Cikin farinciki Hajiya bulkisu ta tarbesu suka zauna shiko Alhaji Umar yakasa rube bakin shi sabida tsabar murna cikin girmamawa suka shiga gaisawa cikin lokaci kad'an aka kawo musu abinci da abubuwan motsa baki
Sun dad'e suna tahira tsakanin barrister da Alhaji Umar Affan da Ashiraf da Ayman suna gefe d'aya suma hira sukeyi amma banda Affan wayar shi kawai yake latsawa itako Hajiya bulkisu jan Momy tayi suka nufi d'akinta ganin momy ta tada sallah yasa Hajiya bulkisu fita kai tsaye bedroom d'in Seeyama tanufa kwance tasameta sefaman sauke ajiyar zuciya takeyi alamar tasha kuka girgiza kai Hajiya bulkisu tayi sannan tace
" amma kekam Seeyama bansan irinkiba wato sokike kijamana abin magana ko ? ace kinajin ba'ki amma ki'ki fitowa gaidasu to wallahi idan mahaifin ki yatasaki yanafad'a babu ruwana inamai Umar tarki dakiyi maza kije ki gaidasu "
Jin Ammi tafita yasa Seeyama sake fashewa dakuka sannan tatashi toilet tashiga tayo wanka sannan tayi sallah simple makeup tayi tafesa turarukanta masu dad'in kamshi sannan tafito
Koda tafita kowa yana wajan dinner amma banda Affan cikin ladabi tashiga gaidasu kanta na 'kasa murmushi Momy tayi tace
" zonan 'yata masha Allah "
Cikin ladabi Seeyama tanufi gurin Momy amma cikin zuciyarta jitake kamar tace bazataba shiko Ashiraf kallonta yakeyi yanason tuno inda yata'ba ganin wannan fuskar amma yakasa tunowa cikin karamci Momy tarungumo Seeyama tana sakamata albarka maganar Ammi tasa Seeyama jin muguwar damuwa
" ke Seeyama jeki had'ama Affan abinci kikaimai yana part d'in yayanki "
Cikin rashin kuzari tami'ke tanufi kitchen cikin zuciyar ta tana fad'in
" amma wannan mugun d'an isane kowa yana nan amma shi yawani ware kanshi hmmm "
Cikin zolaya Alhaji Umar yace
" kai Ashiraf babu ruwanka amma shi d'an'uwanka yakasa sakin jikinshi "
Murmushi Ashiraf yayi sannan yace
" ayshi Affan hakayake bayason hayaniyane Abba ko agida hakayake "
Cigaba sukayi dacin abinci cikin 'bacin rai Seeyama ke had'a abincin tsayin lokaci seda Ammi tasakeyin magana sannan tafito cikin sanyin jiki tanufi part d'in Ayman kodata isa bakin door d'in seda tad'an jima sannan tashiga ko sallama babu
Zaune Affan yake kan d'aya dagacikin cushion d'in madaidaicin parlour kanshi da kafad'unshi kawai Seeyama ke iya hangowa sabida yajuya bayanshi jin 'karar bud'ewar 'kofar yasa Affan jin 'bacinrai dan yasan tabbas itace Seeyama cikin kakkausar muryar shi yace
" ko waye yakoma yayi sallama kokuma yakoma "
Tsuki Seeyama tayi ta'idasa shiga ciki batare datayi sallamar ba har gabanshi ta'isa amma kanta adu'ke ta'aje tiran abincin sannan tace
" dan Allah bawan Allah kataimakeni kajanye maganar aure na inada wanda nikeso dan Allah karka cutar da rayuwa ta "
Wata irin sassanyar ajiyar zuciya Affan yasauke tsayin lokaci danhar tacire rai dazaiyi magana sannan yace
" Alhamdulilah kinrufama kanki asiri nima bana bu'katar auranki dama danna cika umarnin mahaifinane yasanazo inaso kisanar musu bakya sona ni DON bazan ta'ba son wata 'ya mace ba "
Jinya ambaci wannan sunan yasa Seeyama saurin d'agowa cikin sauri tami'ke nunashi tayi tace
" kai kai kaine ? "
wani irin murmushi Seeyama tasaki cikin rawarjiki tanufeshi babu zato yaji tarungume shi dede kunnan shi tace
" kai nakejira My DON kai..... "
Wani irin hankad'ata yayi harseda tafad'i azafafe yace
" wannan wane irin wawancine kiyi gaggawar shiga hankalin ki idan bahakaba senayi mugun wula'kantaki kuma kiyi gaggawar sanar d'azu bakison aure na idan bahakaba to wallahi zakiyi nadama "
Cikin sauri Seeyama tami'ke tace
" bazan ta'ba janye maganar auran kaba koda idan anyi auran zaka rabani da rayuwa ta ne danke nace bazan auri Affan ba to ashe Affan shine DON d'ina gaskiya wannan turaran naka ina matu'kar sonshi kamar karnabar saman 'kirjin ka my Husband "
Cikin mugun ba'kin ciki DON yayo kanta cikin sauri tajuya tafita tanajin wani matsanancin farinciki komawa yayi yazauna yadafe kanshi yanajin zafi cikin zuciyar shi
Yanayin da Seeyama tashiga parlour yasa Ammi yin mamaki amma setabar abin cikin ranta misalin 09:30 Ashiraf yaja hannun Ayman sukafita waje cikin mamaki Ayman yace
" Ashiraf inakake son muje ayanzu ? "
d'an shiru Ashiraf yayi yana nazarin abincewa sannan yace
" wajan mai tea zakarakani "
Kallon shi Ayman yayi cikin mamaki sannan yace
" amma de idan tea kake son sha aybasemunje kan titiba se asa Seeyama tahad'amaka ko Zarah mazata'iya "
Girgiza kai Ashiraf yayi yace
" kaide muje kawai "
Badan Ayman yasoba haka yarakashi tea yasa akahad'a mai kauri da kwai da breed sannan sukataho kasa ha'kuri Ayman yayi yace
" dama baka 'koshiba kabarcin abincin ? "
Murmushi Ashiraf yayi sannan yace
" Ayman banizanciba nasan d'an uwana bai cikomiba ayanzu koda ankaimai abinci nasan baicishiba "
Cikin mamaki Ayman yabishi da kallo kawai cikin zuciyar shi yana tunanin akwai abindake damun Affan koda sukashiga baya parlour kai tsaye suka nuficiki adede lokacin yafito daga toilet dagani wanka yayi jikin shi sanye da farar jallabiya
Fita Ayman yayi yakawoma Ashiraf flet da Cup yafita abincin da akakawo ma Affan Ayman yafita dashi part d'in su Ammi yakaishi kitchen yadawo jin maganar da Ashiraf keyima Affan yasa Ayman juyawa sabida bayason jin abunda baishafeshiba
" haba DON kadaure ka'aje komi har mubar 'kasarnan kanaganin yadda Abba yanuna yadda yake 'kaunarka afili bazaiso ganin wannan yanayin nakaba kadingacin abincin da akakawo maka ko....... "
" bazan ta'ba cin abincin wata mace ba Ashiraf kuma bazan iyacire komi daga rainaba lallene nayi maganin Seeyama sabida naga kanta yanayimata rawa 'kila setasake shan marina a Sudan kamar yadda tasha a Saudiyya karona 2 "
Jin wannan furucin yasa Ashiraf tuna Seeyama a hankalin Affan keshan tea d'in Ayman da Ashiraf se janshi da hira sukeyi amma ya'ki kulasu
Ammi kam takasa ha'kuri tashi tayi tanufi bedroom d'in Seeyama jin alamar bud'e 'kofa yasa Seeyama saurin waigowa ganin Ammi yasa Seeyama saurin nufota cikin tsantsar farinciki tarungume ta tace
" Ammi Affan shine DON d'ina Ammi shine nake matu'kar so nake burin yazama ubana 'ya'yana "
'Dan tureta Ammi tayi tace
" tafican dawannan rashinkunyar taki amma dase wahalar dakanki kike "
Cikin zuciyar Ammi kuwa farinciki ne sosai takeji aranta zamatayi tafarayimata nasiha mairatsa zuciya sannan tafita washegari Seeyama dakanta tashiga kitchen dan had'ama DON breakfast kallon takwai Ammi keyi Zarah ma abin mamaki yabata bayan tagama takoma bedroom d'in ta wanka tayi sannan tazo gaban mirror tsayin lokaci tana makeup wasu riga da sikat nawata kyakkyawar atamfa tasha d'inkin yayi matu'kar amshar jikinta
Cikin wani irin taku tafito sezuba kamshi takeyi kallon ta Ayman yayi yace
" Seeyama wannan kwalliya haka gaskiya sirikinnan nawa yanada sa'a "
Saurin du'kar dakanta tayi sabida su Abba duk suna gurin gaishesu tayi shima Abba farincikin hakan yayi sosai yace
" Seeyama kije kikaima Affan breakfast yanzu yagaidamu yafita shibazai iyazama cikinmu yaci abinciba mijin naki bayason hayaniya "
Jin haka yasa Seeyama nufar hanyar kitchen dan dama abindatake sonji kenan cikin wata irin tafiya ta'isa part d'in awannan lokacin bakinta d'auke da sallama yanzuma zaune tasameshi yana kallon News hannun shi ri'ke da Cup yanashan tea har gabanshi ta'aje tiran breakfast d'in cikin wata irin murya tace
" barka da safiya my baby "
Cigaba dashan tea d'in shi yayi kamarma baijitaba murmushi Seeyama tayi tace
" baby gaskiya kayi matu'kar kyau wannan saddar tayima kyau sosai kamar ranar angoncinmu "
Ganin bashida niyyar koda kallonta yasa tazauna kusadashi hannunta tad'aura saman 'kafad'arshi cikin 'bacin rai yawatsa mata sauran tea d'in dake hannun shi sannan yasauke mata wani mugun mari har 2 baiko tsaya sake kallon taba yafita daga part d'in kai tsaye part d'in su Abba yanufa
Wani irin mugun ba'kinciki Seeyama keji cikin 'bacinrai tace
" ni kayiwa haka DON nasha alwashin sekabani ha'kuri akan wannan abun aure nidakai babu bashi senasa kasan mace ba abar wula'kantawa bace "
Bin bayanshi tayi Affan nashiga yasamu dady da Abba cikin ladabi yace
" dady kugafarceni zankoma yau sabida zangabatar dawani ayki nagaggawa "
Murmushi dady yayi yace
" haba Son yakamata kabari agama wannan hidimar bikin ko ? "
Cikin rashin damuwa Abba yace
" a'a Alhaji Ibrahim kabarshi yatafi aykinshi yanada matu'kar mihimmanci zamuyi komi koda bayanan sekutafimai da matar shi babu komi Affan katafi Allah yamaka albarka bayan wannan bikin zamuzo ganin mahallinka nida Amminku da 'yan'uwanka "
