K'uri Naseer ya mata yanda ta kifa kanta k'asa ta kasa d'ago idanu ta dubesa.... D'an gyaran murya yayi kana yace "Reina...." shiru bata amsa sa ba dukda da wani irin siga ya ambato sunan nata....
"Reina please look up..." Ya sake fad'i sanda ya kamo 'yan yatsun hannun ta...
Ba tareda ta dubesa ba murya na rawa irinta mai shirin yin kuka ta soma fad'in "Ba saida nace kar kaje kai kad'ai ba, saida nace zan bika kace ba haka ba.... Ka kalli yanda suka maka fisabilillahi..."
Shikam Naseer kallon ikon Allah kurum yake zuciyarsa na masa wani irin dad'i baisan Salma ta damu dashi har haka ba... Lokaci guda kuma ta basa dariya wai saida tace zata bisa saikace idan ta bisan wani abin zata tare masa,...
K'ok'arin maida dariyar sa yayi kana ya kuma matsowa dab da ita ya kewaye hannunsa ta bayanta ya tallafota cikin jikinsa, cikin murya mai cikeda sigan lallashi ya soma fad'in "Reina I'm sorry OK, next time zanji maganar ki..." Ya d'an kwanto da fuskar sa dab nata yana k'ok'arin k'unshe dariyar sa yace "Matar Soja zata k'waci Soja next time,.."
Maganar sa ya bata dariya tasan magana ya mata cikin magana, d'an rufe fuskarta tayi had'i da murmusawa....
Shid'inma murmushin yayi kana yace "Amma kuma idan naje dake sukayi kuskuren tab'a min ke nan ne zan fice masu a giya, sabida zan iya rasa rayuwata akan kare ki da tsare maki mutuncin ki Reina...."
D'ago kai tayi tana dubansa shid'inma ita yake duba, sai sannan ta samu ta kalli ciwon nasa sosai... Tausayin sa ya kuma cikata.... Saurin sunkuyar da idanunta tayi don bazata iya jure kallon k'wayar idanunsa masu rikita mata lissafi ba....
Naseer ya d'an kuma shigar da ita jikinsa yana sakin numfashi a hankali sabida ribs d'insa dake masa ciwo ko numfashi yayi, tsan-tsan k'aunarta na ratsa zuciyar sa, a hankali cikin wata irin kasalcecciyar murya yake fad'in "Reina bamu gaisa ba...."
Kunya ce ta d'an kama Salma don kusan kullum idan sun had'u sai Naseer ya tuna mata batun gaisuwa, itako bawai gaisar dashi'inba ne bata yi, gaba d'aya rikiicewa take idan ta gansa shiyasa har gaisuwar ma mancewa take....
"Soja kayi hak'uri ganin ciwonka ne yasani na mance, Ina yini, ya jiki...." Ta fad'i murya can k'asan mak'oshi...
Murmushi yayi yana d'an murza yatsan hannunta guda yake amsa ta, lokaci guda yake nuna mata wasu salo na soyayyar sa
Gaban Salma ne ya shiga dukan tara-tara jin sababbin abubuwa da Sojan nata ke yi mata wanda bai tab'a mata irinsu ba...
Saitin kunnenta yake rad'a mata "Reina ki cire hijab d'in mana ki sha iska..."
A zabure ta d'ago lokaci guda ta bige masa ribs d'insa dake masa ciwo.... D'an sakin k'ara yayi a hankali yana k'ok'arin kama wajen... Salma cikeda tsoro take fad'in "Wayyo I'm sorry Soja, bansan da ciwo wajen ba... Da zafi koh..."
Naseer kuwa ganin duk ta rikice ya sanyasa kuma narkewa saikace ba Soja mai fama a fagen daga ba....
Sai faman d'age rigar nasa yake yana wani tattamke idanu yana k'ananan k'ara, Salma kuwa duk ta rud'e ta zaci zafin gaske yake ji, a tamanin ta shiga neman yanda zataga fridge, k'ofar dake a dining area ta nufa aiko kitchen ne nan ta hangi fridge daga side, cikin sauri ta bud'e tana duba ice...
Salma tana dawowa wajensa ya kuma narkewa.... Goran ruwan k'ank'aran take k'ok'arin manna masa a wajen saidai gaba d'aya ta kasa sai rawa da hannunta keyi....
Saurin runtse udanunta tayi ganin ya kwaye rigar nasa sosai jikinsa ya bayyan...
Naseer kuwa na hankalce da ita, sai k'unshe dariyar sa yake ganin yanda ta runtse idanunta alamun bata son ganin jikin sa...
"Reina it hurts...." Ya fad'i murya can k'asa sai kace mai jin jiki da gaske....
Salma gaba d'aya ta birkice a d'an daburce take fad'in "Okay.. Okay... Kayi hak'uri kaji.... Lokaci guda ta shiga manna masa ruwan k'ank'aran had'i da kawar da kanta gefe.... Kana ganin yanda hannunta ke rawa zata baka dariya....
Sai kallonta yake tana kuma birgesa.... Ganin sai shivering take ya sanya Naseer kamota ya jawo jikinsa lokaci guda ya soma k'ok'arin yaye hijab d'in dake jikinta....
Ai Salma kam da sauri ta rik'e hijab d'in gam tana faman muzurai tamkar wacce tayi ma Sarki k'arya...
Saitin kunnenta yake rad'a mata "I've the right.. I'm your husband kar ki hanani kallon abinda Allah ya halarta min....."
Sosai ta rintse idanunta, itakam wllhi da yasan kalan kunyarsa da takeji da ya daina mata wasu abubuwan...
D'inkin riga da skirt ne na atampa a jikinta, ya mata kyau sosai ya zauna d'agwas a jikinta.... Sam bai tab'a k'are ma jikinta kallo irin na yau ba.... Cikin ransa kurum yake furta "Masha Allah, shi kansa yasan he's blessed...
Ganin tak'i bud'e idanu tak'i kallon sa yasa yin d'an gyaran murya kana yace "Ko mutum ya bud'e idonshi ko kuma na cire rigana gaba d'aya...."
Bai kai aya ba tayi saurin ware idanunta tana girgiza masa kai cikeda shagwab'a take fad'in "Nidai a'a Soja..."
Taso basa dariya, murmusawa yayi kana yace " Toh wai yaya za'ayi kiyi jinyar tawa da irin wannan kunyar.... Ko Momy bata sanar dake jinyar mijinki zaki zo ba...?"
D'an muskutawa tayi kana ta kuma sunkuyar da kanta k'asa.... Murya can k'asan mak'oshi tace "Soja ai ni ban iya jinya ba..."
Ya murmusa yana mai jinjina yarintar ta kana yace "Kar ki damu zan koya maki yanda zakiyi...." Ya k'arashe yana kwantar da ita cikin jikinsa....
D'aura tafin hannunta yayi saman nasa tamkar masu wasan tafa-tafa, Salma sai kallon hannun nasa take wanda yake tamkar jini zai fito itakam tana mamaki idan ta tuna mahaifiyarsa bak'ar fata ce, sam babu alamun surki ajikinsa, ko damn shike haka nan Allah yake ikon sa tunda, ta kuma tuna cewa shid'in mahaifin sa ya biyo.... Tana cikin tunanin ta tsinkayo muryarsa yana fad'in "Waini shekarunki nawa ne....?"
Kai tsaye ta basa amsa da "I'm clocking 20, December 29th zan cika..."
Naseer ya d'an murmusa kana yace "Noted gwara da kika sanar dani date d'in sabida ya zama saved a kwanyata... Ilham ma ta gama sec school ne...?"
Girgiza masa kai tayi kana tace "Batadai yi jarabawar fita ba amma aji shida take..."
Naseer ya jinjina kai kana yace "Yayi kyau, yanzu sai maganar schools d'inku idan abubuwa sun lafa da yardar Allah...."
Salma da tuni dad'i ya mamaye mata zuciya zasu koma school batasan sanda ta mak'ale sa tanai masa godiya ba....
Murmushi kawai yake yana dubanta yanda ta cika da murna zuciyarsa tai masa dad'i... D'an kunya taji ta sake sa a hankali kana tace "Soja mun gode...." Bata rufe baki ba ya d'ora d'an yatsan sa saman leb'enta kana yace "Godiyar nan ta isa haka Salma, we are one okay...."
A hankali ta jinjina masa kai tana murmushi... Shima d'in murmushin yake yana dubanta kana yace "Nifa har yau ba'ace min ana sona ba.... Ko har yanzu ban sami karb'uwa bane...?"
Saurin rufe fuskarta tayi tana murmushi...
Hannayenta data rufe fuskar dasu Naseer ya kamo ya sauk'esu k'asa fuskarta ya bayyan.... Idanunsa k'uri a fuskarta labb'ansa d'auke da murmushi... Cikin wata irin sassayan murya yace "Kar ki damu my love for you is enough for the both of us...."
A hankali ta ware idanuwarta tana dubansa murmushin saman fuskar sa bai gushe ba.... Lallai Soja masoyinta ne na hak'ik'a... A hankali ta maida nata idanun k'asa...
Naseer yana son janta da wasa sabida ta saki jiki dashi, d'an kamo hannunta yayi kana yace "Zo muje...."
Mik'ewa tayi tana tambayarsa ina zasuje... Bai amsata ba har saida suka isa wata 'yar madaidaiciyan parlor wanda kayan motsa jiki ne kurum a ciki saiko wasu couches guda biyu na hutawa....
Kallon mamaki take binsa dashi, tadai ga lafiya bai ishesa ba yaushe kuma za'a motsa jiki, itakam tsoron irin wad'an nan machines d'inma take... A hankali tace "Soja me zamuyi..."
Bai amsata ba sai zaunar da ita saman couch da yayi ya isa gaban TV yana jona wayoyi... Saida ya ida had'a komai kana ya dawo yanda take hannunsa rik'e da headphones da kuma control d'in game...
D'an d'agota yayi ya zauna cikin couch d'in daga baya yayinda Salma ta zamto a d'an gabansa ya mata matashi da jikinsa, Yana k'ok'arin saka mata headphones yake fad'in "Xbox zamu buga, fad'i wani mission kike so....?"
Murmushi kurum tayi kana tace "nidai ban iya ba...."
Murmusawa yayi had'i da d'an jawo hancinta kana yace "Zaki koya ne...." Daga haka mak'ala mata headphones d'in yayi shima ya saka ya bata control d'aya shima ya rik'e guda.....
Salma sai faman dariya take ganin ba iya abin tayi ba sai gwara motocin take, idan kuwa taji k'aran drift ta cikin headphones d'in ko ta gwara motocin sai ta k'ank'ame sa cikeda tsoro tana mai yin dariya... Shid'inma biye mata yake yana dariyan.... Idan ka gansu gwanin sha'awa kaman DUNIYAR SU ta tabbata a haka cikin jin dad'i da annashuwa....
*******
Abun duniya ya dami Shareefah, rashin dawowar su Mamy ya d'aga mata hankali... Ta kira wayoyin su sau babu adadi baya shiga... Yanzu kam sosai hankalinta ya tashi, mik'ewa tayi ta nufi BQ ta tadda Deluwa, tana tambayarta ko su Mamy sun sanar da ita yanda zasuje...
Deluwa tace bata sani ba, gate ta nufa ta iske Baba mai gadi shima yace bai sani ba saidai yaga Hajiya a mota akazo aka d'auketa ita kuwa Shareefah acab'a ta d'ale...
Shareefah tayi jigum tana tunanin lamarin, tasan za'a rina Mamy da Azeema tamkar Tom and Jerry ne, idan Mamy ta k'ulla wani abin Azeema taje warwarewa, toh kodai asibiti wajen Daddy sukaje...? Amma da asibiti ne da Mamy ta sanar da ita... Mik'ewa tayi ta gabatar da sallan isha abinda ta jima batayi ba kana zuciyarta ta raya mata taje dai asibitin ta duba.... Ko cire hijab d'in batayi ba ta suri car keys d'inta ta fice....
********
Dr Basheer nata neman layin Dr Fawaz ya sanar dashi farfad'owar Alh Ali Safwan bai sami layin Fawaz d'in ba... Layin Naseer ya shiga nema nan ma bai samu ba, lokaci guda ya tuna ya karb'i layin d'ansa da suka jima tare jiya.... Nan yayi dialing laying Affan....
Affan sanye da kayan training yana judging yaga kiran likitan Daddy na shigo masa, tsayawa yayi yana d'an goge gumin fuskar sa kana ya shiga amsa kiran....
Cikin wani irin murya mai cikeda farin ciki yake fad'in "Dr are you serious.... Alhamdulillah... Alhamdulillah.... Gani nan zuwa Dr...." Daga haka katse wayar yayi ya k'arasa gidansa a d'ari, ko tunawa da Naseer baiyi ba ya suri motar sa ya nufi ganin mahaifin sa.... A hanya ya hangi Ilham da Momy zasu tsallake kwalta....
Lokaci guda ya paka motar nasa a gefe kafin ya nufosu, fuskar sa cikeda annuri...
Momy tana hangosa ta Saki murmushi....
"Kai kuma ina ka nufa da daren nan...." Momy ta tambaya sanda yake k'arasowa...
"Momy badai salesman ku akayi ba...." Affan ya tambaya....
Jinjina masa kai Momy tayi kana tace "Gashi kuwa gida muka nufa, sauran kayan da safe a d'auko...."
Idanunsa naga Ilham wacce murmushin ta ya k'aru tun sanda ya k'araso wajen kana yace " Amma Momy ai da nazo na maidaku gida, gashi patient ta wahala...."
Momy ta murmusa kana tace "Ai likitan ne yace ta d'an ware jini tunda babu wani nisan d'aga hankali...."
Affan yace "Still dai Momy muje na k'arasa daku...."
Sai sannan ya jiyo muryar Ilham tana fad'in "A'a Ya Affan nafin son tafiyar k'afan ne sabida jikina ya warware, mun gode da kulawa...."
D'an murmushi yayi kana yace "Are you sure...."
Jinjina masa kai kurum tayi fuskar ta cikeda murmushi....
"Ina ka nufa ne wai da daren nan, ko gari zaka shiga..." Momy ta kuma tambayar sa....
Affan na murmushi yake fad'in "Momy Daddy ne..... Daddy is out of comma, yanzu likita ya kirani yake sanar dani...."
Hamdala suka dinga yi, Ilham kuwa murmushi mai sauti take kana tace "Ya Affan da gaske kake, Dan Allah ka gaisar min da Daddy kaji.... Naji dad'i wllhi...."
Murmushi Affan yake cikeda jin dad'i kana yace "Insha Allah Ilham zan sanar dashi kina gaishe shi" Ya juyo ya dubi Momy kana yace "Momy ni na wuce...."
Momy ta masa fatan sauk'a lafiya had'i da addu'an k'arin sauk'i wa Daddy kafin ya wuce....
*******
Ganin motar Fawaz a parking lot ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba, wata zuciya tace what if Jamila ta sanar da Fawaz komai....? K'irjinsa ya kuma bugawa da k'arfin gaske.... Shi kad'ai ya shiga girgiza kai b'angare na zuciyar sa tana raya masa kai haba bazata iya ba duk rashin kunyar ta.... He already threatened her....Lokaci guda ya saki murmushi musamman da ya tuna an kawar masa da Naseer for good... Duniya sabuwa, baibi takan Fawaz ba kai tsaye sashen mahaifiyar sa ya nufa...
Zaune ya sameta a parlor sai aikin hura sigari take, don sigari shine zikirinta na dare.... 'yar plate d'in dake bisa center table d'in guntu-guntun karan sigari wanda aka zuk'e sunfi biyar cikin ta.... Ga kuma wata kwali a gefe.... Yanda k'amshin turaren wuta ke kama gidajen mata masu yawan huld'a dashi haka warin sigari ya kama parlorn Innah....
Yana k'arasowa kwalin ya d'aga ya zari guda lokaci guda Innah ta dondala masa wutan sigarin daga jikin wanda take faman zuk'a....
Suna had'a idanu suka fashe da dariya.....
Alh Kabeer yace "Ya zama tarihi, yau na cika maki burin ki ..."
Innah ta feso hayak'in sigari ta hancinta kana tace " Ban tab'a jin dad'i irin na yau ba A DUNIYAR MU, Mafarki na ya zamto gaskiya, dama irin mutuwar wulak'anci da nake so yayi kenan a k'one shege.... Kabeer a yau ka nuna min cewa kai d'an halak ne, ban tab'a saka maka albarka ba amma yau zan saka maka....."
Bata kai aya ba wayan Alh Kabeer ya soma ruri ganin Maina ne mai kiran ya sanyasa saurin d'agawa...
"Ya ka koma wajen ka tadda mushen nasa....?" Ya tambaya cikeda isgilanci....
Maina ya shafi kansa kana yace "Mai gida banga mushen sa ba, hasalima ban tadda kowa wajen ba, ina zaton dai sun wani wajen suka jefa sa amma kam akan idanuna suka watsa masa petur ni na tabbata sun k'onesa...."
D'an Jim Alh Kabeer yayi kafin yace "Shikenan kayi sauri ka bar wajen zamu had'u gobe da safe...." Daga haka d'if ya katse kiran...
Innah ta dubesa tace "Yaya mai ake ciki...."
Murmusawa yayi kana yace "kar ki damu ya zama mushe k'ila ma karnuka sunyi daldalan sa...." A tare suka tuntsire da wani shegen dariyar bosawa....
********
Mamy ce ta soma farfad'owa sanda taji ana shureta da k'afafu.... Da k'yar ta bud'e idanunta, tana farkawa taga Laure akanta... D'an zabura tayi had'i da matsawa baya...
Laure ta murmusa tace "Haba aminiya me yayi zafi ina zaki gudu, badai tsorota kika soma ba, sai kace wata dodanniya, haba Ma'u nice dai Laure taki mai warware matsaloli....."
Mamy ya jikinta ke faman rawa tak'urewa waje guda ta kuma yi kana tace "Laure kiyi wa Allah ki k'yalemu mu tafi... Ki tausaya mana Laure..."
Dariya Laure ta kwashe dashi kana tace "Ma'u bari na gwada maki tabbacin cewa bazaki bar wajen nan ba...."
Lokaci guda Laure ta bud'e murya ta kirawo Steven dake bakin k'ofa kana tace "Bani madubin nan...."
Take yabi umarninta ya mik'a mata....
Dai-dai fuskar Mamy ta nuna madubin lokaci guda Mamy ta hangi kanta cikin madubin.... Malu d'in da ta hango an taltale mata gashi tass harda shafe hoda ya sanya Mamy sakin k'ara tana k'ok'arin kai hannaye kanta...
"Yanzu Laure da gaske aski kika min, da gaske yankamu zakiyi....?" Cewar Mamy murya na rawa...
"Ga zahiri kuwa kin gani ko bakiga malu akanki bane....?"
Mamy ta soma girgiza kai tana kuma ahafa taltal d'in kanta take fad'in "Wayyo ni Asma'u wayyo Allah na.... Laure ban tab'a tsammanin A DUNIYAR MU akwai 'yan adam irinki ba...."
Mamy bata kai aya ba Laure tace "Aka samu irinki ma ballanta irina...."
Dai-dai lokacin aka shigo da Azeema itama an mata aski tal-tal, an shafe da hoda sai shining kan take....
Wurgi da akayi da ita ya sanya ta bud'e idanu a zabure.... Hango Mamy da tayi kayi bad'e da hoda ya sanya Azeema sakin k'ara tayi saurin shafan nata kan, nan taji itama babu alamun suma....
K'ara Azeema ta saki tana kuka take fad'in "Ina suma ta, wllhi Laure kin cika 'yar wuta... Mamy aski fah aka mana da gaske..... "
Laure ta shek'e da dariya kana tace "Au wai dama baku yarda gidan yanka kuka zo ba, tunda an kwashe sumar ku zaku yarda yanzu.... Steve kawo masu abincin idan sunga dama suci idan kuma basuci ba yunwa taci uwasu don ba k'anwar uban kowa bane...." Daga haka Laure tayi ficewar ta tana amsa wayar oganta...
********
Shareefah hawaye Affan hawaye sanda Daddy ya kamo hannayen su, dukda ba sosai ake jin maganar nasa ba yaran nasa sun basa tausayi sanda ya tuna mahaifiyar su ce ke yunk'urin kashe sa.....
A hankali Daddy yake ambaton Asma'u...
Shareefah ta kuma rik'o hannun Daddy cikin nata kana tace "Daddy zata zo.. Zata zo insha Allah.. Yanzu za'a kawota kaji...." Ta k'arashe maganar tana duban Affan dake binta da kallon tuhuma domin shima cike yake da mamakin rashin ganin mahaifiyar tasu a wajen....
******
Mamaki ya cika Momy ganin Falaq kwance saman kujera ita kad'ai a parlor tana barci sauro sai cizon yarinyar suke... D'an girgiza kai kurum tayi kafin ta d'auki yarinyar don kwana biyun nan sam basu gane kan Jamila ba.....
Mamaki bai gama cika Momy ba saida ta k'araso corridor taga Ilham tsaye bakin k'ofa tana rok'on Jamila da ta bud'e mata k'ofar... Ga kukan Jamilar kana jiyowa daga cikin d'akin....
*****
Mik'ewa yayi ya lek'a window ya hangi motar mahaifin sa.... Yana wani irin huci yake furta "I'm gonna kill you... I swear I'm gonna kill you..."
Tamkar mahaukaci ya tokari k'ofar d'akinsa ya fice...
Kai tsaye sashen mahaifiyar sa ya nufa bai same sa a nan ba.... Fitowa yayi yana tafiya tamkar zai kifa da k'asa ga wani irin huci da yake yi Ya nufi sashen Innah
Babu kowa a parlorn k'asa haka yasa ya nufi sama kai tsaye...
Alh Kabeer yana balcony yana amsa waya yayinda Innah ke zaune a parlorn tana shak'an hayak'inta... Kaman daga sama sai ganin Fawaz tayi ya banko k'ofar parlorn ya shigo, fuskar sa tayi wani irin jazir haka nan idanunsa, bata tab'a ganinsa cikin makamanciyar wannan kamanni ba, a d'ari ta mik'e tsaye tana murmushe ragowar sigarinta da hannunta....
Tun kafin ta sami zarafin masa magana ya nufo ta.... Innah gaba d'aya cikinta ya d'uri ruwa, a tunaninta Fawaz yaji tattaunawarsu da Kabeer ne... Tuni ta soma jada baya tana muzurai take fad'in "Fa...Fawaz la......"
Bata ida magana ba ya tokari kujeran gefensa da ta tare masa hanya kana ya isa gaban Innah , cikin wani irin murya yake fad'in "Where is he....!!! Where the hell is he....!!!!
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*50*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Fatan alkhairi Aysha Mrs Splendid Allah bar k'auna ya d'ayyiba zuri'a ina k'aunarki nima fisabilillah 💕🤝🏼*
*Masoyana masu bibiyan labaruna ana musulmin tare, nima ina k'aunarku a duk yanda kuke Sameena nai maku barka da Sallah Ubangiji ya maimaita mana Ameen..💕🤝🏼*
A d'ari Alh Kabeer ya katse wayan da yake ya isa k'ofar balcony d'in ya danna mata lock, banda gumi babu abinda ke keto masa dukda sanyi-sanyi dake kad'awa a garin....
