*PAGE 11*
Inna Talatu ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai sannan tace "zaka ko gani lokaci ne kawai zai iya tabbatar da zan iya ko bazan iya ba,, amma zaka gani da idanunka idan wannan munafikin auren naku zai yiyu! Kuma yanzu ka cigaba da fuskantar barazana da tashin hankali kenan har abada a cikin rayuwarka Mamman,,, saina nuna maka ainahin mummunan halayyarta sai ka gwammace ma kid'i da karatu saina wargaza duk wani farin ciki naka! ".
Mal.Mamman yace "ni surutunki ko haukarki baya tayarmin da hankali,,, sannan farin ciki yanzu na fara kasancewa a cikinsa gida dai nawa ne inada ikon in auri mace d'ai d'ai har guda uku bayan ke Talatu,, domin ba gidanki ba ne nawa ne ko kare na jawoshi na kawoshi cikin gidan nan baki isa ki koreshi ba bale mace matata uwar yarana masu zuwa ".
"hmm tun yanzu kaje ka d'aukota ku kwana idan har ka cika namiji bak'in jarababbe,,, nifa bana magana biyu magana d'aya nakeyi tak saboda haka kasha kuruminka angon Lawiza aure dai ko to kaje kayi! ".Inji Inna Talatu cikin bak'ar magana..
Malam Mamman yace "aiko baki ce ba sainayi aure saboda haka ki daina b'ata miyan bakinki a banza ".
"naji mijin mace hud'u ".Fad'ar Inna Talatu ta tashi sannu a hankali ta shige cikin kitchen,, tana cigaba da aikace aikacenta batare da ta k'ara sauraren maganar Mal. Mamman ba..
Shi kuma Malam ganin Inna Talatu ta fita batunsa,, tana aikace aikacenta dole yasa ya mik'e tsaye yayi shigewarsa cikin d'aki,,, domin yayi barci dama ya gaji sosai...
**********************
Lawwali ne zaune bakin k'ofar gidansu da leda cikeda nama yana ci,,, ga pure water masu sanyi guda biyu yana sha..
Yana tsakar cin naman saiga Gwamma ta fito daga cikin gidan,,, tana fitowa idanunta ya kai ga ledar naman da Lawwali keci akan kwad'ayi irin na Gwamma ta fitar da halshe tana lasar baki,,, sai naga ta matso kusa ga Lawwali tana kallonsa shi kuma ya k'ara juyar da kansa kamar bai ganta ba tare da tamk'e fuska.
Gwamma ta dafa kafad'arsa tace "Lawwali juyo da fuskarka mana nice fa kawai domin ka samu nama,, zaka juyamin baya ko mi nayi maka ne?".
"aini banma lura da ke ba yaya Gwamma,, to yanzu mi kikeson inyi miki ne? ".Inji Lawwali yana cigaba da cin naman..
Gwamma tace "ban gane mi nake so kayimin ba ai kasan abinda nake so,, to naman da kakeci zaka sammini nima in had'iye kwad'ayina ".
"hmm yaya Gwamma kenan har kin manta ko to bari in tuna miki,, ranar nan ba kece kikasa Innarmu ta dokeni ba harda gaya mata nace mata ita mayya ce,, ta bani mugun kashi har na suma ke kuma sai dad'i kawai kikeji abinki saboda haka bazan sammiki namana ba ".Cewar Lawwali..
Gwamma tace "dama inada niyar baka hak'uri k'anena dan Allah kayi hak'uri ka yafemin,,, abinda ya faru ya riga ya faru wlh bazan sake yi maka munafurci a wurin Inna ba,, muddin ka bani nama naci kuma ai nasan abinda ake fad'a gaskiya ne Innarmu k'usurgumar *MAYYA CE*,, kuma babanmu kishiya zaiyi mata saboda mugun halinta da bayada k'yawo kullum kullum ci masa mutunci takeyi akodayaushe akowane lokaci ".
Lawwali yace "ya isa abar maganar domin ke bakinki bayada linzami,, saura kuma gobe ki k'ullamin munafurci ko gulma da ko idan kikaga abu a wajena mutuwa zakiyi bazan baki ba,, saboda haka kiyaye ".
"bazan ma k'ara ba wallahi aini banda kamarka a cikin wannan duniya,,, daga yanzu ko wani naga zai tab'a min kai sai inda k'arfina ya k'are ".Cewar Gwamma.
Lawwali yace "Allah yasa da gaske kikeyi har cikin zuciyarki ".Sannan ya bata sauran naman da ya rage da pure water guda,, da sauri Gwamma ta fisge ledar saboda kwad'ayi har miyau ya fara dalala daga cikin bakinta,,, ta fara d'aukar tsoka biyu tasa cikin bakinta tana ci tana gyad'a kanta cikeda matuk'ar jin dad'i ..
Sannan tace "da gaske k'anena nagode sosai,, amma fa kada ka fad'ama kowa ka bani nama naci ".Tana cin naman tana lasar yatsun hannunta..
Lawwali yace"to aini ba irinki ba ne mai tonon asiri,, ni kinga tafiyata nayi wurin wasa kuma naman da kikaga inaci babane ya sayamin domin kada kiyimin wata fassarar ta daban ".Bai saurari abinda zata ceba ya k'ara gaba yayi tafiyarsa.
Gwamma tace "ni dai ko satowa kayi ina ruwana muradina shine ni dai inci nama mai dad'i,,, saboda haka ko naman mutane ne ka samo saina cishi babu abinda ya dameni ".Ta cigaba da cin naman bayan ta cinye tas tareda lashe takarda da hannunta,, sannan ta sha ruwan pure water ta kuma wanke hannayenta,,, sannan ta juya tayi cikin gida..
********************
***Inna Talatu ta cigaba da kamun kurwar mutane tana mayarda su fa ra ko kaza,, daga baya ta gasa naman mutane ko ta cishi hakanan d'anye kullum kullum saita fita kamun kurwa a kowane lokaci,,, idan ta hango mutum daga nesa ta kama tsura mishi idanu kenan domin tana hango kayan cikin mutane,,, idan kai ma'aboci yawan addu'a ne da iznin Allah ba zata iya kamaka ba,, idan mutum ya zama lusari mara son addu'a kallo d'aya ne ta chafke kurwar mutum tayi gaba da ita.
Haka zataje ta aje kurwar wurin murhu ko wurin randar ruwa masu sanyi,,, idan abin yayi kwana biyu mutum ya kama tsananin rashin lafiya sosai wani za'a samu jikinsa da sanyi wani ko yayi mugun zafi kamar garwashi,, to wanda jikinsa yakeda sanyi kurwarsa tana aje ne a wurin randar ruwa wanda jikinsa yakeda zafi kuma ta aje kurwarsa kusa ga garwashi,, haka mutum zaiji kamar ana sukar jikinsa allura saboda zafi da rad'ad'in ciwo..
Wani ma idan ya gagari mayyu aljannu suke ba kurwar mutum,, domin a halaka mutum kowa ya huta.
_Allah ubangiji ya karemu daga muyagun k'addarori da kuma fad'awa tarkon wahala_.
**Kwanakin auren Malam Mamman da Lawiza sai k'ara gabatowa yakeyi,, Inna Talatu kuwa sai k'ara cin mutunci da tozarci takeyi masa kala kala daban daban,,, ta k'untaceshi ta hana mishi zama cikin gidan sosai saboda tsabar masifa da fitina irin tata,,, bayada halin ya dad'e k'warai cikin gidansa batare da sun kachame da rikitaccen fad'a ba. Komai ta d'auko jefarsa takeyi dashi ba adda ba na wuk'a ba,, harda duwatsu jifarsa takeyi dasu sai ya kauce domin kada tayi masa illa ko ta halakashi..
Ganin haka ne yasa dole ya rage yawan zama cikin gidansa,, sai dai idan ya dawo daga kasuwa yayi wanka ya fita can wurin majalisarsu ya zauna,,, idan yaga abokansa sunyi gidansu su dawo shi sai dai kuma ya k'ara gaba wata majalisar ya zauna,, acan waje zaici abinci yayi komai sai tsakar ya daidaici tayi barci ya dawo gida,, amma duk da hakan bai tsira ba ashe tana nan tana jiranshi yana dawowa ta aza mishi ruwan bala'i da masifa tana zage zage,, da yake yaga dare ne yayi kunnen uwar shaggu da ita yayi kwanciyarshi cikin d'akinsa..
Tayi fad'anta na rashin dalili ta gaji,,, sannan daga baya ta kwanta tana jin haushin rashin kulata da baiyi ba..
Ana saura kwana uku auren Malam Mamman da Lawiza Kwatsam!! Inna Talatu ta tashi da tsakar dare,,, misalin k'arfe 12:15am na dare ta girgiza sannan ta karanta wasu d'alamisai na tsafi da sihiri,, nan da nan wurin ya gameda da bak'ar guguwa da tururin hayak'i,,, guguwar ta daina yawo ta tsaya cak hayak'in ya shige cikin jikin Inna Talatu ta rikid'a ta koma mage......
Managed it please munada matsalar wutar nefa shiyasa.
