K'ofar d'akin Azeema ta hanga hakan ya bata tabbacin suna ciki.... A tamanin ta nufi d'akin tana mai ci gaba da huci...
Salma kuwa hango Shareefah da tayi a haka ya sanyata mik'ewa babu shiri tayi bayan Azeema tana wulli-wulli da idanu....
Shareefah kuwa fad'i take "Fito ki fice daga gidan nan, shegiya karuwa sauran titi....."
Azeema na rik'e Shareefah tana fuzgewa tana fad'in "Ki k'yaleni na sallami mayya.... Idan baki sani ba ki sani itace yarinyar da Affan ya d'aga hankali akanta yanzu gashi ta kuma hura asirin ma Naseer ya shak'a a iska.... Wllhi Allah sai ta bar gidan nan......"
Daga Salmar har Azeema kallo suka bi Shareefah dashi ba tareda sun furta koda kalma guda ba......
Shareefah ta kuma yunk'ura tayi kan Salma ta kuma b'oyewa bayan Azeema.... Shareefah sai fincika take k'arshe rarumo takalmi tayi a shoerack tayi saitin Salma dashi tuni Salma ta sunkuya sai a fuskar Azeema.... Azeema ta rik'i goshinta cikin azaba....
Salma ta dubi Azeema fuska fal damuwa take fad'in "I'm sorry don Allah kiyi hak'uri kinji......" bata kai aya ba ta fice a guje ganin Shareefah ta nufo ta gadan-gadan...
A guje Shareefah ma ta take mata baya... Dabara ta fad'owa Salma tayi saurin janyo k'ofar corridor d'in da zai sadaka da stirs ta kulle.... Waige-waige ta soma yi a parlorn nan ta hangi tarin fruits saman dinning table.... A tamanin ta nufi dinning table d'in jin Shareefah na k'ok'arin bud'e k'ofar....
Ayaba ta d'auka ta b'are tayi jifa da b'awon dai-dai k'ofan kafin ta nufi sashen Daddy a tamanin...
Dai-dai hanyan shiga suka kusan cin karo da Mamy... Huci kawai Mamy keyi sanda sukayi ido hud'u da Salma wacce ta nufo a guje tamkar an zaburo ta.... Ganin irin kallon da Mamy ke mata ya sanyata soma ja da baya..... Ganin Mamyn na k'ok'arin nufota yasata kuma juyawa a guje ta koma shashen su Mamyn
Shareefah da batasan da b'awon ayaba ba tana fitowa ya kwasheta ta zube k'asa saman tiles... K'aran azaba ta saki lokaci guda Azeema ta k'araso tana gimtse dariyarta take fad'in "Babe wa ya fad'a maki cin uwar yarinyar nan ba tareda mun karanceta ba zai mana sauk'i, nima ai tunda na ganta naji kuma itace Salma na gane itace wacce Affan ya susuce akanta kina ganin idanunta kaman ta mujiya wannan da gani anyi shu'umar k'auye cin uwar irinsu wahala ne dashi....."
Shareefah dai sai faman sosa kunkuminta take yanda ta tik'u a k'asa..... Kaman daga sama suka hangi Salma ta shigo a guje basu san waye ya biyota a guje ba... Tuni suka mik'e suka haye stirs...
Salma tana ganin b'awon ayaban nan ta kauce masa, su Mamy kam inaa sam bata kula ba, aiko tana takewa ya kwasheta ta zube a k'asa lokaci guda ta saki k'aran azaba...
Cikin sauri Salma tayi burki ta k'araso tana k'ok'arin taimaka wa Mamy.... Duba d'aya Mamy ta mata ta kuma sakin k'ara tana fad'in "Kar ki tab'a ni mayya, na tabbata naku salon shan jinin kenan.... Tuni su Shareefah sun nufo k'asa Shareefah na d'ingisawa da k'yar don zaiyi wuya idan bata sami targad'e ba...
Ihun Mamy da Daddy yajiyo ya sanyasa nufowa sashen nasu babu shiri, cikin sauri yake tura keken nasa
Shareefah da d'ingishi ta nufi Salma tana fad'in "Wllhi baki isa ki nakkasa min uwa na barki ba......"
Salma ta soma ja da baya tana niyyan arcewa suka jiyo muryar Daddy yana tambayan ba'asi....
Cikin sauri Shareefah ta k'arasa dukda d'ingishin da take tamkar zata runtuma ihu take fad'in "Daddy ba wannan mayyar bace zata kashe mu tasha jinin mu nida Mamy... Daddy wllhi b'awon banana ta saka mana a hanya muka fad'i Mamy kuwa sai tattamke idanu take tana nishi da k'yar yayinda Azeema taci gaba da matse k'afafun Mamyn cikin salo na mugunta..... Dundu takai ma Azeema tana fad'in "Don ubanki sake min k'afafu kafin ki k'arasa ni...." Azeema ta gimtse dariyar ta don tasan tabbas idan Mamy bata sami kariya ba toh kuwa taji mummunar rauni...
Dafe kansa Daddy yayi lokaci guda kafin ya d'ago yana duban Salma da hawaye ya wanke mata fuska....
"Salma yaya akayi haka ta faru.....?"
Goge hawayenta tayi kafin ta soma fad'i cikin murya irin ta mai kuka.... "Daddy ba wancan Auntyn bace(tayi nuni ga Shareefah) ta saka b'awon bananar don taga Mamy na bina a guje wai na hau na zame shinefah Allah Ya kiyaye ban taka ba sai tsautsayin ya fad'i kan Mamy... Daddy nidai so nake na tafi wajen Inno ta...." ta k'arashe tana goge ragowar hawayen ta...
Gaba d'aya k'uri suka mata cikeda al'ajabi, bakinsu ma gaba d'aya nauyi ya masu sun kasa furta komai.... Lallai yau sunga sharri da k'afafunta.....
Alh Ali ya dubi Mamy dake zube har lokacin a haka kana yace "Hakane abinda ta fad'i...? "
Mamy da bakinta ya mata nauyi tama rasa me zatace sai jiyo muryar Azeema tayi tana fad'in "Eh wllhi haka ne Daddy, amma kayi hak'uri Daddy hakan bazai kuma faruwa ba Insha Allah...."
Mamy baki sake ta kuma dawo da dubanta ga Azeema wacce tayi maganar hankali kwance sai ka rantse iyakacin gaskiyarta kenan...
Shareefah zatayi magana Azeema ta girgiza mata kai had'i da kashe mata idanu guda, dole ta had'iyi maganar ta ba don taso ba...
Girgiza kai kurum Alh Ali yayi kafin yace "Shiyasa a kullum nake fad'a maku shi mugunta bashida alfanu watarana sai ka tona ramin da zaka apka ciki ba tareda ka sani ba, yanzu ina amfanin wannan Al'amari....?" ya dawo da dubansa ga Shareefah kana yaci gaba da fad'in "And you bansan yaushe kika soma koyan mugun hali ba, da sam babu ruwanki, toh ina maki gargad'i kada ki kuskura ki soma kinji ni koh...."
A hankali Shareefah ta gyad'a kanta kafin tace "Bazan kuma insha Allah Daddy..." Ta tako da k'yar har gaban Salma kafin ta rik'o hannayen Salma tace "Kiyi hak'uri Salma haka bazai kuma faruwa ba insha Allah I promise...."
Salma dai d'an murmushin yak'e tayi wanda iyakacinsa fatar baki ko mak'ogoro bai je ba, don haka kurum take ji a jikinta bata yarda da Shareefah ba....
Mamy baki sake take binsu da kallo cikin zuciyarta tana fad'in ta shiga uku Azeema sunyi biyu a cikin gidanta don yanda taji yarinyar nan ta tsara zance ta kare kanta lallai akwai jan aiki a gabanta, gata k'aramar yarinyar har tasan ta tsara wannan zance ko tsoron idanunsu bataji ba, kai wannan tama dama Azeema ta shanye, bata isa ba dole tasan abinyi kafin ta wayi gari sun k'arasa ta, don wannan ta rik'a ta kuma wayewa ba k'aramar makira za'ayi ba..... Ta yunk'ura zata tashi ta saki k'aran azaba tana rik'e katerenta guda.....
Daddy Ya nufota cikin sauri yana mata sannu, duban su Shareefah yayi kana yace "Maza su kira malam Bala akai Mamy gidan d'auri..
Azeema tayi wuf tace "Daddy ka mance ai ba'a samunsu da dare saidai a lallab'a zuwa safiya, akwai man zafi sai a shafe mata k'afafun kafin safiya...."
Cikin tashin hankali Mamy take fad'in "Yo sai na zauna da k'afafun har safiya suka kuma yin tsami......?"
"Mamy fah hak'uri zakiyi wllhi babu masu d'auri da dare...." Azeema ta kuma fad'i sanda suke k'ok'arin janye Mamyn
Da k'yar suka tallafeta su duka ukun suka nufi stirs da ita.... Shareefah tana fad'in "Nifa na gaji kunsan nima ankle d'ina ciwo yake min., ku tsaya mu huta kar mu zube a k'asa gaba d'aya....."
Azeema kuwa cewa take "Muje dai daure Shareefah mahaifiya ce...."
Wani k'ara Shareefah ta saki lokaci guda ta saki Mamy tana rik'e ankle d'inta.... Tuni Azeema ma ta saki Mamy da gayya ta durk'usa tanai ma Shareefah sannu
Gaba d'aya sun tarawa Salma nauyi ai tuni suka zube k'asa daga Salmar har Mamyn... Mamy ta kuma sakin k'aran azaba tana fad'in "wayyo ku kiramin Affan ya d'agani....."
Azeema sai matse dariyar ta take.... Daddy kuwa daga k'asa yake fad'in kuyi hankali fah..."
Azeema ta amsa da toh Daddy kasan mu duka mata ne sai a hankali....
Haka saida Mamy ta gama jigata kafin aka isa d'akinta, Azeema ta shiga gyara mata kwanciyar Mamy tana fuzgewa tsabagen takaici... Shareefah kuwa tuni ta dafa Salma sun fice sun nufi d'akin Shareefar...
D'aki ya rage saura Mamy da Azeema.
Mamy na huci take fad'in "You'll pay for this..."
Azeema ta murmusa tana wasa da bakin sumar ta kafin ta matso daf da Mamy murya can k'asa take fad'in "Yau kinga ranar k'afafun Daddy, da ace baki nakasa sa ba da yanzu ya tallafe ki ya tarairayeki......." Cikin wani irin gurnani Mamy takai damk'a ma Azeema tana fad'in "Ki iya bakinki yarinya wllhi duk randa na warke zan shayar dake mamaki....."
Azeema ta kuma murmusawa kana tace "Yaushene zaki warken.? Kina tunanin sabuwar makamin da ta shigo gidan nan zata bari ki warke ne.....?" ta kuma yin murmushi kafin tace "And the worse part zata iya zama sirkar ki, idan hakan ta kasance zan mugun tausaya maki..... Amma kar ki damu I'll be there for you Aunt.... Na sani sooner or later zaki nemi taimako na, idan lokacin yazo I'll be your Ally...." ta k'arashe tana shu'umin murmushi had'i da ciza lab'enta na k'asa...
Har ta fice Mamy bata daina binta da kallo ba tana nazarin kalaman nata, tabbas idan ya tabbata wannan yarinyar ce Affan ya tada hankali akanta Azeema zata mata amfani wajen kawar da ita, idan yaso daga baya sai tasan yanda zatayi da Azeemar.... Ta k'arashe tunanin nata murmushi fal saman fuskar ta....
A d'akin Shareefah ta taddasu, Shareefah ta fito mata da kayan bacci kala daban-daban tana fad'in ta zab'i wanda ya mata ta saka... Azeema ta k'araso fuska d'auke da murmushi ta shiga d'add'aga kayan baccin tana juya tana manna su jikin Salma... K'arshe ta d'auko wani kalan ja mai kyaun gaske tace ta saka sa zai amsheta... Shareefah ma ta d'auko wani pink tana fad'in a'a ta saka wannan sai yafi amsar ta...
Salma dai kallo kawai ta bisu dashi cikeda mamakin wai kayan bacci ma sai wanda zai maka kyau saikace wata matar aure... D'an murmushin yak'e tayi ganin sun mata cha su duka biyu aka saikace mayu kana tace "A'a kar ku damu aima inada shi.... No kayan jikina ma is okay zan iya bacci dashi... Yanzu sallah zanyi...."
Gaba d'aya suka bita da kallo don su kam tsakanin su da sallah saidai suji anayi a masallatayya ko kuma su hangi mahaifin su na yi, ko randa 'yan ibadan Mamy ke kusa tayi....
"Ganin sun mata k'uri ya sanyata saurin fad'in "Inane bathroom...?"
A tare suka mata nuni da bathroom d'in lokaci guda suka bita da kallo sanda ta kwab'e abayan jikinta, riga da skirt d'in da ta d'ora abayan bisa ya bayyana.... Gaba d'aya suman tsaye sukayi suna binta da mayen kallo don duk yanda mace mai diri ta kai toh fah Salma takai....
Har ta shige toilet suna bin steps d'inta da kallo..... Saida suka jiyo sautin rufe k'ofa da tayi kafin suka juyo suka dubi juna a tare...
Azeema ta matso dab da Shareefah sosai kana ta sassauta murya tace "Babe kinga abinda na gani.....?"
Tsaki Shareefah tayi kana tace "Kiyiwa Allah ki rik'e kwad'ayinki don wllhi muka gwada mata kanmu kashinmu ya bushe a gidan nan bazamu cimma burinmu na salwantar da ita ba..."
Azeema ta murmusa kana tace "Yaushe kika soma tunanin da ni banyi ba.... Ko karan hauka ya cije ni bazan bi yarinyar nan ba, amma bazan iya kwana d'aki guda da ita ba... Kwana d'aki guda da ita Is a torture I swear......"
Shareefah ta Kai mata duka tana dariya take "Fad'in mayya bazata iya jurewa ba.... Kawai mu bar mata d'akin ki mu sai muke kwana a nawa d'akin..."
Jinjina kai Azeema tayi kana tace k'warai hakan za'ayi.... Suna nan a haka har Salma ta fito suka bata masauk'inta d'akin shareefah... Gaba d'aya su duka biyun kowa son kyautata mata yake har ta rasa wace gwana, da k'yar aka samo mata abin sallah a d'akin Mamy shid'inma sabida bak'i ake ajiyesa, wajen nuna mata alk'ibla ma saida sukayita musu, wannan tace nan ne wancan tace can ne, abin sai mamaki yake bata tamkar wacce tazo gidan Maguzawa marassa sallah balle salati , saida suka tafi har BQ aka tambayo Baba Delu mai masu aikatau ta nuna alk'iblan... Duk wannan rawan jiki da sukeyi bashi yasa Salma ta Saki jiki dasu ba...
Tana ida sallan tunanin 'yan uwanta ya fad'o mata, a hankali ta Saki murmushi kana ta furta "Kwanan zamu ga juna insha Allah.. Nayi kewarku gaba d'aya..." ta k'arashe tana k'ok'arin maida k'wallan dake k'ok'arin zubo mata... Tunanin Soja ne ya fad'o mata tasan sai yanda k'arfinsa ya k'are wajen nemo mata danginta.... A hankali ta d'aga rigarta ta d'auko chewing gum d'in da ya bata had'i da k'ura masu idanu, lokaci guda ta Saki murmushi tana shinshina takardan chewing gum d'in, k'amshin turarensa ya kama jikin takardan.. A hankali ta saki murmushi tana tuno farkon had'uwansu... He's really kindhearted... Allah Ya biyasa taimakon da yakeyi, bazata tab'a mantawa da taimakon sa a gareta ba.... Bataci chewing gum d'in ba sai jawo drawer da tayi ta zuba su ciki har lokacin bata daina murmushi ba... A haka ta d'an kishingid'a har bacci yayi gaba da ita......
*****
Bai koma base d'in nasu ba gida ya wuco don dama gobe yake son ya tafi garin Jama'are da yardar Allah....
Ya gama komai na d'abi'unsa kafin ya kwanta, zama yayi yana kallon wani series film mai suna Blacklist lokaci guda ya saka pause sanda ya soma tuno ko wani hali take ciki yanzun.... Sabon kwana d'aya tak sukayi amma yanajin tamkar sun jima da sabawa... A hankali ya saki murmushi lokaci guda wayar salulansa ta soma ringing... Ganin Shareefah ce mai kira ya sanyasa sakin gajeren tsaki kafin ya saka wayar a silent ya mik'e ya kashe kallon gaba d'aya, don gobe da wuri yake son fita, yayima Affan alk'awari and he won't let him down zai cika alk'awarinsa da yardar Allah.....
*****
Washigari misalin k'arfe takwas na safiya ya fito cikin shiri, jampa kalan ruwan k'asa harda hula, sai yayi matuk'ar masa kyau, bai faye saka manyan kaya ba hasalima saida dalili yake sakawa, idan ka gansa da manyan kaya toh juma'a ne ko kuma zaije wajen da ya lak'anci manyan kayan, toh tafiyar tasa ta yauma ta lak'anci manyan kaya tunda b'adda kama yake son yi.....
A parlor ya tadda Mama Tani na d'an aikace-aikace suka gaisa kana ya tambayeta ko Innah ta sauk'o.. Nan ta sanar dashi bata tashi ba gashi Innah idan tana bacci babu mai zuwa kanta ya tasheta gaba gad'i sai Lubna ko kuma Fawaz idan yana nan... Su biyun nan ne basu biye ma dokar ta, Kabeeru kuwa gaisar da ita dama ba wai ya shalle sa bane, duk sabida Naseer take irin wad'an nan abubuwae.. Idan da sabo yama saba..
Mama Tani ta masa tayin abinci, ba wani abincin kirki yaci ba tea kawai yasha ya mata sallama... Ta masa a sauk'a lafiya had'i da rakasa da kallon tausayawa domin kuwa sosai Soja ke bata tausayi, ace a gida ka fita zakka sannan mahaifiyar ta washe ka tamkar mutuwa akwai abin tausayi, Allah sarki gashi shi kuwa ya d'auki hakan k'addara na rayuwar sa..
Jikin motar sa Lubna ta hangesa ta tafi da gudu tana fad"Oyoyo Ya Naseer, yaushe kazo ban sani ba....."
Deeni dake faman goge motar Lubnar galla mata harara yayi had'i da tab'e baki..
Naseer ya murmusa yana mai zura key jikin mota yake fad'in "Jiya da dare nazo Probably kina bacci...."
D'an turo baki gaba tayi cikeda shagwab'a take fad'in "Amma Yaya shine baka tashe ni ba, kasan nayi kewarka, sanda zakayi tafiyar kofah sallama bamuyi ba..."
Naseer ya murmusa ya d'an shafi kanta "Toh kiyi hak'uri k'anwata, ai gashi yanzu na dawo..."
Ta d'an murmusa tana sanne kai take fad'in "Toh Yaya.... Ya Affan fah... Shi yaushe zai dawo....?"
Gaban Naseer ya bada dam! Don yasan a sangarcin Lubna sai ta saka sa gaba tayita masa kuka har ya janyo hankalin Innah ta sauk'e zafi akansa.. Donma Lubnar tana shakkan sa da baisan yanda sangarcin nata zai kasance ba...
Fuskar rashin wasa ya saka kafin yace "School zakije..?"
Ganin fuskar sa babu walwala ya sanyata shan jinin jikinta, saida taji dama bata masa maganar ba, don yayan nata Allah Ya masa gizo, a hankali ta jinjina masa kai alamun eh..
Naseer ya jinjina kai had'i da furta "Good, muje na kaiki....."
"Yaya kayi hak'uri bafah soyayya nake ba...." ta fad'i kaman zatayi kuka..
Shi dariya ma taso basa, d'an dakewa ya kumayi kana yace "Nace muje na kaiki ko bakiji bane..."
"Yaya bafah Gubi zanje ba Yalwa zanje...." ta kuma fad'i tana k'ok'arin ja baya..
Deeni kuwa daga yanda yake tsaye sai d'aukanta da wayarsa yake yana dariya k'asa-k'asa
Naseer ya d'an bud'e murya "Nace ki shiga mota mu tafi..."
Cikin sauri ta zagaya ta bud'e mazaunin mai zaman banza ta shige..
Sanda suka zo wucewa Deeni harda sara ma Naseer yana fad'in "A sauk'a lafiya rankashidad'e...."
Suna had'a idanu da Lubna ta galla masa harara... Shiko harda mata dariyar k'eta had'i da fito da harshe yayi mata gwalo.... Aikam yana son mai taka ma Lubna burki da wannan rawan kan nata...
