A hankali Salma ke k'ok'arin bud'e idanunta da suka mata nauyi ga tari da ta soma yi sabida shak'an hayak'in sigarin Innah da tayi....
Hazo-hazo ta soma gani tamkar mutum ne zaune gabanta har ta k'arashi bud'e idanun nata sosai... Fuskar Innah ya bayyana cikin idanunta.... Ta yunk'ura zata tashi sabida tsananin figici da tsoro amma saijinta tayi a d'aure gam-gam.... Abunda ya faru ya shiga dawowa kwanyarta.... Jikinta ya shiga rawa sosai ba tareda ta iya koda ihu ba....
Murmushi Innah ta sakar mata tana kuma zuk'an sogarinta dake tsakankanin yatsunta kana tace "Barka da zuwa sirkata, matar d'ana abin alfahari na...."
Salma kasa furta komai tayi jikinta bai daina karkarwa ba... D'aga kan da zatayi ta hango Alh Kabeer da kaya irinta laboratorians sai had'a wasu abubuwa yake cikin sirinji wanda yafi kama da acid.... Ba tareda ya juyowa ba yake fad'in "I'm glad you're finally awake Mrs Naseer Sa'oud Santana...." Ya k'arashe yana wata irin kafiran dariya dai-dai sanda ya saita sirinjin dake hannun sa....
Banda kallon kallo babu abinda Salma ke binsu dashi ga k'irjinta dake bugu kaman zai fito waje...
"Ina ne nan, a ina nake... Dan Allah ku maidani gida, na rok'e ku dan Allah kada ku cutar dani...." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya...
Tsawa Innah ta daka mata kafin taci gaba da fad'in "Kabarinki ne nan... Idan kuma kinga kin fita da rai toh Naseer ya fanshi rayuwarki ne ta hanyar kashe kansa...." Ta k'arashe tana kuma zuk'an sigari had'i dayin wata irin dariya mai tsananin sauti...
Kuka Salma take tana girgiza kai kana ta soma fad'in "Dan Allah Innah ki tausaya mana kar ki cutar damu, dan Allah kada kice Soja ya kashe kansa... Wllhi dai-dai da rana guda bai tab'a tunanin sab'a maki a matsayinki na mahaifiyar sa ba...."
Kabeer ne ya katseta da fad'in "K'anwarmu ki kwantar da hankalin ki zaki fita daga wajen nan a raye muddin Addarki ta amince dani ta yarda zata bini duk yanda na nufa A DUNIYAR MU.... kin fahimta...?" Ya k'arashe maganar yana d'ago zungureriyar allurar wanda tafi kama da irin alluran da ake ma dabbobi dabbobin ma irin su doki da danginsu....
Jikin Salma yaci gaba da k'yarma ganin wannan zungureriyar allura da tayi ga kuma wani shud'in ruwa cikinta wanda ba sai ance maka poison bane.... Shi kansa hannayensa rufe cikin gloves ya had'a ruwan....
"Dan Allah... Dan Allah kuyi hak'uri kar ku cutar da Addah da Soja... Na rok'i arzikin ku.." Batakai aya ba Innah ta d'auketa da mari da bayan hannunta wanda saida yasa fuskar Salma kifawa, ta saki k'ara a gigice...
Cikin sauri Innah ta kuma kamo fuskar Salmar had'i da matse hab'arta da kakkausan hannunta wanda yake k'ashi da fata ne zalla, cikin hura hanci da zare idanu take fad'in "Idan d'iyata Lubna ta amince ta dawo gareni sannan tsinannen yaron nan Naseer ya kashe kansa da hannayensa toh na tabbata maki zan k'yaleki da ranki... Na kashe rayuka da dama don cimma burina na d'aukar fansa akan jinin Hidaya.... Wllhi wllhi kaman yanda mahaifiyarsa tayi sanadiyar mutuwan tawa mahaifiyar toh shima sai ya bak'unci lahira..... Kabeer saita min computern nan ka kira layin Naseer ka hasko ma tsinanne matarsa a hannunmu na tabbata ganinta haka zaisa ya kar kansa, sannan Lubna zata zo gareni... Abinda nake buk'ata kenan kurum A DUNIYAR MU..."
Izuwa lokacin kam ba wahalan da take ciki bane ke damunta, a'a kalaman Innah ne wanda suka matuk'an girgiza mata zuciya ya shiga bugawa a kwanyarta, tsoro da firgici ya kuma wanzuwa a tattere da ita.... Hasashenta na cewa Soja ba jinin Innah bane yana nema zama gaskiya.... Ta nemi kukan da take ta rasa... Sai wani mugun kallo kurum da ta shiga bin Innah dashi dukda azaban rik'on da Innar ta mata....
****
Gaba d'aya sunyi tsuru-tsuru a parlorn gidan, kowa hankali tashe sun hallara waje guda....
Naseer na tsaye ta d'an gefe yana amsa wayar DPO yayinda Jamila da Ilham aka rasa mai lallashin wani cikin su... Banda masifa cikin waya Naseer baya komai, gaba d'aya ya susuce ya fice a giya... Don sanda ya shiga d'akinsa yaga burbud'in hodar da suka shek'awa Salma a hanci, da alama shi ya bugar da ita har suka samu suka sace ta, ba kowa yake tunanin zaiyi wannan aiki ba sai Yayansa Kabeer...
Huci kurum Naseer keyi ga idanunsa da sukayi jazir lokaci guda ya nufi k'ofa yana fad'in "I swear I won't let you get away with it this time around.... I'm gonna kill you...."
Ai a d'ari Fawaz ya k'arasa yana k'ok'arin rik'osa yake fad'in "Uncle pls calm down, muyi abin nan a tsanake, yanzu idan ka fita ina ka nufa, bamu san waya d'auketa ba sannan ka kira barikin....." Tsawan da ya darara wa Fawaz ne ya sanyasa had'iye zancen sa...
Naseer na wani irin huci yake fad'in "You're insane Fawaz, matar nawa bansan yanda take ba Kake tunanin na zauna cikin gida tamkar mace... Idan ban fita na kashe duk wanda ya saceta ba..... Bazan tab'a yafe ma kaina ba sannan bazan kuma saka kaki na ba... Get the hell out of my way...." Ya k'areshi yana k'ok'arin hankad'e Fawaz lokaci guda wayarsa ta shiga ruri....
Video call yaga anai masa da wata layin da bai sani ba.... Hannunsa har na rawa sabida tsananin b'acin rai da yake ciki ya d'aga wayar....
Fusakan Yayansa Kabeer ne yayi arangama dashi cikin video d'in yana murmushinsa na k'eta da ya saba kafin yace "Hello bro... It's nice to see you again... Ya kake ya kewar matarka... Don't tell me a cikin awanni k'alilan da baka ganta ba har hankalin ka ya tashi... Oh come on Soldier don't be a coward...."
Gaba d'aya parlorn tsit tayi suna sauraren Alh Kabeer daga cikin wayar...
Naseer dake faman huci da tururi murya a dake ya soma fad'in "Yaya don't do this, ka dawo da Salma, idan akan Santana Corporation I promise I'll give you back... Zan mayar maka da Kampanin, but please don't hurt her.... I swear if you dare touch her I won't think twice , I'll kill you my self...."
Dariyan da Alh Kabeer ya fashe dashi ne ya katse Naseer.... Sasai yake dariya kafin yace " You know you're so delusional Naseer, you're an idiot, baka fahimtar komai..... Da ace kana fahimta da tuntuni ka fahimci waye kai, amma baka fahimta ba... You don't even know who you are.... Baka sani ba... All you know shine taimakon mutane jin tausayi da jin k'ansu...."
Cikin sauri Naseer ya katse sa da fad'in "Tell me where the hell are you....?"
Bai bashi amsa ba sai hasko masa fuskar Salma da yayi Innah sai faman jan sumar kanta take da k'arfin gaske, ga bakinta a d'aure babu halin ihu... Sai tamke idanuwanta take alamun tana jin jiki.... Innah kuwa tamkar ta samu kazan da ba'a tsoma cikin ruwan zafi ba haka take cisge suman Salma da iya k'arfinta....
Jiri ne ya soma k'ok'arin kada Naseer lokaci guda Fawaz ya amshi wayar yana gani, cikin sauri ya tallafi Naseer dake k'ok'arin kifawa....
Hawaye ne suke k'ok'arin fitowa daga idanun Fawaz lokaci guda Aunty Saudat da Jamila suka k'araso suna kallon video d'in... Wani k'ara Jamila ta saki had'i da zubewa k'asa tana kuka sosai.... Jin kukan nata ya sanya Ilham da ba ganin komai take ba fashewa da wani sabon kuka fad'i take. "Addah mai ya sami Salma, mai ya sami 'yar uwata, Addah kice min babu abinda ya sami 'yar uwata... Meyasa duk kuka min shiru ku min magana.. Ina Salma....?" Duk wannan sumbatu da Ilham keyi babu wanda ya sami zarafin amsata...
Lokaci guda Kabeer ya daina hasko su Innah da Salma, ya dawo da fuskar video d'in kansa kana yaci gaba da fad'in "Well I'm quite sure ku duka yanzu kunsan halin da take ciki....."
"Dad you're not human... Wllhi kaida Innah ba 'yan Adam bane.... Wai dan Allah su waye ku... Su waye ne ku....?" Fawaz ya k'arashe hawaye sosai na zarya a kumatun sa....
Murya d'add'aya Naseer yake fad'in "Yaya mai kuke so... What do you want from me... Wllhi zan baku just tell me mai kuke nema daga wajena...."
Fuskar Innah ne ya bayyana jikin screen d'in yanda ta soma fad'in "Rayuwarka kawai nake buk'ata Naseer... Ka kashe kanka da hannayen ka zan sake maka matarka, sannan d'iyata Lubna ta dawo gareni....."
Lubna dake kwance jikin Momy kuka kawai take don gaba d'aya ji take wannan duniyar tai mata d'aci sosai... Ko motsa jikinta bata iyayi balle tayi tunanin tashi.... Wannan wane irin tashin hankali ne wanda ko a labarai basu tab'a saurara ba...
Baisan k'iyayyar da Innah take masa yakai haka ba... Ashe tuntuni rayuwarsa take farauta..... Hawaye suka shiga zarya a fuskar sa... Cikin wani irin murya yake fad'in "Idan na kashe kaina zaku saketa....?"
Innah ta murmusa kana tace "Har sai ka tambaya..."
Cikin sauri Alh Kabeer ya hankad'e Innah kafin ya soma fad'in "Kitty nasan kina jiyoni... Idan kika amince dani zan sake k'anwarki... Sannan Naseer ka kashe kanka kaman yanda Innah ta bid'a..... And don't be stupid kayi tunanin tracking d'inmu don kayi finding location d'in da muke.... I know you such a fool zakayi tunanin yin haka... Toh kar ka b'ata wa kanka lokaci, the moment muka gama wannan wayar zan karya sim d'in sannan zamu canza location... Nasan abinda nake yi, ni ba sakarai bane kaman kai....."
Cikin sauri Jamila ta k'araso ta finciki wayar daga hannun Fawaz, tana kuka sosai take fad'in "I'll go with you... Zan bika, zan tafi da kai, but please kar ka cutar da 'yar uwata, dan Allah ku k'yaleta wllhi na yarda na amince zan bika koma ina ne...." Kuka ya hana Jamila ci gaba da magana....
Lubna ce ta k'araso da sauri tana kallonsu ta cikin screen d'in take fad'in "Innah pls, dan Allah ku k'yale Salma, na yarda zan biki amma kar ku cutar da Ya Naseer da Salma... Don Allah....." Itama kuka yaci k'arfinta..
Dariya Alh Kabeer ya fashe dashi kafin yace "Kunma raina mana hankali.... Naseer is your turn, kai kuma fah zaka cikita condition d'in namu ko kuwa ka zab'i a kashe Salma farin cikin rayuwar ka....." Ya k'arashe maganar yana d'ago sirinjin yana mai ci gaba da fad'in "Ta mutu har abada idan na mata wannan alluran..... Kai naman jikinta gaba d'aya diddigewa zaiyi kaga kuwa ba mutuwar dad'i zatayi ba.... Zaka kashe kanka ko kuwa ka zab'i na hudata da alluran nan...."
"You'll regret this moment...!!" Ya fad'i a hankali kafin yasa hannu a gefen wandonsa ya ciro bindiga wanda ya sanya illahirin mutanen dake wajen kuma firgita....
Lokaci guda Naseer yayi pointing bindigar a gefen kansa dai-dai nan suka sunce wa Salma d'aurin bakinta suna nuna mata Naseer dake rik'e da bindiga ya saita a dai-dai kansa....
Kuka Salma take sosai tana girgiza masa kai take fad'in "Soja don't, dan Allah ka bari su kasheni na tabbata bazasu dawwama suna zalunci A DUNIYAR MU ba, na tabbata watarana zasu tsinci kawunansu cikin k'ask'anci da wulak'anta.... Ko bayan raina Soja ka sani ina k'aunar ka, Salma tana sonka da duka zuciyarta.... Ko bamu kasance tare A DUNIYAR MU ba, zamu kasance tare a lahirar mu da yardar Allah... Soja kar ka kashe kanka ka yak'i wad'annan azzalumai biyu wanda suka jima suna zalunci.... Ka yak'e su na tabbata kaine a samansu......" Ta k'arashe tana kuka sosai....
Bai san sanda ya durk'usa saman gwiwoyin sa ba bindigar tana saitin kansa, kuka sosai yake wanda bai tab'a irinsa ba, cikin tsananin kuka yake fad'in "Reina mai amfanin ci gaba da rayuwa A DUNIYAR MU inaji ina gani su cutar dake..... Wannan shine abinda suka jima suna so..... Babu mai tabbata idan na tafi suma zasu tafi...." Naseer ya k'arashe yana kuma saita bindigar, fatar jikinsa gaba d'aya ta sauya launi zuwa jazir....
Aunty Saudat kuka take sosai tana girgiza kai ma Naseer...... Lokaci guda Fawaz yayi ta maza ya fuzge bindigar... Kan kace me ya saita bindigar akansa..... Fad'i yake "Let her go Dad... Or I'll shoot my self,..." Ya fad'i yana tsananin huci bindigar na saitin kansa banda tururi babu abinda yake...
Naseer a zuciye ya mik'e yana duban Fawaz cikeda mamaki kafin ya soma girgiza kai yana fad'in "Fawaz what are you doing.... Don't Fawaz bani bindigar nan.... Ka bani nace...!!" Ya k'arashe cikin tsananin daka tsawa
Fawaz na huci bindigar na manne da Kansa yake fad'in "No Uncle.... Wllhi bazan baka ba... And the moment ka k'araso nan zan harbata.... Just stay there....." Ya dawo da dubansa ga Innah da Kabeer wanda tashin hankali ya nuna k'arara a fuskokin su kana yaci gaba da fad'in "Dad ko ku sakota ko na harbe kaina....." Cikin tsananin huci yayi maganar...
Lubna da Jamila tuni sun wuce sun bud'e wa Detectives biyu k'ofar baya cikin sand'a don tuni suka silale suka soma iyaka nasu k'ok'arin tunda aka soma buga wannan dabi, fad'a daga nesa sai Allah, badai k'arfin mutum ba don komai ka iya faruwa...
Detectives d'in a sad'ad'e suka shigo kafin suka ciro k'ramar comfutar su, suka warwareta cikin k'ank'anin lokaci sukayi connecting da wayar dasu Naseer keyi, ko wannensu headphones manne a kunnen sa sai faman danna computer d'in suke.... Kan kace me abinka da technology har sun gano location d'in su Innah...
Detective d'aya yayi alama ma Fawaz kan yaci gaba da jan su Innah har agents d'insu su samu su isa location d'in.....
Naseer juyawa yayi yana duban Lubna da Jamila kafin ya masu alama na jinjina da babban yatsar sa k'asa-k'asa.....
Wata kafiran murmushi Kabeer yayi kana yace "Fawaz I wasn't born yesterday, wllhi nasan bazaka kashe kanka ba....." Ya dubi Naseer still yana murmushi kana yace "I know this one of your tricks.... Salma zata ci gaba da zama a nan tunda gaba d'ayanku kunsa abinda aka umarce ku...." D'if suna ganin hannunsa ya kashe kiran.....
"Don't Dad.. Dad!!! " Fawaz ke fad'i amma ina tuni Kabeer ya kashe kiran...
Naseer kam a tamanin yayi wajen Detectives wanda suma cire headphones kunnuwan su sukayi kafin Naseer ya soma tambayar su... Cikin sauri suka mik'e gaba d'aya suna tattara kayansu suke amsa Naseer d'in kana suka ce sun gano location d'in zasuyi gaggawa su tafi yanzu...." Ai ko rufe baki basu ida ba Naseer yayi waje a d'ari.... Fawaz ya tako masa baya...
Dafa Fawaz Naseer yayi yana k'ok'arin shiga mota yake fad'in "You stay here Fawaz, ka kula da abubuwa a nan sannan banaso rayuwar wani ya kuma shiga had'ari a dalilina.... Ka kuladasu a nan kaji...." Ya k'arashe yana bubbuga kafad'un Fawaz... Bai jira cewar Fawaz d'in ba ya shige mota.... A d'ari suka fice Naseer da 'yansandan waya manne kunnuwar su...
Suna ficewa motar Sojoji daga Base d'insu suka iso gidan domin tsaida doka, tuni sun kewaye gidan suka shiga bata tsaro.....
Fitar su Naseer da kad'an Deeni da Mama Tani had'i da wata mata wanda sun d'anso suyi kamanni da Deeni sukayi sallama a parlorn gidan.....
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*57*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
K'erere Innah ke dubansa kafin tace "Kabeer ni zaka ma rashin mutunci ni zaka juyama baya.... ashe kanada wacce ta fini A DUNIYAR MU..?"
Da mamaki yake dubanta kafin ya fashe da wata irin dariya sai kuma ya shafi hab'arsa yace "So kike na maimaita maki... Amfaninki guda d'aya tak da kikayi sanadiyan zuwata duniyar.... Sannan amfaninki ya k'are a wajena tunda ta tashi mana, jinki na bari kika rab'eni yanzu ban janyo ma kaina tashin hankali bane... Ai billahillazi kinji na rantse raba hanya zamuyi....."
Bai kai aya ba Innah ta darara masa tsawa tana wani irin huci take fad'in "Kai ka kiyayeni... Wllhi nida ka gannin nan Kwangiri ce tarkon jirki, Kutuwar Uwa a zauna dake dole.... Duk yanda zakaje bakada wata nasara idan babu ni...."
Dariya ya shek'e dashi harda bubbuga k'afa kana ya d'an dai-daita kansa yace "Ni kuma Murucin kan dutse ban fito ba saida na shirya... Aini kin badani tunda kika gudu ma Naseer, yaron da tuntuni ya kamata ki gama dashi amma kika kasa.... Banida lokacin ki ina d'auko Kitty wllhi wllhi zanbar garin nan koma mu bar k'asar baki d'aya....."
Shaye da mugun mamaki Innah ke dubansa bata kuma furta koda kalma guda ba sai k'arasawa wata k'ark'ashin bishiya da tayi ta zauna sabida sam batajin dad'in jikinta tunda tayi gudun nan....
****
Basu tarar da kowa a gidan ba sai motar Kabeer dake pake a waje saiko zanin Innah da tayi wurgi dashi.... Duk wani binkicen da zasuyi sunyi ya kuma tabbatar masu Innah da Kabeer guduwa sukayi, dole aka baro wasu 'yansanda a gidan sabida tabbatar da tsaro...
Naseer da Affan basu koma gida ba kai tsaye station d'in suma suka wuce, suna planning ta yanda zasu soma nemo su Innah don tuni sunyi filing case....
*****
Tana nan tsaye jikin window tana lek'en dawowarsa gaba d'aya barci baiga idanunta ba, ta kuma duban agogon bango dake manne a parlorn ya nuna k'arfe shad'aya na dare da wasu dak'ik'ai ... A hankali ta sauk'e ajiyan zuciya tausayin kawunansu na kuma cika mata zuciya... Har ta hak'ura da jiran nasa ta sadakar bazai dawo ba sai kuma taji k'aran bud'e gate... Cikin sauri ta kuma dawowa jikin window d'in had'i da yaye tapkeken labulen turkey da ya mamaye window d'in tana lek'e
Affan da Naseer d'in ne suka shigo Affan ke driving yayinda Naseer ke mazaunin mai zaman banza, Da alama Fawaz ma dawowar su yake jira, don suna isowa ta hangi fitowar sa shima...
Tsayuwa sukayi su duka ukun suna tattauna lamarin wanda kunnuwanta sam basujiyo mata ba.... Sun d'an jima a wajen kafin ta hangi Affan ya masu sallama ya fice yayinda Naseer da Fawaz suka nufi sashen Naseer d'in su duka biyu... Tana son sanin halin da yake ciki, tana son kasancewa taredashi don tasan yana buk'atar mai d'ebe masa kewa cikin d'inbin damuwan da yake fama dashi... Tausayinsa gaba d'aya ya cika mata zuciya... K'arasawa tayi ta zauna saman coffee chair dake daga can k'arshen parlon ta d'an yaye labulen sosai yanda zata iya hango fitowar Fawaz daga sashen Naseer d'in....
Har gyangyad'i ya d'an soma sand'anta can ta hangi Fawaz ya fito ya nufi nasa sashen.... A hankali ta mik'e tana kuma gyara zaman hijab d'inta kafin ta fito ta nufi sashen Naseer d'in...
Tana isowa ta tarar k'ofan parlorn a bud'e take don tana d'an turawa ta bud'e gaba d'aya...
Yana nan zaune a parlorn ya rik'e kansa da duka hannayen sa biyu.... Bata tab'a ganinsa cikin yanayin ba gaba d'aya sai taji idanunta suna k'ok'arin rau-rau...
K'amshin da ya doki hancinsa ne ya sanyasa d'ago fuskar sa.... K'uri ya mata yana kallonta yanda taja ta tsaya daga bakin k'ofa... K'ak'aro murmushi yayi ya sakar mata lokaci guda ta soma takowa ta nufosa.... Saidai tana isowa yanda yake ya mik'e ya rungumeta sosai cikin jikinsa....
Gaba d'aya tausayin Soja ya cikata jin kalan bugun da k'irjinsa keyi.... Duk sai jikinta yayi sanyi sosai...
A hankali yake fad'in "I want to cry... Salma ina so nayi kuka ko pain d'in dake k'irjina zai ragu.... Please tell me this is not happening.... Dan Allah kice min mafarki nake ba Innah ta bace.... Salma na kasa yarda Innah tana duka wad'annan k'azaman laifuka.... Dan Allah kice min mafarki nake....." Ya k'arashe siririyar hawaye tana gangaro masa daga idanunsa guda....
A hankali Salma ta masu mazauni saman Sofa don tuni Naseer ya jirge mata nauyinsa gaba d'aya....
Bai saketa ba sai k'ank'ameta da ya kuma yi k'irjinsa naci gaba da bugu cikin sauri.....
"Soja kayi hak'uri wannan ba komai bace face jarabawa daga mahallacin mu.... Insha Allah komai zai wuce ya zama tarihi... Kayi hak'uri kaji...."
Kallonta yake yanda take maganar cikin rawar murya kafin ya kamo hannayenta ya matse su sosai cikin nasa idanunsa na duban fuskarta yake fad'in "Salma meyasa zasu gudu.... Inada tambayoyi da dama da zan masu..... Salma ko finafinai ban tab'a karo da makamancin wannan lamari ba sai kuma ace gashi a gidanmu yana faruwa akaina... Idan nace maki kwanyata tana dab da tarwatsewa ban maki k'arya ba....." Ya k'arashe murya na rawa tamkar ba Sojan data sani ba gaba d'aya sai ta nemi kalma guda a bakinta ta rasa, don tasan muddin tace zatayi magana toh fah kuka kawai zatayi....
