Lokaci guda idanun Jamila suka kad'a sukayi jazir, zare shades d'in dake mak'ale idanunta tayi tanai ma Fawaz wani irin duba lokaci guda ta k'arasa sosai har gaban table d'in nasa zuciyarta ta shiga tuno mata lokacin mutuwar Inno, cikin karaji ta soma fad'in "You're all the same.... Dukkanku d'aya ne... Baku kula da lafiyan majinyata sai lokacin da kula bazaiyi wani amfani ba, ince damuwarku kud'i ne... Fine, gasu nan, akwai su yanzu nafi k'arfin wulak'ancin ku...." Ta k'arashe tana zazzago kud'i cikin jakanta tana zubawa saman table d'in Fawaz wanda yayi mutuwar zaune hard'e da hannaye yana dubanta...
Gaba d'aya illahirin mutanen dake d'akin kallo suke faman bin Jamila dashi, su Dr D'alha kuwa kasa ci gaba da duba majinyata sukayi sai kallon mamaki da suma suke bin Jamilar dashi...
Nafisa kuwa rawa jikinta ya hau yi ga Falaq rungume cikin jikin ta..... A hankali ta shiga janyo Jamila tana mai bawa Dr Fawaz hak'uri Jamila kuwa fuzgewa take tana fad'in "Ki barni na fad'a masu idan sun rasa mai fad'a masu gaskiya ne... Har yau bazan mance ba wllhi alhakin mutuwar mahaifiyata a wuyarku yake...."
"Jamila kiyiwa Allah kizo mu tafi... Drs kuyi hak'uri don Allah...." Marisa bata kai aya ba Dr D'alha yace "Barin duba yarinyar dama na sallami wad'an nan..." Ya k'arashe yana nuni da mutanen dake gabansa...
Jiyo muryar Fawaz sukayi yana fad'in "A'a Dr zan duba yarinyar kar ka damu...." ya kai dubansa ga Nafeesa wacce ke rungume da yarinyar kafin yace "Biyo ni da ita..."
Babu musu Nafisa tabi bayansa Jamila ta take masu baya lokaci guda...
Wani d'aki mai d'auke da gado kaman na theater sai kujera da d'an table suka shigo.... Nafisa tana mik'a masa yarinyar ta fice tana mai alama wa Jamila kan cewa zasu had'u idan ta fito... Jinjina mata kai kurum Jamila tayi kafin Nafisa ta fice....
Fawaz kuwa tunda ya amshi yarinyar sai yagama kaman ya santa dukda shid'in mai yawan huld'a da yara ne wasu sukanyi kama da juna a yaran da yake dubawa amma wannan yarinyar kaman sanin da ya mata na daban ne haka yake ji....
Saman gadon duba marassa lafiyar ya d'aurata ya shiga aikin dubata..... Jamila tana kallon yanda ake jagwalgwala mata d'iya ana su tab'a wuyarta dasu k'irjinta.... Ba tareda ya dubi Jamilar ba yace "Since when zafin jikin ya fara, sannan kin bata wani magani ko baki bata ba....?"
Idanunta kan d'iyarta take basa amsa...
"I don't know bansan sanda zafin jikin ya soma ba.... Sannan ni ban bata wani magani ba..."
Sai sannan ya karkato yana duban Jamila sosai kafin yace "Wace irin uwa ce ke da zakice baki kula yaushene jikin 'yarki ya soma zafi ba, ko kinsan temperature d'inta is very high, yakai stage d'in da zata iya soma convulsion.... You see you're not even serious ba likitoci bane kurum basuda kula kuma baku da kula, baki tashi kinzo da wuri ba kin wuce mutane da dama wanda wasu tun farar safiya suke nan saida ciwon d'iyarki yayi tsanani kika taho, kika tsallake d'umbin mutanen dake bisa layi sabida son zuciya irin taki kika ce lallai saidai a soma ganin d'iyarki bayan suma suna son 'ya'yan sun nan kaman yanda kike son naki, in fact sunma fiki son yarn nasu tunda sun riga ki zuwa..."
Bai jira cewar Jamila ba yayi saurin ficewa yana mai gargad'in Jamilar da kada ta maidawa Falaq kayanta....
Jamila ta bisa da kallo har ya fice jiki a sanyaye don dai kam batada amsar basa... K'arshe k'arasawa tayi kusan d'iyarta tana mata fatan samun lafiya...
Jim kad'an Dr Fawaz ya shigo shida wani nurse na miji, lokaci guda aka d'auki jinin Falaq don yin gwaji,.... Sai faman zirga-zirga suke daga Nurse d'in har Fawaz d'in wani ikon Allah kasa ci gaba da ganin majinyata yayi ya tare wajen Jamila da Falaq....
Bayan shud'ewar wasu mintoci result ya fito tsananin zazzab'in malaria ne ya rapke yarinyar, take yasan wani irin drip zai saka mata lokaci guda ya umarci nurse d'in ya kawo masa....
Jamila dai tagumi tayi tana kallon ikon Allah.... Sanda nurse d'in ya fice Fawaz sai faman rubutu yake a file d'in yarinyar yana sake dubata....
Wayar Jamila kuwa sai ringing take, ganin Alh Kabeer ne ya sanyata jan tsaki batama san ta furta "Sai kayi kuma, ai wllhi tunda ka dake ni saidai ka nemi wani gidan kwanan ba dai wajena ba.."
Chak Fawaz ya tsaya da rubutun da yake ya karkato yana duban Jamila da tayi maganar, shi a duniyar sa ya k'i jinin yaga ana dukan mace ana cin zarafinta... Amma baiyi tsammanin yanda take da courage namiji zai doketa ba..... Lokaci guda yaji tausayinta ya rufesa, harga Allah baison ganin ana cin zarafin mace.... Yana tsaye yana wannan tunanin yaga sai faman goge hawaye take, ta cire shades d'in fuskar ta nan ya hangi rod'i-rod'in ja a fuskar ta alamun duka abinka da farar mace tuni sassa na fuskar sunyi ruhu-ruhu sunyi ja.....
Saurin daina kallonta yayi sabida gabansa da yayi wani irin mugun fad'uwa ya shiga zancen zuci shi kad'ai _Lafiyarka Fawaz ya kake kallon k'urilla haka wa matar wani..._ Saurin neman tsari da shaid'an yayi had'i da istigfari saidai kuma ya kasa ci gaba da rubutun da yake cikin d'akin dole ya fice.... Zuciyarsa yana tir had'i da Allah wadai da maza masu dukan mata....
********
Su duka uku sukayi tsaye akansu Mamy dafe da Crutches d'inta Azeema da Shareefah sun sakata a tsakiya, yayinda Salma da Ilham ke zaune hannayen Ilham d'in rik'e cikin na Salma Mamy taci gaba da watsa masu bak'ak'en maganganu Azeema da Shareefah na tayata...
"Toh kuma ai da yawon karuwancin kuka kama da kunfi samun riba, don nidai kam wllhi bazan tab'a bari d'ana ya aureki ba Salma, ke ko mafarki nayi ya aureki zanyi wuf na farka na kuma yi sadaka mafarkin ya zama shiririta, ni dama nasan kud'in jinin karuwai ne waysan me kike wa Affan baya ganin laifin ki..... A sannu kuma zaku bar gidan nan angulu ta koma gidanta na tsamiya yawon karuwancin da kuka fito..."
Ta k'arashe tana watsa masu mugun kallo likaci guda ta shiga cangwalawa su Azeema dake faman keketa dariya suka take mata baya...
Sosai abin yayima Salma ciwo bata da bakin ramawa don kuwa Addah ita ta jefa kanta cikin wannan hali ita ta janyo masu wannan tozarci da muzanawa....
********
Sai wajajen bayan magrib drip d'in Falaq ya k'are, har lokacin Fawaz bai tafi gida ba dukda lokacin tashin sa ya wuce, duk wanda ya damesa da tambaya cikin coworkers d'insa saidai kawai yace masu overtime yake....
Ya jima yana tsaye cikin d'akin yana tunanin da shi kansa bai isa yace ga tunanin ba nan ya hangi ledar maganin Falaq sun mance... Cikin sauri ya suri ledar ya fito
A farfajiyan wajen ya hangesu da Nafisa da alama godiya take mata..... Lokaci guda kuma yaji ya kasa tunk'arar yanda suke ai sai nurses su raina sa, juyawa gefensa yayi ya hangi wata cleaner take ya kirata ya bata ledar ya nuna mata wanda zata baiwa.... Daga nan office d'insa ya wuce don shirin tashi..
*******
Jamila kuwa bayan komawarta gida tasha mamakin ganin kud'ad'enta cikin ledar maganin kenan Dr d'in nan ya maida mata kud'ad'en... Samun kanta tayi tana mai murmusawa kafin ta shiga had'a masu abinda zasu ci...
A b'angaren Fawaz kuwa tunda ya koma gida tunanin yarinyar nan da mamanta ya hanasa sukuni, abu ne da bai saba ba ya zauna yana tunanin wasu, jinyar da mahaifiyar sa ke ciki ma bazai barsa yayi ba, amma abin mamaki wai yau tunanin mace da d'iyarta ya sanya sa gaba, macen ma matar aure matar wani da d'iyar wani... Wannan wani irin masifa ne... Duk k'ok'arin sa ganin kada yayi tunanin sai yayi, dafe kansa yayi yana karanto duk addu'ar da tazo bakinsa amma kam ya shiga wani irin yanayi....
******
Yauma saida Alh Kabeer ya lallasa mata duka sabida fitan da tayi bada saninsa ba sannan tak'i d'aga wayarsa sanda ya kira duk a zatonsa da saurayin nata take tare shiyasa tak'i d'aga wayarsa gaban sa, wato sun daina yi a gida sabida ya sani.... Ko sauraren ta baiyi ba sanda take fad'a masa rashin lafiyar Falaq cocaine d'insa bata fad'a masa dai-dai k'arshema ce mata yayi ta maida Falaq yanda ta d'aukota tun wuri don babu yanda za'ayi hark'a ta tafi masa da kyau ga yarinya...
A wannan dare sam bai bar Jamila ta kula da d'iyarta maras lafiya ba haka ya kwaso mata buk'atarsa gashi gaba d'aya a gidan ya kwana bai tafi ba, ga Falaq ta cikasa da kuka haka ya dinga toshe kunnuwan sa da pillow har gari ya waye... Ko wanka baiyi a gidan ba yayi ficewar sa ya nufi gida....
*****
Fawaz ya fito cikin shirin tafiya office ya hangi mahaifin nasa na fitowa daga mota alamun yanzu shigowar sa gidan.... Da mamaki Fawaz ke binsa da kallo har mahaifin nasa ya nufo cikin gidan sai faman waige-waige yake tamkar maras gaskiya
"Dad.... Lafiya, ina ka fito sassafen nan...?" ya jiyo muryar Fawaz kaman daga sama..
Murmushi ya sakar ma Fawaz yana dad'a gyara wuyar rigarsa wanda ake d'aura mata suit a sama, kana ganinsa kasan a birkice yake sam babu nutsuwa a tattare dashi...
"Son har an fito kenan.... I'm so proud of you Fawaz, you're hard working and dedicated...." ya k'arashe yana yangare baki uwa gonar auduga kana gani kasan dole yake haka kaman mai tsoron kada a gano laifin da yakeyi...
D'an murmusawa Fawaz yayi da gefen bakinsa wanda da gani iyakacin sa kenan fatar bakin kafin yace "Dad baka amsa min tamabayata ba, ina ka fito this early morning...?"
"Auw... Auho, kasan jiya akwai aiki sosai a company so dole na kwana a can.... As you can see yanzu dawowata kuma wanka kawai zanyi na koma...."
Kallonsa kawai Fawaz yake kaman mai son gano wani abu kana yace "Amma Dad haka ka bar Mum ta kwana, yanzu ne take tsananin buk'atar ka, look I'm not saying kar kayi aikin ka but family comes first, haba Dad ko wani irin aiki ne ya kamata ka bari ka dawo wajenta she needs you now more than ever...."
D'an sosa kansa Alh Kabeer yayi saikace shine yaro gaban Fawaz d'in kafin yace "Son kasan yanayin ciwon mahaifiyar ka wllhi yanzu babu hali na shiga kanta duk abinda ta runtumo sauk'e min take ai kai shaida ne, shiyasa ma watarana nake ji gwara na kwana ina aiki a office kar nima ta illatani ayi biyu..."
D'an girgiza kai Fawaz yayi kana yace "But still Dad ba yanda muka iya, ciwon Mum jarabawa ne garemu baki d'aya A DUNIYAR MU, muyi k'ok'arin cin jarabawar, sannan abin mu gode ma Allah ne ma tunda abinda take yi alamun sauk'i ne ya fara samuwa...." ya k'arashe murmushi kwance saman kyakkyawan fuskar sa...
Alh Kabeer kuwa saida 'yan hanjinsa suka kad'a sanda yaji furucin Fawaz na k'arshe... Murmushin yak'e yayi kafin yace "Haka ne Dr, Saudat sauk'i ya soma samuwa..."
Still murmushi saman fuskar Fawaz yake fad'in "Yeah insha Allah, na shiga yanzu na samu tana bacci banson tashinta sai na dawo na dubata insha Allah... I'll go ahead Dad..." ya k'arashe yana gyara zaman suit d'insa...
Saurin jinjina masa kai Alh Kabeer yayi yana fad'in "You take care Son..." Har saida yaga shigewar Fawaz mota kafin ya sauk'e ajiyan zuciya ya nufi cikin gidan yaji dad'in samun Saudat na barci zai sami zarafin narka mata alluran don yasan idan idanunta biyu tayi ta raruman abu tana jifansa dashi kenan, a 'yan kwanaki biyun nan haka take masa...
**********
Gaba ki d'aya jikinta ciwo yake mata sabida dukan data sha a wajen Alh Kabeer, ko motsa hannunta tayi sai taji a jikinta, tana tak'ure waje guda tana kuka tana mai tausayawa kanta da rayuwar d'iyarta.... Sosai jikin Falaq ya kuma yin zafi, har kaman ta soma shid'ewa sabida tsananin zafin jikin.... Gashi yarinyar bata shan maganin sai an rirrik'eta tayita wustil-wutsil kenan tana amayo da maganin irin dai yanda yara marassa son magani ke yi... Uwa uba Jamila batada k'arfin rirrik'e Falaq sabida ciwo da illahirin jikinta ke mata, sai yanzu take tuno 'yan uwanta tasan da tana tare dasu da saidai taga ana jinyar Falaq... Ganin yarinyar na jin jiki sosai ya sata shiryawa ta nufi asibiti tana kuka...
A dai-dai k'ofan ward d'in yaran ta kusa cin karo da Dr Fawaz.... Gabansa yayi wani irin mugun fad'uwa ganin tana kuka sosai ga fuskarta yauma a kukkumbure alamun an jifgeta..
Baisan sanda bakinsa ya bud'e ya soma fad'in "Yauma ya bugeki koh, dukan ki ya kumayi koh... Madam I'm sorry to say your husband is an Animal.... Baisan me yake yi ba in fact...." bai kai aya ba ta tsresa da fad'in "Dr pls Falaq ce ka ceci ratuwarta kada ta mutu pls...."
Ta k'arashe tana mik'a masa yarinyar... Cikin sauri Fawaz ya amsheta suka nufi cikin ward d'in, tuni wasu nurses biyu sun take masa baya....
Ruwa aka saka mata don ya lura abinda ya dawo da ciwon rashin shan maganin da batayi bane bisa k'a'ida... Dan haka dole ya saka mata maganin cikin drip....
Haka Jamila ta zauna gefen Falaq tana mai ci gaba da zuban hawaye... Cikin sauri Fawaz ya fice daga d'akin..
Kai tsaye office d'insa ya nufa yana tunanin dabbanci irin na wasu mazan, idan bazaka iya zama da mace ba ka sauwak'a mata mana, amma ba ka zauna kana musguna mata kana cin zarafinta ba, yanzu wannan matar ga jinyar d'iya da take ga kuma muzgunawar miji da wanne zata ji..... Ya d'an girgiza kai had'i da fuzar da iska, sam wasu halittan mutane ne kurum dasu amma sun maida kansu dabbobi na k'arfi da yaji, yana buk'atan yayi serious magana da mijin matar nan...
Nurse guda ya kira ya sanar da ita ta kirawo masa Nafisa..
Ita kanta taji mamakin kiran da Dr Fawaz ke mata, k'awayenta kuwa sai cewa suke "Lallai Nafisa zaki cire tuta idan Dr Santana ya k'are ji da kansa yace ke yake so...." Sai zolayarta suke suna dariya, ita koh tab'e baki kawai tayi kana tace "Kwadai ji dashi, kuda kuka sanma yanayi har yake gabanku, ku zauna kuyita damuwa da wani namiji kuna zubda kai ana rainaku...." ta k'arashe tana mai gyara sandals d'inta kafin ta fice...
Zaune ta taddashi a ofishin nasa ta shigo da sallama sannan ta soma gaidashi..
Bayan ya amsa ne yaci gaba da fad'in "Tambaya nake so na maki gameda wannan k'awar taki mai yarinya..."
Nafisa tace "Au Jamila...?"
Fawaz ya gyad'a kai kana yace "Ina tunanin itace, wacce dai kika rakota jiya..."
Nafisa ta jinjina kai tace "Eh itace Dr..."
D'an jinjina kai shima yayi kana yace "Kinsan gidanta ne, kinsan mijin da take aure....?"
"Aure kuma...?" Nafisa ta nanata fuska fal alamun tambaya...
"Ko ba matar aure bace...? Ina ta samo yarinya toh....?" ya kuma jero mata wad'an nan tambayoyi a jere..
Nafisa ta d'anyi murmushi had'i da girgiza kai kana tace "A'a Dr Jamila ta rabu da mijinta mahaifin d'iyarta tuntuni, hasalima batada aure a yanzu don ko jiya saida na mata wannan tambayar tace min bata kuma yin wani aure ba... Akwai wani abu ne Dr...?"
Mamakin tambayar k'arshe da ta masa yayi kafin yayi saurin girgiza kai yace "A'a no..no babu komai, shikenan you can go...."
Saida ta d'an rusuna kafin tayi masa sallama ta fice... Mamakin lamarin ya kuma cika Fawaz, idan ba matan aure bace meyasa jiya tayi furunci da tayi... Toh waye me dukan ta haka.... This is complicated, idan ba macen aure ba yaya za'ayi tayi furucin da tayi jiya akan mijin ta...? Ya jima yana nazarin abin shi kad'ai tambayoyi k'unshe cikin zuciyar sa babu mai basa amsa
Ko da ya dawo d'akin su Jamilar ta lura da wani irin strange kallon da yake mata, gaba d'aya sai tajita ba'a sake ba tana alla alla drip d'in Falaq ya k'are su tafi gida...
Aiko yana k'arewa ko jiran k'wakk'waran sallama batayi ba ta sungumi d'iyarta suka fice, sanda Fawaz ya shigo d'akin baiga kowa ba sai handbag d'in Jamila da alama mancewa tayi... Saurin d'aukan jakan yayi ya shige motar sa ya nufi gate yasan duk yanda akayi batayi nisa ba don basu jima da fita ba ga dukkan alamu...
Aiko yana fitowa gate ya hangesu sun shige cikin wata cab.... Cikin sauri yabi bayan motar da yaga sun shige.
Dama yau Jamila bada motar ta fita ba sabida babu fuel ciki...
Suna tafe a hanya ta daiga kaman motar bayansu su yake bi.. Ta kuma d'an lek'awa da kyau ta daiga wannan likitan ne mai biyosu, saurin duban mai taxi d'in tayi kana tace "Malam sauk'e ni a nan.. Babu musu mai taxi yayi yanda tace...
Fawaz kuwa ganin sun tsaya yasa sa fitowa cikin sauri daga nasa motar...
Sai sannan ta nemi jakan ta ta rasa, take Fawaz ya biya mai taxi d'in Jamila kuwa tanata mamakin yanda ta baro jakan ta
"Dr Lafia kake bina...?" ta tambaya sanda Fawaz yake rufe wallet d'insa bayan ya gama biyan mai taxi..
"Ai kinyi laifi ne kin karya doka shiyasa na biyoki..." ya bata amsa kai tsaye..
Murmushi ta d'anyi kana tace "Na sallami kaina ba'a sallameni ba koh..."
Murmushin shima yake kafin yace "Good tunda ma kinsan laifin da kikayi.... Yanzu muje na k'arasa daku gida kinga Falaq tana buk'atan hutu..."
Murmushin yak'e Jamila tayi kana tace "A'a Dr mijina ya hana ni shiga motar da bata haya ba..."
Murmushi saman fuskar Fawaz yake fad'in "Ban biyoki ba saida nasan cewa ke d'in ba matar aure bace.... Saidai nayi mamaki jiya da naji kina waya da wani tamkar da mijin aurenki kike... I'm sorry idan na shiga hurumin da ba nawa ba...."
Gaban Jamila yayi wani irin yankewa ya fad'i lokaci guda... Rasa abin fad'a masa tayi sai kuka dake neman kufce mata...
Fawaz yayi shiru yana dubanta kafin ya d'an sassauta murya yace "Kiyi hak'uri don Allah ba nufi na bane na tayar maki da hankali... Bazan sake maganar ba insha Allah shige na kaiku ko dan albarkacin Falaq kada ki k'i amsar tayi na..."
Bata kuma cewa komai ba sai juyawa da tayi tabi bayansa a hankali...
Suna isowa layin ta sanar dashi zasu sauk'a sai tsoro take kar Allah Ya kawo Alh Kabeer ya ganta ta fito daga motar wani..
D'an k'ak'aro murmushi tayi tanai ma Fawaz godiya, sai sannan ya d'auko handbag d'inta zai mik'a mata har ta saka hannu zata amsa tana kuma masa godiya taji yak'i sakin jakan, sosai yake duban fuskar ta yanda yayi rod'i-rod'in duka..
Muryar sa ta jiyo yana fad'in "Kyakkyawan fuska irin taki bata cancanci duka ba, hasalima k'awata ta da killaceta ya kamata a dinga yi ga namijin da yasan kima da daraja na d'iya mace, ya sake ki ya zago yana dukanki yana kuma bibiyan ki... I don't know ko a gidan iyayen ki kike zaune, amma ki sani duk wad'anda suke tare da ke suna ganin yana cin zarafinki haka basu d'auki k'wakk'waran mataki ba suma basu k'aunarki kuma basu kishin kansu ba balle su san kishin ki, d'iya mace is a great treasure ga wanda ya sani... I'm sorry idan kalamaina sunyi maki zafi, I'm just saying the fact, wllhi da inada iko akanki da na shigar dashi k'ara sannan bazan gajiya ba sai na gansa rot behind bars paying for his damn crime...."
I zuwa lokacin bugun zuciyar Jamila ya k'aru sosai, fuzge jakan tayi niyyan yi amma kuma sai ta kasa, jikinta yayi wani irin mugun sanyi... Fawaz kuwa sakar mata jakan yayi kafin yace "Alfarma d'aya tak zan nema wajen ki, kuma inaso kimin wannan alfarman ne ba don ke ba sai don Baby Falaq.."
Kaman bazatace komai ba sai kuma tace "Ina jinka..."
Fawaz ya d'an murmusa kafin yace "Contact d'inki zaki bani..."
Saida ta d'ago ta kuma dubansa kafin ta shiga girgiza masa kai alamun a'a...
Saida ya d'an murmusa kafin yace "Tun farko na fad'a maki zan karb'a ne sabida Falaq, don Allah kada ki hanani.."
Yanayin maganganun sa yakan sa ta jita cikin wani irin yanayin da bazata iya masa musu ba, lokaci guda taji bakinta ya shiga karanto lambobin..
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*32*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Yinin ranar zubur tunanin likitan nan ke damunta, idan kuwa ta tuno Alh Kabeer saidai taji zuciyar ta na mata k'una, harga Allah bata tab'a jin abinda take ji gameda likitan ga ko wani namiji ba, dukda bata isa tace ga abinda take ji ba amma kam yanayi ne maras fasaltuwa, gaba d'aya sai ta zamto sukuku da ita, a 'yan kwanakin ko samarukan ta bata kulawa, Alh Kabeer kuwa harga Allah ta gaji da zama dashi, bata tab'a tsammanin akwai namijin da zai faye mata kud'i ba sai yanzu, gashi tunda Dr Fawaz ya amshi lambarta bai kira ba, dukda yace dama ya karb'a ne sabida yaji lafiyar Falaq d'in.... Kullum wulak'anci safe daban na dare daban Alh Kabeer ke mata duk a dalilin d'iyarta ita kuwa sam bata jin zata iya rabuwa da Falaq a yanzu, watarana haka zai kwaso damuwar sa ya jibgeta son ransa, bata tab'a sanin rayuwar bariki k'arya bane sai yanzu, tabbas ta yarda Duniya mayaudariya ce, domin kuwa a 'yan kwanakin har wani irin rama tayi, gashi yanzu ba wani kud'i yake bata ba saidai yazo ya sauk'e buk'atar sa akanta cikeda cin zarafi..... Tabbas Duniya ta soma yima Jamila d'aurin goro tun ba'aje ko ina ba...
