"Zan sanyaka cikin farin ciki da nishad'i mai d'orewa,,, zan zamo fitila mai haskaka rayuwarka zan sadaukar da farin cikina domin samun farin cikinka,,, biyayya ga iyaye ya zamo wajibi agareni domin samun aljannata agobe k'iyama ".Cewar Salma cikeda matuk'ar natsuwa da hankali. Alal hak'ik'a Ummaru yaji dad'in kalamanta sosai wani sanyi ne da jin dad'i ke kwaranya acikin zuciyarsa,,, ayanzu ya tsinci kansa cikin tsananin farin ciki da murna mara misaltuwa,,, ya kuma k'ara tabbatarwa da yayi dace da masoyiya ta gari abar alfahari ga kowane d'a namiji,,, ya riga ya sadak'ar idan Allah ya yarda ba zaiyi nadamar auren Salma ba a rayuwarsa,,, saboda daga ganinta kasan yarinya ce mai tarbiya da natsuwa gata da hankali da girmama na sama gareta,,, gata da sanyin hali da k'yakk'yawar d'abi'a ta ko'ina tayi batada matsala a rayuwa,,, tanada tausayi da jink'ai musamman akan yara ko nakasassu,,, batada girman kai ko kad'an..
Cikin tsananin farin ciki da shauk'in so,,, Ummaru ya d'ago idanunsa ya kalleta cikeda matuk'ar farin ciki da samun mace tagari yace "hak'ik'a Allah ubangiji abin godiya ne daya had'a ni da mace tagari d'iyar mutanen kirki,,, wadda takeda tarbiya da girmama manya,,, nima zan rik'eki amana bisa gaskiya da tsoron Allah zan zama jigon rayuwarki abar alfaharinki akodayaushe,,, zan kasance inwa agareki domin kada rana ya illatamin ke ".Cewar Ummaru cikeda matuk'ar nishad'i sosai.
Salma tayi murmushi wanda ya k'ara bayyanar da tsantsar k'yawon fuskar da Allah ya bata,,, sannan tayi masa kallon soyayya tace "naji dad'i matuk'a Allah ubangiji ya gwada mana lokacin auren lafiya,,, sannan idan muka zamo miji da mata Allah ya bamu zaman lafiya da kuma juriya da hak'urin xama da juna ".
Sai asannan ne Kabiru ya sake magana yana murmushin jin dad'i,,, saboda yadda suka amince da juna farat d'aya ya matuk'ar bashi sha'awa.
Yace "hak'ik'a nayi farin ciki matuk'a ta yadda kuka fahimci juna batare da wata matsala ba,,, sannan kukayi biyayya ga maigirma baba maigari,,,, ku masu biyayya ne da bin maganar manya Allah ubangiji ya gwada mana lokacin aure lafiya,,, sannan kuma ya baku yara masu albarka da biyayya agareku ".
"Amin amin abokina amma fa ka iya addu'a mai k'yau,,, Allah ya sauki matarka Hanne lafiya".Inji Ummaru cikeda zolayar Kabiru.
Salma tace "amin ya rabbi ".Kanta duk'e tana mai wasa da yatsun hannunta.
Alokacin ne Kabir ya harari Ummaru da wasa,,, sannan ya d'auko dubu hud'u daga cikin aljihunsa ya mik'awa Salma yace "gashi ta sayi kayan kwalliya ba yawa tayi hak'uri ".
Salma ta nok'e tak'i amsa,,, tana jijjiga kai alamar a'a ba zata amsa ba,,, "bangane mi kike nufi da haka ba Salma ".Cewar Ummaru.
"ai shine na gani ina bata tana wani jijjigar kai kamar mage ".Inji Kabiru cikeda fara'a.
"ina nufin ni bazan amshi kud'inka ba saboda babana ya gargad'eni akan na daina amsar kud'in samari ".Inji Salma cikeda ladabi.
Kabir yace "dama kin saba amsar kud'in wasu ne? Kuma naga Ummaru ba wani bane mijinki ne idan Allah ya yarda ".
"a'a nidai kawai ku barshi baba zaiyimin fad'a agida wlh nagode sosai da soyayyarka agareni,,, ina sonka ba domin abin hannunka ba Ummaru idan kukaje gida ina gaida Hanne da sauran mutanen gida,,, na barku lafiya cikin aminci da k'auna ".Inji Salma cikeda natsuwa tana gama fad'ar wannan magana tayi shigewarta cikin gidansu,,, batare da tsaya ta saurari kalaman da zasu fito daga cikin bakinsu ba..
Sukayi tsaye suna mamakin irin tarbiyar da Salma takedashi,, sannan ga iya tsara magana mai ma'ana da muhimmanci.
Can dai Kabiru ya dubi Ummaru yace "abokina mu wuce zuwa gida Allah ne ya tausaya maka,,, ya baka mace mai tarbiya da sanin ya kamata ".Yace tareda mayarda kud'in cikin aljihunsa ya ajiye.
"haka ne Kabiru mu wuce zuwa gida yanzu,,, aini nayi matuk'ar farin ciki domin kakata ta yanke sak'a ".Cewar Ummaru tareda da jan hannun Kabiru suka d'unguma zuwa gida,,, suna tafiya suna fira cikeda matuk'ar farin ciki da walwala sosai..
*********************
***Bayan sati d'aya ya zagayo mutane da dama aranar assabar,,, suka shaida d'aurin auren Ummaru Sala mafarauci da Ummu Salma Garba maigari akan sadaki dubu talatin lak'adan,,,,d'aurin auren ya samu halartar mutane da dama daga wasu garuruwan daga nesa abokanin maigari,,, anyi taro lafiya an watse lafiya cikeda mutunci da karamci,, anyi abinci kala kala aka rabawa mutane k'yauta ,,,,an raba lemun k'walba irinsu fanta,, coke da dai sauransu..