Yana nan mak'ale cikin jikinta ya kasa barinta ta tashi balle ta nemo masa abin tab'awa don tasan babu komai a system d'insa... K'arshe data damesa zata tashi saima kwanciya bisa laps d'inta da yayi had'i da lumshe idanunsa...
******
Washe gari tuni Fawaz yasa anyi manyan hotunan Innah da mahaifinsa an rubuta WANTED k'asar hotunan da manyan harrufa...
Naseer kam kasa cewa komai yayi da ya gani, banda abin Fawaz wannan ai bankad'an asiri ne da tonon silili wa Santana Family.... Saidai Fawaz d'in ko ajikinsa idan da wad'anda yafi tsana A DUNIYARSA toh wad'annan bayi biyu ne... Bashida burin da ya wuce a rapke su su soma d'and'ana kud'ansu...
****
A hankali ta soma bud'e idanunta abubuwan da suka faru suka shiga dawowa kwanyarta.... Zabura tayi zata tashi saiji tayi an rik'e hannunta anai mata sannu da harshen fillanci.... Mamy ta ware idanunta sosai nan ta fahimci yanda take, d'an bukka ne sai kuma gadon azara da take bisa...
Takai dubanta ga macen data rik'e hannunta wacce ke faman mata sannu cikin harshen hausa wannan karan dukda hausar gwari-gwari ce bata fita sosai....
Mamy ta soma karanto salati tana tambayar a yanda take....
Matar kuwa tuni ta mik'e tana kwand'arwa mijinta kira tana fad'in matar ta tashi
Dattijon ya shigo hannunsa d'auke da wata k'ok'o wanda ko ba'a ce maka ba ruwan addu'a ne cikinta nan ya shiga yayyafawa Mamy dake faman masu sunbatu sarara, lokaci guda kuwa tayi shiru ta daina sunbatun bayan Dattijon ya yayyafa mata ruwan...
Zama yayi daga can gefen matarsa su duka suna duban Mamy kafin Dattijon ya soma magana cikin harshen hausa wanda shima nashin ba fitowa sosai take ba...
"Sannunka bawan Allah.... Kar ka damu ka tsira da izinin Allah... Fad'a mani me ya kawo ki gonata....?"
Ya k'arashe yana duban Mamy wanda banda kuka babu abinda take....
Kallonsu take su duka biyu kana tace "Bayin Allah don Allah ina ne nan, a ina nake....?"
Dattijo da matarsa suka dubi juna kana sukace "K'auyen Durun kake baiwar Allah..." Matar taci gaba da fad'in "Mai gidana ne ya tsince ka a gonar sa.. Kai kuwa waye ya satoka don ga dukkan alamu mugaye suka sace ka koh..." Ta k'arashe tanayi wa Mamy k'uri tamkar zata shige cikinta...
Mamy ta shiga matsawa da baya don ita gaba d'aya tsoron mutanen duniya take yanzu....
Murmushi matar tayi kana tace "Kar kaji tsoro kaji koh.... Babu abinda zamu maka, ka tsira da yardar Allah...."
Mamy ta shiga jinjina kai cikin sauri, kafin ta dubi mutanen tace "Dan Allah ku taimaka min na k'arasa cikin Bauchi wllhi satoni akayi..." Ta k'arashe muryarta na rawa sosai....
Matar ta d'an dubi Mamy kana tace "Jiya baka a hankalinka da maigidana ya kawoki nan, sanda na baka abinci haka kayita turawa bama kasan kanayi ba... Da alama yanzu hankalinka ya dawo.... Toh garin yaya aka sace ka....?" Bafulatanar ta kuma tambaya tana gyara zama, basai ance maka masu son jin labarai bane....
Mamy bata amsata ba sai mik'ewa da tayi sosai sai kuma taji d'akin ya kasa ma tsawonta cikin sauri ta nufo waje tana fad'in "Gida nake son tafiya, dan Allah ku maidani gida...."
Gaba d'aya mata da mijin suka mik'e suka biyo Mamy waje...
Ganin sun tare gabanta su duka biyu ya sanya cikin Mamy bada wani sauti.... A razane take fad'in "Bayin Allah don Allah kada ku cutar dani... Wllhi ukuban da na shiga ciki ma kawai ya isheni ishara A DUNIYAR MU, dan Allah ku k'yaleni haka nan kada ku cutar dani...."
Dattijon ya murmusa kafin yace "Karfa ka damu ba cutar dakai zamuyi ba, so muke ka bamu labarinka...."
Mamy kam tuno Azeema da tayi ya sanayata zubewa ta zauna dirshan a wajen hawaye bai daina fito mata ba sanda ta shiga kwararo masu bayani....
Dattijo ya dubeta cokeda tausayawa kana yace "Tabbas kinga iftila'i amma Allah na sonka da alkhairi sannan kuma kwanarka ne bai k'are ba shiyasa ka kub'uta... Maganar asirin mijin ki kuma kar ka damu zamuje har garin a warware sihirin da yardar Allah... Amma yanzu ni kiwo zanje, ga mai d'akina zata shiga cikin Bauchi tallan kindirmo idan yaso sai ku tafi tare taga gidan naka koh. ..." Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye, Mamy kam da anbi nata da tun yanzu an tafi an warware sammon Daddy, amma tunda wannan Dattijo yace zai taimaka mata taji dad'i sosai... Ko abinci bata iya ci ba, ita dai kurum su isa cikin garin Bauchi damuwarta.... Bafillatanar tana ida had'a kayan tallanta suka fito suka nufo bakin titi, Mamy sai faman raba idanu take... Wanda duk bai mata farin sani ba sam bazai ganeta ba....
*****
Tana tsaye d'akin Naseer tana tattara masa d'akin taji kaman motsin mutum.... D'an barin abinda takeyi tayi had'i da lek'a parlor taga babu kowa.... Lokaci guda ta dawo cikin d'akin taci gaba da abinda take...
Daga yanda yake lab'e wata kafiran murmushi yake.... Yasan yin haka ne kurum zaisa su rabu da Naseer for good sannan Kitty ta amince ta bisa cikin lallama....
Salma kam sam batasan da mutum cikin d'akin ba, kai tsaye ta shiga kintsa kaya cikin wardrobe, bada bayan da zatayi kuwa saiji tayi an toshe mata hanci da 'yar tsumma.... Ta shiga wutsil-wutsil tana k'ok'arin ihu.... Tana zare idanu nan sukayi ido hud'u dashi yana kafiran murmushin nan nasa.... Duk k'ok'arin k'watan kanta da take ta kasa... Kan kace me idanunta sun rufe ruf jikinta ya sake....
Cikin sauri ya sungumeta yana 'yan lek'e-lek'e yabi hanyar da yasan babu mai ganin sa ya fice a gidan abinka da wanda yasan gidan ciki da bai....
****
Shareefah tana k'unshe a d'aki tana kuka ga ciwo da ya addabeta sai jiyo k'aran bud'e gate tayi... Ta mik'e da k'yar tana lek'en window nan taga Daddy ne da Affan, an sallami Daddy Affan ya dawo dashi gida.....
Wasu sabbin hawaye suka shiga gangaro mata don duk gayu irinta Shareefah kunyar shiga mutane take sabida d'oyin da take....
Tana gani Affan ya bud'e bayan mota ya ciro wa Daddy wheelchair d'insa ya wareta ya dawo mazaunin Daddyn yana k'ok'arin taimaka masa.....
Dai-dai sanda Affan ya d'aura Daddy saman wheelchair d'insa suka ji k'aran bud'e k'aramar k'ofa... A tare suka juya suna duban masu shigowa...
Sun dai fahimci d'aya matar bafulatana ce mai tallan kindirmo saidai d'aya matar ce basu shaida ta ba.....
Mamy tamkar kazan da k'wai ya fashe mata a ciki haka take tafiya, Baba Mai gadi kansa bai shaida Mamy ba... Don har ya taso daga bancin sa yana k'ok'arin hanasu shiga sai jiyo muryar Affan yayi yana fad'in "K'yalesu Baba Daddy yana son kindirmo..."
Bafulatana dai sai kalle-kalle take tana kuma duban Mamy da kanta na kife a k'asa...
Saida suka iso sosai Affan ya soma k'ok'arin shaida Mamy, babu crutches d'in nata saidai cangwala k'afar da takeyi da k'yar...
A hankali ya saki wheelchair d'in Daddy yana k'ok'arin k'arasawa gareta... Tuni Daddy ma ya d'ago kai yana duban matar sosai... Shareefah dake mak'ale jikin window a hankali ta furta "Mamy....!!" Cikin wani irin sauri da gudu ta nufo waje hawaye na ambaliya a fuskarta...
K'arasowar da Mamy zatayi sai ta fashe da kuka sosai.....
Muryar kukanta da Alh Ali Safwan yaji sai yaji wani irin abu ya tokari k'irjinsa tamkar an sauk'e mar guduma....
"Asma'u..!!" Ya fad'i murya na rawa...
Tuni Mamy ta durk'ushe a wajen tana kuka sosai....
Affan duk k'arfin hali irin nasa saida yaji hawaye na zarya a fuskar sa, shin wannan Mamyn sa ce, cikin kwanaki uku ne ta koma wannan halitta.... Anya Mamy ce ba canzata akayi ba.... Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un... Abunda zuciyarsa ta shiga ambato masa kenan.....
"Asma'u mai ya dawo dake gidana... Kinzo ki k'arasani da k'arfi ne bayan mahallici na ya tayar dani.... Me kike nema wajena Asma'u? Mai kike nema A DUNIYAR MU...."
Kuka Mamy take tana k'ok'arin matsowa kusan Daddy tana kai hannayenta kusan k'afafunsa amma tuni ya soma jada kekensa baya hawaye suna fitowa daga idanunsa shar-shar.... Bazai tab'a mance auren soyayya da sukayi da Asma'u ba.... Amma sai gashi itace ke yunk'urin kashesa wannan Al'amari da mai yayi kama.... Sautin Mamy suka soma jiyowa cikin tsananin kuka take fad'in
"Daddy ka yafe ni, ka yafe ni dan Allah.. Wllhi na gane kuskurena A DUNIYAR MU, wllhi na fahimci Duniya ba komai bace face wani waje da za'ayi rayuwa k'alilan sannan bayi gaba d'aya su koma ga mahallicin su.... Wllhi na amince duk mai son Duniya yana tareda wahala... Daddy na tuba zan shuka Alkhairi A DUNIYAR MU domin dacewa a lahirar mu wacce itace rayuwa dawammamiya.... Daddy ka yafe min Affan ku yafe min, nasan na zalunce ku gaba d'aya, yafiyarku ne kawai zaisa na sami sassauci a rayuwata.... Na aikata munanan laifuka A DUNIYAR MU amma Ubangijina ya fahimtar dani haka tun kafin a isa lahira... Na tabbata azaba da uk'uban da nasha tun A DUNIYAR MU bai kai kwatankwacin wanda zan tarar a lahira ba da na tafi ina mai aikata sab'o da shirka.... Daddy ka yafe ni na rok'i arzikin ka, wllhi da k'afafuna zan tafi na warware sammon da nayi maka ka kasa tafiya, akaje k'asashe da dama aka gagara gane kan cutar.... Wllhi zanje in warware, nidai kawai buk'atata kace ka yafeni don Allah ba don ni ba....." Ta k'arashe tana mai kuma kifa kai a k'asa idanunta suna ci gaba da zuban ruwa...
K'irajensu yaci gaba da bugu... Alh Ali baisan Asma'u bata k'aunarsa har haka ba... Yanzu dama ita ta nakasa shi shekara da shekaru yana zaune saman keken guragu... Anya Asma'u 'yar adam ce... Shin har mace zata cutar da mijin da suka jima tare suka hayayyafa tare, suka gina gida guda tare, suka riga suka zamto abu guda... Idan zata iya haka ma irin wannan mutumi toh inaga sauran Al'umma, wani irin cutarwa zata masu... Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un, ashe ya jima yana zaune da mushirika azzaluma cikin gidansa bai sani ba.... Bai iya furta komai ba sai bugu da k'irjinsa keyi babu ko k'akk'autawa...
Shareefah zubewa tayi a wajen tana wani irin kukan da bata tab'a irinsa ba...
Affan kuwa jin abin yake tamkar wani a tarihi irin na zamanin jahiliya da babu addini ballantana sanin Allah... Yanzu wannan matar mahaifiyarsa ce... Duk laifukan nan ita ta aikatasu... Ya nemi kukan da yake ya rasa...
Bafulatana dai tsuguno gefe tayi irin yanda suke idan zasu zuba kimdirmo wa masu siya tana kallon ikon Allah kana ta shiga tafe hannaye tana sallalami da surutai cikin harshen fillanci...
A hankali Affan ya soma k'ok'arin janyo keken Daddy yana son shigar dashi gida ba tareda ya kuma duban Mamy ba...
Da gwiwa take k'ok'arin matsowa kusan su tana fad'in "Aff....!!"
Saurin katseta yayi da fad'in "Don't Mamy, don't you dare call my name, I don't know you... Ban sanki ba... Kuma ki fice mana a gida, bamu buk'atan 'yar Adam irinki a cikin gidan nan.... Wllhi wllhi kar ki kuskura kizo kusan mahaifina baya buk'atarki a rayuwarsa....." Yanda yake maganar zaka fahimci tsan-tsan tashin hankali a tattare dashi, hannayensa dake rik'e da wheelchair d'in Daddy har wani b'ari suke sabida tsananin b'acin rai da tashin hankali... Cikin sauri ya shiga tura Mahaifinsa wanda ya gagara koda raba fatun bakinsa guda biyu ballantana ya sami zarafin magana...
Mamy ta d'ora hannu aka tana kuka sosai, tuni d'an mayafin dake kanta ya sub'ule k'wandilan kanta ya bayyana... Gaban Shareefah ya kuma fad'uwa... K'afafunta na rawa ta doso mahaifiyar tata...
A hankali Shareefah ta durk'usa saman gwiwoyinta tana duban Mamy sosai, sai ta nemi ciwon da take ji ta rasa, tabbas halittar Mamy ya sauya daga Mamynta da ta sani a baya... K'afafun Mamy Shareefah ta soma k'ok'arin dubawa tana tunanin ta yanda zataga k'ofato a k'afafun Mamy... Kafin ta sami zarafin Magana Mamy ta rungumota sosai cikin jikinta tana kuka da duka zuciyarta... Azeema kawai take tunowa cikin zuciyarta da irin halin data barota ciki... Allah sarki Duniya abin tsoro tafi gabaruwa iya jima....
*****
Innah na zaune gefen kujeran da aka d'aure Salma ta shiga busa mata hayak'in sigari tana son tada ita... Aiko tuni Salma ta soma tari tana k'ok'arin bud'e idanu....
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*60*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Dukda shekaru da ya d'iba rabonsa da gidan ya gane gidan kuma ya yarda d'an tasi d'in gidan Sa'oud Santana ya kawo su, gidan yana nan da yanayinsa irinta masu kud'in wancan lokaci saidai wasu gyare-gyare na zamani da aka kuma k'awata sa dashi.... Hannun matar da suke tare ya rik'e suna masu ci gaba da tafiya
Tabbas dukda girma da ya nuna a fuskar mutumin zai iya tuna tamkar ya sansa a lokutan baya..... Bai daina kallon wad'annan bayin Allah ba har saida suka nufo gidansu gadan-gadan... Sojojin dake tsare da gate ne suke yunk'urin hanasu shiga gidan.... Har lokacin Naseer bai sami zarafin motsawa ba sai k'irjinsa dake bugu cikin sauri.... Salma kam sam batama lura da halin da Naseer d'in ke ciki ba.... A hankali yaci gaba da tuk'a motar har ya iso gate d'in nan da nan kuwa attention d'in Sojojin ya dawo ga ogansu.... A dai-dai lokacin Dattijon balaraben nan ya juyo yana duban Naseer... Duk da tsawon shekaru da ya kwashe bai ganshi ba tabbas zai iya shaidawa d'an 'yar uwarshi ce.... Tabbas wannan Naseer ne.... Shima Naseer d'in k'uri yayi wa mutumin yana hango fuskar Aunty Saudat a tattaredashi...
"Naseer....!!!" Mutumin ya fad'i ruwa na k'ok'arin cikowa idanunsa....
Bugun k'irjin Naseer ya k'aru a hankali ya bud'e marfin mota ya fito waje...
****
A dai-dai stairs sukayi kusan cin karo da Fawaz da alama gate ya nufa don ya hango gate d'in a bud'e sannan ya hangi mutane tsattsaye....
Gabanta ya kuma yankewa ya fad'i... A hankali Fawaz ya kauce mata had'i da kauda kansa gefe kafin ya shige cikin sauri.... Kallo ta bisa dashi lokaci guda taji zafin k'irjinta ya k'aru... Cikin sauri ta lumshe idanunta tana mai ci gaba da taka steps d'in da k'yar.... Saidai tana cikin k'ok'arin haurawa taji tari yana zuwa mata akai-akai.... Hannu tasa tana k'ok'arin k'unshe bakinta..... Saida ta d'an tsuguna a wajen kafin tarin ya lafa.... Saidai tana cire hannunta a bakinta taga jini cikin hannun nata.... Wani sabon tashin hankali ya ziyarce ta... Shafa bakinta ta kuma yi taga dai tabbas jini ke fita daga bakinta... Cikin sauri ta k'ara ga doguwar madubi da aka k'awata hanyar dashi tana kallon fuskarta cikin madubin.... Da gaske dai jini ne jini ke fitowa idan tayi tari... Cikin sauri ta soma girgiza kai sabbin hawaye suna kwararo mata.... Sallaman mutane da ta jiyo daga parlorn ya sanyata daina kukan da take... Dukda tasan duk yanda akayi Naseer ne ya dawo da Salma bata iya k'arasawa wajensu ba sai hayewa sama da tayi cikin sauri.... K'ofar d'akin Lubna ta soma shigewa yanda ta hangi Lubnar kwance saman cinyar Aunty Saudat tana shafa kanta alamun kwantar da hankali... Cikin sauri tasa kai ta shige.... A dai-dai k'ofar d'akin da Momy take ta hangesu gaba d'aya daga Momyn har Ilham da Falaq.... Momy na bisa darduman sallah yayinda Ilham ke kwance rigingine Falaq na bisa k'irjinta.... Wasu hawaye suka zubo wa Jamila.... Cikin sauri ta k'arasa nasu d'akin ta shige had'i da kullo k'ofar domin tasan bazata iya had'uwa da kowa a wannan yanayi da take ciki ba... Abubuwa sun taru sun mata yawa cikin zuciyarta, ga rashin Fawaz ga uwa uba cutan da Alh Kabeer yace ya shafa mata.... Can k'uryar d'aki ta samu ta zauna had'i da tak'urewa waje guda ta kifa kanta tana kuka maras sauti, shikenan k'ila farkon symptoms d'in HIV d'in kenan idan kayi tari jini ya fito.... Tunanin da zuciyarta ya dinga raya mata kenan wanda ya kuma tsundumata cikin wani sabon tashin hankali....
****
Gaba d'aya hallara sukayi a parlorn, Salma ta tafi ta rungume 'yar uwarta Ilham suna kuka sosai..... Fawaz kam idanunsa naga balaraben da suka shigo tareda Naseer wanda tunda ya d'aura idanu akansa ya kasa d'agawa ga k'irjinsa dake faman bugu.....
Shima wannan Dattijo duban Fawaz ya dingayi yana jin wani babban Al'amari a tattare dashi.... Idanunsa naga Fawaz har baisan sanda Aunty Saudat da Lubna suka sauk'o parlorn ba..... Momy ta k'arasa ta kamo hannun Lubna ta had'esu gaba d'aya dasu Salma ta rungume tana zaune tsakiyarsu don jikinta na bata wani abin ne zai kuma faruwa....
Hawaye ke gangaro mata tana takowa cikin parlorn, juyawar da zaiyi ya hangeta tana takowa cikin tapkeken parlorn..... Lokaci guda ya mik'e k'afafunsa na rawa ya soma takawa ya nufeta shima kukan yake..... Yana k'arasowa yanda take ya rungumeta ba tareda ya iya furta komai ba sai kuka da yakeyi tamkar k'aramin yaro.... Aunty Saudat kam cak ta tsaya ba tareda ta maida masa martanin rungumar ba.... Sai tunanin sanda ya barta a wannan same parlor yayi tafiyar sa shekaru ashirin da d'oriya da suka gabata, abubuwan suka yawo a kwanyarta, ta tuna tana binshi tana rik'oshi amma haka ya b'anb'areta daga jikinsa yasa k'afafu ya tafi ya barta wa mutanen da suka tassama halak'ata da k'arfin gaske..... Lokaci guda tamkar wacce aka zabura ta shiga k'ok'arin b'anb'are jikinta tana kuka sosai tana ture mutumin tana fad'in mai ya dawo dashi ya b'ace bata son ganin sa... Duk cikin harshen arab take maganganun... A d'ari Fawaz ya k'arasa yana k'ok'arin janye mahaifiyarsa daga rik'on mutumin yake fad'in "Malam lafiya... Wai waye kai....."
Kuka Aunty Saudat take sosai sanda Fawaz ya rungumeta sosai yana huci yana duban mutumin.... Naseer ne ya k'araso yana k'ok'arin janye mutumin a hankali.... Baiko iya bawa Fawaz dake tambayar ko wanene mutumin amsa ba.... sai jiyo muryar wannan mutumi sukayi cikeda tsananin mamaki hausa yake
"Saudat ki yafeni... Ki yafeni d'iyata wllhi tunda na tafi na barki a nan ban sami kwanciyar hankali ba, arzikin da na tafi dashi baimin amfani ba k'arshe na rasa komai na koma abin tausayi abin kwatance A DUNIYAR MU.... Ki yafe dan Allah.."
Sai sannan Fawaz da sauran jama'an wajen suka fahimce wanene wannan mutumi.... Idanuwan Fawaz suka shiga zubda hawaye, girgiza kai kurum yake yana duban mutumin da mahaifiyarsa..... Kafin ya sami zarafin magana ya jiyo muryar mahaifiyarsa cikin kuka tana fad'in "Abbu meyasa? Meyasa ka tafi ka barni..... Why..? Baka damu ba all the suffering I went through.... Sun baka kud'ad'e ka aurar dani ma d'ansu wanda suka tasamma kasheni shida mahaifiyarsa Abbu why. .... Wllhi bani buk'atar kuma ganin ka A DUNUYAR MU ka tafi ka tafi ka k'yaleni....." Ta k'arashe tana kuka sosai da duka zuciyarta...
Fawaz dake hawaye kallonsu yake su duka biyu kafin ya soma fad'in "What's going on... Make faruwa ku min bayani dan Allah meke faruwa,...?"
Dattijo Suhail ne yakai dubansa ga Fawaz, a hankali ya taka ya isa har gaban Fawaz yana kallon sa lokaci guda ya rungumesa sosai yana fad'in "Na tabbata kai jika na ne kai jini na ne....?"
Fawaz yayi k'arfin halin b'anb'are Abbu daga jikinsa kaman yanda sukaji Aunty Saudat ta kirasa yana goge hawayen idanunsa yake fad'in "Dan Allah ku fahimtar dani, wai meke faruwa ne... Mai ya faru shekarun baya.....?"