Innah da gaba d'aya ta birkice batasan sanda ta soma nunawa Fawaz k'ofar balcony ba ba tareda ta iya furta koda kalma ba don ita kanta da za'a yanka naman jikinta da k'yar a sami jini sabida firgita ta Fawaz yayi.....
Kaman zai kifa ya nufi k'ofar, saidai yana murd'a ta yajita a kulle, da k'arfin da Allah yayi masa ya shiga bugun k'ofar yana fad'in "Kabeer Santana ka bud'e k'ofar nan....!!!"
Innah har tsakar kanta take jin bugun, Lubna dake faman seat up a d'akinta lokaci guda take waya da abin k'aunarta Deeni, d'abi'arta ne duk dare takan motsa jiki a d'akinta.... Tuni suka saka aya wa hiran tasu daga ita har Deenin don sun jiyo hayaniyar Fawaz da bugun k'ofar....
A d'ari Lubna ta mik'e kafin ta d'au wayarta tace da Deeni "My Stalker I'll call you back..." bata jira cewar Deeni ba ta katse wayar ta fice a guje ta nufi parlorn Innah yanda take tsammanin daga nan hayaniyar ke fitowa....
Bugun k'ofar yake da iya k'arfinsa jijiyoyin jikinsa sunyi rud'u-rud'u bai daina fad'in "Dad you better open this door... Dad ka bud'e k'ofar nan....!!"
Innah ta k'araso tana k'ok'arin janye Fawaz, baisan sanda yayi wurgi da ita ba sai hannun Lubna dake k'ok'arin shigowa...
Lubna da tuni jikinta ya soma karkarwa don wannan bak'on abune a gidansu bata tab'a ganin irin hakan ba.... Murya na rawa take tambayar Innah lafiya....
Innah bata iya amsata ba don sosai ta buge kwankwasonta.... Lokaci guda suka bi Fawaz da kallo wanda gaba d'aya tamkar baisan mai yakeyi ba....
Da k'arfin gaske ya tokari k'ofar ta bud'e
Alh Kabeer sai faman muzurai yake daga angle... Fawaz tamkar zaki haka yake takowa gabansa...
Kafin yayi wani aune Fawaz ya cakumosa had'i da mak'ure sa yana fad'in "How dare you Kabeer Santana ... Wllhi yau babu mai hanani kashe ka...." Ya shiga janyosa....
Fad'i yake "Fawaz ka saurare ni Son...."
Inaa Fawaz tuni ya fettosa yana fad'in "Wllhi yanda ka lalata min rayuwa yau kaima sai kayi nadamar haihuwata kaman yanda nayi nadamar kasancewa d'anka...." Ji kake gush-gush Fawaz ya shiga kai wa magaifinsa wasu irin duka da tokari....
Lubna kuka Innah kuwa ko gizau bataji mamaki ba sabida tasan akwai ranar faruwan irin haka, ko sati biyu masu kyau ba'ayi ba Kabeer ya wawwanketa da mari masu ji da lafiya, wannan shine what goes around comes around.... Abu guda dai da ya dameta shine ba dukan wasa Fawaz keyima mahaifinsa ba.. Duk yanda akayi babban abu ya masa ko kuma ya gano cewa shine sanadiyan ciwon mahaifiyar sa... Bazata jure kallon irin dukan da Fawaz keyima d'an da tafi k'auna a duniya ba
Innah tayi ta maza ta soma k'ok'arin rik'o Fawaz tana fad'in "Lafiyar ka Fawaz, mahaifin naka...."
wani tsawan da ya dararawa Innah saida ya sanyata had'iye maganar ta....
Ganin ya shiga janyo Dad d'in nasa k'asar bene ga jini na fita daga hancin sa ya kuma Kid'ima su gaba d'aya... This is not the Fawaz they used to know....
Lubna jiki na rawa ta shiga dialing layin Naseer...
Suna tsaye kitchen suna had'a coffee cikin soyayya da k'aunar juna yaga kiran Lubna, duba time ya kuma yi kafin ya d'aga wayar...
Cikin tsananin kuka Lubna take fad'in "Ya Naseer dan Allah kazo, dan Allah kazo kafin Fawaz ya kashe Yaya.... Yaya wllhi dukan kisa Fawaz keyiwa Yaya...."
Innalillahi kawai Naseer ke nanatawa cikin ransa... Fawaz yaron kirki mai ladabi shine da dukan mahaifin sa.... Dukda shi kansa nada babban issue da d'an uwan nasa amma bai tab'a tunanin akwai ranar da zai d'aga hannu da sunan dukan sa ba.... Cikin sauri yace da Lubna "I'll be on my way.... Gani nan yanzun nan...." Daga haka katse kiran yayi ya nufi d'aki da sauri yana rik'e ribs d'insa dake ciwo....
Salma ta bisa da kallo yanda ya canza lokaci guda... A tamanin tabi bayansa tsoro da firgici sun nuna sosai a fuskar ta....
Tana ganin ya zari key ta zura hijab hawaye na k'ok'arin zubo mata take fad'in "Wllhi Allah wllhi babu yanda zakaje salon su sake maka wani abin...."
Dafata ya d'anyi kana yace "Reina wannan wani issue daban ne okay, just wait for me here, I promise I won't take long okay. ."
Girgiza masa kai take kana tace "Wllhi nidai bazan bari kaje kai kad'ai ba wllhi saidai na bika..."
Kallo yake binta dashi yanda take hawaye, yasan ta damu dashi sosai.... Rik'o hannunta yayi suka fice badon yaso zuwa da ita ba saidai bazai iya barinta cikin zullumi da kuka ba sannan baida lokacin tsayawa mata bayani.....
*****
Wani irin gudu yake bisa kwalta duka ciwon dake jikinsa, Salma sai binsa da kallo take cikeda tsoro.... Ko wani mota wucesa suke tashi guda sabida gudun da yake falfalwa ga duhun dare sauk'in abin akwai street lights....
Mintuna kad'an ya kawosu gidan nasu dake GRA Sir Kashim street....
A d'ari taga Naseer yayi parking ko ta kanta baibi ba ya fice ya nufi cikin gidan, Salma kuwa cikeda tsoro ta take masa baya jikinta sai rawa yake ganin yanda Sojan nata ya zamto lokaci guda..
A parlorn k'asa yaci karo dasu Fawaz sai dukan mahaifin sa yake wanda ya koma tamkar maras numfashi sai jini dake bin bakinsa da hancinsa...
Innah da Lubna kuwa rungume juna sukayi sai hawaye dake kwararo masu, rabon Innah da kukan gaske tun mutuwar uwarta sai yau da jikanta ke dukan d'anta da tafi so fiye da komai....
Cikin wani irin murya Naseer ya ambato sunan Fawaz wanda saida mutanen wajen gaba d'aya suka kuma firgita... Lokaci guda ya k'arasa ya finciko Fawaz had'i da d'aukesa da wata mahaukaciyar mari wanda saida ta kaisa k'asa....
Innah cikinta ya bada wani k'ugi ganin Naseer tsaye a gabanta rayayye ba macecce ba....
Alh Kabeer ma da jini ke faman gangarowa daga hancinsa da bakinsa shaye da mamaki yake duban Naseer d'in, a zaton su i zuwa wannan lokaci Naseer ya jima a k'iyama
Salma daga bakin k'ofa take tak'ure a lab'e tana dubansu, ga k'irjinta dake bugu...
D'agowa Fawaz yayi yana mai ci gaba da huci yake duban Naseer kana yace "Uncle you stay out of this.... Ka k'yaleni na kashe wannan wanan mutumin...." Baikai aya ba Naseer ya kuma d'aukesa da mari yana wani irin huci ga ribs d'insa da yake jinsu tamkar zasu bar jikinsa sabida yanda zuciyarsa ke bugu da sauri da sauri sabida tsananin b'acin rai....
Fawaz rik'e da fuskar sa yake duban Naseer d'in murya na rawa yake fad'in "Uncle you slapped me because of this worthless...."
Baikai aya ba Naseer ya katse sa da fad'in "Kayimin shiru kafin na b'abb'allaka a wajen nan..... Who the hell you think you are huh... What has gotten into you... Shaye-shaye ka soma ko me.... This is not you Fawaz.... A cikin hankalinka kake d'aga hannu kana dukan mahaifin ka..... Lafiyanka lou....?"
Fawaz bai daina tururi ba hawaye basu daina zuba masa ba yake fad'in "Uncle I'm sorry, amma idan dai akan wannan mutumin ne saidai kayi hak'uri don wllhi bazan tab'a yafe masa ba cutan da yayi min..."
Shaye da tsananin mamaki Naseer ke duban Fawaz d'in
Lokaci guda Fawaz ya dawo da dubansa ga Mahaifinsa dake yashe a wajen yana d'igan jini kana yaci gaba da fad'in
"You ruined my life for good.. Ka cutar damu nida mahaifiyata.. You've been cheating on her.... Sabida bata da lafiya.... Sabida batasan abinda ke wakana ba, .... You lied to me....." Hawaye suka ci gaba da zubowa daga idanunsa sanda yaci gaba da fad'in "I can't believe you two had an affair, So itace mistress d'in taka, wacce kake cin amanar mahaifiyata da ita... Allah ya halarta maka auren mata d'aid'ai har guda hud'u meyasa baka aura ba, meyasa ka zab'i....." Kasa ci gaba da magana yayi lokaci guda ya d'ago hannayen sa yana goge hawayen da suka wanke masa fuska... Girgiza kai yayi kana yaci gaba da fad'in "You've no idea how shameful it is being your son..... I hate you... I hate you Dad... I hate this place.."
Alh Kabeer banda girgiza kai baya iya komai...
Jinin dake bakinsa ya share kana yace "Fa.... Fawaz ..Son....."
Baikai aya ba Fawaz ya katse sa da fad'in "Don't you dare.... Kar ka yarda ka kuma kiran Sunana ballantana ka kirani d'anka, wllhi nafi tsanarka fiye da komai A DUNIYAR MU, .... I don't wanna be in this family anymore... Zan tafi zan bar maka ita, amma ka sani I'm leaving with my Mum, bazan barta ma azzalumi irinka ba..." Daga haka sa kai yayi ya fice daga parlorn.....
Mamaki ya cika zukatansu, yanzu kam sun fahimci dalilin Fawaz , takaicin dolancin Kabeer ya cika Innah, batasan yaya akayi har ya had'a nema da d'an cikinsa ba kuma neman ma neman bariki dama ace nema na aure ne da sauk'i, tana murna yayi hankali yayi wayo ashe har yanzu yana nan a dolonsa, gadai Naseer shi yazo ya k'wacesa hannun d'an cikinsa dake neman aikasa lahira kenan k'arya ya mata bai kashe Naseer ba, wani k'atutun bak'in ciki ya kuma tasowa ya tokare mata mak'oshi...cikin sauri ta nufi upstairs tamkar zata kifa, yaukam da zata sami cocaine shi zata shak'a ko tension d'in dake kanta zai tarwatse ko kwalin sigari goma ta zuk'e bazataji dai-dai ba yau kam.....
Gaban Salma ya dinga fad'uwa sanda ta tuna kalan k'aunar dake tsakanin Fawaz da Jamila, sai yanzu abubuwa da dama suka shiga dawowa kwanyarta, ta kuma kai dubanta ga Alh Kabeer tabbas shine mutumin da tayi tozali dashi yana sunbatar Jamila.... Lokaci guda ta runtse idanunta hawaye suka shiga kwaranya mata, ashe shine mahaifin Fawaz.... Cikin sauri ta fice daga parlorn ta tsaya daga can gefen wani dogon wuta k'wari sai shawagi suke saman k'wan wutan, durk'ushewa tayi a wajen tana kuka sosai....
Lubna jiki a sanyaye hawaye na bin k'uncinta ta nufi upstairs, ji take dama batayi witnessing wannan babban abin kunya da takaici ba, tamkar wacce ruwa ya shanye haka ta nufi d'akinta...
Har lokacin Naseer bai daina binsa da kallon mamaki da takaici ba...
K'ok'arin mik'ewa yake yana kuma share jinin dake gefen bakinsa, yazo zai wuce Naseer kai a k'asa.... Lokaci guda saiji yayi Naseer ya damk'o hannunsa saitin kunnensa yake fad'i masa "Yaya idan an girma asan an girma, na zaci ka canza halayyanka tuntuni ashe baka canza ba.... Wa gari ta waya yanzu....? kar ka mance akwai maganar mu da kai....." Daga haka bai jira cewar sa ba ya janyosa suka nufo waje..
Salma tana hangosu ta mik'e tana goge hawayenta lokaci guda ta d'an b'oye jikin doguwar sandar wutan....
Girgiza kai Alh Kabeer yake murya na rawa yake fad'in "Naseer believe me I have nothing to do with what happened at the company, banma san meke....."
Murmushi Naseer yayi kana ya katse sa da fad'in "Don't take me like a complete imbecile now, kana tunanin duk abinda kakeyi a kampanin ban sani bane,.... Sabida kar nasan me kake k'ullawa shiyasa kwanaki kasa a sace ni don kada na samu na hallaci taron da akayi a kwanakin baya, mutumin daka turo baiyi nasara ba..... Yau kuma mutanen daka amshe masu dukiyoyinsu da sunan Santana Corporation sunso k'ona ni Allah bai basu nasara ba, Yaya ka dubi kanka kayi ma kanka hisabi, Allah ba azzalumin kowa bane, ka dubi fuskata ka dubi naka yanzu mu duka mun sami rauni, mutanen da suka bugeni a dalilin ka sai Allah ya kawo d'anka yaji maka irin raunin da akaji min, toh ka sani idan kanada sauran tunani wannan ya isheka ishara...Sannan Fawaz yaron kirki ne kayi pushing d'insa to the world ne shiyasa hakan ta kasance, toh kayi hankali ka gyara halayyarka kafi....." Bai kai aya ba Alh Kabeer ya katse sa da fad'in "You watch your mouth.... Ba a shiga tsakanin d'a da mahaifi kaine zakaji kunya.... Sannan da kake maganar Kampani abunda nayi ma Kampanin nan har ka mutu bazakayi ba... Wait waima since when ka soma damuwa da Kampanin I thought kace kabo baka buk'ata daga kampanin.... Let me remind in case ka mance, ni Kabeer Santana ni ne shugaban Kampanin Santana Corporation sai yanda naga dama zanyi kuma kai baka isa kayi komai ba....." Ya k'arashe yana wani irin huci tamkar zai daki Naseer d'in
Murmusawa Naseer yayi kana ya d'an dafa kafad'an Alh Kabeer da hannunsa lokaci guda ya d'an yi jim tamkar mai tunani kafin ya shiga d'an bubbuga kafad'an Alh Kabeer d'in a hankali kana ya soma fad'in "Emm Yaya, I don't wanna lose the remaining little respect I have for you... Amma tunda haka kace... We shall see.. Kaje gaka ga Kampanin, kuma ko yanzu ka sake tambayata zan sake fad'a maka... I don't want single cent a cikin dukiyar saidai bazan zuba idanu ka wulak'anta hard working d'in Abbah na ba....... Sannan bazan bari son zuciyarka ya cutar da mahaifiyar mu da kuma k'aramar k'anwarmu ba.... I swear I won't allow you...." Ya k'arashe fuskar sa dab dana Alh Kabeer wanda ke faman dariya mai sauti tamkar tab'ebb'e irin dariyan rainin hankali.... Bai kuma fad'in komai ba sai wucewa da yayi ya bar Naseer tsaye a wajen yana binsa da mugun kallo....
Juyawan da zaiyi sukayi idanu hud'u Salma wacce ke rakub'e hawaye na ci gaba da kwarara mata.... Jikin Naseer yayi sanyi sosai, baiso Salma ta tadda Familyn sa haka ba... Yanzu mai zatayi tunani, ta shigo gidan rashin girma da karamci.... Lokaci guda yaji takaicin Yayan sa ya kuma lullub'esa.... A hankali ya tako ya iso yanda take tsaye....
Banda k'una babu abinda zuciyarsa keyi.... Ganin kukanta na k'aruwa ya sanyasa rungumota cikin jikinsa.... A hankali yake furta "Reina I'm sorry.... Harga Allah banso kika tarar da wannan al'amari ba, kiyi hak'uri kinji..."
K'ak'aro murmushi tayi kana tace "Soja Jamila 'yar uwata ce koda bakazo dani ba ya shafe ni nima sannan koda ace ba Jamila bace abunda ya shafe ka ya shafe ni nima.... Ka daina bani hak'uri rayuwa ta gaji haka, ba komai yake zuwa mana yanda muka tsara ba, kuma ba komai muke samu yanda muke so ba, tabbacin mu 'yan Adam kenan..... Saidai a duk yanda rayuwa tazo mana muyi k'ok'ari mu karb'eta hannu bibbiyu sai Allah ya shige mana gaba A DUNIYAR MU.... Allah ya k'ara maka k'ok'ari a bisa wanda kake yi, Allah kuma ya dad'a tsareka ya kareka da kariyan sa..."
Murmushi Naseer yake ba tareda ya iya furta koda kalma ba, a iya tsawon rayuwar sa yana muradin rana irin wannan wanda za'ace ya sami mai kwantar masa da hanakali irin haka abunda ya rasa A DUNIYAR SA... ALLAH Sarki yau gashi Allah ya cika masa burinsa, at least idan baida mahaifiya da zata sauraresa ta tausasa masa zuciya yau sami mata, kuma irin macen da ya jima yana mafarkin samu.... Bai iya furta komai ba sai rungumarta da yayi... A hankali yake furta mata Kalman So......
Sun d'an d'ibi lokaci suna tsaye wajen, duk wannan runguma akan idanun Innah suke yinsa, ganin Naseer na numfashi ba k'aramin tada mata hankali hakan yayi ba... Ta tsane sa, ta tsani rayuwar da yake ciki, ga dukkan alamu suna tsananin son juna shida wannan tsinanniyar yarinya mai suffan mayu.... Kad'a kai kurum tayi had'i da zuk'an sigarinta kana ta sauk'e labulen....
Hannayenta ya rik'e yana dubanta kana ya soma fad'in "Reina inaso nayi magana da Fawaz before we leave, I won't take long kinji...."
Gyad'a masa kai tayi ba tareda ta furta komai ba, hannunta ya rik'o suka nufi wani sashe cikin gidan wanda take tunanin na Naseer d'in ne... Wutace ya kukkuna ya zaunar da ita parlor had'i da kunna mata kayan kallo, saida ya manna mata kiss a chick d'inta kafin ya fice yana fad'in bazai jima ba...
Salma dai jigum kawai tayi tunanin rayuwa a duniyar su ya tsaya mata a rai, kallon TV d'in kawai take ba wai don tana fahimta ba, tunanin ta kacaukam naga 'yar uwarta Jamila, tasan she must be going through a difficult situation, 'yar uwarta tana buk'atar ta, tasan 'yar uwar tata mai kuskure ne amma ita shaida ce cewa Jamila ta repenting, ta gyara halayyarta, she must be brokenhearted sabida tasan kalan soyayyar da take ma Fawaz... Allah sarki Rayuwa A DUNIYAR MU mai zuwa juyi-juyi, takan zo maka ta yanda baka tsammata ba.... A hankali tasa bayan hannunta ta share hawayen ta...
****
"Amma mai yasa baki kirani kin sanar dani tun da wuri ba.....?" cewar Affan dake tsaye gefen Shareefar sosai damuwa ya nuna a fuskar sa...
"Affan wllhi ban zaci abin zai zama haka ba... Kasan Mamy kasan yanda take yin abubuwanta wasu lokutan ba tareda ta sanar da kowa ba..."
Girgiza kai kurum Affan yayi yana kuma duba lokaci, baisan ta yanda zai soma nemo su Mamy a daren nan ba.... Shafe sumar kansa yayi had'i da fuzar da iska lokaci guda ya zauna gijif cikin kujera dake gefensa...
D'an dafasa Shareefah tayi hawaye na neman ciko idanunta, Affan ya d'ago ido yana dubanta lokaci guda tausayinta ya rufesa.. Mik'ewa yayi ya kamo hannunta kana yace "Hey, it's okay.... Kar ki damu kinji zasu dawo, I'm sure zasu dawo or maybe suna gida yanzu haka... Kar ki damu kinji...."
Jinjina masa kai kurum Shareefah tayi ba tareda ta iya furta komai ba... Affan ya sakar mata murmushi kana yace "Idan Daddy ya tambayeki ni tell him d'auko Mamy naje... Insha Allah yanzu zanzo da ita kinji koh...."
Jinjina masa kai tayi kana tace "Allah sa sun dawo..."
Affan ya murmusa yana fad'in "Stop exaggerating things Shareefah, I'm quite sure ko ina suke sun dawo gida by now.... Yanzu zan zo da ita insha Allah..."
Shareefah dai jinsa kurum tayi amma itakam tunda taji wayoyinsu bai shiga jikinta yayi sanyi...
*******
Daga bakin k'ofa yayi tsaye yana duban Fawaz dake rik'e da wasu pills a hannunsa sunfi goma yana k'ok'arin afawa a bakinsa.....
Naseer ya d'anyi gyaran murya wanda hakan ya hana Fawaz afa k'wayoyin...
Naseer ya k'arasa shigowa cikin d'akin had'i da zama gefen Fawaz...
Shiru na 'yan wasu dak'ik'ai ya gifta tsakanin su...
Kaman babu mai cewa komai cikin su Naseer ya d'an muskuta yana duban Fawaz dake dunk'ule da k'wayoyin cikin hannun sa.... Bud'e murya ya d'anyi kana yace
"Do you think taking those pills you holding would make you feel better.?..... Fawaz kai likita ne kasan illar k'waya wa lafiyar ka mu cire a d'abi'ance ko a shari'ance kasan k'waya ba abune mai kyau ga lafiyar ka ba... I know this is not easy for you... But that doesn't mean zakayi duk abinda zuciyarka ta raya maka.... Fawaz challenges na rayuwa dole musan yanda zamu dinga overcoming d'insu... Yanke hukunci cikin fushi da b'acin rai ba komai zai jefa mu ciki ba sai tarin nada da dana sani, wanda hausawa ke cema k'eya.... Fawaz duk abinda ya sameka a rayuwa a matsayinka na musulmi ka fawwala wa Allah kada ka biyewa zuciyarka... Mahaifiyarka tana buk'atar ka... You need to be strong, you're not alone.. You've me and I'll always be here for you kaji koh...."
Hawaye Fawaz yake baisan sanda ya rungume Naseer yana kuka sosai ba...
"Uncle I'm sorry... I know I shouldn't have reacted that way... But Uncle I just can't stand that man anymore... I hate him, wllhi bana fatan na bud'e idanu na na kuma ganinsa ballantana ace ina kwana gida d'aya dashi.... Uncle to be honest with you I'm sick and tired of this life being so unfair..."
