi burge ni dashi? He is very neat ga class gashi baya san hayaniya he is jst d perfect Mr.right 4 me cuz he is damn handsome...
Wani irin harara Ruth ta watsa mata tace "hey! hey!! hey!! Hang it there Miss! Naji kina ta wani surutun banza ne ni yanda nake son shi kamar raina lokacin da aka ce min he is d must handsome guy a asibitin nan naji ya burge ni dana ji cewa he is d first _youngest general surgeon_ a hospital din nan tunda aka gina shi yasa na fara zuwa church ba dare ba rana in fara aiki as a nurse kuma tare dashi at last God answered my prayers na samu aiki...
The first day i set my eyes on him i knw d guy is damn hot kuma a lokacin naji am completely in love with him.. in kika lura bana barin kitson attachment dina ya wuce 2 weeks nake sake sabo nd always fixing my nails nd applying heavy makeups in banda abinki ai na fiki komai babu abinda ze yi dake kuma ni na fara son shi sbd haka u better take back ur words na cewa u love him badan ke frnd dita bace dana miki abunda bazaki manta dan kinyi kuskuren fada min cewa kina sonshi domin in dai am still alive bazan bari wata ta kwace mun shi ba cuz he is *Mine* mine alone!
Jessica ta tsaya kallon Ruth ta kasa cewa komai cuz she is totally speechless a ranta tana jinjina ma Ruth dan tasan in dai tana son abu to zata iya komai akan abun.... cike da sanyi gwiwa tace ma Ruth "kin san dai shi so ba kai kake sama kanka ba nd u won't knw when u r falling in se dai kawai kaga kana son mutum so don't try to force me akan abunda bazan iya ba kuma it might be possible ya soni cuz dukkan mu be ce yana son kowa a cikin mu ba we r all trying to win his heart!
Wani irin zafi maganan yayi ma Ruth ji take kamar ta rufe Jessica da duka amma se ta fara kwantar ma da kanta hankali ido ta rufe a ranta tana cewa "control Ruth control karkiyi misbehaving karki tsaya cacan baki kawai ki nuna mata action show her u can do it show her u can easily win his heart...hka tayi ta lallaba kanta a hankali ta bude ido ta kalli Jessica tace "gaskiyar ki ne yanzu mu bar wannan maganan kowa taje yayi trying luck din ta.........
Baki bude Janan ta tsaya kallon ikon Allah sbd taga haukan nasu yayi yawa no wonder in suka ganshi suke wani rawan jiki.. haushin su da taikaici ya kamata dan ta tsani taga mace tana ma namiji rawan kai ita bata ma ga wani abun burgewa a wajen Dr.Godwin ba ji tayi zaman office din ya gundure ta tana duba agogonta taga daya saura... jakarta ta dauka ta fita a office din ba tare data tankasu ba... daidai ta kusa karasawa kofar theater room Dr.Godwin ya fito yana share zufa da hanky.. kamar ance dago! kawai ya hango Janan ta kusa karasowa, jikin bango ya jingina yana jiranta... cikin tafiyar ta a hankali kanta a kasa ta zo zata gifta shi taji ance......
*_pls am sorry cuz zaku jini shiru na dan wani lokaci sbd fama da nake yi da ciwon ido amma In shaa Allah dana samu sauki zan cigaban muku da wannan littafin_*
*_ina barar addu'ar ku_*..... *_taku har kullum_*
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/5, 12:34 AM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潱馃拫: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂� *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潳鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿�
*_Alhamdulillah am getting better nw... thank u guys 4 d prayers Jazakumullah bi khayr_* 鉂も潱鉂b潳鉂b潳鉂も潱
_Dedicated this page to_
_Khairat Dabai_
_Little Eesher_
_Fateema M.Sabo_
_nd ol d grp members of_
_GYARA SHINE MACE_
7鈨�7鈨�
Ji tayi ance "ina zaki je?
A razane ta juyo dan ta tsorata sbd batayi tunani akwai mutum ba.. ganin Dr.Godwin ne yasa ta dan bata rai sannan tace "lokacin salla yayi"
"Ohhh kin fito bada izini na ba koh? Dama kin san akwai laifi akan ki yanzu kin karama kanki wani... saura kije ki dade...
Bata bashi amsa ba ta juya har ta fara tafiya se ta tuna da suit din shi baya ta dawo ta ciro a jakar ta cikin wata farar leda me kyau ta miqa mishi amma bata ce komai ba se ma kau da kanta gefe da tayi ganin bata da niyyar magana yasa shima ya yi kamar be ganta ba se ma ciro wayar shi daya yi ya fara dannawa irin shima yayi banza da ita.... hannun ta ne ya fara sagewa jin be amsa ledar ba yasa ta juyo tana kallon shi gani tayi yana danna waya kamar be san tana wajen ba gashi ya hada rai kamar be taba daria ba.. cike da jin haushi tace "gashi mana"
Yi yayi kamar be ji ba se da ta kara magana yace "ohh dama ashe kina da baki?miye wannan"
"Suit dinka ne na jiya da baka amsa ba na dawo maka dashi"
"Ko dai kika tafi dashi kika hana ni hala kina so ne in bar miki ban sani ba tor tunda se yanzu kike kawo wa ki riqe na bar miki"
Tace a ranta "lallai ma guy din nan yace wani abu ita me ma zatayi da suit din"...
Ce mishi tayi "ni bana so cuz ba abun da zanyi dashi"
Yace "ohh! Kina fada mun indirectly wannan is too cheap 4 u tor karki damu zan zabo miki wanda yafi kowanne tsada in kawo miki though ni bana sa kaya me arha se dai designers me arha a ciki shine 50k" ya wani kashe mata ido daya...
Zata yi magana yayi sauri katsata ta hanyar daura yatsa akan leban shi yace "shhhhh say no more ki tafi kiyi salla kuma in kika fi 20mins ni da ke ne" be jira ta sake magana ba ya wuce abun shi...
Haushi ya kamata kamar ta pashe tana tafe tana mita a ranta "shi wannan guy din ban san meke damun shi ba komai se ya wani tsaya yana iyayi ni ina ruwana da tsadan kayan shi ya cika miskilanci a haka waencan marasa aikin yin suke wani sonshi har suke so suyi fada" mitchwwwww taja tsaki... haka ta kai wajen da aka kebe nayi salla tayi alwala ta shiga seda tayi nafila tadan jira sannan liman ya tayar bayan an idar ta tsaya tayi adkhar sannan ta fito tana sa takalman ta taji muryan Zee tana cewa "yar halas yanzu muke maganan ki kwana biyu bamu hadu ba ikon Allah ashe rabon zamu hadu ne yasa da muka fito daga massalaci muka tsaya anan" cike da jin dadin ganin su Janan ta wani rungume su tace kawayen albarka wallahi kwana biyu nayi kewar ku kuna raina
Eesher tace "ku akwai latest fa dama nace se mun hadu duka zan fadi muku"
bayan masallacin suka koma suka zazzauna Eesher ta fito da wafer sticks da bounty chocolate ta miqa musu duk sun kosa ta fada masu ganin tayi shiru yasa Janan cewa "hohoho! haba kiyi magana mana kin tsaya yanga se kace kin gammu da hula"
Zee tayi carap tace "gane mun hanya wai makaho yaso tsegumi" daria suka yi sbd maganar ta basu daria..
