Kasa gasgata abinda ke shirin faruwa tayi.... A'a kodai kamanni ne... Kai badai Alhaji Kabeer bane baban Fawaz.... Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un... Shin dama Alh Kabeer shine mahaifin Fawaz...? Sai yanzu take tuna a asibiti tabbas taji ana kiran Fawaz Dr Santana, sai yanzu abubuwa da dama suka shiga dawowa kwanyar ta... Sam bata kawo haka ba sabida ko kad'an Fawaz baya kamada Alh Kabeer, kenan mahaifiyar sa ziryan ya d'auko.... Jiri na neman kada ita daga zaunen da take...
A b'angaren Alh Kabeer ma bai iya amsa Fawaz ba sai zufa dake faman keto masa ta ko ina.... Meke shirin faruwa... Mai ya kawo Kitty gidan shi.....? Yana cikin wannan tunani ya jiyo muryar Fawaz yana fad'in "Dad finally na kawo maka ita.... Ka k'araso ku gaisa..." murmushi kwance saman fuskar Fawaz ya shiga janyo hannun mahaifin nasa cikin parlorn....
Bibbiyu Alh Kabeer ya soma gani yayinda Jamila ke zaune a wajen tamkar wacce aka dasa, idan da za'a yanki naman jikinta bata tsammanin jini zai fito sabida tsaban yanda komai na jikinta ke neman d'aukewa, da za'a ce mata mafarki ne ba gaskiya ba da sai tafi son hakan.. Alh Kabeer abokin lalatan ta shine mahaifin saurayin da take so taci burin Aura.... Ya Allah kasa ba gaskiya bane. Allah kasa a farkar da ita daga wannan mummunar mafarki da take.... Kaman daga sama ta jiyo muryar Fawaz yana fad'in "Jamila ga Dad ya sauk'o ashe dai bai fice ba da rabon zaku gaisa...."
K'ak'aro murmushi tayi wanda yafi kama da yak'e ta shiga sunne kai tana k'ok'arin had'o kalaman da zatayi amfani dasu wajen gaisar da Daddyn Fawaz... Alh Kabeer kuwa zuciyar sa sai tururi take da k'yar yake iya amsa Jamila....
Fawaz ya d'an dubi mahaifin nasa yaga gaba d'aya tamkar baya hayyacin sa.... A hankali ya furta "Dad are you okay...?"
Alh Kabeer ya kuma murmusawa wanda hausawa ke kira da yak'e kai tsaye kafin yace "La.... Lafiya... Lafiya Son, eh.. Eh... Ba shakka ka zab'o Mace mai kunya gashi ta kasa d'ago kanta mu gaisa sosai..." Ya k'arashe yana mai ci gaba da murmushin...
Fawaz ya d'an murmusa kana yace "Ai Dad bamuma yi zaton zamu sameka gida ba don sosai take kunyar ka..."
_Yo dole taji kunyata ta bini ta kuma bi d'ana, abun sai ya mana yawa..._ cewar Alh Kabeer cikin zuciyar sa...
Aunty Saudat ce ta soma matsawa baya tunda taga Alh Kabeer ya sauk'o parlorn... Ta shiga murd'a 'yan yatsunta a hankali.. Lokaci guda ta rarumo throw pillows dake gefenta ta shiga wurgin Alh Kabeer dashi....
Kafin Fawaz ya cimmata Alh Kabeer ya cimmata ya rik'eta gam yana mai fad'i ma Fawaz... "Maza jeka ka kira Innah, kar ka damu kaji da bak'uwar ka mu zamu kula da ita.."
Cikin sauri Fawaz ya mik'e yana fad'in "Toh Daddy.." Saida ya d'an dubi Jamila kana yace "I'll be right back Jay...."
Bata sami zarafin amsa sa ba sai jinjina kai kurum da tayi....
Aiko tamkar wanda yake jira Fawaz na ficewa ya saki Aunty Saudat ya k'araso gaban Jamila dake k'ok'arin jada baya... Saidai kafin tayi wani katab'us tuni ya capkota....
Jamila da tuni jikinta ya soma rawa tamkar mazari, a hankali take furta "Dan Allah ka min rai ka sake ni kada Fawaz ya shigo ya same mu a haka..."
Murmushi ya sakar mata kafin yace "Kitty kin wahalar dani da yawa.... Na fad'a maki bazaki iya tseren mun ba... You are mine...." Bai jira cewanta ba ya matse fuskar ta Ya shiga kissing d'inta..
Lokaci guda ta hankad'ashi hawaye na kwararowa daga idanunta.... Cikin sauri ta mik'e ta suri jakkanta ta nufi k'ofa....
Ganin Aunty Saudat na k'ok'arin rarumo abu zata runtuma masa ya sa baibi bayan Jamila ba wacce tuni ta fice cikin tsananin tashin hankali.....
A tare Fawaz da Innah suka shigo, sosai Fawaz yayi mamakin rashin ganin Jamila da baiyi ba...
Kan mahaifiyar sa ya k'arasa yana k'ok'arin taimaka wa mahaifin nasa yake tambayar sa Jamila...
Babu ko kunya ya shiga tsara wa Fawaz k'arya...
"Wllhi Son taji tsoron mahaifiyar ka sosai ta tafi... Fawaz a ganina ka ajiye maganar aure a gefe har sai mahaifiyar ka ta sami lafiya.... Kaga a garin irin haka duk budurwar da ka samu zata gujeka, ka bari mahaifiyar ka ta sami lafiya first..."
Innah dai sai binsu da idanu take, a zuciyarta kuwa haushin Kabeer k'unshe ciki.. Ta yaya zai soma addu'an waraka ma Saudat.. Ai idan Saudat zata warke toh saidai a lahira...
Fawaz mik'ewa yayi da sauri yana fad'in "Daddy barin bi bayan ta, ni na kawota ni ya kamata na maidata...." Bai kai aya ba Aunty Saudat ta zube... Fawaz yayi saurin durk'usawa yana jijjiga mahaifiyar nasa, lokaci guda yake duban mahaifin nasa yana fad'in "Dad pls ka kira layin Likitan ta..."
"Yeah Son... Right a way..." Cikin sauri Alh Kabeer ya fice..
A d'ari ya fice daga gate d'in gidan sauri-sauri gudu-gudu yana neman hanyar da Jamila tabi...
Abinka da unguwa maras hayaniya sosai can ya hangeta sai sauri take tana neman abun hawa ga hawaye sharkaf idanunta... Kuka take tamkar ranta zai fice....
Cikin sauri ya cimma ta Ya shiga janyo hannunta...
Sosai take kuka tana k'ok'arin k'watan kanta take fad'in "Ka sake ni... Na tsane ka.. Na tsani sanin ka da nayi... Allah Ya isa shigowa rayuwata da kayi...." Bata kai aya ba ya d'auketa da wani wawan mari.... Fincikota yayi suka mak'ale cikin d'an wani lungu.... Yana wani irin huci yake dubanta kafin yace "How dare you... Just how dare you... Ta yaya zaki soma soyayya da d'ana my very own flesh and blood .... Kinyi hauka ne Jamila, ta yaya zaki soma soyayya da Fawaz..." ya k'arashe yana mai shak'e mata wuya jikin matsin garun...
Sosai take kuka tana girgiza masa kai.... Da k'yar ya sassauta rik'on da yayi mata jin numfashinta na neman d'aukewa...
Cikin karaji yaci gaba da fad'in "Kin san ina sonki, soyayyan da ban tab'a yima wata d'iya mace ba... Kitty meyasa kika barni... Ina tunani Kin barni ne sabida wani namiji daban, ashe sabida d'ana ne... You are in love with my son... Why? Why Kitty.... You know how much I love you.... You can't do this to me.... No you just can't.... Wllhi KE DA FAWAZ nafi k'aunar ku fiye da komai A DUNIYAR MU.... Kitty bazan iya rabuwa da d'ayanku ba..... Wllhi da inada hali da na kashe Fawaz har lahira sabida soyayyar da nake maki.. Alk'awari nayi duk mutumin da kika barni sabida shi Wllhi sai na kashe shi..... Meyas Fawaz Kitty... Why Him...." Ya k'arashe hawayen taurin rai na gangarowa daga idanun sa.... Lokacin guda ya soma k'ok'arin kai mata sumba... Cikin sauri ta kuma hankad'a sa gefe...
Hawaye suna ci gaba da kwaranya mata take fad'in "Na canza a lokacin da canji baimin amfani ba.... Na canza rayuwata sabida soyayyar da nake ma Fawaz... Wllhi Wllhi bansan Fawaz d'anka bane. Sabida ku d'in bakuda abu guda da ya had'aku ta hanyar hallaya ko kamanni.... Wllhi na tsaneka na tsani kaina... The last thing I want in this life shine nayi hurting Fawaz... Fawaz bai cancanci haka ba.... Fawaz yanada zuciya mai kyau... Wllhi ka cuce ni...."
"Shut up..! Shut the hell up..!! Ki daina fad'in kina son wani a gabana musamman Fawaz.... Kar ki sake kiran sunan d'ana... D'ana tsarkakakke ne bai cancanci mace irinki ba..... Wllhi Jamila kinji na rantse idan baki fita hanyar Fawaz ba..... I'll tell him everything.... Every single thing da mukayi between us... So ina shawartan ki.. Mu ci gaba daga yanda muka tsaya, idan ba haka ba zaki shiga k'unci mafi muni A DUNIYAR MU..." Ya k'arashe yana mai murmushi da gefen bakin sa lokaci guda yana wasa da 'yan yatsun hannun sa saman wuyar ta..."
Cikin sauri ta ture shi ta matsa gefe, tana wani irin huci take watsa masa kallon k'yama kafin tace "Ko babu Fawaz alk'awari nayi bazan koma rayuwar daduro ba... Na canza ma kaina har abada insha Allah... Da sannu zaka girbe abinda ka shuka..." Daga haka tayi saurin sa kai zata shige...
Saurin fincikota yayi ta kuma fad'owa jikin sa yana wani irin huci yake fad'in "Kitty idan kika ga na rabu dake toh wllhi mutuwa kikayi ko kuma ni ne na mutu... But as far as ina numfashi A DUNIYAR MU zan rayu dake.... Kuma kinji na rantse idan bakiyi hankali ba zan gayawa Fawaz who you really are...." Yana kaiwa aya ya zaro wayarsa cikin aljihu ya ciro wata sim ya saka ciki had'i da mik'a mata wayar lokaci guda kana yace "Oya take this... We keep on touch.."
K'in karb'a tayi sai kallon tsana da take watsa masa har lokacin hawaye na gangaro mata...
Murmushi yayi had'i da shafar hab'arsa wanda d'abi'ar sa ce kana ya finciko jakanta ya jefa wayar ciki yace "Wannan wayan just the two of us.. Mu biyu kawai nake so mu dinga magana da ita.... Jamila babban kuskuren da zakiyi shine kiyi tunanin guje min, don nasan idan kinada sauran kunya Fawaz kam ko idanu bazaki sake k'auna ku had'a ba...." Daga haka murmushin ya kuma yi da gefen bakin sa kafin ya huro mata kiss saman tafin hannun sa yace "I love you Kitty...." Daga haka juyawa yayi cikin sauri ya fice daga lungun....
Jamila da gaba d'aya duniyar ta shiga juye mata batasan sanda ta durk'usa saman gwiwoyinta a wajen ba ta shiga rusa wani irin kuka da bata san tanayi ba hannayen ta duka biyu aka....
*******
Kai tsaye gidan sa ya kaita don yasan idan ya fice da ita daga barikin a yau za'a sami error... Saman gadon d'akinsa ya kaita ya kwantar... Lokaci guda ya zauna saman bedside yana k'are mata kallo don har lokacin bata farfad'o ba, ya jima yana kallonta kafin ya mik'e ya shiga rufe duk wani window na d'akin... Saida ya rufe ko ina sannan ya kunna AC had'i da hura garin hodar cikin d'akin sabida ta kuma shak'a ta jima tana baccin... Daga haka ficewa yayi ya nufi ofishin su....
*****
Tambayoyi da dama gameda mutumin Naseer yayi mata kafin daga bisani ya umarci securities su saka idanu sosai idan sunga mutumi mai zubin bayanan da Salma tayi, daga bisani ne suka nufi asibiti wajen Daddy... Sosai Salma ta tausaya wa Daddy... Saida aka basu wani kaya irinta likitoci masu shiga theater room suka saka harta takalma saida aka basu wasu suka saka kafin suka shiga d'akin da Daddy ke kwance.. Sai sautin na'uran bature kawai kake jiyowa, idanun sa a lumshe ga na'ura mai taimakawa da numfashi na manne hancin sa... Allah sarki Daddy idan ka gansa dole ka tausaya masa...
Ganin Salma zata soma hawaye yasa Naseer matsowa daf da ita ya d'an kamo kafad'un ta Ya rungume.. A hankali ta d'ago kai tana duban sa... Murmushi ya d'an sakar mata lokaci guda yana mai girgiza kai alamun kada tayi kuka
Murmushin itama ta k'ak'aro tana mai jinjina kai domin kuwa duk sanda jikkunan su suka had'e waje guda yanayi ne maras fasaltuwa take tsintar kanta ciki....
******
Saida ta sha kukan ta mai isarta kafin ta ajiye wayar a k'asa ta d'auki dutse ta dinga dandatsa wayar da iyaka k'arfinta.. Saida tayi ruk'u-ruk'u da wayar Alh Kabeer kafin ta mik'e ta nemi adaidaita ta shige... Zuciyarta k'unshe da takaicin rayuwar da ta tsoma kanta ciki a baya...
*****
Mamaki ne ya cika Momy don tun daga waje take jiyo sautin kukan Falaq..... A tamanin Momy ta tura k'ofar gidan ta shige cikin Saudi.... Wani kayan mamakin shine ganin Falaq da tayi ita kad'ai a d'aki zaune saman katifa sai faman calla kuka take harda shan zuciya alamun taci kuka... Cikin sauri Momy ta k'arasa ta d'auketa had'i da d'orata saman kafad'arta tana lallashi "Yi shiru abinki Baby na.. Suka barki ke kad'ai a d'aki ko zasu zo su sameni ne..." Ta k'arashe tana kuma jijjiga Falaq d'in. . Kira Momy ta shiga doka ma Jamila da Ilham amma bata jiyo muryar ko mutum d'aya da sunan amsawa ba .. Ah'ah ta dai san sanda zata fice aiki ta bar Jamila da Ilham a gida.. Amma ko bayi ne bazau shige su duka biyu ba dole d'aya ta zauna da Ilham...
"Toh ko dai fitane sukayi...?" ta tambayi kanta a fili... Batakai ga samo amsar tambayar ta ba ta jiyo k'aran tura k'ofa.. Cikin sauri ta nufo parlorn...
Yanayin da taga Jamilar ciki ya sanya jikinta yin sanyi.... Kafin ta sami zarafin tambayar ta ko lafiya... Jamila ta zube jikin Momy tana kuka da duka zuciyarta..
Jikin Momy yayi sanyi da ganin irin kukan da Jamila keyi tamkar wacce aka mata mutuwa....... Tun tana lallashinta tana tambayar ta me ya faru har dai ta k'are ta zubawa sarautar Allah idanu, shab sai ta mance da batun rashin ganin Ilham da batayi ba....
A daidai Maiduguri bypass dab da Awala Hotel motar su ta tsaya suna hanyarsu ta komawa Air Force base, dama garin tayi bak'ik'irin sabida hadari da ya rufe ko ina... Mutane sai gudu suke suna neman mafaka, sosai hadarin ya had'e garin... Kan kace me ruwa ya kece tamkar da bakin k'warya... Lokaci guda aka soma iska mai k'arfin gaske hankulan mutane suka kuma tashi masu abin hawa parking suke su nemi wajem fakewa... Gaba d'aya tsoro ya cika Salma dan wannan ruwa da iska bata tab'a ganin irinsa ba... Hankalin Naseer ya tashi sosai ganin yanda firgici da tsoro ya nuna a fuskar ta... Kan ya sami zarafin magana saiji sukayi pole d'in wuta dake gefen su ya fad'i da k'arfin gaske.... Aiko nan Salma ta saki k'ara batasan sanda ta fad'a jikin Naseer ba.... Aiko yayi saurin rufeta da k'irjinsa yana karanto innalillahi.. Lokaci guda ya d'auki duk wani abin da zai d'aukana motar kafin ya bud'e masu yana ce da ita maza su fice..
"Soja ina zamuje...?" ta tambaya murya na rawa..
Jacket d'insa na Camo dake ajiye bayar motar ya d'auka ya rufa mata kana yace "Zaman mu a nan had'arine Salma, zamu nemi wajen fakewa ne.."
Salma na k'ank'ame jikinsa suka nufi cikin hotel d'in
*Sameena ce...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*42*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
"Jamila kukan nan ya isa haka don Allah... Ki min bayani wai meke faruwa ne...?" cewar Momy wacce gaba d'aya damuwa ya nuna a fuskar ta...
Bayan hannu tasa tana share hawayen cikin kuka take fad'in "Momy rayuwar ce kawai na tsana.. Momy wllhi na tsani wannan rayuwar wllhi mutuwa ya fiye mun alkhair....."
Bata kai aya ba Momy tayi saurin sa hannu had'i da toshe bakinta cikin tsananin tashin hankali Momy ke fad'in "Kul Jamila kar na sake jin makamanciyar wannan magana a bakin ki.... Kinsan kuwa haramun ne bawa ya dinga addu'an yankewar rayuwa ma kansa... Ko me ya sami bawa ya fawwala wa ubangiji lamarin sa ba ya dinga fad'in duk kalman da yazo bakin sa ba.... Ko wani irin rayuwa ka tsinci kanka ciki A DUNIYAR MU toh kuwa babu shakka jarabawa ne daga mahaliccin mu, walau na jin dad'i ko na akasin sa..... Fad'a min meke faruwa...?"
Maimakon ta amsa mata tambayarta sai kuma k'ara tuntsurewa da wani irin kuka tayi, i zuwa lokacin zuciyar Momy ta karaya... Ilham ce kawai ta fad'o ranta... Cikin murya mai cikeda tashin hankali take fad'in "Jamila Ilham ce.. Ina Ilham, me ya sameta.. Fad'a min ina take....? "
Dubanta Jamila take shaye da mamaki tamkar wacce aka sinkaya ta mik'e a tamanin ta shiga duba lungu da sak'o na gidan.... Lokaci guda Momy ta take mata baya...
Duban Momy take still hawaye na gangaro mata kana tace "Momy ina Ilham...?"
Momy ma da mamaki take duban Jamilar kana ta soma girgiza kai tana fad'in "Jamila ke zan tambaya Ilham domin kuwa tare na barku, sanda na dawo gida daga Clinic ban tadda kowa cikin gidan nan ba sai Falaq.... Ba tare kuka fice ba.... "
Ai Momy bata kai aya ba Jamila ta soma ganin jiwa na neman kada ita.... Murya har na rawa take fad'in "A.... A... A'a Momy ba tareda ita na fita ba.... Na barsu a gida itada Falaq.... Wllhi... Wllhi tare na barsu itada Falaq... Nasan bazata fita ta bar Falaq ita kad'ai ba mu duba ko ina...."