Saurin toshe bakin Fawaz Naseer yayi yana girgiza kai kana yace "Fawaz ka daina magana kaman ba musulmi ba, ka karb'i k'addara a duk yanda tazo maka... Kar na kuma jin kayi magana makamancin haka okay... We'll face this together as family..."
Gyad'a masa kai kurum Fawaz yayi yana share hawayen sa kafin Naseer ya mik'a masa hannu yace "Give me those..."
Babu musu fawaz ya mik'a masa k'wayoyin kafin ya tak'ure ya kwanta saman gadon sa...
Shafa sumar Fawaz d'in Naseer yayi kafin ya gyara masa kwanciyar sa ya Jawa bedcover ya rufa masa... Ya d'an jima yana zaune gefensa yana tunanin yanda rayuwa take zuwa masu... A hankali ya furta "Alhamdulillah ala kulli halin...."
Mik'ewa yayi da k'yar don gaba d'aya jikinsa ciwo yake masa, saida ya sumbaci sumar Fawaz kafin ya fice had'i da kashe masa fitila...
Fawaz da idanunsa ke lumshe wasu hawayen ne masu d'umi suka zubo masa, baisan yanda rayuwa zata kasance ba idan ya rasa Uncle Naseer, mutunin da yake fahimtar sa fiye da kowa....
Tsayuwa yayi jikin kujeran da take kwance barci yayi gaba da ita, a hankali ya zagayo ya zauna kusan kanta..... K'uri yayima fuskar ta, kana ganin barcin zaka fahimci cikin tsoro tayisa...
🌖🌖 *A DUNIYAR MU*🌖🌖
*51*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin barci take jin kaman hannun mutum a fuskarta... A hankali ta ware idanunta nan kuwa sukayi idanu hud'u da Naseer... Murmushi ya sakar mata kana yace "Na tashe ki koh...."..
D'an yunk'ura tayi ta mik'e tana musttsuke idanu da duka hannayenta biyu don batasan sa'in da barci yayi gaba da ita ba... Likaci guda takai dubanta ga agogon bango dake mak'ale a parlorn ya nuna k'arfe shabiyu da wasu dak'ik'ai... Zaro idanu waje tayi tana dubansa kana tace "Soja mu tafi dan Allah... Inason sanin halin da Addah ke ciki...."
D'an jim Naseer yayi kana yace "Reina kiyi hak'uri mu kwana a nan, gobe da sassafe idan Allah ya yarda sai mu tafi, I can't see clearly, kinga dare yayi sosai...."
Shiru Salma tayi tana dubansa har lokacin jinin da ya taru gefen idanunsa bai sake ba... D'an sadda kanta k'asa tayi had'i da jinjina kan nata... Taji wani iri, Soja zaiga kaman bata damu da lafiyan sa ba, baima kamata yayi driving a halin da yake ciki ba.
"Taso muje ki kwanta...." ya fad'i yana k'ok'arin rik'o hannunta... K'irjinta sai bugu yake tana tunanin da yanda zata soma kwana d'aki guda da Soja...
Kai tsaye cikin bedroom d'in nasa suka nufa, mamaki ya cika Salma ganin d'akin tas-tas har wani k'amshi yake irin k'amshin da Soja keyi, kenan harta d'akinsa ya kama k'amshin sa sab'anin wasu mazaje da saidai kaji tsamin daud'ansu ya kame d'akunan barcin su.... Ta kuma yarda Soja d'an gayun k'arshe ne, komai nasa well arranged gwanin ban sha'awa...
Murmushi ya sakar mata ganin tayi tasye tana rarraba idanu kana yace "Ki saki jikin ki gidanki ne nan kuma d'akin ki ne kinji koh..."
Murmushin yak'e ta sakar masa kafin ta zauna daga can angle tana kallon wasu hotuna da aka jere su saman wani d'an stand ko wanne cikin k'aramin frame... Naseer na ficewa ta k'arasa tana kallon hotunan sosai... Wasu shida abokan aikinsa ne da kayan soji sun rirrik'e bindigogi jirage na shawagi a bayan su wasu kuwa shi kad'aine.... Idanunta ya sauk'a kan wani hoton dattijon bature rik'e da yaro wanda bazai gaza shekaru goma shabiyu ba ko ba'a fad'a mata ba Naseer ne da mahaifin sa don tsananin kamannin su... D'aukan hoton tayi tana kallo tana murmushi.. Da ganin irin rik'on da sukayi ma juna zaka fahimci sun shak'u sosai.... Tana nan tsaye Naseer ya shigo da alama waya ya ida yi...
Har ya iso yanda take tsaye batasan ya shigo ba sai jin mutum tayi a bayanta ya rungume ta ya had'e hoton da hannayen ta ya rik'e
"Kin gane su waye a hoton....?" ya tambaya yana sauk'o da fuskar sa dab nata...
Jinjina masa kai take lokaci guda tana murmushi kana tace "Abbah ne da little Soja..."
Murmushi Naseer yayi mai bayyan hak'wara kana yace "Ashe dai zaki iya gane mijin naki.."
Saurin rufe fuskar ta tayi tana murmushi alamun taji kunya....
A hankali Naseer ya ajiye hoton kana ya masu masauk'i saman kujera dake gefensu lokaci guda yake rikita ta da salon soyayyar sa...
Gaba d'aya ya rikita mata lissafi, murya na rawa take fad'in "Soja nidai barci nake ji...."
Cikin kunnenta yake rad'a mata "Kar ki damu barcin zamuyi, maza tashi ki canza wannan kayan naki zai tak'uraki.."
Ai baikai aya ba ta shiga girgiza masa kai kana tace "A'a zan iya haka, bai tak'urani ba ai... Ka gani, ka gani..." Ta shiga k'ok'arin mik'ewa tana jajjawo rigar nata k'asa... Gaba d'aya ta birkice...
Murmushi kawai Naseer yake yana kallon yanda tsoro ya bayyana sosai a fuskarta kafin ya janyota jikinsa yana fad'in "Relax Reina, babu abinda zan maki, kar ki damu zanyi hak'uri har sai randa kika zama ready, no need to rush things... Sleeping beside you yafi mun komai dad'i A DUNIYAR MU, na bud'e idanu na ganki a gefena, na fara yin tozali da kyakkyawar fuskar ki each and every blessed day...." Ya k'arashe idanunsa a lumshe still tana mak'ale cikin jikinsa...
Lamo tayi cikin jikin nasa kunyar sa da k'aunar sa na kuma dabaibaye mata zuciya....
*****
A masallaci Naseer ya had'u da Fawaz bayan sun ida sallan asuba... Sosai Naseer ya kuma masa nasiha don sun d'an jima cikin masallacin har saida gari ya soma wayewa...
Salma kam duban kanta tayi jikin mirror tana kuma tuno kalan baccin da sukayi jiya itada Soja, a hankali ta saki murmushi tana rintse idanunta, ta d'ago hannu tana duba yanda take yawo cikin pyjamas d'insa... Wani sabon kunyar sa ya kuma lullub'eta... Uwa uba soyayyar da ya kasheta dashi a jiya, gaskiya Sojanta d'aya ne tamkar ga dubu.. Sam bata zaci ya iya soyayya irin haka ba... Sauri-sauri ta shige bathroom d'insa don yin wanka tasan idan yana d'akin bazata iya ba...
Kayan k'amshi kala-kala a bathroom d'in, ko wanne suna ma'ajiyan su, kayan gyaran suma sunfi komai yawa a toilet d'in, ba sai ance maka ba yana son kwalliyan suma... Wanda take zaton shower jell ne ta d'auka tana karantawa, aiko shid'in ne nan ta samu tayi wankanta..
Cikin sand'a take fitowa daga bathroom d'in tana addu'an Allah sa bai shigo d'akin ba... Ga mamakinta wata doguwar riga ta hanga ajiye saman gadon nasa had'e da mayafinta... Murmushi tayi sanda ta k'araso tana k'arema rigar kallo... Tabbacin bashi a d'akin ya sanyata sakin jiki ta k'are shirinta tsaf, rigar kuwa tai mata kyau sosai a jikinta... A hankali take jiyo magana daga parlorn nasa... Kaman wata b'arauniya haka ta soma sand'a ta nufi parlorn...
Ganin shida Lubna ce ya sanyata d'an sauk'e ajiyan zuciya tasa kai zata koma caraf Lubna ta hangota... Mik'ewa tayi tana murmushi ta isa gareta lokaci guda tayi hugging d'inta tana fad'in "Auntyn mu sannu da zuwa, ai bansan tare kuke tun jiya ba...."
Salma dai murmushi kawai take ba tareda ta Saki jiki da Lubnar ba, don bata mance karonsu da Lubnar ba wancan lokacin sanda ta ganta tareda Affan....
"Dama fitowarki nake jira mu k'arasa ciki mu karya..."
Salma ta dubi Lubna ta dubi Naseer...
Sarai ya fahimci bata Saki jikinta bane...
"Lubna idan batason shiga ciki ki barta taci a nan...." cewar Naseer dake k'ok'arin mik'ewa...
"Kai Yaya please mana..."
Kafin yayi magana Salma tace "Ba komai zan shiga ciki..."
Naseer ya d'an k'araso dab da ita kana yace "Are you sure baki tak'ura ba....?"
Murmushi ta sakar masa had'i da jinjina kai...
Lubna sai murmushi take hannunta sakale cikin na Salmar... Cikeda murna tace "Yauwa Antin mu, ni wllhi Yaya dama kar ku tafi ku zauna a nan kawai...."
Murmushi kawai Naseer yayi had'i da d'an dungurin Lubna kana yace "Ki kular min da ita sai na shigo...." daga haka ya nufi bedroom...
"An gama Yaya...." Lubna tace sanda suka soma tafiya...
Muryar Lubna data jiyo tana introducing matar Naseer wa ma'aikatan gidan ya sanyata nufowa k'asa babu shiri.. Batasan Naseer ya rik'a har haka ba, ya kawo mace cikin gidan ya kwana da ita ba tareda sanin ta ba.....
*******
Sassafe ya fice a gidan ba tareda kowa ya sani ba, ganin babu motar mahaifinsa a parking lot ya tabbatar masa da cewa shima ya fice....
Tana nan tak'ure a d'aki Ilham na faman rarrashinta suka jiyo muryar Momy daga parlor tana fad'in "Fawaz kayi hak'uri bazaka iya ganinta a yanzu ba..."
Fawaz ya d'an shafi sumar sa kana yace "Momy dan Allah ki k'yaleni na ganta...."
"Fawaz don't make this difficult please leave...." Momy ta kuma fad'i tana jijjiga Falaq dake goye a bayanta....
"Momy bazan bar wajen nan ba sai na mata magana, dan Allah ki k'yaleni na ganta...."
Kafin Momy ta sami zarafin magana sai ganin Jamila sukayi ta k'araso wajen, idanunta luhu-luhu, kana ganinta kasan batayi barci ba daren jiya...
A hankali ta bud'e murya idanunta naga Fawaz wanda shima d'in ita yake duba sai faman huci yake,
"Momy ba damuwa zan gansa...." tayi maganar murya a dake...
Momy dai kallonsu su duka biyu tayi tamkar wanda suke jira a hura masu wusil d'in wasan dambe kana ta dubi Jamila da kyau tace "Are you sure daughter...?"
Jinjina mata kai kurum Jamila tayi ba tareda tace komai ba....
Momy tana shigewa Jamila ta k'araso cikin parlorn dai-dai lokacin da Fawaz ma ya k'araso...
*******
Gaba d'aya Salma ta razana da ganin mahaifiyar Naseer, karonsu na farko a gidan Momy da rashin mutunci tazo masu, amma yau har cewa take ta taso daga saman carpet ta dawo bisa dining table, kujeran ma kusan nata...
Salma dai sai juya cokalin hannunta take ba tareda ta iya saka komai cikinta ba....
Innah ta murmusa tana kuma k'arema Salma kallo kana tace "Ki saki jikinki ki ci abinci kinji koh....." Ta juya tana kallon Mama Tani dake kuma ajiye wasu jugs na alfarma wanda duk safiya sai an markad'e natural fruits d'abi'ace na gidan, kana tace "Tani kawo mata abin shan gabanta, zuba mata ta sha ya bud'e mata cikin nata...."
Mama Tani dai jinjina kai kurum tayi tana mamakin soyayyan da Innah take wa matar Naseer, Innah da bata sauk'owa k'asa sai wajajen azahar yau gashi ta sauk'o har tana karin kumallo da farar safiya sabida matar Naseer...
Lubna ta sauk'o daga upstairs hannunta d'auke da handbag kana ta dubi Salma tana murmushi tace "Auntyn mu ni na wuce sch, sai mun sake had'uwa...."
Murmushi kawai Salma ta sakar mata had'i da jinjina kai... Lubna ta kuma yima Innah sallama kafin ta fice.... Ta window Innah ke hango Deeni yanda yake rawar k'afa sanda Lubna ta k'araso garesa... A hankali ta saki k'wafa kafin ta maido da dubanta ga Salma
Ga mamakin Salma matsowa Innah tayi dab da ita tana k'ok'arin manno fuskarta dana Salmar... Gaban Salma sai fad'uwa yake lokaci guda ta shiga matsawa da baya....
Innah ta murmusa kafin tasa hannunta wanda yake tamkar k'ashi zalla ta rik'o Salma gam, cikin kunnenta take rad'a mata, meye kike matsawa baya baki sona ne, ko ban maki bane.... Gwara ki bari na k'aunace ki idan kina son zama da d'ana a matsayin miji, da ganinki k'aramar kilaki ce tunda kika biyo shi har gida kika kwana a d'akinsa tun bai kawo mana ke ya nuna a matsayin mata ba...."
Bugun zuciyar Salma ya k'aru, wai mahaifiyar mijinta ne wannan... Baki na rawa ta soma fad'in "Innah wllhi ni...ni ba kilaki bac...." Kasa ci gaba da maganar tayi jin hannun Innah a wasu sassa na jikinta..... Ta nemi ihu ta rasa sai kyarma da jikinta keyi... Innalillahi kawai take nanatawa cikin zuciyarta don ta kasa katab'us... Abu saikace a film... Ta kasa gaskgata abinda take ji wai mahaifiyar mijinta ke mata.... A zabure take k'ok'arin mik'ewa jikinta na karkarwa.... Innah ta murmusa had'i da d'an matsawa gefe tana mai duban Salma da jikinta ke tsananin rawa kana tace " Kar kiji tsoro ba abinda kike tunani bane.... Bincikawa nake naga wacce irin mace aka aura wa d'ana... Kinsan DUNIYAR MU saida bincike...." Ta k'arashe tana wani irin murmushi...
Salma kam gaba d'aya ta rasa bakin magana, ko motsawa ta kasa sabida tsoron duniya da ya cika mata zuciya... Abu tamkar a labarun mujiraman fari....
Sosai idanun Naseer ke haifar masa da tsoro shiyasa ma bai iya masa k'arya, tun ranar da ya tsorata sa da bindiga ya daina masa k'arya gameda ciwon Aunty Saudat....
Dr Yusuf ya k'arashe dubata da zaiyi kana ya d'an d'ago yana duban Naseer d'in had'i da gyaran murya..
"Akwai improvement sosai sabida ga dukkan alamu memory d'inta ka iya dawowa koda wani lokaci..."
Naseer ya murmusa yana duban Aunty Saudat wacce ta masa k'uri...
D'an k'arasowa yayi ya mik'awa Dr Yusuf hannu sukayi masabaha kana yace "Dr this should be between us, ko ma Fawaz ban yarda ka fad'i ba ballanata mijinta kafihmce ni....?"
Cikin sauri Dr Yusuf ya jinjina masa kai kana yace "Insha Allah Captain zanyi yanda kace, sannan therapy class d'in zai iya somawa nanda wasu satuttuka..."
Naseer ya murmusa had'i da jinjina kai kana ya kamo hannun Dr Yusuf yace "I'll walk you out..."
Tare suka fice Aunty Saudat tabi bayansu da kallo... A hankali ta sauk'e ajiyan zuciya ta tuna abubuwa da dama da suka faru A DUNIYAR SU... Wani hoto dake dunk'ule a hannunta ta warware tana gani.... Idanunta sun kad'a sunyi jazir, idan akwai wanda tafi tsana a duniya bai wuce mutumin dake cikin hoton ba..... A hankali tasa bayan hannunta ta share hawayen da suka zubo mata... Dole taci gaba da pretending hauka muddin tanaso ta taimaka wa Naseer wajen gano abubuwa da dama da suka shige masa duhu A DUNIYAR SA..
****
"Sabida kud'i ne, sabida kud'i kika zab'i wancan rayuwar.... Fine, idan don kud'i gasu nan, you can have it... Karb'e su duka...." Tamkar tab'ebb'e haka yake ciro kud'ad'e a aljihun sa yana watsa mata....
Girgiza kai kawai take tana dubansa kafin tace "Fawaz duk abinda ka fad'i akaina haka ne, kuma na yarda da wannan hausa da hausawa ke cewa kwad'ayi mabud'in wahala, nasan na shiga matsi da tasko na rayuwa amma banbi hanyar da ya dace ba... Fawaz banida zab'i a wancan lokacin, mai zakace ga d'iyar da take dab da rasa mahaifiyarta dake tsananin jinya, mai zakace ga likitoci da suka juya baya suka k'i taimakawa, mai zakace ga masu kud'i da suka d'auki taimako sana'a musamman ga d'iya mace A DUNIYAR MU... Fawaz wannan shine labarin Jamila, wannan shine dalilin da ya jefa Jamila halin data tsinci kanta ciki A DUNIYAR MU... Alhamdulillah, ko ban kasance da kai ba ko yau na koma ga mahalicci na zanyi farinciki sabida na daina aikata sab'on da nakeyi., Abu na k'arshe da zan rok'a daga gareka shine yafiyarka, Ka yafe min Fawaz, nasan na zalunceka rashin sanar dakai ko ni wacece tun a fari... Amma ka sani nayi hakan ne badon komai ba sai don k'aunarka da nakeyi, ina tsoron kada na sanar dakai bak'in laifin da nayi a baya ka k'yamaceni ka gujeni..." ta k'arashe muryarta na tsananin rawa...
Jikin Fawaz yayi sanyi sosai, ji yayi yana son sanin asalin labarin su... A hankali ya zauna daga can kujeran da ya mik'e idanunsa naga wani b'abgaren yake fad'in "Bansan ko zan iya yafe maki ba sai kin sanar dani labarinki gaba d'aya..."
Ta kuma sa bayan hannu tana goge hawayen da suka wanke mata fuska, tausayin junansu ya cikata ganin yanda Fawaz ya bata baya alamun baya k'aunar su had'a idanu...
K'ak'aro murmushi tayi kana ta gyara zama kafin ta soma basa labarinsu gaba d'aya tun iyayenta suna raye har zuwa aurenta da Alh Nuhu, da kalan gwagwarmayan da suka sha a rayuwa, rasa mahaifinsu da kuma k'ona masu muhalli da akayi dare tsaka, ciwon mahaifiyarsu da irin wahalan data sha wajen neman taimako.... Bata ankare ba sai jiyo sautin kukansa da tayi... Lokaci guda itama ta kasa ci gaba da magana sai kuka....
Sabon tsanar mahaifinsa ne ya cika zuciyarsa sanda yaji shine ummul haba'isan komai, duk tarin dukiya irin nasa ya kasa taimaka mata saida ya nemi wani abu daga gareta... Cikin zuciyarsa yake mamakin yanda mutane suka kasance babu tausayi balle imani A DUNIYAR MU... Jin kukan nata yak'i k'arewa ya sanyasa juyowa yana dubanta, kaman zaiyi magana sai kuma ya kasa, cikin sauri ya mik'e ya fice daga gidan idanunsa basu daina zuban hawaye ba....
*****
Kallo Daddy yake binsu dashi daga Shareefar har Affan d'in don izuwa wannan lokaci sun rasa mai zasu sanar dashi...
"Affan ku fad'a min yanda mahaifiyarku take..." Daddy ya kuma fad'i yana kallon Affan d'in
Kame-kame Affan ya soma don bison sanar da Daddy gaskiyar lamarin regarding his health condition...
Tuni hawaye sun soma bin k'uncin Shareefah...
Girgiza kai Daddy ya d'anyi hawaye na gangaro masa, idanunsa naga silin yake fad'in "Nasan bazata iya zuwa nan ba, bazata iya dubana ba.. Asma'u bazata iya kallona da idanunta ba... Da zata sami dama da ta k'arasa kasheni kaman yanda take buri..."
Gaba d'aya cak suka tsaya suna duban Daddy dake wasu irin maganganu wanda suka fi danganta maganganun nasa da sunbatu....
*******
Da izzansa yake horn yanson shiga Kamfanin... Sabbin securities wanda baisan dasu ba yaga guda d'aya daga cikin su ya nufo sa...
"Sir kayi hak'uri dokace aka d'oramu akanta cewa kada mu barka ka shiga..."
Shaye da mamaki Kabeer Santana ke duban mutumin kana yayi wata dariyar rainin hankali yace "Ka tab'a jin yanda shugaban k'asa yazo shiga k'asar sa aka hanasa....?"
"Eh toh mu aikin mu muke, bazaka shiga kampanin nan ba....."
Kan bala'incan... Dukda kumburin dake fuskar sa bai hanasa banko k'ofar motar ya fito yana wani irin huci yake fad'in "Uban waye yace kada ku barni na shiga nida Kampani na... Ko baku gane ni bane, I am Kabeer Santana, owner of Santana Corporation,..."
Murmushi security d'in yayi kana yace "I don't care who the hell you are, I'm only doing my job here, kuma aikina shine na hanaka shiga, kuma bazaka shiga ba no matter what you does..."
Kasa furta komai yayi sabida tsananin mamaki, yau shine aka hanasa shiga Kampanin sa, ba kowane ya fad'o ransa ba illa Naseer, ya tuna argument d'insu na jiya, lallai Naseer ya taro yak'in da bazai ci ba... Dole ya nuna masa cewa shid'in yaro ne, ya kashe ubansa ma ballantana shi.... Cikin sauri ya shige motar sa ya tada ya bar wajen yana k'ok'arin kunna sigari. banda tafasa babu abinda zuciyarsa ke masa...
*******
Zaune kurum take a motar amma sam hankalinta da tunaninta baiga labarun da yake kan mata, abinda Innah ta mata ya tsaya mata a rai, itakam jikinta na bata wannan mata ba itace ta haifi Naseer ba... Sam zuciyarta tak 'iaminta mata cewa Innah ce mahaifiyar Naseer... Muryarsa da ta jiyo ya ambato sunanta ya sanyata saurin d'agowa tana dubansa
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*52*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Gaba d'aya ta zamto wata irin sukuku har yanzu tsoro da tunanin abinda Innah tai mata bai bar jikinta ba, Inama zata iya sanar da Soja ga abinda mahaifiyar sa tai mata, kai ta ina zama ta soma sanar dashi, ta kasa sanar dashi ga abinda Shareefah ke aikatawa ballanta Innar sa mahaifiyar sa.... Innalillahi wa Inna'ilaihirajji'un... Wani irin rayuwa muka tsinci kanmu ciki A DUNIYAR MU....?