Komai na bikin anyisa a wadace cikin rufin asiri da wadatar zuci,,, amarya tasha kwalliya da chanza kaya kala kala masu k'yawo sosai..
'Yan uwa da abokan arzik'i sunzo na nesa da na kusa,,, dare nayi da misalin k'arfe 9:00pm na dare dai dai aka d'unguma akaje aka kai amarya d'akin mijinta,,, sai dai muce Allah ubangiji ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba mai tarin albarka.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SHEKARU UKU*
Bayan shekaru uku abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda k'aruwar haihuwar da Ummaru mafarauci ya samu,,,,,matarsa Salma ta haifi d'a namiji na farko mai suna Habibu,,, ta biyu kuwa ba'a dad'e da haihuwarta ba mai suna Husna. Shima Kabiru d'iyansa biyu da Hanne matarsa ta farko Yusrah na biyu Yusuf shima dai k'arami ne,,, haka dai suke kula da iyalansu tareda basu kulawa da nuna soyayya na gaskiya,,, zumuncinsu ya k'ara k'arfi sosai a tsakaninsu komai tare suke yinsa cikeda yarda da aminta da junansu,,, idan kaga yadda sukeyin zumunci saikayi mamaki sosai saboda kana rantsewa da Allah kace 'yan uwan juna ne amma abin ba haka yake ba sone gamon jini da kuma k'auna matuk'a..
Ba laifi Kabiru da Ummaru yanzu sun zama shahararrun masu kud'i,, musamman Ummaru da ya zamo shahararren mafarauci wanda ya gaji ubansa Sala mafarauci,,,,,yafisa zamowa babban mafarauci a cikin garin Gumi da sauran k'auyukkan dake kewayenta,,, babu inda labarin jarumtarsa da shahararsa baije ba,,, kowane irin daji komai hatsarin daji da aljannunsa yana iya shiga ciki yayi farauta ya dawo gida lafiya k'alau,,, babu dabbar da take gagararsa kamawa ba sai dai idan baiyi idanu biyu da dabbar ba,, alk'awarin daya d'auka na fansar jinin iyayensa dana baba Labaran bai manta ba yana nan dai yana shirye shiryen d'aukar fansa!.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
***Ab'angarensu Sagiru,, Ila da Lawwali sun zama shahararrun 'yan kasuwa masu kud'i dai dai gwargwado,,, ganin sunyi kud'i yasa suka gina gidajensu kusaga juna,,, sannan kowane daga cikinsu ya nemo mata budurwa baba Labbo yayi musu auren soyayya.
Lawwali sunan matarsa Aliya,, Sagiru Adama,, shi kuma Ila Ladidi haka dai aka d'aura aurensu cikin wadatar zuci da rufin asiri sosai,,, d'aurin aurensu ya tara mutane da dama 'yan uwa da abokan arzik'i duk sunzo wurin bikinsu Lawwali,,, haka aka kai kowace amarya gidan mijinta cikin mutunci da lumana..
_Allah ubangiji ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba mai tarin albarka,,, wad'anda basuda aure ya kawo musu mazajen aure nagari masu halayyar k'warai._
Gwamma kuwa haka dai ta cigaba da cin naman mutane da mu'amalar iskanci da Sule,,, duk da irin matakan tsaro da aka sanya mata bai hana mata aikata maita ba! Babu abinda ta bari na naman mutane dana aljannu kowa bata bari ba,, gashi mutane sai tsoronta sukeji saboda amintattun maigari sun tabbatar masa da Gwamma *MAYYA CE* babba kuwa,,, komai na Gwamma cikin wayo da dabara takeyinsa na kamun kurwar mutane da aljannu!.
Maigari yanajin wannan maganar hankalinsa ya d'unguma sosai gabansa ya bada rasssss! Jikinsa sai makarkatar tsoro yakeyi saboda yaga alamar Gwamma ta zarce Inna Talatu MAYYA rashin imani acikin maita,,, ya aika dogarinsa guda ya kira masa surukinsa wato Ummaru d'an Sala mafarauci,,, batare da b'ata lokaci ba sukazo tare maigari ya kwashe labarin komai ya gaya masa cewa Gwamma ce shahararriyar mayyar da ta addabi rayuwar mutane sosai,,, Ummaru ya nuna masa ya kwantar da hankalinsa shine zai kamata da hannunsa sannan daga baya ya kasheta har lahira,, Ummaru yaba maigari shawarar asanarda mutane domin susan irin abubuwan da suke faruwa agari,,, maigari ya sanardasu komi gameda Gwamma mayya da kuma irin tsafe tsafen da take aikatawa ya gaya musu tafi mahaifiyarta shahara da gunguma akan maita,, domin ita har naman aljannu ci takeyi bawai ga mutane kawai ta tsaya ba.
Mutane suka k'ara rikicewa da d'imaucewa akan tashin hankali,,, gashi yanxu sun k'ara tabbatarwa Gwamma tafi mahaifiyarta shahara da gunguma akan maita da mugunta iri iri daban daban,,, sannan batada tausayi da imani ko kad'an,, bayan maigari ya gama nasa jawabi.
Ummaru yayi nasa jawabi inda ya nuna musu dasu kwantar da hankalinsu zai d'auki babban mataki akanta sannan zai kamata ya gana mata azaba sannan ya kasheta! Ya k'ara nuna musu dasu k'ara dagewa da yawan yin addu'a domin Allah ubangiji ya kawo musu k'arshen zaluncin Gwamma,,, kuma su kulada iyalansu tareda yin taka tsan tsan domin gujewa afkawa cikin tarkon Gwamma mayya,, yana kawo k'arshen maganarsa suka umurci mutane kowa ya watse ya kama gabansa,,, kallo d'aya zakayiwa mutane ka hango tashin hankali da rikicewa k'arara akan fuskarsu,,, masu raunin zuciya banda hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa babu abinda sukeyi,,, suna tafiya suna jimamin abinda yake faruwa marasa dad'in saurare da kuma ji,, ga kuma zullumi da fargabar akan kodayaushe mutum ana iya kame masa kurwa ya mutu har abada.........
