_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 1*
Wasu yara ne ke wasa su uku,,, yaran bazasu wuce shekara goma sha uku ba zuwa sha hud'u .'Dayar ce mai suna Fatima ta dubi 'yan uwan wasanta Maryam da Fadila,,, tace "Maryam ya kamata muje gida yanzu fa,, mun dad'e sosai muna wasa gashi rana ta fara fitowa ".Fadila tayi charab ta chafke maganar tana hararar Fatima,, sannan tace "ke idan kin gaji da yin wasa ne mu bamu gaji ba,, saboda haka ga hanya nan ki wuce zuwa gida babu wanda ya tareki ".Fatima ta dubi Fadila duba na rashin son fad'a,, tace "haba Fadila dad'ina dake akwai saurin fushi,, ni dama wasa kawai nakeyi muku na fad'i haka ne saboda kada a nememu arasa a gida "."To wa ne aiki ne zamuyi idan muka koma gida,, nidai gaskiya ban gaji da yin wasa ba ".Cewar Fadila cikeda rashin son maganar.
Sai asannan ne Maryam ta dubi Fadila tace "ya isa Fadila abar maganar,, kada abin ya zamar muku fad'a a tsakaninku muji kunya. Amma ai gaskiya Fatima ta ke fad'a ba k'arya ba ".Fatima tace "k'yaleta Maryam ai ya riga ya wuce adaina tunawa "."To shikenan babu komai ai ".Cewar Maryam dayake ita yarinya ce nutsattsiya mara son magana sosai,, sunyi shiru dukansu na tsawon lokaci,,, can dai Fadila ta katse musu shurun tace "ku zo mu fara 'yar chahu muna gamawa muyi gida ko,, amma nice ta farko ".Fatima da Maryam suka gyara zamansu domin suji dad'in wasar,, Fatima tace "ni ce ta biyu "."Ni kuma ta uku ".Inji Maryam cikeda natsuwa da kwanciyar hankali.
Suna tsakar wasarsu cikeda matuk'ar jin dad'i da nishad'i sosai,,,daga ganin yadda sukeyin wasar suna cikin walwala da farin ciki. Sun jima sosai suna wasa can dai suna batun tashi gidajensu,,,,saiga Iya Gwamma tazo wucewa zuwa gidanta. Ta zo zata wuce ne sai kuma ta dawo baya wurinsu Maryam,,, suna ganinta suka durk'usa su uku suna cewa "Iya ina kwana,, ya gida?.Lafiya k'alau 'yan uku masu kamada juna,, kuma 'yan matan gobe mi kukeyi anan ne? ".
Suka had'a baki wurin cewa "wasa mukeyi Iya Gwamma,, mi zamuyi miki Iyarmune ko wani abu kikeso mu siyo miki ne?".Iya Gwamma ta tsura musu idanu na wani lokaci tana kallonsu,, irin kallon na k'urilla da bai dace ba. Baki da hanci ta saki tana musu kallon kwad'ayi,,, da k'urilla nason cimma wani buri nata. Can dai da k'yar ta daure ta b'oye damuwarta da kwad'ayinta,,tace "muje gidana in baku kud'i ku siyomin biredi da madara shagon Mande ".
Fadila tayi saurin cewa "to Iya su Fatima ku tashi muje gidan Iya mu amshi kud'i,, mu siyo mata biredi da madara ".Maryam da Fatima jikinsu duk yayi mugun sanyi tsoro da fargaba ya bayyana a cikin zuk'atansu,, su kansu basu so zuwa ba amma babu yadda suka iya. Kamar suce basu zuwa ba amma ba zasu iya kallon tsabar idon Iya Gwamma ba,, suce ba zasu iya ba saboda ko banza tayi jikoki dasu. Can dai Fatima ta tattaro dauriya tace "to Fadila, Maryam tashi muje mana kinyi shiru lafiya dai? ".Maryam itama ta mik'e tsaye tace "Lafiya k'alau Fatima ".Tana kakkab'e jikinta da yayi k'asa saboda wasa,, su ma su Fatima suka kakkab'e jikinsu,, Iya Gwamma ta dubesu tace "ku wuce muje zuwa gidan na gaji da tsayuwa ".
Suka ce "to Iya ".Iya Gwamma ta sasu agaba suna tafiya,, ita kuma ta tsaya abayansu tana k'are musu kallon k'urilla tasa lasar baki da fitar da halshe,,, su Maryam suna tafiya suna fira cikeda matuk'ar jin tsoro da fargaba akan abinda kan iya faruwa dasu. Saboda maganar gaskiya da sunsan Iya Gwamma ce zata biyo ta inda suke,,, da tuni sun cikama bujensu ko zanensu iska. Domin Iya Gwamma ta shahara wurin maita da kuma sata a cikin unguwarsu,,, babu wanda baisan da zamanta ba sannan babu inda sunanta baije ba akan ita *MAYYA CE*.
**********************
*****Acan gidansu Maryam kuwa Mama Sa'ima ce zaune da yayan Maryam mai suna Mubarak,,,, suna firarsu ta tsakanin uwa da d'a. Yaya Mubarak ne ya dubi Mama Sa'ima yace "Mama tun d'azu muna fira banga giftawar yarinyar nan Maryam ba,, wai ina taje ne kuma? ".
"Hmmm Mubarak sun fita tun d'azu itada su Fatima,, gashi yanxu har azahar tayi basu dawo ba ".Inji Mama Sa'ima fuskarta tana bayyanar da damuwa.
Saida gaban Mubarak ya buga da k'arfi,, ya bada rasssss! Sannan ya tattaro natsuwarsa wuri d'aya,,, domin kada ya tashi hankalin mahaifiyarsa. Ya dubeta duba na natsuwa ya tausasa halshensa,, yace "Mama ki kwantar da hankalinki Insha Allahu suna waje suna wasa,,, kuma yanzu nan zanje ince su dawo gida hakanan. Ai wasan ya isa yau sai kuma gobe ".
"Da kako k'yauta Mubarak kayi sauri kaje kace ta dawo gida hakanan,,, saboda ina tsoron kada Alhaji ya dawo bai sameta gida ba. Nasan ni zai azama fad'a ni kuma ban aiketa ba wurin yin wasan banza ba ".Cewar Mama Sa'ima cikeda damuwa da tsoro..
Mubarak ya dubi uwar yace "ki daina damuwa Mama yanzu nan zan turo k'eyarsu,, insha Allahu Alhaji ma bazai san ta fita ba ".
Uwar tace "to Allah yasa tun can ka fara dukan shegiya domin Maryam agaskiya batajin magana,, kullum ina gaya mata idan ta fita wasa ta daina kaiwa azahar bata dawo gida ba. Amma tayi kunnen uwar shaggu da maganata saboda tana son babanku ya sani gaba ya cimin mutunci,,, wallahi yau kam sai jikinta ya gaya mata zata yabama aya zak'inta ".Ta fad'a cike da jin haushin Maryam.
Mubarak ya mik'e tsaye sannan ya dubi mahaifiyarsa,, cikeda lallashi yace "kiyi hak'uri Mama Maryam bazata koma dad'ewa awaje ba,,, yanzu zanje in korosu su dawo gida wlh amma dan Allah kada ki duketa Mamanmu ".
"Naji bazan duketa ba ,,, saboda kai ka haifarmin 'yar ko Mubarak ".Inji Mama Sa'ima cikeda sababi da masifa.
Mubarak ya sassauta murya yace "ba haka bane Mamanmu,, ganin nayi bugu baya magani sai dai addu'a da nasiha Allah ubangiji ya shirya mana zuri'armu. Kuma ya huci zuciyarki yake mahaifiyata,, kiyita hak'uri damu wata rana sai labari ".
Jikin Mama Sa'ima yayi matuk'ar sanyi akan maganar Mubarak,,hak'ik'a tasan duk abinda ya fad'a gaskiya ne babu k'arya acikin maganarsa. Kuma tasan Mubarak yaro ne mai natsuwa da iya kalamai masu dad'i da kwantar da hankali ga mai sauraronsa,, sannan yanada kaifin tunani da hangen nesa,, Mama Sa'ima ta numfasa tace "na hak'ura Mubarak Allah ubangiji yayi muku albarka,,, sannan ya shirya mini ku shirin addinin musulunci ".
"Amin Mamanmu,, toni zan wuce yanzu ".Cewar Mubarak.
Maman tace "Allah ya kiyaye hanya Mubarak yasa kayi saurin ganosu ".
Mubarak yace "Amin ".
Yaja k'ofar gidan ya bud'e tareda da fita,,, domin ya koro su Maryam su dawo gida hakanan..
**********************
Su Maryam suna tafiya suna fira har sukazo bakin k'ofar gidan Iya Gwamma,,, sukaja suka tsaya suna jiran harta iso dayake sun fi ta saurin yin tafiya kunsan abu da tsohuwa. Suka zauna suna hutawa can saiga Iya Gwamma ta iso tasa makulli ta bud'e musu k'ofar gidan,,, ta umurcesu dasu shiga cikin gidan dayake yara ne sosai babu wanda yasan ciwon kansa. Suka kutsa kai zuwa cikin gidan tareda Iya Gwamma,, suna shiga babu kowa cikin gidan sai komattsai da raggad'ud'an Iya Gwamma. Babu abinda ke tashi cikin gidan sai k'amshi soyen nama da k'arnin jini,,, dayake su Maryam yara ne babu abinda suka fahimta gameda Iya Gwamma .
Iya Gwamma ta tura ganbun d'akinta ta shiga cikin d'akin,,, ta d'an jima sosai sannan ta fito da kud'i ga hannunta d'ari uku da hamshin. Taba Fatima kud'in tana shafar hannun Fatima da wayo da wayo,,, tace "gashi ku siyomin biredi na d'ari da hamshin madara ta naira d'ari,,, inada sugar da bonbita naira d'arin da ya rage ku d'auka na baku "..
Fatima tace "mun gode Iya amma da kinbar kud'inki,,, ki k'ara ki sayi wani abu ".
Iya Gwamma tazo wurin kan Maryam tana shafa cikin dabararsu ta mayyu,, tace "Ayya 'yar nan k'yautace na baku kuma ba'a maida hannun k'yauta baya ".
"dallah rufe mana baki! Munce kibar kud'inki amma kinzo kinata damunmu da surutunki na banza,, bamu son kud'inki ko ana amsar k'yauta dole ne "Inji Fadila cikeda fitsara da tsiwa.
Iya Gwamma ta dubeta cike da tsananin mamakin rashin tsoronta,, ta bugi Fadila da wasa tace "amma yarinyar nan bakida kunya,, kinsan koni wa cece nayi fa jikanya dake yarinya".
Fadila itama ta dunk'ule hannunta cikeda rashin kunya,,, tayima Iya Gwamma mugun bugu a bayanta. Saida Iya Gwamma ta zabura da k'arfi! Tana mamakin k'arfin hali da rashin tsoro irin na Fadila. Fadila ta harari Iya tace "ina ruwana da kin yi jikanya dani tsohuwa,,, sannan sanin koke wa cece bayada wani amfani gareni! ".Tana murgud'a bakinta.
Hak'ik'a Fatima da Maryam sunyi matuk'ar jin tsoro da firgita! Akan abinda Fadila tayima Iya Gwamma,,, babu abinda jikinsu keyi sai makarkatar tsoro da fargaba. Can dai cikeda masifar tsoro suka had'a baki wurin cewa "dan Allah Iya kiyi hak'uri wallahi haka Fadila take da tsiwa ".
Iya Gwamma idanunta sukayi jawur saboda b'acin rai zuciyarta sai tafasa takeyi akan bak'in ciki,,, jijiyoyin kanta sukayi rud'u rud'u akan b'acin rai. Can tayi ajiyar zuciya na bak'in ciki ta daure tace "babu komai yaran nan amma ta sani taci alfarmarku,,, da wallahi bazata sake yima wani rashin kunya ba,,,amma ta je duniya ce zata ga abinda zai biyo baya! "".
"Mtsss aikin banza! Babu abinda zan gani sai alkhairin Allah,, kurwata kur! Kici kanki kisha bak'in ruwa ".Cewar Fadila tana tofar da yawu,, cikeda masifa da bala'i. Su Maryam ne sukaja hannunta da k'arfi suna bata hak'uri,, suka nufi hanyar zuwa shagon Mande suna tafiya Fadila tana ta masifa da bala'i,,, haka suka kama bata baki suna lallashinta. Suna isa shagon Mande dole tayi shiru suka siye abinda ya kaisu sannan suka juyo zuwa gidan Iya Gwamma.
Suna dawowa suka ba Iya Gwamma aikenta,, sannan su Fatima suka k'ara bata hak'uri akan abinda ya faru. Ta nuna musu babu komai ai tareda yi musu godiya sosai. Sannan sukayi juyawarsu zuwa gidajensu. Bayan fitarsu ne Iya Gwamma ta k'yalk'yale da dariyar mugunta harda fad'uwa k'asa akan makirci,, can tace '"hak'ik'a Fadila kin kawo kanki gidan mutuwa! Sai kinsan kinyi mini rashin kunya. Ko 'yan uwanki da basuyi min komai ba,,, bazan tab'a k'yalesuba balantana ke mara mutunci,, zakiyi nadamar abinda kika yimin a rayuwarki! "Hhhhhhhh haka dai Iya Gwamma ta cigaba da surutunta na son ganin bayansu Maryam..........
_More comment more typing_
_Mugirat Musa_😍
,
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 2*
***Iya Gwamma ce ta kama surutunta na hauka,, mai cikeda bak'in ciki da b'acin rai akan abinda Fadila tayi mata. Can naga Iya Gwamma ta shiga cikin wani d'akin da yake gefen d'akinta da take barci da saka kayayyakinta,, tana shiga ciki ta fito da wata k'warya cikeda jinin mutane. Ta samu wuri saman tabarma ta zauna tanata sambatu da maganganu irin na masu sihiri da tsafi,,, ta jima tanayi saiga rugugin tsawa da hayak'i! Suna bayyana ruwan jinin dake cikin k'warya suna chanza kala daga ja zuwa kore-kore. Nan da nan naga ruwan jini sun fara tururin tafasa,, kamar an azashi saman wuta. Nayi duba zuwa ga idanun Iya Gwamma sunyi jawur kamar barkono,, ga jijiyoyin kanta sun mik'e tsaye rud'u rud'u halittar jikinta gaba d'aya ta chanza,, ko'ina a cikin jikinta gashi ya k'ara tsawo zago -zago kamar k'aho,,, bakinta babu abinda ke fitowa sai wuta mai mugun zafi. Can naga tayi wasu d'alamisai na tsafi saiga photonsu Maryam su uku ya bayyana a cikin k'warya,, suna tafiya zuwa gidajensu. Iya Gwamma tayi duba cikin k'waryar jini da idanunta jawur kamar kan jaki,,, tace" saina kasheku! Saina cinye namanku d'anye yara! Zan nuna muku ba'a yima mayyu rashin kunya akwana lafiya,,, hhhhh na kama kurwarsu ni Gwamma jikar mayya d'iyar *MAYYA* .Saina banbance muku atsakanin aya da tsakuwa,,, k'ananan marasa kunya kawai daku! ".