Muryar Naseer ya kuma katse mata tunanin nata....
"Salma kin tabbata babu abinda ke damunki....?"
K'uri ta masa tausayinsa na ratsa zuciyarta... Cikin sauri kuma ta soma girgiza kai had'i da d'auke fuska daga barin kallon nasa kana tace "Babu... Babu komai... Kawai tunanin Addah nake...." Ta k'arashe murya na rawa...
Naseer ya d'an murmusa kafin yace "Kar ki damu yanzu zamuje ki ganta kinji koh...."
Gyad'a masa kai kurum tayi ba tareda tace komai ba... Cikin tsanaki ya maida hankalinsa ga tuk'i...
****
Girgiza kai Affan yake yana rik'e da hannun mahaifinsa murya na rawa ya soma fad'in "Daddy me kake fad'i... Daddy bamu fahimceka ba... Daddy ka mana bayani dan Allah...."
Shareefah kam banda hawaye babu abinda take....
Hawaye basu daina zubowa daga idanun Daddy ba, dad'a matse hannun Affan yayi murya na rawa yake ci gaba da fad'in "Affan ni kaina ban sani ba..... Ni kaina ban zaci zan kuma bud'e idanu A DUNIYAR MU ba, nasan Asma'u tanada son abin duniya amma ko kusa ban zaci zata iya kasheni ba, da ace mafarki nake da sai ya fimin sauki fiye da zahiri....."
Cikin sauri Affan ya k'wace hannun sa daga rik'on da Daddy ya masa yana mai ci gaba da girgiza kai yake fad'in "No...no no Daddy... I'm quite sure something's wrong,.."
Duban Shareefah dake tsaye tana hawaye yayi kana yace "Kije ki kirawo Doctors d'in nan.... Basu duba Daddy sosai ba... I'm sure fad'owar da yayi ya tab'a masa brain. .kiyi sauri Shareefah...." Ya k'arashe yana kuma damk'e hannun Daddy sosai cikin nasa....
Shareefah ta shiga jinjina kai tana fad'in "Yeah sure... Haka ne Affan...."
Kallonsu kurum Daddy yake cikeda tausayi har Shareefah takai k'ofa ta jiyo muryar sa na fad'in "Kar ki kira wani likita Shareefah, babu abinda ya sami kwanyata, a cikin hankalina nake, nasan dole irin haka ta kasance idan na sanar daku..... Banso fad'a maku ba, saidai baki na ya gaza b'oye abinda zuciyata ke son b'oyewa... Affan mahaifiyarku farautar rayuwana take....."
Bibbiyu Affan ya soma gani... Jiri na neman kada shi... Kalamun Daddy sai faman yawo suke a kwanyar sa... Mahaifiyar sa mahaifiyar sa ke neman rayuwar mahaifinsa.... Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un.... Wace irin rayuwa ce wannan wace irin duniya ce wannan.... Kasa motsa koda d'an yatsan sa Affan yayi sai bugu da zuciyarsa ke masa...
Shareefah kam k'unshe bakinta tayi tana kuka lokaci guda ta fincike k'ofan d'akin ta fice a guje tana girgiza kai....
********
Momy suka samu a parlor tayi jigum ta rapka uban tagumi... Naseer da Momy suka soma gaisawa Salma kam tuni ta shige ciki da saurin gaske.....
Tak'ure ta hangi Jamila sai rawan sanyi take alamun zazzab'i na kad'a ta....
"Addah...!" ta fad'i murya na rawa....
Jamila ta d'ago rinannun idanun nata tana duban 'yar uwarta.... Cikin sauri ta mik'e ta nufi Salma dukda kad'awa da jikinta keyi......
Rungume juna sukayi hawaye na zubo masu.... Cikin muryar kuka Jamila ke fad'in "Salma I can't take it anymore... I just can't...."
K'ok'arin maida hawayenta Salma keyi murya na rawa take fad'in "I'm here.. I'm here sister, you're not alone kinji...."
"Salma meyasa rayuwa haka... Why.. Why life has to be so unfair, why is this happening, Salma bazan iya ba...."
Hannayenta Salma ta rik'o tana share hawayenta lokaci guda ta masu masauk'i saman katifa kafin ta rik'o hannayen Jamilar, cikin muryar kwantar da hankali ta soma fad'in "Addah all these are part of life challenges, A DUNIYAR MU mun shiga jarabawa da dama, A DUNIYAR MU mun had'u da mutane kala daban-daban A DUNIYAR MU muna kan ganin jarabawa da k'addara na rayuwa... Amma insha Allah this too shall pass, komai zai wuce ya zamto tarihi, nasan ubangijin mu akwai tanadin da ya mana na jin dad'i ko bamu samu A DUNIYAR MU ba, inai mana fatan mu samu a lahirar mu.... Kar ki manta hadisi ne guda Manzonmu tsira da amincin Allah su k'ara tabbata a gareshi yace _Ita wannan Duniya kurkukun mumini ne sannan kuma Aljannar kafiri ne._
Duk abubuwan da suke faruwa damu A DUNIYAR MU tuni Allah ya hukunta faruwan hakan.... Mu karb'i k'addaran mu hannu bibbiyu, kaman yanda sauran suka wuce haka wannan ma zai wuce... Ki kwantar da hankalin ki, ki mik'a wa Allah lamuranki don shine majib'icin Al'amran mu... You have us, ni Ilham your daughter Momy, ga kuma Soja.... Bazamu tab'a barinki ba, together we will overcome this kinji...." ta k'arashe murmushi saman fuskarta dukda hawaye dake gangarowa daga idanun nata...
K'ak'aro murmushi Jamila tayi ba tareda ta iya furta komai ba ta rungume Salma hawaye suna kuma zubo mata....
Naseer ya d'an shafi sumar sa yana duban Momy kana ya fuzar da iska had'i da d'an ware hannaye da idanu yace "Momy wani sa'in abubuwan da suke faruwa A DUNIYAR MU sai naga kaman mu kad'ai Allah yake jarabta, tabbas idan bakada k'arfin imani zaka iya butulce ma rahamar ubangijin ka.... A kullum idan na tuna iyayen kakkanni na har suka koma ga mahaliccin su mushirikai ne sai nace toh ni Allah ya min babban rahama da ya tsamo ni daga cikin su na kasance a nan kuma ina mai kad'aita shi... Babu rahamar da tafi wannan A DUNIYAR MU, Momy duk wani tashin hankalin da na tsinci kaina ciki idan na tuna wannan rahaman kawai sai nace Alhamdulillah...."
Murmushi kurum Momy take tana dubansa kana tace "Naseer haske, hak'ik'a haska hanyar jama'a da dama A DUNIYAR MU, idan na tuna rahamar da Allah yayi min ya had'ani da kai har na karb'i addinin islama sai nace had'uwa da kai haske ne a gareni... Mutane masu kyawawan d'abi'a irin naka dole su had'u da iftila'i da jarabawa da dama a rayuwa... Har kullum bazan gushe ba inai maka addu'an cin nasara a rayuwar ka.... Allah yayi maka albarka Naseer...."
Bai iya furta komai ba sai wani irin sanyi da jikinsa yayi ba tareda sanin dalili ba......
*******
Bayan wani gini ta samu nan cikin asibitin ta zauna saman wasu dakali taci gaba da rusa kukanta, nadama mai tarin yawa ya shigo ratuwarta.... Duk sab'awa Allah da takeyi bata tunanin zata iya kisa, balle har tayi tunanin kashe mijinta uban 'ya'yanta, ta tuna yanda take k'aunar Naseer ta yaya zata soma tunanin kashesa.... Lokaci guda wani sabon kuka ya kufce mata... D'umin da taji daga k'asanta ya sanyata daina kukan da take tayi saurin mik'ewa tsaye sabida k'aik'ayi da ya addabeta daga k'asan nata.... Tsoro bai gama cikata ba saida taji wani wari-wari na fitowa daga jikinta, toh ko dai gudawa ne ke zubo mata, jikinta ya shiga rawa sanda ta soma janyo skirt d'inta tana k'ok'arin dubawa.... Wani k'ara ta kuma sakewa sanda taga wani koren ruwa mai warin gaske na fitowa daga jikinta yana bin k'afafun ta......
******
"Addah akwai zazzab'i a jikin ki dan Allah ki bari muje asibiti" Salma ta kuma fad'i kaman zatayi kuka...
Murmushi Jamila tayi kana tace "Salma ciwon kai ne kawai kar ki damu zai daina...."
Ilham dake rungume da Falaq a gefensu tace "Addah don Allah kije asibiti kinji dan Allah...."
Jamila ta kamo hannun Ilham tace "Auta kar ki damu zanji sauk'i ne...."
K'iranta Auta da tayi sai tayi sounding tamkar Innon su, haka take kiran Ilham Auta... Lokaci guda gaban Ilham ya yanke ya fad'i... Wasu irin tunani sarara suka shiga yawo a kwanyarta.....
Momy ce ta d'an masu knocking ta shigo had'i da k'ak'aro murmushi ta sakar masu, sai sannan Salma suka samu gaisawa itada Momy...
"Salma ko zakuje duba jikin Daddyn ni sai na zauna da Addarku a gida idan yaso daga baya sai muje...." Cewar Momy dake amsar Falaq daga hannun Ilham....
Ilham tayi karaf tace "Nima inason zuwa Momy, inaso na gaisar da Daddy naji muryar sa...." D'an murmusawa Momy tayi tana jinjina yarintar Ilham kana tace "Ai sai kuje gaba d'aya harda Addar taku...."
Jamila tayi saurin girgiza kai had'i da janyo bargo ta rufe k'afafunta kana tace "Momy bazan iya zuwa ba.... Su dai suje kawai daga baya zanje....."
Salma dake binsu da kallon mamaki bud'e murya tayi kana tace "Daddy ya farfad'o ne..?"
A tare Ilham da Momy suka jinjina mata kai kana Momy ta d'aura da "Ai tun daren jiya ya farfad'o inaga Affan ya mance ne bai sanar da Naseer ba don shima sai yanzu nake sanar dashi...."
Jigum Salma tayi dukda hamdala da murna da take jerowa can k'asar zuciyarta tsoron farkawan Daddyn take, tasan Soja ya kamu da soyayyarta yanzu itama kuma ta kamu da soyayyarsa, tsoronta kada Soja ya saketa kaman yanda yace a baya...... Lokaci guda taji jikinta yayi sanyi k'alau... Momy ta d'an dafata kana tace "Maza tashi kuje yana jiranku a parlor..."
Jiki a sanyaye Salma ta mik'e had'i da k'arasawa ta rik'o hannun Ilham dake k'ok'arin zura hijab d'inta.....
Naseer na hango su ya mik'e tsaye yana zura hannaye cikin aljihu lokaci guda yake sakarwa Salma murmushi, itama d'in k'ak'aro murmushin tayi ta sakar masa kafin yace "Mujen ku koh...."
Jin muryarsa yasa Ilham soma gaidasa, ya amsa mata da sakin fuska had'i da tambayanta k'arfin jiki, Ilham ta amsa da "Jiki yayi sauk'i sosai.."
"Allah ya k'ara afuwa ya dad'a kiyayewa..."
Ilham na murmushi ta amsa masa, kafin taci gaba da lalumen hanya da sandar ta ta nufi k'ofa...
K'arasowa Naseer yayi ya d'an rank'wafo da fuskar sa dai-dai fuskar Salma yana mai gyara mata mayafinta data janyosa ya rufe mata fuska sosai don bataso Naseer yaga kukan da take, cikin sassanyar murya yace "How's she....?"
Salma ta d'an saka yatsa guda tana share idanunta d'aya da hawaye ke mak'ale ciki kana ta jinjina kai tace "Yayi affecting d'inta sosai.... Amma insha Allah zai wuce.."
Naseer ya d'an k'ak'aro murmushi had'i da sakalo hannun Salma guda murya can k'asa yake furta "Ina sonki....."
Murmushi kawai ta d'anyi kafin suka fice....
******
Tafe yake da wasu files a hannunsa ya samu ya d'an gudu ma tarin matan da yake dubawa a matsayin sa na gynecologist, kasancewar yau talata ya kasance shine da duty......
A hankali yake jiyo sautin kuka har ya k'araso wajen, da shike mutane basu faye bin wajen ba shiyasa sam baiji mamakin jiyo sautin kukan mutum a wajen ba...
Yanda ya hangeta kanta kife da gwiwa ga kudaje sai shawagi suke sun yanyameta dukda cewa kallo guda zaka mata ka fahimci 'yar gayun k'arshece amma wannan likitan yayi mamakin yanyameta da kudaje sukayi....
Saida ya d'an k'araso kusanta sosai yaji warin dake tashi a jikinta
D'an toshe hancinsa yayi kafin ya isa gareta yana mai sallama....
Shareefah tana d'ago kai ta kuma fashewa da kuka tana fad'in "Malam kar kazo kusana dan Allah ka tafi ka k'yaleni...."
Mamaki ya cika likitan a zatonsa tana d'aya daga cikin matan da sukazo asibitin don ganinshi, sabida har bucking d'insa ake, yanayinta kawai ya gane ya gane tana tsananin buk'atan taimako....
Hannu bibbiyu Shareefah ta saka tana susa gabanta... Likitan nan ya d'anyi saurin d'auke kai cikedata tausayi kana yace "Wani Dr kikazo gani...."
Cikin kuka Shareefah take fad'in "Ba Dr nazo gani ba kuma bazanga wani likita ba,... Dan Allah bawan Allah ka tafi ka k'yaleni naji da abinda nake ji....." Ta k'arashe tana susa harda tsalle, ji take tamkar ta cire skirt d'in tayi wurgi dashi....
Tausayinta ya cika likitan nan, akwai mata masu fama da lalura mai shige irin na wannan mata akasari kunya yakan hanasu ganin likita har ya zame masu babban ciwo, wanda wasu daga cikinsu shaye-shayen jahilci da cushe-cushe da sunan maganin mata shike janyo masu hakan, wasu kuma ta hanyar fasik'anci suke samu musamman mata masu bin jinsin 'yan uwansu mata, toh dalilin haka kunyan abinda suka aikata yakan hanasu neman magani dukda sukan sha wahala sosai kafin su warke.... Har yasa kai zai wuce ya barta nan wajen tsaye sai kuma ya dawo da baya yana dubanta yanzu kam harda mararta take kamawa...
Bud'e murya yayi yace da ita "Sunana Dr Siraj Adam, idan kinason gani na ga lambar ofishina a cikin asibitin nan, kiyi azama ki yak'i cutar dake jikinki tun kafin ta kaiki ga halak'a gaba d'aya...." ya k'arashe yana ajiye mata wata 'yar takarda a gefenta...
Shareefah ta kuma fashewa da kuka tana fad'in "Shikenan ta faru ta k'are rub'ewa nayi... Wayyo Allah na... Wayyo wllhi na tuba... Kaico kaicona kaicon son zuciya irin tawa...." Lokaci guda ta kuma d'aura hannu aka tana kukan nadama...
*****
Girgiza kai kurum Affan yake yana duban Naseer kafin yaci gaba da fad'in "Naseer wllhi bazan fita nemanta ba, Daddy ma yace babu abinda zaiyi da ita, macen da take neman rayuwar mijinta akan wani biyan buk'ata nata na duniya... Haba haba Naseer ka auna idan taka mahaifiyar ce... Wayasan su waye suka saceta, na tabbata hakkin Daddy ne yasa ta fad'a mugun hannu.... Na kasa yarda wai mahaifiyata ce ke yunk'urin kashe mahaifina..." Ya k'arashe muryarsa na tsananin rawa...
Naseer ma jigum kawai yayi gefen Affan dai-dai lokacin da Salma da Ilham suka k'araso wajen, hawaye sharkab idanunsu...
Affan yana hango Ilham yaji hawaye na k'ok'arin ciko idanunsa, ya tuna abubuwan mugunta da yayi mata, Mamy duk ita ta janyo masa har ya zamto monster, k'ila da ace ta zamto mutumiyar kirki da bai zamto azzalumi ya azabtar da makauniyar da batada hakkinsa ba, baijin zai tab'a yafe ma kanksa....
Saurin mik'ewa Naseer yayi ya rungume Salma suka d'an fice a wajen, tuni ta cusa kanta cikin k'irjinsa tana kuka, abubuwan sun masu yawa A DUNIYAR SU, Allah sarki daga wannan sai wancan kullum cikin zullumi da fargaba suke....
Da sauri Affan ya mik'e ya kamo sandar Ilham yanai mata alama da kujera kana ta zauna....
Kasa ce masa komai tayi sabida tausayin sa da ya cika mata zuciya...
Murya na rawa ta soma fad'in "Ya Affan kayi hak'uri.... Ita rayuwa ta gaji haka, ba komai yake zuwa mana yanda muke so ba... Kayi hak'uri kaji, ka tuna Allah yayi mana ni'imomi da yawa wanda sam bazamu iya biyansa ba... Na baka misali da mahaifiyata, munaji muna gani muka rasata sabida k'odarta basa aiki, na'uran bature da za'ayi amfani dashi wajen taimakawa ya kwatanta aikin da k'oda keyi a jikin d'an Adam sai an biya mak'udan kud'ade... Ashe da Allah zai barmu da aikin k'oda ma kawai da babu kowa cikin duniyar nan, sai yayi mana k'oda guda biyu harda spare don mu kasance masu godiya a gareshi, babu kwabo a kullum k'odar nan take aiki ta cire abinci da abinsha daga cikin jini.... Shin da wannan ni'imar kawai ubangijin mu ya barmu bai kai mu gode masa ba.... Ya Affan ina fad'a maka wannan maganganu ne sabida kada wani k'addara na rayuwa ya same ka kayi tunanin butulcewa wa rahamar ubangijin ka, a duk yanda bawa ya tsinci kansa ya kasance cikin godiyar mahallicin sa, sabida da ace zai barmu da Al'armuran rayuwar mu a hannayen mu da tuni babu mai numfashi A DUNIYAR MU... Kayi hak'uri ya Affan ka karb'i k'addaranka ka tuna akwai wani babban rahama da Allah ya kuma maka bari maka mahaifinka da yayi a raye har ya bud'e wani k'ofa mai duhu haske ya bayyana A DUNIYAR MU... Allah ya bamu ikon cin jarabawar dake jarabtarmu dasu A DUNIYAR MU...."
Kasa furta komai yayi sai kallon mamaki da yake binta dashi, jikinsa ya kuma yin sanyi, tsoron mahaliccin sa ya kuma ratsa zuciyarsa, kallon wannan makauniya mai cikeda wadatan zuci yake babu ko k'yafta idanu... Shin A DUNIYAR MU dama akwai mutane irin haka masu tsananin tawakkali da godiya ma ni'imomin ubangijin su, Allah sarki gadata dai makauniya amma Sam bata d'auki nakasan dake jikinta tawaya wa rayuwarta ba... Tunda yake a rayuwarsa bai tab'a sauraren kalaman da suka haifar masa da nutsuwa cikin zuciyarsa irin ta yau ba... Ji yake tsan-tsan soyayyarta na ratsa zuciyarta...
A hankali ya mik'e ya tako gabanta, durk'usawa yayi saman gwiwoyinsa idanunsa naga fuskarta, sanyi na ratsa zuciyarsa kallon fuskarta da yakeyi....
Sandar ta ya kama ya rik'e hakan ya bata tabbacin yana durk'ushe gabanta ne... K'irjinta ya yanke ya fad'i tana tunanin toh meye ya durk'usar dashi gabanta.. Bata ida tunaninta ba ta jiyo muryarsa yana fad'in
"Ilham thank you... Thank you for being here....."
Murmushi take kumatunta suna lotsawa kana tace "Ka daina min godiya, you were there for me sanda nake asibit... Besides Daddy nima Daddy na ne kuma yanada zuciya mai kyau, yana buk'atan ka yanzu morethan ever, you need to be strong for your family..."
Murmushi yayi mai bayyana hak'wara tamkar tana ganinsa kana yace "Ilham bansan yanda zaki d'auki maganata ba amma magana mai girma nake son fad'a maki, ki bani dama na sanar dake pls....."
Gabanta ya kuma yankewa ya fad'i toh mai zai sanar da ita haka.... Shiru tayi ba tareda ta iya furta komai ba...
Ganin tayi shiru yasa Affan kuma fad'in "Kin bani dama na fad'i...."
Idanunta k'uri tamkar suna gani take duban wani wajen.... A hankali ta shiga jinjina masa kai ba tareda tace komai ba...
Murmushi Affan ya kuma yi kana ya kamo sandar ta sosai.... Saida ya sauk'e nannuyan ajiyan zuciya kana yace "Ilham wani ya tab'a sanar dake yana sonki....."
Maganar taso bawa Ilham dariya dukda taji muryar nasa babu alamun wasa cikinta... Murmusawa kurum tayi kana tace "Kai Ya Affan wace irin tsokana ce wannan, ni kuma soyayya, ai bankai nayi soyayya ba tunda Addah Salma ma aurenta zuwa kawai yayi babu shiri... Sannan koma na kai waye zaiyi soyayya da makauniya kamata...."
Daga jin yanda tayi maganar k'uriciya ce fal cikinta...
Affan ya murmusa yana enjoying magana da ita kana yace "Tam naji baki kai ba.... Amma yanzu idan wani yace yana sonki zaki amince...."
Murmusawa tayi kad'an mai d'an sauti kana tace "Ya Affan kenan let's change the subject, ai dai kaga ni yarinya ce..."
D'an b'ata fuska yayi tamkar tana dubansa kana yace "Ai na zaci kinzo nan ne ki tayani hira ko zan d'an mance d'umbin damuwar da nake ciki...."
Tana d'an wasa da sandarta take fad'in "Sosai ma I'm here for you...."
Affan ya d'an jinjina kai kana yace "Amma dai kinsan rashin gani bai kawo cikas ma soyayya muddin kana son mutum koh ba haka ba...."
Dariya ta d'an soma yi kana tace "Enough with soyayya pls Ya Affan... Yanzu ka tashi mu shiga mu kuma duba jikin Daddy, naji Ya Naseer na cewa zaku wuce station maganar case d'in Mamy..."
Bai ce mata komai ba sai mik'ewa da yayi ya kamo sandar nata ya zame mata tamkar d'an jagora sannan yace "Naseer dai zaije station case d'in Mamy amma banda Affan, ko Daddy ma cewa yayi babu ruwansa da ita baklantana ni..."
Ilham batace komai ba sabida tausayin sa da ya ratsa zuciyarta, bata tab'a ganin fuskar sa ba amma tanaji tafi muradin da ace zata kuma gani A DUNIYAR SU toh fuskar Affan take k'aunar fara kallo....
Hangosu dasu Naseer sukayi ya sanyasu k'arasowa wajen su...
Naseer ya d'an dubi Affan kana yace "Shareefah fah....?"
Tambayar Shareefah da yayi saida yasa jikin Salma yin d'an sanyi, shi kansa ya kula da hakan....