****
Shirye-shiryen bikin Naseer da Shareefah ake kan faman yi sabida k'aratowa da bikin yayi,... Yayinda kowa ke shirin wannan babban biki a b'angaren Salma ba haka bane, yauma kaman kullum tayi tagumi a balcony tana tuno abinda ta gane ma idanunta ba labari aka bata ba, Aunty Shareefah da Aunty Azeema suna aikata mad'igo, shin idan ta bari Soja ya auri irin wannan mata da saninta hakkin sa bazai kamata ba, Soja ya kyautata mata, ya ceci rayuwar ta sannan ya mata taimakon da babu mahalukin da yayi mata shi A DUNIYAR SU bayaga iyayenta da suka kawota duniya.... Shin haka zata zuba idanu Soja ya auri Aunty Shareefah...? Kaman daga sama sai ganin Shareefah tayi tsaye akanta ta kuma biyota...
A fusace Salma ta mik'e zata bar wajen Shareefah ta kuma damk'o hannunta tamkar mai shirin yin kuka haka fuskar ta ta koma, cikin murya wanda yafi kama da ta mai kuka Shareefah ta soma fad'in "Salma please... Don Allah kar ki sanar dashi, ki tausaya min ki tuna zafin a rabaka da masoyi,.." I zuwa lokacin Shareefah ta soma hawaye lokaci guda taci gaba da fad'in "Salma ina son Naseer with all of my heart.... Wllhi ba halinmu bane sharrin shaid'an ne...."
Fizge hannunta Salma tayi tana share hawayen dake zubo mata take fad'in "Wani irin ba halinku ba bayan ni shaida ce harta Ilham saida kuka bibiyeta sabida kun ganta makauniya.... Meyasa zanyi shiru na bari ya auri mace me k'azamin rayuwa wanda ko dabbobi basayi, wllhi ko dabba baya bin jinsin sa, ban tab'a jin akuya tabi 'yar uwarta akuya ba saidai tabi bunsuru..... K'azamin laifin da Allah Ya halak'a Al'umma akan aikata irinsa... Ta yaya zan bari Soja ya auri irin wannan macen..."
Ta k'arashe tana kuka sosai...
Shareefah ma share hawayen idanunta tayi kafin tace "Salma saidai kuma idan son Naseer kike...?"
Kallon mamaki Salma ta bita dashi kafin ta shiga girgiza kai tana fad'in "What...! No kema kinsan wannan bazai tab'a yuwuwa ba, Soja ya min abubuwa na alkhairi ne kuma kinsan ance d'an halak bai mance alheri.... Bazan iya zuba idanu ya auri cuta ma kansa ba...." ta k'arashe tana duban cikin idanun Shareefah tamkar wacce take jira su doku...
Murmushi Shareefah tayi kafin tace "Salma ki rufa ma kanki asiri and turn a blind eye.... Wllhi wllhi wllhi idan kikayi sanadin fasa aurena da Naseer zan fito maki ta yanda bakiyi tsammani ba, wllhi zaman gidan nan zai maki d'aci nasan bazaki tab'a so a lalata rayuwar makauniyar k'anwarki ba, karkiga muna baki dama kina rama duk wani abinda aka maki, zan iya kashe rai akan Naseer....."
Daga haka wucewa Shareefah tayi ta bar Salma nan tsaye zuciyarta na kuma mata zafi....
Durk'usawa Salma tayi a wajen tana tunanin rayuwar da Duniyar su ta tsinci kanta ciki.... Share hawayen ta tayi sanda ta jiyo muryar Ilham da kuma Shareefah a bayanta, saurin juyawa tayi don harga Allah tsoron ganin k'anwarta tare dasu Shareefah take, tsoron duniya ya k'ara shiga zuciyarta sosai... Bata gama mamaki ba saida taga Shareefah rik'eda leda hannunta guda rik'e da Ilham take fad'in "Au Ilham there she is... Gatan can sai ku haura sama ku gwada kayan naku ko zaiyi sizing d'in ku...."
Salma ta mik'e tana bin Shareefah da kallon mamaki Ilham kuwa sai murna take tana fad'in "Salma muje mu saka pls.... I'm so excited...." ta k'arashe tana k'ok'arin lalumo hannun Salma...
Wani irin kallo Salma tabi Shareefah dashi yayinda Shareefar ta sakar mata wani irin murmushi...
A daren ranar da tunanin abin Salma ta kwana, haka ta koma sukuku da ita a 'yan kwanakin kana ganinta kasan akwai abinda ke damunta...
Su Mamy da cangwalellen k'afarta ba'a sama ba'a k'asa dukda har lokacin da crutches take cangwalawa, gaba d'aya su Salma yanzu basa gabanta, inama take da lokacin su d'iyarta zata auri Captain Naseer Santana, soon Shareefar ta zata zama Santana's...
A b'angaren Innah ma ba'a cewa komai sai wasa da kud'i take wa su Mamy tunda ta lura imanin su kenan, burinta gab yake da cika Naseer ya auri Shareefah ta ida nufinta akan Naseer d'in, tabbas tasan zuciyar Naseer ta kusa bugawa bata fasa k'udirinta ba dole Shareefah ta amince mata da buk'atar ta da wannan kad'ai zata kashe rayuwar Naseer ya zamto maras amfani tasan idan zuciyar sa bai buga toh kuwa shakka babu shima zai zamto tamkar 'yar uwar mahaifiyar sa Saudat.... Innah ta kuma murmusawa tana busa hayak'inta...
*******
Ba tareda sanin kowa ba ta fice a gidan adaidaita ta samu ta tsare ta sanar dashi barikin Sojin sama ta nufa, da k'yar ta sami adaidaitan da ya d'auketa sabida nisan wajen gashi duk abu da Soja sai a hankali....
*******
Naseer na tsaka da horas da wasu runduna na soji wayar salulan sa ta shiga ringing, securities na gate ne suka sanar dashi zuwan Salma...
"Salma...!" Ya maimaita cikeda mamaki, d'an murmushi yayi domin kuwa lokaci guda ya tsinci kansa cikin Farin ciki maras misaltuwa.... Cikin sauri ya bar abinda yake ya d'auki motar sa ya nufi main gate...
Tana ganinsa ta mik'e tsaye ta had'i da sandarewa tamkar wata Sojia....
"Salma...!" ya kira sunanta fuskar sa d'auke da murmushi sanda yake k'ok'arin nufota....
Sojojin kuwa tuni suka soma sandarewa suna sara wa ogan nasu, inaa shikam idanunsa naga Salma wacce gaba d'aya babu walwala a tattare da ita
Kasa furta komai tayi sai kallon da take faman binsa dashi, zuciyart cike da tausayin sa...
"Salma lafiya dai koh...." ya k'ara tambaya yana mai dubanta ganin gaba d'aya babu walwala a tattare da ita...
******
Kaman mahaukaciya haka Shareefah ta nufo k'asa a guje sanda ta tabbata Salma ta fice daga gidan, zuciyarta ya shiga dukan tara-tara... Ta shiga tashin hankali maras misaltuwa... A d'ari ta nufi sashen Affan tana k'walla masa kira...
*Toh fah Uwar Shemah sai kuyi shirin saka anko, My Sisi bikin fah yazo🤪 su Meela su Parrot.... Ina zan manceki Shawty ta hannun daman Innah murhu bikin naku ne🤣 Anmunah, Asiyat Aysha Ameera, Deejah Xee, Sameerah Queen Billy, Najaat and Co manyan k'waye ku sha kuruminku akwai cashewa yasin 😂💃🏻🤣*
*Fatan Alkhairi makaranta littafan Sameena masu bibiyan labarunta 🤝🏼😻*
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*33*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Da mamaki Affan ke dubanta jin duk wannan kiran da take faman rangad'a masa wai Salma take nema...
D'an girgiza kai yayi kafin yace "Amma dai kinsan kin yanke min barci na koh...?"
Shareefah ta kuma dafe kanta kana tace "Affan wllhi Salma bata cikin gida, ni na tabbata base d'inku ta tafi, nadai b'oye maka ne kawai amma wllhi ta jima tana son Naseer, yanzu haka ma na tabbata wajen sa kawai ta tafi.... Affan idan k'arya nake maka mu tafi barikin ku yanzu... Salma's only using you but she never loved you, Naseer take masifan so...."
Bibbiyu Affan ya soma gani, yana huci ya d'ago yana duban Shareefah kana yace "No.. no this is crazy, look Shareefah karma ki soma wannan maganar wanda sam hankali ba kamawa zaiyi ba...."
Bai kai aya ba ta shiga jawo hannunsa suka nufi motar ta, batayi wata-wata ba ta bud'e frontseat ta tura Affan ciki...
"Shareefah what are you doing... What's the meaning of all this...?"
Bata amsa sa ba sai tada mota da tayi, tana mai karya kan motar had'i da horn wa Mai gadi take fad'in "Gaskiya zan nuna maka...."
*******
"Ina jinki Salma, meyasa kikazo nan ke kad'ai yayi nisa da yawa is not safe.... , hope all is well...?" ya k'arashe yana d'an bud'e idanunsa...
Kame-kame ta d'an soma yi ta rasa abin fad'i ga bugu da k'irjinta keyi Momy Lami ce ta fad'o mata d'an murmushin k'arfin hali tayi kafin tace "Am am... Dama nazo .... Ina son gaisawa da Momy ce, tunda na tafi ban kuma waiwayota ba..."
Murmushi Naseer yayi dukda zuciyar sa na raya masa tamkar ba wannan bane abinda ya kawo ta d'in..
"Toh banda abinki Salma ai da kin sanar dani na kawo ki koh...."
D'an murmushin itama tayi tsan-tsan tausayin sa na ratsa zuciyarta....
"Mu k'arasa....." ta jiyo muryar sa yana fad'in haka... A hankali tabi bayansa tamkar wacce ruwa ya shanye...
Suna tafe yana janta da tad'i saidai ya lura bata amsawa saiko um da um-um.... Shi kansa ya lura akwai abinda ke damunta... D'an burki yayi kafin ya dubeta sosai yace "Salma are you sure you're fine...? Ko akwai abinda ke damunki ne...?"
Saurin d'ago kai tayi ta d'an dubesa kafin ta sadda kan k'asa tana mai k'ak'aro murmushi take k'ok'arin had'a kalmomi a bakinta.....
"Eh... I'm.. I'm just.... Fine, babu abinda ke damuna...." ta k'arashe tana duban wani gefen tana hango Sojoji sai kai komo suke....
Murmushi Naseer yayi yana mai amsa gaisuwar da Sojoji masu wucewa ke masu...
Salma kam sai bin barikin da kallo take, tana tuna sanda bata da lafiya lokacin da Soja ya kawota....
Wasu tsofaffin jiragen yak'i suka wuce tanata binsu da kallo Naseer na hankalce da ita, sai yafi jin dad'in tafiyar da suke da k'afa.... D'an gyaran murya yayi kafin yace "Kina so ki shiga jirgin ne....?"
D'ago kai tayi tana dubansa had'i da k'walalo idanuwa waje sai kuma tayi saurin sunkuyar da kai sabida yanda idanun Naseer ke haifar mata da bubuwa da dama...
Murmushi take tana mai d'an girgiza kai take fad'in "A'a ni bazan shiga ba.... Ko sai mun shiga kafin mu isa gidan Momyn sannan ka iya tuk'a jirgin ne....?"
Murmushi yayi mai bayyan hak'wara sosai yake jin dad'in hira da ita
"Eh mana na iya tuk'a jirgi amma jirgin yak'i, saidai idan zan d'aukeki ki rakani filin yak'in...." ya k'arashe still na d'an dariya maras sauti...
Salma ta kuma k'walalo idanu waje tana girgiza kai take fad'in "Waii....a'a ni dai bazan je ba...."
Naseer ya kuma murmusawa kafin ya d'an sha gabanta yana mata wani irin duban da sam baisan yanayi ba a hankali ya furta "I thought duk yanda na tsinci kaina zaki iya bina, koda gaba da filin yak'i ne...."
Daskarewa Salma tayi tana dubansa yanda yayi maganar ga k'irjinta dake dukan tara-tara..
Saurin saita kansa Naseer yayi kafin ya murmusa yace "Hey relax... Just kidding...."
Murmushin itama tayi kafin tace "Soja har yanzu bamu iso ba..."
"We're almost there... I'm sorry na d'auko ki da k'afa ke baki saba da wahala ba.... Kinsan mu wahala a jinin mu take Soldiers..."
Salma ta murmusa kana tace "Idan dai tafiya yanki na wahala ne toh kuwa tabbas bazai zamto wahala a wajenmu Fulbe ba sabida mun gaji tafiya da k'afafu...."
Naseer ya kuma murmusawa zuciyar sa na masa wani irin sanyi da dad'i kana yace "Auu na mance ai, gaskiya ne kun gaji tafiye-tafiye...."
Suka d'an dara gaba d'aya lokaci guda dai-dai sanda suka iso gidan Momy Lami....
Sosai Momy taji dad'in ganin Salma, nan ta shiga zolayar Naseer ango to be.... Shiko sai biyeta yake sanda taci gaba da fad'in "Ai na zaci amaryar ka kawo min na ganta kafin a kawo mana ita mai gaba d'aya...."
Naseer ya d'an murmusa kana yace "D'iyar ki dai na kawo maki nasan kunyi kewar juna..."
Momy ta kuma murmusawa had'i da janyo Salma jikinta tana fad'in "Aiko ka kyauta don wllhi ni kaina inata son sake ganin d'iyata Salma, gashi kullum k'ara kyau take..."
Salma dai d'an murmusawa kawai tayi had'i da rufe fuska alamun jin kunya... Shiko gogan ya kasa daina kallon Salma, abubuwan ta sosai yake burge sa, yana bala'in son mace mai kunya....
********
Koda suka iso barkin basu sami Naseer a yanda ya kamata su samesa ba.
Affan ya d'an fuzar da iska yana duban Shareefah kafin yace "See... Haka kurum kin fito dani, banyi niyyan zuwa barikin nan yau ba..."
Shareefah tace "But Affan baka tunanin this is somehow strange... Ka kira Naseer kaji a yanda yake, sannan ka tambayesa idan yana tare da Salma nemanta ake a gida, I'm quite sure idan basu tare hankalin sa zai tashi..."
Affan shiru yayi yana subanta kafin yasa hannu a aljihu ya ciro wayar sa, lokaci guda ya shiga kiran layin Naseer.....
Naseer yana ganin Affan ne mai kira saida ya d'ago ya kuma duban Salma da tuni ta mik'e tabi Momy kitchen tana tayata shirya 'yar tray d'in da take shirin serving d'insu...
Shiru yayi yana sauraron Affan d'in kafin yace "You mean ba'a san ta fito ba a gida...?"
Affan ya jinjina kai tamkar Naseer d'in na ganinsa kafin yace "Yeah kuna ta ina...?"
Take Naseer ya sanar dashi yanda suke..
Shareefah ta dubi Affan bayan sun ida wayar kana tace "You See, kaga abinda nake fad'a koh... That mere girl lied to you, she doesn't love, dama na fad'a bibiyan Naseer take....."
"Enough please...!!" Affan ya katse ta kafin ya zura wayar a aljihu yana fad'in "Muje..."
Mamaki ne ya cika Shareefah da Affan jin Salma wajen Momy Lami tazo.... Gaba d'aya Shareefah ta rasa bakin magana sai k'arasawa da tayi tana hugging Salma take fad'in "Salma wllhi we were all worried about you ne.... Ai bamusan wajen wannan matar kika zo ba...." ta k'arashe tana mai kallon raini wa Momy Lami...
Affan kuwa harara kurum yake faman watsa wa Shareefah, kaman ya tokareta haka yake ji don takaici...
Naseer ya girgiza kai ba tareda ya furta komai ba, Momy ce ta janyo hannun Salma suka keb'e
"Salma ina sauraren ki, wacece ita wancan maras d'a'an.."
Saida Salma ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace "Ita ce Soja zai Aura...."
Momy tayi shiru tana nazarin abun don kuwa sam bata hango soyayyar Shareefah a idanun Naseer ba, sannan koda basu furta ba shida Salma tana jin wani babban Al'amari a tattare dasu...
Bayan sun fito tafiya ne Shareefah ta janyo hannun Salma suka d'an tsaya daga baya, tamkar mai rad'a take fad'i mata.... "Ki kallesu suna son junansu tamkar Yaya da kuma k'ani so please don't try to bash their heads, ki tsaya a matsayin ki, ki k'aunaci Affan da zuciya guda sabida ina mai tabbatar maki yana k'aunarki beyond your expectation, ni kuma na maki alk'awari I'll be by your side bazan goyi bayan Azeema ta kasance da Affan ba..."
Murmushi Salma tayi kafin tace "Yo dama ina zaki goyi bayan d'an uwanki ya auri k'azama irinki ai dole ki masa fatan samun na gari kaman yanda nima nake fatan Soja ya sami ta gari... Ina fata kin fahimce ni..."
Murmushin yak'e Shareefah tayi kafin tace "Salma k'arfin halinki ka iya janyo maki rayuwa mai cikeda k'unci A DUNIYAR MU... "
Salma bata kai ga amsata ba suka jiyo muryar Naseer na fad'in "Wai me kuke tattaunawa ne haka, kuyi sauri kuzo ku wuce gida hadari ya soma rufe garin..."
Shareefah ta bisa da mayen murmushi kafin tace "Eh my Soldier muna k'arasowa.."
Duban Salma ta kuma Yi kafin ta d'an karkata kai tace "Idan kunne yaji toh fah tabbas jiki ya tsira..."
Salma bata furta komai ba sai kallon tsana data raka Shareefah dashi...
Affan ya lura da yanayin Salma, a hankali ya bud'e murya yace "Salma are you alright...?"
Lokaci guda suka had'a idanu itada Naseer, su duka sunama juna kallon da basu san sunayi ba... Saurin saita kanta tayi had'i da yin murmushin da yafi kama da yak'e kafin ta shiga gyad'a masa kai tana fad'in "Eh... Eh lafiya ta Lou...." Shareefah ta d'an dafata tana mayaudariyar murmushi take fad'in "Kasan budurwar taka da kunya Allah dai ya kaimu lokacin bikin ku da zaran anyi namu..."
Affan ne daketa faman murmushin jin dad'i ya sami zarafin amsawa da ameen, Salma da Naseer kam sam basu sami zarafin amsawa ba...
Gaba d'aya sukayi sallama ma Naseer suka wuce gida Shareefah sai rawar kai take uwa angon biri, shi kuwa gogan sai basarwa yake yayinda Salma ta tsinci kanta da jin haushin abinda Shareefar keyi..
*******
Ana sauran kwana biyu d'aurin auren ya tattaro ya dawo gida, gaba d'aya gidan nasu ya zama busy sosai, mutane shige da fice kawai ake...
Jamila ta sami sauk'in tak'urin Alh Kabeer, i zuwa wannan lokaci ta amince ma zuciyar ta shakka babu soyayyar wannan likitan ne ya kamata lokaci guda, haka kurum taji tana son k'aurace ma sab'on da take, a iya rayuwarta tayi zaton kud'i shine jin dad'in rayuwa, a tunanin ta maza basu wulak'anta matan titi sai na cikin gida tunda ta gani wajen mijinta na fari uban d'iyarta Alh Nuhu, sai gashi wanda ya sameta a layin ma na wulak'anta ta, tabbas Inno tayi gaskiya data masu hud'ubar tsare mutuncin su, yau da ace bata hau motar kwad'ayi ba tabbas tasan da hakan bai faru da ita ba.... Ta kuma goge hawayen nadaman da suka zubo mata kafin ta d'auki paper da pen tayi note ta ajiye bisa dining table... D'aukar d'iyarta tayi ta sab'a had'i da tattara kayanta kana ta cika ma rigarta iska, ko motar da ya bata ma bata d'auka ba..
*****
Naseer ya kuma duban Fawaz yana d'an ware idanu had'i da yin murmushi kafin yace "So tell me, a ina take surkar tawa...."
Dariya Fawaz ya d'anyi yana mai kai spoon d'in trifle bakinsa yake fad'in "Uncle bazaka yarda dani ba sabida ni kaina ban yarda da abinda zuciyata take sanar dani ba shiyasa ma ban kuma bin takan ta ba, I don't know, it just can't happened...."
Kallon sa Naseer yake yana nazarin sa, sai yake jin labarin soyayyar Fawaz tamkar nashi ne da Salma, wacce tuni ya yak'i zuciyar sa a tunanin sa.... Saida ya sauk'e ajiyan zuciya kafin shima yakai chocolate truffle bakinsa kana yace "Fawaz whatever your heart keeps telling you ka zauna sosai kayi tunani akai, so tari mukan so abu ya zamana a k'arshe bamu samu, Allah yafimu sanin abinda yasa ya hanamu abinda muke so, tsarin Allah shine dai-dai... Son ka sani a kullum kana tare da addu'o'in mu, bani da burin da ya wuce naga rayuwar ku ta inganta fiye da tawa, all of you..."
Murmushi Fawaz yayi kafin yace "Uncle na gode, na gode da kyawawan shawarwarin ka, kai d'in daban ne...."
Murmushi Naseer yayi kafin ya d'an yi kafin ya mik'a hannun sa saman sumar Fawaz had'i da d'an barbaza suman kana yace "Ka gama ci muje kasan inada commitments sosai yau kada ka b'ata min schedules d'ina..."
Saurin tuttura abincin desert d'in nasa yayi kafin ya mik'e yana fad'in "Ni na isa na b'ata schedules d'in Soja salon a jefani a guardroom.... Koda yake Aunty Shareefah bazata bari ba..."
Dariya maras sauti Naseer keyi kafin ya d'an kama kunnen Fawaz yana fad'in "Ka faye son wasa bansan yaya akayi kayi karatun likitancin ba ma...."
Fawaz yana d'an k'ara had'i da dariya yake kama kunnen sa yanda Naseer ya ja...
******
Tun daga gate d'in gidan kake jiyo sautin Kid'a na tashi alamun ana shirye-shiryen biki, yau kusan kwana uku kenan ana banka Kid'a a gidan Mamy tunda aka shiga satin bikin
Fawaz ne ke driving yayinda Naseer ke zaune mazaunin mai zaman banza, sai faman zuba Fawaz keyi dukda ba wani amsa sa Naseer d'in keyi ba...
Kaman wacce aka jefo ta sai ganinta suka gabansu dai-dai lokacin da zasu karya kwanan gidan Daddy, itama kuma gidan ta nufa...
Da k'arfin gaske Fawaz ya danna birki had'i da horn.... Bakisu d'auke da ambaton Allah.. Naseer fad'i yake "Careful Fawaz....."
Taimakon Allah d'aya basu bi kanta ba gashi harda yarinya a hannun ta... A tare suka fito suka nufi yanda take...
Gaba d'aya burki sukayi domin kuwa Naseer ya gane Baby Falaq, shi kuwa Fawaz baki har na rawa yake furta "Uncle itace.. Itace wacce nake fad'a maka..."
Mik'ewa Jamila tayi saurin yi tana duban Fawaz fuskar ta d'auke da murmushi take fad'in "Dr....".
Kallonta sosai Fawaz yayi kafin yace "Hope dai bakuji ciwo ba..."
D'an girgiza kai tayi kana tace "A'a bamuji ciwo ba.."
"Ina zaki da kaya haka....?" Fawaz ya kuma tambaya..
Sai sannan Naseer ya furta "Inaga dai kinji rok'on 'yan uwanki ne kin dawo wajen su..." yayi maganar fuskar sa d'auke da murmushi..
D'an murmushin yak'e tayi dukda ba wani gane Naseer d'in tayi ba ta dai ga shida Fawaz sunada zubin turawa k'ila duk yanda akayi d'an uwansa ne sannan ko ba'a fad'a ba sunada danganta da Alh Ali Safwan tunda gashi har sun san da zancen su... Lokaci guda kuma zuciyarta ta shiga bugu da sauri tana tunanin kada su Salma sun sanar dasu zaman bariki take....
Cikin sauri ta saita kanta tana mai ci gaba da jan trolley d'inta take fad'in "Barin k'arasa ciki.. Na gode..." Sauri sauri ta shige ba tareda ta kuma dubansu ba dukda mafarkin sake ganin likitan da ta dinga yi...
Har saida ta shige gate kafin Fawaz ya d'auke idanunsa daga dubanta...