Suna ficewa video d'in yayi playing yana kallo yana dariya, ya samu abin rufe bakin tsiwan ta...
******
Mamy fah k'afa tayi tsami ko motsawa daga saman gado ta kasa balle a tafi gidan d'auri, haka dole aka tafi akazo da mai d'auri har gida duk tayi fitsari a jikinta da yanda take kwance...
*Sameena Aleeyou...*
[25/07 16:20] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*22*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
Har k'ofan class ya kaita ganin mutane nata zirga-zirga alamun lecturer d'in bai shiga ba yasa Naseer karkatowa sosai yana dubanta ganin ta d'ona baki gaba ya sanyasa kamo hannayen ta kafin ya soma fad'in "Lubna ba wai cewa nayi karkiyi soyayya ba but pls for now ki ajiye maganar Affan a gefe and focus on your studies.... Look, you're my only sister ina sonki sosai bazan so naga wani yayi hurting d'inki ba... Affan is my best friend although na d'auke shi kaman k'ani.... Duk cikin abokansa no one knows him like I does... Ba wai ina nufin yanada wani mugun hali bane, no.... I just don't want you to get hurt... I don't think I can watch my only sister trying to jump into a swamp and allow her, neither can I see any good thing coming her way and decide to hinder it.... Just try to understand that I'm only doing this to protect you, to keep you safe from getting hurt, Okay....." ya k'arashe yana k'ok'arin share mata hawayen dake neman wanke mata fuska...
D'ago idanu tayi tana dubansa kafin ta soma fad'in "But Ya Naseer... Ina son Affan so much, pls kar ka rabamu...." kuka ya hanata ci gaba
Gaba d'aya sai yaji tausayin ta ya rufesa yasan sam babu soyayyan k'anwarsa a zuciyar Affan already wata ta mallake wannan gurbin.. D'an k'ak'aro murmushi yayi kana yace "Com'on but you've your family and we all love you so much.... Bana son ganin hawayen nan kinji... Ki nutsu kiyi karatun ki....." ya k'arashe yana saka hannu a aljihun wandon sa.... Wasu kud'ad'e ya ciro ba tareda ya mata magana ba ya d'auki handbag d'inta ya bud'e zip d'in ya saka mata kud'ad'en a ciki.....
Kallonsa kawai take tana murmushi take goge hawayen ta... Godiya ta masa kafin ta bud'e motar ta fice... Saida har ta shige class kafin ya kunna motar sa ya bar wajen.....
********
Mamy sai ihu take babu ambaton Allah ko zata sami sauk'in azaban da take sha, da k'yar aka samu aka d'aure k'afar sai ashar take narka ma Azeema sanda taji Mai d'auri yana fad'in ai da an kaita tun ajiyan don ko sun kulle gidan har k'wank'wasa masu ake idan an kawo marassa lafia, sanadiyan haka ne ma suka daina kulle gidan wasu na kwana a zaure ko za'a kawo majinyata...... Alh Ali girgiza kai kurum yake jin irin ashariyan da Mamy keyi tamkar tab'ebb'iya...
Mai d'auri ya dubi Daddy kana yace "Alhaji tsagewan k'ashi ne nan da sati d'aya zuwa biyu zata sami sauk'i da izinin Allah, sai ta kiyaye abinda zai jawo ta fama ciwon..."
Daddy Ya jinjina kai kana yace "Mun gode malam, sannan za'a kiyaye insha Allah mu k'arasa ta waje...."
Malam mai d'auri ya nad'e jakarsa ya nufo bayan Daddy.. Bayan sun gama maganar su da Daddy Ya masa sallama ya nufi hanyar fita... Daga yanda ta lab'e ya hangeta suka sakar ma juna murmushi kafin ya waiga gefe da gefe kana ya k'araso yanda take lab'e a sace...
Dariya suka fashe dashi su duka biyu kafin tace "Ina fata kace ma Daddy basai an yi hoton k'afar fah...?"
Malam Audi ya jinjina kai kana yace "Duk yanda kika umarta hakan akayi, jagwalgwala mata k'afar kawai nayi kuma babban kariya ne ba tsagewar k'ashi ba..."
Azeema tayi wata kafiran murmushi kafin tasa hannu a bra d'inta ta ciro kud'ad'e ta mik'a wa Malam Audi kana tace "Aikin ka yayi kyau, idan abu ya kuma fin haka kyau zaka kuma jina...."
Godiya ya kuma mata yana washe baki kafin ya wuce... Bayan shud'ewar wasu mintoci ta fito daga mab'oyar ta ta shige gida...
Kai tsaye d'akin Mamy ta wuce tana gaidata... Mamy ko amsata batayi ba sai huci kawai take tana tunanin kalan cin uwar Azeema da zatayi idan ta warke, gashi mai d'auri ya sanar da ita sati guda zuwa sati biyu ta warke, tayi k'wafa had'i da kauda kai gefe.....
Azeema kuwa kauda kai gefe tayi tana murmushin mugunta har ta fice daga d'akin.. Tasan idan Mamy ta zamto babu k'afafu toh fah sai abinda taga dama don zata zamto tamkar wakiliyar Mamy wajen aikata sharri, komai ita zata ke wakiltawa don haka mallakan Affan sam bazai mata wuya ba....
*****
Hankalinsa gaza kwanciya yayi, ji yayi yana son sanin halin da take ciki, ko babu komai ita d'in amanar aminin sa ne.... Cikin sauri ya karya kan motar ya d'auki hanyar gidan Ali Safwan....
Mamy na zube saman kujera a parlor k'afarta mai ciwo an d'aura saman pillow yayinda Shareefah ke gefenta tana kallon shirin fina-finan India da ake nunawa a zeeworld suka jiyo knocking
Shareefah ce ta shiga rangad'a kirawa Delu tana fad'in tazo ta duba mai k'wank'wasa k'ofa....
Mamy tayi caraf tace "Yo aikin banza har sai ta baro aikinta a kitchen tazo bud'e k'ofa me amfanin wad'ancan mayun dake zaune gidan nan suna ci mana arziki...."
"Wai Salma da Azeema kike nufi..." ta tambaya tana duban Mamy...
"Kinfini sani...." Mamy ta bata amsa kai tsaye..... Dai-dai nan Salma ta sauk'o cikin jan atampa d'inkin doguwar riga mai manyan fulawowi, ta yane kanta da mayafin abaya sosai tayi fasali.... Shareefah ta bita da kallo lokaci guda k'irjinta yayi wani irin bugawa ba tareda tasan dalili ba.... Gaisar da Mamy Salma ta soma yi.... Mamy kuwa sai hura hanci take tana watsa mata mugun kallo..... Zata zauna saman carpet Mamy tayi caraf tace "Ke ke ke.... Kul kar kika zauna min saman carpet salon ki barbad'a min wani asirin koh....." bata kai aya ba suka kuma jiyo knocking
Tana mai ci gaba da watsa ma Salma harara take fad'in "Jeki duba k'ofa......"
Babu musu Salma ta nufi bakin k'ofa lokaci guda Shareefah ta rakata da harara bacin sanda ta fito murmushi ta sakar mata...
Sandarewa tayi a bakin k'ofar ganinsa da tayi murmushi kwance saman fuskar sa..... Kallon-kallo suka shiga bin juna dashi ba tareda furta koda kalma guda ba..... Har ransa yaji dad'in ganinta haka, da alama ta kwantar da hankalinta
"Soja sannu da zuwa.... Kazo d'aukata mu tafi ne....?" ta fad'i full of excitement
Sai lokacin hankulan su Shareefah yayi wajen... A tamanin ta mik'e ta nufo su tana k'are masa kallo ganin yanda ya kafe Salma da idanu baya ko k'yaftawa...
Murmushin yak'e Shareefah tayi kafin ta d'an saita kanta ta k'araso tana mai fad'in "My soldier ka kasa hak'ura kenan da rashi na, nasan bazaka iya jure fad'anmu ba.... Bismilllah k'araso mana....." ta k'arashe tana tsare haban Salma
Bai iya furta koda kalma ba sai bin bayan Shareefah da yayi..... Salma kuwa jiki a sanyaye ta fito bakin k'ofar parlorn ta zauna... Batasan dalili ba amma tana ji zamanta a waje zai fi mata sauk'i
Ya sha mamakin ganin Mamy babu lafia, sanda Shareefah ta mik'e don kawo masa abin tab'awa nan Mamy ta soma sanar dashi yanda ciwon nata ya kasance..
"Wllhi am Naseer yarinyar nan kasheni ne kawai batayi, bataga girmana ba bata tausaya ma shekaru na ba ta saka mani b'awon ayaba a hanya na fad'i....."
Shiru Naseer yayi yana saurarenta yana mamakin Salma zatayi irin haka....Dai-dai nan Shareefah ta ajiye masa abin tab'awa
Kallon Shareefah yayi sanda Mamy ke ci gaba da bayani kafin ya sassauta murya yace "Me yasa baki sanar dani tun a jiya ba...."
Shareefah ta d'an murmusa had'i da zama d'an gefensa kana ta soma fad'in "Na kira wayar ka yafi a k'irga baka d'aga ba..... Don ma Mamy nada dauriya, ni ban tab'a ganin mutum irin yarinyar da ka kawo mana ba..... Ace randa kika soma zuwa gidan mutane ki karya matar gidan.... Amma dai kar ka damu mu a wajen mu komai ya shige nasan yarinta ke damunta da rashin wayewa kasan su a ruga sam babu tarbiya balle addini gradually zata adopting hali da d'abi'un mutanen birni....."
Har ta k'arashe bayanin ta bai tankata ba.... D'an fuzar da iska yayi kafin ya dubi Mamy ya shiga bata baki....
Mamy ta kaikaito tana dubansa da kyau kana tace "Naseer kayiwa Allah ka maida yarinyar nan yanda ka d'aukota kafin ta kashe mu gaba d'aya.... Irinsu 'yan shan jini ne balle kai da kake jazir tsaf zata shanye maka jini wannan....."
Bai iya furta komai ba sai mik'ewa da yayi yana tambayan ko Daddy Ya tashi... Shareefah ta gyad'a kai kafin tace bara ta rakasa., Sallama yayi ma Mamy kafin suka fice suka nufi sashen Daddy
Salma tana ganin sun fito ta nufosu cikin sauri tana fad'in "Soja don Allah kaje dani...."
Wannan karan fuska babu walwala yake dubanta, Shareefah na hankalce da irin duban da yake ma Salmar zuciyarta tayi sanyi lokaci guda..... Cikin sauri ta d'an dafa kafad'un Salmar kana tace "Kar ki damu just trust him, tunda yace zai taimake ki zaiyi nasan my soldier kirkinsa daban ne cikin........" Muryar Naseer ne ya katse ta
"Salma why..? Meyasa kikayi haka..? Meyasa zaki sakawa Mamy b'awon ayaba a hanya... Ko meye Mamy ta maki ya kamata ki mata haka.... Huh....? Now tell me meyasa kikayi haka, and don't lie to me.."
Kasa amsa Salma tayi sai idanunta da sukayi rau-rau,
Cikeda makirci Shareefah ta soma fad'in "Haba my Soldier tsautsayi dai bata wuce ranar ta, don Allah kada ka mata fad'a kaji, I'm quite sure yarinta ne kawai...." Ta k'arashe tana mai rik'o Salma had'i da share mata hawaye.... Bai kuma bin kansu ba don kukan nata har cikin k'ahon zuciyar sa yake ji, cikin sauri ya nufi sashen Daddy
"Ya isa haka Salma ki daina kukan nan... Kinji ni bansan meyasa Mamy ta fad'a masa kece sanadiyar jinyarta ba bayan an kashe magana jiya..." ta k'arashe tana kuma goge mata ragowar hawayen
Kallonta kurum Salma tayi zuciyarta na ayyana mata abubuwa iri daban-daban, bata furta komai ba suna nan tsaye wajen Shareefah na lallashi har Naseer ya fito...
Da gudu ta k'arasa gabansa tana kuma share fuskarta take fad'in "Soja dan Allah kayi hak'uri... Wllhi it was an accident, ba nufi na kenan ba.... Dan Allah kar kace bazaka je dani ba kaji......"
D'an jim yayi yana dubanta yayinda Shareefah ke faman karantar sa.... Girgiza kai kurum yayi kana yasa kai ya wuce cikin sauri... Shareefah ta take masa baya dad'i kaman ya karta
Salma jiki a sanyaye ta nufi cikin gidan... Shikenan k'ila ma bazai kuma kula da damuwar ta ba.... Gaba d'aya sai taji duniyar tai mata babu dad'i...
*********
Duk wani information da ya kamata ace ya samu gameda iyalan Jauro Yakubu bai samu ba, wuninsa zubur a garin shiru kake ji.... Yamma lis yake shirin barin garin nan ne ya gamu da Malam Dauda wanda ya taimaka masu, Malam Dauda ya sanar dashi ya sami labari kwanaki an gansu a tashar motoci sannan tabbas sun bar garin.... Saidai babu wanda yasan wani gari suka nufa don dreban motan da suka shiga kwana uku da suka wuce yayi had'arin mota ya rasa ransa...."
Naseer yayi shiru yana nazarin kalaman, bai fice daga garin ba har saida suka je tashar motocin shida Malam Dauda domin tabbatarwa.... Sosai yayi godiya wa Malam Dauda ya kuma sanar dashi zai iya dawowa ko yaushe... Wajajen k'arfe shida saura ya baro garin...
*********
Tunanin halin da ya barta ciki ya hanasa sukuni, gani yake tamkar bai kyauta wa Affan ba, idan ya runtse idanunsa ita yake hangowa tana matsan k'walla.... Duk wani abinda yayi niyyan yi kasa yi yake tunaninta gaba d'aya ya hanasa sukuni.... Ya dubi agogon bango dake manne a d'akin ya nuna k'arfe goma da kusan rabi, dare ya d'an ja ba hali yaje gidan a yanzu..... Fuzar da iska yayi lokaci guda ya mik'e ya nufo parlor had'i da kunna TV ya shiga kallon da ba fahimta yake ba.....
Washe gari kuwa sassafe ya tafi gidan, su Shareefah sai rawan k'afa ake duk a zaton ta sabida ita yake zuwa gidan akai-akai, koda Mamy ta tambayesa Lafia yayiyo wannan sammako sai ce mata yayi jikinta yazo dubawa, dad'i ya kuma lullub'esu... Sai waige-waigen ta yanda zai hango b'ullowar ta yake amma wayam baiko ga k'yallinta ba....
Tuni Shareefah ta d'ago masa zancen auren su nan yake sanar da ita a dai d'an bari Mamy ta samu lafiya kafin ayi batun....
Shareefah sai falli take tana cikasa da surutu shi kuwa idanunsa k'uri ma k'ofar corridor ko zai hangota.... K'arshe kasa daurewa yayi saida ya tambayi Shareefah Salma...
Shareefah da bak'in ciki ya tokare mata mak'oshi daurewa tayi had'i da yin murmushin yak'e kana tace "Ai.. Ai basu jima da ficewa ba itada Azeema...?"
Karkatowa yayi ya dubeta sosai kana yace "Da safen nan.... Zuwa ina....?"
Shareefah ta kuma muskutawa tana mai ci gaba da murmushin yak'e take fad'in "Breakfast.... Breakfast yau Salma tace a restaurant take son yin break tana son jin yanda mutane ke ji idan sunje cin abinci a waje don bata tab'a experiencing ba.... Shiyasa Azeema ta kaita ni kuma na zauna a gida na kula da Mamy...." Ta d'an ja fasali tana dubansa kafin tacee"Amma meyasa ka tambayeta..?"
Tamkar wanda ya dawo daga duniyar tunanin ya d'an ware idanunsa kana yace "No babu komai, so nake na mata tambayoyi gameda tsautsayin da ya apka masu..."
Shareefah batace komai ba sai gyad'a kai da tayi tana mai duban mug d'in dake gabansa take fad'in "Kasha tea d'inka pls kar ya huce..."
Tamkar wanda yake jira nan ya d'auki mug d'in ya shiga kwankwad'a kana ganinsa kasan ba dai-dai yake ba...
Lokaci guda ya mik'e da niyyan tafiya tunda wacce yazo dominta bata nan.... Shareefah ta mik'e don yimasa rakiya
Salma dake mak'ale bayan k'ofa ta gama jiyo komai samun kanta tayi da kasa fitowa saima wani sanyi da jikinta yayi.... A hankali ta juya ta koma d'aki lokaci guda ta kifa kanta tana kuka... Tabbas bata tab'a ganin makira mai fuska biyu irin Shareefah ba, haka kurum taji bata son tarayyarta da Soja, sam bai cancanci Shareefah ba domin kuwa shid'in mutumin kirki ne... Goge hawayenta tayi tana mai ayyanawa a ranta tunda kalan zaman da Shareefah ta zab'a suyi kenan tazo gidan da sannu zata saita ta ta daina munafunci... Ba tana mata kallon k'aramar yarinya ba tsaf sai ta dawo da ita kan saiti, yanzu 'yan uwanta ne a ranta bari ta gama da issue d'in dake gabanta tsaf zata gyara ma kowa zama a cikin gidan... Da wannan tunani ta mik'e ta nufi bathroom don wanke fuskar ta...
*******
Kusan kwana uku kenan ya jera yana zuwa Jama'are babu zancen da ya canza gameda labarin iyalan Jauro Yakubu.... Sannan ko yaje gidan su Shareefah baya samun ganin Salma... Gaba d'aya hankalinsa yayi kanta kacaukam ko office yaje aikin kenan tunanin halin da take ciki, duk ya danganta hakan sabida Affan yakeyi...
Salma kuwa ta dage da addu'a wajen kai kukan ta ga mahallici, Allah Ya bayyana mata danginta cikin k'oshin lafia, tasan soja na iya k'ok'arinsa koda bata saka sa a idanunta ba, bazata gushe ba tana masa addu'an samu nasara a rayuwa ba...
Yau tana tsaye jikin famfon bayi ma flowers tana alolan sallan la'asar ta hangi ana bud'e gate... Mik'ewa tayi da kyau don ganin mai shigowa, lokaci guda zuciyarta ya raya mata Soja ne, haka kurum ta tsinci kanta cikin farin ciki har batasan sanda murmushi ya cika fuskar ta ba....
Ganin tabbas motar kalan blue ce ya sanyata saurin k'arasa alolan kallabi a hannu ko k'arasa d'aurawa batyi ba ta nufi gate d'in tsaban murna, gani take k'ila yaukam su Innon ta Ya kawo mata...
Yana k'ok'arin parking ta iso tana washe baki take fad'in "Soja sannu da zuwa ina su Inno......" burki tayi da kalaman nata ganin yayi rolling tint glass d'in da ya rufe motar dashi, wannan ba baturen Sojan da ta sani bane, wankan tarwad'a ne wannan sannan shima sanye yake cikin kaki
Affan kuwa dubanta kawai yake cikin rashin yarda da abinda yake gani, baisan ko gizon da take masa bane ya biyos har gidansu... Dukda ta k'ara kyau ai bai mance wannan kamannin nata ba.... Bai manta had'uwa d'aya tak da sukayi ba....
Su duka biyun k'uri sukayi ma juna, ta rasa yanda tasan fuskar amma tabbas ta tab'a ganin shi saidai wancan lokacin ba da kayan Soji ta gansa ba.... Bata ankare da tunanin da take ba sai jinta tayi rungume cikin jikin mutum murya can k'asa yana furta
"Pls let me hold you.... Da gaske kece, ba gizo kike min ba... I thought na rasa ki kenan, I thought ganinki sau d'aya da nayi bazan kuma ba, Salma kar ki k'ara barina..... I... I love you....."
Azeema data hangosu daga window d'in d'akinta a d'ari da sittin ta nufo k'asa yanda Mamy ke zaune a parlor tamkar mahaukaciya take fad'in "Mamy Mamy!! Affan tana shan jinin Affan gasu can a waje ya manne cikin jikinta...."
Mamy ta zaro idanu waje tana fad'in "Badai Affan d'ina ba yaushe ma ya dawo garin....?"
Shareefah ta nufo k'asa a guje jiyo hayaniyar su da tayi..
"Mamy billahillazi gata can rungume jikinsa......" Azeema ta fad'i tana k'ok'arin ficewa waje... Shareefah ta take mata baya a tamanin... Ai Mamy ko zogin ciwonta bataji ba ta gunguro k'asa ta soma jada gindi ta nufi waje tana kwararo ashariya wanda yasa Alh Ali turo kekensa ya nufo waje shima.