Affan ya d'an ware hannayen sa had'i da tab'e baki kana yace "K'ila ta koma gida...." Don shi gaba d'aya har Shareefar haushinsu yake ji sabida yasan duk yanda akayi wani abin suka k'ulla tunda yaji dalilin fasa aurar da Shareefah yasa Mamy ke yunk'urin kashe Daddy.....
******
Ko komawa wajen Daddy bata kumayi ba sabida tsananin kunyarsa da taikaicin rayuwar data tsunduma kanta ciki da take, dukda Daddy bai fito fili ya sanar da ita dalilin fasa aurarta ma Naseer da yayi ba, jikinta ya bata, domin kuwa Daddy ya mata hannunka mai sanda sannan ya mata nasiha kan ta tuba ta gyara halinta tun da sauran numfashinta a duniya... Shareefah tana isa gida kulle kanta a d'aki tayi tana kukan nadama da takaici na rayuwa..
*******
Tun yana bisa babur jikinsa ke basa kaman ana binsa, har ya k'araso lungun su, sai ya juya yaga babu kowa..... Abin ya soma damun Deeni don koda ya shigo tsakar gidansu yaji tamkar mutum ba biye dashi... Dabara ta fad'o masa... Wani d'an tsibiri dake gefen tsakar gidan nasu ya haye bayansa ya b'oye yana lek'en ko zaiga mai binsa...
Aiko nan yaga Maina ya fito daga bayan k'yaure yana waige-waigen ta yanda zai hango Deeni ga bindiga a hannun sa... Deeni ya kusan sakin fitsari a wando hango bindiga da yayi, Maina kuwa waige-waigen yanda zaiga Deeni yaci gaba kafin ya ciro wayarsa yayi dialing layin Innah...
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*53*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Gaban Deeni bai daina dukan tara-tara ba sanda Maina ya cire bakin handkerchief d'in da ya toshe rabin fuskar sa dashi, fuskar ta bayyana gaba d'aya, sarai ya sansa ya gane sa sabida yana ganinsa jifa-jifa gidansu Lubna... Amma mai ya masa da tsanani yake neman rayuwar sa... Wayar da yaji Maina nayi ya sanyasa kasa kunnuwa had'i da tak'urewa
"Eh Innah na biyosa har gidan nasu amma ya b'ace min ban gansa ba...."
Daga d'aya b'angaren tsaki Innah tayi tana murza karan sigari tsakanin yatsunta kana tace "Kar ka zama dolo solob'iyo kaman Kabeer da yace min ya gama da Naseer ashe k'arya ne.... Ka kashe min shi har lahira ta haka ne kurum zai rabu da d'iyata Lubna..."
Maina ya murmusa sabida duk duniya babu macen da yake k'auna irin Lubna a nashi dolancin...
"Innah karkiji komai idan dai wannan yaro ne ya mutu an gama bani barin gidan sai na karsa bai dace da Lubna ba, sai kinga kurkukun da yake rayuwa kisan cewa sam bai dace....."
Katse sa tayi da fad'in "Ba dogon zance na tambayeka ba, kawai ka cikata min aikin da na saka ka, kar ka dawo min baka kashe sa ba..." Daga haka feso hayak'i tayi tsakankanin wushiryarta kana ta latsa wayar d'if ta kashe tana tunanin saura Naseer....
Deeni da k'irjinsa bai daina bugu ba, saurin toshe bakinsa yayi, yana mamakin rashin imanin Innah har yakai tasa a kashe mutum, dama shi tuntuni ko ganin Maina yayi a gidan Sa'oud Santana basa gaisawa sabida tasu batazo d'aya ba daga shi har uban gidan nasa.... Ganin Maina ya soma bud'e-bud'en k'ofofi ya sanya Deeni dira bayan garu a hankali sabida bindiga ce hannun Maina bazai iya fad'a dashi ba, koma ba bindiga bane cikin Deeni sarkin tsoro ya riga ya d'uri ruwa yaga mutuwa kusa.....
Jin k'aran kaman mutum ya Dirk's bayan katanga ya sanya Maina saurin nufa wajen a tamanin, nan ya hangi Deeni na gudun famfalak'i.... Duk irin gudun da Maina keyi don ya cimma Deeni bai commas ba..... Tuni Deeni ya shige ribibi cikin wani tashan motoci da baida nisa da gidansu...
Maina sai shafe fuska yake yana tsuka.... Ba don yaso ba haka ya juya ya koma gidansu Deeni yana kuma k'arema gidan kallo, bazai bar kewayowa ba har sai ya farauci rayuwar Deeni ko ba don komai ba ko don ya mallaki Lubnar sa abar k'aunarsa da yake kwana da ita yake tashi da ita, kuma bai isa komawa ya sanar da Innah bai kar Deeni ba....
Dawowa gidansu Deenin yayi yana kuma duba d'akunan.... Can ya hangi tamkar mutum ne a kwance amma da alama barci yake... K'arasawa yayi sosai yana duban mutumin.... K'irjinsa yayi wani irin yankewa ya buga tamkar an sauk'e masa guduma... Abubuwan da suka faru shekarun baya suka shiga dawo masa, cikin zuciyarsa ya furta "Malam Ladan dreban Alh Sa'oud, ya tuna sanda ya jefosa k'ark'ashin gada aikin da Innah ta soma sakashi a rayuwarsa tun yanda k'uruciya sosai a jikinsa, kai amma,... Kai ba zai yuwu ace wannan Malam Ladan bane sabida tun a wancan lokacin ya mace, a jefo ka k'ark'ashin gada ba wasa ba....
Cikin sauri ya fice a gidan zuciyarsa bata daina bugu ba sabida abinda ya gani...
****
Deeni kam a bakin tasha ya kwana sabida tsabagen tsoro, tunanin mahaifinsa dake gidan ne ya addabesa, alla-alla yake gari ya waye yaje ya duba mahaifinsa don bai isa komawa a daren nan ba tsaf Maina zaisa karsa, gwara da ya gudu ya janyo hankalinsa bazaiyi tunanin na cikin gidan ba balle ya d'agawa mahaifinsa hankali tunda gashi har biyosa a guje yayi....
Sassafe ya nufi gida sai waige-waige yake tamkar b'arawon asuba.... Kai tsaye mahaifinsa ya soma dubawa da alama duk draman da ya faru jiya a gidan mahaifin nasa bai sani ba....
"Zahraddeeni lafiya kake waige-waige haka..." Abbah ya tambaya yana mai kallon Deenin....
K'ak'aro murmushi Deeni yayi kana yace "Babu komai Abbah barin dama maka kunun ka sai kasha magani...."
Bai jira cewan Abban ba ya mik'e still sai faman waige-waige yake kana ganinsa zaka fahimci a birkice yake.... Duk wasu duties na safiya da yake yi wa mahaifin sa saida yayi su kafin ya dawo ya zauna gefen Abba...
Kallonsa Abbah yake yana murmushi lokaci guda ya kamo hannayen sa kana yace "Allah yayi maka albarka Zahraddeni, kar ka damu kai jan gwarzo ne kuma jarumi mai neman lahiran sa ta hanyar kyautata wa mahaifa... Insha Allahu zaka sami nasara a rayuwa koda bana nan...."
Jikin Deeni ya d'anyi sanyi domin kuwa duk a 'yan kwanakin Abbansa tamkar hud'uba da nasiha ta ban kwana yake masa d'an k'ak'aro murmushi Deen yayi kafin ya sumbaci hannun mahaifin nasa yace "Abbah ina sonka fiyeda komai A DUNIYAR MU... Zanyi komai don farin cikin ka kuma da izinin Allah zaka sami lafiya zaka kuma takawa A DUNIYAR MU...."
Murmushi Abbah yayi kafin yace "Maza ka tafi aiki kada ka makara kaji koh..."
Gaban Deeni ya bada daram, tunanin ta yanda zai soma zuwa gidan Sa'oud Santana yake a wannan safiya, tunda ya fuskanci farautar rayuwar sa suke akan d'iyarsu... Dai-daita kansa yayi k'ok'arin yi kana ya jinjina kai yace "Abbah yau bani son tafiya na barka so nake na zauna da kai...."
Abbah ya murmusa kana yace "A'a Zahradden kar muyi haka da kai, shi aiki amana ce, idan aka d'auke ka akayi da kai ga ranaku da zakake zuwa toh fah idan ka tsallake rana guda bakajeba ba tareda wata k'wakk'waran dalili ba toh wannan kud'in ranar aiki guda da kaci kaci haramun ne... Ka tashi kaje kaji Allah yayi maka albarka...."
Murmushi Deeni ya sakar masa kana yace "Na gode Abbah, sai na dawo...."
Abbah ya jinjina masa kai yana mai murmusawa....
Deeni kam har ya fice ya kuma dawowa ya nufi d'akinsa, envelope d'in da Abbah ya basa cikin kwanakin nan ya d'auka ya shiga juyawa, bai bud'e ba sai mak'ale ta a hannunsa da yayi, tunda farautar rayuwar sa ake gwara ya bawa Lubna ajiya yasan ko shi yayi nasaran kar Maina ko Maina yayi nasaran kashe sa sak'on Abbah yana hannu mai kyau kuma yasan Lubna zata kula masa da mahaifin sa amma kafin ya bar duniya sai ya sanar da ita farautar rayuwar sa da mahaifiyarta keyi.....
Saida ya lek'a lungu da sak'o kafin ya fito daga cikin gidan, lokaci guda wayarsa ta hau ruri ganin Lubna ce mai kiran nasa ya kuma sa gabansa fad'uwa... Cikin sauri ya d'aga wayar
Daga d'aya b'angaren cikeda shagwab'a Lubna ta soma fad'in "Haba my superglue test d'in fah 7:30 ne gashi har bakwai saura baka iso ba...."
Deeni ya d'an shafi goshinsa kana yace "Kina ina....?"
"Gida mana waiting for you..." ta basa amsa kai tsaye....
Saida ya kuma lellek'a lungun gidan nasu kafin yace "Lubna my life's in danger bazan iya zuwa gidanku ba, amma idan zaki iya fitowa ko a titin unguwar gwallaga ne sai mu had'u...."
D'an Jim Lubna tayi kafin tace "Kaga ni kada ka tsoratani ba'a wasa haka...."
Deeni ya shafi naman goshinsa had'i da fuzar da iska kana yace "Wai na tab'a maki wasa haka ne, wllhi da gaske nake rayuwata tana cikin had'ari dan Allah kedai ki fito kawai....."
Tasan Deeni da son wasa amma yaukam he sounds serious... sauk'en ajiyan zuciya tayi kafin tace "Gani nan zuwa....."
Bata jira cewar sa ba ta katse kiran ta shige motarta ta bar gidan.....
Yana fitowa ya hangi su Ubi saman dakali suna suracen safiya da kayan maye.... Nan suka soma tangad'i suka nufesa suna fad'in "Sai babban Yaya, a taimaka mana da na karin kumallo...."
Deeni ya d'anyi tsaki kana yace "Ko na baku ba abinci zakuci ba k'waya zaku kuma tarawa da hayak'i a cikin ku da sanyin safiyar nan...."
Aljan ya kame bakinsa da duka hannaye biyu yana wani k'asa-k'asa da kai uwa k'adangare yake fad'in "Yasin nikam abinci zanci babban Yaya... Wllhi sai ka auri baturiyar nan... Allah ya tsare mana kai...."
Murmushi kawai Deeni yayi kafin yasa hannu aljihun gaban rigarsa ya zaro d'ari uku gudan d'ari biyu da kuma naira d'ari ya mik'a masu kana yace "Idan dai da gaske abincin zakuci zai isheku sayan masa...."
Ubi na washe baki yake fad'in "harda taushe ma yasin ko ba dage-dage...."
Cikin sauri Deeni yasa kai ya wuce suka bi bayansa suna fad'in
"Godiya muke babban Yaya mijin baturiya, yasin ranar aurenku har Landan sai munje ko ya kuka ce gais(guys).." Duk suka amsa da "hakane K'waro"
*****
Haka ta dinga watsa gudu saman kwalta.... Dai-dai wasu kanti ta hangesa hannunsa rik'e da takarda sai muzurai yake...
Tana ida parking ya k'arasa ya shige... Kallon mamaki take binsa dashi
"Wai lafiyarka kuwa....?" ta tambaya tana dubansa...
Still bai daina lek'e-lek'en hanya ba yake fad'in "Kin tabbata babu wanda ke biyoki...."
Girgiza kai tayi kana tace "Wai miyene ke faruwa....?"
"Lubna rayuwata ake farauta...." Ya fad'i yana muzurai
*****
Wani jahilin mari Innah ta d'auke Maina dashi Aunty Saudat dake zaune gefensu tamkar mahaukaciyar gaske sai tsige babyn robar hannunta take tana abubuwa irin na marassa hankali...
"Kai wani irin dole ne dak'ik'i, kaida Kabeer bansan waye yafi wani dolanci ba.... Tunda kace mutumin yayi maka kama da Malam Ladan mai yasa baka kashe shi ba... Ka d'ibo k'afa kazo kana gaya min, idan kuwa Malam Ladan ne kuma da hankalin sa bai mutu ba yana numfashi toh ka sani Maina kashina ya bushe sirrina gaba d'aya na kan Malam Ladan..... Na tabbata da dalilin da yasa Tani da Deeni suke aiki gidan nan...."
A hankali Aunty Saudat ta soma rarrafe tana wasu abubuwa irinta marassa hankali har ta fice daga parlorn basu hankalta da ita ba.....
Can ta baya ta hangi Mama Tani.... Tana k'arasawa ta janyo hannun Mama Tani suka keb'e...
Mama Tani jikinta ya shiga karkarwa jin Aunty Saudat tana mata magana babu alamun tab'in hankali ciki...
"Mama Tani, ki bar gidan nan kafin su kashe ki, ki san yanda zakiyi ki tseratar da Deeni da mahaifinsa...."
"Hajiya lafiya ban gane me kike nufi ba...." Mama Tani ta fad'i baki na karkarwa...
"Ki bar gidan nan nace maki, kiyi yanda nace kawai kar su kashe ki...." Daga haka bata jira cewar Mama Tani ba ta wuce cikin sauri tana mai ci gaba da abubuwan haukan ta.....
Innah na huci ta finciko hannun Maina tana fad'in "Muje banson dolanci...."
Cikin sauri suka fice daga gidan....
****
Lokaci guda kuma Deeni ya d'an Saki murmushi ganin yanda hankalin Lubna ya tashi kana yace "Kar ki d'aga hankalin ki shikenan babu komai, dawo mazaunin ki...."
Kallonsa Lubna take da mamaki kana tace "Ban gane babu komai ba... Kace min ana farautar rayuwarka sannan ka dawo kace babu komai.. Deen wai dan Allah meke faruwa ne...?"
Deeni ya bud'e marfin mota ya fito kana yace "Ki dawo mazaunin ki nace koh, ko bakiji ni bane..."
A kufule Lubna ta finciki marfin marfin motar ta fice sukayi canjin wajen zama Deeni ya soma driving kai tsaye hanyar ATBU taga ya d'auka....
Shaye da mamaki take dubansa kana tace "Amma dai kasan bazan je makaranta ba batareda ka sanar dani abinda ke faruwa ba...."
Deeni bai amsata ba sai kwalan motar yake, gwara ya kaita makaranta ya koma ya d'auki mahaifinsa ko barin garin ne gwara suyi don gaba d'aya hankalinsa bai kwanta ba..
Hango motar Innah da yayi can gabansu yasa sa rage speed, zuciyarsa na bugawa ya soma fad'in "Kashe ni suke son yi sabida ke, sabida basu son alak'armu dake.... Lubna mahaifiyarki farautar rayuwana take...."
Shaye da mamaki Lubna ke dubansa kafin tace "Kayi hauka ne.... Meye kake fad'i?"
Deeni da tashin hankali ya nuna k'arara a fuskar sa girgiza kai yake yana fad'in "Lubna wllhi gaskiya nake fad'a maki, ki yarda dani wllhi Innar ki neman rayuwata take, Lubna inaga gwara mu yanke alak'ar dake tsakanin mu nida ke bazamu iya kasancewa tare ba...."
Lubna da tuni hawaye sun soma zuba mata da k'arfin gaske tace "Shut up! Idan kana son rabuwa dani sai ka biyo ta wannan hanyar, meyasa ku maza kuke da mugunta da son zuciya, sai mutum ya kamu da soyayyar ku sai ku rabu dashi..... Naka salon kenan Deeni... Mahaifiyata zaka d'aurawa sharri don kana son rabuwa dani.... Nasan Innah bata k'aunar alak'armu amma wllhi bazata iya kashe rai ba, nasan da zaran munyi aure zata k'aunace ka kaman yanda ta soma k'aunar matan Ya Naseer...." Kuka sosai ya kufce mata
Deeni da gaba d'aya hankalinsa ya tashi ganin tana hawaye.... Girgiza mata kai ya soma kana yace "Lubna ki saurare ni pls... Wllhi gaskiya nake fad'a maki...."
"Ya isa please...!" Ta katse sa, cikin kuka taci gaba da fad'in "I was wrong, I was wrong about you too... Kaima baka k'aunata, this is so unfair.... Zan fita daga rayuwarka kuma kada ka sake neman yanda nake....." Daga haka sa hannu tayi zata finciki marfin motar, Deeni yayi saurin sakata a lock, idanunsa sunyi jazir sanda ya soma fad'in "I love you.... I lkve you ultimately, soyayyar da bazan tab'a iya maki k'arya ba... ban tab'a soyayya da wata mace ba A DUNIYAR MU sai ke... Lubna Sa'oud Santana ina sonki with every beat of my heart.."
Cikin kuka ta katse sa da fad'in "Enough please.... don't make me hate you, ka daina fad'a min kalaman da sukeda zafi a gareni... If you really do love me kaman yanda kace bazakayi tunanin barina ba kaman Affan ya min, kaida shi duka d'aya ne.... I was wrong da nayi tunanin farin ciki na na tareda kai...."
Huci kurum Deeni yake yana dubanta ga idanunsa da suka kad'a sukayi jazir baisan sanda ya danna giyan motar lokaci guda ya finciki motar yana sharara gudu saman kwalta, can ya hangi motar Innah ta yanki wata kwanan.... Bai kula Lubna ba sai fincikar motar da ya ci gaba da falfala gudu....
"Ina zaka kaini...?" ta tambaya tana dubansa...
Ko tankata baiyi ba sai tuk'i da yakeyi idanunsa naga motar Innah dukda nisa da suka masu...
Kifa kanta tayi saman cinyarta tana ci gaba da kuka maras sauti tana tambayar zuciyarta meyasa soyayya ke wahalar da ita A DUNIYAR SU.....
*****
Tana zaune ita kad'ai a parlor tana tak'ure waje guda sabida har yanzu bata jin dad'in jikinta, kaman daga sama sai ganin mutum tayi akanta ya shigo cikin parlorn, abinka da irin gidajen barracks babu katanga saiko k'ofar parlor direct...
Cikin sauri Jamila ke k'ok'arin mik'ewa tana jada baya, baki har na rawa take fad'in "Kar ka kashe mu..... Me ya kawo ka....?"
Ganin na k'ok'arin matsowa ya sanyata kuma jada baya murya na rawa take fad'in "Wllhi zan maka ihu yanzun nan...."
Tana yunk'urin yin ihu taji ya capkota ya danne bakinta, wata irin kafiran murmushi yake kafin ya soma fad'in "Kitty wllhi bazan tab'a rabuwa dake ba, na fad'a maki... Balle ma ba yanda za'ayi ki rabu dani dole k'arshe ki dawo gareni sabida abinda nazo gaya maki yanzu....
Jamila na hawaye take k'ok'arin k'watan kanta amma ta kasa...
Alh Kabeer yana wata irin kafiran murmushi yake fad'in "I'm HIV positive, I infected you.... Babu namijin da zai yarda dake yanzu dole kici gaba da rayuwa dani...." Daga haka yasar da ita yayi a wajen ya fice cikin sauri...
Jamila ta soma gani duru-duru, innalillahi kurum take nanatawa cikin zuciyarta, maganar sa na mata yawo a kwanyarta.... He's HIV positive.... Ya saka mata k'anjamau.... Girgiza kai take tana tattab'a jikinta take girgiza kai lokaci guda ta Saki wani k'ara wanda saida yasa jama'an gidan fitowa babu shiri...
******
Naseer tsaye a police station yana kwararo bayanin b'acewar su Mamy da Azeema wa DPO Ayuba abokin Engr Bala da ya taimaka masu sai ganin kira da wata bak'uwar layi yayi tana shigo masa....
Kaman bazai d'aga ba don tsaka yake da bayani ya kuma ganin kiran excusing kansa yayi kana ya d'an fice yana mai k'ara wayar a kunnensa
K'irjinsa ne ya buga jin muryar mai maganar, a hankali ya furta Aunty..!"
Aunty Saudat dake faman waige-waige sassauta murya ta kuma yi kafin tace "Naseer kana ina kazo yanzu don Allah... Kazo kafin su kashe mu gaba d'aya..."
"Aunty kin sami lafiya ne? Su waye zasu kashe ku, Yaya ya sani....?"
Saurin katse sa tayi da fad'in "Naseer na warke tuntuni kazo kawai dan Allah, sannan kar ka sanar da Kabeer kazo gida..."
Cikin sauri yace "Okay gani nan, gani nan zuwa yanzun nan...." Daga haka kotakan DPO bai kuma bi ba ya fice a birkice...
*****
Alh Kabeer na fitowa yaga kiran Innah... Yana d'agawa yasan hankalinta a tashe yake nan ta soma fad'i masa
"Kabeer kazo ka sameni a duk yanda kake, Malam Ladan dai da ka sani direban Sa'oud yana raye bai mace ba...."
Tsaki Alh Kabeer yayi kana yace "Innah bakisan mai kike fad'i ba, mutumin nan ya mace tuntuni...."
Innah ta katse sa da fad'in "Bana son taurin kai da dolanci.... Maina zai sanar dakai yanda muke yanzun nan, ka k'araso duk yanda kake..."
Daga haka mik'awa Maina wayar tayi tana ci gaba da huci...
Maina yana amsar wayar yayi masa kwatancen guest house d'in Innah don wajen zasu kai Malam Ladan su azabtar dashi suji da gaske shine bai mace bane ko kuwa kamanni ne.....
Daga can nesa gefen wani garu da ya d'an tare Deeni yayi parking har lokacin Lubna bata d'ago kanta ba, kanta na kife saman cinyoyinta tana kuka
Deeni na hangosu daga yanda sukayi parking k'ofar gidan, Innah ce ta bud'e marfin mota ta fito dai-dai lokacin da Lubna ta d'ago idanunta tana duban yanda Deeni ya kawota... Hango Innah da tayi ya sanyata daskarewa suka zuba masu ta mujiya daga ita har Deenin
Wata mota ce ta k'araso wajen lokaci guda wasu 'yan mata guda biyu masu suffan kafirai suka fito daga motar, kai tsaye suka nufi Innah ba tareda b'ata lokaci ba suka sunbatar ta sunai mata wasu irin abubuwa mai tsananin girgiza zuciyar mai imani....