Haka dai ta cigaba dayin sambatunta,, tana tofe -tofe a cikin k'warya. Saiga inwar kurwarsu Fadila ta bayyana a cikin k'warya,, Iya Gwamma ta k'yalk'yale da dariyar mugunta da kuma farin ciki mara misaltuwa na cikar burinta....
**********************
Su Fadila suna tafiya suna firarsu cikeda walwala,, kamar babu abinda ya faru dasu agidan Iya Gwamma. Basu jima sosai ba suka had'u da yaya Mubarak,, bayan sun kawo wajen garkar gidajensu. Yaya Mubarak ya dubesu cikeda matuk'ar mamaki yace "Yara manyan gobe ina kuka shiga ne,, tun d'azu nake zagayar gari nemanku ".
Maryam da Fatima suka sunkuyar da kansu cikeda fargabar da irin amsar da zasu bashi,,, tsoro da fargaba ne ya bayyana k'arara akan fuskokinsu. Su biyu ne suka dubi Fadila domin sunsanta wurin rashin tsoro da dauriya,, da iya tsara k'arya da gaskiya akan lamarin rayuwa. Fadila ce ta numfasa tareda k'yafta musu idanu akan su saki jikinsu,, kada yayi saurin gano abinda zata furta k'arya ne. Su Maryam suka gyad'a mata kai alamar to,, duk da yake babu abinda sukeyi sai wuru -wuru da idanunsu alamun rashin gaskiya duk ya bayyana a fuskokinsu.
Fadila ce tayi murmushi mai k'ayartar da fuskarta tace "yaya Mubarak wasa mukaje gidan k'awarmu Hassana,, shiyasa ne kayi nemanmu baka ganmu ba ".
Mubarak yayi shiru na minti biyu yana nazarin maganar Fadila,, amma acikin zuciyarsa ko kad'an bai aminta da maganarta ba. Domin kuwa kallon d'aya yayi musu ya gane basuda gaskiya,, amma dayake shi ma d'an zamani ne ya nisa sannan yace "Ok ba matsala amma dan Allah ku daina dad'ewa awaje,, wurin yin wasa domin kuwa yanzu zamanin nan namu ya lalace. Akwai abubuwa da yawa da zasu iya cutar daku wanda bana fatar haka,, saboda zuciyata bazata iya d'aukar hakan ba ".
Fatima taja dogon numfashi tace "insha Allahu yaya zamu kiyaye maganarka,, ai domin muje gidansu Hassana ne yasa muka dad'e sosai".
"haka ne gaskiya yaya Mubarak ai da tun d'azu mun dawo gida ".Cewar Maryam.
Mubarak yace "to 'yan k'annena na yarda daku nasan ba zakuyi abinda za'a ce Allah yayi wadaran da halinku ba,, saboda haka ku wuce zuwa gida ".
Fadila tace "zamu kiyaye yayanmu karka damu ".
"Allah yasa da gaske kukeyi ".Inji Mubarak.
"Amin Yayanmu ".Cewar Fatima da Maryam atare cikeda sanyin jiki. Yaya Mubarak saida ya raka Fatima da Fadila har bakin k'ofar gidansu,, dayake gidansu d'aya baban Fatima shine yayan baban Fadila. Bayan yah Mubarak yaga shigewarsu cikin gidansu,, yazo yaja hannun Maryam yana yimata nasiha tareda maganganu masu lurassuwa cikin hikima da iya magana..
**********************
Mubarak ne da Maryam suka shigo cikin gidan,, tareda da furta sallama a bakinsu. Mama Sa'ima ta amsa musu yayinda take k'ok'arin kwashe sharar da ta kammala yanzu nan,,, tasa parker ta kwashe sharar tana zubawa cikin kwandon shara. Alokacin ne Mubarak da Maryam suka k'araso cikin tsakar gida,, suka samu wuri suka zauna saman tabarma. Mubarak ya dubi Mama Sa'ima yace "sannu da aiki Mamanmu "."Yauwa Mubarak".Inji Mamansu bayan ta fito daga wurin kwandon zuba shara,, ta zauna kusaga Maryam ta harareta tace "sannu Maryam sarkin yawo,, Mubarak gidan uban wa kagansu? ".
Maryam ta sunkuyar da kanta cikeda matuk'ar tsoro da fargaba! Tace "Mama dan Allah kiyi hak'uri gidansu Hassana mukaje wasa ".
"tabbas haka suka gayamin Mama,,,tayi ba dai-dai ba ayi mata hak'uri bata sakewa ".Cewar Mubarak.
Mama Sa'ima tace "naji Mubarak amma wallahi Maryam ki kiyayeni ! Inba rainin wayo da hankali ba,,, ki fita daga cikin gidan nan tun safe baki dawo cikin gidan nan ba sai yanzu bayan azahar. Saboda bak'yajin maganata to zan gayama babanki nasan shi ,,,zakijin maganarsa saboda kinajin tsoronsa mara jin magana kawai ".
Maryam ta fara zubarda hawaye ,,,muryarta tana rawa tace "na tuba Mama ki rufamin asiri kada ki gayama baba,,,,wayyo wayyo Allah! Wayyo kaina wallahi Allah bana k'arawa komi kikace shi zanyi Mama. Yaya Mubarak ka taimaka ka k'ara bata hak'uri kaji ".
Yaya Mubarak ya dubeta cikin tausayawa da k'aunar k'anwarsa,,, yasa hannu ya jawota ya rungumeta a jikinsa yana lallashinta. Yace "ya isa ya isa Maryam share hawayenki Mama zata hak'ura kinji,, kuma idan Allah ya yarda bazan bari ta gayama Alhaji abinda ke faruwa ba ".
"To Yaya ".Cewar Maryam tana shessheka tana ajiyar zuciya,, saboda kukan da tayi.
"to tashi uwar son jiki kije kiyi wanka sannan kici abinci,,, nidake ne a cikin gidan nan matuk'ar kikace bazakiji maganata ba,,,,sai rayuwarki tayi matuk'ar b'aci sosai wawuya wadda bata san ciwon kanta ba"..Inji Mama Sa'ima cikeda matuk'ar b'acin rai sosai.
Maryam ta mik'e tsaye tayi hanyar zuwa d'aki domin tayi wanka,,, sannan taci abincinta..
Alokacin ne Mubarak ya k'ara cewa "Mama ayita hak'uri k'urciya ne wata rana zata daina,,, sannan nima zan k'ara saka mata idanu sosai ".
"hmmm haka ne Mubarak amma zamanin nan abin tsoro ne,,, ya zama dole mutum ya k'ara lura da d'iyansa. Saboda mayyu sunyi yawa a cikin mutane sosai kowa ka gani yaci magani ne domin yayi kud'i,, ko ya cimma wani buri nashi wurin bid'ar abin duniya sai mutum ya zama maye kowa ya kama gudunsa,,, kuma ba ko'ina ake amso maganin ba illa wurin bokaye da 'yan bori. Mutane sun manta da cewa babu mai talautawa da azurtawa idan ba Allah kad'ai ba. Sun manta da cewa babu mai iya ba mutum abinda Allah bai bashi,,, da ace wani bawa yana iya azurtar da d'an uwansa da ya fara azurtar da kanshi kafin kuzo neman taimako wurinsa. Ba'aganshi walak'ance cikin k'azanta da datti ba ".Inji Mama Sa'ima.
Mubarak yace "haka ne gaskiya Mama Allah ubangiji ya bamu ikon bin gaskiya da kuma gyarawa,, wad'anda suka b'ace Allah ya daidaitasu akan hanyar gaskiya ".
Mama tace "Amin summa amin Mubarak ".
Suka cigaba da firarsu cike da tsananin jin dad'i da nishad'i sosai,, sunyi nisa cikin fira ne saiga sallamar Alhaji Suleiman ya shigo cikin gidan. Suka amsa masa Mubarak ya gaidashi tare da yi mishi sannu da zuwa,,, ya amsa mishi fuskarshi cikeda fara'a da murna sosai. Mama Sa'ima itama tayi masa sannu da zuwa ya amsa mata,, ta amshi kayan da ke hannunsa suka shige cikin parlourn d'akinsu.
Mubarak ya jima sosai yana tunani akan al'amarin rayuwa,, sannan daga baya shima ya shige cikin d'akinsa. Ya shiga cikin toilet yayi wanka sannan ya sanya singlet da guntun wando domin shan iska,, ya kunna vedio ya sanya American film ya fara kallonshi cikeda natsuwa da kwanciyar hankali....
*Ku biyoni sannu domin jin ko wa cece Iya Gwamma,,, da kuma jin tushen labarin*.
_Share&Comments_
~Muje zuwa~
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 3*
**Yaya Mubarak yayi nisa sosai a cikin kallon American film d'in da yakeyi,, ko k'wakk'waran motsi bayayi sosai saboda yadda ya mayar da hankalinshi kacokam a wurin kallon vedio. Da gani babu tambaya kasan yanajin dad'in kallonshi,,, hankali kwance yake gudanar da komai nashi..
Ab'angarensu Mama sa'ima kuwa suna shiga cikin d'akin,,, ta taya Alhaji cire kayan jikinsa. Bayan ta gama cire masa kayan tas ta barshi da singlet da guntun wando,, sannan ta ja hannunsa kamar yaro k'arami ta kaishi cikin toilet tareda had'a mishi ruwan wanka,, bayan ta gama duk abinda ya kamata ta fito ta bar Alhaji domin yayi wankansa. Tana fitowa ta k'ara gyare bedroom d'in tareda sa ma d'akin room freshner mai k'amshin dad'i matuk'a,,,, sannan ta fitoma Alhaji jalabiya fara da zai saka a cikin gida tareda da feshe jalabiyar da perform mai k'amshi,, sannan ta samu wuri ta zauna a cikin d'akin tana jiran fitowar uban 'ya'yanta..
Bayan minti goma sha biyar saiga Alhaji ya fito daga wanka,, yazo kusaga Mama Sa'ima. Tana ganinshi tayi murmushi sannan ta d'auko lotion mai k'amshi ta fara shafa masasannu sannu cikeda nuna matuk'ar kulawa ga mijinta. Babu abinda Alhaji yakeyi sai lumshe idanu ma'ana yana jin dad'in yadda take bashi kulawa,, bayan ta kamalla shafa mishi mai neta d'auko jalabiyarsa ta sa mishi,, tana gama sa mishi suka zauna a tare suna fuskantar junansu. Alhaji Suleiman ya dubeta duba mai cikeda k'auna da son matarsa yace "Ummu Maryam Allah ubangiji yayi miki albarka hak'ik'a ke mace ce ta gari mai biyayya ga mijinta,, ina alfahari da kasancewarki matata uwar 'ya'yana,,,nasan nayi dace da farin cikin rayuwata mai sona kuma mai son farin cikina,, da gudun b'acin raina banda tamkarki a cikin zuciyata ".
Alal hak'ik'a kalaman Alhaji Suleiman sunyi matuk'ar sanya Mama Sa'ima cikin tsananin nishad'i da farin ciki sosai,,, sunbi jini da jijiyoyin jikinta suna shawagi a cikin zuciyarta. Ta dubi Alhaji cikeda matuk'ar nishad'i sosai tace "Amin ya Alhajina kasani biyayya ya zama wajibi agareni nayi maka muddin ina numfashi a doron k'asa,,, kaine silar farin cikina hasken idaniyata,,, idan ban faranta maka ba waye zan farantawa aljannata tana k'ark'ashin tafin k'afarka fa mijina,,, idan ka d'aga k'afa in shiga idan ka take shikenan! Taya zanyi sakaci har na tab'e Abban Mubarak,, ina matuk'ar alfahari da kai Alhajina ".
Alhaji ya rik'o hannunta yana murmushin jin dad'i,, sannan yace "haka ne matata idan har miji ke d'agama matarsa k'afa ta shiga aljanna,, to ni tawa k'afar a d'age take matata kuma insha Allahu zaki shigeta ".
"Ina godiya Alhajina,, to ya kasuwar? ina fatar ana samun ciniki sosai ".Inji Mama Sa'ima..
Alhaji Suleiman yace "lafiya k'alau Alhmdlilah,, agaskiya ana samu ciniki sosai ".
Mama Sa'ima tace "masha Allah komai yayi k'yau matuk'a,,, dama haka ake son ji Allah ubangiji ya k'ara taimakawa ya bada sa'a da nasara "..
Alhaji yace "Amin amin Ummu Maryam,, ina yaran nan suke ne Mubarak da Maryam d'in? ".
"hmm Mubarak yana d'akinsa Maryam kuma na barota ta gama cin abinci zata kwanta,,, kasan yaran idan suna gida kodayaushe suna cikin d'aki shiyasa ba'a sanin suna nan ko basa nan ".Cewar Mama Sa'ima..
Alhaji yace "haka ne musamman Mubarak akwai shi da son zama cikin d'aki kamar mace,,, shiyasa ma bai fiye son zaman shago ba,,, Maryam ko taso zaman d'aki ai ita mace ce gidan wani zataje ".
Mama Sa'ima tace "ai zai saba da zaman shago saboda namiji dole ya fita ya nemo,, Maryam kuma ai lamarinta sai addu'a saboda akwaita da rashin ji wallahi ".
Alhaji ya harareta da wasa cikin tsokana yace "a'aaa kada ki sanyama 'yata ido barta tayi rashin jinta,,, ai komai yanada lokacinsa addu'a dai zamu dinga yi akan Allah ubangiji ya shirya mana yaranmu "..
"kunfi kusa kodayake bakason a ce ga laifin Maryam,, addu'a takobin mumini ce Allah ya shirya mana zuri'armu ".Inji Mama Sa'ima.
Alhaji yace "Amin yanzu dai naji magana ba'a dinga takurawa 'yata ba,, ana cewa tayi kaza kaza ba "..
Mama tace "kaidai ka sani da dad'in bakinka ".
Yace "harda ke kinsan inada mana "..
Mama tace "nasan mi? ".
Alhaji yace "inada dad'in baki mana,, kuma har kin yaba ".
Mama tace "rashin aikin yi dai ".Tana murmushi sosai..
"da ni dake bamuda aiki yi ba ".Fad'ar Alhaji yana dariya sosai..
Mama kauda kanta tayi gefe guda,, tana ta dariya sosai mai cikeda matuk'ar farin ciki da walwala,, Alhaji shi ma yana tayata dariya tareda da jifanta da kallon soyayya da k'auna...
*********************
***Agidansu Fatima kuwa suna isa cikin gidan sukayi sallama,, aka amsa musu suka samu uwayensu zaune wuri d'aya suna fira cikin farin ciki da nishad'i. Su Fatima suka samu wuri kusaga iyayensu saman tabarma suka zauna,, bayan sun zauna ne sukayi shiru basu ce komai ba saboda sunsan sunyi laifi...
Iyayen nasu sai firarsu sukeyi kamar basu gansu ba,, can dai Fatima da yake batada hak'urin yunwa ta bud'i baki da k'yar tace "Umma yunwa nakeji fa,, tun safe rabon dana koma saka wani abu cikin bakina ".
