"""" haka kuwa akayi da yamma abba yaje yasamu Umma da maganar tayi farin ciki sosai kuma tayi addu'ar Allah yasa alkhairi fatan ta daya Allah sa asma'u ta amince da zancan
godiya abba yayi mata yatafi akan idan asma'u tadawo tagayamata yana son ganinta
Daren ranan haka sarah tayishi banda kuka ba abunda take idonta ya kunbura yayi ja har wani zazzabin wahala yarufeta se sambatu take ita kadai kamar mahaukaciya gashi taki cin komai kuma taki fadan abunda yake damunta har aysha tagaji da tambayarta tayi tafiyarta
yanzu haka ma kuance take akan gado ta lulluba da bargo se kyarman sanyi take hawaye nadiga akan pilonta
Aysha ce taturo dakin tashigo dasauri takaraso bakin gadon tana fadin subhanallah sarah jikin ne har yanzu
Ko kanta takasa dagawa da kyar ta iya bude idonta takalleta
Bargwon aysha tadan yaye tana taba goshinta da yayi raw kamar garwashi
Tashi kisha magani tafada tana balle mata magani taimaka mata tayi ta tashi zaune da kyar ta yarda tasha maganin hawaye wani nabin wani
Cike da taikaci aysha tace wai ni sarah meyake damun kine kike wannan kuka haka kamar an aikomaki dasakon mutuwa
Kawda kai tayi tana share hawayen fuskarta batace komai ba
hanyar fita aysha tanufa tana fadin gaskiya zanje nakira AK dole yasan halin da kike ciki tunda ni kinki gayamun
Saurin riko hannunta sarah tayi tace a'a base kinkirashi ba zo zan gayamaki
Dawowa tayi tazauna tace to ina jinki
Labarin wayar dataji ahmad nayi tabata da kuma yanda suka kwashe
Cike da mamaki aysha tace amma wallahi ahmad yabani mamaki shiyasa ance kaidai kaga mutum shi yanzu ko kunyar AK bazaiji ba ko yana ganin bazai iya daukan mataki akansa bane to wai ma ita yarinyar yar waye agarinnan
Kai sarah takauda hade da tabe baki tace bansanta amma wallahi zan nemota bazan barta ba i will punish her senasa tayi kuka kamar yadda tasa nayi I will make her suffer sannan kuma inkasheta
Tashi sarah tayi tanufi bathroom tana boye dariyarta tace yanzudai bari nahada maki ruwa kiyi wanka kyadan ji karfin jikinki inyaso semuyi magana amma gaskiya abunda kika ma ahmad Sam baki kyewta ba
Sunkuy dakai sarah tayi tace nasani nima I don't know what come over me nakasa controlling kaina ne amma ko zuwa anjima zanje nabashi hakuri
Dadai yafi aysha tafada tana rufo kofan toilet din
Hannu sarah takai tadauki wayarta ta kunna photon ahmad ne akan screen din wayar yana sanye dawasu
Kayan sport farare da eyepiece akunnensa yana murmushi yayi kyew matuka
Rungume wayan tayi akirjinta wasu hawayen nakara gangarowa akan kuncinta cikin muryan kuka tace 😭 don't leave me please ahmad I can't live without u
asma'u ce tafito cikin shirinta nafita kusan Umma tazo tzauna tana fadin yanzu Umma bazaki gayamun waye yazo Neman aurena wajan abba bako
Murmushi Umma tayi tace a'a inkinje kyaji ai ance waka abakin mai ita tafi dadi fita tayi tana fadin to senadawo
Har tayi nisa se kuma tayanke shawaran bari tabiya wajan aikin su ahmad maybe zata sameshi acan
Haka kuwa akayi sedai tanazuwa securities din suka hanata shiga wai dole seda izinin Wanda tazo wajansa zasu barta tashiga tayi juyin duniya sunki gashi rana se dukanta take
Yahya ne yazo wucewa yahangeta atsaye tarike kugu jitake kamar tahausu da duka
Nufo wajan yayi yana fadin wanake gani haka kamar asma'u
Murmushin farin ciki tayi tace nice Yaya dama nan kake aikine
Eh yafada yana kallon guards din yace lafiya naganki anan
Zufar goshinta ta goge tace wallahi wani abu nazo yi shine wa'yannan gumakan suka hanani shiga tafada tana Satan kallon guards din dasuka zaro ido jin ankirasu gumaka😳
Dariya yahaya yayi yana kallon guards din yace let her in she is my sister
Sannan yakalli asma'u yace muje ko gaba yayi tana biye dashi atsorace tawuce gaban guards din dan yanda suke kallonta ganin take kamar zasu rufeta da duka
Seda ya nuna mata office din ahmad sannan ya juya yana fadin idan kinfito kisameni abakin get zan baki sako ki kaywa zainab
Seda tadan jima atsaye kafin ta kuankuasa kofar
Daga ciki ahmad yabada izinin Shiga
Ahankali ta tura kofar tashiga wani daddaden kanshin turarene yadaki hancinta ga sanyin AC dayaratsata lumshe ido tayi ahankali tayi sallama
Dagowa ahmad yayi yana amsa sallamar
Mikewa yayi da murmushi afuskarsa yanuna mata kujera yana fadin bismillah zauna mana
thank u tafada tan zam akan kujera
Murmushi yayi yace asma'u ko
damamaki tace ya akayi kaganeni
Tashi yayi ya nufi dan karamin frig din dake gefe yadauko goran ruwa da cup sannan yadawo gabanta yatsaya seda yatsiyaya mata ruwan yamika mata sannan
Yadawo yazauna yana fadin kuna kama sosai da my flying bird shiyasa naganeki sunan ki kuma abakin khadeeja naji saboda duk rabin firarmu to akanki ne
Murmushi tayi takurbi ruwan hannunta sannan ta ijiye cup din tana karema office din kallo ahankali ta furta wannan office ne ko wurin hutawa
Murmushi ahmad yayi yace me kika gani
Kunyace takamata dan sam batasan maganr tafito fili ba Murmushi tayi tace nice decoration
Thank u yafada yana tunanin to mezai kawo asma'u office dinsa yama akayi guards suka barta tashigo
Kamar tasan tunaninda yake ta
Katse shirun dafadin ahmad nazo baka hakuri ne akan abunda khady tamaka kuanaki duk da nasan maybe kama manta but I can't have peace of mind ahmad ina kaunar khady sosai bana iya jure ganin abunda zai cutar da ita komai kankantarsa
sadda kanta tayi kasa taci gaba dafdin nayarda da kai nasan kana sonta tsakani da Allah dan Allah karka cutar da ita I know she is so disturbing sometimes but she have a good heart
Idan tamaka laifi ka kwatanta mata zata gane amma dan Allah kar kace zaka rabu da ita
Tunda tafara magana ahmad yake binta da ido yana murmushi shi kawai kamarsu da khadeeja take birgeshi
Tashi yayi yadawo kujeran kusa da ita yazauna yace aunty!!!
Saurin dago kai tayi tace aunty kuma
Eh yafada yana danne dariyarsa
Idan ma dan wannan ne ki kuantar da hankalinki ni naga deeja inaso kuma aurenta zanyi namaki alkawarin zan kula da ita fiye da yadda zan kula dakaina
Idan ma baki yarda ba se in ware maki daki daya agidan dazamu zauna kinga se ayi komai agabanki yakarashe maganar yana kwashewa da dariya
Itama dariyar tayi tace a'a ai abun bai kai haka ba nunashi tayi da yatsa cikin sigar wasa tace amma idan ka cutar da ita to ko abangwan duniya kuke se kaganni kuma zan dauki mataki
Hannunsa daya yadora saman kansa yana murmushi yace I promise aunty
Kauda kai tayi tana murmushi tace
Now stop calling me that aunty I don't like it
Dariya suka sa suduka kamar wa'yanda suka shekara dasanin juna
Daidai nan sarah tazo shiga office din tahangosu suna dariya
cak tatsaya tana kallonsu nunfashinta na barazanar dawkewa wasu hawaye masu zafi suna tsere akan kuncinta nan take taji kanta nasarawa
Saurin labewa tayi ganin suna fitowa daga office din
Muje mana inzaga dake kiga company dinmu ...
ahmad yafada yana rufo kofar office dinsa
Ido asma'u tazaro hade dafe kirji tace nikuma asuwa??
rufamun asiri
Dariya ahmad yayi yace to muje inrakaki mana
Kai ta girgiza tace a'a koma kawai kayi aikinka daganan ma nagode
Sarah dake labe tana jinsu jitayi kamar tazo tarufe su da duka nan take taji tatsani asma'u
Murmushi yayi yajuya yana fadin to nine da godiya ki gaida umma senazo insha Allah
Ganin Ahmad ya koma office yasa sarah tayi saurin bin bayan asma'u
koda asma'u tafito ta isko yahya yana jiranta abakin get wata sakon takarba sukayi sallama ta tafi
Yana juyowa yaga sarah tsaye agabansa taharde hannaye tana hararensa dajajayen idanuwanta
Gaidata yayi zai wuce tace kai zonan
Dawowa yayi gabanta yatsaya yana fadin gani ma
dawre fuska tayi tace wacece waccan da naganku tare
Sunkuy dakai yayi yace nasanta sosai madam kanwata ce kuma a unguwa daya muke
tsaki tayi tace waye ubanta anan garin
Saurin dago kai yayi yakalleta
Dakai nake malan ...
tafada tana daka mai tsawa
Hade fuska yayi yace malamin makaranta ne sunansa malan mahammadu ana kiransa magaji amma yajima da rasuwa
Hannu Tamika mashi tace bani wayanka
Damamaki yace wayata kuma
Daure fuska tayi tace ko ban isa bane
Mikamata wayan yayi yana ji kaman ya tattaka ta
Fisge wayan tayi ahannunsa tashiga wurin pics tana dubawa cikin Sa'a kuwa tahadu da photon asma'u Wanda sukayi da zainab ranan suna
murmushin mugunta tayi lokacinda tayi cropping photon asma'u ta tura awaynta cilla masa wayan tayi tajuya kamar zata tashi sama tanufi office din ahmad
Dakarfi ta bige kofan tashiga
Saurin dagowa yayi ganin sarah ce yasa yahade fuska yaci gaba da abunda yake bai kara kallon inda take bama
Ahasale takarasa ta fizge takardan hannunsa tana fadin yaushe kafara shigo dayan mata office dinka
Hannu yadaga mata yace sarah ya isa haka kiyi abunda yakawoki kibarmun office dina
Kugu tarike tana fadin ba inda zani seka gayamun wace karuwace tafito daga....
Bata karasa ba yakifeta da wani wawan mari seda kanta yabugu da table dafe kanta tayi tare dasakin wata kara
[18/07, 15:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧DOMUN KANWATA👩👧
Na( Maryam Muhammad jibril)
Dasunan allah mai rahama mai jinkai.....✍
6⃣0⃣
Gudu yake banawasa ba sarah duk tagama tsorata dayaninsa Sam batayi tunanin abun zaikai hakaba gaba daya yanayinsa ya canza
Yana isa company tun kafin yagama parking yafito daga motar zagayowa yayi tabangarenta yafincikota yana rike da hannunta suka nufi ciki
Ma'aikatan wajan suna gaidashi amma ko kallonsu baiyiba binsu sukayi da kallo suna mamakin yaw lafiya AK yashigo awannan halin
Office din ahmad yanufa direct yana isa ya banke kofar yashiga
Saurin dagowa ahmad yayi dan ganin waye
saurin mikewa yayi tsaye yana fadin AK lafiya meyafaru
Wurgi da sarah yayi har saida tafado kan ahmad
Cike da mamaki ahmad ya maidata gefe daya yanufo AK yana fadin easy AK wai meyake faruwa ne
Nima bansani ba kawai ina zaune tazo tasameni da wata banzanr magana wai kafasa aurenta....... baka sonta...... baka menene ...... Shirme dai iriri
Sunkuny dakai ahmad yayi yana murza hannunsa
Kusa dashi AK yamatso yakama hannunsa yana fadin bawai nazo nan dan nayarda da abunda tafada bane sedan ina so ka karyata abunda tafada agabanta taji
I know u can never do this to me ever
Shuru ahmad yayi yakasa furta koda kalma daya
Cikin muryan kuka sarah tace why are u silent kafadamasa abunda kafadamun mana ai bandauka zakaji kunyar abunda ka aikata ba
kafadansa AK yadafa yace friend say something kawai kacemun karyatake I will punish her for hurting u
riko hannunsa yayi cikin rawar murya yace AK ...I'm... I am Sorry ...but....she is....she is right
what do u mean???
AK yafada yana kafe ahmad da jajayen idanuwansa
Nasan ban kyewta ba danayi karyan cewa inason sarah tunda farko amma alokacin bansan mezance ba saboda abun yazomun abazata kuma bazan iya cewa banasonta abainan jama'a that will make u feel bad
Shiyasa kawai na amsa mata but I am really sorry
Ja dabaya AK yayi yazauna akan kujera tare dasauke wata nannayar ajiyar zuciya yana shafa kansa
Sannan yadago yakalli ahmad yace
Fine Naji wannan amma dagaske bazaka aureta ba shi kuma akan wane dalili
Matsowa kusa dashi ahmad yayi yana fadin AK ni inawa sarah kallon kanwata ne bantaba jin wani Abu dayashafi soyayya atare da ita ba ada nayi niyyar zan aureta ahakan amma daga baya nafara son wata yarinya kuma aurenta zanyi
Inada tabbacin idan na auri sarah bazan iya yin adalci atsakaninsuba saboda bazan iya controlling feelings dina akan wacce nakeso ba to akan wane dalili zan aureta
Karan bude kofa sukaji koda suka juya sarah suka ga tafita daga office din ko ba'afada sunsan kuka take
Tunda yafara magana AK kebinsa da wani irin kallon danakasa fassara manufarsa cikin sanyin murya yace
Ahmad kabani mamaki senake ganin kamar ba ahmad dina bane wannan Yaushe kafara boyemun sirrinka yaushe kafara soyayya meyasa zakama kanwata danafiso fiye dakomai karyan cewa kana sonta seda nagama sakankacewa zaka aureta shine zaka zomun da wannan maganar nayarda dakai fiye dayadda nayarda dakaina amma meyasa zaka yaudareni
Riko hannunsa ahmad yayi cikin rawar murya yace AK dan Allah kafahimceni nima bansan ya akayi nafara sonta ba bansan miye soba se akanta ni kaina ina mamakin yawshe nayi zurfi asonta dahar nakejin bazan iya rayuwa batare da ita ba
Turesa AK yayi dakarfi harsaida yafadi kasa cikin kakkawsar murya yamike tsaye yana fadin
Ba abunda zaka gayamun ahmad koma wacece inada tabbacin baka jima da haduwa da ita ba
Yaushe har kayi nisa asonta miye ma so ahmad akan sone zaka cutarmun da kanwata har zaka iya dawkan hannu kamareta kafi kowa sanin irin son datake maka baka tunanin halin dazata shiga idan tarasaka kuma ita wacce kakeso din kanada tabbacin cewa tana sonka ??
Tashi ahmad yana kakkabe rigarsa yazo gaban AK yatsaya yana fadin wai yanaga ka dauki abun dazafi ne AK
Nasan nayi laifi ban kyewta ba amma tunda wuri nayi kokarin sanar dakai sedai Sam kaki kasaurareni
Yes dagaske banjima da haduwa da ita ba amma shi so lokaci guda yake faruwa kuma bandamu yasoni ko kar tasoni ba Abu daya nasani shine ni ina sonta kuma mutuwa ce kawai zata hanani aurenta
zancan halin dasarah zata shiga kuma ai bani kadai bane namijin dayarage aduniya ba zata iya samun Wanda zata so yasota har yasa tamanta dani
amma ni bazan iya aurenta ba saboda bazan iya yimata adalci ba ni kuma bana fatan na cutar da wacce kakeso fiye da kowa aduniya
cikin murya mai kaman rada AK yace kenan yanzu kana nufin .....ba zaka ....auri kanwata ba kenan
Sunkuy dakai ahmad yayi cikin sanyin murya yace
I am sorry friend but I can't
Jadabaya AK yafarayi yana fadin sorry !!! Sorry!!!
ur sorry means noting to me since u broke my trust bantaba tunanin zaka ki jinina ba ahmad bantaba tunanin zaka So kanka a abotar mu ba
Daidai nan yafice daga office din yana rufo kofar dakarfin gaske
Zaunawa ahmad yayi yajiginar dakansa hade da lumshe ido yana murza goshinsa da yafara daukan zafi
Ahankali yake fadin
Meyasa bazaka fahimceni ba AK khadeeja nakeso ita kadai zan iya aura nazauna da ita na kula da ita kamar yadda nama yayarta alkawari bazan iya auren kanwarka ba bazan iya zama da mace biyu ba sarah bata dace dani ba
kace naso kaina dan naki auren kanwarka nikuma idan kahanani auren wacce nakeso saboda kanwarka ni kaso kenan kome!!!!