Daga Lubna har Deeni daskarewa sukayi suna ganin abun tamkar ba'a duniyar su ba...
Innah ta darara masu tsawa 'yan matan suka natsu kafin taci gaba da fad'in "Wayace kuzo yau, ke Nandy bace maki nayi mu had'u jiya ba shine baki tashi zuwa ba sai yau, ke kuma Alisha banida buk'atarki yanzu sabida kinbar jikinki gaba d'aya ya sakwarkwace...... Bana sha'awarki sam..."
Ashly ta shiga mokad'ewa tana tank'washewa tana juyi gaban Innah take fad'in "Haba Hajiyar mu mai 'ya'yan banki, Ashly ake yayi yanzu ki duba da kyau ki gani...." Ta k'arashe tana kuma daduman Innah...
Dole Innah ta kora su Ashly sabida biyan buk'atar ta na yau yafi k'arfin su Ashly batasu take ba..."
"Innah bamu da time, kinsan idan muka gama da Ubansa dole mu sauk'o Kansa don ni na tabbata da biyu ya turasa aiki gidan, sannan itama Tani dole ta bak'unci lahira sabida ruhuwar asirin mu...." cewar Maina dake faman gyara bindiga cikin jacket d'insa
Innah ta jinjina kai kana tace "Maza, tafi ka kawo min shi a raye na azabtar dashi azaban da ya kamata ya sha tuntuni kafin mu aikasa lahira....
Gaba d'aya Deeni duru-duru yake gani, yama rasa meke faruwa... Kansa ta juye lokaci guda... Sam baima kula da Lubna wacce tuni ta sume cikin motar ba.... Iyaka abinda yake tunawa shine Maina ya tafi d'auko mahaifinsa.... A d'ari biyu ya finciki motar yana gudun da baisan ya iya irinta ba...
Saida ya hau saman kwalta zaija giya yaji hannunsa saman na Lubna wacce jikinta tuni ya sake gaba d'aya tamkar macecciya...
Wani sabon tashin hankali ya ziyarci Deeni....
"Lubna...! Lubna..!! Lubna...!! " Ya shiga ambato sunanta yana jijjigata inaa batamasan anayi ba...
Tashin hankalin da bai tab'a tsintar kansa ciki ba ya shiga, yama rasa wanne zaiyi gaba d'aya, ga dukkan alamu Lubna bata numfashi
*****
Mamy da Azeema gaba d'aya fuskarsu yayi bak'i sun canza kamanni ga malu tal kai, tamkar basu ba... Idan ka gansu bazaka shaida su ba, ga uwar ramar da sukayi a d'an kwanaki biyu jal, Mamy kam bataci komai da ake kawo masu ba amma Azeema kam ta kasa jure ma azaban yunwa saida taci...
Bayan Laure ta fice mai gadin ya lallab'o ya taddasu don tunda yaji labarinsu tausayinsu ya cikasa...
A hankali yake furta "Zan taimaka maku, sabida ku kad'aine d'akinku daban a gidan nan ba'a had'aku da yaran da ake kawowa ba, yau ta fice farautar yara bata gida, ina fata bakuci abincin gidan nan da ake kawo maku ba..."
Mamy kam ta kasa manana sai karkarwa da jikinta keyi....
Azeema na hawaye take rik'e da Mamy da jikinta bai daina karkarwa ba kana tace "Baba ka taimaka mana dan Allah, ka fitar damu daga gidan nan dan Allah..."
Baba mai gadi da tausayi ya kuma rufesa gyad'a ma Azeema kai yayi kana yace "Taimakon kun zanyi d'iyata shiyasa nake tambayar ku da fatan bakuci abincin ba..."
Azeema ta rasa me zata ce masa cikin sauri ta shiga jinjina masa kai tana mai ci gaba da hawaye...
Baba yace ku biyoni a hankali....
Cikin sauri Azeema ta rungume Mamy dake d'ingisawa suka soma biyo bayan Baba cikin sand'a...
Ta wani k'aton rariya Baba ya bud'e masu kana yace "Idan kunci abincin gidan nan bazaku iya tsira ba sabida tsafi dake ciki, shiyasa ma na tambayeku tun a fari....."
Jikin Azeema yayi sanyi sosai wasu sabbin hawaye na kuma gangaro mata, cikin sauri ta shiga gyad'a kanta sanda taji wani k'arfin zuciya na zuwa mata kana tace "Kar ka damu Baba zamu iya gudu insha Allah, kawai ka taimake mu mu fita..."
Baba ya jinjina kai kana yace "Ko kunji kira kada ku jiyo, ko me kuka gani gabanku kada ku razana kuci gaba da tafiya kawai babu jiyowa.... kuje Allah kareku..."
Daga haka Baba ya shiga turasu ta k'aton rariyan dake cikin babban ramin abun wucewar ruwan gidan....
Azeema sai godiya take masa Mamy kam ko uffan ta kasa fad'i cangwalawa ma da k'yar takeyi Azeema na taimaka mata....
Ga mamakin su suna ficewa suka nemi gidan suka rasa...
*Toh fah..! mai karatu nesa ta matso kusa kuci gaba da bin Sameena domin jin yanda labarin nan mai cikeda da sark'ak'iya da kwamacala zata kasance A DUNIYAR MU*
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*54*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Firgit Azeema ta farka daga mafarkin da take wai har sun fice a gidan... Ashe dai mafarki ne take d'an barcin da yayi awon gaba da ita, ta kai dubanta ga kwanon abincin da aka shigo masu dashi tana tuna abinda Baba Maigadi yace mata cikin barcinta, tsabagen yunwa ko d'aga hannu Azeema bata iya yi, idan ka gansu itada Mamy tamkar wasu ribatattun yak'i.... Ta d'an lek'a window taga Steve na nan k'ame a bakin k'ofa baiko gifta ba.... Wasu sabbin hawaye suka gangaro wa Azeema... Ta kuma kai dubanta ga Mamy wacce keta faman tasbihi da 'yan yatsun hannunta tana neman dacewa wajen ubangijinta, Allah sarki wuya maisaka arne salati inji hausawa, amma ga dukkan alamu nada da tuban gaske ne ya kama wad'annan bayi...
Rarrafawa Azeema tayi ta k'arasa ga Mamy sukayi ma juna k'uri, tuni hawaye ya shiga gangaro masu rabonsu da abinci yau kwana biyu. Kullum aka shigo da abinci saidai a fitar dashi a haka.... Mamy da k'yar ta iya bud'e murya tace
"Azeema ko bayan raina ina fata asirin da Laure ta kaini akayiwa Daddy ya karye, inama zan kuma fita daga wannan kabari da naje har garin Jama'are na tone sammon da mukayi masa... Azeema tsoron duniyar nan nake, wllhi duk taurin raina da bushewar da tayi a baya ban zaci Laure zata iya yanka d'an Adam ba...." Mamy ta kasa ci gaba da magana sai hawaye.... Azeema ta d'an d'ago hannu da k'yar ta rik'e hannun Mamy ba tareda ta iya cewa komai ba sabida tsananin yunwa dake addabar ta....
Mamy taci gaba da fad'in "Bansan Laure matsafiya bace har haka, Nida nike d'iyar Malamai mai zai had'ani da gidan boka idan ba sharrin shaid'an da sharrin Laure ba... Azeema ina son mijina ina k'aunar sa... Inama zan kuma ganin sa na rok'e shi gafara koda bazai gafarta min ba, ina ma zan kuma ganin 'ya'ya na na rok'esu gafara koda bazasu gafarta min ba..."
Murya na rawa Azeema take fad'in "Mamy insha Allah zasu yafe maki ko bayan babu rayuwar mu, sannan Mamy idan Laure ta kashe mu ta kwashe mana duk wasu zunubanmu dake tsakanin mu da mahallicin mu, Alhamdulillah tunda kin tuba kin daina shirka dama shine babban laifi wanda idan mutum yaje wa mahaliccin sa dashi bazai tab'a gafarta masa ba, amma duk sauran laifi Allahu Gafurun ne kuma Arraheem ne.... Ki daina kuka kinji Mamy....."
Mamy kam batasan sanda ta rungumo Azeema ba su duka biyu hawaye na kwararo masu... Suna nan a haka suka jiyo muryar Laure tana rangad'a wa Steve kira...
Lokaci guda ta k'araso d'akin dasu Mamy suke, ganinsu da tayi rungume da juna ya sanyata shek'ewa da wani irin dariya had'i da tafa masu kana tace "Munafukan banza munafukan wofi... Gobe iwar haka kayukan ku sun isa Enugu.... Gwara ma kuci abinci akaiku da kumari...." ta k'arashe tana bud'e abincin dafeffiyar farar shinkafa da jar miyan kaza... Tab'e baki tayi ba tareda tace komai ba, jiyo dunkurmiyar muryar Steve tayi yana fad'in "Ma no mind 'em if hunger wear them welwel I assure you they will eat...."
Laure ta murmusa kana tace "K'yale 'yan iska kana ganinsun nan kaman mutane arziki, ko wacce cikinsu shu'umar kanta ce...."
Azeema ce ta katse ta da fad'in "Anty Laure don Allah ki bar Mamy ta tafi ko don warware sammon da akayiwa Daddy, don Allah idan yaso ni ki kaini Enugun...."
Laure ta zubawa Azeema ta mujiya tamkar zata bata amsa mai dad'i lokaci guda kuma ta shek'e da dariya kana ta kawaikwayi muryar Azeema tana maimaita abinda tace.... "Wannan sammo ai saidai ya mutu dashi, don dama idan ya warke kan Ma'u zai koma kaman yanda boka yace, toh kinga kuwa tunda babu Ma'u ai bazan bari ya warke ba sabida kaina zai komo, dan haka haka nan zai dawwama da ciwonsa..... Idan kunada rabon ganawa da juna saidai a wata rayuwar amma kam ba A DUNIYAR MU ba...." Tana gama fad'in haka ta dubi Steve sanda take ficewa kana tace "Steven cema su Danny su fito da mota....."
Cikin sauri ya take mata baya....
Suna ficewa wani sabon kuka ya tunk'aro Mamy.... Ga azaban yunwa da ya addabeta... Lokaci guda tasa hannu ta jawo kwanon abinci don har numfashinta tamkar d'aukewa yake sabida tsananin yunwa....
*******
Duk jijjiga Lubna da yake bata ko alamun bud'e idanu ba.... Hawaye tuni sun wanke masa fuska.... Cikin wani irin murya yake fad'in "Lubna wllhi k'arya nakeyi ko kasheni zasuyi bazan tab'a rabuwa dake ba saidai su kasheni... Dan Allah ki tashi kar ki tafi ki barni... Kin manta munce zamu rayu tare A DUNIYAR MU sannan a lahirarmu muyi fatan kasancewa tare.... Lubna don't leave me please.... Dan Allah ki tashi....." Lokaci guda kukan sa ya k'aru, sam ya mance da Maina da tuni ya tafi kai mahaifinsa wa Innah.... Saurin d'ago kai yayi ya d'au jakanta ya shiga zazzagewa nan yaga wayar salulan ta, hannu har na rawa ya shafi wayar Allah yasa batasa a lock ba, lokaci guda ya shiga dialing layin Naseer....
Naseer dake faman falfala gudu saman kwalta nan yaga kiran Lubna na shigo masa, k'irjinsa bai daina bugawa ba sabida furucin Aunty Saudat na cewa _Zasu kashe su...._ baisan su waye zasu kashe sun ba.... Lokaci guda ya d'aga wayan Lubna
Hankalinsa bai ida tashi ba saida ya jiyo akasin muryar Lubnar cikin salulan.... Cikin tsananin kuka Deeni yake fad'in "Soja ka taimake mu, ka taimake ni.... Kace mun Lubna bata mutu ba zata tashi....."
Kana jin maganganun Deeni kasan ba cikin hayyacinsa yake yinsu ba.....
Naseer baisan sanda ya cakka birki tsakiyan kwalta ba... Zuciyarsa na bugu da sauri da sauri... Mai ya sami k'anwarsa... Kafin ya sami zarafin magana wayar ta d'auke.... Cikin tsananin tashin hankali ya matse wayar a kunnensa yana fad'in "Hello! Hello..... Waye ne kai waye... Mai ya had'aka da wayar k'anwata...." Gaba d'aya ko gane muryar Deeni baiyi ba....Innalillahi kawai Naseer ke karantowa... Baisan sanda ya kwali motar ba ya nufi gida, yasan babban tashin hankali ne ke faruwa a gidan nasu.....
Deeni kuwa ganin wayar Lubna ta mutu ya sanyasa kwalan motar ya d'auki hanyar da zai sadasa da asibiti mafi kusa......
******
A birkice Mama Tani ta iso gidan, tana tambayar mahaifin Deeni ina Deeni...?
Yanda ya ganta hankali tashe ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba.... Murya na rawa yace "Tani lafiya...?"
Tana k'ok'arin kamosa daga saman katifa take fad'in "Nima ban sani ba barin garin zamuyi, ce min akayi rayuwarmu na cikin garari... Ban sani ba bansan me mukayi ba Yaya...."
Mik'ewa tsaye da Mama Tani zatayi sukayi idanu hud'u da Maina.... Baki na rawa tace "La lafiya bawan Allah..." Tsaf ta ganesa don tana ganin sa gidan Sa'oud Santana...."
Maina yayi wata kafiran murmushi sanda suka had'a idanu da Malam Ladan.....
"Ashe baka mutu ba...." Maina yace yana hura bakin bindiga....
Murmushi Malam Ladan yayi kana yace "Ban mutu ba kuma ko yau na mutu Alhamdulillah burina ya cika na tabbata sak'ona zai isa ga iyalan Sa'oud na gaskiya....."
Mamakin kalaman dake fitowa daga bakin Malam Ladan ya cika Mama Tani, ta kuma tuno abinda Aunty Saudat ta sanar da ita.... Kallon Malam Ladan tayi cikeda mamaki kana tace "Yaya ina kasan marigayi Sa'oud..?"
Murmushi Malam Ladan yayi kana yace "Nasan sa shekarun da suka shud'e tun kina Jihar Yobe baki dawo garin nan ba.... Kuma aiki da aka sama maki a gidan Sa'oud, Hannatu ce tayi sanadi don mu cikita burinmu mu cikita k'udirinmu akan wasu azzaluman bayi wanda suka jima suna wanzar da zalunci A DUNIYAR MU....."
I zuwa lokacin hawaye sun ciko idanun Mama Tani jin abinda d'an uwan nata ke fad'i... "Yaya Hannatu fah kace, macen da ta tafi ta rabu da kai cikin wannan hali na jinya, ta yaya ta sama min aiki....."
Malam Ladan ya murmusa kana yace "K'warai kuwa, Hannatu dole tasa mikayi nesa da juna sabida wannan k'udiri namu ya cika, Hajiya Dije tasan Hannatu amma batasan ki ba.... Mun turaki aikatau a wannan gidan ne sabida amanar da Allah ya bar mana na sanin gaskiyan lamari ya isa wajen d'an marigayi Sa'oud, a wancan lokacin idan ya sani bashida girma da zai iya kare kansa, amma yanzu ya kawo k'arfi zai iya yak'an mak'iyansa wanda suka jima suna zaluntar sa...."
Kan Mama Tani gaba d'aya ya juye tama rasa meke faruwa..... Lokaci guda suka jiyo sautin dariyar Maina kana yace "Ka gama bata labari tsohon banza zata bak'unci lahira dama yanzu, kai kuma taurin ran da kayi kak'i mutuwa tuntuni tun lokacin da ya kamace ka ka mutu ka doge kace bazaka mutu ba sai ka karb'i horo da azaba, toh tunda hakan ka zab'a mun tanadar maka nau'i-nau'i na azaba......"
Malam Ladan ya murmusa kana yace "Dije bazata canza ba kuma nasan akwai ranar irin faruwan haka... Saidai kaman yanda na sanar dakai ko yanzu kuka kasheni na gode wa Allah, Allah ya gani na ida sak'on gaskiya, idan na tafi na tadda Sa'oud zaiyi farin ciki sabida gaskiya ta bayyana A DUNIYAR da ya tafi ya barta cikin duhuwa....." baikai aya ba Maina ya d'aukesa da wata jahilan mari....
Mama Tani ta saki k'ara cikeda tsoro take rok'on Maina kada ya kashe mata d'an uwa...
Tsawa ya darara mata kafin ya saita ta da bindiga yana fad'in "Kece zaki soma bak'untar lahira keda aka had'a baki dake shekara da shekaru....."
Jikin Mama Tani ya d'auki rawa ganin bindiga ra'il ainu ana saita ta dashi......
"Kayi hak'uri dan Allah, wllhi bansan komai ba, bansan maganganun da kuke ba... Dan Allah....."
Bata kai aya ba Maina ya saita bindiga sosai yana wata irin murmushi.... Lokaci guda ya saki bindigar
Wani irin k'arfi yazo wa Malam Ladan tuni ya ture k'anwarsa harsashin ya samesa a goshinsa.... Allahu Akbar....
Mama Tani takai dubanta ga d'an uwanta lokaci guda ta saki wani irin k'ara wanda saida su Ubi dake bayan gidan suna cin masarsu suka jiyota...
"Kai K'waro wai bakuji ihu cikin gidansu Babban Yaya ba.." Cewar d'aya daga cikin su,
"Kai eh wllhi nima naji, kunsan fah Abbansa kawai yake bari a gidan ya tafi aiki..." Aljan ya fad'i cikeda kulawa...
"Kai ku tashi muje mukar duk d'an tsinanniyar da muka tarar a gidan....." Ogannen cikinsu ya fad'i yana zaro wata wuk'a gefen wandon sa.....
Tuni sun d'unguma sun nufi gidan....
Maina sai tokarin gawar Malam Ladan yake yana fad'in "Uban wa yace ka mutu yanzu, uban wa yace maka naka rayuwar akazo d'auka... Azaba ce ta kamace kafin mutuwa....."
Mama Tani kuka take tana rungume da gawar d'an uwanta... Sam basuji shigowar su K'waro ba, sabida hankalin Maina da tunanin sa yayi nisa wajen tunanin kalan d'iban albarka da yau Innah zata masa ya kuma failing d'inta, tunda a raye tace ya kawo mata Malam Ladan...
Yunk'uran da zaiyi da niyyan juyowa yayi tozali da wad'annan halittu sun kewaye k'ofar d'akin suna dubansu...... Ga Mama Tani kwance saman gawan Yayanta tana kuka sosai tana fad'in "Yaya kada ka tafi ka barmu a lokacin da muke tunanin ka soma samun sauk'i..."
"K'waro duba mana kashe shi yayi.....?" Cewan Ubi dake tsaye yana zaro jajayen idanunsa.....
Maina ya d'ago bindiga yana pointing d'insu yake fad'in "Duk shegen da yazo nan sai na kashe sa...."
Ga mamakin sa dariya suka fashe masa dashi kana sukace "Ai bari kaji ko Ak47 ka d'auka yau bazamu barka ka fice daga nan ba, ko kashe mu zakayi gaba d'aya idan dai akan Abbah ne wllhi saidai ka k'arar damu....."
"Arne jininka ya halarta....." Cewan d'aya daga cikinsu....
"Ai ba jini bane kurum ya halarta, aci uabnsa tukunna, a d'and'ana wa tsinanne azaban duniya kafin ya tafi ya tarar da na can...." Aljan ya fad'i yana wasa wuk'a jikin garu....
Maina kuwa tuni ya d'ana bindiga suna nufosa... Saidai yana harbawa yaji wayam babu harsashi cikinta.....
*********
A birkice ya shigo gidan saidai ganin gidan nasu wayam babu kowa yasa gabansa kuma fad'uwa... Badon rikicewa da yayi ba ai da bai biye na Aunty Saudat da tace kar ya sanar da jami'an tsaro kar ya sanar da d'an uwansa yazo kurum shi kad'ai... Matan da yasan she's lunatic....
Hangota da yayi yasa sa k'arasawa a guje yana tambayarta "Aunty ina Lubna.... Meke faruwa ne kam... Su waye masu neman rayukan mutan gidan nan....."
Aunty Saudat dubansa take murya na rawa tace "Kardai basu kashe Deeni ba Lubna suka kashe.... Naseer Innah da Kabeer sun kashe Lubna... Naseer ina Fawaz, ina d'ana.....?"
Kan Naseer ya juye gaba d'aya... Yama rasa gane meke wakana.... A d'ari ya nufi sashe-shae na gidan yana hangamewa....
******
Mamy ta kuma kallon Azeema tana murya na rawa kana tace "Da dai kin barni naci abincin nan, Azeema bamuda da wani ghost of chance, Wllhi Laure kashe mu zatayi don bata da d'and'anin imani...."
Azeema ta kamo hannun Mamy tana dubanta kana tace "Mamy jikina ya bani zamu fita a gidan nan... Na tabbata mafarkina bazai zama banza ba.... Ki daure ki k'ara daurewa har Allah ya taimake mu....."
Cikin sauri Azeema ta mik'e ta d'au fork d'in da aka kawo masu na cin abinci ta k'arasa jikin k'ofa, ta lek'a ta tabbata Steve baya nan.... Cikin dabara ta soma bud'e lock d'in k'ofar da cokali mai yatsun....
******
Cikin tsananin tashin hankali suke bugun k'ofa wa Jamila suna rok'onta kada ta kashe kanta kaman yanda take ikirari.... Salma ta koma gefe ta suri wayar Momy ta shiga dialing layin Naseer cikin tsananin kuka da tashin hankali...
Ganin kiran Momy na shigo masa ya saka gabansa wani mugun fad'uwa... Hannun Naseer na tsananin b'ari yake d'aga kiran...
Kukan da ya jiyo Salma nayi ya haifar masa da wani sabon tashin hankali
"Soja don Allah kazo ka taimake mu, kazo don Allah kafin Addah ta mutu....."
Abinda ya jiyo Salma na fad'a masa kenan a cikin wayar.....
Kasa cewa komai yayi sai bud'e murya da yayi yana fad'in "Wai meke faruwa ne A DUNIYAR MU....? Shikansa yasan na cikin tsananin buk'atar taimako bazai iya yi shi kad'ai ba... Lokaci guda ya shiga neman layin Affan....
Bayan sun ida magana da Affan dawowa ga Aunty Saudat yayi kana yace "Aunty zama ba namu bane, ban gane duk abubuwan da kike fad'i ba.... Amma dole mu fice mu nemi taimakon 'yan sanda, Lubna da Jamila duk bamusan wani hali suke ciki ba...
Gyada masa kai kurum tayi ta nufi bayansa yana doka kira wa masu tsaron gidan, lokaci guda yake dialing layin Fawaz bai shiga.....
*******
Asibitin Dr Fago Deeni yakai Lubna, shi baima san asibitin yara bane, tohma shi ina ruwansa ko asibitin yara ne, shi kawai damuwarsa yayi saving rayuwarta ne, asibiti mafi kusa ya nema...