Salma sai kokawan k'watan kanta take daga jikin Affan lokaci guda Mamy ta bud'e murya ta kirawo sunan sa... Saurin cikata yayi ya d'ago yana dubansu ga Mamy zaune dirshan a k'asa sai kururuwa take tana fad'in "Na shiga uku ni Asma'u an kawo mini Karuwa gida.... "
*Sameena Aleeyou...*
[25/07 16:20] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*23*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
Mamaki ne ya cika Affan ganin k'afar mahaifiyar nasa da d'auri
Baki na rawa ya tsuguna yana fad'in "Mamy what happened to your leg.... Mamy me ya same ki..."
Ko zarafin amsa sa bata samu ba, gaba d'aya sai tofin Allah tsine kurum take ma Salma... Tuni idanun Salma sunyi rau-rau don lokaci guda taji tsanar Affan sabida abunda ya mata, tuni ta bar wajen a guje tana goge hawayen dake zubo mata.... Shareefah tabi bayanta cikin sauri....
Dafe kansa yayi da hannu bibbiyu kafin yace "Mamy please.... For Allah's sake kiyi shiru hakan nan, Mamy yanzu fah dawowa ta, pls don't stress me out...."
Daddy dake gefe saman wheelchair d'insa girgiza kai kurum yayi yayinda Mamy taci gaba da fad'in "Aikin banza aikin wofi, banda maita da karuwanci daga dawowar sa ta taresa da runguma wayasan uwar me ta shafa masa, d'ana namiji tilo...."
"Kiyiwa Allah kiyi shiru..... Wai ke shikenan kullum cikin tada tarzoma, kiji da ciwon dake jikin ki amma kina neman k'arama kanki damuwa... Haba wace irin rayuwa ce wannan...." cewar Daddy cikin tsananin fushi..
Duban Affan dake tsaye rai b'ace yayi kafin yace "Shigo da mahaifiyarka ciki...."
Babu musu Affan ya ajiye jakan sa k'asa yasa hannu ya tallafi Mamy suka bi bayan Daddy... Sai sannan ta soma jin zafi tana sakin k'ara..
Azeema tayi wuf ta d'auki jakan Affan ta wuce dashi sashen sa..
Koda suka isa parlorn Alh Ali bakin Mamy bai mutu ba, sai masifa take tana fad'in Salma zata lashe mata d'anta...
Cikeda b'acin rai Daddy yace "Bakiga laifin d'anki da ya rungume 'yar mutane ba sai laifi innocent yarinya kike gani... Meyasa kike da fad'an son zuciya ne Asma'u, na zaci wannan ciwo da kikaji zai ishe ki ishara ki bi Duniya a sannu ashe sam bazaki canza hali ba.....?"
Affan ya d'an shafi kansa don shi sam bai d'auki rungumar Salma da yayi zai zama babban issue haka ba gashi yarinyar taji haushi taje tanata kuka ga ran Daddyn sa ya b'aci....
"Daddy I'm sorr....." Kayi min shiru" Daddy Ya katse sa.... Kafin yaci gaba da fad'in "Na d'auka ka canza wannan rayuwar naka... Ka sani sam hakan ba waye bane, ci baya ne da salon lalata Al'umma da DUNIYAR MU ta tsinci kanta a ciki yau, babu wani wayewa da turawan yamma zasu kawo mana wanda koyarwan addinin mu bai kawo mana ba.... Kar na sake ganin irin haka ya faru a gidan nan kana jina koh..."
A hankali Affan ya jinjina kansa kafin yace "Insha Allah Daddy za'a kiyaye...." Daddy Ya murmusa don yasan tabbas yanzu Affan ya canza gaba d'aya idan da ace da ne yayi masa wannan maganar da saidai ya tsula masa rashin kunya ya fice yana mai yin fito....
"Come here Soldier...." Daddy Ya bud'e masa hannaye... Cikin sauri ya k'aras yayi hugging mahaifin nasa
Daga bisani ne Daddy Ya sanar dashi duk irin d'awainiyar da Naseer yayi har kawo Salma gidan da yayi.... Affan kuwa cikin zuciyar sa yaketa mamakin meyasa Naseer d'in bai sanar dashi komai ba... Shashantar da zancen yayi don yasan Naseer idan yana aikin alkhairi har baiso mutane su sani, yanzu haka dalilinsa na b'oye masa kenan.... Shi yanzu babban burinsa bai wuce ya kuma ganin Salmar sa ba gashi ya sanyata kuka.... Oh shit.... Sosai yaji zafin b'acin ran nata har cikin ransa
Tattaunawa suka kuma yi da mahaifin nasa gameda ciwon Mamy, shi Affan cewa yayi bai yarda da masu d'aurin nan ba gwara aje asibiti ayi hoto asan wani irin ciwo taji.... Daddy yayi na'am da shawarin nasa don bazaiso matarsa ta k'are tamkar shi ba, dukda bawa baya wuce k'addarar sa a rayuwa....
Bayan sun gama tattaunawar su Affan ya mik'e ya nufi d'akinsa yanda ya tarar Azeema ta ida kimtsa masa komai.... Murmushi ya d'an sakar mata had'i da mata godiya.... Wani sa'in idan tana masa wasu hidiman sai ya d'an dinga jin nauyi ba don komai ba sai don gani da yake tamkar Azeema k'awar Addar sa Shareefah ce duk da zasu iya zuwa sa'anni shida Azeemar koma ya girme mata da shekara guda....
Kaman ta had'iyesa haka tabisa da kallo sanda ya soma kwab'e takalman k'afansa, jikinsa ne ya basa tana nan tsaye a wajen... D'an d'ago kai yayi yana dubanta kana yace "Akwai wani abu ne...?"
Ta kuma murmusawa kafin ta girgiza kai alamun babu kana taci gaba da fad'in "Me kake son ci kasan bamusan kana tafe ba, da mun girka maka favorite d'inka...."
D'aga gira sama yayi yana kallonta yanda take rangwad'a kafin yayi tak'aitaccen dariya mai bayyan hak'wara kana yace "No it's alright ba damuwa zanci komai, kar ki damu fah....."
Azeema ta murmusa kafin tace "You sure...?"
Gyad'a mata kai yayi lokaci guda yana mai cigaba da abinda yake....
A hankali ta tako ta zauna saman couch dake gefe... D'ago kai ya kumayi yana dubanta fuska d'auke da alamun tambaya..
Azeema ta d'an sauk'e ajiyan zuciya kafin ta soma fad'in "Affan kayi hak'uri da jinyar Mamy, wllhi duk cikinmu bamu zaci yarinyar nan zata iya ai......"
Saurin dakatar da ita yayi da fad'in "Azeema I'm terribly exhausted, I need to get some rest..... Could you please excuse me...."
Jiki a sanyaye ta mik'e tana murmushin yak'e wanda hausawa ke ce ma kafi kuka ciwo ta nufo waje...
Girgiza kai kurum yayi had'i da rufe k'ofar kafin ya kwab'e kayan jikinsa ya shige bathroom...
Zuciyarta tamkar ta fashe sabida takaicin gwaleta da Affan yayi,..... Can ta hangi Salma ta k'ofan baya ta kifa kanta da gwiwa tana matsan hawaye....
Azeema tayi murmushi mai cike da makirci kafin ta k'arasa, a hankali ta zauna gefen Salma... Salma tayi saurin d'agowa a d'an tsorace tana mai jada baya....
Azeema ta d'an murmusa kana ta zauna dab da Salmar.... Cikin tattausan murya ta soma lallashin Salma
"Kiyi hak'uri idan dai Affan ne haka halinsa yake na rungumar 'yan mata...." ta d'an ja fasali had'i da sauk'e ajiyan zuciya kafin taci gaba da fad'in " Waima don yanzu abun nasa yayi sauk'i, ko da yake wayasan me yake aikatawa a barikinsu idan ya tafi, ni farkon zuwata gidan nan har fyad'e yaso ya min Allah Ya kareni, ma'aikata kuwa a gidan nan dalilinsa Mamy ta daina d'aukan 'yanmata don sai ya bisu ya matse su...."
Kallonta kawai Salma keyi ba tareda ta iya furta komai ba, ita yanzu abun nasu har tsoro ya soma bata, she dosn't know who to trust, kowa da kalan nasa salon.... Sannan maganganun Azeema ya kuma dasa mata tsoro da tsanar Affan, she's lost gaba d'aya kwanyarta ya cakurkud'e babu wanda zatace ta yarda dashi a gidan bayan Daddy.... Bata iya furta komai ba har Azeema ta k'arashi shera zancen ta...
Ganin tayi jigum tamkar mai tunanin ya sa Azeema d'an dafata kana tace "Salma ke yarinya ce, ki kula da kanki kar ki kuskura ki bari Affan ya yaudare ki da sunan soyayya domin kuwa haka yake yima sauran 'yanmatan kindai san ko a mafarki mahaifiyar sa ba bari zatayi ya aureki ba don haka ki tsare mutuncin ki kar ki kuskura ki yarda dashi, shawarin da zan iya baki kenan...." ta k'arashe tana mai d'an jijjiga kafad'an Salma a hankali....
Kallo Salma tabita dashi har ta b'ace ma ganinta kafin tasa bayan hannu ta share hawayen ta... A hankali ta kuma tak'urewa waje guda tana mai tunanin 'yan uwanta wanda take tsananin kewar su.... Tabbas ta tsinci kanta a wani irin DUNIYA mai wahalan fasaltuwa.....
******
Tsaye yake gaban full length mirror sai faman k'are ma kansa kallo yake, tunda yake zuwa wajen Shareefah bai tab'a tsayuwa da sunan shiri gaban madubi ba sai yau, sai faman tsefe suman sa da ya sha gyara da shampoo d'in head and shoulders yake, ya kuma tura yatsun hannunsa cikin sumar yana dad'a gyara masu direction fuskar sa d'auke da murmushi, ya canza style d'in sumar sa yafi sau uku kafin daga bisani ya d'auki agogon Aldo d'insa wanda yake zallan silver ya d'aura a hannunsa na hagu...
Saida ya feshe jikinsa da turarukan sa designers kafin ya nufi ma'ajiyan takalman sa ya d'auko wata sandal bak'a mai kyaun gaske wanda yake tsananin haska farar k'afarsa ya saka... Yayi kyau sosai har ya gaji, kana ganinsa kaga d'an gayun k'arshe, cikeda farin ciki yake tafe a motar sa don yau yanada babban labari ma Salma gameda 'yan uwanta, ya sami wanda ya sanar dashi cewa lallai garin Bauchi suka taho
******
Tana gama lectures hostel ta wuce wajen k'awarta Faty.. Don Faty gaba d'aya bata courses d'in da sukayi yau tayi dropping d'insu sabida CO da suka mata yawa....
Faty na zaune a d'aki ta lula yanar gizo don bata yarda ba sai tayi tracking Kelly ta nemo sa ta amshi kud'ad'enta yanda ya shiga ya fita don Allah Ya gani bazata iya yafe kud'ad'en nan ba....
Kaman daga sama saiji tayi an banko k'ofa an shigo, cikin sauri mik'e tana fad'in "Babe Lafia meke faruwa.....?" ta k'arashe tana rik'e Lubnar dake kuka sosai...
"Babe please talk to me, wai meke faruwa ne....?" ta kuma tambaya sanda Lubna ta zube saman katifa...
Cikin kuka take fad'in "Faty baya d'aga wayata, baya replying messages d'ina.... Ya Naseer was right Affan baya sona....." ta k'arashe hawaye na ci gaba da gangaro mata...
K'uri Faty ta mata babu ko k'yafta idanu kafin tace "Oh gal.... Yeah yeah it's good to cry, let it out.... Yi kukan ki kiji sanyi....."
Sosai Lubna tasha kuka kafin tayi shiru tana tunanin rayuwa... Hannayen ta rik'e cikin na Faty take ci gaba da fad'in "I won't force myself on him, laifi na ne tun farko dana nuna masa tsan-tsan soyayya...."
Faty da gaba d'aya fuskar ta ta koma kalan tausayi gyara zama ta kuma yi kafin tace "Amma Lubna baifa ce maki baya sonki ba, sannan Ya Naseer hasashe kawai yake, don't jump to conclusions so easily, ki bari kiji daga bakinsa...."
Mugun kallo Lubna ta watsa mata da watery eyes d'inta kafin tace "Na jira naji ta bakinsa naji takaici ko me, nasan baya nan yayi tafiya wayarsa bata shiga na tsawon kwanaki, amma d'azu a class da na kirasa tana ringing, na kira yafi a k'irga bai d'aga ba, na masa text no reply, what else me kuma kike so nayi, at least da ya kunna wayar sa idan da gaske yana sona ko ban zamto mutum ta farko da zai soma kira ba zan zamto ta uku, ke naji aje bai kirani ba, meyasa da na kirasa yak'i d'agawa... I'm pretty sure Ya Naseer bazai min magana haka kawai ba dole akwai wata a k'asa.... Affan baisan zuwa wajena ba saidai ni na d'ebi k'afa na kai kaina duk da sunan soyayya,.." Kasa ci gaba da maganar tayi sai goge sabon hawayen da ya kuma zubo mata da tayi, cikin kuka taci gaba da fad'in..."Na gaji, na gaji da dakon soyayyar sa I've already made up my mind bazan k'ara neman yanda yake ba saidai idan shi ya nemeni..." Ta k'arashe tana mai kwanciya bisa katifar....
Faty d'an jinjina kai tayi had'i da sauk'e ajiyan zuciya tana kuma duba web d'in da take bisa a sace, don da ace Lubna ta sani da ta k'yaleta taji da batun bin sawun kud'ad'enta da yafiye mata wannan daramar da tazo tana mata like a drama queen.....
*********
Gabansa ne yayi mugun fad'uwa ganin motar Affan a gida, yeah ya sani akwai Sojojin da suka dawo yau amma sam baiyi zaton harda Affan ba, kenan kai tsaye gida ya k'araso kuma sam bai ko sanar dashi ta wayan salula ba...
Yana nan zaune cikin mota yana tunani ya hangi Affan d'in ya fito daga sashen Daddy sanye da k'anan kaya, inner black da farar 3quater, saurin fitowa daga motar yayi yana sakata a lock yake fad'in "Soldier, what a surprise..."
Murmushi Affan yayi sanda ya hangosa kafin ya k'araso sukayi hand shake..
"Kai haka ake dawowa babu ko waya....?"
Affan ya kuma murmusawa sanda suka nufi fararen kujeru dake zube a farfajiyan gidan
"Abinda ka min na rama....." ya fad'i dai-dai lokacin da suke zama bisa kujerun...
Murmushi mai bayyana hak'wara Naseer yayi kafin yace "Well, kace 50/50 kenan...."
A tare suka d'an dara kafin suka ci gaba da tattaunawar nasu....
Tafe take cikin flowers ya bayan gidan ko zata sami backdoor da zai fitar da ita daga gidan ba tareda kowa ya ganta ba, gwara taje nemo 'yan uwanta da kanta taga alaman zama a wannan gida sam bazai ficceta bar, tunda tazo gidan babu abin alkhairi da ya tab'a faruwa sai sharri..
Sam batasan da fish pond a wajen ba, ashe ta gefen pond d'in take bi wanda ruwa ne dam a ciki saidai an jima ba'a amfani dashi, tsantsin gefe kwatsam ya kwasheta aiko nan tayi juyi sai cikin ruwan wanda yake da d'an tsayi sosai... Wani k'ara ta Saki lokaci guda don kuwa shakka babu ta buga kanta
A tare Naseer da Affan suka mik'e, Naseer ne ya hangi facal-facal d'in da take cikin ruwa... A hankali ya furta "Salma.."
Wani irin tsalle yayi had'i da barin wajen ya nufi pond d'in, tuni Affan ya take masa baya....
Baiyi wata-wata ba ya fad'a cikin ruwan ya cirota sai faman tari take tana sosa kanta yanda ta buga...
Lokaci guda Affan ma ya durk'usa yanai mata sannu fuskar sa fal damuwa
Naseer da ya mata k'uri muryar sa har na rawa yake tambayar ta "Salma me kike yi a nan hope dai bakiji ciwo ba..."
Sai faman rarraba idanu take, ta dubi wannan ta dubi wancan yanda suka tasata gaba su duka biyun tama rasa maganar waye zata soma amsawa... Kuka ta fashe dashi tana fad'in "Soja nidai don Allah ka kaini wajen 'yan uwana don Allah... Ni na gaji da zaman nan gidan..." ta k'arashe tana tamke hijabinta da ya jik'e shak'af
Kallon juna Affan da Naseer sukayi dai-dai lokacin da su Shareefah suka k'araso wajen...
Kallo suka bisu dashi shaye da mamaki ga Salma a jik'e sannan Naseer ma a jik'e yake....
"Lafiya..? What's going on here...?" Shareefah ta tambaya tana mai bin Naseer da kallon tuhuma
Bai amsata ba sai duban Salma da yayi ya soma fad'in "Ki kwantar da hankalin ki komai yazo k'arshe insha Allah, saura k'iris ku kasance tare da family d'inki....."
Affan da jikinsa ya d'anyi sanyi lokaci guda, duban su Shareefah yayi kafin yace "Ta fad'a cikin fish pond ne, ku shigar da ita gida pls...."
Shareefah zatayi magana Azeema tayi saurin k'arasowa ta tallafo Salma tana fad'in "Ayya sannu Salma, muje ciki ki canza....."
Suna shigewa Affan ya mik'e yabi bayansu cikin d'an sassarfa
Naseer kuwa yana nan durk'ushe wajen, d'an bud'e murya yayi ya kira sunan Affan...
Affan d'in ya juyo yana duban sa... A hankali ya furta "Make sure she's safe...."
Affan bai ce komai ba sai tafiya da ya ci gaba da yi zuciyar sa tana gaya masa wasu abubuwa gameda Naseer d'in
Har suka shige Naseer na kallonsu kafin ya jiyo muryar Shareefah tana fad'in "And why are you also wet..... Meyasa sai kaine zaka shiga ka cirota, meyasa ba Affan ba.... Meyasa kai...." ta kasa ci gaba da magana don izuwa lokacin hawaye ya soma zubo mata...
D'an kauda kai gefe yayi had'i da fuzar da iska lokaci guda ya mik'e yana dubanta tuni zuciyarsa ta soma karaya, don shi abinda sam baison gani shine kukan mace, sosai ya d'an sassauta murya
"Shareefah meyasa ke a kullum tunanin ki yake baki ba daidai ba, yanzu harta taimako ma sai anmin tambaya akai, why.... Kinga karma mu soma samun matsala akan Salma, babu komai tsakani na da ita, ki kwantar da hankalin ki knji ni koh..."
D'an jinjina kai tayi tana share hawaye kafin tace "Toh nidai kawai ayi maganar auren mu cikin satuttukan nan pls Naseer...."
D'an murmusawa yayi kafin yace "Da zaran Mamy ta d'an sami sauk'i za'ayi batun auren mu insha Allah, kinji koh.... Now wipe those tears, banson ganin su...."
Naseer gwani ne wajen tsara kalaman da zai mantar da ita duk wani bak'in ciki take taji sanyi ya mamaye mata illahirin zuciyarta sai faman masa shagwab'a take shi kuwa hankalinsa da tunanin sa gaba d'aya naga halin da Salma ke ciki, biyeta kawai yake badon yaso ba
Koda Azeema ta kai Salma d'aki saida ta kuma kitsa mata abubuwa gameda Affan d'in, kafin ta fice ta barta don yin wanka...
Azeema na sauk'owa parlor ta tarar da Affan zaune da alama jiran sauk'owan nata yake.... Saurin mik'ewa yayi yana tambayanta jikin Salmar...
Azeema ta d'an ware dara-daran idanunta had'i da d'an bud'e hannaye kafin tace "Well, she's fine...."
"Kin tabbata bata buk'atan wani abu....?" Ya kuma tambaya yana duban Azeemar
Gyad'a masa kai tayi kana taci gaba da fad'in "Idan akwai abinda take buk'ata bai wuce danginta ba, ko nace Naseer don shine yace zai samo mata su, yanzu ma maganar da ta gama fad'a min kenan, naga alama akwai shak'uwa sosai a tsakanin su kodayake bari dai nayi shiru kar na shiga hurumin da ba nawa ba...." ta k'arashe tana rik'e lips d'inta da yatsun hannunta
Affan yayi shiru yana nazarin kalaman Azeema, tabbas maganar ta zai iya zama gaskiya, amma ai shi yasa Naseer d'in ya nemo mata 'yan uwanta, tunda yanzu ya dawo ya kamata Naseer yayi nesa da Salma.... Lallai dole ya taka masa birki. Bai kuma bin takan Azeema ba sai ficewa da yayi cikin sauri ya nufi waje yanda ya hangi Shareefah da Naseer d'in tsaye gefen furanni
Naseer na hangosa ya soma takowa yana tambayar sa yaya Salma take....