Cikin sauri Momy ta aza Falaq a baya ga ruwa da ake tamkar da bakin k'warya ba don haka ba da tuni ta fice gate.... K'arshe dai sauk'e Falaq tayi ta mik'awa Jamila tana fad'in "Barin tambayo masu tsaron gate ko sunga ficewar ta...." Jamila kam inaa bata sami zarafin amsata ba sai faman bud'e bud'en k'ofa take tana kiran sunan Ilham....
*******
An jima ana ruwan domin har izuwa wannan lokaci ruwan ake kan faman shek'awa.... Tari Ilham ta soma yi tana k'ok'arin mik'ewa saiji tayi hannayenta da k'afafunta a d'aure... Ta kuma jijjiga tana k'ok'arin neman hanya tsira inaa ji tayi ko gizau ta kasa da d'aurin da aka mata.... Lokaci guda abunda ya faru ya shiga dawowa kwanyar ta... Batasan sanda ta saki kuka lokaci guda ba.... A tamanin Affan ya nufo d'akin yana watsa mata mugun kallo... Lokaci guda ya d'auketa da wani wawan mari cikin yanayi na canza murya dukda baya tunanin zata iya fahimtar muryarsa ya soma fad'in "Ki min shiru shegiya makauniya kawai...."
Ilham da marin ya shigeta sosai don har shatin yatsun Affan sun fito a fuskar ta girgiza kai take tana dad'a bud'e idanunta masu zuban hawaye take fad'in "Wanene kai... Dan Allah waye kai.. Me nayi maka bawan Allah... Dan Allah kaji tausayi na kada ka cutar dani...."
Maimakon taji maganar sa sai sauk'an rank'washi dataji a tsakar kanta lokaci guda taji ya soma d'aure mata baki da wani tsummar.... Kokawa take k'ok'arin yi dashi amma ta kasa dukda rawa da jikinta keyi.... Saida ya rufe mata baki da wata tsumma kafin ya zauna can nesa da ita yana dubanta yanda take kuka sosai tana mai son yin magana ko ihu...
Murmushi Affan yayi lokaci guda yana tuna kalan damuwar da Salma zata shiga idan ta fahimci ta rasa 'yar uwarta daga nan yasan Naseer ya rasa kwanciyar hankali sun rasa farin ciki... Cikin ransa yake furta _I'm gonna make your lives impossible A DUNIYAR MU..._
Har lokacin da muryar da ba tasa ba yake ci gaba da fad'in "Idan baki min shiru ba sai na k'arashe fashe gwala-gwalan idanunki nan na kuma maidaki makauniyar gaske...." ya k'arashe yana mai k'ura mata idanu...
Lokaci guda yaji tayi shiru ta daina k'ok'arin ihun da take sai shan zuciya take har lokacin idanun ta suna zuban hawaye....
Affan ya k'ura ma k'wayar idanunta idanu wanda taketa faman juyasu hawaye na ci gaba da kwarara.... Daga nan mik'ewa yayi ya fice daga d'akin ya dawo parlor had'i da kunna TV, hankali kwance ya kwanta bisa doguwar kujera yana kallon sa....
Ilham kuwa sai da ta firgita jin k'arar rufe k'ofa da akayi,, ta kuma tak'urewa jikin garu... Sai faman k'ok'arin murza hannayen ta take cikin d'aurin da ya mata, hannuwan sunyi layin rod'in ja alamun jini ya taru wajen...
Jin ta kasa b'alla d'aurin ya sanyata zubewa wajen tana mai ci gaba da zuban hawaye, tunanin 'yan uwanta ya cika mata zuciya lokaci guda ta shiga jero duk addu'o'in da suka zo zuciyarta....
********
Sun jima suna zaune a reception, Salma ta tak'ure cikin jacket d'in Naseer shi kuwa sai faman murza hannayen sa yake sabida sanyi da ya sauk'a a garin lokaci guda.... Lokaci zuwa lokaci yake mik'ewa ya lek'a window ko ruwan ya tsaya dukda suna iya jiyo k'aran zuban ruwan alamun ba mai tsayawa nan kusa bane.... Ga Magrib ta sako kai, gaba d'aya hankalin Naseer bai kwanta ba ganin yanda gaba d'aya Salma ta tak'ure waje guda, tsoro ya bayyana sosai a tattare da ita, yasan ma duk yanda akayi ta soma jin yunwa.... D'an k'arasowa kusanta yayi yana dubanta kaman bazai ce komai ba sai kuma ya zauna dab da ita... Murya can k'asa ya soma fad'in "Are you hungry....?"
Girgiza masa kai tayi hawaye na neman zubo mata don gaba d'aya tunda aka soma ruwan nan tunanin 'yan uwanta ya addabeta don gaba d'aya gani take kaman wani abu ya same su, ji tayi kawai su take son gani....
Murya tamkar zata kurma ihu tace dashi "Soja nidai gida nake son zuwa....."
Naseer ya d'an shafi sumar sa wanda har lokacin da damshin ruwa a ciki had'i da d'an fuzar da iska kana ya d'an muskuta ya zaro wayar sa a pant pocket d'insa yana mai fad'in "Ki kwantar da hankalin ki barin kira azo a d'auke m...." Burki yayi da maganar nasa ganin wayar tasa ta riga ta mutu babu chaji...
"Ya Salaam..!!" ya furta a hankali...
A d'an razane take dubansa kafin tace "Soja lafiya...?"
K'ak'aro murmushi yayi kana yace "Lafia lou.. Wayar ce ta mutu ashe babu chaji... Kin gane bari na tambayi receptionists d'in nan ko zan samu a waj....."
Bai kai aya ba Salma ta katse sa da fad'in "A'a Soja nidai ban so ka tambayi wad'an nan 'yan matan waya... Kawai mu jira dai a ida ruwan sai mu tafi....."
Kallon mamaki Naseer ke binta dashi... Me hakan yake nufi..? Wai Salma bata so ya ari wayan 'yan matan dake aiki a otel d'in... D'an murmushi yayi da gefen bakin sa don haka kurum yaji zuciyar sa na masa wani irin sanyi... D'an shafa sumar sa yayi yana mai tunanin maganar nata...
Ganin ya mata k'uri yasara jin kunya.... A hankali ta sadda kanta k'asa.... Lokaci guda ruwan ya kuma kecewa tamkar da bakin k'warya, sai k'aran tashin rufin kwanu da kake iya jiyowa daga gari had'i da fad'uwan bishiyoyi... Koda ya sami waya ma zaiyi wuya su iya fita su hau kwalta a wannan ruwa da iska wanda yake tamkar disaster..
Agogon hannun sa ya duba bakwai saura gashi ko magarib basuyi ba.... D'an dubanta yayi yanda ta toshe kunnuwan ta gaba d'aya ta cusa kai cikin jacket d'in.... A hankali ya d'an rank'wafo dab da ita, sabida k'aran ruwa dake zuba yasan bazata jisa ba idan yayi magana daga nesa... Saitin kunnenta ya duk'a yana fad'in.
"Would it be OK idan muka samu mafaka da yafi wanda muke ciki a yanzu...."
Saurin d'ago idanu tayi sai kuma taga fuskar sa dab nata... K'irjinta yayi wani irin bugawa... A hankali ta sauk'e kanta k'asa ba tareda ta iya furta komai ba....
Hannu yasa ya d'an d'ago fuskar ta kad'an kana yace "I'll be right back...." Bai jira cewarta ba ya nufi receptionists d'in.... Salma ta bisa da kallo k'irjinta na faman lugude lokaci guda...
Bayan shud'ewar wasu dak'ik'ai Naseer ya dawo yanda ya barta hannunsa rik'e da Key....
Hannu yasa ya d'au handbag d'inta kafin yace "Taso muje kiyi sallah ki canza jik'akk'un kayan nan...."
Ai Salma a d'ari ta zaro idanuwa tana dubansa lokaci guda tace "Na'am... Iye....." Sai faman muzurai take..
Murmushi Naseer ya d'anyi kafin yace "Ko na soma gaba zaki cimma ni...." ya k'arashe cikin sigan wasa...
Ga k'asar rigarta har d'iga yake.... Tamkar wacce aka dasa haka tayi zaune a wajen.... D'an murmusawa ya kuma yi kafin yace "Kinga taso muje, you might catch cold idan kika zauna da kayan jikin nan naki....."
Tamkar wacce ruwa ya shanye haka ta mik'e ta soma bin bayansa receptionists d'in kuwa sai kallon su suke..... Salma kam gaba d'aya sai ta tsargu gani take kaman kallon 'yar iska ake mata tunda nan ai hotel ne.....
Second floor d'akin yake, tas-tas dashi ko ina a gyare..... Kasa shiga tayi har Naseer ya shige tana nan tsaye bakin k'ofa....
Karkatowa yayi yana dubanta yanda take faman raba idanu....
"Salma shigo mana..." ya fad'i yana cire agogon hannun sa...
"Soja nidai tsoron d'akin hotel nake ana ruwan sama kada tsawa ya fad'o min....." ta fad'i tana kuma ware idanu...
Sosai tabawa Naseer dariya saidai baiyi dariyar ba sai ko d'an tak'aitacce...
"Kar ki damu ke ai ba sab'o kike ba tsawa bazai fad'o maki ba, maza shigo abinki...." ya fad'i yana mai ci gaba da abinda yake...
Har ta shigo cikin d'akin sai kuma tayi tsaye sororo a tsakiyar d'akin... Naseer ya kuma d'agowa yana dubanta...
"Salma are you OK..? " Ya tambaya yana mai mik'ewa tsaye sosai...
Murmushin yak'e tayi kana ta d'an gyara tsayuwar ta tace "I thought zaka fice ne.....?"
D'an zaro idanuwar sa yayi waje kana ya d'an langab'e kai yace "Salma na fice kuma ..... Bazaki ara min d'akin naki ba nima na fake....?"
Kunyar sa da taji ne ya sanyata sunkuyar da kai k'asa... Naseer kuwa kallonta kawai yake yana murmushi kafin ya nufi toilet don d'auro alwala...
"Wayyo Soja wllhi kunyar ka nakeji....." Ta fad'i a hankali kafin ta tak'ure can k'arshen d'akin... Tana kalkonsa har ya fito daga bayin hannun rigarsa a nad'e kwantantun sumar da suke a hannayen sa sun kwanta luf... Hasken fatar sa ya fito sosai... Gabanta ya yanke ya fad'i
Warware hannun rigar yake ba tareda ya dubeta ba yace "Zan sauk'a k'asa nayi sallah, ki shiga kema kiyi alwala zan kawo maki riga ki canza sabida kar sanyi ya kama ki...."
Har ya fice Salma bata dawo dai-dai ba... Chab lallai ma Soja... Itace zata cire kaya a d'akin hotel saikace arniya.. Ai wllhi saidai uwar mura ya kamata... Ta fad'i cikin zuciyar ta lokaci guda ta mik'e ta cire jacket d'in ta jingine masa a wata hanger kafin ta nufi bathroom don d'auro alwala.....
*******
Ta window d'in gidansa yake lek'en su Momy Lami tare da wasu sojoji suna jinjina lamarin... A tamanin ya mik'e ya lek'a d'akin da Ilham take... Har lokacin tana nan kwance saman carpet hawayen idanunta har sun bushe... Murmushi Affan yayi kafin ya janyo k'ofar ya rufe....
Window ya kuma komawa yana lek'en su Momy wannan karan harda Jamila, suna tsaye cikin lema da alama basu ko jin ruwan da ake don k'iris ya rage bai d'agasu sama ba harda lemar tasu... Sojojin kuwa suna sanye cikin rigunan ruwa rik'e da manyan tocila a hannayen su duka hasken wutan lantarki da ya gauraye barikin...
Ganin sun nufo hanyar gidansa yasa sa saurin mik'ewa had'i da kintsa kansa... Likaci guda ya kunna talabijin sai ka rantse kallo yake da gaske... Yana sauraren sanda suka soma masa knocking
******
Hankalin Fawaz idan yayi dubu ya tashi, ya kira layin Jamila yafi abinda yafi bata d'aga ba, gashi sai zabga ruwa ake babu k'akk'autawa, ji yake bazai iya barci baiji dalilin tafiyar ta bayan suna zaune lafiya-lafiya tamkar wanda aka sinkaya sai mik'ewa yayi ya zari car keys d'insa...
Dad d'insa na parlor shima tunanin lamarin yake sai ganin Fawaz yayi ya fito a birkice
A tamanin Kabeer ya mik'e yana bin Fawaz da ta mujiya...
"Son ina zaka a ruwan nan...?" ya tambaya idanunsa k'yam kan Fawaz d'in...
"Daddy bata d'aga wayata gashi ta tafi ko sallama bamuyi ba...."
Kallonsa Alh Kabeer keyi babu ko k'yafta idanu kafin ya mik'e ya k'araso dab da Fawaz d'in d'an dafasa yayi lokaci guda ya jawo hannun sa suka zauna cikin parlorn....
"Fawaz na fad'a maka zaiyi wuya ka sami macen da zata soka tsakani da Allah alhali tana sane da lalurar mahaifiyar ka... Bakasan mutane da sharri ba koh.. Wasu har ce mata zasuyi muddin ta auri d'an mahaukaciya toh 'ya'yanta zasuyo gadon hauka.... Son zaiyi matuk'ar wahala ka sami mai sonka tsakani da Allah A DUNIYAR MU..."
Girgiza kai Fawaz keyi yana mai duban mahaufin nasa yake fad'in "Daddy wllhi Jamila ba haka take ba... Zan iya baka shaidar cewa bata d'aya daga cikin irin wad'an nan matan... Dad ina son Jamila soyayyar da bazan iya rabuwa da ita ba... Ina sonta with all my heart..."
Wani mugun miyau Alh Kabeer ya had'iya ba tareda ya iya furta koda kalma ba sai gumi dake neman tsartsafo masa dukda sanyi dake kad'awa cikin garin...
******
Cike da tashin hankali Affan ke dubansu kafin ya shiga girgiza kai lokaci guda ya shiga masife Sojojin...
"Wani irin rashin hankali ne har za'a fice da mutum baku sani ba... Barci kuke ko menene.. Ko kuwa searching motoci masu shige da fice ne bakuyi... Goodness bakuma san aikin ku ba... Wllhi yarinyar nan ta b'ace zaku iya fuskantat hukunci mafi tsauri tunda kunsan dokar.."
Cikeda rusunawa guda d'aya yace "Sir Wllhi a iya sanin mu dai-dai wannan lokacin da suka ce ba'a ganta ba babu Wata bak'uwar mota data shigo barikin nan.. Hasalima yarinyar nan makauniya ce babu yanda za'ayi ta fice ita kad'ai... Kuma wllhi yau bamu sha komai ko karan sigari balle ace hankulan mu basa jikin mu, right Soja..."
Ya k'arashe yana mai duban na gefen sa...
Jinjina kai shima yayi kana yace "Iyakacin gaskiyar kenan Sir, saidai kuma idan ta fad'a wani wajen ba'a sani ba.. Ko ruwa ya tafi da ita ko kuma ta apka wani wajen...."
Bai kai aya ba Jamila dake kuka sosai ta shiga girgiza kai tana fad'in "Wllhi 'yar uwata bata mutu ba... Affan don Allah ka kira Naseer mun kirasa yafi abinda yafi wayar sa bata shiga...."
K'uri Affan ya mata kafin ya d'an sassauta murya yace "Kar ki damu insha Allah za'a sameta, zamu duba cikin barikin nan sosai sabida babu yanda za'ayi ace ya fice... Kinga kalan yanayin ruwan da akayi yau.. Ya fad'ar da gininnka ya kuma d'aye rufin kwano...So komai ka iya faruwa musamman da shike ba gani take ba... Amma ku kwantar da hankalin ku yanzu zamu fita da sojoji a shiga searching gaba d'aya barikin kunji koh..."
A hankali Jamila ta gyad'a kai Momy na rungume da Falaq tama kasa fad'in komai .... Affan ya d'an k'araso kusan Momy kana yace "Momy kuje gida pls insha Allah zamuyi komai kada ku d'aga hankulan ku..."
Momy ma dai jinjina masa kai kurum tayi kana tace "Shikenan Affan Allah Ya taimaka, amma kam abin akwai ban mamaki...." rik'o hannu Jamila tayi suka nufi hanyar gida yayinda Affan ya kad'a kan soji guda biyun yana mai fad'i ma guda d'aya yaje Ya had'o masa kansu....
*******
Cikin sand'a ta kuma lek'owa wannan karan leda ta hanga saman gadon gefe kuma riga ce ta soji kalan kakin su na Sojin sama, blue da kuma ash.... Saida ta tabbata baya d'akin kafin ta fito a tamanin ta d'auki rigar ta kuma komawa bathroom ta saka... Rigar ta sauk'o mata har kusa gwiwa... Abayarta da take ta faman bugewa taji ta d'an sha.. Sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin ta d'aura abayar a sama, at least zata d'an ji d'umi tunda ta canza 'yar rigar dake cikin abayar nata...
Ba don ta fahimci gabas d'in ba ta fuskanci yanda take tunanin zai iya zama alk'ibla ta tada sallar ta... Magrib da isha tayi don already lokaci yayi... Tana zaune tana lazimi taji an turo k'ofar an shigo... Yanda kasan b'arauniya haka ta mik'e zunbur tana raba idanu... Shikam Naseer wannan tsoro nata dariya yake basa... Leda ce a hannunsa wanda basai ance maka abinci bane cikin ta....
"Kinyi sallar...?" ya tambaya yana ajiye ledar saman carpet...
Cikin sauri ta shiga jinjina masa kai alamun eh...
"Toh ina kika kalla, I mean alk'ibla...?" ya kuma tambaya sanda yake zama saman chaise lounge
Kai tsaye ta shiga nuna masa direction d'in da ta kalla da hannunta ba tareda tayi magana ba...
Naseer ya d'an kuma murmusawa kana yace "Masha Allah kin kalli dai-dai kuwa.... Wait ya naji maganar ki ya d'auke, ko amsa ni baki son yi...?" idanunsa k'uri akanta...
Nan ma batace komai ba sai murza 'yan yatsun hannunta da take yi...
Zaman sa ya kuma gyarwa cikin zuciyar sa yana fad'in _yanzu zan saka ki maganar dole yarinya.._ A fili yace
"Zo naji rigar naki koda sauran jik'a kika kuma sakawa"
A d'ari ta d'ago idanu tana dubansa lokaci guda tace "Na'am"
"Ok ashe dai maganar naki bai d'auke ba... Maza zo naji damshin rigar naki..." ya k'arashe fuskar sa babu alamun wasa..
Twisting yatsunta take kan faman yi lokaci guda ta soma murmushi wanda yafi kama da yak'e kana tace "Aima ya bushe Soja, ka gani fah...." ta k'arashe tana kuma bubbuge rigar...
Naseer dai murmusawa yayi ganin duk ta rud'e lokaci guda ya mik'e ya tako yanda take tsaye..