Mahaifiyar Fatima mai suna Nusaiba ta banka mata wata uwar harara,, sannan ta bud'i baki tace "to sabon salo inda kukaje ne baku ci abinci ba,, na aikeki yawon gantali da sakarci ne ? Da zaki zo kina damuna yunwa kikeji yau naga bak'ar munafuka,,, salon ubanki yaji yace ina miki horon yunwa ko,, Fatima Fatima! Ki fita daga cikin idona mai yawon sakarci da wawanci ".
Mama Nafisa mahaifiyar Fadila ta harari su Fadila,, tace "k'yaleta Nusaiba ai gara ita tayi magana,, wannan mai taurin kunne _(ta nuna Fadila)_ ko magana batayi ba saboda tasan batada gaskiya,,,gameda shegen yawon nan saina saka ki cikin turmi nayi miki dakan tankwan d'an bashirwa! Munafuka 'yar iskar yarinya ".
"Ni banga dalilin yawon banza ba miye kuka nema kuka rasa ne? Saboda Allah salon ku jawo ma kanku wani mugun abu! Ga mayyu a garin nan kamar tsaki,,, saboda haka zamu d'auki mataki akanku tunda bakujin magana ".Inji Umma Nusaiba.
Mommy Nafisa tace "mataki ya wuce musa Fadil ya basu matsiyacin kashi idan suka koma,, saboda naga sun raina Nabila basajin tsoronta kwata kwata,,,ni wlh idan rayuwata ta b'aci ina iya yi muku mugun bugun walak'anci da halaka,, saboda naga lalama batayi muku musamman ke Fadila mai kunne roba ".
Umma Nusaiba tace "ba wani Fadila aiko ba ita kad'ai zakiyima fad'a ba,,, ko Fatima ba baya ba wurin rashin jin magana ba,,,mu samesu rana d'aya mu basu kashin k'warai ko zasuyi hankali "..
Mommy Nafisa tace "naji amma ai tafita rashin jin magana,, amma nasan maganinsu ".
"babu wani ta fi ta duk d'aya suke ".Inji Ummu Nusaiba.
Fatima ce ta tattaro dauriya,, tareda marairaice fuskarta tace "Mommy,, Umma dan girman Allah kuyi hak'uri Insha Allahu bazamu sake ba,, dama gidansu Hassana ne mukaje shiyasa muka jima sosai bamu dawo ba ".
"munsan munyi kuskure ayi mana afuwa,,, bazamu k'ara aikata kwatankwacin haka ba ".Inji Fadila..
Mommy Nafisa taja mugun tsoki mtssss! Saboda ita akwaita da saurin d'aukar zafi da wuri,, ta juyar da kanta wani gefe domin kada suga fuskarta. Umma Nusaiba ce taja dogon numfashi tace "komai ya wuce yarana ubangiji Allah ya k'ara shiryaku,, Nafisa baki ce komai ba ".
Mommy Nafisa tace "ai kin riga kin gama magana Nusaiba,,, nima na hak'ura Allah ubangiji yayi musu albarka ".
Su Fadila sukace "amin mun gode sosai Iyayenmu ".Suka mik'e tsaye atare suka nufi cikin d'aki domin suyi wanka suci abincin rana,, iyayen mata suka cigaba da firarsu cike da walwala da annashuwa mara misaltuwa..
*ASALIN LABARI*
Maryam 'ya ce ga Alhaji Suleiman da Hajiya Sa'ima,, asalinsu 'yan nijar ne kasuwanci ne ya kawosu Nigeria acikin garin Gumi Zamfara state. Suleiman da Sa'ima 'yan uwan juna ne domin kuwa auren zumunci akayi,, sun taso ne tun suna yara suna matuk'ar k'aunar junansu fiye da yadda kuke tunani. Sun taso gidan mutunci masu nagarta da son zumunci,,,a familynsu sun kasance sunada had'in kai da kuma k'aunar juna babu gulma ko hassada da nuna k'yashi. Komai nasu a had'e yake abin burgewa da sha'awa matuk'a,, idan ka shiga cikin gidan da yake babban gida ne ba zaka iya gane wani banbamci ba,, saboda ba zaka iya gane wannan d'an wa ne ba ko d'an wance ce ba saboda had'in kai da zumunta,,, hak'ik'a famili ne mai matuk'ar k'aunar juna da yarda da 'yan uwa...
Sun had'a auren Suleiman da Sa'ima domin zumuncinsu ya k'ara k'arko,, masha Allah akayi dace ko su yara ne masu biyayya da k'aunar juna. Sun bada had'in kai cikin tafiyar da rayuwar aurensu cike da aminta da juna da zaman lafiya na hak'ik'a,, kowanensu yana k'ok'ari wurin ganin ya farantama d'an uwansa tareda k'yautatawa juna domin samun farin ciki da annashuwa mai d'orewa har abada ....
_Share &Comments_
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 4*
Domin samun farin ciki da annashuwa mai d'orewa har abada,,, zamansu zama ne na fahimtar juna da amana,, tausayi da tsananin shak'uwa a tsakaninsu. Dukansu suna k'ok'ari wajen ganin sun sauke hak'k'in dake bisa kansu na auratayya,, Suleiman ya kasance mutum ne mai sauk'in kai da tausayin na k'asa dashi bayada rowa ko k'yashi ko kad'an. Yanada son bayarda k'yauta da taimako gashi kuma mai tsananin biyayya da ladabi ga mahaifansa,, haka itama Sa'ima mace ce wadda batada matsala a rayuwarta,, tanada kirki da k'yakk'yawan d'abi'u tanada son mutane da yawan fara'a. Haka take kowa nata ne babu ruwanta da shiga sabgar daba ta taba,,,, shiyasa lamarin aurensu yazo da sauk'i matuk'a saboda shi bayada matsala hakama Sa'ima batada wata matsala..
Haka suka cigaba da gudanar da rayuwar aurensu cike da jin dad'i da farin ciki mara misaltuwa,,, kowanensu yasan abinda ya dace ya kamata zaman lafiya ya wanzu a cikin gidan aurensu. Babu abinda sukeyi sai sunyi shawara tare su kashe tare su binne tare babu mai jin sirrinsu,, Alhaji Suleiman kasuwanci yakeyi tun anan nijar kafin harakar ta bunk'asa sosai .Itama Sa'ima tana saisuwa su kayan miya cikin gida irinsu,, maggi star racco,, daddawa,, maggi ajino motto,, gishiri,, kanwa,, sabulun wanka da wanki,, k'uli -k'uli,, tankwa da dai sauran kayayyakin miya..
Sunyi wata biyu da yin aurensu saiga ciki ya bayyana a jikin Sa'ima,, sunje asibiti an auna wata d'aya da satittikka zo kuga murna da farin ciki a fuskokin wad'annan bayin Allah. Bayan sunje gida suka sanarda 'yan uwa da abokan arzik'i duk wanda suka fad'ama sai yayi murna da farin ciki sosai,,, zo kuga farin ciki da nishad'i a cikin zuciyar iyayensu Alhaji Suleiman. Haka dai Sa'ima ta cigaba da samun kulawa ta musamman ta b'angare biyu iyayenta dana mijinta,, duk abinda take so shi akeyi mata na daga abubuwan ci da abinci mai gina garkuwar jiki,, haka abubuwan ke tafiya cikeda matuk'ar kulawa da tarairaiyarta. Shima kanshi uban gayya wata kulawa ya k'ara bata yana shagwab'ata da tarairaiyarta hundred percent,,, haka dai Sa'ima ta cigaba da rainon cikinta da bashi kulawa fiye da tunanin mai karatu,,, kwanaki suka cigaba da tafiya suna zama watanni..
Watanni takwas sukazo alokacin ne bayan sallar asuba,, ciwon nak'uda ya kama Sa'ima tun tana nishi hmhmhmhm hmhmhmhm hmhmhmhm babu wanda yaji,, har tazo ta fara kiran sunan mahaifiyar Suleiman. Inna ta shek'o da gudu ta taimaka mata tana mata addu'a harta santalo santalelen d'anta,, k'yakk'yawa son kowa k'in wanda ya rasa. Bayan Innar Suleiman ta gyarata ta kuma gyara ko'ina sai k'amshi yake tashi ,, can ta shiga cikin gida ta sanarwa kowa da kowa. Zo kuga yadda ake tururuwa zuwa ganin sabon jariri sabon jini,, haka dai mutanen unguwa suka cigaba da zuwa ganin jariri tareda yi mata barka da haihuwa,,, haka dai suka cigaba da zuwa dubiyar Sa'ima...
Sati yana zagayowa ranar suna yaro yaci suna Mubarak,, hak'ik'a 'yan uwa da abokan arzik'i sunyi matuk'ar k'ok'ari wurin ganin sun fitar da Sa'ima kunya,, anyi mata abin arzik'i k'warai da wadata raguna biyu manya -manya aka yanka da tinkiya d'aya. Haka dai akayi bikin cikin rufin asiri da wadatar zuci,, bayan maraice tayi kowa ya kama gabansa ya wuce zuwa gida..
*********************
Bayan shekaru biyar da haihuwar Mubarak,, Alhaji Suleiman ya kwaso iyalinsa daga mahaifarsa nijar ya dawo Nigeria zamfara state cikin garin Gumi. Ya cigaba da kasuwancinsa cikeda kwanciyar hankali,, itama matarsa ya bata jari domin ta cigaba da sana'arta da takeyi acan nijar..
Garin Gumi gari ne mai tarihi da d'umbin albarka,, sunayin kasuwanci da kiwo amma ba sosai ba babbar sana'arsu shine noman k'warya. Itace sana'ar da mafi akasari da 'yan garin keyi da kiwo amma ba sosai ba,, garin ba za'a kirashi k'auye sosai ba kuma ba za'a kirashi birni ba yana dai tsaka tsakiya. Mutanen garin mutane ne masu addini da tsoron Allah,, komai nasu zad sha'awa suke gudanar dashi...
**Anan garin ne Mama Sa'ima ta haifi Maryam atsakaninsu da Mubarak akwai tazarar shekaru shida,,, zo kuga murna alokacin da Mubarak yaga ya samu k'anwa fara tass k'yakk'yawar gaske ta bugawa a mujalla,,, hak'ik'a Allah yayi halitta a nan domin kuwa kallo d'aya zakayima jaririya ka gano sai anyi k'yakk'yawar mace abar kwatance da kallo cikin mutane. Haka dai Mama Sa'ima ta cigaba da rainon Maryam itada Mubarak,, shima Alhaji Suleiman Allah ya d'ora masa tsananin k'aunar iyalinsa wato yaranshi,, komai yi musu yakeyi gwargwadon iyawarsa domin samun farin cikinsu da walwalarsu....
Fatima 'ya ce ga Malam Nura da Nusaiba,, kuma yaya ne ga Nazifi mahaifin Fadila da mahaifiyarta Nafisa. Nura da Nazifi sun kasance 'yan uwan juna uwarsu d'aya ubansu d'aya,,, sun kasance 'yan asalin jahar kebbi amma sun dad'e cikin garin Gumi sosai tun kafin su fara tara iyali sosai,,, babbar sana'ar da suka dogara da ita shine noman k'warya da ita suke ci suna rufama junansu asiri. Ahaka suke d'aukar nauyin iyalinsu cikeda zafin nema da wadatar zuci,,, shiyasa ake son mutum mai zuciyar neman na kanshi domin kada mutum ya dogara ga wani. Zuri'arsu zuri'a ce mai had'in kai da zumunta,, tareda da matuk'ar kulawa da kuma soyayya da juna. Kan mazan a had'e yake babu wani munafurci ko gulma,,, hakama matansu sunada had'in kai matuk'a d'aya batayin abu saida shawarwarin junansu. Duk abinda suka yanke shawara shi sukeyi tare shiyasa ko yaransu Fatima,, Fadila,, Nabila da Fadil kansu yake a had'e cikeda matuk'ar tausayin juna da girmamawa..
Familinsu family ne masu matuk'ar k'aunar juna,, da fahimtar juna haka suke tafiyar da rayuwar aurensu cikeda zaman lafiya da soyayya..
***Iya Gwamma 'yar asalin Gumi ce gaba da baya,,, 'ya ce ga Malam Mamman da Ina Talatu tanada k'ane guda mai suna Lawwali ita Iya Gwamma. Inna Talatu mayya ce da taci magani a wurin wani babban boka mai suna LOK'ORO,, boka LOK'ORO shahararren boka ne da ya shahara a cikin garin Gumi da kewayenta. Sunanshi ya bazama ko'ina a jahar zamfara da k'auyukanta ,,,yana bada magani ne ga wad'anda suke son suyi kud'i sosai ko wani cimma burinsu na duniya. Babban matsafi ne dake aiki da bak'ak'en aljannu da dodonni,, ya shahara wurin mugunta da kashe rayuka na mutane harda aljannu. Bayan Inna Talatu ta amshi magani domin ta zamo mai arzik'i to kwatsam! Bata zamo mai kud'i ba ta rikid'a ta zama k'usurgumar MAYYA wadda nan da nan ta fara cin naman mutanen unguwa da na k'etaren gari,,, tun tanayi a b'oye mutane basu sani ba har yazo ya bayyana afili kowa ya gano ita mayya ce. Nan da nan mutanen gari da wad'anda take mu'amala dasu suka fara gudunta domin ceton ransu dana iyalinsu,,,ko'ina ka gani anyi gungu a majalisu babu abinda suke fad'a idan ba Inna Talatu *MAYYA CE* cin naman mutane takeyi da satar kurwa! Harda yaranta su Gwamma ake tarewa a hanya ake ce musu d'iyan mayya kunyi hasara,, Gwamma kuwa kashi takeyima yaran mutane idan ko warinta ne saisu kacame da dambe sosai. Ta samu yaro tayi masa mugun cizo sai jini ya fito tasa halshenta ta lashe jinin ta had'iye mak'wat kamar mayya ,,,tabar yaron nan kwance k'asa yana kukan ciwo wiwiwihhh.
Lawwali yana gefe guda yana kallon yadda take dukan yaron mutane kamar ta samu jaki,,, shi dai babu ruwanshi saboda yanada matuk'ar natsuwa da sanyin hali. Bayason hayaniya ko tashin hankali ko kad'an idan ka ganshi kana cewa ba Inna Talatu ce ta haifeshi ba,,, saboda natsuwarsa da hankalinsa..
Gwamma ce take kakkab'e jikinta da k'asa bayan ta gama chasa d'an mutane,,, ta juyo ta dubi Lawwali tana harararshi tace "shege raggon namiji kanajin ana zagin mahaifiyarmu amma kayi shiru,, sai dai ka koma gefe kana kallona ina fad'a,,, Allah yayi wadaran naka ya lalace! Wawan banza mai zuciyar kare ".
"yaya Gwamma kiyi hak'uri ni banyi shiru ba ne domin in b'ata miki rai ba,, nayi shiru ne saboda aganina fad'a baya kawo maslaha a cikin wannan lamari,,, kuma ai duk abinda suka fad'a ai gaskiya ne saboda Innarmu ta aikata maita! ".Inji Lawwali cikeda rashin son tashin hankali.
Gwamma ta zaburo mai da k'arfi cikeda jin haushin maganarsa,,, tace "Innarmu ce mayya saboda bakada hankali,, lallai Lawwali anyi tsinannen yaro d'an banza! Yanzu nan zanci ubanka ".