Affan da Shareefah suka kalli juna kafin Affan d'in yace "Captain let's have a little chat...." ya k'arashe sanda ya nufi jikin motar Naseer d'in..
Shareefah kuwa gida ta nufa don ta hangi Azeema na mata alama da hannu alamun ta taho, cikin sauri ta nufi Azeema don tasan akwai wata a k'asa...
"Naseer pls banaso mu samu matsala da kai akan Salma, bayan na d'auke ka aboki still kai d'in yaya ne a gareni koda ace baka neman Shareefah.... Na gode da duk d'awainiyar da kayi akan Salma, sannan inaso ka min favor guda, ka maida ragamar neman 'yan uwan Salma a hannu na sabida ni ya cancanta nayi... Kasan irin son da nake mata, nasan ka sani so pls kaja baya da ita kar kuyi shak'uwar da zai kaimu ga samun matsala...."
Murmushin k'arfin hali Naseer yayi kafin yace "Affan abinda kake tunani bashi bane, kuma bazai tab'a faruwa ba.... Sannan insha Allah zanyi yanda kace, zan mik'a maka ragamar nemo dangin Salma kaci gaba daga yanda na tsaya.... Insha Allah babu macen da zata shiga tsakanin mu har ta rabamu, and lastly ina maka fatan alkhairi...." Ya k'arashe fuskar sa d'auke da murmushi
Gaba d'aya sai nuayin Naseer d'in ya lullub'e Affan, gani yake tamkar bai kyauta wa Naseer ba.... Saida ya d'an dafi goshinsa kafin yace "Naseer ina fata ka fahimce ni pls..."
Murmushi Naseer ya kuma yi had'i da dafa kafad'un Affan
"Na fahimce ka Soldier, kar ka damu.. ... Yanzu ni gobe inada aiki da yawa da munje munga yanda abin zai kasance, sannan jibi ma akwai taro da za'ayi a Santana Corporation shima zuwan nawa na under probability don akwai possibility d'in rashin halarta ta satin nan aiki ne sosai a gaba na, so inaga I may not be able to make it , zan sanar da kai unguwar da aka kwatanta min ana zaton mutumin da ya tsince su a nan yake, idan yaso sai mukeyin waya kawai...."
Murmushi Affan yayi had'i da jinjina kai kana yace "Naseer.... Na gode...."
Naseer d'inma murmushi yayi lokaci guda ya soma zura Key jikin marfin motar sa yake tambayan Affan d'in yaushe za'a kai Mamy asibiti
Nan Affan yake sanar dashi sunyi waya da likitan yace gobe zaizo Bauchi daga Kano, idan yazo zaizo shi har gida ya dubata kafin aje ayi hoto...
Naseer ya jinjina kai had'i da mata fatan samun lafiya suka yi sallama kafin ya wuce gida...
Driving kawai yake amma hankalinsa kacaukam naga tattaunawar da sukayi da Affan, baisan Affan da Shareefah me suka hasasho ba har suke masa wannan zance mai kama da zargi.... D'an fuzar da iska yayi lokaci guda ya girgiza kai shi kansa bai isa yace ga abinda ke damunsa ba a halin yanzu...
*****
Deeni ya kuma karkata mirror dake mak'ale gaban motar yana dubanta, har yanzu kuka take maras sauti, sosai jikinsa yayi sanyi da ganin hawayen nata...
Murya can k'asa yace "Miss ina muka nufa....."
Cikin kuka take fad'in "Ban sani ba may be to hell....."
Deeni ya ware 'yan madaidaitan idanunsa wanda kwantaccen gashin gira ya k'awatasu kafin ya d'an girgiza kai ya kuma fad'in "Miss bansan abinda ya sameki ba amma kiyi hak'uri pls, idan akan video d'in nan ne I promise zan goge, but pls ki daina kuka... Kinfi kyau idan kina masifa da tsiwar da kika saba amma ba kuka ba...."
Goge hawayen idanunta tayi tana dubansa ta cikin mirror kafin tace "Do you think I'm beautiful...?"
D'ago idanu yayi yana dubanta ta cikin mirror d'in su duka suna kallon juna kafin ya saki murmushi da gefen bakinsa kana yace "Kind of....."
"Amma kana tunanin inada kyaun da nafi k'arfin wulak'anci namiji...?" ta kuma jefo masa wannan tambaya
Saida ya d'an kuma tab'e baki kafin yace "Ko wace mace tafi k'arfin wulak'anci as far as tasan martaba da daraja da Allah Ya mata a matsayinta na d'iya mace, sannan duk namiji dake wulak'anta mace he's not a real man... So ina muka nufa....?" ya k'arashe yana tafiya cikin slow
Ta kuma goge hawayen da suka zubo mata kafin tace "Koma inane ka kaini yanda zan mance damuwar dake cikin raina...."
Deeni ya k'ura mata idanu ba tareda ya furta komai ba...
*Sameena Aleeyou...*
[25/07 16:20] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*24*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
Waje ne mai tarin ni'imomi wanda ita kanta bata tab'a sanin akwai irin wajen a garin ba, ruwa sai kwaranya yake cikin duwatsu ga ciyayi sunyi kore shar gwanin ban sha'awa...
D'an d'ago idanu tayi ta kuma duban Deeni kafin tace "Yaya akayi kasan dakwai irin wannan waje mai dad'in zuwa da kuma dad'in zama...."
Gajeren murmushi yayi kana yace "Na kasance ina son keb'ewa wasu lokutan, idan na d'ebo damuwata nakan zo nan na zauna na d'an tsawon awanni ina kallon ruwa na kwaranya cikin ikon Allah nakan ji damuwar dake damuna ya ragu...."
Lubna tayi shiru tana sauraren sa sanda yaci gaba da jefa k'anan duwastu cikin ruwan...
"Kaima damuwar mace ke sa kaji kana son keb'ewa...?" ta tambaya idanunta k'uri akansa
Murmusawa ya kumayi had'i da girgiza kai kana yaci gaba da fad'in "Sam ba damuwar mace bane hasalima ban tab'a kasancewa cikin soyayyar wata d'iya mace ba koda yake....." Shiru yayi ya kasa ci gaba da magana sabida hawaye da suka ciko idanunsa
Jikin Lubna ya d'anyi sanyi a hankali ta furta "Kaima kayi experiencing heartbroken kaman yanda nayi....."
Deeni yayi murmushi wanda yafi kama da murmushin takaici kafin yaci gaba da fad'in "Worse than yours...."
Lubna ta d'an tab'e baki kana tace "Toh wai dama kai d'in har wani soyayya kake, a yanda kake d'in nan, ita budurwar taka batasan cewa kai driv......"
A fusace ya katseta da fad'in
"I'm not talking about girls, in fact I don't give a damn about them.... I'm talking about my Mum...." Hawaye yaci gaba da kwaranya masa sanda yake fad'in "She left me when I was very young, ta tafi ta barmu sabida tsananin jinya da mahifina ke ciki, I was only 12 then.... Na rik'e k'afafunta na rik'e hannayenta na rok'eta cikin kuka amma bata fasa k'udirinta ba, ta tureni tayi tafiyarta, tunda ta tafi bata waiwaye mu ba kusan shekaru goma shabiyar...lokacin da mahaifina ya soma jinya, Mama Tani ita ke kula damu har kawowa k'arfina.... Bansan soyayyan uwa ba sai nata... Ki fad'a min wannan baifi zafi da ciwo ba.... Tell me....!" Ya k'arashe cikin d'aga murya
Gaba d'aya jikinta sai yayi sanyi, tausayin sa ya cikata.. Kasa furta komai tayi ganin ya mik'e ya nufi mota.
Ta jima tana zaune a wajen cikin tsananin tausayin rayuwar Deeni kafin ta mik'e jiki babu k'wari ta nufi motar.. Sanda ta isa ta samu kansa kife saman steering wheel da alama har lokacin hawaye yake... Murya can k'asan mak'oshi ta soma fad'in
"Kayi hak'uri don Allah... Wllhi ba nufi bane na tuno maka wannan babban tashin hankali, tabbas nawa nafila domin kuwa bansan yanda zan kasance ba idan Innah tayi abandoning d'ina.... I'm sorry please..."
Bai tanka ta ba sai goge fuskar sa da yayi shima murya can k'asa yace "Ina muka nufa....?"
A hankali tace dashi "Gida...."
Cikin sauri yayi key wa motar suka bar wajen...
Har suka isa gida jikin Lubna a sanyayeye yake, saida taga tafiyar sa kafin ta shige gida don yau ko wajen Mama Tani bai lek'a ba... Tausayin sa sosai ya cika zuciyarta har saida taji tafi damuwa da tashin hankalin da ya shiga a yanzu fiye da wanda take ciki, da wannan tunani ta nufi cikin gida tamkar wacce ruwa ya shanye....
*******
Duk yanda Affan zaiso Salma ta saki jiki dashi tak'i sakin jiki dashi, kyautata mata yake fiye da kowa a cikin gidan.... Gashi Mamy sam bata son b'acin ran Affan sabida tuntuni fushinsa na nufin fushinta ne. ... Haka wasu lokutan take d'an dannewa idan taga yanda yake rawar k'afa akan Salmar, gashi ta lura sam yarinyar Affan baya gabanta, koda yake tasan taku ne kawai irin na 'ya'yan mayu, don babu d'iya macen da zatak'i Affan d'inta santalelen saurayi maiji da kyau da k'uruciya uwa uba ga nasara na rayuwa.... Tana nan tana hankalce dasu muddin taga Salma ta soma sakin jiki da Affan saita b'ullo masu ta hanyar da basuyi tsammani ba....
*****
Kallon Innah Naseer yayi a karo na biyu kana yace "Eh toh ba lallai naje taron ba don gaskiya inada aiki da yawa a gaba na..."
Innah tayi murmushin jin dad'i kana tace "Ah ai gwara ka tsaya kayi aikin ka don dai lunching shigo da kayayyaki da za'ayi ai ba sai ka baro aikin ka kaje ba, d'an uwanka ya rik'e amanar dukiyoyin mu gaba d'aya, sannan mu idan muka je ai ya wadatar...."
Naseer ya d'an murmusa kana yace k'warai kuwa Innah, zuwan ku ya wadatar...."
Dai-dai nan Alh Kabeer ya shigo fuska fal fari'a ya d'anyi hugging Naseer lokaci guda ya gaida Innah kana yace "Soldier ya batun lunching d'in namu, zaka sami halarta kuwa...?" ya k'arashe yana zama bisa sofa...
"Maganar da mukeyi da Innah kenan ka tarar, kasan aikina ya hanani sanin komai gameda Kampanin amma tunda kana nan sannan kaine shugaban kampanin ai inaga babu wani matsala koda ace ban sami halarta ba......"
Alh Kabeer ya d'an saka fuskar damuwa kaman da gaske kana yace "Amma gaskiya banji dad'i ba Captain, ya kamata ka dinga participating a hidiman kampanin nan, da yawan shareholders basu sanka ba, saidai suji sunan ka da manyan shares d'inka....."
Murmushi kawai Naseer yayi kafin yace "Toh Yaya amma dai still I'm not sure idan zanje...."
Innah tayi wuf tace "Kar kayi wasa da aikin ka, kowa yasan ba sabida abun duniya kake aikin da kake ba sai don taimakon Al'umma wanda nasan harta ni mahaifiyarka ina samun ladan don haka bana fatan abinda zai kawo maka mishkila a aikin ka, idan baka da time kar ka tak'ura kanka kaji....."
Wani tunani ne ya gifta kwanyar Naseer, meyasa suke haka... Meyasa yake ji can k'asar zuciyarsa sam bai yarda da mahaifiyar tasa da d'an uwansa ba.... Tak'aitaccen murmushi yayi yana ayyana abubuwa da dama cikin zuciyar sa....
Har ya bar wajen Innah bata daina watsa wa Alh Kabeer harara bar, mik'ewa tayi ta masa alama da ya biyota d'aki... Cikin sauri ya take mata baya... Suna shiga ta watsa masa mari maiji da kafiya...
"Ashe kai har yanzu dolo ne, banda dak'ik'anci da sakarci yaushe zamu barsa ya halarci taron nan muddin muna so mu sayar da kason sa cikin dukiyar, ayi rubutu da komai a nuna cewa shi ya saida tunda gaba d'aya ba wani sanin wainar da ake tuyawa a kampanin yayi ba, kai kuma da shashanci irin naka ka fara k'wad'aita masa shiga cikin hidiman Kampanin a dama dashi..."
"Amma dai Innah....."
"Rufe min baki sauna kawai, duk wannan fad'i tashin da nakeyi ba sabida kai da ni nakeyin su ba, tunda sanin kanka ne kwabo bamuda shi a wannan Kampanin, dukiyar Naseer da Lubna ne, kuma shi kad'ai zamu kawar mu sami kwanciyar hankali na har abada....."
Alh Kabeer yaci gaba da sosa fuskar sa yana hura hanci yanajin Innah ta kusan kaisa bango da marin da take sharara masa don yana gab da ya soma ramawa...
*******
A waje ya hangesu itada Daddy fuskokinsu cikeda annuri da alama Daddy na matuk'ar jin dad'in hirar nata, saida ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin ya tunk'aresu.
Daddy na hangosa ya fad'ad'a murmushin sa.....
"Affan k'araso mana....." Ya fad'i sanda Salma ta juyo tayi duba guda ma Affan d'in..
"Daddy barka da hantsi...." Ya fad'i sanda yake zama gefen darduman.... Lokaci guda Salma ta mik'e tana k'ok'arin barin wajen...
Affan yayi saurin bud'e murya yace "Daddy dama so nake na d'auki Salma mu tafi unguwar da Family d'inta suke na samo su....."
Ai ko gama rufe baki bai ida ba Salma ta dawo ta zauna dirshan a gabansa tana fad'in "Don Allah da gaske, da gaske kakeyi, ka gano yanda suke... Zaka d'aukeni muje....." Gaba d'aya ta daburce sabida murna kallon Daddy tayi lokaci guda kana tace "Daddy pls kayimin izini na bishi naje na gansu kaji Daddy...."
Daddy sai murmushi yake ganin yanda lokaci guda farin ciki ya cikata... Ya kuma kallon Affan wanda annurin fuskar sa ya kasa gushewa..
A hankali Daddy Ya jinjina mata kai kana yace "Na maki izini Salma, sannan nayi farin ciki sosai...."
Cikin sauri ta mik'e tana fad'in "Zan shirya yanzu....." bata jira cewar su ba ta shige cikin gida harda d'an tsallen murnan ta...
Daddy ya juyo da dubansa ga Affan kana yace "Affan Allah Ya maka albarka k'ok'arin da kayi..."
Affan yana murmushi yake furta "Ameen Daddy, for Salma zan iya yin komai...... Murmushi kawai Daddy yayi ba tareda ya furta komai ba....
Mamy na zaune saman carpet k'afafu mik'e saman kushin Salma tazo ta shigeta a guje, saida ta zabura
"Ke! Ke.... Meye haka dangin mayu....."
Burki Salma tayi ta kuma dawowa da baya had'i da d'aura hannu a kunkumi kana tace "Ki kwantar da hankalin ki yau d'in nan zan bar maku gidanki, idan yaso ki dafa ki cinye kinga kuwa maita ya k'are a kanki......"
Zabura Mamy tayi tana huci don babu halin tashi ta shiga fad'in "Ke ni kike fad'a ma haka, munafuka annamimiya..." ta k'arashe tana k'ok'arin rarumo apple cikin plate zata wurga wa Salma dai-dai nan Affan ya shigo.... A hankali ta maida hannun ta ajiye tana mai ci gaba da watsa ma Salma harara... Salma kuwa kashe mata idanu guda tayi kafin ta nufi stirs...
Zama Affan yayi gefen Mamy cikeda farin ciki yanai ma Mamy sannu da jiki.... Koda suka zo fita shida Salma saida Mamy tayita kururwa tana fad'in Salma ta lashe mata kurwan d'a... Azeema da Shareefah kuwa dama basu nan sun tafi rage sayayyan kayan auren Shareefar.....
Har saida Daddy Ya shigo ya saita Mamy kafin aka samu tayi shiru, amma kam shakka babu harta mak'ota sun jiyo kururwar Mamy...
******
Ya gama shirinsa tsaf cikin business suit sosai shigar ta amshe sa, nan ya kira yayan nasa ya sanar dashi a masa reserving seat d'in sa don yana nan tafe...
Alh Kabeer zufa ta shiga keto masa ta ko ina, cikin sauri ya d'aga wayarsa ya kira layin Innah amma bata d'aga ba, don wayar tana silent sannan tana cikin jaka, yayinda suke tafe ita da Lubna a cikin motar zasu tafi taron, su duka biyun suna make a bayan motar, Innah sai magana take ma Lubna amma hankalin Lubna Sam bai tareda ita, gaba d'aya tunanin Deeni take don yau kusan kwana uku kenan bai zoshi aiki ba gashi wani ikon Allah ta kasa bud'an baki ta tambayi Mama Tani dalilin rashin zuwan nasa...
Hankali tashe ya kira layin Goga....
"Hello Goga kana jina "Bana so ya halarci taron nan, do everything possible kai idan ta kama ka kashesa ne ka kashe sa, zuwansa taron ka iya kawo cikas ma rayuwata...
Goga ya jinjina kai kana yace "Amma dai Mai gida kasan Soja ne kisan sa akwai had'ari babba a ciki..."
"Allah yasa bakin ak47 ba soja ba...." Sai kuma yayi shiru tamkar mai tunani kafin yace "Gaskiyar ka ne, ka b'atar dashi na k'ank'anin lokaci har zuwa sanda taron zai watse..."
Goga yace "An gama mai gida...."
Suna gama wayar Jamila ta fito daga toilet na cikin office d'insa tana mai goge fuskar ta da hand towel... Murmushi ya sakar mata kafin yace "Ki ida shiryawa Laminu ya ajiyeki a gida..."
Tana mai fente fuska da kwalliya take amsa sa.
"A'ah take your time, ba sauri nake ba idan kun gama taron ku ka ajiyeni a gida kasan ba kasafai nake son driver d'inka na kaini waje ba...
Bai ce mata komai ba sai kunna sigari da yayi had'i da ficewa... Jamila ta bisa da kallo don ta lura tamkar wani abu na damun sa.....
Suna tafe a mota sai faman janta da hira yake tana amsa masa jifa-jifa, don ita bata da burin da ya wuce ta ganta gata ga 'yabuwanta...
Affan yanason kiran Naseer ya tambayesa exact location d'in amma baiso Salma ta gane da taimakon Naseer d'in ya samo mata 'yan uwanta. Pakawa yayi gefen kwalta wajen masu recharge card yace da ita bari ya d'an saya kati.... Jinjina masa kai kurum tayi had'i da sakin murmushi don sai yanzu take ganin tsan-tsan kindness d'in Affan...
Yana sauk'a wayar Naseer ya shiga nema..
Naseer ya d'an rage speed kafin ya d'aga wayar...
Daga d'aya b'angaren bayan sun gaisa Affan yace "Captain kana ina ne....?"
Naseer yana k'ok'arin shiga kwana yake fad'in "Santana Corporation na nufa......"
Bai ida rufe baki ba ya hangi mutum tsaye gabansa....." Cikin sauri ya danna horn had'i da katse kiran Affan d'in yana fad'in "Zan kiraka back pls....."
"Naseer, Naseer..." Inaa ya katse kiran... Affan ya d'an fuzar da iska yana tunanin abinyi... Zuciyarsa ta basa ya tafi Santana Corporation ya sami Naseer kawai don yau alk'awari ya d'aukar ma kansa sai ya cika ma Salma burinta na samo 'yanuwanta
****
"Malam lafiya ka tsaya tsakiyar hany......" baikai aya ba yaji sauk'an katako a k'eyarsa
Duru-duru ya soma gani sanda suka fincikosa daga cikin motar da k'arfin gaske Goga ya jawo shi ya watsar sa saman kwalta, da shike titine da mutane basu faye bi ba sai jifa-jifa hakan ya basu daman ci gaba da dukan Naseer..
Naseer na gani duru-duru hakan bai hanasa yin azama cikin dabaru tasu ta sojoji yakai wa Goga wata naushi a gefen kunne....
Tuni goga ya rik'e kunnen sa don tuni ya soma jiyo sautin jijiyoyi tamkar suna tsinkewa cikin kunnuwan sa...
Naseer ya mik'e yana goge jinin dake fitowa a hancisa kafin ya kauce cikin sauri ganin goga ya kuma rarumo katakon zai runtuma masa...