Tashi Affan yayi yamusu sallama dede 'kofar fita yaci karo da Seeyama wani irin kallo yayimata wanda yasa dole seda ta kauda idanunta bin bayanshitayi tasha gabanshi cikin raunanniyar murya tace
" baby karka tafikabarni dan Allah idan bakason inazuwa inda kakene bazan kuma zuwaba "
Wani irin kallo yayimata har yayigana seya tsaya yace
" kitaimaki kanki kicemusu bakison aurena dan idan kikabari ba'kinciki da damuwa sune zasuzama abokan rayuwar ki "
Yanagama fad'ar haka yanifi part d'in Ayman dan had'a kayanshi cikin kuka Seeyama tajuya tana shiga tanufi bedroom d'in ta kan bed tafad'a tasaki kuka amma cikin ranta tasha alwashin setasa DON yasota somai tsanani
Har airport su dady suka raka Affan kiran Affan dady yayi yace
" DON nasan babu wani aykAdazakayi amma kace haka nasan sabida bakason wannan auranne to amma yazakayi shikenan zamutahoma da matarka idan kaje kaje kagano matarka kotana bu'katar wani abu "
Jinjina kai kawai yayi zuciyar shi cikeda kunci yajuya yashiga jirgi cikin mamaki Ayman yananata zancan
" Matarshi ? kenan Affan yanada wata matar amma shine babu wanda yasanar shiyasa ya'ki sakinjikin shi da 'kanwata lalle hakan bazai ta'ba yiyiwaba "
Suna isa Ayman yashiga cikin bedroom d'in Ammi zaune yasameta cikin takaici yace
" Ammi wallahi bazamu yardaba ashe Affan yanada mata ? " shin..... "
Cikin sauri Ammi tami'ke azafafe tace
" mata ? lalle to 'yata bazata zaunada kishiyaba sede afasa wannan auran ko yasaki waccan matar tashi barinasamu Abban naku inah........ "
" karku sake wannan auran babu fashi kuma bazai rabuda matarshiba akan tamu 'yar sannan karku sake kubari kowa yasan wannan maganar ciki hadda Seeyama "
Cikin 'bacin rai Alhaji Umar yafita azafafe Ammi tace
" lalle wallahi bazan ta'ba yardaba idan kunsan wata aybakusan wataba "
Nigeria yau kwanaki 3 da dawowar DON amma baije gurin Kausar ba tuna maganar Dady yasa yashirya yanufi skul d'in nasu cikin wani had'add'an yadi mai kyau da tsada kallon d'aya zakayimai kace masha Allah
Daga Al'kalamin ✍🏻
NPEEDY A Aji ♣♥♠
Love u all sisters comments
Shere
[13/06 11:43 am] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠ RUFAFFIYAR ZUCIYA ♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵
♠
Story & Written
By
NPEEDY A AJI
Dedicated to
My Hajjaju
🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟
G.W.F
home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫
ANA TARE 🤝🏻😍🌹
🅿 { 19 to 20 }
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Kuka sosai Kausar keyi dandanan wani irin ciwon kai yakamata cikin kuka tace
" innalinlahi wa'inna ilaihirraju'u yanzu wannanne mijina marar imani da tausayi ? yazanyi a ranar dayasan banida budurci tayaya zan'iya wanke kaina awajan wanda babu tausayin mace a zuciyar shi ko kad'an Allah kaceceni "
Sake fashewa tayi da kuka had'ida dafe kanta shiko DON wurin wani ayki dayabada yawuce tunkafin yayi parking zugar ma'aykatan gurin sukanufoshi bud'e murfin motar yayi yaziro 'kafarshi batare dayafitoba kallon su yayi tsayin lokaci sannan yace
" ina fatan kunjuya ginin kamar yadda nace ? "
'Daya dagaciki yace
" rankashi dade anjuya kuma in sha Allah nanda 3 weeks zamu kammala ginin zaka iyashiga kagani "
Maida 'kafarshi ciki DON yayi yace
" banida lokacin tsayawa gani yanzu amma idan naga baiyiba to zaku kuma rusheshi dan haka seku kiyaye "
Rufe motar shi yayi yafigeta kallon bayan motar sukayi d'aya daga ciki yace
" yaro amma Allah yabashi mugun kud'i kaga wannan gidan mukammu masuyinshi munsan yashihara "
Ganin tunkarowar jerin wasu motoci yasa sukayi shiru nesadasu sukayi parking Alhaji Sambo ne da abokanshi kaitsaye gurinsu suka nufo cikin yatsina fuska Alhaji Sambo yace
" waye yabaku kwangilar wannan ginin sannan waye mamallakin wannan katafaran gidan "
'Daya daga cikinsu wanda shine oga yace
" Alhaji gaskiya bamusan waye mai wannan gidan ba kuma musede akiramu tawaya abamu umarni "
Tsawa Alhaji bala yayimai yace
" wanda yabarnan yanzufa waye shi ? maiyasa baifito daga motar ba ? karku renamana wayo mana duk maihawa waccan dan'kareriyar motar shine mai wannan gidan karku 'batamana lokaci ku'batama kanku waye mai wannan ginin dakukeyi ? "
Cikin 'bacin rai wani yace
" haba Alhaji gaskiya muwannan tuhumar ta'ishemu haka kudakuke manyan 'yan kwangila kunkasa sanin mai wannan gidan semu dan Allah kuzomuje kan aykinmu "
Juyawa sukayi suduka sukabarsu anan tsaye cikin 'bacinrai Alhaji Hamisu yace
" barsu semun gano wanda akaba kwangilar wannan katafaran ginin dan wallahi sede ayi 50 50 komu tasa 'keyarshi zuwa kiyama bashikad'e zeci wannan arzikinba "
DON yana shiga yanufi cikin bedroom d'in da Kausar take haryanzu shasshekar kuka takeyi babu alamar damuwa cikin ranshin yace
" Kifito kikwashi kayanki gasunan a parlour "
Daganan besakecewa komiba yajuya yafita kai tsaye cikin bedroom d'in shi yashiga toilet yashiga yayi wanka yasa kayan shan iska yafito parlour TV yakunna yafara kallon news gurin daya aje kayan Kausar yakalla ganin basu gurin yasashi girgiza kai
Misalin 8pm Kausar tafito daga cikin bedroom fuskarta tayi matu'kar kumbura gawata irin yunwa datakeji kitchen tanufa amma taduba ko ina babukomi na sarrafawa aciki dole tadawo parlour tazauna cikinta sefaman 'kugi yakeyi ga ciwon kai
Babu jimawa dazaman Kausar DON yashigo hannunshi ri'ke dawasu ledoji bedroom d'in shi yanufa ko kallon inda Kausar take baiyiba cikin damuwa tabishi dakallo ganin yunwa naneman kassarata yasa tami'ke cikin sanyin jiki tanufi bedroom d'in shi
Tsaye tayi bakin 'kofar tafarayin sallama amma shiru babu amsa har sau 4 tabud'e baki zatasake yadakamata wata irin tsawa
" wannan wane irin wawancine kinyi d'aya na amsa amma se maimaitawa kikeyi idan babu abinda yakawoki kiyi gaggawar fita "
Cikin sanyin jiki tashiga cikin zuciyarta kuwa cewa takeyi
" sede idan aljanun dake cikin bedroom d'inne sukaji amsawar ka "
amma azahiri cewatayi
Yaya barkada dare dan Allah yaya kataimakamin damagani kaina ciwo yakeyi kuma inajin yunwa naduba kitchen babu komi nasarrafawa "
Wani irin kallo yayi mata kamar bazaiyi maganaba zuwacan yace
" tashi kibani guri kije wajan 'yan'iskan samarinki subaki "
Dagahaka baisake cewakomiba yamaida hankalin shi kan system d'in shi jiki a sanyaye Kausar tabar cikin bedroom d'in d'ayan bedroom d'in tanufa cikin mamaki ta'idasa shiga sabida hango wata leda datayi saman freezer cikin bedroom d'in cikin sauri takai hannu wani had'ad'an abincine da yoghurt
girgiza kai tayi tace
" gaskiya yaya Affan mugun miskilancinka yayi yawa yaushema yashigo ciki oho Allah kabani juriyar zamadakai yaya Affan "
Dukda yunwar datakeji amma bata'iyacin abincin sosaiba tashi tayi tayowanka tayi shirin bacci kwanciya tayi amma takasa rintsawa tunanin abubuwa dayawa sunhanata bacci wasu irin hawaye suka shiga gangaro mata cikin shasshekar kuka tace
" Dady wane lefi na'aykata maka kahad'ani da wanda zai'iyayin ajalina kamar yadda yakeda ciwon zuciya nasan nima senakamu dashi sabida ba'kin cikin dazaita dasamin Allah kasakamin akan wannan sar'ka'kiyar da'aka kullamin "
Rurin da wayar shikeyi yasashi maida dubanshi kan phone d'in ganin maikiran wayar yasa yakai hannu yad'auka cikin girmamawa yayi sallama dagacan 'bangaran akace
" my son an kammala komi gamaida auranka yanzu Seeyama tazama matarka zamutaho nanda kwanaki 2 zamukaima amaryar ka saban gidanka dake cikin Kaduna kafin akammala wannan ginin naka na Abuja kayi 'ko'kari kazo tarbar amaryarka Allah yabaka ikonyin adalci a tsakaninsu "
Wani irin kululin ba'kin ciki DON yaji yatasomai yatekare mishi wuya da'kyar yace
" kayi ha'kuri Dady bazan samuzuwa a wannan lokacin ba sabida aykin danikeyi amma idan nakammala zanyi 'ko'karin zuwa "
Murmushi dady yayi sannan sukayi sallama ture system d'in DON yayi sabida wata sabuwar damuwa yakeji
" wai Amaryata ? ni Affan tayaya zan'iya gudanar da rayuwa tareda mace macanma har 2 ? "
Jin zuciyar shi naneman fara ciwo yasa yashiga toilet yasakarma kanshi ruwa cikin 'bacin rai Alhaji Sambo yashiga cikin parlour Hajiya Aysha zibewa yayi kan cushion batare dayace mata komiba
Kallon shi Abdulhakim yayi yamaida duban shikan TV batare dayacemai komiba cikin tuhuma Hajiya Aysha tace
" Alhaji lafiya ? tund'azu kainike jira natambayeka amma kashigo babuko sallama maiyafaru ? "
Girgiza kai Alhaji Sambo yayi sannan yace
" inafa lafiya Aysha ansamu wani saban d'an kwangila yafara mamaye komi gashi har yanzu munkasa gano wayeshi cikin lokaci kad'an zaimaye gurbin Alhaji Isma'il komi nawa yafarayin 'kasa dole nami'ke dan tunkarar abinda zaizamarmin barazana gabada gaba "
