Daddare AK na kuance akan gado yakurama TV dake jikin bangon dakin ido yana kallon wani horror film mai ban tsoro
Kwance yake duk ya takure wuri guda gashi yakashe fitila se hasken TV kawai yadan haska dakin
Yanajin anturo kofa yayi saurin kallon wurin adan tsorace ganin asma'u ne yasa ya hade fuska yacigaba da kallonshi
Bata kulashiba tawuce bathroom
Bayan wani dan lokaci tafito sanye dakayan baccinta dogon wando da riga mai dogon hannu kalan pink
AK da yadukufa yana kallo yaji tasaki wata kara atsorace ya diro daga kan gadon yana tayata ihun
Ganinta dayayi atsaye tana kallonsa yasa yawaske hade da daure fuska
Cikin rawar murya tace dan ...dan Allah kacire wannan film din tsoro nakeji
Tsaki yayi Yakoma kan gado yakuanta yana fadin ai ba danke nasaka ba bare kice nacire
Yanda kike din nan ai bai kamata kiji tsoron aljanu ba
Dan allah kacire ba kyewfa kallon irin wannan da daddare
Dogowa yayi yakalleta sannan yamaida kallonsa kan TV can kasan makoshi Yace
Saboda me
Suna fitoma mutum dagaske ko kayita mugun mafarki
Banza yayi da ita yaci gaba da kallonsa
Towel tasa tana goge gashin kanta tanufi saitin gado zata dauki pilo da blanket dinta
Sam baysan tabar wurin ba sedai yaji kamar Abu kusa dashi afirgice yamatsa daga kan gadon yana kunna bedside lamp
Dariya tayi tace sekace dole kanajin tsoro ka kashe mana
Blanket dinta ta dauka tayi hanyar fita tana fadin nidai in sunzo maka ziyara kar ka kirani
a'a tsaya mana ina kuma zakije
Juyowa tayi da mamaki tace kamar ya ina zanje ko kamanta inda nake kuana ne
Daure fuska yayi yace ba inda zakije yau nan zaki kuana
akan wane dalili
Malama ba yanda zakijamun matsala awurin grany haka kawai tazo taganki kina kuana a Palo takara yin fushi dani dama da kyar ta hakura
Buga kafa tayi da kasa kaman tafashe da kuka tace Allah ni bazan kuana anan ba Palo zan kuana haka kawai
hahaha yarinya sama zuciyarki ruwan sanyi ba abunda zanyi dake
I have better things to do
Dawowa tayi tana zunbura baki tace wai kodai tsoro kakeji ne dan nace aljanu zasu zo maka ziyara
Harara ya watsamata yana nuna mata gefen gadon daga kasa yace kishinfida blanket dinki anan coz I can't share my bed with u
a'a ni gaskiya bazan shinfida anan ba
Dayan gefen takoma tashinfida blanket dinta tana fadin
haka kawai kazo shiga bayi kabi takaina
Komawa yayi yakuanta yana murmushi
Washegari dasafe ahmad yana zaune apalo yadafe kai yana tunani ya kira wayan khadeeja yafi akirga amma taki tadaga jin anturo kofa yasa Yayi saurin dago kai tunaninsa Momy ce zunbur yamike ganin AK atsaye bakin kofa yaharde hannaye akirji yana kallonsa
Karasowa yayi cikin dakin yana fadin why are u surprised to see me
Zaunawa ahmad yayi yana sauke ajiyar zuciya yace kawai dai naga kajima bakazo bane
Kusa dashi AK yazauna cikin sassanyar murya yace har yanzu fushi kake dani ne
Saboda na auri budurwarka ko saboda ranan na tureka dakarfi har kafadi ?
Shiru ahmad yayi baice komai ba
Kamo hannunsa AK yayi yakai kirjinsa yana fadin nasan saboda na tureka ne to Karama seka huce haushinka akaina amma dan Allah nagaji dazama ni kadai ahmad meyasa zaka barni alokacinda nafi bukatarka
Kauda kai ahmad yayi yana boye hawayen fuskarsa
Jiyo da fuskarsa AK yayi cikin karyayyan murya yace come on friend please stop this drama
Tunda muka taso bamu taba irin wannan ba kwana biyu dabana tare dakai I can't handle things
I am sorry ....
