Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
01
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇丨賲丕賳 丕賱乇丨賷賲...
*Assalamu'alaikum fans we're back again da yardan Allah, Allah yasa ku SHAK'U da wannan labarin ma kaman yanda kuka SHAK'U da Hajiya Fad'ime ikon Allah Lol.... Allah shi bamu ikon rubuta khairan.. Ameen!*
Mari ya kuma kwasheta dashi a karo na babu adadi, lokaci guda ya kuma mak'uro wuyanta yana huci tamkar zaki.... Tuna tana kuka mai sauti har ya koma maras sauti sai zallan hawaye.
Dukda k'ak'arin da take hakan baisa ya saketa daga mak'urin da yayi mata ba.... Da k'arfin gaske yayi wurgi da ita da bugu da k'arfen bagrag dake gefe a cikin d'akin.....
Cikin karaji yaci gaba da nunata da belt d'in hannunsa yana fad'in "Be careful, I'm warning you duk ranar da kika kuma tuhumata a ina na kwana kinji na rantse sai na maki wulak'ancin da yafi na yau, useless kawai... Ke wacece? Who the hell you think you are da har zaki tsareni da tambayan yanda na kwana...? Ko ce maki akayi ni d'in d'anki Fawaz ne huh..?"
Yayi wata murmushi kafin yaci gaba da fad'in "Lallai Saudat kin sami kanki har ni kike tuhuma saikace kin mance wanene ni, yaci ace kin saba dani da halina tunda tun ina matashi d'an shekara 18 nake aurenki, kinga ak'alla yau kusan shekaru 25 muna tare.. Kar ki mance baduk'un mahaifinki sabida kud'in mahaifina ya lik'a min ke tun banida wayo tun bansan wanene ni ba ballantana na gane abu mai kyau da maras kyau..."
Takowa yayi har gabanta yanda take durk'ushe tana cazgan kuka wanda idan da sabo yabi jikinta dukda ba'a sabo da wahala.... Hannu yasa ya damk'o sumarta had'i da d'ago fuskarta kafin ya soma fad'in "Barikiji na fad'a maki bin matan banza wllhi yanzu na soma bazan daina ba koda zamu had'a nema da Fawaz, sannan aurosu ne bazanyi ba, tunda nasan aurosu na nufin kwanciyar hankalin ki ne, ni kuma sam kwanciyar hankalinki ne banaso, kinsan inada mak'udan kud'ad'en da duk yanda naje zan sami mace irin wacce nake so ba irinki ba zabiyar banza da wofi...." Ya k'arashe yana mai ciro wasu pills a cikin aljihunsa.... Matse bakinta yayi yana danna mata pills d'in yake fad'in "Ki sha maganin nan tun kafin ranki ya b'aci.."
Wani irin kuka take tana girigza kai alamun bata so hakan bai hanasa danna mata su cikin bakinta ba, haka dolen maganin suka wuce mak'ogoron ta babu ko ruwa dukda girman magungunan.....
Yana gama tura mata su ya fashe da wata kafiran dariya shi kad'ai tamkar tab'ebb'e.....
*Alh Kabir Santana kenan* president na shaharerren kampanin nan wato *SANTANA CORPORATIONS*
*************
INNAH ta dubesa a karo na biyu kafin ta tunsture da dariya tana mai ajjiye karan sigarin dake hannunta saman 'yar wata k'aramar plate dake bisa center table d'in...
"Kayi min dai-dai Kabiru, kar ka fasa d'irka ma tsinanniya maganin mahaukata har sai ta zama cikakkiyar mahaukaciya, muddin tanada hankali tofah sam bazamu cimma burinmu akan NASIR ba, a koda yaushe nayi yunk'urin kawar dashi shegiyar yarinyar nan Saudatu tana wuce min gaba.... Tunda kuwa tace fad'a dani ta d'auko aiko kaga ta d'au Dala babu gamo..."
Alh Kabir magidanci d'an shekaru 45 ya dubi mahaifiyar tasa wacce ak'alla bazata gaza shekaru sittin a duniya ba kafin yace "Wato Innah nasha fad'a maki wllhi akanki akan farin cikin ki babu abinda bazan yi ba tunda har na kawar da Sa'oud Santana a doron k'as....." Bai kai aya ba Innah ta danne bakinsa ta rufe kafin taci gaba da fad'in "Koda wasa baniso na kuma jin ka furta kalami irin haka koda a keb'antaccen waje muke....."
Kallon juna sukayi ido cikin ido kafin suka kuma fashewa da wata kafiran dariya......
**************
Sanye yake cikin kayan training na sojoji a rantsettsiyar Base d'insu dake garin Bauchi wanda ko ina ka juya kalan shud'i kawai kake gani wato blue.... Matashi ne wanda ak'alla bazai gaza shekaru 34 a duniya ba, kallo d'aya zaka masa ka fahimci sam bashida jinin bak'in fata a tattare dashi, ma'ana duk yanda akayi wannan bawan Allah zama ce ta kawo k'asar bak'ak'e har ya koma d'an k'asa.....
Wayace manne a kunnen sa na dama, basai ance maka answer waya yake ba. Daga looks d'in da yake dashi a fuskar sa zaka fahimce tsantsan tashin hankalin dake kwance saman fuskar sa....
Cikin nutsuwa da kwantar da hankalin mai sauraren nasa ya soma fad'in "Aunty Saudat kiyi hak'uri, nasan kinayi, da ace inada halin shigar da Yaya kotu da nayi, but kinsan yin hakan na nufin Innah ta min baki... Aunty Saudat ina tsananin tausayin ki sannan ina gujema ranar da Fawaz zai dawo k'asar nan ya tarar da abinda akema mahaifiyar sa, bansan Yaya wani irin mutum bane amma kiyi hak'uri zanzo gidan ko gobe insha Allah kinji..... Ki kwantar da hankalin ki....."
Ya jima yana tsaye a wajen yana nazarin abubuwar dake faruwa A DUNIYAR SU har baisan sanda amini kuma k'ani a gareshi ya k'araso yanda yake ba wanda shima basai ance maka Sojan bane, shid'inma sanye yake cikin kayan training.... Dogon saurayi wanda yarinta sosai ya nuna a fuskar sa, bazai wuce shekaru 25 ba duwa da shida....
"Captain lafiya kayi tsaye a nan ka bar horas da rundunar naka..." cewan matashin Sojan saman da bai jima da k'arasowa wajen ba....
D'an bud'e madaidaitan idanunsa yayi kafin yace AFFAN waini baka mamakin abubuwan da suke faruwa A DUNIYAR MU rayuwa ta koma tamkar ta maguzawan farko, munyi watsi da d'abi'un da addinin mu ya koya mana, mun koma tamkar zamanin jahiliya....."
Bai kai ayaba Affan ya dakatar dashi da fad'in "Kaga soldier pls don't start with your wa'azi, haba kai kullum NASIR baka da aiki sai wa'azi, kai inaga idan an kwana biyu ajjiye aikin Airforce zakayi ka koma malanta.... Yanzu bama wannan ba yanzu mukayi waya da Daddy yace min suna hanyarsu ta zuwa Bauchi gaba d'ayansu hardasu Mamy, inaga wannan karan kam har Jama'are zasuje gaba d'aya kasan maganace ta aure, so inaga ya kamata kaima kayi weekend d'in nan a gida koma ka soma sanar dasu Innah tun yanzu..." ya k'arashe yana lank'washe yatsun hannunsa had'ida d'an motsa jiki wanda d'abi'ace tasu ta sojoji musamman idan suna atasaye....
D'an fuzar da iska Nasir yayi had'ida d'an yin still kafin ya jingina jikin k'arfen fence d'in da aka kewaye wajen dashi kana ya furta "Allah Ya kawosu lafiya" a tak'aice....
Affan ya rakasa da kallon mamaki domin wani sa'in miskilancin Nasir na damunsa, Sam baida hayaniya, hidiman gabansa kawai yake bai shiga sabgan mutane....
*************
*Kaduna*
Murmushi Mamy ta sakar mata lokaci guda tana juya d'iyar tata tana ganin yanda tayi kyau tamkar wata African Queen...
"Sweetheart ina mai tabbatar maki duk miskilanci Nasir wannan karan kam dole ya hakace akanki, kinga yanda kika cicciko kuwa gaskiya maganin Tasalla yana aiki, munje sai asaran kud'ad'enmu muke wajen sayan magunguna masu d'an karan tsada ashe ga sauk'i da arha har gida har d'aka...."
SHAREEFAH matashiyar mace 'yar kimanin shekaru 29 a duniya ta murmusa had'i da yin fari da idanu kafin ta soma fad'in "Nifah Mamy ba wannan ba damuwata yanzu bai wuce yanda aka soma maganar auren nan ba Nasir ya kuma watsa mana k'asa a ido, don wllhi yace ya fasa aurena yanzu kam inaga k'aramin hauka zanyi, and Mamy what worries me the most shine INNAH case ce, zata iya hana Nasir aurena don nasan sarai bata mance wulak'ancin da na mata a Brazil ba...."
Mamy tayi murmushi kafin ta shafi gefen fuskar Shareefah tana mai fad'in "Haba daughter ki daina abu kaman bani na haifeki ba..... Nayi imani da Allah duk barikancin Innah Dije a bayana take, nasan meye imaninta ba komai bane illa kud'i dukda d'umbin dukiyar da mijinta ya mutu ya bari mata bata daina kwad'ayin wasu su shigo mata ba....."
Mammy tayi murmushi had'i da k'arasawa jikin wargajejen tagar wanda ya sha kwalliya da labulaye na alfarma kafin taci gaba da fad'in "Asm'au nake murucin kan dutse ban fito ba saida na shirya, maza k'arasa shirinki barin duba Daddyn ki......."
Daga haka ficewa tayi ta bar Shareefah cikeda farin cikin zata garin masoyinta abun k'aunar ta....
Karo suka kasanyi da juna lokaci guda Mamy take watsa mata mugun kallo domin duk sanda take k'ulla wani abin a gidan sai ta biyo hanyar ta....
A hasale take fad'in "Wai ke AZIMA shashashar ina ce inyi? Kina tafiya kai a sama bagazan bagazan kamar ba mace ba.... "
Azima matashiyar budurwa wacce bazata gaza shekaru 24 ba tayi murmushi tana wasa da bakin gashinta wanda d'abi'arta ce kafin tace "Mamy kenan, wai ke kullum a tsarge kike ne...? " Ta sassauta murya kafin ta matso da kunnenta sautin bakin Mamy tana mai ci gaba da fad'i cikin sigan rad'a "Fad'a min what are you up to this time around, kinsan your secret is always safe with me, oya fad'a min....."
Tsaki Mamy tayi had'i da yin k'wafa ta wuceta cikin sauri, itakam ta kwaso ruwan tafasa kanta da hannunta abun har mamaki yake bata wai Azima ce ke shige mata hanci da k'udundune, Azima d'iyar d'an uwanta ta data d'aukota tun tana shekaru k'alilan ta maidata 'yar aikinta na k'arfi da yaji wai yau itace ke sakata fad'uwan gaba.... Lallai kuwa tun wuri gwara ta tari abin tasan yanda zatayi da yarinyar kafin ta zame ma rayuwar ta nightmare.....
**********
Ko tankata baiyi ba har ta k'arashi tsiwar ta da masifar ta, babu yanda ya iya he really needs the job, rayuwan mahaifinsa na cikin garari dole ya shanye duk wani wulak'ancin da LUBNA zata masa a matsayinsa na driver d'inta, amma har cikin ransa ji yake kaman ya rufeta da d'an banzan duka ya fasa bakin rashin kunyar da wannan yarinyar murd'a d'aya zai mata ya kareraya ta....
Tana make a owners corner suke zagaya cikin Babbar Universityn ta Bauchi, wato Abubakar Tafawa Balewa University..... LUBNA SA'OUD SANTANA kenan budurwa 'yar kimanin shekaru 21 wacce ta taso cikin sangarta gata da soyayyar 'yan uwanta........
**************
*Garin Jama'are, jihar Bauchi*
Wasu 'yan mata guda biyu ke tsaye a wani babban gidan gona wanda babu kalan shanayen da babu, kama daga shanunmu na gida har zuwa irin shanayen madaran nan wato Bulls. Wannan tampatsetsen gidan Gona bana kowa bane illa Alh Ali Safwan, mahaifi ga AFFAN ALI SAFWAN da kuma SHAREEFAH ALI SAFWAN, wannan gidan gona Allah Ya albarkace da k'osassun shanu masu lafiya wanda a kullum akan cire zallan madara ganga ganga....
Cikin tsanaki wad'annan 'yanmata suke tafiya rik'e da kafad'un juna, iskan damin yana hurasu, ga ciyayi sunyi kore shar gwanin ban sha'awa.... Ga dukkan alamu suna cikin nishad'i domin kuwa kana iya jiyo sautin 'yan wak'e wak'en da suke cikin harshen fillanci....
D'aya daga cikin 'yanmatan ne ta tsuguna k'ark'ashin saniya guda nan ta soma tastan nonon saniyar cikin k'warewa.... Har lokacin basu daina 'yan wak'e wak'en su ba, ita kuwa d'ayar tsaye tayi tana sauraren 'yar uwar tata murmushi kwance saman fuskar ta....
Lokaci guda tayi fatali da bokatin da take tsatsan nonon saniyar wanda saida ya haifarma wacce take tsayen birkicewa... Cikeda tashin hankali take lalume da hannayenta tana bud'e manyan idanunta wanda suke bud'e tas tamkar mai gani take fad'in "SALMA lafiya, me ya sameki 'yar uwata....." aya ta dasa wa maganar nata sanda ta jiyo muryar wacce ta kira da Salma tana fad'in "Adda Jamila oyoyo, ina kika baro Falaq...."
Wacce Salma ta kirada Adda Jamila yatsina fuska tayi tana taunar chewing gum tana wani totttoshe hanci had'i da kauda kai gefe kafin ta soma fad'in "Ni dalla matsa min, sai warin nono kike kin wani zo kin shafa min, bansan sanda zaku waye ba sam, kuna zuwa makaranta tamkar baku zuwa, ko cemaku akayi a riga kuke, sam bakuda banbanci da 'yan matan riga," Ta kai dubanta d'aya budurwar dake k'arasowa wajen nasu da k'yar kafin ta dawo da dubanta ga Salma wacce ta cika tayi fam kafin tace "Ita ma wancan makauniyar tatsan nonon take ko me....."
Daidai lokacin da ILHAM ta k'araso rik'e da sandar ta na d'an jagora take fad'in "Addah sannu da zuwa, kin zo lafia...?
*Sameena Aleeyou... 鉁嶐煆�*
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*02*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
A kufule Salma ta soma tafiya ta nufi sashen da gidansu yake wanda yake a cikin gidan gonar, Jamila na mata magana ko amsata bata tsaya yi ba, wannan d'abi'ace ta SALMA duk yanda take ganin girman mutum idan ya zubar da girman take sa take yi tsaf, sannan bata barin kota kwana balle tayi tsami, kowa ya shaide ta da wannan d'abi'a don tun tuni tun bata kawo iwar haka ba ita ke amshe wa 'yan uwan nata fad'a.
SALMA matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru 19 a duniya itace d'iya ta biyu ga marigayi Jauro Yakubu wanda gaba d'aya illahirin ma'aikatan wannan gidan gona da iyalansa suke kiransa da Baffah kafin Allah yayi masa rausuwa, JAMILA me kimanin shekaru 25 a duniya itace d'iyar fari wacce tuni tayi aure a cikin garin Jama'aren tanada yarinya guda d'aya mai suna Falaq, sai autar su ILHAM 'yar kimanin shekaru 17 a duniya wacce Allah Ya jarabceta da matsalan rashin gani.....
Innoh (Kaman yanda suke kiran mahaifiyar tasu) tana zaune bisa darduma a farfajiyan gidan Salma ta shigo baki a ture tana mita... Innoh na tambayarta Lafia? Inaa ko zarafin amsata bata samu ba sai masifa take da hausarta wanda fillanci yafi yawa a ciki.... Hango Falaq da tayi tana rarrafen ta gefen Innoh ya sanyata sakin murmushi ta k'arasa a guje kaman k'aramar yarinya ta suri yarinyar tana mata wasa yarinyar kuwa sai k'ek'yata dariya take, har ta mance bak'in cikin da uwar yarinyar ta k'unsa mata domin kuwa gaba d'ayansu Allah Ya jefa masu soyayyar Falaq cikin zukatansu...
A tare Ilham da Jamila suka shigo yanda suka tarar daga Innoh har Salmar wasa suke kanyi ma Falaq...
Ilham wacce sam bata gani sai muryoyinsu da take jiyo cikin kunnuwanta sai murmushi take tana mai rayawa a cikin zuciyar ta inama wataran Allah zai bud'e mata idanu taga Falaq, sautin yarinyar yana mata dad'i a cikin kunnuwan ta...
Innoh na hankalce da Ilham wacce ke tsaye tana murmushi tausayin d'iyar tata ya rufe ta, a yayinda su Jamila da Salma sukayi nisa cikin nishad'i, Allah sarki d'an uwa mai dad'i har sun mance fad'an da sukayi an ci gaba da raha..
Mik'ewa Innoh tayi ta kamo Ilham had'i da zaunar da ita cikin 'yan uwan nata, daga Jamila har Salma kallo suka bi Innoh da Ilham dashi, zukatan su cikeda tausayin nak'ason da 'yar uwar tasu kedashi a halittan ta..
Da sauri Salma ta mik'a ma Ilham Falaq ta d'aurata bisa cinyarta... Aiko nan Ilham ta shiga murmushi bai bayyana hak'wara lokaci guda tana shafa Falaq....
Shiru Jamila tayi abubuwa da dama suna ziyartan zuciyarta, ta sani tabbas 'yan uwanta suna son d'iyarta Falaq, inama yanda suke sonta haka mahaifinta ke sonta, tunowa tayi da wa'adin da ya d'ibar mata idan bata sanda yanda zatayi da d'iyarta ba toh kuwa tana gab da barin gidan sa don shi ba sabida haihuwa ya aureta ba, sabida holewa ya aureta yanda take kyakkyawan bafulatanar nan. Ciki wajen uku Alh Nuhu na zubar mata sai akan Falaq Allah yayi zata haifa, gashi yanzu ta soma ganin canji daga gareshi....
**********
"Kai kaga, what's that your name again... Kaga me ma kake da suna, Deeni kake ko wa, ni bana tafiya less than 180 ka k'ara speed, wannan ai sai kasa na gaji...."
Batayi shiru ba k'awarta Faty KT dake zaune gefenta ta yamutsa fuska kafin tace "Ke ni wllhi duk jina nake ma na gaji saikace a amalanken shanu muke..."
Haba nan fah Lubna ta kuma harzuk'a ta shiga balbala masifa.....
ZAHRADDEEN kuwa ya kawo iya wuya, bai tankasu ba sai gyara seatbelt d'insa da yayi, basu ko kula da hakan ba sai tsiwa sukeyi....
Wani irin kwasan motar yayi ya soma wasa da rayukansu bisa kwalta.....
Mannewa da juna sukayi waje guda daga Lubnar har Fatyn sai ihu suke, shiko kaman cewa suke ya k'ara, ta mirror yake kallonsu yana munafukin dariya, sai yayi kaman zai rage wuta sai ya kuma kwasan motar, tuni Faty ta cire d'an kwali ta rik'e a hannu tana ihu, shiko Deen k'arshema earpiece ya manne kunnuwar sa dasu....
Saida suka jigata ya gama race dasu kafin ya cakka wata uwar burki wanda saida ya haifar masu hautsinewar 'yan hanjinsu...
Faty na nishi take duban Lubna da k'yar take fad'in
"Babe kiyiwa Allah kicema wannan BABY DRIVER d'in ya ajiyeni, wllhi ban shirya mutuwa ba....." ta k'arashe tana nishi...
Haki Lubnar ma take tana fad'in "Babe bakiga ma abinda yayi ba, toshe kunnuwan sa fah yayi da earpiece baima sauraren mu ..."
"Kai Baby Driver...!!!" Suka fad'i a tare cikin had'e murya....
Ko kulasu baiyiba sai kwasan gudu suke a hanyar Main Campus da zai kaika har Air Force Base....
A harzuk'e Lubna tayi tsalle ta komo frontseat, earpiece d'in kunnensa ta fincike tana fad'in "Meye kasha a wannan kwanyar taka... Are you insane or what? Baka ganin nan highway n....."
Batakai aya ba yaja burki ya kashe motar ya zare key d'in ya nufi cikin daji....
Baki hangame suka bisa da kallo har ya gangara cikin bishiyoyin....
Lallai wannan talakan babban d'an rainin hankali ne... Lubna tace a cikin zuciyarta, a kufule ta fincike marfin motar ta fice tabi bayansa...
Fati KT baki hangame take kallon ikon Allah... Aiko bata isa zama ita kad'ai cikin mota a hanyar Gubi ba yanda ake satan mutane kaman kaya...
"Bismillahi..." ta fad'i had'i da bud'e marfin mota... Tun daga nesa take sakawa mai babur hannu bibbiyu tana taresa..
_Ni kuwa Sameena nace yau su Fati KT babur za'a hau a koma cikin sch 馃ぃ... *Sha zumami* kuke ji yanda akwai zak'i nan take bibiya..._
Sai falfala gudu yake cikin motar sa k'irar 407 wanda take Blue kalansu na Sojin Sama, lokaci guda yake sauraren wasan k'wallon k'afan da ake bugawa na duniya wato World Cup a radion motar sa.... Daga can gefen kwalta ya hangi mota kaman na gidansu... Toh amma mai zai kawo motar gidansu ta tsaya a nan, kuma da alama babu kowa cikin motar, shi gashi bama sanin lambobin motocin gidan yayi ba balle ya gane, sam baiyi relaying akan dukiyan gado da mahaifinsu ya mutu ya bar masu ba, 'yar 407 d'insa da aka raba masu sojoji ya ishe sa, sam Nasir ba mai son abin duniya bane, harta dukiyansa wanda yake samu da guminsa rabinsa a charity foundation suke tafiya, wannan d'aya ne daga cikin kyawawan d'abi'u na Nasir Sa'oud Santana...