Jinjina kai Hajiya Aysha tayi sannan tace
" to Allah yakyauta ashe akwai babban 'kalubale agabanmu kaida mukeso kazama tamkar Alhaji Isma'il amma abin yagagara se yanzu rana tsaka asamu wani gaskiya dasake amma Alhaji dukba wannan ba tukun banga takardun d'ayan Company ninaba karde suna gurinka gas....... "
Cikin tsawa yadakatar da ita dafad'in
" Kai Hajiya Aysha karki maidani matsiyaci mana tayaya duk abinda bakiganiba naki sekikama tambayata kinta'ba bani ajiyar wasu dagacikin kadarorinki ? to daga yau idan kika sake tambayata wani abu dayashafi kadararki sena baki mamaki "
Tashi yayi yafita afusace cikin ba'kin ciki tabishi da kallo kallonta Abdulhakim yayi yace
" Momy Dadyne yad'auka "
Cikin takaici da'bacinrai tace
" rufemin baki shasha kawai bazaka'iya karemin dukiyataba haba Abdulhakim kanaganin yadda mahaifin ka keson tsiyatani amma baka iya hanawa ? kefa bayaran goge bane kasanwasu abubuwan narayuwa amma kake bari mahaifin ka nacutar dani akan idanun ka "
Cikin dakewar zuciya Abdulhakim yace
" Momy bazan iyasaka baki ko hannu akan dukiyarki ba dakuma tsakaninki da dady ba sabida banason na'bace a duniya kamar yadda brother na ya'bace acikinta sanadin son kud'inki Momy kinza'bi kud'i akan Brother na gashi yatafi har yanzu babu labarinshi kuma banga kinyi nadamaba tayaya zansa kaina cikin lamarin dukiyar ki nima kiturani duniy........ "
Wani zazzafan mari tad'auke shi dashi tace
" a'ina kaji wannan labarin ? sannan kakalli tsabar idona kake gayamin haka "
Juyawa Abdulhakim yayi yanufi bedroom d'in shi batare dayace mata komiba kaikomo Hajiya Aysha tashigayi a tsakiyar parlour ta afili tace
" waya sanar da Abdulhakim wannan labarin ? Waya gayama bana tunanin Affan kodan tarin dukiyar shi danikeso dole nayi tunanin ina yake amma bazan gaji daneman barrister Ibrahim ba dan nasan dukiyar Affan tana gurinshi idan Affan yamutu nice mai hak'kin mallakar dukiyar shi hmmm dole nasake mi'kewa wajan neman barrister "
Daga Al'kalamin ✍🏻
NPEEDY A Aji ♠♥♣
Comments and shine plssss
[13/06 6:57 pm] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠ RUFAFFIYAR ZUCIYA ♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵
♠
Story & Written
By
NPEEDY A AJI
Dedicated to
My Hajjaju
🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟
G.W.F
home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫
ANA TARE 🤝🏻😍🌹
Assalama alaikum ina godiya agareku maitarin yawa masoya Allah yabar zumunci
Am dan Allah fan's indena wuta ana binada fetir sisters 😊 idan na'kone tayazan'iya typing 😊 ana tare
🅿 { 21 to 22 }
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Tunda safe DON yafita babu jimawa yadawo tare dawata Doctor fuskar nan tashi atamke yanufi cikin bedroom d'in tsakiyar gado yahanko Kausar tadu'kun'kune se rawar sanyi takeyi cikin sauri ya'karasa hannun shi yad'aura saman goshinta cikin sauri yajanye hannun shi sabida tsananin zafin dakan yad'auka juyawa yayi zaisauka daga kan bed d'in cikin rawar jiki Kausar takamo hannun shi cikin galabaitacciyar murya tace
" yaya Affan dan Allah kabani magani kayimin dan Allah badanniba yayana "
Kallon cikin idanunta yayi karo na 2 dayaji tausayin wata 'yamace tuno yarinyar dayayima fayd'e yayi jiyayi tamkar muryarta batare da saninshiba yashafi fuskarta sannan yajinjina mata kai yafito tare yakoma cikin bedroom d'in da doctor hard'e hannuwan shi yayi gefe yana kallon yadda take duba Kausar bayan tagaka tadubeshi tace
" ranka shidad'e matarka tanafama da matsananciyar damuwa wadda zata iyahaddasa mata jininta yahau gaskiya tana bu'katar kulawa kuma yakamata tadingacin abinci sosai kuma akan lokaci asiyomata wa'innan magungunan " taci abinci tasha "
Amsar paper yayi sukafita tare komawa Kausar tayi takwanta maida doctor yayi sannan yasiyo magungunan yabiya Restaurant yasiyo mata abinci yadawo kamar yadda yabarta haka yadawo yasameta ganin shi yasa tayun'kura tatashi zaune mi'ka mata magungunan da abincin yayi yafita batare dayace komiba kallo tabishi dashi
Shiko yanafita yawuce bedroom d'in shi wanka yayi yafita yana cikin driving yaji shigowar text cikin wayar Kausar bud'ewa yayi text ne daga Amina kamar haka
" Aminiyata nasan duk inda kike kinacikin damuwa kiyi ha'kuri dawannan mugun sharrin da akayimiki in sha Allah Allah zaitona asirinsu kibama yaya DON ha'kuri kidawo Skul koda bazaki zauna cikin Skul ba kinsan yanzune lokacin jajircewa wajan karatunmu kinji Aminiya ta
Parking DON yayi yakashe motar yajinginar dakanshi jikin kujerar motar yalumshe idanunshi yana nazarin wannan text d'in afili yace
" idan har hakane to waye yayimata sharri ? Kay karyane wannan Plan ne amma zansa ido akan komi nata "
Tada motar yayi yanufi office kad'an Kausar taci abincin tasha magungunan zuwa can tami'ke toilet tanufa tayi wanka ahankali take shiryawa wata had'ad'iyar joguwar riga tasaka jin nan knocking yasata jumbula hijab d'inta tafito bud'ewa tayi wani dagacikin ma'aykatan gidan ne yace
" sannu Hajiya dama yalla'baine yace mushigo dakaya "
Basu hanya tayi sukafara shiga dakayan abinci kalakala komawa ciki Kausar tayi zuwacan tafito kitchen d'in tashiga sun shiryakomi bud'e freezer kitchen d'in tayi shima ancikashi dakayan bu'kata hakama freezer parlour
'Dan murmushi Kausar tayi har cikin ranta tajidad'in haka kobabukomi dalilinta yakawo duk wannan cikin natsuwa tad'aura abinci tanayi tana tuna yadda yashafi fuskarta d'azu dandanan gidan yabud'e da kamshi cikin wani lokaci takammala abincin tashirya kan dining sannan tanufi bedroom d'in shi gyaramai ko ina tayi tasakemishi bedsheet dukda d'akin babu datti kamar macace aciki macanma mai tsananin tsabta wani irin kamshi maidad'i yagarwaye cikin bedroom d'in fitowa tayi tagyara parlour shima yad'au kamshi sannan takoma bedroom d'in ta
Wani wanka takumayi simple makeup tayi tafesa turarukanta masu sanyin kamshi sannan tafito parlour zamatayi kan cushion d'in dake kallon 'kofar shigowa parlour misalin 06:30 DON yadawo idan bacikin natsuwa kakeba bazakaji sallamar shiba
Cikin sauri Kausar tami'ke amsar bag d'in hannun shi tayi kamar bazai bataba sekuma yasakar mata cikin siririyar muryarta tace
" sannu da dawowa yaya "
Batare daya amsaba yace
" yajikin naki ? "
ahankali tace
" Alhamdulilah yayi sau'ki "
Wucewa yayi kaitsaye cikin bedroom d'in shi cikin mamaki Kausar tabishi da kallo dan bata ta'ba tunanin zai iyatambayarta ya jikintaba bin bayanshi tayi koda tashiga baya cikin bedroom jin 'karar saukar ruwa yasatasan yanacikin toilet ke'babban guri tasamu ta'ajemai bag d'in sannan tad'akko mai wasu kaya mararsa nauyi ta'ajemai kan bed tafita
Yajima cikin toilet sannan yafito ganin kaya saman bed d'in shi yajiwani 'bacinrai gaban mirror yanufa yashafa 'kyatattun mayukanshi had'ida fesa turaruka haryasa hannu zai d'akko wasukayan seyatuna zancan doctor afili yace
" har abada bazan zama silar saka koda ma'aykacin gidan Dady ne amatsalaba balle yarshi jininshi koda raina bayaso zansa wannan kayan "
'D'aukar kayan yayi yasa sannan yazauna kan sofa system d'in shi yabud'e yafara ayki aciki jin shiru bai fitoba yasa Kausar shiga kitchen fruit tayayyanka mishi kalakala had'ida lemon mango tanufi bedroom d'in bakinta d'aukeda sallama
Ahankali ya'amsa amma idanun shi nakan system d'in aje tiran tayi agaban shi tace
" yaya sannu dahutawa please nasan bakaci komiba ga fruit nasan kanasonsu nashiryamaka dinner dan Allah yaya karka'ki ci danson da kakema Allah da manzon shi dakuma Abba bai kalletaba amma yakasa cigaba da aykinshi
Juyawa Kausar tayi hartakai bakin door d'in yace
" zonan "
Cikin sanyin jiki da fargaba tadawo wayarta yami'ka mata had'ida key d'in mota yace
" dawannan motar zakidinga zuwa Skul amma tareda security idan kingadama kicigaba da shashanci bawai nabarki bane kiguji ranar dazamuyi karo na 2 kince sharri akayimiki ko ? tozanyi bincike akan haka kitabbatar kinsha magungunan ki kafin ki kwanta zaki iya tafiya "
Tashi Kausar tayi cikin zuciyar ta tace
" Alhamdulilah tunda baka hanani zuwa Skul ba Allah yabaka ikon bincikawa nafita daga zargi "
Bayan fitar Kausar DON yakalli fruit d'in gabanshi wani irin damuwa yaji tunawa da mahaifin shi yayi tare sukeshan fruit afili yace
" Allah yaji'kanka Abba na Momy maiyasa kikamin haka ? kindasamin 'kiyayyar duk wata 'ya mace acikin raina amma nakasa mantaki Momy maiyasa maiyasa ? "
Wasu zafafan hawaye suka gangaro saman fuskar shi rufe system d'in yayi yajinginar dakanshi yalumshe idanunshi yana tunanin rayuwar shi tabaya
Sudan
Cikin 'bacin rai Ammi tacema Hajiya Saratu wato 'kanwar ta