"Eh mana na fad'a ai gaskiya d'aci gareta k'arya kuma tanada matuk'ar dad'in d'and'ano mai zak'i yaya Gwamma ".Cewar Lawwali cikin jin haushin maganar Gwamma.
Nan da nan cikeda matuk'ar zafin nama da jin bak'in cikin maganar Lawwali,,, aiko Gwamma bata tsaya b'ata lokaci ba ta kwashe Lawwali da wani mugun mari mai matuk'ar zafi da rad'ad'i tareda gigita rayuwar d'an Adam! Ai saboda k'arfin marin saida Lawwali ya wintsilo k'asa da k'arfi,,, saida bakinshi ya fashe da jini jinshi da ganinshi suka d'auke na wucin gadi..
Yana kwance k'asa Gwamma ta nuna shi da yatsa cikeda zafin rai da tafasar zuciya tace "ina yi maka gargad'i da kada ka kuskura ka k'ara aibata mahaifiyarmu,,, idan ana zaginta kana kallo kana k'yalewa toni bazan k'yale ba,,, duk wanda ya nemi da ya zagi uwata to sai inda k'arfina ya k'are ciki kuwa harda kai da muke ciki d'aya,, wallahi wallahi! Akan mahaifiyata zan iya kashe rai har lahira!!! Kuma duk wanda ya shiga cikin gonata saina afka mishi koda kuwa kaine Lawwali,, yaron banza mara kishin uwarsa ".
Nan taja jikinta tabar Lawwali kwance a k'asa yana kukan rad'ad'in marin da tayi masa mai zafi sosai,,, ta kama hanyar zuwa gidansu babu abinda Lawwali keyi sai zubar da hawayen bak'in ciki da takaicin abinda Gwamma tayi masa,, kuma yasan ya fita gaskiya a cikin wannan lamari yasa hannu ya share jinin dake fita daga cikin bakinsa yana shassheka da ajiyar zuciya.....
_Share&Comments_
*I luv you my fans more more*
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 5*
Yasa hannu ya share jinin dake fita daga bakinsa yana shassheka da ajiyar zuciya,, idan banda rad'ad'i da ciwo babu abinda zuciyarsa keyi saboda marin ya shigeshi sosai matuk'a. Dak'yar Lawwali ya mik'e tsaye yana shafa kuncinsa da yake yi masa zafi da rad'ad'i,,, ya kakkab'e jikinsa daya b'aci da k'asa ga shatin hannun Gwamma nan ya fito b'aro b'aro a fuskarsa,,, haka dai yaja k'afafunsa yana tafiya dak'yar domin ya nufi gidansu...
Gwamma ce naga harta iso gidansu ta afka cikin gidan ba tare da sallama ba,, Inna Talatu ce da Malam Mamman ta iske ya dawo gida domin yayi wani mantuwa a gidan,,, ya dubi Inna Talatu yace "Talatu baki ga wata bak'ar leda ba dana yi mantuwa da ita ba,, ta mutane ce idan kin gani ki mik'omin sauri nakeyi zan wuce ".Inna Talatu ta harari Malam Mamman sannan ta buga tsoki mtsssss tace "maganar banza kenan Mamman mi zanyi da bak'ar ledarka idan na gani,, ko kuwa ni na sakaka yin mantuwa ne? Da har zaka zo kana damuna da surutunka na banza da yofi! "."Kinga Talatu ba haka ba ne ai tambaya baya zama laifi,, daga tambaya sai masifa wai miyasa rayuwarki yanzu ta chanza ne? Idan wani abu nayi miki ya kamata ki sanar dani in gyara kuskurena mu fahimci juna,, batare da wasu sun jimu ba ".Inji Malam Mamman cikeda lalama,,, yana dibe dibe ko zai gano inda ya ajiye ledarsa da ya manta,,, Inna Talatu ta k'ara hasala sosai tace "babu abinda ka yimin Mamman tambaya ce kawai bana so,, domin ni tambaya b'atamin rai takeyi da ka shigo cikin gidan nan ya kamata ka bani ajiyar ledar,, amma baka bani ba ka ajiye da kanka sai yanzu da baka gani ba kake neman takuramin da tambayar munafurci,, to ka diba inda ka ajiye kada ka dameni da tambayarka "."Allah ubangiji ya huci zuciyarki Talatu nasan nayi ba dai -dai ba amma kiyi hak'uri kinji ".Cewar Malam Mamman bayan ya shige cikin d'akin yana cigaba da bincikensa..
"da hak'uri ta mutu sadakar nawa ka bani tsohon banza bak'in munafiki! ".Cewar Inna Talatu cikeda bala'i da masifa.
Tun d'azu Gwamma tana tsaye babu abinda tace,, illa kallonsu da takeyi uwarta tana zagin ubanta. Sai alokacin ne Gwamma ta bud'i baki tace "Inna na dawo fa naga tun d'azu baki lura dani ba,, kinata surutunki ".
"To d'iyar k'warai sannu da zuwa ya gajiyar hanya,, ina kika baro k'anenki ne? ".Inna Talatu ta fad'a yayinda take dube dube ko zata hango Lawwali a bayan Gwamma..
Gwamma taja numfashi tace "lafiya k'alau na dawo Inna Lawwali kuwa na baroshi a bayana kan hanya ".Saiga Malam Mamman ya fito daga cikin d'aki rik'e da ledarshi a hannunsa,, alamar kenan yaga ledar ya dubi Gwamma da Inna Talatu yace "aaa Gwamma kin dawo ko ".
"Eh na dawo baba ".Cewar Gwamma.
Malam Mamman yace "to yayi k'yau Allah ubangiji yayi muku albarka ".
Tace "Amin baba ".
Malam Mamman yace "to ni Talatu zan wuce can kasuwa naga ledar da na tambaye ki,, kika yimin bak'ar magana wadda babu dad'in ji balantana saurare kamar ni ba mijinki ba ne ".
"to tunda ka gani ka isa barka kada ka gayamin maganar da batada dad'i,, inko rama wallahi domin ba tsoronka nakeji ba! ".Inji Inna Talatu MAYYA.
Malam Mamman yace "ai nasan bakijin tsoro na Allah ubangiji ya shiryeki Talatu! Rayuwarki tanada matsala sosai wlh,, ni inada aikin yi na barki lafiya masifaffar banza ".Yana fad'in wannan maganar yasa kai yayi tafiyarsa zuwa kasuwa,, batare da ya tsaya ya saurarin irin martanin da zata mayar mishi ba..
"kaine masifaffe ba ni ba ai wannan rainin wayo ne,,, daga kawai kaga ina maka shiru-shiru sai raini da walak'anci ya shigo,, wallahi bazan tab'a barin ka gayamin magana ba dad'i ba amma ba komai zanyi maganinka! ".Cewar Inna Talatu tana d'aga murya k'warai ta yadda wanda yake bakin garka,,, zai iya jiyo muryarta.
Sai asannan ne Gwamma ta iya bud'a baki tace "kiyi hak'uri Inna wannan abin bai kawo kallo ba,,, kuma bai dace ba kina d'aga murya sosai har na waje suna jinki ".
Inna Talatu tace "haka ne d'iyar albarka rayuwata ce ta b'aci sosai wlh,, shiyasa ki kaga inata fad'a amma yanzu tunda kinsa baki na daina fa,, mi ya faru ne naga kamar bakinki yanada magana ?".
"ke dai bari Inna ayau Lawwali yayi masifar b'ata min rai da bani takaici ".Cewar Gwamma.
Inna Talatu tace "mi yayi miki ne har ya b'ata miki rai ne? ".
Gwamma ta kwashe labarin duk irin fad'an da takeyi da yaran mutane da suke kiran Inna Talatu mayya,,, da kuma marin da tayima Lawwali da kuma maganganun da sukayi,, babu abinda ta b'oyewa Inna Talatu komai ta gaya mata..
Inna Talatu taja dogon numfashi tareda huci mai zafi,, sannan tace "yanzu Lawwali ni yake zagi harda kirana da mayya,, yau ko wa yayi masa tsaye saina halakashi! Nayi masa mugun bugu sosai wlh,,, yadda idan yaji ana zagina ko baiyi fad'a ba bazai saka bakinsa ba waishi mara kuny....
Inna Talatu bata k'arasa maganar da take sonyi ba,, saiga sallamar Lawwali yayi sannan ya shigo cikin gidan da fasasshen bakinsa. Inna Talatu ta jawo hannunsa kamar abin arzik'i tana k'ara shafe masa jikinsa da jinin dake fita daga cikin bakinsa..
Sannan ta tambayeshi kamar batasan komai ba tace "Lawwali uban waye ya fasa maka baki harda jini,, wa ye ya mareka harda shatin yatsu? Ka gayamin yau ko ni ko maishi mutuwa kad'ai ke rabamu wlh ".
Lawwali yace yana zubar da hawayen takaici "Inna Yaya Gwamma ce ta mareni saida na fad'i k'asa,, sannan ta dinga zagina babu iyaka ".
"ita Gwamman to naji mi kayi mata ne data mareka? ".Inji Inna Talatu.
"haka kawai ne banyi mata komai ba ".Cewar Lawwali.
Inna Talatu ta harzuk'a da hasala sosai,,, batayi wata wata ba ta kwashe Lawwali da matsiyacin mari biyu masu k'yau,,, ta ka mashi tana ta kashi kamar ta samu jaki. Babu abinda Lawwali keyi sai kuwwa yana kuka domin ya samu agaji cikin gaggawa,,, saboda ba k'aramin duka Inna Talatu takeyi masa cikeda matuk'ar takaicinsa da zafin rai tana cewa "da kai za'a had'a baki ana zagina ko ana cemin mayya baka damu ba,, saboda bakasan zafina ba amma 'yar uwarka da tasan zafina shi ne za kace mata ai gaskiya yaran suke fad'a domin na aikata maita! Yanzu saboda munafurci na tambayeka kace bakayi mata komai ba ,,,yau saina kasheka in kashe banza! ".Haka dai Inna Talatu ta kama dukan Lawwali sosai tana zaginsa..
Babu abinda Lawwali keyi sai kukan bak'in ciki da zafin duka,, yana cewa "na tuba na tuba Inna,, Inna bazan sake ba wallahi sharrin shed'an ne ki ya femin zan mutu zan mutu! ".Nan ya fad'i k'asa ya some duk da haka bata daina dukansa ba,,, sai da tayi masa lilis da duka sannan daga baya ta gano cewa ya suma,, taje ta d'ebo ruwa a randa masu sanyi ta watsa mishi a jikinsa. Gwamma dai tana zaune tana kallon duk abinda ke faruwa hankalinta kwance,, can yaja dogon numfashi ya tashi zaune yana kuka duk gaba d'aya jikinsa yayi rud'u rud'u akan duka,,, Inna Talatu tace "gobe ma ka k'ara da sai naci namanka d'anye wlh! Kuma yau duk ubanda ya d'aure maka gindi ba za kaci abincin dare ba,, mu zuba mu gani ni da kai shege ya fasa! ".Tana gama fad'in maganganunta taja hannun Gwamma sukayi shigewarsu d'aki.
Lawwali yaja jikinsa sannu ya shige cikin d'akin da babu komai sai tarkacen kayayyakin aikin gida,, ya samu wata tsohuwar tabarma data yakuce akan tsufa ya kwanta. To haka abin ya kasance kuwa domin Inna Talatu hanama Lawwali tayi abincin dare da yunwa ya kwana,, mahaifinsa kuma baisan abinda yake faruwa ba a cikin gidan ba..
*********************
Da misalin k'arfe 12:00am na dare ne Inna Talatu ta tashi sannu a hankali,, tana dubawa ko Malam Mamman da Gwamma sunyi nisa cikin barcinsu. Ai kuwa taci sa'a babu abinda sukeyi sai minshari da gurnani na barci,, ta lab'ab'a sannu a hankali ta fito waje tareda zare sakatar gidan..
Tana fitowa waje ne duk unguwar tsit ta ke kowa yayi barci babu abinda kakeji sai kukan tsuntsaye dana wasu halittu,, ga wata irin sansanyar iska da ta ke busowa mai dad'in gaske. Sai da Inna Talatu ta dubi yamma gabas,,, kudu da arewa sannan ta duba kowace hanya babu kowa,,, sannan naga ta kama wata hanya siririya wadda ta nufi cikin daji,, tana ta tafiya har ta kawo wurin wata bishiya nan da nan naga ta cire tufafinta ta koma zindir haihuwar uwarta. Tana cire tufafinta ta isa wani wuri inda babu abinda ke tashi sai wuta wal wal wal,, wai ashe wurin 'yan uwanta mayyu ta zo domin suyi bugun wuta..
Wasar bugun wuta shi ne abinda mayyu keyi da daddare musamman alokacin zafi,, zindir haihuwar uwarsu sukeyi tareda canza kamanninsu ,, suna taruwa a cikin daji suna wasar bugun wuta shi ne su kama zagayar dajin gari bakinsu da hammatarsu sai fitar da wuta sukeyi wal wal wal zad tsoro!,, zasu jima sosai sunayi sannan daga baya kowa ya kama gabansa.
Suna gamawa ne Inna Talatu taje wurin bushiyar da ta aje kayanta ta d'auka ta sanya ta nufi gidan mijinta,, tana cikin tafiya kawai gani nayi ta girgiza da k'arfi! Ta rikid'a ta koma karya mai k'wala k'walan ido da halshenta ya kai tsawon igiyar shanya,, bakinta sai feso wuta yakeyi jawur tana kukan karnuka ohww ohww ohww babu dad'in saurare da ji hayak'i bak'i kawai ke fita daga cikin jikin karyar.
Ta kusa kawowa gida ta had'u da Lado zaiyi fitsari,,, komai na kayan cikinsa tana gani kamar irinsu hanji,, hanta ,, zuciya da duk wani abu da ku ka san d'an Adam ya keda haka suke ganin komai na mu kamar yadda ku ka ga skeleton,,, ai kuwa babu b'ata lokaci tasa halshenta mai kamar igiya ta jawoshi sai da tayi sama da shi ta koma tayi k'asa dashi,, sannan ta bugashi a k'asa cikeda maita. Lado babu abinda yakeyi sai kuwwar neman agaji amma ina dare ne kuwwarka banza.
Babu wanda zai jishi balantana ya kawo masa agajin gaggawa,, haka kawai yaji kamar an tsinke mishi jijiyoyin jikinsa saida Inna Talatu tayi masa azaba da mugunta iri iri daban daban sannan tayi wani mugun sihiri,,, wata irin mahaukaciyar guguwa ta ga me wurin tana zagayesu na wani lokaci,, saiga wani farin abu mai surkin ja ya bayyana a tafin hannun Inna Talatu,,, yana bayyana ta karanta wasu d'alamisai na tsafi da sihiri abin ya zama fa ra ta tura cikin jakarta ashe kurwar Lado ce ta mayar fa ra ta nufi gida da saurinta.
Tana shiga cikin gidan ta girgiza ta sake rikid'a ta koma mutum,,, sannan ta lallab'a sannu a hankali ta kwanta domin kada wani daga cikin d'iyanta ko mijinta su ganta.....