Dattijo Suhail na hawaye yake fad'in "Wannan shine abinda ya dawo dani, wannan shine mak'asudin dawowata wajen nan.... Koda Sa'oud da Dije zasu kuma hanani fad'awa wa d'an 'yar uwata asalinsa zan sanar dashi sannan zan nemi gafaran d'iyata akan abunda na mata a baya... Sabida na tabbata hakkinta shi yabibiyeni a rayuwa....." Ya k'arashe yana mai takowa gaban Naseer wanda bugun k'irjinsa ya k'aru....
Abbu Suhail yakai hannu ya kamo hannayen Naseer dake tsaye tamkar mutum mutumi kafin ya soma fad'in "Naseer ka yafe min, ka yafeni d'ana, ka yafeni rashin sanar dakai da banyi ba tuntuni, ka sani ba'a sona bane ban sanar da kai ba, iyakaci umarnin mahaifinka nabi...." Hawaye suka ci gaba da kwararowa daga idanun Abbu Suhail yayinda Naseer ke binsa da kallo lokaci guda jikinsa yayi wani irin sanyi ba tareda sanin dalili ba....
Abbu Suhail yaci gaba da fad'in "Hidaya 'yar uwata ce, mahaifiyarka k'anwa take min..... A lokacin data haifeka Allah ya karb'i rayuwarta... Mahaifinka Sa'oud Santana da mai d'akinsa Dije su suka zab'i a rufa al'amarin sabida tun tasowarka a hannun Dije matar Sa'oud ka taso tamkar ita ta haifeka... Sanda na rasa mai d'akina mahaifiyar Saudatu nazo k'asar nan da Saudatu a lokacin naso sanar dakai dukda k'arancin shekarun da kake dashi amma ban sanar dakai ba sabida mahaifinka ya hana...." Muryar Dattijo Suhail ta carke sanda kuka yaci k'arfinsa..... Parlorn tayi tsit sai sautin kuka kake jiyowa.... Zukata sun kuma girgiza shin wannan wane irin Al'amari ne.....
Naseer har lokacin ya kasa motsawa daga yanda yake tsaye.... Sunan matar da yaji Abbu ya ambata a matsayin mahaifiyarsa yake kan nanatawa HIDAYA.... So wannan shine asalin dalilin da yasa Innah bata tab'a k'aunar sa ba... Ashe shid'in ba d'anta bane.... Ashe mahaifiyarsa ta gaskiya ta jima da rasuwa.... Gaba d'aya rayuwarsa yayisa ne akan Innah ce mahaifiyar sa, gaba d'aya rayuwarsa yayisa ne wajen kyautata mata da neman aljannarsa ta k'ark'ashinta..... Abubuwan da Innah ta dinga masa na musgunawa tun yana yaro ya shiga dawowa kwanyarsa, kalan tsanan da tsangwama da ta masa, ashe ba ita ta haifesa ba,.... Duk rayuwar da yayi bai tab'a addu'a wa mahaifiyar sa ba.... Meyasa Abban sa zai masa haka mai yasa bai sanar dashi ba... Meyasa ya dank'a amanarsa a hannun azzaluman mace wacce tayi sanadiyar barinsa duniya..... A hankali Naseer ya soma takawa ba tareda ya dubi kowa dake cikin parlorn ba dukda juyawa da duniyar ke masa, Salma ta bisa da kallo itama hawayen ne ke zarya a kumatun ta, gaba d'aya sai ta nemi nata tashin hankalin da take ciki ta rasa, ji take tamkar ta mik'e a guje ta rungumesa....
A haka ya dinga tafiya har saida ya isa sashen sa kafin ya maida k'ofar ya kulle.... Waje ya samu ya zauna abubuwan suna kuma yawo a kwanyar sa.... Yakai dubansa ga hitonsa da mahaifinsa dake ajiye saman stand dake a cikin d'akinsa... K'arasawa yayi ya d'auki hoton had'i da k'urawa hoton idanu.... Cikin wani irin murya mai tsanin rawa ya soma fad'in "Why...? Abba Why... Abba meyasa, meyasa kayi haka...... Abba meyasa ka min haka......" Kasa ci gaba da magana yayi sai wani irin kuka da ya kufce masa lokaci guda ya durk'ushe saman gwiwoyinsa a wajen yana rik'e da hoton yake kuka tamkar ransa zai fita......
***
Affan ne ya shigo sashen Mamy ya tarar har lokacin Mamy bata fice a gidan ba tana nan rakub'e can k'asan carpet tana kuka uwa mai yawon neman taimako, Shareefah ta kawo mata abinci tana rok'onta taci....
Cikin sauri yana wani irin huci ya k'arasa ya wafce plate d'in abincin daga hannun Shareefah, gaba d'aya daga Mamy har Shareefah d'ago idanu sukayi suna duban Affan d'in dake faman huci da turiri....
Cikin wani irin murya yake fad'in "Mamy why just can't understand that you have no place here.... We've nothing to do with you... Is it so hard to understand huh....? Kin kasa fahimta ne... Ki gode ma Allah ban mik'a ki ma 'yansanda ba.. Sannan hakan ba yana nufin bazaki fito da Azeema ba kenan..... Da wannan zaman da kikeyi da tashi kikayi kika dawo da ita don na tabbata bokan ki ne ya tsafe ta..... Mamy I'm afraid idan baki dawo da Azeema ba zaki tafi jail....." Ya k'arashe yana wani irin huci...
Kuka sosai Mamy take tana girgiza kai take fad'in "Affan wllhi wllhi ka yarda dani, wllhi ba laifina bane.... Wllhi duk abinda na fad'a maku iyakacin gaskiyata kenan.... Affan don Allah ku tausaya min wllhi nayi nadama nayi danasanin sanin hanyar gidan boka... Wllhi sharrin Laure ce... Ku tausaya mini......" Ta k'arashe tana k'ok'arin janyo k'afar Affan da tuni ya matsa daga kusanta....
Shareefah kam kuka sosai take tana rungume da Mamy take fad'in "Wllhi bazata je jail ba haba haba Affan... Baka da imani ne, Mamy ta tuba ta gyara halayenta, kuma wllhi na yarda da labarin data bamu... Malami ya kamata a nema ayi addu'a a rok'i Allah ya kub'utar da Azeema ya bayyana mana ita, sannan mu tafi a warware sammon dake jikin Daddy...."
Batakai aya ba suka jiyo muryar Ali Safwan yana fad'in "Bana buk'atar a warware komai... Nafiso na koma ga mahallici na a haka sabida ranan gobe k'iyama na samu shaidan da zan tsaya gaban mahaliccina cewa ta cutar dani..... Na tabbata wanda ya zalunceka A DUNIYAR MU kaine a saman sa idan anje lahira, yanda alk'alin alk'alai zaiyi shari'a da gaskiya daidai da daidai baza'a tauye wa kowa ba..... Babban damuwata ba k'afafuwana bane, Azeema itace damuwata, sai yanzu na fahimci ta jima tana wargaza duk wasu shirinki na cutar da Al'umma Asma'u.... A lokacin da na gansu itada Shareefah suna aikata mummunar sab'o naji sam ta sane min a rai daga ita har Shareefar... Saidai kuma na yarda duk d'an Adam yanada nasa good side d'in, na tabbata koda ace tana wani sab'o tsakaninta da mahaliccinta tanada nata good side d'in sannan na yarda idan kaga bawa aikata laifi ba aibanta shi zakayi ba ko ka muzanta shi, addu'a da fatan shiriya shi ya kamata kayi masa sannan kayi addu'an Allah ya kareka daga fad'awa irin aikin sab'on da yake aikatawa... Yau na tabbata da na muzanta ta na koreta a gidana da batayi yunk'urin ceton rayuwa na ba..... Amma sai gashi a ranan da kika turoni saman bene Azeema ce ta soma zuwa ta kirawo d'auki, kika bini asibiti don ki gama dani, nan ma bata barki ba ta bi bayanki ta hanaki aiwata k'udirinki, bata tsaya a nan ba.. Ta biki har yanda kike tunanin zakije a kashe maki ni ta hanyar asiri sai kuma reshe ta juye da mujiya... Wllhi nayi imani da Allah ko wad'annan ayyukan alkahiri da Azeema tayi zai isa mahaliccinta ya gafarta mata wad'ancan laifukan da tayisu a baya tunda tsakaninta dashi ne, Shi kuma AlGafur ne kuma mai Rahama...."
Ya juyo ga dubansa ga Shareefah wacce ta tak'ure sosai tana hawaye kana yace "Wannan ya isa izna a gareki.... Ki tuba kibi Allah kisan wancan laifi da na kamaku kunayi shi yasa ban aura maki Naseer ba sabida bazan cutar dashi ba na aura masa Salma nitsetsiyar yarinya... Ba wai nak'i ki bane saidai inaso ki gyara halinki.... Abubuwa da dama sun faru A DUNIYAR MU wanda na tabbata sun ishe masu hali irin naki ishara Asma'u.... Zaki iya zama a cikin gidan nan kodon Shareefah amma a halin yanzu bansan matsayin aurenki a gidan nan ba... Wllhi daraja guda kikaci darajan 'ya'yana sgiyasa na maki wannan alfarma, sannan ki sani ni ba azzalumi bane bazanso naga kin tagayyara ba..... Ki zauna kiyita istigifari wa mahaliccin ki don laifin da kikayi yafi ko wani laifi girma da muni a sikeli... Allah yayi mana muwafak'a ya datar damu, ya tsare mu da imanin mu daga bijire masa.... Affan maza shige mu tafi sallan isha...." Ya k'arashe yana tura tayun wheelchair d'insa...
Affan da jikinsa yayi sanyi sosai a hankali yabi bayan mahafin nasa....
Mamy da Sahreefah suka kuma rungumar juna suna kuka mai cikieda da tarin nadama da ban tausayi....
****
Wannan dare ma iya cewa gidan Sa'oud Santana kwana zaune akayi koma kwana tsaye, Momy ita ta sauk'i Suhail da matar da take tunanin matarsa ce a d'akin bak'i don banzai yuwu a gama wannan warware-warware ba a dare guda....
Ko kad'an Jamila bata sanar da 'yan uwanta halin da take ciki ba, saidai kana ganinta zaka fahimci lafiya bai isheta ba, gaba d'aya ta tashi hankalinta ta tsangwami rayuwarta, duk yanda Momy taso jin abinda ke damunta tak'i sanar da ita.. A b'angaren Salma kuwa kwana tayi tunanin Soja da halin da yake ciki, hasashenta na cewa ba Innah ce ta haifi Soja ba ya kuma tabbata, itakam ko a finafinai bata tab'a gani ko jin labarin masu hali irin na Innah ba, tamkar ba 'yar Adam ba.... Haka nan ta kwana tana zullumin halin da Soja ke ciki...
Washe gari har wajajen azahar basuji d'uriyan Naseer ba... Abin duk ya dami Salma dukda mutanen gidan kowa ya k'ulene a uwar d'aki tamkar masu takaba, ma'ikata ne kurum saiko Momy masu zirga-zirgan... Dukda haka sosai abin ya dami Salma... Momy na hankalce da ita yanda ta rafka tagumi ta k'urawa k'ofar sashen Naseer d'in idanu ko zataga fitowarsa... A hankali Momy ta k'araso kusanta kafin ta d'an dafata...
"Daughter...." D'ago kai Salma tayi tana dubanta damuwa fal fuskarta...
K'ak'aro murmushi Momy tayi ta sakar mata kana tace "Kije ki duba shi kiga yaya ya kwana kinji koh...." murya cikeda kulawa tayi maganar..
Salma ko tamkar wacce take jira, cikin sauri ta mik'e tana fad'in "Toh Momy, zanje... Barinje na dubashi....." Gaba d'aya a birkice take yin maganar...
Cikeda tausayawa Momy ke dubanta kafin ta mata rakiya har k'ofa..
Har sun kai k'ofar Momy ta k'arasa saman dining table ta d'au bawl na fruit salad wanda Falmata bata jima da ijiyewa ba ta mik'a mata kana tace "Nasan bashida appetite wannan zai taimaka maza kai masa..."
Salma ta murmusa ta amsa tana mai fad'in "Toh Momy..." Kana ta nufi sashen Naseer...
Saidai ga mamakinta a bud'e taga sashen nasa kuma bataji alamunsa ba... Ta shiga tana mai sallama amma shiru ba'a amsata ba.... Ko ina saida ta duba a sashen nasa bataji alamunsa ba... Jiki a sanyaye ta fito ta nufi cikin gida...
***
Hannayen sa sakale a aljihu yake duban likitan kana yace "Dr kana nufin saidai a yanke k'afafun kenan....?"
Dr ya jinjina kai kana yace "This the only solution Captain, already veins d'in k'afafun nasa sun daddage dole a yanke kafin yaci gaba da rayuwa, idan yakai wasu awanni ba'a yanke ba komai ka iya faruwa....."
Naseer ya d'an shafi goshinsa kafin ya jinjina kai yace "Shikenan Dr ayi yanda ya kamata.... Ni zan wuce akwai corps guda biyu da zasu tsaya a nan kafin ya sami lafiya..."
Dr ya jinjina kai kafin ya mik'a hannu wa Naseer sukayi masabaha Naseer d'in ya wuce....
***
"Madu ka duba runfar nan da kyau don jiya wllhi nidai naji kaman motsi cikinta, yanzu haka macijin kwanakin nan ne ya dawo....." D'aya saurayin ya fad'i yana nad'e hannun riga..
Sandar gora dake gefensa ya rarumo kafin ya mik'a wa abokin wata daushiyar itace yace "Kai alk'ur'an yau macijin nan zai bak'unci lahira don uwarsa ni na tabbata turensa aka mana angama runfar mu tafi ci gaba, mukar tsinanne yaje yace ma wanda ya turosa mun karsa..."
Yana ida fad'in haka suka shiga bugun shirgin kwalayen dake cikin rumfar
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*59*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Girgiza kai Lubna take tana duban Deeni cikin rashin yarda da kalaman dake fitowa daga bakinsa... Da gaske Deen sallama yake mata, da gaske tafiya zaiyi ya barta.... Ta shiga tuno tun farkon had'uwarsu da kalan rigima da fad'an da sukayi kafin su soma soyayya.... Muryarsa ya kuma katse mata tunani sanda yake ci gaba da fad'in "Bana buk'atar wani abu ya kuma had'ani da Santana's, I'm leaving this place for good, I lost my father a sabidasu.... Sun jefa mahaifina cikin tsananin jinya... K'arewa mahaifana sun rabu da juna shekara da shekaru duk a sabida su, basu basu dama sun rayu tare da juna A DUNIYAR MU ba.... Bazan kuma zama inaji ina gani su kuma d'aid'aita rayuwa ba.... I'm sorry Lubna, ina k'aunarki amma bazai yuwu mu kasance tare ba.... Take this... Idan Naseer yazo ki bashi, ajiyan da mahaifina ya jima yana masa kaman yanda mahaifiyata ta fad'i....."
Ya k'arashe yana mik'a mata envelope d'in....
Idanun Lubna basu daina zuban hawaye ba, cikin murya irinta mai kuka take fad'in "Deen na fahimce ka, kuma dole irin haka ta kasance.... Dole kayi komai domin kare family d'inka, sannan babu mai kuma k'aunar ya rab'e mu.. Ni kaina da inada halin tsame kaina daga cikin wannan zuri'a da nayi... Amma saidai babu hali tuni alk'alamin k'addara ya rubata hakan... Thank you Deeni... Thank you for everything..." Kasa ci gaba da magana tayi sabida tsananin rawa da muryarta keyi...
K'ok'arin danne kukan daketa son kufce masa yake kafin yace "Goodbye Lubna... Idan da rabon mu sake had'uwa A DUNIYAR MU zamu had'u kinji....." Cikin sauri ya juya ya nufi k'ofa yana jiyo sautin kukan Lubna na k'aruwa yake fad'in "Ummi Mama Tani mu jenku.. Muje kafin abubuwa su kuma kwab'ewa....
Mama Tani na hawaye ta isa gaban Aunty Saudat saidai kasa magana tayi sabida kuka da ya kufce mata..... Macen da Deeni ya kira da Ummi k'arasawa tayi ta dafa kafad'an Lubna kana tace "Kiyi hak'uri mahaifinki mutumin kirki ne koda mahaifiyarki ta kasance akasin haka... So tari bamu samun komai d'ari bisa d'ari A DUNIYAR MU, so da yawa rayuwa takan zo mana baibai ba yanda muka tsara ba A DUNIYAR MU, amma idan munyi hak'uri muka amshi jarabawar mu hannu bibbiyu sai muga alkhairi a k'arshe... Naso na sami Naseer na damk'a masa wannan takardu hannu da hannu kaman yanda mijina yaso saidai hakan bai yuwu ba... Ina fata zaku bashi......" Ta k'arashe tana kallon Lubna dake kuka sosai....
Babu wanda ya kuma iya cewa komai cikin parlorn har su Mama tani suka fice cikin kuka.. Deeni kam tuni ya fice yana goge hawayen dake zubo masa....
Juyowa Lubna tayi bayan sun b'ace ma ganinta lokaci guda ta rungume Aunty Saudat tana kuka sosai..... Jamila da Ilham ma rungume da juna suna faman jimamin 'yar uwarsu had'i da tausayin Deeni da Lubna kai da duk wanda wannan iftila'i ke kan shafa.....
***
Sauri-sauri Alh Kabeer ya cire simcard d'in daga cikin tablet d'in da suka gama amfani dashi wajen kiran Naseer... Lokaci guda ya k'ona sim d'in kafin ya jefa tab d'in cikin 'yar jakansa yana k'ok'arin warware d'aurin da sukayima Salma yake fad'i ma Innah tayi sauri su bar wajen nan don jikinsa na basa Naseer ka iya tracking d'insu....
Tsegege Innah ke dubansa sai k'ok'arin kwance Salma daga jikin kujeran yake kana ta janyo sa baya cikin karaji tana fad'in "Toh da kake kwanceta nufinka tareda ita zamu tafi... Ai banka wa shegiya wuta cikin ginin nan ya kamata muyi sannan muyi tafiyarmu...."
Tsaki Kabeer yayi yana dubanta kana yace "Seems you don't have brain in that skull of yours....." Bai ko kuma kulata ba ya koma yaci gaba da yunk'urin kwance Salma...
"Yo ni uwar me naji kace... Kai billahillazi k'onata zanyi tunda na lura Naseer na bala'in sonta, nasan idan ta mutu inbai sami tab'in hankali ba zuciyarsa zata buga kaga na cimma burina na salwantar da rayuwarsa...."
A hasale ya d'ago yana watsa wa Innah mugun kallo kafin yace "Shiyasa nace maki sam bakida tunani balle lissafi, toh idan mun kasheta da me zamu dinga threatening Naseer, azabtar da ita da zamukeyi yanaji yana gani ba tareda ya iya yin komai ba shine kawai zai d'aid'aita Naseer sannan ta haka ne kurum Kitty da Lubna zasu yarda su biyo mu... Ko baki gane bane....."
Salma da hawaye ke zarya a idanunta binsu da kallo kurum take tana ganin tamkar wasu halittinu daga wani planet ba'a nasu duniyar ba, ta dubi wannan ta dubi wancan haka ta kallonsu suna masu ci gaba da argument d'in...
Lokaci guda ya kuma sunkuyawa yana k'ok'arin ci gaba da warware d'aurin...
Innah dake faman huci lokaci guda ta rarumi wani kututturen katako dake gefe ta sauk'e ma Kabeer a gadon bayansa tana fad'in "Wllhi k'arya kenan... Babu wanda ya isa ya hanani kashe yarinyar nan....."
A d'ari ya mik'e yana sosa k'eyarsa yake fad'in "Kutuman uban chan... Kasheni zakiyi.. Toh kafin ki kasheni bari ni na kashe ki.... Ya k'arashe yana k'ok'arin rarumo alluran da yaso cakkawa Salma.... Saidai tuni Innah ta hangame babban randar da ya dama acid d'in ciki tana fad'in "Ka matso kusana wllhi sai na maka wanka da wannan ruwa mai tururin....
Wannan bidiri da suke gaba d'aya ya d'auke hankulansu sam basuji isowarsu Naseer ba....
Kabeer ne yaji kaman motsin mutane k'irjinsa ya yanke ya fad'i.... Cak ya tsaya ya daina biye Innah had'i da kasa kunnuwarsa yana son tabbatar da abinda yake jiyowa.... Da baya da baya ya soma matsawa yana fad'i wa Innah....
"Innah kunnuwana suna jiyo min wasu sauti... We should get ready... Dole mu tafi da yarinyar nan itace kawai garkuwan mu...." Bakin Salma na d'aure babu halin ihu sai k'walalo idanuwa waje take tana iyaka nata k'ok'arin...
K'aran tafiya da suka jiyo yana nufosu sosai ya sanyasu saurin nufa d'aya k'ofan suna k'ok'arin bud'eta saidai gaba d'aya sun kasa bud'e k'ofar...
A tamanin suka dawo ga window bugu guda suka mata ta bud'e... Aiko suna Naseer suna shigowa d'akin Innah ta d'aga k'afafunta ta haye windown... Ko zafin fad'uwar da tayi bataji ba dashike dama ba jiki ne da ita ba.... A d'ari ta mik'e tana mai ci gaba da gudun famfalak'i fatarinta na d'agawa sama...
Kabeer rik'e da randar ruwan acid d'insa yake fad'in idan d'ayansu ya motsa daga position d'insa zaiyi wanka wa Salma dake d'aure a wajen da ruwan acid d'in...
Girgiza kai Naseer keyi yana k'ok'arin d'aga k'afarsa guda yake fad'in "Yaya ka ajiye abinda ke hannun ka.... Ka...."
Baikai aya ba Kabeer ya katse sa da fad'in "Don't you dare move an inch... Kaji na rantse maka wllhi kana motsawa zan watsa mata wannan ruwan ta diddige gaba d'aya......"
Kallon kallo kurum suka shiga aika ma juna, ji yake tamkar yayi tsalle ya mak'ure Yayan nasa, ko motsawa Kabeer ya hanasu yi balle suyi alamawa 'yan uwansu dake waje suyi k'ok'arin rafke Innah....
A hankali Kabeer ke k'ok'arin matsawa baya yanason tsira ma rayuwarsa idanunsa k'yam akansu da zaran sunyi motsi zai saita randar ruwan acid d'in zuwa fuskar Salma... A haka ya dinga jada baya har ya iso tagar da Innah tabi ta arce.... Aiko yana isa Naseer yayi kukan kura ya nufesa don alwashi ya d'aukarwa kansa wannan karan dole yayi karon batta da Yayan nasa koda zai rasa ransa ne....
Runtse idanunta kurum Salma tayi sanda taga Alh Kabeer ya d'ago langar ruwan acid d'in yana yunk'urin watsawa Naseer... Tuni 'yan sanda sun janye kujeran da Salma ke kai... Saidai d'aga langar da Alh Kabeer zaiyi hannun langar ta b'alle gaba d'aya ruwan acid d'in ya kware masa a duka k'afafunsa biyu.... Wani irin azabebben k'ara ya saki sanda ya zube k'asa.... Yana k'aran yana duban k'afafunsa tun daga cinyoyinsa sai wani irin hayak'in tururi suke wanda ya kusa turnuk'e wajen gaba d'aya, naman k'afafunsa suka shiga daddagewa tamkar audugar da taji wuta.....