_Share&Comments_
[7/4, 11:36 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 25*
**Mutum ana iya kame masa kurwa a cinye ya mutu abanza,,,, batare da anyi saurin ganowa ba sai daga baya ai kuwa mutane suna komawa gidajensu,,, maganar Gwamma k'usurgumar mayya ce ya bazu ko'ina a cikin garin Gumi,,, mata da k'ananan yara suka tsorace da rikicewa! Wasu ma babu abinda sukeyi sai kuka da zubar da hawayen bak'in ciki da tsoron mutuwa,,,, gashi babu halin mutum yace zai gudu yabar gari yayi gudun hijira,,, to ganin haka ne yasa mutane suka rage yawan fitar dare ko irin gungu nan da samari da dattijawa keyi acikin dare suna fira yanzu babu shi,,, saboda kowa yana tsoron masifar Gwamma da kuma ta cinye mutum a banza babu me cetonsa,,,, Ummaru mafarauci shi kad'ai kawai ke fitowa acikin tsakar dare yana yawon farautar kamun Gwamma mayya,,, kullum kullum yake fitowa nemanta amma har yanzu shiru Allah bai bashi ikon kamata ba,,, domin duk yawon nemanta da yakeyi tana ganinsa acikin madubin tsafinta,,,,, idan taga yadda Ummaru d'an Sala mafarauci yake yawon nemanta kamar yadda mafarauci ke neman namun daji saita bushe da muguwar dariya sosai tace "hhhhhhhhhhh Ummaru kenan ba zaka iya kamani cikin sauk'i sosai ba sai kasha bak'ar wahala,,,, kafin ka kamani sannan kashe mutane yanzu na fara! Babu ubanda ya isa ya hanamin cin naman mutane dana aljannu duk duniya,,, kafin na mutu sainayi abubuwan da har abada ba zaku tab'a mantawa dani ba,,,,,,saina shayar daku ruwan guba da bak'in cikin da zai kasheku d'aya bayan d'aya,,,, babu gudu babu ja da baya wannan alk'awari ne na d'auka araina kuma saina cikasa,,, saina cikasa! ".
Haka dai takeyin maganganu iri iri daban daban na d'aukar fansar jinin mahaifiyarta,,,,,saboda ita Gwamma duk da mutane sun gano ita mayya ce bata damu ba,,, sannan hankalinta kwance yake alokacin ne ma ta k'ara k'aimi wurin cin naman mutane da aljannu,,,,, mutum sai yana zaune cikin kasuwa ko majalisarsu akirasa ace 'yarsa ko d'ansa ko wani d'an uwa nasa ya mutu! Kullum safiyar Allah idan gari ya waye saita kashe kusan mutum goma ko fiyeda hakan,,, ganin mutuwar da akeyi ne yasa maigari da sauran mutanen gari suka fita cikin hayyacinsu,, tsoro,, tashin hankali,, fargaba duk suna taredasu akodayaushe akowane lokaci,,, Ummaru ma abin yana matuk'ar damunsa na yadda Gwamma take shammatarsa ya kasa kamata,,,, amma sai ya nasa acikin zuciyarsa duk daren dad'ewa sai ya kamata sannan komai b'oye b'oyenta da sihirinta tabbas wata rana sai dubunta ya cika..
**Washe gari da safe misalin k'arfe 11:00am na safe,,, bayan Gwamma ta share gidan gaba d'ayansa tsab,,, dayake nan Sule yake kwana acikin gidan akodayaushe sukayi wanka tare,,, sannan tayi musu breakfast tea da bread suka karya.
Bayan sun gama karyawa ne kowanensu ya shirya cikin sabbin kayansu mai k'yau,,, sannan Sule da Gwamma sukazo har bakin k'ofar gidan zatayi masa rakiya,,, suna zuwa bakin k'ofar Sule ne ya dubeta cikeda so da yaudara yace "farin cikin rayuwata mi kike buk'ata ne,,,, Idan zan dawo in sayo miki ?".
Gwamma tayi murmushi tace "zumana ka siyomin kifi mara k'arni da lemu da ayaba,,, sannan ka biya wurin Iya Abu mai saida langab'u ka sayomin shi ".
"hmmm duk a ina zaki saka wad'annan abubuwan da kika lissafo?,,,mata dai akwai ku dason cin dad'i da kwad'ayi".Cewar Sule cikin zolaya da wasa.
Gwamma ta hararesa da wasa sannan tace "duk acikin cikina kaidai ka sayomin babu ruwanka,,, muradinka dai kada nak'i ci ya lalace a banza aiku maza bakuda son dad'i ko kad'an sai d'aci ".
"ke ni ban iyawa da masifarki wasa nake nakeyi miki,,, zan siyo miki duk abinda kike buk'ata Gwammata,,, ai bakisan yadda nake sonki ba saboda haka ki daina shakku akan zan sayo ko bazan sayo ba ".Cewar Sule cikeda matuk'ar lallashi da dad'in baki.
Gwamma tace "to naji yanzu dai kayi magana mai ma'ana sosai ".
Sule yace "to ni dai yanzu zan wuce saina dawo ko ".
"to saika daw...... ".Bata k'arasa maganar ba saiga Lawwali yayi musu sallama,,, Sule ya amsa masa cikeda fara'a da murna sosai yayinda Lawwali ya dubesa ya tamk'e fuskarsa alamar bayason wata magana da Sule,,, Sule ya hango k'iyayyarsa acikin idanun Lawwali saboda haka batare da b'ata lokaci ba yaja k'afafunsa yayi wucewarsa zuwa inda zaije,,, Gwamma kuwa tana ganin irin kallon da Lawwali keyiwa Sule dole itama tasha masa toka tareda da yi masa jagora zuwa cikin gidanta.