A tare suka nufi motar sukayi horn mai gadi ya bud'e masu... Naseer ya d'anyi gyaran murya kana yace "So wannan itace labarin da ka bani d'azu..."
Fawaz yayi saurin jinjina kai kana yace "Uncle a ina ka santa, sannan wani magana naji kayi gameda ita...?"
Naseer ya d'an murmusa sanda yake parking gidan kuwa akwai mutane da dama sai kai komo ake ko k'yallin Jamila basu hango ba kafin yace " it's a long story Fawaz ka bini bashi sai an gama da hidimar bikin nan...."
D'an jinjina kai Fawaz yayi ba tareda ya kuma furta komai ba, don kuwa gaba d'aya ya shiga rud'ani...
A parlorn Daddy Shareefah ta masu masauk'i duk burin Fawaz na yazo ya gaida Auntyn nasa sai ya zama wani sukuku dashi, abubuwa da dama suna yawo a kwanyar sa...
****
Jamila kuwa kasancewar dakwai 'yan biki shiyasa sam ba'a lura da shigowar ta ba sai 'yan uwanta, haka suka rungume juna suka kulle kansu a d'aki suka ci kukan su, ko babu komai burinsu ya cika 'yar uwar su ta dawo garesu....
Su Mamy basu tashi lura da zuwan Jamila ba sai dare lokacin 'yan kaikomon shirye-shiryen biki sun watse..
Mamy tamkar mahaukaciya haka ta dinga bore tana fad'in wllhi karuwan nan bata da matsuguni a gidan ta.. Ilham kuwa dake rungume da Falaq d'inta kuka ta dinga yi tana rok'on Mamy da tayi hak'uri ta bar Addar su ta zauna... Mamy tamkar wacce ake ingizata, su Azeema kuwa sai kallon ikon Allan suke... Saida Daddy yayi magana guda ya tabbatar babu yanda Jamila zata tafi zata zauna da 'yan uwan ta kaman kowa a cikin gidan... Haba nan fah Mamy ta kuma birkicewa ta shiga haurawa sama da cangwalellen k'afarta tana kwaso kayan su Salma tana watsar waje....
Basu sami daman saita Mamy a gidan ba saida Affan ya kwarkwance mata gaba d'aya ya nuna mata shima zai bar gidan har ya shiga jibga kayan sa a mota tamkar Affan d'inta na da.... Duk hak'urin da Mamy ke bashi yak'i ji yak'i gani, dama haka yake idan ransa ya b'aci...
Mamy ta kuma rik'o rigarsa tana fad'in "Affan ka min rai kada ka tafi..."
Fizge rigarsa ya kuma yi yana wani irin huci yake fad'in "Zan tafi a karni a filin yak'i sai ki huta,... Ina son Salma, ina son aurenta soon, a haka ne da wannan d'abi'ar taki zan aureta cikin kwanciyan hankali.... Bazaki tab'a barin rayuwata cikin kwanciyar hankali ba gwara na tafi ki rasa ni gaba d'aya ki huta...."
Girgiza kai Mamy take tana fad'in "Wllhi Affan na tuba na yarda su zauna... Idan ka tafi aka kashe ka nima binka zanyi Affan..."
Ganin tana kuka sosai ya sanya Affan karkatowa had'i da rungumeta, yana son Mamynsa sosai amma baison halinta ko kad'an...
K'wallan da Salma ke k'ok'arin mayarwa ya kasa komawa saida ya zubo, Affan ya cancanci ya mallake ta koda babu d'igon soayyar sa a zuciyarta, tabbas ta yarda Affan masoyinta ne, ta yarda zai iya komai wajen kareta da 'yan uwanta..
A hankali Jamila ta tako ta rungume Salma ganin hawaye na zuba bisa k'uncin ta...
Duk wannan drama da ake yi Daddy bai fito ya saurara ba, don yanaji k'iris ya rage bak'in cikin Asma'u ya haifar masa da mummunar cuta.. A halin da ake ciki ma ba wani jin dad'in jikinsa yake ba.... Ya yanke shawarin zaije ya sameta da dare suyi magana sosai bayan kowa ya kwanta, don tunda ta soma hidiman biki ta k'aurace wa d'akin Daddy sabida idan tanacan bazata samu ta dinga waya da Laure son ranta ba, ta turata can bakin border a had'o wa Shareefah kayan mallakan miji ta hanya tsafi da Asiri, Laure kuwa sana'a ta bud'e mata don duk wani gudumawa da ake kawowa tuni Mamy take tura mata...
Ko kad'an basuji alamun tab'a k'ofan parlor ba, da shike sun jima suna kallo suna hira a parlorn har suka soma aikata sab'on nasu a parlor, sam basuyi tunanin akwai mai shigowa ba...
Kasa ci gaba da tura keken sa yayi sai hawaye dake gangaro masa... Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un.. Cikin kunnuwar sa yake jiyo sautin Shareefah tana fad'i ma Azeema "Baby zanyi kewarki na d'an lokuta, da zaran an gama zaman amarci zamu ci gaba daga yanda muka tsaya..." Ta k'arashe su duka suna masu sunbatu ma juna
Jiri ne ke neman kada Daddy daga saman wheelchair d'insa... Shareefah, Shareefah dai d'iyarsa, ko tsawon shekaru nawa suka d'auka suna aikata wannan mummunar sab'o a gidansa wa ya sani, wai itace yake shirin aurar da ita a gobe....
Ikon Allah ne ya isar da Daddy parlorn sa amma yanda yaga rana haka yaga dare...
A b'angaren Salma ma bata wani sami bacci ba tunanin rayuwar dake shirin tunk'aran Soja ya hanata sukuni... Dole tayi shiru a d'aura auren nan ko don Daddy da Affan, suna da zuciya mai kyau, sanin abun zai iya jefa rayuwar su cikin garari musamman Daddy...
******
Yayinda aka ci gaba da shagalgulan biki, shiko Daddy tunanin hanyar da zai b'ullo wa lamarin yake, da ace fad'a masa akayi ba gani yayi ba, toh kuwa shakka babu zai musa... Saidai kuma shid'in ganau ne ba jiyau ba, tabbas aura wa Naseer Shareefah akwai babban cutarwa a ciki, sannan tabbas bazai iya fitowa fili ya sanar da Naseer ga laifin da d'iyarsa keyi ba.... Gaba d'aya Daddy Ya sauya
Su Shareefah amarya kuwa tuni ancigaba da shagulgulan events
****
Kallon Mamy kurum yake yanda take faman rawan k'afa, tun farar safiya algaita ke faman tashi a gidan... Musamman ta shirya Daddy yau babu hantara balle tsangwama.. Abinda ya d'an bawa Mamy mamaki shine duk yanda Daddy Ya d'aukaki auren nan a baya taga yau ya sauya, ya koma wani iri haka nan, ko magana baya yi... Tuni ta danganta hakan da kewar Shareefah da zaiyi...
A b'angaren Innah ma fah babu sauk'i yau har hula ita ta saka wa Naseer ta feshe sa da turaruka.. Fawaz da Lubna kuwa sai zolayar su suke.. Irin Innah na murna za'a kuma yin surka.. Cikin zuciyar Innah kuwa fad'i take _Wannan surkar zuwanta yafi mata zuwan ko wacce surk dad'i, zata yarda Naseer k'wallon mangoro ta huta da k'uda..._
Kana ganin Naseer kaga ango, babbar rigar ta amshe sa abinka da wanda bai saba sakawa ba sai yayi matuk'ar masa kyau.. Duk yanda ya wuce watsa k'amshi yake, Marok'a kuwa tun daga gida suke biye dashi suna wasa sa.. Fari mai farin Aniya...
K'arfe sha d'aya na safiyar ranar asabar aka hallara a masallacin juma'a dake gefen gidan Daddy don d'aura auren Naseer Sa'oud Santana da kuma amaryar sa Shareefah Ali Safwan..
Daga gidan Mamy kana iya jiyo loudspeaker d'in masallacin...
Bibbiyu Mamy ta soma gani sanda taji sunan da bata tab'a tsammani ba na tashi cikin loudspeaker ma'ana da ita ake d'aurin auren...
Wani k'ara ta saki tamkar zararriya lokaci guda tayi watsi da crutches d'inta tana shirin zubewa a k'asa jama'an dake wajen suka tallafe ta...
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*34*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Fatan Alkhairi Barrister Asma'u.. Ubangiji ya bar k'auna 💕🤝🏼*
Daga Naseer har Affan mik'ewa sukayi cikin wani irin yanayi... Kallon juna suke yayinda masu algaita suka ci gaba da busawa daga waje domin kuwa tuni an d'aura aure....
Girgiza kai Affan yake hawaye na kwararo masa lokaci guda, ji yake tamkar mafarki yake ba gaskiya bane... Ta yaya za'a masa irin wannan butulci da cin amana.... Kasa furta komai yayi sanda ya tabbatar gaskiya ne ba mafarki ba.... Baisan yaya akayi ya fice ba shidai kurum yasan duniyar ta soma juya masa, bibbiyo yake kallon jama'an dake tare a wajen kunnuwar sa
suna jiyo masa sauti tamkar daga nesa-nesa..... Idan ba wani ikon Allah ba yana gab da zubewa..
Fifita ake kanyima Mamy masu Kid'an data kwaso kuwa basu daina ba, mutane sai mamaki suke domin kuwa kafin a sanar da wannan d'aurin aure Mamy tafi kowa takawa dukda macogal d'in k'afarta sai gashi tayi watsi da crutches lokaci guda...
Hannu aka Mamy ke ihu tana birgima a k'asa tamkar 'yar bori take fad'in ta shiga uku ta mutu ta lalace... Mutane kuwa sai fifita suke mata
Batasan sanda tayi fatali da makeup kit d'in mai shera mata kwalliya ba sanda Azeema ta kai mata labarin da d'uminta, ta fito tana wani irin ihu tayi hanyar waje saidai kafin ta fice Azeema ta shiga kiran masu Kid'an nan su taimaka mata a shigar da Shareefah d'aki a kulle.... Taro fah ta birkice gaba d'aya
Duk wannan bidiri da ake su Salma basu sani ba suna can d'akin su, ita tana jimamin Soja ya zama mijin Aunty Shareefah yayinda Ilham da Jamila ke shiryawa, da shike akwai sautin kid'a na tashi a cikin gidan shiyasa sam basu jiyo k'aran speaker d'in masallacin ba, mutanen dake haraban gidan ne kawai suka iya jiyowa...
Wani fincika Shareefah tayi ta nufi d'akinsu Salma yanda kasan sabuwar kamun hauka...
A tamanin suka mik'e gaba d'aya suna rarraba idanu..... Azeema sai k'ok'arin janye Shareefah take ....
Kai tsaye Salma ta nufa tana wani irin kuka mai sauti take fad'in "Salma kin cuce ni, ke azzaluma ce, kin rantse sai kin rabani da Soja.... Ki zuba ruwa a k'asa ki sha... Amma wllhi wllhi wllhi ni Shareefah bazan tab'a barinku ku rayu cikin aminci A DUNIYAR MU ba, wllhi sai na zame maku fitina ta ko....." bata iya k'arasawa ba sai zubewa da tayi a wajen.... Azeema tayi saurin tallabo ta yayinda Jamila ta taya ta......
Gaba d'aya sun zama confused babu kaman Salma wacce garin ya soma juya mata, bata fahimci komai ba a duk abubuwan da Shareefah ta fad'i..... Batasan yaya akayi ba amma ta ganta zaune saman gado Ilham na rik'e da hannayen ta....
Murmushi Daddy keyi hawaye na neman kwararowa daga idanunsa sanda suka fito daga cikin masallacin yana mik'a wa Naseer hannu wanda ya koma tamkar mutum mutumi tun bayan shud'ewar wasu dak'ik'ai.... Wai yau shi Naseer Santana shine ya zamto mijin SALMA... Yau rana ce da ya kamata a d'aura aurensa da Shareefah sai kuma akasin hakan, sannan da ace ba mahaifin Shareefah bane yayi wannan aure tabbas zaice b'atan suna yayi amma sai gashi sadakin da ya bayar domin auran Shareefah an d'aura masa aure da watan ta.....
Kasa mik'a ma Daddy hannu yayi suyi masabaha sai girgiza kai da yake cikin tsananin rud'ani yake furta "Daddy I'm confused..... I need an explanation... Daddy please what's going on.... Daddy don Allah ka sanar dani..."
Cikin sauri Fawaz ya k'araso ya rik'e uncle d'in nasa tausayin sa fal zuciyar sa...
Alh Ali Safwan hannu yasa ya goge hawayen da suka zubo masa kafin yace "Naseer ka sani bazan tab'a cutar da kai ba, sannan ka sani a rubuce take SALMA itace matarka, ina fata zakayi na'am da canjin da na maka....."
Naseer ya ci gaba da girgiza kai yana fad'in "Daddy still ban gane ba, ban gane komai ba....."
Hannun Naseer dake tsaye kansa Alh Ali ya kamo kafin yace "Mu shiga cikin gida na maka bayani....
Kasancewar dakwai mutane da dama a bakin masallacin da kuma gate d'in gidan yasa basu samu shigewa cikin gidan lokaci guda ba saida Daddy Ya tsaya yana gaisawa da jama'a yana masu godiya, shi kuwa Naseer tamkar wani hoto haka yake rik'e da wheelchair d'in Daddyn, Fawaz na biye dasu don bazai iya barin Uncle d'in nasa cikin wannan yanayi ba...
Fawaz ne ya d'an keb'e da wani abokin Naseer d'in Captain Sadiq suka d'anyi magana... Kafin Captain Sadiq ya sami sauran Friends d'in nasu
Kaman wata mahaukaciya haka ta dinga koran mutane 'yan biki tana fad'in biki ya watse, wasu har dukansu da crutches d'inta take tana fad'in su fice su bar mata gida, masu Kid'a ma haka ta fafure su, Mamy ta koma tamkar zautacciya... Dama babu danginta da ta gayyata balle na mijinta, waye ma zaizo hidimar Mamy matan da bata so kowa nata ya rab'eta, Azeema dai da ta zame mata k'arfen k'afa itace ke tare dasu tamkar wacce tasha fitsarin kaza sabida rashin zuciya da kuma son abun duniya da ya rufe mata idanu ko soyayyar d'an Mamy da ya rufe mata idanu....
A d'ari biyu Azeema ta nufo k'asa tana k'walla kira wa Mamy tana nuna mata hanyar cikin gida tana fad'in "Mamy kizo kar mu rasa Shareefah sai sumewa take... Mamy don Allah kizo..."
Ai babu shiri Mamy ta sab'i crutches d'inta ta soma cangwalawa ta nufi ganin d'iyarta kafin ta dira masu Salma ta masu uwar watsi tunda tasan yau kam saidai Affan ya goya mata baya....
Mamy tayi kan Shareefah tana kuka take fad'in "Shareefah ta kar ki tafi ki barni, an zalunce mu kam amma ki sani d'aukan fansa ya zame mana wajibi...." sai faman bubbuga fuskar Shareefah take tana hawaye..
Azeema dake gefe murmushin jin dad'i kurum take domin kuwa plan d'inta ya tafi dai-dai, A daren da Daddy Ya kamasu tsaf taji zuwan Daddy tak'i tayi alerting Shareefah sabida tasan babu yanda za'ayi Daddy yaga tana wannan laifi ya aura mata Naseer, sannan tasan Daddy bazaiyi tunanin bawa Naseer makauniya ba sabida zaiga kaman ko don ba shi ya haifesa bane yasa ya bashi mai nakasa, sannan tasan bazai tab'a bawa Naseer Jamila ba sabida Naseer auren budurwa ya nema Daddy bazai sauya masa da bazawara ba... Tasan dole Salma ce kawai Daddy zaiyi replacing d'inta da Shareefah... Idan kuwa haka ta kasance tasan Affan bazai tab'a samun Salma ba k'areshe dole itace zata mallaki kayan ta..... Ta kuma yin wani murmushi tana duban Shareefah da Mamy da suka koma abin tausayi lokaci guda.... Bata mance ranar data lab'e taji suna fad'in da zaran Shareefah ta auri Naseer zasu san yanda zasuyi su rabu da ita.... Tabbas ganinta kawai suke amma ta wuce tunanin su nesa ba kusa ba.....
*******
Daddy ya umarci Naseer ya haura dashi parlornsa na sama...
Naseer ya dubi Fawaz kana ya masa alama kan ya jira sa a waje....
Cikin sauri Fawaz ya ninjina kai kafin yayi yanda Naseer d'in ya umarta...
Fawaz na fitowa ya hangi su Salma suna shirin ficewa daga gidan, saurin k'arasawa yayi yana fad'in "Ina kuma zaku je....?"
Jamila ce kawai ta sami zarafin girgiza masa kai kana tace "Dr dole mu bar gidan nan don tsira da rayuwar Mu, bazan iya bari rayuwar 'yar uwata ya shiga garari ba....." Ta k'arashe tana kuma rik'o hannun Salma wacce gaba d'aya hankalinta baya tare da ita, kana ganinta zaka iya shaida hakan.. Gani take abubuwan kaman a wasan kwaikwayo suke faruwa koma da ace mafarki ne da sai tafi aminta wa zuciyarta, tabbas ta kasa yarda hakan a gaske yake faruwa...
Fawaz ya d'an girgiza kai kafin yace "A'a a halin yanzu Uncle shike da iko da Salma, don Allah kuyi hak'uri ku koma cikin gida insha Allah komai zai zama normal..."
Aya ya dasa wa maganar nasa hango Mamy da sukayi ta nufi sashen Mamy tamkar zata tashi sama, sai ka rantse bada crutches take tafiya ba.....
Ko kallo basu ishe Mamy ba tasa kai sai tafiya take, gaba d'aya suka bita da kallo daga Jamila har Fawaz idan ka d'auke Salma da ba fahimtar komai take ba, Ilham kuwa ba gani take ba, damuwar halin da 'yar ywarta ke ciki shi ya cika zuciyarta...
Gyaran murya Daddy yayi zai soma magana Mamy ta turo k'ofar ta shigo tana wani irin tururi da huci tankar zakanya, ko kallo Naseer bai isheta ba, idanunta naga Ali Safwan tamkar wacce zata rufesa da duka haka take dubansa....
Ganin yanayin Mamy d'in yasa Daddy d'an dafa Naseer wanda yayi zaman rak'umi a gefensa bisa carpet kafin yace "Naseer kayi hak'uri kaje gida, zan nemeka zuwa dare sannan na baka matarka ka tafi da ita..."
Jinjina kai Naseer yayi ba tareda ya iya furta koda kalma kafin ya mik'e ya fice ba tareda ya iya duban Mamy ba, itama Mamy d'in ko kallo bai isheta ba, har i zuwa lokacin idanunta na bisa Ali Safwan....
Salma tana hango Naseer ya fito daga sashen Daddy k'irjinta ya buga tamkar an sauk'e guduma... Kafin su ankara sai gani sukayi ta runtuma a guje ta koma cikin gida... Sai sannan Jamila da Fawaz suka kula da abinda ya sanyata gudu hango Naseer da tayi ne... Fawaz ya d'an dubi Jamila dake rungume da Falaq hannunta guda rik'e da Ilham kafin yace "Ki kula da 'yar uwarki don Allah, tana buk'atar kulawan ki sosai, barin k'arasa wajen Uncle Naseer...."
Jinjina masa kai kurum Jamila tayi kafin suka sakar ma juna murmushi Jamila taja hannun Ilham suka koma cikin gida... Daga Naseer har Fawaz waje suka nufa don kuwa motocin su gaba d'aya suna waje...
Tuni Naseer ya kwab'e babban gare da hula, kana ganinsa kasan ba daidai yake ba, d'an dafa Fawaz yayi kana yace "Fawaz ka k'arasa gida, nasan suma hankulansu a tashe yake suna tunanin halin da muke ciki ko nace na tsinci kaina ciki.... Zan wuce dubo Affan kaga baya cikin gidan nan, kuma na kira can barikin mu ance baije can ba, sannan baya d'aga wayata...." Shiru ya d'anyi had'i da dafe kai..
Fawaz kuwa girgiza kai yayi kana yace "Uncle bazan iya tafiya na barka cikin wannan halin ba, idan nemo Affan zakaje saidai mu tafi tare, in fact I can't even let you drive a halin da kake ciki..."
Naseer ya d'an fuzar da iska yana duban Fawaz kafin ya d'an jijjiga kafad'unsa yace "Fawaz zan I... I can go through this, I know I can.... Na sani komai muk'addari daga Allah.. Sannan Allah baya d'aurawa rai abinda bazata iya ba, kar ka damu Son, na gode da kulawar ka, kaje gida pls, kaima kana buk'atar hutu...."
D'an jinjina kai kurum Fawaz yayi ba wai don yayi niyyan tafiyar ba, tausayin Uncle d'in nasa fal zuciyarsa, k'arfin hali kawai yake amma kam babu wanda irin wannan abu zai faru dashi ba tareda wani k'wakk'waran bayani ba ya zama dai-dai.. Saidan kawai dama Uncle d'in nasa jarumi ne, shi ya sani...
Sallama sukayi kafin had'i da fatan alkhairi ma juna kafin suka shige moticinsu...
*******
Ya jima yana zaune k'asar bishiyan hawaye na neman gangaro masa, tabbas da zaiyi kukan da sai yafi jin dad'i akan k'uncin da ta tare masa cikin zuciyar sa... A hankali yake furta "Why all this... Why... Why.. Shareefah was right... Gaskiya ta fad'i da tace suna son juna, Naseer na tabbata samun Daddy kayi ka sanar dashi Salma kake so, nasan Daddy Na, nasan kalan kyautatawar sa, nasan bazai tab'a maka abinda baka so ba Naseer, ...... I was stupid da na yarda ba son Salma kake bar.... Meyasa zaka min haka, sabida nayi breaking heart d'in 'yar uwarka Lubna, shine bari ka rama ta hanyar rabani da Salma.. The love of my life... Why Naseer... Meyasa zaka min haka...." Muryar sa ta soma rawa lokaci guda...
Wani irin huci Affan ya shiga yi, lokaci guda ya dunk'ule hannunsa ya shiga kai duka ma bishiyar da iyaka k'arfinsa... Hawayen azaba suna tsartsafowa daga idanun sa...
******
Girgiza kai Daddy yayi hawaye na kuma zubo masa yake fad'in "Kin sani Asma'u kika kasa sanar dani, why... Meyasa, meyasa baki sanar dani ba, sabida ha'inci da son zuciya... A haka ne kike so mu baiwa Naseer mu cuci bawan Allah, sabida d'iyarmu ce, na tabbata bazaki so Affan ya auri Azeema ba abokiyar fasik'ancin nata... Kuma wllhi kinji na rantse da mahallici na sai na sanar da Naseer dalilina na hanasa auren tilon d'iyata mace na kuma Aura masa Salma.... Sannan nasan idan nayi bayani wa Affan zai fahimce ni inhar na isa dashi..Don haka ki fice min a d'aki banson ganin ki Asma'u...." ya k'arashe yana goge k'wallan dake ciko idanunsa...
Mamy na huci taci gaba da fad'in "Kai Ali wllhi wllhi baka isa ba, dole ka warware auren shiriritan da kayi..... Kai nifa yanzu bakada sauran amfani a wajena domin kuwa baka da komai yanzu, sai zama bisa keken guragu, duk fad'i tashin da nake na ganin Shareefah ta auri Naseer inace sabida rayuwar mu ta inganta nake, banda tsiya babu komai a tattare da kai, sun tsafe ka sun baka a damun fura ka sha, ka gwammaci rayuwar wancan tsinanniyar yarinyar ta inganta akan na d'iyarka... Toh wllhi baka isa ba, bazan tab'a bari ka sanar da Naseer komai ba...."
******
Shareefah tana mik'ewa ta nufo parlor a tamanin nan ta tarar dasu Salma sunyi jigum-jigum kaman masu makoki.. Kwalliyan fuskar ta duk ta zazzago ta koma tamkar Zombie... Kitchen ta nufa a tamani ta rarumo wuk'a tayi kan Salma tana fad'in sai ta kasheta.. Azeema kuwa a tamanin ta fice tayi sashen Daddy yayinda Jamila ke faman kokawan k'wace wuk'an hannun Shareefah...
Duk iya k'ok'arinsa kasawa yayi da k'arfin gaske Mamy ke gunguro dashi bakin stairs... Daddy fad'i yake "Asmau kiji tsoron Allah kada ki aikata laifin da zaki zo kina da kinsani a baya..."
Mamy bata fasa turasa tana cangwala crutches d'inta take fad'in "Uwar da na sani ne.. Baka da wani amfani a wajena, kasheka bazai tab'a zame mun da na sani ba, tunda duk wani hanyar alkhairi toshe mun lake... Da zamanka gwara babu kai.. Don idan baka nan ni zan san yanda zanyi na had'a auren Shareefah da Naseer... I'm sorry my dear husband uban 'ya'yana sai mun had'u a rayuwa ta gaba... Tana kaiwa nan ta gungura keken nasa ya soma gangarowa daga saman bene... Sai huci take tana hura Hanci... Lokaci guda Azeema ta saki gigitaccen k'ara sai sannan Mamy ta kula da ita...