Seda Aisha tayi gyaran murya kafin tace "kun san me yake faruwa ne" a tare suka hada baki wajen cewa "aa se kin fada"
"Bazan fada ba kuyi guessing"
"Mitchwwww kefa yar rainin seti ce in bazaki fada ba ki barshi baza a yi guessing din ba" cewar Zee
Aisha ta kyalkyale da daria sannan gace "tor iya tsiwa karki tsiwance ni ...dama Pharouk ne ya aiko magabatan shi har anyi maganan komai yanzu an tsaida rana nan da wata biyar kunga bayan saukan" mu da wata uku tunda yanzu saura 2months saukan
A tare suka wani rungume ta cike da jin dadi...
tace "ni ku sake ni kar ku karya ni wannan irin matsa da kuka mun"
Janan tace "aww daga abun arziki se ki fara korafi Allah dai ya kaimu musha biki abu namu" Zee ta karasa da fadin "wai akace maganin a kwabe mu" suka tafa
Aisha tace "kuma dai kuyi kuyi ku fito da mazajen aure musha biki"
Janan tace "tor rasa kunya kar kiga munyi shiru ki raina mu nima My Dr.Imran yazo ya nemi izini gun Abbiey kuma ya tabbatar mun very soon ze aiko in shaa Allah"
Zee tace "hehhehe kice tuwo na mai na za ayi gaskiya muna da sha bukunkuna"
Aisha tace "Allah ya nuna mana lokacin ke kuma Zee ya muke ciki yaushe ne naki bikin?
"Hmm kanku ake ji ni dallah karku dame ni" inji Zee
Janan da Aisha suka kalli juna suka tuntsire da daria dan sun san halin Zee kwatakwata bata kula samari.....
Sunyi hira sosai har suka tuno daya daga cikin babbar kawar su wato Fateema M.Sabo wacce tana Bauchi tana shan karatu suna waya sosai da ita...
Janan tace "aiko in shaa Allah zamuje mu gaida Innar M.Sabo kafin ta dawo huta maybe ma tana nan za ayi sauka da bikin ki Eesher tunda sun kusa hutu
Allah ya kaimana ran" suka amsa da Ameen...
Kamar ance Janan ta duba agogon ta aiko taga karfe daya da minti 45 ido ta zaro waje ganin taci mintuna sun kai 45 bata koma office ba tasan yau ba karamin wulakanci zata sha wajen Dr.Godwin ba... zunbur ta miqe dan gaba daya tama manta da warning din da yayi mata da sauri tayi ma su Zee sallama ta wuce suka ce "ki jira mu tafi tare mana
tace "aa karku damu sauri nake yi"
Gudu-gudu sauri sauri ta doshi office din seda tayi Addua'a ta shafa sannan ta bude kofar a hankali tana sa kafa cikin office din sukayi ido hudu da Dr.Godwin gaban ta ya bada darammm!!
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/18, 12:38 AM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰 *MATAR DOCTOR*鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鉂b殰鉂も殰鉂も殰鉂b潳鈿�
*Rukky Bae*馃槒馃槒馃槒
_Dedicated this page to all my primary and secondary sch frnds and classmates.._ _my unforgettable_馃槏
_One love to u guys_鉁�
7鈨�8鈨�
Suna hada ido da Dr.Godwin gaban ta ya bada darammmm!! Kasa motsawa tayi daga bakin kofar ganin haka yasa shi dauke ido a kanta ya cigaba da danna laptop..
Yar siririyar ajiyar zucia ta saki sannan ta taka a hankali ta koma wajen zaman ta.. Duk abun da suke yi idon su Jessica yana kai sedai basu kawo komai a ransu ba...
Haka suka zauna shiru babu me cewa komai..
2:20pm Se lokacin Janan ta tuno bata ci komai ba se ruwan shayi gashi har ya kare duk da ba wani yunwa take ji ba amma tana so ta dan ci wani abu ko zata ji dadin bakin ta.....
Da sauri ta bude jakarta ta ciro wafer sticks din da Eesher ta basu ta miqawa su Jessica suka ce basu ci.. Bude abunta tayi tana ci har ta gama sannan ta dakko bounty chocolate shima tana ci... Wani irin kara suka ji daga wajen da Dr.Godwin yake da sauri suka kalli direction din suka ga se buga kanshi yake yi akan table ga jini a gefen girar shi a rude duk suka miqe suka yo kanshi Jessica da Ruth sukayi saurin riqe shi a tsawace yace "take off ur filthy hands frm my body" da sauri suka dauke hannun su daga jikin shi suka ce "sorry sir"
Ganin haka yasa Janan komawa baya dan tsawan ya razanata...
Da hannu biyu ya riqe kanshi sbd juyin da yake yi ga jini yana diga a kayan shi damma kayan baki ne.. Gabaki daya duk ya canza fuskar shi tayi jajawur.. Janan na kallon shi taji ya bata tausayi a hankali ta nufi first aid box dake cikin office din ta dakko hydrogen, cotton wool da plaster cike da tsoro ta karaso bakin table din ta tsugunna...Tunanin ta tsaya yi can dai ta daure cikin rawar murya tace "ex...cuse me" jin muryar ta a kusa dashi yasa yayi saurin bude ido tare da sauke hannu daya yana kallon ta amma be ce komai ba ganin kayan aiki a hannun ta yasa ya fahimci inda ta dosa... A hankali ya cire hannun shi.. Cike da mamakin yanda be yi gardama ko tsawa ba Janan ta fara goge mishi jinin... Hydrogen ta zuba jikin auduga ta shafa a kan ciwon..
Arrrrrgggghhhh ya saki kara sbd zafi da sauri ya ture hannun ta ya kwanta akan table din dan yaji zafi sosai...
Reaction dinshi yaso ya bata daria amma ta daure ta sake matsowa da hydrogen din da sauri ya riqe mata hannu yana mata kallon karki sa akwai zafi ta fahimci kallon amma se ta kalli hannun daya riqe mata alaman ya saketa da sauri ya cire hannun shi yana kallon fuskarta...a haka ta samu ta karasa har ta sa mishi plaster din sannan ta tashi zata wuce da sauri yace "auush" komawa tayi ta durkusa dan bata san me yasa yace auush ba... Ganin ta tsugunna yasa yace "baki bani magani ba"
Tace "oops! Ina yake?
ya mika hannu daidai gefen bakin ta ya ciro karamin chocolate din daya maqale a wajen yasa a baki tare da lumshe ido sannan yace " wannan ne magani na''
Janan kasa magana tayi se ma tashi da tayi ta maida kayan cikin first aid box din dan alamarin shi ya fara ishen ta...