Sharb'e k'afan Goga yayi ya shiga masa dukan sa'a..... Lokaci guda ya mak'ure hannayen sa waje guda had'i da matse kansa jikin mota...
Goga sai k'ak'ari yake yana son k'watar kansa amma ya kasa...
Naseer yaci gaba da fad'in "Ka fad'a min wa ya turo ka...."
Goga ya kasa magana sai tattamke idanu yake....
"Auw bazaka fad'a ba koh...." cewar Naseer dake k'ok'arin saka hannu a suit pocket d'insa lokaci guda ya ciro 'yar k'aramar bindiga yana fad'in "Zaka fad'a ko sai na fasa kanka...?"
Goga da tuni jikinsa ya soma rawa yaga mutuwa kusa tuni ya soma bawa Naseer hak'uri yana fad'in "Kar ka kasheni dan Allah... Wllhi zan fad'a amma don Allah ka min alk'awari bazaka sanar dashi ba wllhi idan yasan na fad'a maka cewa shi ne zaisa a kasheni duk yanda na shiga...."
Naseer ya kuma manna bakin bindigar a k'eyarsa yana fad'in "Ka fad'a min waye ya turoka...."
Goga kuwa jin Naseer yayi kicking bindigar murya na rawa yake fad'in "Alh Kabeer... Alh Kabeer Santana, shi yace nayi kidnapping d'inka don kar Kay samu halartan taron da za'ayi a Kampanin... Dan Allah kar ka kasheni Yallab'ai....."
Bibbiyu ya soma gani duniyar ta shiga juya masa har baisan sanda Goga ya k'wace ya fece a guje ba
Sunan yayita nanatawa a zuciyar sa Kabeer Santana, his very own brother..... Shi ya turo a bugesa a sacesa a hanasa zuwa taron.... Toh me yake shiryawa,...? Kasa samun amsar tambayar sa yayi don gaba d'aya tunaninsa ya juye... Kenan ya jima yana shirya masa abu ba tareda saninsa ba, a iya rayuwar sa ya zaci Innah ce kawai bata k'aunar shi ashe harda d'an uwansa.... Toh meyasa haka, lallai ya kamata ya dad'ayin taka tsan-tsan don gano musabbabin abubuwan da suka jima suna faruwa a rayuwar gidansu... Cikin sauri ya shige motar sa ya nufi Kampanin
*****
Batasan yanda suka zo ba amma ta lura tamkar taro ake.... Affan ya d'an dubeta kafin yace "Barin karb'i sak'o a nan sai mu wuce koh...."
Salma cikeda tsoro take dubansa ganin mutane da yawa sai faman shige da fice suke kafin tayi rau-rau da idanu tace "Nidai binka zanyi wllhi tsoro nake ji."
Affan ya d'an murmusa ganin ta soma sakin jiki sosai dashi kana yace "Shikenan sauk'o muje toh..."
Babu musu ta bud'e marfin motar ta sauk'o cikin sauri..
Suna dai-dai farfajiyan Kampanin a dai-dai lokacin da Jamila ta fito da niyyan tafiya don Ilham ta kirata ta sanar da ita Falaq nata kuka da alama bata da lafiya, shiyasa Jamila ta fasa zama ta fito da niyyan tafiya...
Salma daketa faman bin tafka-tafkan benayen da kallo kaman daga sama saiji tayi ta bangaji mutum..... Muryar mace taji tana mata sannu.... Cikin sauri ta d'ago don sam bazata tab'a mance mai irin muryar ba...
Mutuwar tsaye tayi tana dubanta.... Murya cikin wani irin rawa ta furta "Addah...!"
Dai-dai lokacin Jamila ta bar tattara jakanta da ya watse a k'asa ta d'ago tana duban Salmar itama...
*Sameena Aleeyou...*
[25/07 16:20] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*25*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
*Fatan Alkhairi *FATYMA ALEEYOU... Na gode da yabo da kuma addu'o'inki na alkhairi a gareni Allah shi bar k'auna馃馃徏馃挄*
Kasa tab'uka komai sukayi su duka biyun sai hawaye dake gangarowa daga idanun su.... Affan da yayi mutuwar tsaye yana kallon ikon Allah a hankali ya rage tsayinsa dai-dai fuskar Salma yake fad'in "Kin santa ne wacece ita....?"
Gaba d'aya Affan bai gane Jamila ba duk da ya tab'a ganinta sau d'aya sanda suka kai ziyara gidan gona shida Daddy..... Wannan tafi zubin asalin 'yan gayu bazaka tab'a tunanin tayi rayuwan wahala a baya ba
Salma bata iya amsa sa ba don tuni Jamila ta rungumeta cikin wani irin kuka had'i da shauk'i.....
Cikin kuka taci gaba da fad'in "Addah wllhi na nemeku kuma ku nake kan nema wllhi daidai da rana guda daidai da dak'ik'a guda tunanin ku bai tab'a gushe min ba..... Addah ina sonku wllhi kar ku tab'a tunanin ban nemeku ba....." kuka yaci k'arfinta..
Affan gaba d'aya jikinsa sanyi yayi don sai yanzu ya fahimci tabbas wannan 'yar uwar Salma ce..... Murya can k'asa yake ambaton sunan Salma don kuwa sosai yake jin rad'ad'in kukan da take yi ...
Cikin sauri Jamila ta d'ago tanai mata wani irin duba daga ita har Affan d'in kan kace me ta d'auke Salma da wani irin wawan mari....
Salma ta bita da kallon mamaki lokaci guda Affan ya harzuk'o yana fad'in "Ke lafiyar ki zaki mareta...."
Jamila tana huci ta shiga jijjiga Salma tana fad'in "Salma waye wannan ki fad'a min wanene shi.... Salma me kika maida rayuwar ki.... Namiji, namiji Salma..... Ki fad'a min waye shi...."
Daga Salma har Affan mamaki ne ya cikasu, suna binta da kallo
Hawaye na gangaro ma Salma ta shiga girgiza kai ba tareda ta iya furta koda kalma ba....
Affan ya yunk'uro yana fad'in "Don't hurt her again... Is not what you think, ba abinda kike tunani bane.. Sunana Affan Ali Safwan, I know you're familiar with the name, mu muka tsinci Salma.... A gidan mahaifina take zaune sannan a kullum burinta ta kuma had'uwa daku, babu cutarwa tsakanin mu da Salma, cikin amince da burin taimaka mata wajen sake had'uwa da danginta muke zaune da ita... In fact dalilin da yasa kika ganmu yau a tare ba komai bane illa neman ku da muka fito yi..... Pls don't hurt her kinji, and don't think otherwise...." Ya k'arashe murya can k'asan mak'oshi....
Jikin Jamila yayi wani irin mugun sanyi tamkar an tsunduma a fridge tabbas sai yanzu ta gane Affan, zuciyarta ta kuma karaya don ita a tunanin ta Alh Ali Safwan idan ya samesu takunkumi zai kafa masu, hasalima ashe tuntuni suke neman su.....
A d'ari da sittin Maina yayi burki yana hango Jamila da Salma, tabbas bai mance fuskar Salma ba sanda ya umarci yaransa su bita su kashe ta.... Da baya da baya ya dinga komawa har saida ya isa ya kirawo ogansa Kabeer Santana
Motar su Innah tana ida parking Naseer na shigowa shima....
Ai Lubna tunda ta hango Affan tsaye da 'yanmata ta fice a tamanin ta nufi wajen tana fad'in "Affan dama akan wad'an nan shirgin kake wulak'antani.... Gwada mini wacece budurwar taka cikinsu yanzu na watsar mata da hak'wara..." ta k'arashe tana kwab'e takalman k'afarta tamkar zararriya....
Cikeda tashin hankali Affan yake fad'in "Lubna don't.... Don't make a sin here....."
Inaa Lubna ko sauraren sa batayi ba tayi kan Jamila don ta lura tafi gayu, tuni Salma ta shiga k'ok'arin kare 'yar uwarta....
Dai-dai lokacin Naseer ya k'araso a tamanin yana k'ok'arin janye Lubna da bakinta ya gaza mutuwa....
Alh Kabeer kuwa da Maina daga yanda suke lab'e suke hango show d'in...
Hankulan mutane tuni yayi kansu, Lubna sai fincika take tana fad'in "Ya Naseer ka barni na cire masu hak'wara wllhi irin karuwan nanne masu yawon neman maza ma'aikata ma'aikata
Da k'yar Naseer ya janye Lubna yana fad'i ma Affan su tafi don Allah..... Sam baima gane Jamila ba hankalinsa na kan Salma da gaba d'aya hawaye ya wanke mata fuska....
Cikin sauri Jamila ta janye hannun k'anwarta suka fice a wajen Affan ya take masu baya...
Innah kuwa sam batayi zaton Naseer zaizo sa wajen ba.... Wayarta ta ciro ta shiga neman layin Alh Kabeer sanda Naseer ya janye Lubna suka nufi can wani gefen....
"Pls ku bari na kaiku gida...." Cewan Affan da gaba d'aya baiji dad'in abinda ya faru ba....
Uwar harara Jamila ta watsa masa kafin tace "Kaga Malam abunda kukayi na alkhairi Allah Ya saka maku amma k'anwata bazata koma gidan ku ba, wayasan wannan mahaukaciyar budurwar taka me zata mata.... Shige mu tafi Salma ta k'arashe tana kuma fizgan Salmar....
Affan na girgiza kai yasha gaban su kana yace "Kiyi hak'uri wllhi idan na koma babu ita hankalin Daddy zai tashi... Don Allah...."
"Dakata....!" Jamila tayi saurin katsesa kana taci gaba da fad'in "Don't insist don Wllhi bazan kuma barin Salma tayi nisa damu ba... Kai ni banma yarda da kai a kusan k'anwata ba...."
Affan zai kuma yin magana Salma ta girgiza masa kai kana tace "Ba komai na gode da taimakon ka, ka barni nabi 'yar uwata a yanzu na maka alk'awarin insha Allah zamu taho gaba d'ayanmu muyi ma Daddy godiya kaji...."
Kasa furta komai Affan yayi sai kallon da yake binta dashi.....
Yana nan tsaye a wajen tamkar gunki har suka shige adaidaita...
"Ki min shiru nace...!!!." Naseer ya kuma kasteta cikin tsananin daka tsawa kafin yaci gaba da fad'in "I thought nasihar da na maki ta shiga jikin ki, lafiyar ki Lubna...? Kinga abinda kikayi a bainar jama'a a Kampanin mahaifin ki.... Haba Lubna wannan ba d'abi'arki bace.... Look ki saurare ni da kyau ko a ina na kuma jin kinyi abu makamanci haka zanyi punishing d'inki kina jina...."
A hankali ta shiga gyad'a kai baki a ture kafin tace "Yaya kayi hak'uri bazan sake ba insha Allah...."
Naseer bai ce komai ba har lokacin a dake yake dubanta kafin ya girgiza kai ya fice cikin sauri ya nufi waje don gano wani hali Salma ke ciki...
Lubna ta goge hawayen ta lokaci guda ta shiga neman layin Deeni tana addu'an Allah yasa ya d'aga wayar ta don ta fasa zama wajen taron gwara tayi tafiyar ta gida.... Ta kuwa yi sa'a ya d'aga.... Yana d'agawa ta fashe masa da wani irin Kuka..
Hankali tashe ya mik'e zunbur yana tambayarta abinda ke faruwa....
****
Affan ya hanga yana k'ok'arin zura Key wa mota, ya k'arasa cikin sauri...
Innah da Alh Kabeer daga saman bene ta window sukayi k'uri ma Affan da Naseer suna sauraren tattaunawar nasu...
"Naseer I'm afraid.... Ina tsoron kada na rasata kenan...."
Naseer ya d'an shafi sumar sa kafin yace "Affan, bazasu kuma b'acewa a garin nan ba, kuma nasan zasu zo har gidan Daddy maybe suna buk'atan keb'ewa ne da juna na d'an lokaci, abunda sukayi going through abu ne mai matuk'ar wahala da tsananin tashin hankali..... Amma kace min 'yar uwar tata daga compnayn nan ta fito... Toh me take yi a nan...?" Ya k'arashe fuskar sa fal alamun tambaya
D'an fuzar da isaka Affan yayi had'i da bud'e hannaye kana yace "I don't know,.... Ko maybe aiki take a nan d'in...."
Shiru Naseer yayi tamkar mai nazari kana ya d'an dafa kafad'an Affan yace "Kar ka damu Affan insha Allah komai zai tafi normal. What's important now shine Salma ta sami family d'inta hankula zasu kwanta sannan I'm quite sure she's happy now...." Ya k'arashe yana murmushi mai bayyana hak'wara wanda shi kansa baisan yana yi ba...
Affan ya bisa da kallon mamaki ganin murmushin ya kasa gushewa a fuskar Naseer... K'ak'aro murmushin shima yayi kana yace "Yeah... Yeah she's happy..... Ni zan wuce soldier sai munyi waya.."
Naseer ya jinjina kai suka kuma yin masabaha kafin Affan ya shige motar sa ya bar wajen...
Innah ta dubi Alh Kabeer baki sake shaye da mamaki sanda ya gaya mata ai ya tura yaronsa ya sace Naseer da alama mission d'in bata yuwu ba.....
Hannun ta har na rawa ta d'aura masa mari mai ji da lafia tana huci take dubansa....
Rik'e da fuskar sa yake dubanta...
"Kai wani irin babban dolo shashasha ne ban sani ba, kullum ina nusar da kai hanya baka fahimta, na jima banga babban dak'ik'i dolo irinka ba.... Banda wauta ta yaya zaka tura wani lusari kace ya yak'i Soja... Toh yanzu sai ka sanar dani yaya suka wanye... Kai wannan dolancin naka shi zaisa duk wani sirrin mu ya bud'e..... Kai ni bari kaji na fad'a maka kud'ad'en nan ma kai nake yak'in su idan don tani ce ban damu ba na rasa ko kwabo muddin zanga Naseer cikin azaba uk'uba da tsananin masifa wanda zaisa DUNIYAR MU ta zame masa tamkar jahannama, banida burin da ya wuce d'aukan fansa gashi kana yunk'urin ruguza min duk wasu shirye-sgiryen da nake shirin yi... Wllhi tallhi kayi sanadin da har Naseer ya fahimci cewa ba nice na haifesa ba wllhi sai na k'ona komai na Kampanin nan kowa ya rasa, nasan bakada mafarkin da ya wuce mallakar wannan Kampani kai kad'anka..."
Kafin ya sami zarafin magana Maina ya turo k'ofar Office d'in yana rarraba idanu yana dubansu yake fad'in "Yallab'ai anfa soma gudanar da taro da umarnin Naseer don gani nayima tuni ya d'ale stage ya soma speech...."
Innah da Alh Kabeer suka dubi juna a tare... A tamanin suka fice suka nufi hall d'in...
Idanu hurhud'u sukayi da Naseer sanda suka shigo hall d'in.... Ganinsa a haka ba k'aramin fad'uwar gaba ya sauk'ar masu ba...
Naseer kuwa hankali kwance yaci gaba da gudanar da speech d'insa wanda tuni ya mutane sun shiga rattaba masa tafi jin yanda yake magana da kaifin hankali da tsan-tsan tunani... Daga k'arshe magana yayi akan Mazaje masu musgunawa matayen su a gidajen auren su, yayi jawabi kan matsaloli da DUNIYAR MU ta tsinta kanta a ciki, Ciki harda yanda iyaye sukayi watsi da tarbiyan 'ya'yan su bayan cewa 'ya'yan amana ce a garesu.... Idanun Alh Kabeer k'uri kan Naseer kafin ta dawo da dubansa ga Innah wacce itama shi take duba... Haka kurum zukatan su suka cika da tsoro gani suke tamkar Naseer martani yake maida masu a hankali.... Daga k'arshe addu'an alkhairi yayiwa mahaifiyar sa Innah yana mai fad'in kalan k'aunar da yake mata... Lokaci guda ya k'arasa har gaban ta yayi hugging d'inta waje ya kuma kaurewa da tafi..... Sosai Naseer ya burge illahirin mutanen dake wajen...
Gaba d'aya babu wanda ya nustu ya saurari speech d'in Alh Kabeer.... Daga bisani ne aka soma presenting sababbin kayayyaki da aka shigo dasu kampanin wanda dama mak'asudin taron kenan....
Koda aka kammala taron bai samu ya cimma Naseer ba don tuni yayi ficewar sa ya cika ma rigar sa iska don zai wuce airport k'arfe hud'u dai-dai ya d'auko Fawaz, shi kad'ai ne ya sanar dashi exact date d'in da zai dawo ko mahaifinsa Alh Kabeer bai sani ba ya dai sanar dashi dama cikin satin zai dawo amma bai sanar dashi rana ba... Naseer yana tafe yana tunanin rayuwar da duniya ta tsinci kanta ciki a yau, lallai dole ya d'an saka hankali gameda abubuwan da suke wakana a kampanin mahaifn nasa ba don tara dukiya ba sai don hakan zai taimaka masa wajen gano abubuwa da dama da yake son ganowa musamman yau da tarin employees a kampanin suka kawo masa koke-koken su wanda akasari akan d'an uwansa mai running Companyn ne wato Alh Kabeer.... Lokaci guda ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin ya maida hankalinsa kan tuk'in da yake yi...
Alh Kabeer ya jima yana tsaye jikin mota yana tunanin kalamai masu harshen damo da ya jiyo daga bakin Naseer.... Hankalin sa ya gaza kwanciya gani yake tamkar Goga ya sanar da Naseer shi ya tura sa... Watsa wa Maina mugun kallo yayi sanda ya bud'e marfin mota kafin yace "A nemo min Goga yanda ya shiga ya fita...." Bai jira amsar sa ba ya shige mota Laminu ya tada motar suka bar wajen...
Maina kuwa duk damuwar sa bai wuce yarinyar da ya gani d'azu ba, gashi Alh Kabeer bai tsaya sunyi zancen ba... Komai ka iya faruwa domin shakka babu itace yarinyar da suke farautar rayuwar ta...
******
Kasa shiga gidan tayi sai kallon databi 'yar uwar tata dashi jin mai gadi nai mata barka da dawowa Hajiya..
"Hajiya...!" Salma ta nanata a hankali kafin ta kuma duban Jamila tace "Addah wai shin a nan ne zanga su Inno dasu Ilham...? Addah gidan su waye nan d'in...?"
Hannayen ta Jamila ta kuma rik'owa ba tareda ta furta komai ba suka nufi cikin gidan...
Ilham ce rungume da Falaq ta taso ta bud'e masu sanda Jamila ta k'wank'wasa..
Fuskar Ilham d'auke da murmushi take fad'in "Addah sannu da dawowa...." Bata kai aya ba Salma ta rungume su gaba d'aya daga Ilham d'in har Falaq lokaci guda kuka ya kufce mata..
Ilham ma hawaye ne suka shiga gangaro mata ta shiga shafa fuskar 'yar uwarta... Tana murmushi tana hawaye take furta "Addah Salma, kece koh... Nasan kece...."
Taci gaba da shafa fuskar Salma tana mai ci gaba da murmushi had'i da hawaye ta kai hannu hannu gefen kumatun Salmar dake kuka da duka zuciyarta kana tace "Yeah... Dimple... No dimple..." Gaba d'aya sukayi dariya daga Salmar har Ilham d'in sabida wasan da suka saba kenan... Idan Ilham ta shafi fuskar Salma tace Dimples? sai Salmar ta amsa mata da no Dimples....
Lokaci guda suka kuma rungume juna...
****
Kallonta Deeni yayi a karo na biyu zuciyarsa na masa zafi kafin ya d'an bud'e murya yace "You know..... Just learn how to love your self... Meyasa zaki kuma koma mishi bayan duk wulak'ancin da ya maki... Dama dole ma ya maki wulak'anci kullum kina hanyar zuwa wajen shi....."
Mik'ewa tayi cikin kuka tana fad'in "Toh ni ce maka akayi yanzu ina son sa... Kawai ba ganinsa nayi da 'yan matan nashi bane... Just put your self in my shoes, idan kaine ya zakaji..."
Deeni baice komai ba sai kallon da ya bita dashi... K'yaleta yayi tasha kukan ta kafin yasa hannu a aljihu ya ciro hankee ya mik'a mata
Saida ta d'ago idanu ta dube shi kafin tasa hannu ta karb'a ta soma share hawayen ta..