Jin mahaukacin ihun da Azeema ta saki ya sanyasu gaba d'aya nufowa parlorn Daddy...
Shareefah kuwa ganin mahaifinta na kwance cikin jini ga keken sa a gefe ya sanyata sakin wani mahaukacin k'ara tayi kansa tana jijjigasa tana kuka sosai take ambato sunan sa....
Salma da Ilham manne juna sukayi suna kuka dukda Ilham d'in bata ganin abinda ke faruwa amma tasan Daddy ne ya shiga cikin wani hali...
Jamila ce ta ciro wayarta a rud'e tayi dialing lambar Fawaze... Baiko isa gida ba yaga wayar Jamila... Hankali tashe ya karya kan motar sanda yaji abunda take sanar dashi daga cikin wayar, ga koke-koke da yake jiyowa daga cikin wayar....
Mamy ma a tamanin ta kwanta saman Daddy da Shareefah tana kuka sosai sai ka rantse iyakacin gaskiyarta kenan... Azeema ce kurum ke watsa wa Mamy mugun kallo...
********
Duk joints d'in da yake tunanin zai sami Affan wajen bai same sa bar.. Yana tsaka da driving wayar Fawaz ya shigo masa.. Nan Fawaz d'in ke sanar dashi abinda ke faruwa...
Innalillahi wa inna'ilahirraji'un kawai Naseer ke iya ambatawa kafin yace "Fawaz kayi sauri ka isa gani nan k'arasowa nima..." Saurin karya kan motar Naseer yayi cikin tsananin tashin hankali...
Koda Fawaz ya k'araso da k'yar aka samu aka matasar da Mamy da Shareefah daga kan Daddy... Nan Fawaz ya d'an shiga dubasa tabbas kuwa Daddy na numfashi bai mutu ba... Daidai lokacin da Naseer ya k'araso Fawaz ke fad'in "Uncle yana numfashi he's still alive mu k'arasa asibiti..
Take Mamy ta had'iyi kukan da take k'irjinta yayi wani irin yankewa ya buga ta soma gani duru-duru...
*****
Wani wawan tsalle Innah tayi tamkar 'yar biri ta damk'o wuyar Alh Kabeer tana fad'in "Meyasa baku kashe su ba tun tuni... Meyasa baku kashe yarinyar ba.... Ka b'ata min komai, ka rusa komai ka wargaza....."
Azabane ya ishe sa baisan sanda ya had'a Innah waje guda yayi jifa da ita ta bugu da jikin kujera ba..
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*35*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*ZBI mutanen Innah Mamy da Azeema 🤪 ina yinku yasin yanda duk baku tsammani.... Tsakanina daku sai kyakkyawan fata na alkhairi.... Allah shi bar k'auna❤🤝🏼*
Yanda kasan birin tashe haka Innah ta kuma mik'ewa da alama ko zafin buguwan da tayi bataji ba ta kuma cakumo Alh Kabeer tana wani irin huci take fad'in "Dolancin ka shike jawo mana koma baya, tun a fari saida na hanaka k'ona gidan gonar mutumin nan...wai duk kayi ne akan mushiness Naseer tunda surkinsa ne sai gashi burina na Naseer ya auri Shareefah na kashe shi ta hanyar amfani da ita bai cika ba.... Kabeer a karatun dolanci kazo na farko.... Sam bakada amfani tunda ka kasa kashe min Naseer...."
Jefar da ita ya kuma yi yana sosa wuyar sa kafin ya matso daf da ita yana huci yake fad'in "Da kinsan tashin hankalin da nake ciki da baki soma wannan maganganun naki ba.... Yarinyar nan itace tasan yarana da na tura don k'ona gidan gonar sai gashi ta tabbata Naseer ita ya aura... K'arewa mun zama family..... A duk randa tayi idanu hud'u da Maina komai na iya wargaje....." Bai kai aya ba yaji saukan wawan mari a fuskar sa, ga hannun nata k'ashine zalla amma idan ta watsa masa mari sai yaga taurari suna yawo cikin idanunsa....
Kukan kura yayi ya cakumo Innah lokaci guda ya shiga kifa mata mari babu ko k'akk'autawa, idan kuwa ya mareta sai tayi juyi tamkar mai rawan k'oroso.... Girgiza masa kai take tana k'ok'arin k'watan kanta inaa ya had'eta waje guda ya nad'e sai kifa mata mari yake fad'i yake "Wllhi duk marina da kika sha yi sai na fanshe su yau...." saida ya mata lilis kafin yasa hannu a suit pocket d'insa ya zaro wata 'yar leda mai d'auke da garin cocaine lokaci guda ya turbud'e hancin Innah da cocaine d'in.... Kan kace me Innah ta soma layi tana vibrating... Lokaci guda ta zube a wajen...
Tsaki yayi don gaba d'aya zuciyarsa wani irin tafarfasa take... Lokaci guda ya shiga janyo Innah a k'asa ya watsa ta cikin d'akinta had'i da jawo k'ofar ya rufe harda wani karkad'e hannu saikace wanda ya zubda dotti.... Sauri-sauri ya suri motar sa ya fice daga gidan....
******
Intensive care aka ajiye Daddy, babu mai shiga d'akin da yake saiko likitoci, daga cikin glass d'in da ya raba tsakani Mamy ke hangosa.... Banda addu'an Daddy Ya cika bata komai.... Sai matse k'walla da gyalenta take yanda kasan gaskiya....
Faran rigar angoncin Naseer kuwa duk ta b'aci da jini..... Tafe suke tare da likitocin suna masu bayani shida Fawaz... Mamy da Shareefah kuwa sai kuka suke an rasa mai bama wani hak'uri... Azeema na rakub'e gefe tana dubansu..
Naseer suna had'a idanu da Shareefah ta kuma fashewa da wani sabon kukan, kallonsa take cikin farar shaddar sa duk da ya jirkita sannan babu babban garen amma ya mata kyau sosai, wai yanzu wannan zankad'ed'en Sojan da ta k'wallafa ma buri haka tanaji tana gani saidai a kai masa Salma matsayin mata... Wllh bazata tab'a barin hakan ta kasance ba gwara kowa ya mutu a rasa gaba d'aya ko Naseer d'in ne ya mutu kawai kowa ma ya rasa tunda ta rasa.. Tsanar Salma na kuma tasiri cikin zuciyar Azeema....
Saman wata kujera Naseer ya samu ya zube bisa, hannayen sa duka biyu dafe da kansa, shi kansa bai isa yace ga abinda yake ji cikin zuciyar sa ba, a b'angare guda jinjina buwayar ubangiji yake, tabbas Allah zai iya canza lamuransa a duk sanda yaso... Ya sani yanajin babban Al'amari gameda Salma... Ko kusa bai tab'a kawowa ko tunanin shida Salma zasu kasance k'ark'ashin inuwa guda ba a matsayin ma'aurta... Wai yau sai gashi shi d'in ne mijin Salma... Ta yaya zai soma kallon Salma... God! Me zai soma fad'a mata, wacce irin rayuwa zasuyi matsayin ma'aurta....? Mecece makomar rayuwar Shareefah.... Sosai ta basa tausayi dukda baisan dalilin Daddy na janye wannan aure ba amma tabbas yasan akwai babban Al'amari.. In fact shi sam bai yarda da Mamy ba, duk da tace gangarowa yayi daga saman bene bai yarda ba... Sabida abin akwai abubuwan dubawa ciki... Shin meke faruwa a gidan Alh Ali Safwan..? Duk wannan tambayoyi ma zuciyar sa yake babu mai amsa masa su.... Lokaci guda tunanin Affan ya fad'o masa, his brother from another mother..... Ta yaya zai soma had'a idanu da Affan bayan yasan kalan soyayyar da yake ma Salma.... Wannan wani irin Al'amari ne.... Shafa sumar kansa yayi had'i da kwantar dasu baya lokaci guda ya mik'e ganin likitocin sun fito daga d'akin Daddy...
*******
Salma ta kuma goge hawayen da suka zubo mata kafin ta dubi Jamila cikin muryar kuka taci gaba da fad'in "Addah bansan me nake ji ba.. ... Wllhi ban isa nace ga abinda nake ji ba.... Bansan ta yanda zan soma zaman aure da Soja ba... Addah ni harga Allah d'an uwa na d'auki Soja kuma wllhi sosai nake kunyar sa yaya za'ace kuma shine mijina..... Addah bazan iya ba...." ta k'arashe muryarta na tsananin rawa....
Saurin rungumeta Jamila tayi kafin tace "Salma ki sani hakan tuntuni a rubuce yake Soja shine mijin ki... Kar ki mance a duk sanda kika shiga yanayi na neman taimako sai Allah Ya turo maki Soja... Allah yasan dalilin da yasa Soja ya zama mijinki... Wllhi ni harga Allah naji dad'in wannan aure fiye da yanda baki tsammani na tabbata you tow will make a perfect couple... Allah Ya sanya maku albarka cikin aurenku maza tashi kiyi sallah raka biyu zakiji sanyi da nustuwa cikin zuciyar ki...."
Jinjina kai kurum Salma tayi kafin ta mik'e jiki a sanyaye har ta kai k'ofar bathroom sauka jiyo sautin Ilham cikin yanayi irin ta mai kuka take fad'in "Don Allah mu tafi mu duba jikin Daddy wllhi hankali na ya gaza kwanciya... Ni tsoron asibiti nake tunda na rasa Inno ta...."
Wasu sabbin k'walla suka ciko idanun Salma . Allah sarki ko yaushene zasuji dad'i A DUNIYAR SU sai Allah... Koda yake duk abinda ke faruwa muk'addari ne daga Allah....
Jamila ce ta matsa kusa Ilham had'i da kamo hannayen ta kafin tace "Sweetheart ki kwantar da hankalin ki Insha Allah Daddy zai sami lafiya just keep on praying for him okay..."
A hankali Ilham ta jinjina kai sai ta kuma fad'in "But Addah I'm scared..... Gani nake kaman zamu rasa shi shima yanda muka rasa Baffah da Inno... Wai mukam zamuji dad'i A DUNIYAR MU Kuwa...?"
Duk k'ok'arin maida hawaye da Jamila take saida suka gangaro.... Cikin sauri ta rungume k'anwar tata lokaci guda tayi bursting cikin kuka... A guje Salma ma ta k'araso ta rungume su baki d'aya sai kuka suke abin tausayi....
Gaba d'aya Naseer ji yayi yana son sanin halin da Salma ke ciki gashi an shiga da Daddy theater baison barin waje su Mamy suga rashin kyautawar sa mussaman da shike babu Affan a wajen...
Sai kaikomo yake a wajen yana so ya lallashi Shareefah da irin kukan da take amma ya kasa, shi sam baison ganin mutane cikin tashin hankali...... Lokacin sallan la'asar ne tayi suka wuce masallaci nan cikin TH d'in suka gabatar da Sallah.... Dole Naseer ya cire cuff links d'insa yayi folding hannun rigar sa yanda jini ya b'abb'ata......
Fawaz ya kaikaito yana dubansa bayan sun ida sallan... Tausayin Naseer ya cika zuciyar sa, kana ganinsa zaka gane k'arfin hali kurum yake... D'an dafa hannun Naseer d'in yayi kafin yace "Uncle idan kana buk'atan wani abu kar ka mance ina nan...."
Kallonsa kurum Naseer ya d'anyi had'i da k'ak'aro murmushi kana yace "You know Fawaz.... I don't know.... Ji nake kaman mafarki nake na kuma kasa farkawa... Sannan har yanzu na rasa wanda zai farkar dani.... Quite alright bana jin bak'in cikin auren Salma in fact wani Al'amari ne da sam banyi zaton zai tab'a kasancewa ba A DUNIYAR MU sai gashi ya faru.... Fawaz dole na shiga rud'ani, ina da tambayoyi da yawa da nake son yima Daddy.. Sai gashi ban samu daman yi masa wad'annan tambayoyi ba..."
D'an damk'e hannyen Naseer Fawaz yayi kafin yace "Uncle I know you're strong... You can go through this..... Nasan Uncle d'ina jarumi ne...." ya k'arashe murmushi kwance saman fuskar sa..
Saurin rungume sa Naseer yayi yana fad'in "Thank you Fawaz.. Na gode...."
"That's what family are supposed to do, support each other.... Ka daina min godiya pls Uncle..." cewar Fawaz yana mai k'ank'an da murya
Su duka biyu murmushi saman fuskokin su suka mik'e suka fito daga masallacin.... A hanya Naseer ya d'an dubi Fawaz yace "I'm worried about her.... I know she must be having a hard time.... Fawaz ban sani ba ko zata amshe ni a matsayin miji.... Already soyayyar Affan ne cikin zuciyarta.... Shiyasa na fad'a maka abubuwa da dama suna yawo cikin kwanyata... Bana so na zamto sanadin k'uncin Affan da Salma mutane ne masu matuk'ar mahimmacin a rayuwata..."
"Uncle na fahimce ka, insha Allah things will get better soon..... Ka kwantar da hankalin ka pls..... Okay if you want zan kira Jamila na tambayeta mijin Salma na son sanin halin da matar sa ke ciki.."
Murmushin fatar baki kurum yayi kafin yace " Kanada son wasa Fawaz...."
Fawaz kuwa murmusawa yayi ba tareda yace komai ba... Saida ya san yanda yayi ya silale ya kira Jamila ya tambayeta well being d'in Salma a cewar sa Naseer ke son sani.... Koda Jamila ta sanar da Salma sak'on Naseer haka gabanta ya dinga fad'uwa... Gaba d'aya yanzu ji take ko idanu bazata iya had'awa dashi ba...
*******
Wajajen almuru aka fito da Daddy Mamy sai kuka tana k'ok'arin bin gadon da ake turosa bisa, Shareefah ma kukan take... Azeema kuwa sai harara take narka masu a zuciyarta tana fad'in _Munuafukai saikace gaskiya sonsa suke..._
Likitoci ne suka hana su Mamy shiga d'akin da Daddy yake, sannan suka buk'aci kowa na iya tafiya don har lokacin Daddy a intensive care unit yake, ba'a buk'atan mai jinya ya zauna dsshi, sabida zai d'au lokaci ma kafin ya farfad'o
Wannan furuci na likitoci ya haifar wa Mamy mummunar fad'uwan gaba... Cikin sauri ta soma fad'in
"A'a ban gane naku salon ba... Majinyaci baya buk'atan mai zama toh idan wani abu ya faru fah... Wllhi sam bazan yarda ba... Dama ance mayu ne likitocin asibitin nan salon ku lashe min kurwar miji... Wllhi dole na zauna da mijina ehe..."
Likita guda ne ya dubeta kana yace "Madam hak'uri zakiyi dokar asibitin kenan... Mijinki zai sami duk wani kulawa da ya kamata, duk abinda ya faru dashi muna sane.... Kiyi hak'uri ki tafi gida har sai mijinki ya fito daga intensive care kafin ki sami damar ganin shi..... Idan kina son ganinsa saidai ta cikin glass d'in nan amma babu halin shiga..."
Mamy ta mik'e tana k'ok'arin dafe crutches d'inta take fad'in "Wllhi k'arya kenan.. Kai likita naci uwar ka a bariki yo har ni za'a nuna wa salo....." Azeema ce tayi saurin k'arasawa ta dafe Mamy tana murmushi take duban likitocin kana tace "Kuyi hak'uri Drs kunsan Mijinta ne dole ta zamto out of control.... Zamu tafi kaman yanda kuka buk'ata..."
Mamy na k'ok'arin fuzge hannunta daga rik'on da Azeema ta mata.. Azeemar ta kwanto da kanta saitin kunnen Mamy cikin sigan rad'a take fad'in "You better behave yourself.. If not, wllhi zan fasa k'wai...."
Jikin Mamy ya shiga karkarwa sanda Naseer yake kuma bata hak'uri kan tabi umarnin likitocin.... Tsaf ya karanci yanayin ta yana mai nazari akai...
Azeema ta murmusa kafin ta k'arasa ta rik'o Shareefah da har lokacin kuka take... Idanunta duk sun kumbure....
Mamy kam da zata sami damar runtuma ihu da tayi ko taji sanyi a zuciyarta... Gaba d'aya bama fahimtar hanya take ba.. Ga k'irjinta dake mata wani irin zogi da rad'ad'i yinin ranar guda...
*******
Mamaki da takaici ne ya cika sa ganin sak'on da Jamila ta bar masa... Dama rabonsa da ita tun da aka soma hidimar bikin Naseer... Shi kad'ai ya tak'ure waje guda yana girgiza kai hannunsa dunk'ule da takardan da ta bari masan yake fad'in "Kitty why..? Meyasa kika barni... I love you.. Wllhi ina sonki, kina tunanin zan iya rayuwa babu ke ne... No.. No..no bazan iya ba.. Wllhi bazan iya ba... You're mine ke tawa ce.... Duk yanda kika tafi zan nemo ki kuma zamu kasance tareda dake har abada A DUNIYAR MU...." ya k'arashe yana mai sakin k'ara had'i da bubbuga kansa da hannayen sa.. Lokaci guda ya zaro cocaine d'insa a suit pocket d'insa ya shiga shak'a da k'arfin gaske tana harbawa brain d'insa.... Haka ya dinga shak'ar garin Cocaine daga bisani zubewa yayi a wajen bacci yayi gaba dashi babu sallah balle salati....
*****
Fawaz ne ya maidasu gida don Naseer kam tuni ya kuma wucewa neman Affan...
Tunda suka shigo gidan Shareefah ke tunanin kalan rashin mutuncin da zata shek'a wasu Salma... Mamy kam tuni ta wuce upstairs ya shiga watsi da kayan su Salma..
Kuka suke suna rok'on Mamy tayi hak'uri ta k'yalesu... Inaa Mamyn ma kuka take tana kuma watsi da kayan ga duhun dare ya soma tana fad'in wllhi sai sun bar mata gida...
Shareefah dai tamkar maras lafiya haka ta kwanta a parlor.. Tana kallon ana wannan bidiri bata iya furta komai ba... Saidai a duk sanda ta dubi Salma sai suji ta kuma fashewa da wani irin kuka...
Salma na kuka take fad'in "Mamy don Allah ki bar 'yan uwana su zauna, na yarda ni zan tafi amma don Allah kada ki koresu basu da wajen zuwa...."
Bata kai aya ba Mamy ta hankad'ata da sandar crutches d'inta.... Shigowar Naseer kenan ya tallafi Salma ta fad'o cikin jikin sa...
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU*🌖🌖
*36*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kallon juna suke su duka biyun yayinda suka zame ma sauran mutanen dake wajen tamkar TV.... Wani irin yanyi maras fasaltuwa suka tsinci kawunan su ciki.... Bugun k'irjin Salma ya k'aru, itakam da zai saketa ta fad'i k'asa da sai yafi mata sauk'i....
Yayinda Shareefah tayi mutuwar zaune Mamy ta bud'e murya ta shiga doka salati da sallalami tana tafe hannaye take fad'in "Arnanci!!!... Kin mak'ale jikin shi tun kafin akai ki kin k'i sakin sa.... Eh lallai zamani ya kawo mu..... Koda shike ba kansa farau ba kinyi ma Affan a layi ballanta yanzu da kika sami dam...."
Muryar Naseer da Mamy ta jiyo ne ya sanyata dasa aya... Saida ya mik'ar da ita sosai, fuskar sa fal damuwa, idanunta a k'asa kana ya d'an sassauta murya yace "Are you hurt..?"
Cikin sauri ta girgiza masa kai tana k'ok'arin b'oyewa bayan Jamila saiji tayi Naseer ya rik'e hannunta gam... Cikin wani irin yanayi ta d'ago tana dubansa shima ita yake duba.... Shareefah kuwa idanunta naga hannayen su yanda yake sakale cikin na juna... Wani wawan ihu ta kurma had'i da nufosu tamkar sabuwar kamun hauka take fad'in wllhi sai ta kashe Salma saidai itama a kasheta...
Lokaci guda Naseer ya tare Shareefah yana wani irin duba mai cike da gargad'i yake fad'in "Kiyi hak'uri basai kin kasheta ba, zasu bar gidan yanzu kaman yanda kuka buk'ata...." Ya d'an kaikaito yana duban su Jamila kafin yace "Muje koh..."
Cikin sauri Jamila ta shiga gyad'a masa kai ta juya tana gwalo wa Mamy
Mamy baki sake take dubansa sanda taga bil hakk'i Naseer ba sakin hannun Salma zaiyi ba gashi ya jata sun nufi waje... Lallai bokan su Salma ya iya aiki, dole ta kira Laure yanzun nan taji a ina nata bokan ya tsaya da har wad'annan iftila'i ke faruwa da ita...
A tamanin Shareefah ta take masu baya tana wani irin kuka take fad'in "Naseer pls... Don Allah kada ka min haka, Naseer ka tausaya min ka tuna kalan shekarun da muka d'iba a tare.. Naseer rana d'aya ace na rasa ka.. Kar ka manta muna son junan mu... Naseer wllhi ni na tabbata ba da yarinyar nan aka d'aura auren nan ba wllhi mai shelan ne dai baiji da kyau ba.... Naseer please...." Kasa ci gaba da magana tayi lokaci guda kuka yaci k'arfinta..
Salma ma idanunta a k'asa amma hawaye ke zuba...
Kan ya sami zarafin magana wayar sa ta soma ringing Fawaz ne mai kira... Bai d'aga wayar ba saida ya k'arasa ya Bud'e masu motar sa.... Shareefah ta kuma yin kukan kura ta tare Salma tana fad'in "Ta shiga ina..? Wllhi babu yanda zata shiga... Wllhi babu gaminka da ita...." Tana k'ok'arin janyo Salma Azeema ta k'araso ta janyeta tana mai bawa Naseer hak'uri take ci gaba da fad'in "Naseer kar ka damu kuje ni zan kula dasu... Allah kad'e fitina..."
Bai sami zarafin amsa mata ba sai shigewa mota da yayi ya tada, ga kiran Fawaz na kuma shigo masa lokaci guda yayi key ma motar..
Jamila kuwa harda d'agawa Shareefah hannu tana mata gwalo..
Shareefah sai kokawan k'watan kanta daga hannun Azeema take lokaci guda ta gantsarawa Azeemar cizo tana fad'in "Ki sake ni.. Wllhi babu yanda zasu bi Naseer...."
Azeema ta kasa rik'e dariyar ta lokaci guda ta kuma jawo Shareefah dake k'ok'arin nufan gate kana tace "Haba darling ki k'yalesu haka nan mana, ko bakiga tsan-tsan soyayyar junan su a idanun s....." Aya tayi wa maganar ta ta nufi cikin gida a guje ganin Shareefah ta rarumo cutlass tayiyo kanta dashi sam bazaka ce akwai sauran hankali a tare da ita ba...
Mamy tana ganin Azeema ta shigo a guje tamkar wacce aka biyota da bindiga... Tuni ta rarumi crutches d'inta tana k'ok'arin warewa nan taga ashe Shareefah ce... Bata tare Shareefah ba sai cewa tayi " Bita... Bi kafura ki kashe min ita... Mu toni k'asa mu turbud'e ta annoba.."
Haka Azeema ta saka key ma k'ofa tak'i bud'ewa sai faman dariya take... Downfall d'in Shareefah da Mamy sosai ya mata dad'i, basuga nata ba taga nasu... Ta kuma kad'a kai kana tace "Kad'an kuka soma gani... Wani tsiyan sai na auri Affan..." Lokaci guda ta zube saman gado tana wasa da bakin kitson ta take kafiran murmushi.....
Tunda suka shiga motar babu mai cewa komai, babu kaman Salma wacce kanta ke kife tun shigar ta motar, motsi mai kyau bata kuma yi ba... Banda lugude babu abinda k'irjinta keyi...
Waya na mak'ale a kunnen sa Fawaz yaci gaba da fad'in "Uncle wllhi Innah ce ta kulle kanta a d'aki tak'i bud'ewa, yanzu haka babu kalan magiyar da bamu mata ba nida Lubna kan cewa ta Bud'e amma tak'i.... Nasan hakan bazai wuce nada nasaba da lamarin aurenka ba...."
Naseer ya d'an sata kallon Salma da wutsiyar idonsa kafin yace "Shikenan Fawaz... Ka gane kar ku tak'urata, zan k'araso gidan bada jimawa ba.... Ka kula da Lubna kaji..."
A hankali Fawaz ya gyad'a masa kai kafin ya dubi Lubna da tayi jigum yace "Ke dalla babu abin damuwa, ki kwantar da hankalin ki 'ila ma bacci tayi abinta mu muna nan muna damuwa..."