" wallahi idan har nabari Seeyama tazauna da kishiya to basunana bulkisu ba ina bazai ta'ba yiyuwaba "
Ta'be baki Hajiya Saratu tayi tace
" Amma nikam kinbani mamaki baikamata kiyita kishirta yanzuba ni aganina wannan tarin dukiyar tashi ita yakamata musan yadda zamuyi mukwashi rabanmu sannan semu dawo kan kishiyar tata "
Jinjina kai Ammi tayi tace
" yauwa 'kanwata to tayaya ? "
Murmushi tayi sannan tace
" bayan ankai amarya koda da wata 1 ne semuje akan ganin d'aki semu tafida Ayman da jabir idan mukaje semuce zasu zauna agunshi sutayashi kulada dukiyar shi kinga bazai'ki jinin shiba daganan semusasu ahanyar damukeso nasan yaranmu bazasu bamu kunyaba sannan munemi maganin dazamu bama Seeyama dataje tasamu ciki kinga shikenan mun tattare komi "
Wata irin shewa suka saki
Ya Allah Allah kashiryar damu
Daga Al'kalamin ✍🏻
NPEEDY A Aji ♠♥♣
Comments & shere plsssss
[15/06 3:26 pm] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠ RUFAFFIYAR ZUCIYA ♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵
♠
Story & Written
By
NPEEDY A AJI
Dedicated to
My Hajjaju
🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟
G.W.F
home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫
ANA TARE 🤝🏻😍🌹
Assalama alaikum ina godiya agareku maitarin yawa masoya Allah yabar zumunci
🅿 { 23 to 24 }
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Misalin 11pm Kausar tafito daga bedroom d'in ta kitchen tashiga d'akko Lipton sabida sabo datayi dashanshi duk dare sanye take dawata doguwar rigar bacci marar hannu mai taushi da santsi wani 'karamin gyale ne tayafa saman kanta sumar kanta takwanta lif saman bayanta sezuba kamshi takeyi
Cikin natsuwa tagama had'a Lipton d'in wanda yaji kayan kamshi har tasa cup 1 sekuma tazuba awani cup d'in yazama 2 saman 'karamin tire tasa ahankali take tafiya kamar maijin tausayin 'kasa cikin bedroom d'in DON tanufa takoyi sa'a abud'e yake
Bakinta d'auke da sallama tashiga yanayin data ganshi yasa yasata saurin ajiye tiran hannun ta saman tebur batare dajin wani tsoroba tanufi inda yake cikin gigita tad'aura hannunta saman 'kirjin shi dede setin zuciyar shi kamar yadda taga yad'aura wani irin bugu taji zuciyar shi tayi cikin tashin hankalin tace
" yaya ina maganin ka ? dan Allah kasanar dani inda yake ? "
Kallonta yakeyi amma yakasa magana se jawo numfashin shi yakeyi da'kyar tashi tayi tanufi bincikawa amma babu alamar zata ganshi gabad'aya tagama rud'ewa sabida wani irin nishi dataji yanayi cikin sauri tabud'e freezer shi cikin sa'a taganshi
Cikin sauri taciri yadda yake sha Lipton d'in tada kawo tad'akko sannan tanufi gunshi nufar bakinshi tayi da maganin amma ya'ki bud'e bakin hannu yami'ka mata tasame maganin sannan ya amshi cup d'in Lipton d'in yasha amshar cup d'in tayi ta'aje tacigaba dayi mai sannu amma kamar badashi takeba cikin zuciyar ta tace
" kana cikin rashin lafiya ma sekayi miskilanci Allah yasauwa'ke "
Tsayin lokaci sannan DON yafara samun sau'ki wani irin zazza'bi ne kuma yataso mai wata irin rawar sanyin yashigoyi cikin rawar jiki yaja blanket yarufe jikin shi hadda kanshi amma dukda haka rawar sanyi yakeyi har ha'koranshi nahad'uwa
Cikin tausayawa Kausar ta d'an dafa jikin shi jin hannunta ajikin shi yasa yajanye blanket d'in daga saman fuskar shi kallon ta yayi da nuna alamar tacire hannunta amma ita bata fahimci maiyake nufiba ganin batada niyyar janye hannunta shikuma gawani mugun sanyi dayakeji yasa yatashi zaune cikin sauri ganin haka yasa Kausar furgita da razana tafad'a kanshi batare da saniba
Wani irin zafi taji jikinshi yad'auka shiko DON wani irin d'umi yaji yanashigar shi wanda koda yarufa baiji rabin hakaba kasa yimata magana yayi cikin tsoro Kausar tafara 'ko'karin tashi d'ago kantatayi takalli fuskar shi girgiza mata kai yayi ahankali alamar karta tashi
Sauke ajiyar zuciya Kausar tayi cikin sanyin jiki tamaida kanta saman 'kirjinshi jin d'umin bai garwaye jikin shiba yasa yazagayo da hannuwan shi bayanta yamatse ta tsam wani irin tsoro Kausar taji yakamata
Ahankali DON ya gyara kwanciyar shi yanamai sake rungumeta tsayin lokaci suna ahaka wani irin baccine yayi gaba da DON itako Kausar takasa rintsawa ganin baccin shi yayi nisa yasa tafara 'ko'karin janye jikinta amma setaji yasake rungumeta sosai fuskarsu na kallon juna zubamai ido Kausar tayi cikin zuciyar ta tace
" masha Allah lalle Allah yayi kyakkyawar halitta anan Allah yabaka komi DON amma yahanaka farinciki ni Kausar nayi al'kawarin samarmaka dafarin ciki dauwamamme in sha Allah Allah kabani iko "
Jin kiran sallar asuba yasa DON bud'e idanun shi ahankali cikin mamaki yake kallon Kausar dake shan baccinta hankalinta a kwance kamshin jikinta yabugi hancin shi kallon sumar kanta yayi cikin sauri yarumtse idon shi sannan yasake bud'esu yanayin rungumar dayayi mata yakalla take nan abinda yafaru jiya yadawo mai rumtse idon shi yayi yace
" oh my God tayaya haka ? mai kenan nayi ? "
Cikin zafin rai yayi yun'kurin tashi amma ina yakasa kwatakwata jikin shi babu 'karfi gawani irin yanayi dayakeji zuba mata idanun shi yayi yakasa kaudasu tuni yaji kamar ya ....... Bud'e idon da Kausar tayi yasa tunanin shi tsayawa ganin yana kallon ta yasatayin mutuwar kwance tamke fuska yayi yace
" se yaushe zakigamajin d'umin jikin nawa ? "
Cikin mamaki Kausar takalli yadda yarungume ta tsam cikin sanyin jiki tajanye jikinta akunyace tami'ke hanyar fita tanufa har takai bakin 'kofa yace
" Idan kinyi salla kidawo kisanar dani dalilin dayasa kika shigomin cikin bedroom cikin dare "
Karasa fita tayi tana maimaita kalaman shi cikin ranta tana fita tasauke ajiyar zuciya had'ida dafe 'kirjinta tace
" yaya Affan yananufin tuhumata zaiyi ? waima yaushe zangamajin d'umin jikin shi bayan shine yari'keni amma ya'ki yarda dahakan sabida miskilancin shi "
Shiko DON tashi yayi zaune yadafe kanshi yana tuhumar kanshi maiye wannan ya aykata ? wani irin takaici yakeji afili yace
" yau nine tareda mace a kan bed d'aya ? kuma rungume kay gaskiya ina akwai abinda keshirin faruwa dani "
Tashi yayi fuskar nan tashi amatu'kar d'aure yashiga toilet seda yayi wanka sannan yayi alwala yanufi masallaci
Cikin sanyin jiki Kausar tafito kitchen tanufa doya tafere ta d'aura sannan tafito tanufi bedroom d'in shi cikin sauri tagyara mai shi tsaf sannan tafito kitchen takoma lokacin doyar tadahu kunun gyad'a ta d'aura cikin lokaci kad'an tadama sannan tafasa 'kwai tafara suyar doyar cikin natsuwa takeyin komi had'a mishi nashi tayi dukda tasan balallene yaciba har cikin bedroom takaimai sannan takoma tad'uki nata tanufi bedroom d'in ta
Wanka tafarayi cikin sauri sabida lecture d'in safe gareta batad'au lokaci ba wajan shiryawa bayan tagama tazauna wajan yin breakfast shima cikin sauri agaggauce tafito parlour ri'ke da bag d'inta bedroom d'in DON tanufa amma cikin mamaki baidawoba tunda yafita masallaci
Cikin damuwa tazauna kan sofa tanamai addu'ar Allah yasa yashigo yanzu kimanin 15 minutes dazamanta yashigo kallon d'akin yayi cikin ranshi yace
" lalle yarinyar nan "
Jin sautin muryarta tana gaidashi yasan tanacikin bedroom d'in ko kallonta baiyiba yanufi bakin bed d'in shi yazauna wayarshi yad'akko yafara latsawa ajiyar zuciya Kausar tasauke cikin sakka tace
" yaya zantafi Skul nakusa rasa lecture "
Kamar bazaiyi magana ba zuwa can yace
" idan kinfad'amin dalilin dayasa kika shigomin cikin bedroom jiya sekitafi "
Cikin wani irin yanayi tace
" nazo kawo maka Lipton ne shine naga bakada lafiya "
Kwanciya yayi yalumshe idanun shi sannan yace
" tunda bazaki fad'i gaskiyaba tashi kibani guri ay kinsan banacin abinda duk wata 'ya mace tadafa dan haka wannan bashibane dalili tashi kikoma bedroom d'inki bana bu'katar wata magana kuma "
Dan danan idanun Kausar sukacika da hawaye jiki a sanyaye tami'ke kamar yadda yace cikin bedroom d'inta takoma batasan lokacin da hawaye suka shiga gangarowa daga idanun taba
Ajiyar zuciya DON yasauke idanun shi alumshe tuno surar jikin Kausar yashigayi sekuma yayi saurin jan tsuki tashi yayi yashiga toilet wanka yayi yafito cikin sauri yashirya cikin 'kananun kaya sosai yayi matu'kar yin kyau key d'in motar shi yad'auka yafito
Cikin bedroom d'in Kausar yanufa zaune take tayi tagumi duk takaici ya'isheta cikin yanayin miskilancin shi yace
" idan kingama kukan kitaso mutafi ki d'akko key d'in motar ki "
Yana gamafad'ar haka yajuya jin wannan furucin nashi yasa Kausar jinwani irin sanyi cikin ranta cikin sauri tad'auki bag d'in ta da key d'in tafita yana gaba tana bayanshi kusan tare suka isa jikin motar shi