_Share&Comments_
[6/21, 9:56 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 12*
Inna Talatu ta rikid'a ta zama mage mai fari da bak'i,,,,,sai naga ta fice da sauri daga cikin dak'in kamar k'iftawa da bismillah,,tana kawowa wurin sakatar ta kalli k'ofar da idanunta wani farin haske ne ya fito daga cikin idanunta ya shafi sakata,,, sai kawai naga k'ofar ta bud'e kanta,,, magen ta wuce da saurinta tana wani masifaffen gudu mai cike da al'ajabi da matuk'ar ban tsoro!..
Abin ya matuk'ar bani mamaki kuma ya d'auremin kai ni Mugirat ,,,nabi magen da sauri saboda kada ta b'acewa ganina tana sauri ina biye da ita har muka kawo k'ofar gidansu Lawiza,,, sai naga magen ta tsaya tana duban k'ofar gidansu Lawiza na d'an lokaci ,,,,ta bud'e bakinta kenan saiga jar iska ta bayyana suu suu suu ta nufi k'ofar gidan ya bud'e da sauri,,, magen bata tsaya b'ata lokaci ba ta afka cikin gidan da gudu..
Tana shiga sai na ga ta nufi d'akin dake gefen dama ta afka cikin da sauri,,, tana shiga ta iske Lawiza kwance kamar matatta tana barci,,, magen ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma mutum wato ainahin siffarta Inna Talatu,, saboda k'arfin hali da kuma rashin imani saida tayi wani sihirin da ya tayar da Lawiza daga barcinta mai dad'i sosai,, Lawiza ta falka a firgice! Cikeda matuk'ar tsoro da gigicewa ta daure dak'yar tace "wa ye yake tayar dani a cikin wannan tsakar dare? ".
Inna Talatu ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya sosai,,, wanda akan haka saida d'akin ya kama girgiza tanbal tanbal,, abubuwan dake cikin d'akin suka kama fad'uwa k'asa suna halakewa,,,idanun Inna Talatu suka k'ara ja hannunta ya k'ara tsawo zago zago farcenta yayi tsini kamar allura,,,ta dubi Lawiza cikin takaici da haushi tace "nice Talatu matar Mamman wanda kike shirin aura saboda bakida hankali! ".Lawiza taji gabanta ya buga da k'arfi rasssss tsoro da tashin hankali ya bayyana akan fuskarta ,,,tace "baiwar Allah mike tafe da ke,, shin mi ne ne dalilinki na zuwa wurina a cikin tsakar dare ,,,a ina kika shigo saboda nasan rufe gidanmu akeyi idan dare yayi sosai? ".
Inna Talatu ta banka mata harara da idanunta jawur kamar kan maciji,,, sannan tace "yanzu kuwa zan baki amsar tambayoyinki yarinya! Ni da kike ganina ayanzu gaba gareki *MAYYA CE NI TALATU*,,, ta sihiri na shigo cikin gidanku dalili kuma shine nazo ne in kasheki har lahira! Saboda mijina da kikeson ki aura ni talatu nafi k'arfin inyi kishi da kowace irin jakar mace a duniya,,, saboda kishi dani masifa ne son mijina bala'i ne kallona ma jafa'i ne,,, saboda haka ba gargad'i nazo yi miki ba d'aukar ranki nazo yi in kasheki in kashe banza shegiyar bazawara! ".
Hankalin Lawiza yayi matuk'ar k'ololuwar tashi zuciyarta duk ta karaya,,, ko'ina a jikinta zufa ne ke tsattsafo mata saboda tsananin tashin hankalin da take cikinsa..
Ta fara zubar da hawayen bak'in ciki da afkawa cikin tarkon wahala,,, tace "dama ashe maganar da mutanen gari ke fad'a akanki gaskiya ne ke mayya ce! Na rok'eki dan girman Allah kiyimin rai kada ki kasheni,, idan har domin mijinki ne wlh na hak'ura dashi har abada dama saida nace masa bazan auresa ba amma ya nacemin,, ashe da rabon zan fuskanci abinda yafi k'arfin tunani nabar miki mijinki wlh nabar miki mijinki! ".Ta sake fashewa da wani irin gigitaccen kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro!.
"k'arya kike munafuka azurakar mace! Bazan tab'a yarda da maganarki ba domin ku 'yan Adam kunada sab'a alk'awari,,, kuma na riga nasha alwashin duk wadda ta kusanci mijina ko ta nuna tana son uban 'ya'yana hukuncin mace shine mutuwa! Mutuwa! Saboda haka wallahi bazan tab'a barinki a raye ba,,, kwanciyar kabari shi yafi dacewa dake daga yau zuwa kwana biyu ".Inji Talatu cikeda matuk'ar hasala sosai..
Lawiza tayi kuwwa da k'arfi ta sake fashewa da kukan bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,,, jikinta babu abinda yakeyi sai makarkatar tsoro! Tashin hankali da rikicewa ne ya bayyana a fuskarta dak'yar cikin rud'ewa tace "na shiga uku ni Lawiza! Na kawo kaina gidan mutuwa ka cuceni Malam Mamman ka cuceni Malam Mamman,,,saboda saida nace bazan aureka domin matarka mayya ce amma kace sharrin mutane ne ba haka ba,,, gashi yanxu na jawowa kaina masifar da zata kashe batare da na cika burina ba,, iyayena ku yafemin 'yan uwana ku yafemin! ".Tana ta kukan bak'in ciki da takaicin rayuwa..
Inna Talatu tace "maganar banza da yofi lokaci yana tafiya,, saboda haka yanzu zanyi miki abinda ya kawoni in wuce gidan mijina wanda ni kad'ai ce matarsa a duniya! ".Hhhhhhhh ta fashe da dariya sosai sannan tayi amfani da hannunta,, tana ta surutai na sihiri wani bak'in abu ne ya bayyana a cikin hannun Inna Talatu MAYYA,, Lawiza babu abinda takeyi sai kukan bak'in ciki tana ja da baya da baya cikin firgici da tsananin tsoro! Ganin haka ne yasa ta fasa wani irin uban kuwwa da k'arfi domin neman wanda zai iya kawo mata agajin gaggawa! Tace "kiyi hak'uri Talatu na tuba na biki ki yafemin wlh bazan sake ko kallon mijinki ba ".
Inna Talatu tace "kije kiyita kuwwa Lawiza babu wanda zai jiyo kuwwarki bale yazo ya ceceki,,, kafin nazo saida nayi wani mugun sihirin da ko kinyi kuwwa babu wanda zai jiki balantana yazo ya ceceki,, hmmmm gashi kuwa harna kwad'aitu da namanki!Saboda ina hango komai na kayan cikinki da k'asusuwanki kin tara mai sosai fa ".Kiyi hak'uri ko nawa kikeso zan baki koda zan rasa duk abinda mahaifina ya mallaka zan baki,, nidai burina da fatana kada ki kasheni da duk abinda kike buk'ata zan b.... ".
Inna Talatu bata bari ta isuwa maganar da take sonyi ba,,, tayi amfani da hannunta ta kame mata kurwa ta sanya kurwar Lawiza cikin jakarta da sauri..
Tana kama kurwar Lawiza ta some tare da ruwan hawaye saman fuskarta,,, Inna Talatu ta ganin haka ta girgiza ta sake rikida ta koma mage,, tana komawa ta fice da sauri daga cikin gidan zuwa gidan mijinta..
**********************
***Washe gari da safe koda Lawiza ta tashi daga barci lafiya k'alau ta tashi kamar babu abinda ya faru da ita jiya,,, ci kin gidan kuwa har mutane sun fara taruwa 'yan uwa da abokan arzik'i sai ayyuka kawai sukeyi na 'yar garar da za'a kai gidan miji,,, babu abinda ke tashi sai surutu da ya yar mutane cikin gidan kowace ka kalli fuskarta farin ciki da murna kawai zaka hangowa,,,Inna Lawiza kamar ta zuba ruwa ak'asa tasha akan murna da matuk'ar farin ciki saboda mijin da Lawiza ta fara aure rasuwa yayi ya barta yaro guda mai suna Audu,,, haka dai suka cigaba da gudanar da komai cikin natsuwa da nishad'i sosai..
**Abangaren Malam Mamman shima sai shirye shiryen aurenshi kawai yakeyi cikeda matuk'ar farin ciki da nishad'i sosai,,,, ya gyara d'akin da zai saka Lawiza cikinsa harda saka sabon panting,,, yayi mata kayan lefe kala shida,, takalmi biyu,, hijabi biyu,, sark'a biyu da dai sauransu duk abinda kukasan ake sakawa a cikin lefe ya sanya mata bibbiyu,,, sannan ya aje a cikin d'akin dazai sakata Malam Mamman ya d'auki turmi biyu na daban yaba Inna Talatu ,,, tak'i amsa masa tareda wurga masa kayansa a saman fuska cikeda matuk'ar son tashin hankali! Tace "amshi tsiyarka Mamman! Saboda niba matsiyace ba inada suturata,,, kuma ba gidan matsiyata ka d'aukoni ba da suturata kaje ka aureni alokacin kuma kana fak'irinka! ".
Malam Mamman yace "sannu mai arzik'i har abada Talatu ba zaki tab'a yin hankali ba da karatun ta natsu ba,,, kibi duniya a sannu domin zata koya miki hankali wata rana kuma nasan zakiyi nadama anan gaba alokacin da nadamar da batada amfani,,, aure dai babu fashi sai nayi duk abinda zakiyi kiyi mahaukaciya! ".