Harara Lubna ta galla masa kafin tace "Ai dai kasan na saba zama muyi hira da ita a irin wannan lokacin don haka dole na damu..."
Fawaz ya d'anyi tsaki kana yace "Ke wllhi sam bazaki girma ba, bakida damuwa wllhi... Sabida bakiga kalan tashin hankalin da Uncle ke fuskanta ba shiyasa kike fad'in haka... Wai don Innah tak'i bud'e maki k'ofa shine duk kika d'aga wa mutane hankali... Ke wllhi dama ban biye ki ba.. Allah sa Uncle ya dawo ki kuma stressing d'insa..."
Murgud'a masa baki tayi tana fad'in "Eh d'in nayi d'in ai ana biye min ne... Wani ma yayi mana..."
Tab'e baki yayi yana dubanta kafin ya tattari wayoyin sa saman center table, ya nufi hanyar fita.. Yana tafe yake fad'in "Waike auta koh.. Duk sun tara maki wautan wllhi.... Banida lokacin ki gwamma naje nayi research da na biye ma sangartan ki...."
Bata amsa sa ba itama sai jawo remote da tayi ta shiga canza channel tana fad'in "Wllhi dama ka isheni foodnetwork nake son kalla..."
Har ya kai k'ofa ya juyo yace "Stop acting like a real chef... Baki iya komai ba sai jagwalgwalo truffles d'in da kikayin ma basu yi dad'i ba cin dole kawai nayi...."
Dariya Lubna tayi kana tace "Oho dai haka dai kayita santi harda neman k'ari..."
Fuskar sa d'auke da murmushi ya fice.. Duk randa Lubna tayi aure yasan zaiyi kewarta....
******
Kai tsaye gidan Momy Lami ya kaisu don yasan idan ya kaisu gidan iyayen shi things would get more complicated... Zamansu da Momy Lami shine kawai solution kafin Al'amra su canza...
Sosai Momy ta tsausaya wa Naseer da Salma, ta tuna zuwansu gidan satin da ya shige masoyan su suka biyo sawun su, wato Shareefah da Affan, sai gashi yau sun dawo mata matsayin ma'aurata... Bayan sun gama tattaunawa da Momy ta rakasa har waje had'i da masa addu'an kariya.....
A d'akin ta samesu sunyi jigum-jigum
Momy ta d'an sakar masu murmushi Jamila ce kawai ta maida mata martanin murmushin nata... Ta k'araso ta d'auki Falaq tanai mata wasa kana ta d'an dube su tace "Ku saki jikin ku, Salma kam nan gidan su new.. Saidai kuyi hak'uri da yanayin gidan kunsan abinku da mai Fafutukan na kai..."
Jamila ta d'an murmusa kafin tace "Haba dai Mama ai munyi rayuwa a yanda yafi nan matsi... Wllhi kar ki damu zamu zauna a duk yanda muka tsinci kawunan mu ciki A DUNIYAR MU muddin zamu sami zaman lafiya da amunci abunda yayi k'aranci A DUNIYAR MU..."
Momy ta d'an murmusa tana duban Salma wacce tayi jigum ta had'e tagumi.. Tana son suyi magana amma sai sun d'an keb'e... Duban Ilham tayi wacce ke wasa da hannayen Falaq kana ta murmusa tace "Oh ai kekam kinfi uwar yarinyar ji da ita na lura sanda kuka zo ma tana hannun ki.. Koda yake k'ila don kuna kama ne shiyasa..."
Gaba d'aya suka murmusa idan ka d'auke Salma.. Jamila kuwa cewa tayi, "Ai kuwa wllhi Mama kaman kinsan a hannunta take yini, wanka komai ta iya mata duka da ba gani take ba, amma tafi masu ganin kulada yarinyar..."
Momy ta murmusa tausayin Ilham na kuma ratsa ta kana tace "Allah sarki kinsan dama wani haka Allah ke yinsa mai son yara... Allah dai ya d'ayyiba mana..." suka amsa da Ameen.. Karb'an Falaq d'in Momy tayi ta sab'ata a baya, don itama babu laifi akwai son Tara's... Jamila sai murmushi take...
******
Mamy da Shareefah zaune a parlor suna jimamin lamarin sai ganin an banko k'ofar parlorn sukayi... Hannun sa rik'e da kwalban whiskey d'insa..... Yanayin sa na can baya shine a tattare dashi yanzu...
Mamy jiki na rawa ta mik'e tana k'ok'arin dafe crutches d'inta take dubansa... Baki har na rawa take fad'in "AA... Affan.. Affan meye wannan, Affan halin da ka kuma komawa kenan... Wayyo ni Asma'u na shiga uku.... Affan don Allah kada ..." Bata kai aya ba ya daka mata uban tsawa da fad'in "You shut your mouth!, and don't you dare come near me...."
Daskarewa Mamy tayi tana dubansa yanda yake tafiya yana tangad'i... Shareefah ma baki sake take dubansa...
Dai-dai jikin staircase ya isa ya dafe ya shiga k'walla kira ma Salma kaman zai d'aga gidan...
Jin babu wanda ya amsa sa yasa sa juyowa yanai masu Mamy da Shareefah wani irin kallo..... Take jikinsu ya shiga kyarma suka tuna lokutan baya idan ya shawo kayan mayen sa basu fad'a masa dai-dai ba toh duk wanda ya samu jibgan sa yake..
Matsowa kusan su ya shiga yi yana fad'in "Where is she...? Ina take... Ku fad'a min ina take....!!" ya k'arashe cikin d'aga murya sosai.. A tamanin Shareefah ta d'iba a guje ta haye sama yayinda Mamy ta shiga saita crutches d'inta, 'yan hanjin cikinta tuni sun kad'a don tuni Affan ya nufota...
"Affan ka saurare ni... Dan Allah ka saurare ni...." Aya tayi wa maganar nata ganin ya zube saman kujera ya karya k'afa d'aya kan d'aya ya ci gaba da kora ruwan kwalban sa yana fad'in "Naseer...! I'll teach that imbecile a lesson....."
Mamy ta bisa da kallo cikeda taisaya ma d'an nata, bata tab'a tsammanin Affan zai koma ruwa ba...
D'ago kai yayi yana dubanta da rinannun idanunsa tana nan tsaye akansa..
"Get out of my sight..." ya fad'i yana kuma kwankwad'an barasar sa.."
"Affan.... Son pls kar ka lalata rayuwar ka akan wancan banzar yarin...."
Aya ta saka ma kalaman nata ganin wani irin duban da ya mata...
Jiki a sanyaye ta soma cangwala crutches d'inta duniya ta mata zafi... Gashi duk kiran da take ma Laure bata d'agawa... Abin ya soma damun Mamy, kiran farko da ta mata ta d'aga taji ta soma complain tuni ta rangad'a mata k'arya cewa gaban boka take... K'arshe ma daina d'aga wayar Mamy tayi gaba d'aya... Abubuwa sun taru sun rincab'e wa Mamy....
Azeema ce ta lek'o ta gansa zaune a parlorn sai sunbatun sa yake... Tayi murmushi don ta tabbata su Mamy an b'oye a d'aki kafin ya nad'a masu na jaki...
Tana ganin yanda yake waiwaina kwlaban giyar yana ambato sunayen Naseer da Salma, daga bisani bucewa kwalbar tayi ya bita da kallo yana dariya.. Shi kad'ai sai bin gefe yake yana layi kar ya taka kwalaben.... Ganin da gaske zaibi cikin kwalaben ya sanyata saurin k'arasowa ta tallafe sa...
Kallonta ya dinga yi yana mai ci gaba da sunbatun sa yana fad'in irin soyayyar da yake ma Salma.... Sai bawa Azeema sunan Salma yake har suka isa d'akin sa...
Azeema ta kwantar sa bisa gado had'i da cire masa takalma
Tuni Ya shek'o amai ya b'ata kayan jikin sa.. Babu ko k'yank'yani Azeema ta shiga kwab'e masa rigar tana binsa da mayen kallo..
K'aran cangwala crutches d'in Mamy data jiyo ya sanyata saurin jifa da rigar Affan ta soma k'ok'arin cire nata rigar... Cikin sauri ta haye gefensa had'i da d'aura kanta a b'angare na jikin sa lokaci guda ta jawo bedcover ta rufa masu tamkar masu bacci....
Mamy ta jima tana tsaye tana knocking tana rok'onsa ya Bud'e mata taga halin da yake ciki, sannan ta sanar dashi halin da mahaifin sa ke ciki ko zaisa ya ajiye halin da ya dawo dashi... kk'arshe dai gajjiya tayi da k'wank'wasawa ta yanke shawarin tura k'ofar tunda tasan a buge yake zaiyi wuya ya kulle k'ofar..
Tana tura k'ofar ta daskare tana shirin watsewa a k'asa... Zafin k'irjinta ya k'aru...
Azeema kuwa wani juyi tayi tana musmuskuta idanu.... Mamy batasan sanda ta malmalo ashar ta watsa wa Azeema ba....
A d'ari tayi kanta tana k'ok'arin sauk'e mata crutches take fad'in "Don ubanki tsinanniya karuwa... Ki bi d'iyata macen ki lalata mata rayuwa yanzu ki dawo kan namijin shegiya kariya.... Don uwarki yau zaki bar gidan nan..." Ta shiga k'ok'arin janyo Azeema lokaci guda saiji tayi Affan ya rik'e hannun Azeema gam, ya hana Mamy janyeta dukda ba a cikin hankalin sa yake ba, shidai kawai gani yake Salma ce tare dashi
Cikin muryan maye Affan ke fad'in "Mamy..... You get out of this place...."
Azeema ta d'ago tana duban Mamy had'i da sakar mata murmushi kana tace "You heard him right...? Maza a fice.. And pls switch off the lights on your way out...."
Jiri Mamy ta soma gani na neman kada ita... Take taji k'walla sun ciko idanunta... Shikam Affan tuni bacci yayi gaba dashi...
Mamy fuska wanke da hawaye ta fice.... Azeema harda mata saida safe...
A corridor ta zube tana kukan da batasan tana yi ba..... Abubuwa sun taru sun mata yawa... Ga mijinta a gadon asibiti, ga kukan Shareefah har yanzu bata daina jiyowa ba... Ga Affan ya koma ruwa... K'arewa ta gansa da mace akan gado dole zuciyarta ya kusa bugawa... Azeema ta cuceta... Kai itakam wannan tazo mata ba yanda take so ba.... Hannu Mamy ta d'aura aka tana mai ci gaba da furta "Na shiga uku! Na shiga uku!! Na mutu na lalace....!!!" Ta kuma rarumo wayarta da sauri tana dialing layin Laure nan ta kuma jin wayar a kashe... Wani k'aran ta kuma kurmawa don ihun nata shine samun sauk'in ta....
********
Tunanin ta gaba d'aya ya hanasa sukuni, shi kad'ai sai murmushi yake... Time ya duba dare ya d'an ja... But he just couldn't help kawai shi so yake ya kuma jin muryar ta...
Take ya janyo wayar sa ya shiga dialing layinta....
Har ta soma barci taga kiran Fawaz na shigo mata saida ta murmusa kafin ta d'aga da sallama...
Cikin sanyin murya ya amsa mata daga d'aya b'angaren...
Bayan sun gaisa ne tace "Dr Lafia dai koh...?"
Fawaz yama rasa mai zaice mata, Falaq ce ta fad'o zuciyar sa yayi saurin sakin murmushi kaman tana ganin sa kafin yace "Ya baby Falaq, ya jikinta hope yayi sauk'i yanzu...?"
Murmushi Jamila tayi kafin tace "Alhamdulillah ta sami lafiya.... Amma Dr are you sure lafiyar Falaq kawai ka kira kaji da daren nan...?"
Fawaz ya kuma yin juyo a gado had'i da sakin murmushi kafin yace "Eh toh Uncle d'ina yace na tambayi yaya amaryar sa take....?"
Dariya maras sauti Jamila tayi kana tace "Oh Dr nifa jikina na bani kaman kai kake tsara zancen nan ba Uncle d'inka ba..."
Shima dariyar ya d'anyi kana yace "Well, tunda kince haka..... Yanzu zan samu nayi barci peacefully at least naji lafiyar ku.."
Jamila tayi murmushi soyayyar Fawaz na dad'a ratsa zuciyarta.... A baya idan akace zata kula yaro saita k'aryata, domin ita tuntuni matar manya ta d'auki kanta shiyasa ma ta nace ma auren Alh Nuhu, sai gashi wai yau ita ke kula yaro wanda k'ila idan basu zo age mates ba ta girme masa.... Tabbas ta yarda da buwayar ubangiji sam mutum kada ya zamto mai cika baki, fatan samun na gari shine ginshik'i...
Saida suka sha hiran su cikeda jin dad'i kafin sukayi sallama.. Salma da idanunta a lumshe suke tana kan sauraren Jamila, domin kuwa sam barci bai ganta ba a wannan dare... Idan ta tuna abubuwan da suka faru a wannan rana sai taga tamkar za'a tashe ta ace mata mafarki take... Tunanin sa da yanda suka soma had'uwa shi yayita ziyartan zuciyarta....
A b'angaren Naseer ma sam barci bai gansa ba, haka ya dinga tuna lamarin yana jinjina buwayar ubangiji kafin daga bisani ya mik'e ya nufi bathroom ya d'auro alwala yazo ya tada sallah...
*******
Innah kam ba ita ta farka ba sai safiya... Gaba d'aya fuskarta ta kumbura, bakinta ma yayi suntum.... Ta dubi kanta jikin mirror tana tuno abubuwan da suka faru a jiya..... Zuciyarta naci gaba da mata zogi da d'aci... Kai inaaa ai dole ma ta tirsasa wa Naseer sakin wancan yarinyar, bata santa ba amma jikinta na bata d'iyar kirkice... Ta yaya zata bari Naseer ya sami macen k'warai ai wllhi sai yanda k'arfinta ya k'are.... Ta tuna kalan kud'd'en da tayita baiwasu Mamy duk don auren nan ya yuwu.. Ashe dolaye ne basuda maraba da d'anta Kabeeru.... Ita kad'ai ta dinga huci tana zagaye d'aki ko k'ofa bata fito ba.. Sanda su Naseer suka had'u suna rok'onta ta bud'e k'ofar tass ta wanke su da bala'i babu kaman Naseer, harda ce masa yaje yayi yanda yake so da rayuwar sa tunda abinda ya zab'ar ma kansa kenan auren macen da ba'asan asalinta ba.... Fawaz fad'i yake "Innah kiyiwa Allah ki bud'e k'ofar kiji yanda lamarin yake..."
Inaa Innah kam ko amsa sa batayi ba... K'arshe cewa tayi su bar mata k'ofar d'akin ta....
Lubna ce ta fashe da kuka tana fad'in "Innah don Allah ki bud'e min, wllhi tun jiya nake kuka..."
Lubna rabin ran Innah bazata iya jure sauraren kukan ta ba... Sai sannan ta k'arasa ta bud'e k'ofar
K'iris ya rage basu kwasa a guje ba ganin yanda halittar fuskar Innah ya sauya.. Fuska suntum haka baki ma, ga idanuwan sun mule ciki
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*37*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Fawaz da Lubna har suna had'e baki wajen fad'in "Innah lafiya.. Mai ya sameki....?"
Naseer kam k'uri ya mata ba tareda ya furta komai ba...
Innah ta watsa masu harara kafin taja tsaki ta zauna saman gado kana tace "Mai yasa baku tambayi wannan ba... Tunda kalan auren da ya zab'ar ma kansa kenan ace ina mahaifiyar sa wai saidai naji an d'aura masa aure da mace maras asali balle tushe..." Ta k'arashe tana mai nuni da Naseer wanda yayi tsaye tamkar mutum-mutumi... Innah ko tuni ta soma matsan k'walla, ba abu k'ank'ani bane ke sata hawaye sabida bushewar zuciya irin tata...
Fawaz ya d'an girgiza kai cikeda tausayin Naseer kafin ya d'an durk'asa had'i da kama hannayen Innah yace "Yanzu Innah wannan dalili har yakai yasa ki kulle kanki a d'aki ki kwana kina kuka... Dubi yanda halittar fuskar ki ta canza gaba d'aya... Haba Innah ki dinga ragar wa Uncle pl....." bai kai aya ba ta fizge hannunta tana wani irin huci ta kuma mik'ewa tana fad'in "Ku fita... Ku fice min nace...."
Naseer ya kamo hannayen Lubna da Fawaz yana girgiza masu kai alamun suyi yanda tace d'in don gaba d'aya gani suke tamkar ba itace ba tamkar wacce aka canza ta.... Kaman wata sabuwar kamun hauka haka take koransu...
Saida ya fitar dasu kafin ya dawo d'akin wajen Innah...
Ta d'ago ido ta dubesa gabanta yayi wani irin yankewa... Ji tayi bazata iya jure kallon k'wayar idanunsa ba domin kuwa gani take kaman ya riga ya san sirrinta, lokaci guda tsoro ya cika zuciyarta....
Naseer ya d'an zauna saman kujeran dake gefe ba tareda ya furta komai ba... K'irjin Innah kuwa sai lugude yake, shikenan yau kashinta ya bushe yanzu haka malohon d'antan nan ya sami Naseer ya sanar dashi komai, toh ko kuma yasan k'udirinta akan Shareefah ne....? Cikinta yabada wani sauti,. Tana k'ok'arin mik'ewa ta jiyo sautin sa na fad'in
"Innah har kullum bazan gajiya wajen neman gafarar ki ba, ki sani duk abinda zanyi a rayuwa idan zai haifar da fushinki toh kuwa babu shakka zanyi iya k'ok'arina nayi avoiding wannan abun koda ace farin ciki na ne.... Innah kaman yanda kika tsinta aurena da Salma a sama wllhi nima haka na tsinci abin, ni na sani aurena da Salma buwayar ubangiji ne.... Bansan meyasa mahaifin Shareefah ya zab'ar min Salma a matsayin mata ba, amma nasan ko menene hujjar sa tanada k'wari sosai.... Salma da 'yan uwanta suna buk'atan taimako,..." Lokaci guda ya labartawa Innah tun farkon had'uwar su sanadiyar k'onewar gidan gonar Ali Safwan..... Innah ce tayi saurin katse sa tana mai ci gaba da hawaye take girgiza kai tana fad'in "Naseer don Allah ka saki yarinyar nan... Wllhi hankali na sam bai kwanta da ita ba... Duk yanda akayi annoba ne su tunda duk yanda suka zauna sai fitina ya auku.... Naseer ka rufa min asiri ka guntule auren nan bana fatan na rasaka...." Ta k'arashe tana mai k'arasowa gabansa still hawaye saman fuskar ta....
Abin akwai abin dubawa ciki... Wai shine Innah ke rok'onsa haka tamkar ba itace mai saka sa abu dole a baya ba..... Yau gaba d'aya ta birkice tamkar mai tsoron aukuwar wani abu... This is quite weird..... Mamaki bai gama kamasa ba saida yaga Innah durk'ushe gaban sa hannayen sa rik'e cikin nata take fad'in "Naseer don girman Allah ka saki yarinyar nan, kai da ita sam baku dace ba... Kai kowa yasan asalinka ita kuwa bamu sani ba... Kai d'an manyan mutane ne ita kuwa akasin haka ne... Naseer alfarma d'aya kenan da nake nema wajen ka a rayuwata a matsayina na mahaifiyar ka.... Don Allah Naseer ka saki yarinyar nan yanzu...."
Kallon Innah yake cikeda mamaki kafin ya d'ago hannayen nata yana k'ok'arin k'ak'aro murmushi yake fad'in "Innah ki kwantar da hankalin ki, aurena da Salma akwai hikiman Allah cikin sa... Jikina na bani akwai abubuwa da dama da suka shige min duhu A DUNIYAR MU sannan sanadin aurena da Salma sai kig....."
Saurin katse sa tayi tana girgiza kai k'irjinta na ci gaba da bugu take fad'in "Naseer na gama magana zaka saki yarinyar nan da ka k'i da ka so...."
Kafe Innah kurum yayi da idanu yana karantar ta kafin ya mik'e ba tareda ya kuma furta koda kalma ba ya nufi k'ofa....
Saurin shan gabansa Innah tayi tana fad'in "Naseer ni mahaifiyar ka ce ni nasan abunda yafi dacewa da kai... Yarinyar nan sam bata dace da kai ba...."
Naseer ya d'anyi jim kafin yace "Idan kika zauna da ita zaki fahimci alkhairan da suke tattare da ita..."
Innah na girgiza kai take ci gaba da fad'in "Sam ban amince ka kawo min wannan yarinyar matsayin matarka cikin gidan nan ba... Wllhi kaji na rantse zan maka baki muddin ka sake ka kawo min yarinyar nan cikin gida na ba.... Kai ko barikin ku ne ban yarda ka kaita ba.... Nidai Hajiya Asma'u ta cuce ni ta gama dani tunda tana gidan akayi wannan auren rainin hankalin... Banda mugunta da munafunci idan aure suke so yarinyar tayi ai akwai d'ansu meyasa basu basa ba sai nawa d'an.... Wllhi wllhi ban amince maka tarewa da yarinyar nan ba..." Daga haka tura k'ofarta tayi ta koma cikin d'akin tayi zaman ta....
Naseer ya jima na tsaye a wajen yana wasu irin tunani sarara... Da Innah tasan cewa shi kansa baisan matsayin aurensa da Salma ba a yanzu har sai Daddy Ya sami Lafia ya fayyace masu komai, sam da bata d'aga hankalinta ba..... Girgiza kai kawai yayi kafin yayi ficewar sa...
A farfajiyan gidan ya had'u da Fawaz ya fito sashen mahaifiyar sa.... Nan Naseer yake tambayar sa jikin Aunty Saudat...
Fawaz yace "Da sauk'i sosai Uncle kasan yanzu har sunana tana ambato..."
Naseer yayi murmushi had'i da jinjina kai kana yace "Da kyau Allah Ya k'ara mata lafiya.... Kaci gaba da kula da ita Fawaz kasan mahaifinka is a busy man... Kar ka kuskura Dr yazo ganinta baka a wajen.... Kaci gaba da lura da komai... Da sannu nasara zata samu...."
Fawaz ya jinjina kai kana yace "Haka ne Uncle.... Yaya kuka k'are da Innah rigima..."
Tak'aitaccen murmushi Naseer yayi da gefen bakin sa kana yace "Kar ka damu things will work out insha Allah... Nasan da sannu zata amince da Salma... Ehen Office ka nufa..?" ya k'arashe yana duba agogon hannun sa
Fawaz ya d'an girgiza kai kana yace "Sai 12 insha Allah..."
Naseer ya jinjina kai kana yace "Okay aika nake so da Allah ka kai gidan Momy...."
Ya k'arashe yana mai k'arasawa jikin motar sa... Fawaz na biye dashi yana amsawa...
********
A hankali yake bud'e idanunsa da suka masa nauyi.... Hasken rana kuwa ya haske labulayen alamun gari ya waye sosai.... Sai sannan ya soma recalling abubuwan da suka faru a jiya, baisan yaya akayi ya iso d'akinsa ba yadai ga babu riga jikinsa.... Ya d'an yunk'ura zai tashi sai jin mutum yayi cikin jikin sa.... Kan bala'i.... A tamanin ya kaikaito yana dubanta sosai yanda take bacci peacefully da alama itama babu tufafi jikinta...
"Whattt!!!" Ya furta da k'arfin tsiya.... Baisan sanda ya kai ma Azeema wata tokari ba saida ta fettu gefen chaise of drawers.... Bagatatan taji tokarin da Affan ya mata, ta saki k'aran azaba tana waige-waige...
Nan ta hangesa yana k'ok'arin zura rigar sa ta Camo lokaci guda ya isa closet d'insa yana k'ok'arin ciro belt...... Ai a tamanin Azeema ta bar soshe-soshen jikin da take riga a hannu ta nufi k'ofa saidai kafin ta isa k'ofa Affan ya cimmata... Lock yayi ma k'ofar yana wani irin huci yake nad'e belt d'in yana fad'in "Don't you dare move an inch...."
Azeema jiki na rawa ta shiga girgiza masa kai tana k'ok'arin jada baya... Saidai kafin ta ankare Affan ya shiga zabga mata belt d'in tamkar aikosa akayi... Azeema na sonyi ihu bataso su Mamy sosai dukan ke shigan ta batasan sanda ta shiga ihu tana talewa ba... Gashi babu riga jikinta sai 'yar bra... Shiko Affan tamkar ba mutum yake duka ba haka yake jibgan Azeema, gaba d'aya huce haushin sa yake akanta baiji bai gani...