Cikin girmamawa ma'aykatan gidan suka fara gaidasu hannu yami'ka mata fuskar shi atamke ganin tana kallon shi yasa cikin d'an fad'a yace
" kibani key d'in motar ki "
Mi'ka mishi tayi cikin zuciyar ta tace
" ikon Allah sekace nasan gaibune "
'Daya dagacikin ma'aykatan yaba yace
" kashiga waccan motar kabimu abaya ku kuma nasanar daku daga yau kune masu tsaron lafiyar ta kuma nace komi 'kan'kantar abu idan har yafaru to asanar dani maza kushiga mota muje "
Kallon ta yayi alamar tashiga jiki babu 'kwari tashiga shima yashiga driver yatada mota motoci hudu 2 ta Security se tashi seta Kausar ta security d'aya nagaba seta su sannan dayarta security a baya
Suna shiga cikin harbar Skul d'in idanun jama'a dayawa sukayo kansu cikin sanyin jiki Kausar tafito adede lokacin da Ameera tazo wucewa kallonta ta tsayayi sabida batayi tunanin dawowar Kausar cikin Skul d'in ba
Ahankali DON yafito daga cikin mota kud'i yami'ka mata cikin yanayin maganar shi mai cike da izza yace
" karki fasayin abinda kikaga dama nikuma bazan fasayin hukunci ba "
kallon security d'in yayi yace
" duk namijin dakuka gani yazo kusada ita nabaku umarnin kuyimai mugun duka kod'an gidan ubanwaye "
Yana gama fad'ar haka yakoma cikin mota drive yaja sukajuya tareda motar security d'aya kallon securities d'in Kausar tayi cikin zuciyar ta tace
" inama amfanin wannan abun sekace watamarar gaskiya anhad'ani da wa'innan 'kattin dababu alamar imani atare dasu "
Jin ihun Amina da sauran 'kawayenta yasa Kausar juyowa cikin farinciki suka rungume juna Ameera da 'kawayen ta sunagefe suna yimusu kallon banza ganin haka yasa Amina tace
" wai harna fara kallon 'kyallin amarci a fuskarki gaskiya garada mijin ki yamaidake kusadashi kinga kyasamu cikakkiyar kulawa "
Dariya suka saki dukansu cikin mugun ba'kin ciki da razanar abinda kunnuwanta sukaji tayo gunsu tana huci tace
" Ke Amina wace banzar magana kikeyi ? kina nufin wai DON d'ina shine mijin Kausar ? "
Murmushi Amina tayi tace
" gyara maganarki DON d'in Kausar zakice banakiba tuni DON yazama mallakin Kausar ita kad'ai dan haka kisamama kanki lafiya "
Cikin zafin rai tasha'ko wuyan hijab d'in Amina wata irin tsawa d'aya dagacikin Security d'in yayi sannan yace
" idan baki saketaba senayi miki muguwar zana ko kallon banza kikayima 'kawar matar boss wallahi sena canzamiki halitta "
Wani irin mugun tsoro yakama Ameera sabida taga babu alamar wasa cikin idanun shi sakinta tayi tabar gurin cikin takaici da mugun ba'kinciki
suma su Kausar tafiya d'aukar lecture sukayi suna tafiya suna hira bayan sunfito sukanemi guri suka zauna kallon Kausar Amina tayi tace
" Kausar kidage wajan janyo hankalin mijinki mace zata'iya sauya ra'ayin mijinta karki bari wata tacinasara akan mijnki "
Ajiyar zuciya Kausar tasauke sannan tace
" zan iyayin komi dan ganin nasaka yaya Affan cikin farinciki amma inajin tsoran ranarda zamu sha'ku yanemi hak'kin shi aguna tayaya zan'iya fahimar dashi idan yasan banida abindazanyi tun'kaho dashi adaran farkon tarayyata dashi Amina yayazanyi "
Wasu hawaye masuzafi sukashiga gangarowa daga idanun ta cikin tausayin Aminiyar tata Amina tace
" karda wannan yasa kikasa janyo hankalin DON zuwa kanki mudage da addu'a in sha Allah kafin zuwan lokacin gaskiya zata bayyana idanma bata bayyana ba Allah zaisa yafahimceki karki sare Allah yasani cutarki akayi kuma bazaibari ki tozartaba mudage da Addu'a in sha Allah komi zaizo cikin sau'ki sannan kar kiga ba'ayi hidimar bikinkuba ki'ki bama mijinki kulawa wannan wani abune dayazama al'adarmu aure de yariga ya d'auru kuma kinzama halak agurinshi shima yazama halak agurinki kidage Kausar Allah yabaki irin namijin dako wace mace keso karki kula da yadda yanayinshi yake kinfini sanin halin yaya DON tare kuke tsayin wasu shekaru dan Allah kikula Aminiya ta ki'aje komi kulada mijin ki sannan kidinga jawo hankalin shi kan mahaifiyar shi baikamata yagujetaba dukda cewa ita takoreshi uwa uwace tafigaban wasa "
Murmushi Kausar tayi sabida taji dad'in wannan shawarwarin da Amina tabata shiko DON daganan office yawuce yana shiga yatadda wasu najiran shi seda yasha ruwan tea sannan yabada umarnin sushigo wani dattijone dawani matashin saurayi umarnin zama yabasu sannan yace yana sauraransu
cikin matu'kar damuwa wannan dattijon yace
" dan Allah yalla'bai kataimakemu wasune sukeson cinye mana dukiya sun siya company na amma sunhanani kud'in wata kwangila suka amsa zasuyi agurin suka matsamin sena siyar musu ganin idan bansiyarba zan'iya rasawa duka shine nasiyar musu amma shiru idan naje gurinsu basuma bari abarni nashiga dan Allah yalla'bai idan babu wannan company bamusan yazamuyiba "
Pen d'in hannunshi ya'aje saman paper dayake rubuta bayanan shi yace
" kasan sunayensu dagurin zaman su ? "
'Daga kai yayi yace
" Alhaji Sambo da Alhaji bala "
" Alhaji Sambo ? "
DON yasake maimaita sunan sallamar su yayi bayan sunbar number waya da address d'in su ajiyar zuciya yasauke yace
" dama ina jiran ranar da wani zai kawo mana 'karar Alhaji Sambo "
Daga Al'kalamin ✍🏻
NPEEDY A AJI ♠♥♣
Comments and shine plasss
[16/06 4:51 pm] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠ RUFAFFIYAR ZUCIYA ♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵
♠
Story & Written
By
NPEEDY A AJI
Dedicated to
My Hajjaju
🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟
G.W.F
home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫
ANA TARE 🤝🏻😍🌹
Assalama alaikum ina godiya agareku maitarin yawa masoya Allah yabar zumunci
🅿 { 25 to 26 }
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Yau ne aka tahoda amaryar DON daga Sudan wato Seeyama cikin gidanshi na Kaduna babban gidane mai d'auke da part 2 kowane 'bangare kashiga sekaji kamar karka fito sabida tsaruwar shi da kayan more rayuwa dake cikin harabar gidan kanta abin kalloce kowane part yana d'auke da babban parlour se 4 bedroom daga ciki ma wani parlour ne madedeci mai d'auke da 2 bedroom se sama mai 1 bedroom da 'karamin parlour duk yadda zan maka tsarin wannan gidan yawuce nan
Cikin shagwa'ba Seeyama tace
" Umma wato 'kanwar mahaifiyar ta kalli yanzu har 8pm fa amma banga DON ba "
Ta'be baki Hajiya Saratu tayi tace
" ayko bazakiga DON ayau ba sabida ance wai yana wajan aykinshi bazai samuzuwaba se nan dawasu kwanaki sabida rashin darajar ki amma ace akawoma Amarya kowane irin aykine ay kad'auki hutun shi "
Wani irin ba'kin ciki Seeyama taji cikin fusata tace
" kenan nikad'e zanzauna idan kuka tafi gobe maiye nufin DON akaina to wallahi yadda yasani ba'kin ciki shima sena sakashi komin dad'ewa dole zaizo ay "
Dafata Hajiya Saratu tayi tace
" kwantar da hankalin ki 'yata ayni babu inda zani inanan kinga dama mijina yarasu yarana guda 2 nataho dasu girman gidan nan yayi yawan dazaki zauna ke d'aya dukda cewa waccan idan tazo d'a........ "
Katseta Seeyama tayi dafad'in
" wacece zatazo ? "
Cikin d'an daburcewa da nadamar su'butar bakin datasoyi tace
" a a wacce kuma kinga zancan zuciyata ne yafito fili kinsan mu yanzu ba'a rasamu da yawan tunani "
Kallo ta Seeyama tayi sannan tasake cewa
" amma gaskiya Umma zamanki anan baiyiba taya zaki zauna agidana kuma hadda yaranki gaskiya a 'a "
Salati Hajiya Saratu tasa had'ida ri'ke baki sannan tace
" amma bansan bakida tunaniba se yau amma nasan kinasane da d'inbin dukiyar da Affan kedashi ko ? kina tunanin wa'innan mari'kan nashi dan Allah suke zaune dashi ? to idan wani nakibaizo yazauna dakeba tosu zasusa nasu dukdan suci dukiya sannan kawo kunnanki kiji "
Cikin 'kasada muryar takeyi mata magana akunne kamar suna tare dawani dariya Seeyama tasaki hada shewa tace
" gaskiyane Umma nagane kiza'bi duk part d'in dayamiki acikin gidannan "
Cigaba da tattauna yadda zasugudanar da al'amuransu sukayi
Tofa
Cikin damuwa Momy tace
" gaskiya Alhaji zuciyata takasa natsuwa da wannan auran na Affan bana zargin Alhaji Umar amma matarshi banyarda da itaba idan basu cutar da Affan ba to zasu cutarmin da Kausar ita kanta Seeyama nalura batada kirki gaskiya karaba auran Kausar da Affan sabida nalura Hajiya bulkisu tanaganin kamar dan dukiyar Affan mukabashi auran Kausar sannan haryanzu ita Seeyama batasan Affan yanada wata matar ba "
Wani irin kallo yayi mata sannan yace
" duk wanda zaice dan dukiyar DON nabashi auran Kausar yaje yaitafad'a sannan duk wani mai nufin wani da sharri Allah baya bacci shine maikare wanda aka zalinta dan haka karki sake zuwamin da maganar raba auran DON da Kausar mutukaraba idan zakibi 'yarki da addu'a to kibita idan kuma zakitsaya tsegumi to kitayi "