Inna Talatu tace "hmmm kaidai akeji Mamman wannan maganartaka baya tayar mini da hankali,, aurenka auren banza bai shafeni ba kana bari dai har a d'aura auren tukun kafin ka cikani da kurin banza ".
"aure ne kamar anyi an d'aura kina ji kina gani,, babu abinda zaki iya yi na maji dad'i sosai da kika k'i amsa saina k'ara ma Lawiza amaryarta matata farin cikin rayuwata ".Cewar Malam Mamman cikeda lalama..
Inna Talatu taja mugun tsoki mtsssss sannan tace "kodai bak'in cikin rayuwarka ce babu abinda ya dameni,,, da ran mai toka da mutuwarsa duk d'aya ne ga hankaka! Saboda haka kaga tafiyata inada aikin yi ".Inna Talatu tayi shigewarta cikin d'akinta batare data tsaya sakejin abinda zai fito daga cikin bakinsa.
"gara da kikayi wucewarki cikin d'akinki,, jahila wanda batasan muhimmancin miji ba da darajarsa ko kad'an ba ".Inji Mal. Mamman..
Allah ubangiji yaba mata mazaje nagari,, mazan kuma yabasu mataye nagari masu tsoron Allah da iya d'aukar dukkan lalurorinmu..
Ana saura kwana biyu a d'aura auren Lawiza da Malam Mamman,,, sai Lawiza ta tashi da wani mugun ciwon ciki sosai kuka kawai takeyi da murje murjen ciwo,, babu abinda takeyi sai danna cikinta tana kukan ciwo da nadamar rayuwa.
Lawiza ta kamayin shure shure da k'afarta sai birgima takeyi,, idanunta har wani k'ak'k'afewa da juyewa sukeyi akan rad'ad'i da zafin ciwo can naga ta fasa ihu da wani gigitaccen k'ara tayi kuwwa da k'arfi! Wani irin jini ne ke fita a cikin bakinta da hancinta gunduwa -gunduwa.
Innar Lawiza ce ta shek'o da gudu da saurinta,, tana shigowa cikin d'akin gabanta ya fad'i rasssss! Da taga abinda d'iyarta ke fissuwa hmmmm,,
tace "Lawiza mi ya sameki? Ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!.....
_Share&Comments_
[6/25, 6:20 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 13*
Innar Lawiza tace" Lawiza mi ya sameki ?Ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Na shiga uku na lalace ".Cikin kid'emewa da matuk'ar tashin hankali,, tana kuka mai cikeda bak'in ciki da k'uncin rayuwa..
Dak'yar Lawiza ta bud'i baki tace cikin matuk'ar zafi da rad'ad'in ciwo,, idanunta suna rufewa suna bud'ewa "kuyafemin Innata hak'ik'a nasan bayan mutuwata zaku kasance cikin bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, kuyi hak'uri wannan itace k'addarata kuma haka Allah yaso sannan na baki amanar Audu ki kulamin dashi ko bayan raina,,, ina son kisan cewa ashe matar Malam Mamman Talatu k'usurgumar mayya ce itace sanadin ciwona saboda haka ku kiyaye kanku Inn..... ".Ai bata k'arasa maganar ba idanunta suka k'ak'k'afe nan ta rasu ga jini duk ya b'ata jikinta,,, Innar Lawiza ta fasa gigitacciyar k'ara tayi kuwwa da k'arfi! Ta fashe da kukan tausayin kansu tana jijjigar gawar Lawiza tana cewa "dan Allah Lawiza ki tashi karki tafi ki barmu! Wallahi na yafe miki duniya da lahira,,,,babanki nasan shima zai yafe miki yau naga ta kaina wannan wa ce irin k'addara ce,, wannan wa ne irin rashin imani ne? 'yar tawa guda da nake kallo inyi farin ciki an kashemin ita,, Allah ya isa Talatu Allah ya isa Talatu!Bamu yafe miki ba duniya da lahira sai kinyi mummunan k'arshe a rayuwarki! Baban Lawiza baban Lawiza ".Ta sake fashewa da wani rikitaccen kuka tana ihu tana ifface iffacen kamar mahaukaciya sabon kamu,,, baban Lawiza da yanzu ya shigo cikin gidan ya shek'o da gudunsa,,, domin yaji kuka da kuwwa yana shiga cikin d'akin yaga Lawiza kwance cikin jini bata motsi,,, hankalinsa yayi matuk'ar tashi sosai gabansa sai fad'uwa yakeyi dummmmm! Yana ganin yadda duk Innar Lawiza ta yatsume da gigicewa yasan kila mai faruwa ta faru,,, yazo kusaga gawar Lawiza yana kallonta na wani lokaci can ya d'aga hannun Lawiza yana saki hannun ya fad'i alamar babu rai kenan,,, yasa hannunsa ya shafe mata idanu tareda furta "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'akhalufni khari minha! Allah ubangiji ya jik'anki Lawiza da rahama ".
Yasa hannunsa ya jawota a jikinsa ya rungume Innar Lawiza yana lallashinta,,,, yana shafar mata baya alamar lallashi cikeda matuk'ar tausayin kansu,, sannan ya dubeta cikin raunin zuciya yace "kiyi hak'uri Innar Lawiza ubangijin da ya bamu Lawiza ya amshi abarsa,,, saboda haka muyi hak'uri Allah ubangiji ya jik'anta da rahama yasa ta huta ".
Innar Lawiza ta d'ago rinannu idanunta da suka rikid'e sukayi ja,,, ta saki wani sabon kuka tace "ya zamuyi baban Lawiza,,,shikenan ta tafi ta barmu ba zata dawo ba,,, shikenan bazan sake ganinta ba har abada,,, shikenan Audu ya zama bayada uwa,,, wannan wa ce irin rayuwa ce mai cikeda bak'in ciki da k'uncin rayuwa? ".
"kiyi hak'uri domin Allah mad'aukakin sarki da ya bamu Lawiza a matsayin d'iya yafimu sonta,, kuma komai na duniya sai mutum yayi hak'uri mutuwa dole ce dukkan mai rai saiya d'and'ani zafin mutuwa,,, to ya zamuyi idan ba hak'uri ba muma lokaci ne kawai muke jira Allah ubangiji yasa muyi k'yakk'yawan k'arshe,,, bari inje in sanarda mutane abinda yake faruwa ".Cewar baban Lawiza cikeda sanyin jiki da tsananin damuwa.
Ita dai Innar Lawiza babu abinda takeyi sai kukan bak'in ciki da mutuwar Lawiza,,, fuskarta tayi jawur majina da hawaye sun b'ata mata fuska yab'e yab'e zad tausayi,, baban Lawiza ya fita daga cikin gidan saboda ya sanar da mutane da 'yan uwa..
*********************
***Agidan Malam Mamman kuwa shi ne ya shiga cikin d'akin dazai saka Lawiza ya share tasss,,,,sannan ya gyara ko'ina cikin d'akin ya k'ulle d'akin ya fito ya zauna.
Yana zaune ne ya kira Gwamma ya aiketa domin ta siyo masa fura da nono,,,,tazo ya bata d'ari biyar ta siyo masa furar d'ari nonon d'ari,, ta amsa mashi ta wuce domin ta siyo masa furar.
Bayan wucewar Gwamma ne Inna Talatu ta fito daga cikin d'akinta itada Lawwali,,, ta dubi Malam Mamman tana wani yi masa rikitaccen murmushi cikin zuciyarta wani nishad'i ne da farin ciki ke wanzuwa a cikin zuciyarta,,, saboda tasan ta riga ta kashe Lawiza har abada! Sai dai Mamman ya nemi wata matar badai Lawiza ba kuma muddin tana raye babushi babu k'ara aure,,, sannan tayi masa walak'antaccen kallo tace "Mamman angon Lawiza saura kwana biyu ka angwance ko? Ya kamata ka k'ara kawo kayayyakin miya wad'annan da ka kawo baya isa fa ".
Malam Mamman yace "hmmm lallai duniya akwai makirar mace,,, har kin sauko Talatu ko kuwa wani sabon salon munafurci ne kika b'ullo min dashi? ".
Inna Talatu ta banka mishi uwar harara tace "ban gane ba Mamman daga magana sai kace wani sabon salon munafurci na b'ullo dashi,,, ada fa aurenka ya dameni ayanzu ko matan duka garin nan zaka aure babu abinda ya dameni,, saboda haka kaje kayita harakarka ".
"aiko bakice babu ruwanki ba bashi zai hana in fasa abinda nayi niya ba,, saboda haka naji zan k'aro kayan miyan ko banason abin tashin hankali kada ki b'atamin ranar farin cikina ".Fad'ar Malam Mamman fuskarsa tana bayyanar da farin ciki sosai..
Inna Talatu tace "kaidai akeji anyima akuya wanka wannan kuma ba damuwata bace ".
Malam Mamman yace "ai naga alama Talatu kishiyar Lawiza,,, Lawiza amarya a gidan Malam Mamman kwana biyu kawai ya rage in zama ango,, mijin Talatu da Lawiza ".
Da yake Inna Talatu tasan abinda ta aikatawa Lawiza,, ta kasheta har abada bazai ganta ba tace "tabbas haka ne mijin mace biyu Talatu da Lawiza takawarka lafiya ango mijin amarya gaba haske baya k'amshi ".
Malam Mamman har cikin zuciyarsa yayi matuk'ar mamakin yadda Inna Talatu bata wani nuna damuwa ba ko tashin hankali ba,,, a fuskarta wani annuri ne ke bayyana a cikin fuskar Talatu babu abinda takeyi sai murmushi da dariya sosai..