_Share&Comments_
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 6*
Tana shiga cikin gidan ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma mutum wato ainahin siffarta,,sannan ta lallab'a sannu a hankali ta kwanta domin kada wani daga cikin d'iyanta ko mijinta ya ganta..
Washe gari tunda safe Inna Talatu ta tashi ta share gidan tsab,,, sannan ta aza tukunya saman murhu ta zuba ruwa ta barta nan wuta na ci bal bal bal harta dad'e saman wuta,, bayan ruwan sun tafasa ta d'auko gunba ta dama kunu,,, sannan ta d'auko kaskon suyar k'osai ta aza saman wuta tareda sanya mangyad'a a cikin kaskon. Nan da nan ta shiga cikin d'akin ta d'auko k'ullun k'osai ta fara suyar k'osai cikin natsuwa da kwanciyar hankali,, k'amshi sai tashi yakeyi yana game gidan baki d'aya,, haka dai Inna Talatu ta cigaba da aikinta tana wak'e wak'enta irin na mutanen da,, daga ganin yadda takeyin aikin tana cikin nishad'i da farin ciki sosai,, ta jima sosai tana suyar sannan ta kammala ta fissuwa kaskon saman wuta ta aje gefe,, tareda kashe wutar murhu..
Tana gamawa ta d'ebo ruwa a famfo ta shige toilet domin tayi wanka,, bata jima da shiga wanka ba saiga Malam Mamman ya fito daga cikin d'aki yana gugar bakinsa da asuwaki,, shi ma yaje famfo ya d'ebi ruwa a bokiti domin yayi wanka ya tsaya yana jiran fitowar Inna Talatu..
Ta jima sosai tana yin wanka sannan ta fito daga cikin toilet,, Malam Mamman ya dubeta yace "har kin fito daga wanka Talatu? ".
"Eh mana na fito har na gama had'a karin safe ".Inji Inna Talatu MAYYA.
Malam Mamman yace "to yayi k'yau gaskiya kinyi sauri sosai,, dan Allah kafin in fito ki tabbata kin had'amin komai nawa karin kumallo ".
Inna Talatu tace "to Mamman karka damu yanzu nan zan had'a maka komai ".
"na ko gode miki sosai ".Cewar Malam Mamman tareda shigewa cikin toilet,, domin ya tsabtace jikinsa yaje wurin sana'arsa..
Inna Talatu kuwa wucewa tayi cikin d'akinta tana shafa man shafi,, bayan ta gama komi ne ta sanya tufafinta masu dama dama ,,,sai alokacin ne Inna Talatu ta lura da bata tayar da Gwamma ba daga barci,, ta je ta tasheta daga barci sannan ta juya ta nufi hanyar d'akin da Lawwali yake kwance,, ta tayar dashi daga barci tana zaginsa saboda haushinshi da takeji sosai ,,Lawwali ya tashi yana wuru wuru da idanu ya duk'ar da kanshi k'asa yana sauraren irin zagin da Inna Talatu ke masa akan rashin so..
Bayan ta gama zaginsa ta fito daga cikin d'akin tayi cikin d'akinta,, ta iske har Gwamma ta gama karin kumallo,, shi ma Malam Mamman har yasha kunun da k'osai ya shirya yayi wurin neman na kansa,, Inna Talatu ta samu wuri ta zauna saman kujera ta fara cin k'osai tana shan kunu cikin natsuwa da nishad'i,, bayan ta kamalla cin abinci ne ta dubi Gwamma cikeda matuk'ar k'aunar d'iyarta tace "Gwamma babanku ya fita ne,,, ina fatar kin k'oshi sosai babu abinda kikeso? ".
Gwamma tace "Eh ya fita Inna kuma ni a k'oshe na ke,, babu abinda nake buk'ata ".
"babu damuwa d'iyar Inna ".Inji Inna Talatu.
Lawwali ne naga ya shiga cikin kitchen ya d'ebo kunu da k'osai cikeda fargaba da matuk'ar tsoron Innarsa,, zullumi da fargaba ne suka bayyana k'arara a saman fuskarsa,, duk abinda yakeyi Inna Talatu tana lura dashi sai dai bata ce dashi ci kanka ba yaja k'afafunsa ya yi cikin d'akin da ya kwanta barci..
Su kuma Inna Talatu da Gwamma suka cigaba da firarsu cike da tsananin k'aunar juna da wasa da dariya,, babu abinda suke yi sai shewarsu da kuma yin muguwar dariya ta yadda ko wanda yake waje zai iya jiyo dariyarsu da surutunsu..
Shi dai Lawwali yana nan lab'e cikin d'aki bayan ya gama cin abinci,, ya kwanta yayi shiru yana tunani can naga yana zubar da hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa kamar marayan da bayada uwa ko uba,, ayadda na fahimta Inna Talatu ta tsaneshi bata sonshi hmmm wai kamar ba ita ta haifeshi da cikinta ba,, ko da yake ba abin mamaki ba ne sau da yawa iyaye su kan tsani 'ya'yansu akan *SON ZUCIYA* da hujjar banza..
**********************
Ab'angaren Lado kuwa kafin gari ya waye sosai ya farfad'o daga dogon suman da yayi,,,, ya tashi tsaye yana kakkab'e jikinsa Sannan ya nufi cikin gidansa,, ya shiga da sallama matarsa Hassi ta amsa mashi tareda yi masa sannu da zuwa,, domin ita azatonta daga masallaci ya fito tana surfen hatsi ta ga Lado ya nufi randar ruwa ya d'iba a cikin buta yana arwala,, bayan ya gama ne ya shiga cikin d'aki ya shimfid'a sallaya yana sallah..
Hassi ta daina surfen da takeyi tayi tsaye sakatoto kamar wawuya,, tana ta mamaki da al'ajabi akan mijinta,, tana ta addu'ar Allah yasa ba wani abu na cutarwa ba ya gigita mata miji ba ya fita cikin hayyacinsa..
Bayan Lado ya gama sallah ne ya fito waje wurin matarsa,, Hassi ta kalleshi cikeda matuk'ar tsoro da gigicewa tace "Lado lafiya naga ka sakeyin wata sallar asuba bayan wadda kayi a masallaci? ".
Lado ya d'ago jajayen idanunsa yaja wani dogon numfashi,, sannan yace mata "aike yau na auna arzik'i da tuni sai dai a kawo miki gawa ta na mutu,, sai dai kiyi takaba ki sake sabon aure Hassi ".
"Subahanillah!!! Ta ya hakan ya faru? Inji abin da sauk'i Lado ".Tace cikeda matuk'ar tashin hankali da zullumi..
Lado ya kwashe labarin komai gameda karyar daya had'u da ita,, da irin azabobin da aka gana masa da kuma sihirin da tsafin da ya gani karyar ta aikata,, babu abinda ya b'oye mata na dangance abinda ya faru.
Hassi ta buga k'irjinta da k'arfi! Tace "karya fa kace daga zuwa wurin yin fitsari ".
Yace "Eh mana karya ce na gani ".
Tace "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! In dai har karya ka gani to babu shakka *MAYYA CE* ka had'u da ita Lado,, wayyo Allah Allah yasa kada ta cutar da kai na shiga uku na lalace ni Hassi! ".
Lado yace "mayya kuma ni ina ni ina mayya Hassi,, ki rabani da shirmenku na mata kunfi kowa shegen tsoro da koke koke ".
Hassi ta fashe da kuka mai cin rai tace "ba wani koke koke sai gaskiya,, mijina ka yarda da maganata wallahi *MAYYA CE* ta tare ka kan hanya ".Tana k'ara gunjin kuka sosai..
"ni kinga tafiyata idan kika daina kuka zuwa anjima zan dawo,, kinzo kinata cika ni da surutun banza mtsssss! ".Inji Lado yaja k'afafunsa yayi wucewarsa yana ji nini..
Ya bar Hassi zaune tana ta kukan damuwa da fargab akan yadda abin zai iya kasancewa,, saboda har cikin zuciyarta da jikinta ya bata abinda ya had'u dashi ba alkhairi ba ne.....
_Share &Comments_
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 7*
***Saboda har cikin zuciyarta da jikinta ya bata abinda Lado ya had'u da shi ba alkhairi ba ne,, kuka kawai takeyi mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro,, ta jima tana hawaye harta gaji da yin kuka sannan ta shige cikin d'akinta domin har kanta ya fara ciwo akan damuwa..
Lado kuwa yana fita bai zarce ko'ina ba sai cikin kasuwa rumfar da abokinsa yake zama,, yana zuwa yayi sallama Idi ya amsa masa sannan sukayi musabaha da juna,, Lado ya zauna saman benchi kusa ga Idi sannan yace "Abokina ya kasuwar? Ina fatar dai komai yana tafiya dai-dai ".
Idi yaja dogon numfashi yayi ajiyar zuciya yace "Alhmdlilah Lado komai dai-dai,, ina ka fito ne yanzu? ".
"gida na fito kai dai na baro Hassi can tanata koke koken banza,, ganin nayi ta dameni da kukan banza shiyasa na fito nabar mata gidan ".Inji Lado.
Idi yace "kai kuwa abokina baka k'yauta ba taya zaka baro iyalinka cikin damuwa,, baka tsaya ka saurari abinda ya sanyata kuka ba,, kai wa ne irin mutum ne kai Lado ".
Lado yace "ba haka ba ne Idi akan wata 'yar magana ce dana gaya mata,, maganar bata taka ka ra ta karya ba shi ne ta ke kuka ".
"to wannan wa ce irin magana ce da ta sanyata kuka nan da nan? ".Cewar Idi yana jimamin maganar..
Lado yace "yanzu kuwa zan baka labarin abinda ya faru dani jiya abokina ".Ya kwashe labarin komai abinda ya faru da shi,, da kuma irin abubuwan da karyar tayi masa na mugunta iri iri daban daban ya gaya masa ..
Bayan ya gama gaya masa labarin sai Idi ya dubeshi cikin jimami da tausayawa,,, yace "Abokina hak'ik'a ka ga tashin hankali da bala'i a daren jiya,, ina rok'on Allah ubangiji ya tsayar nan yasa abin ba mai cutarwa ne ba,,, amma fa Hassi tana da gaskiyarta saboda mayyu suna iya komawa kowace irin halitta na dabbobi irinsu karya,, ma ge,, rago,, jaki da dai sauransu,,, saboda haka ka daina ganin laifinta ".
Lado yace "haka ne gaskiya amma duk abinda Allah ya tsara zai samu bawa ,,babu mahani sai ya same shi ni na yarda da k'addarata duk abinda ya sameni daga Allah ne ba daga wani ba ".
"tabbas maganarka haka ta ke Lado,,, Allah ubangiji ya tsare mu daga shairin mugayen mutane da aljannu,,, yasa kuma mu dace baki d'ayanmu ".Inji Idi cikin sanyin jiki da damuwa.
Lado yace "Amin abokina ".
Suka bar firar nan suka fad'a firar kasuwanci da kuma abubuwan da ke faruwa a cikin duniyarmu,,,, babu abinda ke tashi sai muryarsu da dariyarsu cikeda matuk'ar k'aunar juna da amintaka da junansu..
***** ***** ***** ***
***Washe gari da safe misalin k'arfe 11:00am na safe,, bayan Malam Mamman ya fita zuwa kasuwa wurin sana'arsa,,,, Inna Talatu ce ta aiki su Gwamma da Lawwali su sayo mata kayan miya kasuwa,,, daga nan zuwa kasuwa da k'afa akwai nisa sosai,,, bayan sun wuce ne Inna Talatu ta fissuwa fa rar da ta saka cikin jakarta jiya da dare,, tana cirowa ta je ta aje fa ra wurin tulun ruwa masu sanyi da ya ke gefen filin gidan,, tana aje fa ra (grasshopper) sai naga fa ru (grasshoppers )masu yawa sosai. Ta aje su kusan wuri guda ashe dai duk kurwar mutanen da Inna Talatu ta kama ne domin ta cinyesu,, ta samu wuri ta zauna tana ta sambatun sihiri da tsafi idanunta sunyi matuk'ar ja kamar garwashi,, gashin jikinta ya fito yayi zago zago kamar dodanniya,,, gashin kanta ya koma fari fat kamar tsohuwa..
Hak'oranta suka yi zago zago kamar gatari,, nan da nan naga ta d'aga hannunta sama tana ta tsafi ta jima tana yi sai naga anyi wata irin mahaukaciyar tsawa! Ta bayyana ratsatsatsa ratsatsatsa fasss fasss fasss !!!Gidan ya kama girgiza komai na gidan ya kama rawa da girgiza da sauri da sauri,,, wani bak'in hayak'i ne yazo wurin Inna Talatu yana ta zagayarta har tsawon minti talati,, sannan ya daina Inna Talatu tasa hannunta fartuna zagal zagal,,, ta yi amfani da wutar da ke fitowa daga cikin bakinta ta d'auko fa ru(grasshoppers) guda biyar tana gasa su da wutar bakinta ..
Kuwwa da kururuwa kawai kurwar sukeyi da k'arfi! Har ma kana jin kukan mutane sosai kawai ke tashi ya cika gidan gaba d'aya,,, hayak'i duk ya gauraye gidan!. Inna Talatu tana gamawa ta sa fa run cikin bakinta ta lak'umesu ba tare da b'ata lokaci ba,, har wani gurnani da nishi takeyi cikeda matuk'ar jin dad'in naman da ta keci na mutane,, tana gama ci ta nufi wurin murhun wuta sai naga wasu fa ru masu yawa ta ajesu nan..
Wai ashe mayyu idan suka kama kurwar mutune,, zasu mayar da ita fa ra ko kaza ko k'aton rago da dai sauran dabbobi iri iri daban daban da suke mayar da mutane..
Idan mayyu suka kama mutum suka mayarda kurwarshi fa ra ko kaza,, za suyi ma fa rar tsafi domin kada ta tashi ta je ko'ina ma'ana ta tsaya a inda anka ajiyeta,, sai mayyar ta ajeta wurin tulun ruwa masu sanyi sai kaga jikin wanda aka kama yanada matuk'ar sanyi sosai,, idan kuma aka aje fa rar wurin murhun wuta zaka samu jikin wanda mayya ta kama yayi zafi sosai kamar garwashin wuta. Wasu kuma suna aje kurwar saman gidan tururuwa,, shi kuma zai ji kamar ana sukar jikinsa da allura.
Wasu kuma kaza suke mayar da kurwar mutum su je su saisuwa,,, su samu kud'i to fa ana yanka kazar nan shikenan mutum zai mutu har lahira,, wasu kuma rago suke mayar da kurwar mutum su je can kasuwa su sai suwa musamman ga sallar layya,, xa'a ga mutane suna ta mutuwa to akwai mutuwar Allah akwai wadda sanadiyyar mayya ta maida shi rago ta sai suwa idan aka yanka ragon sai mutum ya mutu,, batare da ansan *MAYYA CE* ta kamashi ta cinye ba..
Akwai abubuwa da dama da mayyu sukeyi fiye da wad'anda na ambata,, addu'a ce kawai mafita agaremu 'yan uwana musulmai,, amma maganar gaskiya mayyu sunyi yawa a k'asarmu ta hausa ba yaran ba,,,ba manya ba tsofaffi,, budare,, samari maza da mata kowa a cikin wannan zamanin zaka iya samunshi maye _(Allah ubangiji yayi mana mafita da kuma maganin abinda bamu iya yima kanmu )_..