Daga haka Barrister yafita yabar parlour kiran wayar DON yayi sukayi magana sannan yashiga motar shi yafita
Kimani kwanaki 6 kenan dakawo amarya Seeyama amma DON bai taka hanyar Kaduna ba cikin takunshi na isa DON yafito daga bedroom d'in shi cikin shirin fita office hannun shi ri'keda bag d'in system cikin sanyin jiki Kausar dake jiran fitowar shi tund'azu dan yanzu idan har yananan bata shiga bedroom d'in shi tun wannan ranar
Cikin girmamawa tace
" barka da fitowa yaya "
Gaba yayi har seda yakai bakin 'kofa yace
" da yaushe kike da lecture yau ? "
Cikin sanyin murya tace " 9 zuwa 11"
Jinjina kai yayi sannan yace
" yau zanzo daba'ki inaso kihad'a dinner kamarta mutun 6 akwai kud'i cikin bedroom d'in kid'auka kibawa tabawa tasiyo miki abubuwan da babu saura kiyimin shirmai "
Baijira maizatace ba ya'idasa fita murmushi tayi sannan tanufi bedroom d'in nashi DON yana isa office babu jimawa yafito yana kallon agogon hannun shi cikin sauri aka bud'emai mota yashiga kallon driver yayi yace
" yimaza nakusa makara wajan taron nan zaka kaini "
Daga haka baisake cewa komiba suna isa biyu daga cikin security d'in shi sukabi bayan shi yana shiga yadakatar dasu daga 'kofa taron manyan attajiraine masu jidakansu matasa da dattije ciki haddasu Alhaji Sambo kowoyabi DON da kallo sabida sunga ba'kuwar fuska acikin su kowa yatashi yagabatar da kanshi kamar yadda suka saba gaba'kinsu kallon DON sukayi sunason jin sunanshi batare daya tashiba cikin harshen turanci yace
" Sunana DON Ibrahim "
Jin sunanshi yasa wasu daga ciki sake maimaitawa kowa bud'e system d'in shi yayi yana nuna irin aykinshi ana zuwa kan DON yajuya musu system d'in shi mamaki kowa yashigayi domin irin aykin dasuka d'ad'e suna neman meyi musune tun bayan rasuwar Alhaji Isma'il d'ayadagacikin manyan ba'kin yace
" DON kanada ala'ka da margayi Alhaji Isma'il ne ? "
Kallon shi DON yayi sannan yace
" a'a asalima tarihinshi natadda cikin manyan 'yan kwangila sannan naji inason gudanar da harkar kamar yadda yagudanar "
Tuni wajan yad'auki tafi d'aukacin gurin masoyan margayi Alhaji Isma'il ne wasukuma ma'kiyan shi su Alhaji Sambo sunyi tafine kawai sabida karsujawo idanun jama'ar gurin kansu
Cikin jindad'i ba'kin sukace
" yalla'bai DON kaine zamuba wannan kwangilar idan angama akwai wasu za'a samu kaso nakimanin million 100 semu 'karashe sauran maganar daga baya "
Daga nan taro yatashi tabbas yau DON yaji wani irin farinciki bawai dan dukiyar dazai samuba sedan yadda yaga su Alhaji Sambo sun rud'e
Kuyi ha'kuri da wannan wayana babu caji sosai yau
Daga Al'kalamin ✍🏻
NPEEDY A AJI ♠♥♣
Comments and shine plsss
[17/06 12:55 pm] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠ RUFAFFIYAR ZUCIYA ♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵
♠
Story & Written
By
NPEEDY A AJI
Dedicated to
My Hajjaju
🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟
G.W.F
home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫
ANA TARE All SISTERS 🤝🏻😍🌹
Ha'ki'ka inajin comments d'inku Fans inajin dad'in haka Allah yabar 'kauna 😊 muna tare 🤝🏻🥰
🅿 { 27 to 28 }
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Misalin 4 Kausar tashiga kitchen cikin natsuwa takeyin komi nau'ikan abinci kala 3 tayi shinkafa wadda taji kayan lambu da hanta se tuwon shinkafa da miyar agushi wanda taji naman rago se alkubus da miyar kwai se farfesun dankalin turawa da kaza
Nau'ika jus ma 3 lemon kwakwa dabino da madara se had'add'an sobo wanda yaji kayan kamshi se kunun aya wanda yasamu had'i na musamman
Misalin 7 takammala komi ta jera saman dining da taimakon tabawa tagyara gidan dandanan ya garwaye da kamshi cikin bedroom d'in ta tashiga kai tsaye toilet tashiga tayo wanka yaban tafito d'an 'kara karfin AC tayi sabida jikinta yasamu iska isassa
Gaban mirror tatsaya 'kayatattun mayukanta tashafa had'ida turarukan jiki sannan tayi makeup bud'e wardrobe tayi cikin mamaki ta tsaya tana kallon wata bag a saman kayanta wata farar paper tagani saman bed d'in cikin sanyin jiki tad'auka d'an gajeran burutune kamar haka
" kisa kayan cikin bag d'innan lokacin tarbar ba'kin daga DON "
Ajiyar zuciya Kausar tayi had'ida murmushi afili tace
" nagode ma Allah dakake nunamin matsayi agaban idanun jama'a Allah yasa inga ranar dazaka kuladani alokacin dayazama dagani se kai oh Allah ko yaushe yakawo kayannan bansaniba ? Yaya Affan kenan "
Wata had'ad'iyar Arabiagwan ce mai matu'kar kyau da tsada da wata irin sarka da takalmi se wani tsadadjen turare cikin farin ciki Kausar tagama shirin ta kallon kanta tayi a mirror itada kanta sedatace masha Allah fitowa parlour tayi sezuba kamshi takeyi jin 'karar tada motar shi yasata saurin le'kawa ta window cikin mamaki tace
" Yaushe yashigo "
Bedroom d'in shi tanufa jinjina kai tayi tace
" wanka kawai yayi inaga ba'kin yaje d'akkowa "
Komawa parlour tayi misalin 8pm taji tsayiwar motar shi babu jimawa taji knocking cikin takunta na natsuwa ta'isa bakin door d'in tabud'e dashi tafara had'a ido cikin sakin fuska tace
" barka da dawowa Sweety na manyan ba'ki sannunku dazuwa "
Murmushi DON yasakar mata hannunta yakamo yasumbace shi yace
" ina fatan kina lafiya hayateey ? "
Wani irin mamakine yakama Kausar amma cikin dakewa danuna ba'abubane sabo tayi murmushi tace
" bayan kafita nakasance cikin rashin lafiya mai tsanani amma kana dawowa nafi d'azu kafin kafita lafiya "
Murmushi yasake sakar mata had'ida d'an jawota jikin shi yace
" to kwantar da hankalinki hayateey bazan sake fitaba senan da 2 days kin........ "
'Daya dagacikin ba'kin yayi murmushi cikin nuna shi'awar yanayin dasuke yace
" mude yakamata aji damu indan mukatafi seku cinye kanku wannan irin soyayya haka "
Kallon shi DON yayi yad'an saki murmushi yace
" ayya kuyi ha'kuri kunsan idan kanatare da farincikin ka mantawa kakeyi dakomi mukarasa ciki "
'Dan duka d'ayan yakaimai yace
" wai kaine kuwa DON ? "
DON yace
" gani kuwa hayateey na kad'e take iyaganin wannan murmushi kuma darajarta kuka samu "
Dariya suka saki dukansu nuna fad'in lalle madam kinada sa'a zama sukayi suka fara tattaunawa cikin mamaki d'aya daga ciki yace
" DON gaskiya nayi mamakin yadda kasamu wannan kwangilar cikin sauri haka bayan baka ta'bayin harkar ba sannan kanuna irin aykin dakakeyi bayan babu kod'aya wanda kayi aciki "
Kallon shi DON yayi sannan yace
" idan banta'bayiba ay inaganin masuyi ko ? "
" to ayni yadda kafitar da tsaretsaran ne yabani mamaki tayaya "
'Dan tamke fuska DON yayi yace
" wannan kuma sirrinane bana bu'katar kowa yasani "
Murmushi yayi yace
" haba DON wato haddani za'a nunama aykin SSD d'in bayan nima aykinane "
Banza DON yayi mishi yakalli Kausar dake manne jikin 'kafad'ar shi yace
" hayateey tashi muje mubasu dinner "
Cikin mamaki wani yace
" had'a abincinma seka tayata ? "
'Dan juyowa DON yayi yace
" idan kafad'i haka banga lefinkaba sabida bakayiba kaga bakasan mahimmancinsuba "
Dariya suka saki sannan suka nufi babban dining d'in cikin natsuwa Kausar tabubbud'e musu kalolin abincin cikin muryarta mai sanyi tace
" ga abinci nasankowa da ra'ayinshi "
Kallon juna sukayi d'aya yace
" nikam duka ina bu'kata wannan irin kamshi haka daganin wannan dinner zatayi santi dan yau inaga sena manta hotel d'in dana sauka "
Duka DON yakaimai yace
" kai de bazaka canza haliba hayateey bar kowa yayi Saving d'in kanshi ga plates nan kowa yayi dakanshi "
Murmushi Kausar tayi tace
" hakan yayi Sweety bari nabaka nasan kana bu'katar hakan "
Wani iri DON yaji amma ayau kam babu yadda zaiyi murmushi yasakar mata farfesun dankalin da kaza tazubamai had'ida tsiyayame lafiyayyan kunun ayar dakanta tashiga bashi ahankali yake amsar abincin ganin ita bataci yasa shima yashiga bata shiru gurin yayi bakajin sautin komi sena spoons da plates tsayin lokaci sannan Abubakar yace
" gaskiya DON kayi sa'a banga lefinkaba idan kanunama madam soyayya agaban kowa wannan irin abinci haka kay masha Allah idan natashi aure sena kawo matar kinkoya mata irin wa'innan had'addun girkin "
" hmmm Abubakar kenan ayni tun yanzu zan dinga kawai budurwata takoya lalle Aminu kai nakama da saura kenan ayni 'kafata 'kafar DON kullum ana zand'inga cin abinci "
Tamke fuska DON yayi yace
" to duk baku isaba hayateey na ba baywarku bace kuje kawai Allah yabaku sa'ar kuma "
Tashi DON yayi yakoma tsakiyar parlour suma tasowa sukayi suna cigaba da yaba girkin Kausar har cikin zuciyar DON yaji dad'in haka shi kanshi jiyayi kamar karya dena cin wannan daddad'an abincin
Ganin har 10 tawuce yasa suka mi'ke cikin sakin fuska Abubakar yace