Malam Mamman yayi murmushi yace "tabbas haka ne gaskiya zan baki goron kirarin da kikayimin nida amarya ".Yana rufe bakinsa saiga sallamar wani yaro tareda Gwamma domin kunsan ita batayin sallama,,, suna shigowa Mlam. Mamman ya amsa masa suka iso kusaga Malam Mamman,,,, Gwamma ta bashi sak'on ya amsa tayi tafiyarta wurin mahaifiyarta,,,, sannan yaro ya dubi Mal. Mamman yace "ana kiransa can gidansu Lawiza ".
Malam Mamman yace "lafiya dai mi yake faruwa ne yaro? "..
"lafiya k'alau baban Lawiza ke nemanka ".Cewar Yaron..
Malam Mamman yace "to yaro ".Sannan ya tashi tsaye ya bud'e d'akin daya gyara domin amaryarsa,,, ya aje furarsa da nonon aciki ya jawo d'akin ya kulle d'akin sannan ya juyo ya dubesa yace "muje zuwa ko to Talatu na fita zuwa can gidansu Lawiza ".
"lafiya dai Mamman mike faruwa? ".Cewar Inna Talatu MAYYA..
Malam Mamman yace "nima ban sani ba Talatu zanje can injiyo ko mike faruwa ".
Inna Talatu tace "saika dawo Mamman Allah yasa muji alkhairin Allah ".(Kamar da gaske har cikin zuciyarta alhali kuwa ran nan nata da zuciyarta fari fas akan murna da farin ciki sosai,,, saboda tasan mugun labari na mutuwar Lawiza za'a sanardashi).
Yace "Amin ya rabbi ".Suka sa kai sukayi wucewarsu ayayinda gaban Malam Mamman sai bugawa yakeyi da k'arfi! Rassssss,,, yaji duk jikinsa yayi matuk'ar sanyi wani k'ololon bak'in ciki ya tokare masa zuciya,,, shi kansa jikinsa ya bashi akwai mummunan al'amarin da yake faruwa...
Yana wucewa ne Inna Talatu ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai! Sannan tace "Hhhhhhhhhhh haukar banza da yofi ni za'a kawowa iskanci da rainin wayo! Harda cemin shine mijin Talatu da Lawiza _(ta karkace baki tana kwaikwayon maganarsa cikeda matuk'ar raini)_ to yanzu zaka samu mummunan labarin da zai gigita rayuwarka da tunaninka,,, nasan saika kusa haukacewa da d'imaucewa kuma wlh ko ya nemi wata mata itama kasheta zanyi,,,saboda ni bazan tab'a zaunawa da kishiya ba niba wawuyar mace bace kamar sauran mata,,, ko waye yace zaija dani rabonsa wahala!".
Lawwali da Gwamma wasarsu kawai sukeyi,,, suna kuwwace-kuwwace suna dariya sosai..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
¤¤¤Koda su Malam Mamman suka isa gidansu Lawiza har anyima gawar Lawiza wanka da sallah,,,,suna isa aka fito da gawar Lawiza za'a kaita makwancinta .
Suna zuwa Malam Mamman yaji gabansa ya k'ara bugawa da k'arfi dummmmm!Ya dubi baban Lawiza yace masa "Sani wa ye ya rasu? Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un ".Gabansa yana fad'uwa da sauri da sauri zuciyarsa tana bugawa!.
Sani yace "saidai muyi hak'uri Allah ya amshi ran Lawiza ayau da rana Malam Mamman ".
Gaban Mamman ya bada dummmmm zuciyarsa ta girgiza hankalinsa yayi k'ololuwar tashi sosai! Har wani duhu duhu ya fara gani akan tashin hankali da rikicewa,,, ai kuwa nan da nan ya fad'i k'asa ya some mutanen dake wurin suka saka salati atare! Mutane hud'u suka kamashi suka shigardashi cikin gidan Malam Sani mahaifin Lawiza.
Sauran mutanen dake rik'e da gawar Lawiza cikin makara suka wuce da gawarta zuwa gidanta na gaskiya..
*Allahu Akbar! Duniya kenan wata rana za'a wayi gari duk babu mu a cikinta...*
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
***Suna dawowa daga wurin kai Lawiza gidanta na gaskiya mutane suka taru suna zaman makoki,,, 'yan uwan Sani dana matarsa suke karb'ar gaisuwa kowa ka gani ya zauna jugum yayi shiru yana jimami da damuwa.
Acan cikin gidan Mal. Sani kuma bayan an watsawa Malam Mamman ruwa ya farfad'o daga suman da yayi,, cikin mutuwar jiki da damuwa Malam Sani yace "kayi hak'uri Mamman Allah ya k'addara Lawiza ba matarka bace tun farko,,, sannan ubangijin da ya bamu Lawiza ya amshi abarsa alokacin da yaso ya kuma gadama saidai muyi hak'uri mu bita da addu'a,,, shi kad'ai take buk'ata ".
Innar Lawiza tace "tabbas haka ne gaskiya babu yadda zamuyi haka Allah ya k'addara,,, lokacinta ne yayi kuma bawa bai isa ya gujewa mutuwa ba,,, saboda haka hak'uri zamuyi muma ba zamu wuce lokacinmu ba ".
Malam Mamman ya juyo ya kallesu idanunsa sunyi jawur,,, jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u sannan yace "haka ne Sani nagode sosai da kulawarku akaina,, Allah ubangiji ya jik'anta yasa ta huta mu kuma idn tamu tazo yasa mu cika da imani ".
Suka ce "Amin ".Atare da juna.
Malam Mamman ya tashi tsaye yana musu kallon tausayi da jimami sosai,, yace musu shi zai wuce gida,, Malam Sani ya tashi domin yayi masa rakiya zuwa waje tare da bashi hak'uri da maganganu masu sanyi,,, shidai Mamman jijjiga kansa kawai yakeyi yana saurarensa.......
_Share&Comments_
[6/25, 7:51 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 14*
Shidai Malam Mamman jijjiga kansa kawai yakeyi yana saurarensa cikeda matuk'ar sanyin jiki,,, can dai bayan Malam Sani ya gama yi masa nasiha mai ratsa jiki,,,, bayan ya gama ne sukayi sallama da juna cikeda rashin jin dad'i da jimamin mutuwar Lawiza....
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Malam Mamman ya shigo cikin gidan da sallama cikin sanyin jiki,,, Inna Talatu tana cikin d'akinta amma tanajin muryar Malam Mamman ne ta fito da saurinta tana kallonsa..
Malam Mamman ya zauna ak'ofar d'akinsa yayi tagumi cikeda sanyin jiki,,, yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa da bak'in ciki Inna Talatu ta matso kusa gareshi cikin munafurci da k'ulle-k'ullen makirci,,, ta canza yanayin fuskarta daga farin ciki xuwa zullumi kamar ta damu da damuwarsa,,, tagumi yayi yayi shiru kamar ba Malam Mamman ba sarkin kiza-kiza,,, Inna Talatu tasa hannunta ta jaye hannun Malam Mamman domin son taji gulma kuma ta tabbatar ta kashe Lawiza ko kuwa da sauran aiki agabanta,, kunsan mace duk munin halinta ta iya munafurci da makirci idan tanason taji tsegumi ko gulma.
Ta dubi Malam Mamman zuciyar nan tata fara fass amma afuskarta kamar tana tausayinsa,,, tace "haba Mamman ka daina tagumi babu k'yawo,,,, sannan naga yanayin fuskarka ya canza mi yake damunka,,, mi yake faruwa? ".
Malam Mamman ya d'ago idanunsa wad'anda suka fara canzawa daga launin fari zuwa ja,,,, ya bud'i baki muryarsa tana rawa yace "Talatu dole in shiga cikin bak'in ciki da k'uncin rayuwa saboda mummunan k'addarar da ta sameni,,, ya zanyi da rayuwata,,, wannan wa ce irin k'addara ce mai cikeda bak'in ciki da takaici? ".
"ban gane ba Mamman abinda yake faruwa,,, ya kamata ka sanardani mi ke faruwa? Kayimin bayani dallah dallah yadda zan gane bawai kazo kayi tagumi ba ".Inji Talatu MAYYA cikeda matuk'ar makirci da munafurcinta..
Malam Mamman ya daure yace "Talatu Allah yayima Lawiza rasuwa a yau da rana,,,, kiran da kikaga akayimin d'azu alokacin ne koda na isa za'a kaita makwancinta na gaskiya,,,, ina cikin matuk'ar damuwa Talatu ina son Lawiza domin ta nunamin k'auna amma ubangijin da ya fimu sonta ya karb'i abarsa,,, ya zanyi ne yanzu? ".
Hak'ik'a maganar Malam Mamman ta k'ona ran Inna Talatu,,, amma da yake ta iya kissa da kisisina da munafurci bata nuna masa ba,,, kuma tasan burinta ya cika saboda ta k'ara tabbatarwa Lawiza ta mutu tabar duniya har abada!.
Ta dubeshi cikin munafurci tace "Ayyah Allah sarki duniya kenan! Allah ubangiji ya jik'anta da rahama yasa ta huta mu kuma yasa muyi k'yakk'yawan k'arshe,,,, amma agaskiya Mamman banji dad'in faruwar wannan mummunan al'amarin ba,,, amma ya muka iya lokacinta ne yayi,,,, kayi hak'uri Mamman Allah yana tareda masu hak'uri sannan zaka samu wata matar ka aura insha Allahu ".