Suna zaune ofishin Dr Fago yana kuma masa nasiha gameda duniya sabida Dr Fago ya grime masa abadan amma bayan Uncle d'insa Naseer bashida abokin shawari da ya wuce Dr Faruq Fargo.... Wata nurse ce ta shigo a kid'ime sabida yanda Deeni ya Kid'imota.... A birkice take fad'in "Dr dead body aka kawo....."
Daga Dr Fago har Fawaz a tamanin suka nufo waje...
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*55*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Deeni yana hango Dr Fago ya nufesa yana janyosa yana mai fad'in "Dr ka taimaka min, ka taimaka min pls Dr...." gaba d'aya yanda yake maganar zaka fahimci a tsananin birkice yake... Gaba d'aya nema yake ya birkita likitan ma... Sam Deeni baiko kula da Fawaz wanda fitowar sa kenan....
Dr Fago girgiza kai kurum yake yana duban Deeni dake kuma cakumosa kana yace "Bawan Allah calm down... Baka dubi sunan asibitin nan bane kafin ka shigo, wannan asibitin yara ne, bamuda magunguna manya a nan... Ba...." Bai kai aya ba Deeni ya katse sa da fad'in "Likita likita ne koda kuwa likitan k'wari ne, nidai dan Allah ka taimake ni ka duba min ita don Allah...." Ya k'arashe yana kuma komawa ga Lubna wacce tuni ya kwantar da ita saman doguwar kujera a reception...
Gaban Fawaz bai daina dukan tara-tara ba sanda yayi tozali da 'yar uwarsa Lubna kwance saman kujera tamkar bata numfashi... Dai-dai sanda Dr Fago ya k'arasa yana dubata Fawaz ya k'araso a tamanin had'i da ture Dr Fago ya shiga jijjiga Lubna yana ambato sunanta.... Dr Fago ya zubawa sauratar Allah idanu... Lokaci guda kuma Fawaz d'in ya mik'e ya isa ga Deeni dake faman binsa da kallo shima... Kan kace me Fawaz ya cakumo Deeni yana wajajjaga sa yake fad'in "What did you do to her, mai kayi mata... Ka fad'a min mai kayi mata.....?" Ya k'arashe yana mai yin jifa da Deeni... Tuni Nurses sun soma kawo d'auki, shi kuwa Dr Fago baibi takan Deeni da Fawaz ba ya shiga k'ok'arin duba Lubna dai-dai nasa iyawan....
Fincika Deeni yayi daga rik'on da Fawaz yayi masa idanunsa jazir yake fad'in "Kaje ka tambayi waccar tsohuwar kilakin da bata d'auki sab'o da kisan rai a bakin komai ba wacce kake ikirarin ita d'in kakar ka ce, itace sanadiyan sumewar Lubna.... Banida lokacin ka, na tabbata idan Lubna ta bud'e idanunta kaji sauran bayani a bakinta... Ta mahaifina nake yanzu tunda na kawo Lubna wajen da nake saka tsammanin zata samu tsira da yardar Allah....."
A guje ya nufi k'ofa tamkar tab'ebb'e ya bar Fawaz nan tsaye wanda sam bai gane maganganun Deenin ba....
******
Cikin sa'a lock d'in ya bud'e, banda hamdala babu abinda suke cikin zukatan su.... Azeema ce ta soma sad'ad'owa ta nufo waje, yanda ta hangi wulk'awan wasu matasan maza majiya k'arfi guda biyu... Ta d'an lab'e jikin garu har suka k'arashi wucewar su kafin ta fito.... Can wajen flowers ta hangi k'aton abin wucewar ruwa tamkar yanda ta gani cikin barcinta.... Sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin ta komo d'akin ta tallafo Mamy ta taimaka mata ta dai-daita crutches d'inta kana tayi k'asa da murya tace "Mamy na gano mana hanyar, insha Allah zamu fice daga gidan nan yanzun nan...."
Mamy ma cikin k'asa-k'asa da murya take fad'in "Anya Azeema, anya kinaga zamu iya guduwa....?"
Azeema ta jinjina kai kana tace "Idan Allah ya yarda zamu gudu, idan kuma bamu gudu ba toh tamu kalan k'addaran kenan A DUNIYAR MU, don mutum baya wuce k'addarar sa...."
Jinjina kai Mamy tayi kana tace "Haka ne Azeema, mu gwada idan Allah yayi zamu fita zamu fita idan kuma baiyi zamu fita ba muna rok'onsa ya karb'i rayukanmu yana mai farin ciki damu...."
Lokaci guda fuskar Azeema ya cika da murmushi bata san sanda ta rungume Mamy tana fad'in "Ina sonki Mamy tsakani na da Allah..."
Mamy ma murmusawan tayi kana tace "Ina sonki nima d'iyata tsakanina da Allah... Muje Allah ya bamu nasara..."
Azeema ta jinjina kai kafin suka soma sad'ad'owa suna fitowa kowacce cikinsu da kalan addu'ar dake bakinta.....
******
Ba k'aramin jin jiki Maina yayi ba wajen wad'anan 'yan sara suka, gaba d'aya azaban jahilci suke gana masa kota kan gawan mahaifin Deeni basu ba suka fice da Maina suna d'and'ana masa ukuban duniya.... Mak'ota kuwa tuni sun soma tururuwar shigowa gidan....
Can cikin wani uncomplicated building suka samu suka shimfid'a Maina had'i da d'aure masa baki don karma yayi ihu a kawo masa d'auki...
Aljan ya dubi K'waro yace "Kai k'waro bani k'araran nan, farke min ledar ta a watsa wa d'an kutuma....."
Maina baki a d'aure hannaye duka a d'aure yana ji yana gani suka farke ledar k'arara suka masa zigidir daga shi sai gajeren wando suka shiga watsa masa k'araran nan.... Sai zare idanu yake babu halin ihu.... Aiko k'araran nan tana sallama da fatar sa ya shiga turbud'ewa a wajen yana gwaruwa jikin garu yana son sosa jikinsa, abinka da garu maras siminti tuni jikin Maina ya shiga tsatsagewa jini na tsartowa.... Gefe suka matsa don kar azaban ta shafesu sai dariya suke ganin yanda yake juyi a wajen....
Ganin mutane cike a lungun gidansu ya sanya gabansa mugun fad'uwa, kowa idan ya kallesa sai ya d'an girgiza kai cikeda tausayawa, dama mutanen unguwa mugun tausayinsa suke sabida sunsan shike jinyar mahaifin nasa....
A hankali ya shiga furta "Abbah, Abbah na! Sun kashe min shi, sun kashe min Abbah na.....!" Ya k'arashe maganar cikin bud'e murya, a skwane ya nufi cikin gidan nasu k'irjinsa na ci gaba da bugawa....
Cak Deeni ya tsaya hango Mama Tani da yayi zaune gefen mutum an rufesa da k'yalle har kansa ga mata 'yan unguwa a gefenta sai hak'uri ake bata.....
Lokaci guda hawaye suka shiga gangarowa daga idanun Deeni.... Ya shiga tuno rayuwarsu da mahaifin sa tun sanda ya dawo garin Bauchi shida Mama Tani,.... Ya tuna randa aka shigo masu da mahaifinsa cikin tsananin jinya, ya tuna sanda Mahaifiyarsa tasa k'afafu ta tsallake su ta tafi ta barsu cikin kuka.... Ya tuna a 'yan kwanakin nan nasiha da mahaifinsa ke masa.... Lokaci guda ya k'arasa kan gawan ya yake k'yallen fuskar mahaifinsa ya bayyan tamkar yana murmushi.... Lokaci guda ya shiga girgiza kai yana fad'in "Abbah kar tafi don Allah.... Kar ta tafi ka barni.... Abbah saida suka kashe ka.... laifi na ne da na bari suka kashe ka, laifina ne da na kasance ba jarumi ba... Laifi na ne da na gudu masu na kasa fuskantar su na yak'e su.... Abbah Abbah....!" Kasa ci gaba da magana yayi sai wani irin kuka da ya fashe dashi had'i da kwanciya saman gawan mahaifin sa.... Mama Tani kuwa kukanta ya k'aru sosai tun sanda Deeni ya shigo gidan
Mutane kuwa tausayi ya cika zukatansu daga masu matsan k'walla sai masu ficewa sabida bazasu iya jure kallon wannan abin tausayi ba, an mayar da ran talaka tamkar ran kiyashi, a shigo har cikin gidan mutum a kashe shi sabida rashin galihu.... (K'alubale A DUNIYAR MU)
*******
"Cakumo Innah yayi yana wujijjigata yake fad'in "Why why Innah... Meyasa zaki tura Maina yazo da mutumin, kika san wake biye dashi, kika san tun yaushe suke bincike akanmu ba tareda sanin mu ba.... Shikenan komai ka iya faruwa, wllhi muddin Naseer yasan abinda mukayi ma iyayensa shikenan kashinmu ya bushe daga ni har ke...." Ya k'arashe yana wani irin huci...
"Ni yanzu ba wannan ba k'ara latsa lambar Maina muji wanne yake ciki...." Ta fad'i tana kuma safa da marwa cikin parlorn...
Hannunsa har na b'ari ya shiga dialing layin Maina, aiko sai ringing take....
"Kai K'waro duba rigar mutumin nan naji kaman waya ake masa..."
Aljan ya fad'i yana busa hayak'i saman gini yana kallon Maina da gaba d'aya ya kurje jikinsa wajen Susan k'arara....
K'waro ya zaro wayar yana k'are mata kallo kana ya fashe da dariya yace "Yasin babbar kamu ce... Wannan ai sai tayi hansin alk'ur'an...." Ganin waya na kuma shigowa yasa Aljan cewa "bani ita na amsa...."
Babu musu k'waro ya mik'a masa...
"Alo Aljan gagagri uban kowa ke magana.... Waye mai kira....?" Ya k'arashe yana d'aura k'afa d'aya kan d'aya sai ka rantse shine mai wayar...
Gaban Alh Kabeer ya yanke ya fad'i... Kallon Innah yayi k'irjinsa na bugu kana yace "Wai Aljan ne mai magana, Innah anya wannan Malam Ladan d'in mutum ne, kinga fah daga saman gada muka jefosa bai mutu ba yanzu ga wayar Maina wai Aljan ne mai magana...."
Tsaki Innah tayi tana duban lusarin kafin ta fuzge wayar ta k'ara a kunnenta maimakon taji magana sai k'aran ihun Maina take jiyowa ta cikin wayar don tuni sun bud'e masa baki sun shiga bad'e karjejjen jikinsa da garin barkono.... Sai shewansu da ihun Maina kurum Innah ke jiyowa.... Ai batasan sanda tayi jifa da wayar ba...
Suna a haka suka jiyo magana daga gate, lek'awan da zasuyi kuwa suka hangi 'yan sanda ne ke k'ok'arin shigowa gidan...
Alh Kabeer da tuni gumi ta shiga keto masa mugun kallo yake watsa wa Innah kafin yace "Kin gani koh... Kinga abinda dolancin ki ya haifar mana koh... Da kike ce min dak'ik'i dolo ai yaukam ta tabbata kece dak'ik'iya doluwa....." Ya k'arashe yana bud'e k'ofar baya yake fad'in "Wllhi bazan tsaya 'yan sanda su kameni ba, wayasan uwar me Maina yaje yayi...."
Tuni Innah tabi bayansa a d'ari tana fad'in "Ina zaka tafi ka barni ai k'afata k'afarka...."
D'an k'aramin garu dake bayan gidan ya haye.... Tuni Innah ta tattare zaninta tana k'ok'arin d'alewa garu tamkar 'yar biri, ganin zani zai kawo mata cikas ya sanyata saurin kwancewa tayi wurgi dashi, ya rage mata saura fatari wanda ya wuce gwiwarta kad'an...
Daga saman garun take fad'i wa d'anta Kabeeru ya cab'ota... Aiko nan ta dirgo ya capke ta suka shiga tsula gudu a dajin dake gefe kad'an da gidan.... Don gidan dama a bayan gari yake....
Sargent Idi ya dubi abokan aikin nasa bayan sun gama duba gidan basuga su Innah ba kana yace "Kai anya bamuyi gangancin biye Deeni ba, kunsan bawai saiti ne dashi ba, kar yazo ya jaza mana rasa aikinmu, kar ku mance sanda ya kwashe mu ya kaimu hotel wai yabi sawun matarsa, wllhi Deeni mugun d'an duniya ne, yanzu haka matar nan d'an wani abu k'alilan ta masa yace bari ya tsorata ta tunda d'iyarta yake tuk'awa..."
D'aya abokin nasu yace "Kai nima wllhi duk tunani na kenan.... Deeni ya wuce gaban haka d'an iskan kansa ne zaiyi mata abinda yafi haka, kun mance da har aron kayanmu yana amsa yaje yaci uwar duk wanda ya masa iskanci....."
Lokaci guda suka Shek'e da dariya kafin Sargent Abbas yace "Ga kuma tsoro uwa farin kura da asirinsa zai tonu su gane ba d'an sanda bane da kunga yanda zai arce a guje.... Kai Zahraddeni d'an duniya ne...." Ya k'arashe yana rik'e cikinsa sabida dariya...
"Tab'a mana shi a waya kaji.." Cewar d'an dogon cikinsu...
D'ayan ya shiga dialing layin Deeni baya shiga... Ya d'anyi tsaki yana duban abokan aikin nasa kana yace "Ai kaji d'an iska wllhi kashe wayar ma yayi...."
Dariya kurum sukayi kafin suka ce "Mu kama kanmu mu cika ma rigar mu iska kafin muyi salalan aikin mu....." Lokaci guda suka fice daga gidan
******
Kallon Aunty Saudat yake yana jin k'afafuwan sa sun masa nauyi, gaba d'aya kansa ya juye bai fahimci maganganun da take masa ba wanda yafi dangantasu da sumbatu irinta masu tab'in hankali...
Ta yaya zata ce Innar sa da d'an uwan sa su suka kar Abban sa sannan tana tsoron sun kar Lubna...
Murmushi Naseer yayi sanin tana jinyar hauka kana ya d'an zauna daga can gefenta yace "Aunty kinaso kije gida, na kira azo akai ki gida, kar ki damu kinji I'll take care of everything.... Kije gida ki huta kinji....." Ya k'arashe yana k'ok'arin zaro waya a aljihu...
Girgiza masa kai take tana hawaye take ci gaba da fad'in "Naseer wllhi iyakacin gaskiyata nake fad'a maka... Sannan cikin hankali na nake, nasan irin haka dole ta faru duk ranar da na soma sanar da wani wannan mummunar labari da ta jima tana addabata a kwanyata..... Naseer ka yarda dan......"
Bata kai aya ba Naseer ya mik'e yana wani irin huci yake dubanta.... Baisan meke masa yawo a kwanyar sa ba sai janyo hannunta da yayi ya nufi mota da ita..... Ga dukkan alamu wannan mata bata warke ba....
Saida ya tabbata ya kaita cikin mota ya zaunar da ita kafin ya dawo ya sami DPO Bala yace "DPO zan kai matar nan gida a bata kula ina nan dawowa tunda Fawaz ya sanar dani yana tare da Lubna., idan sai mu tafi wajen su Fawaz d'in muji abinda ke faruwa, sabida idan muka tafi da matar nan abubuwa suna iya rincab'e mana don dama ba lafiya bane ya isheta..." Baiko jira cewar DPO ba ya nufi motar sa kaman zai kifa da k'asa...
******
Ga mamakin su Mamy suna isowa wajen abin fitar rowan nan suka nema suka rasa sai shuke-shuke kawai suka gani.... Gaban Azeema ya yanke ya fad'i sanda ta d'ago kai tana duban Mamy dake durk'ushe gefenta..
Cikin rawar murya take fad'in "Mamy wllhi wllhi a dai-dai wajen nan naga rariyar fitan ruwa.... Kuma gashi yanzu ban gani ba....."
Mamy tace "Kodai baki kula bane, k'ila ta d'aya b'angaren kika gani...."
"Mamy wllhi a dai-dai wajen nan na gani, kinga fulawar da nayi alama da ita....." Azeema ta fad'i cikeda fad'uwan gaba...
Kafin Mamy ta sami zarafin magana sai hango d'an dajjijon mutum sukayi tsaye gefensu fuskar sa ta cika da murmushi....
Lokaci guda suka zabura sabida tsananin firgita... A hankali mutumin yake k'arasowa yanda suke suko tsoro na dad'a cikasu...
"Baba don Allah kayi hak'uri , kada ka fallasa mu don Allah... Ka tausaya mana bamuda zab'in da ya wuce mu gudu ne don tsira da rayuwar mu....." Azeema ta fad'i cikin tsananin rawan murya....
Murmusawa Dattijon ya kuma yi kana yace "K'warai kuwa ga dukkan alamu guduwa kuke son yi, kuma hakan bazai tab'a yuwuwa a gareku ba saida taimako na, sannan ni a k'a'idar taimako na mutum guda jal nake taimakawa... Idan ya wuce mutum guda toh ko kun fita ku duka biyu zaku kuma dawowa gidan nan, amma idan na taimaki guda zai tsira da rayuwarsa cikin yardar Allah..."
K'irajensu suka yanke suka fad'i....
Azeema ta shiga girgiza kai cikin sauri kana tace "Baba idan dai haka ne gaskiya bamu buk'atar taimakon ka, gwara na kuma lalumawa na gano hanyar fitar ruwan nan da d'azun na gani....."
Dattijon bai daina murmusawa ba yake fad'in "Yarinya wannan hanyar ruwa bazaki tab'a ganinsa ba muddin da niyan guduwa a gidan nan kika zo, ni kad'ai ne k'waran mutum da zan taimaka maki kiga wannan hanya da ya b'ace maki... Kuma idan na bud'e maku ita kuka fita ku duka biyu toh babu yanda zakuje zaku dawo cikin gidan nan, k'a'idan taimako na kenan....."
"Yanzu kai bawan Allah kana gani sai a yanka mutum bazaka taimaka ba... Haba, haba Baba... Ran d'an Adam fah ba kiyashi ba....." Mamy ta fad'i tana mai jinjina lamarin...
Shiru yayi tamkar mai nazari yana duban Mamy kana yace "Baiwar Allah ai A DUNIYAR MU an mayar da ran d'an Adam tamkar ta tururuwa sabida neman duniya, da yawan mutane sun zama mushirikai sabida neman Duniya, zanso ace na taimaka maku ku duka biyu, amma taimaka maku ku duka biyu na nufin rasa rayuwata ne nima, kuma idan na mutu shikenan babu mai kuma taimakon wa'enda zasu zo a baya... Nasani rayuwa da mutuwa duka na Allah ne.... Amma har kullum ina son taimakawa wa duk wata rai da za'a shigo da ita gidan nan...."
I zuwa lokacin jikin Mamy da Azeema ya kuma yin sanyi sosai....
Dattijon ya kuma dubansu kana yace "Kun yarda da sharad'in a fitar da mutum guda ko kuma zaku zauna a gidan nan har k'addarar ku ta taddaku.."
Saurin girgiza kai Mamy tayi tana k'ok'arin k'ak'aro murmushi kana ta dubi Azeema had'i da tallafo fuskarta tace "Azeema wannan dama bazai wuce haka nan ba.... You must go... Zaki tafi zaki bar gidan nan... Sanadiyan biyoni da kikayi don wargaza mumnunar shirin da nakeyi kika tsinci kanki a gidan nan, ni kuwa ni na kawo kaina..... Ni yafi cancanta na zauna cikin gidan nan na karb'i k'addara ta da hannu bibbiyu.... Azeema ko bayan raina ki tafi garin Jama'are unguwar siriri k'asar babban bishiyar durumi dake a b'angaren dama ki toni sammon da akayiwa Daddy don ya sami lafiya..... Ina sonki ina k'aunar ki Azeema, sannan ki fad'awa Affan da Shareefah su yafeni ina k'aunarsu... Ko ban kuma ganinsu A DUNIYAR MU ba ki fad'a masu a rayuwar da zamuyi gaba ina fatan na gansu.... Azeema ki rok'a min Daddy gafara, nasan nayi masa ha'inci mafi muni A DUNIYAR MU... Naso na koma naci gaba da rayuwa dashi amma Allah bai k'addara hakan ba.... Ki sanar dashi Asma'u tana k'aunarsa kuma tana neman yafiyar sa don samun nasaran mahaliccinta...." Kasa ci gaba da magana Mamy tayi sabida kuka da yaci k'arfinta..
Azeema kam kuka take tamkar ranta zai fita tana mai girgiza kai, cikin muryar kuka take fad'in "Mamy kece ya kamata ki tafi, kece ya kamata ki warware sammon da akayi wa Daddy...." Lokaci guda ta d'aura murmushi saman fuskarta kafin taci gaba da fad'in "Kije ki rok'i Daddy gafara ya yafe maki.... Sannan ki nemi na 'ya'yanki.... Idan Allah ya numa zamu kuma had'uwa da juna A DUNIYAR MU zamu had'u.... Idan kuma bai k'addara hakan ba ina fata ya sada fuskokin mu da alkhairi a rayuwar da zamuyi bayan wannan.... Ki rok'a mun su gafara gaba d'aya.. Sannan ki sanar da duk wani nawa ina k'aunarsa dukda nasan mahaifana sun rasu akwai sauran dangi.... Mamy ina k'aunarki sabida tun tasowata a gabanki nake tun kafin mahaifina ya amsa kiran mahallicin sa..... zan tafi zan tafi na taddasu da yardar Allah...." Ta k'arashe murmushi sosai saman fuskarta...
Girgiza kai Mamy take tana k'ank'ame da Azeema dake k'ok'arin b'anb'are Mamyn daga jikin nata, lokaci guda suka hangi Baba ya bud'e wargajejiyar mafitan ruwan wanda a gefensu yake tuntuni amma basu gani ba...
Mamy na dogewa tana rik'o Azeema dake turata cikin rariyar da iya k'arfinta tana kuka sosai take fad'in "Ki tafi ki tafi Mamy...."
Mamy na kuka sosai tana jawo Azeema tana dogewa take fad'in "Azeema bazan tafi na barki ba... Don Allah ki daina turani.... Azeemmmaaaa...! " Mamy ta k'arashe da k'arfin gaske dai-dai sanda Azeema ta turata waje da k'arfin gaske... D'if kaman d'aukewan ruwa ta nemi gidan ta rasa... Lokaci guda Mamy ta damk'e kanta had'i da sakin k'aran gaske. Tuni ta zube a wajen sumammiya...
*******
Affan dake gefe bayan ya b'alle k'ofar da Jamila ta gangak'ame kanta ciki tana k'ok'arin kar kanta sai kallon tausayi yake binsu dashi lokacin da 'yan uwan suka rufu kanta suka rungume gaba d'aya suna kuka.. Layin Naseer ya kirawo lokaci guda Naseer ya d'aga cikeda fargaba don yanzu har tsoron waya yake...
"Affan yaya meke faruwa....?" Ya tambaya hankali tashe.. A tak'aice Affan ya sanar dashi abinda ya tarar..