With a cool voice wanda bata tab'a jin yayi irinsa ba ta jiyo shi yana fad'in "Miss you are a special woman, although bit annoying... But that doesn't mean bazaki sami namijin da zai so ki for who you are ba...the one who would treat you like a queen, cherish you, give you all the love that you deserve ..... And above all, zai d'auki duk wani shiririta naki...." Ya k'arashe sihirtaccen murmushi saman fuskar sa...
Sosai jikinta yayi sanyi lokaci guda ta sami kanta da maida masa martanin murmushin da yake mata...
Ganin ta masa k'uri yasa sa d'an ware idanunsa kana yace "So ki min alk'awari Affan ya zama tarihi a rayuwar ki...."
Tana mai murmusawa ta shiga gyad'a masa kai lokaci guda taji bakinta da zuciyarta suna furta "I promise you, na maka alk'awari insha Allah Affan is in the past....."
Har suka bar wajen Lubna bata daina jin wani irin yanayi ba, batasan meyasa ba kalaman Deeni sun sakata jin sanyi a zuciyarta sannan for once taji cewa ita mace ce mai kima... Batasan dalili ba amma tana jin kalaman nasa tamkar daga zuciyarsa direct suke fitowa...
Zasu wuce rumfar mai suyan doya da k'wai a gefen hanya ya d'an karkato kana yace "Miss idan an min izini zan tsaya na saya abinci a nan.."
Baki sake take dubansa kana tace "Street food..?"
Murmushi yayi kafin yace "Don dai baki tab'a ci bane amma akwai dad'i... Wait bari na saya maki kije gida kici kiji, gobe zaki bani labari sannan kullum idan zamu wuce I bet zaki soma cewa a tsaya a saya..."
Bai jira cewar ta ba ya fice a motar yana murmushi yana kallon yanda take yatsina fuska...
K'in karb'a tayi koda ya sayo saida ya marairaice mata fuska kafin ta sami kanta da karb'an ledar... Ganin yana kallon fuskar ta ta mirror ya sanyata sakin murmushi kafin tace "Na gode..."
Murmushin shima kawai yayi kafin ya maida hankalinsa ga driving...
****
Salma ta girgiza kanta a karo na biyu tana bin 'yan uwan nata da kallon tuhuma kana tace "Kunce min Inno zata fito yanzu, shiru shiru har yanzu yanzun batayi ba.... Don Allah ku k'yaleni ni na shiga na ganta...
Mik'ewan da Ilham tayi tana lalume take k'unshe kukanta ya sanya Salma damk'o hannayen Jamila tana fad'in "Addah ki sanar dani gaskiya.... Ki sanar dani yanda Inno ta take..."
Girgiza kai Jamila take hawaye na gangaro mata da k'yar ta iya furta. "Muyi hak'uri Salm...."
Bata k'arasa maganar ba Salma ta mik'e tana girgiza kai hannayenta k'unshe da bakinta lokaci guda ta zube saman gwiwoyin ta...
*Sameena Aleeyou...*
[25/07 16:20] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*26*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
Abubuwa da dama Salma ta shiga tunowa gameda mahaifiyar su, ta tuna nasihar da ta masu ana gobe za'a Far masu, ashe nasiha ce ta bankwana.... Inno Allah yayi maki rahama yakai haske gabarin ki ya sadaki da Baffah da alkhairi..... Gaba d'aya jikinta yayi matuk'ar yin sanyi jin mutumin da Jamila ke aiki a companyn sa shi ya ara masu wannan gidan kafin ya soma amsar kud'in haya a wajen Jamilar.... Sam wannan gida bai mata kama da ace na haya bane sannan ko za'ayi hayansa za'a zuba mak'udan miliyoyi ta ina Jamila zata sami wad'annan kud'ad'en, wani irin aiki take da har zata tara kud'i masu yawa haka.... Sauk'e ajiyan zuciya tayi sanda taji Falaq na k'ok'arin haurawa cinyarta sai faman gwalamniyar ta take, Salma ta murmusa kafin ta sa hannu ta d'auki yarinyar lokaci guda ta shiga hango fuskar Inno a fuskar Falaq.... Sosai Salma ta rungume Falaq wasu hawayen suna kuma zarya a fuskar ta....
********
Innah na tsaye saman window tana hango Deeni da Lubna yanda suka jera suna tafiya saikace wasu masoya.... Bata gama shan mamaki ba saida taga ya rakota har k'ofar shiga cikin gida sannan ya bata wani leda sukayi sallama.... Su duka biyun sai juyowa suke suna duban juna.... "Bala'i...!" Innah ta furta a hankali kafin tayi saurin sauk'owa k'asa ta tadda Lubna zaune saman sofa sai faman murmushi take da alama tayi nisa a duniyar tunani...
"Kee..! Lafiyar ki meye haka , wannan mirmushin fah..?" Innah ta tambaya tana mai dungurin Lubnar...
D'an sosa k'eyarta tayi baki a ture kafin kuma ta mik'e ta shiga juyi gaban Innah tana fad'in "Innah yace I'm special.... I never thought ya iya kalamai masu dad'i haka...."
"Shi Affan d'in....?" Innah ta tambaya tana zama gefenta...
Lubna ta yatsina fuska had'i da girgiza kai lokaci guda kana tace "Ni bance maki Affan ba...." Cikin sauri ta suri ledar doyarta zata shige Innah ta finciki ledar ta shiga shinshinawa tana yatsina fuska....
"Gidan uwar wa kika samo wannan....?" ta tambaya a dak'ile...
Baki a ture Lubna tace "Bani mana Innah, yunwa nake ji..."
Bata tankata ba sai warwarew ledar data soma yi ta shiga bin doyar da kallo.... Ta d'ago ta dubi Lubna...
"Gantalallen abincin kan titi shine zakije kici.... Haba ni nasan wannan shegen yaro akwai abinda ke dashe cikin zuciyar sa.... Toh wllhi barin gidan nan zaiyi...." ta k'arashe tana k'ok'arin ficewa lokaci guda ta shiga rangad'a wa Mama Tani kira... Lubna a tamanin ta take mata baya...
*******
Hannayen su rik'e cikin na juna su duka ukun lokacin da Salma taci gaba da fad'in "Addah zama a wannan gidan mu duka 'yanmata bai kamace mu ba.... Sannan shi wanda ya baki haya ko nace aron wannan gida bamusan manufar sa na yin haka ba... Don Allah mu tattara mu koma gidan Daddy koda Mamy zata tsangwame mu shine kawai tsirar mu...."
Jamila dake faman binta da mugun kallo fuzge hannunta tayi lokaci guda take fad'in "Mutumin da ya bamu wannan gidan bazai tab'a wulak'anta mu ba.... Sannan inada yarinya, ke ni bazan koma d'ofanuwa gidan wasu sunai maka kallon raini ba don na wuce wannan tuntuni... Sannan kuma babu yanda zaku tafi don nasan akan wannan yaron kike son zaman gidan.... Wato already kin fad'a ma soyayyar sa koh....?"
D'an fuzar da iska Salma tayi kafin tace "Addah kar ki kalli wannan batu nawa da wata fuska, sannan ni ba son Affan nake ba dukda shid'in ya sanar dani kalan soyayyar da yake min, amma ki sani zama babu garkuwa a tattare damu had'arine.... Addah mutane A DUNIYAR MU ba kowa ne zai taimake ka da zuciya guda ba wasu........"
Dakatar da ita Jamila tayi saurin yi da fad'in "Salma we are staying here, no one is leaving..... Na gama magana ki tashi ki rik'e hannun Ilham ku wuce d'aki akwai kayayyaki na a wardrobe ki zab'a wanda kike so ki saka....."
Shiru Salma tayi tana bin 'yar uwar tata da kallo, a hankali ta girgiza kai kafin ta mik'e ta tallafo hannun Ilham suka nufi stirs... Suna tafe Ilham take dannar 'yar uwar tata... Jamila ta rakasu da kallo har suka b'ace mata kafin ta sauk'e ajiyan zuciya....
Tana shirin mik'ewa taji knocking... Cikin sauri ta k'arasa tana tambayar ko waye don duk a tunanin ta Affan biyosu yayi..... Ganin Alh Kabeer ne ya sanyata sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kana ta d'an gifta masa ya shigo.....
******
"Innah wllhi Deen da Mama Tani bazasu bar aiki a gidan nan ba.... Kinji na rantse kika sallame su wllhi nima barin gidan zanyi....." ta k'arashe tana rik'e kunkumi
Innah ta bita da kallon mamaki ba tareda ta iya furta koda kalma bar... Eh lallai Lubna ta maidata Kaka sam bata shayinta ballantana shakkan ta... Toh kuwa gwara tun wuri ta salwantar da rayuwan wannan matsiyacin yaron da bata isa had'a iri da matsiyata ba.... Da wannan tunanin Innah ta shige tana huci... Lubna ta dawo da dubanta ga Mama Tani lokaci guda ta sakar mata murmushi kana tace "Mama Tani don Allah kiyi hak'uri kinsan halin Innah... And pls kar ki fad'a wa Deen about this...."
Murmushin k'arfin hali kurum Mama Tani tayi don itama kusancin Deenin da Lubnar ya soma bata tsoro... Tana tsoron kada su fad'a tarkon da bazasu iya tsallakesa ba.... Lallai dole yau taja kunnen Deeni, da wannan tunani ta ci gaba da aikinta don ta samu ta kammala da wuri ta tafi unguwar su Deenin....
********
Kaman wani tsohon maye haka ya soma shinshinata yana fad'in "Kitty I can't hold my self....."
Jamila taci gaba da ture sa a hankali take fad'in "No bazai yuwu muyi wani abu yau a gidan nan ba, k'anwata mai idanu yau tana gidan nan....."
"Haba Kitty kinsan dai idan ina tare dake sam bana iya rik'e kaina ki barni na rage zafi......" ya k'arashe yana kuma kai mata sumba....
Dai-dai lokacin Salma ta tsaya cak jikin staircase tana kallon abun tamkar almara... Addah Jamila 'yar uwar su.... Bakinta ya mata nauyi ta nemi kuka ta rasa, dirshan ta zauna a dogon corridor d'in d'akunan tana ganin duniya na juya mata, sai yanzu ta gane dalilin Jamila na marinta da tayi sanda ta ganta da Affan, ashe ita abunda take yi kenan, sai yanzu ta gane dalilin da yasa bazata bar wannan gidan ba.... Lokaci guda tunanin hud'ubar iyayen su a kullum kafin su bar duniya y shiga yawo a kwanyar Salma.... Tabbas A DUNIYAR MU akwai mutane kala daban-daban... Wato shi wannan shi ya taimaki su Jamila amma ba taimakon Allah da annabi ba saidon zai sami wani abu shima... Lokaci guda ta kuma tuna kalan taimakon da Soja ya mata da kariya da ya bata ba tareda ya nemi komai daga gareta ba, ta kuma tuno gwagwarmayar da suka sha a gidan Daddy da yanda halin Daddy gaba d'aya ya banbanta da na Mamy.... Sai lokacin hawayen k'unci ya shiga zarya a fuskar ta d'aya na bin d'aya.....
A haka Jamila ta isketa bayan sunyi sallama da Alh Kabeer kan cewa a hotel zasu ke had'uwa tunda yanzu Salma tazo....
K'irjin Jamila yayi wani irin yankewa ganin Salma zaune dirshan a wajen.... Zuciyarta ya shiga bugawa sauri sauri... Allah dai yasa babu abinda ta gani... Koda yake tunanin mutuwar Inno ce bai bar jikinta ba, wata zuciya ta rad'a mata haka....
A hankali ta durk'usa tana mai k'ok'arin kai hannunta jikin Salma take fad'in "Sistu hak'uri zamu......."
Bata kai aya ba Salma ta matsa gefe cikin wani irin kuka tana mai girgiza mata kai alamun kada tazo kusanta...
"Salma waike bakisan tawakkali bane....."
Salma ta d'ago tana binta da wani irin kuka kafin tace "Addah did you just say tawakkali..... Wannan shine aikin da kike yi...? Wannan shine rayuwar da kika zab'ar mana..? Addah Why....? Meyasa? Shin har kin mance rashin mahaifiyar mu..? Shin har kin mance hud'ubar da suka mana..... Ina zaki kai tarin zunubin da kike d'iba, wani irin cin amana kikayi wa Ilham.. Sabida bata gani sabida batasan abinda ke faruwa ba... Ina zaki kai cin amana da kikayi wa Falaq? sabida yarinya ce ita, bata san abinda ke wakana ba ba.... Addah ina zaki kai cin amanar da kikayi wa iyayen mu? Sabida basu a raye, sabida sun tafi na har abada.... Ina zaki kai cin amana da kikayi wa mahaliccin ki? Sabida baki ganin sa shiyasa kike ganin zakiyi duk kalan rayuwar da kika zab'a A DUNIYAR MU...? Toh ki sani wllhi yana kallon ki kuma zai tsai dake ya tambayeki daki-daki ranar da gabb'ai zasu bada shaida.... Addah kar ki bari shaid'an ya rinjaye ki... Kiji tausayin Falaq ki tausaya mana kada ki shafa wa rayuwar mu bak'in fenti.... Addah ki tuba don Allah wllhi Allah zai gafarta maki....."
Batakai aya ba Jamila ta mik'e tana wani irin kuka take fad'in "Enough Salma!! Ki sani banida zab'in da ya wuce na jefa kaina cikin wannan rayuwar.... I was desperate, ko ta wani hali zan iya nemo kud'in jinyar Inno a lokacin.... Masu taimako don Allah sunyi k'aranci A DUNIYAR MU...... Mazaje basu kyautawa mata a cikin gidajen auren su sai na kan kwalta.... Salma I'm doing this for us.... For us to survive, pls don't judge me Sis..." lokaci guda ta rik'e hannayen Salma tana mai ci gaba da kuka..
Fincikewa Salma tayi daga rik'on da ta mata tana wani irin huci hawayen k'unan rai na sauk'o mata take girgiza kai kana tace " Wannan bai isheki hujjaba ki sab'awa mahaliccin ki.... We're leaving this place, right now.... Ta wuce d'aki cikin sauri... Jamila tabi bayanta.....
******
Suna tafe a hanyar Airport suka zo dai-dai base d'in su Naseer nan Naseer d'in ya shiga nuna masa yana d'an masa wasu bayanai gameda barikin nasu..
Fawaz yabi ginin da kallo yayi matuk'ar kyau kana yace "Wow a gaskiya Uncle naji dad'i da akayi Base d'inku a garin nan sannan kaima ka dawo garin nan.... At least yanzu zamu dinga kasancewa tare..."
Naseer ya murmusa fuskar sa naga kwalta gaba d'aya Fawaz ya cikasa da surutu..... Komai ya gani sabo a garin sai ya tambaya kasancewar ya jima baya nan....
*****
"Salma pls kar ku tafi, don Allah kar ku tafi sistu I promise I'll provide for us...."
Fincike hannunta Salma tayi tana rungume da Falaq take fad'in "Wllhi bazan bari ki raini Falaq da haram ba...." ta kuma jawo hannun Ilham daketa faman tambayar su meke faruwa, ta daiji sai koke koke suke Salma na fad'in sai sun bar gidan...
Duk yanda Jamila tayi ta hana Salma abu ya faskara... Haka suka fice tana rungume da Falaq hannunta guda rik'e da Ilham... Zuciyarta wani irin zafi da k'una kawai yake mata...
Durk'ushewa Jamila tayi a wajen tana wani irin kuka....
Ilham na hawaye take fad'in "Salma wai meke faruwa ne, meyasa kuke b'oye mun abubuwa, meyasa muka tafi muka bar Addah Jamila... Zamu rasata kaman yanda muka rasaki a baya... Ina kuma yanzu zamuje... Salma don Allah mu koma wajen Addah bazan iya rayuwa babu Falaq ba kullum tare muke wuni....."
Salma tasa bayan hannu ta goge hawayen da suka zubo mata kafin tace "Gidan Daddy zamuje Ilham, sannan ga Falaq a tareda mu, Addah ma zata biyo mu nan bada jimawa ba kinji ki kwantar da hankalin ki...."
Ilham bata iya cewa komai ba sai jinjina kai da tayi zuciyarta k'unshe da tarin tambayoyi....
Har suka shigo gari Dr Fawaz bai daina cika Naseer da surutu ba, Fawaz akwai magana shiyasa ma kullum suke cikin fad'a shida Lubna, don baya ganin tayi yayi shiru sai ya tofah.. Ita kuwa tace ai rainata yayi dukda ya fita amma ita ai Aunt d'inshi ce...
Idanunsa ne ya hango masa ita tsaye bakin kwalta ga baby rik'e a hannunta ga kuma wata 'yar budurwa a gefenta... Gaban sa yayi wani irin fad'uwa, babban tashin hankalin shine hawayen da ya hango suna ambaliya a fuskar ta....
A hankali ya furta "Salmah..! "
Fawaz ya dasa aya wa maganganun da yake yi lokaci guda yabi uncle d'in nasa da kallo... Cikin sauri Naseer ya karya kan motar..
*Sameena Aleeyou...*
[26/07 13:18] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*28*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
K'iris ya rage Alh Kabeer bai saki fitsari a wandon sa ba sabida yanyin da yaga d'an uwan nasa, kana ganinsa kasan he's in guilty conscious, gaba d'aya sai zufa ta shiga tsaststafo masa jira kawai yake yaji ta bakin Naseer, shikenan Naseer ya capke Goga....
"So it was true.... Yaya da gaske ne ka fitar da flyers kasa an raba wa masu k'anan kasuwanci cewa zasu iya shigar da dukiyoyin su komin k'ank'antar kaso Santana Corporation nan da zagayowar shekara zasu kwashi ninkin ba ninkin kud'ad'en su.... Yaya why.. Meyasa kayi haka....?"
Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya Alh Kabeer yayi don har wani sanyi yaji na ratsa sa jin da wani batun daban Naseer yazo masa
K'ak'aro murmushi yayi kafin yace "Haba Naseer kaima kasan bazanyi abinda zai cutar da Al'umma ba, baka fahimci abin bane ko nace su wanda suka sanar da kai basuyi yanda zaka fahimta ba...."
Naseer ya masa k'uri kafin yace "What I don't understand shine kud'in ruwa kakeda niyyan basu ko me...?"
Alh Kabeer ya murmusa kafin yace "No Naseer shiyasa nace baka fahimta ba, baka saba business ba baka san abubuwa da dama da suke wakana ba... Wllhi abinda nayi sabida ci gaban mutanen gari nayi kuma ai dukiyar tasu investing za'ayi a companyn nothing like kud'in ruwa.... Naseer wllhi Allah yaga zuciyata da niyyan taimako nayi ba da wani abu ba...."
Naseer ya jinjina kai lokaci guda yana karantar sa kafin yace "Baka tunanin idan wani abu ya sami dukiyar su hakan ka iya jefa familyn nan cikin had'ari.... What if suka maka turen a kashe ka....?"
Alh Kabeer ya zaro idanu yana duban Naseer da yayi maganar hankali kwance, kana ya d'an dara
"Naseer hakan bazai tab'a faruwa ba, ka kwantar da hankalin ka...."
Murmushi Naseer yayi yana dubansa kana ya d'an bubbuga kafad'un Alh Kabeer yayi shigewar sa ba tareda ya k'ara furta komai ba.... Alh Kabeer ya bisa da kallo har ya b'ace ma ganin sa...
*****
"Zahraddeeni nidai na fad'a maka, ka tsaya a matsayin ka kada kayi abinda zai janyo mana sallama daga ni har kai...." ta k'arashe tana rik'e kunnenta alamun jan kunne
Still murmushi ne saman fuskar Deeni, hannunta ya rik'o kana yace "Mama Tani bazan iya ce maki zan daina tunanin Lubna ba, sannan bazan iya yin nesa da ita ba...."
Kallo kurum Mama Tani ta bisa dashi kana tace "Eh lallai naga alama, Deeni! Deeni!! Deeni!!! Na kiraka sau uku idan ban b'ata lissafi ba... Toh wllhi ka iya kanka, nidai na gargad'e ka tamm...." ta k'arashe tana bubbuge mayafin ta had'i da yafawa
Mik'ewa shima yayi yana murmushi yana wani sosa kai yake fad'in "Har zaki koma, dan Allah kice mata ina gaisheta sannan nayi kewart....."
Baikai aya ba ta kai masa duka yana kaucewa had'i da yin dariya..
"Ja'iri zaka sani ne, ana ce maka ga gabas kana duban yamma koh... Toh wllhi ka fita idanu na..."
Deeni ya kuma murmusawa lokaci guda ya k'araso ya rungume ta ta baya kana yace "Yaya za'ayi na fita idanun Mama ta, nafiso kullum na zauna cikin idanun ki, sabida nasan nine dai sanyin idaniyan ki..."