Suna shiga cikin gidan ta d'auko tabarma ta shimfid'a masa,, tareda da kawo masa ruwa masu sanyi cikin jug,,, Lawwali ya zauna saman tabarma tareda yin bismillah sannan ya dubeta duba na fahimta da natsuwa yace "yaya Gwamma mun yini lafiya,,, ya bayan rabuwa? ".
"lafiya k'alau bayan rabuwa kuma ai kasan inda nike baka nemeni ba,,,, sai yau ka tuna dani ashe dai naka naka ne duk yadda ya lalace ".Cewar Gwamma cikeda jin haushin maganarsa .
Lawwali yaja dogon numfashi yace "Allah ubangiji ya huci zuciyarki yaya Gwamma,,, niba tashin hankali ya kawoni wurinki ba magana ce mai matuk'ar muhimmanci da amfani ta sanya nazo gareki,,, sannan kuma ai nasan hannunka bai tab'a rub'ewa ka yanke kayarsuwa ".
"to ina saurarenka mi yake tafe dakai? ".Inji Gwamma.
Lawwali ya nisa yace"da farko dai inason komai zakiyi a duniya ki sanya tsoron Allah azuciyarki,,, sannan duk abinda mutum zaiyi arayuwarsa yasan Allah ubangiji yana ganinsa koda lullub'e yake acikin rami,,,, shaidun duniya shine shedun lahira yaya Gwamma aikata alkhairi komai k'arancinsa arayuwarki ta duniya ki guji aikata masha'a komai k'arancinsa,,, amatsayina na d'an uwanki kuma k'ane agareki ya zamo dole in sanardake gaskiya koda zakiji haushina ki tsaneni,,, koda hakan zai zamo silar b'acin ranki abinda kike aikatawa acikin garin nan dai bai kamata ba,,, sana'ar maita bata dace dake ba !Ko'ina acikin gari maganarki kawai akeyi ana cewa ke *MAYYA CE* sannan abin takaici da bak'in cikin rayuwa gashi yanxu na gani da idona har namiji kike kawowa acikin gidan nan kuna aikata abinda kuka gadama,, ansha kawomin gulma da jita jita amma ban yarda ba gaskiya sai yanzu ,,,,ki ji tsoron Allah domin ina guje miki yin mummunan k'arshe! Duniya bakiji wani dad'i ba hakama lahira ba zakiji dad'i ba ".
Gwamma ta hararesa tareda jan mugun tsoki mtsssss! Sannan tace "ka gama tsohon munafiki wato an turoka ne domin kazo ka cimin mutunci ko,, wallahi kam baka isa ba kayi d'an k'arami da kai Lawwali maita kuma bazan daina ba! Duk ubanda zaka gayawa jeka gaya masa bana tsoron uban kowa ciki kuwa harda kai! Shege wanda baisan d'an uwa ba ".
Lawwali yayi hucin mai cikeda takaici da bak'in cikin Gwamma,,,sannan yace "Alal hak'ik'a na k'ara tabbatarwa da wanda yayi nisa bayajin kira acikin aikata masha'a da mummunan dabi'a,,, daga fad'in gaskiya ayau shine zaki cimin mutunci ki nunamin ni ban isa in gaya maki gaskiya ba,,, Allah ubangiji ya shiryeki yasa ki gane gaskiya gaskiya ce kuma k'arya k'arya ce ".
"aini ashirye nake kuma kowa shiriyar Allah yake nema bata mutum ba,,, ehehhh maita ce da kuma yin zina bazan daina ba koda kuwa mutum zai fad'i k'asa ya mutu har lahira! ".Cewar Gwamma cikeda jin haushin maganarsa da bala'i..
Lawwali yace "to yayi miki k'yau matuk'a duk dai abinda kikeyi marasa k'yawo,,, Allah yana sama yana kallonki kuma shi zai musu sakayya tun anan duniya ina k'ara tabbatar miki muddin baki daina aikata miyagun ayyuka ba,,, karshenki bazaiyi k'yawo ba !".
"kar yayi k'yau d'in ina ruwanka idan har nayi mummunan k'arshe? To idan aljanna taka ce ka hana in shigeta,,, kuma tun yanzu kazo kasa inyi mummunan k'arshe mara mutunci wawan banza dolo wanda babu tunani da nazari acikin kansa ".Inji Gwamma cikin takaici da haushi..
Lawwali ya tashi tsaye yana cewa "to tunda bak'yajin nasiha na k'yaleki,,, kije kiyita aikata duk abinda kika gadama babu abinda ya shafeni! ".Yana k'arasa maganar yayi tafiyarsa batare da ya tsaya ya saurarin irin martanin da zata mayar masa ba.
"aikin banza yima karen mak'wabta wanka mtssssssss kai har ka isa kace zakayimin wa'azi ko nasiha,,,, to wallahi ka kiyayeni idan ba haka ba barin ganin uwarmu d'aya ubanmu d'aya ina iya kasheka in cinye namanka d'anye! Kuma ba'a komai babu maija dani Gwamma mayya ".Inji Gwamma ta kama sambatu tana zage zage na cin mutunci da tozarci.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Baba Labbo ne zaune da Inna Tani suna fira cikeda matuk'ar farin ciki da nishad'i sosai,,, saboda su yanzu Alhmdlilah babu abinda suka nema suka rasa komai su Sagiru kawo musu sukeyi,,,, na dangane kayan masarufi da mak'ulashe abinci kala kala sukeyi wani buhun shinkafa,,, masara,,,wake da dai sauran kayayyakin abinci wani saiya tadda wani,,, nama sai sun ture da kuma kayan marmari..
Inna Tani ta karkace baki tace "Hhmmm maigida ashe dai Gwamma ta zama k'usurgumar mayya,,, shiyasa rannan ta zama macijiya ta koraka daga cikin gidan yayanka ".
Baba Labbo yace "aike wallahi lamarin akwai ban mamaki da al'ajabi da maigari yana gaya mana,,, ba kiga irin yadda mutane suka rikice suna hawaye ba!Wai ashe ta zama babbar mayya tafima uwarta shahara ".