Tun tana binshi tana kiran sunansa tana masifa tana fad'in ya bata car keys d'inta, har ta gaji ta durk'usa a wajen tana kuka tana ambato Innahar ta..
Ta jima a wajen tana durk'ushe tana kuka kafin ta jiyo muryar sa yana fad'in
"1/1 gobe ki sake min rashin kunya kiga abinda zan maki, k'asan bridge zan wullaki gaba d'aya... Oya tashi mu tafi lafin ki kuma b'atamin rai...."
D'ago rinannun idanunta tayi tana hararansa kafin taja tsaki tace "Ku talakawa tsiyarku kenan da an jawoku inuwa sai ku tura mutum rana, ba don ina tausayin Mama Tani ba wllhi da tuni nasa anyi firing d'in....."
Ganin yasa kai zai kuma kutsawa cikin daji yasata dasa aya ma zancenta tana binshi cikin sassarfa take fad'in
"Kaga, ina kuma zakaje... Toh kaga na yarda 1/1 muje a haka, kaga Faty na mota tana jiranmu...."
Suna tafe yana k'unshe dariyar sa domin kuwa gaba d'aya kukan da Lubna tayi mascara ya zazzago ya b'ata mata fuska, abinka da farar mace sai ta koma tamkar Zombie....
Suna tsaka da neman Fati KT wayar Lubna tayi k'ara, ba kowa bace illa Fatin, nan ta sanar da ita cewa itakam ta koma cikin sch don ta lura wannan driver d'in nata ba mai lafiya bane...
Gama wayarta da Faty keda wuya ta kirawo masoyinta Affan ta sanar dashi gata ta kusan shigowa Base d'insu....
**********
Yana isowa gidan ko sashen Innah baije ba ya nufi sashen Yaya Kabiru
Sosai idanun Nasir suka kad'a sukayi jazir sanda yaga kalan cin zarafin da d'an uwansa yayima matar sa, tausayin Aunty Saudat ya rufesa...
Ta share hawayen da suka kuma zubo mata, cikin muryar kuka taci gaba da fad'in "Nasir idan na gudu ina kake tunanin zanje, wa nakedashi a fad'in duniyar nan, sanin kanka bansan kowa a dangina ba sai mahaifina kuma baya nan ballantana naje gareshi, a halin yanzu banida kowa da zan kalla nasan inada masu lura dani sai ku biyu, daga kai sai Fawaz, sannan bazan iya tafiya na bar Fawaz ba.... Shi kad'aine gudan jinina......"
Ta k'arashe murya na rawa....
Fuzar da iska yayi kafin ya mik'e ya isa bakin k'ofa ya zura takalman sa...
Dariya suke kan k'ek'atawa tamkar marassa hankali, lokaci guda Innah ta dondoni wutan sigarin jikin na Yaya Kabiru ta shiga busawa itama, sam basuji sallaman da yake kan faman rattabawa ba...
K'walla suka ciko idanun Nasir, duk yanda zaiyi k'ok'arin dannewa bazai iya ba, ace wad'anannan sune shak'ik'an sa, wai wannan itace mahaifiyar sa? A kullum da takaicin abubuwan da suke faruwa a DUNIYAR SU yake kwana yake tashi.... Kasa shiga kansu yayi don sam basuyi kama da ace wad'annan D'ane da mahaifiya ba.....
Gefen furaranni ya zauna had'ida yin tagumi da hannu bibbiyu kafin ya furta a hankali... "Ya Allah ka fini sanin lamuran da suke faruwa A DUNIYAR MU, Ya Allah kayima maganinsu, ya Allah ka kawo mana sauyi *A DUNIYAR MU*
**********
Yana sanye cikin lallausar T-shirt mai kalan land army da wando wanda da kad'an ya wuce gwiwan sa ya k'araso yanda suka ajiye motar nasu...
Lubna tana hangosa ta haye jikinsa a guje tana kuka...
Affan ya d'agota yana dubanta yanda duk ta jigata ta canza kamanni kafin ya bud'e murya yace
"Naan badai accident kukayi ba...?" jin bata amsa sa ba yasa shi bin jikin motar da kallo yana duba ta ina aka gwangwatsa a jikin motar wayam baiga komai ba, sai mugun kallon da ya raka Deeni dashi...
Cikin kuka Lubna take fad'in "My Soldier ba wannan mahaukacin driver d'in bane ya ringa gudu dani kaman zai kashe ni ba, sau goma nayi amai kafin mu iso nan..."
"Whattt!! Affan ya furta da k'arfi, kuma duban Deeni dake make cikin mota hankali kwance kunnensa manne da earpiece hankali kwance yana sauraren sauti yayi, kafin yasa hannu ya share mata hawayen ta yana lallashi yace da ita yana zuwa, ya nufi cikin barikin...
Wani murmushin mugunta Lubna tayi yayinda Deeni ya tab'e baki domin kuwa karuwanci yake gani muraran a cewar sa... A fili ya furta "Abbah Allah baka lafiya na huta da ganin bad'ala...." Idanunsa a lumshe yana kad'a kai yana sauraren sabon wak'an da Rara yayima shugaban k'asa yaji an fincike marfin mota an jefosa waje kaman kayan wanki k'artin sojojin suna fad'in "Come out idiot..."
Ai Deeni baisan sanda yayi zaman tahiya yana karanto k'ulauzai ba......
D'ayan ya finciki earpiece d'in daga kunnensa yana fad'in "Remove that idiot...."
Cikin rusunawa jiki har karkarwa Deeni ya cire yana mik'a masu harda sara masu daga durk'ushe..
Su kansu sojojin dariya Deeni ya basu, sai karanto addu'o'in da suka zo bakinsa yake yana fad'in "Mama Tani.. Mama Tani kin kawoni aiki gidan ajalina... Wayyo ni Zahraddeeni shikenan yau za'ayi kabarina, ban sami kud'in jinyar Abbah bah za'a jinyata ni...."
"Will you shutt up my friend!!!" d'aya gardin ya kuma daka masa tsawa... Ai tuni ya kame bakinsa waje guda lokaci guda suka umarce sa ya fara frog jump..
Su Lubna kuwa sun b'ace shiru a apartment d'in Affan dukda hankalinta kacaukam yana wajen Deeni, tasan soji babu imani sam bata so su illata sa kawaidai so take su d'an koya masa hankali...
Kaman wacce aka zabura ta mik'e tana fad'in "Affan zan tafi is getting late..."
*********
Kaman diran mik'iya haka suga Alh Nuhu akansu yana sab'a babbar rigansa wanda take duk'unduk'un yana jawo kaki yana tofarwa . Hajiya Hinde amaryar da yayo a d'an tafiyar sa na kwana biyun tana biye dashi kallabi a goshi sai taunar cingam take irinta gogaggun kilaki basai ance maka 'yar bariki bace...
A tare suka mik'e gaba d'ayansu suna dubansu jin kalaman da suke fita daga bakin macen da Alh Nuhu ya shigo da ita....
*Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*03*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
"Tabd'ijam yanzu dama Alhajin shagali bafualatana mai tallan kindirmo kake aure.... Wllhi har na raina ma kilass d'inka..." ta k'arashe tana k'araras da chwingum tana sab'a d'an figigin mayafinta dake bisa kafad'arta guda...
Alh Nuhu ya hangame bakinsa wanda yake duk dottin goro kafin ya soma fad'in "Wllhi Magajiya shiyasa nace maki kud'ina suka bi bacin haka na horeta da maganar haihuwa da shegen taurin kunne kaman k'anwar fir'auna saida ta bani d'iya .. Kinga yarinyar can mai zubin uwarta...."
Ya k'arashe yana k'ok'arin d'auko Falaq wacce tundaga shigowansu gidan take kuka tamkar taga dodanni...
Cikin azama Salma tayi hobb'asa ta d'auke Falaq, sai hura hanci take sai ka rantse dokuwa dasu zatayi... Cikeda tsiwa ta soma fad'in "Wllhi kunyi kad'an ku shigo har cikin gidanmu kuci mana zarafi muchless this precious soul...." ta k'arashe tana kuma rungumar Falaq cikin jikinta.
Shewa Hajiya Hindu tayi kafin tace "Su fillo anji turamci Allah sa ba zagina kikayi ba yanzu in lallasa maki na jaki...."
Jikin Innnoh gaba d'aya yayi sanyi da lamarin sai binsu da idanu kurum take, dukda dama haka halittar ta take, Mace ce mai tsananin sanyin zuciya...
Sai sannan Jamila tayi ta maza ta k'araso gaban Hajiya Hindu dukda hawayen dake bin k'uncinta bata fasa fad'in "Barikiji na fad'a maki kar ki sake ki d'aura ko yatsa akan k'anwata karuwar banza karuwar wofi...."
"Ayyyiriiiriii nanaye ahayye casss abinki...." cewar Hindu lokaci guda tana mai tafe hannaye... Duban Alh Nuhu dake tsaye gefenta uwa sauna tayi kafin tace "Kai Nuhu kanaji yanda matarka take aibanta ni ka kasa yin komai ko, me ta fini dashi, k'irji ko mazauna.... Bata bayanin matsayina a wajenka ka kuma k'ara mata da takardan sallama...."
Ta k'arashe maganar tana kuma turo kallabi gaba...
Gaba d'aya suka bi Alh Nuhu da kallo sanda yake fad'in "Ke Jamila dama na fad'a maki kar ki haihu domin ni bazan iya d'aukan d'awainiyar yara ba kikayi kunnen uwar shegu kika haifu, toh ki sani daga rana mai kaman ta yau babu ni babu ke, Kuma magajiya tayi gaskiya so kike ki kasheni kici gado kaso biyu kici naki kici na 'yarki shiyasa kika nace kika haihu, kuma wannan da kike gani itace zata maye gurbinki itace zata shike d'akin ki.."
Ya dawo da dubansa ga sauran jama'an gidan kafin yaci gaba da fad'in "Jama'a ku shaida ni Nuhu Alhajin shagali mai taro da sisi na saki matata Jamila Saki biyu masu kyau, na k'ara na saketa saki uku masu kyau babu kome tsakanina da ita...."
Baikai aya ba Hajiya Hindu ta fashe da dariya tana mai rangad'a gud'a taja hannun Alh Nuhu suka fice harda cire daddaud'an hularsa ta maka akanta...
Zubewa Jamila tayi a wajen tana kukan da nasanin auren Alh Nuhu da tayi, Allah Ya jik'an Baffah babu yanda baiyi ba wajen ganin ya hanata auren Alh Nuhu amma son abin hannunsa ya hanata hango abinda kowa yake hanga mata...
Innoh da k'walla suka ciko idanunta cikin sauri ta shige d'aka tana matsan k'walla domin kuwa ba kowa ta tuna ba illa marigayi Jauro mijinta, babu yanda baiyi ba wajen ganin Jamila bata auri wannan mutumi ba amma fir Jamila tak'i ganin hakan, ansan fulani da kunya amma idanun Jamila sun bud'e da son abin duniya, wannan halin kwad'ayi na Jamila yana matuk'ar mata ciwo gaba d'aya ta banbanta da 'yan uwanta a wannan b'angare....
**********
Ran maza ya b'aci dama ance ka guji b'acin ran mai yawan shiru...
Jijiyoyin jikinsa sunyi rud'u-rud'u sanda yake kuma matsowa gab da d'an uwan nasa yana mai ci gaba da fad'in "Yaya I swear to you idan baka daina cin zarafin Aunty Saudat ba I'll sue you, zan d'aureka har igiya yayi saura kuma zan sanar da duniya cewa kai wane irin mutum...."
Baki hangame Alh Kabir ke kallon k'anin nasa wanda sam baya masa irin hakan. Lokaci guda ya fashe da dariya yana tafe hannaye yake fad'in "Bravo! Bravo Nasir, ashe kai har kayi girman da zaka d'aureni... Naga alama k'wayarku ta sojoji ta fara fad'a maka ba dai-dai ba bacin haka har yaushe ka soma nuna min yatsa Nasir, just who the h*ck you think you are...? Toh bari kaji na fad'a maka Saudat matata ce sai yanda naso nayi da ita.... So boy ina shawartanka you better stop interfering if not...." Yayi wata murmushi yana sosa hab'ar sa..
Nasir da flesh d'insa tayi turning red gaba d'aya lokaci guda matso da fuskar sa ya kuma yi sosai dai-dai saitin na Alh Kabiru kafin yaci gaba da fad'in "K'warai na sani matarka ce amma ka fad'a min wata doka ce ko shari'a ta amince maka kaci zarafinta...."
Bai gama yin shiru ba Alh Kabir dake tururi ya tare shi da fad'in "Kaima wata doka ce ta baka damar shigar min gonata k'aramin maras kunya k'aryar Kakin jikin ka kake....."
Ran soja ya kai mak'ura wajen b'aci.... Baisan sanda ya d'aga hannu yana k'ok'arin kaima yayan nasa mari ba.... Kaman daga sama sai jiyo muryar Innah sukayi tana fad'i cikin tsananin tsawa
"Nasirrrrrr!!!!"
Kasa marin Alh Kabir yayi sai murza hannun nashi da yake yi yana wani irin huci lokaci guda ya sauk'e hannun zuciyarsa naci gaba da tafarfasa..
Cikeda bala'i Innah taci gaba da fad'in
"Ashe bakada hankali, ashe kai mahaukaci ne, Nasir yaushe kayi girman da har zaka d'aga hannu kace zaka mari babban yayan ka, kai waye.... Ehhh lallai bansan haukan naka ta kai har nan ba..."
Alh Kabir dake shafa hab'arsa lokaci guda yana wata irin kafiran murmushi yace
"Innah naso ki barsa ya mareni yau d'in nan da na cire masa rashin kunyar sa tsaf, kuma kajini da kyau Nasir wllhi wllhi you'll pay for this, d'aga hannu da kayi da sunan attempting duka na wllhi you must pay the price, I won't let you get away with it...." Daga haka ficewa yayi yana wani muzurai lokaci guda yana huci..
Innah ta bisa da kallo zuciyarta tayi bak'ik'irin sabida an tab'o ruhinta Kabiru....
A harzuk'e ta kuma duban Nasir dake tsaye a wajen yana huci tamkar wanda aka dasa a wajen kafin ta k'arasa gabansa 'yar firit kaman ka hure domin kuwa duk sigari ya k'arar da ita, cikin tsananin fad'a take fad'in
"Kana jina wllhi idan ba so kake nayi maka baki ba kabi d'an uwanka ka basa hak'uri, bana son shashahsancin banza da wofi ni ban baka wannan tarbiyar ba...."
Kallon Innah kurum yake cikeda mamakin hali irin nata, da k'yar ya tattaro kalamai saman harshen sa hannu yasa ya kamo hannayen Innah cikin sanyin murya ya soma fad'in
"Innah kiyi hak'uri ba nufi bane na b'ata maki, but Innah pls open your eyes for once..... Innah na sani shine d'anki mafi soyuwa a gareki na sani kina tsananin son Yaya and ban tab'a jin k'yashi ko wani abu makamancin haka akan banbancin da kike nunawa tsakanina da Yaya Kabir ba.... But Innah pls ki barni na karb'a wa matar sa 'yancinta na irin cin zarafin da yake mata... Innah Aunty Saudat mace ce, uwa ce sannan 'ya ce... Innah how would you feel idan aka ce yau Lubna tayi aure irin haka na faruwa da ita a gidan miji....."
Bai kai aya ba Innah ta fincike hannunta daga rik'on da ya mata, tana hura hanci take fad'in "cika min hannaye na, mai mugun alkaba'iri... Fatan ka ya k'are akan ka ba dai akan d'iyata Lubna ba... Kuma wllhi tallahi kaji na rantse maka idan baka fita daga hidiman gidan Kabiru ba wllhi sai na maka baki kuma na sallama ka daga cikin 'ya'ya na......"
Daga haka ta wuce fuuu uwa zata tashi sama..
Kallo ya bita dashi har ta b'ace ma ganin sa, da k'yar ya zube cikin sofa yana dafe da goshinsa yake ambato Allah a zuciyar sa.
Waya manne a kunnenta tana labarta ma Faty yanda suka k'are da mutuminsu Deeni Baby driver sai k'yak'yata dariya suke nan ta hangi Yayanta Nasir zaune cikin kujera.... Ai da gudu ta tafi ta haye jikinsa cikeda murna..
***********
Rabonsu da Bauchi yau kusan shekaru uku, komai na gidan an rufesa da farin k'yalle wasu kuwa anyi sealing d'insu a manyan kwalaye, nanda nan ma'aikata suka soma aikinsu na goge-goge da share-share..
Ganin bataga Azima cikin ma'aikatan ba ya sanyata saurin haurawa bene tana k'walla mata kira, ita kad'ai sai huci take...
A tare Azima da Shareefah suka fito domin dama su duka biyun suna d'akin Shareefah ne suna firfito da kaya daga cartons...
"Mammy lafia kin bamu tsoro..." cewar Shareefah dake tsaye daga stirs hannunta rik'e da frame..
Mamy na huci take fad'in "Ina Azeema...?"
Shareefah ta d'an juyo da dubanta ga Azeema wacce ke k'ok'arin sauk'owa daga benen kafin ta tab'e baki tayi komawarta d'aki..
Mugun kallo Mamy ta watsama Azeema sanda ta k'araso gabanta kafin ta bud'e murya tace "Kina saurare na tunda kika ce bazaki koma Daura ba toh wllhi bazan barki kiyita zama min a gidana ba kina cinye min arzikin gida ba, dole kimin aikatau idan ba haka ba ki tattara ki koma akulkin ubanki don kin riga da kin sanni Azeema bana rab'ar mutum sai zan sami riba..."
Murmushi Azeema tayi da gefen bakinta kafin tayi k'asa da murya
"Mamy wuya bata kisa, sannan wulak'anci da gori sam bazasu tab'a d'ad'ara na ba muddin zan sami abinda nake so, kuma ko me zakimin a matsayinki na k'anwar mahaifina bazan ban fad'i ba idan na maki aikatau and lastly Mamy kiyi a hankali idan bakiso na sanar da Nasir Santana wacece macen da yake shirin sure...." Ta k'arashe tana murmushi had'i da wasa da k'arshen gashinta...
Mamy ta rakata da kallon mamaki tana huci... Ai cikin sauri ta take ma Azeema baya tana fad'in "Billahillazi kikayi yunk'urin wargaza auren Shareefah da Nasir sai na wargazaki nima, don ubanki waye ya koya ma Shareefah bin maza idan ba ke ba... Munafuka algunguma yau zaki bar gidan nan don ba'a haifi wacce ta isa tazo har gidana ta hanani rawan gaban hantsi ba....."
Da k'arfin gaske Mamy ta jawo Azeema ta hankad'ata waje sai jikin Affan da shigowar sa kenan....
Da sauri ya tari Azeema yana bin mahaifiyar sa da kallon mamaki...
Azeema tayi k'ok'arin k'walk'walo hawaye cikin zuciyarta kuwa sanyi ne ya mamaye gaba d'aya ganin abunda take kwana dashi ta tashi dashi a gabanta kai k'arewa ma tana rik'e cikin jikinsa....
Affan ya dubi Azeema dake share fake hawayenta kafin yace "Hope dai bakiji ciwo ba..."
Girgiza masa kai tayi alamun a'a kannan a k'asa uwa mutuniyar arziki, cikin sauri ta masa godiya had'i da komawa cikin gida ta samu waje ta lab'e tana hango yanda Affan da Mamy zasu wants...
Affan yaci gaba da watsa ma Mamy mugun kallo domin kuwa wani sa'in ruwan kwalban nasa basa fad'a masa dai-dai, idan ya kwarkwance uban kowa yake ci.... Dukda yanada tarin d'abi'u marassa kyau amma yak'i jinin yaga ana wulak'anta bil adama musamman Mace...
Cikeda daburcewa Mamy ta soma fad'in "Son ashe kaima kana tafe ..." ta k'araso zatayi hugging d'insa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu kana yace
"Mamy don't tell me har yanzu baki daina nuna banbanci tsakanin 'ya'yanki da Azeema ba, for what Mamy? Azeema's also your daughter, haba Mamy an daina irin wannan yanzu...."
Ya k'arashe yana sassauta murya wanda hakan har saida ya bawa Mamy mamaki don idan a da ne saidai ya sille mahaifiyar tasa tass, lallai aikin soji ya amshi Affan sosai tunda gashi ya soma hankali...
Murmushin yak'e tayi wanda hausawa ke cema yafi kuka ciwo kafin ta rik'o hannunsa tana fad'in "Haba son kasan bana wulak'anta Azeema sai ta kular dani kasan d'an rik'o da fitina...."
Affan ya murmusa had'i da rik'o kafad'un Mamy yana mai ci gaba da fad'in "Mamy hak'uri zakuyita yi damu, Ina big sis take...?"
Bata basa amsa ba sai bin handbag d'in dake rik'e hannunsa tayi da kallo kana tace "Affan ina ka samo jakan mata...?"
Tambayar da Mamy ta masa yasa Azeema kai dubanta ga hannun Affan d'in, lokaci guda gabanta ya yanke yayi wani irin fad'uwa..
Shi gaba d'ayama ya mance da jakar dake hannun nasa... D'an d'ago jakar yayi yana murmushi kafin yace
"Oh this? Jakar Lubna ce nayi dropping d'inta a gida so sai ta mance jakarta a motata..." Ya k'arashe maganar fuskar sa d'auke da murmushi...
"Wacece Lubna..?" Mamy ta tambaya
"Lubna Sa'oud Santana k'anwar Nasir surkinki...." ya k'arashe maganar yana kwab'e takalman k'afarsa...