Shafa rigar ya shiga yi lokaci guda Salma ta runtse idanunta k'irjinta sai faman bugu yake tamkar ta runtuma ihu...
K'unshe dariyar sa ya d'inga yi ganin yanda ta runtse idanunta... A hankali ya matso da bakinsa saitin kunnun ta tamkar mai rad'a yake fad'in "Eh ya bushe amma da sauran danshi..... Rigar nan zata sanya ki mura, ina d'aya rigar da na kawo nace maki ki saka...?"
Murya can k'asan mak'oshi tace "Soja wllhi nidai bazai sakani mura ba, kuma ma ai na saka wancan rigar ma.... Nidai don Allah mu tafi gida kaga an ida ruwan...."
"Ban gane Kin saka ba... Sai kuma kika sake d'aura jik'akk'en rigar akai....?" ya tambaya yana dubanta..
"Soja don Allah mu tafi gida..." amsar da ta basa kenan idanunta na k'ok'arin rau-rau...
Hannunta ya kamo suka zauna saman chaise lounge kana yace "Amma don baki fita kinga sabon hadarin dake had'uwa bane koh... Kuma kinga na rasa masu gyaran mota, ruwan nan yayi gyara sosai ko nace yayi b'arna.... In fact ko masu motar haya baki gani a waje...."
Baki a ture idanunta na k'ok'arin kawo ruwa take fad'in "Does that mean bazamu tafi gida ba kenan....?"
D'an matsowa dab da ita yayi lokaci guda ya sanya hannun sa ya kewaye kafad'arsa dashi ta d'an shigo cikin jikinsa kana ya soma fad'in "Kiyi hak'uri kinji na saka wayata a caji da zaran tayi caji zanyi waya azo a d'auke mu... Kar kiyi kuka kinji.... _REINA_...."
Dukda bata fahimci mai ya fad'i a kalaman sa na k'arshe ba amma kam ta fahimci kaman wani suna ne ya kirata dashi..
"Reina.." ta maimaita a fili kana tace "Me hakan yake nufi?"
D'an murmusawa yayi kafin yace "Ki bini bashi next time zan fad'a maki..."
A hankali ta samu kanta da gyad'a masa kai tana mai k'ok'arin maida hawayen ta.... Mik'ewa Naseer yayi ya d'auko ledar da ya shigo dashi, take away na abinci ne nan ya baza masu saman carpet d'in ya d'ago kai yana dubanta kana yace "Oya let's eat., ko kuma kinfi so nazo wajen na baki a baki....." ya k'arashe cikin sigan wasa..
Murmushi kawai tayi tana mai dubansa yanda barkwanci ke bala'in masa kyau.... Lokaci guda take jin abubuwa da dama gameda shi... A hankali ta mik'e ta sauk'o saman carpet d'in....
"Ehen ina jinki bani labarin garinku...." ya k'arashe yana gyara mata zaman spoon d'in cikin pack d'in..
Saida ta murmusa kana tace "Labarin garin mu..?"
Naseer ya jinjina kai kana yace "I want to know more about you.... Nima idan kin gama bani sai na baki wasu daga cikin labaruna da baki sani ba.... Amma nafi so ki fara min da labarin samarukan ki don nasan kafin Affan kinyi wasu...." Ya k'arashe idanunsa naga wani gefen daban...
D'an sanyi jikin Salma yayi kana ta d'an turo baki tace "Chabb ai niko a garin mu banida saurayi duk tsoro na suke sabida fad'ata... Harta Addah Jamila nike karb'a mata fad'a....."
Dariya Naseer keyi maras sauti har saida jijiyoyin goshinsa suka d'an firfito yana k'ok'arin saita kansa yake fad'in "Kice ke boss ce babu mai maki wargi... Allah sa dai baki dambatuwa dasu...."
D'an kunyar sa taji lokaci guda ta murmusa kana tace "Ai a baki ne kawai, idan Baffah ko Inno sukaji nayi fad'a zan fuskanci fushinsu, don Inno ta sanar damu duk Mace mai wasa da maza kariya ce... Amma fah 'yan mata tsararraki na dukan yarinya nake idan ta min ba daidai ba, wacce ta fini kuma na saka mata tarko ta apka ciki...."
Naseer bud'e idanunsa yayi sosai yana dubanta murmushin bata gushe saman fuskar sa ba yake fad'in "Wato shiyasa kika sanyawa Shareefah b'awon ayaba a hanya koh....?"
Salma ta kuma murmusawa kana ta sadda kanta k'asa... Ambato Shareefah da yayi yasa ta jin wani iri sannan lokaci guda ta tuna bak'in sab'on da Shareefah ke aikatawa wanda da ace zata iya sanar da Soja da tuni ta sanar dashi, gani take har kwanan gobe Soja Shareefah yake so, tasan bazai tab'a sonta ba...
Ganin tayi shiru yasa Naseer d'an k'ura mata idanu lokaci guda yana karantar ta...
Gyara zamansa ya kumayi kafin yace "Kici abinci kada ya huce..."
Mak'e masa kafad'u tayi
"Why..?" ya tambaya yana dubanta
"Nima sai ka bani labari..." ta fad'i tana duban wani gefen daban
Naseer ya d'an murmusa kana yace "OK Reina kar kiyi fushi, don dai bada labari ai bazai had'a fad'a ba...
"OK, ni ban zauna a gidanmu sosai ba yawanci rayuwata a makaranta nayi shi... That's why ban shak'u da mutane sosai ba.. Hasalima ada tsoron mutanen nake ji bana shiga hidiman kowa, Lubna da Fawaz su biyu ne mutanen da nasan ina zama dasu suka dariyata... Sud'inma ya samo asali ne tun suna yara sabida Allah yayini mutum mai k'aunar yara.... Idan na dawo hutu daga sch toh kullum ina tareda su..." Shiru yayi kaman bazai ci gaba da magana ba sai kuma ya d'an murmusa kana yaci gaba da fad'in "Ina son Abbah na sosai.... Sannan nayi kukan rashin shi sabida shine mutum na uku da zan iya cewa na shak'u dashi sosai a wancan lokacin... Sam ni ban shak'u da mahaifiyata ba hasalima tafi shak'uwa da Yaya na Kabeer..." fasali ya d'an ja lokaci guda idanunsa suka kad'a sukayi jazir... Jikin Salma yayi sanyi..
Naseer ya d'an murmusa kafin yaci gaba da fad'in "Back then sanda nake k'arami, nakan d'auki lamarin sabida banbancin launin fata da nake dashi da mahaifiyata shiyasa take nunawa a fili tafi son d'an uwana mai launin fatar ta.. Musamman da na lura mahaifin mu yafi jana a jikin sa sai tunanina ya kuma bani k'ila duk wanda kuka zo kala d'aya zaifi sonka ne da kuma nuna maka k'auna.... Bazan mance ba akwai lokutan da nake daka gawayi na shafe jikina dashi ko mahaifiyar mu zata soni.. Amma ina babu abinda yake canzawa... Da na lura tana k'aunar Lubna sai na amince ma kaina tawa k'addarar kenan A DUNIYAR MU bazan sami wannan soyayyar uwa da ake fad'i ba... But you know I still love her, and I'll keep on praying for her. Sabida nasan ko bata nuna min tana sona ba deep inside tanayi sabida bazaka haifi d'a ka k'isa ba ko yaya yake..."
Tausayin Soja ya cika zuciyar ta lokaci guda taji labarin sa na neman sakata k'walla, ta shiga tuno kalan soyayyar da iyayen su suka nuna masu sanda suke raye... Allah sarki ashe wai har mutum taken haifi d'a yak'isa... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar sa naci gaba da fad'in
"Naso sanda na gama karatun secondary school na zauna da mahaifa na... But tunda Abbah ya riga ya rasu, ni kuma banason zama nayita b'atawa Inna rai don nasan fushinta ka iya tasiri a rayuwata shiyasa ma na dad'a yin nesa da gida, na gwammaci nayi jami'ata a wani garin daban.... Don a lokacin Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da kuma Ahmadu Bello duk sun bani admission, so sai na tafi can ABU yanda na karanci pure mathematics later on nayi applying mathematics d'ina a Nigerian Air Force... Sabida ina avoiding duk wani dalili da zai sakani nayi zaman gidanmu... So a lokacin da nake base d'inmu na Kaduna a nan na had'u da Familyn Affan har nema ya shiga tsakani na da Shareefah..." Shiru ya gifta tsakanin su ko wanne da tunanin da yake yi cikin su...
Mik'ewa yayi hannayen sa sakale cikin aljihun wandon sa kana ya d'an dubeta yace "Barin duba wayar idan tayi caji sai na kira azo a d'auke mu koh..."
Bata iya dubansa ba sai jinjina masa kai da tayi har ya fice idanunta na k'asa... Dukda ta rasa iyayen ta amma ji take tamkar labarin rayuwar Soja yafi nasu abin tausayi A DUNIYAR SU, tabbas ba k'aramin jarabawa bane ace mahaifiyar ka data haifeka bata sonka.. Allah sarki Soja harga Allah ta kuma ganin girmansa a idanunta...
******
Turo k'ofar Affan yayi yana dubanta daga yanda yanda yake tsaye.. Saida ya jima yana k'are mata kallo kafin ya k'arasa shigowa cikin d'akin hannunsa rik'e da ledar snacks...
Ilham tana jin an turo k'ofa ta shiga jada baya har lokacin bakinta a d'aure yake...
Affan ya jawo stool ya zauna bisa kafin ya daka mata wata uwar tsawa cikin wani irin murya yaci gaba da fad'in "Kina jina zan bud'e maki baki amma don kici abinci ne kawai ba don kimin kuka ba.. Kika min kuka kinji na rantse sai na kashe ki a wajen nan kuma nabi na kashe sauran 'yan uwan naki, kina so su mutu...?" ya k'arashe yana zare mata idanu tamkar tana ganin shi..
Cikeda tsoro Ilham ta shiga girgiza kai sababbin hawaye suna kwararo mata..
Affan ya murmusa kana yace "Good.." lokaci guda yasa hannu ya shiga warware tsummar dake d'aure da bakin nata...
Allah sarki bakin har ya tara jini yayi jajazir sabida azaba.. Dab da ita yake zaune ya shiga tura mata meat pie a baki yana fad'in "Oya open your mouth and eat... Kika zubo min dashi sai na b'alle maki wuya makauniya kawai..."
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*43*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Fatan Alheri d'iyar mutan Machika Aysha Sada.... Allah k'ara fasaha da baseera 💕🤝🏼*
Had'iya kawai take ba don tanajin dad'in ci ba saidon tsan-tsan tsoro da ya cika zuciyarta... A duniyar ta bata tab'a cin karo da azzalumin mutum irin mutumin da ya sato ta ba... Bata tunanin mutumin nan mai sallah ne don da ace yana sallah tabbas da ya sami gutsirin imani cikin zuciyar sa.... Hawaye suka ci gaba da kwaranya a idanun Ilham... Ga fitsari da ya tak'ura ta tamkar ta saki a jikinta, uwa uba bata yi sallolin da suke kanta ba....
Baki na rawa tace dashi "Dan Allah inaso nayi sallah...."
Kallo ya bita dashi yanda tayi maganar kafin ya murmusa yace "Kodai kina so ki gudu... Banda abinki nan da kike gani a wata Duniya kike yanda babu mai iya taimaka maki kuma wllhi kuskure d'aya kikayi zan kashe ki nabi na kashe sauran 'yan uwan naki...."
Lokaci guda tunanin iftila'in da ya auka masu a can Jama'are ya fad'o mata... Jikinta da zuciyarta suka shiga raya mata tabbas wad'ancan azzaluman mutanen ne suka biyo su....
Girgiza kai ta shiga yi lokaci guda tana fad'in "Dan Allah me muka maku kuka tak'urawa rayuwar mu, kun koramu daga mahaifar mu kun k'one komai, mun rasa mahaifiyar mu a sanadiyar haka.... Shin me muka maku da tsanani kuke neman rayuwar mu.. Su waye ku.. Shin babu tausayi da imani ne A DUNIYAR KU.... Dan Allah bawan Allah kaji k'aina ka maidani wajen 'yan uwanan ko don lalurar da nake....."
Batakai aya ba taji ya had'e labb'anta waje guda ya matse da k'arfin gaske... Cikin karaji yake fad'in "Kowa kansa ya sani A DUNIYAR MU.... Kin karya dokar da na kafa maki ko kin mance nace maki babu magana idan na bud'e maki baki abinci kawai zakici... Wayace kiyi magana..."
Ilham bata amsa sa ba sai hawaye dake gangaro mata sabida yanda ya matse mata fatun bakinta bazata iya magana ba....
Huci yake yana dubanta tamkar wanda ya tuna wani abin sai kwance mata hannayen ta da yayi ya kwance d'aurin k'afar ma kana yace "Kina jina minti biyar na baki kiyi duk wata ibada da zakiyi..."
Nan ma bata amsa sa ba sai k'ok'arin d'ago hannuwan ta da suka tara jini tayi ta share fuskar ta da ya jik'e da hawaye... Affan ne yayi directing d'inta har bathroom,
"Kina jina ina jiranki a nan cikin d'aki naji kinyi fit sai na fasa kanki...." daga haka bai jira cewar ta ba ya fice daga bathroom d'in ya janyo k'ofar da k'arfin gaske....
nan tayi tsaye har saida taji ficewar sa kafin ta silale a wajen tana kuka maras sauti...
Yana fitowa parlor yaga kiran Naseer na shigo masa.. Saida ya saita kansa kafin ya d'aga wayar.. Nan Naseer ya sanar dashi buk'atar sa cewa ya taho Awala ya d'auke su shida Salma...
"Awala..?" Affan ya nanata yana mai duban agogon bango dake manne a parlorn nasa lokaci guda k'irjinsa yayi wani irin bugu...
Jin yayi shiru yasa Naseer d'an shafe naman goshinsa kana yace "Ba abinda kake tunani bane Affan... Na fad'a maka alk'awari nayi Salma taka ce...."
Cikin zuciyar Affan tafarfasa kawai take lallai ma Naseer ya raina masa hankali... Yace suna hotel waima shine zaije ya d'auko su sannan harda wani cewa ba abinda yake tunani bane.... Naseer da Salma sunci amanar sa, he won't let them get away with this... This innocent makauniya will pay the debt.....
A fili kuwa gyaran murya yayi kana yace "Naseer ka kalli time kuwa, bayan wannan ma baku san halin da muke ciki a nan ba, kuna can hotel kuna holewar ku or whatever mu muna nan muna neman Ilham ta b'ace ba'a ganta ba...."
Zunbur Naseer ya mik'e yana fad'in "Me kace Affan..."
Lokaci guda Affan ya sanar dashi halin da ake ciki.. Hankalin Naseer idan yayi dubu ya tashi, baima san ta yanda zai soma sanar da Salma ba.... Affan ne ya katse masa shirun nasa da fad'in "Naseer bazan iya fitowa ba coz har yanzu nemanta muke kanyi... Daga haka bai jira cewar Naseer d'in ba ya katse wayar zuciyar sa na ci gaba da tafarfasa... Suna can suna soyewar su shida Salma.. A fusace ya kuma komawa d'akin da Ilham take don dama shi ya rufe bathroom d'in, k'ura ma handle d'in k'ofar idanu yayi yana kallon yanda take ta k'ok'arin bud'ewa... Zuciyar sa sai faman tafarfasa take masa tana kuma ingiza sa akan abinda yayi niyya...
******
Cikin sauri Naseer ya kira wayan yaron sa guda ya fad'a masa location d'in da yake jiransa... Gaba d'aya kasa komawa d'akin yayi don baisan me zai soma fad'awa Salma ba.. Gaba d'aya hankalin sa yayi mugun tashi...
Bayan kaman minti ashirin Samir ya iso hotel d'in... Salma da har barci ya soma d'aukanta sai jin shigowar Naseer tayi, haka kurum ta tsinci kanta da fad'uwan gaba...
Naseer ya d'an dubeta kana yace "Taso mu tafi..."
Ita dai mik'ewa kurum tayi amma kam ta razana da yanyin da ta gansa ciki... Bata ko iya tambayar sa ba sai suran jakarta da tayi ta shiga bin bayan sa....
******
Kuka Ilham keyi tana kuma tak'urewa jikin garu bata daina rok'onsa kada ya lalata mata rayuwa ba yaji tausayin ta.... Lokaci guda Affan ya d'auketa da wani wawan mari wanda saida ta kifa k'asa, lokaci guda bakinta ya fashe jini ya hau zuba....
Da k'arfin gaske ya kuma fincikota ya shiga d'aure mata baki da hannaye.. Sai faman fincika Ilham take numfashin ta na neman shid'ewa sanda Affan ke kokawan rabata da suturanta.... Lokaci guda idanunta suka kafe tamkar ta mace...
Affan dake rik'e da ita yana wani irin huci lokaci guda hawaye suka shiga kwaranya masa, kallon gefen bakinta yayi yanda jini ke zuba, ya kuma duban makafin idanunta yanda suka kakkafe.... A hankali ya saketa ya koma gefe can k'arshen d'akin yana kuka sosai kukan da ya jima baiyi irin sa ba.. Tun daga farkon had'uwarsu da Salma ya shiga tunowa har zuwa aurenta da Naseer... Ya tuna kalan k'aunar juna da yake hangowa cikin idanun junan su.. Ya tuna yanda suke k'aunar juna shida Naseer tamkar brothers.... Yana son Naseer tamkar jinin sa.... Meyasa burin d'aukan fansa ya cika zuciyar sa.. Meyasa ya kasa yak'i da zuciyar sa...
Tamkar wanda aka zabura a tamanin ya nufi parlor ya d'auko goran ruwa ya shiga shek'awa Ilham... Lokaci guda idanuwanta suka shiga motsawa.... Cikin sauri Affan ya sureta bai sunce d'aurin bakin nata ba ya fice da ita daga gidan.....
Bayan wasu gini ya shimfid'ata lokaci guda ya k'ura mata idanu tausayin ta da haushin kansa suka cika zuciyar sa.... Cikin sauri ya mik'e ya bar wajen ba don yaso ba sai don kada wani ya gansa... Har lokacin ba'a daina k'anan yayyafi ba... Haka yana ji yana gani ya tafi ya bar Ilham a wajen...
A parlorn gidansa ya zauna ya tak'ure waje guda tunanin Duniya ta cika zuciyar sa..... A hankali ya soma furta "Ina sonki Salma soyayyar da ta tassama jefa rayuwata ga halak'a... Amma .. Nasan Naseer na sonki fiye da yanda nakeyi,.... I just have to let you go even if it will break me....." lokaci guda siriryar hawaye ta zubo ma Affan... Runtse idanunsa yayi yana mai tuno halin da ya bar Ilham ciki ga bakinta a d'aure... Cikin sauri ya mik'e ya zura jacket d'insa ya fito waje... Dai-dai lokacin dasu Naseer suka iso
Daga yanda yake hangosu saman kwalta ya kasa ci gaba da tafiyar.... Kaman ya juya cikin gidan nashi sai kuma nufosu da yayi... Cikin sauri Naseer ya umarci Samir ya tsaya...