"ai Allah yasa kanada k'arar kwana agaba da yanzu Gwamma macijiya ta lak'umeka zama guda,,, ni wallahi abin har mamaki yake bani wai cin naman mutane takeyi ".Inji Inna Tani tana kallon baba Labbo tana masa dariyar k'eta.
Baba Labbo yace "haka ne gaskiya da yanzu ina can cikin kabari kwance,,, aini yanzu ko bakin k'ofar gidan nan bazan iya k'ara giftawa ba saboda in tsira da rayuwata ".
Inna Tani ta bushe da dariya sosai tace "maigida akwai ka da tsoron bala'i,,, ai b'oye b'oye baya maganin mayyu saboda ko'ina kake suna ganinka,,, addu'a itace maganin mayyu kuma takobin mumini ce "............
_Share&Comments_😘
[7/6, 5:42 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 26*
"Addu'a itace maganin mayyu kuma takobin mumini ce,,,, sannan mace mai yara k'anana da basu iya yin addu'a ba,,,, ya zama dole ta dinga yi musu addu'o'in neman tsari tana shafe musu jiki akodayaushe,,,, ba wai mace ta nuna son jiki ko k'yuya ba ".Inji Inna Tani,,, "tabbas maganarki gaskiya ce Tani,,, babu yadda zaka saki baki bakason yin addu'a sannan kace wani abin cutarwa bazai tab'a cutarka ba ".Cewar baba Labbo yana murmushi,,, Inna Tani ta dubesa tace "aini yanzu lamarin duniyar nan tsoro yake bani sosai,,, yanzu kaga mutum lafiya k'alau jibi ace maka ya zama mayye cin naman mutane yakeyi ko takeyi ".Baba Labbo yace "kwarai da gaske ma ai kinga yanzu idan da ace Gwamma lafiyarta k'alau,,,, bai dace ace na barta zaune ita kad'ai tana aikata abinda ta gadama ba ,,,,saboda naji ance yanzu har namiji yake shigowa cikin gidan nan yana tayata kwana,,, to daga barcin tare da k'ato saimi zai faru? Sai iskanci da abinda ba'a so shine zai iya biyowa baya "."Af ai iskanci da yin maita yanzu ya zama ruwan dare,,,,, saboda yanzu yanada wuya kaga wanda baya aikata d'aya daga cikin wad'annan abubuwan dana ambata,,,,, kaga kuwa saidai mu dage da yawan yin addu'a akan Allah ubangiji ya karemu daga muyagun k'addarori muda iyalanmu ".Inji Inna Tani cikeda matuk'ar sanyin jiki da natsuwa,,, baba Labbo yace "amin ya rabbi Tani lamarin mutanen yanzu sai a hankali,,,, ai Gwamma ta koyar dani darasin rayuwa idan kace ka faye shiga cikin abinda bai shafeka ba,,,, matsalolin rayuwa mutum zai jefa kansa ciki kuwa "."Hmmm maigida kenan wata rana kana bani mamaki sosai,,,, ai duk abinda ya shafi Gwamma ya shafeka saboda koba komai 'yar yayanka ce uwa d'aya uba d'aya ba lafiya bane,,, sannan kuma ko kwatance za'ayi sai dai ace yanzu d'iyar Mamman da Talatu,,, Mamman yayan Labbo mijin Tani mai wake kaga kuwa anan hannunka bai tab'a rub'ewa ka yanke kayar ,,,,ka dai k'yaleta ne saboda kaima tafi k'arfinka ne,,,, amma ako'ina akaje kaine ya kamata ka rik'eta amatsayinta na marainiya domin kaine dolenta ".Baba Labbo yayi dariya yace "babu k'arya a cikin maganarki Tani shiyasa nake k'ara sonki,,, saboda kinada natsuwa da hangen nesa Allah ubangiji yayi miki albarka kuma ya barmu tare "..
Inna Tani taji dad'in addu'arsa k'warai da gaske,,,, wani farin ciki da nishad'i ne ke wanzuwa acikin sassan jikinta gaba d'aya,,, tayi murmushi tace "amin amin maigidana ".
Firarsu suka cigaba da yi mai dad'i da ma'ana sosai,,, daga ganin yadda suke gudanar da rayuwar aurensu babu abinda suka nema suka rasa a cikin zamantakewarsu...
*********************
***Aliya ce matar Lawwali zaune tana tankad'ar garin tuwo,,, ga d'iyarta nan mai suna Hajara tana wasar k'asa agefe,,,, ita kuma uwar ta mayarda hankalinta kacokam wurin aikinta,,, can bada jimawa ba saiga sallamar Lawwali ya shigo cikin gidan,,, fuskarsa murtuk'e babu alamun fara'a ko walwala ana hango b'acin rai acikin k'wayar idanunsa ,,,,Aliya dai ta amsa masa sallamarsa cikin sanyin jiki ta kawo tabarma ta shimfid'a masa cikeda ladabi da girmamawa,,,, bayan ya zauna ne ta kawo masa ruwa masu sanyi cikin kofi ya d'auki ruwan yasha,,,, sannan yayi ajiyar zuciya yace "Alhmdlilah Allah ubangiji yayi miki albarka ".
Aliya tayi murmushi tace "amin baban Hajara amma mi ye yasa ka shigo cikin gida da b'acin rai?Har baka iya b'oye b'acin ranka kafin ka shigo cikin gida ".
Lawwali yaja dogon numfashi sannan yace "kede bari Aliya abin ne akwai matuk'ar b'acin rai da ban takaici,,,, wai nine zanje wurin yaya Gwamma in bata shawara akan abinda take aikatawa bai dace ba,, shine ta kama yimin fad'a da cin mutunci abin babu dad'in ji balantana saurare ".