Mamy da tuni dad'i ya mamaye illahirin zuciyarta murmushi ta soma tana fad'in "I smell something... Iyye kace trade by barter za'ayi..."
Murmushi kawai Affan keyi yana mai haurawa sama lokaci guda yana rangad'a kira ma Shareefah...
Azeema dake mak'ale a lungu idanunta kad'awa sukayi lokaci guda, sai nanata sunar macen da Affan ya ambata take cikin zuciyarta...
Kai tsaye sashen mahaifinsa Alh Ali Safwan Affan ya nufa yanda ya tarar da mahaifin nasa zaune saman wheelchair d'insa hannunsa rik'eda jarida idanunsa manne da farin tabarau na k'ara k'arfin gani...
Alh Ali Safwan Dattijo d'an kimanin shekaru sittin a duniya ji yayi tamkar ya tashi ya rungume d'an nasa lokacin da ya d'ago suna duban juna saidai babu halin yin hakan sakamakon shanyewar k'afafu da ya samu a 'yan kwanakin baya...
Cikin sauri Affan ya k'araso ya rungume sa daga zaunen da yake... Sosai Alh Ali Safwan ma ya rungume d'an nasa suna jin d'umin juna.... Shareefah ce ta lek'o ta tarar dasu a haka nan itama ta k'arasa ta rufu akansu..
Affan ya d'ago yana dubanta ta kai masa mintsili..
Alh Ali Safwan kuwa dad'a matse yaran nasa yayi kaman mai tsoron kar a k'wace masa su, domin tun bayan lokacin da ya sami matsalar shanyewar k'afa yake tsananin k'aunar yaga Family d'insa sun zama complete musamman da shike Affan Soja ne ba mai a man gida sosai ne ba.
**********
Zaune yake a Study d'insa k'afarsa d'aure bisa teburin dake gabansa shi kad'ai yake huci yana murza zoben dake 'yar yatsar hannunsa na tsakiya.... Lokaci guda ya shiga hango sanda Nasir ya d'aga hannu da sunan zai maresa, zuciyar sa ta kuma yin bak'i... Cikin sauri ya d'auki wayar sa dake bisa teburin ya shiga dialing wata lamba...
"Hello Maina kana jina, inaso ka had'a yaranka akwai aikin da zaku min....."
Daga haka ya kashe wayar d'if lokaci guda sanda ya hango kalan muguntar da ya k'ulla wa Nasir... Lokaci guda ya fashe da wata irin kafiran dariya har yana buga benchin dake gabansa....
************
*Jama'are*
"Adda kinga irin abinda yasa nace maki wllhi sam nak'i jinin masu arziki, da yawansu basu san darajar d'an Adam ba sun zaci kud'i da abinda duniya shine mutum alhali kuwa ba haka bane, mutunci yafi komai....."
Jamila dake kan faman cazgan kuka mugun kallo kurum ta watsa wa 'yar uwar tata kafin ta mik'e a kufule ta shige d'aki tana tunanin kalan rayuwar k'uncin da zata soma a gidan su tunda ta saba da rayuwar gidan Alh Nuhu cin kaji da k'wai da saka suturun da taga dama, kaf garin d'aid'aiku ne masu iya competition da ita ko gidan biki aka je, gashi yanzu ta tashi mata, tasan bata isa kuma yanzu ta shiga taro ba sai an sako chaptern ta gaba...
Salma ta bita da kallo yayinda Ilham ta rungume Falaq sosai cikin jikinta idanunta na neman kawo ruwa....
***********
"Daddy ai d'azun nan ma muka rabu da Nasir d'in har yana ce min regarding your health condition ai da ka bari kawai anyi komai a Kaduna zaifi sauk'i abin yayi wani iri gidan Mata su tashi su zo.. So sai nake ce masa kar ya mance muma tushenmu kenan Bauchi Jama'are zama ce kawai ta kaimu Kaduna, kuma Daddy zaiyi auren babbar d'iyar sa ai ya kamata yazo mahaifar sa.... Sann..." Ya d'anyi shiru yana sosa kai yayinda suka bisa da kallo daga Daddy d'in har Shareefar suna mamakin canzawar da Affan yayi, lallai had'uwa da Nasir k'ila shi ya canza Affan gaba d'aya..
Daddy yana murmushi yake fad'in "Ehen ina jinka go ahead..."
Affan ya d'an murmusa kafin yace "Daddy nima kuma ai inaso a tambaya min auren Lubna...." Ya k'arashe cikin k'asa da murya...
Shareefah ta d'au pillow ta jefa masa tana dariya sosai take fad'in "See this boy har yaushe ka kai auren, don kawai alluranku ta sojoji ta bud'a maka k'ashi sai kace zakayi aure..."
D'an gimtsewa yayi kafin ya dubi ta yace "Ke Shareefah kin faye raina min don bakiga yanda ake bani girma a barinkinmu ba ko..."
Shareefah na dariya taci gaba da fad'in "Daddy see this boy wai shi gani yake ya girma, toh ni ina ruwata da kakin ka you'll always remain my lil bro.."
Dariya sukayi gaba d'aya harda Daddyn kafin yayi gyaran murya ya soma fad'in
"Toh Soldier naji naka buk'atan kaima, amma yanzu ka bari a k'arashe da na yayarka kafin a sauk'o kanka... Kuma naji dad'in maganar da kukayi da shi Nasir d'in sosai... Dama a can Jama'aren nake so ayi komai dukda na jima banje ba tun kafin wannan lalura ta sameni, akwai abubuwa da dama da suka kamata naje nayi a Jama'are shiyasa ma na assala zuwa Bauchin cikin harda ta'aziyan marigayi Jauro bafulatani da yake kular min da share-sharen gidan gona ta..."
Affan ya d'anyi still kafin yace "Daddy kasan har ina mancewa da wancan gidan gonar.."
Daddy Ya murmusa kafin yace "Zaka tuna yanzu kam tunda duka tare zamu tafi gaba d'aya domin iyalan Jauro sun cancanci gaisuwar mu....
**********
Deeni ya kuma yin k'ara sanda Mama Tani ta nad'o ruwan d'umi da mantega ta matsa masa a kwankwason sa, tana yi tana mita.
"Inyi, haba Deeni kanada shegen shiga hurumin da bai shalle ka ba, saida na gargad'eka kafin na kaika aiki gidan can... Ai ga irin abinda ka zaja ma kanka, don ka ganka mai girman jiki sai kace zakayi tsaurin idanu ma soja koh....."
Deeni dake kwance bisa katifar sa kafi tabarma sai nishin azaba yake yana fad'in "Mama Tani kiyiwa Allah ki daina min matsar nan haka..."
"Yo bani dainawa sai naji ka daina kukan nan..." Ta fad'i had'i da kuma matse masa kwankwason sa..."
Deeni ya saki k'ara lokaci guda suka jiyo nishin mahaifin sa na fita sama-sama daga d'aya d'akin yana ambato Zahraddeni..
"Wayyo ni Deeni.... Mama Tani kiyiwa Allah kije ki duba min Abbah na kar ya mutu, nasan kina k'ok'ari damu Allah zai baki lada...."
Mama Tani ta kalle sa cike da tausayawa kafin ta mik'e ta nufi d'akin k'aninta Ayuba....
*Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU*馃寲馃寲
*04*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
Tana dirowa daga saman gadonta window ta isa ta yaye tapkeken labulen tana hangen yanda yake tsayuwa zaman jiranta ta fito, saidai yau kam wayam bata gansa ba. Saida ta d'an sauk'e deep breath kafin ta nufi bathroom don yin wanka...
As usual tana sauk'owa downstairs ta shiga rattaba wa ma'aikatan gidan kira, idan da sabo sun saba da wannan d'abi'a ta Lubna gaba d'aya tayita raba masu aiki kenan har sai ta fice makaranta su sami sukuni....
Ta d'ago ta kuma duban Falmata a karo na biyu kana tace "Kika ce Mama Tani bata kwana gida ba sannan Deeni baizo aiki ba...?"
Falmata ta kuma jinjina mata kai alamun eh tana mai amsa mata..
Gyad'a kai Lubna tayi kafin ta mik'e ta suri mayafin ta da handbag d'inta tana shafa screen d'in wayarta take tambayar ko Falmata tasan gidan nasu...
D'an jim Falmata tayi kafin tace "Eh toh a dai unguwannin loko suke mun tab'a dai zuwa sau d'aya, wata k'ila na gane don gaskiya gidan a cikin lungu yake sosai..."
"Muje ki kaini..." abinda ta fad'i kenan kawai ta nufi k'ofa..
Falmata ta bita da kallo ga tarin ayyukan da suke gabanta kuma dole tayi su kafin Innah ta fito amma babu yanda ta iya b'acin ran Lubna a gidan kan iya janyowa Innah ta sallameta... Cikin sauri ta take mata baya...
***************
Vibrating d'in da wayarsa ke kan faman yi ne ya tada shi daga baccin da yake, don daren jiya gaba d'aya baiyi wani baccin kirki ba tunanin rayuwar da ake a cikin gidansu sam ya hanasa sukuni salloli ya ringa yi yana kai kukansa wa mahaliccin sa majib'icin lamuransa, bashi ya sami wani baccin kirki ba sai bayan sallan asubahi...
Murmushi ya d'anyi da gefen bakinsa sanda yakai dubansa saman screen d'in yaga mai kiran nasa kafin ya shafa saman screen d'in ya k'ara wayar a kunnen sa...
Daga d'aya b'angaren Shareefah babu ko sallama ballantana gaisuwa, cikin shagwab'a ta soma fad'in
"Haba my soldier yanzu ka kyauta min kenan don Allah, tun jiyafa nazo garin nan amma ka kasa zuwa ka ganni gashi har Affan yazo...." ta k'arashe tamkar mai shirin yin kuka...
Saida ya stretching k'afafunsa kafin ya d'au remote d'in AC ya kashe lokaci guda ya sauk'o daga saman gadon ya nufi tapka-tapkan windows d'in wanda aka k'awatasu da navy blue cottons na alfarma ya shiga yayesu gaba d'aya... Nan hasken rana irin ta hantsi ya haske masa fuska, yana d'an rage girman idanun sa wanda dama basu faye girman ba... Cikin daddad'an muryar sa ya soma fad'in
"Miss complain, ai na zaci yanzu kin girma kin daina complain..... Mu gaisa mana first before any complain...." yanda yayi maganar dole ya kashe wa mai sauraren sa jiki..
Baki a ture tamkar yana ganinta ta kuma jawo Azeema cikin jikinta tana mai ci gaba da fad'in "Bafah complain bane... Anyways good morning....!"
Saida ya kuma murmusawa cikin ransa yana mai fad'in Shareefah will never change... A fili kuwa amsa mata gaisuwar nata yayi kafin ya k'ara da...
"Kiyi hak'uri ba wai nak'i zuwa bane, wasu hidima ne dai suka kunno kai suka sha gaba na a nan gida, amma kiyi hak'uri yau d'in nan ina tafe insha Allah, idanma kina so a gidanku zanyi breakfast..."
Batasan sanda ta ture Azeema dake mata wasu salo ba ta mik'e tsaye saman gado tana fad'in "My soldier da gaske... Oh that's so sweet of you... Okay okay I'll cook breakfast for you, me kake son ci...."
Murmushi yake kan faman yi yana shafa sumar sa data sha low-cut yake fad'in "Anything light.... As far as kece kikayi zanci.."
Dad'i da sanyi suka mamaye illahirin zuciyar Shareefah, lallai yanzu kam da alama Nasir bazai watsa masu k'asa a idanu ba, gaba d'aya ya kuma canzawa ba kaman wancan lokacin ba, bata ankara ba saiji tayi Azeema ta jawota ta fad'o jikinta... Kallon kallo suka shiga yima juna lokaci guda suna murmushi...
Kamo face d'in Shareefah Azeema tayi kafin ta soma fad'in "Baby kece zaki soma min kishiya and I'm not ready yet...."
Murmushi Shareefah tayi tana wasu irin salo ma 'yar uwar tata take fad'in "Ohhhh girlfriend don't look at it this way, kinsan bazamu tab'a rabuwa..."
Azeema tayi murmushi kafin tace "Toh me kike tunani idan mijin ki ya sani....?"
Dariya Shareefah tayi tana duban Azeema kafin tace "You so funny Azeema, ta yaya zai sani, karfa ki mance mun jima a cikin wannan hark'ar babu wanda ya tab'a sani, in fact ko Mamy bata sani ba k'arewa ma ta zaci nida ke ba wani shiri sosai muke ba... So pls don't let that bother you kin gane..."
Kallon ta kawai Azeema keyi ita kad'ai take sak'a abubuwa daban-daban cikin zuciyarta kafin tayi murmushi suka kuma yi kafin suka kuma had'ewa waje guda... _(Wa'iyazu billah... Hak'ik'a wannan ma wani babban k'alubale ne da yayi tsamari A DUNIYAR MU.. ALLAH ka kawo mana sauyi ka tsare DUNIYAR musulmi Ameeen!)_
***********
"Babe wllhi gani nan a wata unguwa I can't even pronounce the name.... Kin gane duk yanda za'ayi just sign the attendance for me, idan na gama abinda nakeyi zanzo...." Daga haka kashe wayar tayi ta juyo da dubanta ga Falmata kafin tace "But are you sure mota na shiga nan..?"
"Ai k'aramar Hajiya saidai ki ajiye motar a nan don ban tsamman tana shiga ba..."
Lubna ta d'an dafe kanta had'i da yin gajeren tsaki kafin ta danna security lock taceda Falmata "Fito muje..."
Yatsina fuska Lubna ta shiga yi tana bin mutanen wannan yanki da kallon k'ask'anci her whole life bata tab'a zaton akwai irin wad'an nan unguwannin ba a cikin garin.... Sai tsallake kwata take da k'yar tana tattare skirt d'inta...
Wasu samari kuwa da suke zaune saman wata dakali a bakin kwatar sai ashar suke d'ayankan ma tangad'i yake yana fad'in "Kai Baaba kaga waccar cikan toshe hanci take ta shigo loko...." A tare suka fashe da dariya d'ayan yace baturiya ce ragowar turawan mulki mallaka, kai Baaba wllhi kakanninta sune suka kame kakannin mu suka maidasu bayi mu rama masu akanta wllhi..."
Sauran biyun suka fashe da dariya suna fad'in "Eh wllhi ku tashi muje...."
Suna tafe sai ganin an kewayesu sukayi wasu irin halittu tamkar sun diro daga wani planet... Lubna taci gaba da yamutsa hanci tana b'oyewa bayan Falmata..
*************
"Allah sarki Ilham kar ki damu wata rana insha Allah zaki kuma gani A DUNIYAR MU, Allah zai bud'e maki idanunki ki kuma gani..." ta k'arashe tana rik'o yatsun hannun 'yar uwar tata...
Murmushi Ilham tayi tana mai bud'e manyan idanunta wanda sam bata gani dasu take fad'in "Adda Salma kenan mai zan gani A DUNIYAR MU, duniyar data cika da sab'on mahaliccin mu, duniyar data cika da zalunci da son zuciya.... Addah Salma Allah yasan dalilin da yasa ya d'auke min ganina, sannan ko bai sakani daga cikin masu gani A DUNIYAR MU ba Ya albarkace ni da wasu tarin ni'imomin wad'anda k'wara d'aya bazan iya biyansa ba ciki harda mallaka min ku da yayi a matsayin 'yan uwa. Addah Salma Ubangijina yamin tarin ni'imomi wanda dole na kasance mai godiya a gareshi a kullum... Don Allah ki damuwa da lalurar da nake fama dashi kinji 'yar uwa....."
Salma wacce hawaye suka jik'a fuskar ta gaba d'aya batasan sanda ta rungume 'yar uwar tata ba tayi bursting cikin kuka sosai....
Jamila dake rungume da Falaq daga chan gefensu hawayen ne taji itama suna sauk'o mata, gashi ta lura Innoh tana cikin tsananin ciwo tun jiya da Alh Nuhu ya mata wulak'anci daurewa kawai take bata so ta d'aga ma yaran hankali.... Yanzu duk ranar da akace babu Innoh tasan responsibilities da dama ne zasu hau kanta ga k'anne ga d'iyarta wanda dukansu tana burin ta sama masu rayuwa mai inganci... Anya zamanta a haka babu aure babu aikin yi zai ficce ta, toh ma idan kayi auren mazan ba baka suke ba sun gwammaci su baiwa karuwai a waje, aikin yi kuma sai kai d'an wane ne a baka... Wai shin yaya zatayi ne..? Kasa samo amsar da tayi ya sanyata mik'ewa ta shige d'aki duba Innoh don bataso k'annen su fahimci halin da ake ciki.....
************
Har yanzu cinyoyinsa da k'wank'wason sa basu sake sa sosai ba, yana tafe da k'yar yana dafe bayansa da hannu guda d'aya hannun kuwa rik'e da ledar bredi.....
Mamaki ne ya cika Deeni ganin motar Lubna a pake a cikin unguwar su, lambar motar ya kuma dubawa da kyau yaga babu shakka motar ce, toh amma me ya kawo motar nan..? A iya saninsa jiya sojoji ne suka kawo shi har gida suka watsar dashi.... Toh ko a nan suka bar motar ne... Kai amma ai ko d'azu da zai fito baiga motar ba sai yanzu... Cikin sauri yana d'ingisawa ya nufi kwanar su....
"Ke bakijin hausa ko toh yau zakiji don babanki.... Yimana rawan Ashwariya da Furyanka (Priyanka) don ubanki ko kiji a jikin ki...." ya k'arashe maganar yana tangad'i
Falmata ce tayi ta maza ta shiga basu hak'uri Lubna kam mamaki yama hanata furta koda kalma sai ta mujiya data zuba masu....
"Kai Baba tunda bazatayi ba kawai mu ma shegiya d'aukan amarya..." cewar d'aya mai gashi kaman d'an wasan tashe...
Hankalin Falmata sosai ya tashi ganin wad'annan b'ata garin suna yunk'urin janyo Lubna...
Ai baisan sanda yayi jifa da ledar bredin dake hannunsa ba ya nufesu a tamanin lokaci guda ya kai ma d'ayan naushi a hancin sa... Gaba d'aya matasawa baya sukayi suna fad'in "Sai babban Yaya, wllhi raini ta mana hankali zamu koya mata....."
"Rashin hankalin ku ta kawo nan koh, k'wayar naku bata fad'a maku dai-dai koh, banyi warning d'inki akan tsare 'yanmata ba koh,... Bani nan.." ya fizgi mayafin Lubna daga hannun su kafin ya k'arada ku b'ace nace..."
Gaba d'aya suka soma tafiyarsu irinta 'yandaba suna fad'in "Sai hak'uri babban Yaya...!"
Dawo da dubansa ga Lubna yayi wacce keta faman yatsina fuska, ba tareda yace komai ba ya mik'a mata mayafinta...
Saida ta kuma rausayar da idanu kafin ta amsa lokaci guda ya jeho mata tambaya
"Me ya kawo ki unguwar nan bakisan zuwansa a gareki nada had'ari sosai ba koh...?"
Bata amsa sa ba sai jeho masa tambayar da itama tayi
"Mai ya hanaka zuwa aiki yau...?"
Kallon mamaki ya bita dashi kafin ya kalli Falmata da tuni ta matsa gefe....
Lallai yarinyar nan babban 'yar rainin hankali ce, ta kaisa barikin sojoji a nakasa sa yau kuma tazo tana masa tambayar renin hankali...
Saida ya gyara tsayuwar sa ya rik'e kunkuminsa sosai kafin yace "Na daina aikin ne...."
Lubna ta bisa da kallon mamaki irin batama ji mai yace d'in nan ba.....
"Pardon..."
"Nace maki na bar aikin ko dole ne, kuma ki tattara k'afafunki ki bar unguwar nan kafin wasu su kuma tare ki..." Daga haka yasa kai yana d'ingishi ya isa ya d'au ledar bredin sa zai shige gida kenan sai tsinkayo muryarta yayi tana fad'in
"Ni kake gayawa ka bar aiki,.... Toh ka sani daina aikin ka yana nufin daina aikin Mama Tani a gidanmu, nasan bazaka so hakan ta kasance ba... Sannan duk kwana guda da bakazo ba zan cire a cikin albashin ka....."
Daga haka juyawa tayi ta nufi motar ta...
Deen ya bita da kallon mamaki har ta b'ace ma ganin sa...
*Sameena Aleeyou... 鉁嶐煆�**
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU*馃寲馃寲
*05*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
A tsakar gidan ya tadda Mama Tani tana yafa mayafinta da alama ta fito kenan.
Kallo guda ta masa ta lura tamkar wani abu na damunsa, tana zura takalmanta take fad'in "Zahraddeeni ni zan wuce naga jikin Abban naka da sauk'i sosai don ya shanye kokon da na d'an had'a mas.." burki tayi da maganar nata ganin yayi tsaye tamkar wanda ruwa ya shanye...
D'an matsowa kusa dashi sosai tayi kafin tace "Deeni yaya dai ko jikin naka ne....?"
Murmushin yak'e Deeni yayi kafin yace "Mama Tani Allah Ya saka maki da alkhairi da duk irin d'awainiyar da kike damu..."
Murmushi tayi har cikin ranta tana son Deeni dukda ya kasance maras jin magana, bata tab'a haihuwa ba amma tanajin Deeni tamkar d'an da ta tsuguna ta haifa.. D'an gimtsewa tayi lokaci guda kana tace
"Deeni na hanaka yimin godiyar nan, idan banyi maku ba fad'in duniyar nan ma su waye zanyi inyi banyi maku ba, ahir d'inka da min godiya kana jina koh... Tam ni na wuce ka kula da mahifinka zan lek'o zuwa yamma da yardar Allah..." ta k'arashe sanda ta soma tafiya..
Deeni na biye da ita yake amsawa har ta fice daga gidan...