AK yana isa gida bangaren sarah yanufa kafin yakarasa aysha tazo ta tareshi tana fadin AK sarah
A firgice yarike hannunta yana fadin meyafaru da sarah ??
Ban saniba tundazu tashigo tana kuka kuma tarufe kofar dakinta taki tabude
Dagudu yakarasa kofar dakin yafara knocking sedai shiru ko motsinta bayaji duk yarude se buga kofar yake kamar zai ballata yana magiyar tabude amma taki
Cike da damuwa yace sarah open the door please
come down OK?
I am here everything will be fine I promise
Cike da mamaki aysha tace wai meyake damunta ne
Ko kallonta baiyiba bare tasa ran zai amsa mata bashiri yakira dai daga cikin ma'aikatan gidan yataimaka mashi suka balla kofar
Kuance suka sameta atsakar dakin Sam ba alamun nunfashi atattare da ita dagudu yakarasa wurinta yajanyota jikinsa yana kiran sunanta amma shiru yaron gidan mai suna Nura shine yayi dabaran kiran family doctor dinsu awaya aysha banda kuka ba abunda take
Hannunsa yakai daidan saitin zuciyarta amma baiji alamun tana bugawa ba nan take jikinsa yafara rawa jijjigata yake dakarfin gaske kamar zai karyata yana fadin a'a a'a sarah please don't leave me keda grany kunake gani naji dadi arayuwata idan kika tafi yazanyi for god sake say something
gefen fuskarta yafara bubbugawa cikin rawar murya yake fadin kitashi namiki alkawarin zan taimaka maki kinji zansa ahmad ya aureki I promise I will make u proud kinsan duk abunda kike so ina maki please wake up ganin ba alaman zata tashine yasa yafashe dakuka ya rungumeta tsam ajikinsa yana surutai kala kala
Ahaka doctor din ya iskosu dasauri AK yamike daga zaunen dayake akasa yanufi doctor yana fadin doctor please help my sister
Bring her to bed ...doctor din yafada yana ijiye briefcase din dake hannunsa
Cak yadauketa yadawrata kan gado doctor yamatso yafara dubata yana fadin idan badamuwa kudan jirani daga waje
AK yakasa fita seda aysha taja hannunsa tafita dashi
Cike da takaici yace wai tun kika ji shiru adakin meyasa baki kirani ba
Nakira mana amma wayanka akashe
Ina mutanen gidan suke
Bansaniba tafada tana ware hannayenta
Bangaran inna ladidi yanufa ahasale yafara buga musu kofa
rai bace tafito tana fadin kai lafiya wayene natsani.....ganin AK datayi atsaye fuskarnan a murtuke yasa ta hadiye sauran maganarta tana fadin oh AK Ashe Kaine
Fuska ahade yake fadin kinji karan knocking din danamaki amma bakiji lokacinda nake balla kofar dakin sarah ba
Meyasamu dakin sarah da ake balla kofar
Mutuwa tayi
Afirgice tace mutuwa kuma AK subhanallahi yo idan ma mutuwar ce fisabilillahi haka zaka fadamun ita salan zuciyata tabuga
Kai yakauda hade da cije lebensa nakasa sannan ya juyo yace
Ankayata wancan babban palon ne badan yazama na ado ko na family meeting ba a'a sedan yazama cibiyar kara donkwan zumunci da kaunar juna manufarsa kenan amma dazaran kunbiya bukatar Ku acan shikenan se kowanne yashige bangaransa bawanda zaisan halin da dan uwansa yake ciki
Kuma nagayamaki kanwata tamutu amma har yanzu dai ke takanki kike wai kada zuciyarki tabuga bana tunanin ma kinada zuciyar ajikinki
Hade fuska tayi tace to wai meyasamu sarah ne naga duk kafita hayyacinka ne
Idan kinso sani kizo kiduba da kanki ....
Yafada yana juya baya yakoma
Dakallo tabisa seda yabace mata sannan ta tabe baki takoma ciki tana fadin dama kasaba ai idan wani Abu yasamu sarah to ko bacci hanamu kake wai mutayata jaje bare kuma ance batada lafiya ai munshiga uku shiyasa na guanmace ni nayi ciwo akan sarah koba komai nasamu nayi bacci mtswwwww
Suna tsaye abakin kofa shida aysha doctor yafito dasawri AK yakarasa wajansa yana fadin doctor ya jikinta meya sameta hop she is OK
Dafa kafadansa doctor yayi yace be strong man kanwarka lafiyarta kalau kawai dai damuwa ce tayimata yawa kuma da alamum tajima rabonta da abinci
Juyowa yayi yakalli aysha saurin sunkuy dakai tayi tana wasa da yatsunta
maida kallonsa yayi kan doctor yace
To yanzu ya jikinta
Jiki dasauki yanzu dai namata allura tana bacci ga wannan idan ta tashi taci abinci tasha wannan se kudan barta tahuta kadan anjima zan dawo
Godiya yama doctor din sannan sukayi sallama yatafi nura narike da briefcase dinshi suka fita
ahankali yatura kofar dakin yashiga aysha nabiye dashi abaya kusa da ita yazauna bakin gadon yana kallon yanda take sauke nunfashi ahankali lokaci guda duk tacanza tayi wujiga wujiga kamar ba sarahn dayasani ba yar gayu mai son kwalliya nan take yaji tawsayinta yakama da ahankali yashafi gashin kanta da ya barbage akan pilon datake kuance akai
Aysha nadaga gefe haushi duk yacikata ganin yanda duk yarude akan sarah har yake fadin wai ita da grany kawai yake gani yaji dadi to ita kuma ko oho kenan ko
Kusa dashi tamatso tadafa kafadansa tana fadin AK naga lokaci yana tafiya ko kama grany maganrmu
Wani gigitaccen kallo dayawatsa mata ne yasa tayi waje tana fadin bari nashirya mata abunda zataci idan tafarka dakallo yabita seda tafita sannan yamike ya gyara mata bargon sannan yafita
bangaren grany yanufa mamaki ne yakamashi ganin yan uwansu makil apalon wasu yaganesu wasu kuma bai sansu ba suna ganinshi suka haw shewar ango ango
Bayabo ba fallasa ya amsa gaisuwarsu ya wuce dakin grany tana zaune kan gado tana lissafa kudi
Tana ganinsa tawashe baki tana fadin ahh abidi karaso mana dazu naje dakinka banganka ba gaka baki ko
zama yayi abakin gado baice komai ba
Lafiya abidi grany tafada tana karantar yanayinsa
Ajiyar zuciya yasauke sannan yace sarah ce ba lafiya grany
Afirgice tace subhanallahi me yasameta
ba wani Abu bane dasauki ma yanzu doctor yaduba ta
Tashi tayi tana fadin bari naje naganta baiwar Allah ai bansaniba kasan ba shiri mukeba
a'a barshi kawai yanzu tana bacci anjima kyaje
Dawowa tayi tazauna tana fadin to Allah yasawake
Ameen yafada yana yana mikar da bayansa kan gadon
Baki grany tawashe tana fadin abidi kaga su bala da shehu sunzo ko
kai yagirgiza yace a'a ban gansuba suna ina
Suna sashen baki dazu suka zo gobe insha allahu zasuje suga magabatan yarinyar dazaka aura tunda ta amince
Damamaki yace ta amince fa kikace koda yake ba abun mamaki bane dan tayi saurin amincewa auren AK hausawee dama nasan za'arina
nan take yaji yarinyar bata kuanta mashi ba dan yafison mace mai aji ba mayyar abun duniya ba wani dogon tsaki yaja hade da kauda kai
Hade fuska grany tayi tace to ana maganar arziki mekuma yakawo tsaki yadai kamata kaje Ku gana da yarinyar taganka kufahimci juna
Mikewa yayi yanufi hanyar fita yana fadin tunda ta amince kafin taganni that means bata bukatar ganina abunda takeso daban
Baki bude grany ke kallonsa har yafita girgiza kai tayi tace gaskiya akwai abunda yake damun yaron nan
Ahmad ne zaune a dining yasa abinci agaba se juya cokalin yake amma yakasa koda loma dayane Momy dake gefe tana kallonsa tafahimci akwai abunda yake damunsa tunda yashigo gida dazu
Kujeran Kusa dashi tajo tazauna tana fadin ahmad wai meyake damunka ne kuana biyu naga kanada damuwa amma kaki fadamun kuma na lura kaman auren sarah ne bakaso to meyasa zaka takura kanka ana dolene
Sunkuy dakai yayi kasa baice komaiba
Dakai nake magana kayi banza dani
Dago kansa yayi yafara bata labarin abunda yafaru tun a airport har izuwa yau
Shiru tayi bayan tagama saurarenshi can tadago tace gaskiya baka kyewta ba ahmad amma banga laifinka ba shi mutum bayada ikon saka so ko cirewa sedai kawai ince Allah yashige mana gaba kuma kasamu AK kabashi hakuri yanada saukin kai nasan zai fahimceka kasan yanda yakeson kanwarsa
Shiru yayi baice komai ba
Murmushi tayi tace oh kai kwa duk yan matan da suke binka kamar hauka karasa wacce zaka so se khadeeja wannan karamar yarinyar
Se alokacin yadago kai yana murmushi yace kai Momy khadeejan ce Karama
Tashi tayi tana fadin nidai kahada ni da aiki da zaka kamun suruka trouble maker
Dariya yayi yace Momy ai irinsu akeso
Abangaren Umma da abba kuwa shiri suke bana wasa ba izuwa yanzu kowa a dangi yasan da zancan auren asma'u kowa yayi farin ciki da wannan ala'amarin
Bakamar khadeeja datake jin kamar tajanyo ranar tadawo yau
Bangaren asma'u kuma duk tafita hayyacinta tsakanin jiya da yau har wata yar rama tayi tana mamakin wane kalan aurene wannan da za'ayishi asati guda kuma har yanzu angon bai nemi yaganta ba bayan tanada tabbacin bai Santa ba
Dakin sarah AK yakoma daga bakin kofar yatsaya yana kallonta ahankali yabude idonta tasaukesu akansa
Saurin karasowa bakin gadon yayi yana fadin Ashe kinfarka murmushin dole tayi tana kallonsa ga hawaye na gangarowa agefen fuskarta
zaunawa yayi
daga gefenta aysha kuma tana tsaye gefen kanta tana kallon ikon rabbi
Yatsansa yasa yana goge mata hawaye cikin muryan lallashi yace stop crying kanwata kukan nan naki yana daga mun hankali ki kuantar da hankalinki Ahmad bashi kadai bane namiji aduniya ba zaki samu Wanda yafishi komai ....
Katsesa tayi dafadin bashi kadai bane namiji aduniya ba amma ni shikadai nakeso kuma shi zan aura he only belongs to me takarshe maganar tana kara fashewa da kuka
Nasan kina sonsa kanwata amma kiyi kokarin danne sonsa kimanta dashi
ahasale yakarashe maganar dafadin just forget him saboda yace bazai aureki ba
😭I can't..... I can't Yaya bazan iya mantawa da ahmad ba and I won't let him go !!!
Kauda kansa yayi gefe guda yana jin wani irin haushin ahmad dayajefa kanwarsa awannan halin
Aysha ce tace ni ina mamakin wace yarinya ce wannan da ahmad yamutu akanta har yake wulakanta sarah
nima dai bansaniba AK yafada yana kallon sarah
Saurin tashi zaune tayi tafara Neman wayanta
Menene inji aysha tana tayata daga bargon dake kan gadon
Kan dressing mirror tanuna mata tana fadin bani wayana
Dauko wayan tayi Tamika mata
Tana karba tafito da photon asma'u Tamika ma AK tana fadin wannan ce yarinyar
Karban wayan yayi yana dubawa zunbur yamike yana fadin wannan ai nasanta
Kafeshi sukayi da ido suna son jin a ina yasanta
Kanshi yashafa yana fadin no wonder shiyasa ranan naganta agidansu ahmad kuma ina yawan ganinta a unguwar amma bansan ko wacece ba
Babanta malamin makaranta ne sunansa malam mahammadu amma ana kiransa magaji sedai yajima da rasuwa
Tunda tafara magana AK yakafeta da ido yanason tuna ina yataba jin sunan
saurin rikota yayi yana fadin wait kika ce babanta malamin makaranta ne sunansa magaji kuma yajima da rasuwa ko
Kai ta gyada mai alamar eh
Zama yayi akan gado tare dasa hannayensa biyu yana shafa sumar Kansa data hargitse lokaci guda
Kusa dashi aysha tamatso tadafashi tana fadin lafiya AK menene kasanta ne
Dago da kansa yayi yana kallon sarah yace itace yarinyar da grany takeso na aura
Dip suka dauke wuta ba mai motsi ba kamar aysha datake jin kamar tasaki fitsari
Wata nannawyan ajiyar zuciya ta sauke arenta take fadin ohh thank god kaga bazata amince da auren AK ba tunda tanason ahmad
Kamar yaji mai tace yayi saurin fadin ina mamakin meyasa zata amince da aurena bayan kuma tana son ahmad
Dirowa daga kan gado sarah tayi tana fadin haba nifa nasani seda nagayama ahmad yarinyar nan basonsa takeba kawai kudinsa takeso shine yanzu taji AK hausawee yana Neman aurenta mezai hana ta amince bayan tasan ya ninka ahmad kudi
To yanzu miye abun yi inji aysha datakejin kamar ta kurma ihu saboda tashin hankali
mikewa AK yayi yana fadin kawai zanje nasamu grany nagayamata abunda yake faruwa inada tabbacin ita dakanta zata nemi afasa auren
saurin riko hannunsa tayi tana fadin Yaya dan Allah kataimake ni kar kafasa aurennan
Shiga gabanta aysha tayi cike da Bacin rai tace sarah hankalinki daya kike fadan wannan maganar kuwa
Tureta sarah tayi seda takusa faduwa AK yayi saurin rikota tafado kansa
Cikin daga murya sarah tanunata dayatsa tace
da yayana nake magana bake ba so stay out of it
Gefen fuskarta AK yashafa da hannunsa yana fadin come down baby take it easy
meyasa kike so na aureta
Hannunsa takamo cikin dasashshiyar muryanta take fadin
Yaya kaga kai kasan yarinyar kasan cewa kudi ne kawai agabanta mayaudariya ce shikuma ahmad bai saniba ko zamu shekara muna fadamasa ba yarda zaiyi ba Idan har kafasa aurenta shi zai aureta kaga zata cutar dashi nasan kana son ahmad bazaka so wani Abu yasameshi ba so please help us !!!
No sarah I can't do this bazan iya auren yarinyar da ahmad yake mutuwar so ba
Yaya please kafahimci abunda nake nufi natabbata ba ahayyacinshi yake ba wayasani ma ko asiri tamasa kawai dan tacimma nufinta akansa kaga idan ka aureta zamu koyamata darasi shikuma ahmad zai gane ba dagaske take sonshi ba natabbata zai dawo gareni kai kuma ka ceto abokinka daga hannunta
Shiru yayi nadan lokaci yana tunani
Aysha ce tadafa kafadansa tana fadin AK dan Allah kar kayarda da shirmen sarah tayama zaka sauri wannan yarinyar bayan kasan ahmad yana sonta dawane ido zaka kalleshi
Katseta yayi dafadin
ZAN AURETA KODAN FARIN CIKIN KANWATA
Sannan naceto abokina daga tarkonta I will punish her senasa ta tsani rayuwarta se nasa ta durkusa gaban ahmad da sarah tanemi yafiyarsu
Rungumeshi sarah tayi cike dafarin ciki tana fadin Yaya thank u
You are my hero
Girgiza kai aysha tayi tafita daga dakin aguje tana sharan kwalla
Dakallo AK yabita yana yunkurin binta sarah tarikoshi tana fadin a'a barta Yaya zan mata magana nasan zata fahimceni
Ok bari nasa akawomaki wani Abu kici se kisha magani
Bakin gado yakaita yana fadin come and have some rest
Bayan kuana biyu......