Su Jessica dake tsaye tuntuni suka kalli juna cike da mamakin abunda ya faru tsakanin Dr.Godwin da Janan... Wani tari Ruth tayi wanda ya tuna mai suna office din yace "zaku iya tafia se gobe as u can see am sick sannan kuma ba muda aiki daya rage ganin ku makes me fall sick again and again"
Jiki a sanyaye suka dau bags din su suka fita suna ta maganan su Janan a haka har suka samu abun hawa kowa ta wuce gidan su...
Bangaren Janan kuwa ganin ya ce su Jessica su tafi itama ta dauki jakar ta tana jiyowa taga yana rawan sanyi remote din AC ta dauka ta kashe ta dakko suit din shi da yaki amsa ta daura mishi a jiki.. A hankali ya fara rufe ido tace "can i go? Tunowa yayi da itama tana fama da mura kuma yaji dadin taimakon da tayi mishi duk da be nuna mata ba.. kai kawai ya daga mata alamar eh zata iya tafia...
Cike da murna ta fara tafia se taji yace "hey come"
Dawowa tayi tace "gani"
Yace "ki dau wayata ki kira mun Lawal yazo ya wuce dani gida I can't stay here all alone"
A ranta tace "ni ina nasan wani Lawal ma?
Kan table din ta duba bata ga wayan ba ta duba side drawers duk bata gani ba tace "nifa banga wayan ba"
Cikin muryan jin jiki yace "yana cikin aljihu na ki ciro"
Wani irin zare ido tayi tace "whattt! ni zan ciro daga aljihun ka??
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/20, 4:38 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂� *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿�
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
7鈨�9鈨�
Wani zare ido tayi tace "whattt! Ni zan ciro wayar daga aljihun ka??
Yace "yea ke zaki ciro"
Tace "no gaskiya bazan iya ba ka ciro da kanka ni kuma se na kira in fada mishi yazo ya dauke ka"
Yasan sarai bazata ciro ba shi kuma ya fara gajia da magana dan jin shi yake very weak
Jikin shi na karkarwa ya sa hannu a aljihun ya ciro hannun shi se rawa yake yi yana miqa mata wayar ta subuce a hannun shi da sauri Janan ta taro ta kafin ta karasa kai wa kasa..
Unlock button ta danna se taci karo da wayar an sa mata password
Kallon shi tayi cike da kosawa tace "what's d password"
Yace *"Momma*"
Tana sawa ya bude to her greatest surprise taga hoton ta a wallpaper na wayar.. Kasa motsi tayi sbd mamaki kwatakwata bata taba zaton zataga hoton ta a wayar shi ba ita bata ma san lokacin da ya dauke ta hoton ba da sauri ta shiga gallery dan ta goge hoton namma dai akwai password Momma ta fara sawa yaki buduwa ta rubuta Godwin nan ma yaki buduwa duk abun da ta zata a matsayin password ta sa hakura tayi sbd tayi trying passwords daban daban amma yaki yayi... Numb din Lawal tayi dialing tasa a hands free ringing daya ya dauka tare da fadin "hello liltle master"
Janan tace "ehmm... Ba shi bane nurse ce shi yace in kiraka kazo ka dauke shi cuz bazai iya driving ba"
Lawal yace "OK gani nan zuwa nan da 5mins"
Kwantawa yayi akan table ya riqe kan shi da hannu.. Har ta juya kamar zata wuce se taji yana fidda nishi da kyar da sauri ta karasa kusa da shi ta ce "meke damun ka?
Da kyar ya bude baki a hankali yace "kaina!kaina!!kaina ze tsage"
Gaba daya ta rasa me ya kamata tayi se can ta tuno da addua'ar da ake yi ma me ciwon kai a cikin ruwa
( _Suratul Fatiha kafa 7_))
(( _Ayatul kursiyyu kafa 7_))
((_Falaq, Nasi da Ikhlass kafa uku uku_))
_se ayi Bissimillah a shanye sannan a shafe fuska da ragowan.. Bi'iznillah za'a samu sauki daga ko wacce irin ciwon kai_......
Cup ta dauka dakko da ruwan gora ta zuba tayi mishi addua'an durkusawa tayi ta miqa mishi tace "take this"
kasa amsa yayi sbd jikin shi ba karamin rawa yake yi ba ganin bazai iya amsa ba yasa ta runtse ido tare da istigfari tace "open ur mouth"
Kamar karamin yaro ya bude baki tayi Bismillah sannan ta bashi seda ya kusa shanyewa sannan ta cire kofin daga bakin shi ta zuba a hannu hade da sake yin Bismillah ta runtse ido ta shafa mishi a fuska..
A hankali ya fara rufe ido tare da sauke nannauyan ajiyan zucia cikin dan kankanin lokaci bacci me nauyi ya dauke shi...
Waje ta samu ta zauna tana jiran Lawal ya zo ta wuce... Ta kai kusan 7mins sannan taji ana knocking kofa zuwa tayi ta bude wani ta gani suka gaisa sannan yace "nine Lawal nazo wajen little master ne" se a lokacin ta gane muryan shi tace "awww! come in yana bacci ne"
Tana gaba yana baya suka karaso cikin office din suna shiga Lawal yaga kanshi kan table yana bacci yana sauke nunfashi a hankali tare da ajiyar zucia...
Jakarta ta dauka tayi ma Lawal sallama sannan ta wuce.. Shi kuma ya tsaya jiran Dr.Godwin ya farka...
Bayan like 30mins ya farka yana bude ido yaji kanshi ya dena ciwo da sauri ya miqe sbd wani kuzari yake ji yana waigawa gefen shi yaga Lawal yace mishi "where is she?
Lawal yace "ta tafi"
Shiru yayi hade da dafe kanshi yace "Lawal let's go home I need to rest nd hv a shower".......
Lawal ya taimaka mishi suka fito suka rude kofan tare da wucewa...
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/26, 7:13 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰 *_MATAR DOCTOR_*鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂�
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
8鈨�0鈨�
*_Washe gari_*
Cikin nishadi da kuzari Dr.Godwin ya tashi tun da yake be taba jin dadin jikin shi irin yau ba.. Farin suit ya yasaka da farin sleeve se red neck tie da farin cover shoes ba karamin kyau yayi ba... Suman kanshi me yawa ya taje sannan ya dau brief case din shi ya fito har ya kai tsakiyan parlor Agnes ta fito da sauri daga kitchen ta tsugunna har kasa tace "good morning oga!
Kai kawai ya daga ba tare daya amsa ba Ya cigaba da tafiya tace "ehmmm oga u nvr chop ur breakfast is ready I don put them on d table"
Be kalle ta ba ya cigaba da tafiya har ya kai bakin kofa ya waigo yace "yau bazan yi breakfast ba ku cinye keda me gadi" be jira abun da zata ce ba ya wuce...