Koda ya dawo cikin gidan tagumi yayi a tsakar gidan, ta yaya ma zaiyima Mama Tani sanadin aikin ta, macen da ta tsaya sosai akansu, shin ya kyauta idan ya jawo Lubna tasa aka koreta, shakka babu bai kyauta ba sam.... Da wannan tunani ya nufi d'akin mahaifin sa...
*************
Tsawa Innah ta kuma daka mata a karo na biyu...
"Kina jina wllhi kika kuma kai Lubna irin wad'an nan wajajen a bakin aikin ki, kafin na sallalmeki kuma sai na d'aureki, salon ki kai min d'iya mayu su lasheta, itama Tani d'in zata dawo ta sameni... Tsinannen yaro daga ganinsa babu alkhairi a tattare dashi, dole na sallame sa ya bar aiki a gidan nan.."
Har ta juya ta soma tafiya ta kuma juyowa ta dubi Falmata dake rusune a wajen tace "Idan Tani d'in ta dawo ki turo min ita..." ko sauraren amsar Falmata bata tsaya yi ba ta soma tafiya tana huci, gata dai tamkar ka kama ka karya....
******************
Shareefah da Mamy ba'a sama ba'a k'asa, idan kaga saman dinning table d'in sai ka zaci bak'i biyar aka gayyata dukda ba wai tsan-tsan yawan abincin bane a'a kalolin abincin ne daban-daban wanda aka sari English dishes, ko wanne kuma tsugul-tsugul a cikin dishes...
Sosai Nasir yaji dad'in tarban da aka masa a gidansu Shareefah, gaba d'aya sukayi break d'in a saman teburin idan ka d'auke Azeema dake k'ule a d'aki laptop a gabanta tana kan faman bincike a yanar gizo...
Searching sunan Lubna Sa'oud Santana ta shiga yi... Nan tayi clicking kan Lubna Santana bayan wasu sunaye masu shige da na Lubnan sun bayyana mata..
Ta jima tana kallon hotunan Lubna... Tabbas budurwar batada makusa Masha Allah... Bayan ta gama nazari akan Lubna nan tayi zumin wani picture d'inta dana friends d'inta, tafi bada hankali ma d'ya k'awar tata da taga kusan ko ina suna tare.. Murmushi Azeema tayi sanda ta gama duk wani dube-duben da zatayi....
Nasir da Daddy sun jima sosai suna tattaunawa dukda d'an kunyar Daddyn da Nasir d'in keji, nan ya sanar dashi a satin nan insha Allah Yayan shi Kabiru zaizo shi a tsaida komai, sosai Alh Ali Safwan yaji dad'in hakan.... Daga bisani Affan ma ya shigo yayi joining d'insu sukayita labari gwanin dad'i...
Bashi ya bar gidan ba sai goshin sallan azahar, Shareefah kam sai haushi take kan ji bata samu sun sha soyayya da Nasir ba yanda taso, Daddy da Affan sun taresa da surutu.... Haka yayita lallashinta kafin ya tafi ya tabbatar mata zai dawo gobe da dare....
****************
Yana gama tura mata pills d'in ta zube a wajen tana shure-shure had'ida wani irin nishi mai ban tausayi.... Kallon juna sukayi shida Innah lokaci guda suka tunsture da dariya.... Innah tasa k'afa ta shureta nan sukaga har bacci yayi gaba da ita, dama akasarin magungunan haka nan suke mata..
Wani dariyan suka kuma yi kafin Innah ta zauna cikin sofa had'ida d'aura k'afafu d'aya bisa d'aya.
"Kabir Allah dai yayi maka albarka, tabbas kai d'an halas ne wanda baya sab'a dokar mahaifiyar sa, idan naga Saudatu cikin uk'uba har zuciyata nake jin sanyi, tabbas yanzu batada sauran hankali, mun haukata ta da k'arfin gaske, abu na gaba inaso da zaran Fawaz ya dawo k'asar nan, ka ja d'anka a jikin ka kafin tsinannen yaron nan Nasir ya janye sa.."
Alh Kabir yayi wata munafukar murmushi ya shafi hab'arsa kana ya soma fad'in "Innah kar ki damu ni nasan abunda nake yi, abu guda da zaimin cikas idan Fawaz ya dawo shine kar ya fahimci ni na haukata mahaifiyar sa zai iya tsanata na har abada..."
Saida ta mik'e tsaye kafin ta soma fad'in "Ashe kai shashasha ne, toh yaushe zaka bari ya fahimci hakan..?"
"Innah karfa ki mance Fawaz karatun likitanci yake yi kuma likitancin ma na fannin yara wanda suda likitocin mahaukata ai bambancin su k'alilan ne, tunda yaro babu hankali haka mahaukaci ma babu hankali...."
Innah ta murmusa kafin ta kuma gyara zama ta soma fad'in
"Wani sa'in idan kayi abu sai naga kaman ka d'an d'auko wautan ubanka kad'an, kar ka damu amma wayo na da ka d'auko tafi yawa a tattare da kai... Ka samo likitan mahaukata ka biyasa ko nawa ne ya zamto shine likitan Saudat, na tabbata Fawaz idan yaga haka dole zai yarda, sannan abu na gaba ka gargad'i Saudat idan ta sanar da Fawaz abinda kake mata zaka kashe Nasir..... Na tabbata bazata tab'a so wani abu ya sami Nasir ba ta dalilin ta tunda shi kad'aine mai tausayin ta... Sannan yanda ka dasa mata tsoronka cikin zuciyarta da rashin d'and'anin imani da kake dashi da dole ta saduda ta amshi haukar da k'arfin gaske....." ta k'arashe tana kyasta lighter lokaci guda ta dondala wutar ma tabar dake bakinta..
Alh Kabir ya jima yana murmushi cikeda jin dad'in shawarin Innah kafin shima ya dandali wutar sigarin suka ci gaba da busawa tare...
"Innah ya maganar auren Nasir d'in fah...?" ya tambaya yana kuma duban ta..
"Inaso ya auri yarinyar domin akwai fansa na akanta, kasan bana yafiya sam, duk wanda ya min abu shida danginsa gaba d'aya sai d'and'asa masu uk'uba a cikin ruwan sanyi...."
Kabir yayi murmushi yana hura hayak'in sigari ta hancin sa da baki lokaci guda ya gyara zaman sa kafin yace "Mai ya had'aki da yarinyar..?"
"Kar ka damu ita yarinyar tasan abinda ta min, kuma sam banaso Nasir ya auri mace mai kamun kai, wannan yarinyar itace dai-dai dashi don haka inaso ka tsaya sosai akan maganar auren har sai komai ya wakana...."
Alh Kabir ya murmusa domin kuwa a b'angaren sa ya tanadar da d'aukan fansan abinda Nasir ya masa a yammacin jiya... Tabbas bazai fasa k'udirin sa ba, tun daga kan iyalan matar da zai Aura zai soma d'aukan fansa har ya gangaro kan sa....
*************
Sosai abin ya basa mamaki ganin yau Yaya Kabiru har hira sosai ya zauna yanayi dashi kuma musamman akan maganar auren sa, abun bai gama basa mamaki ba saida yaga Innah ma yau faram-faram take yi dashi, gaba d'aya sai yanajin abin banbarak'wai dukda har kullum mafarkin da yakeyi kenan iyalan gidansu su kasance ciki....
Kan kace me an soma gudanar da shirye-shirye babu kama k'afan yaro, sannan wani abin mamakin Yaya Kabiru ya rage tak'ura ma Aunty Saudat da duka musamman idan a gaban Nasir ne, drugs ne kurum bai fasa bata ba, wanda a halin yanzu har ya soma juya mata kwanya sosai, shi kansa Nasir d'in baisan Yayan nasa na d'irka ma Aunty Saudat drugs ba, amma kam yanzu shakka babu yaji dad'in yanda ya rage jin sautin kukan ta, da alama yayan nasa nutsuwa ya soma sauk'o masa...
**************
Yatsina fuska Mamy ta kuma yi tana ci gaba da mitan ita sam bata son zuwa k'awye...
Alh Safwan yayi shiru domin shi mutum ne maras son tashin hankali, d'ago kai yayi ya dubeta kafin ya soma fad'in "Ba damuwa Asma'u kuna iya zama a gida kedasu Shareefah idan yaso nida Affan zamuje, amma ki sani auren Shareefah a Jama'are zan d'aura..."
Kauda kai gefe tayi had'i da tab'e baki lokaci guda ta soma fad'in. "Banda d'aura ma kai wahala ina kaga lafiyar yin tafiya, kana nan sai an fitar sai an shigar, babu yanda banyi da kai ba ka saida gidan gonar nan ka huta amma ka k'i, mutane sai cutanka suke sam baka gani...."
Har ta k'arashi masifar ta bai tankata ba sai tura tayun wheelchair d'insa da ya soma yi lokaci guda yana kiran layin Affan...
Wani uwar tsaki Mamy taja had'i da ficewa daga d'akin...
D'aki ta shige tana tunanin maganganun da Malaminta ya sanar da ita, duk ranar data kuskura ta ta shiga garin Jama'are sammon da tayi ma Alh Ali Safwan zai warware ya koma kanta, ma'ana zai sami lafiyan k'afafu ita kuma zata zama gurguwa... Tun ba yauba taso ya sayar da gonar ta amshe kud'in yak'i saidawa, ita yanzu babban damuwarta kar ya tattari auren Shareefah ya kaisa garin Jama'are, dole tasan nayi, dole tasan yanda zatayi ta zuga Shareefah kan cewar kar ta yarda aka kai d'aurin aurenta k'auye... Da wannan tunani ta saduda har tayi masu rakiya zuwa waje.....
Affan ne ke driving yayinda Daddy ke gefen mai zaman banza don yanzu bai iya zaman baya dole yake zama a gaba domin ya mik'e k'afafun sa, Mamy da kanta ta nad'e keken guragun nasa ta saka a bayan mota.. Sallama da juna sukayi kafin suka fice suka d'auki hanyar garin Jama'are
*************
"Hajiya don girman Allah kiyi hak'uri amma kar kice zaki sallami Zahraddeeni yaron abin tausayi ne...."
Innah ta kuma mik'e 'yan siraran k'afafunta saman center table kana taci gaba da fad'in "Naji tashi ki bani waje banida lokacin surutu..." ta k'arashe tana dangwala remote...
Mama Tani ta d'an girgiza kai had'i da mik'ewa lokaci guda...
**************
Gidan gonar tayi nesa sosai da cikin garin Jama'are da kusan tafiyar rabin awa....
Ya jima yana bin gate d'in wajen da kallo sanda Affan yake rangad'a horn... Masu tsaron gate d'in sun sha mamakin ganin uban gidan nasu yau shi da kansa ne yazo, saurin hangame masa sukayi suna masu kwasan gaisuwa, a haka ma'aikatan wannan gidan gona suka ringa zuwa suna kwasan gaisuwa cikeda mamakin lalurin da ya sami uban gidan nasu wanda duk basu sani ba sai Manager d'insa wanda ba kowa bane illa d'an uwansa Alh Mudi, wanda sabida tsaban bala'in Mamy bai zuwa chan Kaduna gidan d'an uwan nasa saidai ya rik'e masa amanar dukiyar sa...
Nan suka shiga zagaye gidan gonar Affan ma na biye dasu.....
Bayanta ya hanga sai sauri take da alama jama'an da ta gani ne ya sanyata yin sauri, haka kurum yaji yana son ganin fuskarta, sauri-sauri shima ya ringa binta har baisan sanda ya rabu dasu Daddy dake tsaye jikin garken wasu shanaye ba ana masa bayani....
Gabanta ya yanke ya fad'i ganin wannan mutumi yak'i daina binta, dabara ce ta fad'o mata nan ta shige cikin garken shanaye ta b'uya..
Sanda ya k'araso wajen bai ganta ba mamaki ne ya cika sa, toh kodai b'acewa ne tayi, sai waige-waige yake yana neman ta yanda zai ganta
K'unshe dariyar ta tayi ganin yanda yake rarraba idanu yana rik'e da kunkuminsa yana furta "Toh ina ta shiga...."
Gaba d'aya batasan durk'ushe take a bayan saniya guda ba, aiko nan saniya ta yunk'ura zata mik'e nan ta wuntsilota bata fad'a ko inaba sai cikin wani rami da refuse ke taruwa dangin kashin shanayen.... Ai batasan sanda ta k'walla wani irin k'ara ba lokaci guda, jikinta jagab kashin shanaye...
Baki hangame Affan ya juyo yana dubanta, kad'an ya rage bai runtuma a guje ba don a zatonsa aljana ce, kawai dai k'arfin hali irinta sojoji ya sanyasa tsayuwa...
K'arasowa wajen yayi da sauri yana dubanta lokaci guda ya toshe hanci yana furta "Eww! Who..... are.... you..?" yanda yayi maganar kalma bayan kalma
Bata basa amsa ba sai kukan da ta kuma fashewa dashi...
A hankali ya soma furta "Hey it's okay, ki daina kuka me ya kawoki nan....?"
Nan ma bata amsa ba sai kukan data kuma fashewa dashi tana dubansa, i zuwa lokacin Affan ya zaci kurma ce, maganan kurame ya soma mata da hannu lokaci guda ya isa jikin wani garwan ruwa ya d'auko chak ya juye mata tun daga kanta..
Nan dattin ya fice daga jikinta asalin kalan fatar ta da kamanninta suka bayyana...
Kai tsaye baza'a kirata fara ba, tafi yanayi da mutanen yankin Ethiopia, batada wani tsananin kyau saidai tana suffa irin ta d'iya mace sannan idan kayi mata kallo guda lokaci d'aya zakaji ta shiga ranka, walau na miji walau mace, wannan baiwa ne da Allah yayi mata....
Ganin yayi tsaye ya mata k'uri kaman tsohon maye ya sanyata saurin cire kallabin dake kanta ta warware ta rufa a jikinta, ta gwammaci sumarta ya bayyana akan a gane mata halittar jikinta...
D'an ware idanunsa Affan yayi ya soma mata maganar kurame alamun yana bata hak'uri, saidai kafin ya ankare har ta soma tafiya cikin tsananin sauri...
Taku kad'an yayi yasha gabanta fuskar sa a murtuk'e yake fad'in "Ku kuramen nan bansan meyasa bakujin hak'uri ta dad'i ba....."
Bai kai aya ba ya hangeta ta nufi wani hanyar cikin tsananin sauri tamkar zata kifa da k'asa, ai shima a tamanin ya take mata baya....
Tarban girma Innoh tayima Alh Ali Safwan, ganinsa ya tuno mata da marigayi mijinta, Daddy ma hawaye ya ringa yi da k'yar ya iya resisting kukan nasa. ... Nan yake tambayan Mal Mudi ina Affan ya tsaya... Mal Mudi baikai ga basa amsa ba Salma ta shigo cikin sauri Affan na biye a bayanta..
Gaba d'aya suka bisu da kallon mamaki....
Affan d'inma mamaki yayi ganin Daddyn sa zaune tsakar gidan...
Da mamki Innoh ke duban Salma kana tace "Salame ina kika jik'a jikin ki haka...?" Salma bata amsata ba sai shigewa d'aki datayi da sauri don canza kayan jikinta..
Affan dake tsaye a wajen tamkar wanda aka dasa sai jiyo muryar Daddy yayi yana fad'in "K'araso mana Affan.."
Babu musu ya k'araso ya zauna gefen Daddy.. Nan Daddy yayi introducing d'insa masu Innoh. Nan da nan shima aka cika gabansa da dangin madaran shanu..
Shikam Affan idanunsa da hankalinsa kacaukam naga k'ofa yaga yaushene kurman nan zata fito...
*Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*06*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
Mamaki ne ya cika Affan sanda yaji Salma tana gaida Daddyn sa, ashe dama tana ji sarai tayi masa banza d'azun, kuma yin hakan da tayi sai ya kuma jin ta burgesa sosai...
Daddy Ya amsa mata cikin sakin fuska kafin ya dubi Innoh yace "Itace cikon ta ukun su kenan...?"
Innoh ta jinjina kai kana tace "Eh Alhaji itace Salma d'iya ta biyu ga marigayi..."
"Allah sarki Allah dai ya masa rahama ya d'ayyiba abinda ya bari.." Gaba d'aya suka amsa da ameen idan ka d'auke Affan dake faman bin Salma da mayen kallo...
Gaba d'aya yaran suka tattara suka nufi can wani b'angaren ya rage saura Innoh da Daddy. Affan ma ya fice shida Baffan sa Mudi.....
Alh Ali Safwan ya gyara zama bisa tabarmar azaran yayi had'i da d'anyin gyaran murya kafin ya soma fad'in "Wato Harira a gaskiya zamanku a wannan daji yayi wani iri dukda tsaron dake a cikin gidan gonar nan, yaranki gaba d'aya 'yanmata ne wanda dukanku kuna buk'atan zama a k'ark'ashin kulawar wani.... A ganina me zai hana ku koma zama a gidana dake cikin garin Bauchi tunda ni ba wani zama nazo yi ba...."
Shiru Innoh tayi tana nazarin kalaman nasa, rana a tsaka su bar garinsu mahaifar su abin da kamar wuya dukda cewa danginsu gaba d'aya suna k'asar Kamaru (Cameroon) toh amma rana d'aya su tattara su bar gari babu shiri babu komai abin yayi banbarak'wai dukda cewa shi Alh Ali mutumin arziki ne...
Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa Daddy kuma yin wata gyaran murya irinta manya kana yaci gaba da fad'in "Ba lallai sai yanzu ba, nima inaso idan na koma na sanar da mai d'akina akan batun, sannan kema kina iya sanar da yaranki don kiji nasu ra'ayin suma...."
Innoh ta jinjina kai kafin tace "Ehh toh wani hanzari ba gudu ba Alhaji, ba wai nak'i maka bane, kamar yanda na shaida maka ita babbar tasu wato Jamila bata jima da rabuwa da mijinta ba, sannan akwai d'iyar shi mutumin a hannun Jamila, barinmu garin nan ka iya sa shi Alh Nuhu yayi k'arar mu kotu idan yaji mun tafi da d'iyarsa wani garin dukda ba wai son d'iyar yake ba amma kasan d'an Adam a yau sai Allah..."
Shiru Alh Safwan yayi tamkar mai nazari kana ya jinjina kai yace haka ne, kinyi gaskiya... Babu damuwa duk ranar dai da kukayi shirin komawa can d'in zaku iya komawa..." Yasa hannu jikin wheelchair d'insa ya ciro wani kati mai d'auke da lambar gidansa da adireshin sa ya mik'a ma Innoh yace "Ga adireshin gidan idan kunyi shawari da yaranki idan kun yanke komawa chan gidan namu babu wani matsala, ina mai tabbatar maki zamu zauna daku cikin amana da yardar Allah...."
Innoh ta jima tana juya katin a hannunta kafin ta shiga yi masa godiya....
Wajajen bayan la'asar suke shirin fita daga garin, daga gidan Baffah Mudi basu koma can gidan gonar ba, sam Affan baiso hakan ba yaso ya kuma ganin Salma kafin su wuce amma Allah baiyi ba.....
******************
Saida ya gama gana mata kalolin azaba kafin ya sauk'e buk'atar sa akanta cikin wulak'anci da cin zarafi, gashi ba kalamai masu dad'i bane suka biyo baya sai na tozarci da cin zarafi....
Tana jin sanda ya sanya k'afafu ya shureta ya fice daga d'akin....
Kai tsaye Study d'insa ya wuce yana amsa wayoyi wanda akasari daga kampanin su ne, daga bisani wayar Maina ya shiga kira, bugu biyu ya d'aga yana kod'asa kaman yanda ya saba...
Alh Kabir sai murmushi yake yana sosa hab'ar sa yana jin dad'in kirarin da Maina ke masa...
"Kana jina banaso a sami failure don't let me down Maina, da k'arfin gaske nake so na talauta sa, ka tabbata babu saniya mai rai da za'a cire...."
Daga d'aya b'angaren Maina ya fashe da dariya kana yace "Bakada kyau Mai gida, za'ayi yanda ka umarta, Alh Ali ya talauce an gama....."
Dariya Alh Kabir ya kuma fashewa dashi shi kad'ai yana juya k'afafu... A fili yake furta "Na fara d'and'ana maka kenan Naseer tun daga iyalan matar ka, zaka gane fad'a da aljani ba riba...." Dariya ya kuma fashewa dashi shi kad'ai harda tafe hannaye....
A farfajiyan gidan yaci karo da Naseer alamun dawowar sa kenan..
Murmushi Alh Kabir ya sakar masa kafin ya k'arasa da sauri had'i da basa hannu sukayi masabaha, murmushi Naseer d'inma ke yi lokaci guda ya soma gaida Yayan nasa...
Alh Kabir tamkar mutumin arziki haka yake amsa gaisuwar Naseer d'in had'i da jansa da hira, hannunsa dafe da kafad'a Naseer dukda Naseer d'in ya d'ara masa a tsawo suka k'arasa cikin wasu 'yan bukkoki wanda aka k'awatasu da kujerun shak'atawa na alfarma.
Akasarin hiran nasu akan auren Naseer d'in ne, yanda Alh Kabir ya shaida wa Naseer cikin satin nan zaiyi k'ok'ari komai ya wakana, ya k'arada
"Brother kayi hak'uri da duk wani miss understanding da suka shiga tsakanin mu a baya, na gane wasu abubuwan da na maka a baya basu kamata ba, ka yafe min pls...."
Naseer yayi murmushin jin dad'i kafin ya rik'o hannayen Alh Kabir yace "Yaya komai ya wuce, mu duka 'yan Adam ne kuma muna kuskure A DUNIYAR MU shiyasa hannun ka bai tab'a rub'ewa ka yanke ka yar.... Duk tsanani duk wuya strong bond d'in dake tsakanin ku bazai bari tab'arb'are ba, ina rok'on Allah yasa hakan ya d'ore mu samu peace A DUNIYAR MU....."