Naseer ko kula da hakan baiyi ba sai sunkuyawa da yayi ya cakumo Yayan nasa ya shiga dukan fuskar sa da iyaka k'arfinsa... Irin dukan sa'a yake masa don ko kula da cewa Alh Kabeer ya sume Naseer beyiba... Wani irin dukan huce haushi kurum yake masa.. Yana dukansa hawaye suna fitowa daga idanunsa..... Kuka sosai Naseer keyi don saida polisawan nan suka amshe Kabeer kafin Naseer ya sakesa ya nufi Salma a guje..... Cikin sauri ya shiga kwanceta yana duban idanunta dake ambaliyan hawaye....
Yana gama kwanceta rungumeta yayi lokaci guda su duka tayi bursting cikin tsananin kuka had'i da k'ank'amesa sosai....
Siriryar hawaye ne ta gangaro daga idanunsa sanda ya lumshe su yana k'ank'ame da ita yake fad'in "I'm here.... I'm here, babu abinda zai kuma faruwa kinji koh....." Ya k'arashe yana kuma shafa bayanta a hankali alamun lallashi.. Salma ko sai shan zuciya take tsaban kuka ta kasa furta koda kalma....
Jacket d'insa ya cire ya rufa mata kafin ya rik'ota cikin jiknsa suka fice daga wajen suka nufi mota.... Suna jiyo ihun Alh Kabeer sanda 'yan sanda suka fito dashi a hannu suka watsa sa bayan hilox d'insu.....
Driving kawai Naseer keyi amma bawai hankalin sa na jikinsa bane, sam baiso Innah ta tsere ba, yanada tambayoyi da dama da yake son yi mata, tabbas zama bai gansa ba har sai ya nemo Innah yanda ta shiga ta fita....
D'an kallon Salma da har lokacin bata dawo dai-dai ba yake, murya can k'asa yace "are you alright, kinajin wani ciwo...?"
Ba tareda ta amsa sa ba ta soma girgiza kai alamun babu bata jin komai.... Yasan dole yakaita likita ya duba masa ita sabida ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba....
Mota 'yan sandan ne da Naseer ke biye bayansu suka tsaya a station d'in nasu, shima lokaci guda yayi parking don dole ya duba ko Maina ya dawo cikin hayyacin sa zai iya masa magana dan yasan shine kawai zai iya sanin ina Innah ta dosa tinda Kabeer kam babu halin magana yana kan shan azabar duniya da ya zuba ma kansa....
Cikin station d'in yayi parking motar sa lokaci guda ya d'an sauk'o da kansa saitin fuskar Salma da har lokaci jikinta bai daina rawa ba, gaba d'aya dai bata dawo dai-dai ba... Hannayen sa yasa ya kamo nata hannayen had'i da matsowa sosai kusanta kafin ya soma fad'in "It's okay my love, babu abinda zai kuma faruwa da izinin Allah kinji koh...."
Bata iya cewa komai ba sai jinjina masa kai da tayi still tana hawaye....
Hannu yasa ya shiga share mata hawayen yana fad'in "Banson ganin hawayen nan haka nan kinji koh... Everything would come to an end kinji koh.... Barin shiga nan yanzu zan fito kinji koh...."
Saurin d'ago idanu tayi tana dubansa fuskarta cikeda tsoro kafin ta soma girgiza kai wasu sabbin hawaye na fito mata.... "Soja nidai bazan zauna ni kad'ai ba tsoro nake ji....."
Ganin yanda duk ta kuma birkicewa lokaci guda ya sanyasa kuma rik'ota cikin jikinsa yana lallashi, yana jiyo yanda k'irjinta yake bugu da sauri da sauri.... K'ok'arin kwantar mata da hankali yake kafin suka nufi cikin station d'in a tare tana nan mak'ale cikin jikinsa tamkar masu tsoron a rabasu.....
Saida ya shigo da ita yaji dama asibiti kawai ya wuce da ita don gaba d'aya sabon rikicewa tayi sai kuka musamman da tayi tozali da Maina wanda dukda canzawa da kamanninsa yayi bata mance fuskar nasa ba sanda suke cinnama gidansu wuta....
Cikin kuka take nuna Maina da yatsa tana fad'in "Wllhi shine shine ya biyoni zai kasheni, shine sanadiyar k'onewar gidanmu... Shine sanadiyan rabuwata da Inno ta har ta koma ga mahaliccinta bamu kuma had'uwa ba... Wllhi shine Soja...." Ta k'arashe tana kwantar da kai cikin k'irjin Naseer da wata sabuwar tashin hankali ta ziyarcesa.... Sai yanzu abubuwa da dama suka shiga yawo a kwanyar sa.. Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un... Me kuma ke shirin faruwa kardai Innah da Kabeeru sune silan k'onewar gidan gonar Alh Ali Safwan... Toh mai ya masu.. Shin wad'an nan wasu irin mutane ne.... Lokaci guda ya fice da Salma daga wajen don bazai yuwu ya tsaya da ita a wajen ba.... He needs to get to the bottom of all this, dole ya zama very strong dole ya shirya ma fuskantar duk wani tashin hankali da zai kuma b'ullo masa A DUNIYAR SU domin kuwa tabbas jikinsa na basa wani babban tashin hankali na shirin ziyartar sa.....
***
Yana k'arasowa gate d'in gidansu Sojin suka shiga sara masa suna gaidashi... Ana k'ok'arin hangame masa gate ya hangi wata mota wanda ko ba'ace maka ba taxi ce tayi parking can gefen gidan nasu... Wani balaraben mutumi ne da wata mata bak'ar fata suka fito daga cikin motar... Gaban Naseer yayi wani irin yankewa ya fad'i.... Tuk'a motar da ya kasa ci gaba da yi...
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*60*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Dukda shekaru da ya d'iba rabonsa da gidan ya gane gidan kuma ya yarda d'an tasi d'in gidan Sa'oud Santana ya kawo su, gidan yana nan da yanayinsa irinta masu kud'in wancan lokaci saidai wasu gyare-gyare na zamani da aka kuma k'awata sa dashi.... Hannun matar da suke tare ya rik'e suna masu ci gaba da tafiya
Tabbas dukda girma da ya nuna a fuskar mutumin zai iya tuna tamkar ya sansa a lokutan baya..... Bai daina kallon wad'annan bayin Allah ba har saida suka nufo gidansu gadan-gadan... Sojojin dake tsare da gate ne suke yunk'urin hanasu shiga gidan.... Har lokacin Naseer bai sami zarafin motsawa ba sai k'irjinsa dake bugu cikin sauri.... Salma kam sam batama lura da halin da Naseer d'in ke ciki ba.... A hankali yaci gaba da tuk'a motar har ya iso gate d'in nan da nan kuwa attention d'in Sojojin ya dawo ga ogansu.... A dai-dai lokacin Dattijon balaraben nan ya juyo yana duban Naseer... Duk da tsawon shekaru da ya kwashe bai ganshi ba tabbas zai iya shaidawa d'an 'yar uwarshi ce.... Tabbas wannan Naseer ne.... Shima Naseer d'in k'uri yayi wa mutumin yana hango fuskar Aunty Saudat a tattaredashi...
"Naseer....!!!" Mutumin ya fad'i ruwa na k'ok'arin cikowa idanunsa....
Bugun k'irjin Naseer ya k'aru a hankali ya bud'e marfin mota ya fito waje...
****
A dai-dai stairs sukayi kusan cin karo da Fawaz da alama gate ya nufa don ya hango gate d'in a bud'e sannan ya hangi mutane tsattsaye....
Gabanta ya kuma yankewa ya fad'i... A hankali Fawaz ya kauce mata had'i da kauda kansa gefe kafin ya shige cikin sauri.... Kallo ta bisa dashi lokaci guda taji zafin k'irjinta ya k'aru... Cikin sauri ta lumshe idanunta tana mai ci gaba da taka steps d'in da k'yar.... Saidai tana cikin k'ok'arin haurawa taji tari yana zuwa mata akai-akai.... Hannu tasa tana k'ok'arin k'unshe bakinta..... Saida ta d'an tsuguna a wajen kafin tarin ya lafa.... Saidai tana cire hannunta a bakinta taga jini cikin hannun nata.... Wani sabon tashin hankali ya ziyarce ta... Shafa bakinta ta kuma yi taga dai tabbas jini ke fita daga bakinta... Cikin sauri ta k'ara ga doguwar madubi da aka k'awata hanyar dashi tana kallon fuskarta cikin madubin.... Da gaske dai jini ne jini ke fitowa idan tayi tari... Cikin sauri ta soma girgiza kai sabbin hawaye suna kwararo mata.... Sallaman mutane da ta jiyo daga parlorn ya sanyata daina kukan da take... Dukda tasan duk yanda akayi Naseer ne ya dawo da Salma bata iya k'arasawa wajensu ba sai hayewa sama da tayi cikin sauri.... K'ofar d'akin Lubna ta soma shigewa yanda ta hangi Lubnar kwance saman cinyar Aunty Saudat tana shafa kanta alamun kwantar da hankali... Cikin sauri tasa kai ta shige.... A dai-dai k'ofar d'akin da Momy take ta hangesu gaba d'aya daga Momyn har Ilham da Falaq.... Momy na bisa darduman sallah yayinda Ilham ke kwance rigingine Falaq na bisa k'irjinta.... Wasu hawaye suka zubo wa Jamila.... Cikin sauri ta k'arasa nasu d'akin ta shige had'i da kullo k'ofar domin tasan bazata iya had'uwa da kowa a wannan yanayi da take ciki ba... Abubuwa sun taru sun mata yawa cikin zuciyarta, ga rashin Fawaz ga uwa uba cutan da Alh Kabeer yace ya shafa mata.... Can k'uryar d'aki ta samu ta zauna had'i da tak'urewa waje guda ta kifa kanta tana kuka maras sauti, shikenan k'ila farkon symptoms d'in HIV d'in kenan idan kayi tari jini ya fito.... Tunanin da zuciyarta ya dinga raya mata kenan wanda ya kuma tsundumata cikin wani sabon tashin hankali....
****
Gaba d'aya hallara sukayi a parlorn, Salma ta tafi ta rungume 'yar uwarta Ilham suna kuka sosai..... Fawaz kam idanunsa naga balaraben da suka shigo tareda Naseer wanda tunda ya d'aura idanu akansa ya kasa d'agawa ga k'irjinsa dake faman bugu.....
Shima wannan Dattijo duban Fawaz ya dingayi yana jin wani babban Al'amari a tattare dashi.... Idanunsa naga Fawaz har baisan sanda Aunty Saudat da Lubna suka sauk'o parlorn ba..... Momy ta k'arasa ta kamo hannun Lubna ta had'esu gaba d'aya dasu Salma ta rungume tana zaune tsakiyarsu don jikinta na bata wani abin ne zai kuma faruwa....
Hawaye ke gangaro mata tana takowa cikin parlorn, juyawar da zaiyi ya hangeta tana takowa cikin tapkeken parlorn..... Lokaci guda ya mik'e k'afafunsa na rawa ya soma takawa ya nufeta shima kukan yake..... Yana k'arasowa yanda take ya rungumeta ba tareda ya iya furta komai ba sai kuka da yakeyi tamkar k'aramin yaro.... Aunty Saudat kam cak ta tsaya ba tareda ta maida masa martanin rungumar ba.... Sai tunanin sanda ya barta a wannan same parlor yayi tafiyar sa shekaru ashirin da d'oriya da suka gabata, abubuwan suka yawo a kwanyarta, ta tuna tana binshi tana rik'oshi amma haka ya b'anb'areta daga jikinsa yasa k'afafu ya tafi ya barta wa mutanen da suka tassama halak'ata da k'arfin gaske..... Lokaci guda tamkar wacce aka zabura ta shiga k'ok'arin b'anb'are jikinta tana kuka sosai tana ture mutumin tana fad'in mai ya dawo dashi ya b'ace bata son ganin sa... Duk cikin harshen arab take maganganun... A d'ari Fawaz ya k'arasa yana k'ok'arin janye mahaifiyarsa daga rik'on mutumin yake fad'in "Malam lafiya... Wai waye kai....."
Kuka Aunty Saudat take sosai sanda Fawaz ya rungumeta sosai yana huci yana duban mutumin.... Naseer ne ya k'araso yana k'ok'arin janye mutumin a hankali.... Baiko iya bawa Fawaz dake tambayar ko wanene mutumin amsa ba.... sai jiyo muryar wannan mutumi sukayi cikeda tsananin mamaki hausa yake
"Saudat ki yafeni... Ki yafeni d'iyata wllhi tunda na tafi na barki a nan ban sami kwanciyar hankali ba, arzikin da na tafi dashi baimin amfani ba k'arshe na rasa komai na koma abin tausayi abin kwatance A DUNIYAR MU.... Ki yafe dan Allah.."
Sai sannan Fawaz da sauran jama'an wajen suka fahimce wanene wannan mutumi.... Idanuwan Fawaz suka shiga zubda hawaye, girgiza kai kurum yake yana duban mutumin da mahaifiyarsa..... Kafin ya sami zarafin magana ya jiyo muryar mahaifiyarsa cikin kuka tana fad'in "Abbu meyasa? Meyasa ka tafi ka barni..... Why..? Baka damu ba all the suffering I went through.... Sun baka kud'ad'e ka aurar dani ma d'ansu wanda suka tasamma kasheni shida mahaifiyarsa Abbu why. .... Wllhi bani buk'atar kuma ganin ka A DUNUYAR MU ka tafi ka tafi ka k'yaleni....." Ta k'arashe tana kuka sosai da duka zuciyarta...
Fawaz dake hawaye kallonsu yake su duka biyu kafin ya soma fad'in "What's going on... Make faruwa ku min bayani dan Allah meke faruwa,...?"
Dattijo Suhail ne yakai dubansa ga Fawaz, a hankali ya taka ya isa har gaban Fawaz yana kallon sa lokaci guda ya rungumesa sosai yana fad'in "Na tabbata kai jika na ne kai jini na ne....?"
Fawaz yayi k'arfin halin b'anb'are Abbu daga jikinsa kaman yanda sukaji Aunty Saudat ta kirasa yana goge hawayen idanunsa yake fad'in "Dan Allah ku fahimtar dani, wai meke faruwa ne... Mai ya faru shekarun baya.....?"
Dattijo Suhail na hawaye yake fad'in "Wannan shine abinda ya dawo dani, wannan shine mak'asudin dawowata wajen nan.... Koda Sa'oud da Dije zasu kuma hanani fad'awa wa d'an 'yar uwata asalinsa zan sanar dashi sannan zan nemi gafaran d'iyata akan abunda na mata a baya... Sabida na tabbata hakkinta shi yabibiyeni a rayuwa....." Ya k'arashe yana mai takowa gaban Naseer wanda bugun k'irjinsa ya k'aru....
Abbu Suhail yakai hannu ya kamo hannayen Naseer dake tsaye tamkar mutum mutumi kafin ya soma fad'in "Naseer ka yafe min, ka yafeni d'ana, ka yafeni rashin sanar dakai da banyi ba tuntuni, ka sani ba'a sona bane ban sanar da kai ba, iyakaci umarnin mahaifinka nabi...." Hawaye suka ci gaba da kwararowa daga idanun Abbu Suhail yayinda Naseer ke binsa da kallo lokaci guda jikinsa yayi wani irin sanyi ba tareda sanin dalili ba....
Abbu Suhail yaci gaba da fad'in "Hidaya 'yar uwata ce, mahaifiyarka k'anwa take min..... A lokacin data haifeka Allah ya karb'i rayuwarta... Mahaifinka Sa'oud Santana da mai d'akinsa Dije su suka zab'i a rufa al'amarin sabida tun tasowarka a hannun Dije matar Sa'oud ka taso tamkar ita ta haifeka... Sanda na rasa mai d'akina mahaifiyar Saudatu nazo k'asar nan da Saudatu a lokacin naso sanar dakai dukda k'arancin shekarun da kake dashi amma ban sanar dakai ba sabida mahaifinka ya hana...." Muryar Dattijo Suhail ta carke sanda kuka yaci k'arfinsa..... Parlorn tayi tsit sai sautin kuka kake jiyowa.... Zukata sun kuma girgiza shin wannan wane irin Al'amari ne.....
Naseer har lokacin ya kasa motsawa daga yanda yake tsaye.... Sunan matar da yaji Abbu ya ambata a matsayin mahaifiyarsa yake kan nanatawa HIDAYA.... So wannan shine asalin dalilin da yasa Innah bata tab'a k'aunar sa ba... Ashe shid'in ba d'anta bane.... Ashe mahaifiyarsa ta gaskiya ta jima da rasuwa.... Gaba d'aya rayuwarsa yayisa ne akan Innah ce mahaifiyar sa, gaba d'aya rayuwarsa yayisa ne wajen kyautata mata da neman aljannarsa ta k'ark'ashinta..... Abubuwan da Innah ta dinga masa na musgunawa tun yana yaro ya shiga dawowa kwanyarsa, kalan tsanan da tsangwama da ta masa, ashe ba ita ta haifesa ba,.... Duk rayuwar da yayi bai tab'a addu'a wa mahaifiyar sa ba.... Meyasa Abban sa zai masa haka mai yasa bai sanar dashi ba... Meyasa ya dank'a amanarsa a hannun azzaluman mace wacce tayi sanadiyar barinsa duniya..... A hankali Naseer ya soma takawa ba tareda ya dubi kowa dake cikin parlorn ba dukda juyawa da duniyar ke masa, Salma ta bisa da kallo itama hawayen ne ke zarya a kumatun ta, gaba d'aya sai ta nemi nata tashin hankalin da take ciki ta rasa, ji take tamkar ta mik'e a guje ta rungumesa....
A haka ya dinga tafiya har saida ya isa sashen sa kafin ya maida k'ofar ya kulle.... Waje ya samu ya zauna abubuwan suna kuma yawo a kwanyar sa.... Yakai dubansa ga hitonsa da mahaifinsa dake ajiye saman stand dake a cikin d'akinsa... K'arasawa yayi ya d'auki hoton had'i da k'urawa hoton idanu.... Cikin wani irin murya mai tsanin rawa ya soma fad'in "Why...? Abba Why... Abba meyasa, meyasa kayi haka...... Abba meyasa ka min haka......" Kasa ci gaba da magana yayi sai wani irin kuka da ya kufce masa lokaci guda ya durk'ushe saman gwiwoyinsa a wajen yana rik'e da hoton yake kuka tamkar ransa zai fita......
***
Affan ne ya shigo sashen Mamy ya tarar har lokacin Mamy bata fice a gidan ba tana nan rakub'e can k'asan carpet tana kuka uwa mai yawon neman taimako, Shareefah ta kawo mata abinci tana rok'onta taci....
Cikin sauri yana wani irin huci ya k'arasa ya wafce plate d'in abincin daga hannun Shareefah, gaba d'aya daga Mamy har Shareefah d'ago idanu sukayi suna duban Affan d'in dake faman huci da turiri....
Cikin wani irin murya yake fad'in "Mamy why just can't understand that you have no place here.... We've nothing to do with you... Is it so hard to understand huh....? Kin kasa fahimta ne... Ki gode ma Allah ban mik'a ki ma 'yansanda ba.. Sannan hakan ba yana nufin bazaki fito da Azeema ba kenan..... Da wannan zaman da kikeyi da tashi kikayi kika dawo da ita don na tabbata bokan ki ne ya tsafe ta..... Mamy I'm afraid idan baki dawo da Azeema ba zaki tafi jail....." Ya k'arashe yana wani irin huci...
Kuka sosai Mamy take tana girgiza kai take fad'in "Affan wllhi wllhi ka yarda dani, wllhi ba laifina bane.... Wllhi duk abinda na fad'a maku iyakacin gaskiyata kenan.... Affan don Allah ku tausaya min wllhi nayi nadama nayi danasanin sanin hanyar gidan boka... Wllhi sharrin Laure ce... Ku tausaya mini......" Ta k'arashe tana k'ok'arin janyo k'afar Affan da tuni ya matsa daga kusanta....
Shareefah kam kuka sosai take tana rungume da Mamy take fad'in "Wllhi bazata je jail ba haba haba Affan... Baka da imani ne, Mamy ta tuba ta gyara halayenta, kuma wllhi na yarda da labarin data bamu... Malami ya kamata a nema ayi addu'a a rok'i Allah ya kub'utar da Azeema ya bayyana mana ita, sannan mu tafi a warware sammon dake jikin Daddy...."
Batakai aya ba suka jiyo muryar Ali Safwan yana fad'in "Bana buk'atar a warware komai... Nafiso na koma ga mahallici na a haka sabida ranan gobe k'iyama na samu shaidan da zan tsaya gaban mahaliccina cewa ta cutar dani..... Na tabbata wanda ya zalunceka A DUNIYAR MU kaine a saman sa idan anje lahira, yanda alk'alin alk'alai zaiyi shari'a da gaskiya daidai da daidai baza'a tauye wa kowa ba..... Babban damuwata ba k'afafuwana bane, Azeema itace damuwata, sai yanzu na fahimci ta jima tana wargaza duk wasu shirinki na cutar da Al'umma Asma'u.... A lokacin da na gansu itada Shareefah suna aikata mummunar sab'o naji sam ta sane min a rai daga ita har Shareefar... Saidai kuma na yarda duk d'an Adam yanada nasa good side d'in, na tabbata koda ace tana wani sab'o tsakaninta da mahaliccinta tanada nata good side d'in sannan na yarda idan kaga bawa aikata laifi ba aibanta shi zakayi ba ko ka muzanta shi, addu'a da fatan shiriya shi ya kamata kayi masa sannan kayi addu'an Allah ya kareka daga fad'awa irin aikin sab'on da yake aikatawa... Yau na tabbata da na muzanta ta na koreta a gidana da batayi yunk'urin ceton rayuwa na ba..... Amma sai gashi a ranan da kika turoni saman bene Azeema ce ta soma zuwa ta kirawo d'auki, kika bini asibiti don ki gama dani, nan ma bata barki ba ta bi bayanki ta hanaki aiwata k'udirinki, bata tsaya a nan ba.. Ta biki har yanda kike tunanin zakije a kashe maki ni ta hanyar asiri sai kuma reshe ta juye da mujiya... Wllhi nayi imani da Allah ko wad'annan ayyukan alkahiri da Azeema tayi zai isa mahaliccinta ya gafarta mata wad'ancan laifukan da tayisu a baya tunda tsakaninta dashi ne, Shi kuma AlGafur ne kuma mai Rahama...."
Ya juyo ga dubansa ga Shareefah wacce ta tak'ure sosai tana hawaye kana yace "Wannan ya isa izna a gareki.... Ki tuba kibi Allah kisan wancan laifi da na kamaku kunayi shi yasa ban aura maki Naseer ba sabida bazan cutar dashi ba na aura masa Salma nitsetsiyar yarinya... Ba wai nak'i ki bane saidai inaso ki gyara halinki.... Abubuwa da dama sun faru A DUNIYAR MU wanda na tabbata sun ishe masu hali irin naki ishara Asma'u.... Zaki iya zama a cikin gidan nan kodon Shareefah amma a halin yanzu bansan matsayin aurenki a gidan nan ba... Wllhi daraja guda kikaci darajan 'ya'yana sgiyasa na maki wannan alfarma, sannan ki sani ni ba azzalumi bane bazanso naga kin tagayyara ba..... Ki zauna kiyita istigifari wa mahaliccin ki don laifin da kikayi yafi ko wani laifi girma da muni a sikeli... Allah yayi mana muwafak'a ya datar damu, ya tsare mu da imanin mu daga bijire masa.... Affan maza shige mu tafi sallan isha...." Ya k'arashe yana tura tayun wheelchair d'insa...
Affan da jikinsa yayi sanyi sosai a hankali yabi bayan mahafin nasa....
Mamy da Sahreefah suka kuma rungumar juna suna kuka mai cikieda da tarin nadama da ban tausayi....