_6:50am_
Yana zuwa asibiti ya fito sanye da bakin glasses cikin takun shi na kasaita ya dinga wuce mutane nurses nata gaishe shi amma be amsa ba sedai yau fuskan shi na dauke da murmushi ga wani annuri dake fita daga fuskan...Yana shiga office din shi yaga babu wacce tazo a cikin su... Yasha ko su Jessica sun zo hakan be dame shi ba se rashin ganin Janan da wuri da beyi ba... Har aka fara shigo da files babu wacce tazo se can yaji knocking yace "yes"
Su Jessica ya gani duk daukan shi Janan ce wani gutun tsaki ya saki suna gaida shi ko kallon su be yi ba suka ce "hw is ur health sir?
Yi yayi kamar be ji su ba
Jiki a sanyaye suka zauna... Sunyi zaton ze musu abun da yake ma Janan in tazo latti ne sbd su samu shiga a wajen shi se suka ga yayi banza dasu.... Tunda suka zauna suke kallon shi sbd kyan da yayi kamar ance ya dago aiko ya kamasu suna kallon shi wani irin banzan kallo ya watsa musu wanda yasa sukayi saurin sauke kansu kasa.....
_7:15am_ ta yi knocking yace "come in" Janan ce ta bude kofan ta shigo as usual kanta a kasa bata dago ta kalle shi ba tace "good morning"
Be kulata ba jin yayi shiru yasa ta dago daidai nan ya sakar mata wani murmushi wanda ya kara fito da ainihin kyaun shi da sauri ta kauda kai shi kuma ya amsa da "morning"
Ta gaisa dasu Ruth sannan ta zauna su ko se faman hararanta suke yi bata ma san sunayi ba
7:30am patients suka fara shigowa can wani mutumi ya shigo dauke da matar shi yana zufa yace "Dr. Matata na bleeding pls Doctor ka taimaka min"
Seda ya cire glasses din dake idon shi yace "kaje kayi clearing bills dinka sannan zamu karbeta"
Hular kanshi ya cire yan firfita yace Doctor labour ne yazo mata da garda Dan Allah ka taimaka kar baby da matata su mutu"
Dr.Godwin yace "bana amsan patient se anyi clearing bills ka gane?
Kamar mahaukaci haka mutumin ya fita ya ajiye ta akan wani kujera dake wajen ... Da gudu yaje wajen biyan kudin nan fa aka fada mishi nawa ze biya mutuwar tsaye yayi sbd bashida kudin kuma be san inda ze samu ba... Komawa office din Dr.Godwin yayi yace "Dr. Bani da kudin amma zan biya half in yaso kafin a gama zan nemo sauran..
Dr.Godwin yace "if u r not ready u can go outta my office as u can see I hv lots of patients waiting 4 me"
Mutumin yace "Doctor ka taimaka min pls help me kaji tausayin matata"
Kamar ya watsa ma Dr.Godwin garwashi haka yaji maganar cikin tsawa yace "kar ka kara cewa in taima ke ka cuz ni bana taimako a rayuwata sannan kuma tausayi!! Bani da tausayi kuma bashida muhalli a waje na domin ban san mene ne tausayi ba sbd haka pay or leave kuma asibitin nan bana taimako bane koma na taimako ne to ni bana taimako"
Janan dake zaune daga gefe ganin yanda matar ke nishi ga jini duk ya bata kayan mijin yasa ta fashe da wani irin kuka da sauri ta taso taje gaban Dr.Godwin tayi kneel down tace "Dr.plsss ka karbeta wallahi in be biya kudin ba ayi deducting a salary dina"
A razane mutumin ya juyo yace "aa kar ki fadi haka bana so in sa kowa a cikin matsala"
Tace "karka damu in shaa Allah babu matsala"
Dr.Godwin yana kallon su ga Janan na zubda hawaye ji yayi zuciyar shi na daci tana bugawa da sauri amma baya jin ze iya amsan wannan patient din sbd in ya tuno wasu dalilai nashi
Yana cikin tunani yaji Janan ta riqe kasan wandon shi tana kuka me tsuma rai...
Gaba daya kanshi yayi zafi be san lokacin daya daka mata tsawa yace "stay out of this or else.....
Cikin kuka tace ''or else what?
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/28, 12:04 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂ゐ煍呪潱馃攨鉂ゐ煍呪潱馃攨鉂ゐ煍呪潱馃攨鉂ゐ煍呪潱馃攨鉂ゐ煍呪潱 *_MATAR DOCTOR_*馃攨鉂p煍呪潳馃攨鉂p煍呪潳馃攨鉂�
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
8鈨�1鈨�
Cikin kuka tace "or else what??
Shiru yayi yana kallon ta gabadaya bai ji dadin tsawan dayayi mata ba kuma batayi deserving haka daga wajen shi ba cuz shima jiya ta taimake shi amma bazai iya mata godia ba kuma baya jin ze iya karban patient din sbd abun da ya faru dashi wanda bazai taba mantawa ba har abada amma kuma yana ji a cikin ranshi ze iya karban patient sbd Janan amma bazai bari ta gane sbd ita zeyi hakan ba....
Gyaran murya yayi sannan yace "kina so kisa kanki cikin matsala baki san su ba basu sanki ba zaki daukan ma kanki bashi anyways ko sun gudu ke baki isa ki gudu ba sbd haka dole za a rubuta agreement kin yarda?
Da sauri tace "eh na yarda"
Paper da Biro ya dakko suka rubuta agreement din harda phone number da signature..
Dr.Godwin ya kara da cewa "duk abun da yaje ya dawo don't blame anybody blame ur self.....
Se lokacin ya kalli matar gani yayi kamar bata nunfashi a hankali ya tako yazo gaban mijin ya durkusa tare da daga hannun matar yabass! hannun ya dawo abun duba bugun zucia ya dakko ya gwadata nan yaga zuciarta na bugawa alaman tana da sauran rai cikin sauri yace ma Janan "ki shirya ta kema ki shirya ku biyoni dakin theatre.. Kai kuma kaje ka bada half payment din kace _'Surgeon G'_ ne ya aiko ka" be jira komai ba ya wuce don shiryawa.... Mutumin ya kalli Janan yace "Allah yayi miki albarka kuma na miki alkawari bazan taba disappointing dinki ba"
Jiki a sanyaye ya mike yana share hawayen dake kan fuskar shi a haka ya bar office din...
_2hrs later_
Dr.Godwin ya fito daga dakin theatre yana cire hand gloves ita kuma Janan da wata nurse suka turo matar zuwa dakin hutu... Tunda aka fito da matar Janan ke trying number'n mijin amma switched off.. Hankalinta ba karamin tashi yayi ba sbd any moment from now matar zata iya farkawa kuma ana bukatar abubuwa dayawa kamar su pads kayan sawar matan da kuma na babies da dai wasu abubuwan da bazaa rasa ba..
Tana cikin tunanin abun yi ne taji ance "me yasa kike tunani? Number'n shi yaki shiga ko?