Murmushi kurum Alh Kabir yake yana karantar d'an uwan nasa, lokaci guda yayi hugging kafad'un Naseer d'in...
Innah daga window d'in d'akinta tana hangensu tana hura sigari tana murmushin k'eta ita kad'ai... A fili ta furta
"Saudat da Naseer bazasu tab'a jin dad'i A DUNIYAR MU ba muddin ina numfashi... Na tsani farin fata kamar yanda Hidaya ta tsani bak'in mutum ta gallaza min azaba wllhi tallhi billahi bazan tab'a barinsu suji dad'i ba, Sa'oud ne ya had'a mu kuma ya rabamu tunda ya riga ya shura lahira....."
*_TIRK'ASHI_* WAI SHIN MENENE SUKA FARU SHEKARUN BAYA A GIDAN MARIGAYI SA'OUD SANTANA??
_*Waiwaye*_
A k'arshen k'arni na ashirin zuwa farkon k'arni na ashirin da d'aya turawan k'asar Faransa sun mamaye wata birni mai suna Casablanca dake k'asar Morocco, Kakannin Sa'oud Santana sun kasance daga cikin wad'ancan turawa sun zauna a birnin Casablanca na tsawon shekaru... Banbance banbancen launin fata da na addini yayi tasiri sosai a wancan lokacin sabida sam larabawan gani suke turawan Faransa sun masu fin k'arfi suda k'asar su, mahaifin Sa'oud ya had'u da wata balarabiya 'yar asalin k'asar ta Morocco wanda a dalilin haka yasa ya karb'i addinin musulunci, iyayen sa sunyi baran-baran dashi akan abinda yazo dashi. Na farko sam basu ya auri wata jinsi da ba'a cikinsu take ba ma'ana basu so ya auro balarabiya, na biyu karb'an addinin islama da yayi... Hakan yasa suka sanya masa tak'unk'umi wanda yasa dole ya d'auki matar sa suka baro k'asar Morocco.
Sun zauna a k'asashen Africa ta arewa da dama cikin larabawa daga wannan garin zuwa wancan garin sakamakon kasuwanci da mahaifin Sa'oud keyi babu kama k'afan yaro, dukda banbancin launin fata da yake samu daga wajen wasu larabawan.. A cikin tafiye-tafiyen nasa ne ya k'araso Africa ta yamma yanda ya yada zango a k'asar Nigeria..
Ya zauna a k'asar Borno tun a wancan lokacin tana Barno empire tana had'e da garuruwa da dama a arewa maso gabashin k'asar nan...
Mahaifin Sa'oud wato Naseer Santana ya kasance yayi arziki sosai zuwa k'asar Nigeria da yayi wanda hakan ya sanyasa ya zauna a k'asar Nigeria bai kuma canza k'asa ba.. Ya had'u da wani mutum mai suna Baana, wanda ya rik'e masa amanar dukiyar sa bisa gaskiya da rik'on amana har sun koma tamkar 'yan uwan juna, dad'i da k'ari a k'asar Nigeria ne matarsa mai suna Najwa ta haifo masa santalelen yaro na miji don haka babu batun tafiye-tafiye da d'anyen goyo... Yaro yaci suna Sa'oud sannan ya taso cikin soyayyan iyayen sa da mak'ota da abokan arziki....
Sa'oud da iyayen sa suna zaune a k'asar Borno wata rana sak'o ya tadda Nasir cewa iyayen sa Allah Ya masu rasuwa sakamakon had'arin mota da sukayi... Haka ya tattari iyalansa gaba d'aya suka tafi birnin Casablanca, yayi kuka sosai sanin cewa iyayen sa a mushurikai suka mutu gashi babu halin yayi masu addu'a...
Naseer Santana ya jima a can k'asar ta Morocco sanin dukiyar sa na hannun na gari, dama tilastawa na iyayen sa ne yasa shi barin k'asar bagatatan, mai d'akinsa ma tafi son zama a k'asar su cikin 'yan uwanta...
A haka suka shafe shekaru har Sa'oud ya kai shiga makaranta suka saka shi a nan birnin Casablanca... Daga baya iyayen sa sun dawo Nigeria yanda suka barsa a can yana karatu gaban Kakannin sa iyayen Babarsa..
Bayan wasu shekaru Sa'oud ya shak'u da kakannin sa sosai har yana jin bazai iya rabuwa dasu ba, a haka har ya kai munzanin shiga jami'a, I zuwa lokacin iyayen sa ma sun son d'ansu ya dawo garesu amma rana tsaka bazasu iya d'auke sa kwatsam ba yin hakan rashin kyautawa ne ma Dattijan...
Bai baro k'asar Morocco ba har saida ya kusan kammala karatunsa na jami'a sannan kakannin sa suka aura masa Mace a dangi mai suna Hidaya
Yakan d'aukota suzo k'asar Nigeria duba iyayen sa amma fir Hidaya takan nuna bata son k'asar Nigeria bata son bak'in mutum... Haka Sa'oud zaiyita nuna mata cewa da fari da bak'i dama ko wani irin mutum duka Allah ne yayi su kuma yana son kayansa sannan babu wanda yafi wani a wajen Allah sai wanda yafisu tsoronsa... Hidaya takan jisa kawai domin kuwa ita sam babu yanda za'ayi ta k'aunace bak'in fata..
Suna shekara ta biyu da aure Allah yayi ma kakanin Sa'oud rasuwa dole suka tattara suka dawo Nigeria wajen iyayen sa...
Baana mai kula ko nace mai hidima ma Naseer yanada matar aure da d'iya k'wara d'aya tak mai suna Dije,...
Dije tayi aure har ta haihu saidai sun rabu da mijin, lokacin da Sa'oud da matar sa suka dawo k'asar nan sai aka basu Dije ta ringa taya Hidaya da aikin cikin gida tunda batada aure a lokacin... Muzgunawa babu irin wanda Dije bata gani ba a wajen Hidaya, har manna mata dusten guga mai zafin gaske ta tab'a yi sabida kawai ta tsanin bak'in mutum, wani sa'in Sa'oud ne yakan k'waci Dije, gashi babu hali tazo da goyon jarirn d'anta shima sai ya karb'i nasa tsaraban a hannun Hidaya, idan Dije tace zata bar aikin mahaifiyarta ita ke tausar ta tana sanar da ita akwai ranar d'aukan fansa na nan na zuwa mata idan ta jure duk wani wuya har ta samu ta shiga gidan Sa'oud, domin ita batada burin da ya wuce Dije ta auri Sa'oud.... A 'yan wad'annan lokuta Allah yayi ma mahaifin Sa'oud wato Naseer Santana rasuwa, Sa'oud yayi kuka sosai wanda tun bayan rasuwar Naseer Najwa ma ta soma ciwo, ba'a jima sosai ba itama tace ga garin ku...
Kasa zaman Maiduguri Sa'oud yayi dole ya gangaro ya dawo k'asar Bauchi da zama, gashi har lokacin Allah bai basu haihuwa ba shida iyalinsa, mutuwar iyayen Sa'oud sosai ya shiga jikin Hidaya sannan taga yanda bak'ak'en fata suka masu kara, tabbas ta yarda musulmi d'an uwan musulmi ne, tun daga wancan lokacin ta daina hantaran bak'in fata...
Sa'oud ya tattaro dukiyar mahaifin sa gaba d'aya ya dawo dasu k'asar Bauchi yanda ya gina shararren kampani wanda mutane da dama suna amfana dashi wajen zuba kasuwancin su a ciki mai suna *Santana Corporation*
Gaba d'aya suka dawo garin ta Bauchi harda Dattijo Baana da iyalansa Dije da mahaifiyarta da kuma d'anta Kabiru, dadowarsu Bauchi da kad'an mahaifin Dije ya rasu, sunci kuka sosai ita da mahaifiyarta yanda Sa'oud yayi alk'awarin bazai tab'a barinsu ba
Yanzu kam sosai Hidaya ta sake dasu, bata hantaransu saima rok'onsu gafara da take yi, Kabir har ya koma tamkar d'anta, tana son yaron domin abubuwa na mugunta data masa a baya sai tana ganin kaman Allah bazai tab'a yafe mata ba, d'aukan yaron da take yi yasa ta shak'u sosai dashi, tun yana jin tsoronta sabida farin fatar ta yana ganin kaman babban doll baby ce har ya saki jiki da ita yana ganinta zai soma murna, duk wannan abunda ake zuciyar Dije bai warke daga gyambon d'aukar fansan da ya mamaye sa ba, har yau idan ta d'aga bayanta akwai tabon da Hidaya ta mata da dutsen guga, sannan ta d'au alwashin saita rama ko ba dad'e ko ba jimawa muddin tana numfashi...
Ana haka bayan wasu 'yan shekaru Hidaya ta sami ciki, wai zo kaga murna wajen wad'annan bayin Allah, wato Sa'oud da Hidaya, haka akayita tarerayan cikin har ya girma, Dije da mahaifiyar ta ma sun nuna soyayyar su sosai ga cikin Hidaya, haka Maman Dije tayita d'irka ma Hidaya wasu irin magunguna da sunan maganin zak'i ba don komai ba sai don Hidaya ta mutu d'iyarta ta auri Sa'oud, idan tak'i sha haka zata kalallameta da baki tace rubutu ne zaisa ita da abinda ke cikinta suyi lafiya, abinka da wacce ta jima bata haihu ba tuni sai ta karb'a ta kurb'e...
A haka wani rana zata wuce d'aki tana haurawa bene da k'yar tanayi tana hutawa, daidai k'ofar d'akin su Dije ta jiyosu sai shewa suke suna fad'in tsinanniya ta kusan margayawa ta basu waje, abubuwan da kunnen ta suka jiyo mata babu dad'in saurare, dukda wasu hausar ba fahimta take ba, take taji abinda ke cikinta na juya mata jin duk shirinsu akan su kasheta ne Dije ta auri mijinta, wani irin k'ara ta Saki tana rirrik'e cikinta don bata so ta rasa abinda ke cikinta, ta gwammaci ita ta mutu amma shi ya tsira...
A tamanin suka fito rik'e da k'ugu suna dubanta, duk a zatonsu bataji abubuwan da suke fad'i ba, Maman Dije ta nufota da sauri tana tattare zani take fad'in "Mun shiga uku, Hidaya nak'udar ce..."
Jada baya Hidaya take tana mannuwa jikin staircase take girgiza kai tana karkad'a hannu tana kame cikinta da hannu guda take furta "Kar ki zo kusana, kar ki cutar da abinda ke cikina, naji komai, ashe ba son gaskiya kuke min ba, shin ta yaya Sa'oud zai yarda da auren d'iyarki idan yaji bak'in aikin da kukayi, nasan na maku laifi a baya sannan na cutar daku, amma cutar da na maku baikai na d'aukar rai ba.. Shin dama haka Mutane suka koma A DUNIYAR MU, meyasa baku rama iya abinda na maku ba meyasa zaku cutar da abinda ke cikina.... " muryarta ya carke sanda ta kuma jin wani sabon murd'a na taso mata, sosai ta rik'e staircase tana wani irin nishi... Ganin haka yasa Maman Dije nufota a tamanin, itako Hidaya ta razana da ganin yanayin matar cikin sauri ta matsa gefe aiko Maman Dije tana k'arasowa takai capka ma k'arafan staircase kan kace me tayi juyi ta apka k'asa...
Wani irin gigitaccen k'ara Dije ta saki lokaci guda ta nufi mahaifiyarta dake mashasshara tana ambato sunanta dai-dai lokacin da Sa'oud ya shigo gidan, ga Dije da mahaifiyarta a k'asa rai a hannun Allah ga matarsa saman bene tana nak'uda, cikin sauri ya yarda abubuwan dake hannunsa dangin kayan wasa yaso ma Kabir da unborn child d'insu.. Kan matarsa yayi a tamanin yana jijjigata amma ina nishi da k'yar take, cikin sauri ya sureta ya fice da ita, wannan abu ba k'aramin bak'anta ran Dije yayi ba, Matarsa ta kashe mata uwa, sannan baibi ta kansu ba ya suri matar sa ya fice da ita, tabbas idan mahaifiyarta ta mutu gaba d'aya sai ta d'au fansa akansu..... Kuka take sosai tana rungume da mahaifiyar ta, lokaci guda Kabir ya k'araso a guje yana d'aukan kayan wasa, wata uwar tsawa Dije ta daka masa wanda yasa sa watsar da kayan wasan babu shiri, hannu tasa ta janyo d'anta ta had'e ta rungume da mahaifiyarta tana wani irin kuka.....
Duk yanda akayi a ceto rayuwar Hidaya abu ya faskara, Allah sarki Hidaya dai Allah yayi mata cikawa bayan anyi k'ok'arin ceton ran abinda ta haifa ta bari, haka Sa'oud ya rungume jaririn cikin jikinsa yana kuka da duka zuciyar sa, hak'ik'a yana son Hidaya so na gaskiya gashi mutuwa ta masu yankar k'auna...
Sanda ya shigo gidan rungume da d'ansa Dije ma tana kwance saman gawar mahaifiyarta ga Kabir d'an shekaru goma na taya ta kuka, sai lokacin Sa'oud ya lura da abinda ya faru, wani sabon kuka ya kuma b'alle masa...
Kusan tare-tare aka gabatar da komai na mutuwar Maman Dije da kuma Hidaya, Allahu Akbar wannan shine tashin hankali wanda ba'a saka masa rana....
Haka rayuwar gidan ta koma tamkar babu masu rai cikinta sai Kabir dake kai komo a tsakani, shi kuwa Sa'oud da k'arfi saida ya iya rainon jariri Dije koh kullum cikin jimamin mutuwar mahaifiyarta take, idan ta jiyo sautin kukan jaririn da yaci sunan mahaifin Sa'oud wato Naseer har cikin k'ahon zuciyarta take jin tamkar ta shak'e yaron ya mutu ko zata huta, batada burin da ya wuce ta d'auki fansar ta akan abinda Hidaya ta haifa ta bari, zuciyarta ta kuma bushewa ta kuma k'ek'ashewa. Da wannan tunani ta mik'e ta fito parlor yanda ta tarar sai kokawan canza ma Naseer napkin Sa'oud keyi.... Tasa bayan hannu ta share hawayen taurin rai da suka zubo mata kafin tayi murmushi ta isa garesu ta amshe Naseer kan kace me har ta shirya yaron tsaf ya daina kuka.
Da murmushi Sa'oud ke dubanta had'i da yi mata godiya, yana mai tausaya mata na rashin mahaifiyarta da tayi..
A haka rayuwa taci gaba da tafiya masu Dije na kula da Naseer tamkar ita ta tsuguna ta haifesa, idan Sa'oud ya nuna mata jin dad'insa bisa yanda take kula da Naseer sai ta nuna masa cewa ai d'a na kowa ne, kuma tana tausayin duk wanda ya rasa mahaifiya sannan rana guda suka rasa mahaifansu ita da Naseer..
Murmushi kawai Sa'oud yakanyi yana mai jin wani abu a hankali cikin zuciyar sa gameda Dije, a haka rayuwa taci gaba da tafiya masu har dai ya fayyace mata yana son aurenta, itama tuni ta aminta dashi yanda suka tafi can Maiduguri aka d'aura masu aure suka dawo Bauchi gidansu da yaransu Kabeer da kuma Naseer.
Naseer bai ragewa mahaifinsa komai ba, bashida tsananin kyau amma yanada structu irinta mazaje sannan kallo guda zaka masa ka gane tsan-tsan bature ne. Sa'oud da Dije sun yanke shawarin b'oye ma Naseer cewa ba Dije bane ta haifesa bayan ta masa magiyan kar ya sanar dashi ba itace ta haifesa ba, Sa'oud ya kuma jin dad'i ganin yanda Dije ke son Naseer har ta kai ta barahi a matsayin d'anta, ya tabbata Naseer bazaiyi kukan maraici ba.
A haka yaran suka taso tamkar Yaya da k'ani dukda Kabir ya d'arama Naseer da shekaru kusan goma saidai d'aya bature ne d'aya bak'in fata ga sunan mahaifinsu iri guda,kasancewar shi Kabir d'in bai shiga makaranta da wuri ba shiyasa ya d'ara Naseer d'in da aji kad'an a primary school. Idan yara sun damesu da tsokana fari da bak'i sai Kabeer yace shi Innar su ya biyo yayinda Naseer ya biyo Abbansu. Wasu suk'i yarda sai sunzo gidan sun gane ma idanunsu su yarda.
Tunda Naseer ya soma girma Innah ta soma hantaran sa akan d'anta Kabeer, gashi sam Kabeer baida kunya bai ganin girman na gaba, idan kaji an kawo k'arar fad'a cikin gidan toh Kabeer ne.
A haka Kabeer ya kai shekaru goma sha takwas tuni ya soma bin 'yanmata yana lalata su, sosai abin yake damun Sa'oud Santana, idan yayi magana Innah tace aure yake so ayi masa,.
Wata rana Sa'oud ya had'u da k'anin mahaifin Hidaya a can k'asar Morocco wani zuwa da yayi duba dangi, nan Sa'oud ya buk'aci Suhail ya biyosa Nigeria suyi aiki tare tunda iyalinsa bata jima da rasuwa ba kuma yana son canza environment ko zai mance abin, tuni Suhail ya amince da batun mijin 'yar uwar tasa suka biyo Sa'oud Nigeri shida d'iyarsa mai suna Saudat, yarinya 'yar shekaru goma sha hud'u, Sa'oud ya sanar dashi dokokin gidansa cewa kar ya tab'a sanar da Naseer cewa ba Dije bace ta haifesa.. Mamaki ne ya cika Suhail ganin shida d'iyar 'yar uwarsa amma bashida halin sanar dashi shi d'in uba yake ga mahaifiyar sa...
Tunda Kabeer ya k'yalla idanu kan Saudat yake bobiyanta yana neman ya lalata yarinya gashi ba yarensa take ji ba domin kuwa ita da mahaifinta basu jin komai sai larabci.. Koda Suhail yayi magana Innah tayi kicin-kicin tace sharri zai k'ulla ma d'anta don yaga shine ya fito bak'in fata....
Haka Sa'oud yayita tausan Suhail k'arshe Suhail yace bazai iya ba zai koma can k'asar su domin kuwa sam Kabeer ya hana ma d'iyarsa sukuni dukda k'arancin shekarunta..
Haka Kabeer ya tada masu hauka a gidan shidai saidai a Aura masa Saudat, babu yanda Sa'oud baiyi ba ganin Kabeer ya cire maganar auren a ransa abu ya faskara, Innah kullum kuka tana rok'on Sa'oud ya taimaka ya shawo kan Suhail ya aura ma Kabeer Saudat don cewa yayi muddin ba'a aura masa Saudat ba toh kuwa zai kashe kansa..
Mahaifin Saudat kuwa da yaga sun damu har haka sai ya yanke masu dukiyar da zasu bada kaso biyu na cikin dukiyar Sa'oud Santana kafin ya bawa d'ansu Kabeer auren Saudat, hankalin Innah sosai ya tashi da jin irin kud'ad'en da Suhail ya yanke, amma yaya zatayi tanada k'udirin d'aukan fansa akan duk wani jinin Hidaya da zata sami dama akansa, don haka batayi k'asa a gwiwa ba wajen ganin Alh Sa'oud ya biya wad'anan kud'ad'e da Suhail ya buk'ata..
Sa'oud ba don yaso ba akayi wannan aure, Saudat da batasan wainar da ake tuyawa ba sai gani tayi an rufe kanta an kawota d'akin mutumin da take tsananin tsoro, mahaifinta kuwa tuni ya tattari dukiyar sa ya cika ma rigarsa iska...
Babu yanda Abbah Sa'oud baiyi ba Kabeer da matarsa su zauna a cikin gidan amma fir Innah tak'i yarda a cewarta yanda Kabeer yakeji da tashen balaga abin kunya za'atayi a cikin gidan gwara suje can gidansu daban basuji ba basu gani ba domin tanai masa kunyar d'an fari..
Haka babu tausayi a zuciyar Kabeer had'i da yarinta kullum yana aikin abu guda da k'aramar yarinya, tun tana masa kuka yana biyeta har ya soma saka mata hannu idan kukan nata ya ishesa. Innah kuwa a kullum tana koya masa yanda zai muzguna ma Saudat, Innah bata b'oye masa komai ba na nufinta wajen son d'aukar fansa ba akan Saudat..
A haka watan Saudat tara cif ta haifo yaronta namiji kyakkyawa mai kamanta, tun kafin jinin bik'i ya d'auke mata Kabeer ya kuma far mata, ala dole Innah ta d'auko mai kula ita Saudat d'in ganin Kabeer zai kasheta bata d'auki fansarta ba wajen azabtar da Saudat..
Da wannan Saudat ta sami sauk'in jarabar Kabeer, shiko tuni ya koma bin 'yanmatan sa da ya saba. Shekaran Fawaz uku a duniya Innah ta haifo d'iyarta mai kama da Naseer sak mahaifinsu suka biyo, saidai kawai Naseer ya nuna mata tsananin hasken fata.. Haka Lubna ta taso cikin soyayyan 'yan uwanta babu kaman Naseer yana son Fawaz da Lubna sosai, haka Alh Sa'oud soyayyan Fawaz da Lubna ya shiga zuciyarsa sosai...
A haka Innah ta tak'ura aka tura Naseer makarantar kwana lokacin da yakai munzanin aji hud'u a standard, shi kuma Kabeer a lokacin ya sami gurbin karatu a jami'ar Maiduguri hakan yasa Abbah Sa'oud yasa Saudat ta dawo gidan da zama...
A haka rayuwa taci gaba da tafiya, Innah bata yarda da ma'aikata kwanaki k'alilan suke ta sallamesu sabida bataso kowa ya shigo ratuwarta ya b'ata mata shirinta,..