Yanayin da yaga Affan ciki yasa jikinsa yin sanyi....
"An sameta....?" Naseer ya tambaya yana dubansa...
Kasa furta komai Affan yayi sai d'an girgiza kai da yayi kana yace "Naseer we couldn't....." Kasa ci gaba da maganar yayi sabida halin da ya tabbatar babu shakka ya bar Ilham ciki... Dai-dai lokacin Salma ta k'araso waken yayinda Naseer ke ci gaba da fad'in "No Affan bazai yuwu Ilham ta b'ace ba... Dole tana cikin barikin nan batayi nisa ba, su waye a gate sanda abun ya faru... Kai no way.. Barikin nan bata lalace har haka ba... Affan idan da gaske b'ata tayi gaba d'ayanmu zai shafe m....."
Bai kai aya ba Salma ta k'araso tana kuka sosai hannayen ta k'unshe da bakinta take fad'in "A'a badai Ilham d'ita ba... Dan Allah ina 'yar uwata ku sanar dani tana lafiya....."
Naseer yayi saurin rik'ota ya matse cikin jikinsa yana kwantar mata da hankali ganin tana neman fita daga control...
Affan kuwa juyawa yayi yana k'ok'arin maida hawayen dake neman zubo masa, a yau d'in jinsa yake tamkar lusari ba Soja ba.. Dole ma yaji hakan, sabida abinda yayi cin amanar kakin jikinsa ne.. Ya wulak'anta aikinsa, lokaci guda ya kuma tuna halin da ya barta ciki...
K'ok'arin saita kansa yayi lokaci guda ya take masu baya domin tuni sun nufi gidan Momy....
Shiru kawai Naseer yayi yana sauraren lamarin daga bakin Momy, yayinda Salma da Jamila suka rungume juna suka tak'ure waje guda suna aikin kuka...
Momy taci gaba da fad'in "Tare da Affan aketa binciken kaman yanda ka fad'a shima hakan yace, dole dai kawai a tsaurara bincike cikin barikin nan... Kar ta lalace ta zamto tamkar wasu barikin da tsaro yayi k'aranci, kodashike bamu sani ba ko ta fice ta fad'a wani wajen don ruwan da akayi yau ya tsorata kowa.."
Naseer ya juya yana duban Affan dake tsaye daga gefe d'an dafa kafad'ansa yayi kana yace "Kaje gida ka huta zamu ci gaba da gudanar da binciken..."
Saurin girgiza kai Affan yayi kana yace "Naseer bazan iya komawa gida ba har sai an samo Ilham...."
Naseer ya d'an tasare sa da idanu kafin ya jinjina kai ba tareda yace komai ba yasa kai zai fice... Har ya kai k'ofa sai kuma ya juyo yana duban yanda Salma ke kuka da duka zuciyar ta..
K'arasawa yayi ya durk'usa gabanta a hankali ya kamo hannayen ta... Cikin muryan kwantar da hankali yake fad'in "Insha Allah zan samota, zan taho maki da ita kinji... Ki daina kuka...."
Bata iya ce masa komai ba sai kwanciya da tayi cikin jikin Jamila, lokaci guda Jamila ta kuma rungumar 'yar uwar tata...
A tare Naseer da Affan suka fice
*******
Gabaki d'aya barikin ta birkice lokaci guda, hankula sun tashi, ko ina bincike ake dukda dare da ya soma ja.... Affan da tawagar sa hakama Naseer da nasa tawagar
Shi yasan yanda ya ajiyeta don haka bai sha wahalan jan zugansa suka nufi wajen ba.... Gabansa ya yanke ya fad'i sanda ya hangi tamkar bata wajen... Cikin sauri ya kuma kutsawa nan ya hangeta jikin reshen bishiya sai k'ok'arin yanka d'aurin hannunta take tana neman tsira a d'ari sauran Sojojin suka k'araso lokaci guda Affan ya d'agota yana fad'i ma sauran Sojin the should call an ambulance.......
Tuni labari ya riske su Naseer... A asibiti suka tadda su Affan likitoci sun shiga duba Ilham don tuni ta kuma sumewa...
Take Naseer yayi waya ya sanar da Momy, ai basuyi wata-wata ba suka nufo asibitin suma...
Daga Jamila har Salma godiya suka dinga yima Affan, shi kuwa fir yak'i barin asibitin, fatan sa bai wuce Dr ya sanar dashi Ilham na numfashi....
Naseer sai jinjina lamarin yake a kwanyar sa, wannan abu da matuk'ar ban mamaki yake, waye yayi wannan abu kuma kan wani dalili yayi...? Tambayar da tayita yawo kenan a kwanyar Naseer... Dole su d'au tsatsauran mataki, bazasu bari hakan ta kasance a barikin su ba...
Dr na fitowa suka mik'e gaba d'ayansu... Jamila Salma da Momy tuni sun soma kwararo wa Dr tambaya gameda Ilham d'in..
Sauk'e ajiyan zuciya Dr yayi kana yace "Ku kwantar da hankulan ku ta farfad'o.."
Nannauyan ajiyan zuciya Affan ya sauk'e lokaci guda
Dr yaci gaba da fad'in "saidai har yanzu tsoro bai saketa ba, ga dukkan alamun an azabtar da ita...."
Gaba d'aya mamaki suke wani irin azaba za'a gana wa mutum a rana guda har ya fice a hayyacin sa.. Lallai ko wanene wanda yayi wannan aika-aika ya cika azzalumi, Allah sarki gashi bata gani ballantana ta bayyana sa...
Dr yaci gaba da fad'in "Mun mata alluran barci sabida ta samu hutu...."
Salma na share hawaye take fad'in "Dr zamu iya shiga mu ganta... " Jinjina masu kai yayi kana yace "K'warai kuwa kuna iya shiga amma bamu so a tada ta sabida tana tsananin buk'atan hutu..."
A tare suke jinjina kai Jamila da Salma har suna had'a baki wajen cewa, "Bazamu tada ta ba Dr...."
Naseer ya d'an k'araso yanda Affan ke tsaye kafin ya dafa kafad'an sa yace "Weldon Soldier..." Shiru ya d'an gifta tsakani kaman babu mai cewa komai cikin su sai kuma Naseer d'in yaci gaba da fad'in "Affan... I won't break my promise.... Salma take ce...."
Saurin girgiza kai Affan yayi yana duban Naseer d'in kana yace "Naseer pls ka daina cewa Salma tawa ce..... Koda ace soyayyar Salma zai zama ajali na wllhi zan hak'ura da ita for you.... Naseer Salma kai take so sannan kaima kana sonta... Dan Allah ka rik'e matar ka hannu bibbiyu ka daina danganta ta da wani alhali da aurenka akanta..... Fatana Allah Ya baku zaman lafiya mai d'aurewa had'i da zuri'a d'ayyiba....." ya k'arashe murmushi kwance saman fuskar sa..
Kasa furta komai Naseer yayi sai kallon da yake bin Affan dashi, lokaci guda murmushi ya cika fuskar sa, bai san sanda yayi hugging Affan ba don harga Allah baisan me zaice masa ba....
Da k'yar Affan ya bar asibitin ba don yaso ba... Tunanin halin da take ciki da zullumi duk ya taru ya cunkushe masa zuciya...
Koda ya koma gida ma a parlor ya tak'ure yana tunanin abubuwa da dama da suke kan faruwa A DUNIYAR SU, tunanin mahaifin sa ya fad'o zuciyar sa... Tabbas idan da zaisan abinda yayi zaiyi fushi dashi na har abada... A wannan dare barci baiga idanun Affan ba, ko ya runtse idanu Ilham yake hangowa yanda ya wahalar da ita ya azabtar da ita bisa laifin da sam babu nata ciki, Allah sarki lallai makanta babban jarabawa ce a rayuwa, tabbas da ace tana gani bazai sami damar gallaza mata da yayi ba..... A hankali ya shafi sumar sa tunanin yak'i barin kwanyar sa.... Tamkar wanda aka zabura ya nufi drawers d'insa da yake jera whiskeys d'insa....
Zama yayi ya dinga kwankwad'a ko hankalin sa zai kwanta....
******
Har gari ta waye tangarau Salma na kwance gefenta hannuayen su cikin na juna... Jikin Ilham d'in duk tabo yanda ta kukkurje kanta don neman hanyar tsira... Kukanta ne ya farkar da Salma ta mik'e zunbur ta zauna tana mai lallashin Ilham d'in
Kuka Ilham d'in keyi tana fad'in "Salma I was so scared, na zaci mutuwa zanyi.. His hands were all over my body.... Salma na tsane sa ban sansa ba amma na tsane shi fiye da komai A DUNIYAR MU... "
Daga yanda yake tsaye bakin k'ofa yake jiyo sautin maganar ta da kukanta cikin k'aramar muryarta, gabansa ya yanke ya fad'in jin yanda take fad'in ta tsane sa.... Bai iya k'wank'wasa k'ofar ba sai juyawa da yayi cikin sauri ya fice daga asibitin.....
Salma ta d'anyi hugging Ilham tana share mata hawayen take fad'in "Ilham mu godewa Allah, Allah bai bashi nasara akanki ba.... Soja ya tabbatar min suna kan bincike kuma idan suka zak'ulo azzalumin mutumin nan zai fuskanci hukunci irin wanda ta dace dashi kinji koh...... Ki daina kuka insha Allah bazamu k'ara ficewa mu barki ke kad'ai a gida ba kinji koh...."
Ilham bata iya cewa komai ba sai kwanciya cikin jikin Salmar da tayi tana mai ci gaba da hawaye had'i da k'ank'ame jikinta. .
********
Hannun ta rik'e da basket na abinci ta nufi hanyar clinic d'in, dai-dai zata tsallaka kwalta ya hangeta, a d'ari ya k'araso yanda take lokaci guda yayi parking...
Gabanta ya yanke ya fad'i ganin motar Fawaz ne... Sauri-sauri ta soma tafiya don bataso ya cimma ta..
Gudu-gudu yake binta yana fad'in "Jay pls... We need to talk, Jay dan Allah ki tsaya, ki tsaya ki fad'amin me na maki.....?"
A zuciye ta juyo tana wani irin huci take fad'in "Fawaz kayiwa Allah ka daina bina......"
"No Jamila sai kin fad'a min me na maki, Kin tafi daga gidanmu babu sallama sannan nayita kiran ki baki d'aga ba... Jamila what's going on...?"
K'ak'aro murmushi tayi kana tace "Fawaz zamuyi maganar wani lokacin, ka tafi aiki zaka makara...."
Girgiza mata kai yayi kana yace "No Jamila, it has to be now, ki fad'a min sabida lalurar Mum kika tafi, sabida bazaki iya zama da sirka mahaukaciya ba... Wannan shine dalilin ki...."
K'walla suka soma k'ok'arin cikowa idanun Jamila, cikin sauri tasa bayan hannu tana sharesu kana tace "Fawaz nida kai bamu dace ba, you're Young and fresh, kaje ka nemi daidanka dan Allah..." Daga haka bata jira cewar sa ba taci gaba da tafiya....
Saurin shan gabanta yayi fuskar sa tayi jazir yake fad'in "No... Wasa kike yi koh, kice min wasa kikeyi don Allah...."
Murmushin takaici tayi kana tace "Kasan meye ka bani hanya na wuce...."
Lokaci guda ya kuma girgiza kai yana mai fad'in "Idan matan duka duniya za'a kawo min... I'll still choose you.... I love you , pls let's fix this, dan Allah kada kice zaki rabu dani... Wllhi ban tab'a soyayya da Wata d'iya mace ba sai akanki... Dan Allah kar ki bari labarin farkon soyayyata ya zamto kariyan zuciya....."
Yanda yake maganar ya kuma karyar mata da zuciya, hawaye suka shiga wanke mata fuska... Inama zata iya sanar dashi gaskiyar lamarin inama ba Fawaz bane..... Cikin sauri ta d'ago a fusace take fad'in
"Dr I beg of you, please, please just stay away from me, dan Allah Fawaz....." Daga haka tasa kai ta soma tafiya cikin sauri ta nufi asibitin.... Lokaci guda shima ya take mata baya
*******
Tana nan tsaye a window har Lubna da Deeni suka fice... Fuzar da iska tayi kafin ta suri wayarta ta shiga neman layin Maina... Bugu uku ya d'aga....
"Hajjaju nawa, babu wata bayan ke...."
Innah ta murmusa domin kuwa duk lokacin da Maina ya mata wannan kirari har cikin ranta take jin dad'i dukda har yanzu bata sami yanda take so dashi d'inba...
"Kana jina....."
Maina ya gyad'a kai daga d'aya b'angaren tamkar wacce take kallonsa kana yace "Ina jinki Hajiyata, kud'i kike buk'ata a ciro maki akai maki gidan holewa, ko kuma sabbin 'yan mata kike buk'ata..." (Guest house d'inta)
Innah ta murmusa tana hura sigarinta kana tace "K'aramin shed'ani... Kaima kasan a halin yanzu nafi buk'atar ka fiye da 'yanmatan..."
Maina ya murmusa had'i da shafa kansa kana yace "Wllhi Hajjaju badon tsoron karona da mai gida ba da tuni an wuce wajen nan... Kinsan Mai gida akwai saka idanu a lamura, idan ya fuskanci akwai wani abin tsakanin mu zan iya samun matsala....."
Murmushi Innah tayi tana kuma zuk'an sigarinta kana tace "Kar ka damu yanzu bama wannan ba.... Aiki nake so kamin...."
Maina ya gyara zama kana yace "Toh Hajjaju ina sauraren ki...."
Innah ta jinjina kai kana tace "Yayi kyau.... Kasan yaro drivern Lubna...?"
Maina ya jinjina kai kana yace "K'warai kuwa...."
Ta kuma murmusawa sigarinta na mak'ale tsakanin yatsun ta kana taci gaba da fad'in "Shi nake so ka kashe min shi har lahira.... Bana son a sami mishkila idan ka cika aikin ka, kanada lada mai tsoka.... Idan mun had'u a gidan holewa zamu k'arasa bayanin..."
Daga haka bata jira cewar Maina ba ta gutsire wayar... Lokaci guda ta zuk'i sigarinta tana mai fashewa da wani irin dariya....
*******
Zaune kurum yake a office tunanin Fawaz da Jamila ya hanasa sukuni... Gashi ya kira sabon layin da ya bata bata d'agawa, d'aya tsohon layinta ma bai shiga... Yasan duk yanda akayi canza layi tayi, dole yasan abin yi before she causes hell for him
******
Har suka iso asibitin Fawaz bai daina binta ba... A bakin wajen suka had'u da Naseer Jamila sai faman goge hawayen idanunta .... Burki Fawaz yayi lokaci guda Jamila tasa kai ta shige...
Kallon tuhuma Naseer kema Fawaz don yaga sanda Jamila ke share hawayen idanunta....
*Sameena Aleeyou....*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*44*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
"Ka bata lokaci Son, kaga halin da suke ciki a yanzu...." cewan Naseer dake jingine jikin mota idanunsa naga Fawaz d'in
Fawaz ya d'an shafi sumar sa kana yace "Uncle wllhi bazan iya barci bata min bayani ba...."
Katse sa Naseer yayi da fad'in "Na yarda kana sonta tunda ko kunyata bakaji... Amma banda abinka Fawaz bakaga halin da 'yar uwarsu ke ciki bane, don dai jiya baka a barikin nan ne da kaga kalan tashin hankalin da muka shige ciki..."
Fawaz ya kuma fuzar da iska kana yace "Uncle Nass Wllhi jikina na bani canzawan da Jay tayi sam baida alak'a da abinda ya faru da Ilham... Amma kaman yanda ka ce zan d'an bata space na d'an wasu lokuta..."
Naseer ya jinjina kansa kana yace "Good, yanzu maza ka wuce aiki direct daga nan, and banda tunani, concentrate kaji koh..."
D'an jinjina kai Fawaz yayi fuska d'auke da murmushi, sosai yake jin dad'i idan uncle d'in nasa na treating d'insa tamkar yaro....
******
"Hello ina jinki Laure, toh Laure yaya kike so nayi bayan wayar ki ba shiga yake ba...." Mamy ta kuma gyara zamanta sosai kana tace "Ke 'yar gari kina nufin Boka zai min komai...."
Daga d'aya b'angaren Laure ta murmusa irin ta k'wararrun 'yan bariki kana tace "K'warai kuwa Ma'u, yanzu abinda nake so dake ki shirya ni kuma zan taho na d'auke ki...."
Mamy baki har kunne take fad'in "Ko kefa k'awar amana, ai ni da har na zaci kin goge ni a babin rayuwar ki ne... Yanzu naji k'warin gwiwar cin uwar duk wanda ya shige min rayuwa... Zan shirya sai ki taho ki d'auke ni muje ayita ta k'are... Ali Safwan bakinsa zan saka a rufe min ruf tunda na lura ran k'arfe ne dashi..."
Laure ta shek'e da dariya kafin tace "Ma'u bazaki canza ba sai kin ganni...." Daga haka sallama sukayi Laure sai faman murmusawa take....
Azeema dake lab'e jikin k'ofa murmusawa tayi kana tace cikin ranta _Allah sarki Mamy, ai k'afarki k'afata, tare zamuje wajen bokan na maida asirin kanki...._ Sauri-sauri Azeema ta bar wajen jin Mamy ta mik'e tana shiri...
********
Daga wajen mahaifin sa kai tsaye k'ofar wani dank'areren store yayi parking ya shiga lodan kaya irinta dubiyan marassa lafiya, duk abinda ya gani sai yaga zata so abin... Haka Affan ya dinga jidan kaya, wani abin idan ya d'aga sai ya tambayi masu store d'in nasu view d'in ko maras lafiya zata so abin... D'ayan ya k'are yace
"Yallab'ai amma dai Madam ce babu Lafia koh..."
Murmushi kawai Affan yayi ba tareda ya furta komai ba... Saida ya jida kaya sosai masu kantin sai Allah son barka suke masa da fatan samun lfiya ga wanda ankama sayyayan.... Daga nan Affan hanyar Base d'insu ya d'auka kai tsaye.. K'irjinsa sai faman lugude yake, gani yake kaman zata gane shine ya azabtar da ita..
********
Lubna zaune gefe yayinda Abban Deeni ke kwance idanunsa a lumshe.... Tausayin su ya cika zuciyarta, tana ganin sanda Deeni ya shigo ya tallafi kan mahaifin nasa ya basa ruwa ya sha.. Har saida ya gama sha kafin Deeni ya maida kansa ya kwantar...
D'an karkatowa yayi yana duban Lubna da hawaye ke neman wanke mata fuska... K'ak'aro murmushi ya d'anyi kana yace "Hey don't cry OK, I'm used to it, Idan kinsan kuka zakiyi ki tashi ki fice mana a gida shiyasa nace bazan kawo ki ba, kika nace sai na kawo ki. ." Ya k'arashe yana galla mata mugun kallo dukda d'an rawa da muryar sa keyi....
"You so silly you know.... You never take things serious...." Ta fad'i tana watsa masa harara har lokacin hawaye na zuba idanunta...