Lokacin da nake fada miki u should stay out of this matter kinki ji gashi tun yanzu kin fara shiga tension kuma kin san yanzu dole a samu wanda ze zauna da ita ko kece zaki bar aikin ki ki zauna da ita cuz naga tausayin ki yayi yawa"
Shiru Janan tayi dan bata san me zata ce ba kanta a kasa tace "nagode da taimakon daka mata"
Dr.Godwin yace "taimako? Ba taimako bane wannan naga dama ne kawai cuz I don't hv d heart to help, I don't help anyone in my life kuma I don't want anyone to help me sbd komai nake so I will do it my self ko banyi da kaina ba I can use my money cuz I hv money kin gane?
"u r mistaken cuz money cannot buy everything!
Wani irin murmushi yayi me kama da na yake yace "money is life!!
Zata sake magana ya katseta da fadin "shhhhh ya isa haka.. Ya wuce abun shi......
Jiki a sanyaye ta koma cikin dakin da aka bar matar dan hutawa ta kira dayar nurse din suka kai ta dakin da akayi admitting dinta.. Har ta juya zata koma dan dakko babies din taji matar tana fadin "ruwa!ruwa!! a bani ruwa! a bani ruwa! Karku kashe ni ku maida min baby marainiya!
Salati Janan ta dinga yi sbd batayi zaton matar zata farka yanzu ba....
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/28, 8:40 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂も殰鉂b殰鉂� *MATAR DOCTOR*_鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿�
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
_Dedicated this page to my lovely sisters_
_Firdausi Zubairu_
_Maryam Zubairu_
_Fateemah Zubairu_
_Safiyya Zubairu_
_Asma'u Zubairu_
_I really love nd cherish u guys_馃槏馃槏馃槏馃槝馃槝馃槝
8鈨�2鈨�
Salati Janan ta dinga yi sbd batayi zaton matar zata farka yanzu ba.. Da sauri ta karasa gaban gadon ta zauna a gefe tana shafa kan matar a hankali tare da tofa mata adduo'i cikin kankanin lokaci bacci me nauyi ya dauke matar wani wawan ajiyar zucia Janan ta saki sannan ta tashi taje ta dakko yaran gashi ba a zo da gadon saka yara ba ko kaya babu a jikin su se zanin asibiti da aka rufe su dashi se kuka suke yi abun gwanin ban tausayi.. Wani empty gado ta daurasu wanda yake nesa kadan dana matar duk sun jigata sbd kukan da suka sha se faman tsotsan hannu suke yi cike da tausayi Janan ta bar dakin ta koma office din Dr.Godwin duk da tana cike da fargaba sbd matar zata iya farkawa kuma tana bukatar alluran bacci in ta farka se kuma alluran jijiya sbd rage mata yunwa.. Cikin nutsuwa ta bude kofar ko knocking batayi ba sbd tunanin daya cika mata zucia.. Kamshin turaren Dr.Godwin ne ya alamtar mata tana cikin office dinshi
Tana dagowa suka yi ido hudu dashi da sauri ta kauda kanta ita ta rasa dalilin dayasa bata iya hada ido dashi kuma yana mata kwarjini sosai..
Wajen zamanta ta koma ta dauki jakarta sbd tana zaton akwai wasu yan kudi a ciki kuma zasu ishe ta siyan ma yaran kaya.. Gefen table din Dr.Godwin ta tsaya amma ta kasa magana sbd bata san ta ina zata soma ba..
A hankali ya dago yana kallon ta se yaga ta bashi tausayi yau kadai har ta rame ta fita daga hayyacin ta kamar itace bata da lfya... Ji tayi a jikin ta yana kallon ta da sauri ta dago suka sake hada ido amma wannan karan bata dauke ido ba itama ta shagaltu da kallon shi seda taji alaman hawaye na kokarin sakkowa daga idonta cikin azama ta dauke idonta amma kafin nan har hawayen su zubo.. Farin hanky ya mika mata yace "ki share hawayen ki cuz ganin su yana daga min hankali"
Cike da mamakin kalman daya fito daga bakin shi ta karbin hanky din tana kallon shi.. Shi kanshi be san ya fadi hakan ba sedai har cikin zuciar shi hawayen ta yana damun shi kuma he mean what he said... Ganin taki magana yasa shi cewa "me ya faru ko kina son wani abu ne?
Kai ta daga amma bata ce komai ba
Yace " me kike so tor?
"Ehhmm.. Dama...dama ina so ne in dan fita zan siyo abu ne shine nake so ka bani izini pls don't say no cuz fitan is very very important plssss" ta hade hannayen ta waje daya..
Yayi niyyar ya hanata amma yanda take pleading ta kashe mishi jiki badan yaso ba yace "u can go"
Godia ta tsaya mishi ya daga mata hannu alamar baya so
Gudu gudu sauri sauri ta bar office din... A bakin gate din asibitin ta samu adaidaita kasuwa ta fadi mishi zata ba bata lokaci ya dauke ta.. Siyayya daidai gwargwado tayi wanda matar da yaran zasu bukata sannan ta dawo asibitin...
Dakin da aka kwantar da matar ta wuce tana zuwa ta tarar da yaran har sunyi bacci sbd wahala ga fuskar su duk jirwayen hawaye... Drawer'n gefen gadon ta ajiye kayan shayi da madaran yaran da ta siyo.. Pharmacy din dake cikin asibitin ta tafi ta karbo alluran bacci dana jijiya ta dawo tana shigowa dakin daidai nan yaran sun farka... Hannuta ta mika ta dauki daya ta bata ruwa da madara sannan ta dauki dayar itama ta bata a tare suka saki gyatsa ita kuma Janan tayi murmushin farin ciki..
Wata tsohuwa dake asibitin wanda Janan ke kira da _'Innata'_ ta roke ta akan tayi ma yaran wanka babu musu ta karbe su sbd tana son Janan...
Bayan minti 30 se gashi an shigo da yaran pess sun sha wanka kayan da Janan ta siyo musu me kalan pink nd white aka sa musu nan yara suka fito gwanin ban shaawa dari biyar ta ba Inna amma taki karba tace "haba 'yata sbd na miki abune zaki bani kudi? Ai kinfi karfin haka daga wajena"
Janan tace "aa Innata ba dan kinyi min abu bane kyauta ce na baki kuma dan Allah ka ki ki karba"
Badan taso ba ta karba hade da yima Janan godia
Janan tace "nice da godia Innata"
A haka tsohuwar ta bar dakin cike da farinciki... Janan na cikin yi musu wasa taji matar na fadin "La'ilahaillah Muhammadurrasulullah (SAW)"
Janan ta tashi taje wajen ta har ta gama bude ido tana shafa cikin ta tace "Baiwar Allah na haihu ne? Ina abun da na haifa ko ta mutu ne?
Janan tace "eh kin haihu kuma bata mutu ba"
"Tor ina take in ganta?
Janan ta koma wajen gadon ta dakko daya ta mika mata ta sake komawa ta dakko dayar cike da mamaki matar tace "wannan kuma fa?
Janan tace "duka yaranki ne"
Kina nufin 'yan biyu na haifa?
Janan tace "eh 'yan biyu ne kuma duka mata"
"Alhamdulillah ina Baban su yake?