Wani rana Abbah ya dawo daga sallan mangariba yaga abinda yayi tsananin girgiza sa ya tada masa hankali ya kuma basa tsoro, ba komai ya gani ba illa Dije dake k'ok'arin biyar buk'atar kanta da matan d'anta da k'arfin tsiya... Baisan sanda jikinsa ta d'auki rawa ba, murya na rawa ya daka mata wani irin tsawa yana mai ambato sunan ta...
A zabure ta mik'e daga kan Saudat dake faman kuka da duka zuciyarta..
Innah ta zuba gwiwoyi a k'asa tana rok'onsa yayi hak'uri sharrin shaid'an ne..
Abbah baisan sanda hawaye suka shiga kwaranya masa ba, wannan wani irin fitina ne ace mace na neman 'yar uwarta mace sannan k'arewan rashin tsoron Allah ki nemi matan d'anki da kika tsuguna kika haifa ..... Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un...
Kuka Innah take tana rik'e da k'afafunsa take fad'in "Ka min rai Sa'oud sharrin shaid'an ne..."
Cikin kuka shima ya fizge rigar sa yana fad'in "Da me na rage ki Dije da har kike neman d'iyar d'anki, shin dama wannan dalili ne yasa baki iya zama da ma'aikata, shin kinsan girman zunubin neman jinsi, wannan wacce irin fitina ce take faruwa A DUNIYAR MU....
Kuka Innah take tana rok'onsa gafara, Abbah bai fasa furta mata kalman saki ba, dai-dai lokacin da Kabeer ya shigo gidan domin basu san yana tafe ba...
Alh Sa'oud yaci gaba da fad'in "Nayi d'an da na sanin aurenki da nayi da kuma mallaka maki d'ana Naseer da nayi, kin cuce ni kin ci amanata, Allah shi zai min sakayya tsakani na dake..
Kabeer yayi jifa da jakkar sa ya shigo ya rik'e mahaifiyar sa yana jijjigata yake fad'in "Innah why? Meyasa kika fad'a masa gaskiya, meyasa kika sanar dashi burin mu akan shi, meyasa kika sanar dashi bak'in aikin da kukayi akan matarsa Hidaya... Shikenan yanzu Innah komai ya kwab'e mana bazamu mallaki dukiyar sa ba....."
Innah na kwab'arsa ya kasa shiru sai jijjigata yake don shi duk a zatonsa asirin Innar tasa ce ya tonu...
I zuwa lokacin Abbah ya soma rik'e k'irjinsa da jin irin miyagun ayyukan da Dije da mahaifiyarta sukayi, da k'yar ya soma tafiya yana rik'e da k'irjinsa har ya isa jikin table da wayan land-line ke bisa, d'auka yayi da k'yar zaiyi dialing lambar 'yansanda suko sai kacaniya suke... Ai Innah na hangosa a tamanin tayi kansa lokaci guda ta jawo irin k'anan table mahad'in center table da ake saka su tsakankanin kujeru ta rusa ma Abbah akansa, ya saki k'aran azaba ya soma shure-shure wanda hakan ya sanya Saudat fitowa a guje...
Ganin yana yunk'urin tashi yasa Kabeer jawo wani table d'in ya shiga sauk'e masa akai, tun yana k'ara had'i da salati har ya daina sai shiru kake ji.... Allah sarki Sa'oud Santana yace ga garinku Allah yayi masa cikawa a sanadin wad'annan azzalumai guda biyu...
Saudat ta Saki wani irin k'ara ta juya d'aki a guje jikinta na wani irin rawa tamkar mazari... Innah na huci tamkar zakanya tace da Kabeer "Bita kaci ubanta don na tabbata baka da sauran imani...."
A tamanin ya take mata baya ya shiga gana mata ukuban da bai tab'a gana mata irin sa ba.....
Naseer bai tashi sanin mahaifinsa ya rasu ba saida wasu ma'aikatan kampanin Baban sa suka tafi har makaranta suka masa ta'aziya. A ranar ya dawo gida yana kuka maimakon yaji kalaman lallashi daga bakin Innar sa sai bala'i data balbale shi dashi tana fad'in dawowar sa gida bazai sa Abban su ya dawo ba...
Tun daga wannan lokaci abubuwa suka kuma sauyawa, tsanar da Innah tayima Naseer ta kuma fitowa fili sosai,..
A b'angaren Innah bata fasa bibiyar Saudat ba don dama bin 'yan uwanta mata da take yasa mijinta na farko mahaifin Kabeer ya saketa, Saudat bata samu sauk'i da fitinar Innah ba har saida Fawaz da Lubna suka soma girma, Innah ta koma bin 'yan mata a waje... Sannan Kabeer ma ya rage gana mata azaba tunda Fawaz ya soma girma, saidai lokacin da Fawaz yakai mumzanin shiga jami'a ya bar k'asar a lokacin Kabeer da Innah suka d'aura linzamin gallaza ma Saudat tsoron kada ta sami kanta da yawa wataran ta fallasa su bak'in aikin da sukayi a shekarun baya....
*_Ci gaban labari_*
******************
*Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*07*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
An saka bikin Naseer da Shareefah nan da sati uku masu zuwa, shirye-shirye babu kama k'afan yaro a duka family guda biyun... List d'in events Shareefah ta masa paper guda, tun yana k'irgawa kama daga kan English night, Arabian night, barbeque, crossing of sword....... Kai k'arshe d'ago kai yayi yana dubanta ganin events d'in sunk'i k'arewa...
D'ago takardan yayi yana juya lokaci guda yana dubanta yake fad'in "Shareefah what's this?... This is ridiculous wad'annan events d'in sunyi yawa, look I want a simple wedding, wannan shirme ne ai da shiririta, mu da muke neman albarka a auren mu mai zaisa mu cika kayan shed'an haka...." ya d'an girgiza kai kana yaci gaba da fad'in "You perfectly well know me, kin sanni kin san ni wani irin mutum ne, so pls karma mu fara...."
Shareefah ta kuma tura baki gaba tana fitowa daga cikin kujeran tana kuma bank'aro k'irji waje take fad'in "Amma dai Naseer kasan fah nice d'iyar fari a gidan nan, kuma kasan Mamy tana son hidima sosai, haba Naseer a ido kanada wayewa sosai, sannan kamannin ka irin na western people don Allah kar ka ba dani....."
Had'e hannayensa yayi waje guda had'i da d'aura hab'arsa kan hannun nasa yana dubanta, shi wllhi ya zaci girma zai sa Shareefah tayi hankali amma da alama har yanzu batayi ba.. Jinjina kai yayi kafin ya soma fad'in "Kina jina, kamanni ne kawai nake dashi na western people sabida jininsu da nake dashi a tattare dani, amma d'abi'u na da Al'aduna sun banbanta da nasu, kuma banda abinki auren da babu hayaniya ciki yafi k'argo da albarka...."
Shareefah ta cika tayi fam, sai faman shure-shuren k'afafu take alamun taji haushi... Ko kulata bai kuma yi ba, sai shafa wayar salulansa da ya shiga yi...
Daga parlorn dasu Innah da Mamy da kuma wata k'awar Mamyn ke zaune Innah na hango su Naseer da Shareefah ta cikin k'ofar glass d'in da ya raba corridor d'in dake tsakankaninsu...
Lokaci guda Shareefah sukayi ido hud'u da Innah... Murmushi Innah ta sakar mata had'i da kashe mata ido guda..
Gaban Shareefah ya kuma yankewa ya fad'i, wannan matar ga dukkan alamu bata manta had'uwarsu a wancan karan ba, amma kuwa itama dole ta fito mata a asalin 'yar barikin ta ta haka ne kawai zasu wanye...
Murmushi Shareefah ma ta sakar mata had'i da kashe mata idanu guda..
Bayan su Innah sun tafi Hajiya Laure k'awar Mamy gyara zama tayi sosai tana duban Mamy kafin tace "Asma'u wai wannan mata mai suffan kafiran farin itace uwar Naseer d'in, chab toh ai ni na zaci Sa'oud Santanan mata biyu ke garesa, kinsan barikin wannan matar kuwa...?" ta k'arashe tana rik'e hab'a...
Murmushi Mamy tayi kafin tace "Haba Laure nifa da kika ganni nan banga barikancin da zai firgita ni ko ya bani tsoro ba muddin zan sami masu gidan rana, nasan Innah nasan imanin ta kud'i ne, shiyasa ko zan tsiyance sai Shareefah ta auri d'anta, don nima kud'in nake farauta a wajen su, kinsan da kud'i ake neman kud'i.....,
Hajiya Laure rik'e da hab'a tana duban k'awar tata tace "Oh kice sai kanadashi akeyi da kai A DUNIYAR MU..."
Dariya suka fashe dashi lokaci guda suna masu tafe hannaye.
****************
Tunda suka dawo daga Jama'are tunanin 'yar bafulatanar nan ya hana Affan sukuni, bashida burin da ya wuce ya kuma sanyata a idanun sa, ya tuna sanda ta fad'a cikin kashin shanu.. Shi kad'ai yayi murmushi yana tuno kalan kukanta abin burgewa, yeah babu k'arya he's feeling something for her, as a matter of fact baik'i su kasance kullum tare ba,..
A haka Naseer ya shigo office d'in ya samesa... Kallon mamaki ya bisa dashi ganin ya k'ura ma glass cup d'in hannunsa idanu shi kad'ai sai juyawa yake, Naseer ya murmusa kafin ya kai hannu ya amshi cup d'in yace "Hey you alright?"
D'an sauk'e ajiyan zuciya Affan yayi kafin yace "You know she's.... quite different, ka gane duk 'yan matan da nayi ta banbanta dasu, kai banma tab'a had'uwa da irinta ba, yeah quite alright da yawa daga cikinsu sun fita kyau but she's just different...."
Murmushi mai bayyan hak'wara Naseer keyi lokaci guda ya ajiye files d'in hannunsa bisa table yana mai bud'e files d'in yake fad'in "You so silly you know... Ka gane wad'annan sunayen recruits d'in ne, jibi za'a tafi dasu Kaduna baki d'aya cos......" Burki yayi da maganan nashi ganin har lokacin hankalin Affan bai tareda shi.. D'an girgiza kai yayi had'i da rufe file d'in ya zagayo ya zauna a mazaunin sa, teasingly ya soma fad'in "Ka dai san nace bazan baka k'anwata ba sai ka zama good boy, don't forget our deal soldier...."
Sai sannan Affan ya d'ago yana dubansa, lokaci guda Lubna ta fad'o zuciyar sa, shi wllhi harga Allah Ya mance da wata Lubna, Tirk'ashi... Murmushin yak'e lokaci guda ya mik'e yana gyara zanzaronsa had'i da sara ma Naseer d'in yake fad'in "I apologize Captain ayimin afuwa..."
Murmushi kawai Naseer yayi kafin ya tura masa file d'in gabansa yace " Gashi ka tafi da file d'in ka duba su one by one, ko wanne da room no d'insa k'asan sunansa..."
Sara masa Affan ya kuma kafin ya masa wani yarensu na soji da su kad'ai suke ganewa kafin ya fice...
***************
"Hello ina so mu had'u dake, had'uwa ta sirri...."
Murmushi Shareefah tayi kafin tace "Nasan za'a rina wai an saci zanin mai hauka, ... Kin kasa gane meyasa nak'i baki had'in kai wancan lokacin, duk rashin kunyata bazanyi hark'a dake ba a matsayin ki na mahaifiyar mutumin da nake shirin aure.... Idan kina so zan had'aki da 'yanmata sabbin jini amma nikam ki barni ma d'anki don Allah....."
Dariya Innah ta fashe dashi karan sigari a bakin ta kana taci gaba da fad'in "Kina tunanin zan bar d'ana ya aureki haka kawai ne alhali babu abinda zan samu, burin ko wacce uwa d'anta ya sami mace ta gari kinga kuwa haka kawai bazan so Naseer ya aureki ba alhali nasan ke d'in shed'aniya ce...."
Shareefah ta murmusa had'i da zama saman gado lokaci guda ta d'aura k'afafunta d'aya bisa d'aya tana mai ci gaba da fad'in "Innah kenan, amma fah duk yawon bariki na ban tab'a had'uwa da salamemmiya irinki ba, a shekarun kin nan kamata yayi ki tuba ki koma ga Allah, sannan ni da kike gani ranar da na auri Naseer na daina wannan bak'in sab'o...."
"Kina zuwa ne ko baki zuwa, kinsan inada makamin da zanyi amfani dashi lokaci guda na hana Naseer aurenki sabida ni mahaifiyar sa ce dole ya yarda dani ke kuwa kalma d'aya tak zan fad'i akanki na hanasa auren ki har abada..."
Shareefah ta kuma murmusawa kafin tace "Me yayi zafi shi ba wuta ba, idan dai Shareefah ce kar ki damu kin sameta an gama, turo location ki kuma bani minti talatin masu kyau..."
Tana jin sanda Innah ta kece da wata kafiran dariya kafin ta kashe wayar....
Zuciyar Innah tayi fari sol, ta tuna sanda suka had'u da Shareefah a Brazil taso nemanta Shareefah ta watsa mata k'asa a idanu, tabbas yanzu Shareefah bazata k'ita ba tunda tana son d'anta, sannan ba wai tsananin buk'atar Shareefah bane ya dameta, a'a so take tayi amfani da wannan daman su saban hark'ar tare sai bayan Shareefah ta auri Naseer sannan ta nuna ma Naseer b'aro-b'aro abinda take yi da matarsa tasan idan bai had'iyi zuciya ya mutu ba toh kuwa zai haukace.... Wani dariyan ta kuma fashewa dashi lokaci guda kafin ta soma fad'i a fili
"Naseer wannan sai yafi maka komai ciwo a duniya, mutuwan azaba zakayi, wannan shine babban burina na son ka auri Shareefah, wannan shine babban uk'uba mafi muni da na tanadar maka..."
************
Kallo Azeema ta rakata dashi tana murmushi k'asa-k'asa kafin tace "Ai ke baki iya ba, meyasa kika nuna mata baki so tun a farko..."
Shareefah ta sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin tace "Haba Azeema ya kike magana haka, wllhi k'yamar matar nan nake ke kinsan da ke kad'ai nake hark'an nan... Amma wannan tsohuwa sigari duk ya rinata ya k'arar da ita, ke wannan idan an dubata babu kalan cutan da baza'a sameta dasu ba...."
Azeema ta kuma murmusawa kafin tace "Idan na fahimce ki k'yamarta kike ji...."
Kan tayi shiru Shareefah ta shiga gyad'a kanta alamun eh...
Azeema ta matso kusa da ita sosai kafin ta sassauta murya tana fad'in "I have a solution, amma nima zaki biyani don inada buk'atan kud'in dama, akwai abubuwa da dama da zanyi dasu..."
Shareefah ta kalleta da mamaki kafin tace "Girl don't be silly bakiji nace maki tace bata son kowa sai ni ba, mai zaisa ki kai kanki gareta..?"
"Nasan abinda nakeyi, ke kam ki zo muje kawai ba dai kince asalin smoker bace.. Zo muje..."
Hannun Shareefah Azeema ta rik'o suka shiga lek'e-lek'en parlor don kar Mamy ta gansu tare ta hanasu fita... Ganin babu kowa a parlorn yasa su ficewa cikin sauri.....
*************
A bakin kwalta Azeema tayi parking kafin tayi dialing wata lamba....
"Ina cikin wata faran Vibe, kazo straight na ganka...." daga haka katse wayar tayi...
Shareefah dai sai kallon mamaki take bin Azeema dashi, waima yaushe tazo garin yaushe tasan mutane a garin har haka...
Jim kad'an wani matashi ya rufa hood akansa ya k'wank'wasa masu gilashin motar...
A hankali tayi rolling glass d'in ta mik'a masa kud'i ya mik'e mata wani k'ulli cikin faran takarda...
"Na gode sai ka kuma jina..." godiya saurayin ma yayi mata kafin ya shige yana jajjawo hood d'in yana rufe fuskar sa kana ganinsa kaga maras gaskiya.
Shareefah kasa hak'ura tayi, dukda tasan Azeema's smart amma wani sa'in tana tsoron kaidin Azeema...
"Shi wannan d'in waye, sannan meye wannan kika karb'a, Azeema nifa ba cewa nayi a kashe matar nan ba, kawai so nake ta daina damu na...."
Idanun Azeema naga kwalta sanda taci gaba da watsa gudu bisa kwalta d'in take fad'in "Shareefah kenan, idan mutum ya nuna maki shi d'an bariki ne toh ki nuna masa Kin fisa iyawa, idan ba haka ba zaki kwan ciki.... Kema just trust me...."
Shareefah bata kuma cewa komai ba sai duba masu sunayen streets da taci gaba da yi...
Adireshin gidan da Innah ta turo masu a can bayan gari ne, gidan shi d'aya a wajen babu mak'ota..
Mai gadi yana ganin su bai tambaya ba ya hangame k'ofa, don yasan duk randa Innah tazo gidan toh fah iri da kalan 'yan mata sunyita shige da fice kenan...
Shareefah ta kalli Azeema bayan sun gama parking tana jira taji me zasuyi next..
D'an muskutawa Azeema tayi ta ciro kwalin sigari cikin aljihun wadonta, pen d'in dake ajiye gaban motar ta d'auka had'i da zaro sigari guda d'aya cikin kwali.... Shareefah dai sai kallon ikon Allah take tana jira taga me Azeema zatayi da pen da sigari...
A hankali ta ringa tura pen d'in cikin karan sigarin tana rage dusan dake cikin sigarin saida ta kai kusan rabi kafin ta bud'e takardan da ta amsa wajen saurayin can, a hankali ta dinga zura garin cikin sigarin har ta gama...
Shareefah baki sake tace "Azeema meye wannan.."
"Ganyen wuwi....." Azeema ta bata amsa kai tsaye...
"Zamu kunna sigarin yanzu kiyi kaman kina sha, kina shiga bayan kin zauna kaman zaku soma hark'a sai ki mik'a mata shi cikin bakin ta, idan ta fita hayyacinta saikiyi alarting d'ina na shigo mu tattare ta... karfa ki kuskura ki sha just pretend....
Murmushi Shareefah tayi kafin ta gyad'a kai tace "A gaisheki Azeema lallai na yarda bariki iyawa ne....."
A haka ta fice ta nufi cikin gidan hannunta rik'e da karan sigari tamkar tana sha....
Zaune ta hangi Innah a katafaren parlorn d'an k'aramin plate wanda yake d'auke da guntu-guntun sigari had'i da ashes alamun tasha sigari ya kai kara uku...
Innah tana hango Shareefah ta mik'e tana kwarkwasa uwa blugari ta nufeta.. Itama Shareefar tuni ta kuma canza salon takun ta..
Tuni Shareefah ta soma aikin da abubuwan da Azeema ta fad'a mata tayi su, aiko kan aje ko ina ta had'a Innah da wannan karan sigari, nan Innah ta dinga zuk'a tana fesa hayak'i.... Ai kan aje ko ina Innah ta soma layi tana rawa tamkar an saka mata batir....
*Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*09*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
Kunnenta na gefen hagu manne da earpiece da alama waya take... Lokaci guda ta kuma sakin murmushi kafin tace "Kar ka damu kaikam ka gama naka part d'in, tunda na shigo makarantar ai samunta bazai min wuya ba... Zamuyi waya kaikam...." daga haka katse wayar tayi lokaci guda ta shiga bin 'yan mata dake shawagi a k'ofar hostel d'in wasu na kai komo yayinda wasu ke hira cikin motocin samarukan su wasu kuwa suna zazzaune saman kujeru na shak'atawa, kasancewar yamma ce an firfito daga lectures shiyasa k'ofar hostel d'in ya zamto busy sosai...
Wasu 'yan mata Azeema ta hango sun jero layi suna tafiya kusan su takwas a layi guda. Kana ganinsu basai ance maka freshers bane, aka kuwa yi sa'a ta gefen motar ta 'yan matan suka zo wucewa, d'an rage glass d'in motar tayi kafin ta d'an fito da kanta waje tace "Sannun ku 'yanmata..."
A tare suka juyo suna amsa mata jin muryar mace ce 'yar uwar su...
Nan Azeema take tambayar su ko sun san wata Faty KT... Ai 'yan matan nan har suna had'e baki wajen cewa "Shazumami zakice, tab ai duk makarantar nan babu wanda bai santa ba, yanzu ma muka fito lectures tareda ita tana carrying maths 111.."
Abin har yaso bawa Azeema dariya ganin tambaya d'aya ta masu amma sun shiga fad'in abinda ba'a tambaye su ba..
"Toh da Allah ko kunsan yanda zan sameta....?" Azeema ta kuma jefo masu wata tambaya...
D'aya daga cikin 'yan matan ne ta hangi Faty na k'arasowa cikin takunta na yanga sai ka rantse wata d'iyar shugaban k'asa ne nan ta bud'e murya tace
"'Yar halak tak'i ambato, gatan can tana tafe....."
Gaba d'aya suka juya suna duban Faty dake k'arasowa cikin takunta na yanga... Godiya Azeema ta masu kafin suka wuce suka nufi hostel..
Tun daga nesa Azeema ke k'arewa Faty kallo, sanye take cikin kimono ash color kanta ta d'aura navy blue headtie idanunta rufe cikin shades sai farin fatar ta kake hangowa, hannunta kuwa rik'e da 'yar k'aramar jaka red color k'irar vine haka nan k'afarta sanye da red wage shima k'irar vine.... Duk yanda 'yar gayu takai toh Faty ta kai...
Murmushi Azeema tayi sanda Faty ta k'araso dab jikin motar ta zata wuce..
"Faty KT manya-manya...." cewar Azeema cikin kashe murya.
Juyowa Faty tayi tana mai cire shades d'in idanunta, idan bata b'ata ji ba tabbas daga motar nan taji an kira sunanta...
Kallo tabi Azeema dashi yanda taga fuskar Azeema d'auke da murmushi.