****
Wannan dare ma iya cewa gidan Sa'oud Santana kwana zaune akayi koma kwana tsaye, Momy ita ta sauk'i Suhail da matar da take tunanin matarsa ce a d'akin bak'i don banzai yuwu a gama wannan warware-warware ba a dare guda....
Ko kad'an Jamila bata sanar da 'yan uwanta halin da take ciki ba, saidai kana ganinta zaka fahimci lafiya bai isheta ba, gaba d'aya ta tashi hankalinta ta tsangwami rayuwarta, duk yanda Momy taso jin abinda ke damunta tak'i sanar da ita.. A b'angaren Salma kuwa kwana tayi tunanin Soja da halin da yake ciki, hasashenta na cewa ba Innah ce ta haifi Soja ba ya kuma tabbata, itakam ko a finafinai bata tab'a gani ko jin labarin masu hali irin na Innah ba, tamkar ba 'yar Adam ba.... Haka nan ta kwana tana zullumin halin da Soja ke ciki...
Washe gari har wajajen azahar basuji d'uriyan Naseer ba... Abin duk ya dami Salma dukda mutanen gidan kowa ya k'ulene a uwar d'aki tamkar masu takaba, ma'ikata ne kurum saiko Momy masu zirga-zirgan... Dukda haka sosai abin ya dami Salma... Momy na hankalce da ita yanda ta rafka tagumi ta k'urawa k'ofar sashen Naseer d'in idanu ko zataga fitowarsa... A hankali Momy ta k'araso kusanta kafin ta d'an dafata...
"Daughter...." D'ago kai Salma tayi tana dubanta damuwa fal fuskarta...
K'ak'aro murmushi Momy tayi ta sakar mata kana tace "Kije ki duba shi kiga yaya ya kwana kinji koh...." murya cikeda kulawa tayi maganar..
Salma ko tamkar wacce take jira, cikin sauri ta mik'e tana fad'in "Toh Momy, zanje... Barinje na dubashi....." Gaba d'aya a birkice take yin maganar...
Cikeda tausayawa Momy ke dubanta kafin ta mata rakiya har k'ofa..
Har sun kai k'ofar Momy ta k'arasa saman dining table ta d'au bawl na fruit salad wanda Falmata bata jima da ijiyewa ba ta mik'a mata kana tace "Nasan bashida appetite wannan zai taimaka maza kai masa..."
Salma ta murmusa ta amsa tana mai fad'in "Toh Momy..." Kana ta nufi sashen Naseer...
Saidai ga mamakinta a bud'e taga sashen nasa kuma bataji alamunsa ba... Ta shiga tana mai sallama amma shiru ba'a amsata ba.... Ko ina saida ta duba a sashen nasa bataji alamunsa ba... Jiki a sanyaye ta fito ta nufi cikin gida...
***
Hannayen sa sakale a aljihu yake duban likitan kana yace "Dr kana nufin saidai a yanke k'afafun kenan....?"
Dr ya jinjina kai kana yace "This the only solution Captain, already veins d'in k'afafun nasa sun daddage dole a yanke kafin yaci gaba da rayuwa, idan yakai wasu awanni ba'a yanke ba komai ka iya faruwa....."
Naseer ya d'an shafi goshinsa kafin ya jinjina kai yace "Shikenan Dr ayi yanda ya kamata.... Ni zan wuce akwai corps guda biyu da zasu tsaya a nan kafin ya sami lafiya..."
Dr ya jinjina kai kafin ya mik'a hannu wa Naseer sukayi masabaha Naseer d'in ya wuce....
***
"Madu ka duba runfar nan da kyau don jiya wllhi nidai naji kaman motsi cikinta, yanzu haka macijin kwanakin nan ne ya dawo....." D'aya saurayin ya fad'i yana nad'e hannun riga..
Sandar gora dake gefensa ya rarumo kafin ya mik'a wa abokin wata daushiyar itace yace "Kai alk'ur'an yau macijin nan zai bak'unci lahira don uwarsa ni na tabbata turensa aka mana angama runfar mu tafi ci gaba, mukar tsinanne yaje yace ma wanda ya turosa mun karsa..."
Yana ida fad'in haka suka shiga bugun shirgin kwalayen dake cikin rumfar
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*61*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ihun mutum da suka jiyo daga cikin shirgin ya sanyasu dakatawa da bugun cikeda mamaki.... Aiko basu ida mamaki ba saida sukaga dartijuwan mace ta fito cikin shirgin maimakon ta tsaya ta basu bayani sai artawa da tayi a guje dukda ciwo da jikinta ke mata domin kam ta bugu dukda ba jikinta direct aka samu ba.....
Matasan nan maimakon abin ya basu tsoro saima dariya da ta basu.... Mamakin yanda akayi ta shige shirgin nan suka dingayi.... Madu yace "Kai Mati k'ila dai macijiyar ce ta rikid'a ta zama mutum...."
"Toh waya sani mudai mun jibgeta ta kuma dawowa bazamu fasa ba..." Ya k'arashe yana jifa da sandar hannun sa....
Saida tayi gudu sosai kafin ta samu wani k'asan bishiya ta d'an d'aga bujenta had'i da ciro 'yan kud'ad'en data sata a kantin su Madu wanda ta tabbata zai isheta kud'in mota.... Amma da kafin ta bar gari tana buk'atan ganin 'ya'yanta Lubna da Kabeer, tasan duk yanda akayi watsestten yaron nan Naseer ya kame mata d'a... Zuciyarta ya shiga bugawa da sauri da sauri sanda ta tuna komai ka iya faruwa da Kabeer, bata k'aunar wani abin ya samesa... Lokaci guda taji tana son ganinsa duk hanyar da zatabi ta gansa zata bi, tunaninta guda da ya addabeta shine samun mafaka kafin ta gama abinda zatayi a garin ta cika ma rigar ta iska, wata zuciya tace toh ki koma rumfar samarin nan.... Toh kuma idan ta koma suka fahimce ta masu sata fah....?? Rafka uban tagumi Innah tayi tana tunanin lamarin ga bak'ar yunwa dake azalzalanta..... Ta shiga tunanin rayuwar daula da tayi a baya, mulki babu kalan wanda batayi ba yau gata nan a tagayyare wajen barci ya gagareta balle abinda zata sanya a bakinta.... A hankali ta kuma gyara kwanciyarta jikin bushiyar ga k'ashushuwanta dake faman mata ciwo....
***
Bai komo gidan ba sai wajajen bayan la'asar yanda ya tarar Abbu da mai d'akinsa Kaltume suna kwararo bayani wa Aunty Saudat da Momy yanda akayi suka had'u har sukayi aure....
Abbu yaci gaba da fad'in "Sanda na baro Nigeria da dukiyata wanda na amsa daga wajen Sa'oud Santana da sunan kud'in auren d'iyata Saudat ban koma k'asarmu Morocco ba sai na yada zango a k'asar Mali birnin Bamaco.... Ban damu na koma Casablanca ba sabida na riga na masu sallama na fita da fita na ne.... Toh a k'asar Mali naci gaba da juya dukiyata hankali na kwance ba tareda tunanin wani hali na baro d'iyata ba.... A nan k'asar Mali na koyi yaren Hausa domin yanda nake zaune ma yankin hausawa ne 'yan asalin k'asar Nigeria... Mutanen da nake zaune dasu na yarda dasu su suka cutar dani suka kassarani, suka yashe duk wani dukiya nawa sukayi tafiyar su, wanda har rana mai kaman ta yau bansan yanda suka nufa ba... Mahaifin Kaltume shine kawai mutumin da bai gujeni ba don duk wanda nake taredasu suke cin arziki k'ark'ashina daekariyar arziki ta sameni gujemin sukayi..... Shi kad'aine bai guje ni ba kuma yaso jin gaskiyar labarina... Ban b'oye masa komai ba yanda ya nuna min nayi kuskure na tapka babban kuskure A DUNIYAR MU, ya umarceni na zo k'asar Nigeria na duba d'iyata... Ban iya zuwa ba sabida bansan da wani ido zan soma duban Saudat ba.... Duk yanda yaso nazo Nigeria nak'i zuwa, ina nan zaune a birnin Bamaco har ya aura min d'iyarsa Kaltum sabida yanda yaga na koma tamkar wanda baiso yaci gaba da rayuwa.... Toh bayan aurenmu da Kaltum Allah yayi masa rasuwa, nasan nayi rashi sannan Duniya ta kuma bani tsoro, na d'auki alwashin zuwa k'asar Nigeria na fuskanci d'iyata koda bazata yafeni ba sannan na sanar da Naseer koshi wanene koda Sa'oud bazai bari ba. Saidai kuma da nazo na tarar Sa'oud ya rigayemu gidan gaskiya sannan bai sanar da d'an 'yaruwata wacece mahaifiyar sa ba....." Sosai yake duban Aunty Saudat dake zuban hawaye kana yaci gaba da fad'in "Saudat ki yafe ni, ki yafeni dan Allah wllhi naga iftila'i na rayuwa da dama A DUNIYAR MU, kuma na yarda duk wanda ka zalunta koda bawanka ne ba d'anka ba Allah zai saka masa, zukatan mutane sun cika don son duniya da abinda ke cikinta A DUNIYAR MU, bamu hangen lahirarmu burinmu kawai yaya zamu sami duniya tako wani irin hanya.... Iyaye sukan saida 'ya'yansu ta hanyar auren dole duk don su sami duniya basu tunanin had'arin da hakan ka iya haifarwa, su saida farin cikin d'iyoyinsu duk akan duniya, ina fata iyaye masu irin wannan d'abi'a zasu hankalta su gyara... Kuma na yarda tarin dukiya bashine jin dad'i A DUNIYAR MU ba, kwanciyar hankali yafi komai dad'i, Saudat ki yafe min dan Allah kinji d'iyata....."
Baikai aya ba sai gani yayi ta taso ta rungumesa tana matsan hawaye... Cikin muryar kuka take fad'in "Abby na yafe ka, na yafeka duniya da lahira.... Allah ya yafemu gaba d'aya...."
Naseer dake tsaye daga k'ofa baisan sanda murmushi ya kufce masa ba, Allah sarki ashe Aunty Saudat jinin sa ce, ashe 'yar uwarsa ce.... Lokaci guda ya saka d'an yatsar sa had'i da goge idanunsa... Hannun mutum ne yaji ya dafa sa ya d'an juyo yana duban ko wanene, Fawaz ne shima murmushi kwance saman fuskar sa... A hankali Naseer ya furta "Alhamdulillah... Fawaz zumuntar mu ta k'aru....." Fawaz bai iya cewa komai ba sai rungume Naseer da yayi.. A tare suka k'arasa cikin parlorn..... Abbu na dubansu da murmushi saman fuskar sa ya bud'e masu hannu yana fad'in "Kuzo 'ya'ya na....." Babu musu suka k'arasa suka rungume juna
Momy da Kaltum suka d'an share hawayen da ya zubo masu.... Lubna da Salma dake tsaye jikin staircase a hankali suka k'araso cikin parlorn suma murmushi kwance saman fuskar su....
Naseer ne ya d'an juyo yana duban su, Salma kam saurin sunkuyar da kanta k'asa tayi, k'arasawa yayi tsakiyarsu ya kamo hannayensu suka k'araso har gaban Abbu kafin Naseer yayi introducing d'insu matar shi da kuma k'anwar shi, Abbu ya kuma jin dad'i ya sanya masu albarka.. Hankula suka d'an soma dai-daita a wannan family....
Lubna ce ta tuna sak'on da Deeni ya bar mata cikin sauri ta mik'e ta nufi d'aki ta d'auko sak'on.... Kai tsaye ta bawa Naseer tana masa bayani...
K'irjinsa ya yanke yayi wani irin fad'uwa, donshi yanzu har tunanin b'ullowar wani sabon Al'amari yake.... Gaba d'aya parlorn akayi tsit ana duban Naseer dake k'ok'arin bud'e envelope....
Wasu takardu ne suka soma fad'owa daga cikin envelope d'in tamkar wasik'a.... A hankali ya soma warwarewa, baisan yaya akayi ba saiji yayi bakinsa na karanta wasik'ar taryan-taryan...
_Assalamu alaikum wa rahmatullah.... Zuwaga d'ana Naseer... Wasiyace da ya kamata na sanar dakai tuntuni saidai Allah bai k'addara zan sanar dakai da bakina ba....._ Kasa ci gaba da karatun Naseer yayi sai k'ura wa takardan idanu da yayi....
Abbu ne ya k'arasa ya amshi takardan kana yaci gaba da karantawa kaman haka
_Naseer d'ana nasan duk daren d'ad'ewa gaskiya zata bayyana maka A DUNIYAR MU, amma ka sani duk randa wannan Al'amari ta bayyana maka kada kayi fushi dani domin kuwa na aiwatar da hakan ne sabida tunanin shine maka dai-dai..Naseer na b'oye maka asalin mahaifiyar ka ce sabida tsananin soyayyar da nake maka bana son ka tashi cikin maraicin rashin uwa... Amma daga baya na fahimci dole duk daren dad'ewa haka na iya bayyana maka cewa Dije ba ita ta haifeka ba.... Idan wannan Al'amari ya bayyana maka kayi mana addu'a da fatan dacewa nida mahaifiyarka Hidaya... Ka sani kaida Lubna ina k'aunarku fiye da komai na rayuwata, sannan ko bayan babu ni ka rik'e 'yar uwarka kuma k'anwar ka da amana sabida ku biyu tak Allah ya mallaka min A DUNIYAR MU.... Duk da bani na haifi Kabeer ba ban yarda ku canza sa a matsayin wa ba koda gaskiya ta bayyana maku.... Jikina na bani bazaka dawo daga makaranta har mu kuma had'uwa A DUNIYAR MU ba, amma idan har Allah ya raba ganawa zanbar wannan sak'o ma direba na Malam Ladan har ya isa gareka.... Ina maka wasalci da gaskiya da rik'on amana a duk yanda ka tsinci kanka... Allah yayi maku albarka gaba d'aya ya d'ayyiba zuri'arku...Ameen... Daga mahaifinka SA'OUD NASEER SANTANA...._
Abbu yana ida karantawa ya linke takardan.... Naseer kam jigum yayi yana saurare har aka ida karantawa.... Ashe Kabeer ba yayansa bane, kai bai tab'a tunanin a duniya ana samun mutane irin Innah da Kabeer ba wannan shine dalilinsu na son ganin bayansa da k'arfin gaske, ashe shid'in barene acikin su ALLAH Sarki duniya abin tsoro, sai gashi duk wasu tarko na mugunta da sukayita kafa masa Allah yana tseratar dashi..... Yana cikin tunanin yaji Lubna ta rik'o hannunsa ta kwantar da kanta cikin jikinsa tana hawaye....
Fawaz ma k'arasawa yayi ga mahaifiyarsa suka rungume juna suna hawaye... Fad'i yake "Mum ashe Dad ba d'an Abbah bane... Shiyasa mana, shiyasa suka kashe Abbah, ashe ba jinin sa bane.... Ashe nan ba gidanmu bane Mum, .... Mum na gaji da Nigeria, zan tafi nikam bazan kuma iya ci gaba da rayuwar k'asar nan ba... Tunda na dawo babu abin arziki da na tarar sai na akasin haka.... I'm leaving this country for good.... Na gaji wllhi...." Ya k'arashe muryar sa na tsananin rawa...
Hannun Naseer yaji saman kafad'arsa... Ya d'ago yana dubansa... Wasu hawaye na kuma zubo masa ya rungume Naseer yana fad'in "Uncle I'm tired, zan tafi wani wajen daban and start a fresh...." Ya kasa ci gaba da magana sabida kuka da yaci k'arfinsa... Rungumesa sosai Naseer yayi cikin k'arfin hali don dolensa ya zama very strong... Cikin kwantar daehankali ya soma magana ma Fawaz...
"Fawaz we're still family.... Ka daina cewa zaka tafi kar ka mance ko Abbah bai had'amu ba Abbu ya had'amu, Fawaz kai jinin mu ne ko ina kaje kazo.... Sannan baka da gidan da yafi nan, I'm still your only Uncle..... Kar na kuma jin kayi magana irin haka kaji koh... Yanzu gaba d'aya tunani zamuyi yanda zamu fuskanci wannan Al'amari, idan kana kuka kuma Lubna mai zatayi, be a man kaji"
Jinjina masa kai kurum Fawaz yayi ya shiga share hawayen da suka wanke masa fuska..
Naseer ya d'an tattare naman goshinsa had'i da fuzar da iska kafin ya d'an ware hannaye yace "Har yanzu babu labarin Innah, babu wanda ya ganta... Shi kuma Yaya d'azu daga station nake muka wuce asibiti sakamakon ruwan acid d'in da ya zuba wa k'afafunsa likitoci sunce saidai a yanke k'afafun.... So yanzu na bari za'ayi aikin...."
Aunty Saudat ce ta dubesa kana tace "Gaskiya Naseer kanada imani da tsananin tawakkali waye zai tsaya kula mutumin da ya farauci rayuwarsa har ya kula da jinyar sa.... Ire-irenka k'alilan ne bayan duk kalan abubuwan da suka maka...."
D'an k'ak'aro murmushi Naseer yayi kana yace "Aunty duk wanda ya k'ullaceka da sharri ka saka masa da akasin haka zaka kasance saman shi A DUNIYAR MU, sannan a lahira ma kaine a sama..... Fatana Innah da Yaya su tsaya a zartar masu da hukuncin da ya kamace su, don bana so su tafi duniya ta koya masu hankali, su karb'i hukuncinsu da sauran mutuncin su zaifi masu sauk'i kuma muma zaifi mana sauk'i tunda babu yanda muka iya duk yanda mukaje muka zo sud'in namu ne...."
Gaba d'aya mutanen parlorn jinjina halin Dattako irin Naseer suke, babu kaman Abbu wanda murmushin dake saman fuskar sa ta kasa gushewa....
Momy ma kallonsa take tana murmushi tana jin sonsa har cikin ranta tamkar ita ta tsuguna ta haifesa....
****
Bayan gari Innah ta nufo duk ta d'aid'aice ta fice hayyacin ta, nan ta hangi wasu 'yan mata sai safaran abinci suke suna kai ma customers d'insu.... Innah tayi hamma ta had'iyi miyau.... Da jan k'afafu ta isa rumfar 'yan matan nan....
Budurwar sai faman cakalan chewing gum take tana k'wark'wasa sanda ta nufi samarukan tana raba masu abincin.... Innah ta rakub'e daga can gefe tana hangan yanda suke loman abincin....
Saurayi guda ne ya lura da Innah wacce ta kafesu da idanu... Wani mugun tsuka yayi kafin yace "Ke Piky da Allah kizo ki kori wannan almajiran tsohuwar ai saita sa mutum ya k'ware..."
Shiko d'ayan saurayin cewa yayi "Ni k'yama ma ta bani wannan ai zata sanya mutum amai....."
Cikin sauri wacce suka kira da Piky ta k'araso wajen tana k'wark'wasa take fad'in " yaya yaya wacece a wajen.....?" Kallon mamaki take bin Innah dashi kana tace "Ke chuuss lafiya, me kikeyi a nan...."
"Abinci zaku taimaka min dashi don Allah, wllhi 'yan kud'ad'e na gaba d'aya an sace an yasheni, ku taimaka min da abinci don Allah...." Innah ta fad'i cikin wani irin murya...
Dariya suka kwashe dashi kana budurwar tace "Ke tsohuwar kilaki kar ki raina ma kanki hankali, ce maki akayi muna taimako ko kuma kinga alamun taimako a tattare damu.... Gwara tun wuri ki cika ma rigarki iska kafin Magajiya ta fito ta taddaki, wannan ke daga ganin naki zamanin baki sami kasuwa da yawa ba shiyasa kika d'aid'aice haka... Tashi ki b'ace min a nan...." Ta k'arashe tana watsa wa Innah sauran ruwan wanke-wanke
Innah ta mik'e da k'yar da zummar tafiya nan idanunta ya sauk'a saman teburin da samarukan nan ke cin abinci, karan sigari ta hanga Wanda rabonta dashi tun tana cikin sauran hayyacinta, tana tsananin buk'atar zuk'an sigari koda bata sami abinci ba.... Tattare fatarinta tayi ta faki idanun mutanen dake wajen kafin ta daka wani tsalle takai ma karan sigarin nan capka lokaci guda ta ari na kare ta arce a guje.....
Ai samarin nan a d'ari suka mik'e suka bi bayanta suna watso ashariya.... Tuntub'e da Innah tayi karan sigarin ta fad'i k'asa ya sanyata zubewa a k'asa itama... Wad'annan samari babu ko d'and'anin tausayi cikin zuciyarsu dukda shekaru irin na Innah basu fasa k'wallo da ita ba..... Suka shiga janyota a k'asa tamkar kariya.... Tuni karuwan dake layin sunyi chaaa suna kallo don dama abin kallo bai masu kad'an...
"Wllhi yau sai mun maki tsirara dan uwarki, zigidir zamu maki yanda gobe bazaki sake sata ba.... Kai Aska kwab'e mani fatarin shegiya...." Ya k'arashe yana zuge belt d'in wandonsa...
Innah ihu take tana rok'insu su mata rai kar su daketa.... Inaaa tamkar aza masu wuta take..... Karuwan kuwa sai shewa suke suna tafi babu mai yunk'urin ceton Innah...
Jikin wata k'arfe su Aska da abokinsa suka d'aure Innah bayan sun kwab'e d'an bujen nata suka shiga wasafata babu akan karan sigarin naira ashirin babu d'igon imani cikin zuciyarsu balle tausayi.....
Tun Innah tana ihu idan an sauk'e mata bulala d'aya har ta daina.... Saida Magajiya tazo wajen a d'ari tana fad'in "Haba Aska wai lafiyarku wani iya shege ne wannan, yanzu mai wannan tsohuwar ta maku kuka tak'uneta jikin k'arfe kuna bugu inyi....?"
"Uwar daba ki fita kawai daga wannan zancen sata tayi kuma kinsan hukuncin b'arawo a layin nan..."
Girgiza kai Uwar daba tayi kana tace "Mai ta sata...?"
"Sigari ta sata..." Ya bata amsa kai tsaye...
"Yanzu kan sigari ne kuka farfasa ma tsohuwar nan jiki.. Kwance ta zan biya...." Ta k'arashe tana cusa hannu cikin riga...
Saida ya kuma kwand'arawa Innah bakin k'arfen jikin belt a tsakar ka kafin ya kwanceta... Ta kuwa kuma sakin k'aran azaba....
Uwar daba ce ta janyota har cikin gidan sauran karuwan na biye da ita suna taunar cingam...
****
Mamy hankali ya soma dawowa jikinta, ta soma dawowa asalin Asma'un ta, yau har wanka tayi ta cakare ado cikin lallausar leshinta, da kanta ta shiga kitchen ta d'aura masu breakfast, gaba d'aya k'ok'arinta ta karkato hankalin Ali Safwan ne ya kuma dawowa gareta... Shareefah kam tuni ta fice ganin Dr Siraj, don sun riga sunyi waya dashi yace da ita ta same sa a asibitin sa basai taje TH ba, hakanma sai yafi mata sauk'i...
Kai tsaye d'akin Affan ta soma nufa don Daddy kam ya mata iyaka da b'angaren sa, zuciyarta sai faman bugu yake sanda tayi sallama a k'ofar Affan.. Sanin darajan Sallama ne kurum ya sanya Affan amsa mata.... Kallo d'aya yayi mata ya ganta d'auke da k'aramin tray sai k'ok'arin k'ak'aro murmushi take wanda yafi kama da yak'e...