K'ak'aro murmushi yayi yana mai dubanta, sunada abubuwa in common shida Lubna, ji yake k'aunarta na kuma ratsa b'argo da tsokar sa..... A hankali ya mik'e kana yace "Zo muje idan Abba yaji kukan ki yau bazai bari muyi barci ba...."
Cikin sauri ta mik'e tana kuma share hawayen da bakin mayafinta duk tozali ya b'ata mayafin...
A d'an madaidaicin tsakar gidan suka tsaya....
Deeni yana rakata da harara irinta wasa yace "Ashe wai dama kinada imani haka, kinga dubi yanda duk kika b'ata Vail d'inki, haka zaki shiga class, ew it's embarrassing, ko yanzu kin tashi sahun big girls ne...."
Gajeren tsaki tayi tana k'ok'arin sunce belt d'in takalminta Deeni ya shiga matsawa da baya yana k'unshe dariyar sa yake fad'in "I apologize, ayimin afuwa, wannan takalmi naki kaman k'afar shed'an kika sauk'e min ai na rasa mai min jinyar Abba na.... Haba my Stalker kiyi hak'uri kinji...."
K'wafa tayi kana tace "Abinda ka iya kenan neman magana...."
Deeni ya murmusa kana yace "Hey you so beautiful..."
Yastina fuska tayi kana tace "I know... Shiyasa ka nace min ai..."
Jinjina kai yayi yana murmushi kana yace "Yes I love you....." Ya k'arashe murya can k'asan mak'oshi...
Lubna ta gyara zaman mayafinta kana tace ina sauraren ka, labarin da kace zaka bani...."
Agogon wayar sa ya duba had'i da d'an fuzar da iska kana yace "Zakiyi lattin school, ki bari sai wani lokacin tunda yanzu nayi guda d'aya na kawo ki kinga Abbah na..."
Girgiza masa kai tayi kana tace "Ka mance dama bason shiga class d'in Dr Salis nake ba, ya faye disgracing mutane...."
D'an b'ata fuska yayi kana yace "Do we have to talk about it again... Ba na hanaki k'in shiga class ba, you know I don't want you to end up like that friend of yours....."
Lubna na murmushi tace "Wai kana nufin Faty...."
With a straight face yace "Who else..."
Murmushi ta d'anyi kana tace "Ai Faty inaga final semester d'inta take, kasan yanzu bama wani shiri, sannan bata faye zaman Bauchi ba, ko da na tambayeta sai ce min tayi wai business trip take..."
Deeni ya d'an girgiza kai kana yace "Allah sa dai kar kwad'ayinta ya kaita ga halak'a, Allah kuma ya shiryi masu hali irin nata su baro garin iyayen su su taho wani garin da sunan karatu su bud'e wani sabon shafi na rayuwa..."
Lubna ta jinjina kai kana tace "Ameen my Stalker, kuma wllhi rayuwar da muka tsinci kanmu ciki kenan A DUNIYAR MU, saidai addu'a..."
Deeni ya jinjina kai kana yace "Haka ne sai addu'a Duniyar mu kam, barin kuma lek'a Abbah sai na fito mu wuce..." A hankali ta jinjina masa kai ba tareda ta furta komai ba....
********
Sosai Mamy ta gama shirinta 'yar posa d'inta mak'ale a hammata, ko sallama ma Shareefah bata yi ba, ta d'au crutches d'inta ta shiga cangwalawa....
Azeema tana ganin Mamy ta nufi gate ta sad'ad'o itama....
Mamaki bai gama cika Azeema ba saida taga hamshak'iyar jeep d'in da akazo d'aukan Mamy ciki, tana nan lab'e jikin k'arfen gate, motar tana tashi Azeema tasa hannu ma d'an babur ta d'ale tuni ta umarcesa subi bayan jeep d'in.....
*******
K'irjinsa sai dukan tara-tara yake sanda ya soma knocking a k'ofar,..
Jamila ce ke zaune gefe ta rapka uban tagumi ta lula duniyar tunanin makomar rayuwar ta, sam bataji knocking d'in da ake ba, Ilham na gefenta tana barci drip d'aure a hannunta na hagu....
A karo na uku Jamila ta jiyo k'wank'wasa k'ofar cikin sauri ta mik'e ta nufi k'ofar, ganin Affan ne ya sanyata sakin murmushi tanai masa sannu da zuwa....
Shima murmushin ya sakar mata yana mai amsawa lokaci guda Jamila ta basa hanya ya shigo cikin d'akin, sai yafi jin dad'in samunta da yayi tana barci.. ... Gaisawa da Jamila suke yana ajiye manyan ledojin dake hannun sa, idanunsa k'uri kan Ilham d'in yake tambayar Jamilar jikin nata....
Idanunsa ya sauk'a kan hannunta yanda ya murd'esu da k'arfin gaske har saida shatin zobensa ya fito, lokaci guda abubuwan da ya mata suka shiga dawo masa, gabansa ya shiga dukan tara-tara...
K'ok'arin saita kansa yayi kana ya dubi Jamila yace "Aima kaman barci take koh....?"
Jamila ta jinjina masa kai kana tace "Tunda aka saka mata k'arin ruwan take barci....."
Affan ya d'an jinjina kai kana yace "Allah Ya bata lafiya..."
Jamila ta amsa da Ameen a tak'aice don gaba d'aya itama ba jin dad'in jikin nata take ba....
Sallama yayi da Jamila ya fice don gaba d'aya jinsa yake ba dai-dai ba... Jamila kuwa sai mamakin lodin sayyan da Affan yayi take, cikin zuciyarta take fad'in _Allah sarki Affan da Daddy sun fita zakka ba kaman Mamy da Shareefah ba... Affan nada mutunci kaman mahaifin sa...._ lokaci guda takai dubanta ga k'anwarta wacce ke barcin ta hankali kwance, inama itace ta sami wannan barci, inama tanada kwanciyar hankali kaman yanda kowa ke ciki.... Lokaci guda ta sauk'e nannauyan ajiyan zuciya hawaye na neman ciko idnunta...
*******
Sister Nafisa ta d'an rusunar da kai k'asa kana tace "A gaskiya Dr bansan tsohon mijin Jamila ba, amma dai nasan ba'a garin nan yake ba, can garin da suka baro yake...."
Shiru Fawaz yayi yana nazarin maganganun Nafisa kana yace "Na gode Nafisa kina iya tafiya...."
Rusunawa ta kuma yi kafin ta masa fatan kasancewa lafiya ta fice....
Tunanin ya kasa barin kwanyar Fawaz..... Toh idan mijinta na da baya garin nan waye mai tak'ura ma rayuwar ta.... He really need to get to the bottom of this.... Yana son Jamila so na tsakani da Allah sam baiso ya rasata.... Da wannan tunani ya tattara stuffs d'insa ya fito daga office d'in.....
**********
Tsaf driver d'in ya lura da babur d'in dake biye dasu, murmushi kawai yayi ba tareda yace komai ba... Mamy dai gaba d'aya tunda ta shige motar nan sanyin AC ya ratsa ta bata kuma sanin yanda kanta yake ba....
Sam tafiyar bai dami Azeema ba dukda taga sun d'au hanyar ficewa daga gari, tasan gidan boka su Mamy da aminiyar ta suka nufa, gidan boka kuwa ba'a yinsa a cikin gari...
D'an mashin d'in ne yayi burki ya tsaya kana yace "Baiwar Allah wllhi na gama tafiyata saidai fah ki k'arasa da k'afa..."
Azeema tana bugun bayansa take fad'in "Haba Malam wani irin tashanci ne wannan mu k'arasa mana kaga a slow ma suke tafiya..."
Wata uwar ashar ya kwararo mata kana yace "Ke Alqur'an bazan je ba, tashanci ya wuce wanda kike yi...... Ke k'warank'easa idan baki sauk'a ba zan tara maki na jaki a nan... Ki d'auko ni tun daga cikin gari ki sanyani bin bayan hamshak'iyar mota, salon kuje ku yanka ni. Yasin nasha na tauri, nasan irinku, masu kai kayukan 'yan acab'a ko, toh kuwa saidai ki kai na uwar ki... Shegiya 'yar biyan gurb'atattun 'yan siyasa wato zab'e ya kusa bari kuyi kati da kaina..... Sauk'a kafin na faffalaki...."
A tamanin Azeema ta sauk'a tana watsa masa mugun kallo tace "Banza talaka, abinda kuka iya kenan, hassada wa masu kud'i, haka zaka k'are a tsiya..."
Lokaci guda taja dogon tsaki, ta tattari skirt d'inta a hannu ta shiga bin bayan motar da tuntuni take tafiya a slow....
Wani dank'areren gida a daji Azeema taga motar ta shige.. A fili ta furta "Eh lallai malaman tsubbu sun sami d'aurin gindi a k'asar nan.. Ai wllhi sai na shiga anyi dani...."
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*45*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Fatan Alheri gareku members na SAN, ina k'aunar ku tsakani da Allah... Har kullum kyawawan addu'o'inku gareni sukan sakani farin ciki.... Allah Ya bar k'auna, Sameena taku ce ❤🤝🏼*
Mamaki ne ya cika Azeema sanda taga motar ta paka amma Mamy bata fito ba Hajiya Laure ce dai ta fito sai faman cakala cawing gum take.... Tana nan tsaye tana mamakin rashin fitowar Mamy saiji tayi an toshe mata hanci da wata tsumma.... Duk kalan wutsil-wustil da Azeema keyi bata iya k'watan kanta ba, daga nan bata kuma sanin yanda kanta yake ba...
*******
Mamaki ya cika Deeni jin kalan tambayoyin da mahaifin sa ke masa, a hankali ya d'an nad'e k'afafun sa kana yace "Toh Abba dai-dai da rana guda kak'i sanar damu sunan mutumin da ka masa aiki sanda kake da lafia, nasan kayi aiki a garin nan tun muna jihar Yobe, Abbah sanda ka kwaso mu ka dawo damu garin nan a lokacin tsautsayin jinyar nan ta sameka, haka kurum rana tsaka Ummi ta tafi ta barka, harta Mama Tani tace batasan ma waye kayi aiki a garin nan ba iyakaci dai tasan mutumin attajiri ne, Abbah da ace sunada mutunci da sun taimaka maka tuntuni shekara da shekaru, dan Allah Abbah kayi hak'uri ka amshi taimakon da Lubna take shirin yi maka, nima ba so nake ba amma banida zab'i, sam har raina ji nake tamkar laifina ne da ban tashi na nemi kud'i sosai na maka jinya ba...."
Murmushi Abbah yayi kafin ya kamo hannayen Deeni yace "Zahraddeen akwai ranar da komai zai wuce zai zamto labari, kar ka damu da jinyata, A DUNIYAR MU akwai tarin mutane iri daban-daban, wasu mutanen mukan zab'i mu sadaukar da rayuwar mu garesu ba don komai ba sai don taimakawa wajen kawar da gurb'atattu wanda sukeda illa sosai A DUNIYAR MU, wani sadaukarwan tamkar shada ce idan rayuka da dama zasu kub'uta.."
Shiru ya d'an gifta tamkar bazaice komai ba, sai kuma ya murmusa ya d'an mik'e kad'an ya d'aga bakin katifar sa..... Wata envelope doguwa kalan ruwan k'asa ya ciro, wanda da gani basai ance maka takardu ne ciki ba....
Zahraddeeni dai kallon mahaifin nasa kurum yake cikeda tsoro, a iya zamansu bai tab'a zaton mahaifin sa na dogon zance haka bai saki layi ba, don tun bayan faruwan had'arin mota da yayi ya zama tamkar zararre wanda har ce masu akayi a asibiti had'arin ne ya d'an shafi kwanyar sa... Amma abinda ya bashi mamaki matuk'a shine yau Abbah garas yake magana ba tareda ya kawo shirirta ciki ba.... Mik'a masa envelope d'in da yayi ya sanyasa dawowa daga duniyar tunanin da ya tafi....
"Zahraddeen, jinyata da kayi Allah ubangiji ya maka albarka, Allah Ya baka 'ya'ya wanda zasu tausaya maka suji k'anka kaman yanda kaji nawa, Kaida Tani Allah Ya biyaku da mafificin alkhairi...."
Deeni dai bai iya furta komai ba sai kallon mamaki da yake bin mahaifin nasa dashi...
"Karb'i wannnan takardu ne masu matuk'ar amfani, takardu ne da na ijiyesu ma d'an marayan Zakin da aka jima ana zalunta A DUNIYAR MU, Zahraddeen wad'annan takardu zasu fayyace abubuwa da dama da suka shige duhu A DUNIYAR MU, da sannu zan sanar da kai yanda zaka kai takardun amma na rok'i arzikin ka daka adanasu har sai lokacin yayi.... Sannan mahaifiyar ka koda ta dawo gareka ka karb'eta hannu bibbiyu sabida nasan a kwana a tashi zata dawo gareka....."
Izuwa lokacin jikin Deeni yayi sanyi gaba d'aya, lokaci guda yaji k'walla sun ciko idanunsa.... Girgiza kai yake yana fad'in "Haba Abbah, wllhi babu abinda zanyi da matar nan na mance ta na goge ta a babin rayuwata tun sanda ta saka k'afafu ta fice ta barmu, idan inada wata mahaifiya A DUNIYAR MU toh kuwa ko shakka babu Mama Tani ce...." Ya k'arashe hawaye na k'ok'arin gangaro masa
Girgiza kai Abbah yayi had'i da sakin murmushi yana duban Deeni kana yace "Zahraddeeni mahaifiyar ka bata tafi ta rabu dakai haka kurum ba hasalima ni na umarceta...."
Girgiza kai kurum Deeni yake yana duban mahaifin nasa cikin rashin yarda da abinda kunnuwan sa ke jiyo masa..... Shin wai meke faruwa ne...? Tambayar da yayi ma kansa kenan...
Yana mai ci gaba da girgiza kai yake fad'in "Abbah ban fahimci komai ba, don Allah ka fahimtar dani, shin wai meke faruwa ne, mai ya faru shekarun baya, shin wani irin aiki kayi a garin Bauchi shekaru ashirin da d'oriya da suka shud'e, ... Abbah don Allah ka fahimtar dani....." Ya k'arashe muryar sa na tsananin rawa...
Abbah ya d'an kuma murmusawa hannunsa rik'e cikin na Deeni yake fad'in "Zan fahimtar da kai, zan fayyace maka komai insha Allah nan bada jimawa ba..... Abinda nake so da kai ka adana wannan k'undi da na baka har sai ranar da na fayya ce maka komai...."
Ya k'arashe yana nuni da babban envelop d'in
Gaba d'aya Deeni ya zamto confused bai fahimci komai ba, hasalima shi kansa bai fahimci shi d'in waye ba a halin yanzu.....
*********
Wajajen k'arfe hud'u da rabi Affan ya kuma komawa asibitin, cak ya tsaya bakin k'ofa yana sauraren tattaunawar nasu
"Addah toh meyasa zai damu har ya kawo min irin wad'annan kaya, nidai gaskiya sunyi yawa banaso dukda ban gani ba amma irin kyaun kayan da tsadan su da kika fad'i yasa sam naji bana so...."
Jamila ta murmusa kana tace "Haba Ilham karfa ki mance kalan kirkin Affan tuntuni shid'in daban yake dasu Mamy, wllhi kyautatawa ce kurum yasa ya kawo maki ki amsa kinji sannan ki masa godiya domin kuwa shine mutumin da ya tsince ki....."
Gaban Ilham ya yanke ya fad'i, a hankali ta furta
"Shi ya tsince ni....."
Jamila ta jinjina kai tamkar Ilham d'in na kallonta kana tace "Yafi kowa tsananin shiga tashin hankali sanda kika b'ace sannan bai huta ba dai-dai da dak'ik'a guda saida ya samo ki... Affan da Daddy ai sun fita zakka a gidan Mamy....."
Ilham dai sauraren ta kurum take amma kam k'irjinta sai faman lugude yake, haka kurum ta tsinci kanta da lulawa wata duniyar tunani... Sallaman Affan ya katse Jamila... Da murmushin ta ta mik'e tanai masa sannu da zuwa...
Ilham kuwa muryar ce ta shiga yawo a kwanyar ta, haka kurum ta tsinci kanta da fad'uwan gaba.... Wannan murya ya mata shige dana mugun mutumin can, saidai wannan batakai na wancan gwab'i da firgici ba... Gaba d'aya bata sauraren su sanda suke gaisawa tayi nisa duniyar tunani... Muryar sa ta kuma jiyowa yanai mata sannu da jiki....
Bata iya amsa sa ba sai faman jujjuya makafin idanunta take.... Shid'inma gaba d'aya k'irjinsa bugu yake, shi gani yake ma tamkar tana kallon sa, jira kawai yake ta d'ago muryar sa dukda cewa ya canza muryar nasa a wancan lokacin..... Jamila ce ta katse ma Ilham tunaninta da fad'in. "Lil Affan ne ke gaidaki...."
K'ak'aro murmushi Ilham tayi tana k'ok'arin amsa masa... Shiko har lokacin k'irjinsa bai bar bugu ba, sai tuno daren jiya yake, ya sauk'e idanunsa kan hannayen ta da k'afafunta yanda sukayi shati dai-dai yanda ya d'aure da igiya.... Zuciyar sa sosai take masa zafi gaba d'aya tausayinta ya rufesa....
Rurin da wayar Jamila ya soma ya sanyata d'an ficewa daga d'akin don tuntuni Fawaz ke kiran layinta bata d'agawa, wannan karan private number ta gani tasan shid'in ne ya b'oye lambar sa tunda bata d'aga kiran sa.....
Jamila tana ficewa Affan ya sad'ad'a gaban Ilham... Saitin fuskar ta yake waving hannayen sa, don shi gaba d'aya kyaun idanunta bai masa kama da ace wai bata gani ba..... Ganin tana k'ok'arin muskutawa yasa sa saurin matsawa baya saidai tuni ya hankad'e drawer...
Da sauri ya runtse idanunsa...
Ilham ta d'an yi jim kana tace "Addah....."
Saida Affan ya saita kansa sannan ya d'anyi gyaran murya yace da ita "Ai ta d'an fice amsa waya...."
Jinjina kai kurum Ilham tayi, itadai kam wannan murya badon Affan bane da sai tace wancan b'arawon ne...
Affan ya kuma daidaita kansa kana yace "Hope babu yanda ke maki ciwo yanzu...?"
A hankali ta jinjina masa kai, da k'yar ta iya bud'e bakinta da yayi mata nayu kana tace "Babu sai d'an kad'an...."
Jinjina kai yayi tamkar tana ganinsa yana mai k'ok'arin janta da hira dukda ba sakin jiki tayi dashi ba... Gaba d'aya abin sai yana mata banbarak'wai wai najmiji da suna Kande..... Dukda tuntuni Affan yanai masu kirki amma yau d'in ta rasa dalilin da yasa take jinsa wani iri.....