Malam Mamman ya dubeta yana mamakin kalamanta sosai,,, shi kansa yasan Talatu batada tausayi ko imani amma ji yadda take masa nasiha kamar ta k'warai,,,,,,, amma da yake bayason ya fara zarginta yasa yayi saurin kauda wannan magana gaskiya.
¤¤¤Malam Mamman yace "tabbas haka ne amma ina cikin damuwa,,, sannan mantawa da Lawiza alokaci guda abu ne mai matuk'ar wahala sosai,,, amma bazan tab'a mantawa da Lawiza ba acikin rayuwata ba har abada ".
"haka ne baidace kayi saurin mantawa da ita ba,,,, idan Allah ya bani ciki muka samu d'iya mace sunan Lawiza za'a saka mata saboda k'aunar da kakeyi mata,,,, amma ka daure ka rage yawan damuwa saboda kada kamu da wata cutar hak'urin dai shi ne yafi dacewa ".Cewar Inna Talatu.
Malam Mamman yace "eh mana maganarki haka take nagode sosai da kulawarki gareni,,, kuma idan Allah ya yarda zan rage sa damuwa acikin raina ".
Inna Talatu tace"da kam yafi Mamman karka damu ai dole in tausaya maka,,, saboda anzama d'aya tuntuni "...
Inna Talatu ta cigaba da bashi maganganu masu dad'i,,, da nasihohi masu ratsa zuciya da jini..
*** **** *** *****
*BAYAN WATA SHIDA*
••••Bayan watanni shida abubuwa da dama sun faru,,, ciki kuwa harda kamun kurwar da Inna Talatu keyi tana cinyewa ko ta mayarda kurwar kaza,, rago,, tunkiya,, bunsuru da dai sauran dabbobin dake cikin duniya to mayyu suna iya komawa kowace irin halittar dabbar da suka gadama.
Inna Talatu ta addabi mutanen gari itada sauran mayyu,,, babu abinda sukeyi sai kashe rayuka da cin naman mutane,,, mutanen gari duk sun tsorata da kid'emewa akan mayyu idan suka hangosu daga nesa,,, kowane mutum ko mace zai iya cikawa wandonsa ko bujensa iska k'afa mi naci ban baki ba! Mutane kowa sai kaffa kaffa yake da d'iyansa saboda gudun kada su had'u da mayyu su lamshe musu kurwar d'iya ko mata.
Idan matar aure ce tana kaffa kaffa da mijinta domin kada mai afkuwa ta afka musu,,, amma duk da hakan basu tsira ba domin har gida ake zuwa a lamshe musu kurwa ,,,saidai kaga mutum ya fad'i k'asa rikcham! Idan yana tsaye idan kuma zaune yake sai aga mutum ya fara aman jini yana murk'usu,, can ya fara shure shuren mutuwa yana kakarin mutuwa nan da nan ya rasu! Akwashi gawar mutum ankaishi mak'abarta! Haka abubuwan suke faruwa cikeda matuk'ar tashin hankali da rikicewa .
Rayuwar garin ta zamo cikin rashin kwanciyar hankali da rashin natsuwa,,, saboda akodayaushe akowane lokaci mutum za'a iya kame masa kurwa a cinye ya mutu! Shiyasa mutane basuda natsuwa ko walwala.
***Ab'angarensu Hassi kuwa bayan rasuwar mijinta Lado,,, sukaje itada Mariya ta tayata
zaman idda domin ta d'ebe mata kewar Lado da mutanen gida.
Alokacin ne Hassi duk ta rame tayi bak'i akan tunanin mijinta,,, wata rana har kuka takeyi saboda tunani da zullumi,,,alokacin idan kaga Hassi saita baka matuk'ar tausayi haka Mariya zata kama ta tana kuka ,,,tayi mata nasihohi masu sanyi tareda da bata hak'uri akan lamarin rayuwa,,, haka al'amarin nasu ya cigaba da tafiya hartayi watanni hud'u da kwana goma kenan,,, sannan ta fita daga takaba tayi wanka fes tayi kamar ba ita ba tareda sanya sabuwar sutura.
Bayan wani lokacin ne akayi rabon gado sannan Hassi itada Mariya suka koma gidansu da zama,,,, al'amarin nasu dai komai cikin tausayawa Na'ima da Hassi suke yinsa daga Innarta har babanta babu maison b'acin ranta,,, duk abinda take so shi sukeyi mata babu shakka,,, shiyasa Na'ima takeyin sagarci da shagwab'arta babu mai takura mata ko hantararta.
Anan ne wata rana Hassi Allah ya kawo mata miji nagari mai tsananin k'aunarta tsakani da Allah ya aureta,, sunansa Iliya ba saurayi bane yanada matarsa Dije da yara uku mace biyu namiji d'aya,,, haka dai akayi auren cikin wadatar zuci da rufin asiri sosai,,, aka kaita gidan mijinta sukayi zamansu lafiya da Dije.
Da yake Dije mace ce mai halin dattako da karamci,,, kirki da sanin ya kamata shiyasa zamansu ya zamo abin sha'awa da burgewa,, babu gulma ko tsegumi balantana haukan kishin da bayada k'yau ko misali..
***** ******** ******
Macijiya ce naga ta fito daga cikin gidan Malam Mamman cikeda da saurinta kamar iska,,, ta kama tafiya ta nufi wata hanya mai yawan hakukuwa da itatuwa.
Abin mamaki macijiyar tana tafiya tana waige waige kamar mutum,,, can naga ta nufi cikin sark'ak'k'iya da duhun ciyawa ga k'oramai agefen daji,,, ga itatuwa dogaye manya -manya a ko'ina cikin k'usurgumin dajin baka iya hango tsawon dajin da girmansa saboda yawansa.
Macijiyar tayi ta tafiya tana ratsa hakukuwa da kuma k'oramai tana wucewa,,, tana kawowa wurin wani rami mai matuk'ar zurfi da ban tsoro wata irin guguwa ce da bak'in hayak'i ne suka game wurin nan da nan fass fasss fasss! Tass tass tass saboda tsananin tashin hankali da bala'i! Abin yakai tsawon minti ashirin sannan ya tsaya cak ya daina,,, saiga wata irin mahaukaciyar dariya ta bayyana b'ut akayi fitar burgu acikin ramin kamar walk'iya,,, nan da nan wata irin guguwa mai k'arfi ta zagaye wurin cikeda sihiri da tsafi! Babu abinda ke tashi cikin guguwar sai kukan namun daji da muryar mutane,,, can dai guguwar ta daina yawo a doron k'asa.
Wani irin murgujejen k'aton mutum ya bayyana tsulut kamar aljani,,, kallo d'aya nayi masa amma kamar inyi amai saboda halittarsa babu k'yawon gani,, domin ido d'aya garesa atsakiyar kai ga kuma k'aho biyu agefen dama da hagu duk jikinsa gashi ne zago zago kamar rago,, halshensa yakai tsawon k'afar mutum mai tsawo hak'oransa sunada tsini kamar wuk'a,,, fatarsa bak'ik'irin kamar gawayi. Ya dubi macijiyar da babban murya mara dad'in saurare yace "yake Talatu ki koma zuwa ainahin siffarki ".
Ai bai rufe baki ba Inna Talatu ta girgiza sannan ta rikid'e zuwa ainahin siffarta ta mutum,,,, ta dubi boka LOK'ORO tace "ya kai wannan k'urgumin boka mai babban matsayi a cikin duniya,,, ina mik'o gaisuwata da girmamawa agareka,,, tsawon rai da shahara sun tabbata agareka ".
Boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya,, dariyarsa da muryarsa bibbiyu take fitowa dajin ya gauraye gaba d'aya yana tanbal tanbal kamar zai kife a cikin k'asa !Yace "godiya nake da gaisuwar ban girma amma inason ki sani Mamman mijinki yana nan yana neman wata budurwa fara ce tass mai suna Salima da aure,,, yana yawan zuwa wurinta fira yau zai sanardake yana neman aurenta ance ya turo magabatansa,,, saboda haka ki iya takonki domin gujewa afkawa cikin wahala da nadama! 'Yarki Gwamma zata gajeki a wurin maita zata shahara cikin maita da mugunta iri iri daban daban,,, Lawwali bazai gajeki ba saboda halinsu yasha banbanci dana Gwamma ".
Inna Talatu ta bushe da dariya sosai tace "nagode sosai babban boka LOK'ORO aikinka yana k'yawo sosai,,, nayi farin ciki sosai 'yata zata gajeni amma ko Lawwali bai gajeni ba babu komai boka,, sannan ni auren Mamman bai dameni ba domin cinye namanta zanyi ta mutu har lahira alokaci guda! ".
Boka LOK'ORO yace "aikinki yana k'yau shiyasa nake k'ara sonki saboda bakida imani bale tausayi,,, saboda ni banason haraka da mai tausayi da sanyin hali sannan idan zaki dawo kizo da Gwamma domin ta saba da aljannunmu tun yanzu,,, kafin ta zamo shahararriyar MAYYA gagararriya! ".
"zanzo da ita yah mai girma boka LOK'ORO, ".Cewar Inna Talatu cikeda matuk'ar farin ciki .