Shirye shirye yakan kama atsakanin gidajen biyu dan tuni magabatan ahmad suka suka je sukasami abba da duk wani abu na al'ada kuma sukace basa bukatar komai daga wajan iyayen amarya abba yayi farin ciki matuka nan take aka tsaida dawrin aure ranar juma'a a central mosque
Umma ma shiri take bana wasa ba gyaran jiki asma'u kesha nafitan hankali Umma dakanta kemata dama guana ce awannan Wurin cikin kuana biyu asma'u ta canza tayi wani fresh da ita ko ina bata zuwa daga daki se bayi sedai daga ka ganta kasan tana cikin damuwa nakadan ba
Su khadeeja da nusaiba ba'akama hannun yaro kullun suna zirga zirgan zuwa kasuwa da shagon dinki damma abba yace bawani party ko dinner nan daza'ayi ana dawra aure akayi walima za'akai amarya dakinta
Bayanda basuyi dashiba amma yaki
haka suka hakura
Abangaren grany ma tagama shirinta tsap yau za'akai lepe akwatina goma shabiyu kuma tsadaddun kayane acike makil bawanda zaice a Nigeria ta hada lepenta ko yan uwansu sundawka akasan waje aka hado
Sarah ma tsake da ita ake komai tun grany tana mamaki har tasake sukaci gaba dashiri
AK kam idan bawanda yasani ba bawanda zaice shine angwan bayanda grany batayi ba dashi akan yaje Yaga asma'u kafin dawrin aure amma yaki ba inda yake zuwa daga daki sai masallaci rashin ahmad akusa dashi duk seyaji bayajin dadi kuma har yanzu yana jimamin tayadda ahmad zai fuskanci abun anya kwa baiso kansa dayawa ba wata zuciyar tace ai kayine saboda shi kuma sadaukarwa ce wata rana shidakanshi zai godemaka akan abunda kayimasa
Da wannan tunanin yake dan samun natsuwa amma ya yanke shawaran tura ahmad Turkey saboda bayaso yasan dazancen auren harsai komai ya kammala
Abangaren aysha kuwa
duk dacewa sarah tashayo kanta ta amince da maganar auren amma sam takasa sakewa tana tunanin matakin da iyayenta zasu dawka akanta idan suka dawo dan duk abunda yafaru itace sila
Ga inna ladidi da bashir sun sakata agaba da tsokana wai tayi kuantai wani lokaci tahade fuska ko tayi tsaki wani lokacin har kuka yitake
ganin abun yayi yawa tashirya zatayi tafiya amma AK yahanata wai tatsaya ta tayashi cin uban amaryarshi ....lol😅
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( Maryam Muhammad jibril)
6⃣5⃣
Gida yasha gyara banawasa ba hatta paitin gidan ansake shi
sedai AK bai yarda kowa yasan da zancen aurensa ba saboda bakowa yasan asalin sunansaba kowa yafi saninsa da AK hausawee
tun ajiya yayi nasaran tura ahmad turkey kan harkokin kasuwancin su batare da ahmad yasan zancan auren aminin nasa ba haka yatafi yana kokonton akwai abunda AK keboye masa ko khadeeja ma se awaya yafada mata zancan tafiyarsa
seda grany tamatsama AK sannan ya amince akan zaije ya gaida abba da Umma sannan yaga asma'u daga can
Seda yafara zuwa wurin abba yagaidashi cike da ladabi da girmamawa yasamu tarba ta musamman daga wajan inna dan rasa inda zata sashi tayi
yadan jima awurinsu seda sukayi sallar isha'i sannan yawuce gidan su asma'u bayan ya ijiye mata bandir din kudi itada sauran mutanen gidan
Yana isa gidan su asma'u aka mishi iso har cikin palon gidan
Nan ma cike da ladabi yagaida Umma da sauran mutanen dasuka zo taron biki Umma tayi farin ciki matuka saboda tayaba da nagartar AK nan take taji ya kuantamata duk wani zargi yafita aranta tasamu nutsuwa
Bayan sungaisa da Umma tanufi ciki akan zata turo asma'u sugaisa
Dakin asma'u tanufa cike da farin ciki
Bakin gado ta iskota azaune khadeeja kuma tana gefe tana sallah
Kusa da ita Umma tazauna tana fadin asma'u tashi kije Ku gaisa ya iso
Tashi asma'u tayi jiki asanyaye tana fadin Umma kidan jira khady tagama tarakani mana
Daure fuska Umma tayi tace dan Allah wuce yana jiranki me khadeeja zata maku banda shirme da surutu
Tafa hannu khadeeja tafarayi alaman adan jirata
Dariya Umma tayi tace ai kuma sedai kiyi
Sannan tajuyo tana ma asma'u alamar ta tafi
Fita tayi daga daki tana gyara zaman gyalen data rufe fuskarta dashi
Tunda tanufo palon wani fitinannen kanshin turare yadaki hancin AK shakan iska yayi ya furzar yana lumshe ido yana hangota ya kauda kai yana daure fuska
Ahankali takaraso palon tazauna daga gefe ta takure wuri guda tana gaidasa
Wani kallon tsana yawatsa mata aransa yana fadin afuska kamar mutuniyar arziki dama kindaina ba kanki wahala dan nasan ainahin wacece ke
Mamaki ne Yakama asma'u jin bai amsa gaisuwarta ba kamar tadago takallesa se kuma tadake data tuna bawannan ne karo nafarko dayafara mata haka ba
Shuru sukayi apalon bawanda yace komai har natsawon lokaci
Wata karamar yarinya ce tazo wucewa ta palon AK yakirata
Tana zuwa kusa dashi tagaidashi yace ya sunanki tace nafisa
Yace yawwa nafisa je kicema Umma uncle zai tafi
Dagudu yarinyar ta tafi tana fadin toh
Haushi ne Yakama asma'u ahasale tamike tanufi dayan dakin tana jan tsaki
Da kallo yabita yana murmushin mugunta aransa yana fadin kin kusa shigowa hannu yarinya wannan tsiwar taki zata zama tarihi arayuwarki
Shigowan Umma ne yakatse mashi tuna ninsa mikewa yayi yana fadin Umma nizan wuce dare yayi se wani lokacin
Murmushi Umma tayi tace to Allah yakaimu ina ita kuma wannan yarinyar take
Murmushin yake yayi yafita yana fadin Umma kibarta kawai tahuta gajiya ce tamata yawa zamuyi waya anjima
Murmushi Umma tayi tace to shikenan ka gaida gida Allah yakiyaye
Khadeeja ce tafito aguje tana gyara zunbulelen hijabinta tanufi waje tana salati
Dakallo Umma tabita tana dariya
Dawowa tayi jiki asanyaye tazauna tana fadin haba Umma meyasa zakimun haka kinsan kwa yanda nakosa naga mutuminnan shine zaki mun cikas
Dariya Umma tayi tace to kuana nawa yarage khadeeja har sai kin gaji da ganinsa
Langwabe kai tayi tace Umma bazaki gane ba....
bata karasa ba tahango damen kudi akan kujerar da AK yatashi
Saurin tashi tayi tanufi wajan tana fadin umma ango yayi kwai
Kauda kai Umma tayi tana fadin kefa kin cika shirme wane irin kwai kuma
Kudin tadakko tanufi umma tana washe baki tace wannan shine fidduniya hasanatan
Karban kudin Umma tayi tace kawo khadeeja nabama asma'u wayasani ma ko yamanta ne mukuma mayun kudi kawai muhau kai ni wallahi da nagansu kafin yatafi da bazan karba ba
Kinga ko yanzu yamuka kare da tsegumi wai auren kudi mukama asma'u
Tsaki khadeeja taja tace Umma idan kika biye ta mutane to ko abinci bazakiciba Allah dai yabasu zaman lafiya kawai
Hannunta takai kan kudin tana fadin amma dai wannan kwan kikawoshi nasoyeshi
Bige hannunta Umma tayi tace dallah can matsa kudin nan ijiyesu zanyi khadeeja gaskiya bazan Ciba
Tashi khadeeja tayi tana kuasar hijab dinta tawuce daki tana fadin kawai dai ki ijiye inda bazan ganiba
Rana bata karya
Yau takasance juma'a kuma itace ranar daurin auren AK da asma'u
Dasafe misalin karfe 11narana sarah da aysha ne zaune abangaren AK suna fira
AK yadago yakalli sarah yana murmushi yace ya ake ciki ne wai zancan bikin nan wane shirye shirye kukeyi
Dariya tayi tace bawani shirin da ake ni abun ma dariya yake bani kaman wasan yara
Dariya aysha tayi tace amma ina mamakin meyasa dangin amarya ko kawayenta basu nemi wani Abu da yashafi kudi ko gudunmawa daga wajan angoba
Tashi AK yayi yanufi daki yana fadin abbanta yace bawani shagalin da zasuyi walima kawai ta isa
Sarah tace eh haka naji abakin grany
Mu kuma idan ankawota zamu hada dan kwarya kwaryan party anan gidan daganan kuma kowa ya watse
Aysha tace AK ya kukayi da momyn ahmad dataji zaka auri wata daban daki yashiga yana fadin bansan yasukayi da grany ba nasan abakinta taji
Misalin karfe 14:00 dubbanin jama'a suka shaida *auren* ABID da ASM'AU akan sadaki 500.000
a central mosque dake Abuja
Anci ansha anmore duk da dai bahaka akaso ba amma anji dadi grany da inna baki yaki rufuwa
asma'u kuma tundaga lokacin tafara kuka khadeeja natayata har izuwa lokacinda za akaita dakin mijinta kuka take kaman ranta zaifita tsam tarike Umma da inna taki sakinsu haka da aka kaita wurin abba yamata nasiha da kyar aka banbarota ajikinsa
Motoci na alfarma suka zo daukan amarya tasamu rakiyar mutane da dama su Ummi ne akan gaba se Momy da zainab din yahya da sauran dangi da yan uwa sedai ba kawayen amrya dan asma'u batada wata kawar data wuce khadeeja yan matan wurin duk kawayen khadeeja ne
Tun amota asma'u ke kuka khadeeja na gefenta tana lallashinta har suka iso dankareren gidan AK wato (hausawee Mansion)
Inda suka samu tarba ta musamman daga wurin dangin ango bangren grany akafara kaita bayan anmata nasiha da sauran abubuwan al'adarsu sannan aka nufi bangaren AK da ita baki bude kowa keyawo agidan tundaga get wasu sukafara santin gidan bare daga ciki aljannar duniya sekafita waje zaka San dare yayi yan mata sun zage se selfi ake ana turo baki
Da kyar so Momy suka tattara su suka fita dasu
Asma'u nazaune akan gado khadeeja tashigo kusa da ita tazauna tana fadin ammah kinga gidanki kuwa adduniya wama fiha Yasin aka sakeni tsab zan bata agidan nan gaskiya yahadu
Momy ce taleko tana fadin to khadeeja kuzo mutafi dare yayi konan zaki kuana
asma'u tayi saurin fadin eh Momy kubarta anan
Tashi khadeeja tayi tasukuyo saitin kunnen asma'u cikin rada take fadin ammah gara ma kibarni natafi I'm just 17 karku rudani gashi ahmad baya gari bare ayi namu gobe
Tureta asma'u tayi tana fadin Allah ya shiryeki kekam
Dariya Momy tayi tace tafara halinta ko saurin barin wurin khadeeja tayi tana fadin a'a Momy kawai cewa nayi zaman aure ibada ne yi nayi bari nabari
Dariya Momy tayi tabi bayanta tana ma asma'u seda safe akan se sunzo walimar gobe
Sunkuy dakanta tayi cikin guywowinta tana zubar da kwalla yaune karo nafarko dazata kuana batare da ummanta ko khady ba tunani dai iriiri take yi har dare yayi tsawo amma ba ango ba alamarsa
Gidan yayi shuru ba kajin motsin kowa
har karfe dayan dare amma AK baishigo ba tun tana tsoron shigowarsa har tafara damuwa
Ganin dare yaraba tafara tunanin ko lafiya
Shi kuwa AK yana can wurin aysha yana lallashinta dan tunda taji andaura aure tafara rusa kuka tana shagwaba iri iri
atakaicedai bashi yashigo ba se karfe biyun dare
Ahankali ya tura kofar yashiga tana zaune agefen gado tana gyangyadi
Tsaye yayi daga bakin kofa yana kallonta tana bacci batamasan yashigo ba
Cikin sanda yanufi dan karamin frig din dake gefe ya dauko goran ruwa mai sanyi yadawo tagefenta ya tsaya yana bude gorar ruwan yana murmushin mugunta
Daga goran yayi sama yafara kwarara mata ruwan tundaga kanta
afirgice tafarka tana Jan dogon nunfashi tana goge ruwan fuskarta tana fadin miye haka dan Allah
Wannan wane irin rashin iman....
Nunfashinta ne yakusa dawkewa ganin AK tsaye agabanta rike da goran ruwa fuskarnan tashi kamar baitaba dariya ba
Nunashi tayi dayatsa muryanta narawa take fadin kai....kuma...mekake anan
Kara daure fuska yayi yafara matsowa kusa da ita tana ja dabaya seda yakaita jikin bango
atsorace tarufe idanunta kam tana sauke nunfashi ahankali
Hannunsa daya yakai jikin bangon cikin murya mai kaman rada yake fadin
Kina mamaki ne ...
Son abun duniya ya rufe maki ido har takai baki damu dakisan waye mijinki ba Yaya kamaninsa suke Yaya halayensa suke wannan duk bai dameki ba tunda kinsamu abunda kike kwadayi
Da mamaki tabude idonta tana kallonsa cikin rawar murya tace ni bansan abunda kake magana akai ba
Ban nemi nasan kamanninka ba saboda badan haka na aureka ba
Juyawa yayi yana fadin yes!!! Dama nasan badan haka kika aureni ba sedan kinsan ina da kudi
Matsowa tayi daga jikin bango tana fadin Kaine kudi yadama ni basa gabana na amince da aurenka ne sedan kawai inada tabbacin abbana bazai zaba mun abunda zai cuceniba
Kuma nasan wacece grany shiyasa kawai na amince da na'aureka amma danasan Kaine wallahi daba abunda zaisa na aureka mezanyi da....
Juyowa yayi ahasale ya cabki wuyanta idonshi yayi ja nan take yarikide yazama tamkar wani zaki a tsorace asma'u ke kallonsa tana kokarin kwace wuyanta daga hannunsa amma takasa koda motsa hannunsa ne
Cikin kakkausar murya yake fadin ke bakyama jin kunyar fadan wannan maganr agabana ko kina tunanin bansan ko ke wacece ba idan kinyi nasara akan abokina to ni Nafi karfinki
sena hukuntaki senasa kin tsani rayuwarki I will make ur life a living hell
I will destroy ur happiness daga yanzu kinyi bankuana da farin ciki arayuwarki
ba abunda zai biyo baya se da kinsani danadama kuma bazata miki anfani ba
Turata yayi dakarfi akan gado tafadi tana tari tana shafa wuyanta daysha damka
Hanyar fita yanufa zai fita tayi saurin tashi tashiga gabansa cikin rawar murya take fadin
wai miye laifina da na cancanci wannan hukuncin daga gareka kawai dan na amince da aurenka
Idan kasan bakasona meyasa ka aureni
Kallonta yayi sama da kasa ganin yanda tayi wujiga wujiga ga doguwar rigarta tajike sharkab da ruwa
Kwashewa yayi da dariya wadda daga gani kasan taketa ce kyalkyalata yake bawasa har da dafe ciki baki bude asma'u ke kallonsa takasa magana
cikin dariyar yake fadin come on laugh kiyi dariya kila tazama itace takarshe dazakiyi arayuwarki
Sannan yatsagaita da dariyarsa yamatso kusan yana fadin
Tambayata ma kike wai miye laifinki ko to bari nafadamaki
kinsan ahmad
wane ahmad tafada tana ja dabaya
Wani malalacin murmushi yayi yace karma kice mun harkin manta da saurayinki da kika yaudara bayan kinsa yayi nisa asonki kika watsar dashi kika aureni dan kinji zancan kudi
Kikasa kanwata ta zubar da hawaye daga ranar da taganki a office dinsa daga ranan tadaina farin ciki
kika rabani da aminina tunda muke dashi bamu taba fada ba se akanki
Lokaci guda kika shigo rayuwarmu kika ruguza mana ita dayanzu mosoyiyata ce anan dakin amma adalilinki tana can tana zubar da kwalla
Wannan auren punishment ne agareki sekinyi dakinsanin rayuwarki senasa kin tsani rayuwarki sekowa yasan true color dinki sannan zan sakeki
Yana kainan yatureta daga gabansa yawuce yana banko kofar dakarfi
Nan take jikin asma'u yafara rawa durkushewa tayi awurin tafashe da wani irin kuka mai cin rai cikin kukan take fadin
😭meyake shirin faruwa dani ne menayima waya'nnan mutanen zasu dawki alhakina ni bansan meyake magana akai ba wayyo Allah nah!!!