Mamy da Shareefah a stirs suka had'u da juna domin kuwa sun jiyo ihun Azeema... A tare suka nufi sashen Affan d'in suna buga masa k'ofa.... Inaa bai bud'e ba sai wargaza Azeema yake...
Shareefah ta dubi Mamy kana tace "Wllhi mu shafa ma kanmu Lafia mu bar wajen nan da alama haukan tasu ta soji ta motsa dama yaya lafiyar kura balle taci nama... Wllhi Affan zai iya fitowa ya had'e damu ya jibga kin dai san ba'a basa hak'uri...."
Mamy ta jinjina kai b'angare na zuciyar ta na mata dad'i ko babu komai anci uwar Azeema dole taji sanyi a ranta... Cikin sauri ta shiga cangwala crutches d'inta tana fad'in "Gaskiyar ki ne.. Gwara yaci uwar kafura ma gobe hanyar d'akinsa bazata bi ba....."
A tare suka nufo parlor suka zauna saman kujeru suna jiran sauk'owan Affan da Azeema....
Affan ne ya soma sauk'owa yana tafiya cikin sassarfa... Tuni Mamy da Shareefah suka kuma nustuwa yanda kasan monitor a ajin primary school....
Ko kallo basu ishesa ba ya nufi k'ofa... Shareefah tayi saurin mik'ewa tabi bayan sa...
Mamy kuwa saurin d'aukan crutches d'inta tayi ta nufi dubo Azeema...
"Get the hell out of my sight..." ya fad'i sanda yake k'ok'arin bud'e motar sa...
Shareefah ta d'an yi rau-rau da idanu had'i da kamo hannayen sa cikin muryar kuka ta soma fad'in "Affan you are not the only one suffering.... Affan nima sun munafunce ni... Naseer da Salma sun cuce mu sun yaudare mu sun munafunce mu... Affan a dalilin k'in aurena da Naseer yayi hawan jinin Daddy Ya tashi ya fad'o daga stirs..." kukanta ya k'aru sanda taci gaba da fad'in "Affan Daddyn mu na asibiti rai a hannun Allah... We need to work as a team to ruin those two...... We shouldn't let them get away with what they did.... Affan idan muka barsu suka rayu cikin farin ciki sunyi riba......"
Huci kawai Affan yake kafin ya fincike hannun sa daga rik'on da Shareefah ta masa... Kallonta cikin ido yake tamkar wani damisa kafin ya soma fad'in "Don't you dare hurt Salma.... Ina sonta da duka zuciyata... Wllhi Shareefah idan wani abu ya sami Salma zan wulak'anta ki without being pathetic, Ko me zakiyi ma Naseer ki masa shi kad'ai don't involve Salma, idan kinga dama ma ki kashe shi I don't bloody care..." Daga haka bud'e marfin mota yayi ya shige.. Don harta Daddyn sa ma haushin sa yake ji, bazai bi takansa ba...
Shareefah baki sake take dubansa har ya fice daga gate d'in gidan a guje.... Lallai ta yarda da maganar Mamy Salma da asiri suke aiki bacin haka tana a matsayin jinin sa yake fad'in zai tozarta ta akan Salma... Wllhi wllhi bazata tab'a barin Salma taji dad'in rayuwa A DUNIYAR SU ba
Azeema ta kuma murmusawa kafin ta shafi gefen fuskar Mamy tace "Kar ki damu tsaban farin cikin da na sanyasa ciki ne a daren jiya muka farka da wasan duka.. Kinsan idan dad'i yayi yawa baka sanin mai kake yi..... Sannan Mamy banda abinki ai saidai ki mana fatan alkhairi don na riga nayi video d'inmu jiya... Kinga babu macen da zata gani ta aminta da auren d'anki... Sannan Mamy karfa ki mance sirrinki a tafin hannu na yake.... Wllhi tallahi kikayi wasa zan sanar dasu kece mai yunk'urin kashe mahaifin su kuma na tone komai kowa ya sani.. Don daga nan sai gaban Naseer Santana..."
Mamy dai huci kawai take tana watsa wa Azeema wani irin mugun kallo kaman ta shak'eta ta murk'usheta ta Mace a wajen, ba don ciwon nan nata da yake kawo mata cikas ba wllhi da tuni ta shak'e Azeema ta gama da babin ta....
Ganin tayi tsaye tana huci ya sanya Azeema k'ara matsowa daf da Mamy..... D'ankunnenta take tab'awa lokaci guda ta sassauta murya sosai tana fad'in "Mamy duk yanda zakiyi wllhi nafi k'arfin ki... Kuma kinji na rantse maki da kanki zaki tursasa wa Affan aure na... Don na tabbata idan kika kwaso makaman ki da sunan yak'i dani, toh masifan da kike ciki a yanzu sai ya fiye maki sauk'i fiye da wanda zaki shiga...." Ta k'arashe tana murmushi kafin ta shafi fuskar Mamy tayi shigewarta ta bar Mamy a wajen zuciyarta tamkar ta faso ta fad'o waje....
Driving yake yana hango fuskar Naseer a idanun sa... Shi kad'ai yake ayyana kalan revenge d'in da zai d'auka akan Naseer.... Wllhi Wllhi muddin yana numfashi Salma zata dawo garesa.. Sannan zai shayar da Naseer mamaki kalan wanda bai tab'a sha ba..
*******
Shopping maiji da Lafia Naseer ya umarci Fawaz yayi... Haka aka dinga shigar da kaya gidan Momy...... Tasan Naseer da hidima dama balle ya sami dalili....Tausayin Salma da Naseer ya cika zuciyar ta... A hankali ta mik'e ta nufi d'aki yanda Salma ke zaune tayi jigum abin tausayi..
Fawaz ya d'an kuma karkata kai yana duban Jamila wacce keta zabga murmushi kana yace "Idan na soma da bazawara ai kinga babbar sunnah na d'abbaka..."
"Dr bansan ka iya tsara kalamai har haka ba sabida ranar farko da na ganka... Kallon miskili na maka wanda furta kalma ke masa wahala.." ta k'arashe tana wani fari da idanu..
Fawaz ya murmusa da gefen bakin sa kumatun sa gefe guda ya loste kafin ya d'an girgiza car keys yana fad'in "Kallon da mutane suke min kenan musamman a wajen aiki... Kinsan dole saida tsarewa sabida guje ma raini...." Ya k'arashe yana d'an d'aga mata gira sama..
Murmushi ta d'anyi had'i da tab'e baki kana tace "Amma kuwa yayi suiting d'inka, naji mamaki da baka disga ni ba bayan masifar da na maka gaban abokan aikin ka..."
Wannan karan murmushi mai bayyana hak'wara yayi kana yace " Rashin tsoronki shine abu na farko da ya birgeni... Ina son mace mai courage... Shiyasa nayi mamaki da tsohon mijinki ya tak'ura wa rayuwar ki ya hanaki sukuni..."
Take annurin fuskar Jamila ya d'auke sabida ba kowa ya fad'o mata rai ba illa Alh Kabeer... Gashi tun daren jiya yake damunta da kira tak'i d'agawa.. K'arshe text ya tura mata cewa ta gama gudunta da sannu zai cimmata, ita d'in tashi ce...
Fawaz ya lura da canzawan da tayi.. D'an gyara tsayuwar sa yayi had'i da gyaran murya kafin yace "I'm sorry.. Ba nufi na bane na tuna maki shi... Duk yanda nakai da guje ma tunanin abin yak'i barina... Wllhi Jamila alk'awari na d'auka duk randa na had'u dashi I'll make him pay... Duk wani k'unci da ya jefa ki ciki..."
Kallon Fawaz kawai take hawaye na neman ciko idanunta.... Bata fatan Alh Kabeer yayi hurting Dr Fawaz sabida tsakani da Allah take son sa.... Amma tasan duk randa ya gano tana soyayya da wani farin cikinta na iya yankewa... Saurin saita kanta tayi had'i da masa sallama tana sanar dashi zata shiga ta duba Falaq... Fawaz ya bita da kallo cikeda tausayawa sam bazaka ce tayi aure har tanada d'iya ba.. Allah Ya mata halittan k'aramin jiki... Salma duk itace mai d'an girman jiki cikinsu....
Har ya shige motar sa yaga ledar kayan wasan Falaq da Ya jibgo mata.. D'auka yayi ya ajiye bakin k'ofa kafin yayi wucewar sa, zuciyarsa na masa wani irin sanyi..
*****
Motar Lubna na fitowa daga gidan na Affan na danno kai
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*38*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Sarai Deeni ya gane motar Affan ne... Duk horn d'in da Affan ke dannawa Deeni alamun ya koma ciki shi ya shigo Deeni yak'i komawa... Dubansa Lubna tayi taga yanda lokaci guda ya saka fuska tamkar ba Deeni ba, abin yaso bata dariya.... Su Deeni wai an iya kishi sarai itama ta fahimci motar Affan ne mai shirin shigowa cikin gidan.....
"Rankashi dad'e kaci girma mana ka bashi hanya ya shige..." Ta fad'i tana k'ok'arin k'unshe dariyar ta...
Wani kallo Deeni ya watsa mata kafin yace "Ai nan ba barikin su bane balle ya mana iko.... Mani aka bud'e gate don haka ni zan soma fita idan yaga dama yabi ta sama ya shige gidan..." Ya k'arashe yana turo hular sa goshi had'i da kwanciya cikin seat....
Lubna tasan kafiya irin na Deeni bazaiyi d'inba tunda yace bazaiyi ba, d'an murmusawa tayi d'abi'unsa na kuma burgeta kana tace "Toh wai kishi ne kake ko me...?"
Ido guda ya d'an bud'e yana kallonta still a kishingid'e yake kana yace "Ba kishi nake ba, I'm only doing my job... Ke sauk'a ki koma baya.... Ai nama manta ne kika zauna a gaba, oya koma baya kafin Innah ta hango ki kisa tayi firing d'ina... Kinsan koda zan iya ajiye aikin nan yanzu bazan iya ba....."
Lubna na murmushi tayi saurin katse sa da fad'in "Sabida bazaka iya jure rashina ba koh...."
Murmushin shima yayi kana yace "Ni dai ban fad'a ba...."
Turo baki tayi ta soma k'ok'arin bud'e k'ofa... Da sauri ya danna lock daga gefen sa kafin yace "Ke dalla bakisan wasa ba.. Look at you... Wai tayi fushi..."
Murgud'a baki tayi kana tace "Eh d'in kuma wllhi sai ka bani hak'uri if not bazanyi karatun ba ko naje class..."
Sihirtaccen murmushi yake, domin shi harga Allah sangartan ta na burgesa, dad'i da k'ari su duka biyun fad'ansu abin burgewa ne...
A hankali ya furta "Hey... Don't be mad okay... I'm sorry kinji...." ya k'arashe sihirtaccen murmushi saman fuskar sa...
Itama murmushin take gaba d'aya sai zuba love suke sun mance da Affan dake jiran su bashi hanya...
A fusace Affan ya fito yana huci kaman wani kububuwa ya nufosu... Lokaci guda ya shiga buga glass d'in gefen Deeni...
Lubna ce ta soma fitowa tanai ma Affan wani irin duba kana tace "Malam Lafia? ka tare mana hanya, ko baka gani ne....?"
Shaye da mamaki Affan ke duban Lubna.... A hankali ya soma takowa yanda take tsaye jikin motar... Sai sannan Deeni ya finciki marfin mota ya fito... Lokaci guda ya tsare gaban Affan...
Affan ya bi Deeni da kallon mamaki... Deeni ma tsallen kwad'on da Affan ya sanya sa a barikin su ya tuna.. Duk da tsoro da ya d'ura ma Deeni ruwa a ciki bai hanasa huci yana duban raini ma Affan ba... Da zaka tab'a k'irjin Deeni da kaji yanda take bugu da sauri-sauri sabida tsabon tsoro... Amma dole ya zamto gwarzo gaban macen da yake so, sam bazai bar wani ya wulak'anta ta a gabansa ba....
Murmushin rainin hankali Affan yayi yana duban Deeni don har lokacin mamakin Deeni yake, sai wani huci yake yanda kasan lallasa sa zaiyi....
"Wow..! Interesting, so kake ka nuna mata jarumtar ka... Toh ai ka riga ka b'ata abin tunda ka nuna mata ragwancin ka tun farko... Don nasan baka mance wancan tsallen kwad'on ba.... Idan kuma baso kake....."
Deeni ne ya katse sa da fad'in "You watch your mouth Soldier... A gaban Mace mu duka sojoji ne... Wanda yafi jarumta shine wanda yayi nasaran mallakan zuciyarta.... Idan dawowa kayi wajenta don ka riga ka rasa wancan toh kayi kuskure.... Sabida ka samu dama tuntuni bakayi amfani da damar ba.... Soldier ina baka shawara ba makarantar koyan yak'i kawai Ya kamata ka tsaya ba ya kamata ka tafi makarantar koyan soyayya sabida na kula abinda ka rasa kenan kuma yake wahalar da kai a rayuwa....."
Baikai aya ba Affan ya cakumo wuyar rigar sa yana wani irin huci yake fad'in "How dare you....!!"
Cikin sauri Deeni ya finciki wuyar sa daga rik'on da Affan ya masa shima hucin yake yana mai fad'in "Let go of me..." cikin zuciyar sa kuwa addu'a yake Allah sa kada Affan ya kai masa hannu ko k'afa don shakka babu za'a sami error, a fili kuwa sai wani huci yake...
Deeni yana hura hanci yake ci gaba da fad'in "K'aryar kakin dake jikin ka kake... Deenin da ka sani a baya daban da wanda ka sani a yanzu.... Kayi kad'an na k'yaleka kaci zarafina balle ka kaiga cin zarafin mace mai daraja da matsayi a idanuna......"
Baikai aya ba Affan dake faman turiri ya dunk'ule hannu yakai ma Deeni wata wawan naushi a hanci wanda saida yasa Deeni juyin masa kafin ya zube a k'asa... Lubna ta saki k'ara cikeda tashin hankali tayi kan Deeni... Sai sannan hankulan masu gadi ya dawo gsresu a tamanin suka nufo su.... Suna k'ok'arin d'aga Deeni da jini ke bin hancinsa da bakin sa...
Lubna kuwa tuni ta cire takalmin k'afarta wage ta shiga rusa ma Affan tana kuka tana fad'in ya fice a rayuwar su...
Affan ya zuciya ya kamo hannayen ta tuni Deeni ya kuma mik'ewa duka jinin dake bin hancinsa bai fasa duban Affan yana huci yana fad'in "Let her go you coward...."
"Coward..!!" ya nanata a hankali, shine wani banza ke kiransa Coward da kakin sa.. A tamanin ya kuma sakin hannun Lubna yayi wurgi da ita ya nufi Deeni... Masu gadi suka shiga rik'esa d'aya security d'in a d'ari ya nufi cikin gida yana k'walla kira ma Innah don sun tsorata da hidimar Affan..
Affan fad'i yake.. " I didn't come here for you, Ki fad'awa Munafukin Yayan ki zanzo na tafi da Salma coz tawa ce ba tasa ba..."
Ya juya yana duban Deeni kana ya kad'a 'yan yatsun sa yace "Zamu had'u sai ka maimaita abinda ka fad'i..."
Daga haka motar sa ya wuce cikin sassarfa lokaci guda ya bar k'ofan gidan a guje....
Da sauri Deeni ya k'araso yanda Lubna ke zube a k'asa tana bin gate d'in da kallo.... Durk'usawa yayi gabanta kafin yace "Are you alright...?"
D'an murmushi ta masa kafin ta jinjina kai lokaci guda kuma tace "You're crazy you know..? Wa yace kayi fad'a dashi... huh!? Ko ka mance shi Soja ne..."
A kufule Deeni yace "You shut up.! And so what if he's a soldier.... Ban damu da duk abinda zai sameni ba idan dai zan tsare mutuncin ki.... Da gani ma ba cikin hankalin sa yake ba..."
"Whatever..!" ta fad'i tana mik'ewa tsaye lokaci guda tana karkad'e jikin ta kana ta kuma dubansa tace "Kaga mu koma ciki Mama Tani ta wanke maka ciwon nan naka..."
Harara ya galla mata kana yace "Ni nace maki na min ciwo... Wuce muje already ma kinyi latti..."
Hannu a kunkumi take fad'in "Wllhi bazaka kaini sch da wannan ciwo ba......"
Kafin Deeni ya sami zarafin magana su Innah sun k'araso wajen Mama Tani na biye da ita....
Innah a tamanin tayi kan Lubna ta shiga dudduba ta tana fad'in "Auta da fatan babu abinda ya sameki...?"
Kafin Lubna ta sami zarafin bata amsa ta nufi Deeni tana huci take fad'in "Zaka bar gidan nan... Annoba dangin tsiya, fad'a min uwar me kayiwa d'iyata.."
Lokaci guda Lubna ta tare gabanta tana fad'in "Innah idan baki masa godiya ba bakya koresa ba, bakiga fuskar sa duk jini ba.. Ki dinga tsayuwa kina jin ba'asin abinda ya faru kafin ki d'au hukunci... Deeni dai da kika tsana yau shine ya cece ni don ba don shiba da tuni Affan ya harbe ni, yau da saidai kiji ana makoki na... Deeni shi ya saving d'ina...."
Innah ta dafe hannu k'irji tana gwalalo idanuwa waje take fad'in "Na shiga uku ni Dije, bindiga Auta... Lallai yau da ya tsokalo ma kansa yak'in da barikin su ma bazasu iya ba... Maza wuce mu shige gida kin fasa zuwa karatun..." Ta k'arashe tana janyo Lubnar ba tareda ta kuma bin kansu Deeni ba...
Deeni da Lubna suka kashe ma juna idanu suna masu murmushi, harda d'aga mata babban d'an yatsa alamun jinjinawa...
Yana cikin murmushi saiji yayi Mama Tani ta talle k'eyarsa... Ya d'an sa hannu yana sosawa yake fad'in "Wayyo Mama Tani wllhi na zaci wawan Sojan nan ne ya kuma dawowa da na nuna mas...."
"Ni dalla rufe min baki...." Mama Tani ta katse sa kafin ta shiga janyo hannunsa suka nufi cikin gida tana mai ci gaba da fad'in "Deeni bazaka tab'a jin magana ba, banda shirirta irin taka ina kai ina fad'a da Soja wato har ka mance wancan karan da suka kumbura maka cinyoyi koh..."
Bakin Deeni bai mutu ba yake ci gaba da fad'in "Ai wancan lokacin bansan matsayin Lubna a zuciyata bane amma yanzu kam I'm ever ready to fi......" K'eyarsa ta kuma dungurewa tana fad'in "Ni rufe min baki...abinda ka iya kenan cika baki... Kaikam wannan kaida Lubnar akayi auren bansan waye gwani wajen sangarci ba..."
Deeni na murmushi yake fad'in "Goyon ki ne fah Mama Tani, ke kika sangartni da yawa ki daina ganin laifi na..."
Bata kuma amsa Deeni ba don tasan bazaiyi shirun ba ta wuce dashi backyard ta shiga goge masa ciwon sai d'an k'ara yake... Lubna kuwa tana jin haka ta hau lek'ensu ta window sai faman k'yak'yata dariya take lokaci guda ta d'au wayarta ta shiga d'aukan video, tsan-tsan soyayyar sa na kuma shiga zuciyar ta...
*********
Kusan kwana uku suna sab'ani da Affan gashi ko office Affan bai zuwa dukda ance masa an gansa a barikin nasu, sannan da yawan wanda suka ga Affan sun sanar dashi a bar d'insu na soji ake ganinsa..... Sosai hankalin Naseer ya tashi sam baiso Affan ya koma ruwa ta dalilin sa, Kai tsaye apartment d'in Affan ya nufa yana mai addu'an Allah yasa ya same sa....
Ya jima yana danna bell, ko alamun mutum baiji ba, har ya juya da niyyan tafiya yaji k'aran fashewar kwalba daga cikin gidan.... Cikin sauri ya shiga murd'a handle d'in k'ofar nan kuwa ta bud'e...
Ganin yanda gidan ya hautsine sosai ya d'aga hankalin Naseer, ga kwalaben giya tako ina... A hankali yake takawa har ya isa tsakiyar parlorn yanda ya hangi Affan rakub'e can k'asan carpet idan ya shanye kwalban giya sai yayi jifa da ita ta fashe.....
Tausayin Affan ya cika zuciyar Naseer.... A hankali ya isa ya zauna dab dashi...
Affan ya d'ago rinannun idanun sa yana duban Naseer kafin yayi murmushi yana furta "Wow! Lucky me... A visit from an unexpected guest.. You welcome Amigo... Join me...." Ya k'arashe yana mik'a masa kwalban giyar dake hannun sa....
D'an kau da kai Naseer yayi cikeda tausayin Affan, lokaci guda ya d'aid'aice kaman ba shi ba..... A hankali ya dawo da dubansa ga Affan d'in had'i da k'ak'aro murmushi ya sakar masa kana ya girgiza kai yace "No thanks...."
Affan ya kuma murmusawa kafin yace "Ina fatan kazo min da ita...."
Naseer bai amsa sa ba sai karb'an kwalban giyar da yayi ya ajiyeta gefe kana yace "Affan I came here basically because of you and your dear life....... But da alama bazamu iya magana yanzu ba... Seems You're drunk...."
Dariya Affan ya fashe dashi kana yace "Look Naseer I'm not drunk, a cikin hankali na nake, so tell me what's wrong with my life...."
K'uri Naseer ya masa kana yace "Affan alot of things are wrong with your life.... Your life is in jeopardy...."..
"Hold it..... Ka gane Naseer ka tashi ka tafi zaifi mana sauk'i..."
Girgiza kai Naseer yayi kafin yace "Affan bai kamata ka jefa rayuwar ka cikin garari ba akan Mace...."
Mik'ewa tsaye Affan yayi dukda d'an tangad'i da yake yana wani irin duba ma Naseer kana yace "Just look at yourself Naseer, kaji abinda kake fad'i...? Look I don't want all these nonsense anymore.. Pls stop pestering my life... I have my life to live, so leave me alone to do what I want with it, okay..."
Nasser ma mik'ewa tsaye yayi kan k'afafunsa yana mai duban Affan yake fad'in "Affan you're my best friend, and our friendship is quite going beyond ordinary friendship, we're becoming brothers.. bana tunanin zan ganka kana abunda bai kamata ba na k'yale ka, Affan kar ka jefa rayuwar ka cikin halin da zaka zo kana nadama a k'arshe...."
"Naseer please, don't let me loose my temper on you, because if I do... You won't like me for anything... Ka tafi ka k'yaleni dan Allah... Wllhi na tsani ganin ka..."
D'an tattare naman goshinsa Naseer yayi had'i da fuzar da iska kafin yace "Enough Affan....!" Jin Affan baiyi shiru ba yasa Naseer daka masa tsawa cikin fad'in "I said enough..!!! Ina ce duk akan ta ne, sabida ita ka koma something else.. Fine, zan saketa da zaran Daddy Ya sami lafiya ya fayyace mana komai... And I promise babu abinda zai shiga tsakani na ita... I won't allow you to go astray a dalilin rasa macen da kake so... "
Lokaci guda Affan ya katse sa yana mai tafe hannaye yake fad'in "How generous... Gaskiya ka birge... Look get out of here.. Get out I said..." Ya k'arashe yana mai nuna masa k'ofa..
Nasser da idaniyan sa suka kad'a sukayi jazir duban Affan kurum yake ba tareda Ya iya furta komai ba..."
"Hope you still remember the way to the door...?" ya k'arashe yana watsa ma Naseer mugun kallo..
Har kokacin Naseer bai furta komai ba sai ficewa da yayi cikin sauri, zuciyar sa na masa zafi... Kai tsaye gidan sa ya wuce ya zauna saman Sofa a parlor had'i da rapka tagumi da hannayen sa biyu .lokaci guda ya ciro wayar sa yayi dialing layin Momy Lami...
Momy da Jamila suna zaune sun tasa Salma gaba suna mata nasiha yanda harta abinci ba wani ci take ba duk ta rame a 'yan kwanakin don harga Allah bata san makomar rayuwarta ba.. Kiran Naseer da Momy ta gani ya sanyata d'an matsawa gefe tana amsawa...
Shiru Momy tayi tana nazarin buk'atar Naseer d'in don batasan yaya zasu kwashe da Salma ba... Saida ta d'an sauk'e ajiyan zuciya kafin ta k'arasa ta tadda Jamila da Salmar har lokacin suna tare...
Jamila ce ta d'an d'ago ta dubi Momy yanda tayi tsaye sororo ta rasa abin fad'i kana tace "Momy lafia dai koh..?"
Sauk'e ajiyan zuciya Momy ta kuma yi kana tace "Yace yana son ganinta zasuyi magana, just the two of them... Yana jiranta a apartment d'insa, ya ce na kai masa ita...."