"ayyah baban Hajara hak'uri zakayi domin koba komai itace sama da kai,,, kuma yayarkace kaine ya zama dole kayi mata biyayya kuma shiriya tana hannun Allah,,, da kad'an kad'an sai kaga ta daina yin duk abubuwan da takeyi ".Inji Aliya cikeda matuk'ar lallashi da ladabi..
Lawwali ya nisa yace "Aliya kenan bakisan ainahin halayyar yaya Gwamma ba,,, mace ce mai matuk'ar taurin kai da tsattsauran ra'ayi kuma duk abinda ta sama gaba komai rashin k'yawonsa,,,, ba zata daina ba yanzu ma bari in sanardake gaskiyar lamari maigari yace idan aka kama mayyu akashesu! Sannan Ummaru d'an Sala mafarauci yawon nemanta yakeyi ruwa a jallo saboda itace ta kashe masa iyayensa da yayan babansa,,,, ta cinye namansu ni kuwa ina jiye mata mummunan k'arshe da mugun hukunci ".
Aliya tace"hmmmm amma kam wannan hukuncin yayi tsauri da yawa gaskiya,,,, ana kama mutum kenan ana kashesa! To ka cigaba da hak'uri kana zuwa kana lallashin yaya Gwamma har ta daina maita,,, kafin hukuncin maigari ya hau kanta akasheta abar mana abin gori da fad'a,,, surutu,,, gulmace gulmace ko munafurci ".
"abin gori da surutu na nawa kuma saboda ni idan na fita waje,,, har nunani akeyi ana zund'ena da nunena da cewa ga k'anen Gwamma mayya can tafe,,, wasu ma har guduna sukeyi wai saboda basu yarda niba mayye bane domin Innarmu wai gadon maita tabar mana! ".Cewar Lawwali cikeda matuk'ar takaicin yadda rayuwar Gwamma ke tafiya tana cin naman mutane da aljannu!.
Aliya tace "hak'uri zaka k'ara yi ai mutane iyawa dasu sai Allah,,, sannan ya zama dole ka toshe kunnuwanka daga jita jitar mutane da tseguminsu,,,,,,saboda haka ka daina damuwa akan anyi ance da surutun mutane ".
"idan banyi hak'uri ba mi zanyi musu? Kedai Allah ubangiji ya sawwak'a yasa mu dace ".Inji Lawwali..
Aliya tace "amin baban Hajara Allah ubangiji ya sanyaya maka zuciyarka ".
Aliya ta cigaba da yi masa kalamai masu dad'i,,, sannan kuma ta k'ara nuna masa muhimmanci hak'uri da juriya akan zamantakewar rayuwar duniya,,,,, ta dinga lurar dashi ya dinga toshe kunnuwansa daga jita jitar mutane......
Allah ubangiji yaba kowa abokin rayuwa nagari..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SHEKARU HUD'U*
Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kama sauran mayyu,,, da suka addabi rayuwar mutane ana kashewa,,, Ummaru ya kama mayyu kusan ishirin yana kashewa acikin wad'annan shekarun da suka wuce,,, yayi yayi ya kama Gwamma shahararriyar mayya amma ya kasa saboda ita yanzu ta k'ara shahara da gunguma akan harakar maita! Duk wanda takeso take kwad'ayin namansa kamesa kawai takeyi,, duk da yake Lawwali yayi zuwa kusan goma yana yi mata nasiha akan ta daina maita! Amma wanda yayi nisa bayajin kira sai dai taci masa mutunci tana zaginsa,,, zuwa na goma da yayi tayi masa kashedi da inya k'ara takowa gidanta da sunan wa'azi saita kashesa ta cinye namansa! Yabar ganin uwarsu d'aya ubansu d'aya,,, jin ta fad'i haka dole yasa Lawwali yajawa k'afafunsa linzami ya daina zuwa kwata kwata saboda yasan duk abinda Gwamma tace tanayi,,, to tabbas zata iya aikatawa domin yasan halinta batada tsoro tanada dakakkiyar zuciya.
To acikin wad'annan shekarun ne Gwamma ta haifi 'yan biyu mace da namiji da Sule saurayinta,,, namijin sunansa Hassan macen sunanta Suhaila,,, bayan yaran sun fara girma da tasawa taga ai amfanin Sule ya k'are koba komai tagama morarsa,,, gashi taga yanzu shima har nasiha da wa'azi yakeyi mata akan ta daina maita! To ita kuma da mutum ya dameta akan tabar maita gara yahau risho da wandon leda,, ganin da tayi Sule yana neman takurawa rayuwarta yasa dole ta kame masa kurwa ta mayar ita zakara,,, arannan ne ta yanke zakaran ta cinye abinta tasha ruwa tayi gyatsa.
_Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Allah ubangiji ya rabamu da aikata masha'a da kuma biyewa *SON ZUCIYA*..._
Aka wayi gari Sule ya mutu abin kamar almara,,, akayi masa wanka aka kaisa makwancinsa na gaskiya,,, Allahu Akbar duniya ba matabbata bace duniya mai cikeda bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, Gwamma ta cigaba da gudanar da rayuwarta cikeda kwanciyar hankali da jin dad'i,,,tareda da kula da yaranta cikeda matuk'ar k'aunarsu batason ko k'uda ya tab'asu idan da son ranta ne,,, babu abinda take so da k'auna fiyeda yaranta.
Ita dai cigaba da cin naman mutane dana aljannu kawai takeyi wata rana ta mayarda kurwar mutane zakara ko rago taje can kasuwar wani gari,,, inda ba'a santa ba tana samun kud'inta cikeda wayo da 'yan dabaru ta haka ne take samun kud'ad'e tana ciyarda yaranta da kashewa kud'i .......