Saurin safe kanta tayi data tuna maganganunsa
Cike datashin hankali take fadin ohh my god kenan ya aureni ne amatsayin budurwan ahmad ganin dasuka mun a office dinsa ranan tunaninsa nice khadeeja
Wayyo Allah nagodemaka daka kubutar da kanwata daga sharrinsu dayanzu itace ahalin danake ciki yanzu wayyo khadyta Allah yashiga tsakaninki dasu
Haka dai tayi rusa kuka tana sambatu iri iri jin kanta yana Sara mata yasa ta sulale awurin taci gaba da kukanta har bacci yadauketa
AK kuma yana fita daganan farm house dinsa yanufa cikin Daren dayake banisa acan ya kuana se dasafe yanufo gida
Cikin sanda yashigo gidan dan kar kowa yagansa da gudu gudu ya hawra sama yana waigen bangaran grany yana isa yatura kofar yashiga
akuance ya iskota inda yabarta jiya da alama tun baccin jiya da yadauketa bata farka ba da har yanzu kayan jiya ne ajikinta
Toilet yanufa batare da yasake kallon inda takeba
Karan knocking din dataji ne yatasheta daga baccin datake ahankali tafara bude idonta tana fatan duk abunda yafaru jiya yakasance mafarki ne ba gaske ba
Wasu sababbin hawayene suka gangaro afuskanta lokacinda take karema dakin kallo tana tuno abunda yafaru jiya
Jin anata knocking yasa tatashi jiki asanyaye tanufi kofa Sam bata lura da yanayin datake ciki ba
Grany tagani tsaye abakin kofa rike dawata kwalla tana washe baki
Dip murmushin fuskarta yadauke lokaci guda tana kallon asma'u sama da kasa cike damamaki ta ijiye kwallar Tana fadin lafiyanki kuwa asma'u yanaganki haka meyasameki ina abidi din yake
Zatayi magana kenan taji anrungumota tabaya atsorace ta juya dan ganin waye
AK tagani atsaye yana mata murmushi cikin shirinsa tsab yayi kyew matuka sekanshi yake zubawa janyota yayi jikinsa yana fadin good morning darling ...
Baki bude take kallonsa ko kifatawa batayi
Takasa cewa komai
Juyowa yayi yakalli grany dake tsaye tana kallonsu tana murmushin jin dadi
Yace
Ohh grany ashe kina nan kintashi lafiya sannan yamaida kallonsa kan asma'u yana murmushi yace kinganta ko gajiya ce tamata yawa tun jiya dasuka zo take bacci se yanzu da kyar natasheta
Juyawa grany tayi tana murmushi tace kuyi sawri kushirya ana jiranku akasa kashiga da wannan kwallan ciki
Yana ganin grany ta tafi yajanye jikinsa daga asma'u ya wuce batare da yace komai ba
Dakallo tabisa har yafita sannan ta dauki kwallan tashiga da ita ciki
Zaunawa tayi abakin gado tana share hawaye
Sarah ce tashigo dakin rike dawasu kaya ahannunta ta ijiye abakin gadon tana fadin amarsu ta ango ina kwananki
Lafiya asma'u tafada tana kauda kai
Murmushi tayi tace ko dayake ban damu dasanin ya kika kuana ba dan nasan Yayana yakula dake yanda yadace
Kayan tanuna mata tana fadin ga wannan kiyi sawri kishirya ana jiranki
AK ne yashigo yana fadin kidan Zane mata fuska da kawalliya karta tsorata mana yara da jajayen idonta
Dariya suka samata ahasale tadauki kayan tanufi bayi tana fadin
Kune abunda tsoro bani ba
tana shiga ta turo kofar dakarfi
Sedai mamaki ne yakamata ganin bawani alamun wurin wanka awurin
Wani makeken wurine dafadinsa har yafi nadakin girma
Drowa ce gaba daya azagaye dawurin Cike makil da kaya kamar anbude shago dayan gefen kayantane awurin amma yawancinsu dogayen riguna ne se English wear masu bala'in kyew dayan gefen kuma kayan AK ne Jere awurin daga kasa kuma takalmansa ne kala kala gefe guda kuma turaruka ne da kayan shafa kala daban daban sewani daddaden kamshi ketashi awurin
seda ta kwashi tsawon lokaci tana zagaye wurin amma bataga alamun kofa ba tsaki taja tafita tana fadin yanda mai dakin yake arikece haka komai nasa yake ahargitse
ahankali tabude kofar ta leko kanta dan ganin ko suna nan AK kawai ta hango azaune yana waya
tsaye tayi tana kallonsa tana wasa dayatsunta
Har yagama wayar ya jiyo ahasale yana fadin
Malama tundazu me kika tsaya yi dabakiyi wankan ba ko kina jira nazo namaki dakaina ne
Kauda kai tayi tana zunbura baki tace Allah ya kyewta ni wurin wankan ne bangani ba
Dariya ce takusa kwacemasa yadake yamike yana Jan tsaki ya nufota yana fadin banza yar kawye
Matsawa tayi tabasa hanya yashiga tabisa abaya tana zunbura baki tana gunaguni
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na ( Maryam Muhammad jibril)
7⃣0⃣
Yana shiga yadanna wani Abu daga gefe kawai drowowin suka bude Sega hanyar dazata sadaka da bathroom tafito tsakanin drowan kayanshi data Asma'u
Baki bude take kallon ikon allah seda taga ya waigo wurinta sannan tayi sawrin kauda kai tana daure fuska
Hanyar yanuna mata yana fadin dallah zo ki wuce
Gefenshi taraba tashiga tana zunbura baki
Leko kansa yayi cikin bayin ya nuna mata irin abunda yadanna awaje yana fadin idan kin gama wannan zaki danna inbaki iyaba kuma ki kuana aciki
Saurin danna abun tayi kofar tafara rufewa tana hararansa tace to jeka malam naji
Sabon shafin kallon tabude datashiga bayin saboda bayin har yafi dakin girma
Komai nabayin farine tas gawani katon madubi daya mamaye rabin bangon daga gefe anjerishi da duk wasu abun bukata
Sewani katon shower irin natsaye dinnan daga gefe guda gawata drowa daga gefe anjereta dasabulan wanka da shampoo kala kala wani wuri taga anzagayeshi dawasu manyan labulai kalan golden kamar kar taje se kuma takarasa ahankali tayaye labulen
Wani dan faffaden bathtub tagani awurin wanda girmansa kaman dan madaidaicin seeming pool
Daga gefe anjera sabulai da turarukan wanka kala daban daban
Cike da birgewa take kallon wurin jitayi kamar tashi se kuma taba zuciyarta hakuri takoma wurin shower
Seda tashafi kusan awa daya kafin tafito mai kawai tashafa se turare tasaka kayan da sarah takamata
Wata doguwar riga ce milk color mai kama da wedding gown se tayafa gyalen rigar duk da batayi wata kwalliya ba amma tayi kyew sosai seda tajima atsaye kafin ahankali ta turo kofar tafito
atsaye yake yakafe kofar da ido da alama ita yake jira
Yana ganin tafito yayi hanyar fita batare dayace komai ba
Seda yakai bakin kofa ya waigo yaganta atsaye inda take batada niyyar motsawa
Iska ya shaka ya furzar sannan yadawo inda take atsaye
Tana ganin yanufota tafara jadabaya tana fadin me kuma nayi
Baice komai ba yacapko hannunta yayo waje da ita seda yarufo kofa sannan yasaki hannunta yayi gaba yana fadin to yanzu idan kinga dama kizo ko kizauna
Haryayi nisa tayi saurin bin bayansa dan ko za'akasheta batasan hanyar dazata kaita kasa ba
juyowa yayi ita kuma tataho suka kusa cin karo
Saurin cin birki tayi tana daure fuska
Kusanta yamatso fuska ahade cikin murya mai kaman rada yace
Wallahi kinji narantse idan har kika bari grany tafahimci abunda kefaruwa senamiki abunda se kinmutu baki manta dani ba
Kauda kai tayi aranta tana fadin ko yanzu ai kamun
Kina jina ...
Yafada yana daka mata tsawa
Atsorace tadaga kai tana fadin eh eh allah naji
Gaba yayi tana binsa abaya har suka sawko babban palon gidan inda yasha decoration da manyan furanni da balalan masu kyew gawani daddaden sawti natashi ahankali
Wurin acike yake da zalla matasa samari da yanmata yawancinsu duk kawayen sarah ne dana bashir da kuma sauran family
Manyan kuma suna bangaren grany suna tasu walimar
Tunda suka sawko kowa kebinsu da kallo dan sun hadu iya haduwa amma fuskarnan tasu ahade ba alaman far'a
DJ naganin sun iso ya sawya salon kidansa inda yakoma na soyayya nan take aka hau shewa da tapi
Seda suka fara zuwa bangaren grany suka gaida su sunsha tsokana daga wurin kakannin AK
Sedai kawai Suyi murmushi su sadda kai
Sun dan jima awurin kafin suka dawo Babban palon
Sarah da aysha nabakin kofa suna tarban baki amma aysha naganinsu hankalinta duk yakoma Kansu nan take taji wani bakin ciki ya lullubeta
Fa'iz da nusaiba ne suka iso gidan se washe baki suke suna bin gidan da kallo sunci ado sunyi kyew cikin shiga ta ya'yan masu kudi dan abba na kokari wajan saya musu sutura daga su har khadeeja
Takusan su sarah suka wuce amma sam basu gane suba
khadeeja nadaga baya suna gaisawa da yahya datagani aharabar gidan
Tunda tanufo wurin Tagane sarah sadda kai tayi kasa tana fadin badai wannan bace kanwar Ak datake son ahmad
To ko dayan ce dakwa nayi abun kunya amma ai sune basuda gaskiya awaccen ranar
Dawannan tunanin takaraso wurinsu
Sunkuy dakanta tayi zata wuce sarah tace
Ke !!! Tsayawa tayi bata juyoba
Karasowa gabanta tayi tana leken fuskarta
Cak tatsaya tana kallonta tana son tuna inda tataba ganinta
Cikin kakkawsar murya tace
Ke mara kunya uban me kike anan me kika zoyi
Daure fuska khadeeja tayi tace ubanda kowa yake anan shinazo yi
saurin riko sarah aysha tayi tana fadin sarah stop it kanwar amaryan mu cefa tafada tana kefta mata ido
wucewa khadeeja tayi tana jan tsaki
Cike da takaici sarah tace no wonder tunda nafara ganinta naji natsaneta
Khadeeja tana Shiga ta isko asma'u na gaisawa dasu fa'iz da gudu takarasa ta rungumeta
Bayan sungaisa asma'u tace ina Umma
Murmushi khadeeja tayi tace Umma tana gida jiya kuana tayi tana fira cike da farin ciki kamar ba itaba
Fuskan tawsayi asma'u tayi batace komai ba
Dafata khadeeja tayi tace ammah lafiya naganki wani iri ne
Murmushin dole asma'u tayi takauda kai tana fadin kawai ina missing din Umma ne
Kauda zancan khadeeja tayi dafadin meyasa bakiyi make up ba dase kinfi kyew
Fa'iz ne ya zunguri khadeeja yana nuna mata AK dake gefe
Azaune yana waya
Baki tawashe tace laaaaa wallahi kwa shine kai ammah gaskiya kun bala'in dacewa guy dinnan yahadu dayawa Ashe mijin ammah tane
Sadda kai asma'u tayi batace komai ba
Karasawa wurinsa khadeeja tayi tana washe baki
Yana ganinta yadaure fuska hade da kauda kai dan koba'a fadaba yasan tahada wani Abu da asma'u saboda kamar dayagani afuskanta
Tana isa wurinsa tazauna akujerar kusa dashi tana gaidashi
Bayabo ba fallasa ya amshi gaisuwarta
Murmushi tayi tace baka sanni bako?
Girgiza kai yayi alaman a'a
Kanwar matarka ce ..
Tafada tana kokarin gano yanayin fuskarsa
Murmushin yake yayi yakauda kai yace
Sannunki toh ya Umma
lafiya ..
Tafada atakaice
Satan kallonsu asma'u keyi tana tsoron kada khadeeja tagano halin da ake ciki
Sadda kai khadeeja tayi cikin sanyin murya tace i hop u like my sister
Saurin kallonta yayi Da mamaki yace meyasa kika ce haka
Saboda ban hango farinciki atattare daku ba nasan inada kananun shekaru amma daga kallon kwayar idon yayata nakan tantance halin datake ciki
Nasan yanda aurenku ya kasance kunyishi batare da kun fahimci juna ba
Amma yayata tanada sawkin kai kuma tanada hali mai kyew idan kabata hadin kai dan lokaci kankani ya isa kafahimci wacece ita
She has a golden heart please don't break it
Takarashe maganar muryanta narawa
Maida kallonsa yayi kan asma'u yaganta tana Gyara ma nusaiba dawrin dan kwali suna dariya
Yajima yana kallonta sannan ya jiyo ya kalli khadeeja yana murmushi yace
Bana so nakaiga zuciyar bare har nakaryata
Murmushi tayi amma badan tagane meyake nufi ba
Tashi yazo yi tayi saurin rikoshi tana fadin tsaya mana ai bamu gama ba
Zaunawa yayi yana girgiza kai sedai baisan meyasa ba Sam bayajin haushinta
Dariya tayi tace sorry ni haka nke sedai kayi hakuri amma har yanzu baka gayamun ya kaga yayata ba
Kallonta yayi yace what is ur name
Dariya tayi tace khadeeja.....
Juyowa yayi suka fuskanci juna sannan yace
Deeja I've found ur sister like a very big book look interesting but very boring
Bude baki tayi dashirin magana yayi saurin katseta da fadin ohhh khadeeja ina fatan kizama yar jarida nan gaba Zakiyi ma kasa anfani
Tabe baki tayi tace kana nufin inada surutu kome
Dariya yayi baice komai ba
Itama dariyar tayi tamatso kusa dashi cikin rada tace wai acikin yan matan nan biyu nawaje wacece kanwarka
Mai kama dani...yafada atakaice
To dayan fa wacece
My girlfr.....
baikarasa ba yayi saurin fadin no she is my cousin
Zatayi magana kenan kiran ahmad yashigo wayarsa
Tashi tayi tabashi wuri takoma wurinsu asma'u sukaci gaba da fira
Daga wayar AK yayi tare da sallama
Tadayan bangaren ahmad ya amsa sallamar yana fadin friend nifa na iso yanzu haka ina company
OK yafada atakaice
Shiru ahmad yayi nadan lokaci yana mamakin haryanzu AK yana fushi dashi jin karan music na tashi yasa yayi kasa da murya yana fadin kana ina ne naji hayaniya
Ina gida mana..
Ok kuna wani shagali ne
Nayi aure friend ...
Dip nunfashin ahmad ya tsaya cike da mamaki yace aure fah kace AK
Eh... jiya kuma ....
Cikin sassanyar murya ahmad yace
Aysha... ka aura ne??
a'a... watace daban
Wakenan ??
Idan kazo zaka ganta I know u will be shock
Ok ..
Ahmad yafada yana ajiye wayar da mamakin wacece AK ya aura kuma meyasa bai auri aysha ba
AK yana gama wayar ya juya baiga khadeeja ba girgiza kai yayi yana murmushi sannan yama sarah alama tazo
tana zuwa yace sarah munyi waya da ahmad ya iso yanzu kuma yana hanyar zuwa nan gidan
Murmushi tayi cike da farin ciki tace wow!!! Kai amma naji dadi har nakosa yazo dan naga ya zai yi idan yaga budurwarsa amatsayin matarka
Kauda kai yayi da damuwa afuskarsa dan karfin hali kawai yake amma bayason ganin bacin ran ahmad
MC ne yafara sanarwa na kowa yasamu wuri yazauna zasu fara shirye shiryensu
Dariya fa'iz yayi ya kalli khadeeja yana fadin deeja yau zamu rakashe ...
Dariya tayi tabashi hannu suka kashe
Sarah dake kallonsu tawuce wurin aysha tana murmushin da bansan kona miye ba
Bayan kowa ya zauna
MC yabukaci kowa yashigo fili yataka dan taya ango da amarya murna
Haka kowa yatashi yafara rawa fa'iz da khadeeja nadaga zaune banda dariya ba abunda suke
Cike da takaici sarah ke kallonsu
Tana fadin wallahi yaran nan haushi Duke bani ni Sam banga lokacinda suka wuce ba da ban barsu sunshigo ba
Dariya aysha tayi meyasa bazamu dan buga wasa ba
Tsaki sarah tayi tace wasa dawa?
Dasu man badai kin iya rawa ba ?
To bari kiga
Tana gama fadan haka tamike tanufi wurin MC wata magana tamasa akunne naga yayi murmushi
Sannan yanemi kowa Yakoma yazauna
Bayan kowa yazauna sannan ya nemi ganin kannin amarya guda biyu
Kallon kallon aka fara tsakanin fa'iz da khadeeja
Sannan tamai alama dasuje
Tsakiyar filin suka je suka tsaya cike da birgewa kowa ke kallonsu saboda Kansu daya gashi suna yanayi wasuma sunzata yan biyu ne
Bayan sun gaisa dakowa sannan MC yabukaci ganin kannin ango guda biyu
Nan take aka hau tapi da shewa ganin sarah da aysha sun fito cikin shiga tariga da wando sunyi kyew sosai
Juyowa asma'u tayi takalli AK dake gefenta azaune tana fadin wai mezasuyi??