Ai Momy bata ida rufe baki ba Salma ta mik'e zunbur tana k'walalo idanuwa waje
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*39*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Girgiza kai Salma ta shiga yi cikin sauri "Momy dan Allah nidai banson zuwa wllhi bazan iya zuwa ba... Kinji dan Allah..."
Gaba d'aya ta daburce lokaci guda
Hannayenta Momy ta rik'o suka zauna saman kujera, cikin sanyin murya take fad'in "Salma kiyi hak'uri ki tafi kiran mijin ki, babu wanda yasan abinda zai fad'a maki kinga tunda kukayi aure baku zauna kunyi k'wakk'waran magana ba... Dan Allah ki amsa kiransa kinji daughter..." Ta k'arashe murmushi kwance saman fuskar ta...
Girgiza kai Salma take hawaye na neman zubo mata take fad'in. "Nidai dan Allah ku daina cewa soja mijina ne.... Kuma fah Momy bansan yaya zan soma dubansa ba... I just don't know, banso na had'u dashi don Allah... Ko menene kawai ya sanar daki... Don Allah kinji..."
Sai sannan Jamila ta mik'e ta dawo kusa da Salma had'i da dafa kafad'un ta cikin sanyin murya mai kwantar da hankali Jamila ta soma fad'in "Come on Salma, kar kiyi haka wa Naseer, at least kije ki tunda yace magana yake so kuyi besides bai cancanci haka daga gareki ba... Oya share hawayen nan..." ta k'arashe tana goge mata hawayen lokaci guda Jamila ta shiga shirya Salma..
Kallonta kawai Salma keyi sanda ta d'auko wata doguwar riga ta mik'a mata...
Girgiza kai Salma tayi kana tace "Kai Addah this is not necessary.... Dan Allah ki barni kawai naje da kayan jikina..."
Muryar Ilham suka jiyo tana fad'in "Gaskiya dai ki canza na jikin ki Addah Salma, ki karb'i wanda Addah Jamila ta baki ki saka..." ta k'arashe tana rolling manyan idanunta da sam basa gani tana mai wasa ma Falaq...."
Ba don taso ba ta amshi rigar ta saka. Ya kuwa zauna sosai a jikin ta... Jamila ta kuma d'ibo kayan kwalliya zata fente mata fuska ai a tamanin Salma ta mik'e tana girgiza kai take fad'in "Kai Addah Wllhi a'a... Haba aima sai yace har kwalliya nayi masa.... Addah pls ki fahimci aurena da Naseer ba kaman ko wani aure bane... Don Allah ki k'yakeni na tafi haka...."
Jamila bata kulata ba sai shafa mata powder take tana fad'in "Aurenki kaman na kowa ne tunda aurene da shaidu da kuma sadaki.... Wow kiga yanda kikayi kyau..." ta k'arashe tana nuna wa Salma k'aramar madubi...
K'ara Salma ta saki ganin kwalliyan da Jamila ta cab'a mata don dama ita sam ba gwanar kwalliya bace... Cikin sauri ta zari tissue paper ta shiga goge fuskar ta.. Momy kuwa sai dariyar su take...
Da k'yar Salma ta yarda ta bar powder a fuskar ta amma kam sauran kwalliyan duk ta goge su...
Jamila ta d'au mayafin rigar ta rufa mata.... Harda fesheta da turaruka.... Tayi kyau kam babu laifi
Har suka fito k'ofar gidan k'irjin Salma bai daina bugun tara-tara ba.... Cak ta tsaya ta kasa ci gaba da tafiya lokaci guda ta d'ago tana duban Momy Lami kana tace "Momy dan Allah....." Lokaci guda Jamila ta k'araso tana murmushi ta kamo hannayen Salma kana tace "Kar ki mance ko meye zai sameki zamu kasance tare as... Family kinji..." A hankali Salma ta saki murmushi kafin ta jinjina kai... Hannunta Momy ta kama kafin tayi sallama da Jamila suka wuce...
Kallo Jamila ta bisu dashi murmushi kwance saman fuskar ta.... Tana nan tsaye bata koma cikin gida ba har saida taga b'acewar su... Tasa kai zata juya cikin gida kenan taji tsayuwar mota...
Cikin sauri ta kuma jiyowa don jikinta ya bata shine... Aiko shi d'in ne, sanye cikin k'anan kaya yayi matuk'ar kyau yarintar sa ta fito k'arara.... Tana nan tsaye fuskar ta d'auke da murmushi har ya fito daga cikin motar shi d'inma murmushi kwance saman fuskar sa....
Ganin ya nufota yasa ta d'auke kai daga dubansa still murmushi saman fuskar ta...
Sallama ya soma mata da murmushin nan nasa.... A hankali ta amsa kafin ta k'arada "Amma dai yau ba aiko ka yayi ba....?"
Fawaz ya d'an jingina jikin k'aramar garun yana d'an sosa kansa da keys d'insa fuska d'auke da murmushi yake fad'in "Mu gaisa mana first, sannan nima zuwata daban ba auren Uncle nazo gyarawa ba nawa auren nazo garawa...."
Jamila ta murmusa had'i da d'an rufe fuska kana tace "Banji a jikina za'a barka ka auri bazawara harda d'iya ba.. Bismillah mu shiga ciki..." ta k'arshe tana mai masa iso...
"Kar ki damu, nan ma yayi... Ehen me kike cewa...?"
Murmushi Jamila tayi had'i da d'an juya idanu kana tace "Bance komai ba Dr.... Ya aiki..?"
Saida ya kuma murmusawa kafin yace "Duk randa na auro bazawaran mai d'iya zaki maimaita abinda kika fad'i yanzu.... Ina baby Falaq...?"
Jamila ta d'an rausayar da idanu kana tace "Tana ciki tareda Ilham..."
Fawaz d'inma murmusawa yake kana yace "Anya Ilham zata bamu d'iyartan nan kuwa mu raineta a gidan mu...?"
Wannan karan d'an darawa Jamila tayi kana tace "Falaq d'iyar Ilham ce sai yanda taso za'ayi.."
D'an d'aga gira sama yayi kana yace "I see... Yaushe zamuje ki gaida Mum kinsan na fad'a maki batada lafiya... And finally na samu nayi introducing d'inki wa Family d'ina..."
D'an zaro idanu waje Jamila tayi kana tace "Da wuri haka.. I tot mun gama magana sai an gama da issue d'in auren su Salma first..."
Fawaz ya d'an mata k'uri kana yace "Ai gaisuwa nace madam, kuma sam ban sanar dasu cewa sister d'in matar Uncle nake nema ba kinga idan munje sai na fad'i masu a lokacin.... A ganina kaman hakan zaifi... Pls don't say no, ya kamata ki je kiga mahaifiyata tana cikin tsananin jinya...."
Shiru Jamila tayi tamkar mai tunani kafin ta d'an jinjina kai kana tace "Shikenan Dr I'll think about it... Don dai kawai kace tana cikin jinya ne amma kasan zuwa gidansu saurayi ba d'abi'ar mu bane..."
Ya kuma murmusawa kafin yace "Na fahimce ki... Kar ki damu gaisuwa kawai zakiyi, inaso na nunawa mahaifiyata ke koda bata cikin hankalin ta..."
Jamila ta d'an murmusa lokaci guda ta tsinci kanta da fad'uwan gaba mai tsanani...
******
Kanta a k'asa sanda suka k'arasa shigowa cikin parlorn, ga bugu da k'irjinta keyi musamman da ta jiyo muryar sa na amsa sallamar Momy..... Shi kuwa Naseer mutuwan tsaye yayi yana dubanta bata tab'a masa kyau irin na yau ba.... Bugun zuciyarsa ya k'aru... Momy dai kallo ta bisu dashi su duka biyu.. D'an gyaran murya da tayi ya dawo da hankalin Naseer...
K'ok'arin saita kansa yayi yana mai murmushi yake nunawa Momy wajen zama yana fad'in "Momy sannun ku da zuwa, ku zauna please..."
Momy ta d'an murmusa sanda taja hannun Salma suka zauna bisa sofa har lokacin idanun Salma a k'asa...
Gaisawa suke da Momy amma hanakalin sa kacaukam akan Salma yake.... Bayan sun ida gaisawa shiru ya gifta na d'an wasu dak'ik'ai.... Momy ce ta d'an yi gyaran murya kana ta mik'e tana mai duban Naseer take fad'in "Ni zan... Jira a waje..."
Ai a tamanin Salma ma ta mik'e zunbur rik'e da hannun Momy murya har na rawa take fad'in "Momy wllhi nima binki zanyi...."
Momy ta d'an murmusa kana tace "Soja dai ya zamto maki dodo ko Salma, toh kar ki damu ki sakin jikin ki kuyi magana zan jiraki a nan waje..."
Naseer dai k'uri ya masu yana kallon ikon Allah... Da k'yar Salma ta yarda ta koma saman sofa ta zauna... Momy tana ficewa Naseer ya take mata baya....
Godiya ya mata kafin yace taje babu damuwa zai maido da Salma gida...
Momy ta d'an murmusa irinta manya kafin tace "Soja karfa zancen yayi tsawo kasan har yanzu abin na jikinta bai saketa ba, har yanzu gani take kaman mafarki ne..."
Naseer ya fahimci Momy, d'an sosa kansa yayi kana yace "Kar ki damu Momy ba jimawa zamuyi ba... Zan maidota anjima kad'an da yardar Allah.."
Momy ta jinjina kai kafin suka kuma yin sallama... Salma tana jiyo sautin tafiyar sa had'i da rufe k'ofa gabanta yayi wani irin yankewa ya fad'i.. Cikin sauri ta kuma mik'ewa tana mai girgiza masa kai take rok'onsa ya bar k'ofar a bud'e....
Harga Allah taso basa dariya yanda kasan wanda zai guntule mata kai... D'an murmusawa yayi ganin yanda ta razana sosai kana ya isa jikin k'ofar ya bud'eta gabad'aya yana murmushi yake fad'in "Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zan maki magana kawai nake so muyi .."
Kunya ya rufe Salma, kar dai Soja yayi tunanin wani abin daban take nufi, sam ita ta kasa yarda wai shid'in mijinta ne..
Naseer ya zauna cikin d'aya daga cikin jerin kujerun yana kallon yanda take faman wasa da 'yan yastun hannun ta... Shiru ya gifta na wasu dak'ik'ai don shi kansa baisan ta yanda zai soma ba...
D'an gyaran murya yayi had'i da muskutawa ya d'an turo wajen kujeran kafin ya kirawo sunanta a hankali...
Kasa d'agowa tayi ta dubesa har lokacin idanunta a k'asa... Dabara ta fad'o wa Naseer don yasan kafin ya sako mata zancen serious sai ya soma janta da d'an wasa sabida ta saurare shi sosai ta basa had'in kai su tattauna lamarin ..
"You look good..." Ya fad'i fuskar sa d'auke da murmushi.. Still idanunta a k'asa. K'irjinta na ci gaba da bugawa ta kuma jiyo muryar sa yana fad'in "Can't I even have a glance... Haba Salma Soja ne fah.. Okay fine, idan baki so mu tattauna at least zan ci darajan gaisuwa...."
Sai sannan ta d'an murmusa tana k'ok'arin had'iyan miyau a bushesshiyar mak'ogoronta take gaidashi...
Naseer ya amsa da sakin fuska sannan ya d'aura da "Ko har yanzu tsoron barikin namu kike don na lura baki so Momy tayi nesa dake, kar ki damu baza'a harba bindiga ba...."
Murmushi mai d'an bayyana hak'wara wannan karan tayi kafin tace "Soja yaya jikin Daddy, ina son sanin halin da yake ciki...?"
Naseer ya d'an sauk'e ajiyan zuciya kana yace "Toh da sauk'i kenan zamuce tunda har yanzu yana numfashi, amma still bai fita a coma ba..."
A hankali Salma ta furta "Allah Ya bashi Lafia..."
Naseer ya amsa da Ameen.... Dak'ik'ai suka d'an kuma shud'ewa yana karantar Salmar lokaci guda..
Har ta cire rai bazai kuma magana ba ta jiyo muryar sa yana fad'in "I know this is not easy for you either....." Shiru ya d'anyi yana k'ok'arin had'o kalamai saman harshen sa kana yaci gaba da fad'in "Salma na umarci Momy ta kawo ki nan ne sabida mu samu muyi magana gameda rayuwar mu, nasan kina sane da abinda ya faru, abun yazo mana bazata ko nace ba yanda muka yi tsammani ba... I was to marry Shareefah... Kwatsam Al'amarin ya juye.. Though ban sani ba ko ke kinada masaniyan akan dalilin da yasa Daddy ya aiwatar da wannan Al'amari,...... Salma to be honest har yanzu gani nake kaman mafarki ne maybe watarana za'a tashe ni....." Ya d'an ja fasali zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri... Saida ya d'an fuzar da iska had'i da bud'e hannaye kafin yaci gaba da fad'in "I....I... I know you love him..... And yeah... He loves you as well, Salma Affan yana sonki... Ko kad'an banso na zamto sanadin rabuwar ku....." Kasa ci gaba da maganan yayi lokaci guda
Salma kuwa izuwa lokacin ta kasa rik'e kukan da take k'ok'arin rik'ewa..... Kuka take tana k'ok'arin toshe bakinta bata so sautin kukan nata ya fito .....
K'uri Naseer ya mata tausayinsu su duka biyu na ratsa zuciyar sa.... A tunanin sa sabida tsananin son Affan da Salma keyi take wannan kuka... Gashi a b'angaren sa soyayyar ta kullum growing yake cikin zuciyar sa bayan giftawan ko wani dak'ik'a....
A hankali ya mik'e daga kujeran da yake zaune a kai ya k'araso gaban kujeran da take ya d'an durk'usa gabanta..... Kukan Salma ya k'aru... Duk juriya irinta Naseer hawaye ne yaji suna neman ciko idanunsa sabida tausayin kansa da rayuwar da zaiyi babu Salma a tare dashi, gashi dai ya sameta amma ya sani su biyun are not meant to be together.... Yana son farin cikin Salma sannan yana son farin cikin Affan, bazai zamto sanadin yankewan farin cikinsu ba...
Cikin sanyin murya ya soma fad'in "I promise bazan zamto sanadin k'uncin ku A DUNIYAR MU ba, Salma both you and Affan kunada matsayi a wajena.... Zan iya sadaukar da farin cikin ratuwata ma dukan ku biyu, as far as zaku kasance cikin farin ciki....." Kasa ci gaba da magana yayi jiyo sautin kukan nata k'aruwa yake...... Gaba d'aya zuciyar sa ta kuma yin weak, izuwa lokacin bazai iya juran ganin kukan nata ba... Bai san yaya akayi ba shidai kawai ya tsinci kansa yana mai rungumar ta... Sosai ya matse ta cikin jikinsa, murya na rawa yake fad'in "Please ki daina kukan nan.... It hurts.... It really does hurt... Look I promise da zaran Daddy ya sami lafia... I.... I'll divorce.....you, and.... and finally zaki kasance da Affan... the love of your life...."
Bai saketa ba bata daina kukan da take ba.... Duk dauriya irinta Naseer saida yaji siriryar hawaye tana neman fitowa daga idanunsa... Tsananin tausayin su yake ji su duka uku, shi kansa, Affan da kuma Salma.. Tabbas da zuciya tana shawartan mutum kafin ta soma son wani abu ko k'in wani abu, tabbas da basuyi tarayya akan soyayyan mace guda ba shida aminin sa....
Sandarewa Affan yayi yana kallon su yanda Naseer ya rungume Salma kaman zai maidata cikin sa... Zuciyan Affan ta kuma karaya,... Tabbas sabida maganar da Naseer ya fad'a masa ya sa shi zuwa gidan, Naseer ya sanar dashi babu abinda zai shiga tsakanin sa da Salma hasalima sakinta zaiyi..... Sai gashi ya tadda akasin haka.... He was stupid da ya yarda ma ransa Naseer zai saki Salma..... Zuciyarsa ta shiga masa zafi.... Cikin sauri ya juya ya fice daga gidan yana kallon hanya bibbiyu.....
Saurin k'watan kanta tayi daga rik'on da Naseer ya mata lokaci guda ta mik'e ta nufi k'ofa har lokacin idanunta basu daina zuban ruwa ba.....
Saurin mik'ewa yayi ya tare gabanta lokaci guda rinannun idanunsa akanta...
"Soja please....." ta kasa ci gaba da maganar.
Girgiza mata kai yayi kana yace "No Salma bazan barki ki fice kina kuka ba.... Baki san kukan ki yanada zafi da rad'ad'i ba....?"
Yanayin maganar nasa ya sanyata saurin d'ago idanu tana dubansa... Lokaci guda kuma ta sauk'e kanta k'asa.... Ta sami kanta tana mai jinjina kai had'i da goge hawayen fuskar ta...
Murmushi Naseer yayi kafin ya d'an sassauta murya yace "Look up, d'ago kanki na gani ko hawayen ya k'are gaba d'aya..."
Murmushi tayi still kanta a k'asa..
Naseer ya soma takowa daf da ita... Bugun k'irjinta ya k'aru... Saida ya k'araso dap ita sosai yana ganin tsakiyar kanta kafin ya d'an rage tsawonsa yasa hannu ya tallafo fuskar ta lokaci guda yasa hannu ya shiga share mata hawayen su duka sunyi k'uri ma juna ba tareda sanin sunyi d'in ba....
Salma ce ta d'anyi yunk'urin matsawa baya saidai kuma tuni Naseer ya rik'o kunkuminta yana duban Face d'inta sosai itama cikeda tsoro take dubansa...
A hankali yake sakin sassanyar murmushi kana yace "Duk sanda kika kuma yin kuka ko bani a wajen zan jiyo ki so ko kin koma gida babu kuka kinji....."
Murmushi tayi wanda yafi kama da yak'e dukda ragowar hawayen dake idanunta kafin ta shiga gyad'a masa kai da sauri tana k'ok'arin k'watan jikinta take fad'in "Soja..please.... Let go..."
Murmushin ya sakar mata kafin ya cikata a hankali had'i da saita kansa... "Muje na maidaki gida...." ya fad'i yana d'aukan wayar sa saman kujera.....
Ai Salma kam tuni tayi gaba ta fice a zaton ta Momy Lami tana nan waje har lokacin tana jiransu.. Tsigar jikinta sai faman tashi yake tunda Naseer ya rungume ta.. Ta kasa yarda da abinda ya faru tsakanin su biyun, maganganun da Naseer ya fad'a mata suka shiga yawo a kwanyarta lokaci guda zuciyarta ta shiga mata zogi wato dai Soja baya sonta, Aunty Sharefah yake so...
Muryarsa ta jiyo yana fad'in "Muje koh...".
Ba tareda ta dubesa ba baki a ture tace "Toh ai banga Momy ba..."
Naseer ya d'an murmusa had'i shafa sumar kansa kana yace " Tasan a good company ta barki shiyasa ta tafi...." ya k'arashe teasingly
Bata kuma cewa komai ba don shirun nata yafi mata sauk'i... Tafiya suke su duka biyun babu mai cewa komai, kowannen su da tunanin da yake cikin zuciyar sa.. Salma kuwa sai buga sauri take don ko kad'an bata so su jera da Sojan saidai abinka da Soja wanda dama tafiyar nasa yafi kama da sassarfa sam ta kasa tsere masa...
*******
Murmushi Affan ya saki sanda ya tuno kalan rungumar da ya ga Naseer yama Salma... Lokaci guda yayi jifa da kwalban giyan ta fad'i ta fashe... Is like shi kad'ai ne ke shan wahala su suna can suna cin soyayyar su... Lokaci yayi da zai tarwatsa masu farin cikin da suke ciki.... Ya saki wata murmushi kafin ya soma furta "Naseer idan Salma bata cikin kwanciyar hankali toh kuwa tabbas kaima bazaka kasance cikin kwanciyar hankali ba... Zan tarwatsa Farin cikin da kuke ciki kaman yanda kuka tarwatsa min nawa... I want to see you suffering...." ya k'arashe yana hura hanci... Hanyar da zaibi don wahalar dasu ya shiga nemowa.... Lokaci guda ya saki murmushi sanda ya tuna makauniyar k'anwar Salma... A fili ya furta "Yeah.. The blind one...." Lokaci guda kuma yayi bursting cikin tsananin dariya had'i da zubewa saman kujera...
******
Jamila na murmushi ta kuma dungurin Salma ganin har lokacin sam babu walwala a tattare da ita kafin tace "Ke wllhi kun bala'in dacewa baki gani ba sanda kuka jero...."
Salma dai bata ce komai ba sai tab'e baki da tayi.... Jamila ta kuma murmusawa had'i da kashe mata idanu kana tace "Zama ki daina wannan nok'e-nok'en ne sabida ni nasan kina son sa...."
Wani kallo Salma ta galla mata. In a furious tune take fad'in "Ni nace ina son shi... Allah Ya sawwak'e ni.... Wllhi bana sonshi nima kaman yanda baya sona, Addah Wllhi Anty Shareefah Soja yake so...." ta k'arashe hawaye na neman zubo mata...
Tausayin ta Ya cika Jamila, a hankali ta rungumeta tana lallashin ta....
Da dare Naseer kasa barci yayi, idan ya runtse idanu saidai ya hango fuskar Salma tana kuka... Haka kurum zuciyar sa ta dinga raya masa k'ila har yanzu kuka take.. Gaba d'aya sai yaji zuciyar sa na masa zafi... Uwa uba da ya tuno kalaman da ya fad'a mata... Anya kuwa ba kuskure yake shirin yi ba... Amma hakan shine kawai masa mafita, rabuwa da Salma... Lokaci guda ya runtse idanun sa yana mai tuno yanayin da ya bar Affan ciki...
A b'angaren Salma kuwa idan ta runtse idanu saidai ta hangota cikin jikin Soja... Zuciyarta ya dinga bugawa da sauri, abun ya kasa barin jikinta gaba d'aya jinta take tamkar ba ita d'inba... Cikin sauri ta mik'e ta nufi bathroom don yin wanka ko zata daina jin jikinsa da hannayen sa cikin nata..
*******
*Bayan kwana uku*
Zaune ya sami Naseer d'in a Office, fuskar sa d'auke da murmushi ya shigo... Saida Naseer ya mik'e tsaye ganin bak'on abu tattare da Affan d'in..
Bai daina murmushi ba saida ya k'araso yayi hugging Naseer
Da mamaki Naseer ke duban sa... Affan ya kuma sakin murmushi yana d'an bud'e idanunsa yake fad'in "Hey don't ask me yaya nake... As you can see, quite steady ...."
D'an murmushi Naseer yayi had'i da girgiza kai kana yace "Banyi tsammanin haka daga gareka ba..."
Affan ya kuma murmusawa kafin yace " Naseer regarding what we've been through lately..... I.... I'm sorry, kayi hak'uri na yarda da shawarwarin ka.. And insha Allah bazan kuma komawa d'abi'an da na tassama ba... Insha Allah na canza.... Naseer don Allah kayi hak'uri gaskiyar ka ne, mu ajiye maganar auren ka da Salma muyi focusing akan jinyar Daddy...."
Murmushi Naseer yayi kafin ya dafi kafad'an Affan yace "Brother harga Allah naji dad'i cikin raina sannan insha Allah idan Daddy Ya sami lafiya zan baka chance to be with her.. "
Affan ne yayi saurin d'aura hannunsa a bakin Naseer kana yace "Pls Naseer mu ajiye wannan maganar a gefe... Kar ka damu dani, muyi fatan alkhairi ma junan mu..."
Murmushin dake saman fuskar Naseer ta kasa gushewa baisan sanda yayi hugging Affan ba zuciyar sa na masa sanyi..
Affan kuwa kafiran murmushi kurum yake had'i da k'ura ma waje guda idanu...
*******
Mamy ta tura crutches d'inta bayan mota ta cangwala ta shige gaban motar yayinda Shareefah ke tuk'a motar... Suna ficewa Azeema ta tari babur tabi bayansu
Azeema tana ganin sun karyi kwanan gidan su Naseer ta saki murmushi kafin ta zaro wayarta cikin jaka ta shiga dialing layin Naseer...
Jin bai d'aga ba don dama ba kasafai yake d'aga layin da bai sani ba musamman idan yana tsaka da aiki... Lokaci guda Azeema ta tura masa sak'o
Murmushi take kan faman cikin zuciyarta tana mai furta _Bazan tab'a barinku kuyi nasara ba.._
A tare suka fito bayan sun gama tattaunawar su Innah na make cikin motar tana binsu da kallon raini, yayinda Mamy ta cangwala ta fito daga motar tana saka wa mai adaidaita hannu... Shareefah ta lek'o ta window tana fad'in "Mamy kin tabbata babu matsala zaki iya zuwa asibitin ke kad'ai?"