Murmushi tayi lokaci guda ta rungume shi itama kafin tace "Allah maka albarka Zahraddeni..."
Amsawa yayi da ameen still murmushi saman fuskar sa...
*******
Washe gari da sassafe kafin ya tafi office ya nufi office gidan Jamila ya soma biyawa yaga k'anwarta da Maina yace itace tabbas yarinyar da yaci karo da ita sanda aukaje banka ma gidan wuta....
Ya jima yana knocking ba'a bud'e ba har yayi tunanin ko basu ciki ne, Mai gadi ne yake sanar dashi ai jiya wata tazo ta tafi dasu amma yana tunanin Hajiya ita kad'aice a ciki... Alh Kabeer ya jinjina kai yana nazarin kalaman Mai gadin kafin yaci gaba da bugun k'ofar, Da dai ya gaji da bugu da danna bell ya k'are ya shiga murd'a handle d'in aiko Yana tura k'ofan sai kuwa ta bud'e...
Kallo yabi gidan dashi yaji tsit... Nan ya shiga kiran Jamila tamkar yanda ake kiran Mage
"Mus mus mus... My Kitty... My Kitty ina kike ne.... Ina kika shige?" yaci gaba da haurawa stairs yana mai ci gaba da kiran nata....
Hango k'ofar d'akinta yayi a bud'e ta tak'ure saman gado sai kuka take, hannayen ta rungume da 'yar rigar Falaq.... A tamanin ya shige ya haye saman gadon ya d'agota ya rungume jikinsa yana fad'in "Haba Kitty meyasa kike kuka haka salon ki haifar wa kanki zazzab'i, look kinsan bazan iya ganin ki cikin wannan yanayi ba, gaya min meke damunki...."
Kuka ta kuma fashe masa dashi tana fad'in "Duk sun tafi, sun tafi sun barni, sun tafi da Falaq, sun tafi da farin ciki na..."
Dad'a kwantar da ita yayi cikin jikinsa kafin yace "It's okay, ki daina kukan nan haka, oya tell me ina suka tafi..?"
Ta d'an share hawayen idanunta tana gyara rigar baccin dake jikinta shiko sai binta da mayen kallo yake.. Nan take sanar dashi gidan mutumin da suke zaune a gidar gonan sa kafin a k'ona nan suka tafi, harda d'iyarta Falaq...
Alh Kabeer ya kamo 'yan yastun hannunta kana yace "Jamila kar ki tab'a damuwa, you've me sannan bazan tab'a wulak'antaki ba sannan idan sunfi son zama a can fine, ki k'yalesu I promise you bazan tab'a barinki ba..." ya k'arashe yana mai murza 'yan yatsun hannunta a hankali..
D'ago pale face d'inta tayi kana tace "Ka min alk'awari zaka kasance taredani har abada...."
Saida yayi kissing hannayen ta kafin yace "I love you ultimately, to the point that I can't do without you..... Jamila I'll never leave you....you have me completely, I'm all yours, nayi alk'awarin saka ki cikin farin ciki na har abada...." Ya k'arashe yana saka hannu a aljihu... Key d'in DC d'in da yazo dashi ya shiga nunawa a fuskar ta kana yace "This is yours Kitty, ki sani ni Kabeer Santana zanyi komai muddin zai sakaki farin ciki...."
Shaye da mamaki take binsa da kallo lokaci guda tasa hannu ta amshi key d'in ta shiga juyawa.... Wani irin runguma ta masa tana murmushin da yafi kama da dariya tuni ta mance bak'in cikin da take ciki.... Shiko gogan abin nema ya samu bai fice office d'in ba saida suka hole ayarsu, daga bisani yayi waya wa driver d'insa ya fad'a masa location yace yazo ya d'aukesa... Su Jamila kuwa sabuwar Duniya... (Allah kayi mana tsari da yaudara irinta Duniya)...
*******
Salma tayi shiru tana sauraren 'yar uwar tata Falaq na bisa cinyarta tana d'an mata wasa... Ilham taci gaba da fad'in "Salma wllhi ba mafarki bane, I'm quite sure naji mutum na tab'ani cikin barci, abinda ya dad'a bani tsoro shine sassan jikina da naji ana tab'awa, nasan Falaq na kwanciya a jikina amma wllhi Addah Salma wannan babban mutum ne...." Ta k'arashe fuskar ta fal alamun damuwa...
Salma ta d'an sauk'e ajiyan zuciya kafin tace "Meyasa baki tashe ni ba....?"
Ilham ta d'an ware manyan idanunta tamkar na mai gani kana tace "Salma wllhi tsoro naji, naji tsoro sosai...."
D'an murmusawa Salma tayi ganin yanda Ilham ke rarraba idanu tamkar ta kuma jin mutumin a jikinta kana ta rik'o hannun Ilham tace "Ilham babu komai, I'm sure rashin sabo ne kawai yasa kike jin hakan, na zauna a gidan nan na tsawon kwanaki na tabbata babu komai...."
Ilham ta d'an jinjina kanta had'i da sauk'e ajiyan zuciya kana tace " Aunty Azeema da Aunty Shareefah sunada kirki sosai kiga yanda suke d'awainiya damu..."
Salma bata ce komai ba sai d'an murmushin yak'e da tayi tamkar Ilham d'in na dubanta, don ita sam bata yarda da Azeema da Shareefah ba, hasalima taku take don samun yanda zata gyara ma ko wacce zama a cikin su, bata so suyi hurting 'yan uwanta don haka dole tasha maganin zama dasu....
*******
Azeema ta dubi Shareefah suka kuma tafawa kafin tace "Ke nifa sabida na razanata nayi hakan amma wllhi saida naji gaba d'aya sha'awarta ya addabeni...."
Shareefah ta tab'e baki kana tace "Haba ke kuwa wannan k'wailar dama dai babbar ce toh akwai mamora...."
"Ke wa ya gaya maki wllhi sai kin shafa jikinta kiji lafiyar laushi sannan akwai abubuwan ma ba yanda kike zato bane...."
Sukayi dariya a tare kafin tace "Next step, da fatan kin sanar da Delu shinkafa da mai da barkwano za'ayi...."
"Eh mana amma fah kinsan Affan baici...." Shareefah ta bata amsa...
Azeema ta murmusa kana tace "Naki wasa ne yanzu zanje na sameta na sanar da ita d'an kad'an za'ayi bak'inmu ke son ci idan yaso abincin gida sai tayi wani abin daban..."
Shareefah ta shek'e da dariya kafin tace "Amma kuwa kinyi dai-dai yanzu bara naje na san yanda za'ayi ta yarda ta bini...."
A tare suka mik'e suka fito, Azeema ta nufi BQ Shareefah kuwa ta nufi d'akin su Salma...
Saida ta d'anyi knocking kafin ta shigo fuskar ta fal murmushi, ma Falaq ta soma yin wasa harda karb'anta ta d'agata sama tana cillata, Ilham sai murmushi take yayinda Salma ke binta da wani irin kallon rashin yarda...
Cikin sauri Ilham tace "Aunty barka da safiya...?"
Shareefah tayi murmushi kana tace "Barka Ilham da fatan kin wayi gari lafiya,...?"
Ilham ta amsa da Lafia lou sannan ta k'arada "Ina d'aya Auntyn da muryoyinku nake gane ku, muryarki ta d'anfi ta wancan Auntyn kauri...."
Shareefah ta d'anyi tak'aitaccen dariya kafin ta rik'o hannayen Ilham tace "Kinada baiwa sosai Ilham dukda kin kasance maras gani...."
Ilham tayi murmushi kawai ba tareda ta furta komai ba... Kallon Salma dake k'ok'arin d'aukan Falaq Shareefah tayi kafin tace "Matar k'aninmu so nake na d'an tambayi favor pls..."
Ilham sai murmushi take jin sunan da Shareefah ta kira Salma dashi... Ita kanta Salmar saida ta nanata sunan a zuciyar ta..
Shareefah taci gaba da fad'in "Pls kasuwa nake so kimin rakiya na cire anko sannan ki tayani zab'en kayyayakin fitan biki...."
Gaban Salma yayi wani irin yankewa ya fad'i wato dai da gaske Soja zai auri Shareefah... Kallon kallo suka shiga yima juna daga Salmar har Shareefah sabida taga yanda yanayin Salma ya canza lokaci guda...
Saurin saita kanta Salma tayi kafin ta shiga girgiza kai cikin sauri tana fad'in "No no ai ni ban iya zab'e ba, hasalima banida wannan wayewar, kuma kinga banson yin nesa dasu Ilham in case zasu nemi wani abu...."
Shareefah ta marairaice fuska kana tace "Haba mana Salma, am I asking for too much, dan Allah ki rakani, beside su Ilham basu kad'aine cikin gidan nan ba akwai Azeema gasu Deluwa, pls don't say no...." ta k'arashe fuska fal kalan tausayi...
Kafin Salma ta sami zarafin magana sai jiyo muryar Ilham sukayi tana fad'in "Addah Salma ki rakata pls, kar ki damu nida Falaq mun saba zama tare, mu biyu rak Addah ke bari idan ta tafi aiki, don Allah ki rakata tunda ta buk'aci kije d'in....."
Salma zatayi magana Shareefah ta kuma cewa "Pls mana Salma...."
A hankali ta jinjina kai kana tace "Shikenan naji zan raka ki...."
Shareefah wani rungumarta irin na murnan nan, Ilham kuwa sai murmusawa take lokaci guda tana rik'e da Falaq tana shafa kwantattun filla-fillan sumarta wanda sam basuda cika...
Salma dai ba don taso ba ta soma shiri gaba d'aya batasan me zata ce ma 'yar uwar tata ba don ta lura gaba d'aya ta yarda dasu Aunty Shareefah...
A tare suka sauk'o k'asa gaba d'aya sukayi break, basu tarar da Mamy ba da alama Delu bata sauk'o da ita ba tukuna.. Daga bisani suka nufi sashen Daddy gaida sa, a parlor suka tadda sa yana karanta jarida suka gaida shi gaba d'ayansu, sai murmushin jin dad'i yake, tabbas yasan Shareefah tafi mahaifiyarta, nan Shareefah ta sanar dashi zasu fita itada Salma yako masu izini cikin jin dad'i...
Affan daga windown d'akinsa ya hangi su Shareefah da Salma zasu fice, cikin sauri ya zura slippers d'insa ya nufo k'asa...
"Ina zakuje da safen nan....?" ya tambaya yana mai k'arasowa
Shareefah ta dubi Salma da gaba d'aya ba'a sake take ba sannan ta maida dubanta ga Affan wanda ya kafe Salma da idanu kana ta murmusa tace " Bafa wani safiya bane kaga shad'aya fa ta d'an gauta, Kasuwa zamu zata tayani zab'en kayyakin fitan biki sannan bamu sani ba ko itama muga wanda zai dace da ita, don fatanmu shine ana gama bikin mu a saka naku...."
Tuni Affan ya hau washe baki ba tareda yasan yanayi ba,... Salma kuwa k'wafa tayi had'i da kauda kanta gefe...
"Wow da inada halin binku da na biku don dai yau munada zuwa asibiti da Mamy ne... Amma...!" ya d'an ja aya yana duban Salma kafin ya rage murya yace "Pls ki kawo min tsaraba...."
Murmushin yak'e kawai Salma tayi kafin ta jinjina kai tace "Imsha Allah...."
Saida ya sauk'e wata deep breath don ya zaci bazata amsa sa ba, to his surprise kuma sai ta amsa.. Dad'i ya mamaye zuciyan Affan yasan a hankali zaiyi winning Salma...
Shareefah ta bisu da kallo tana wani munafukin murmushi kafin tace "Toh love birds zamu iya tafiya..."
Affan ya d'an murmusa kafin ya k'araso yayi rad'awa Shareefah a kunne, da Kansa ya bud'ewa Salma marfin mota....
Azeema na tsaye ta windown parlour akan idanunta akayi komai, tayi k'wafa kafin ta koma cikin parlourn lokaci guda ta shiga sakin murmushin mugunta....
*******
Misalin k'arfe d'aya da wasu dak'ik'ai lokacine da ake kiraye-kirayen sallan azahar a masallatayya, Azeema ta mik'e ta nufi kitchen ta bud'e robar barkwanon taga harda 'ya'yanta daga gani zatayi zafi, ta saki murmushi kafin ta shiga d'aukan abincin tana shiryasu a dinning table dama ta sanar da Deluwa idan ta gama girkin zatazo ta jerasu da kanta...
Robar man gyad'a ta d'aga ta tunstire da dariya lokaci guda ta shiga yaryad'awa saman tiles, bayan ta gama yaryad'a mangyad'an ta kuma bud'e robar barkono ta zuba shi saman table d'in, tanayi tana murmushin k'eta...
*Sameena Aleeyou...*
[26/07 13:19] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*29*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
Zaune ta tadda su Ilham a d'aki tana k'ok'arin shirya Falaq duk da ba gani take ba amma Allah yayi mata kalan nata baiwar da fasaha....
Azeema ta murmusa kafin ta k'araso da sauri tana fad'in "A'a Ilham shiri ne ake haka..." ta k'arashe tana mai k'arasawa had'i da d'aukar Falaq
"Bani ita na shiryata, idan dai muna gida pls ki dinga bari mu mata wanka mu shiryata...." ta k'arashe tana zare ma yarinyar manyan manyan idanunta....
Ilham kuwa sai murmushi take sanda sanda Azeema ta k'arb'i yarinyar...
"Aunty ai na saba zan iya...."
Murmushi Azeema tayi lokaci guda tana k'arewa Ilham kallo kana tace "A'a kar ki damu me amfanin mu bari dai ki ga na shiryata..."
Bata jira cewar Ilham ba ta sauk'a k'asa a d'ari ta barbad'a barkono cikin diaper d'in Falaq kafin ta dawo taci gaba da shirya Falaq tana jan Ilham da surutu...
Aiko ana d'aura mata diaper d'in Falaq ta calla k'aran azaba... Cikin sauri Azeema ta danne bakin yarinyar da k'arfin gaske...
A d'an firgice Ilham ta mik'e tana ware idanu take tambayar lafia...?
Azeema ta murmusa kafin tace "Kar ki damu na goyeta yanzu zatayi barci..." Ta k'arashe tana rik'o hannun Ilham d'in da hannu guda yayinda Falaq ke matse a hammatar ta hannunta matse da bakin Falaq d'in...
Jikin Ilham a sanyaye take biyeda Azeemar sanda tayi masu jagora zuwa dining table sai sannan ta Saki bakin Falaq yarinyar har tayi kuka ta gaji, sai shesshek'a take had'i da wani irin nishi.... Azeema ta shiga jijjigata lokaci guda hankalin Ilham yayi mugun tashi lalume ta shiga yi tana tambayar Azeema me ya sami Falaq...
Azeema bata fasa jijjigata ba tana fad'in "Ilham I don't know inaga dai rikici ne kawai irinta yara..
Cikin tashin hankali Ilham ke fad'in "Kawota pls, kawota...."
Dai-dai lokaci dasu Mamy da Affan suka turo k'ofar parlorn suka shigo, Mamy dafe da crutches d'inta tana cangwalawa Affan ya hangi Ilham zatabi ta saman mangyad'a shi gaba d'aya baima lura da Azeema dake k'ok'arin dulmula wa Falaq barkono a idanu ba.... Tuni Azeema ta daskare lokaci guda Affan ya tafi a d'ari ya tallafi Ilham don tuni ta kusa fad'uwa... Ashe kuwa mangyada har kusan k'ofa ya gangaro Mamy sam bata ankare ba sai sauri take ta raba tsakanin Ilham da Affan... Ji kake tum Mamy ta zube a k'asa lokaci guda ta saki gigitaccen k'ara Azeema ta kuma juyowa a birkice kwatsam robar barkonon nan tayi wani tumbling sai a fuskar Azeema k'ara ta saki tana k'ok'arin jifa da Falaq Affan ya kuma taro Falaq yana fad'in "Wai meke faruwa ne haka... Lord of mercy meye wannan...?"
Ina Azeema sai ihu take tana lalumen hanyar kitchen yayinda Mamy ta rik'e k'afarta mai ciwo tana ihu tamkar wacce ake zarema rai...
Gaba d'aya sun birkita Affan, ga Falaq ma sai kukan azaba take Ilham na jijjigata...
Zaunar dasu Ilham yayi bisa sofa kafin ya dawo ga Mamy wacce ke ihu tana fad'in "Affan wllhi 'yan shan jini ne, kaga 'yar uwarta ta jefa min b'awon ayaba nabi kai yanzu kuma makauniyar ta zuba min mangyad'a a hanya nabi kai... Wllhi dole su bar gidan nan idan baso kuke su kashe ni ba...."
Affan ya d'an dafe kansa kana ya sassauta murya yace "Mamy koda ita ta zubar na tabbata bata gani ba domin kuwa itama ta kusan bin saman mangyad'ar, Mamy ki mata uzuri da lalurarta pls..."
Baki sake Mamy ke dubansa kafin tace "Uwar lalura Affan... Nace uwar lalura, shikenan ka zuba idanu a kasheni... Wayyo na shiga uku ni Ma'u wai wane irin asiri sukai maka ne kam...."
Ilham kam tuni hawaye ya shiga bin k'uncinta jin Falaq ta kasa yin shiru ana haka su Shareefah suka shigo a birkice don tunda aukayi parking suke jiyo sautin kukan Mamy...
A tamanin Shareefah ta k'araso wajen Mamy yayinda Salma ta nufi Ilham da Falaq...
Salma ta amsheta tana jijjigata take tambayar Ilham d'in me ya sameta...
Mamy ta dad'a kufula ganin Salma ta hayeta tanufi wajen 'yan uwanta.... Ihun da take ta daina kafin ta malmalo wa Salma wata ashariya taci gaba da fad'in "Wllhi kurwata kur barikuji na fad'a maku... Dangin jaraba dangin mayu...."
Dai-dai nan Azeema ta fito fuskarta tayi jazir haka nan ma idanunta tamkar jan gauta, fuskar kuwa yanda kasan mai fama da cutar eczema duk yayi rod'i-rod'in azaba....
Shareefah ta had'iyi dariyarta don sosai Azeema ta bata dariya, yanda kasan wata kurar tashe...
Affan ya dubi Azeema kana yace "Ina jinki meyene ya faru, me ya kawo mangyad'a da barkono parlour...?"
Azeema ta kuma goge fuskarta kana tace "Deluwa ce ta zubar bata sani ba inaga, mu kuma mun fito yin lunch kenan..."
Girgiza kai kawai Affan yayi yayinda Mamy taci gaba da rantse rantse tana fad'in babu ruwan Deluwa....
Affan ya dubi Salma dake faman jijjiga Falaq yace "Ki haura da ita upstairs ki sake mata wanka inaga barkonon ya d'an shafeta ne itama..."
Salma ta jinjina masa kai tana mai raka Azeema sa mugun kallo wacce tuni ta kwanta a parlorn saman doguwar kujera ta lumshe idanun don har lokacin bai daina mata zogi ba...
Hannun Ilham Salma ta kamo Falaq na bisa kafad'arta suka nufi sama..
Affan da Shareefah kuwa taimaka wa Mamy sukayi suka kwasheta suka kuma komawa asibiti....
Saida Affan ya biya BQ ya sanar da Deluwa taje ta gyara parlorn kafin suka wuce asibitin....
******
Tuni Salma ta soma cire wa Falaq kaya, Ilham kuwa hankali tashe take fad'in "Angel I'm sorry kinji, bansan me ya sameki ba....."
Salma dai bata amsa Ilham ba sai kwab'e wa Falaq kaya take...
Cak ta tsaya da abinda take sanda ta cire diaper d'in taga 'ya'yan barkwano a ciki... Ta kuma duban jikin yarinyar taga yanda yayi jajazir alamun taci azaba.... Take idanunta suka kad'a sukayi jazir hawaye ya cikosu, toh kodai Ilham batasan da barkono ciki ba ta saka wa Falaq...
D'an saita kanta tayi kafin tace "Ilham yaya akayi barkono ya shigo diaper d'in Falaq...?"
"Barkono kuma...?" Ilham ta tambaya tana jujjuya idanu fuska fal damuwa...
"Eh mana barkono gashi nan ya memmele mata jiki... A parlor ne kika shiryata....?"
Ilham ta soma girgiza kai cikin sauri kana tace "Aunty Azeema ce ta shiryata kuma a nan a d'aki ta shiryata, gaskiya saidai idan fitar mu parlor ne ya shiga cikin jikin nata ba da sanin Anty Azeemar ba, don wllhi har goyonta saida tayi Salma..."