Hannayensa yaware yace ohoo yanda kike da ido biyu nima haka nakedasu to muzubasu muyi kallo
Kauda kai tayi cike dajin haushin kanta dan Sam bata San lokacinda ta tambayesa ba
MC yabukaci kowa ya nutsu yanzu za'a kalli gasan rawa tsakanin kannin ango da amarya
Cike da firgici khadeeja takalli fa'iz
Sedai ga mamakinsa murmushi taga yanayi
Zunguranshi tayi tana fadin kai wai kaji abunda yace Kuwa
Dariya yayi yace haba deeja wani ma yayi rawa bare dan makadi haka kawai ma mun zage mun tiki rawa bare kuma abikin ammah shima kuma wai gasa
Kansu sarah aka fara inda suka zabi wakar dasuke so dakansu
Nan take DJ yasaki kida su sarah da aysha suka fara takawa rawa suke bata wasa ba amma sarah tafi aysha iyawa
Har suka gama su khadeeja nagefe suna kallonsu
Tapi aka hau yi ana shewa kowa nayaba rawansu
Bayan hayaniya talafa MC yabukaci kannin amarya su shigo fili
Fa'iz yakalli khadeeja yana fadin deeja muje mana
Jadabaya tafarayi tana fadin gaskiya fa'iz bazan iyaba mutane sunyi yawa kunya nakeji
Nan take aka hau nunasu dayatsa ana dariya
Juyowa AK yayi yana kallon asma'u yaga fuskanta ta canza tana kallon fa'iz daya sadda kai yakasa motsawa
Sarah da aysha kuma se dariya suke suna tapa hannu (ni kwa nace girma yafadi😏)
Dariya yayi yace inaga kanwarki bakinta kawai ta iya sarrafawa amma banda gangar jiki hahaha
Sadda kanta tayi kasa batace komai ba
Kallonta khadeeja tayi setaji duk bataji dadi ba kamar takoma amma tayaya
Karban microphone din fa'iz yayi cikin dakewa yafara fadin
Hello guys!!! kanwata ba guduwa tayiba kuma batsoro taji ba
Kunsan duk macen da tacika mace ansanta da Jan aji da basarwa
Rawanta Nada tsada so u have to beg for it !!!
nan take aka fara tapi ana kiran deeja!!! Deeja!!! Deeja!!!
Karasowa fa'iz yayi kusa da ita cikin rada yace deeja please u have to this for our sister kalla kiga yanda angonta kemata dariya duk danasan wasa ne amma bazataji dadiba
Murmushi tayi tace ok let's do it
Hannunta yakamo suka dawo filin rawan
nan aka hau tapi ana daukan su photo saboda sunbirge kowa awurin
Karban microphone din MC yayi yana fadin
ok twins which song are u ready to dance on ??
Kallon mutanen wurin khadeeja tayi tana fadin mun basu zabi
Tapi aka haw yi ana shewa kowa nafadan wakan dayakeso
Nan dai DJ yasakar musu wakar humma song suka fara rawa
Haba ai nan take kowa yamike akafara daukansu video saboda yanda suke bin kidan suke rawa kuma komai tare suke yinshi gwanin sha'awa
Shi kanshi AK sunbirgeshi
Tun kafin sugama kowa yafara tafa musu ana basu winning
Haushi ne Yakama sarah cike da takaici taja aysha suka bar wurin
Har suka gaji amma anki bari su sauka daga wannan wakar takare se asaka wannan se da kyer suka kwace kansu
Dariya asma'u tayi tamike tsaye tana kallon AK tace
Inafata kanada isashshen jinin da za'adiba akarama kanninka dan naga sunada bukatarsa
Zai yi magana kenan ya hango ahmad atsaye agabansu kaman gunki yana kallonsu
Murmushi yayi ya mike yanufosa yana fadin ohhh welcome back Friend
Shuru ahmad yayi yakasa magana yana mamakin me kuma yayar khadeeja take anan
Asma'u kuma data basu baya Sam bataga ahmad ba
Hannu AK yasa yajanyota yana fadin meet my wife
Cike da masifa ta jiyo da nufin magana amma cak tatsaya ganin ahmad agabanta
Sadda kanta tayi kasa bawanda yace komai
Wani malalacin murmushi AK yayi daya hango mamaki karara afuskar Ahmad
Jadabaya AK yayi yana murmushi yace bari nadan Baku waje kuyi magana sannan ya juya yanufi wurin da yahango aysha atsaye
Yana tafiya ahmad yakalli asma'u cike da mamaki yace wai dama kece AK ya aura garin Yaya dama kunsan juna ne
Dagowa tayi ta kallesa cikin rawar murya tace yanzu ba lokacin magana bane Ahmad khadeeja tana nan wurin ga sarah
dan Allah katafi banaso sugane akwai wani Abu atsakaninku
Tana kainan ta juya tanufi bangaren grany tana boye kwallar data cika mata ido
Da kallon tawsayi yabita ahankali ya furta something is fishy
Sarah ce tazo kusa dashi tana murmushin mugunta tana girgiza kai
tace ohhh so sad !!!
Kayi mamakin ganin budurwanka anan gidan ko sannan ta langwabar dakanta tacigaba dafadin
to ya na iya naso nafita hanyarka amma nakasa shiyasa nadauki wannan matakin
Wani kallo mai cike da tsana yawatsa mata yaraba tagefenta zai wuce tayi saurin riko hannunshi tace tsaya mana Yaya baka tambayeni ya akayi yarinyar dakake ikrarin tana sonka tayi saurin amincewa auran wani batare da saninka ba
Daidai nan khadeeja tazo wucewa tahangosu kamar ance yadaga kansa kawai ya hangota tana barin wurin da sauri har tana hadawa da gudu
Cike da takaici yabige hannun sarah yana fadin kirike tatsuniyarki bana bukatarta
Sannan yabi bayan khadeeja yana kiran sunanta
Ahasale sarah tanufi bangarenta tana fashewa da kuka
Tafiya kawai khadeeja take bata Masan inda tanufa ba sedai kawai taganta a garden shakan wani iska mai dadi tayi ta lumshe ido sannan tazauna adaya daga kujerun wurin tana kallon katon seeming pool din dake gabanta
Kusa da ita ahmad yazo yazauna
Sunjima ahaka bawanda yace kala
Secan tasauke ajiyar zuciya batare data kalleshiba tace yaushe kadawo??
Dazu....
Yafada atakaice batare daya kalleta ba shima
Meyasa baka gayamun ba
Nakiraki wayanki akashe
Daganan kuma suka kara yin shiru nadan lokaci kana cikin cikin sassanyar murya ahmad yace
I am sorry...
Se alokacin tajuyo takalleshi tana murmushi tace no I'm sorry
Kallonta yayi yana murmushi baice komai ba
Sadda kanta tayi kasa ahankali tafurta I missed u
Missed u more yafada cikin jin fadin maganarta
dagowa yayi yana kallonta yace meyasa baki gayamun AK yana son yayarki ba
Fuskar tawsayi tayi tace nima kaina bansan AK ne zai aureta ba sedaga baya
damamaki yace kamarya ??
Nan tabashi labarin abunda yafaru
Ajiyar zuciya ya sawke Dayagama jin bayaninta sannan yadago yakalleta da damuwa afuskarsa yace deeja ni inada shakku akan wannan auren
Meyasa kace haka
Ranarda asma'u tazo office dina sarah taganta kuma aranar nake gayamata bazan aureta ba inada wacce nakeso to setayi tunanin asma'u ce wacce nakeso din
Shakan iska yayi ya furzar sannan yacigaba da fadin
Deeja nasan wacece sarah tana kokarin ganin tasamu duk wani abunda takeso
Shikuma AK zai iya yin komai dan farincikin ta
Ni bansan meyake faruwa ba amma hankalina yakasa kuanciya da aurenan
Cike da damuwa khadeeja tace nima nayi wannan tunanin saboda dazu nazo wucewa naga AK tare dawannan cousin din tasa aysha kuma ayanda nagansu hankalina bai kuanta ba shiyasa nazo inaso na tambayi ammah
Sekuma naganka da sarah
Ahankali ta furta meyake faruwa ne
ki kuantar da hankalinki balalle ne abunda muke zargi yazamo gaskiya ba
Saurin barin wurin tayi tana fadin bari naje naga ammah
Asma'u ce tashigo bangarensu azaune taga AK apalo yadafe kai
tsaye tayi tana kallonsa aranta tana fadin to shikuma wannan meke damunsa
Dagowa yayi ya kalleta cikin kakkawsar murya yace kallon me kike mun bayan duk ke kika sakani awannan halin
Shiru tayi tasadda kanta kasa batace komai ba
Tasowa yayi yakaraso wurinta yana fadin duk lokacinda abokina yayi tafiya idan zai dawo ni nake Zuwa natarboshi na rungumeshi nakawoshi gida muci abinci tare muyi fita tare amma yanzu ta dalilinki ko sannu dazuwa mai kyew nakasa yimai
Kin ruguza mun rayuwata kin rusa mun farin cikina kin cutar da aminina bazan taba yafemaki ba
Yana kainan ya tureta daga bakin kofar seda tafadi ahasale yabanke kofar yafita
Cak yatsaya yana kallon khadeeja dake tsaye abakin kofar fuskarta sharkap da hawaye tana jifanshi dawani kallo mai cike da tsana
tagefenta yaraba ya wuce batare dayasake kallonta ba
Kamar kartashiga har ta juya sekuma tasa kai cikin dakin
asma'u naganinta ta tashi azaunen datake akasa tana share hawayen fuskarta
Rungumeta khadeeja tayi tafashe dawani irin kuka mai ban tausayi
Dafa kanta asma'u tayi cikin rawar murya tace khady menene lafiya meyafaru
Cikin kuka khadeeja tace ammah meyasa !!! Meyasa!!! Kika boyemun halin da kike ciki
Mutuwar tsaye asma'u tayi dan Sam bataso khadeeja tasan halin datake ciki ba
Dagota tayi tafara Share mata hawaye cikin rawar murya take fadin
Ni ba abunda yake damuna khady I like the house ...
the family was nice..
And I like my husband he is good man ...
And grany was taken care of me ..
Kuma kince Umma tana farin ciki
Wannan kadaima.. ya isheni...
Katseta khadeeja tayi dafadin
a'a ammah bazai yuwu ba mutanen nan basa sonki kawai yaudarar ki sukayi Sam baki dace dasuba
Jan hannun asma'u tanafadin kizo mukoma gida kawai
Rikota asma'u tayi cikin muryan kuka tace no khady please bazan iya tafiya ba kiyi tunanin kuana daya da bikina aganni agida me mutane zasuce za'ama su abba dariya wane hali Umma da inna zasu shiga kinsan basuda cikakkiyar lafiya idan abba yaji kanshi zai dorawa laifi zaice shi yajamun bazai yafema kansaba
Kuma narabu dasu kanki zasu koma bazasu kyaleki ba
Sulalewa kasa khadeeja tayi tana wani irin kuka mai cin rai dogowa tayi takalli Asma'u data safe kai saboda bata iya jurar kukan khadeeja
Cikin muryan kuka khadeeja tace ammah
Tun ina Karama kike wahala akaina yanzu na girma ma amma baki huta ba zaki kara fuskantar wata rayuwar akaina wallahi hakan yasa natsani kaina ...
Saurin toshe mata baki cikin rawar murya tace a'a khady kidaina fadan haka wannan nadaukeshi amtsayin jarabawa ne daga Allah kuma nakarbeta hannu biyu inafata Allah yabani ikon cin jarabawar
Kin manta kintaba gayamun cewa inada hali mai kyew zaki tayani da addu'a Allah yabani miji nagari ba kya tunanin addu'ar ce Allah yakarba
Da kyar asma'u ta lallashi khadeeja tayi shiru sannan ta roketa akan kar tagayama kowa halin datake ciki ahmad tabari dakanta zata mai bayani
bayanin datama khadeeja shitama ahmad amma da kyar ta shayo kansa ya hakura da zacan da cewa yayi se yaje yasanar da grany halin da ake ciki
Bayan angama taro kowa ya watse tun aranar yane uwansu suka koma
Ahmad ne yamaida Momy dasu khadeeja gida
Gidan yayi shuru har antattare angyara yakoma yanda yake da
Kowa na bangarensa
asma'u har ta kuanta taji anturo kofa afirgice ta tashi zaune ta kure kofar da ido 😳
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: AK ne yashigo yana cire coat dinsa
Ganin yanufo gadon yasa tayi saurin driwowa kasa tana zare ido
Ko kallonta bai yiba ya ijiye coat din akan gado sannan yakalleta yana fadin kewai kallon namiye
Ko kina tunanin zan kuana wuri daya dake ne idan kina bukata ta kibiyoni inda nake
Kauda kai tayi tana fadin ba'abunda zanyi dakai so zaka iya tafiya
Nasan kina so natafi dan kisamu daman zuwa wurin ahmad
Sannan yamatso kusa da ita yace
kina son ahmad ko?
Eh... Tafada atakaice
Girgiza kai yayi yace karya kike bazaki iya son kowa ba saboda kudi kawai kike so
Matsawa tayi daga gurin tana fadin kai kuma bawanda zai soka saboda kanada bad altitude
Dressing room dinsa yanufa yana fadin u will suffer nan gidan dakike kwadayin shiga seya zame maki prison saboda ba inda zakije
Dakallo tabishi tana fadin idan dai har zakayi nesa dani badamuwa
Juyowa yayi yana kallonta yace bakinki zai mutu ranarda nayi ball dake daga gidan nan ahmad ya auri sarah ni kuma na auri aysha
Sannan yadawo kusa da ita yace kina mamaki kinji nace aysha ko to itace budurwata
Tayarda na aureki ne dan tasan ko giyar wake nasha bazan fada sonki ba
Dariya tayi tace ta amince ne saboda batasan me ake cewa so ba datana sonka dabata yarda ka auri wata ba
Shiru yayi nadan lokaci kamar mai tunani can kuma yace tasan cewa kudi ne agabanki
Kauda kai tayi ahankali tafurta ni bansan meyasa mutane suke haukan kana birgesu ba bayan ni kuma inaji kadameni
Ahasale yace
be quite kar ki manta agidana kike kuma adakina sannan yajuya yanafadin so yakamata ki girmama ni
Itama ahasale tace kai kuma karka manta kana magana da matarka ne
Juyowa yayi da mamki yana kallonta sannan ahankali ya furta mata?? Mata fa kikace?? To idan ma bacci kike kifarka wannan matsayin yafi karfinki kuma bazaki taba samunshi ba
Nagaya miki this is just the beginning of ur suffering!!
Kauda kai tayi tana fadin I am already regretting it
Dariya yayi yace to ai baki maga komai ba tunda auren kawai kika gani senasa kin tsani kanki
Karasowa tayi gabanshi tana fadin wai ma meyasa katsaya kana magana dani kamata yayi ace kana wurin budurwanka yanzu ni kahanani bacci katafi kawai gobe kaacigaba da cimun fuska
nayarda nan din prison ne awurina all tnx to u
Fita yayi daga dakin yana fadin u are welcome
Dakallo tabishi sefa yafita sannan tadauke coat dinshi da ya ijiye akan gado tanufi dressing room tana mitar ta tsani taga kaya akn gado
Cikin sanda AK ya sawko dwonstairs yanufi hanyar fita yana Satan kallon bangaren grany
Har yakai kofa kamar daga sama yaji tace
Abidi ina zuwa cikin wannan Daren
Runtse ido yayi hade da cije lebe bai jiyowa ba kuma nai yi magana seda tace bada kai nakeba sannan ya juyo yana sadda kai irin na mara gaskiya
Ganin ba wasa afuskar grany yasa ya kalalo murmushi yana Sosa kai yace grany zan dan fita ne ahmad yan jirana
Daure fuska tayi tace ba inda zakaje wannan lokacin kamata yayi ace kana tare da matarka
Buga kafa yayi da kasa kaman zai fashe da kuka yace haba mana grany bafa dadewa zanyi ba
Amma bata saurareshiba ta tasa keyarshi seda taga yashiga bangarensa sannan ta juya tana masifa
Asma'u har tayi shirin kuanciya cikin doguwar rigan baccinta har kasa mai kyew
Taji anturo kofa
Atsorace ta juyo ganin AK atsaye yasa tayi saurin daukan gyelenta ta yafa tana fadin
Mekuma yadawo dakai...