Boka LOK'ORO yace "to Talatuwa Innar Gwamma ki tafi zuwa gidanki cikin farin ciki da nishad'i sosai,, duk abinda kika sama gaba kece zakiyi nasara ki kashe kowa kici naman kowa! ".Yana gama fad'ar wannan magana ya b'ace b'at kamar k'iftawa da bismillah,, kamar kuma wata halitta bata tab'a zama a wurin ba.
Inna Talatu tana ganin boka ya b'ace itama ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma tsuntsuwa,,, ta tashi sama ta lulluk'a a cikin sararin samaniya,,, tana ta gudun bala'i da masifaffen saurinta.......
_Share&Comments_
[6/25, 8:12 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 15*
Tana ta gudun bala'i da masifaffen saurinta kamar walk'iya ce ta gifto ta wuce da sauri,,,,,abin akwai ban mamaki da matuk'ar al'ajabi akan tsuntsuwar wato Inna Talatu MAYYA...
Haka dai ta cigaba da tafiya har ta iso bayan gidan Malam Mamman,,, abayan gidan akwai hakukuwa da yawa tana sauka ta k'ara girgiza da k'arfi,,, sannan ta rikid'a zuwa ainahin siffarta ta dawo mutum sannu a hankali,,,, tana dawowa siffarta ta fito daga cikin hakin ta nufi cikin gidan Malam Mamman,,, tana shiga cikin gidan ta isko Lawwali wasa kawai yakeyi ita kuma Gwamma tana cikin d'akin Innarta tana kwana..
Lawwali ya dubi Innarsa yace "Inna sannu da zuwa ".
Inna Talatu tace "yauwa Lawwali ina Gwamma take ne? ".
"tana d'aki tana kwana Inna,,,, sannan da kika fita da safe Gwamma tayi tafiyarta yawon banza da neman magana ".Inji Lawwali cikeda dad'in baki.
Inna Talatu tace "ya isa bashi na tambayeka ba,,, babu ruwanka da sha'anin Gwamma saboda haka ka rabani da surutunka na banza ".
Lawwali yace "to Innarmu na daina fa ".
Suna surutu saiga sallamar Malam Mamman ya shigo cikin gidan,,, Lawwali ne ya amsa masa sallamarsa yana yi masa sannu da zuwa,,,, Mamman ya amsa tareda sa mishi albarka Inna Talatu tayi masa sannu da zuwa,,, ya dubi Talatu sannan ya amsa gaisuwar da tayi masa...
Malam Mamman yayi gyaran murya,, tareda ajiyar zuciya yace "ina son magana dake Talatu ".
"ina saurarenka Mamman ".Inji Inna Talatu cikeda natsuwa,,, ta mayarda hankalinta kacokam wurinsa tana kallonsa.
Malam Mamman yace "da farko dai kinsan dai aure nufin Allah ne shine ke k'addara abu tun ranar gini ranar zane,,, saboda haka na nemi auren wata yarinya mai suna Salima har gidansu sun yarjemin in turo magabatana asaka rana,,, shi ne nace bari in sanardake abinda ke faruwa,,, saboda kada kiji abin daga sama zan tura iyayena gobe asaka sati biyu ad'aura auren,,,, shine nace bari in sanardake ko akwai shawarar da zaki bani ?".
Inna Talatu ta dubesa duba na munafurci da k'ulle-k'ullen makirci,,, tace "Alhmdlilah agaskiya na tayaka murna da farin ciki sosai,,, Allah ubangiji ya gwada mana lokacin biki lafiya musha bidiri mu dargwaji kaji,,,, ai shiyasa akeson mutum komai ya samesa yayi hak'uri da juriya domin babu abinda yakeda tabbas a rayuwa,,,, komai kaga ya samu bawa to muk'addari ne daga Allah ".
"tabbas haka ne maganarki gaskiya Talatu komai na duniya yanada farko yanada k'arshe,,,, saboda haka ki gayamin abinda ya kamata asiyo kafin biki na dangane da abinci da sauran abubuwan buk'ata ".Inji Malam Mamman cikeda matuk'ar farin ciki da nishad'i sosai,,, saboda shi azatonsa Inna Talatu yanzu ta sauko kuma ta gyara halayyarta,,, daga mugun hali zuwa k'yakk'yawar d'abi'a,,, baisan wannan yana daga cikin tarkon makircinta ba da munafurci irin na Inna Talatu MAYYA ba ".
Inna Talatu tayi murmushin da iyakarsa a leb'en bakinta baikai zuci ba,,, sannan tayi wata wawuyar ajiyar zuciya tace "mi kakeci na baka na zuba ka bari har lokacin biki ya k'ara k'arasowa mana,,, bakada matsala indai nice matarka Mamman aure ne kamar kayishi ".
"tooo.. Too bakomi uwargidana sarautar mata kece Innar Gwamma da Lawwali,,,, kece haske gidan Malam Mamman ".Cewar Malam Mamman cikeda zolaya da jin dad'i..
Inna Talatu tace "a'aaa wannan kirarin duk ni kad'ai naji dad'i matuk'a,,, mijin Talatu angon Salima babansu Gwamma da Lawwali ".
Hak'ik'a Malam Mamman yaji dad'i sosai da kirarin da Inna Talatu tayi masa,,, akan farin ciki ya ciro d'ari biyar daga cikin aljihunsa ya bata k'yauta,,, ta amshe kud'in tana zaginsa tareda da tsine masa a cikin zuciyarta.
Wata irin tsanarsa ce ta k'ara ninkuwa da kishinsa a cikin zuciyarta,,, ta fad'a cikin zuciyarta "lallai Mamman zaka tafka babban kuskure a rayuwarka,,, zakasan ni babu mai tabani ya kwana lafiya in kashe mutum ya mutu har lahira ba'a bakin komai yake gareni ba! Amma da sannu zakasan ko wa ce ce ni Talatu idan ma ka gano ni *MAYYA CE* naga kanason ka kawomin tangard'a sai in kasheka! ".Da yaga tayi shiru na wani lokaci,, Malam Mamman ya tab'a Inna Talatu .
Yace "lafiya dai Talatu ya naga kinyi shiru kina tunani? ".
"lafiya k'alau wlh farin ciki ne yayimin yawa sosai,, shiyasa kaga nayi shiru ina tunani nagode sosai da wannan k'yautar daka bani mijina Allah ubangiji ya k'ara bud'i na alkhairi ".Cewar Inna Talatu tana dariyar yak'e da baikai zuci ba..
Malam Mamman yaji dad'in addu'arta matuk'a yayi murmushi yace "amin amin Talatu Allah ubangiji yabarmu tare har abada ".
Inna Talatu tace "amin amin Mamman ".
**Suka cigaba da firarsu cike da tsananin jin dad'i da nishad'i,, saboda shi Malam Mamman agaskiya yaji dad'in sauyawar Inna Talatu har cikin zuciyarsa,, bai kawo zarginta ba ko wani mugun zato akan taba ya yarda da ita ne da zuciya d'aya,,,amma baisan ita munafukar Allah ba haka bane a cikin zuciyarta ba,,, tana nan tana binsa da mugun nufi da k'ulle k'ullen makirci da sharri..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
***Awashe gari da misalin k'arfe hud'u da rabi 4:30pm na yamma magabatan Malam Mamman ya tura can gidansu Salima.
Anyi musu tarba ta musamman da nuna karamci da dattako,,, hak'ik'a iyayen Salima mutanen k'warai ne da sukasan mutunci da sanin ya kamata,,, komai cikin sauk'i da wadatar zuci akayisa ansa sati biyu aranar juma'a za'a d'aura auren Malam Mamman da Salima,,, sun baro gidan suna masu farin ciki da murna sosai akan yadda aka tarbesu hannu bibbiyu cikin sakin fuska da fara'a.
Haka dai abubuwan suke tafiya cikeda zalunci da cin amana,, Inna Talatu taje da Gwamma wurin boka LOK'ORO har ya bama Gwamma maganin maita! Itama ta zama k'usurgumar mayya,,, uwarta Talatu ta kama kurwar mutane ta cinye ita Gwamma ta kama ta cinye.
Saboda tsabar shahara da gunguma a wurin Gwamma ita idan ta kama kurwar mutane ko gasawa batayi,,, sai dai taci naman d'anye hakanan batare da ta gasa ba,,, yaro komai k'ank'antarsa Gwamma tana kameshi mishi inwa (Shadow) ta cinye batare da b'ata lokaci ba.
Ana nan kwatsam!Ana saura kwana d'aya auren? Malam Mamman da Salima,, aka wayi gari itama ta mutu irin mutuwar Lawiza alal hak'ik'a awannan rana iyayenta da 'yan uwanta sun shiga cikin matuk'ar tashin hankali da rikicewa! Kowa awannan rana idan ka ganesu sai sun baka tausayi saboda mahaifiyar Salima har yassuwa zane tayi ta ruga da gudu ta haukace! Saboda tsananin bak'in ciki da b'acin rai sannan kuma ita kad'aice ke gareta amatsayi 'ya a duniya.
Mutanen gari 'yan uwa da abokan arzik'i suka bita da gudu,,, domin su kamota suka babbazu cikin daji suna nemanta,,, sunbi lungu da sak'o na daji har suka gaji amma ko ma kamada ita basu gani ba ganin mutane da yawa daga cikinsu sun galabaita yasa dole suka juyo sukayo cikin gari gidajensu .