Bayan Inna Talatu ta gama cin naman mutanen da ta kama,,, ta samu ruwa masu sanyi ta sha ta yi gatsa..
Sannan ta samu kujera k'arama ta zauna tana dama fura cikin roba,, sai wani gyad'a kai takeyi kamar ba ita ba ce ta gama cin naman mutane ba!.
Babu jimawa sai ga su Gwamma sun dawo daga inda ta aikesu,, suna isowa suka d'auko tabarma suka zauna tare da aje kayan miyan gefe cikin bak'ar leda.
Alokacin ne Gwamma ta dubi Inna Talatu MAYYA tace "Inna mun dawo ga aiken da ki kayi mana fa ".
Inna Talatu tace "na ga ne ku d'iyar albarka,, Allah dai yayi muku albarka Gwamma ".Tana cigaba da dama furarta cikeda matuk'ar kwanciyar hankali da jin dad'i.
"Amin Inna ".Inji Lawwali.
"ku tashi ku shiga cikin d'aki ku ci abinci idan na gama dama furar zan sha,, in rage muku sauran amma kuyi wanka kafin ku ci abincin ".Cewar Inna Talatu.
Suka ce atare "to Inna ".Suka tashi tsaye suka shige cikin d'aki suna ta dariyar murna da farin ciki..
**** *** **** **** ***
Acan cikin kasuwa kuwa Malam Mamman ne zaune da Mande suna fira cikin farin ciki da nishad'i sosai ..
Malam Mamman ya dubi Aliyu Mande yace masa "kasan wani abu kuwa Mande ?".
"sai ka fad'a Mamman ina jinka ".Inji Mande mai shago..
Malam Mamman yayi doguwar ajiyar zuciya sannan yace "kwata kwata al'amarin Talatu yana bani mamaki da tsoro,, duk ta chanza kwanakin nan ta zama kamar ba itace mu ka shafe tsawon shekaru muna soyayya ba,, sannan kuma bayan munyi aure muna zaune zaman lafiya babu mai jin kanmu,,, amma yanzu ta tsiro da wani hali mara k'yawo bata ganin girmana ko mutuncina,, zagina tareda rashin kunya kawai takeyi min,, ni yanzu na rasa yadda zanyi da ita wlh sai na ke ganin kamar maganar mutane ta fara tabbata Talatu ta zama abin k'yama wato mayya ce ".
Mande yace "Subahanillah!! Zato zunubi ne koda ya zamo gaskiya ne kada ka zamo mai d'aukar gulma da jita jitar mutane,, kuma ka ga duk k'azantar da ba ka gani da idonka ba tsabta ce,,, ni dai shawarar da zan ba ka amatsayina na amininka kuma abokinka kayi hak'uri kayi hak'uri domin Allah yana tare da masu hak'uri,, komai da kake gani a rayuwa sai mutum yayi hak'uri sannan ya ke zamowa wani abu a rayuwa,, Annabinmu Muhammad (S. A. W) wanda yafi kowa daraja a duniya an zagesa an dukesa an jefeshi da duwatsu wanda sanadiyyar haka nan saida kanshi ya fashe da jini amma yayi hak'uri,, balantana mu da bamu kowa fa ce bayin Allah,, kaje ka cigaba da hak'uri da ita komai na duniya yana da farko yana da k'arshe zaizo ya wuce kamar ba'a yi sa ba ".
Malam Mamman yace "nagode sosai da shawararka abokina hak'ik'a kai mutum ne na gari,, wanda ya san abinda ya kamata insha Allahu zanyi amfani da shawararka".
"yauwa Mamman ka k'ara hak'uri akan hak'uri duniyar yanzu guda nawa ta ke,, lamarin duniya d'an hak'uri ne wata rana sai labari,, Allah ubangiji yasa mufi k'arfin zuciyarmu ".
Malam Mamman yace "tabbas haka ne gaskiya,, amin amin ubangiji Allah ya amshi bakinka ".
"amin amin ".Inji Mande.
Haka dai suka cigaba da firarsu cike da tsananin yarda da juna da shak'uwa,,, abotakarsu zad sha'awa da burgewa ta yadda suke ba ma juna shawarar k'warai batare da wani munafurci ba ko hassada ba.. ....
_Share &Comments_
[6/21, 9:55 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 8*
***Bayan Malam Mamman da Mande sun gama firarsu ne,, sai kowa ya maida hankali kan sana'arshi suka cigaba da lura da jama'ar da ke zuwa wurinsu da kuma masu kai kawo,, domin gudun sata ko afkuwar wani abu mara k'yawon gani..
**** **** **** ****
***Ab'angarensu Lado da Idi abokinsa kuwa bayan Lado ya jima sosai a wurinsa suna fira,,, to zuwa wani lokaci mai tsawo yayi masa sallama zai wuce gidansa,,, Idi yaji dad'i sosai na ziyarar da abokinsa ya kawo masa ya d'auko sabulun wanka da na wanki yace akaima Hassi,,,,Lado yak'i amsa sai da Idi ya nuna matuk'ar b'acin ranshi sannan ya amsa da k'yar yana yi masa godiya sosai,, Idi ya nuna masa babu komai ai yi ma kaine kuma maida k'yauta baya ne ka tsinceshi acan gaba ne,, Lado yayi masa sallama sannan ya juya zuwa hanyar gidansa cikeda matuk'ar sanyin jiki..
Hassi ce zaune saman kujera k'arama tana cin abinci,, bayan ta gama kukanta tun d'azu babu abinda takeyi sai tunani da zullumin maganar Lado,,, ta ga Lado bai yarda da maganarta ba balantana ayima abun tufkar hanci shiyasa ta bar abin cikin ranta,,,, da niyar gobe zata tambayi Lado iznin zuwa gidansu ta sanar da iyayenta duk abinda ake ciki..
Haka dai ta cigaba da sak'a da warwara a cikin zuciyarta,,, tana cin abincinta sosai can naji takun tafiyar Lado ya shigo da sallama a bakinsa,, hannunsa rik'e da ledar sabulun da Idi ya bashi,,, Hassi ta amsa masa sallamar tareda juyar da kanta gefe saboda a d'azu taji matuk'ar haushin akan yadda yak'i yarda da maganarta,,, tareda da nuna mata halin ko in kula da tana kuka akan abinda ya faru..
Lado ya d'auko tabarma ya shimfid'a kusa gareta,, sannan ya zauna yana fuskantarta yace "Innar Na'ima dan Allah kiyi hak'uri ki daina fushi dani,,, in dai akan abinda ya faru ne wlh na yarda da maganarki na amince muje gidanku anemi mafita ".
Hassi ta juyo tana kallonsa tace "hmm naji komai ya wuce amma ni bance dole sai ka yarda da maganata ba ".
"ki dai yi hak'uri Allah yana tare da masu hak'uri Hassi,, alal hak'ik'a nasan akwai mayyu a cikin garin nan addu'a kawai ce mafita akan kowane lamari,, ina Na'ima take ne? Na ji banji muryarta ba ".Inji Lado cikeda lalama.
Hassi tace "haka ne gaskiya,, Na'ima an aiko daga gidanmu an d'auketa ".
Lado ya bata ledar da ke hannunsa sannan yace "to ya yi k'yau kice yau zasu sha rashin ji da b'arna,, wannan ledar da nazo da ita Idi yace a baki ".
Hassi ta bud'e ledar ta ga sabulun wanka da wanki,, murmushi kawai takeyi can ta nisa tace"ai kuwa mun gode sosai Allah ubangiji yabar k'auna da zumunci,,, sannan da kake cewa Na'ima rashin ji gareta ai acan gidanmu ustaziya ta ke zama,, idan ba haka idan tayi musu b'arna Mariya kashi take bata saboda ita babu ruwanta da yaro "..
"Amin ya rabbi matata,, ai kuwa idan ta bugar min Na'imata zamu had'u gobe ni da ita".Cewar Lado.
Hassi ta yi dariya tace "ina zaka ga Mariya kuma? Balantana ka had'u da ita ".
Lado yace "gidan zamuje gobe da ni da ke idan Allah ya yarda ".
Hassi tace "Allah ya kaimu gobe lafiya ".
"Amin amin ".Cewar Lado..
Hassi ta mik'e tsaye ta shiga cikin d'akinta,, ta kawo masa abincinsa da ruwa masu sanyi cikin jug ta aje gabansa,,, Lado ya wanke hannunsa da ruwa sannan yayi bismillah ya fara cin abincinsa cike da natsuwa da walwala,,, Hassi tana gefensa sai murmushi takeyi masa cike so da k'auna..
*********************
Malam Mamman ne zaune yana wankin kayansa ga Inna Talatu xaune gefe tana kallonsa,,, sai harararsa takeyi tana yatsina fuskarta cikin gadara da nuna isa,,, can Malam Mamman ya dubeta duba na fahimta da natsuwa yace "Talatu wai mi ye dalilin abubuwan da kike yimin,,, mi nayi miki ne? Na ga kina yimin wasu abubuwa wad'anda bana jin dad'insu ".
Inna Talatu tace "hmmmm kai dai Mamman kanada matsala,,, ka sha tambayata nace baka yimin komai ba kawai rayuwa ce ta canza ,,amma kazo kana son matsa min da surutu ".
Malam Mamman yace "ba damuwarki nake sonyi ba,,, ina son zamanmu ne ya koma kamar da babu tashin hankali ko hayaniya a cikinsa,, kuma bansan abinda nayi miki ba Talatu duk kin tsane ni kamar auren dole akayi miki tun farko bada son ranki ba akayi auren ba kina sona ina sonki ".
"hmmmmmmm Mamman ka gama tatsuniyar taka to bari kaji! Ni fa yanzu ba da ba ne babu shegen da ya isa ya takura min,,, saboda ayanzu bana tsoron kowa ciki kuwa har da kai domin na yi wuya na isa yanka! ".Inji Inna Talatu.
Malam Mamman ya cigaba da wankinsa yana shanyawa ga igiyar wanki,, bayan ya gama shanya kayansa ya dubi Inna Talatu cikin tsananin b'acin rai da takaicin maganarta,,, yace "Talatu ina son ki san wani abu guda d'aya naji ke baki tsoron kowa,, karki manta ni fa mijinki ne aljannarki tana k'ark'ashin tafin k'afata idan na d'aga ki shiga ciki,,, idan na ta ke ba zaki shiga aljanna ba,,, ya kamata ki san irin maganganun da za ki gaya min ba wai ki dinga yimin magana tsauri tsauri ba kamar ke ce mijin ni ne matar,,, mace ta iya magana da tausasa kalamanta zuwa ga mijinta ba wai ta dinga sako magana duk yadda ta gadama ba,, ni fa bari in gaya maki kin isheni gaskiya! Ina raga miki ne saboda darajar 'ya'yan dake tsakaninmu ba wai domin ina jin tsoronki ba ".
"ahayyeh ahayyeh nanayeh yau naji maganar banza da yofi! Ai ban san kana jin haushina ba Mamman sai kayi min mugun bugu ka sakeni,,, sannan da kake cewa sai ka d'aga k'afarka sannan in shiga aljanna to bana so ka take!!! Yanzu idan na mutu kazo ka kaini cikin wuta to wlh rashin kwanciyar hankali da rashin zaman lafiya yanzu aka fara a cikin gidan nan ".Cewar Inna Talatu cikeda matuk'ar masifa da son tashin hankali.
Malam Mamman yace "ba ni zan kaiki wuta ba mugun halinki ne zai kaiki cikin wuta,,,, saboda haka to tunda abin naki bana arzik'i ba ne,,, ba zai yiyu in ta zama cikin rashin kwanciyar hankali da tashin hankali ba saboda haka ki saurareni da k'yau Talatu aure zan k'ara yi! ".
Dummmm gaban Inna Talatu ya buga da k'arfi!,, zuciyarta ta girgiza hankalinta yayi k'ololuwar tashi sosai,,,babu abinda zuciyarta keyi sai bugawa da k'arfi da k'arfi amma dolenta ta tattaro natsuwarta da dauriya ta sanyama zuciyarta,, saboda kada Malam Mamman yayi saurin gano ta firgita ko tsorata..
Cikin dauriya da nuna rashin tsoro Inna Talatu tace "Mamman kenan k'aryarka ta sha k'arya tunda dad'ewa sosai baka tashi cewa zaka yimin kishiya ba sai yanzu! To wlh daga yau ka k'ulla aure da masifa da tashin hankali,,, kuma wannan auren ba zai tab'a yiyuwa ba! Amma dan Allah ka gwada ka gani idan ka na shakkar maganata ba zata iya yiyuwa ba,,, zan nuna maka ni kishina yafi *KISHIN JAHILCI*".
Malam Mamman yace "mi zaki iya yi ne Talatu ai ko haukacewa zakiyi kibi duniya,,, sai na k'ara aure Insha Allahu idan kika ga banyi ba to mutuwa na yi mahaukaciya wadda batasan ciwon kanta ba ".
"mahaukata dai ga fili ga mai doki nan sauran sukuwa,,, kayi auren in gani ba sai kana raye zakayi auren ba ko? Zan nuna maka ni na haifu ga iyayena ".Inji Inna Talatu cikeda matuk'ar masifa..
"duk abinda zakiyi Allah ya fiki Talatu aure ne dai sai nayi,,, ina raye zaki gani da idanunki! ".Cewar Malam Mamman yaja takalminsa ya barma Inna Talatu gidan tana ta fad'a da tsinema Malam Mamman..
Inna Talatu ta kama yin fad'a da zage zage kamar ta ari bakin kura,,, bakinta har kumfa yake fitarwa akan bala'i idanunta suka rikid'a sukayi jajir saboda tsabar tashin hankali da bala'in da suka bayyana k'arara akan fuskarta..
Ta sha alwashin babu ita babu zama da kishiya har abada,,, ta yanke shawarar irin matakin da zata d'auka a cikin zuciyarta!!!.
**********************
***Washe gari da da rana misalin k'arfe hud'u 4:30pm na yamma,,, Lado da Hassi suka shirya suka je can gidansu Hassi ziyara,,, bayan sun je gidansu Hassi lafiya k'alau suka iske Baba Abubakar da Inna Lami sun gaishesu cikin girmamawa,,, suka amsa musu fuskarsu a sake cikin fara'a da murna sosai. Mariya da take gefe tareda Na'ima ta gaisar da su Hassi,,, suka amsa mata cikin sakin fuska da walwala,,, Mariya ce ta d'auko tabarma ta shimfid'a musu suka zauna tare..
Hassi ce ta duk'ar da kanta k'asa tace "baba mun same ku Lafiya ".
"lafiya k'alau kuka same mu Hafsa ".Cewar Baba Abubakar.
Inna Lami tace "ina fatar kina zaune da mijinki lafiya Hafsa? ".