****
Idanun Jamila sun kad'a sunyi jazir domin kuwa harga Allah da ace tasan Alh Kabeer ne ke kiranta da babu abinda zaisa ta d'aga wayar.... Daga d'aya b'angaren ya kuma shek'ewa da dariya kana yace "Kitty meyasa kike tunanin zaki tsere min, kina shan mamaki koh, a ina na sami layinki...." Murmusawa ya kuma yi yayin da zuciyar Jamila ke ci gaba da tafarfasa
"Kar ki mance Kitty inada hanyoyi da dama da zan sami contact da ke, hanya mafi sauk'i Fawaz ne....."
Juyawa idanu tayi tana wani irin huci lokaci guda ta shafi goshinta kana tace "You really have no shame.... Wllhi kaji kunya, kuma abinda kake so bazai tab'a kasancewa ba.... Nasani na rasa Fawaz har abada amma kaima ka sani ka rasani har abada...."
"Shut the hell up...!" ya daka mata tsawa kana yaci gaba da fad'in "Wllhi k'arya kikeyi, ina sonki kuma dole na rayu dake A DUNIYAR MU... Jamila babban kuskuren da zakiyi shine kiyi tunanin guje min.... Nasan abu na k'arshe da baki k'aunar gani A DUNIYAR MU shine k'uncin Fawaz, wllhi idan kikayi tunanin guje min zan gaya ma Fawaz who you really are..."
Murmushin takaici tayi domin kuwa ji take zuciyarta na mata wani irin k'una lokaci guda tace "You stop threatening me, So kake Fawaz ya sani fine, but before you does, zan fad'a masa da bakina.... I don't care anymore, na riga da nasan na rasa shi for good, and now, you'll be the one to lose him, sabida nasan idan ya riga yasan wanda ya lalata min rayuwa mahaifin sa ne, zaka kasance abinda yafi tsana A DUNIYAR MU... Insha Allah bazaka sake gani na a wannan rayuwar ba domin zanyi nesa da wajen nan, zan tafi wani DUNIYAR daban and start a fresh....."
Zufa ne kurum ke faman tsartsafo masa bakinsa har yana had'i kalamai yake fad'in "Don't hang up on me... K'aramar 'yar iska wllhi tallahi kada ki kuskura ki sanar da d'ana komai... Or else I'll destroy you within a second....."
Murmushi Jamila tayi tana goge hawayen da suke zubo mata kana tace "Shege ka fasa, ka shigo bariki ta d'auki rayuwata, ina jiranka...." Daga haka d'if ta katse kiran... Lokaci guda tayi dialing layin Fawaz tana wani irin tururi da huci...
Alh Kabeer kuwa tana katse kiran a tamanin ya fice a gidan ya nufi Abubakar Tafawa Balewa University Teaching Hospital Bauchi.....
******
Sau wajen biyu ta kira bai d'aga ba, k'arshe text ya tura masa tana so su had'u su finalising matsalan dake faruwa tsakanin su.....
****
Sanda ta shigo d'akin ta samu Affan sai faman b'are ayaba wa Ilham yake yana fad'in "You know banana's good for a patient, yanada sinadarai da yawa a cikin sa... In fact best fruit d'ina kenan...."
Duk wannan zuba da yake yi Ilham bata amsa sa ba, saidai kawai murmushi take kan yi, batasan meyasa bar, amma taji dad'in hiran da yake mata sosai, ko don babu namijin da ya tab'a mata hira irin haka ne k'ilan shiyasa....
A hankali yake mik'a mata yana fad'in "Let's see ko zakiyi guessing direction d'in da hannu na yake, oya karb'a mu gani...."
Ya k'arashe fuskar sa d'auke da murmushi yana yawo da hannun sa mai rik'e da ayaban kusan idanunta...
Murmushin itama take lokaci guda ta sami kanta da bin unarnin sa, hannunta na dama ta d'aga ta shiga k'ok'arin lalub'e...
Sai murmushi mai d'an sauti yake yana kallon yanda take faman jujjuya k'wayan idanunta kana yace "There.... Yauwa kinyi kusa, saura kad'an..."
D'an dariya mai sauti take da k'aramin muryarta kana tace "Kai Ya Affan bazan iya amsa ba....."
Murmushi yake kana yace "Alright kin bada gari, toh mik'o hannun ki na d'aura maki bisa...."
Murmushin itama tayi kana ta mik'a masa hannun ta... Affan yabi hannun da kallo yanda shatin d'aurin da ya mata yayi jajazir... Tausayin ta Ya cika zuciyar sa... A hankali ya d'aura mata ayaban saman hannun ta
Ilham ta saki murmushi sanda taji ayaban saman hannun ta, a hankali ta furta "Na gode...."
Bai amsata ba sai kallon da yake faman bin fuskar ta dashi, kama daga idanunta, hancinta har zuwa bakin ta...
Jamila dake tsaye daga k'ofa tana duban su hawaye na kuma gangaro mata, ji tayi bazata iya shiga d'akin ba.... Domin kuwa wad'annan biyun sunyi mata kama da masoya.. Allah sarki Fawaz d'inta, ta rasa har abada... Cikin sauri ta juya tana mai ci gaba da share hawayen ta...
******
Marin da aka wanke Mamy dashi yasata farfad'owa had'i da bud'e idanu babu shiri.... Ihu ta soma tana fad'in "Wayyo kwarankwatsa ta fad'o min... Wayyo tawa halak'an ta sa....."
Aya tayi ma kalaman nata tana duban k'artin mutanen dake kanta d'aya bayan d'aya... Jikin Mamy ya soma rawa sanda komai ya soma dawowa kwanyar ta, baki na rawa take fad'in "Zabaniyawa ku yafe ni, Wllhi na tuba, na tuba, Wllhi zanbi Allah......"
Mari aka kuma d'auketa dashi saida jijiyoyin kunnuwanta sukayi spark
Ta kuma sakin ihu a birkice ta d'ago kai tana kallon su don ko riga babu a jikin su yanda kasan Wrestlers, uwa uba ga bak'i ga muni, itakam ko a wasan kokawa bata tab'a ganin irin mutanen ba, gaba d'aya ta birkice
Daga can gefe ta hangi Azeema kwance tamkar maras numfashi... Zuciyarta ta kuma yankewa... Tana ji tana gani aka d'ibo bokatin ruwa aka shek'a wa Azeema, lokaci guda Azeema ta tashi a birkice tana shirin surawa a guje taji an d'auketa da jahilin mari, saida ta kifa k'asa... K'ara ta saki tana rik'e kunnen ta...
Ba tareda mutanen sunce dasu komai ba sukayi ficewar su had'i da rufo k'ofar... Mamy da Azeema basu daina bin bayan mutanen da kallo ba jikin su na kyarma...
A firgice Azeema tace da Mamy, A DUNIYAR MU muke kuwa Mamy ko kuwa har an busa k'aho mun soma karb'an namu azaban ne.....?"
Jikin Mamy bai daina kyarma ba take fad'in "Azeema a ina muke.....?"
"Mamy ke zan tambaya don nima ke na biyo..... Ina bokan naku...?"
Mamy na shirin kuka take fad'in "Wayyo, wayyo Laure ce Wllhi, Laure sayar dani tayi... Wayyo ni Asma'u tawa tazo k'arshe..."
Azeema da cikinta ya kuma d'uran ruwa girgiza kai take tana fad'in "Ba ke kika shiga uku ba Mamy ni ce a uku.... Wllhi da na sani da ban biyo ki ba tunda cinikin kanki kawai akayi banda nawa...." Ta k'arashe tana d'aura hannu bibbiyu aka tana kuka....
*******
Fawaz na ficewa daga TH Alh Kabeer yana isa, hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, sai faman kiran wayan Fawaz d'in yake bai d'agawa...
Fawaz kuwa da tuni ya d'auki hanyar Air Force base sabida wani dad'i da ya mamaye zuciyar sa sanda yaci karo da sak'on Jamila cikin wayar sa, yasan Jamila tashi ce bazata iya rabuwa dashi ba kaman yanda shima bazai iya rabuwa da ita ba... Saida ya tsaya a hanya ya sayi Furen soyayya (Tsuntsun soyayya ba inji Anmunah da Mai Amada Lol)
*****
Hannayen su rik'e cikin na juna idanunsu na kallon cikin na juna yake ci gaba da fad'in "Reina I can't hide my feelings anymore, I can't deny it anymore...... From the very first time I saw you, Reina jikina ya bani you're the one.... I love you Salma, I love you with every beat of my heart, Salma I can't lie to you anymore... Even if you'll reject me, I'll still tell you the truth... Ina sonki Salma tsakani na da Allah... Ina sonki da duka zuciyata, Salma ki bani dama na nuna maki how far my love goes for you.... I love you....." ya k'arashe sanda siriyar hawaye ke fitowa daga idanun Salma, gani take tamkar mafarki ne ba gaskiya ba... Murmushin dake saman fuskar ta bai gushe ba still hawaye na gangaro mata...
Shid'inma murmushi yake yana duban fuskar ta lokaci guda sai ji yayi fuskar sa na sauk'owa kusan nata a hankali... Lokaci guda Salma ta lumshe idanunta don gaba d'aya Sojan nata ya zame mata wani sarki, k'irjinta sai faman bugu yake da sauri... Idanun Naseer k'yam akan lips d'inta sanda yaci gaba da matsowa da nasa fuskar.... Har saida suka soma jiyo d'umin numfashin juna dai-dai lokacin wayar sa ta soma ringing...
Cikin sauri Salma ta d'an kauda kai gefe had'i da matsawa baya, saidai ji tayi hannunta na rik'e har lokacin cikin nasa..
D'aga wayar yayi ganin mai kiransa still idanun sa akanta, yana rik'e gam da hannunta yake amsa wayar..
"Hello Engr ina sauraren ka... Subhanallah, kana nufin sun kewaye kampanin gaba d'aya..?"
Daga d'aya b'angaren Engr Bala yace "Wllhi Captain gasunan da gallons na petur k'ona Kampanin suke da niyyan yi, sun hana ko wani security zuwa kusan su... Hankula a tashe suke.."
Naseer ya d'an shafi kansa had'i da fuzar da iska kafin yace "Pls Engr make sure everyone is safe.. Gani a hanyata, ina zuwa yanzun nan.." Daga haka katse kiran yayi yana jimamin lamarin, duban Salma yayi da tashin hankali ya nuna sosai a fuskar ta kana ya tallafi gefen fuskar ta yace "Reina akwai matsala a Kampanin mu, suna buk'atana a wajen, zan dawo bada jimawa ba kinji koh..." Ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa
Saurin mik'ewa tayi tana dubansa itama kaman wacce zata kurma ihu idanun ta sunyi rau-rau. Cikeda shagwab'a take fad'in "Soja are you you'll be safe., ko zakaje dani.. A'a wait kodai zaka tafi da wasu sojin...?"
Murmushi yake yana dubanta cikeda jin dad'i kana ya janyota jikinsa yace "Come here..." Matse ta yayi sosai cikin jikin sa kanta dai-dai k'irjinsa, cikin wata irin sassanyar murya yake fad'in "Hakkin su ne a Kampanin, bason su bane sukayi haka, but kar ki damu kinji, insha Allah I'll fix everything, just pray for me Okay..."
A hankali ta jinjina masa kai ba tareda ta iya furta koda kalma ba, don gaba d'aya jikinta yayi sanyi,
Tana kallonsa yanda yake zura wayar sa a aljihu yana k'ok'arin ciro car keys d'insa..
Har ya kai k'ofa ya kuma juyowa yana duban ta.. Cikin sauri ya dawo ya manna mata peck a gefen kumatunta, saitin kunnen ta ya rad'a mata "I love you..."
A hankali ta lumshe idanun ta tana jin sanda ya fice, cikin zuciyar ta itama ta furta _I love you too...._
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*46*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Momy ta jima tsaye jikin k'ofa tana duban Salma dake faman shafa kumatun ta yanda Naseer ya sumbata, fuskarta sosai ya cika da annuri, kana ganinta basai ance maka tana cikin tsananin farin ciki ba.... Ganin ta cikin farin ciki haka ya sanya Momy jin dad'i sosai... A hankali ta tako ta k'araso har cikin parlorn.. Salma kam inaa batama san Momy ta k'araso wajen ba... Dab da ita Momy ta zauna tana mai ci gaba da kallonta still murmushi bai gushe saman fuskar ta ba.....
Saida dak'ik'ai suka d'an gifta kafin Salma ta kula da Momy dake zaune gefenta..... Kallon da taga Momy na mata ya sanyata jin kunya, cikin sauri ta b'oye fuskar ta cikin tafukan hannayenta tana fad'in "Momy yaushe kika fito ban kula ba...?"
Murmushi Momy tayi mai d'an sauti kana tace "Yo ina kuwa zaki kula kin lula duniyar soyayya domin ga dukkan alamu baki A DUNIYAR MU...."
Sauri bud'e idanu tayi tana duban Momyn kana tace "Dan Allah Momy.... Am I that obvious...?, Momy fah ba soyayya nake ba"
Momy ta kuma murmusawa kana ta d'an ja kumatun Salmar tana fad'in "Ai naga alama, kar dai ya maki wayo ya d'auke min ke ya kai gidan sa domin akwai karattutuka da dama da nake so muyi kafin nan kinji koh....?"
Cikeda kunya Salma ke jinjina kai kana Momy ta mik'e tana fad'in "Maza ki taso ki k'arasa girkin nan a samu akai masu asibiti koh...."
Salma ta mik'e tana amsawa da "Toh Momy..."
*******
A guje yake bin bayan Fawaz d'in dukda highway suke.... Fawaz kam baima san Dad d'in nasa na biye dashi ba sai faman murmusawa yake yana tuno abar k'aunar sa Jay.....
Alh Kabeer a d'ari da tamanin ya kwali BMW d'insa yana huci yake buga steering wheel yake fad'in "Faster! Faster!!..." Yanda kasan wani zararre haka yake faman magana shi kad'ai....
A dai-dai Amo barrack ya samu ya kusan cimma Fawaz....
Daga cikin mirriro Fawaz ke hango mota tamkar ta mahaifin sa na biye dashi.... Mamaki ya d'an kamasa... Aiko ko shakka babu mahaifin sa ne, a hankali ya soma slow har ya paka gefen kwalta....
*******
Shareefah ta kuma duba agogon dake manne parlorn ya nuna shida saura dak'ik'ai, har izuwa lokacin babu Mamy babu Azeema babu dalilin su, gashi ta kira wayoyin su yafi sau abinda yafi basa shiga... D'an jim tayi had'i da tab'e baki cikin zuciyarta tana tunanin k'ilan yanzun haka wani abin suke k'ullawa tunda tasan Mamy da Azeema ba'a rabasu da sharri, yanzu haka wani abin Mamy ke shiryawa Azeema ta take mata baya don warwarewa, those two baka gane masu....
Shashantar da zancen tayi don tasan anything bayan magrib zasu dawo gida... Kitchen ta nufa don neman abinda zata saka cikinta....
******
Da mamaki Fawaz ke duban mahaifin nasa wanda ke faman murmushi babu k'akk'autawa, kana ganin murmushin basai ance maka yak'e bane...
"Dad lafia dai koh..."
Alh Kabeer ya k'araso kusan Fawaz d'in yana mai ci gaba da murmushi yake fad'in "La... Lafiya Son, ai naje hospital ne aka ce min ka fice.... Son akwai magana mai muhimmaci ne da nake so muyi...."
Fawaz dai bai fahimci kan mahaifin nasa ba, d'an murmusawa kurum yayi kana yace "OK Dad, idan na dawo gida zamuyi maganar...."
Saurin dafasa Alh Kabeer yayi kana yace "No.. No Son, it has to be now, come on let's go home okay....."
Still kallon mamaki Fawaz ke binsa dashi, this is totally strange.... D'an saita kansa yayi kana yace "Dad pls ina abin yi yanzu, I promise you daga can I'll come straight home sai muyi maganar kaji..."
Alh Kabeer girgiza kai ya kuma had'i da saka fuskar tausayi kana yace "Haba Fawaz, na rok'e ka abu kace kanada wani abu mai mahimmacin sama dani...." Lokaci guda kuma ya soma magana fad'a-fad'a...
"Alright, fine... Akan wancan bazawarar ce, akanta ce kake cewa bakada lokaci na... Fawaz ban amince ka nemi yarinyar ba balle takaika ga maganar aure... Ka bud'e idanunka sosai, ta fika samun experience na rayuwar aure, aside from that bata k'aunar ka tsakani da Allah, tunda tak'ika sabida mahaifiyar ka...."
Fawaz ne ya katse sa da fad'in "Dad please enough of this already, Jamila ba irin wad'an nan matan bane, da sannu zaka fahimci kyakkyawan zuciya da take dashi...sannan Dad ina sonta a haka koda ta tab'a aure, koda yara nawa ta haifa... What matters is that I love her... Dad please kar mu fara haka da kai, kaje gida kawai idan na dawo sai muyi maganar...."
Rai b'ace Alh Kabeer yace "Fawaz nace bazaka auri yarinyar nan ba... I won't allow you to make decisions anyhow, aure wani abu ne da yake buk'atan hangen nesa, and you are too young for that, dole a taimaka maka da hango abinda zai maka kyau...." Lokaci guda kuma ya d'an sassauta murya kana yace "Come on Son, don't give me that look, see we're talking about your future here, haba Fawaz kadai san bazan so naga wani abu na samun ka ba.. What if tsohon mijinta start harassing you.... Kar ka jefa kanka wani abin daban Son, think about it...." Ya k'arashe kaman mai shirin yin kuka....
"Speaking of that imbecile, Dad wllhi idan ya kuma tak'ura wa Jamila ma wllhi sai na d'aure shi, zan ji dad'i idan ya soma harassing d'ina.. Idan ba'a d'auresu gidan yari Mazaje masu gallaza wa mata bazasu daina ba...." ya d'an sassauta murya had'i da rik'o hannun mahaifin nasa yace "Dad I thought very well kafin na soma nemanta, sannan ka mance sunce love has no conditions.... Kar ka damu Dad my eyes are widely opened, and I can see very brightly.... Nasan ka damu dani ne baka son duk wani abin da zai sameni, ni namiji ne Dad dole na fuskanci challenges na rayuwa, dole na zama strong ba ko yaushe bane iyayen ka zasu kare ka.... Dad kaje gida pls, ni na wuce...." Sai faman duba agogon sa yake ga kiraye kirayen magrib da aka soma, ko sauraren Alh Kabeer bai kuma yi ba ya shige motar sa.....
Tsaye kawai yayi yana kallon bayan motar Fawaz har ta b'ace ma ganin sa, bai zaci abin zai kai har haka ba, bai zaci Fawaz bazai biye umarnin sa ba, bai zaci Fawaz na son Jamila har haka ba.... Sanda yake furta masa yana k'aunarta akan idanun sa ji yayi tamkar ya kai masa tokari saidai bazai iya hakan ba.... Inama wani ne ba Fawaz ba wllhi yau da saidai gawan sa..... Dafe kansa da ya masa nauyi yayi ya shiga sakin k'ara lokaci guda ya dinga dukan tayan mota da k'afafun sa.... Mutane masu wucewa kuwa sai kallon sa suke kaman sabon kamun hauka.... Yana nan tsaye a wajen yana haukan sa wayar Maina ya shigo masa.... Da ashar ya soma d'aga wayar sabida zuciyar sa dake tafarfasa....