Haka dai aka cigaba da cigiyarta da nemanta amma shiru babu wani labari,, asanadiyar haka ne shima baban Salima ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani sai dai atayardashi a kwantar dashi,,, abubuwan dai babu dad'in ji balantana saurare sun faru mutane sun k'ara tsoracewa akan al'amarin mayyu,,, saboda kamasu kawai sukeyi suna canyewa jariri ma ko jaririya tun suna cikin cikin mahaifiya ake kamasu acinye,,,wannan lamarin da gaske yana faruwa ni Mugirat na gani da idanuna azahirin gaskiya bawai labari kawai aka bani ba.
*Azahirin gaskiya ta'adancin mayyu ya wuce duk wani tunaninku mutane.*.
Malam Mamman da yaji labarin mutuwar Salima saida ya fad'i ya suma,, sannan daga baya ya farfad'o saboda matuk'ar damuwa da bak'in ciki saida ya kwanta matsananciyar rashin lafiya sosai,,, duk yayi bak'i ya rame sosai Inna Talatu ke jinyarsa cikeda matuk'ar munafurci tana lallashinsa tareda basa hak'uri,,,idan kaga yadda take kula dashi da tarairayar miji saika rantse da Allah batada masaniya akan komai,,, amma awurin nan muguwa ce azzaluma batada tausayi da tauhidi ko kad'an,,, ita fa arayuwarta bata yarda da k'addara ba indai akan kishiya ce da cikar burinta.
_Agurguje please._
Bayan wasu kwanaki Malam Mamman ya warke garau ya cigaba da harakokinsa,,, tafiya tayi tafiya Malam ya nemi wata mai suna Jummai da aure itama dai ana sauran kwana d'aya da auren ta rasu!.
Sai da Malam Mamman ya nemi mata d'aid'aya har guda bakwai suna mutuwa,, sauran matan sune Karima, Labiba,, Nuratu,, Ummu,,, Lantana,, Falmata,,, Laraba,, Zainabu,,, duk garin gaba d'aya ya d'auka Inna Talatu *MAYYA CE* saboda alokacin basusan Gwamma ta fara maita ba .
Suka zama abin gudu da tsoro a cikin garin gaba d'aya,, babu mai zuwa inda take daga 'yan uwan Malam Mamman har nata kowa gudun ceton ransa yakeyi,,, ko ahanya ne aka tsinkayo Inna Talatu daga nesa sai kaga kowa ya watse domin ceton ransa,,, tun Malam Mamman bai fara yarda da maganar mutane fa har yazo ya fara yarda da maganarsu,,,aiko arana nan ne yayi mata mugun bugu sosai yana zaginta.
Ya dawo kamar ba Mamman ba yana yi mata walak'anci da rainin wayo iri iri daban daban,, shi kanshi alokacin wani tsanar Inna Talatu ne ya dirar masa a zuciya,, yanason ya saketa amma yana ganin idan yayi haka bai dace ba .
Ganin irin abubuwan da Malam Mamman keyi mata na walak'anci da duka sosai,, tabbas taga alamar idan batayiwa abin tufkar hanci da wuri ba zai iya tona mata asiri cikin mutane.
Nan da nan batare da b'ata lokaci ba Inna Talatu ta kama kurwar Malam Mamman,, ta mayarda ita zakara ta cinye d'anye bata tsaya gasawa ba to aranar saida taci kusan fara goma zama guda bayan ta Malam Mamman cikon na goma .
Ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Washe gari da safe mutanen gari suka shiga cikin matsananciyar tashin hankali da bala'i babu abinda sukeyi sai kuka da ifface ifface ,,saboda bayan Mamman mutum tara ne suka rasu alokaci guda idan kayi duba zuwa ga jama'a zakaga mutane idanunsu jawur,,, fuska duk ta kumbura sosai bak'in ciki duk ya bayyana a fuskokinsu k'arara,, haka dai akayi jimami da bak'in cikin rasuwarsu Malam Mamman kowa ya watse.
Ganin da Lawwali yayi mahaifiyarsa ta kashe masa mahaifi! Yasa ya tashi tun kafin ayi sallar asuba ya gudu ya koma wurin k'annen mahaifinsa Labbo,, aka wayi gari Inna Talatu ta nemi Lawwali sama da k'asa ta rasa........
_Share&Comments_
[6/28, 1:56 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 16*
Inna Talatu ta nemi Lawwali sama da k'asa ta rasa a cikin gidan,,, nan da nan hankalinta yayi k'ololuwar tashi cikin kid'ima da fargaba,, haka dai ta daure ta cigaba da harakokinta na cin naman mutane,, Gwamma itama ba baya wurin kamun inwar kurwar mutane tana cinyewa d'anye ba babu tausayi ko rahama acikin zuciyarta ko kad'an,,,mutane sai k'ara tsoracewa da katsewa akan lamarin mayyu sukeyi...
**Inna Talatu ce da Gwamma zaune suna tattaunawa akan yau,,, wa ne gari zasuje kamun inwar kurwar mutane suje can batare da b'ata lokaci ba,, Inna Talatu ce ta dubi Gwamma tace "Gwamma har yanzu bakijin labarin ina Lawwali yaje ya b'oye ba,, acikin garin nan wai?".Gwamma ta karkace baki tace "Inna ayau da dare da naje kamun inwar kurwar mutane,,, na ganshi acan gidan baba Labbo yana b'oya saboda kada ki ganshi wai ".Inna Talatu ta bushe da dariya sosai tace "hmm to ai ko ya gudu ya b'oye can bai tsira ba,, saboda idan inason inci naman jikinsa abu ne mafi sauk'i a wajena ".
Gwamma tace "nima naga wautarshi Inna ai kamun inwar Lawwali shan ruwa ma yafisa wuya sosai,, abinda ya aikata rashin wayo ne babba ".
Inna Talatu tace "yaje yayi tayi fa sannan ina son inja miki kunne ki rik'e wannan haraka ta maita hannu bibbiyu,,, saboda muddin kinayinta babu mai rainaki cikin mutane kowa shakkunki zai dinga yi,,, domin inason ki shahara da gunguma fiyedani inason duniya tasan da zamanki ".
Gwamma tace "zanyi iya bakin k'ok'arina kuma zan kasance mai biyayya ga boka LOK'ORO ,,har sai burinmu ya cika Inna bana wasa a cikin wannan sana'ar gado wato maita !"
"zaki ko shahara sosai da zama gagararriya acikin mutane da aljannu,,, babu wanda ya isa ya tab'aki ".Cewar Inna Talatu cikeda matuk'ar farin ciki da murna sosai..
Gwamma tace "naji dad'i sosai Inna dazan shahara a duniya ".
Inna Talatu tace "ba zakiji dad'i sosai ba sai nan gaba kad'an,, idan shahararki ta bayyana a cikin wannan gari ".
Gwamma tace "to Innata ta kaina".
Haka dai suka cigaba da shawarwari ta yadda zasu b'ullowa al'amarin kamun inwar kurwar mutane,, da kuma yadda zasu gudanar da komai cikin sauk'i....
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SHEKARA BIYAR*
**Abubuwa da dama sun faru acikin wad'annan shekarun da suka wuce,, ciki kuwa harda kamun kurwar mutane dasu Inna Talatu keyi suna cinyewa,, domin abin nasu yayi tsamari sosai sun hana shak'at da jin dad'i a cikin gari,, mutum bayada halin ya fito daga cikin gidansa ya dad'e yana a cikin kasuwa face sun kamesa,, ganin sun addabi rayuwar mutane yasa kowa yake addu'ar Allah ubangiji ya kawo k'arshen Inna Talatu MAYYA.
Saboda har yanzu basusan Gwamma ta zama k'usurgumar *MAYYA CE* shahararra a wurin mugunta da cin naman mutane,, domin ayanzu tanada shekara goma sha takwas Lawwali kuwa sha shida,, tamafi Inna Talatu mugunta saboda ita har naman aljannu ci takeyi saboda ta shahara da gunguma akan maita! Tana alak'a da dodanni wurin abokanka,,, batada tsoro ko shakku uban kowa duk abinda takeso shi takeyi.
Ganin da mutane sukayi kashe rayukan da akeyi agarin nan yayi yawa,, yasa dole suka fara takon sak'a da Inna Talatu sukayita d'ana mata tarko tana tsalkewa,,, domin duk abinda sukeyi tana ganinsu cikin tsafinta,,, ganin abinda suke mata yayi yawa sosai.
Yasa dole wata rana da misalin k'arfe 10:00am na safe,,, bayan sunyi karin safe itada Gwamma tace mata zataje can wurin boka LOK'ORO,, ta tsaya ta fake gida yanzu zataje ta dawo,,, Gwamma ta nuna mata babu matsala saita dawo.
Inna Talatu ta shirya sannan ta saka kai tayi wucewarta zuwa wurin boka LOK'ORO..
********************
Inna Talatu ta girgiza ta rikid'a ta koma kaza sannan ta kama hanyar zuwa cikin k'usurgumin daji mai duwatsu,, dajin da boka LOK'ORO ke rayuwa acikinsa na tsawon shekaru,,, tana isa inda yake ta girgiza sannan ta rikid'a zuwa siffarta ta ainahi,,, wata irin mahaukaciyar guguwa ce ta ratso kusa gareta tana girgizawa da zagayarta na wani lokaci kad'an,, can dai komai ya tsaya cak guguwar ta daina yawo ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma boka LOK'ORO,, idanunsa sunyi jawur kamar barkono jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u halittar yanayin jikinsa duk ya chanza,, ya bud'i baki yace mata "nasan mi yake tafe dake Talatu,, amma ki sake gayamin da bakinki saboda wak'a abakin mai ita yafi dad'i ".