Mamy na washe baki take fad'in "Kar ki damu Shareefah... Zan iya zuwa, nidai damuwata ki kai Innah gidan tsinanniyar matar a raba auren Naseer da Salma don wllhi mayu ne kaman yanda suka so shan jinina da shike kurwata nada k'arfi shiyasa na gagare su haka zasu tand'e da d'anki tass..."
Ta k'arshe tana duban Innah dake make bayan motar tana taunar chewing gum, Mamy yanda kasan masu baran bakin titi, gaba d'aya babu nutsuwa a tattare da ita..
Cikin zuciyar Innah kuwa fad'i take _Ai dama zasu lashe sa da naji dad'i.... Kawai farin ciki ne bazan bar Naseer ya kasance ciki ba A DUNIYAR MU shiyasa ma zanje ayita ta k'are...._ Ta k'arashe tunanin nata tana mai kwanciya cikin kujera..
Shareefah kuwa d'agawa Mamy hannu tayi tana fad'in "Mamy ki gaida Daddy pls,.. Allah sa yau su barki ki shiga wajen sa..."
Mamy na washe baki take d'aga masu hannaye bibbiyu crutches d'inta mak'ale a hammata, tana jinjina kai lokaci guda Shareefah ta kwashi motar yayinda adaidaita ya tsaya gaban Mamy tuni ta shige tana fad'in "Malam TH zaka kaini..."
Azeema ta murmusa kafin tace da mai babur d'in "Malam mubi bayan keken can..."
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*40*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kaman ance ya duba text d'in da ya shigo masa bada jimawa ba... Mamaki ne ya cika sa yana mai k'ara karanta sak'on
Affan dake faman nuna masa wata map yana bayani Naseer yayi saurin d'an bubbuga kafad'ansa kana yace "Muje Affan something's wrong..."
Bai jira cewar Affan ba ya fice cikin sauri.... Gaban Affan ya yanke ya fad'i ganin yanda Naseer ya fice... Allah sa dai ba wani abu bane ya sami Salma... A tamanin ya take ma Naseer baya...
Motar Naseer suka shige suka d'auki hanyar gidan Momy Lami... Affan na tambayar sa Naseer bai sami zarafin amsa sa ba don gaba d'aya a birkice yake, baya fatan wani abu ya sami Salma...
*********
Mamy sai shek'a kuka take a bakin ward d'in tana rok'onsu su k'yaleta ta shiga taga mijinta.... Likita guda ne ya tausayawa Mamy shikam a ganin sa da an bar matar nan ta shiga taga mijinta ta masa addu'a... Saidai kuma wannan doka Naseer ne ya umarce su cewa kada su k'yale kowa ya shiga kan Daddy musamman Mamy har sai ya sami lafia....
Mamy ta koma masu tamkar mahaukaciya sai kururuwa take gashi sam ba'a son hayaniya a wannan wajen...
K'arshe dai yanke shawarin k'yaleta ta shiga likitocin sukayi sabida yanda ta fita out of control....
"Hajiya zamu k'yaleki ki shiga amma pls don't take too long , ki dubasa ki fito... I'll talk to the security man...."
Mamy ta shiga washe baki tana jinjina kai take fad'in "Allah dai ya biya ku.... Tana k'ok'arin mik'ewa taji an kamata ana taimaka mata..... Bata kula waye mai d'agota ba saida ta mik'e tsaye car kana tayi idanu hud'u da Azeema fuskar ta d'auke da murmushi... Gaban Mamy yayi wani irin yankewa ya fad'i tamkar wacce zata runtuma a guje....
*********
Motar Naseer na tsayuwa suka jiyo muryar Shareefah sai zage zage take tana bak'anta su Salma.... Jamila kuwa bakinta bai mutu ba sai mayar mata take yanda take shiga itama ba ta nan take fita ba....
A birkice suka shigo parlorn daga Naseer har Affan....
Salma dai rakub'e take a gefe tana hawaye yayinda Momy keta faman tausan Innah wacce itama ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba.. Tana fad'i ma Momy ta lashe mata d'a...
Idanun Naseer akan Salma ganin irin kukan da take ya kuma sa hankalin sa ya tashi... Saurin k'arasawa yayi yana k'ok'arin janye Innah.... Innah ta kuma fincika tana watsa masa mugun kallo kana tace "Ai bansan rashin mutuncin naka har ya kawo nan ba Naseer... Ka zab'i wata uwar sama dani... A zatona Shareefah ta fad'a ne kawai don ta bak'anta ka sabida abinda ka mata, ashe sam ba haka bane... Gaskiya ta fad'i... Wato kai sarkin kirki koh... Ka kasa kawo min matar naka sai ma uwarka na bariki......" muryar Innah ya soma rawa tana shirin soma kukan munafunci....
Wani mugun kallo kurum Naseer ke watsa wa Shareefah.... Idanun Affan akan Salma... Lokaci guda kuma ya sauk'r idanun sa kan Ilham.... Cikin sauri ya k'arasa ya kamo hannun Shareefah yana fad'in "What has gotten into you Shareefah.... Look don't complicate things the most.... Oya let's get out of here.... Naseer please kuyi hak'uri....."
Shaye da mamaki Shareefah ke duban Affan.... K'ok'arin fincikan hannunta take tana fad'in " Iyakacin gaskiya nake fad'i kuma a babin gaskiya ba'ayiwa Innah adalci ba.. Ka sake ni nace Affan...." Bai saketan ba sai janyeta waje da yake yi da iyaka k'arfin sa.....
Naseer girgiza kai kurum yayi kafin ya kamo hannun Innah yana k'ok'arin ficewa da ita..... Innah na fincika take fad'in "Naseer na fad'a maka ka saki yarinyar nan wato shine ka ajiye ta a nan koh.... Wllhi ka shiga hankalinka idan ba baki kake so na maka ba...."
Zuciyar sa na masa wani irin zafi yaja burki ya tsaya.... Wani irin duba yake ma Innah... Idanunsa sun kad'a sunyi jazir sabida tsananin k'unci... Har ga Allah Ya gaji da kalamun Innah a gareshi.... A hankali ya soma furta "I'll never get tired of putting up with you.... But please don't curse me, I beg of you......" d'an fasali yaja har lokacin bai daina huci ba kafin yaci gaba da fad'in "Kince baki yarda na tare da ita a matsayin mata ba... Fine nayi yanda kike so na ajiyeta a wani wajen daban.. What else, me kuma kike so nayi... Mutuwa kike so nayi, kwanciyar hankali ne baki so ki ganni ciki.... What kind of parent are you..? Haba haba Innah don Allah ki dinga sauk'ak'a min I'm only human....."
Tausayin Naseer ya cika zukatan su babu kaman Salma yayinda Innah taji jikinta ya mata wani irin sanyi tamkar an tsundumata cikin k'ank'ara... Gaba d'aya kasa d'agowa tayi ta dubi Naseer, itakam abin yana damunta yanda yanzu lokaci guda take mugun shakkan Naseer d'in....
Hannayenta Naseer ya kamo kafin yace "Banso nayi maganar a wajen nan ba.... But you keep on pushing me, kiyi hak'uri Innah zamu k'arasa maganar a gida..." Bai jira cewan kowa ba ya shiga janyo hannun Innah wacce take jin hannun Naseer d'in tamkar garwashin wuta a cikin nata hannun dukda laushi da hannun kedashi.....
Cikin sauri Jamila ta k'araso ta rungume Salma yayinda Momy ta k'arasa ta kamo Ilham itama, babu mai iya furta komai cikin su.....
Jamila ta d'an runtse idanunta tunowa da tayi wannan matar zata iya zama kakar Fawaz tunda gashi ga dukkan alamu itace mahaifiyar Naseer.....
********
A tare suka shiga suka ga Daddy Azeema sai murmushi take yayinda Mamy ta cika tayi fam, itakam da da hali da ta tunkud'a Azeema kan kwalta mota tabi kanta.... A tare suka fito har gate d'in asibitin, Azeema ce kawai keyiwa Mamy hira yayinda Mamy bata ko iya amsawa da zaka sanya hannunka saman k'irjinta da ka jiyo bugu da k'irjin keyi tamkar ana sauk'e mata guduma...
"Mamy taxi zamu shige ko adaidaita...?" Azeema ta tambaya fuska d'auke da murmushi....
Tsaki Mamy tayi had'i da kauda kai gefe...
Azeema ta kuma murmusawa kana ta sassauta murya tace " Mamy are you still mad... Sabida na hanaki k'arasa Daddy....?"
Nan ma shiru Mamy bata amsa ta ba....
Azeema ta kuma murmusawa kafin tace "Mamy idan na barki kika k'arasa Daddy ni burina na mallakan d'anki Affan bazai cika ba.... Kar ki damu idan kin tsaya min na auri Affan ni kuma zan baki daman k'arasa sa ta hanya mafi sauk'i....." Ta k'arashe tana gyarawa Mamy mayafinta...
Mamy dai kasa tanka Azeema tayi ta shiga tare mai adaidaita...
Adaidaitan tana tsayuwa Mamy ta soma yunk'urin shiga Azeema na taimaka mata tamkar ta shak'e Azeema haka take ji.....
********
"Addah yaushe ne abubuwa zasu canza A DUNIYAR MU?..." Cewar Salma wacce kanta ke langab'e jikin 'yar uwar tata....
Shafa kanta Jamila ta kuma yi kafin tace "Duk tsanani na tare da sauk'i Salma, mu kuma kalan tamu jarabawar kenan A DUNIYAR MU... kullum cikin zullumi da tsoron fad'awa tashin hankali... Amma Allah bai mance damu ba da sannu sauk'i zai zo mana nan bada jimawa ba...." Ta k'arashe murmushi kwance saman fuskar ta...
Murmushi Salma ma tayi kafin ta rungume 'yar uwar tata tana fad'in "Ina sonku gaba d'aya Addah..."
Jamila ta share hawayen da suka d'an zubo mata kafin tace "Muma muna sonki Salma...."
Momy dake tsaye gefe a hankali ta juya tausayin su ya cika zuciyar ta...
*****
"Shareefah da alama bakiji gargad'in da na maki ba...." Affan ya fad'i yana dubanta..
Mugun kallo ta watsa masa had'i da zama cikin sofa kana tace "You know Affan.. You such an idiot... Kai da ya kamata mu had'a kai mu destroying wad'anda suka ci amanar mu amma da alama kai har ka mance.... Shiyasa na fad'a maka sam baka da wayo... Kowa amfanuwa kurum yake da kai..."
"Be careful with your language..." Ya fad'i fuska a dake.... Dai-dai lokacin Mamy da Azeema suka turo k'ofa suka shigo... Affan yayi saurin k'arasawa ga Mamy ganin kaman hawaye ne kwance cikin idanunta... Aiko Mamy kaman jira take yana k'arasowa ta rungume sa sosai ta shiga rusa kuka ko zataji sanyi cikin ranta...
Affan ya rungumeta sosai yanai ma Azeema kallon tuhuma, Shareefah ma kallon mamaki tabi Azeema dashi don a iya saninta basu fice tareda Azeema ba a gida suka barta...
"Me Ya faru..? Me ya sameta....?" A jere yayi ma Azeema tambayar..
Azeema ta d'an sauk'e ajiyan zuciya kana tace "Daga wajen Daddy muke.... Zuciyar Mamy ya kariya da yawa ganin yanda Daddy ke jin jiki.... Shiyasa taketa kuka don tun a cikin adaidaita nake lallashinta..."
Jikin Affan ya d'anyi sanyi.. Mamy kam kaidin Azeema ya soma daina bata tsoro saidai ma gani take kaman kamuwan Allah ne yake gab da kamata shiyasa Azeema tayi bak'e-bak'e a rayuwarta..
Lallashin Mamy ya soma yi yana sanar da ita Daddy zai sami lafiya da izinin Allah.. Sannan shima daga nan zai wuce ya dubasa... Shareefah kam bata ce komai ba sai tafarfasa da zuciyar ta ke faman yi... Sam bataso su Naseer su taddasu gidan Momy Lami ba sai Innah ta fatattake su a rayuwar d'anta Naseer... Ita abin ma mamaki yake bata yaya akayi su Naseer suka san sunje gidan.. Lokaci guda idanunta suka sauk'a kan Azeema dake faman murmushi....
*********
Bayan shud'ewar sati abubuwa sun soma lafawa musamman tsakanin Naseer da Affan... Sannan babu laifi yanzu kam Salma takan yarda su gaisa da Soja dukda bata wani saki dashi kaman a baya ba.... A b'angaren Jamila da Fawaz ba'a cewa komai soyayyar su kullum k'aruwa take duk da matsa mata da sakk'onni da Alh Kabeer keyi, bata amsawa saidai tayi deleting....
Tsaf Salma ta k'arashe shirinta cikin doguwar riga irinta larabawa wanda yake bak'i sid'ik sannan ta yane kanta da mayafin kayan.... Jamila ta sakar mata murmushi kana tace "Kinyi kyau matar Soja... Nidai don Allah idan kunje ki gayar min da Daddy... Ba don ba'a bari a shiga ba ai da na biku na duba jikin nasa, Daddy mutumin kirki ne.."
Salma ta d'an murmusa had'i da jinjina kai kana tace "Shiyasa nake son naje naga jikin nasa, insha Allah zan sanar dashi sak'on ku koda bazai amsa ni ba sannan da sannu zai sami lafiya da izinin Allah..."
Jamila ta jinjina kai tana mai gyara wa Salma mayafinta.... Salma dai kallon 'yar uwar tata kawai take tana murmushi tana tuna yanda Allah ya karkato masu da hankalin 'yar uwar su ta dawo garesu daga mummunar rayuwar da ta zab'ar ma kanta a baya.....
D'an Far da idanu Jamila ta mata kana tace "Wannan irin kallo saikace na zama Soja...?"
Salma ta d'an kuma murmusawa had'i da dungurin Jamila cikeda wasa kana tace "Kai Addah ai dai kece mai soyayya keda Dr Fawaz... Amma nida Soja ba soyayya muke ba, kuma da zaran Daddy Ya sami lafiya......." Shiru tayi ta kasa ci gaba da maganar nata..
Jamila ta murmusa don izuwa yanzu kowa ya fahimci kalan soyayyar da suke itada Fawaz....
A hankali ta dafa Salma kana ta d'anyi jim....
"Salma ina son Fawaz soyayya da ban tab'a yima wani d'a namiji ba... Dama ashe haka so take... Lallai kuwa idan haka ne tuntuni ban tab'a soyayya ba sai akan Fawaz...."
Ta k'arashe tana murmushi had'i da k'urama waje guda idanu....
Salma da jikinta ya d'anyi sanyi sabida duk abubuwan da Jamila ta fad'i tanaji ga Fawaz, toh kuwa shakka babu tana jin irinsu ma Soja.... Saurin mik'ewa tayi tana k'ok'arin yakishe tunanin. Dai-dai nan Momy ta shigo ta iske su ta sanar dasu zuwan Sojan....
A tare Salma da Jamila suka fito, hannunsu rik'e cikin na juna idanun Salma a k'asa...
Naseer na hangosu ya mik'e tsaye... A kullum idan ya ganta soyayyar ta na kuma shigar sa cikin tsanaki... Jamila ce ta soma gaidashi ya amsa cikin sakin fuska... Salma ma ta gaidashi cikin tsanaki a d'an tak'aice... Fuska d'auke da murmushi ya amsa lokaci guda yake binta da mayen kallo...
Momy ce ta k'araso tana fad'in "Captain da Allah a dai kula min da d'iyata da kyau..."
Naseer ya murmusa kana yace "Insha Allah Momy zan kula da ita fiye da yanda zan kula da kaina...." ya k'arashe idanun sa akan Salma... Daga Jamila har Momy murmushi suke soyayyar da Soja ke nunawa Salma cikin salo na burgesu... Har waje Momy ta masu rakiya yayinda Jamila ta koma ciki tana amsa wayar Fawaz..
Saida Momy taga tashin motar su kafin ta komo parlor ta zauna had'i da rapka tagumi, don tun bayan zuwan Innah gidan Momy ta rasa dalilin da yasa take ji a jikinta tamkar ba Innah ce ta haifi Naseer ba...
Akan idanunsa suka shige mota, abinda yafi k'ona masa rai shine Naseer harda wani bud'e wa Salma mota, wato irin ga sarauniyar birnin zuciyar sa... Kasa motsawa Affan yayi daga wajen zuciyar sa na masa wani irin zogi da rad'ad'i yau ya kamata ya ida bufin sa na tarwatsa farin cikin Salma da Naseer...
Momy ta gama shirinta tsaf kafin ta masu Jamila sallama ta wuce... Jamilar ma shirin fita take don Fawaz ya sanar da ita yana tafe zai zosa ya d'auketa suje ta gaida Mum d'insa, gashi Momy da Salma duk sun fice bata samu ta sanar dasu ba kuma bata so tayita kawo excuse ma Fawaz kar yaga tamkar bata damu da jinyar mahaifiyar sa bane....
Ta gama shirinta tsaf kafin ta matso kusan Ilham wacce keta faman wasa da Falaq, d'an dafata tayi kana tace "Ilham bazan jima ba yanzu zan dawo, ki kula da kanku keda Falaq kinji koh, idan kuma bazaku iya zama ku kad'ai ba sai na fasa tafiyar..."
Murmushi Ilham tayi kana tace "Haba dai Addah, Wllhi zamu iya zama, ai na saba zama daga ni sai Falaq kar ki damu kinji kije ki gaida Momin Doctor yanada kirki..."
Jamila ta murmusa cikeda jin dad'i ta shafi kan k'anwar tata kana ta rungumo su gaba d'aya harda Ilham d'in kafin tace "I love you...."
Ilham ta d'an kuma murmusawa kana tace "Muma muna sonki Addah.."
Rurin da wayarta ya soma alamun Fawaz ya iso yasata mik'ewa ta kuma masu sallama kafin ta fice....
*******
Daga yanda yake lab'e duk yaga ficewar su daga gidan, tun daga ficewar su Salma da Naseer da kuma ficewar Momy har izuwa ficewan Jamila da Fawaz.... Mik'ewa yayi yana wata kafirn murmushi.. A hankali ya furta "It's now or never...." cikin sauri Affan ya ciro k'ullin garin da yake yawo da ita kullum cikin aljihun sa kafin ya nufi gidan Momy....
*******
Gaba d'aya jinta take ba'a sake ba, ba wani amsa masa tad'in nasa take ba har suka iso Santana Corporation.... D'an dubanta yayi kana yace "Barin d'an karb'i aika sai mu wuce koh..." jinjina masa kai tayi had'i da k'ak'aro murmushin k'arfin hali kafin Naseer ya fice, sabida akwai wani bincike da yake yi gameda Yayan sa Kabeer...
*******
Ta gajeren garun bayan gidan Affan ya samu ya dirk'a cikin gidan... Ilham dake faman zura riga gabanta ya yanke ya fad'i, tasan dai babu yanda za'ayi b'aro ya shigo wannan bariki tunda akwai tsaro sosai tun daga gate... Saurin k'arasawa saman katifa tayi ta shafa Falaq dake kan faman barcinta, a hankali ta soma lalumen hanya tana tambayan wenene...?
Bai amsata ba sai zuba mata idanu da yayi.... Lokaci guda ya shiga tuno kalan cin amanar dasu Naseer suka masa, yanda ya rasa farin ciki haka suma bazasu zauna cikin farin ciki ba... Salma tana son 'yan uwanta fiye da komai, da ba don idan ya tafi dasu gaba d'aya harda jaririyar ba zata zame masa liability da ya tattare su gaba d'aya ya saka su cikin k'unci da tashin hankali....
Izuwa lokacin Ilham ta razana sosai , ganin tana k'ok'arin k'arasawa ta rufe k'ofa tana mai fad'in "Toh kodai kunnuwana ne... K'ila babu wanda ya dawo cikin su.... Bata kai aya ba saiji tayi ta bangaji mutum.... Tsoro ya kuma cikata lokaci guda.... K'ok'arin jada baya ta soma ba tareda ta iya furta koda kalma ba, sai tunanin Falaq da take... Saidai kafin tayi katab'us ya capkota lokaci guda ya danna mata 'yar tsummma mai d'auke da garin maganin a hanci... Sai k'ok'arin ihu take tana son k'watan kanta ta kasa.... Lokaci guda jikinta ya sake idanunta suka rufe ruf... Cikin sauri Affan ya sure ta ya fice da ita....
******
Kallon mutumin take kan faman yi don idan bata b'ata gani ba tabbas shine ta gani wanda suka cinna wuta ma gidan gonar Daddy daga bisani ya biyota zai kasheta.... Magana da wani mutumi ya soma ai kuwa ta fahimci muryar sa... Cikin sauri ta bud'e marfin motar ta fito tana dubansa sosai take fad'in "Wllhi shine... Wllhi ba kamanni bane... Shine..."
Mutanen dake kai komo cikin Kampanin suka soma dubanta tamkar mahaukaciya... Shi kuwa Maina tamkar ya saki zawo a wandonsa... A tamanin ya samu ya silale cikin mutane ganin da gaske Salma k'ok'arin nufosa take... Kan kace me mutane sun taru a wajen Salma bata daina kuka ba tana fad'in wllhi shine.... A birkice Naseer ya k'araso wajen had'i da rik'ota yana tambayarta "Salma, meke faruwa, wayene kika gani...?"
Share hawayen ta take da hannu bibbiyu tana girgiza kai take fad'in "Soja wllhi shine.. Wllhi na gansa yanzu a nan.. Shine ya biyo ni zai kasheni bayan Sun k'one gidan gonar..."
Gaban Naseer ya yanke ya fad'i saurin rungumeta yayi cikin k'irjin sa yana kwantar mata da hankali... Abun na neman juya masa tunani... Kenan Salma taga wanda ya k'ona gidan gonar Alh Ali a companyn mahaifin sa, wannan lamari akwai abun dubawa sosai ciki, toh ko kuma wata hidima ta kawo mutumin Kampanin...? Kwanyarsa ta cirke lokaci guda.. Ga kuka da Salma keyi tana fad'i. "Shine sanadiyan rabuwata da mahaifiyata har ta bar duniya.." tafiyan da basuyi ba kenan suka zauna k'asar wata rumfa tana nan rungume cikin jikinsa sai aikin lallashin ta yake...
*******
Tunda suka shigo gidan gabanta ke fad'uwa.. Bata sha mamakin ganin mahaifiyar Fawaz balarabiya ba sabida shid'inma haka yake sak Arabs.. Saidai ta tausaya mata sosai, ga Mace har Mace amma babu hankali... Tuni Falmata ta cika gaban Jamila da kayan motsa baki... Sosai Fawaz ya birgeta ganin yanda yake kula da mahaifiyar sa, sam bai damu ya nuna mahaifiyar sa ba dukda tana cikin jinyar tab'in hankali, lokaci guda ta kuma jinjinama hankali irin na Fawaz..
Fawaz ya d'an dubeta yanda take ta wani san-san da kai.. Murmushi yayi kana yace "Ki saki jikin ki Dad kam ma baya nan da kun gaisa..."
Jamila ta murmusa kana tace "Ai ni naji dad'i ma da baya nan don wllhi kunya nakeji.."
Fawaz ya murmusa kafin yace "Kar ki damu nida Dad d'ina tamkar abokai ne, I'm sure kema zai d'auke ki tamkar d'iya.." Ta d'an murmusa ba tareda tace komai ba...
"Whattt!! You're crazy Maina garin yaya ta ganka...?"
Ya kuma tambaya yana zura riga don fitowar sa kenan daga wanka...
Daga d'aya b'angaren Maina yace "Mai gida wllhi itada Naseer suka zo Kampanin.. Ni kaina bansan me ya kawo Naseer a daidai wannan lokaci ba, I'm afraid he might be spying on you..."
Alh Kabeer ya fuzar da iska yana furta "Damn it...!!! Maina you better get lost... Gani nan zuwa yanzun nan....Daga haka sauri-sauri ya k'arasa shirin sa ya nufo downstairs..
Jamila na bawa Aunty Saudat abinci a baki Fawaz na rik'e da plate d'in gwanin sha'awa idan ka gansu.... Dai-dai lokacin Alh Kabeer ke sauk'owa daga bene...
Cak ya tsaya yana hangesnu fuskokin su cikeda annuri... Bakinsa bai furta ba amma zuciyar sa ta furta masa "KITTY" kasa ci gaba da tafiya yayi sai bugu da k'irjinsa keyi.. Lokaci guda Fawaz ya d'ago yana duban mahiafin nasa.. Murmushi ya saki had'i da mik'ewa kafin ya nufesa yana fad'in "Dad I thought ka fice don banga motar ka ba...."
Jin ya ambaci Dad yasa Jamila d'agowa cikin sauri tana dubansu... Lokaci guda spoon d'in dake hannunta ya fad'i k'asa
0 comments:
Post a Comment