Saida ta wani juya idanu kafin ta nuna kanta da shades d'inta dake rik'e a hannunta tace "Ni Fatin kuwa....? "
Azeema bata amsata ba sai fitowa da tayi daga motar, lokaci guda Faty ta samu ta k'are mata kallo.. Azeema doguwar mace ce wacce batada jiki sam, tanada fari irin mai kashe idanun nan sannan labb'anta bak'ak'e ne sosai tamkar ta mai shan sigari, idanunta manya ne sosai wanda su suka kusan cika fuskar tata, kallo guda Faty ta mata ta fahimci 'yar gayu ce sosai, sanye take cikin golden brown atampa d'inkin riga da skirt ya zauna sosai a jikinta sai d'an k'aramin vail data yane kanta dashi... Kallonta take tana nazarinta don ita sam bata huld'a da talaka lokaci guda muryar Azeema ya katse ta da fad'in "Baki gane ni ba koh... Sunana Azeema Ali Safwan..."
Saida Faty ta kuma dubanta lokaci guda fuskar ta ta cika da murmushi
"OMG! Ashe ke k'anwar Affan Ali kenan...Kece wacce Naseer Santana zai aura?..."
Murmushi Azeema tayi kafin tace "Eh ni k'anwar Affan ce amma sister ta itace zata auri Naseer....."
D'an k'arasowa Faty tayi lokaci guda ta d'anyi hugging Azeema kafin tace "Ashe ke d'in k'anwar mu ce... Pleased to meet you, mu k'arasa ciki mana..."
Babu musu Azeema ta take mata baya suka nufi d'akunan kwanan 'yan matan....
Room of two Faty suka kama tare da Lubna da shike Lubnar ba kwana take ba saidai d'an zama da take tsakanin lectures shiyasa d'akin ya koma tamkar na Faty ita kad'ai... Babu kalan kayan more rayuwa da babu a d'akin, yawancin abubuwan Faty Lubna ke mata su ko kuma samaruka don idan aka dawo hutun semester musamman Lubna take ware masu kud'i na canza set d'in akwatuna, dokar su ce basa maimaita kaya a semester guda...
******************
Jigum sukayi lokaci guda suna jero wa mahaifiyar tasu sannu.
Salma ta dubi Jamila kafin ta mik'e ta d'an jawo hannunta suka fice daga d'akin suka d'an keb'e...
Fuska cikeda damuwa Salma ke duban 'yar uwar tata kafin tace "Adda Jamila haka zamu zuba wa Innoh idanu tana jin jiki, wllhi daurewa kawai take don bata son saka mu cikin damuwa amma wllhi tana jin jiki kinsan Innoh da juriya ma ciwo...."
Jamila ta sauk'e ajiyan zuciya idanunta sun kad'a sunyi jazir ba komai ta tuna ba sai d'azu data tafi gidan Alh Nuhu ta sanar dashi halin da mahaifiyar su ke ciki na jinya, babu kalan rashin mutuncin da basu mata ba shi da matar sa, tak'i sanar da 'yan uwan nata ne don tasan a rashin hak'uri irin na Salma sai taje har gida tace tazo karb'awa 'yar uwarta 'yancin ta.... Saida Salma ta d'an tab'ata kafin ta dawo daga duniyar tunanin data tafi....
"Adda wai meke faruwa tun d'azu kike looking dull, haka d'azun Falaq tayita kuka baki kulata ba Allah yasa yarinyar ta saba sosai da Ilham, idan kuma akan ciwon Innoh ne hak'uri zamuyi mu mata addu'a , tada hankali da damuwa won't solve anything ..."
Sauk'e ajiyan zuciya Jamila tayi kafin tace " Salma shin haka mutane suka koma A DUNIYAR MU, mai kud'i babu ruwansa da talaka, wanda keda halin taimako bazai taimaka ma wanda ke cikin buk'atar taimako ba, mutane kowa ya koma kansa kawai ya sani, shin wane irin rayuwa muka tsinci kanmu ciki A DUNIYAR MU?"
shiru Salma tayi tana sauraren 'yar uwar tata kafin a hankali ta rik'o hannayenta murya na rawa take fad'in "Adda wannan shine halin da muka tsinci kanmu ciki A DUNIYAR MU amma Allah masanin komai baya bacci da sannu zai yassare mana damuwar mu, yanzu musan yanda zamuyi convincing Innoh ta yarda akaita asibiti idan yaso daga baya sai mu nemo kud'ad'en da za'a buk'ata a asibitin..."
Jinjina kai Jamila tayi kafin tace "Allah sa ta amince da zuwa asibitin...." Salma ta amsa da ameen kafin suka nufi cikin gidan yanda Ilham ke zaune gefen katifar Innoh Falaq na bisa cinyarta...
Kallon juna Salma da Jamila sukayi kafin Salma ta d'an mata rad'a a kunne, nan Jamila ta shiga gyad'a kanta kafin ta k'arasa ta d'auki Falaq ta kamo hannun Ilham tana fad'in "Muje lil Sis.."
Babu musu Ilham ta mik'e tabi bayan 'yar uwarta....
Suna barin wajen Salma ta zauna daf da Innoh ta rik'o hannayen ta cikin nata kana ta soma fad'in
"Innoh don Allah ki yarda muje asibitin nan, Innoh don Kin k'ware wajen had'a magungunan gargajiya hakan ba yana nufin bazaki je asibiti ba kenan, Innoh wani ciwon sai likita ya duba ba'a magancesa da ka, kinga bamu so Ilham ta fahimci bakida lafiya...." Salma ta k'arashe maganar kaman zatayi kuka...
Murmushi Innoh tayi kafin ta kuma damk'e hannun Salma ta soma fad'in "Salma d'iyata meyasa kuke b'oyewa 'yar uwarku jinyata, ku sani b'oye mata bazai sa na sami lafiya ba sannan ni nasan abinda nake ji a jikina shiyasa kuka ga banje asibitin ba, ku sanar da 'yar uwarku ko zan sami add'uar ta.... Maza tashi ki kiramin 'yan uwan naki...."
Jiki a sanyaye Salma ta mik'e ta nufi kiran 'yan uwanta....
***************
Mik'ewa Azeema tayi tana gyara Vail d'inta kafin ta kuma duban Faty wacce ta koma tamkar ruwa ya shanye, dafata ta d'anyi kana tace "Relax girl ba d'abi'ata bace cutar da mutane amma banida option ne, ni a ganina taimakon ki zanyi ki saya mutunci ma kanki domin kuwa duk ranar da Lubna ta kafa maki gori zaman ATBU sai ya gagareki, think about it, ace kaman ke ki zauna k'awa tanai maki d'inki tana baki kud'i a account kin zama sidecake bakida say sai abinda tace, tana baki ride a cikin sch wanda har sunanki ya koma shazumami, kinada kyau kinada zubin yaran manya bai kamata ace kin ajiye kanki a wannan matsayin ba, kece ya kamata ki karb'i award d'in face of ATBU sabida kinfita kyau amma anje ana bawa Lubna sabida kud'i da family d'insu kedashi, samari masu kudi da kyau Lubna suke rububi bake ba alhali ba kyau tafiki dashi ba.... Amma koda shike idan kinyi tunani zaki iya nema ta...." daga haka ta nufi k'ofa tana murmushi
Kallo Faty ta rakata dashi har ta fice tana mai tunanin maganganun da Azeemar ta fad'a mata wanda gaba d'aya babu k'arya ko d'aya a ciki....
***************
Gaba d'aya Innoh ta rik'e hannayen su tana mai ci gaba da fad'in "Ko bayan bana nan ku rik'e mutuncin ku, kunga dukanku mata ne mutunci shine babban daraja da mahaliccinku ya maku hijabi dashi, ya lullub'eku dashi kar ku bari koda wasa wani mahaluk'i ya yaye maku wannan sutura da mahaliccin ku yayi maku, ku sani cewa mutunci da sanin darajan kai da kima da Allah yayi wa d'iya Mace yayi k'aranci A DUNIYAR MU wanda hakan ya haifar da fitintunu da dama wanda muka kasa magance sa A DUNIYAR MU, na k'asa baya tausayin na sama, k'arami baya ganin girman babba, sannan shi babba baya tausasa wa k'arami, mun b'ata rayuwar mu da kawunan mu munyi watsi da karantarwa na addinin mu, mun d'auko d'abi'a da koyarwa ta nasara mun ara mun yafa, toh ku sani kar ku kuskura kuyi watsi da darajar da Allah yayi maku A DUNIYAR KU koda bani a raye, bance babu na k'warai A DUNIYAR MU ba, a'a akwai su suna nan A DUNIYAR MU saidai sunyi k'aranci, toh kuyi k'ok'ari ku kasance daga cikin kad'an d'in, Allah yayi maku albarka ya albarkaci rayuwarku ya sanya maku tsoronsa gaskiya da rik'on amana a duk yanda kuka tsinci kanku A DUNIYAR MU....
Basu iya amsata ba sabida hawaye da ya wanke fuskokin su, gani suke tamkar mahaifiyar tasu nasihan ban kwana take masu..... Jamila ce tayi yunk'urin yin magana sai kuma ta kasa... Innoh tasa hannu tana share mata hawayen kafin tace "Ki rik'e hannu na....."
Cikin sauri Jamila ta damk'e hannun Innoh.....
Innoh ta girgiza kai tana mai murmusawa kafin tace "Ba irin wannan rik'on nake nufi ba, ki rik'e k'annen ki da d'iyarki da amana, ki zamto masu garkuwa A DUNIYAR SU, Uban giji yayi mana jagora gaba d'aya......"
I zuwa lokacin kukan nasu ya tsanan ta, harta Falaq wacce batasan me akeyi ba kukan itama take yi, gaba d'aya suka rufu kan mahaifiyar su suna kuka mai ban tausayi.....
******************
Yau ta kama sauran sati guda cif a d'aura auren Naseer da Shareefah, fitowar sa kenan daga mota yaga kira na shigo masa da layin k'asar waje, shakka babu yasan mai kiran bazai wuce d'ansa Fawaz ba, murmushi ya d'anyi kafin ya d'aga wayar da sallama..
Daga d'aya b'angaren a shagwab'e Fawaz ya soma masa magana
"Haba Uncle, haba Uncle saidai kawai na gani Affan yana posting, haba Uncle ka daina sona har haka ne.....?"
Naseer ya d'an shafi sumarsa yana murmushi kafin yace "Dr ayimin afuwa, kasan Uncle d'in naka always committed, dama nafi so sai abin ya matso sosai na kira ka, amma dai kayi hak'uri Uncle yayi laifi.."
Fawaz ya murmusa kafin yace "Na maka uziri, amma dai naso ace sai na dawo ayi bikin tunda watanni ne kawai suka rage min na dawo, wa ya sani ma ko idan na dawo a had'a da nawa....." ya k'arashe cikin rage sauti teasingly
Naseer ya kuma murmusawa kafin yace "You never changed Fawaz, ka maidani Kakan ka koh, zaka sani ne....."
Fawaz d'in ma d'an dariya yayi kana yace "Coz you're my fav..... Ehen Uncle dama inata son tambayan ka jikin Momy Daddy Ya kirani ya sanar dani batada lafia, toh nayi nayi ya sanar dani ciwon nata yak'i fad'a min yace baiso hankali na ya tashi, yafi so na nutsu nayi karatu sosai a final semester d'ina, so da na gwada masa na damu sosai sai Innah ma ta kirani ta sanar dani is not that serious na nutsu nayi karatuna, but I'm still worried, pls inaso if possible ka had'ani nayi waya da ita....."
Naseer ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya yana tunanin yaushene Aunty Saudat batada lafiya, don shi bai sani ba, bai nuna ma Fawaz bai sani ba sai k'ok'arin kwantar masa da hankali da shima yayi kafin ya nufi cikin gidan jikinsa a sanyaye da alk'awarin zaiyi k'ok'ari ya had'a Fawaz d'in da mahaifiyar sa a waya...
Cak ya tsaya a k'ofar parlorn yana sauraren su
Dr Basheer yaci gaba da fad'in "Wato a gaskiya Alh matarka already ta sami cutar _Amnesia_ ma'ana loss of memory, a condition d'inta ba komai zata iya tunawa ba, saidai lokaci zuwa lokaci ciwon zai dinga motsa mata tamkar ta mai hauka, a halin yanzu shirunta zaifi maganar ta yawa,... Amma kar ka damu insha Allah zamuyi iya k'ok'arinmu wajen ganin tunaninta ya dawo......."
Baikai aya ba Innah ta katse sa da fad'in "Toh uban 'yan shisshigi ai ba cewa mukayi ka mata magani ba so muke mu tabbatar ko tanada sauran hankali......."
Daidai lokacin Naseer ya shigo idanunsa jazir, kallo yake kan faman binsu dashi d'aya bayan d'aya kafin ya sauk'e idanunsa kan Aunty Saudat wacce take zaune jigum saman kujera kanta ya karkace gefe guda tamkar wacce ta shekara ashirin tana jinya, a haka har ya k'arasa gabanta ya durk'usa yana mai son tabbatar ma kansa da gaske Amnesia ne ya kamata, a hankali yake fad'in "Aunty pls talk to me, ni ne Naseer....."
Kallon sa kawai Aunty Saudat take ba tareda ta iya furta koda kalma guda ba, Alh Kabeer da tuni ya k'wak'ulo hawayen k'arya k'arasawa yayi ya kamo Naseer yana fad'in "Brother I can't believe my wife's suffering from amnesia, Naseer bana so matata ta mance da ni......." ya k'arashe cikin shesshek'ar kuka....
Kallo kawai Naseer ke binsa da shi zuciyar sa tak'i aminta da kukan da d'an uwan nasa keyi.... Duban Innah yayi kafin ya k'arasa gabanta idanunsa jazir ya soma fad'in "Meyasa bakiso ayi mata magani, meyasa kike son cutar da ita, na kasance mai biyayya a gareki amma kiyi hak'uri wannan karan bazan maki biyayya wajen cutar da rai ba, wllhi tallhi zan bada gudumawa ta tan hanyoyi daban-daban har sai naga Aunty Saudat ta sami lafiya....." Baikai aya ba Kabeer ya rungumesa yana fad'in "Naseer nima bansan meyasa Innah tayi wancan maganar ba amma nima nayi alk'awarin rashin kyautatawa bazai kuma shiga tsakanina da matata ba...." Ya k'arashe yana watsa ma Innah wani irin mugun kallo... Innah kuwa ko a jikinta ko kunya babu ta bud'e murya tana fad'in "Lallai 'ya'ya sun zama marassa biyayya ga mahaifansu A DUNIYAR MU, Naseer har ni kake kalla cikin ido kana min rashin kunya son ranka akan waccar matar, matar da bakasan kalan rashin kunyar da cin zarafin da ta min ba a lokacin bakada wayo......"
Cikin sauri Naseer ya katseta da fad'in "Wai meyasa bamu hak'uri bamu yafiya A DUNIYAR MU, meyasa burin d'aukan fansa ya cika zuciyoyin mu,...." ya d'an sassauta murya kafin ya k'araso gaban Innah sosai yana mai k'ank'an da kai yake fad'in "Innah ko me ta maki na tabbata yarinta ce a wancan lokacin sannan da zakiyi hak'uri da shi yafi alkhairi, Innah Aunty Saudat d'iyarki ce, Innah wannan d'aya ne daga cikin dalilai na na tsoron aure, Yaya yayi repenting gameda abubuwan da ya aikata a baya tunda gashi har likita ya d'auko sabida Aunty Saudat wanda a baya ban tab'a ganin hakan ba, Innah don Allah kema ki tausasa wa matar nan, ki janye bak'in k'ullin da kike dashi akan......." baikai aya ba Innah ta daka masa wani irin tsawa kafin ta shiga nuna masa k'ofa tana fad'in "Fice min a parlor shahararre maras kunya, wanda baisan daraja da kima ta mahaifiyar sa ba, fita nace...."
Zuciyar sa na masa wani irin zogi ya nufi k'ofa sai huci yake, a tamanin Alh Kabeer ya take masa baya....
*Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU*馃寲馃寲
*10*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
*Meela Adeel and Meena Parrot Sameena na maku fatan alkhairi 馃挄馃馃徏*
"Wai meke damunki ne, ban saba ganin haka daga gareki ba, are you sure you alright...?" ta k'arashe tana mai k'urawa Faty idanu
Saurin saita kanta tayi had'i da yin murmushin yak'e kafin tace "Babe babu komai fah, kawai banjin dad'i ne kinsan jiki da jini...."
Lubna ta d'an tab'e baki had'i da jinjina kai kafin tace "Kin tabbata ba sai munga Doctor ba...?"
Faty ta jinjina kai kafin tace "Kar ki damu I'll be fine, ba wani ciwo mai tsanani nake ji ba..."
Lubna ta jinjina kai had'i da d'an tab'e baki kafin tace "Okay I'll go ahead, Allah k'ara sauk'i sauk'i zan kiraki when I reached home..." suka d'anyi hugging juna kafin Lubna ta fito ta tadda Deeni zaune cikin mota yana jiranta...
K'wank'wasa masa glass tayi cikin yauk'in da ta saba tace dashi ya fito ya bud'e mata marfin mota...
Kallo ya bita dashi shek'ek'e kafin yace "Amma ke babu manya a gidanku koh.....?"
Harara ta kuma watsa masa kafin tayi murmushi tace "Okay bazaka bud'e ba kenan, a sallami Mama Tani ka zab'a kenan... Kasan....."
Kafin ta kai aya ya fito a fusace ya bud'e yana fad'in "Dalla shiga muje maras kunya kawai wacce bata sami tarbiya a gidansu ba...."
"Ni kake fad'ama irin wannan kalaman...."
"So, ke wacece... An gaya maki d'in, idan bazaki shiga ba kuma kinji na rantse maki tafiya zanyi na barki...."
Baki sake Lubna ke kallonsa sa shaye da mamaki
"Kai anya ba shaye-shaye kake ba kuwa...?" ta tambayesa tana mai rik'e kunkumi
Gyara tsayuwan sa yayi had'i da karkacewa kafin yace "Toh ai dad'in abin ba ni kad'ai nake shaye-shayen ba, kuma da sauk'i idan ya tsaya akaina baikai ga iyaye na ba...."
Cikin rashin gane ina ya dosa Lubna ke kallon sa, k'wafa tayi tasa kai zatayi tafiyarta don har ta wuce motar....
Cikin sauri ya tako ya sha gabanta fuska a tamke yace "You shouldn't have annoyed me, kuma kinsan dai bazan baki hak'uri ba cos I did nothing wrong...."
Kallo take kan faman binsa dashi yanda yake mata maganar lokaci guda ya sassauta murya... Haka kurum taji jikinta yayi sanyi bata kuma cewa komai ba ta juya ta shige mota...
Saida ya rakata da harara kafin ya take mata baya...
Bayan yayi settling cikin motar ya d'an juyo ya dubeta kafin yace "Destination...?"
Fuska a murtuk'e tace dashi "Air Force base..."
Saida yayi tsaki a hankali kafin A fili yace "A dai rage zuwa wajen namiji kar a kwashi wulak'anci...."
"Inaga dai ka mance tsallen kwad'on da kayi ne halan...?" ta fad'i idanunta naga bisa screen d'in wayarta...
Bai kuma kulata ba sai gudu da ya dinga falfalawa dasu tamkar masu barin gari...
************
Zullumi Faty ta dinga yi tana tunanin lamarin, kaman wacce aka zabura haka ta mik'e ta d'au wayar salulanta tana mai zagaye d'akin ta shiga dialing lambar Azeema...
Murmushi Azeema tayi sanda taga kiran Faty na shigo mata, saida ta silale ta fice can ta baya kafin ta shiga amsa wayar
"Hello finally kin amince kenan..." cewar Azeema lokaci guda tana mai sakin murmushi
D'an jim Faty tayi kana ta soma fad'in "Yeah na amince zan maki aikin amma ki min alk'awari guy d'in bazai lalata rayuwar Lubna ba...."
Murmushi Azeema tayi kafin tace "Kar ki damu nasan abinda nake, I just want to frame her up that's all, Kelly ba abinda zai mata beside ba nufi na bane a lalata rayuwar k'awarki, kawai so nake Affan ya zamto nawa ni kad'ai just me and only me, kin fahimta..."
Gyad'a kai Faty tayi tamkar Azeema na kallonta kafin tace " Yaushe ne aikin?"
Jinjina kai Azeema tayi tana mai fad'in "Perfect, sannan taci gaba "Gobe za'a soma shagulgulan bikin Shareefah da Naseer sai muyi amfani da wannan damar...."
"Shikenan zansan yanda za'ayi na hana Baby driver d'inta binmu, idan yaso saiki min texting location..."
Azeema tayi murmushin jin dad'i kafin suka k'arasa arranging yanda zasuyi daga bisani sukayi sallama da juna da alk'awarin tun yau Faty zata soma jin alert....
***************
"Look Lubna ba wai pushing d'inki nake ba, just try to understand zuwanki nan distraction yake kawo min, and you're fully aware of yanda aikina yake tunda irin aikin yayanki kenan, nasan sabida bamuda nisa da school d'inku shiyasa bakijin wahalan zuwa ko?" ya k'arashe yana bud'e 'yan manyan idanunsa
Tab'e baki Lubna tayi kafin tace "Amma ai garin masoyi baya nisa as they say..."
K'ak'aro murmushi Affan yayi had'i da duba agogon hannunsa kafin yace "Tashi na maki rakiya nima yau zan tafi gida insha Allah zuwa anjima..."
Bai jira amsarta ba ya mik'e ya soma tafiya cikin sassarfa irin tasu ta soji.... A dole tabi bayansa cikin sauri..
Haka tayita narka masa shagwab'a yana biyeta na dole sanda suka iso jikin motar, Deeni kuwa don takaici kaman ya b'ace a wajen haka yaji, yak'i jinin mace mai kai kanta wajen saurayi dad'i da k'ari yanda Lubna da Affan sam basu d'auki tab'a jikin juna da suke ba laifi bane..