Cikin wani irin murya mai cikeda fargaba Mamy tace "Son I... I brought you your breakfast..."
Baiko kalleta ba yaci gaba da abinda yake...
Ganin bazai kulata ba ya sanyata ajiye 'yar tray d'in saman rug... Ta d'an tako kusansa tana fad'in "Affan da kaina na girka maka don Allah kazo kaci kaji..."
Cak ya tsaya ya daina abinda yake ya juyo yana dubanta kafin ya girgiza kai ya maida dubansa ga mirror yana mai fad'in "Bazanci ba musamman da naji kece kika girka...."
Murya na rawa Mamy tace "Affan mai yasa...."
Cikin ko inkula yace "Because everything prepared by you is contaminated....."
Mamy taji wasu hawaye suna sauk'o mata, shikenan iyalanta bazasu kuma yarda da ita ba.. Shikenan zamansu ya koma babu yarda... A hankali ta juya ta fice daga d'akin nasa cikin wani irin sanyin gwiwa, had'i da takaici da danasani mai tarin yawa...
Parlor ta dawo ta zauna saman kujeran dining ta shiga rusa kuka mai tsuma zuciya.... Har Delu ta fito ta taddata a haka...
Mamy ta d'ago kai tana duban Delu wasu sabbin hawaye suka shiga gangaro mata, cikin kuka take fad'in "Delu bazasu kuma yarda dani ba... Shikenan na zamto abin zargi da kokonto had'i da shakku a garesu... Kaico kaicon son zuciya irin nawa, wllhi nayi nadama nayi danasani maras iyaka Delu....."
Delu ta goge hawayen da suka d'an fito mata kana tace "Kiyi hak'uri Hajiya duk tsanani na tareda sauk'i sannan watarana komai zai wuce ya zamto labari...."
Cikin kuka Mamy ta katse ta da fad'in "Yaushene wataranan yaushene komai zai wuce.. Delu da tunanin Azeema kurum aka barni wllhi rayuwa bazata min dad'i A DUNIYAR MU ba, ina iyaka k'ok'arina wajen ganin na dawo da zamantakewar da muke ciki a baya ba don jin dad'i na bane Delu saidon na dawo ma iyalaina farin cikinsu da suka rasa.... Wllhi Delu sam ban damu da farincikina ya dawo ba, damuwata kawai shine nasu ya dawo, nikam nasan har na koma ga mahallici na farin cikina bazai kuma dawowa ba A DUNIYAR MU.. " Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya...
Tausayin Mamy da iyalanta ya cika zuciyar Delu....
****
K'ara ya saki sanda ya dubi k'afafunsa yaga tun daga cinyarsa babu komai ya zama dungulumi.... Cikin wani irin kuka yake fad'in "Where are my legs... Ina k'afafuna.. What happened to me.. Meye ya sameni? A ina nake....?" Duk wad'annan tambayoyi ma kansa yake yinsu... Lokaci guda ya d'ago idanu ya dubi Dr da Naseer tsaye gefen gadon nasa....
Fincika yayi zai cakumo Naseer ya kasa, cikin wani irin huci da karaji yake fad'in "Naseer mai kayi min, what did you do to me... Mai kayi min Naseer.."
Kafin Naseer yakai ga basa amsa sukaji an bud'e k'ofa an shigo... Ba kowa bane illa Fawaz wanda idanunsa suka kad'a sukayi jazir...
Lokaci guda Fawaz ya soma fad'in "Babu abinda ya maka sai alkhairi, abinda LA shuka shine kake girbewa Dad, na tabbata badon Uncle Naseer ya taimaka ya kawo ka asibiti ba da yanzu ka zama tarihi... Da ka cutar da kanka shi sai ya taimaka maka.... Dad wannan ya zama izna a gareka, kayi k'ok'ari ka tuba a zaman da zakayi a gidan yari, don na tabbata a can zaka k'arashi rayuwarka... Wannan shine rayuwar da ka zab'i jefa kanka ciki... D'unbin Al'umman daka zalunta Allah bazai barka ba, kayi k'ok'ari ka nemi yafiyarsa tun A DUNIYAR MU sannan ka amshi hukuncin da za'a yanke maka hannu bibbiyu domin shine tsirar ka..... Ga wannan rubuta wa Mum takardanta, don bazan bar k'asar nan ba sai na tabbata batada sauran alak'a dakai..."
Kallon Fawaz yake hawaye suna gangaro masa... Zaiyi magana Fawaz ya dakatar dashi ta hanyar d'aga hannu yana mai kuma mik'a masa takardan da pen...
Tunda Alh Kabeer yake nadaman rayuwa bata tab'a shigansa ba sai yau.... Hannayensa suna rawa ya rubuta wa mahaifiyar Fawaz saki.... Aiko yana gama rubutawa Fawaz ya d'au takardan ya linke ya saka a aljihu... Har ya juya zai soma tafiya yaji hannun mahaifin nasa ya rik'osa..
"Son ka yafeni dan Allah.. Kuma kace Saudat ta yafeni ina sonta wllhi duk sharrin Innah ce, sharrin Innah ce nason d'ukan fansa akan duk wani jinin mahaifiyar Naseer..."
A tare Naseer da Fawaz suka kuma juyowa suna duban Alh Kabeer jin wani sabon Al'amari na shirin kunno kai...
"Fansa!!! " Naseer ya maimaita a fili...
Alh Kabeer ya jinjina kai kafin yaci gaba da fad'in "Iya tsawon rayuwar da Innah tayi A DUNIYAR MU tayisa ne da burin d'aukan fansa akan duk wani jinin Hidaya da zata sami dama akansa, wannan shine dalilinta da tasa aka aura min Saudat ta zugani mukayita d'aukan fansa akanta... Innah ta kansace tana aikatau wa mahaifiyarka Naseer a lokacin da ta rabu da mahaifina... Mahaifiyarka ta tsangwame mu daga Innah har ni d'anta bata bari ba badon komai ba saidon tsanar bak'in fata da tayi... Wannan shine babban jigo, nuna banbancin launin fata shine asalin kunnuwar wutan duk wani musiba da tashin hankalin da muka tsinci kawunanmu ciki A DUNIYAR MU..." Tas Alh Kabeer ya labarta masu duk yanda abin ya kasance, rasa mahaifiyarta da Innah tayi da duk wani shirinta na d'aukan fansa har kisan Sa'oud Santana da sukayi... Daga k'arshe ya sanar dasu cewa duk nadaga cikin shirinsu na d'aukan fansa akan Naseer k'one gidan gonar Ali Safwan da yayi... Kisan mahaifin Deeni da sauransu...."
Kan Naseer yayi wani irin bugawa... wannan wata irin rayuwa ce mai cikeda burin d'aukan fansa.. Wacce irin rayuwa ce da babu yafiya, wacce irin rayuwa ce da babu tausayi balle imani, saikace a jahiliya period, lokacin da za'a d'auki shekaru ana gaba k'abila k'abila... Ashe har yanzu hakan takan faru bayan tuni muslunci ya ijeyemu k'ark'ashin inuwa guda k'ark'ashin kalma guda... Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un... Kalman da yayita nanatawa kenan cikin zuciyarsa, sai yanzu ya kuma gane yanda tsanar da Innah tayi masa ya samo asali... Duk yanda zaiyi zaiyi k'ok'ari yaci gaba da yak'an Racism tsakanin Al'umma.. Musulmi d'an uwan muslumi ne irrespective of tribe ko kuma launin fata, haka muslunci ya koyar damu.... Duniya ta kuma baiwa Naseer tsoro jin irin muggan abubuwa da Innah tayisu A DUNIYAR TA duk da sunan d'aukan fansa, ciki harda kisan mahaifiyar sa da sukayi itada mahaifiyarta... Baisan yaya akayi ba baisan yaya ya iso gida ba shidai kawai yaga Fawaz na bud'e masa k'ofar mota ne, yana fata tashin hakulan da suke faman shiga ciki suzo k'arshe A DUNIYAR Su...
***
Daddy yasa hannu yana share hawayen sa sanda Malam yaci gaba da fad'in "Alh duk iya istiraha da zanyi gameda wannan d'iya taku bani ganin komai sai jerin kabaruruka... A gaskiya ina tunanin Allah ya amshi abinshi amma kasan sanin gaibu sai Allah, ban isa nace ta mutu ba ko tana raye, saidai muci gaba da addu'a idan tana raye Allah ya bayyanata.. Idan kuma Allah ya amshi abunsa sai mu mata addu'an dacewa domin duk wanda ya kashe wani ranar gobe k'iyama da raunin zai tashi ya kuma damk'e wanda ya kashe shin yana tambayarsa mai yayi masa ya kashe sa... Muyiwa wannan yarinya fatan dacewa, Allah ya gafarta mata kurakurenta sannan ayyukanta na alkhairi su bita... "
Daddy bai iya amsawa ba sai dafe kansa da yayi da hannunsa yana kuka sosai... Mamy dake tsaye jikin k'ofa kuka sosai ya kufce mata, cikin sauri ta fice tana kuka sosai....
A hanya ta had'u da Shareefah dawowarta kenan daga asibiti.. Rungume Shareefah Mamy tayi tana kuka sosai take fad'in "Shareefah Azeema babu... Azeema babu, Azeema ta tafi ta barmu.... Laure ta kashe Azeema....."
Kuka sosai Mamy take lokaci guda suka zube saman kujera daga ita har Shareefar, kuka Shareefah take tana tuna rayuwarsu da Azeema, Allah sarki 'yar uwarta... Tana tsananin k'aunar Azeema don batada k'awa kuma aminiyar da ta fita.... Shareefah sai taso tafi Mamy shiga tashin hankali...
Affan sai ya zama abin tausayi, bai tab'a sanin na k'aunar Azeema ba sai yanzu, koda ba k'aunar aure yake mata ba yanajin wani Al'amari a tattare da ita, Allah sarki Azeema bazata fice a zukatan wad'annan bayi ba...
Yanda Mamy ta koma gaba d'aya ta kuma d'aid'aicewa sai ta bawa Daddy tausayi, musamman da ya lura ta jingina ma kanta hakkin mutuwar Azeema dukda ba wai sun tabbatar ko Azeemar ta mutu bane.. ... A hankali ya turo wheelchair d'in nasa har ya shigo cikin d'akin... Mamy ta d'anyi k'ok'arin saita kanta ga k'irjinta dake bugawa don rabonta da taga Daddy a side d'inta ta mance..
D'an gyaran murya yayi kafin ya soma mata magana cikin kwantar da hankali... "Asma'u ki rage damuwar nan da kike ciki, bamu da tabbacin Azeema ta rigayemu gidan gaskiya ko tana raye.. Andu'a shine gaba, muci gaba da mata addu'a har Allah ya bayyana mana ita, idan kuma ta rigaye amsa kiran mahaliccin mu Allah ya datar da ita da rahamarsa, wannan duniya dukanmu bak'ine cikinta kowa zai tafi babu wanda yazo zama... Ki kwantar da hankalin ki kinji koh, yawan kukan ki na nufin tashin hankalin yaranki ne... Allah yasa mu dace..." Daga haka ya turo kekensa ya fice ba tareda ya jira amsar Mamy ba...
Tabi bayansa da kallo tausayi da soyayyarsa na kuma ratsa zuciyarta..
Mamy rungume da hoton Azeema cikin k'irjinta ta kwana... Idan ta d'ago hoton tana ganinta sai ta kuma tuna rayuwarsu a gidan Laure... Allah sarki Azeema kyawawan ayyukan ki na alkhairi su biki...
Kwana kusan uku Mamy tana nan a haka yau Daddy yace su shirya zasuyi tafiya gaba d'aya... Tunda Mamy taga an d'auki hanyar Jama'are hankalinta ya tashi, ta tuna zancen boka cewa idan ta shiga garin haukacewa zatayi... K'aramin littafin addu'o'i na Hisnul Muslim dake cikin jakanta ta ciro ta shiga karanto azkar don yanzu ba'a rabata da azkar musamman na safiya da maraice...
Affan na tuk'awa Daddy na gaba itada Shareefah suna gidan baya... Affan ne yayi gyaran murya ya tambayi Mamy location d'in bishiyar da tace an birne summon a wajen...
Mamy ta basa amsa dai-dai ba tareda tab'in hankali ba, jin bata haukace ba har suka shigo garin ya kuma tabbatar mata boka jan mak'aryaci ne, babu wanda ya kaisa k'arya duk duniya, boka baya baka komai saidai ya kaika ga tab'ewa da kuma halaka.. .
Har k'ark'ashin bishiyar sukak'araso, ta shiga tuno zuwansu wajen da Laure, sabon tashin hankali ya ziyarci Mamy... K'unshe bakinta tayi tana hawaye tana ji inama hannun agogo zai koma baya da bata aikata abubuwan da ta aikata ba...
Wata mota ce tayi parking daga can gefe dasu, Su Malam D'ayyabu da Alaramma Mukhtari suka fito daga cikin motar suka k'araso gasu Daddy... Nan suka buk'aci su Daddy su matsa daga k'ark'ashin bishiyar... Abin sallah suka shimfid'a daga can gefe suka zauna suka soma karanto addu'o'in karya sihiri da asiri kaman yanda sunnah ya karantar... Can suka hangi wani kusufi k'asar bishiyar daga gefe yana hayak'i sosai... Jikin Mamy ya shiga karkarwa.. lokaci guda ta runtse idanunta hawaye na gangaro mata don tuni komai ya shiga dawowa sabo a kwanyarta...
K'arasawa sukayi wajen suka kuma karanto addu'o'i had'i da basmala da koran duk wasu shaid'anu dake wajen suka soma tonon dai-dai wajen...
Daddy kam hawayene kurum ke zuba daga idanunsa sanda aka ciro k'ullin.... Shareefah da Affan zukatansu ya kuma girgiza, tsoron Duniya ya kuma cikasu...
Mamy kam koda zata zama gurguwar bata damu ba muddin Daddy zai sami lafiya...
Su Malam D'ayyabu suna warware wannan k'ulli hayak'i ya soma tsartsafowa daga k'afafun Daddy.... Addu'o'i suka kuma yi suna tofawa Daddy a k'afafun sa lokaci guda Alh Ali Safwan yaji k'afafunsa sun soma motsawa... Bismillah yayi sanda yaji k'arfi ya ziyarci k'afafun nasa...
Gaba d'aya suka bisa da kallo sanda sukaga yana mik'ewa daga wheelchair d'insa.
****
Jigum Innah ta zauna gaban shirgin wanke wanken gidan karuwan wanda idan batayisu ba toh kuwa tabbas batada abinci... Tana nan tsugune gaban lodin wanke wanken taji Shazali d'an daudu ya fito yana shewa yana tafe hannaye yana fad'in "Wllhi an kuma, an kuma Satan sigarin oga Aska.. Cahpp ayyye b'arauniya bataji dad'i ba wllhi wllhi Oga Aska kar ka yarda wannan karan babu sassauci ehe..." Ya k'arashe yana gyara d'aurin kwali had'i da tafe hannaye da cinya uwa mace...
Aiko Oga Aska ne ya fito yayi kan Innah a d'ari.. Ta zabura zata gudu ya sharb'ota sai cikin kwanukan wanke wanke...
'Yar k'aramar Aska ya ciro a gefen wandonsa ya shiga wasata jikin garu gashi ya danne Innah babu halin gudu...
Innah murya na rawa take fad'in "Wllhi ban sata ba, wllhI sharri ne dan Allah kaji k'aina... Wai mai zakamin ne kake wasa aska..
Dariya ya bushe dashi kana yace "Bakiji sunana ba Oga Aska, kimin wancan karan na maki uzuri ban maki tsattsauran hukunci ba toh yau zakisan dalilin kirana Aska da akeyi a gidan nan.. "Ke Shazali zo ki d'aga mini bujenta..."
Shazali ya k'araso yana k'wark'wasa yake fad'in "'yar uwa sai hak'uri abinda ake wa yara maza shi za'a maki yau da tsufarki..."
Innah gabanta yayi wani irin bugawa ta shiga kururwa sanda ta fahimci mai ake shirin mata
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*62*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Innah bata fasa kururwa ba tana neman agaji da d'auki, kuka take shar-shar da hawaye tana fad'in "Oga ka min rai na tuba na tuba wllhi.. Ko kallon sigari bazan kumayi ba balle na sata, dan Allah kamin rai wllhi ni uwar wasu ce...." Ta k'arashe sabbin hawaye na kwararo mata....
Dariya Shazali ya kwashe dashi gashi yak'i sakin Innah sai kakkauda kai gefe yake shi a dole kunya yakeji, yana gyara d'aurin k'irji had'i da kame hab'a yake fad'in "Oh ni Shazali abin kunya dai bai k'arewa a gidan nan... Kaga Oga i hak'uri ka k'yaleta kasan mu mata rauni garemu....."
Bai kai aya ba Aska ya daka masa tsawa da fad'in "Nace ka rik'e min ita, gobe ko ajiye mata sigari akayi tsakankanin yatsunta saidai ta tsallake...." Ya k'arashe yana k'ok'arin had'e bakin askan sa.... Innah ta danna ihu ganin da gaske wannan tantirin yaro ba afuwa zai mata ba.... Cizon data gantsarawa Shazali ne ya sanyasa sakinta a d'ari ya mik'e yana kame yatsar sa da Innah tayi kusan gutsirewa.... Tuni Innah ta arce ta nufi waje... A dai-dai k'ofa suka kusan yin karo da Uwar daba...
"Yaya haka Chuss waye ya biyoki haka ko 'yan hisba ne suka zo kame....?"
Haki Innah take tana duban Uwar daba dai-dai sanda Aska ya k'araso wajen a d'ari... Innah ta kuma mik'ewa zata arta Uwar daba ta tarota...
Aska na huci yake fad'in "Wllhi Uwar daba ki daina shigar ma wannan 'yar iskar fad'a don takaini bango, babu hali na ijiye sigarina sai ta sata..."
Tafe hannaye Uwar daba ta shiga yi ga d'aurin kallabinta saman goshi wanda hausawa ke cema ture Kaga tsiya...
"Ni wllhi Chuss da Aska kunfa isheni a gidan nan... Masifar ku ta isheni.... Ke wace irin bak'ar mayya ce da bazakiyi zuciya ki daina masa sata ba.. Inyi haba.. Wllhi gaba d'ayanku zan sa Gundumi ya maku hukunci tam.... Ni na gaji da masifarku...."
"Amma ai itace take fara janyowa, wllhi kika kuma min sata kinji na rantse sai kinsha Aska shegiya tsohuwar banza...." Ya k'arashe yana maida askar sa gefen aljihu...
Uwar Daba ta rakasa da harara har ya fice kafin ta dawo da dubanta ga Innah wacce ke lab'e bayanta tana faman muzurai kana tace "Toh ke kuma kina jina... Wllhi Aska baida mutunci matan da suka d'and'ani azaban askar sa a gidan nan ba kad'an ba... Inai maki gargad'i kar ki zamto d'aya daga cikinsu tam... Wuce kije kimin wanke-wanke ko kiyi niyyan azumin da babu lada, kinsan dokata ba'aci a bulus...." Daga Uwar Daba shigewa tayi tana taunar chewing gum..
Shazali kuwa har lokacin bai daina rawan zafin cizon da Innah ta gantsara masa ba...
****
A tare Shareefah da Affan suka k'araso suka rungume Daddy su duka suna hawaye....
Mamy ma hawaye ne kurum ke fitowa daga idanunta, tana son rungumar mijinta saidai bazata iya hakan ba... Kunya abinda tayima bazai barta ta tink'ari mijinta ba... A hankali ta sadda kanta k'asa....
Daddy ya k'arasa wajensu Malam D'ayyabu yana kuma masu godiya, Malam yace ai babu komai wanda duk ya taimaki wani shima Allah zai taimaka masa ta hanyar da baiyi zato ba balle tsammani.... Affan ma k'arasowa yayi yanai masu godiya had'i da tambayarsu ladan aikin su.... Malam yace bazasu amshi ko kabo ba sabida tsakaninsu da Alh Ali ya wuce haka, badon kariyan arziki da ya same sa ba kowa yasan kalan kyautatawa da hidima ma addini da Alh Ali Safwan keyiwa musulunci a lokacin da yake dashi.. Su kyauta sukayi wannan aiki basu buk'atar a biyasu... Babu yanda Affan baiyi ba ko kud'in man mota ne su amsa su k'ara amma fir sunk'i... Haka dole ya hak'ura suka d'unguma suka nufo garin Bauchi...
Sanda suka shigo gari Daddy ya dubi Affan kana yace dashi gidan marigayi Sa'oud Santana suka nufa... Affan ya jinjina kai don shima yana tsananin son zuwa gidan ko badon komai ba sai don yayi tozali da sanyin idaniyarsa Ilham...
Mamy kam jigum tayi a motar yayinda jikin Shareefah yayi sanyi sanda taji gidansu Naseer suka nufa, cire soyayyan Naseer a zuciyarta abu ne mai matuk'ar wuya dukda tasan Naseer d'in baya k'aunarta, insha Allah zatayi k'ok'arin daidaita nutsuwarta koda taga Naseer da matar sa don alk'awari ta d'aukar ma kanta ta shiryu kenan da izinin Allah na har abada, babu ruwanta da mugunta da hassada ma wani, idan Allah ya k'addari Naseer mijinta ne zasu kasance tare, idan kuma ya k'addara ba mijinta bane shikenan Allah ya canza mata da wanda yafisa alkhairi, wanda zai k'aunaceta for who she is.... Tana ida wannnan tunani taji zuciyarta ta cika da nishad'i ba tareda sanin dalili ba. Lokaci guda ta saki murmushi had'i da kwantar da kanta saman kafad'an Mamy...
Kallonta Mamy tayi ta lura da guntun murmushi dake saman fuskar Shareefar, ta kuma kai dubanta ga fuskar Affan dake cikin mirror shid'in ma guntun murmushi ne saman fuskar sa... Family d'inta sun soma dawo da farin cikin da suka rasa A DUNIYAR SU... Fatan ta Allah yasa hakan ya d'ore... Lokaci guda Azeema ta fad'o ranta, cikin zuciyarta take furta Allah ya dawo mana dake Azeema, Allah ya kub'utar mana dake, idan kika dawo our family will be whole again... Allah bayyanaki daughter..." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta lokaci guda tasa hannu tana shafan kan Shareefah dake kwance saman kafad'arta... Rabon Mamy da samun kwanciyar hankali irinta yau tun kafin Laure ta shigo rayuwarta, tabbas ta yarda bijirema Allah da sab'a masa baya haifar da komai sai k'unci da takaicin rayuwa, gashi yanzu data tuba ta mik'a wuya ga mahallicinta DUNIYAR MU tai mata sanyi, ta kuma yarda babu abinda yakai MUGUWAR K'AWA sharri a rayuwa, tabbas ABOKAI suna taka babban rawa a rayuwar d'an Adam, yi k'ok'ari ka kasance da abokai na gari A DUNIYAR MU domin shuka alkhairi....
***
Dukkansu suna tsaitsaye a haraban gidan sunyo rakiyawa su Abbu zasu wuce.... Salma sai k'ok'arin k'watan hannunta take cikin na Naseer shiko yak'i saki, idanma yaji zata zille sai ya kuma damk'e hannun had'i d'an sosa mata cikin tafin hannu, gashi yak'i su had'a idanu sai maganan sa yake wato ma irin ba kulatan nan zaiyi ba... Shiko kunyar su Abbu baiji, ga su Momy ga kowa a wajen...