"ya maigirma boka LOK'ORO abubuwa da dama sun faru acikin wannan lokacin,,, mutane yanzu so suke su kasheni har abada,, sunyi d'anamin tarkuna har sun gaji ina tsallakewa,, ka sanardani ta yadda zan k'ara kare kaina".Inji Inna Talatu cikeda matuk'ar sanyin jiki.
Tana gama fad'in wannan maganar boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya sosai,, wanda sanadiyyar hakan saida k'asa ta kama rawa yace"Talatu babu wani taimakon dazanyi miki domin alk'alami ya riga ya bushe,, mutuwarki ta kusantoki! Ajalinki yana zuwa agareki kwananki ya kusa k'arewa ".
Hankalin Inna Talatu ya d'unguma sosai zuciyarta sai bugawa takeyi da k'arfi da k'arfi,, rayuwarta idan har tayi dubu to ta b'aci sosai,, ta d'ago idanunta jawur tace "boka LOK'ORO wa ye zai kasheni sannan ya zamo ajalina? ".
"Sala mafarauci k'anen baban Lado shine zai kasheki! Amma ba'a cikin sauk'i zai kasheki ba 'yarki Gwamma itama ta kashesa,,, sannan abin yazo ya zamar musu gaba mai tsananin gaske itada Ummaru d'an Sala mafarauci,,kinga kuwa bakida damuwa domin ak'alla ko kinyi k'aranci kinci naman mutane fiyeda dubu 'yarki Gwamma taci d'ari ".Inji boka LOK'ORO yana dariyar mugunta da rashin tausayi!.
Inna Talatu ta bushe da dariya sosai sannan tace "hak'ik'a nayi matuk'ar farin ciki da wannan maganar taka boka LOK'ORO,,, aini burina ya cika koda ya kasheni saboda 'yata ta zamo shahararriyar *MAYYA CE* gagararriya acikin mutane da aljannu,, saboda haka banida fargaba ko shakku akanta ".
Boka LOK'ORO yace mata "tabbas haka ne Talatu ,,,ki tafi zuwa gidanki na barki lafiya ".
Yana gama fad'ar wannan magana ya b'ace b'at kamar bai tab'a wanzuwa a wurin ba,,, Inna Talatu tana ganin boka LOK'ORO ya tafi itama ta rikid'a ta zamo kaza ta k'ara gaba domin zuwa gida...
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Inna Talatu ta koma gidanta ta cigaba da harakokinta itada Gwamma,, amma bata sanarda ita abinda boka LOK'ORO yace ba na gameda da mutuwarta ba,, saboda kada ta tayar mata da hankali.
Haka dai suka cigaba da rayuwarsu ta cin naman mutane da aljannu,,, cikeda matuk'ar kwanciyar hankali.
*BAYAN KWANA BIYU*
Bayan kwana biyu da faruwar magana atsakanin Inna Talatu da boka LOK'ORO,, bayan sun tashi da safe ne sun karya Inna Talatu tace ma Gwamma zataje daji domin ta d'ebo ganyayyakin da zata had'a wani magani,, Gwamma ta nuna mata babu matsala saita dawo,, Inna Talatu ta shirya tayi cikin k'urgumin daji Gwamma tana ganin ta fita itama tayi wurin kamun inwar kurwar mutane da satar kayan jama'a har cikin gida.
Inna Talatu ce ta shigo k'usurgumin daji mai duhu da yawan itatuwa,, yanada manyan duwatsu babu abinda ke tashi cikin dajin sai kukan tsuntsaye dana namun daji daga ganin halittar dajin kasan ba za'a rasa k'wamak'wanmai acikinsa ba.
Inna Talatu ta falfala da wani azababban gudu tana hawa saman wannan icce ta sauka tahau wancan bishiya,, haka dai ta kama yawo acikin dajin cikin tsafi da sihiri harta kallama had'a ganyayyakin da suka kawota,, ta juyo ta kama hanyar zuwa gida tana tafiya tana wak'e wak'enta.
Tayi nisa da tafiya kenan kwatsam! Sai taga Sala mafarauci agabanta kamar an jefosa,, hannunsa rik'eda kwari da bakansa ga kuma kibiyar halbi a d'ayan hannunsa,, jikkarsa ce goye abayansa ya kamo namun daji irinsu,, kura,, damo,, zomo da maciji.
Inna Talatu taja tayi tsaye turus gabanta sai bugawa yakeyi da sauri da sauri,, ta daure ta dubesa da jajayen idanunta b'acin rai k'arara ya bayyana akan fuskarta tace "kai Sala mafarauci lafiya ka taremin hanya,, mi kake nufi ne dani wai? ".
Sala mafarauci yace "kasheki zanyi Talatu saboda na dad'e ina d'ana miki tarko kina tsallakewa,, kin addabi mutanen gari da cin namansu saboda rashin imaninki ko jariri baki bari ba,, yau zan kawo k'arshen rayuwarki da zaluncinki! Ayau komai naki zai zama tarihi ".
"k'aryarka tasha k'arya Sala mafarauci ayau kaine zaka zama gawa bani ba,, sai dai uwarka ta haifi wani d'an idan tana raye amma ba kaiba,, ayau zaka d'and'ani d'acin mutuwa kwanciyar kabari shine yafi dacewa dakai a yanzu babu b'ata lokaci ".Inji Talatu cikeda matuk'ar tashin hankali da bala'i!.
Sala mafarauci yace "lallai kuwa ayau zakiyi nadamar duk abinda kika aikata saina banbance miki tsakanin k'arya da gaskiya! ".
Yana rufe bakinsa suka afkawa juna da azababban fad'a mai cike da rikitarwa da tashin hankali! Sara da suka kawai suke kaima juna cikin matuk'ar juriya da zafin nama.
Sala mafarauci yayita amfani da kwari da bakansa yana kaimata hari tana kaucewa,, sannan ya sareta da takobi ta kauce ya sari iska,,, kibiyarsa ya jefa mata ta kama kallon kibiyar da idanunta,, siririn haske ya bugi kibiyar ta juya domin ta chake Sala mafarauci ya kauce cikin zafin nama da juriya,, haka itama tayita jefo masa abubuwan sihiri irinsu wuta,, mashi,, wukake k'anana yana tsallake tarkonta.
Sun dad'e sosai suna azabtar da juna duk sun yiwa juna rauni sosai,, jini sai zuba yakeyi daga jikinsu akan fad'a,, amma duk da hakan basu daina ba Sala mafarauci ganin yayi Inna Talatu MAYYA tana batun kashesa a banza da yofi! Dole ya k'ara tattaro dauriya da hakurinsa ya sake afka mata cikin zafin nama ya sanya takobinsa yana ya sare mata kai ,,ai kuwa yana sare kan Inna Talatu jini ya kama bulbulowa kamar teku mai ambaliyar ruwa.
Wani irin rugugin tsawa ne ya bayyana dajin ya kama rawa da girgiza komai na cikinsa ya kama da wuta!,, Namun daji da tsuntsaye suka kama gudu domin ceton ransu,, alal hak'ik'a Sala mafarauci yaga abin mamaki da al'ajabi akan mutuwar Inna Talatu,, yasa hannunsa ya d'auki kan Inna Talatu da ya rabuda gangar jikinta yasa acikin jikkarsa ,,,yana sakawa wani k'aramin rami ya bayyana akusa da jinin jikin Inna Talatu,,, abin mamaki jinin ya dinga shiga cikin ramin har ya k'are tsab sannan gangar jikin Inna Talatu ta k'ara matsawa agefen bakin ramin.
Jinin yana k'are shiga ramin,,, ramin ya rufe kansa kamar bai tab'a bayyana a wurin ba,, Sala mafarauci ya juya zuwa hanyar zuwa gida yana tafiya yana tangad'i kamar mashayi,,, ga jinin Inna Talatu duk yayi masa faca faca a jiki ga wani zafi da rad'ad'in ciwon da taji masa sosai, akafarsa ta dama harta zaftari namansa babba yana shillo,,, dak'yar da bala'in dauriya ya kawo gidansa yana kawowa bakin garka ya fad'i k'asa rikcham ya some.
*Ab'angaren Gwamma kuwa bayan ta tafi wurin sace sacenta da kuma kamun inwar kurwar mutane,,, ta jima sosai a wurin kamun kurwar mutane sannan daga baya ta dawo gida tayi wanka tana jiran dawowar Inna Talatu.
Tana, zaune taji gabanta ya buga da k'arfi rassssss! Hankalinta yayi k'ololuwar tashi sosai zuciyarta tana yi mata k'una da tafasa sosai,,, haka kawai taji hawaye sun zubo daga idanunta jijiyoyin kanta sun mik'e tsaye rud'u rud'u halittar jikinta gaba d'aya ta chanza kammani,, safa da marwa kawai takeyi a cikin d'akin ita kanta ta rasa dalilin dayasa hankalinta yayi matuk'ar tashi sosai,, zuciyarta tana yi mata suya da tafasa sosai .......
0 comments:
Post a Comment