" madam ga wannan tunda DON baiyi niyyar gayyatarmu bikin ba amma gashi munzo mun gwashi had'add'an girki "
Suma sauran kyaututtuka sukabama Kausar sosai sukayimata alheri har wajan motocinsu sukarakasu DON nari'ke da hannun Kausar seda motocin su sukagama fita sannan kallon Kausar DON yayi yasaki hannun ta yajuya ciki
Bin bayan shi tayi tana mai saukin abubuwan dasuka faru yanzu tana shiga zaune tasameshi gun dining tanufa dan gyara gurin cikin wata irin murya yace
" hayateey "
Cikin matu'kar mamaki Kausar tajuyo d'an kauda kanshi DON yayi dan shi kanshi baiyi tunanin wannan kalmarce zata fito daga bakin shiba fuskewa yayi yace
" zo nan "
Cikin sanyin jiki Kausar ta'karaso zama tayi kusa dashi cikin shakka sabida yadda taga fuskar shi babu alamar wasa d'an Jim yayi sannan yace
" kin kyauta kin fitar dani kunya yadda banyi tsammaniba tabbas yau kinsa nayi farinciki zanje Kaduna gobe Dady yana nemana idan akwai abinda kike bu'kata kisanar dani "
Cikin in ina tace
" dan Allah yaya katafi dani munyi hutu yau dama inason sanar da kai "
Kallon ta yayi yahad'a rai sannan yace
" zanyi tunani zuwa safe jeki had'amin Lipton kimatsamin lemon tsami guda 3 "
Tashi tayi tanufi kitchen zuciyar ta cike damamaki
" wai yau yaya Affan ne da kanshi yace nakawo mai wani abu abunma nasha oh Allah amma kuma lemon tsami har 3 "
Tana barin gurin ya yadafe mararshi had'ida rintse ido ahankali yatashi yanufi bedroom d'in shi kwanciya yayi d'ago hannun shi yayi tuno irin laushin hannun Kausar yasashi sake runtse idanunshi juya kwanciyar shi yayi yayi rufdaciki ya 'kwa'kube pillow
Yad'an jima da shiga cikin bedroom sannan Kausar tashiga hannun ta d'auke da cup d'in Lipton d'in umarnin ajiyewa yabata batare daya tashiba yayi hakanne dan bayason sake kallon surar jikinta dan yin hakan zaisake sashi cikin matsala
A wannan daran haka DON yakwana da tunanin surar jikin Kausar daya rimtse ido ita yake kallo kamshin jikinta yakeji " Sweety " yasake maimaita kalmar tunda wuri Kausar tashiga kitchen had'a musu breakfast yana dawowa masallaci yace
" kiyi sauri ki shirya idan kuma kika zauna zanyi tafiyata "
Daga haka yashige bedroom d'in shi toilet yashiga cikin sauri Kausar tahad'a breakfast d'in kan dining sannan tanufi bedroom d'in ta cikin lokaci kad'an tagama shiri harma tarigashi fitowa zaune tayi kan cushion tana jiran fitowar shi
Zuwa can yafito kallon ta yayi yai saurin kauda kanshi sabida wani irin abu dayaji ya tsarga dukkan ilahirin jikinshi tasowa tayi tace
" yaya please kayi breakfast kafin mutafi "
Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba sannan yace
" kawomin nan "
Zama yayi kan cushion ahankali yakeyi break d'in har yagama itako tea kawai tasha bayan sungama suka kulle ko ina sannan yakira tabawa yasanar da ita motocin 3 d'aya daga driver se wasu ubankaya d'aya kuma driver da su d'aya Security
Suna isa Kaduna Kausar taji wani irin farinciki cikin sauri maigadi yawangale musu get sunayin parking Kausar tafito tanufi cikin gidan aguje kallo DON yabita dashi yayi 'kwafa
Adede lokacin Momy da Dady suna zaune a parlour shikuma Ashiraf yana cikin bedroom jin ihun Kausar yasa Ashiraf fitowa cikin murna Kausar tafad'a jikin Momy murmushin farinciki barrister yashigayi shima Ashiraf haka ganin wasu had'add'un akwaituna da'ake shigowa dasu yasa kowa baida dubanshi da hankalin shi Kansu
Seda aka gama shigowa dasu sannan DON yashigo akwaiti har set 4 ko wanne 6 6 yana shigowa ya shiga gaidasu cikin girmamawa bayan sun gaisa DON ya kalli Barrister yace
" Dady wannan kayan lefan Kausar ne Momy kuyi magana da ita tafad'i irin kayan datake bu'kata na gida an kammala ginin wannan gidan na Abuja inaso nayi Oder kayan daga Italy "
Yana gama fad'ar haka yami'ke ciki yanufa sabida duk bayajin jikin shi dede tsananin farin ciki yasa barrister kasayin magana sede murmushi itama Momy haka shiko Ashiraf bin bayanshi yayi yana fad'in ango
Tunda DON yashiga ciki bai fitowa seda akafara kiran sallar azahar yana fitowa barrister
" DON yakamata kaje kaga Amaryar ka tsawon 1 week fa da kawota ? "
Cikin razana Kausar takalli DON shima d'in ita yakalla cikin in'ina tace
" dady Amarya kuma yaya Affan ? "
Jinjina mata kai Dady yayi dandanan hawaye suka taru cikin idanunta Kausar tashi tayi aguje tanufi bedroom d'in Momy sake binta da kallo DON yayi murmushi barrister yayi yace
" karka damu my son kaje zamu lallasheta "
Idasafita yayi yana tunanin abubuwa dayawa cikin zafin rai yake drive shi kad'e yana isa maigadi yabud'e mai get ko gama gyara parking baiyiba yakashe motar yafito sabida jikin shi babu karfi cikin muryar shi ta miskilanci yayi sallama saurin juyowa Seeyama tayi
Ganin shine yasa tajuya cigaba da kallon ta tayi ko sallamar bata amsaba ita adole tayi fushi
Shima ko kallon ta baiyiba yanufi bedroom d'in shi
Tofa
Daga Al'kalamin ✍🏻
NPEEDY A AJI ♠♥♣
comments and shine plsss
[18/06 2:28 pm] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠ RUFAFFIYAR ZUCIYA ♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵
♠
Story & Written
By
NPEEDY A AJI
Dedicated to
My Hajjaju
🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟
G.W.F
home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest
KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫
ANA TARE All SISTERS 🤝🏻😍🌹
Ha'ki'ka inajin comments d'inku Fans inajin dad'in haka Allah yabar 'kauna 😊 muna tare 🤝🏻🥰
🅿 { 29 to 30 }
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Cikin mugun ba'kinciki DON yashiga bedroom d'in zama yayi bakin bed yadafe kanshi rintse idanun shi yayi fukar Kausar yake hangowa cike taf dahawaye afili yace
" mai hakan kenufi ? taya zatayi kuka dan an ambaci Amarya to ayni babu wacca nikeso a cikinsu amma meyasa naji babu dad'i lokacin danaga idanunta suncika da hawaye taya nike kallon surar j........ " turo 'kofar Seeyama yasa tunanin da DON keyi tsayawa
Ko sallama babu tace
" kazo Umma nakira "
Daga haka tajuya wani mugun tsaki yaja hayewa saman bed ma yayi yai kwanciyar shi babu alamar ma zaitashi jin shirun yayi yawa yasa Hajiya Saratu tanufi bedroom d'in dakanta
Knocking tashigayi amma shiru jin shirun yasata turawa tashiga cikin mamaki take kallon shi baccin shi kawai yakeyi 'kwafa tayi tafita a parlour tasamu Seeyama tace
" ke Seeyama dagaske kike lokacin da kikaje kiranshi idanun shi biyu ? "
Jinjina mata kai tayi alamar tabbas idanun shi biyu girgiza kai Hajiya Saratu tayi sannan tace
" wato ni ban'isa dashiba kenan ko zetashi yasameni "
Jinjina kai yaron Hajiya Saratu yayi yace
" wato Umma badan kudin danike hangowa ba da wallahi se kaddamar mai "
" gaskiyar ka jabir nima badan hakaba hmmm "
Cewar Ayman d'an zaro ido Seeyama tayi tace
" a 'a ina son shi fa mude samu dukiyar amma banda kisa "
Harararta Hajiya Saratu tayi tace
" kaji banza dakud'i da shi wanne kikafi so idan yamutu ga jabir nan dama yadad'e yana sonki dande wannan kaddararan had'in ne da kakanninku sukayi kukuma kubi ahankali kuna ganin wa'innan mugayen security d'in dayake tare dasu zasu ragamuku idan kukamai koda kallon banza ne to kubi ahankali "
Haka sukacigaba da kulla makircinsu afurgice DON yatashi hannun shi yasa yashare zufar data mamaye fuskarshi ajiyar zuciya yasauke cikin wahalalliyar murya yace
" haba taya wannan mafarkin zaidawomin ? bayan nayi kwanaki banyiba nikam ina zanganki baiwar Allah ? "
Hannu yasa yadafe mararshi yace
" yazanyi dawannan muguwar shi'awar dake damuna musamman cikin kwanakin nan gaskiya babu macan dazan iya tarayya da'ita sede namutu "
Jiki a sanyaye yatashi toilet yashiga wanka yayi yacanza kaya sannan yafito se zuba kamshi yakeyi a babban parlour yasamesu dukansu cikin shuki Seeyama ke kallon shi kallon Hajiya Saratu yayi yace
" barka da hutawa nayi zaton kun koma ? "
Ta'be baki Hajiya Saratu tayi tace
" taya zamu koma mubar 'ya ita kad'e kai yanzu ka kyauta kenan ? Har tsawon sati amma bakazoba se yau kuma kasan yanzu ha'k'kin Seeyama yadawo kanka ko ? sannan nida yara zamu zauna anan kabasu dama sukular maka da dukiyar ka "
Kallonta kawai DON keyi hannu yasa yashifi sajanshi sannan yace
" ke Seeyama tunda kikazo kin kwana da yunwa ? ko kinrasa gurin kwana maikuma zanzo nayi miki to bari kiji aykina yafimin komi ayanzu sannan ni babu wanda zan d'aura akan dukiyata sede nabasu jari sabida mahaifina yasha wahala kafin yatara dukiyar amma bai moretaba yadda yakamata dan haka bazan bari abanzatar da ita abanzaba ban hanaku zamaba amma bana bu'katar adinga shiga rayuwata kekuma Seeyama jibi zan koma idan akwai abinda kike bu'kata kisanar dan idan natafi ba lalle kiganni anan kusaba "