"Abbu idan kuka dawo nan d'in gaba d'aya zaifi, Aunty Saudat ma sai tafi jin dad'i, abubuwa da dama sun faru, Abbu munfi son zamanku a nan idan son samu...." Ya k'arashe murya cikeda kulawa..
Aunty Saudat ce ta jinjina kai kana tace "Gaskiya ne Abby munfi son zamanku a nan, kaga Naseer ba mazauni bane sannan Fawaz ya dage zai koma k'aro karatu, idan akwai namiji babba a gidan gida bazai mutu ba..."
Momy ce ta tari zancen da fad'in "Wannan gaskiya ne Saudat, kuma nima gashi har mun fara sabo da Mama Kaltume kuma ace zata koma Bamaco toh lallai kuwa nima zan koma can barikin mu..." Ta k'arashe tana kuma rik'o Ilham dake tsaye d'an gefenta...
Aunty Saudat ta dubi Abbu kana ta d'an lank'wasar da kai tace "Abby kaji koh kowa watsewa zaiyi ya barmu....."
Naseer ya k'arada "Nima kuwa na tattara mata ta mu tafi ba sai ku zamto ku kad'ai..."
Gaba d'aya suka d'an dara yayinda Salma ke k'ok'arin mintsilin hannun Naseer....
Gyaran murya Abbu ya d'anyi had'i da satan kallon Momy kafin ya saita kansa don shima dolece kawai zatasa sa barin Nigeria bayan ya kuma ganin gida a Nigeria....
"Naji buk'atun ku, kuma insha Allah zanyi tunani akai, ni kaina bana so na kuma yin nesa da d'iyata , toh amma kunga yanayin zuwan da mukayi da kuma yanda abubuwa suka koma... Idan Kaltume ta amince mu zauna a Nigeria zamu zauna, idan kuma bata amince ba saidai mu dinga kawo ziyara, don alk'awari nayiwa mahaifinta zan rik'eta har bayan ransa bisa gaskiya da rik'on amana...."
Abbu yana kaiwa aya suka jiyo muryar Mama Kaltum dake k'ok'arin k'arasowa wajen tana fad'in "Ai nan shine family d'inka suke, kuma nima zanso zaman mu a nan idan ka tambayi shawarina... Babu komai duk lokacin da ka yanke mu komo Nigeria zaka sameni ina mai maka biyayya sabida aure babu yanda baya kai mutum...." Ta k'arashe murmushi saman fuskar ta...
Murmushin shima Abbu yake don yasan matarshi Mace ce mai tsananin biyayya... lokaci guda ya k'arasa ya rik'o hannunta kafin yace "Allah yayi maki albarka.." Gaba d'aya annuri ya cika fuskokin su...
K'aran bud'e gate da suka jiyo ne yasasu maida hankulansu can...
Naseer ya gane motar Daddy Ali Safwan ne.... Saidai yaga kaman mutane ne cike a motar daga gidan gaba har gidan baya....
Daga chan gefen k'aton roundabout dake tsakiyar gidan Affan yayi parking... Suna kallo Affan d'in ya fito ya zagayo mazaunin mai zaman banza ya bud'ewa mahaifinsa, lokaci guda Mamy da Shareefah suka bud'e gidan baya suka fito....
Mamaki bai gama cika su Naseer ba saida suka hangi Daddy na takowa da k'afafun sa.... Naseer kam tsaban farin ciki bai san sanda ya soma takawa a hankali ba har ya isa gaban Daddy... Murmushin dake fuskar Daddy da Naseer ya kasa gushewa...
Cikin wani irin murya Naseer yake fad'in "Daddy da gaske kaine mai tafiya... Daddy da gaske kaine tsaye a gabana....."
Murmushi Daddy kawai yake kafin ya shiga jinjina ma Naseer kai yace "Ni ne Naseer, Allah ya kuma dawo min da k'afafuna, ina da rabon kuma takawa A DUNIYAR MU Naseer, Allah abin godiya ne....."
Tun kan yayi shiru Naseer yayi saurin rungume sa wani sabon farin ciki ya kuma ziyartar sa A DUNIYAR SU, Allah sarki haka nan Allah ke lamuransa, lokaci guda sai ya sauk'ak'a maku duk wani tsanani da kuke ciki bayan k'unci...
Farin ciki wajen su Salma ma ba'a magana kowa yayi farin ciki ganin k'afafun Daddy suna kuma takawa.... Shareefah da Mamy sai san-san da kai suke, harda rungumar su Salma dasu Jamila, kana ganinsu dai kasan nadama ta shigesu....
Gaba d'aya suka d'unguma da niyyan komawa cikin gidan hardasu Abbu masu shirin tafiya, don ya kamata ayi introducing juna....
Affan da tuntuni idanunsa nakan 'yar makauniyar sa saurin k'arasowa kusanta yayi had'i da rik'o sandar ta bayan ya fakaici idanun jama'an dake wajen....
Murmushi kawai Ilham tayi don tasan waye....
"Ya Affan...!" Ta fad'i tana juya dara-daran idanunta da suke fari k'al masu kyaun gaske...
Affan mutuwar tsaye yayi yana duban idanunta kafin yace "Beautiful ya akayi kika gane ni ne....?"
Murmushi ta d'an kuma yi kana tace "Kawai na gane ne....."
Murmushin shima yayi mai bayyana hak'wara kana yace "Nayi kewarki Beautiful...."
Ilham tayi saurin rufe fuskarta da tafukan hannayenta jin har wani sabon suna Yayan nata ya saka mata kana tace "Ya Affan nifa ba Beautiful bace...."
Affan ya kafe ta da idanu kana yace "Toh idan ke ba beautiful ba ke mecece...?"
D'an dariya tayi a tak'aice kana tace "Ni Ilham ce....."
Affan ma ya murmusa kana yace "A beautiful girl with beautiful name, gaskiya ni a jona sunana jikin naki ko nima zanyi kyau... Bari muga *AffaNilham* wow ya kikaji bai maki dad'i ba...."
Wannan karan dariya sosai tayi kana tace "Kai Ya Affan... Mu k'arasa ciki kar aga bamu nan..."
Kallonta kurum yake yanajin tsantsan soyayyarta kafin yasa hannu ya rik'o sandarta suka nufi cikin tapkeken parlorn....
Gaba d'aya idanu ya komo kansu, Mamy da Daddy da mamaki suke duban Affan, basu tab'a kawo hakan ba, ko ba'a fad'a masu ba Affan son Ilham yake, su Naseer kam sun san kwanan zancen....
Ilham kam dukda ba gani take ba sai taji kunya sosai, Mamy ce ta k'arasa ta amshi sandar nata daga hannun Affan d'in tana mai taimaka wa Ilham d'in...
Affan murya can k'asa ya fakaici idanun mutanen dake wajen kana yace "Mamy be careful kar ta fad'i...." Hararan wasa Mamy ta galla masa kafin suka jiyo sautin dariyan mutanen dake parlorn alamun an jiyosu...
Dariya Mamy ma tayi kafin ta kuma rungumo Ilham tace "Muje kinji Daughter..."
Ilham kam kunya kaman ta nitse cikin k'asa, Mamy bata ma bari Ilham ta zauna saman carpet ba yanda 'yan matan ke zaune gaba d'aya, gefenta ta zaunar da ita....
Bayan an gaggaisa da juna had'i da jajanta ma juna abubuwan da sukayita faruwa a 'yan kwanakin ciki harda k'one gidan gonar Alh Ali da Kabeer yayi.... Su Mamy sukayita mamakin lamarin, duniya ta kuma basu tsoro.... Daddy cewa yayi babu komai, komai ya wuce haka Allah ya k'addara...
Jigum Jamila tayi tana tuna irin illan da Alh Kabeer yayi wa rayuwarta, shine silan komai tunda shine ya k'one gidan gonar Daddy har suka shiga cikin tashin hankali maras misaltuwa, shine silan tsintar kanta da tayi a wannan yanayi da take ciki..... She will never ever forgive him for all the damages he caused her....
Su Daddy sun d'an jima sosai kafin sukai masu sallama suna shirin tafiya, nan Mamy ta buk'aci saidai su Ilham su bisu, ko d'an kwana biyu su masu... Jamila kam tafi son hakan don ko babu komai zata daina ganin Fawaz...
Momy dai bataso ba don zatayi kewarsu, runawa da tayi akwai Lubna yasa hankalinta ya d'an kwanta.... Salma ta d'an dubi Momy sanda 'yan mazan suka soma ficewa kana ta marairaice fuska tace "Momy nima binsu zanyi..."
Naseer dake k'ok'arin ficewa saida ya d'an juyo ya kuma dubanta...
Kafin Momy takai ga bata amsa Mamy ta d'an dafata tace "A'a Salma kekam ai matar aure ce, bazakije ko inaba saida izinin mijinki kinji koh... Sannan ba jimawa zasuyi ba kwana d'an biyu kawai zasuyi su dawo kinji, ki kwantar da hankalin ki...."
Salma ta jinjina mata kai a hankali, Shiko Naseer sai sannan ya sauk'e wara nannauyan ajiyan zuciya kafin ya take wasu Daddy baya...
Jikin Shareefah ya kuma yin sanyi ganin ko kallo bata ishi Naseer ba, ta yarda ta amincewa ranta Naseer ba nata bane, cireshi gaba d'aya a zuciyarta shi yafi mata sauk'i ta nutsu ta nema ma kanta lafiya da jinyar dake jikinta
Har suka isa gida Daddy bai daina hango fuskar matar nan a idanunsa ba... D'an ware idanunsa yayi had'i da mutstsuka su kana ya fuzar da iska yana mai furta "Aliyu what's wrong with you, meke damun ka...?" Kasa nemo ma kansa amsa da yayi ya sanyasa mik'ewa yana d'an taka k'afafun nasa da yake ji yau tamkar ba nasa ba, lallai Allah abin godiya ne, kuma ya yarda da wannan magana Bawa kar ya d'ebe tsammani daga rahamar ubangijin sa...
Yana nan tsaye jikin window yana kuma hango fuskar nata yaji muryar Mamy tana sallama...
Juyowa yayi yana dubanta gaba d'aya ta canza kaman ba Asma'unsa da ya sani ba har wani sabon hankali ne ya shigeta, lokaci guda Daddy ya d'an tsuke fuska had'i da amsa mata sallaman nata, lokaci guda ya k'araso ya zauna saman chaise lounge
Mamy kai a k'asa ta k'arasa shigowa d'akin to his greatest surprise zama Mamy tayi saman tapkeken carpet dake malale a d'akin.... Maimakon tayi magana sai kuka ya kufce mata..
Kasa tab'uka komai Daddy sai kariya da zuciyarsa tayi, sam bai k'aunar ganin mace cikin tashin hankali, dukda yasan sunyi soyayya irinta k'uruciya shida Asma'u a halin yanzu bai isa yace ga abinda yakeji gameda ita ba....
Sallaman da Affan yayi ne ya sanya Mamy k'ok'arin had'iye kukanta yayinda Daddy ya d'an shafi kwantattun sumarsa wanda furfura ya k'ara masu kyau....
Affan sai ya d'an sha jinin jikinsa sam bai zaci zai sami mahaifiyar tasa a d'akin mahaifin nasa ba shiyasa bai tsaya neman izini ba sllama kawai yayi ya turo k'ofar, koda yake tsaban zumud'in abinda zai sanar da Daddyn ne shiyasa...
D'an sadda kai Affan yayi kana yace "Em I'm sorry Daddy...."
Kallonsa Daddy yayi fuska cikeda murmushi kana yace "Come here, shigo abinka...."
Mamy tayi saurin goge hawayenta tana k'ok'arin mik'ewa Affan yace "Mamy pls kema ki zauna dama maganar keda Daddy ya kamata nai maku...."
Mamy tayi k'ok'arin saita kanta had'i da k'ak'aro murmushi kafin ta k'arasa can bakin gado ta d'an zauna tamkar wacce za'a zabureta....
Affan na daga can saman carpet gefen k'afafun Daddy ya soma sanar da iyayen nasa buk'atar sa kan maganar asibitin Ilham...
Gaba d'aya sunji dad'i dama shima Daddy da abin a ransa, gaba d'aya suka tsaida maganar a fara duba likita a nan teaching hospital kafin aji yanda ciwon ya samo asali da kuma yanda lamarin zata kaya...
***
Sallama yayi a k'ofar d'akin Momy, ta amsa masa da sakin fuska lokacin ta ida sallan isha kenan, shima dawowar sa daga masallaci kenan... Can saman stool ya samu ya zauna yana mai gaida Momyn, tsaf ta lura dashi magana ne a bakin sa... Linke abin sallanta tayi kafin ta juyo sosai tana dubansa tace "Soja yaya dai akwai wani abin ne....?"
Naseer ya d'an shafi kansa kana yace "Momy dama so nake na d'an tafi can base d'inmu nayi kwana biyu, aiki ya taru kuma tun jiya suke min waya suna nema na... So inaso na d'an lek'a ko kwana biyu ne sai nayi...."
Momy ta jinjina kai kana tace "Haka ne gaskiya kam ya kamata ka lek'a, zaku tafi tareda Salmar ce....?" Ta tambaya tana mai d'aukan casbahan ta saman drawer...
Kaman wanda yake jira cikin sauri ya shiga jinjina kai kana yace "Eh da son samu Momy..."
Murmusawa Momy tayi kana tace "Ai sai ta shirya ku tafi, tana bayi tana alwala bari ta fito sai na sanar da ita koh..."
Naseer ya jinjina kai kana yace "Toh Momy barinje nima na d'an shirya..." Daga haka mik'ewa yayi ya nufi k'ofa..
Yana gab da ficewa daga d'akin Salma ta turo k'ofar bathroom ta fito....
Kallo ya bita dashi daga sama har k'asa tana sanye da doguwar riga mai laushi wanda ya kwanta sosai a jikinta kanta babu d'an kwali manyan kalaba da tayi sun d'an sassauk'a zuwa kafad'unta, ga ga sumar goshinta ruwan alola ya kwantar dasu sosai... Murmushi ya sakar mata itako gabanta ne yayi wani irin fad'uwa, cikin sauri ta d'an maida masa martanin murmushin kafin ta sadda kanta k'asa ta shige... Naseer ya shige zuciyar sa nai masa wani irin sanyi...
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*63*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Fatan Alheri FADEELA TALBA NOVELS 💖🤝🏼*
Sauraren Momy kurum take ba tareda ta motsa daga saman sallayar ba... Ita kad'ai ta lula duniyar tunanin da bata isa tace ga tak'amaimen abinda take tunani ba...
Momy ta ida zuba mata kayan cikin k'aramar jaka kana tayi zipping jakar lokaci guda ta maido da dubanta ga Salma...
"Kin idar da sallan ne...?"
Momy ta tambaya tana mai dubanta..
A hankali ta jinjina mata kai ba tareda tace komai ba, bata san meke shirin faruwa da ita ba amma kam tinda Momy tace ta shirya zasu tafi da Soja take jin matsanancin fad'uwar gaba...
K'arasowa Momy tayi ta zauna daga gefen Salmar kafin ta kamo hannayenta ta shiga jero mata nasiha wanda ya danganci rayuwar aure, kama daga hak'uri wanda shine jigo, ladabi da biyayya ga miji sannan uwa uba tsabtar jiki da muhalli had'i da girki....
Salma dai kanta na k'asa gaba d'aya ta kasa d'ago idanu ta dubi Momyn, wani nauyi da kunyar Momy ne taji ya dabaibayeta lokaci guda, ga sanyi da jikinta yayi tunanin mahaifanta ya shiga ratsa ko wani k'ofa na zuciyarta... A hankali ta shiga gyad'a wa Momy kai tana share d'an guntun hawayen da ya kwararo mata...
Momy ta d'an murmusa had'i da d'ago fuskar Salmar kana tace "A'a daughter banson ganin hawayen nan, besides sati d'an d'aya zuwa biyu jal zakuyi a can, kuma Naseer yace min ya sayo maki waya, ya jonata caji ne, kinga zamuke waya kuma idan kina so da kaina ma zanje..."
Baki a d'an ture tace "Amma Momy Soja ai sai ya sanar dani da wuri fisabilillahi kofa shiryawa banyi ba...."
Maganar taso bawa Momy dariya amma ta d'an gimtse tace "Bakiji abinda Mamy ta fad'a maki ba d'azun ko..? Kuma banda abinki ai shima ba cewa yayi zaku zauna a can ba, aiki zai je shi kuma ma gari d'aya fah muke, haba Salma zamanin fah kai ya waye ba'a gudun miji kinji koh...."
D'an jim Salma tayi had'i da jinjina kanta kana tace "Naji Momy...."
Jinjina kai Momy tayi kana tace "Maza tashi ki shirya yanzu shima zai fito...."
Bata jira cewar Salmar ba ta mik'e ta isa ga drawer dake gefen bedside ta ciro wani turare mai k'amshin gaske ta saka mata cikin jakar nata... Salma dai sai kallo take faman bin Momy dashi yanda taketa shiryata lokaci guda tanai mata bayanai masu buk'atan nutsuwa... Tamkar uwa da d'iya haka Momy ta kintsa Salma tas, harda kwalliya ta sanyata yi sannan ta umarceta da yawaita zama da kwalliya a tattareda ita musamman lokutan data kasance tareda mijinta domin ita mace 'yar kwalliya ce haka Allah ya halicceta...
Sosai Salma tayi kyau cikin wata doguwar riga yadin material mai taushi da kyau wanda yake kalan shud'i da toka, tupke kitsonta tayi tsakiyar kanta kana ta yane kan nata da yalwateccen mayafi ruwan toka, duban kanta ta kuma yi jikin mirror tayi kyau sosai har ta gaji, ga wani ni'imtaceccen k'amshi dake tashi jikinta... Tana nan tsaye a wajen tana k'ok'arin nad'e mayafin akanta ta hangi fuskar sa cikin mirror d'in.. Gabanta ya kuma yankewa ya fad'i saikace yau ta soma saninsa... Bata sami zarafin juyowa ba saidai ta kasa d'auke idanunta daga duban nasa, Yana sanye da black long sleeve shirt, gaban rigar an rubuta _ROY_ d'an gefe kad'an kuma tambarin shararriyar kampanin ne wato Adidas, ba sai ance maka rigar designer bace... Sosai rigar ta fito da asalin suffar jikin sa da kuma hasken fatar sa,.... A hankali take k'ok'arin d'ago idanu har ta kawo ga fuskar sa wanda ya cika da murmushi.... Cikin sauri ta sadda nata kan k'asa...
Cikin takunsa mai cikeda charisma yake k'arasowa cikin d'akin...
Har gaban dressing mirror d'in ya isa ya yanda ya tsaya ta bayanta fuskokinsu suka bayyana cikin madubin... Hannu yasa ya amshi mayafin nata ya shiga rufa mata akanta dukda ba wai ya iya bane....
Yanda ya cukwikuye mata mayafin akan nata abun sai ya basu dariya gaba d'aya..
Kallonta yake sosai yanda take dariya abin burgewa kana ya d'an sauk'o da bakinsa saitin kunnenta yayi mata magana cikin muryar da tafi kama da rad'a
"Meyasaki dariya...? Ko ban iya bane....?"
Fuska d'auke da murmushi ta shiga girgiza masa kai ba tareda ta amsa sa ba...
Naseer yasa hannayen sa ya manneta cikin jikinsa wanda ya jefasu cikin wani yanayi maras fasaltuwa su duka biyun kana yace "Kar ki damu zan koya duk irin wad'annan abubuwan sabida na dinga maki su, gaba d'aya harda k'unshi da kitso...."
Nan ma tak'aitaccen dariya Salma tayi kana tace "Kai Soja kitso da k'unshi saikace mace..."
"Kina mamaki koh, bari ki gani sai na soma maki su ki yarda zan iya... For my queen babu abinda bazan koya ba...." Ya k'arashe yana d'aura hab'arsa saman kafad'anta...
Kallon juna suke cikin dressing mirror d'in kafin ta sinkayo muryarsa yana fad'in "Are you ready.... Shall we go....?"
Batakai ga basa amsa ba suka jiyo sallaman Momy..... Lokaci guda Naseer ya d'an saketa ya matsa gefe yana wani shasshafa kai....
Salma kuwa gaba d'aya kunya ce ta dabaibayeta, cikin sauri ta shiga kwance d'aurin mayafin da Naseer ya cukuikuya mata tana mai gyarawa...
"Soja an fito...?" Momy ta tambaya sanda take shigowa cikin d'akin...
"Eh Momy zamu wuce yanzu insha Allah...."
"Toh Allah shi tsare ya taimaka..."
"Ameen Momy... " Ya amsa sanda yake d'aukan jakan kayan Salma...
Momy taci gaba da fad'in "Yanzu Saudat ke fad'a min sunyi waya dasu Abbu sun isa Kano zuwa dare jirgin su zai tashi, yace ya kira wayarka bai samu ba...."
"Allah sarki, Allah sauk'esu lafiya, zuwa safiya zan kirasu insha Allah...."
Momy ta amsa da ameen kafin ta k'arasa ga Salma dake ciro takalmi cikin shoe rack....
Naseer ya fice yana fad'in bari yayima su Aunty Saudat sallama...
Momy kam wajen d'iyarta Salma ta k'arasa suna kuma yin tasu sallamar....
*****
Gaba d'aya sai gidan ya kuma masu shiru.... Babu su Jamila su Mama Kaltume sun tafi ga kuma su Salma ma sun tafi, gidan ya rage daga Momy sai Aunty Saudat sai ko Lubna wacce itama exams ke gabanta....
Saida suka biya wani Mini Mart suka d'anyi window shopping kayan da zasu buk'ata kafin suka d'auki hanyar barikin nasu....
Tun daga gate Soji ke k'ame masa suna kwasan gaisuwa har suka shiga cikin barikin....
Gidan babu wani dattin d'aga hankali saiko d'an k'ura da yayi... Salma kam tuni ta shiga tattare ko ina tana gyarawa don taji sanda Naseer ya fice yana waya bayan ya ida shigar masu da kayayyakin su.....
Bayan ta ida wanke bathroom ne ta d'aga idanu tana duban agogo bango dake mak'ale a d'akin ya nuna k'arfe tara saura wasu dak'ik'ai.... Sai hamma take alamun barci gashi gaba d'aya ta jik'e rigarta wajen wankin toilet d'in gaba d'aya rigar ta kuma bin jikinta ta kwanta...
K'arasawa tayi yanda luggage d'inta yake ta bud'e tana neman wasu kayan dai-dai lokacin Naseer ya shigo still waya manne kunnensa da alama wani kiran yake amsawa...
Kafeta da idanu yayi yana mai ci gaba da amsa wayar yayinda Salma gaba d'aya ta tsargu da irin kallon da yake mata musamman da ta tuna jikinta jik'e yake.... Ta saci kallonsa sanda taga ya juya kaman zai fice daga d'akin... Cikin sauri ta zari wata doguwar rigar zata shige bathroom saidai taji Naseer ya rik'ota... Cak ta tsaya ta kasa ci gaba da tafiyar da take...
Mazauni ya masu saman gado yana mai ci gaba da amsa wayarsa wanda ko ba'ace ba da abokan aikinsa yake wayar...
Itakam zamanta saman cinyarsa gaba d'aya ya k'ara mata kunyarsa shiko kunyarta bayaji, ta fad'i cikin zuciyarta...
Har ya ida wayan ya d'anyi wasu danne-dannen sa cikin wayar Salma bata sani ba tsabagen bata saki jiki da zaman nata ba, gaba d'aya hankalinta baya wajen...
Kaman daga sama taji muryar sa tamkar mai rad'a cikin kunnenta yana fad'in "Reina what happened.. I mean me ya faru kika jik'a jikin haka... Baki tsoron mura koh....?"