Shiru Janan tayi seda matar ta sake tambayar ta sannan tace "yaje memo cikon kudin asibiti ya dawo"
Cike da tashin hankali matar ta fashe da kuka tana fadin "da kyar ze dawo ba zai taba dawowa ba"
Janan tace "me kika ce?
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [1/6, 7:50 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂� *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿�
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
_Dedicated this page to ol d grp members of_
_MATAN ALJANNAH_
_Thanks 4 ur support鉂も潱 especially Ummu Adnan_
8鈨�4鈨�
Maganar da Janan tayi yasa Dr.Godwin rufe laptop dinshi da karfi yana huci wanda shi kanshi be san yana yi ba lokaci daya idon shi ya kada yayi ja....
Imran daga bangaren shi yace "I love u so much my Angel"
Cikin shagwaba Janan tace "ni dai ban yarda ba I love u more"
Imran yace "aa Angel babu yanda zaayi sanki yafi nawa dan dai baki san yanda nake sonki bane shiyasa kike fadan haka"
"Naji kafi sona yaushe zaka zo tor? Kasan dai nayi missing dinka ko"
"Am so sorry my Angel kina raina aiki yayi yawa ne but in shaa Allah cikin week din nan zan zo in ga cute face dinki da murmushin ki me faranta raina kuma I missed u more"
Janan tace "shikenan my love se ka zo take care of ur self for me"
Seda Dr.Imran ya kara jadadda irin son da yake mata kafin sukayi sallama...
Rungeme wayan tayi a kirjin ta ta ce "I really love u Nurul-qalbee"
Karan rufe laptop din Dr.Godwin ne ya dawo da ita daga yanayin data fada a firgice ta dago suna hada ido taga idon yayi ja ga wani abu dake yawo a cikin kwayar idon shi wanda bata gane me hakan ke nufi ba se wani irin kallo yake binta dashi
Yana yin shi ya tsoratar da ita da sauri ta sunkuyar da kanta kasa...
Jessica da Ruth da suke zaune a gefe suka kalli juna Jessica ta matsa da kanta wajen kunnen Ruth tace "me kika fahimta daga kallon da Doctor yake ma Janan?
Ruth tace "yafi kama da yana jin haushi ko kuma yana kishi"
Jessica tace "noo baki gane ba kallon tsana yake mata.. Baki ga yanda yake kallon ta bane"
Ruth tace "kuma fa haka ne.. Indai kallon hatred yake mata we r safe"
Jessica zata sake magana suka ji Dr.Godwin yayi banging kofar ya fita
juyawa suka yi suna kallon Janan suka ga ko a jikin ta tana ma buga buga talking Tom ( _Hahahaha My Momma's best game_ 馃槀)
_15 mints later_
Dr.Godwin ya dawo cikin office din har yanzu be dawo daidai ba wasu files ya dauka da bakin glasses dinshi ya daura lab coat akan kayan shi yace "follow me"
Jessica da Ruth suka tashi jiki na rawa Janan ko game dinta ta cigaba da bugawa..
Har ya juya ze fara tafiya se yayi tunani in ya barta ita kadai zata iya cigaba da wayan kuma zatayi tunanin ko yana kishin ta ne ko yaji haushin wayar da tayi dazu da wani.. Yace "hey u! I don't need to repeat my self"
Ya juya yayi tafiyar shi su Jessica suka bishi kamar jela..
Tsaki kadan taja sannan ta bi bayan su
Daki daki suka bi suka duba marasa lfya daya bayan daya se wani shan kamshi Dr.Godwin yake yi.. Dakin da aka kwantar da matar nan suka shiga ya dudduba patients suna zuwa kan matar nan Dr.Godwin ya nufi kofa da niyyar fita da sauri Janan ta sha gaban shi tace "Doc.baka duba waccan patient din ba yanzu ta tashi"
Yace "and so what? Bazan iya dubata ba na gaji I need to rest"
Kwalla ne ya ciko idon kamar zata yi kuka cike da mamaki Dr.Godwin ke kallon ta a ranshi yace _"ohh my God! Wannan ta cika shagwaba abun kuka baya mata wuya maybe yanzu in na ki duba patient din nan ta zauna tayi ta kuka dan naga alaman tausayin ta yayi yawa_"
Gadon matar ya nufa yafara duddubata nan yaga komai yayi operation din da aka mata was perfectly OK da alama zeyi saurin warkewa dan bata da kan jiki...
Matar tace "Doctor kishi nakeji zan sha ruwa"
Yace "no bazaki sha ruwa ba yanzu se kin kwana biyu bayan kin fidda iska shine zaki iya fara shan ruwan lipton da fruits da dai abu me ruwa ruwa"
Kallon Janan yayi yace "akwai alluran da za ayi mata na jijiya sbd haka ke se kiyi mata cuz nu bazan iya ba"
Hanyar kofa ya nufa gab da ze fita mijin matar ya shigo rike da kaya niki niki dukkan su suka maida kallon su kan shi suna mamakin dawowar shi a wannan lokaci
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [1/1, 11:07 AM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰 *_MATAR DOCTOR_*鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
_Dedicated this page to my lovely sis who is more than a frnd to me_鉂�
_Hauwa Slim Small_鉂も潱
8鈨�3鈨�
Janan tace "me kika ce"
Kasa maimaitawa matar tayi sbd kukan daya ci karfin ta.. Kallon ta kawai Janan take cike da mamaki...
Ita gaba daya ma ta rasa me zatayi can dai ta nisa ta fara lallashin matar kamar haka "haba baiwar Allah be kamata ki zauna kina kuka ba godia ya kamata kiyi ma Allah daya sauke ki lfya har ga yaran ki biyu kuma a cikin yanayin nan be kamata kina kuka ba sbd baki gama samun sauki ba.. Kamata yayi ace kina bacci yanzu"
Matar tace cikin kuka hawaye wani na bin wani "hmm Nurse bazaki gane abun da nake fada ba ni na san se dai wani iko na Allah mijina ze dawo dan bashi da kudi sannan be san inda ze samo ba" ta sake fashewa da wani matsanancin kuka
Ganin haka yasa Janan mikewa ta karasa kusa da ita ta dakko alluran bacci zatayi mata da sauri matar ta dakatar da ita da fadin "Nurse ba se kinyi min allura ba ki barni inyi kukan ko zan ji dadi a cikin raina"
Janan tace "kiyi hakuri ki sani ke musulmace kuma duk abun da ke faruwa daku muqaddari ne daga Allah kuma jarabawa ce sbd haka ki cire damuwa a cikin ranki ki bada goyon baya wajen neman lfyar ki" da kyar da ban baki Janan ta samu tayi mata allura cikin dan lokaci kadan bacci ya dauke ta sassanyar ajiyar zucia Janan ta saki sannan ta dauki yaran daya bayan daya ta maida su gadon data dakko su se bacci suke yi ta fita harta fara tafiya se can wani tunani yazo mata _"anya zan ba yaran nan su kadai bayan Maman su tana bacci kuma babu wacce zata kula dasu yanda satan jarirai ya zama ruwan dare_ .. _Dayawa daga cikin mutane suka zama babu tsoron Allah a cikin ransu_! _kai!! gaskiya bazai yiwu ba gwara in kaisu dakin kula da jarirai in ba nanny daya ta kulan min dasu tunda se bayan awa biyu Maman su zata farka ni kuma ba lallai bane in dawo ta farka maybe akwai aikin da zan ma Doctor_.... Da wannan shawaran ta koma ta dakko su tare da feeder dinsu in case ko zasu farka su nemi abinci..