*************
Yau jikin Innoh da d'an sauk'i don har sun d'an sami bacci sab'anin kwanaki biyun nan..... Ilham ce ta soma tari sosai jin wani irin hayak'i ya turnuk'eta....
Kan kace me Salma ma ta soma tarin ta tashi a firgice bakinta d'auke da salati nan ta hangi Ilham ma ta mik'e sai lalume da hannayen ta take tana kirawo sunayen su... Saurin duban Innoh dake kwance gefenta tayi wacce ta koma tamkar bata numfashi kafin ta shiga jijjigata tana ambato sunanta,.. Jamila da Falaq dake d'aya d'akin a rikice suka fito waje ganin wuta ya rufe ko ina bata iya ganin komai ya sanyata sakin wani irin k'ara tana k'ank'ame da d'iyarta...
A rikice Salma ta fito jiyo sautin Jamila da tayi, Ilham kuwa sai lalume take da hannayen ta tana kirawo sunan mahaifiyar su.....
Salma ma kusan mutuwan tsaye tayi ganin wuta naci falfal, gashi gidan gonar ba'a gari yake ba balle mak'ota su kawo masu d'auki....
Salma ta dafa Jamila cikin rud'ewa take fad'in "Adda ki shiga kiyi k'ok'ari ki fito da Ilham da Inno kar gini ya afka masu ni kuma barin dubo su Malam Bala (Masu tsaron gate)...
Jinjina kai kurum Jamila take tana rungume da d'iyarta kafin Salma ta d'iba a guje ta nufi hanyar fita dukda wutan dake kuma ci fal-fal
Inno da k'yar ta bud'e idanu tana tari, Ilham na rungume da ita tana hawaye take tambayar su ko meke faruwa, don banda hayak'i da zafi da kuma k'aran k'onewar kayyayaki.... Ganin silin ya soma ci sosai yasa Jamila aza d'iyarta a baya, ta tallafo Innoh lokaci guda ta rik'o hannun Ilham suka soma tafiya.....
K'afafun Salma suka shiga rawa ganin gawar Malam Bala a k'asa jini na bin wuyar sa, jikinta na rawa tana ja da baya ta hangi wasu mutane sai kuma cinna wutar suke shanaye suna kuka abin tausayi, ga Baffah Mudi suna dukansa tamkar aiko su akayi.... Garin ja da baya ta buge wata bokatin bawa shanaye ruwa ai kuwa idanun azzaluman mutanen nan sai akanta..... D'aya daga cikinsu yace "Ku bita ku kasheta...."
Wane irin gudu Salma keyi wanda ita kanta batasan ta iya ba, haka ta dinga haye wuta tana gudu ta nufi 'yan uwanta...
Sanda ta cimma su Jamila jikinta har lokacin bai daina rawa ba, Jamila na tambayarta su Malam Bala ko amsa bata iya bata ba sai rungumo Inno da tayi tana fad'in "Adda mu gudu kar kashe mu, zasu kashe mu muma...."
Ilham fad'i take "Salma wai meke faruwa ne, su waye zasu kashe mu...." Salma bata sami zarafin amsa mata ba take fad'in "Muje Adda, ki rik'o Ilham mu gudu...." Nan suka hangi motar mutanen nan na zuwa, dabara ta fad'o wa Salma tuni ta jasu suka apka cikin wani rami suka b'oye... Haka Jamila ta sanya hannunta da k'arfin gaske ta danne bakin Falaq sabida kukan data soma yi, tana mai cikeda tausayin yarinyar.....
Malam Zubairu ne ya tsira da k'yar ya shiga gari neman d'auki nan ya sami waya ya shiga kiran layin Alh Ali....
Daddy da Mamy da kuma Affan suna zaune a parlor suna hiran yanda shagulgulan biki zai kasance yayinda Shareefah ke side d'in Mamy ana mata gyaran jiki kwatsam wayar Daddy ta soma ringing wanda ya haifar masu da fad'uwar gaba ba tareda sun san dalili ba...
Affan ne ya tashi ya d'au wayar daga saman center table Ya mik'a ma Daddy, Mamy tana fad'in "Waye zai dameka da daren nan yanzu haka ma bazai wuce 'yan neman taimako ba......." Muryarta ne ya carke sanda taji Daddy na salati cikin tsananin tashin hankali...
Malam Zubairu ya sanar dashi komai yanda akayi attacking d'insu...
Daga Mamyn har Affan k'uri sukayi ma Daddy suna sauraren ba'asi.. Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un kurum Alh Ali Safwan ke nanatawa...
"Daddy lafiya, waye ya mutu...?" Affan ya tambaya cikin tashin hankali...
Muryar Daddy na rawa yake fad'in "Affan sun k'ona gidan gonata sun yayyanka mutanen dake ciki...."
K'irjin Mamy ya yanke yayi wani irin bugawa, da k'arfin gaske ta soma fad'in "Shikenan, sun talauta mu ni Asma'u, shiyasa nace ka saida wannan gidan gona tuntuni ga 'yan fashi sun talauta mu, wayyo na shiga uku......" Mamaki ne ya lullub'e Alh Ali jin damuwar Mamy ba rayukan mutanen dake ciki da akayi asara bane wanda ciki harda d'an uwansa, dukiyan da suka rasa ne damuwar ta....
Basu ankara ba sai ganin Affan sukayi ya mik'e tamkar zautacce yana fad'in "Wllhi basu kashe Salma ba, ni na sani zan tafi yanzu na d'auko su...." A guje ya haye upstairs ya rarumo car keys kaman zai kifa k'asa...
Mamy kallabi a hannu tasha gabansa tana fad'in "Ina zakaje su kar ka...."
Ko saurarenta beyi ba yace "Mamy wllhi Jama'are zan tafi a daren nan....."
Salati Mamy ta soma yi tana tafe hannaye take fad'in "Haba shikenan ni nasan tunda Daddy ya d'auke ka ya kaika garin mayun nan sun saka maka a damun fura ka sha .... Aiko baka isa ba, bazanyi rashi biyu ba na rasa dukiya na rasaka ba ehe..." A guje ta bisa a baya, tamkar a film haka Daddy yabi bayan Mamy da kallo yana mamakin yanda rayuwa ta koma A DUNIYAR MU... Jikinsa har na rawa sanda ya shiga dialing layin jami'an tsaro.....
Mamy na rik'e marfin mota Affan yana ja, sai faman gyara d'aurin zani take tana fad'in "Wllhi Affan idan kaga ka fita a gidan nan sunana ba Asma'u ba,...."
Hayaniyar su ya sanya Shareefah da Azeema lek'o window a tamanin
*Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
[25/07 15:49] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*08*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
*Fatan alheri ga duk makarancin A DUNIYAR MU 馃馃徏*
"Ke kinji sunbatu take...." cewar Shareefah da tayi tsaye tana duban Azeema dake zaune saman coffee chair daga bayan parlorn...
Azeema ta murmusa kafin tace "Kuma sunbatun babu kan gado kaman neman fansa take akan Naseer...."
"Shine ai nima abin ya dame ni, kaman da gayya take so Naseer ya aureni, amma babu yanda za'ayi tayi ma d'anta haka, kawai dai inaga don a buge take shiyasa take sunbatu marassa kan gado...." Shareefah ta fad'i k'asa-k'asa tana mai kuma duban Innah da gaba d'aya batasan yanda hankalinta yake ba..
Azeema ta murmusa kafin tace "Koma menene matar nan akwai abinda take b'oyema Naseer bata so ya sani, and is like she's planning a revenge on him, idan kinada wayo Shareefah dama ta same ki, kiyi amfani da wannan damar kiyi threatening d'inta muddin tayi yunk'urin kawo maki cikas a auren da kike shirin yi da d'anta....."
Shareefah ta tsare Azeema da idanu kana ta kuma matsowa daf da ita murya can k'asa tace "Me zamuyi...?"
Azeema na wasa da bakin gashinta lokaci guda tana murmushi tace "Bani wayarki..."
Babu musu Shareefa ta mik'a mata..
Sam Shareefah batayi mamakin videon Innah da Azeema ta soma d'auka ba, ita kad'ai sai murmushi take, lallai a gaida Azeema...
Saida suka gama d'aukan Innah tas har ta zube a k'asa bacci yayi gaba da ita kafin suka tattare ta suka nufi motar ta da ita..
Shareefah ke driving motar Innah yayinda Azeema ke biye dasu a baya...
Azeema ta kalli mai gadin tana murmushi kafin tace "Za'a kai motar Hajiya car wash tayi bacci tana son hutawa tace kar ka bar kowa ya shigo...."
Cikeda ladabi mai gadin ya amsa mata yana kuma hangame gate
Saida suka tabbata sun bar layin kafin suka tsaya suka nemi dutse suka runtuma a glass d'in motar ta gefen driver...
Kallon juna sukayi lokaci guda suka kece da kafiran dariya...
***************
Cikin tsananin tashin hankali tamkar gaskiya tayi dialing lambar Naseer, yana tsaka da meeting yaga kiranta, sau wajen uku yana ignoring can dai da yaga kiran ba na k'arau ba yayi excusing kansa ya fice..
Ko sallama bai samu zarafin yi ba sai jiyo muryarta yayi cikin tsananin tashin hankali tana fad'in "Hello My soldier, Innah ce...."
Baisan sanda ya zabura yana fad'in "Shareefah, Innah kuma... Me ya sameta, meke faruwa..?"
"My Soldier you just couldn't believe it, wllhi fashi aka mata a cikin gari, Naseer meyasa kuke barinta take driving da kanta, ta riga ta tsufa gashi babu wani security a tattare da ita, kunsan dole a saka mata ido musamman idan akasan cewa she's Santana's....."
Shafa kansa yayi yana laranto salati kafin yace "But how's she... Is she okay...?"
"Eh toh da sauk'in za'a ce kenan tunda basu ji mata ciwo ba, kawai tayi collapsing ne kasan abinka da masu age...Gamu nan dai a hanyar gidan naku...."
"Are you sure ba sai anje asibiti ba.... Okay okay ganin nan zuwa right away...."
Shareefah tana katse wayar ta kuma fashewa da wata kafiran dariya ta kai dubanta ga Innah dake bacci a seat d'in baya kaman an tak'ure d'an taure...
Tuni Naseer yayi waya ya sanar da Yayan sa Kabeer kafin ya k'araso daga can base d'in su...
***************
Kallon Innah kawai Alh Kabeer yake yana aunata da idanu, domin shi tunda ya sungumota daga mota yaji warin wiwi a jikinta... Buhun uba ai baisan Innah har manya-manya take hurawa ba, ya zaci hayak'in nata a sigari kawai ya tsaya ashe har manya tana hurawa... Kad'a kai yayi had'i da yin k'wafa shi kad'ai lokaci guda yakai dubansa gasu Shareefah da suka kame saman kujera... Shi gaba d'aya bai yarda da yaran ba ma... Aiko sai kallon kallo suke jefa ma juna...
Lubna ce ta shigo a rikice ta nufi mahaifiyar ta dake kwance saman kujera, don tuni yayanta Kabeer ya sanar da ita...
Azeema ta shiga binta da ido ganin yanayin yarinyar tana wani irin murmushi k'asa-k'asa, a zuciyar ta take ayyana tabbas raba Affan da Lubna sam bazai mata wuya ba....
Aiko Lubna tana hayewa jikin Innah... Innah ta mik'e a firgice tamkar wacce aka saka mata bomb... Gaba d'aya saida suka zabura hakan yayi dai-dai da shigowan Naseer likita na biye dashi...
Muzurai kawai Innah take tana mai tuno abubuwan da suka faru, lokaci guda idanunta suka sauk'a kan Shareefah dake faman sakat mata murmushi..
Mamaki ya cika Innah ganin jama'an gidan gaba d'aya sunyi caa akanta....
Naseer ya k'araso yana mata sannu kafin ya mumarci Dr d'in da ya k'araso...
Aiko Dr na yiwowa kanta ta kuma mik'ewa tana muzurai take fad'in "Meye haka, waye kai, uwar me zaka min...?"
Naseer ya dubi su Shareefah kafin yace su d'an koma d'aya parlorn... Fuska fal fari'a suka kuwa mik'e zuwa d'aya parlorn...
"Innah pls ki bari a dubaki, dukda 'yan fashin basu maki komai ba amma ki bari Dr ya duba ki, kinga kinyi collapsing and bamu san meye yayi causing ba...."
Baki hangame Innah ke dubansu.... "Yan fashi.." ta nanata a zuciyar ta.... Lallai Shareefah shed'aniya ce, amma ko tunda wasan take so yanzu za'a fara....
Duban Naseer tayi fuska a murtuke kafin tace "Kai bana son iskanci da shashashan ci, babu abinda ya sameni kuma ai 'yan fashin basu min komai ba, shegen kinibibi da iyayi ka wani kwaso likita saikace jinya nace maka inayi....."
Bata kai aya ba Lubna ta katseta da fad'in "Haba Innah, Ya Naseer fah gaskiya yake fad'i ke kullum sai kiyita masa masifa......"
Alh Kabeer ne ya mik'e da sauri ya rik'o kafad'un Naseer da yayi tsaye kaman wanda ruwa ya shanye suka d'an nufi wata corridor yana masa kalamai masu taushi..
D'an girgiza kai yayi kafin yace "Babu komai Yaya ina yima Innah uziri sabida shekaru da suka soma kama ta, although nasani tun tasowata bata sona kaman yanda take sonku kaida Lubna, amma nasan deep inside tana sona, babu yanda za'ayi uwa tak'i d'anta, kawai dai kalar nawa jarabawan kenan A DUNIYAR MU and insha Allah zanci gaba da yin hak'uri har na rabu lafia da ita don shine ribar rayuwa...."
K'uri Yayan nasa yayi masa yana mamakin har yanzu ana samun 'ya'ya masu tsan-tsan biyayya ma iyayensu A DUNIYAR SU...
Bayan sun fice Azeema da Shareefah suka shigo suna gaida Innah.. Kallo kawai take binsu dashi tana ganin kalan nasu barikin.
Lubna kam ko ta kansu bata bi ba tayi saurin bin bayan yayunta don a Duniyar ta ta tsani ganin ran yayan ta Naseer a b'ace...
"Yaya kika ga wasan ta bugu koh...?" cewar Shareefah sanda ta matso daf da Innah..
Murmushin yak'e Innah tayi tana watsa mata mugun kallo kafin tace "Kinyi nasara a wannan amma ki sani wasa na gama 'yar tsohuwa zata lillisa ki da k'asa... Naseer d'ana ne sai abinda nace masa zaiyi kuma bai tab'a sab'a umarni na ba.."
Shareefah ta kuma murmusawa kafin tace "Shiyasa ma dole yabi umarnin ki wajen sa shi aurena da zakiyi, idan ba haka ba d'iyarki Lubna ta zamto disaster ma rayuwar ki....."
Innah na huci tasa hannu ta janyo hannun Shareefah sosai kana taci gaba da fad'in "Kar kiyi tunanin sako Lubna cikin wasan nan idan ba haka ba na halak'a ki ta hanyar da bakiyi zato ba balle tsammani....."
Isowan su Naseer cikin parlorn ya sanya Innah had'iye kalamanta tuni Shateefah ta soma pretending tanai ma Innah sannu....
Nan Naseer yake sanar dasu Alh Kabeer cewa su Shareefah ne suka taimaka ma Innah...
Alh Kabeer dai aunasu da idanu kurum yake, a fili kuwa waskewa yayi ya shiga jero masu godiya...
Lubna ta kuma rik'o hannayen Innah tace "Haba Innah an hanaki driving baki yarda, ni gashi kin hanani driving d'in kince ban girma ba har yanzu ke kuma ai kin tsufa ma tuk'a mota, don Allah ki bari haka nan..... Waima ina zakije da yamman nan...?"
"Iye... Na'am, wani irin tambaya kike min saikace wata k'aramar yarinya... Toh gidan Hajiya Tabawa zanje na shaida mata batun bikin yayanki Naseer shikenan, 'Yar jarida kawai...." ta k'arashe had'i da yin k'wafa....
Shareefah ta k'unshe dariyar ta kafin ta mik'e tana fad'in "Toh Innah mu zamu koma Allah Ya dad'a tsarewa...."
Ai Innah kam sam bata sami zarafin amsa mata sai ta mujiya da ta zuba mata... Azeema ma mik'ewa tayi ba tareda tace komai ba ta nufi k'ofar fita, don tun zamanta a wajen take hasashen abinda zata k'ulla ma Lubna, kai tsaye mota ta shige tana jiran k'arasowan Shareefah.
A hankali suke takun su yanai mata rakiya yake tambayar ta yanda lamarin ta kasance, suna masu kuma jajanta ma juna..
Sanda suka iso dab jikin motar yana kuma kallon yanda glass ya tawarwatse, d'an jim yayi kafin ya d'ago ya dubi Shareefah yace "Thank you Shareefah, gaskiya Allah Ya rufa asiri da ya kawo ku, ba don haka ba who knows what they could have done to her..... Ina son Innah ta sosai banson wani abu ya sameta..."
Shareefah ta murmusa zuciyarta fari k'al kafin tace "Haba Naseer ka daina min godiya pls, idan naga Innah cikin halin taimako ban taimaka ba alhali inada halin taimakawan me na zamto, Family d'inka nawa ne, tunda nida kai kwanaki k'alilan suka rage mu zamto abu guda...."
Ya kuma yin murmushi yana dubanta, tabbas yasan Shareefah tanada rawan kai da son nuna ita wata ce, amma wannan hali nata na son mutane da taimaka ma mutane yana burgesa, don tun yana Air Force base d'insu na Kaduna, a lokacin da suka had'u da family d'in Shareefah ya lura duk wani tak'urawa da Mamy kema Azeema Shareefah batayi watsi da Azeema ba, sannan har b'oyewa take bata so Mamy ta gane hakan don kar ta kuma d'aura ma Azeemar karan tsana... Tabbas wannan good side d'in Shareefah ne dake tsananin burgesa....
A haka ya mata rakiya har motar su suka kuma yin sallama da Azeema kafin suka wuce shima ya nufo cikin gidan..
A hanyar k'ofar kitchen ta baya ya had'u da Deeni zaune saman faran kujera yana cin abinci..
Da murmushi saman fuskar sa suke gaisawa da Deenin kafin ya umarce sa idan ya gama cin abincin a share glasses d'in da suka shiga cikin motar Innah... Cikeda ladabi Deeni ya amsa masa don sosai Naseer ke burgesa duk gidan... Har wani sara masa yake ya k'ame idan ya gansa, Naseer kuwa har abun yakan so basa dariya, yana son ya tambayi Deeni ko yayi karatu ko yanada takardar wata makaranta a nema masa aiki mai kyau, don shi sam baiso yaga matashi mai jini a jiki da kuma zafin nema baida future ba, amma yasan yin hakan ka iya janyo masa mtsala da Innnah don yanzu sai tace bashi ya kawosa gidan ba... Saidai kawai yake masa alheri idan yana son taimaka masa.
Mamaki ne ya cika Deeni jin warin wiwi cikin motar Innah, a'ah kai bari dai yayima motar filla-filla... Aiko nan ya hangi guntuwar karan sigari cikin motar, yana shinshinawa yaji warin wiwi k'au ta cika masa hanci... Maimakon yaji takaici ma ta rufesa sai dariyar da ya kufce masa a fili ya furta "Amma wannan mata anyi tsohuwar kilaki, ashe ba taba kawai take sha ba, ikon Allah.... Jin Mama Tani na kiransa yasa sa saurin k'arasa kintsa motar kafin ya tafi kiran Mama Tani...
"Zahraddeni ina rabaka fah da shiga hurumin da bai shafeka ba, banda gulma motar Innah akace kana kula dashi ko ta Lubna iyi....?" ta k'arashe tana dubansa.
Deeni dai dariya yake harda guntun hawaye kafin yace "Mama Tani wllhi wiwi take sha..."
"Na shiga uku ni Tani ina kasan warin wiwi, Deeni anya ba shaye-shaye ka soma ba.." ta k'arashe hannu saman k'irji.
Zaro idanu waje shima yayi kafin yace "Haba shaye-shaye kuma Mama Tani, aide kinsan ina zama cikinsu babu kalan warin kayan mayen da ban sani ba amma ko karan sigari ban tab'a zuk'a ba, amma wannan tsohuwar wllhi wiwi take sha ashe burga take tana d'urawa cikin karan sigari, rufa ido take ma 'ya'yanta, kuma ma ai Soja ne ya sakani gyara motar kinsan ina matuk'ar ganin girman sa bazan iya masa musu ba, kaf gidan nan shi kad'ai ne zakka, ni wllhi gani nake ma kaman ba wannan tsohuwar bace ta haifesa ba...."
Hannu Mama Tani ta kai ta buge bakinsa ganin Falmata ta nufo yanda suke, a hankali taci gaba da fad'in "Kana jina, ko da wasa kar na kuma jin wannan zance a bakin ka balle kayi yakai kunnen Lubna, kajini koh..."
Gyad'a mata kai kurum yayi amma yasan duk randa Lubna ta k'ular dashi zai gaya mata bak'a gameda mahaifiyar ta....
*** **** ****
Yammacin ranar alhamis Azeema ta shirya tsaf ta nufi jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (Gubi Campus, tafiya ne mai ratan gaske daga bakin babban kwalta zuwa cikin makarantar.
Earpiece ne manne a kunnenta da alama amsa waya take.
"Ina jinka.........." ta fad'i lokaci guda tana mai sakin wata murmushi kana taci gaba da fad'in "Kar ka sami damuwa, ai ka gama part d'inka wannan nawa ne, tunda na shigo cikin makarantar nemanta bazai min wuya ba...." ta kuma yin murmushi kafin tace "Shikenan sai na jika........" daga haka katse wayar tayi dai-dai sanda ta paka motar a k'ofan girls hostel......
0 comments:
Post a Comment