Lado yayi saurin yin magana yace "ai Hassi 'yar aljanna ce Inna tana yimin ladabi da biyayya gwargwadon iyawarta,,, bata son b'acin raina ko fushina ko kad'an ban tab'a ganin mace mai k'yawon hali ba irin Hassi ba,,, duk abinda nake so shi ta keyi min koda ace ita bata so Baba ai ni banida abinda zan biya ku dashi na aura min Hafsa da kukayi,, sai dai inyi muku addu'a akan Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairi ".
Mariya tace "Amin ya rabbi ".Cike da tsananin jin dad'i akan yadda aka yabi halayyar 'yar uwarta.
Baba Abubakar da Inna Lami babu abinda sukeyi sai murmushi tsantsar farin ciki ne da jin dad'i yake bayyana a fuskarsu,,, can dai Baba Abubakar yace "na ji dad'i matuk'a akan irin yabon da mijinki yayi miki Hafsa,,, hak'ik'a na k'ara tabbatarwa yau ba ki yassuwa tarbiyar da nayi miki ba,,, kai ma Lado nayi matuk'ar farin ciki akan yadda ka rik'eta amana,,, Allah ubangiji yayi muku albarka ".
Hassi tace "Amin Baba amma akwai maganar da nake son in gaya maka ".
"wa ce irin magana ce Hafsa? fad'i ina saurarenki".Cewar Baban.
Hassi zata bud'i baki ta yi magana kenan! Kawai sai naga Lado ya fad'i k'asa kwance yana birgima kamar mahaukaci,,, babu abinda ke fita cikin bakinsa sai jini mai kamar tsokar nama gunduwa gunduwa,,, yana shure -shure da kakarin mutuwa!
Baba Abubakar da Inna Lami babu abinda suke fad'a illa ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Cikeda matuk'ar tashin hankali da rikicewa,,, Hassi kuma kuwwa ta yi da k'arfi tana kuka tana cewa "wayyo Allah wayyo kaina! Shikenan ta kashe min mijina,, rayuwata tazo k'arshe ni Hassi ".Wa ce ce ta kashe miki mijinki ".Inji Inna Lami cikeda matuk'ar tashin hankali!.
Hassi ta sakewa cewa "ta kashe min mijina! ".Ta fasa wata gigitacciyar k'ara da kuwwa da k'arfi! Ta fad'i k'asa ta sume,,,ai kuwa Inna Lami da Mariya suka sake rikicewa Na'ima banda mahaukacin kuka babu abinda takeyi,, Baba Abubakar da ya ke kusa ga gawar Lado shi ma duk ya rikice ya ya mutse kamar ba babban mutum ba.
Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Kawai yake ambato cike da tsananin rud'ewa da d'imaucewa.....
_Share&Comments_
[6/21, 9:56 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 9*
Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Kawai yake ambato cike da tsananin rud'ewa da d'imaucewa..
Hankalinshi ya yi k'ololuwar tashi duk ya gigice da rikicewa,,, Inna Lami ce yayi mata alama da hannu ta d'ebo ruwa a cikin buta ko kofi ,,, ta nufi randar ruwa da saurinta cikin matuk'ar tashin hankali tana ta kukan k'unci da bak'in cikin rayuwa,,,Mariya kuma sai jijigar jikin Hassi takeyi tana zubar da hawayen tausayin kansu da bak'in ciki.
Na'ima tana gefenta tana kuka sai cewa take yi "Inna,, Inna ci ta ci dan anya (Inna ki tashi dan Allah) ".
Inna Lami ta kawo ruwan da saurinta Malam Abubakar ya amshi ruwan ya yi addu'a mai tsawo,,, sannan ya watsa ma Hassi rabin ruwan ya juyo wurin Lado ya watsa mishi ruwan shima,, sannan yayi umurni da Mariya ta shige da Na'ima cikin d'aki ,,dole ne yasa Mariya taja hannun Na'ima ta shige da ita cikin d'aki ba domin ranta yaso ba saboda ita taso ayi komai gaba gare ta,,, ba sai ta tashi ba amma yata iya dole ta bi umurnin mahaifinta..
Bayan shigerwarsu Mariya cikin d'aki ba,,,, Malam Abubakar ya dubi Inna Lami yaga tana zubar da hawaye yayi mata nuni da ta matso kusa gareshi,,, Inna Lami ta matso kusa gareshi jikinta yanata rawar tsoro da fargabar abinda ke iya faruwa! Malam ya juyo da fuskar Lado ta yadda zasu b'ullo ma lamarin cikin sauk'i,,, yana juyo da fuskarshi yaga duk idanun Lado sun k'ak'k'afe ga kuma jinin da ya b'ata gaban rigarsa babu k'yawon gani ko kallo,,, yasa kunnenshi ya tara a hancin Lado yaji ya ko zaiji yana numfashi..
Ya kai tsawon minti goma yana saurare ko zaiji fitar numfashin Lado amma shiru,,, kamar an shukka dussa ganin haka ne Malam ya d'ago idanunsa wad'anda ruwa sun taru ciki sosai ya dubi Inna Lami cikin matuk'ar sanyin jiki da damuwa,,, yace "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Kulli nafsin za'ikatul mautt hak'ik'a Allah ubangiji yayi ma Lado rasuwa Lami! ".Gaban Inna Lami ya buga da k'arfi rassssss! Fuskarta na bayyanar da tsoro da tsananin tashin hankali,,, dak'yar ta bud'i baki tace "Subahanillah! Allah ubangiji ya jik'anshi da rahama yasa ya huta,,, mu kuma idan tamu tazo yasa mu cika da imani Malam ".
"Amin Lami ".Cewar alokacin ne yasa hannunsa ya shafe idanun Lado..
Inna Lami tana shesshekar kuka tace "Malam fa ya kamata kaje ka sanar da iyayensa da mutane,,, domin ayi masa wanka akaishi makwancinsa ".
"tabbas haka ne yanzu nan kuwa zan je in sanar da iyayensa da kuma mutane ".Inji Malam Abubakar ya fad'a tare da mik'ewa tsaye,,, ya kama hanya ya wucewarsa zuwa waje..
Inna Lami na zaune ta zuba uban tagumi tana kuka mai ban tausayi da tarin damuwa,,, can Hassi taja numfashi tari ne ya sark'eta ta falko daga suman da ta yi,,, Inna Lami tayi hamdala cikin zuciyarta ta k'walama Mariya kira,,, Mariya ta shek'o da saurinta Inna Lami tace ta d'ebo ruwa aba Hassi ta sha taje da saurinta ta d'ebo ruwa a randa masu sanyi aka bama Hassi tasha,,, sai sannu kawai sukeyi mata cike da matuk'ar tausayawa. Bayan ta sha ruwan ne Hassi ta kwanta babu jimawa barci ya kwasheta,,, Inna Lami ta dubi Mariya tace "tashi ki shiga cikin d'aki kada Na'ima ta biyoki waje,,, saboda ta yi k'arama da ganin wannan tashin hankali ".
"ai Inna Na'ima tun d'azu ta yi barci fa,,, shiyasa ma kika daina jiyo kukanta ".Cewar Mariya..
Inna Lami tace "to Allah ya k'yauta ".
Mariya tace"amin".Tana rufe bakinta sai ga sallamar mutane su hud'u,,, sun shigo cikin gidan Inna Lami ce ta amsa musu sallama, Malam Abubakar yayi musu jagora har cikin gidan suka d'auki gawar Lado suka fita da ita waje,,, domin aje gidan mahaifinsa ayi masa wanka akaishi gidan gaskiya..
Suna tafiya da gawar Inna Lami da Mariya suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro,,, tausayin Hassi da Na'ima ya k'ara d'arsuwa a cikin zuk'atansu,,, Hassi ta zama k'aramar bazawara yayinda Na'ima ta zama marainiya abar tausayi...
*** *** *** *** *** **
***Anje an yima Lado wanka da sanyashi cikin likkafani,,, anyi masa sallah sannan aka kaishi makwancinsa.. *(Allahu Akbar duniya kenan rai bak'on duniya ,,,mutum ba'a bakin komai yake ba a cikin wannan duniyar mai cike da k'unci da bak'in cikin rayuwa 😭😭)*...
Kwatsam! Bayan mutuwar Lado sai da mutum kusan hud'u suka rasu a rana guda,,, mace uku maza biyu gami da Lado hak'ik'a a wannan ranar mutanen sun shiga tashin hankali da rikicewa! Akan mutuwarsu Lado ko'ina ka diba mutane ne zaune suna bak'in ciki da jimamin rasa 'yan uwansu,,, mata da yara k'anana kuka kawai sukeyi cike da tsananin damuwa da bak'in cikin rayuwa,,, to ya zasuyi wanda yafi sonsu ya k'arbi ran abinsa dama ita duniya haka ta gada hak'uri shi ne kan gaba da komai,,,, shi ne kuma jigon rayuwa ko munk'i ko munso dole wata rana za'a wayi gari babu mu cikin wannan duniya mai cike da k'alubalen rayuwa ".(Allah ubangiji yasa mu cika da imani muna musulmai)...
_Kunga kenan babu abinda ya gagari mayyu,,, sai dai ikon Allah_..
*BAYAN KWANA HU'DU*
***Bayan kwana hud'u da faruwar wannan mummunan al'amari,,, mutane kowa ya cigaba da harakokinshi...
Inna Talatu ta cigaba da musgunawa rayuwar Malam Mamman tareda ci masa mutunci da tozarci,,, kullum kullum da irin kalar walak'ancin da zata masa kowace safiya idan garin Allah ya waye,,, bayada natsuwa da kwanciyar hankali masifar safe daban ta rana daban ta dare da daban,,, bata ganin mutuncinshi da girmanshi ko kad'an. Har takai ta kawo Malam idan zai dawo gidansa har fargaba da tsoronta yake ji,, ta zame mishi ciwon ajali ya rasa yadda zaiyi da ita bayada natsuwa da kwanciyar hankali ko kad'an,,, a cikin kwanakin nan idan kaga yadda Malam Mamman ya rame sai kun tausaya mishi,,, har ta kai ta kawo ko abincin gidan nan bata aje mishi sai dai yaci acan kasuwa gurin masu sayarwa,, amma haka bawan Allah nan yake hak'uri matuk'a da ita,,, ganin yayi tana shirin kashe shi tunda sauran ranshi yasa dole ya fara neman wata bazawara mai suna Laweeza a cikin unguwarsu da aure..
Inna Talatu MAYYA ta ji labarin neman auren Laweeza da yakeyi amma da yake k'usurgumar *MAYYA CE*,,,sannan kuma ta san muguntar da zata k'ulla yasa ko a fuska bata damu ba bale a cikin zuciyarta..
***Wata rana Malam Mamman ne yayi wankansa sannan ya d'auko shaddarsa sabuwa a cikin kayansa yasa,,,, ya feshe jikinsa da turare sannan ya dubi kanshi a madubi yaga ba laifi ya jawo k'ofar d'akinsa ya kulle da padlock,,, ya fito filin gida Inna Talatu tana zaune tana gyaran shinkafar da zata yi tuwo da ita gasu Gwamma da Lawwali zaune gefe suna wasarsu cikin kwanciyar hankali..
Inna Talatu tana ganin irin wankan da Malam Mamman ya d'auka ga k'amshi sai tashi yakeyi na turarensa,,, ta yi masa walak'antaccen kallo mai cike da raini ta ja mugun tsoki mtsssss! Sannan tace "Mamman mai budurwar zuciya ina zaka je? ".Tayi masa tambayar rainin wayo..
Ya juyo ya kalleta da yake yasan tambayar raini ne ta yi masa,,, yayi murmushin mugunta yace "wurin masoyiyata matata mai son farin cikina,,, tana gudun b'acin raina ta iya kalamai masu sanyaya zuciyar masoyi gata da tarbiya da biyayya,,, ga ta d'iyar mutanen k'warai alal hak'ik'a nayi matuk'ar dace da samun mace ta gari Talatu,,, idan kina zuwa zan kaiki gobe ku gaisa da ita saboda tun yanzu ku saba da juna ".
Hali zanen dutse! Hak'ik'a maganganun Malam Mamman sun matuk'ar k'ona zuciyar Inna Talatu,,, babu abinda zuciyarta keyi sai suya rayuwarta idan har tayi dubu to ta b'aci sosai..
Ta bud'i baki tace "Mamman kenan mi kake ci na baka na zuba? Wato bazawarar da kake nema itace mai kirki ni ce mara kirkin ko,,, itace d'iyar mutanen k'warai ni ce d'iyar mutanen banza ko itace wadda ta iya kalamai ni ban iya ba? To ka rubuta a takarda ka ajiye wlh wannan auren muddin ina raye ba zai tab'a yiyuwa ba! Na fika iya shege na rashin mutunci da hatsibibanci ".
"tabbas ta fiki duk abinda na lissafa harda wanda ban fad'a ba ta fiki,,, sannan baki isa ki hanamin k'ara aure ba Talatu ba zaki hana inji dad'i ba kamar yadda kowane magidanci mai mata biyu keji ,,,idan naga kina son b'atamin gida sai in sakeki ki koma gidanku! ".Cewar Malam Mamman cikeda matuk'ar zafin rai da haushi..
Inna Talatu tace "to sai mi idan ka sakeni nifa ba irin wad'annan matan bane wad'anda ake tsoratarwa da kalmar saki,,, so kake ka kawo wata a cikin gidan nan kazo kana iskanci da ita agaban 'ya'yanka kana tab'a mata nono ko,,, bazai tab'a yiyuwa ba nadai gaya maka gaskiya ".
Malam Mamman yace "sai nayi abin nan da bakiso ko na sadu da ita idan har na aureta ai halat na aikata ba haramun ba,,, ke kinyi kad'an ki haramta min abinda Allah ya halat min ba kuma ko mutuwa zakiyi saina k'ara aure! ".
"hmmm haka kace? To mu zuba mu gani ni da kai shege ya fasa,,, wanda yaji tsoro ya janye d'an wuta ne a tsakaninmu".Cewar Inna Talatu cikeda son tashin hankali..
Mal. Mamman yace "mahaukaciya wawuyar jahila! Ai kece 'yar wuta kuma shegiya dama ai mace idan bata biyayya ga mijinta sunanta 'yar wuta,,, kinyi 'k'arama wlh da ki hana min rawa gaban hantsi,, banda lokacin karya irinki! ".Yasa kai yayi tafiyarsa zuwa inda zaije..
"kaine k'aton kare kuma jahili! Wallahi zaka gane bakada wayo ko dabara,, zan nuna muku ni murucin kan dutse ce ni ban fito ba saida na shirya,,, ni ce ajalinku da kai da ita! Hmmmm yaro baisan wuta ba sai ya taka andaiji kunya ana son ayi aure adinga yi mata iskanci da tambad'a yara suna kallo,,, ni ba zan bari a lalata min yarana ba ".Inji Inna Talatu cikin jin haushinsa..
**********************
Malam Mamman naga yazo baki k'ofar gidansu Laweeza ya samu yaro ya aika domin ayi masa sallama da ita,,, can yaro ya fito daga cikin gidan yace masa tana zuwa Malam Mamman ya bashi naira ishirin yaron ya amsa yayi godiya ya wucewarsa yana jin dad'i sosai.
Bayan mintuna kad'an saiga Laweeza ta fito daga cikin gidan tana tafiya cike da yanga da natsuwa,,, tana isowa wurin Malam Mamman ta gaidashi ya amsa cikin fara'a da murmushi..