Bata sha wahala ba wajen samun nanny din dazata kula dasu kafin ta dawo zuwa anjima..
Office din Dr.Godwin ta koma.. Knocking tayi aka bata izini ta shiga bata kalli kowa ba taje ta zauna su Jessica se hararanta suke ita batama san sunayi ba se a lokacin ta ciro wayar ta a jaka nan taga har 5 missed calls daga Dr.Imran din ta murmushi kadan ta sake tanaso ta kirashi amma tasan Dr.Godwin bazai barta ta fita ba tana cikin tunani wayar ta fara ringing cikin wakan _Ashquii_ kallon gefen Dr.Godwin tayi taga se faman danna laptop yake yi.. Tana so ta dauka amma bata so ta kasa sakewa.. maganar shi ce ta katse da fadin "pick up d call karan yana damu na"
Tace "zan iya fita na amsa sbd kar na dame ku?
Yace "no ki amsa a nan as u can see babu wanda keda time din jin abun da zaki ce cuz we r all busy"
Kamar jira take da sauri ta dauka tare da fadin "Amincin Allah ya tabbata a gareka Nurul-qalbee"
"Kema Aminci da Rahmar Allah su tabbata a gareki my pretty Angel" ya fada daga daya bangaren...
Nan fa suka fara zuba soyayya gaba daya Janan ta manta a inda take da waenda take tare dasu kalaman soyayya kawai take zuba ma Imran..
Tunda ta fara waya Dr.Godwin ya kasa cigaba da aikin shi sedai kawai ya kafe screen din laptop da ido ji yayi zuciar shi na zafi tana bugawa da sauri da sauri... Mamakin kanshi yake yi a ranshi yace _"what d hell is wrong with me_? _meyasa nake damuwa da yarinyar nan_? _meyasa nake jin wani babban alamari a kanta_?
Shi kanshi ya rasa amsan wadannan tambayoyin can wata zuciar tace _"ko dai kana son ta ne_?
A hankali ya furta "no! Bazai yiwu ba no!
Wata magana Janan ta furta cikin shagwaba wanda yasa Dr.Godwin rudewa tare da da rufe laptop din da karfi yana huci wanda shi kanshi be san yana yi ba lokaci daya idon shi ya kasa yayi ja.....
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [January-10-2017 10:09 AM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂� *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿�
_Na sadaukar da wannan page din ga duk mai suna Rukayya_馃槣 _I love y'all_鉂�
8鈨�5鈨�
Mijin matar ne ya shigo rike da kaya niki niki dukkan su suka maida kallon su kan shi suna mamakin dawowar shi a wannan lokacin..
Kallon shi Dr.Godwin yayi sannan ya fita abun shi..
Wajen matar shi ya nufa cikin sauri ya rungume ta yama manta da cewa an mata operation..
"Alhamdulillah! Allah nagode maka! Allah nagode maka"
Cikin farin ciki ya mike ya nufi wajen Janan yace "nagode da haliccin da kika mun kuma nasan babu abun da zan iya biyan ki dashi.. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi ya biya miki dukkan bukatun ki na alkhairi ya baki miji na nagari"
"Ameen" Janan ta amsa..
Yace ina "Doctor yake ba yanzu na ganshi ba"
"Eh yanzu ya fita maybe ya koma office ne"
Gefen gadon ta koma ta saka hand gloves sannan ta dau allura...
Dayan side na gadon ya zauna yana kallon matar shi nan yaga tana hawaye cikin kidimewa yace "Rahma me ya faru kike kuka?
Hannun shi ta kamo tana shashshekan kuka tace "a ina ka samu kudi? Waya baka? Allah yasa ba bashi ka ciyo ba.. Na dauka bazaka dawo ba har ina tunanin ko ka tafi kenan Nurse nata kiran wayan ka a kashe nace mata bazaka taba dawowa ba.. Ka fada min yanda aka yi ka samu kudi"
Ka sani in dai haram ne kada ka ciyar damu dashi ko kayi mana wani abu dashi domin Manzo Allah (SAW) ya bamu lbrn wani mutumi a cikin hadisin shi inda yake cewa _"wani matafiyi ne ya daga hannu yana cewa Ya Ubangiji_! _Ya Ubangiji_! _Amma abin cin shi na haram ne kuma abin shanshi na haram ne sannan tufafin shi na haram ne kuma da haram aka ciyar dashi tun yana yaro tor taya Allah ze amsa mishi"_
"Dan Allah kar ka aikata abun da kasan Allah ya haramta"...
Rungumeta yayi yace " madalla da mace irin ki.. Sunan ki ya dace dake domin ke Rahmace a gare ni .. Allah yayi miki albarka"..
"Tor ai har yanzu baka fada min inda ka samu kudin ba"
"Zan fada miki amma ina abun da kika haifa me aka samu?
"yan biyu ne duka mata kuma Nurse zata nuna maka su amma kafin nan ka fada min inda akayi ka samu kudin"
Sujjada yayi tare da daga hannu sama yayi ma Allah godia.. Gefen gadon ya sake komawa ya zauna ya ce "bayan fitana daga asibitin nan naje gidan Kawu Halliru na fada mishi halin da ake ciki amma kirikiri yace shi ba yada kudi bare ya bani na tashi zan tafi kenan sega danshi Sageeru ya je yana tambayan shi wai pocket money dinshi ya kare a take ya ciro 20k ya bashi ko nagode be ceba ya wuce.. Wai dan wulakancin Kawu se yake ce min "kasan yara in suka tambaya abu ba'a basu ba zasu iya shiga wani hali bance mai komai ba na fito... Gaba daya na rasa inda zan samo kudin har na fara tunanin in saida kayan sawan mu, ina cikin tafiya zan karasa gida naji horn daga bayana amma ban juya ba sbd tunani yayi min yawa
Kamar daga sama naji ana kiran sunana da sauri na juya Ina waigewaige nan naga Muhammad pry sch frnd dina ya fito daga mota.. cikin mamakin yanda akayi ya gane ni na juyo muka gaisa yake tambayana iyali nace suna lfya.. Kallona yayi yace da alama wani abu yana damun na.. Shiru nayi ya dafa ni yace kar in boye mishi komai nan na fada mishi kina asibiti an shiga dake theatre room zaki haihu ana bukatan kudi.. Be tambayeni nawa bane yace in shigo mota muje... Wani super market muka je ya siyo min waenan kayan dana kawo miki.. Har bakin gate din asibitin nan ya ajiye ni sannan ya bude brief case dinshi ya ciro 100k wai inyi manaji sbd babu kudi dayawa a hannun shi kuma in ina bukatar wani abu in kira shi...