Murya can k'asa tace "Wanke bathroom d'in nayi..." Yanda tayi maganar cikeda ladabi ko d'ago idanu batayi ta dubesa ba...
'Yan yatsunta yake murzawa a hankali kana yace "Naga kinsha aiki ke kad'ai, da kin jirani nazo mukayi tare..."
Sai sannan ta d'an dubesa kana ta girgiza kai tace "Haba Soja babu fah wani aiki.... Kuma ban gaji ba fah..."
Naseer ya kuma matso da fuskar sa dab nata, cikin wata irin kasaltecciyar murya yace "Are you sure...?"
Gyad'a masa kai tayi ba tareda ta d'ago fuska ba...
Murmushi yayi mai cikeda nuna farin ciki kana yace "Allah yayi maki albarka...."
Fuskarta naga gaban rigarsa yanda aka rubuta kalmar _Roy_ ta amsa da "Ameen Roy...."
Kallonta yayi sosai yaga yanda ta samo kalmar nata kafin yace "What did you say....?"
Salma ta dubesa tana d'an zaro idanu don itakam sam ba wai ta fad'i bane don ya fito fili hasalima cikin zuciyarta ta fad'i batasan ya fito ba...
Girgiza kai ta shiga yi cikin sauri kana tace "Nifa bance komai ba Soja...."
Murmushi Naseer yake ganin yanda ta daburce gaba d'aya kana yace "Relax Reina, I heard you fah.... Did you say Roy....?"
Murmushi tayi kana tace "A gaban rigarka na gani...."
"Kinsan me kalmar ke nufi...?" Ya tambaya still yatsunta cikin nasa...
A hankali ta girgiza masa kai alamun a'a..
Naseer ya jinjina kai kana yace "What about Reina...?"
D'an kallonsa tayi kafin tace "Ai kace zaka fad'a min wani lokacin...."
Jinjina kai yayi kana yace "Yeah anyi haka... Reina is a Spanish word, yana nufin Sarauniya, and Kalman Roy opposite d'in kalman Reina ne, na baki satan amsa..."
Murmushi Salma tayi tana mai dubansa kana tace "Auho wato dai Roy yana nufin King kenan...."
Shima d'in dariya ya d'anyi kana yace" Gashi kuwa kin fad'i... Kar ki damu kin fad'i a dai-dai don nasan ni ne basaraken birnin zuciyarki....."
Hannaye tasa had'i da rufe fuskarta tana mai murmusawa....
"Oya tashi ki canza wannan kayan kar kiyi mura...." Ya fad'i yana k'ok'arin zuge mata zip d'in...
Zaro idanu waje tayi had'i da rik'e hannayen sa kana tace "Zan.... Zan iya Soja...."
"But I insist..." Ya fad'i yana dubanta da idanun sa masu narkar da ita...
Baiko jira cewarta ba ya janyota cikin jikinsa yana mai ci gaba da zuge zip d'in....
Kuka ta soma masa tana fad'in ita dai zata iya...
K'uri ya mata yana kallon kukan nata don da gaske takeyi abinta... Lokaci guda ya saki rigar nata ya shiga riritata yana fad'in shikenan ya daina...
Hannu tasa tana goge hawayenta, Naseer kuwa sai kallonta yake cikeda mamakin arhan hawayenta kana yace "Kiyi shiru bazan sake ba,"
Bata tankasa ba sai k'ok'arin mik'ewa daga saman cinyar nasa...
Saurin rik'ota yayi kana yace "Ina kuma zakije..."
Kai tsaye ta basa amsa da "toilet...."
Naseer ya d'an had'e gira kana yace "Ai kuma baki isa ba, ki k'i yarda na canza maki sannan kice toilet zaki gudu ki canza, saidai kuma idan zan biki na maki wanka d'iyanin...."
Zaro idanuwa tayi gaba d'aya kana tace "Tabb wanka fah kace Soja, saikace wata baby..."
Naseer ya murmusa kana yace "Toh ai ke baby d'in ce, ko Momy bata fad'a maki kin zama Baby na bane huh..?"
Sadda idanunta k'asa tayi hannunta rik'e da rigarta..
Naseer kuwa dad'a gyara zamansa yayi kana ya d'an soma magana
"Reina nasan kinsan me aure yake nufi, kin kuma san matsayin mijinki a wajen ki, kinsan yanda hakki akanki sannan kema kinada hakki akansa.... So idan da abubuwan da zan k'ara maki akan was'anda kika sani k'alilan ne.... Ki canza kayan sai ki sameni a parlor mu k'arasa maganar koh...."
Bata iya amsa sa ba sai jinjina masa kai da tayi har lokacin idanunta na k'asa..
Tana jin sanda ya mik'e tsaye had'i da manna mata peck a kumatun ta kafin ya nufi parlor, har saida ya fice kafin ta sauk'e nannauyan ajiyan zuciya
****
Gaba d'aya suke zaune a parlorn suna kallon film d'in Avengers infinity idan ka d'auke Jamila dake kwance a d'aki, duk yanda tayi ta kasa yakishe tunanin a ranta.... Tana nan kwance taji kaman tari na taso mata.. Cikin sauri ta mik'e ta nufi bathroom tana yin tarin.... Abin da ya mugun d'aga mata hankali shine wannan karan jinin kaman harda guda yake fitowa cikin tarin nata..... A hankali ta silale k'asa tana k'unshe kukan dake shirin kufce mata
Shareefah ce ta shigo d'akin tana amsa wayar Likitan ta Dr Siraj, tunda ta shigo d'akin take jiyo sauti a hankali daga cikin bathroom d'in kaman na kuka...
A hankali Shareefah ta mik'e ta d'an isa jikin k'ofar bathroom d'in... Shiru tayi tana kuma tabbatar da abinda kunnuwanta ke sauraro mata, tabbas kuka ne..... Ta tuna Jamila kawai suka baro a d'akin kafin su fice parlor...
D'an gyaran murya tayi kana ta shiga k'wank'wasa k'ofar bathroom d'in a hankali tana mai fad'in "Jamila,... Are you alright? Pls ki bud'e k'ofar..."
Saurin mik'ewa Jamila tayi had'i da goge hawayen da suka jik'a mata idanu kafin ta isa ga washbasin had'i da kuskure bakinta, ta d'an d'auraye fuskarta da ta koma very pale kana ta d'au hand towel tana goge fuskar....
Shareefah har ta cire rai bazata amsa ta ba sai kuma taji ana k'ok'arin bud'e k'ofar bayin...
Kallo Shareefah ta bita dashi yanda gaba d'aya kana ganinta kasan she's not normal....
K'ak'aro murmushi Shareefah tayi ta sakar mata kana tace "is all well...?"
Murmushin Jamila ma ta d'an sakar mata kana ta jinjina kai ba tareda ta bari sun had'a idanu da Shareefar ba...
Kallo dai Shareefah ke faman bin Jamila dashi har ta isa saman sofa ta zauna... Lokaci guda Shareefah ta k'arasa had'i da zama gefen Jamila...
"Ina Falaq....?" Jamila ta tambaya ba tareda ta dubi Shareefah ba...
"Tana wajen Mamy, inaga ma ta goyata tayi barci.... Meyasa kike zaune ke kad'ai a d'aki bayan duk muna parlor gaba d'aya, Jamila we've been through a lot, munga jarabawa iri da kala A DUNIYAR MU amma hakan ba yana nufin shikenan bazamu ci gaba da rayuwarmu bane, hak'uri da karb'an k'addara a duk yanda tazo maka shine ribar rayuwar duniya... Kar mu kasance masu fushi ga hukuncin ubangijin mu kinji, dan Allah kiyi hak'uri ki rage shiga damuwa irin haka, idan ke a matsayinki na babba kina haka yaya kike tunanin Ilham zatayi, koda ace bata ganin ki na tabbata tana jin abin cikin zuciyarta.... Please kiyi hak'uri mu amshi k'addarar mu...."
Izuwa lokacin hawaye sun soma zarya a fuskar Jamila, kallon Shareefah tayi kana tace "Shareefah gwara damuwar kowa akan nawa, gwara tashin hankalin kowa akan nawa..."
Shareefah bata bari taci gaba da magana ba ta katse ta da fad'in "Don't talk like that Jamila, nida ke makamancin k'addara iri guda ya auka mana....."
Jamila dake faman murmushi wanda yafi kama da murmushin takaici bata bari Shareefah ta ida maganar ba tace "Shareefah kenan, bana fata iftila'in da ya auka min A DUNIYAR MU ya kuma samun wata 'yar uwata musulma, Shareefah sam ba k'uncin rasa Fawaz da nayi ne ya addabeni ba, a'a... Kunci na da damuwata ba komai bane illa bada kaina da nayi wa mutumin da ya zame jigo na shiga k'uncina A DUNIYAR MU har yayi illa wa rayuwata da na 'yan uwana... Shareefah da ace nasan Alh Kabeer shine sanadiyar k'onewar gidan gonar Daddy wllhi da ban kasance dashi ba, da ace nasan shine silan komai da ban aminta dashi ba... Amma na sab'a hud'ubar iyaye na, na yaye daraja da kima da Allah yayi min a matsayina na d'iya mace nayi watsi dashi.... Shareefah duk ba wannan ba... Wllhi bansan makomar rayuwata ba a halin da ake ciki.. Na tabbata duk abubuwan da suka sameni zasu kasance ishara wa masu kwad'ayi irin nawa.... Bana fata d'iyata ta taso ta tadda mummunar labari na...." Kuka ya hanata ci gaba da magana...
Shareefah dake faman hawaye cikin sayin jiki ta rungumo Jamila murya na rawa take fad'in "Ki daina fad'in haka Jamila, mu duka 'yan adam ne kuma masu kure, babu wanda baya kuskure A DUNIYAR MU wannan halitta ce ta d'an Adam, babu wanda yake d'ari bisa d'ari, sannan mahaliccin mu mai yawan gafara ne mai jin k'ai, tun daga wannan lokacin da kika fahimci laifinki kikayi kyakkyawan tuba ya yafe ki, sannan Falaq bazata girma ta tadda wani b'atanci daga mahaifiyarta ba insha Allah, sabida Allah da zuciya yake aiki yaga tubanki tuntuni... Jamila don Allah ki daina saka kanki cikin damuwa kada ki haifar wa kanki wani ciwon, maza tashi muje parlor kar su Mamy su jimu shiru, Affan ya sayo gizzards a Haisan, na rabaki akwai dad'i sosai, tashi muje kafin ya cinye don nasan sa da son gizzard..." Ta k'arashe tana mik'ewa tsaye had'i da janyo hannun Jamilar...
Jamila dai murmushi kawai ta d'anyi kafin ta shiga bin bayan Shareefah tana tuna lokutan baya yanda tsangwama da hantarar dake tsakanin su, Allah sarki Duniya kenan makaranta mai bada lekca iri daban daban, mai nitsa tantiri mai wargaza nitsattse... Allah kasa mu dace ameen....
****
Zaune ta hangesa saman carpet bayan ta ida shiryawa cikin doguwar rigar bacci mai laushin gaske had'i da rufa hijab akanta, bata mance hud'ubar Momy ko guda ba don saida ma tayi wanka kafin ta shirya,...
Ledoji ne gabansa wanda take tsammanin daga cikin abubuwan da suka sayo ne, ga irin gyad'ar kwalban nan gefensa sai ci yake, idanunsa naga talabijin yana kallon tasha labari na TVC, saida ta d'an sauk'e ajiyan zuciya had'i da saita kanta kafin ta nufesa...
Tunda ta shigo parlorn yake jiyo ni'imteccen k'amshi na bugun k'ofofin hancin sa... A hankali ya juyo yana dubanta yanda take takowa tamkar mai tsoron kada ta silale saman tiles.... Naseer ya shiga sakin murmushi don komai nata burgesa yake...
Can gefe ta isa tana k'ok'arin zama sallama saman bakinta... Bai bari ta zauna ba ya tareta da fad'in "K'araso nan ki zauna..." Ya k'arashe yana mai bubbuga mata gefensa saman carpet d'in..
A d'arare ta zauna sai faman twisting yatsun hannunta take...
Shiko gogan kallo yake kan faman binta dashi kana yace "Turarenki ya min dad'i Reina..."
Kai a k'asa ta basa amsa da fad'in "Momy ce ta bani..."
"Ta baki ko ta bamu, ko har yanzu bamu zamto d'ayan bane...." Ya k'arashe yana janyota kusan sa sosai...
Murmushi ta d'anyi kana tace "Toh ta bamu..."
"Yauwa yanzu kika gyara zancen naki..."
Murmusawa ta kuma yi kana tace "Amma ai turaren mata ne kuma maza basu saka turaren mata...." Ta fad'i tana mak'e murmushinta
Murmushi mai d'an sauti yayi kana yace "Says who, wayace maki maza basu saka turaren mata, koma basu sakawa ni zan soma sakawa sabida nima na matan ne...."
Saurin d'agowa tayi tana dubansa kana tace "Kai kuma na mata..."
Naseer ya d'an dara kad'an kana yace "I mean ni naki ne kuma ke mace ce ko ba haka ba..."
Murmusawa tayi cikeda kunya kafin ta ci gaba da twisting yatsunta...
"Reina ince don ni akayi wannan gayun, toh meyasa kuma aka rufe min da hijab ai bazan gani ba balle nayi grading d'inki...."
"Nifa ba gayu nayi ba Soja, kayan bacci ne..."
Naseer ya mata k'uri sihirataccen murmushi saman fuskar sa kana yace "A wajena ko meye Queen ta saka gayu tayi, zo na cire maki...." Ya k'arashe yana kwab'e mata hijab d'in ba tareda ya jira cewarta ba...
Ledojin gabansa ya soma janyowa kafin yace "Je kitchen ki kawo mana plate da cups..."
A hankali ta amsa masa had'i da jinjina kai kafin ta mik'e ta nufi kitchen d'in... Drawers ta bud'e yanda ta tarar da ko wanne jere a ma'ajiyinsa, ta kuma bud'e wani drawer ta k'asa yanda taga trays a jere, d'aukowa tayi tana murmushi tana mamakin yanda Naseer keda tsari saikace mace, komai nasa kif-kif gwanin ban sha'awa..
Saida ta d'auraye kayan anfanin kafin ta nufi parlorn...
Kallo yake faman binta dashi har ta k'araso cikin parlorn yana kuma godewa Allah da baiwar da yayi masa na mallaka masa Salma matsayin matar sa...
Umartanta yayi tayi serving d'insu... Gasassun kaji ne wanda take tunanin tsayuwansu a Haisan ne ya saya da kuma fresh milk...
Duk nok'ewarta da k'in cin abinci saida Naseer ya tirsasa mata ta d'anci sosai tasha madaran ma, bayan sun gama ci Salma ta tattare wajen na sakawa a fridge ta kai sa fridge...
Bayan ta dawo ta zauna ne Naseer ya turning down kallon da yake gaba d'aya kafin ya juyo sosai suna fuskantar juna, irin zaman cin abinci yayi yana fuskantar ta sosai kana ya d'anyi gyaran murya ya soma magana
"Alhamdulillah, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya ajiyemu k'ark'ashin inuwa guda...... Duk wani abinda zan fad'a maki nasan kin sani saidai hakkina ne na kuma tuntub'arki..." Fasali ya d'an ja kafin yaci gaba da fad'in "Salma lately things weren't easy, abubuwa da dama sun faru ko nace sunakan faruwa, amma Alhamdulillah Allah cikin ikonsa da buwayarsa yana kan wareware mana komai daki-daki... Dole mu gode masa mu kuma gode masa..."
Fasali ya kuma ja kafin yaci gaba da magana, wanda daga bisani 'yan tambayoyi ya mata game da ilimin fiqhu kafin ya d'an masu nasiha su duka biyun gameda zaman da zasuyi k'ark'ashin inuwar aure, don shi zama na aure zama ne na zo mu zauna zo mu sab'a....
Jikin Salma yayi sanyi sosai da jin irin nasihar da Naseer ke mata, yanda yake jawo ayoyi da hadisai sam bata tsammanin 'yan gayu irinsa suna karatun addini har haka ba, Allah sarki ashe ba haka bane ba daga nan take ba, duk yanda d'an Adam yake kar ka gansa ka raina sa, Allah shine masanin mafi kusanci dashi...
Naseer ko ganin tayi La'asar sosai ya sanya sa janyota cikin jikinsa yana lallashi yana amo mata da kalaman soyayyarta da sukayi k'awanya wa zuciyarsa...
Tuni tayi lamo cikin jikinsa sanda ya soma aika mata sak'onnin sa masu wuyan fasaltuwa....
A wannan dare wad'annan ma'aurata biyu sun sha soyayya, daren da zai dawwama cikin zukatansu, Daren da bazasu gushe ba suna ambatonsa da DAREN ALKHAIRI cikin zukatansu...
Can k'asan rug ya zauna yana duban kyakkyawan fuskarta yanda take ta sharan baccin azaba, tausayinta da soyayyarta na azalzalan sa, a hankali ya k'araso ga fuskar nata yana zagayewa da 'yar yatsar sa manuniya, shagwab'a da kukan da tayi ta masa a daren jiya yake tunowa wanda bad haifar masa da komai ba sai tsan-tsan soyayyarta..
A hankali ya furta "I love you Mi Reina, I love you with all my heart...." Shiru ya d'anyi yana mai ci gaba da dubanta yana murmushi kafin ya furta "Thank you for being mine...." Lokaci guda ya manna mata light kiss saman leb'enta..
Duk wannan bidirin Salma tana jinsa saidai kunyarsa bazai bari ta bud'e idanunta ba... Soyayyarsa ne ke ratsa duk wani mahudar gashi dake jikinta... Tana jin sanda ya mik'e ya isa bedside ya d'auki takarda da pen, rubutu yayi kana ya ajiye gefenta kad'an, daga haka ficewa yayi daga d'akin..
Yana ficewa ta bud'e idanu ta d'an yunk'ura ta d'au takardan ta warware.. Murmushi tayi ganin abinda ya rubuta cikin takardan
_Good morning to my beautiful wife, stay in bed sweetheart I'll cook breakfast..._
Murmusawa ta kuma yi kafin ta mik'e da k'yar ta nufi bathroom, wanka ta kuma yi tana tuna jiya wai Naseer ne ya wanke ta, sabon kunyar sa ya kuma lullub'eta, komai hanata yi yayi shi ya dinga tarerayarta tamkar k'wai a hannun yara...
Shiryawa tayi tsaf cikin riga da skirt d'inki atampa wanda ya amsheta sosai ya fito da kyaun jikinta, kallon kanta jikin dressing mirror ta kuma yi don har wani kyau ta k'ara masha Allah...
A hankali take takowa tamkar mai tausayin k'asa, nan ta hangesa tsaye jikin dining table waya manne a kunnesa sai faman jera cups yake, harda wani d'aura apron saman inner white d'insa da kuma Sweatpants d'insa, saikace wani cook d'in gaske, abin har yaso bata dariya..
Naseer yaci gaba da amsa wayarsa da alama da Momy yake wayan..
Murmushi ya d'anyi had'i da shafa kansa sanda Momy ta tambayesa Salma kana yace "Ai tana bacci Momy, bata tashi ba bata d'an jin dad'i ne..."
Daga d'aya b'angaren murmushi Momy tayi don muryan d'an nata sak na angwaye ya mata tsaban nishad'i da taji muryar ta cika dashi.. Cikeda jin dad'i Momy tace "Allah ya bata lafiya ya kuma albarkace ku da zuri'a d'ayyiba.."
Naseer na murmushi ya kuma amsawa da "Ameen Momy, a gaidasu Lubna sai munyi magana..."
Salma kam uwa k'asa ta tsage ta shige ciki don kunya, shikenan Soja ya gama tona mata asiri, k'ok'arin juyawa take da niyyan komawa d'aki saidai tuni Naseer ya k'yallaro ta, don tun kafin ya ganta ma saida ya soma jiyo k'amshinta...
Jin ya ambato sunanta ya sata tsayawa cak ba tareda ta kuma motsawa ba..
K'arasowa yayi har yanda take, kwanto da kansa yayi saman wuyarta yana shak'an k'amshin nata sosai kana yace "Reina da guduwa zakiyi...?"
Salma dai sai murmushi take ba tareda ta iya amsa sa ba...
Juyo da ita yayi suna fuskantar juna saidai bata d'ago fuskarta ba yana nan kife a k'asa..
"Love ko darajar kallo bazan samu ba balle gaisuwa? ..." Ya fad' yana kamo hanayenta
Nan ma murmushi ta kuma yi kafin ta soma k'ok'arin durk'usawa tana gaishe shi...
Saurin d'agota yayi ya mak'ale cikin jikinsa kana yace "Na yafe tsugunon gaisuwar ma ta isar Alhamdulillah, Yaya jikin naki...?" Ya tambaya yana k'ok'arin d'ago fuskarta
Hannu tasa da sauri ta rufe fuskar nata...
D'an had'e rai yayi kana yace "Au bazaki bud'e fuskar nan ba koh saina ku....." Saurin toshe bakinsa tayi da hannunta kana tace "Na bud'e wllhi nidai... "
Sosai Naseer ke dariya kafin yace "Matsoraciya, oya muje na baki abinci..."
Bai jira cewarta ba ya sureta sai dining area... Soyayya suke kan nunawa wa juna yanai mata bayanin abubuwan da ya girka saikace wani Cook d'in gaske, itako sai dariya take...
"Soja amma dai kaine mai maku girki a filin daga koh..." ta fad'i tana d'an darawa
Tak'aitaccen dariya Naseer yayi kana ya d'an gimtse yace "Nifa bana son Sojan nan, kowa ya kirani Soja kema ki kirani Soja gaskiya a sakamin suna..."
Dariya Salma ta d'anyi kana tace "Tam wanne kake so...?"
"Wanda zaki sakamin nake so...." Ya fad'i cikeda shagwab'a wanda hakan har saida yaso bata dariya
"Shiru tayi tamkar mai nazari kana tace "Acikin ukun nan ka zab'a..... _My SalNas, My King or Mi Roy....."_ Tana ida fad'i ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana murmushi
A hankali ya matso kusanta fuskar sa d'auke da murmushi kafin ya kamo hannayen nata ya ciresu daga fuskar ta, k'ura mata kyawawan idanunsa yayi kafin yace "Cikin duka sunayen da kika ambata babu wanda bana so, in fact sunmin dad'i fiye da tunanin mai karatu.. I love you Reina, So much..."
Murmushi ta sakar masa kafin tace "I love you too My Roy..."
Kallonta Naseer keyi cikeda mamaki yanda take furta kalmomin gwanin dad'i...
Soyayya suke kan nunawa juna wajen breakfast d'inma kafin daga bisani wayar Naseer ta soma ruri.. Lambar Fawaz da ya gani ne ya sanya k'irjinsa ya d'an buga kad'an don a tunanin sa an samu labarin Innah ce.. Yana d'agawa yaji muryar Fawaz cikin matsanancin tashin hankali
Saurin mik'ewa Naseer yayi yana satan kallon Salma data bada hankali ma tashan Namun daji da suka kamo wato National Geographic Wild...
D'aki Naseer ya shige yana mai ci gaba da amsa kiran, banda bugawa babu abinda k'irjinsa ke masa, kasa furta komai ma Fawaz yayi sai k'arasawa closet da yayi ya suri jallabiyar sa ruwan Madara ya zura kafin ya nufo parlor yanda Salma take,
Haka kurum yanayinsa da ta gani ya sanya gabanta mugun fad'uwa...
0 comments:
Post a Comment