Nayi duba zuwaga fuskar Laweeza ashe k'yakkyawa ce bak'a ba tilin ba,,, tanada doguwar fuska tareda da dogon hanci ga madaidaicin bakinta,, wanda ya k'ara mata k'yawo sosai..
Malam Mamman ya nisa yace "Lawiza ".
Tace"Na'am ".Tana wasa da yatsun hannunta.
Yace mata "ina son ki bani dama in turo magabatana asa mana rana,,, saboda kinga ni da ke ba wannan ne karo na farko da zamuyi aure ba ke kin tab'a aure harda yaro ni inada mata harda yara biyu,, saboda haka mu ba yara bane da zamu tsaya b'atawa kanmu lokaci ,,,shin miye ra'ayinki game dani kina sona kin aminta naturo magabatana? ".
Lawiza tace masa "na amince amma ina tsoron abinda zaije ya dawo,,, saboda naji ana fad'a agari cewa matarka masifafffar mace ce mafad'aciya sannan kuma ance ana zarginta da maita!.....
_Share &Comments_
[6/21, 9:56 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 10*
Lawiza tace "na amince amma ina tsoron abinda zaije ya dawo,,, saboda na ji ance matarka masifaffiyar mace ce mafad'aciya sannan kuma ance ana zarginta da maita a cikin garin nan,,, kaga kuwa dole hankalina ya tashi sosai in dai domin fad'a ne to abin da sauk'i saboda saina kulata ne zamuyi sa'insa ni kuma ba zan kulata ba idan Allah ya yarda ".
"hmmmm wannan maganar ta maita da akecewa matata tana yi ba gaskiya ba ne,,, wannan zance ne na mak'iya da mahassada wad'anda basu son mutum a rayuwa ko cigaban mutum,,,,lafiyar matata k'alau kawai dai mafad'aciya ce shi ne gaskiyar magana ".Cewar Malam Mamman cikin taushin murya da lallashi..
Lawiza tace "to shikenan na yarda ka turo a sanya mana rana ".
Malam Mamman yace "yanzu naji maganar k'warai Lawizata amma ko gobe ina baki shawarar ki daina yarda da maganar mutane,,, domin su mutane iyawa dasu sai ubangiji duk abinda kakeyi saika samu wanda ya kusheka yakejin haushinka,,,, saboda hassada da bak'in ciki a cikin jinin d'an Adam yake".
Lawiza tace "ai kuwa karka damu komai ya wuce na daina yarda da maganganun mutane,,, ni ke aure ba mutum duk wadda ta kawo tseguminta ko anyi ance zanyi kunne uwar shaggu da ita harta gaji ta k'ara gaba ".
"dako kin k'yauta mana wlh,, sannan karki damu jibi zan turo manyana wurin babanki saboda haka ki sanar da su da wuri,,, ga wani 'yan chanji inbaki farin cikin rayuwata ".Fad'ar Mlam Mamman yana washe mata hak'oransa da suka gogu da aswaki zad sha'awa,,, ya mik'a mata kud'i da kuma bak'ar leda..
Lawiza tasa hannu ta karb'a cikeda matuk'ar kunya da k'aunarsa,,,sannan tace "nagode sosai Allah ya saka da alkhairi ".
Mal. Malam Mamman yace "Amin amin rabin jikina,,, to ni zan wuce gida yanzu ki gaida mutanen gidanku ".(🤣🤣Ka ji su Malam an iya lobaiya da kashe murya).
"zasu ji mijina Allah ya kiyaye hanya ya tsare min kai ".Cewar Lawiza cikeda nuna kulawa da soyayya.
Ai kuwa wannan addu'a da ta yima Mal. Mamman ba k'aramin masifar dad'i yaji ba,, wani irin sanyi ne yabi jinin jikinsa yace "Amin babina ".Sannan ya kama hanyar zuwa gidansa,, ita kuma ta shige cikin gidansu ..
********** ******* ****
***Ab'angaren gidansu Hassi bayan anje ankaisu Lado gidansu na gaskiya shi da sauran mutum hud'u,, da suka rasu rana d'aya..
To bayan Hassi tayi barci mai tsawo daga baya saita falka daga barcin,,, tana tashi da hamma ta tashi daga barci Mariya ce ta d'ebo abinci da ruwa masu sanyi ta kawo mata,, Hassi ta yi bismilla ta fara cin abincinta sai da taji tayi nak sannan ta wanke hannunta ta sha ruwa sosai,,, Inna Lami ce ta had'a mata ruwan wanka ta taimaka mata ta yi wanka sannan aka d'auko kala d'aya tsofaffi daga cikin kayan Mariya aka bata ta saka...
Zuwa anjima da daddare da Malam Abubakar ya dawo gida,, bayan sun kammala cin abincin dare ne Malam Abubakar yayi gyaran murya yace "Hafsa ".
"Na'am baba ".Cewar Hassi cikin mutuwar jiki da fargaba..
Mal. Abubakar ya dubeta cikin tausayinta da tsantsar k'aunar 'yarsa yace "ina so ki saurari abinda zan gaya miki da k'yau,,, ki fahimci maganata cikin natsuwa da kaifin tunani kinsan da cewa komai ya faru da bawa muk'addari ne daga Allah kuma babu wani mahaluk'i a cikin wannan duniya,,, da ya isa kaucewa k'addararsa Allah ya riga ya rubuta a cikin littafinmu duk irin abubuwan da zai samu mutum tun daga farkon haihuwarsa har zuwa mutuwarsa,,,, ana son musulmi na k'warai yayi imani da k'addara mai k'yau ko mara k'yau,,, sannan duk abinda Allah ya baka a matsayin aro na wani lokaci daga baya ya amshi abinsa zakiji ciwo Hassi? ".
Hassi ta gyad'a kai cikin matuk'ar sanyin zuciya da zullumi! Ta bud'e baki tace "a'a baba ".
Malam Abubakar yace "kiyi hak'uri da duk abinda zakiji Hafsa domin Allah yana tare da masu hak'uri,,, ubangijin da ya baki Lado a matsayin miji ya k'addari aurenku ya kuma k'addari samuwar Na'ima a tsakaninku batare da sisinku ba,,, ya amshi ran Lado domin ya fiki sonshi aronsa dama ya baki ".
Hassi tana jin wannan maganar ta fashe da wani rikitaccen kuka mai ban tausayi,,, hankalinta yayi k'ololuwar tashi zuciyarta sai k'una da rad'ad'in zafi sosai takeyi mata ..
Inna Lami ce ta rungumeta tana lallashinta da fad'a mata kalamai masu sanyi a cikin zuciya,, tana cewa "kiyi hak'uri hafsa kiyi ta fad'ar wannan kalma ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Alhumma ajirni fi musibati wa'akhalufni min khari minha,,, da yarda Allah zakiji sauk'i cikin zuciyarki Allah ubangiji ya jik'an Lado ya gafarta masa zunubbansa ".
"kiyi hak'uri yaya Hassi ki daina kuka addu'a kawai ce yaya Lado ke buk'ata a gareki,,, ba kuka ba saboda kukan mai rai akan mamaci azaba ne kuma masifa ne,,, ki tausayawa mana ki daina kuka 'yar uwata saboda nima zaki iya sakani kuka ".Cewar Mariya idanunta sun cicciko da ruwan hawaye..
Inna Lami tace "ki daina kuka ki saurari maganarmu kuma ki fahimcemu Hafsa,,, duk abinda kika gani daga Allah ne sannan ina son ki sanar dani waye kike cewa ta kashe Lado d'azu alokacin da ya fad'i k'asa yana aman jini? ".
Mal. Abubakar yace "tabbas muna son muji wani bayani a cikin bakinki,,, sannan d'azu wa ce irin magana ce kikaso gaya min da baki samu dama ba? ".
Hassi ta d'ago jajayen idanunta wad'anda suka kumbura akan zubar hawaye,, ta bud'i baki dak'yar tace "tabbas ba mutuwa akeyiwa kuka ba sabo ne akeyiwa kuka ,,,baba,, Inna,, Mariya hak'ik'a na yarda komai ya faru da bawa muk'addari ne daga Allah kuma mutum bai isa ya gujewa k'addararsa ba,, Lado ya riga ya zamo ginshink'in rayuwata kuma jigona ni da 'yata mantashi alokaci d'aya yanada matuk'ar wuya agareni sai dai a sannu sannu cikin wani lokaci,,, ku dai tayani da addu'a Allah ubangiji ya k'ara sanyaya zuciyata tareda hak'uri da juriyar rashinsa,,, yanzu kuwa zan baku labarin abinda ya faru da marigayi kafin ya rasu....... ".Nan da nan ta basu labarin da Lado ya bata kafin ya rasu,,, na gamuwarshi da karya alokacin da ya fito waje domin yayi fitsari...
Babu abinda bata gaya musu ba kamar yadda dai ya sanar da ita..
Tana gama bada labarin suka saka salati atare,,, da kuma fad'ar kalmar ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Duniya ina zaki damu wannan ai rashin imani ne,, anya wasu mutane suna tuna mutuwa kuwa,, anya mutane suna tuna kwanciyar kabari da hisabi kuwa,,, anya wasu mutane suna tuna cewa komai daren dad'ewa zasu koma ga Allah ubangijin talikkai? ".Cewar Inna Lami cikeda matuk'ar tashin hankali da jimami..
Mal. Abubakar yayi huci mai zafi da ajiyar zuciya yace ".wannan magana taki akwai alamun k'amshin gaskiya a cikinta na cewa *MAYYA CE* ta kama Lado,,,, amma kuma sanin gaibu sai Allah idan ma itace mun barta ga ubangijin sammai da k'assai wanda baya kwana baya angaje shi zai miki *SAKAYYA* tun anan duniya Hassi,, saboda haka ki share hawayenki ki tashi kuje da Mariya gidanki kiyi takaba acan domin haka ne yafi dacewa ".
"wannan gaskiya ne maganarka ".Inji Inna Lami cikeda matuk'ar tausayin Hassi..
"ya zamo dolena in kiyaye dokokin ubangijina yi muku biyayya ya zamo wajibi agareni iyayena,,, zan tashi in koma gidan Lado inyi takabata acan kamar yadda kuka umurceni amma dan Allah ku tausayamin ku sakani a cikin addu'arku ku rok'armin akan Allah ya sanyamin hak'uri da dangana na rashin Lado ".Cewar Hassi yayinda take zubar da hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa..
Mal. Abubakar yace "karki damu akodayaushe muna yi muku addu'a Hassi,, ki sani albarkarmu da aminci yana tare daku a duk inda kuka shiga a cikin fad'in duniyar nan,, Allah ubangiji ya tsaremin ku yayi muku albarka ".
Mariya tace "Amin ya rabbi baba ".Tana share hawayen da ke fitowa daga idaniyarta.
Inna Lami tace "Allah ya sanya miki hak'uri da dangana akan wannan k'addarartaki,,, ki sani ku masu albarka ne akodayaushe akowane lokaci,,, kuma kuna tareda aminci da yarda Allah saboda haka ku tashi ku tafi gida kafin dare yayi k'warai,, Mariya jeki d'auko Na'ima tana cikin d'aki ku wuce ".
Mariya tace "to Inna ".Ta tashi tsaye ta shiga cikin d'akin ta d'auko Na'ima,,, tasa zanen Inna Lami tsoho ta goyata a bayanta.
Itama Hassi dole tasa ta mik'e tsaye suka yima iyayensu sai da safe,,, iyayen suka k'ara sanya musu albarka tareda yi musu fatar alkhairi a rayuwa,,, sannan su Hassi suka nufi gidan marigayi Lado..
*********************
***Ab'angaren Malam Mamman kuwa bayan ya dawo daga wurin Lawiza yarinyar da yake son ya aura,,, to aranar sai da sukayi fad'a har na tashin hankali da Inna Talatu,, saboda har kwalar rigarsa ta rik'e tareda sa hannunta ta shak'e mishi wuya sosai cike da son kasheshi.
Yayi amfani da k'arfinshi na zama namiji ya b'anb'are hannunta dak'yar ga wuyansa,,, bai b'ata lokaci ba ya kashe ta da wasu mahaukatan maruka hud'u masu rai da lafiya,,, wanda sai da jinta ganinta suka d'auke na wucin gadi ga wani mahaukacin zafi da rad'ad'i da yake fitowa daga kuncinta..
Haka dai rikici da tashin hankali ya cigaba da gudana a cikin gidan Malam Mamman,, wata rana har dambe take cewa tayi dashi cikeda matuk'ar masifa da bala'i shi dai saidai ya ceci kansa domin har makami ko takobi take d'auka tace saita kasheshi,,, haka dai zaiyi dabarar amshe makamin sannan yayi mata matsiyacin duka wanda sai tayi fitsari da tutu cikin wando saboda bak'ar wahala,, amma ba zai hana gobe tayi mishi rashin kunya ba ko tace zatayi dambe dashi..
**Malam Mamman ya aika magabatansa a gidansu Lawiza aka saka ranar aurensa da Lawiza nan da sati biyu masu zuwa.
A wannan ranar Malam Mamman ji yayi kamar anyi masa bushara da gidan aljanna akan tsananin farin ciki da murna sosai,, akan murna ya siyo kwalin minti da chewgam yana rabawa 'yan uwa da abokan arzik'i tare da sanar musu da lokacin aurensa..
Hak'ik'a 'yan uwa da abokan arzik'i sun tayashi murna matuk'a tareda yi masa addu'ar fatan alkhairi a cikin auren da zaiyi,,, haka ya nufo gidansa cikin farin ciki da walwalarsa,, bayan ya shigo cikin gidan tareda sallama a bakinsa ya samu wuri ya zauna yace "Talatu albishirinki ".
Inna Talatu ta hararesa sannan tace "dallah rufamin bakinka tsohon munafiki! Azzalumi maciyi amana,, wato kazo ne kayimin albishir da ka kusa zama ango ko to ai kana bari har a d'aura auren bawai kazo kana yimin cika bakin banza!! Zaka gani idan zakayi auren ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta ".
Yace mata "haukarki ko kishinki na jahilci baya tayar mini da hankali aure ne kamar an d'aura kina gani da idonki,,, saboda haka ki iya tsabtace kalamanki zuwa gareni Talatu ".
Inna Talatu ta juyo ta dubeshi da jajayen idanunta b'acin rai k'arara akan fuskarta ta bayyana,,,tace masa cike da jin haushin maganarsa "bakasan wa ce ce ainahin Talatu ba ganina kawai kakeyi Mamman,,amma zan nuna maka banbanci a tsakanin suga da gishiri zakasan ni ba sakaryar mace ba ce da zata zauna da kishiya,,, wannan auren ba komai ba ne a wurina da ya wuce rusasshe ".
"ba zaki iya ba Talatu aurena kumada Lawiza kamar an d'aura ne ".Cewar Mal. Mamman.
Inna Talatu ta bushe da mahaukaciyar dariya sannan tace "zaka ko gani lokaci ne kawai zai tabbatar da zan iya ko bazan iya ba amma zaka gani da idanunka idan wannan munafikin auren naku zai yiyu! "......
0 comments:
Post a Comment