_Share &Comments_
[7/6, 6:05 PM] Mugiratmusa66: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*MAYYA CE*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥🍥
🍥🍥🍥
🍥🍥
🍥
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍🏻
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 27*
**Ta haka ne take samun 'yan kud'ad'e tana kashewa da kuma kula dasu Hassan,,, haka dai take gudanar da rayuwar gidan da maitarta,,,, Lawwali kuma ganin irin walak'anci da korar kare da Gwamma tayi masa ya watsar da ita gaba d'aya ya fita harakarta,,, saboda yasan tunda ta bud'i baki tace zata kashesa to tana iya kashesa abanza da yofi yabar yaransa da matarsa cikin k'unci da tsananin maraici,,,, baba Labbo ne dama ya tsorace gameda lamarin Gwamma mayya,,, domin tun lokacin da yaje domin ya dawo da ita gidansa ta rikid'a ta koma macijiya ta koresa,,,,,to tun daga lokacin nan bai sake giftawa ko bakin k'ofar gidan nan ba,,,, balantana yaje ya shiga cikin gidan kunsan yadda baba Labbo yakeda masifar tsoron mutuwa da mayyu!. Ummaru mafarauci dai yana nan yana cigaba da bibiyar duk wani motsi na Gwamma,,, sannan duk inda taje yana hankalce da ita yana kallonta babu inda zataje ko tayi wani motsi ba'a kan idon Ummaru ba,,, ya damu sosai ta yadda take azabtar da mutane da cin namansu amma ya gagara kamata! Shiyasa dole wata rana yayi zaune yana tagumi da bak'in cikin rashin kama Gwamma mayya,,, domin zaluncinta da cin amanar mutane sai k'aruwa yakeyi,,, bata tunanin abinda zaije ya dawo a rayuwa bata tunanin ai wata rana dubunta zai iya cika,,, bata tunanin wata rana zata bar duniya baki d'aya taje can ta girbi abinda ta shuka? Ita dai Gwamma gatanan dai kamar ba mutum ba zuciyar nan babu d'igon imani da tausayi,,, ta k'ek'eshe zuciyarta daga barin tsoron kowa bata gudun abinda zai faru,,, bata tunanin kamar yadda aka kama sauran mayyu 'yan uwanta to ita ana iya kamata!.
Mutanen gari kuma kowa ya shiga taitayinsa,,, saboda kada su afka cikin tarkon Gwamma mayya,,,, kowane daga cikinsu ya tashi tsaye tareda dagewa da yawan addu'ar Allah ubangiji ya kawo musu k'arshen zaluncin Gwamma,,, domin susan Ummaru yana iya bakin k'ok'arinsa na ganin ya kamata amma abin yaci tura! Ya kasa kamata saboda yadda takeda k'arfin sihiri da gunguma acikin harakar maita,,, kunsan ta zarce mahaifiyarta Inna Talatu awurin shahara da bunk'asa domin ita har aljannu tsoronta sukeji balantana bil Adama,,,, bata shakkun tunkarar kamun kurwar kowa acikin garin Gumi,,, Ummaru kawai ne take d'an tsoronsa domin kada wata rana dubunta ya cika ya chafketa!.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Ummaru ne zaune yayi tagumi cikeda matuk'ar bak'in ciki da damuwar rashin kama Gwamma,,, ya rasa yadda zaiyi ya kamata.
Salma ce ta jaye hannun Ummaru daga yin tagumin da yakeyi,,, sannan ta dubesa tace "lafiya baban Husna kana tagumi?Babu k'yawo ka daina sama kanka damuwa ".
Ummaru ya d'ago idanunsa da sukayi jawur akan damuwa,,, yace "Salma ina cikin damuwa wai ace wadda tayi sanadin mutuwar iyayena da baba Labaran,,, na kasa kamata sai yawo da hankali takeyimin ta mayardani mahaukaci ko mara sa'a a rayuwa ".
Salma ta kallesa cikeda matuk'ar tausayawa da k'auna matuk'a,,, tace "haba farin cikin rayuwata miyasa zaka damar da kanka,,,akan abinda akodayaushe akowane lokaci kana iya kamata,,,kai bakasan komai yanada lokaci da k'addara ba? Idan Gwamma ce zaka kamata duk ta gama guje gujenta da b'oye b'oyenta sai dubunta ya cika! ".
"ni ba haka naso ba so nayi in kamata yanzu in gana mata azaba,,, sannan daga baya in kasheta kamar yadda ta kashemin iyayena! ".Cewar Ummaru d'an Sala mafarauci.
Salma tace "kayi hak'uri maigidana zaka d'auki fansar jinin mahaifanka,,, kuma ka daina saka damuwa da tunanin abinda bana damuwa ba,,, ni nasan komai daren dad'ewa zaka kama Gwamma ka kasheta har lahira! Lokaci yana nan zuwa ka daina damuwa ".
Ummaru yace "to babu damuwa Ummu Husna,,,, zan daina saka damuwa acikin raina da zuciyata ".
"da kam yafi baban Husna ka saki zuciyarka,,, komai yanada lokaci kuma zaizo ya wuce kamar ba'ayi ba ".Cewar Salma cikeda matuk'ar lallashi.
Ummaru yace "tabbas haka ne gaskiyar maganarki ".
Salma ta cigaba da bashi maganganu masu sanyi,,, da kuma lallashinsa da yayi hak'uri akowane lokaci zai iya kama Gwamma..
*********************
**Bayan shekaru goma ne alokacin ne su Hassan suka girma,,, sunada shekara ashirin da uku,,,, Suhaila ta samu miji mai k'aunarta tsakani da Allah ya aureta,,, amma saida suka kafta tashin hankali da bala'i da Iya Gwamma domin nuna tayi ita ba zata aurar da Suhaila ga Salihu ba,,,, shi kuma dayake yana sonta itama tana sonsa shiyasa ta nace saita auresa,,, babu irin kashi da zagin da Suhaila bata sha ba akan son da takeyiwa Salihu saboda itama Gwamma so takeyi ta gajeta a cikin maita! Ita kuma tak'i bin umurninta domin bataga wata ribar da mayyu suke samu ba idan suka zama mayyu,,, ganin irin haka ne yasa shima Hassan ya bid'i kud'in aure ya fara kasuwanci,,, ya nemi wata Aisha nan mak'wabciyarsu yayi aurensa,,, sannan ya kwashi matarsa ya samu wani gida madaidaici ya saye suka shige shida matarsa hankalinsu kwance..