Tsaki yayi ya kauda kai yana yace daban ysaya fada dake ba dayanzu nafita amma gashi kinja zan bata lokacina anan
Karasowa cikin daki Yayi yafara cire shirt dinsa
afirgice takauda kanta tana fadin wai mekake shirin yi
Kallon kin raina mun hankali yayi mata sannan yace kima daina acting kamar wata mutuniyar arziki bayan kinfi kowa sanin abunda nake shirin yi
Sake kauda kanta tayi tana facing mirror tace abunda kake baka kyewtawa
Karasowa yayi tabayanta yatsaya yana cire belt dinsa yace nan daki nane kuma ahaka nasaba kuanciya idan kinga bazaki iyaba zaki iya zuwa waje ki kuana
ai bai gama rufe baki ba tayi waje aguje sedai tana fita ta tsinkayo grany tafito daga dakin sarah
Saurin shan kuana tayi tadawo dakin tana rufe da idonta
AK yana daga kwance kan gado ya lullube da bargo yarufe ido kamar mai bacci Sam baiji shigowarta ba
Lalube tafara kan gadon tana Neman pilo by mistake ta taboshi
Afirgice ya tashi yana bige hannunta
Atsorace ta bude idonta tana Sosa inda ya bigeta
Tsaki yayi yace to ke koda kinada bukata haka akezuwa ba notice
Daure fuska tayi tadauki pilo tana fadin not interested
Kwace pilon hannunta yayi yace wannan pilo nane kinema wani
Dayan pilon tadauka hade da blanket takoma Palo kan 3sitter ta kuanta ta rufa da blanket din tana jin kewar Umma da khadeeja
har bacci yafara daukanta taji AK na atishshawa
Banza tayi dashi ta gyara kuanciyarta tana fadin alhakina kadai ma ya isheka
Jin abun yayi yawa yasa tamike tanufi dakin
Ahankali ta tura kofar tashiga
Tana shiga taji AK nafadin to wai meke damuna ne ..?
Remote din AC tadauka takashe sannan tanufi wurin kettle tadaura ruwa
Damamaki yake kallonta yana fadin malama lafiya zaki kashemun AC wayasaki
Banza tayi dashi seda ruwan yayi dumi sannan tazubo a cup ta kawomasa
Damamaki yace what are u doing
Kauda kai tayi tace kaina nakeyiwa saboda bazan iya yin bacci dawanan atishawar taka ba
Karban ruwan yayi yana fadin ai daga yau kindaina bacci mai dadi sannan yakai ruwan bakinsa
Da kyar yasha rabin Kofi ya mikamata sauran yana yamutsa fuska kin karba tayi tace idan bakasha dayawa ba bazaka warkeba
Ijiye kofin yayi akasa yana fadin bazaki kasheni da ruwan zafi ba
Daukan copin tayi tamaida tanufi hanyar tana fadin kuma kanemi kaya kasa kafin ka kunna AC
Da kallo yabita seda tafita sannan yaje yakarasa hanye ruwan dumin dayarage yasaka riga ya koma cikin bargo
Washegari dasafe......
Wayanshine keta ringing yana kwance yana bacci
Jiyayi andafashi yariko hannun yana fadin baby I am not feeling well wannan yarinyar taban ruwan dumi naji dadinsu amma...
Bai karasaba asma'u tamaka mai pilon dake hannunta
Afirgice yatashi yana kallonta da mamaki yace mekike anan
Dariya tayi tace mummunan mafarki kake ne
Daure fuska yayi yana fadin kece mummunan mafarkina
Wayarsa Tamika mai tana fadin dan Allah kadauki wayanka tadameni da kara
Fizge wayan yayi ahannunta yana duba mai kiran
Murmushi yakai wayan kunne yana fadin hi baby
Tashi asma'u tayi tanufi dressing room
Tadayan bangaren aysha cikin mryan shagwaba tace honey ina fata ba abunda yashiga tsakaninku
Dariya yayi yace haba wa kema kinsan nafi karfin haka so kawai ki kuantar da hankalinki I only belongs to u
Dariya tayi suka ci gaba da firarsu
Sarah ce da AK zaune abangaren grany suna breakfast
Can sarah tadago tace Yaya idan nasamu lokaci inaso zanyi tafiya
Dagowa yayi yakalleta yace ina kuma zakije awannan lokacin
Yaman ...nakeso naje akwai abunda zai kaini
Sanin acan tayi karatunta shiyasa bai yiwata gardama ya amince
Cike da farin ciki tace thank u Yaya amma kamun alkawarin bazaka kula wannan yarinyar ba
Lomar abinci yakai bakinsa yana fadin kar kidamu ba abunda zanyi da wannan mai fuskan yara ..
AK ne zaune ababban palon kasa yana kiran Nura dagudu Nura yakaraso yadurkusa yana fadin gani yallabai
Kaje wurin grany ka karbomun coffee
Washe baki nura yayi yace ai yanzu nafito daga can nabaro madam tana hada wa tace idan tagama zata kawo
Wace madam din ...
AK yafada cike da mamaki
Sadda kai nura yayi yana fadin madam dai amarya
Gyada kai AK yayi yana fadin takawo to ina jiranta
Asma'u na bangaren grany tafaketa tana koyamata yanda akema AK coffee dan tace yanzu yayi aure bazata iya wahalar hadamai kofee so uku arana ba
Kayan kanshi tadibo tazuba
Damamaki asma'u tace kayan kanshi a coffee kuma grany
Eh haka yake sonshi se kisa ido sosai ki kula
Bayan grany tagama hadawa tabata takaimasa
Yana zaune ta iso da coffee din a cup tadoreshi kan dan karamen faranti da teaspoon agefe se kanshi yake
Grany nadaga nesa tana kallonsu amma baiganta ba
Karban cup din yayi ya kurpa
Saurin furzarwa yayi yana fadin wannan coffee ne kome
Anya ma kintaba hada coffee kuwa
Dawannan bagara naje nasaya natiti basha ba mema yasa grany bata hadamun ba se ke
Karasowa grany tayi tana fadin Abidi dagaske baiyi dadi ba amma ai haka kake sonshi shiyasa nayishi haka kuma baka taba cewa baiyi dadi ba se yau
Da mamaki yake kallonta dan Sam baisan tana wurin ba baki yawashe yana fadin haba ai ina dandana shi nasan ke kikayi yayi dadi sosai
Daure fuska tayi tace to meyasa kakema asma'u magana haka badadin ji
Dariya yayi yace grany mufa ma'aurata ne zamu iya tsokanar junanmu yana kara dankon kauna
To shine kuma seka fara mata tunda sassafe
Satan kallon asma'u yayi yana fadin saboda inaso itama ta iya Wanda yafi naki dadi shiyasa nakushe Wanda takawo
Amma kiyi hakuri grany bazan karaba
Murmushi tayi tace ba komai kudai kuhada kanku kuzauna lafiya kar kuji jiya yanda ake yabon Ku wallahi har cikin raina naji dadi
Abidi dan Allah karike yar mutane amana kaji
Tashi yayi yanufi sama yana fadin idan ma dan wannan ne saranki a inuwa grany
Zaunawa asma'u tayi kusa da grany sukaci gaba da feransu
Inna ladidi ce tafito tazauna asma'u tagadaita
Bayabo ba fallasa ta amsa mata gaisuwar
Sannan take gayama grany sunyi waya da aunty sadiya tace suna hanya yau zasu dawo
Bashir ne yashigo ya zauna daga kasa kusan asma'u yana fadin matar yaya kintashi lafiya
Lafiya kalau tafada tana murmushi
Sannan yajuya yana kashema grany ido yace kin iya zabe nima kisamo mun
Jifanshi tayi da pilo tana fadin kadai karata can akan yan matanka bazan kawo maka yar mutane kakasheta ba
Dariya yayi sukaci gaba da firansu banda inna ladidi datadaure fuska
Da yamma misalin karfe biyar su uncle jamilu suka iso
Bayan sun huta anyi sallan magriba grany ta aika kiransa
Yana zuwa ya gaidata yana washe baki yasan bai wuce zancan auren AK da aysha ba
Sedai ga mamakinsa yaji sabanin haka yafara banbanmi yana masifa grany ta taka mai birki tace yaje ya tuhumi yar'sa ita taki amincewa auren tunda fari dahaka bata faru ba
Ahasale ya banke kofar yafita bangarensa yanufa yana kwalama aysha kira
Tana dakin aunty sadiya tana karban tsarabarta
Atsorace tafara yarfa hannu tana fadin wayyo nashiga uku
Dakin ya iskota yana zuwa yadaka mata tsawa yana fadin wane kalan shirme naji abakin grany wai ke kika ki auren AK hakane
Atsorace tace abba yi hakuri amma ai daga baya nace nahakura amma ya.....
Bata karasa ba taji saukan mari
Dafe kuncinta tayi hade dafashewa da kuka
Saurin rikota aunty sadiya tayi tana fadin lafiya abban aysha yau Kaine da Marin aysha meyake faruwa ne
Fizgo aysha yayi ahnnunta danufin kara mata wani tayi saurin rike hannunshi tana bashi hakuri tace ya tsaya ya saurareta sakinta yayi yana fadin to gayamun meyafaru
Nan tagayamishi cewa grany ce tazaba AK wannan matar amma shi baya sonta ita yakeso kuma har yanzu suna tare yamata alkawarin zancan aurensu yana nan
wani dogon tsaki aunty sadiya taja tana fadin ni dama wallahi najima da sanin tsohuwarnan bason auren yaran nan take ba taga zamu samu abun arziki bari takawo yar uwarta saboda suji dadin cin dukiya to wallahi bata isaba
Girgiza kai uncle jamilu yayi yana cije lebe sannan ya dafa kan aysha yace sorry baby raina ne yabace kinsan yanda najima da borin ganin kin auri AK to kuma lokaci guda naji bai aurekiba ya auri wata can daban kinga ai bazanji dadiba amma dakika mun bayani naji dadi kuma namiki alkawarin idan dai ina raye se mun cimma burinmu
Murmushi tayi tarungumeshi tana fadin ba komai dady
Daganan yanemi ganin matar AK
Suna babban palo tafito tagaidasu aunty sadiya ce kawai tadaure fuska amma uncle jamilu
Da far'arsa suka gaisa har yana tsokanarta wai tayi kama da yan India
Hakan yabata mamaki matuka ba ita kadaiba har grany tayi mamakin yanda tasan jamilu da bakar zuciya taya yasakema asma'u
Koda dare yayi asma'u tahadama AK coffee dakanta takaimasa tas yashanye shi har yana mitar takamasa dan kadan wayasanima ko ita tashanyeshi
Bata kula saba tadauki pilonta da blanket tanufi Palo """
Urs......✍
👩💻Maryam Mhd
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( Maryam Muhammad jibril)
7⃣5⃣
Washegari tunda yadawo daga sallar asuba ya wuceta akuance apalo tana bacci hankali kuance ga darduman datayi sallah nan agefe
Har ya wuce daki se kuma yadawo kan daya daga kujerun palon yazauna sannan yadauki remote ya kunna TV
Tana jinshi tayi banza dashi taja blanket tarufe kanta
Kura volume din yayi karshe
Bubbuga kafa tafara yi kaman tafashe dakuka ta tashi tana fadin wai miye haka dan Allah
Daure fuska yayi yace yarinya tunda kika auri dan Babban gida to kinkare da baccin safe
Kuma nan palona ne inada damar yin abunda naga dama aciki
Tashi tayi tana mutsitstsike ido tanufi ciki tana gunaguni
Bayi tanufa tayi wanka tasaka doguwar rigarta ta less mai kyew sannan tayafa gyale tafito
Inda tabarshi anan ta iskoshi yana gyangyadi
Fita tayi batare da tasake kallonsa ba
Yana ganin tafita ya kashi TV yanufi daki yana hamma
Babban kitchen din gidan tanufa
Nan ta isko ma aikata nata aiki abinci kala kala an juyewa akula
Wurin wata dattijuwa tanufa tagaidata
Damamaki matar ke amsa gaisuwarta
Bayan sun gaisa tace baba meyasa ba ajera abincin a dining ne
Tabe baki tsohuwar tayi tace haka suke yan gidan nan sedai aje atambayi kowannensu meyakeso sannan akaimasa inda yabukata
Gyada kai asma'u tayi sannan tafita
Bangaren grany tanufa bayan tagaidata tace grany ni kwa meyasa ba ahaduwa wuri guda aci abinci ne tunda akwai Babban dining table din dazai dauki gaba daya yan gidan nan
Dariya grany tayi tace hakane fa asma'u kinka shawara me kyew kinsan balokaci guda ake tashi agidan nan ba shiyasa amma yau insha Allah zanyi musu magana za'arika haduwa ana cin abinci
Nan tazauna bangaren grany tashari baccinta se Tara ta farka kamar ance taduba dining kawai tahango mutum azaune yana breakfast
Kuada kai yayi kamar bai ganta ba
Fuska tayi itama tana gyara gyalenta da yafadi
Grany ce tafito tanufi da murmushi afuskarta tace albishirinku
Shiru AK yayi se asma'u ce tace goro fari grany
Wata takarda Tamika ma AK tace ga visan kunan yafito nashirya muku honeymoon zuwa kanada
Afirgice AK yace honeymoon kuma grany
Eh ....
Tafada tana daure fuska
Ko bazaka bane
Sadda kai yayi yana fadin gaskiya grany inada aiki agabana banada lokacin wani honeymoon
Daure fuska tayi tace. To shikenan tunda ban isa nasaka Abu kamun ba dama can ina zargin baka kyewtatama yarinyar nan dan kaganta shuru shuru to wallahi kaji tsoron Allah
Harara ya jefama asma'u yanaji kaman yashakota
Shikenan grany zan je amma gaskiya kanada yayi nisa kuana hudu kawai zamuyi yanzu dai zamu fara zuwa Lagos inyaso karshen watannan semuje honeymoon din
Baki tawashe tace ba komai ni dama sunake kusamu lokaci Ku kafahimci juna
Tana kainan tayi gaba abunta
Tashi yayi yafita yana kallon asma'u aransa yana fadin nasan ke kika cusa ma grany wannan ra'ayin inba haka ba ina tasan wani honeymoon
Yana bangarensa azaune aysha tashigo tana zunbura baki tace wai dagaske honeymoon zakuje
Tsakai yayi yace wane honeymoon niba inda zanje dawannan yarinyar ai se arainani
To yazakayi da grany
I have a plan yafada yana leken kofa
Khaddeja lafiya kince kina son ganina
Eh hakane Tarzan abunda muke zargi gaskiyane
Haba dama nafada maki ni nasan ba banza ba kawai zanje nasamu AK inji akan wane dalili zai cutar da baiwar Allah akan wani selfish reason dinsa
Dakatar dashi tayi dafadin
a'a idan kamishi magana zaije ya sauke akan yayata ne mafita dayace
Wacce kenan
Ka auri sarah !!!
Na aureta fa kikace khadeeja bayan kinsan bana sonta
Amma ai kai kace mun zaka iya yin komai dan farin cikina nikuma farin cikin yayata shine nawa idan har ka auri sarah nasan AK zai daina muzguna mata zasu zauna lafiya
Girgiza kai yayi cike da damuwa yace khadeeja nasan waye AK bazai taba son asma'u ba
Ni kuma nasan yayata abune mai sauki tasa yasota kuma ni nafada maka wannan
Idan har kana sona da gaske to ka auri sarah idan kuma bahaka kawai kamanta dani kar kakara nemana kafita daga rayuwata
Tana kai nan ta juya ta tafi tana share hawayen fuskarta
Dakallo yabita yakasa koda motsa yatsar sane
Tafiya take tana kukan bakin ciki har tabacema ganinsa
Grany ce ta tasa AK agaba akan seyaje da asma'u tayi ma su Umma ban kuana tunda gobe ne tafiyarsu
Ba yanda ya iya haka yasa driver yajasu suka tafi gidan inna suka fara zuwa sunsamu tarba mai kyew abba ma yadawo suka gaidashi cike da fadin ciki yake kallonsu yanama Allah godiya dayaba asma'u miji nagari
Sunjima agidan sannan suka nufi gidan Umma
Dagudu asma'u tashiga gidan tana kiran umma !!! Umma!!!