Abinda Maina ke sanar dashi ya sanyasa tsayawa cak, zuciyar sa na sabon bugu....
"This is hell on earth...." Ya fad'i yana kama sumar kansa... Fuzar da iska yayi kana yace "Kana jina, kar ka bar wajen, ci gaba da b'uya har sai na k'araso...." Daga haka katse wayar yayi ya shige mota yana mai turawa Jamila sak'o don yasan bazata d'aga wayar sa ba...
_You better get rid of my Son in the best way, if not zan kashe sisters d'inki including your daughter.... Love you Kitty.._
Ta karanta sak'on yafi abinda yafi hawaye na kuma gangarowa daga idanunta.... Ta jima tana zaune can bayan asibitin saman wasu kujeru don gaba d'aya batama san anyi magrib ba... Fawaz kuwa koda ya iso kai tsaye masallaci ya wuce ya gabatar da sallan magrib nan ya had'u da Affan, sai faman hira suke a hanyar su ta dawowa daga masallacin... Su duka biyun cikin farin ciki suke...
Momy da Salma suka tadda a d'akin Ilham d'in, bayan sun gaisa gaba d'aya Fawaz yake tambayan Jamila, nan Momy ke sanar dashi ta d'an fice amma tana tunanin batayi nisa ba zai iya kiran wayar ta, jinjina kai yayi yana amsa wa Momy...
Affan ma sallama ya masu zai wuce, saidai kafin ya fice saida ya k'arasa har gaban gadon Ilham, murya can k'asan mak'oshi wanda yasan ita kad'ai ke sauraren sa yace "Patient zan wuce gida, promise me bazakiyi kukan shan magani ba, don idan kinyi daga gidana zan jiyo sautin kukan ki, sannan hakan ka iya hanani barci kinsan bana son hayaniya...."
Murmushi kawai Ilham take kafin ta girgiza masa kai kana tace "Bazan yi ba...."
Affan yace "Promise..?"
Jinjina masa kai tayi ba tareda tace komai ba...
Salma da Momy dai kallon ikon Allah suke fuskokin su cikeda murmushi.... Momy ce tayi gyaran murya tace "Wai ni meye ake k'ullawa ne ba'a so muji....?"
Sai sannan Affan ya d'an d'ago yana shafa sumar sa yake murmushi kana yace "Momy sallama muke ba komai muke k'ullawa ba right patient..?"
Ilham dai bata ce komai ba sai faman murmushi da take tana wasa da 'yan yatsun hannayen ta..... Salma ma sai faman murmusawa take, salon Affan da Ilham ya burgeta....
Momy ta Kuma murmusawa kana tace "I naga alama ai.... Toh maza zo ka wuce saida safe...."
Murmushi yake yana kuma juyowa yana duban Ilham kafin ya fice.... Momy da Salma suka kalli juna had'i da yin murmushi... Gaba d'aya yau Salma jinta take cikin farin ciki, finally Naseer ya fayyace mata zuciyar sa, uwa uba ga Affan sam yanzu bata gabansa, da alama gina nasa soyayyan ya fara a tushiya mai k'wari, Allah yasa hasashen su ya tabbata Affan da Ilham soyayya suke sai tafi kowa jin dad'in hakan, domin Affan mutumin kirki ne....
*******
Daga can ya hangeta tana zaune saman kujeran har lokacin kuka take..... Hannun sa rik'e da furen sa yake takawa a hankali har ya iso yanda take...
Jikinta ya bata Fawaz yana wajen... Saurin d'ago kai tayi tana dubansa.... Lokaci guda kuka ya kuma kufce mata.....
Har cikin ransa yake jin zogin kukan nata, a hankali ya durk'usa gabanta yana duban fuskar ta.... Jamila tayi saurin mik'ewa tana goge hawayen ta take fad'in "What are you doing Fawaz, ka tashi pls....."
Kallonta yake har lokacin bata daina share hawayen dake gangaro mata ba....
Mik'ewa tsaye shima yayi kana yace "Jay kinsan bana son ganin ki cikin tashin hankali don Allah ki sanar dani meke faruwa....."
K'ak'aro murmushi Jamila tayi kana tace "Fawaz I want to tell you nothing but the truth.... Fawaz wllhi sonka ne banayi, bazan iya soyayya da kai ba ba don komai ba sai don bana k'aunar ka....."
Murmushin yak'e Fawaz yayi kana yace "You kidding right? Jay pls don't break my heart.... Pls kar kisa nayi regretting dawowa k'asar nan... Nasan kina sona Jay, kina k'aunata kawai wani dalili kike dashi wanda nasan bazai wuce jinyar mahaifiyata ba.... Jamila don Allah kada kiyi punishing soyayyar mu da dalilin da bai kai ba....." Ya d'an kuma takowa kusanta murya na rawa yake ci gaba da fad'in " Wani abu na maki..? Ki sanar dani pls... Where have I gone wrong? Tell me, I'm ready to mend my path.... But pls kar kice mu rabu da juna... Jay bazan iya ba....."
I zuwa lokacin kukan Jamila yayi yawa.... D'ago fuskar ta tayi tana wani irin huci sanda take tuno fuskar mahaifin Fawaz kana race "You must.... Dole ka rabu dani Fawaz, ko ana soyayya dole ne, kar ka sake zuwa wajena, kar ka sake nemata, it's over between us....." Daga haka sa kai tayi zata shige... Lokaci guda Fawaz ya tsare gabanta huci kawai yake yana dubanta, bata tab'a ganinsa cikin irin yanayin ba, take ya koma mata farkon Fawaz d'in da ta had'u dashi a asibiti...
"Tell me your reason, tell me why, why all this... Why the sudden change of mind....just tell me....!!!" Cikeda fad'a yake maganar...
Kuka take kanta a k'asa domin gaba d'aya fuskar Fawaz ta koma jazir sabida tsananin b'acin rai...
A hankali take fad'in "I'll tell you why .. It's because I love you, and I don't want you to get hurt.... Fawaz banaso kayin engaging kanka cikin matsaloli na, baka cancance ni ba.... Don Allah ka tafi ka nemi dai-daidan ka...."
"You still haven't answered my question... Jamila ki fad'a min meye dalilin ki? Tsohon mijin ki ne....? Is he still harassing you....? Tell me, shi ne dalilin ki....?"
D'ago fuska tayi tana dubansa ido cikin ido, hawayen dake idanunta sun bushe tangararau, murya a dake take fad'in "Fawaz I'm a prostitute, ina tarayya da maza da dama, baka cancance ni ba.... Ka fice daga rayuwata pls...."
Kallon mamaki yake binta dashi ba tareda ya iya motsa koda d'an yatsan sa ba....
Lokaci guda kuma ya saki murmushi kana yace "Wai duk don ki rabu dani ne kike danganta kanki da mummunar sab'o irin haka, Jay na sanki wllhi nasan bazakiyi abinda kike fad'i ba... Karma ki soma......"
Katse sa tayi da fad'in "I'm serious Fawaz, and this is the truth.... Kana iya tambayan Dad d'inka zai fad'a maka komai in details, so stay away from me....." Daga haka sa kai tayi zata shige ya kuma saurin tare gabanta yana girgiza kai, cikin wani irin murya yake fad'in "What did you just say....? Mahaifina, Dad d'ina... But why him....? Tell me why....?" Ya k'arashe idanun sa sun firfito waje sosai...
"Sabida yasan komai, shiyasa zai sanar dakai komai...." Daga haka bata kuma bin takan Fawaz ba tayi shigewarta tana k'unshe kukan dake neman kufce mate......
Bibbiyu Fawaz ya soma gani, duniyar ta shiga juya masa, sama ya koma masa k'asa, gabas ta koma masa yamma yayinda kudu ta koma masa arewa....
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*47*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Daga can bayan motoci yanda suka lab'e suke hangensu, Naseer sai k'ok'arin kwantar wa jama'an hankali yake yana fad'in insha Allah za'a biya kowa hakkin sa, Santana Corporation zatayi komai wajen ganin ta sauk'e hakkin d'inbin jama'an dake kanta...
Da k'arfin gaske dandatson jama'an suka soma fad'in "K'arya ne, bama yi, a biyamu kud'ad'en mu yanzun nan.... Santana Corporation Kampanin zalunci ne, an karb'a kud'ad'enmu da sunan za'a biya mu ninkin baninki ba'a biya mu ba.... Wllhi babu mai hanamu k'one wannan kampanin wanda ake aiwatar da zalunci da son zuciya cikinta...." Cikin muryoyi daban-daban suke ci gaba da fad'in "Santana Corporation Sai mun k'one....!!!"
Murmushi Alh Kabeer yayi kafin ya dubi Maina yace "Dama ta samemu, lokacin k'arasa Naseer yazo,..."
Da mamaki Maina ke dubansa kana yace" Your company's in great danger kana maganar daman halak'a Naseer tazo, bazakace damar hallak'a ka tazo ba.."
Murmushi Alh Kabeer yayi yana shafan hab'arsa wanda dama d'abi'arsa ce kana ya dubi Maina yace, "Da Naseer zanyi amfani na kub'utar da Kampani na, da Naseer zanyi amfani na kub'utar da kaina..."
Maina ya girgiza kai kana yace "Mai gida ban fahimce ka ba...."
Murmushi Kabeer ya kuma yi kana yace "Yo ina zaka fahimce ni kuwa tunda toshesshiyar kwanya ce da kai.... Abinda nake nufi a nan... Mutanen nan hakkin su da na amshe a Kampanin nan suke nema, idan sun k'one Kampanin that means bazasu sami abinda suke nema ba, da ace zasu sameni su k'one ni da yafi masu, sabida ni nasan akasari daga cikin su babu d'igon imani cikin zukatansu tunda ni ne nan nayi deal d'in dasu, duk son abin duniyar su yasa suka fad'a trap d'ina, kud'in ruwa suke so basu samu ba sannan babu uwar kud'in su, kaga da su k'one Kampanin suma su rasa ai gwara su k'one ni...."
Maina ya soma murmusawa don tuni ya d'ago uban gidan nasa...
"Kaga sauk'a zakayi ka kutsa tsakankanin mutanen nan, tunda gari yama soma duhu bazai hango ka cikin dandatson mutane ba... Pretend kaima akwai hakkin ka ciki, kasan yanda za'ayi ka shawo kansu a k'one Naseer instead of the company...." ya k'arashe yana k'ok'arin kunna sigari...
Maina ya d'an dubesa kana yace "Mai gida anya wannan shawari tayi kuwa, Naseer ba Soja ne waya kawai zaiyi soji sumana diran mik'iya a nan...."
Tsaki Alh Kabeer yayi kana yace "Kai mugun gara ne wllhi, banda abinka ai tunda yazo nan wajen faran hula ne shi ba Soja ba, yanada hankali ai bazaiso reputation na family d'insa ya b'aci a idanun 'yan uwansa Soji ba, this is different issue, bazai involving aikin sa ba, nasan Naseer farin sani kawai kayi yanda nace mu rabu da shege mu sami sauk'in kashe matar sa....."
Maina ya murmurs kafin yace "Haka ne Mai gida, na yarda ba kullum bane kanka baya kawo wuta, yaukam ya kawo, domin ko Innah taji wannan k'ok'ari da kayi sai ta jinjina maka...."
Murmusawa kurum Alh Kabeer yayi yana kuma zuk'an sigarin sa kana yace "Kasan yanda za'a yi kana d'orasu dokin zuciya ka b'ace ka bar wajen nan...." Yana gama fad'in haka yayi key wa motar sa gudun kada wani ya gansa, tuni ya bar wajen.....
********
Kasa cin abincin da aka kawo masu sukayi Mamy har lokacin bata daina hawaye ba... Azeema dai dubanta kurum tayi ta tab'e baki kana tace "Amma Allah ya isana wllhi Mamy tsakani na dake, da ace ban biyoki ba da yanzu ina gida, wayasan uwar me za'a mana yanzu, har yanzu babu wanda ya shigo yace damu ga makomar ku...."
Mamy dai mugun kallo kurum take watsa wa Azeema kana ta rarumo crutches d'inta tana nuna Azeema dashi take fad'in "Na rantse kika kuma min magana sai na runtuma maki sandar nan aka... Wani shege yace ki biyo ni, madalla maganin makira irinki kenan.... Ke ba mabud'in sharri ba gashi yau sharri ya bud'e ki.... Kuma Laure na shigowa zansan yanda zanyi na fice na barki a wajen nan, kinga na rabu dake cikin ruwan sanyi....."
Murmushi Azeema tayi kana tace "Mamy kenan, ai nida kika gani ba haka kurum Allah ya kawoni zama gabanki ba, mugun hali da mugun zuciya irin naki shiyasa Allah ya baki kyautana, na kuma zame maki alak'ak'ai na zame maki k'arfen k'afa... Mamy da tuni kin tuba kinbi Allah wllhi da tuni Allah ya kawo maki hanyar rabuwa dani cikin ruwan sanyi tunda k'aunata ce bakyayi.... Duk barikanci na da son abun duniyata wllhi bazanyi shirka ba bazanyi kisa ba.... Amma Mamy ke kinayin duka wad'annan manyan laifuka, gaba d'aya kin koma arniya sabida son duniya, kin zab'i ki zamto kafura ki kashe mijinki uban 'ya'yanki da kuka riga kuka zamto abu guda sabida son duniya.... Duk irin mugunta da ha'intar da kika masa a baya bai isheki ba sai kin nemi rayuwar sa, Ke gaba d'aya Allah na nuna maki ishara baki hankalta sabida zuciyarki ta riga tayi nisa wajen kafurce wa ni'imomin da ubangijin ki ya maki.... Abu na farko Mamy gidan gonar da kika ci buri akansa kika nakasa mijin ki a sabida ki mallake sa Mamy baki mallaki wannan gidan gona ba, sai gashi kina ji kina gani ta k'one k'urumus gaba d'aya da abinda ke cikinta, wannan bai isheki ishara ba.... Kika fad'i kika karye a k'ok'arin koran Salma da kike daga gidan, nan ma baki hankalta ba... Bacin wannan mijin da kikaci burin d'iyarki ta aura, a kunnuwanki ranar auren akayi announcing auren da wata daban, nan ma Mamy hankali da tunanin tuba basu zo maki ba... D'anki da kike jin dad'in shiriya tazo masa a idanunki ya koma mugayen d'abi'unsa, duk baki hankalta kince bari ki gyara kanki ba watak'ila Allah yaji k'anki ya sassauta maki lamuran ki.... kika so d'aukan rayuwar mijin ki duk a sabida duniya,... Daga k'arshe aminiyarki da kike wannan hark'a na sab'awa Allah ta maki butulci ta tona maki rami kika apka ciki, duk baki hankalta ba, har kina iya bud'e baki kina cewa tazo ki saida mata ni ke ki tsira ko.... wllhi Allah Mamy Allah na sonki tunda gashi tun A DUNIYAR MU yayita nuna maki ishara ki tuba ki bisa kin kasa fahimtar hakan, don wasu Allah talala yake masu sai anje chan.... Mamy tun da sauran numfashin ki A DUNIYAR MU, ina mai shawartan ki da ki tuba kibi Allah domin shikad'aine zai tseratar dake daga wannan mugun hannu da muka riga muka shige ciki...."
Jigum Mamy tayi tana duban Azeema ba tareda ta iya furta koda kalma ba, duk abubuwan da Azeemar ta fad'i suka shiga yawo a kwanyarta... Tabbas haka ne duk abinda ta fad'i, duk wannan gwagwarmaya da take har yau burin nata bai cika ba, ga tarin zunuban dake kanta, gashi ita ba hutawa tayi ba... 'yan kud'ad'enta duk ta tarkace su ta baiwa Laure, ga abinda Laure ta mata domin a halin yanzu batama san meye makomar rayuwar ta ba... Lokaci guda hawaye suka shiga gangarowa daga idanun Mamy, ta tuna a baya yanda suke zaune cikin jin dad'i da mijinta da 'ya'yanta, haka kurum Laure ta zugata ta nakasa mijinta ta mallaki gidan gonar sa, tun daga wannan lokaci gashi sai ta rasa nutsuwa gaba d'aya kullum a birkice take.... Gaskiya Laure ta gama cutan ta da ta jefata a wannan hark'a gashi yanzu ta juya mata baya.... Hawaye suka ci gaba da kwararo mata sanda ta tuna mijinta na kwance a asibiti rai hannun Allah... Allah sarki Ali Safwan miji na k'warai sannan uba na gari ma yaranta, ta rusa gidanta da kanta ta halak'a kanta da hannayen ta, yanzu idan Daddy ya mace a haka hakkin kisan sa na kanta... Ina zatakai wannan d'umbin zunubi.... Lokaci guda kuka ya kuma kufce mata.... Bud'e k'ofar da akayi ya sanyata had'iye kukan ta..... Lokaci guda ta d'ago idanu tana kallon wanda ya shigo... Aminiyarta Laure ce da wasu k'artai biyu....
*******
Cikin dandatson mutanen Maina yake faman kustawa yana mai ci gaba da fad'in "Kar mu yarda, mu k'one shi, azzalumai ne, idan muka k'ona Kampanin sunyi riba, shi zamu k'ona mu fanshe dukiyoyin mu, idan muka k'ona kampani mu k'ona harda kud'ad'en mu amma idan shi muka k'ona dole sauran jama'an Kampanin suji tsoro su biyamu hakkin mu.... Mu k'one shi! Mu k'one shi!! Mu k'one shi!!!..."
Lokaci guda wasu daga cikin mutanen suka shiga ele suna wurgi da duk abinda suka rarumo suna fad'in "Gaskiya ne mu k'one shi, azzaluman mutane barin irinsu A DUNIYAR MU babu amfani..!!!"
Naseer sai faman kaucewa yake Engr Bala na k'ok'arin karesa, securities na Kampanin ma suka k'araso suna iya k'ok'arin su amma kunsan ance sarkin yawa yafi sarkin k'arfi...
Engr Bala fad'i yake "Captain gawara mu kira cops this is getting out of hand.... We can't deal with these people,.."
Girgiza kai Naseer yake yana fad'in "Engr bazasu k'ona ni ba, saikace garin da babu addini, duk rashin imanin su bazasu k'ona mutum ba, Yaya shi ya saka mu a wannan matsala, sannan idan mukayi involving cops zai iya zama court case, ni kuma nafiso nasan yawan kud'ad'ensu idan zamu iya biya koda a hankali a hankali ne, idan ya zama court case akawi matsala banaso hanakalin Family na ya tashi musamman Innah ta da k'anwata Lubna, I'm doing this for the two of them, gashi da alama wad'an nan mutanen bazasu bada had'in kai mu ma yi maganar a tsanake ba...."