Naseer ya shafi goshinsa kafin yace "Ka gane tattarosu daga barikin gaba d'aya ka kawosu gidanmu pls...." Jinjina masa kai Affan yayi kafin yace "Gaskiya hakan kam zaifi, barin yi magana da Momy... Muna nan tafe insha Allah..." Daga haka katse wayar yayi cikin sauri kafin ya nufi yanda Momy ke zaune...
Har lokacin Aunty Saudat kuka take had'i da k'ura ma waje guda idanu... Naseer ya shiga doka kirawa Mama Tani don ya bar mata Aunty Saudat hannunta ta kula da ita amma wayam shiru baijita ba......
Tuni ya nufi k'ofa cikin sassarfa, saidai kafin ya isa k'ofa ya jiyo muryar Aunty Saudat tana fad'in "Bazaka sameta a gidan nan ba... Ta tsira wa rayuwarta sannan ta tafi tseratar da ryuwar d'an uwanta da d'ansa...."
Cak ya tsaya ba tareda ya kuma motsawa ba... Wannan magana maras hankali bazai yi sa ba...
Cikin wani irin fad'uwan gaba ya juyo yana dubanta, a hankali ya taka ya isa har gabanta kafin ya durk'usa saman gwiwoyinsa yana fuskantar ta yake fad'in "Aunty ta tsira ma rayuwarta kika ce sannan waye d'an uwanta da ta tafi kub'utarwa...."
Bata kai ga basa amsa ba suka hangi Lubna da Fawaz suna shigowa su duka biyu idanunsu jazir Fawaz na rik'e da ita lokaci guda Lubna ta soma bawa Naseer amsa da fad'in "Mahaifin Deeni shi Mama Tani ta tafi kub'utarwa daga sharrin Innah da kuma Yaya... Ya Naseer Innah ba mutuniyar da muke tunani bace....." Ta k'arashe cikin tsananin kuka lokaci guda ta tafi ta rungume Yayan nata wanda ya koma tamkar mutum mutumi bai gane abubuwan da suke kan wakana A DUNIYAR tasu ba... Fawaz kuwa tuni Mahaifiyarsa ta taso ta rungume sa tana kuka sosai...
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*56*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Hawaye fita daga idanun Fawaz suke amma murmushi yake wanda kake iya hango fararen hak'waransa masu k'ara masa kyau idan ya bud'esu bai daina fad'in "Mum Mum.... I just can't believe you are back to your senses.... Mum since when.. Tun yaushe kika dawo hankalin ki...?" Ya k'arashe yana kuma rik'o hannayen mahaifiyar tasa...
Itama d'in hawayen ne ke zubo mata kana tace "Fawaz tun ranar da ka kawo budurwarka gidan nan tun wannan rana hankali na ya dawo jikina, na b'oye maku hakan ne sabida gudun kada mu fad'awa sharrin mahaifinka da Innah.... Fawaz wad'annan bayi biyu sun azabtar dani sun wahalar dani sun....." Kasa ci gaba da magana tayi sabida kukan da yaci k'arfinta....
Fawaz ma hawayen kurum yake yayinda zuciyarsa ke ci gaba da tafarfasa... Naseer kuwa har wannan lokaci ganin lamarin yake tamkar almara, tamkar a wasannin kwaikwayo, Lubna tana nan rungume cikin jikinsa kuka sosai take itama....
Wayoyin Innah da Kabeer gaba d'aya babu wanda yake shiga, babu wanda yasan yanda suka tafi, lokaci guda an nemesu an rasa wanda hakan ya tabbatar wa Naseer sud'in masu laifi ne.... Abbahn sa ya shiga tunowa, ya tuna sanda ya dawo daga makarantar kwana ya tambayi Innah mahaifinsa sai sallesa tayi tsaf tace dashi ya mutu gangaratsau babu koh tausasawa.... Zuciyar Naseer ta shiga masa zogi da wani irin rad'ad'i wanda bai tab'a jin irinsa ba his whole life... Yanason ganin Innah yana son yimata tambayoyi da dama, a halin yanzu babu wanda yake buk'atan gani irin Innah dole ya ganta kuma dole ta amsa masa d'inbin tambayoyin da yake dasu wanda zai mata....
Shigowan su Affan dasu Momy had'i da su Salma gaba d'aya ya sanya Naseer mik'ewa yana k'ok'arin kwantar da Lubna saman sofa... Saidai tuni Lubnar ta nufi Salma ta rungumeta sosai tana kuka... Yanayin da suka tarar dasu ya bala'in d'aga masu hankali...
Salma rik'e Lubna tayi ba tareda sanin meke wakana ba... Lokaci guda ta sauk'e idanunta kan Sojanta wanda kana ganinsa kasan cikin tsananin tashin hankali yake, bai iya furta masu komai ba sai kamo hannun Affan da yayi suka fice.....
*******
Tafe suke a mota Affan yana kuma jinjina lamarin recently Mamyn sa ta tasamma kashe mahaifinsa yanzu kuma ace Alh Sa'oud ma matarsa da d'ansa ne suka kashe sa... Kai wannan wacce irin rayuwa ce, wace irin duniya ce...
"Affan na kasa yarda na kasa aminta, Affan shin haka yana faruwa A DUNIYAR MU... Toh me Abbah ya masu, meyasa zasu kashe shi... Affan don Allah kace min mafarki nake ba gaskiya bane, dan Allah kace min zan farka daga wannan mummunar mafarki da nake,..."
D'an slow Affan yayi kafin ya paka motar gefen kwalta, juyowa yayi sosai yana duban Naseer da tuni jikinsa tayi jajazir musamman fuskar sa da idanun sa kana yace "Naseer mu kuma kalan tamu k'addaran kenan A DUNIYAR MU, wasu irin iyaye muka samu masu neman Duniya da k'arfin gaske ta hanyar kashe mazajansu hak'ik'a Manzon Allah SWA yayi gaskiya da yace _Al Duniya mata'un, wa khaira mata'ul Duniya Al mar'atul Saliha_ Duniya jin dad'i ne, kuma mafi alkhairin jin dad'in duniya shine mace ta gari.. Hak'ik'a duk wanda baiyi dacen mata ba toh babu komai A DUNIYAR SA face bak'in duhu.... Nasan kana cikin wani yanayi Naseer amma kayi hak'uri ka karb'i k'addaran ka a yanda tazo maka ko nace mu karb'i k'addaran mu a yanda tazo mana, wata rana duk wannan tashin hankula da tarzoma da muke arangama dasu A DUNIYAR MU zasu wuce zasu zamto tarihi da yardar Allah...."
Jinjina masa kai kurum Naseer yayi ba tareda ya iya furta koda kalma ba kafin Affan yaci gaba da driving don yasan gidansu Deeni, lokacin da ya saka tsallen kwad'o a barikinsu akan Lubna da kansa ya dawo dashi gida
Suna isowa suka tarar za'ayi sallah, kai tsaye alwala suka wuce sukayi don suma su samu su sallaci mamacin, Deeni yana hangosu ya d'an kauda kansa gefe, don har cikin ransa haushin duk wani d'an Santana family yake ji... Sun kula da hakan basu tak'ura sun masa gaisuwar ba sabida yanayin da suka gansa ciki.....
Naseer da Affan tareda su akayi komai na mahaifin Deeni, bayan sun komo daga biso ne suka shiga har cikin gida sukayiwa Mama Tani gaisuwa, abin har wannan lokaci damun Naseer yake, wai Innah da Yayan sa Kabeer ne sukayi wannan aika-aika, kenan su kashe rai a wajen su ba komai bane, innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un.... Allah ka mana tsari da sharrin zuciya... Tambayar da yake yi ma kansa shine _Me mahaifin Deeni ya masu suka kashe shi..._ Bai kai ga samo amsar tambayar ba Affan ya d'an dafasa yace suje waje su sami Deeni....
Idanun Deeni sun kad'a sunyi jazir, duk wanda ya gaishesa da k'yar yake iya amsawa, aiko yana hango su Naseer ya mik'e daga wajen yasa kai zai nufi cikin gida...
Affan ne yayi saurin cimmasa had'i da d'an rik'o hannunsa, murya can k'asa yake fad'in "Dan Allah ka bari mu maka gaisuwa..."
D'agowa Deeni yayi yana duban Affan kaman zaiyi magana sai kuma yasa kai yayi shigewar sa cikin gida... Mama Tani tana gani ya wucesu ita da 'yan unguwa masu karb'an gaisuwa Deeni yayi shigewarsa d'aki... Kallo ta bisa dashi kaman zatayi magana sai kuma ta hangi Affan na d'an lek'o kai cikin gidan daga zaure....
A hankali ta mik'e ta isa bakin zauren nan ta iske harda Naseer tsaye a wajen su duka biyun sunyi jigum-jigum
"A'a Soja yaya kuke tsaye a nan lafia dai koh....?" Ta tambaya tana duban su Naseer d'in
Affan ne ya sami zarafin amsata da "Eh lafia Mama dama muna so mu gaisa da Deeni ne sannan muji yanda Al'amarin ya kasance....?"
D'an jim Mama Tani tayi kana tace "Anya kuwa ya kamata ku masa maganar yanzu, da dai ku gaishe san amma d'ago masa maganar yanzu akwai tashin hankali cikinta kunga yanzu aka komo daga biso...." Ta k'arashe cikin k'arfin hali, don daga jin muryar nata k'arfin hali kurum take....
Affan ya d'an jinjina kai kana yace "Haka ne Mama, ayi mana iso mu gaishesa..."
Jinjina kai tayi kana tace "Ku biyo ni...."
Affan ne ya sami zarafin amsata had'i da take mata baya, bai kula da Naseer da gaba d'aya hankalin sa baya wajen ba yayi nisa duniyar tunani sai jin hannun Affan yayi yana janyosa suka nufi cikin gidan...
Daga bakin k'ofa suka tsaya saida Mama Tani ta shiga tayi masa magana wanda basu jiyo ba kafin ta fito tanai masu iso....
Koda suka gaishesa tamkar bazai amsa su ba tamkar bazaice dasu komai ba sai kuma hawaye suka soma zarya a idanunsa sanda ya soma fad'in "Gaisuwa kuka zo mana ko kuwa zuwa kukayi ku dawo min da mahaifina....? Bana buk'atar gaisuwan ku, da lokacin da zaku b'ata a nan da sunan gaishe ni da zuwa kukayi kuka capke wad'ancan azzaluman wanda suka mayar da kisa da sab'on mahallicin su ba komai ba.... Nasan bazaku masu komai ba sabida mahaifiyar ka ce da kuma Yayan ka.... Sun kashe mahaifina sunji dad'i sunacan suna ci gaba da rayuwarsu sabida Allah ya basu arziki A DUNIYAR MU... Toh ku sani idan sun tsere ma hukuncin da ta kamacesu A DUNIYAR MU bazasu tsere ma hukuncin mahaliccin mu ba ranar da gabb'ai zasu bada shaida....."
Duk maganan da yake Naseer ya kasa koda d'ago kansa sabida wani irin tashin hankali da yake ji na kuma taso masa.... K'irjinsa tanai masa zafi sosai.... Affan ne ya d'an d'ago da niyyan yima Deeni magana amma sai gani sukayi Deeni ya mik'e yana nuna masu k'ofa yake fad'in "Ku fita, ku fita kafin na fitar daku da k'arfi.... Ku dukanku aikin tsaron k'asa da kare lafiyar Al'umman cikinta kuke, na tabbata kunsan hukuncin da ya kamace su... Idan baku hukunta su ba k'aryar kakin da kuke sakawa kuke... K'aryar ikirarin Soji kuke.... Ku fice mana a gida... Ku rik'e gaisuwar ku don batada amfani a wajen mu....." Yana ida fad'in haka ya d'aga masu labule sosai alamun su fice sai faman tururi da huci yake ga idanunsa da suka kad'a sukayi jazir....
Gaba d'aya jikin Naseer yayi wani irin sanyi, jinsa yake tamkar wani lusari yau d'in, ganin Duniyar yake tamkar ba tasu ba... Kwanyarsa ta gaza d'aukan abubuwan... Bai tab'a tunani zai gamu da iftila'i makamancin wannan ba A DUNIYAR SA.... Affan ne ya kamo Naseer suka fice daga gidan suka fito har bakin lungun...
Naseer yaja ya tsaya ya kasa ci gaba da tafiya sai tunanin kalaman Deeni yake, sai yawo cikin kwanyar sa maganganun suke....
Affan bai ce masa komai ba sai d'an jingina da garun da shima yayi, lokaci guda tunanin mahaifiyarsa da Azeema ya shiga yawo cikin kwanyarsa, yasan mahaifiyar tasa mai laifi ce amma yana son sanin yanda take da kuma halin da suke ciki daga ita har Azeema...
Wasu matasa ne guda biyu suka zo wucewa suna labarin azabar dasu Aljan suke ganawa wani mutumi cikin uncompleted building dake k'asa kad'an da lungun....
"Baaba wllhi Aljan jan d'an iska ne ko kasan da na tambayesa sai ce min yayi shine mutumin da ya kashe Baban Zahraddeni... Tsohon mutumin nan da ya jima yana kwance yana jinya, shine kurum wani azzalumi ya k'arasa sa....waima da nace ma 'yan iska su mik'asa wa hukuma sai ce min sukayi ai sune hukuman su zasu mar hukunci...."
Abokin yayi dariya yana girgiza... Naseer da ya bisu da kallo yana nazarin kalaman saurayin saurin k'arasawa garesu yayi kana ya masu sallama... Suka amsa da sakin fuska kafin ya soma tambayar su gameda labarin da suke,
Samarin suka masu kwatance har yanda kongon ginin yake.... Naseer ya masu godiya kafin ya k'araso ya janyo Affan suka shige mota suka nufi hanyar da samarin suka kwatanta masu....
Su Naseer suna isa wajen su Aljan suka ahiga haye katanga da window suna guduwa...
Maina na zube a wajen numfashi ma da k'yar yake, hannayen sa da bakinsa a d'aure ga jikinsa duk jini ta ko ina.... Daga Affan har Naseer kallon ikon Allah suke ko Soja iyaka yayi irin wannan azaba wa d'an Adam shiyasa sam ba'ason fad'a da jahili don ko me ya samu rarumaka zaiyi...
Cikin sauri Affan ya k'arasa ya d'agosa had'i da kwance masa d'aurin bakin....
Naseer sabida tsaban takaicin Maina da yake ji gaba d'aya ji yayi tamkar ya shak'e sa ya k'arasa....
Maina sai nishi yake yana bud'e idanu da k'yar had'i da haki tamkar wanda yayi gudun kilometer d'ari... Ko iya masu magana baiyi ba..
Affan dake rik'e da Maina ya dubi Naseer dake faman huci da d'an madaidaicin hancinsa wanda bai faye tsawo da fad'i kana yace "Captain ina muka nufa..."
"Station of course...." Naseer ya fad'i yana k'arasawa jikin mota...
Ruwa-ruwa Affan ya jefa Maina a bayan mota uwa tsumma
*****
Gaba d'aya Jamila ta kasa sakewa a parlorn musamman dataga Fawaz da mahaifiyarsa a wajen, ga Lubna tak'i sakin Salma abin tausayi, kuka take babu k'akk'autawa har muryarta ya daina fitowa... Idan ta runtse idanunta Innah take hangowa da 'yan matan nan, haka idan ta toshe kunnuwanta sautin Innah da Maina ya kasa barin cikin kunnuwanta, da kunnenta take jiyo mahaifiyarta tana fad'in akar mutum, akan idanunta ta kalli mahaifiyarta da 'yanmata, kenan mad'igo mahaifiyarta takeyi... Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un.. Wacce irin rayuwa muka tsinci kawunanmu ciki A DUNIYAR MU...? ALLAH Sarki tun sautin kukan nata na fitowa har ya koma sai zallan hawaye idanunta masu zuban ruwa kuwa sama suke kallo tamkar maras lafiya....
Yanda kasan gidan makoki haka suke zaune a parlorn, babu mai furta koda kalma guda, kowa yayi jigum-jigum, harta Ilham da ba gani take ba tasan gidan cikin matsanancin tashin hankali suke maras fasaltuwa....
Fawaz dake rik'e da mahaifiyarsa a hankali ya d'ago idanunsa yana duban Jamila wacce Ilham ke rik'e da ita gam.... Lokaci guda Falaq ta soma kuka sosai Momy na faman jijjiga ta... Aunty Saudat ta d'ago idanu tana duban yarinyar tausayinta ya cikata... Ta k'arasa ga Momy tana k'ok'arin karb'an Falaq d'in yarinyar tak'i karb'anta sai kuka take...
Ga mamakin su sai ganin Fawaz sukayi ya k'araso yana k'ok'arin amsar yarinyar.. Lokaci guda ta amshi Fawaz ta daina kuka... Gaban Jamila yaci gaba da bugu, wani sabon soyayyar Fawaz yana taso mata ganinsa da tayi rungume da Falaq, shid'inma ita yake duba saidai Aunty Saudat ta kula da yanayin Fawaz da Jamilar, murmushi ta sakar ma d'an nata kafin ta kamo hannunsa tana fad'in yazo suje....
Babu musu ya shiga bin bayanta yana rungume da Falaq d'in tamkar rak'umi da akala....
Suna ficewa Jamila ta runtse idanunta hawaye masu d'umi suka gangaro mata.... Ta ina zata soma rayuwa gida guda da Fawaz, dole ta rok'i Momy su koma base don Allah ya gani bazata iya zaman wannan gida ba... Yanzu haka zuciyarta tsananin zafi yake mata, matsanancin ciwon k'irji take fama dashi saidai bata sanar da kowa cikinsu ba....
******
A tare Affan da Naseer suka shigo cikin cell d'in da aka gark'ame Maina bayan an kira wani jami'in lafiya ya duba tsananin raunin dasu Aljan suka masa don tuni har kunnensa guda sun yanke ga yankan wuk'a a jikinsa waje daban-daban, idan kaga Maina idanba ka masa farin sani bane da k'yar ka ganesa don tuni sun canza masa halitta lokaci guda....
Hannayen Naseer a kunkumi yake k'arewa Maina kallo kafin yace "Ina jinka zakayi magana ko sai na k'arasa ka gaba d'aya......"
Maina ya d'ago yana numfashi da k'yar kana yace "Rankashidad'e ai ni babu abinda zance maka sai godiya da ka kub'utoni hannun marassa imanin nan, nasan da baku zo ba da tuni na jima a barzah....."
Bai kai aya ba Affan ya d'aukesa da wata jahilar mari kana yace "Kai waye sa'anka a nan, tambayarka abu muke ba labarai muka ce ka bamu ba.... Ina bosses d'inka, ina suka shiga.. ?"
Maina da tuni ya saki ihun azaba rik'e fuskar sa yayi yana muzurai kana yace "Rankashidad'e wllhi ban sani ba ban sani ba, idan na fad'a maku kasheni zasuy....."
Bai kuma kai aya ba Affan ya kuma kifa masa wata jahilar Marin wanda saida ya sanyasa canza position d'in zama...
Ya soma k'ok'arin warware belt d'in wandonsa yana k'ok'arin ciro bindiga gefen wandonsa yake fad'in "Ba'a mana wargi idan kun saba yima 'yansanda suda kuka raina......"
Ai Maina bai bari ya k'arashi zuge belt d'in ba ya soma fad'in "Allah taimake ka wllhi zan fad'i.... Suna can suna can gidan holewar Innah, gidan da take kai 'yan matan ta da take hutawa dasu... Can wuntindada eh wllhi can suke... Dan Allah ku min rai kar ku kasheni wllhi duk wani bak'in aikin da nayi su suka sakani....." Yanda yake maganar zaka fahimci a gigice yake...
Daga Naseer har Affan cak suka tsaya suna sauraren ikon Allah..... "Gidan holewarta da 'yan mata..." Abinda Naseer ya nanata kenan a fili... Zuciyarsa taci gaba da bugawa... Anya Innah ba burbud'in maguzawan fari bane... Anya Innah 'yar Adam ce, anya wannan mata itace mahaifiyarsa.....? Sunbatun da zuciyarsa ta dinga jero masa kenan... Ji yake k'afafunsa suna neman gaza d'aukansa... Wai meke faruwa ne a duniyar su.... Gaba d'aya ya kuma shigewa cikin wani tashin hankalin lokaci guda, zafin da k'irjinsa ke masa ya k'aru... Affan ya lura da rawar da k'afafun Naseer keyi cikin sauri ya tallafesa ya zaunar sa saman benci....
Magana Affan yake masa na kwantar da hankali amma ko kalma guda bazai iya cewa ga abinda ya fahimta a sunbatun da Affan d'in ke masa, don yafi danganta maganganun nasa da sunbatu.... So yake koda kuka ne yayi amma ya kasa... Ya nemi yanda akeyin kuka ya rasa.. Innah Innarsa ce duk mai aikata irin wad'annan k'azaman manyan laifuka, itace kisan kai itace mad'igo, toh ma anya musulma ce.... Zuciyarsa yaci gaba da bugawa sai duru-duru da yake gani..
Affan ya dubi Maina yanaso ya basa exact location na gidan saidai ga dukkan alamu Maina baisan me yakeyi ba... Don gaba d'aya bashi a hayyacinsa banda fad'in _Sun karsu Sun karsu_ Baya komai....
Cikin sauri Affan ya fice yana kiran wasu 'yansanda, DPO ya k'araso suna tattauna lamarin da Affan..... DPO Ayuba ya had'a mota guda na 'yansanda suka nufi unguwar da gidan Innah yake... Shi kuwa Affan dole ya d'auki Naseer da niyan maidasa gida don gaba d'aya bai gane kansa ba, saidai suna d'aukan hanyar gida Naseer yace dashi su bi bayan motar 'yansandan...
D'an kallonsa Affan yayi kana yace "Naseer ya kamata...." Bai kai aya ba Naseer ya daka masa tsawa da fad'in "Nace kabi bayansu...!!"
Affan ya bisa da kallo yanda yaga Naseer d'in har wani rawa jikinsa keyi... Cikin sauri ya karya kan motar yabi bayan motar 'yansandan.....
*****
Innah na haki take duban Kabeeru don d'an gudun da tayi gaba d'aya sai haki take abinka da mai busa sigari ji take huhunta tamkar zai fice daga k'irjinta....
"Mai kake shirya mana, ina muka nufa? Don na tabbata izuwa wannan lokaci an soma neman mu..." Ta k'arashe tana k'ok'arin tsugunawa a wajen....
"Mai kuwa na shirya banda barin gari, saidai kafin na bar gari sai na d'auko Kitty na taho da ita don bazan iya rayuwa babu ita ba......" Ya k'arashe yana haki shima sabida gudun da sukaci ba kad'an bane...
"Kitty...? Uwar waye kuma Kitty...?" Ta tambaya tana watso masa mugun kallo...
"Ba uwar kowa bace, Mace guda da nake k'auna kenan A DUNIYAR MU, kuma idan na d'aukota na tattaro duk wasu ajiyana guduwa zanyi daga ni sai ita.... Innah kema sai ki kama gabanki sabida na tabbata zunubanki sunfi nawa....."
0 comments:
Post a Comment