Fitowa Umma tayi da mamaki tarungumeta tana tambayar asma'u kece yanaganki haka kuma
Bayan AK yashigo sun gaisa yake gayamata zancan tafiyarsu tayi farinciki sosai tamusu addu'a
Fita yayi waje yana jiran asma'u tafito
Khadeejace tazo shiga gida kamar daga sama tagansa akofar gida
Tagefensa taraba tawuce amma batace komai ba
Se yaji duk baiji dadin ganinta haka ba kamar yamata magana se kuma ya kyaleta
Tana shiga asma'u tazo da gudu ta rungumeta
Cikin sassanyar murya khadeeja tace ammah ya kike
Lafiya kalau asma'u tafada tana mata alama fa kar Umma tagane
Tadan jima agidan kafin da kyar Umma ta fito da ita waje tace tabar mijinta na jiranta tundaga gida sukayi sallama da khadeeja tana mamkin ina AK zai kai asma'u
Umma ce tarakota har wurin mota sannan Tamika mashi wata leda tace gashi tashice zatamai anfani
Godiya yamata sannan sukabar kofan gidan
Seda suka biya wurin Momy itama suka gaidata amma basu sami ahmad agida
Momy tafuskanci akwai matsala atsakaninsa da ahmad kamar tayi magana sekuma tayi shiru
Tace intayi tsami maji
Sundan jima awurinta sannan suka fito sunzo fita sukaci karo da ahmad zai shiga gida kauda yayi kaman bai gansu ba ya wuce ciki
AK baiji dadin hakan ba amma yasan komai zai wuce
Ahanya yabude ledar yaciro abunda ke ciki
Wata sweater ce mai kyew irin tasakannan
Rigan tabirgeshi amma kawai dan Neman tsokana
Yadaga rigar sama yana fadin wai ni Umma zataba wannan rigar ai sedai ingoge window da ita
Nan take fuskan asma'u ya canza idonta ya cicciko da hawaye cikin muryan kuka tace Umma fa tasakata da hannunta she gave it to u with love amma zaka fadi haka takarashe maganar tana fashewa da kuka
Damamaki yace ohhh to ai ni bansani ba nadauka takice ai
Batace komai ba taci gaba dasharan kwalla
Leko fuskanta yayi yana fadin wai kuka kike
Kauda kanta tayi batace komai se sheshshekar kukanta dake tashi
Dafe kansa yayi yace dan Allah kiyi shiru natsani kuka arayuwata sannan yadago yakalleta yace idan ma jira kike nabaki hakori to gara ma kiyi shiru
Nan madai bata daina kukan ba
Yacema driver yayi playing music
Ai kamar yakara mata kukan ne
Bashiri yace yakashe
Cikin sassanyar muryan dabata taba zaton yanada ita ba taji yace ok I am sorry rigan tayi kyew kuma ina sonta kawai dai nafada ne
Damamaki tadago takallesa yayi saurin kauda kai kaman bashi yayi maganr ba
Shiru tayi tana share hawayenta
Daga nan bawanda yayi magana har suka karasa gida
Suna isa yaran inna ladidi salma da amir suka zo dagudu suka rungumeshi
Rungumesu yayi yana dariya yace yaushe kuka dawo
Atare sukace dazu mukazo grany tace kamana aunty ina take
Bayansa yanuna musu yana fadin gatanan zuwa
Aguje suka je suna mata oyoyo
Washegari tunda safe suka shirya sukama grany sallam suka fito kallon aysha yayi yakashe mata ido
dariya tayi tana rufe bakinta datafin hannunta dan kar agane
Driver ne kejansu basuyi tafiyar awa dayaba suka iso Barcelona hotel bayan yayi parking AK yafito yana mika sannan yaleka yacema asma'u to ai sekifito ko hajiya
Fitowa tayi tana zunbura baki
Bude but yayi yaciro akwati daya yayi gaba baice komai ba
Dayan akwatin tadauka
Tabi bayansa tana fadin inane nan kakawomu
Airport....
Yafada atakaice
Daure fuska tayi tace I am not a fool
Murmushi yayi yace nasan dai baki taba shiga jirgi ba wannan ne karo nafarko
Shiru tayi batace komai ba
Wurin reception yanufa yana fadin jirani anan bari nakarbo mana passing cards dinmu
Dakallo tabisa har yaje yakarbo makullin daki yadawo ya dauki akwati ya nufi wata hanya yana fadin muje karmu rasa flight
Tsaki tayi tace wai mekadaukeni ne ko angayamaka banyi makaranta bani
Wani daki yakaita bayan sun shiga yace
Yarinya anan zakiyi honeymoon dinki kuana hudun nan se sunzame maki tamkar shekara 4 anan wurin
Zama tayi bakin gado tace
Tunda dai karaboni dawancan gidan kabiyani dama zaka barni anan har natsawon rayuwata da ina so
Jan dayan akwatin yayi yafita yana fadin natafi wurin masoyiyata idan kina son wani Abu karki kirani
Tasowa tayi tarufe kofar tana fadin Allah raka taki gona
Bai kulata ba yayi gaba abunsa
Farm house dinsa yanufa yana isa kiran aysha nashigo wayarsa yana dagawa tace ya ake ciki
Dariya yayi yace yanzu na ijiyeta ahotel anjima zanzo
To meyasa bazakazo yanzuba
a'a kinmanta yaw Sunday inada program senagama zanzo
Kashe wayar tayi tana wani malalacin murmushi tace zanyi farin ciki idan Maman asma'u takalli program dinka nayau zatasan karya kuke ba inda kukaje
Yaronsa nagidan mai suna sani yakira yace ya Ciro mai akwatinshi abayan but
Yana fito da akwatin AK yace
Bude zakaga wata bakar jaket asama kabani
Dariya ce ta kwacema sani yayi saurin danneta yana fadin yallabai wannan ai kayan matane a akwatin
afirgice yace what !!!
Dafe kansa yayi dayatuna yabar akwatinsa ahotel yadauko na asma'u
Asma'u nafitowa wanka ta janyo akwati tabude
Ido tazaro ganin kayan AK a akwati
Gashi tariga tawanke nata yazatayi
Hakanan tadauki kayansa tasaka
Murmushi sani yayi yace hakan yana faruwa akan masoya yallabai
Keep quite dan Allah!!!
Shiru sani yayi yana danne dariyarsa
Makullin mota yakarba ahannun driver yashiga aguje yabar wurin
Yana isa yafara bubbuga mata kofa
Tana kunce tasa eyepiece akunne tana bacci
Yajima yana bugawa amma bata budeba gashi lokaci natafiya dole ya karbo spare key yabude dakin
Bakin gadon yakaraso yana mamakin ya akayi bataji karan buga kofar ba
eyepiece din yaciro yasa akunnensa
yagirgiza kai yayi yana fadin shiyasa kagi nan ahargitse
Kamar ance tabude idonta atsorace ta tashi zaune tana fadin wai meya dawo dakai kuma
Damamaki yake kallon rigar dake jikinta
Blanket din yafara janyewa yana fadin bala'i badai kayana kika sakaba
Rirrike blanket din tayi cikin muryan mai shirin fashewa dakuka tace wai me kakeyine haka bakai katafi dakayana to mekakeso insa
Wayanshine yafara ringing tsaki yayi yadaga yana fadin wallahi kicremun kayana kinji nagayamiki
To idan nacire mezansaka haka zan zauna
Dip nunfashin aysha yadauke sandarewa tayi awurin takasa cewa komai
AK yayita hello hello yaji shuru wurgi yayi dawayan kan gado yana kallon Asma'u yace dakinsan tsadan rigarnan tajikinki to ko biyanki akayi bazaki sakata ba
Yau inada program kuma ita zan saka dan haka cireta
Cikin rawar murya tace to kabani tajikinka se inbaka wanna
Cire rigarsa yafara yi tayi saurin kulle idonta tana fadin wai meyasa bakada kunya ne
Jefo mata Rigan yayi yana fadin yi sauri banda lokaci
Bayi tanufa tasanyo rigar tafito masa da waccan
Fizge rigan yayi ahannunta yasaka yana mata dariyan yanda takoma acikin kayanshi
Daure fuska tayi tana tattare wandon dayamata yawa
Akwatinsa ya ja yana fadin kice abunda kike so kisha abunda kike so ki kalli abunda kike so Abu daya ne bazaki samu ba saurayinki ahmad dan tun aranar nasan yagama dake
Kauda kai tayi tace eh naji dan Allah tafi
Rigan jikinta ta shinshina tana yamutse fuska
Fita yayi daga dakin yana fadin dakayannan zaki kare kuanakin ki anan
Seda yafita shima ya shinshina rigar jikinshi yana yamutsa fuska kamar yanda yaga tayi
Aysha takasa hakuri seda taje farm house din AK tana isa sani yacemata ai yakoma wurin matarsa nan take taji jiri na deebarta
Tafito kenan tahadu da AK zai shiga dan baisamu damar yin program dinsa ba lokaci yakure
Damamaki yace me kike anan
Kai zan tanbaya daga ina kake
Daga gidan abokina
Kusan shi tamatso tace daga gidan abokin naka ne kasamo turaren mata
Kauda kai yayi baice komai ba
Fashewa tayi da kuka tace AK meyasa zakamun haka kasan ina sonka amma inaga kaina kawai nakeba wahala gara ma kawai nahakura dakai
Saurin rikota yayi yana fadin come on aysha stop this drama please
Me kike tunani wai ina kula waccan yarinyar kome
Kema kinsan she is not my type mezanyi da ita
Kima daina tada hankalinki akan wannan
Da kyar ya lallasheta tayi shiru sannan yajata suka fita shakatawa
Da kyar Umma tashayo kan khadeeja takira mata Asma'u
Bayan sun gaisa Umma ke tambayanta sun isa
Eh ta amsa atakaice
To ina maigidan nanki
Yana bayi ...
Karban wayan khadeeja tayi cikin sassanyar murya tace ammah ya kike
Lafiya kalau khady ...
I hate it when u lied to me
Cike da mamaki Umma tace meke faruwa ne meyasa kika ce haka
Saurin hannunta khadeeja tayi dan Sam tamanta agaban Umma take
Cikin dakewa tayi murmushi tace kai Umma kincika tsoro kawai dai nasan bata zuwaba kuma tayi nesa damu dole zataji badadi
Katse kiran asma'u hade da sulalewa akasa tafashe dawani irin kuka maiban tawsayi """"
Urs....
*MHD*
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( Maryam Muhammad jibril)
8⃣0⃣
Khadeeja ce tazo wucewa ta layin gidansu ahmad ta gansa yafito daga masallaci
Karasawa wurinsa tayi tana boye hawayenta
Yana ganinta ya kauda kai yana fadin
why are u flowing me since u have no feelings for me
Sadda kanta tayi kasa tace nazo ne naji wace shawara kayanke akan maganar da mukayi jiya
Khadeeja kigane ni bazan iya abunda kike so ba
Bazan iya auren sarah ba bana sonta
Zaka sota daga baya just try it
Bazai yuwo ba khadeeja mutum baya iya sakama kansa son wani
Kenan haduwata dake da fadan da mukayi duk ke kika shirya
a'a bani nashirya kawai yafaru ne
To kigane so faruwa yake dan na auri sarah bashi zaisa AK yaso asma'u ba
Nace miki kibarni ni zan daw mataki akai
Bawani matakin dazaka dauka abunda AK yayi
Yayishine domin kanwarsa
Nima kuma zan hakura dakai ne saboda yayata kai kuma kahakura dani dan farin cikina idan har kana sona ...
Tana kainan tajuya ta tafi tana sharan kwalla
Dunkule hannu yayi yanawshi iska yana cije lebe
Motansa yashiga yafigeta aguje kamar mai shirin barin gari
zaune suke cikin katuwar runfar gidan suna hutawa bayan sundawo daga shakatawa
AK nifa ina jin tsoro dan Allah kar wannan yarinyar ta rudaka
Wai aysha so nawa zan gayamaki ba abunda zai faru baki yarda dani bane kome
Mezanyi dawannan chitti din kawai jira nake ahmad ya auri sarah nayi waje da'ita
Miye kuma chitti ??
Yaren India ne yana nufin karamin abu
Dariya tayi tace nakosa naga ranar da asirinta zai tonu mu koreta daga gidan
Shiru yayi kamar mai nazari yanaji bai kyewta ba dayama grany karyan yayi tafiya kuma baikamata yakai yar mutane hotel ya ijiyeta ba har tsawon kwana hudu
Dafashi aysha tayi tace kana tunanin matarka ne
Kauda kai yayi yana furzar da iska bai ce komai ba
Asma'u nazaune adaki ita kadai
Bayan AK ya aikomata da kayanta tasa
Jitayi zaman ya gundureta tafito waje tasha iska
Restaurant din wurin tanufa
Daidai yahaya yazo wucewa ya hangota
Cike da mamaki yake kallonta shidai yasan ance sunyi tafiya da AK to meyakawota nan kuma
Wayarsa yadauka ya kira grany yana daga gefe
Bayan sun gaisa yake tambayarta yallabai nagari
a'a bayanan sunyi tafiya da amaryansa kuma kar wanda yadamesa da kira
Lafiya kake tambaya ..
a'a ba komai grany dama wata nagani kamar asma'u shiyasa nake tambayar ko sunfasa tafiyar ne
Cike da mamaki tace a ina kaga asma'u
Bai bata amsa ba yakatse kiran yana lalubo numban asma'u yana daga nesa yana kallonta amma ita Sam bata gansa ba
Tana zaune taji wayanta na ringing mamaki tayi ganin numban yahya
Afili ta furta yahya kuma to lafiya
Tajima kafin tadaga wayar tare da sallama
Bayan ya amsa sallamarta yace dama nakira ne naji kun isa lafiya
Lafiya kalau Yaya...
Kinga Lagos ko? Nasan baki taba zuwa ba ...
Eh Yaya yanzu haka ma muna wurin hutawa gwanin sha'awa Ashe Lagos tanada kyew haka
ya wajansu Umma
Lafiya ....
Yafada yana katse Kiran da mamakin meyasa sukayi karyan sunyi tafiya
Me asma'u take ahotal ita kadai ina AK yake
Dole akwai wani Abu
Wani mutum ne yazo yazauna kusa da asma'u dawata jaka ahannunsa yana leken police din dasuka shigo restaurant din
Tunda tagansa taji bai kuanta mata ba daure fuska tayi tace malam yi hakuri katashi ni matar aure ce
Murmushi yayi yamike yana fadin yi hakuri ban saniba
Karasowa police din sukayi cikin restaurant din suna bincika ko ina
Da manager ya tambayesu suka ce sunsamu labarin anshigo da drugs restaurant din dan haka dole su binciki kowa anan
Suna cikin bincike suka iso wurin asma'u
Daukan jakan yayi yana fadin madam is this urs
Atsorace tazaro ido tace no batawa bace
Bude jakan sukayi sega drugs makil acikin jakar
Murmushi yayi yace kinbani mamaki gaki kamar mutuniyar arziki Ashe ke annoba ce kina matsayin mace da darajarki amma kinwatsar da ita kina cutar ya'yan jama'a
Kuka tafara tana fadin wallahi batawa bace nima seyanzu naganta anan dan Allah kasaurareni
Kiran ogansa yayi ya nuna mashi nan take yabada umarnin ayi arresting dinta
Karasowa yahaya yayi yana rokon sukyaleta yasanta wannan ba sana'arta bace yarinyar yar gidan mutunci ce
Sunkuy dakanta tayi data tuna karyan datama yahya kenan dama yaganta awurin shiyasa yakirata
Ba rokon da bai musu ba amma sunce sedai yabiyosu office yabada shaida
Tana kuka haka suka tasa keyarta har cikin motarsu
Lekowa tayi tana kallon yahya cikin muryan kuka tace yaya dan Allah kar ka gayama su Umma abunda yafaru dan Allah!!!
AK na zaune da aysha suna fira amma baisan meyasa ba Sam baya jin dadi hankalinsa yakasa kuanciya
Kamar daga sama yahango grany tana zuwa
Azabure suka mike gaba daya suna kallonta har takaraso fuskarta adaure kamar bata taba dariya ba
Cikin kakkawsar murya tace mekake anan
Shiru yayi baice komai ba
Badakai nake ba uban me kake anan tare da wannan mara kunyar
Ina ka kai yar mutane kai yanzu baka jin kunya abid yaushe kazama haka ban saniba
Hannu tadaga da nufin wanka meshi mari daidai nan sarah takaraso aguje tana fadin a'a grany
Dakatawa tayi tana jifanta da wani irin kallo
Sunkuy dakai sarah tayi tace yanzu Yaya yakirani yana cikin matsala ne
Yayi signing contract ne dawani company kuma yau ne zasu gabatar da meeting idan har baijeba zasuyi tunanin ya yaudaresu ne kuma hakan zai jamai matsala shiyasa baisamu damar tafiya ba
Kallon AK grany tayi cikin kakkawsar murya tace ina asma'u
Sunkuy da kai yayi cikin rawar murya yace tana hotel dazu nabaro wurinta itace ma tabani kwarin guywar yin hakan tace zata miki bayani dakanta tasan zaki fahimta
Juyawa tayi tana fadin muje ka kaini wurinta dan ban yarda dakai ba
bin bayanta yayi suka fita
Ajiyar zuciya aysha tasauke tazauna kan kujera tana fadin natsani yarinyar nan
Tsaki sarah tayi tana hararanta tace ke bazaki iya hakura da AK na minti biyar bane se kin ruguza mana shiri
Kauda kai aysha tayi tana fadin gwara ni ai...