Iya Gwamma ganin d'iyanta sun watse sun barta akan bala'inta da masifarta,,,, rana guda ta kama zaginsu tare da tsine musu albarka su suna can gidajensu basusan abinda yake faruwa ba,,,,, to dayake batada rik'o arayuwarta nan da nan ta fita harakar d'iyan tareda cigaba da cin naman mutane da aljannu,,, babu tsoron Allah ko kad'an a cikin zuciyarta..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*CIGABAN LABARI*
Mama Sa'ima da Alhaji Suleiman ganin yawon Maryam yayi yawa,, dole yasa uwar take sakawa 'yarta idanu da hana mata yawon zuwa ko'ina idan ba makaranta ba,,, saboda gudun kada mayyu su kamata basusan sun riga sunyi fad'a da Iya Gwamma k'usurgumar mayyar da ta addabi rayuwar mutane shekara da shekaru ba,,, Ummaru ya kasa kamata alamar sai taci zamaninta,,, shi dai bai hak'ura ba yana nan yana bibiyar rayuwarta kuma yasan yanzu duk d'iyanta sun gudu sun barta,,, saboda mummunan dabi'ar da take aikatawa wato yin maita da rikid'e rikid'e da tsafe tsafen da bayada k'yau ko addinin musulunci..
Mama Sa'ima ce zaune tana tsintar k'asa acikin shinkafa,,, Mubarak yana zaune gefenta yana tayata suna fira cikin natsuwa da kwanciyar hankali..
Alokacin ne Mubarak ya dubi Mama Sa'ima yace "amma yau ana zafi sosai agarin nan,,, baba yana can kasuwa kuwa gashi akwai rana sosai ".
"zafi ai lokacinsa ne Mubarak ai fita kasuwa ya zama dole ga Alhaji,,, saboda kaga yanzu idan bai fita ba yaran yanzu masu tsaron shago ba kowanensu keda amana ba,,, sai 'yan kad'an daga cikinsu sukeda amana da gaskiya ".Cewar Mama Sa'ima.
Mubarak yace "ai Alhaji yanada hak'uri da juriyar zama da mutane,,, musamman idan mutum ya samu masu tsaron shago ko marasa gaskiya sai yakai zuciyarsa nesa ko ya koresu".
Mama Sa'ima tayi murmushi tace "ai zaman duniya iyawa ne gaskiya idan baka iya zama da mutane sai zama ya gagareka da mutane,,,,, mutum yazo yana fad'a da mutane kowa ya tsanesa,,, ai rayuwar da kake ganinta gaba d'aya sai mutum yayi hak'uri da juriya a rayuwa ".
"haka ne gaskiya Mama ni abinda yake bani tsoro da takaici shine,,, yadda zamanin nan namu ya lalace kowane ka gani ya zama mayye ko mayya,,, saboda tsananin kwad'ayi da son abin duniya da dogon buri! Ni abin yana cimin tuwo a k'warya bansan yadda abubuwan suke faruwa ba? ".Cewar Mubarak cikeda jimamin abinda ke faruwa cikin gari.
Mama Sa'ima tayi murmushi taja numfashi,,,, sannan tace "ai lamarin mayyu sai addu'a saboda yafi k'arfin Al'umma,,, saboda haka koni abin yana damuna babu yadda zamuyi sai hak'uri akan lamarin mayyu! Sai addu'a da neman tsari daga sharrinsu".
Mubarak yace "Allah ubangiji ya karemu daga sharrin masu sharri a cikin mutane da aljannu ".
"Amin ya rabbi Mama ".Inji Mubarak.
*BAYAN KWANA BIYU*
Bayan faruwar wannan al'amarin tsakanin Iya Gwamma dasu Fatima,,, na rashin mutuncin da Fadila tayiwa Iya Gwamma saiya zamo iyayensu Fatima sun hana musu zuwa ko'ina kamar yadda aka hanama Maryam,,,, domin aran nan da suka kama yiwa su Fadila fad'a kamar zasu dokesu da yake Fatima tanada tsoro sosai shine ta sanardasu irin abinda ya had'a su da Iya ta aikesu,,, da kuma rashin kunyar da Fadila tayi mata duk saida ta gaya musu.
To sunsha fad'a sosai rannan akan rashin kunyar da Fadila tayi ma Iya Gwamma,,,,, kamar abasu mugun kashi saboda abinda Fadila tayima Iya Gwamma,,,,,Fadil yayan Fadila kamar ya bata kashi akan rashin kunyar Fadila tayi yawa da kuma tsiwarta..
Amma Iyayennasu mata suka hana ya bugeta saboda sunsan bugu baya horar da yara,,, sai dai addu'a da yawan jama yaro kunne ,,,to wannan maganar dai anan atsakaninsu Iyayen mata suka bar maganar,, basu sanarda Iyayen maza ba saboda sunsan sune da laifi,,, sannan su mazajen zasu yiwa fad'a kunsan ance laifin d'a baya wuce mahaifiyarsa.
Ana nan dai kwatsam! Fadila da Fatima rashin lafiya ya kamasu kusan atare,,, ita Fatima amai da zawo ne takeyi duk ta rame tayi bak'i sannan ta fige babu k'yawon gani,,, ita kuma Fadila ciwon zazzab'i da ciwon kai ne ya kamata sannan ga wasu k'ananan k'uraje nan da suka fara fitowa a jikinta,,,ciwon yayi matuk'ar ramar da ita yasa ta fita cikin hayyacinta k'warai da gaske,, Iyayensu hankalinsu yayi k'ololuwar tashi sosai,,, babu abinda sukeyi sai kukan zuci dana zahiri ga bak'in ciki da k'uncin rayuwa.........
0 comments:
Post a Comment