"Goyo...!" Salma ta nana ta a hankali... Gyad'a kai tayi kafin abubuwan suka shiga dawo mata kwanyar ta, sai yanzu ta gane dalilin da yasa Shareefah tajata suka fice wato don su cutar da 'yan uwanta ne.... Tayi k'wafa lokaci guda ta suri Falaq ta nufi bathroom da ita ta wanketa tsaf kafin ta shafa mata olive a wajen, ta kwantar ta bisa gado ba tareda ta saka mata kaya ba... Kan kace me baccin azaba yayi gaba da yarinyar
Gefen Ilham Salma ta zauna kafin tace "Kina jina... Ko uwarsu ce ta kuma cewa ki kawo Falaq kada ki bata, kinjini koh....?"
"But... Salma why...?" Ilham ta tambaya
"Ni dai nace maki kada ki sake basu Falaq, kema kuma kada su baki abu ki amsa har sai idan ni ce na umarceki...." Bata jira cewan Ilham ba ta mik'e ta fice parlor..
Nan ta hangi Azeema kwance saman kujera idanunta a lumshe har lokacin... Ta kuma duban saman table d'in ta hangi ragowar barkono.... Murmushi tayi kafin ta nufi table d'in ta d'auko sauran barkonon... Kai tsaye d'akin su Azeema ta wuce ta bud'e ma'ajiyan kayansu nan taga layin inners har kashi biyu, ma'ana akwai na Shareefah kenan da kuma na Azeema... Gaba d'aya ta fito da pants d'in ta masu wankan barkono kafin ta ninke tsafe kaman yanda suke ta maidasu ma'ajiyansu.... Ta jima tana tsaye a wajen tana tunanin abin yi, wata zuciya ce ta raya mata ta amince kawai da soyayyan Affan koda bata sonsa ta haka ne kowa zai shiga taitayinsa a gidan, don tasan dole ya dinga taking side d'inta ko wani irin tsiya zata masu... Tayi k'wafa had'i da murmusawa..
*******
Yau har tad'i Salma da Affan suke, abin yayi bala'in masa dad'i, tana hango yanda Azeema da Shareefah ke faman lek'ensu, ta murmusa cikin ranta kuwa cewa tayi bakuma ga komai ba, a b'angaren Shareefah hakan ba wani damunta yayi ba idandai zata bar mata Sojanta ita kad'ai, abun sai yafi damun Azeema...
Daren ranar ma saida Ilham taji ana shafata.. Kan ta ankare an wafce an fici... Tashin Salma tayi tana fad'a mata lokaci guda tana hawaye.. Addu'a Salma ta mata don abin ya d'an soma bata tsoro....
Washe gari da safe su Azeema anyi wanka ana shiryawa, tunda ta saka pant taji kaman barkono... D'an tsaki tayi ta d'auki wani ta saka.... Aiko tana ida sakawa uban azaba na ratsa ta.. Yanzu kam ta yarda ba daga pants d'inta bane tunda har kusan biyu ta saka tana jin hakan..... Shareefah ce ta shigo a guje itama tana tsallen azaba...
Gaba d'aya sai ihu suke suna murk'usoso shafewar basira sam basu kawo pant bane abinka da masu aikata babban laifi tuni Shareefah ta soma fad'in "Ke anya ba bala'i Allah Ya soma sauk'ar mana ba.... Wayyo zogi...."
Inaa Azeema bata sami zarafin amsata ba tuni ta kwab'e skirt d'in tayi wurgi dashi ta had'a harda kampai d'in tayi watsi dasu ta shige bathroom...
'ya'yan barkono da Shareefah ta gani saman kampai d'in Azeema ne ya sanyata kwab'e nata babu shiri....
Abin ya damesu sunsan duk yanda akayi Salma ce kawai zatayi wannan aiki.... Koda suka labartawa Mamy dariya ta dinga yi kana tace "Ku nifa wllhi tsoro yarinyar ke bani, inaga dai ba mutum bace..."
Shareefah tace "Mamy wllhi mutum ce, amma tunda tace kada ayi zaman lafiya a gidan nan ta taro yak'i wllhi, yanzu muka soma cin uwar makauniyar nan har sai sunji su bar gidan nan shi ya fiye masu sauk'i...."
Mamy dai bata furta komai ba sai fad'awa duniyar tunani da tayi, inama ace Laure na nan da tuni ta turata wajen boka anci mata uwar yarinyar nan, don dai kawai yanzu bata da k'afafun fita ne sannan babu kud'i kaman da, gwara kawai su had'a kai da yaranta su kore shegu da makirci.....
Kusan kwana uku ana shafa Ilham da dare the next day sukayi canjen wajen kwanciya da Salma..... Aiko can cikin dare taji ana shafata... A hankali takai capka wa hannun ta gantsara cizo da hak'waranta.... Shareefah babu halin ihu ga azaba, sai kokawan k'watan hannunta take Salma tak'i saki..... Da k'yar ta samu ta k'waci kanta ta fice a guje...
Salma tayi k'wafa had'i da yin dariya tabbas taji alamun hannun mace ce...
Haka Shareefah ta koma d'aki tana cije labb'a.... Maimakon Azeema ta tausaya mata abin sai ya bata dariya ma.....
Rayuwar gidan Mamy ya koma taka tsan-tsan, ba k'aramin shakkan Salma sukeji ba don duk abinda aka mata ko akayi ma 'yan uwanta toh a rubuce ne sai ta rama masu, sam bata barin kota kwana balle tayi tsami, ga Daddy bai ganin laifinta sam uwa uba Affan da soyayyanta ya gama ratsa illahirin b'argo da tsokarsa, Allah sarki sam baisan a B'angaren Salma ba haka bane.... Mamy kuwa ta soma dogarawa da crutches har takan d'an lek'a sashen Daddy...
A b'angaren Naseer kuwa bai faye zaman gari ba yanzu yafi zama a base d'insu tunda ya lura kaman hankalin Affan da Salma ya kwanta sosai yanzu, ya saka ma ransa Salama cewa bazai tab'a samun Salma ba, yin nesa da ita zaifi masa sauk'i sannan gwara yayi maganar aurensa da Shareefah kawai tunda yasan har abada Salma ba tashi bace, babban farin cikinsa shine Salma na farin ciki da Affan, shi dama damuwar sa kenan ta kasance cikin farin ciki koda ba shine sanadin farin cikin nata ba....
A b'angaren Salma ma rashin ganin Soja sosai yake damunta, batasan daliliba amma tasan tana son sake ganin sa, bud'e drawer d'in da ta ajiye chewing gum d'in da ya bata farkon kawota gidan... Aiko suna nan babu wanda ya tab'a... Batasan sanda murmushi ya subce mata ba, ta shiga juyasu tana lumshe idanu, Allah sarki Soja kirkinsa daban ne a cikin mutane.... Lokaci guda tunanin Addar ta Jamila ya fad'o mata, abin mamaki ko nemansu batayi ba balle taji yaya lafiyar su ballantana na d'iyarta.... Ta goge hawayen da suka d'an zubo mata kafin ta mik'e ta nufi bathroom Ilham da Falaq kuwa suna saman gado suna wasan su...
****
A hankali soyayya mai tsafta ke shiga tsakanin Deen da kuma Lubna, abin har mamaki yake bawa k'awayenta musamman Faty, haka Faty zata tasata gaba da mitan cewa sam Deen ba class d'inta bane, ta yaya zata kwaso masu wannan, he's no body ita da ya kamata ta d'auko d'an wani hamshak'i a k'asar nan amma ta tsaya tana soyayya da driver, ta yaya suma zasu samu mazaje masu kud'i idan bata d'auko mai kud'i ba, wannan ai abokan sa duk irinsa ne 'yan tasha...
Wannan magana na Faty sosai ya b'ata ran Lubna, saida ya janyo masu samun sab'ani, gaba d'aya Lubna ta daina kula Faty, don ji take zata iya samun matsala da kowa indai akan Deen ne, mutumin da ya sanar da ita dad'in soyayya, mutumin da ya fahimtar da ita darajanta da kimanta na d'iya mace, Allah Ya gani soyayyar gaskiya take ma Deen wanda sai yanzu ta lura ashe tuntuni itada Affan ba soyayya suke ba....
Hankalin Innah kuwa gaba d'aya bai kwanta ba, kullum cikin damuwar lamarin Lubna take, gashi tunda Fawaz ya dawo basuda daman tak'ura Saudat, wani kula na musamman Fawaz ke bata, gaba d'aya basuda wani nutsuwa daga ita har Kabeer d'in..
A b'angaren Jamila hark'a babu sauk'i ballantana yanzu da takeda abin hawa, dukda Alh Kabeer ya mata kashedin kula wasu samaruka hakan bai hanata kula wasu a bayan idanun sa ba....
Sam yau batasan yana zuwa ba don haka a cikin gidan take hole ayarta....... Ya jima yana kallonsu itada saurayin ta karan sigari mak'ale a bakinsa, warin sigari ne da sukaji ya sanyasu juyawa babu shiri...
Hanjin cikinta suka shiga juyawa, shi kuwa Auwal a tamanin ya suri takalman sa da rigarsa ya fece aka bar Jamila da rarraba idanu... Har gabansa ta tako yanda yake zaune saman kujeran dining table yana hura sigarin sa.... Jiki a sanyaye ta durk'usa gabansa... Kuka ta soma masa tana rok'onsa yayi hak'uri...... Batakai aya ba taji sauk'an mari mai stars a fuskarta
*Sameena Aleeyou...*
[26/07 13:19] Meela Adeel馃槏: 馃寲馃寲 *A DUNIYAR MU* 馃寲馃寲
*30*
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
A gigice Jamila ta rik'e fuskarta had'i da sakin k'ara lokaci guda ta mik'e zata nufi upstairs.... Fincikota yayi yana wani irin huci lokaci guda ya shak'e mata wuya jikin garu, bata tab'a ganinsa cikin yanayin ba.... Kuka take tana k'ok'arin k'watar kanta amma ta kasa.
Cikin wani irin huci ya matso da fuskar sa daf nata kafin ya soma fad'in "Da kinsan yanda nake sonki da bakiyi tarayya da wasu mazan ba.... Jamila ina sonki sannan zan iya kashe duk wanda na ganki tare dashi...." ya k'arashe yana kuma matse ta jikinta garu tamkar wanda zai aikata lahira..
Sai faman k'ak'ari take ga idanunta da fuskarta da suka sauya kala zuwa launin ja sabida tsananin azaba
Da k'yar ta iya furta "Pls... Let go.... You hurting me, Dan... Allah ka k'yaleni wllhi bazan k'ara ba..."
Jifa yayi da ita saida ta gwaru da kujera kafin ya kuma nufota, lokaci guda ta shiga jada baya tana mai girgiza kai tana hawaye tana sosa wuyarta dake mata zogi da rad'ad'i...
Saida ya matso dap kusanta kafin ya durk'uso suna fuskantar juna lokaci guda yasa hannu ya damk'o sumar ta tuni fuskar sa ta koma launin tausayi a hankali yake furta "You see kinsa ina hurting d'inki... Kitty I love you it was never my intention to hurt you.... Meyasa kika karya dokata, Why Kitty...." ya k'arashe yana kuma jan sumarta da k'arfin gaske...
Girgiza masa kai take tana mai ci gaba da hawaye take fad'in "Pls let go... It hurts.. Wllhi nayi alk'awari bazan sake ba...."
Kallo ya bita dashi kafin ya saki sumarta ya mik'e kaman wanda aka zabura ya fice a gidan...
Haka Jamila ta tak'ure waje guda tana kuka, ji tayi babu wanda take son gani kaman 'yarta Falaq yau kam dole ta d'auko d'iyarta ta zauna da ita, at least zata d'an ji sanyi a ranta...
Alh Kabeer na barin gidan ta mik'e tayi shirinta dukda kumburin da fuskar ta tayi, da kwatance ta sami gidan Alh Ali Safwan...
Babu kowa a parlorn sai Azeema dake kallon reality show d'inta, kaman daga sama taji ana knocking... Sam bata son ko motsawa idan ana program d'in ba don taso ba ta nufi k'ofar ta bud'e....
Baki sake take kallon matar da gani 'yar gayun k'arshe ce, tana sanye da dogon riga ta larabawa idanunta rufe cikin shades don bata so aga fuskar ta....
Murmushi Jamila ta sakar ma Azeema kafin tace "Da Allah Salma fah...?"
Azeema ta gyara tsayuwarta kana tace "Bismillah shigo...."
Babu musu Jamila ta kusto kai ta shigo cikin parlorn sai k'are ma gidan kallo take, ta yaya ma zata baro mansion d'inta tazo tana squatting a nan... Ai ta wuce wann level d'in..
"Salma kike nema...?"
Azeema ta kuma tambaya....
D'an sauk'o da shades d'in nata tayi tana ma Azeema wani irin kallon raini kafin tace "So kike na maimaita maki?...."
Azeema baki sake take kallon ikon Allah, har cikin gidansu za'a shigo a koya mata karatun barikanci... Muskutawa ta d'anyi kafin tace "Toh Salma dai ta fice nemo wahalalliyar niece d'inta magani, ita kuma makauniyar....."
Bata kai aya ba Jamila ta mik'e tsaye tana tambayanta ina Falaq me ya sameta.... Kafin ta rufe bakinta suka jiyo kukan Falaq daga upstairs....
Jamila har na tattara rigarta ta nufi yanda take jiyo sautin kukan d'iyar ta...
Ta jima tsaye a bakin k'ofa tana hango Falaq dake zaune saman rug sai kuka take Ilham na rarrashinta tana fad'in za'a kawo mata magani yanzu... Cikin sauri ta k'arasa ta d'auki d'iyarta ta shiga jijjigata tana rarrashinta ga jikinta yayi zafi kaman garwashin wuta...
Ilham ta mik'e da sauri jin muryar Addar su...
Baki har na rawa take fad'in "Addah... Kece, kece kika biyo mu Addah.."
Jamila bata amsata ba sai watsa mata harara da takeyi tamkar tana ganinta kafin ta kwantar da Falaq jikinta ta soma fad'in "Kina jina Ilham ki sanar da Salma kun kyauta da kuka barmin d'iyata cikin tsananin ciwo, a haka ne kuke so ku raine ta.... Toh wllhi tallhi kar wacce ta kuma tako k'afa tazo wajena da sunan d'aukan Ilham... Ungrateful idiots...." ta k'arashe had'i da jan tsaki kaman zata bangaje Azeema haka ta fice daga d'akin Azeema tayi saurin bata hanya tana kallon ikon Allah...
Kuka Ilham ta soma tana k'ok'arin lalumen hanya take nufowa k'ofar tana fad'in "Addah don Allah kada ki d'auke Falaq wllhi muna sonta, Addah pls kar ki d'auke min farin cikin rayuwa......" Bata kai aya ba saiji tayi ta bugu da k'ofa jini ya shiga bin goshinta... Azeema dake tsaye gefe murmushi tayi kafin a hankali ta furta "Wonderful..!"
Jamila kuwa tuni ta fice dama a waje tayi parking ride d'inta...
Haka Ilham ta ci gaba da lalume tana k'ok'arin nufowa k'asa Azeema kuwa tuni ta nufi d'akinsu sai mamakin yanyin uwar Falaq take, gaba d'aya ta banbanta dasu Salma....
********
Yau gaba d'aya kowa Dr Fawaz Santana yake so yaransa su gani, likita ne da yasan aikinsa uwa uba ga iya kula da yara, duk yanda ya wulga sunansa kawai kake ji a babbar asibitin koyarwan Dr Santana.. Su kusan uku ne a duty a b'angaren yaran amma kowa yafi son ganin Dr Santana, nurses kuwa 'yanmatan nan gaba d'aya Dr Santana ya tafi dasu kowa so take a had'a aiki dashi, wasu sabida had'uwar sa wasu ko sabida Family name d'insa da sukaji, gashi shi gaba d'aya baima san suna wannan rawan k'afan ba, sannan duk barkwancin da yake dashi wa yara ne kawai, domin yara ne abokan sa shiyasa yasan madafar aikin sa.... A d'an dawowar sa ba k'aramin nasara asibitin ta samu ba....
*******
Ta zaga private hospitals da dama bata sami likitan yara ba, har asibitin yaran taje akace mata Dr 2 yake tashi, gashi yawancin private d'in atata zuwa 2pm babu Dr saidai ka jira zuwa dare, ga fever d'in Falaq na kuma haurawa sosai, yarinyar sai shivering take abin tausayi... Dad'ata matseta cikin jikinta Jamila tayi tana shafa kanta take fad'in "Don't worry sweetheart, you'll be fine... I know you will..." ta k'arashe tana mai sumbatar Falaq d'in... Cikin sauri ta karya kan motar ta d'auki hanyar TH yanda likitoci basu yankewa....
*******
Salma na rik'e da panadol syrup d'in da ta sayo ma Falaq a hannu tana goge ragowar hawayen ta... Allah sarki Falaq suna sonta suna son zama da ita, inama Affan na nan bai koma Base d'insu ba da ta rok'esa ya kaisu sunga Falaq, ko wani hali take ciki yanzu sai Allah... Kaman Ilham tasan tunanin da take lalumo hannayen Salma tayi kana tace "Salma ki daina damuwa insha Allah Falaq zata sami lafiya muyi mata addu'a nasan soyayyar mu yana tareda ita a duk yanda take daga ita har Addah...." ta k'arashe muryarta na rawa...
Rungumeta Salma tayi tana matsan hawaye, tausayin su ya cika mata zuciya musamman 'yar uwarta Ilham...
******
Wani babban abin takaicin wai shine sai anbi layi.... Nafisa ce ta fad'o mata rai nurse d'in da taso taimakon su lokacin jinyar Inno... Cikin sauri Jamila ta mik'e ta nufi neman Nafisa... Bata wani sha wahala ba kuwa ta sameta...
Sosai Nafisa taji dad'in sake ganin Jamila, saidai gaba d'aya ta canza mata tamkar ba wancan Jamilar ba, bafulatana mai kunya sosai... Gaba d'aya taga sam babu alamun k'auyanci yanzu a tattare da ita...
Nafisa ta amshi Falaq tana kallonta kafin tace "Eh toh kinsan asibitin nan akwai layi sosai balle yau alhamis ranar dutyn Dr Santana abin ba'a cewa komai, amma muje na gwada rok'onsa Dr D'alha shi na kula mutane ba kaman Dr Santana ba bai bari wani yayi chancing wani d'an k'a'ida ne yanda kika san bature koda yake akwai jininsu a jikinsa dol....."
Jamila bata bari Nafisa ta ida zancen nata ba ta janyo hannunta cikin sauri tana fad'in "Muje pls nidai damuwata kawai a duba min d'iyata banso na rasata....."
Cikin sauri suka nufi fannin yaran... Mutane aunkuwa yi layi saman benches don ganin likita... Haka Nafisa ta rik'o hannun Jamila suka kutsa..
Dr D'alha, Dr Fago da kuma Dr Santana sune a cikin d'akin duba marassa lafiyan... Dr Dalha da Dr Fago duka akwai majinyata a gabansu...
Nafisa ta d'an sauk'e ajiyan zuciya sanda ta murd'a k'ofar ta d'an lek'a, gaisar da Dr's d'in tayi su Dr D'alha ne kawai suka amsa ta dama Dr D'alha yana d'an sonta ne, Dr Fago yasan da zancen sai zolayarta yake... Nan ta fad'a masu buk'atar ta...
Dr Fago yace "Toh ai kuwa kinga duk da majinyata a gabanmu saidai idan Dr Santana zaiyi alfarma... Sai sannan ta juya tana kallon Fawaz wanda ke faman wani minor research a cikin wayar sa baima san sunayi ba.... Ai Jamila bata jira amsar Nafeesa ba ta shige wuff tana fad'in "Pls ku taimaka min kar na rasata..."
Muryar da ya jiyo ya sanyasa d'ago kansa lokaci guda ya bar abinda yake yana dubanta...
Kallon files d'in gabansa yayi kafin yace "Akwai file d'inki a nan...?"
Cikin sauri Jamila ta girgiza masa kai kana taci gaba da fad'in "Dr pls taimaka mana zakayi..."
Ki koma sai kinyi submitting file an kiraku sannan ki shigo ko kinfi wad'anda suka rigaki zuwa nan ne...?"
Baki sake Jamila ke kallonsa don wannan idan bata fisa ba zasu zo sa'anni
D'an girgiza kai tayi kafin tace "Kana nufin na fita...?"
Idanunsa naga wayarsa yake fad'in " I'll be saying it twice if I say it again..."
0 comments:
Post a Comment