Suna isa dakin da asma'u take sukaga bata cike da mamaki yatambayi dai daga cikin ma'aikatan wurin shine yake bashi labarin abunda yafaru
Al'amarin ya girgiza shi matuka
Asma'u ce a police station tasasu agaba se kuka take masu tana fadin wallahi batasan komai akan wannan jakar ba
Waya dan sandan yabata yace takira yan uwanta suzo
Karban wayan tayi tana tunanin wazata kira itadai bazata iya kiran Umma ko abba ba
Numban AK takira tana ringing baidagawa
cikin muryan kuka tace ina kira baidagawa
Dariya yayi yace saurayinki ...
Kauda kai tayi tace mijina dai
Yasunan mijinki ...
Konafada bazaka yarda ba
Saboda me koshima dan safaran kayan mayen ne
Girgiza kai tayi alaman a'a
Koshine wanda muka gani a restaurant ...
Nan madai girgiza kai tayi
Ahasale yace to waye
a tsorace tace
AK hausawee
Gaba daya yan sandan suka kwashe da dariya
Seda sukayi mai isarsu sannan dayan officer din yace yallabai kila kowani AK din take nufi
Fashewa tayi da kuka tace shidai wanda kuka sani wallahi shine mijina idan baku yaradaba kuduba social media anyi posting pics dinmu
Dariya sukayi sannan Babban su ya umarci asata a cell idan wani nata bai zoba zai watsata a news kowa yagani
Kuka tafara tana rokonsu amma basu saurareta ba
Umma da khadeeja suna zaune tana tambayarta meke damunta kuana biyu ta sawya
Fa'iz dake gefe azaune yace Umma kila tana kewar asma'u ne
Shiru Umma tayi nadan lokaci sannan tace ni yau inaji ajikina kamar wani nawa yanacikin matsala
Saurin kallonta khadeeja tayi tana fadin Umma duk muna nan waye kuma amatsala
Fa'iz yace to ko asma'u ce
Hararansa khadeeja tayi tace ammah tana tare damijinta ba abunda yasameta
Umma kidaina damun kanki kawai shedan ne kesamaki waswasi
Tana rufe baki suka jiyo sallamar yahya daga waje
Saurin tashi khadeeja tayi tanufi get tana fadin mekuma yakawoshi nan gidan
Lekowa tayi bakin kofa suka gaisa
Sannan yace Umma naciki
Lafiya ....
akan asma'u ne
Saurin fitowa tayi waje tana fadin meyafaru
Dazu naje hotel nahadu da ita to kuma ina nan tsaye sega yan sanda sunzo suntafi da ita
Cike da damuwa tace yan sanda fa kace akan wane dalili suka kamata
Zaiyi magana kenan sukaji Umma nafadin wa aka kama
Murmushin dole khadeeja tayi tace ba kowa
Yahya yamatso kusan Umma yana fadin karya take Umma asma'u yan sanda suka kama
Innalillahi wa inna ilaihiraji'un
Asma'u fa kace yahya a ina
Riko hannunta khadeeja tayi cikin rawar murya tace Umma ki kuantar da hankalinki ba abunda zai sameta bari naje police station din yanzu naji meyafaru
a'a khadeeja shiga ciki kizauna bari ni naje naga ko dagaskene dan ni har yanzu ban yarda asma'u bace
suda sukayi tafiya da mijinta me kuma yahadata da yan sanda
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Da kyar AK ya lallashi grany takoma gida shikuma ya wuce police station
Asma'u na cikin cell tana kuka fatan ta daya kar Umma tafahimci gaskiyar halin datake ciki
wani dan sanda ne yazo ya fito da ita
Tana zuwa ta isko Umma atsaye da gudu tazo ta rungumeta tana kuka
Rikota Umma tayi tana tambayr ta meyafaru taya tazo nan ina mijinta
Kuka kawai take takasa magana
Jijjigata Umma tayi dakarfi tana fadin asma'u kigayamun meyake faruwa ne
zatayi magana kenan taga AK yashigo office din fuska ahade
Yan sandan sunyi matukar mamakin ganinsa
Cikin kakkawsar murya yace akan wane dalili zaku kamata
DPO ne yace sorry AK banyarda ba lokacinda tace Kaine mijinta
Saboda me ?
bazan iya auren ordinary girl bane
I doesn't judge people by their looks but their character
Juyowa yayi yana kallon asma'u yace meyasa baki gayamusu ke matata bace
Matsowa tayi kusansa tace Nagayamusu amma basuyarda dani ba
Kamar daga sama yaji ta rungumesa tana fadin I am glad u are here
Cikin rada yace ke miye haka
Dagowa tayi takallesa tana mai alama da ido cewa Umma tana kallo
Saurin rungumeta yayi cikin kunne yarada mata
Kindamu da ummanku ni kuma nadamu da grany
Sannan ya dagota yana fadin is ok
I am here
U are safe now
Murmushi tayi tace I am sorry for troubling u
Hannunta yariko yace nagode allah Dana sameki anan
Namiki alkwarin bazan kara barinki ke kadai ba kema kuma kar kikara yin nesa dani kinsan yanda nake sonki idan wani abu yasameki yazanyi
I can't bear it
Rungume juna suka karayi bakinta takai setin kunnensa cikin rada tace
u are over reacting kafitar dani daganan wajan mana
Murmushi Umma tayi tana kallonsu cike da birgewa
Sabanin yahya da abun ya dawre mai kai
Janye jikinsa yayi daga nata yana kallon dan sandan yace akan wane dalili kuka kamata
Jakar yanuna masa yana fadin munsamu wannan jakar akusa da ita kuma drugs ne aciki
Daukan jakan yayi yace yanzu daka ganta ahannuna seka kamani kace ina safarar drugs
Wace hujja kake da ita datanuna jakan tatace
Kasan zan iya yin karar ka akan bata mata suna dakayi
Hakuri suka fara bashi akan basusan matarsa bace shiyasa
Hannunta yaja suka fito daga police station din
Su Umma nabiye dasu
Wurin Umma yazo
Yace Umma meyasa kika zo nan kinsan yanda asma'u tadamu da lafiyarki yanzu gashi kindaga mata hankali ni kuma natsani gabinta cikin damuwa
Naji ance asma'u tana nan ne shiyasa nazo
Hannunta yariko yana murmushi yace Umma ki kuantar da hankalinki asma'u matata ce hakki ne akaina na kula da ita wannan ma dayafaru kaddara ce amma namiki alkawarin zan kiyaye
Murmushi tayi tace ba komai abid nidama nasan bada saninka haka yafaru ba allah yatsare gaba
Ameen yafada yana kallon yahaya yace kamaida Umma gida tana bukatar Hutu
Sallama suka musu yahya yaja motar suka tafi
Cikin siriruwar murya tace I am sorry
Juyowa yayi yakalleta takara cewa
Sorry
Baice komai ba yanufi motarsa
Binbayansa tayi suka shiga tare
Khadeeja nagida hankalinta atashe jin shiru Umma batadawo ba
Fitowa tayi da nufin binsu taga ahmad akofar gida
Daure fuska tayi ta kauda kai kaman bata gansa ba
Karasowa wurinta yayi yana fadin yawwa dama ke nake jira
Ya akayi kasan zan fito
Kawai dai naji ajikina ne
To me yakawoka wurina
Cikin sassanyar murya yace gaskiyanki ne nagane nine mai laifi kuma ina so na gyara kuskuren da nayi
na amince zan auri sarah !!!
She was shocked
Ni dai nasan mace daya nakeso arayuwata kuma bana tunanin zanso wata bayan ke
Juyawa tayi takoma ciki tana danne kukanta
Tana shiga tasaki wani irin kuka mai ban tausayi
Tundaga waje yana jiyota runtse ido yayi yana jin zafin kukanta har kasan zuciyarsa yajima atsaye kafin ya juya jiki asanyaye yabar layin
Seda Umma tadawo tabata labarin abunda yafaru a station tana fadamata tayi farin cikin ganin yanda AK ke kula da asma'u
Shiru khadeeja tayi tana tunanin meyasa AK yake yaudaran kowa kawai saboda kanwarsa
Suna isa gida bangaren grany suka nufa
Tana zaune itada sarah suna jiran dawowarsu
Tana ganinsu tamike tana Cike da farin ciki tanufo asma'u tana fadin
Ba abinda yasameki dai ko meyasa baki kirani ba kinsa nashiga damuwa
Riko hannunta AK yayi yace shikenan grany ba gashi na maidomaki ita ba
Fizge hannunta tayi tana fadin dallah yimin shiru duk bakai kaja ba meyasa baka barta agidaba zaka kaita hotel
Riko hannunta asma'u tayi tace
Grany yi hakuri kidaina mishi fada laifi nane ni nace yatafi wurin aikinsa
Kima daina goyon bayansa dan ba yarda zanyi ba yana kokari wurin aikinsa amma yakasa wurin kula da matarsa
Nadauka idan yayi aure zai canza ashe nayi kuskure
Shidai AK yana tsaye kansa akasa yakasa cewa komai
Ba dole ne yadamu dani ba amma yazama dole yadamu dake amatsyinki na matarsa
Juyowa tayi tana kallon AK tace
To bari kaji nagayamaka idan har kasake maimaita irin wannan kuskuren zan dauki asma'u mubar maka gidan
Kudi dai suna iya karewa daga karshe duk watsewa zasuyi subarka kai kadai matarka ce kawai zata zauna dakai
Sekayi shawara...
Tana kai nan tanufi hanyar dakinta rai bace
Dagowa yayi yana kallon sarah da rinannun idanuwansa cikin wata iriyar murya yace
Yaune karo nafarko da grany ta taba mun magana haka
Juyowa yayi yana kallon asma'u yace
are u happy now
Kinsamu abunda kike so
Dafari kin rabani da ahmad yanzu kuma kindawo kan family na gashi ta dalilinki grany tamun abunda bata taba mun ba wallahi jinake kamar....
Hannunsa yadaga da nufin marinta sarah tayi saurin rikoshi tana fadin calm dwon bro
Kibarni kawai nakasheta all my problems will be over
Dafashi tayi tace easy yaya abun bai kai haka ba
tunda na auri yarinyar nan nayi ban kuana da kuanciyar hankali
Kallon Asma'u yayi yace uban wa yace kifita daga dakin mekika jeyi a restaurant
Nataimake ki a station saboda farin cikin ummar ki amma ke kin ruguza mun nawa
banza ...shashasha...
Rikoshi sarah tayi tana fadin yaya kabarta kawai
Zama yayi yana fadin bazan barta ba ita dai zata barmun gidana...
Fita asma'u tayi daga palon tana danne kukanta ...
dafashi sarah tayi tana fadin relax Yaya wannan yarinyar tana anfani da grany ne wajan samun abunda takeso
Kafin mu iya mata wani abu dole se grany tasan gaskiyar wacece ita
Girgiza kai yayi yace I don't think that is possible
Murmushi tayi tace kabar komai ahannuna nidai kawai kasa ahmad ya aureni
Tashi yayi yafita yana fadin zan dawo maki da ahmad rayuwarki nikuma kifitar mun da wannan daga tawa rayuwar....
washegari dasafe...
Cikin bacci takejin music natashi bude idonta tayi taga AK agefe yana motsa jiki (exercise)
Yi yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da abunda yake
Cikin muryan bacci tace wanna wane kalan abune ...
exercise...
Yafada atakaice
To kacanza kidan ko ka kashe music mana
Haka nasaba yin abuna kuma da rock music
tashi tayi tadauki blanket din ta zata wuce ta bige da exercise Weight dinsa yar kara tayi hade da dafe kafa
Dariyar keta yayi yana fadin Inada medical glass idan kinaso zan taimaka miki
Banza tayi dashi ta wuce daki tana dingishi
Knocking akayi awaje yaje yabude
Rebeka yagani atsaye
Bayan sun gaisa tace yallabai yau tun safe grany bata fito kuma bata bude daki ba ....
Bai jira ta karasaba ya fita aguje ya sauka kasa yanufi bangaren grany
Asma'u da fitowarta kenan tayi saurin bin bayansa
Yana zuwa ya isko gaba daya yan gidan akofar grany suna bubbugawa
Saurin karasawa yayi yafara buga kofar yana kiran grany
Nan take hankalinsa yatashi guba kofar yake kamar zai ballata yana kwala mata kira
Ture asma'u dake gefensa yayi yana fadin bari nazagayo ta window naga
Karsawa tayi jikin kofar cikin siriruwar murya tace grany!!!
AK har yakai bakin kofa ya tsaya cak jin anbude kofa
Saurin karasowa yayi wurin grany cikin rawar murya yace
Grany duk ihun da nake kina jina kika yi banza dani...
Katsesa tayi dafadin ni banji ba asma'u kawai naji takirani
Kuma daga yau muryanta kawai zanji tunda kuma ba kwajin maganta duk mai son wani abu yagayamata tagayamun
Grany meyasa kike mun haka bayan kinsan bazan iya yin komai batare dake ba ke kika San komai nawa menake ci menake sha ....
Kanada kudi ai zaka iya dawko wa'yanda zasu kula dakai konawa kake so
Juyawa yayi yakoma bangrensa rai bace
Yanaso yacigaba da exercise dinsa amma yakasa hannayensa biyu yasa yadafe kansa
Daidai nan asma'u tazo wucewa ya fizgota dakarfi
Hannayensa biyu yasa yariko dantsenta dakarfin gaske
Atsorace tadago tana kallonsa yanda idonsa yayi ja kamar bashiba
Cikin kakkawsar murya yace
Wai me kike shirin yine
Ina tsananin kaunar grany ta shiyasa nake kiyaye macin ranta tun ina karami bata taba gayamun maganar danaji zafinta ba se yau
Tunda kika shigo rayuwata kika lalata mun ita
Idan kika sake kika shiga tsakani na da grany sena....
Katseshi tayi dafadin
Ba abunda zakamun da yawuce wannan zama na anan kadai ya isheni
NI ba abunda nafadama grany
Burina shine na hadaku wuri guda
Nafahimci yanda kake son grany kuma nasan akwai zafi idan Wanda kake tsananin so yayi fushi dakai
banji dadin yanda grany tamaka fada akaina ba
Alhali ni ba kowa bace face bakuwa acikin familynku
Zanje namata magana nabata hakuri kuma na kuatanta mata nasan zata fahimta
Tunda tafara magana yake kallon kwayan idonta ko kiftawa baiyi
Riko hannunshi tayi cikin rawar murya tace u are hurting me
Saurin sakinta yayi yaja dabaya yana fadin sorry ....
Fita tayi daga palon tana share kwallan datazubo mata karo sukaci da sarah zata shigo
Karasowa tayi wurin AK tana fadin yaya meyafaru
Abunda asma'u tagayamasa ya maimaita mata yakare zancan dafadin
Kuma danakalli kwayan idonta zalla gaskiya nahango acikinsu inajin tsoro kar ace ....
Shiru yayi bai karasaba yana nazarin maganganunta
Dariya sarah tayi tace Yaya kabani dariya sekace ba wayayye ba
Bakasan halin yan mata mayaudara ba kenan
Idan kuna magana zasuyi kokarin hada ido dakai to daganan zaka yarda da duk abunda yafito daga bakinsu
Natabbata dawannan take anfani wurin ahmad da grany shiyasa tasiye zuciyarsu
Gyada kai yayi yace shiyasa danake kallon idonta ba abunda nakeji se sautin muryanta
Kice nadaina kallon hada ido da ita kenan
Fita tayi tana fadin idan baka hada da ita ba ita zata hada da kai kawai kasan yanda zakayi kafitar da ita daga gidan ne gaba daya ...
Yana zaune adaki ta shigo rike da mug ahannunta yana ganinta yakauda kai
Mikamishi mug din tayi tace ga coffee dinka
Kin karba yayi yace bayaso
Ta juya zata fita
Yace ta ijiye akan dressing mirror
Girgiza kai tadora akai
Tasowa yayi ya nufota yana kauda kai
Yana so yadauko mug din yadako kwalban turare
Da mamki tace wai mekake hakane kwaban turare fa kadauka
Ijiye kualban yayi yadauki mug din yana fadin nasani dama gwadaki nake naga ko kina bukatar glasses
Kauda kai tayi tace kafini bukatar su
To zaki iya tafiya
Karasawa tayi cikin dakin tana fadin inada abun yi
Juyawa yayi yafita yakoma Palo
Dakallo tabishi tana fadin mutum sekace aljani ...
0 comments:
Post a Comment