Engr ya shafi goshinsa kana yace "Alh Kabeer ya wuce tunanin ka Captain, amma kam ya sha jefa Kampanin nan cikin tarzoma, kayi hak'uri dukda d'an uwanka ne amma dole a fad'i gaskiya, ba don kai ba da na cire dukiyata a Santana Corporation, amma lura da nayi bai kamata a bar kampanin hannun gurb'atacce irinsa ba shiyasa na janye k'udiri na, sannan kaima kana buk'atan taimako, you can't do it kai kad'ai, dole ka sami wanda yama Kampanin faran sani ya taya ka....."
Jin mutanen sun nufo su gadan-gadan don sunfi k'arfin securities d'insu ya sanya Engr saurin ciro wayar sa ya shiga dialing layin abokin sa DPO Ayuba...
*******
Ikon Allah ne kawai ya kai Fawaz gida, har lokacin duniya bata daina juya masa ba.... Ya kasa yin tunani k'wara d'aya, abubuwan da sukayita faruwa lately sune suketa yawo a kwanyarsa, ya tuna sanda yayi introducing Jamila wa Mahaifin sa, ya tuna yanda ta kasa d'ago kai ta gaida mahaifin nasa,.... Ya tuna irin maganganun da mahaifin nasa ya fad'i gameda Jamilar.... Wani irin k'una, zogi da rad'ad'i zuciyar sa ke masa wanda da ace zai samu yayi kuka da sai yafi masa sauk'i.... Da k'yar ya iya ciro k'afarsa da suka masa nauyi daga cikin mota, kallo yake kan faman bin gidan nasu dashi.... Ya dubi yanda Dad d'insa ke ajiye motar sa bai ga motar ba, a hankali yaci gaba da takawa har ya isa sashen mahaifiyar sa...
Daga bakin k'ofa yayi tsaye yana dubanta tana zaune cikin kujera tana kallon shirin animation a tashan yara.... Kallonta kawai yake sai sannan hawaye suka shiga gangaro masa.... Tausayinsu su duka biyu daga shi har ita ya cika masa zuciya.... A hankali yake takawa har ya isa gareta.... Flower d'in dake hannun sa ya mik'a mata still hawaye na gangaro masa... Itama d'in lokaci guda hawaye suka shiga zubo mata, ta shiga sa hannayen ta gaba d'aya tana share ma Fawaz nasa hawayen.... Lokaci guda ya kuma bursting cikin tsananin kuka had'i da rungumeta yana mai fad'in "I love you Mum, I love you so much.... I know you went through alot... you've been suffering for all your life.... This life is so unfair why mum, why did you choose that Man... why? Why please... Mum meyasa kika zab'a min shi a matsayin uba, meyasa kika zab'i ya zama mahaifina.... Ki amsa min, meyasa, meyasa please.....!!!" Kasa ci gaba da magana yayi sai k'ank'ame mahaifiyar sa da yayi yana wani irin kukan da bai tab'a irinsa ba a rayuwar sa.....
********
Maina tuni ya silale ya bar wajen, hankula sun kuma tashi, duk k'ok'arin securities d'in ganin sun hanasu abinda sukeda niyya sun kasa, tuni mutanen nan sun sumar da Engr Bala, Naseer kuwa jini sai bin hancinsa yake, sai faman d'auresa da igigiyoyi suke jikin wata k'arfe.... Abun da yake gani na shirin faruwa dashi yayi mugun girgiza sa, bai zaci A DUNIYAR MU akwai mutane da zuciyar su ya bushe har haka ba... Da gaske suke watsa masa petur suna k'ok'arin banka masa wuta.....
*Sameena Aleeyou...*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU*🌖🌖
*48*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Bakin Mamy na rawa ta kuma duban yanda Laure ke yamutsa fuska tana binta da kallon wulak'anci.... "Laure ina kika kawo ni, ina ne nan, nida mukayi dake zamu tafi bakin border wajen boka nakan tsauni, haba Laure kar kimin haka, ki tuna kalan alkhairan da suka faru tsakanin mu a baya, Laure kar ki rabani da dangi na.... Dan Allah ki bar mu tafi insha Allah bazan kuma neman komai daga gareki ba...."
Dariya Laure tayi tana kuma ckala cingam tana kwaiwayan maganar Mamy kana tace "Banza makashesshiya ke ai anjima ba'a mai kwanyar sukunun ba irinki Ma'u, sam bakida tunani kanki a toshe take, toh yanzu da kike min dad'in baki ce maki akayi zan barki ki tafi.... Daga ke har d'iyar taki babu yanda zakuje, kabarinku ne kuka riga kuka shigeta, Ma'au ke kika tona ramin da hannun ki... Waye zaiji tausayin macen da bata tausayin mijinta, banda wauta irin taki, ai da ace nice na sami daman da kika samu a rayuwa toh kuwa shakka babu da hankalina kwance.. Ma'u a komai kinfini ci gaba wannan dalili yasa na lalata rayuwar jin dad'in da kike ciki tunda na lura sam ni bazan sami irinsa ba... Loving children and a caring husband... Kikayi watsi da ni'imomin ki kika biye min, na kaiki na baro ki.... Sannan yanzu haka zancen da nake maki Asma'u wllhi na riga nayi kud'in kanki Allah ya k'aro min wata a bulus...." Ta k'arashe tana duban Azeema dake faman watsa mata kallon tsana...
Mamaki da tsoron duniya suka kuma cika zukatan Azeema da Mamy...
Gaban Laure Azeema ta k'arasa tana watsa mata kallon tsana da k'yama take fad'in "Amma ke bazakiji k'amshin Aljannah ba... Laure wllhi ke 'yar uwata ce... Wani irin mugunta da hassada ne haka da sukayi tasiri zukatan mutane A DUNIYAR MU.. A dalilin hassada da k'eta kika jefa Mamy a gurb'ataccen rayuwa, kika tarwatsa gida gaba d'aya.... Wllhi Allah bazai barki ba domin kuwa tun daga..."
Katse ta Laure tayi da fad'in "Rufe min baki k'aramar 'yar iska, ke yaushene kika san Allahn, awho wa'azi zakimin shegiya gantalalliya karuwa... Ai jinin Ma'u babu na k'warai dukanku kafurai ne... Na kashe ku na rage mugun iri A DUNUYAR MU, yo me amfanin barin macen da take neman rayuwar mijinta.... Kuma duk abinda nayin nan da yarda Ma'u nayisu, da ace bata biyeni ba da babu abinda ya faru... K'aramar yarinya ce ita da har za'ace ni na lalata ta, dama tun can a lalalacen ta take muka ci gaba da watsewa tare, yau kuma reshe ta juye da mujiya wllhi wllhi na amshi kud'ad'en kayukan ku, nan da kwana uku za'a wuce daku Ibadan, idan taurin kanku yayi yawa a guntulesu tun daga nan... Musha romon gangan jiki...." Ta k'arashe tana mai fashewa da dariya...
Girgiza kai Mamy ta shiga yi hawaye na kuma gangaro mata, Azeema ma hawayen take, gaba d'aya basu tab'a nadaman sab'awa mahallicin su da sukayi a baya ba irin ta yau, inama zasuci gaba da rayuwa su mik'a wuyarsu ga mahalliccin su, lallai duniyar su abin tsoro ce, mai coked tarin abubuwan Al'ajabi...
Mamy ce ta dafa crutches d'inta tana mai ci gaba da zuban hawaye har ta k'arasa gaban Laure da k'artai suke tsaye bayanta tamkar dogarai kana ta rusuna gaban Laure ta soma fad'in "Laure na rok'i arzikin ki, ki k'yale Azeema ta tafi, tunda cinikin kaina kawai kikayi, ki k'yale 'yata ta tafi don Allah Laure kada ki cutar da ita.... Na sani abubuwan da nayi ne Allah ke nuna min ishara, ban kashe mijina ba gashi na tona rami na jefa kaina ciki, Alh Ali bawan Allah ne, duk abinda na masa sai Allah ya saka masa tun daga nan duniya, na nakasa sa, nima Allah ya nakasa ni, nayi yunk'urin kashe shi banyi nasara ba sai gashi ni ce zan mutu.... Bazan gushe ba ina rok'on ubangijina gafara a iya kwanakin da suka rage min.... Laure ki duba girman Allah ki k'yale Azeema ta tafi...." kuka yaci k'arfin Mamy... Lokaci guda Azeema ta k'araso ta rungumeta tana kuka sosai itama take fad'in "Mamy bazan tafi na barki a wajen nan ba... Idan kinga na tafi toh kuwa ko shakka babu tareda ke ne.." Ta d'ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Laure take fad'in "Dan Allah ki bar Mamy ta tafi, ki bada kaina a maimakon nata, kar ki rabata da iyalanta... Don Allah ki k'yaleta ta tafi.... Mamy tanada miji da 'ya'ya, zaki jefa mutane da dama cikin k'unci a dalilin rashinta, tunda ni ban ajiye kowa ba don Allah ki kashe ni a maimakon ta...." Ta k'arashe hawaye sosai na zuba a idanunta....
Dariya Laure ta kwashe dashi had'i da yin shewa kana tace "Eh lallai yau ina ganin salo ni Laure, kuce wasan kwaikwayo kuka soma, munafukan banza 'yan iska har yaushe kuka fara son juna.... Aikin banza aikin wofi..." Ta kuma jan wani tsaki kana ta dubi murtuk'ek'en gefenta tace "Steven inaso a masu aski right this very moment, ya kamata a soma preparation tun yau..." Daga haka ficewa tayi ba tareda ta kuma duabansu ba....
Mamy baki sake take duban Laure har ta fice ta kuma duban k'aton da aka ce ya aske masu suma cikin rashin yarda.... K'ank'ame juna sukayi daga ita har Azeema suka tak'ure waje guda abin tausayi.... Kan su ankare k'aton nan ya hura wata garin hoda a d'akin, nan take suka soma tari suna shid'ewa, daga nan basu kuma sanin yanda suke ba.....
*******
Sosai Naseer ya galabaita, suna k'ok'arin cinna masa wuta DPO da wasu abokan aikin sa guda biyu suka k'araso wajen.... Nan take suka kora mutanen suka hanasu abinda sukayi niyya, Naseer kam sosai ya galabaita jikin sa duk jini ga uaban warin man petur da yakeyi.... Cikin sauri suka shiga kwance masa d'aurin suna masa sannu.... Da k'yar yake iya bud'e baki yana amsa su don ba k'aramin jin jiki yayi ba.... Lokaci guda Naseer ya k'arasa wajen Engr da k'yar ya shiga jijjiga sa.... Polisawan kuwa sai faman clearing wajen suke...
Da k'yar Engr ma ya bud'e idanunsa da suka masa nauyi ga kansa bai daina masa zogi ba don tuni sun fasa masa goshi....
Engr ya dubi Naseer yace "Captain are you alright...?"
Jinjina masa kai Naseer yayi da k'yar yana kama gefen hak'ark'arinsa dake masa zogi kana yace "What about you..?"
Shima jinjina masa kan yayi kana yace "Babu komai I'll be fine...."
Dai-dai lokacin da DPO Ayuba ya k'araso yanda suke... Sannu ya shiga yi masu yana tambayar su lafiyan jikinsu, kana ya d'an dubi Naseer dake faman tattamke idanu yace "Captain ya kamata mu k'arasa station kayi filing complaint..."
D'an girgiza kai Naseer yayi had'i da k'ak'aro murmushi kana yace "Kar ka damu officer, I'll fix this insha Allah.. Kawai tsaro za'a k'ara a Kampanin har mu samu su yarda mu negotiating dasu..... Mun gode sosai DPO.." Ya k'arashe yana mik'a wa DPO hannu da k'yar...
Engr dai sai faman share jinin goshinsa yake yana sauraren tattaunawan DPO da Naseer.... Shikam da ta nashi ne da kawai Naseer ya shigar da yayan sa k'ara tunda duk shine ummul haba'isan wannan tarzoma, har ake neman rayukan su, amma yasan Naseer mutumin kirki ne wanda baison tashin hankali, koda wani ne ma ba Yayan sa ba bazai shigar da k'ara ba balle kuma Yayan sa....
*******
Ya jima yana kwance cinyar mahaifiyar sa yana jero mata tambayoyin da yasan shakka babu ba amsa masa su zatayi ba.... A hankali ya mik'e ya nufi sahsne sa ya kulle kansa, don gaba d'aya haushin kowa yake ji, ji yake ya tsani kowa a duniyar musamman 'yan gidansu... Yayi da ya sanin kasancewa a wannan Family, yayi dayasanin dawowa Nigeria, ji yake mutuwa yafi masa sauk'i da wannan rayuwan k'unci da yake ciki.... Inama Allah ya d'auki ransa ko zai huta, inama baizo duniya ya tarar da wannan abu mafi k'unci da muni ba.... Mahaifin sa.. Ubansa mahaifi....
Lokaci guda kuma ya kuma tak'urewa can k'arshen d'akin had'i da matse kansa tsakankanin gwiwoyinsa ko tunanin zai bar kwanyar sa da zuciyar sa....
*******
A b'angaren Jamila ko zarafin komawa cikin asibitin batayi ba tayi wucewarta gida had'i da kulle kanta a d'aki ta shiga rusa kuka tamkar wacce aka sanar da ita ranar mutuwar ta... Nadaman rayuwar da tayi a baya ya cika mata zuciya.... Lokaci guda tunanin mahaifan ta yazo mata, kuka take sosai tana girgiza kai take fad'in "Baffah Inno don Allah ku yafe ni... Ku gafarce ni ko zan sami sauk'i A DUNIYAR MU....." Kuka ya hanata ci gaba da maganar nata...
********
Da k'yar ya samu ya iso barikin nasu, kana ganinsa kasan babu lafia, shi kansa yasan yau d'in kam na buk'atan taimako don komai da k'yar yake iya yinsa.....
Momy na hankalce da Salma wacce keta faman duba agogon waya lokaci zuwa lokaci.... Kafin Momy ta sami zarafin magana wayar ta soma ruri.... Gaban Salma ya yanke ya fad'i ganin mai kiran ba kowa bane illa mutumin da take ta faman duba lokaci a sabida shi, don yace da ita ba jimawa zaiyi ba zai dawo..... Saurin mik'a wa Momy wayar tayi tana mai ci gaba da duban Momyn sanda ta k'ara wayar a kunnen tana amsawa....
Lokaci guda k'irjinta ya kuma bugawa sanda ta jiyo muryar Momy tana fad'in "Soja ka tabbata lafiyarka k'alau.... Kaji muryar ka fah sam tamkar babu lafiya cikinta...."
Daga d'aya b'angaren murmushin k'arfin hali Naseer yayi kana yace "Lafiya Momy kawai aron d'iyarki nake so ki bani, ba don ni ba don Allah...."
Momy ta d'ago idanuwanta ta dubi Salma wacce itama ita take kallo kana ta d'an mik'e ta fice daga d'akin sannan taci gaba da amsa wayar.... Salma kuwa tabita da kallo tsoro bayyane saman fuskarta, banda addu'a babu abinda take cikin zuciyarta, Allah yasa Sojanta lafiya yake...
"Naseer ai bamuyi haka da kai ba...." Momy ta fad'i murya a dake...
Yana ci gaba da matsa towel mai d'umi a hak'ark'arin nasa had'i da d'an tattamke idanuwa yake fad'in "Momy nasan bamuyi haka ba, but taimaka min za'ayi,...."
Yanda yake maganar da k'yar zaka gane baya jin dad'i...
D'an jim Momy tayi kana tace "Naseer anya lafiyar ka kuwa, kaji muryar ka kuwa, da k'yar da k'yar haka nan..."
Saida ya d'anwmurmusa kana yace "Lallai Momy na yarda kinsan d'an naki sosai yanzu, banson sanar dake sabida kada hankalin ki ya tashi, nan ya sanar da ita abinda ya faru dashi a tak'aice...
Salati Momy ta dingayi tana mamakin mutanen wannan duniya... Jin yanda hankalinta ya tashi sosai yasa Naseer kwantar mata da hankali yana fad'in is not that serious ciwon nasa kawai ta turo masa Salma so that she should help him taking care of him...
Cikin sauri ta shiga gyad'a Kai tamkar yana ganinta kana tace "Tana nan zuwa yanzun nan... Allah baka lafiya ya d'auraka kan mahassadanka da mak'iyan ka... Zan turota yanzun nan....." Daga haka Sallama sukayi kafin Momy ta koma d'akin yanda ta baro Salma da Ilham, Ilham d'in sai labari take mata amma Salma kam hankalinta kacaukam baya wajen, burinta kawai Momy ta shigo taji wani hali Sojanta ke ciki....
Momy na shigowa Salma ta mik'e tsaye tana tamabayrta "Momy wai mene ya samesa...?" Yanda tayi tambayar tamkar wacce aka zabura...
K'ak'aro murmushi Momy tayi kana tace "Lafia lou kiyi sallama da Ilham muje na raka ki yana son ganin ki...."
K'irjinta ya bada daram... muryar Ilham suka jiyo tana fad'in "Momy ba Dr yace nima yau zan tafi gida ba....?"
Momy ta jinjina kai kana tace "Eh idan yazo zai sallame mu nida ke sai mu wuce gida, amma kafin ya iso barinyi rakiya wa Addarki koh....."
A hankali Ilham ta jinjina kai kanata tace "Addah Salma saida safe, na gode da k'ok'arinku..."
Salma ta k'araso ta d'an kamo hannun k'anwar tata kana tace "Ki daina mana godiya Ilham, ke d'in dolen mu ce, idan an sallame ku zan sameku can gida, idan kuma ba'a sallame ku ba zan dawo asibiti wajen ki...."
Ilham ta jinjina kai kana tace "Ki gaida Ya Naseer...."
Bata amsa mata ba sai kallon Momy da tayi, Momy ta d'an dafa Ilham tace "Daughter yanzu zan dawo kinji koh..."
A hankali Ilham d'in ta kuma jinjina kanta kana tace "Toh Momy sai kin dawo...."
Salma dai bin Momy kurum take tamkar rak'umi da akala har suka iso gidan Naseer... Da k'yar ya zura rigarsa inner black mai V-neck ya k'araso ya bud'e masu...
Baki sake Momy ke duban fuskar sa yanda yayi jajazir, gefen idanunsa na hagu ya tara jini haka hancinsa tayi ja sosai gefen bakinsa ma alamun ciwo ne.....
Salma kam kallo guda ta masa tayi saurin d'auke kanta gefe sabida hawaye dake neman ciko idanunta...
"Naseer wannan ciwo ne kake cewa kad'an, kaga maza tashi mu wuce clinic...." Cewar Momy hannaye dafe da k'irji....
K'ak'aro murmushi yayi kana yace "Kai Momy sai kace ba Soja nake ba... Babu komai ba sai anje asibiti ba zai daina...." Yana maganar idanunsa nakan Salma...
Jinjina lamarin Momy ta kuma kana suka d'an gaisa, tana hankalce dashi da irin duban da yake ma Salma, itakam gaba d'aya ko gaidashi ta kasa... Fatan samun lafiya Momy ta kuma masa kafin tai masu sallama....
Har Momy ta fice Salma bata iya d'ago fuskar ta ba sabida hawaye ne tab idanunta.....
A hankali ya mik'e ya k'araso kujeran da take zaune.....
0 comments:
Post a Comment