Yana gama fad'ar haka yanufi hanyar fita cikin mamaki kowa yabishi dakallo babu mai abincewa jinjina kai Hajiya Saratu tayi tace
" lalle yaran nan baisan wacece Saratu ba watoma bazai d'auraku kan dukiyar shiba hmmm "
Cikin fushi Seeyama tace
" Umma amma ni kamata yayi kishawomin kanshi kafin musan abinyi "
Jinjina kai Hajiya Saratu tayi
DON nafita yashiga mota yacema security shikad'e zaifita cikin 'bacin rai yake tu'ki parking yayi gefan titi afili yace
" lalle ayki ya'karu agareni ga binciken danikeyi akan wa'inda suka kashemin mahaifina gasu Alhaji Sambo sannan ga wa'innan sukuma dan yadda naga idanun wannan matar zata iya komi akan kud'i hmmm insha Allah duk zan iya daku "
Wayar shi yaciro number Ashiraf yakira bugu 2 yad'aga ata'kaice DON yace
" please bama Kausar waya "
Tashi yayi yanufi bedroom d'in Momy dan tunda tashiga batasake fitowaba mi'ka mata wayar yayi yace
" mijinki ne "
cikin sanyin jiki ta amsa cikin daku shasshiyar murya tayi sallama amsawa yayi sannan yad'anyi jim zuwa can yace
" meyasaki kuka ? kin manta bakida lafiya sosai ko ? kibar kukan ganinan zuwa zamu fita kirakani kiyimin abinci idan zaki iya "
Daga haka yakashe wayar iska yafesar daga bakinshi yace
" narasa yadda akayi nikejin yarinyar nan cikin raina amma ina ganin sabida ...... "
Rurin da phone d'in shi keyi yasashi dakatawa da zancan amsa wayar yayi cikin 'bacin rai yace
" wacece Ameera mai Kausar tayi mata dahar zatasa nazargeta bayan haka hadda cutar da'ita nayi kenan maganar Amina gaskiya ne bari zandawo jibi kucigaba da tsareshi har senazo seya nunamin Ameera "
Kashe phone d'in yayi hannu yasa yadafe kanshi afili yace
" seyaushe zanrabu da matsaloli ne ni Affan "
Tada mota yayi wani katafaran hotel yanufa d'aki yakama sannan yafito bakin wani 'katon supermarket yayi parking yafito yashiga tsayawa yayi yana kallon abubuwan cikin yama rasa maizai d'auka zuwa can yafara jidar kayan ciyeciye sannan yakoma kan wasu kyawawan Rings masu matu'kar kyau na asalin goal guda 2 yad'auka d'aya babba d'aya 'karami bayan yabiya yafito
Cikin sanyin jiki Kausar tafito daga bedroom d'in Momy kitchen tanufa kallo d'aya zakayimata kasan tasha kuka sabida wani irin kumburi da idanunta sukayi rasa maizata dafamai tayi shigowa kitchen d'in Momy tayi kallo ta tayi tace
" wato Kausar bakidena wannan kukanbako ? duk lallashin da Dadyn ku yayi miki amma abanza ko ? koma parlour idan abinci zakici bari nazubamiki amma kidena wannan kuka kin auta ta "
Rungume Momy tayi cikin rawar murya tace
" Momy nadena kukan Allah amma Momy nasan yaya Affan yafison waccan akaina sabida itad'in umarnin Abban shice niko had'ine na kaitsaye Momy amma in sha Allah zanyi biyayya Momy babu abinda nike bu'kata shine yace nayimai abinci tonamarasa maizan yimai kum......... "
Dakatar da ita Momy tayi dafad'in
" ke Kausar shi DON d'inne yasaki kiyimai abinci ? toko idan hakane inada tabbacin yafara sonki tun lokacin da Dadyn ku yazoda DON har yau baita'bacin abincinaba amma ke gashi harma saki yakeyi kwantar da hankalin ki auta in sha Allah zaki kasance cikin matu'kar farinciki agidan DON wallahi harnaji dad'i dakam cikin tsoro da shakka nike ki cigaba dayimai biyyaya kinji "
Fita Momy tayi tana murmushi cikin sanyin jiki Kausar tafara yimai girkin soyayya taliya da kaza tayimai tasha Vegetables fita tayi daga kitchen d'in tayo wanka wasu irin riga da wando tasa wa'inda sukayi matu'kar fito da surar jikinta wata doguwar riga tad'aura asama amma mai sarasara dan ana iya hango nacikin gyara gashinta tayi takamashi da ribon simple makeup tayi sewani irin kamshi takeyi gyalan rigar tad'an yafa saman kanta tafito parlour zama tayi kan cushion tana latsa wayar ta
Momy dake d'an Mesa da ita cikin zuciyar ta tace
" Kausar kenan bansan lokacin dakika fara son Affan ba ikon Allah kenan "
Ahankali yake driving har ya'isa gida bai shiga da motar cikiba yayi parking a waje bakin shi d'auke da sallama yashiga cikin parlour
A hankali Kausar tad'ago kaidubanta tayi zuwa kanshi ganin ledar hannun shi yasata tashi amsar ledar tayi cikin 'kasadamurya tayimai sannu amsawa yayi yana kallon cikin idonta ahankali yace
" kisameni a 'karamin parlour kitahomin da abincin "
Cikin ladabi ta amsa gurin Momy yanufa yayi mata sannu da gida sannan yawuce Momy Kausar tami'ka ma ledar sannan tajuya kitchen babu jimawa dazamanshi Kausar tashiga kallo d'aya yayi mata ya kyauda kai cibamai tayi tami'ke cikin wata irin murya yace
" jiya ke kikabani har naci sosai yauma kece zakibani "
Wata irin kunya Kausar tayi amma yadda taga yazubamata ido yana cije lips din shi yasata zama cikin sanyin jiki dajin kunya take bashi abincin kirjinta yazubama ido dede lokacin Dady yashigo cikin 'karamin parlour batare dayasan suna cikiba kallon yanayin dasuke yayi ganinma basusan yashigo ba yasa yajuya yana sakin murmushi
amsar spoon d'in hannunta yayi bata abincin yashigayi d'an kyauda kanta tayi gefe tana amsar abincin
Bayan sungamaci Kausar takwashe kayan zatafita jin maganar shi yasata tsaya
" idan kin kai kisameni a mota "
Bayan Kausar take kayan cikin bedroom d'in ta tanufa 'katon hijab tasa har 'kasa sannan tafito kitchen tahango Momy cikin jin kunya tace
" Momy wai yace narakashi anguwa "
Murmushi Momy tayi tace
" Allah yasa adawo lafiya "
Fita tayi cikin jinkunya ahankali take tafiya cikin motar tasameshi tana shiga yatada mota ganin 'katon hijab d'in datasa yasashi jin dad'i har cikin ranshi hotel d'in daya kama yanufa ganin dagaske ciki zasu shiga yasa Kausar saurin kallon shi yiyayi kamar baisan tana kallon shi ba
Parking yayi yafito cikin sanyin jiki da fargaba tafito gaba yayi tanabiye dashi har bakin room d'in yabud'e suka shiga zama tayi tatakure kanta guri d'aya shiko cire rigar shi yayi yazauna dagashi se singlet kallon yadda tatakure jikinta yayi yace
" zo "
wata irin fad'uwa gabanta yayi ahankali ta 'iso tamke fuska yayi yace
" kicire wannan 'katon hijab d'in "
babu musu tacire musamman data tuna wai yanada wata matar hadda doguwar rigar tacire wani irin yanayi DON yaji cikin jikin shi tuni idanun shi suka fara canza launi zama tayi kusa dashi cikin dakewa yace
" maiyasaki kuka d'azu ? Kuma wacece Ameera ? "
Cikin sauri tad'ago takalleshi d'an du'kar da kanta tayi tace
" nayi kuka ne sabida kishi dukda nasan kai basona kakeyiba amma ni tun ranar da akasanar dani auranka na kaina nasaka sonka Cikin zuciya ta dole nayi kishi akan mijina bansan auran kaba sede naji batun Amarya amma bazan sake kukaba kamar yadda kace inayima addu'a Allah yabaka ikon yin adalci
Ameera wata 'kawatace amma ada Ameera ita tayi sanadin dasa mugun ba'kin ciki cikin zuciyata wanda babu ranar dazai goge Ameera itace wadda tacema tana sonka a ranar dakaje
Skul d'in mu "
Shiru yayi yananazarin kalamanta bai sake cewa komiba hannu yasa cikin aljihun wandan shi yaciro kyawawan rings dinnan hannunta yakama yasaka mata woow wani irin haska hannun yayi mi'ka mata d'ayan yayi sannan yami'ka mata hannun shi cikin mamaki take kallon shi da ido yanunamata alamar tasame cikin sanyin jiki tasame jawota yayi jikin shi
Wata irin runguma yayimata cikin wani irin yanayi DON ke sarrafa Kausar bakinsu yahad'e guri daya yanama lips d'inta wani irin tsotso tusa hannun shi yayi cikin rigarta wata irin cafka yayi ma breast d'inta yacusa d'ayan hannun shi cikin sumarta
Juyar da ita yayi yafara 'ko'karin cire mata rigarta cikin matsanan cin tsoro Kausar tafara kuka ri'ke hannun shi tayi cikin kuka tace
" dan Allah yaya kabarni banida kwarin gyuwar baka hak'kin ka dan Allah yaya bazan iyaba inajin tsoran faruwar wani saban ba'kin ciki agareni "
Cikin wata irin murya DON yace
" haba hayateey zaki iya kinji nikaina banyi tunanin zan iya aykata hakanba kece mace tafarko danikejin zan iya tarayya dake please kidaure "
Sake rufamata baya yayi kuka tasake saki tana yimai magiya afusace DON yatashi zama yayi bakin bed d'in yana sauke nunfashi tashi Kausar tayi cikin kuka tace
" yaya dan..... "
" dakata Kausar bana bu'katar jin komi wannan ne son dakikace kina yimin ? dama nasan ni mace matsalace agareni babu komi nabarki kuma bazan sake neman ko gaisuwar kiba daga yau karki sake zuwa inda nike mahaifiyata tasa nazama mai RUFAFFIYAR ZUCIYA amma ke kinfara bud'e zuciyata ashe yaudarace bazan sake yarda da wata maceba kuma "
Kuka sosai Kausar keyi tashi DON yayi yashiga toilet yana dafe mararshi sabida wani irin ciwo datakeyimai
Daga Al'kalamin ✍🏻
0 comments:
Post a Comment