Kinji yanda akayi na samu kudin.. seda na shigo asibitin sannan naga waya ta babu chargy"
Hamdala tayi tare da kara gode ma Allah sannan tayi ma Muhammad addua'a.. Amma bata ce komai ba akan Kawu..
Janan ce ta katse su da fadin "bari ayi alluran sbd ki samu bacci" bata jira komai ba ta mata.. Mituna kadan bacci ya dauke ta.. Mutumin da Janan suka fito yana ta mata godia.. kudi ya dakko ya bata wa na abubuwan data siya amma taki karba sbd ita duk sun bata tausayi kuma sun fita bukata sannan ita Dan Allah tayi musu badan su biyata ba..
Seda yaje yaga yaran shi yayi musu huduba da addua'a sannan suka tafi Office din Dr.Godwin yayi mishi godia ya fita ita kuma Janan ta zauna har time din tashi yayi Dr Godwin bace komai ba ta dau jakarta ta fita be hana ta ba....
鉂も潱鉂b潱鉂b潳鉂b潱
_ina so inyi anfani da wannan daman wajen ba dukkanin masoya na hakuri na rashin jina kwana biyu wannan ya faru ne sakamakon rashin samun lokacin da banyi_ _Makaranta yasha kaina_ _amma in shaa Allah zaku dinga jina a duk sanda na samu chance_
_ina sanku fiye da yanda kuke so na_馃槝馃槝馃槏
_Pls ku sani cikin addua'an ku_
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [1/29, 11:58 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰 *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潳鈿溾潱鈿�
_Wannan page din na sadukar dashi ga dukkan masoya na ina son ku fiye da tunanin ku_馃槝馃槏馃槏
*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
8鈨�6鈨�
_2 days later_
Yau ya kama Friday bayan Janan ta dawo daga asibiti Dr.Imran ya kirata yake sanar da ita ranan Lahadi magabatan shi zasu zo ayi maganan aure sbd haka ta fada ma su Ummiey... Cike da mamaki da jin kunya tace "Nurul-qalbee Allah ina jin kunya bazan iya fada mu su ba"
"Haba Angel wa kike so ya fada mu su tor?
"Ka fada ma Big Bro ko ka fada ma Bro Saleem plsss"
"Tor shikenan tunda haka kike so in mun gama waya zan kira Khaleel din in fada mishi"
Hira sosai suka yi kafin yayi hanging call din sannan ya kira Khaleel sun gaisa sosai tare da barkwanci irin na abokai nan yake shaida masa abunda ya fada ma Janan..
Farincin ciki sosai yayi da Janan zata samu miji kaman Imran...
Yana dawowa gida ya sanar da Ummiey ita kuma ta fada wa Abbiey....
A ranan Abbiey ya kira ya fada ma dangin shi na Makarfi sannan ya fada ma yan uwan Ummiey dake Gombe kowa se fatan alkhairi da sa albarka yake...
_Sunday_
Tun asuba Ummiey da dangi suke aikin tarban baki sosai suka gyara gidan se kamshin turaren wuta yake hade da kamshin girke girke kala kala...
Janan na tashi tayi wanka ta dau hijab da jakanta tayi ma Ummiey Sallama ta tafi gidan su Zee sbd bazata iya zama a gidan ba..
Karfe 2 daidai Baban Imran da yan uwa da abokanan arziqi suka zo gidan su Janan.. A parlor'n baki aka musu mausaki... Bayan adduo'i da gaisuwa suka gabatar da abunda ya kawo su aka tattauna suka tsaida lokacin aure nan da watanni shida masu zuwa suka bada komai da ake bukata harda sadaki aka rufe taro da addua'a suka ci suka sha kowa ya tafi yana san barka da yaba hali irin ta zuri'ar su Janan
Su kansu yan gidan su Janan din sun yaba da kokari tare da halin dattako irin na zuri'ar su Imran..
Se yamma Janan ta dawo gida cike da jin kunya.. Tana shigo yan uwa suka fara mata barka da zuwa suna tayata farin ciki se fadi suke "Allah ya sa Albarka Amaryar wata 6 masu zuwa"
Da gudu ta wuce dakin ta harda sa key ta zauna a tsakiyan gado tana maida nunfashi amma can kasar zuciar ta wani farin ciki ne mara misaltuwa....
Sallan Magrib tayi bata tashi daga kan sallayar ba ta cigaba da Dhikiri tana jira a kira sallan Isha'i ta gabatar...
Ummiey ce ta shigo dauke da food flask da plate a hunnun ta ta ajiye mata a kan stool na dakin tace "ga abincin ki na san yau bazaki sake fitowa ba sbd kunya karki mata ki kwanta da wuri gobe Monday karki makara...seda safe"
tana gama fadar haka ta juya ta bar dakin...
Janan na idar da sallah ta ci abincin ta sannan ta wuce bayi tayi wanka tasa kayan bacci tana hawa gado wayarta ta fara ringing murmushi tayi amma ji take kamar kar ta dauka sbd shi kanshi Imran din yau wani irin kunyar shi take ji da kyar dai ta dage ta daga tare da sallama cikin siririyar muryarta... Cike da zumudi da farin ciki Imran ya amsa tare da fadin "My Angel, my Amarya ykk? Ya gida? Ya komai da kowa? Ya aiki? Ya...
Janan cikin daria tace "ya..ya din ya isa haka mana yau gaisuwar naga har wani sabon ta ta akayi tor komai da kowa lfya lau Alhamdulillah"
Imran yace "torh Mata's nayi shiru haka amma gaskiya yau ina ciki farin ciki mara misaltuwa"
"Ohhh har na zama Matar taka kenan?
"ai ni gani nake tamkar kin zama mallaki na har na kosa lokacin yazo a kawo min ke daki na.. Ranan ban san wani irin farin ciki zanyi ba"
"Hmmm Nurul-qalbee kenan inda rai da lfya wata 8 kamar gobe ne ai"
Cikin sauri ya katse ta da fadin "a haba Malama ki dena kara min lokaci wata 6 ne ni inda so samu ne a maida shi wata 3 bari inje in samu Daddy in fada mishi gaskiya a matso da bikin ko in ce ke kika ce a dawo dashi wata 3"
Cikin zaro ido tace "haba Nurul-qalbee yaushe na fadi haka pls karka fada kafin ace bani da kunya"
"Tor naji na daina amma duk sanda kika kara cewa wata 8 tor sena fada kin ce a dawo dashi wata 3"
Seda dare yadan fara sannan yayi musu addua'a suka shafa...
Yace "ki kwanta se kinyi bacci zan kashe"
Batayi musu ba ta kwanta seda yaji alaman numfashin ta na sauka a hankali sannan yace "ki kwana lfya Angel Allah ya kare min ke daga sharrin shedan"
Bata amsa ba sbd baccin ta yayi nisa....
0 comments:
Post a Comment