Yafada cikin rawan murya
Rungumeshi ahmad yayi Yana kuka shima AK kukan yake yana kara ba ahmad hakuri
Cikin rawar murya ahmad yace
AK I am ready to marry sarah where and whenever u want
Nagane kuskurena Ina wahalar dakaina akan yarinyarda bata Masan inayi ba nadauka tanasona Ashe kudina kawai takeso dataga Wanda yafini kudi da komai shine ta..
Bai karasa ba AK ya rungumesa cike dafarin ciki yace dama nagayamaka ahmad Nagode Allah dayasa kagane gaskiya adaidai lokacinda yadace
Hannunsa yaja yana fadin zo muje kagayama sarah
inaso naga ya chitti zatayi idan taganka tare da sarah
Riko hannunsa ahmad yayi yana murmushin dole yace to ai kabari nayi wanka nashirya ko haka zanje wurin budurwa
Dariya AK yayi yace to jeka zanje wurin Momy kafin kagama
Dakallo ahmad yabisa har yafita sannan ya rintse ido hade da dafe kai yana tunanin anya yayi ma Kansa adalci Kuwa bayajin zai iya rayuwa batare da khadeeja ba
Cike da farin ciki AK yashigo gida yana kwalama sarah kira
Kap mutanan gidan nafalo azaune da mamaki suke kallonsa suna tambayar Meyafaru
Wurin sarah yanufa yana fadin sarah I have a surprise for u
Murmushi tayi tace miye
Nuna mata ahmad Dake tsaye bayansa yayi yana fadin nacika maki alkawarinki ga ahmad yadawo gareki yayarda zai aureki kuma nanda kuana biyu ka.....
Batajira yakarasa ba tanufi wurin ahmad tana tambayar da gaske yayarda zai aureta
Hakuri yaba grany dasauran mutanen gidan akan abunda yafaru kwanaki
Nan kowa yafara saka albarkacin bakinsa akan yarinyar data yaudari ahmad
grany tace wai Wace yarinya ce wannan
Duddubawa AK yayi baiga asma'u awurin ba sama yanufa yana kiran chitti
daidai falo sukaci karo Zai shiga ita kuma Zata fito
dafe kai yayi yana kallonta yace nagayamiki kina bukatar glasses amma baki yardaba something is wrong with u eyes
Sosa goshinta tayi tace alamu sun nuna kaine ke bukatar glasses saboda .....
Katseta yayi dafadin chitti muje kasa akwai abunda zan nuna maki
Kallon bayanta tayi dagefenta sannan takalleshi damamaki tace are u okay
Daure fuska yayi yace what??
tafa hannu tayi tana dariya tace naga alama matsalan ba a idonka takeba a kwakwalwa ne
Tunda kafara gane gane
Hannunta Yakama yajata zuwa kasa yana fadin
kece dai yau zakiyi mugun gani ur ex-boyfriend is getting married to my sister
Kusan ahmad yakaita yana murmushi yace gashi kafadamata taji da kunnenta zaka auri sarah
Grany tace meyasa zaice haka
Dariya yayi yace haba grany asma'u fa matata ce kuma Yaya awurin sarah so yakamata ahmad yasanar da ita zancan aurensu
Murmushi grany tayi tace taji dadi dayafara girmama asma'u amatsayin matarsa
Cikin sassanyar murya ahmad yace ma AK idan bazai damu ba yanaso yayi magana da asma'u in private
Take ur time...
Ak yafada yanama sarah alamar kar tace komai
Gefe suka koma tafara tambayarshi meyasa zai auri sarah bayan baya sonta ya khadeeja zatayi idan taji zancan zai yi aure
Hakuri yabata akan rashin cika mata alkawarin dayadauka zai auri khadeeja kuma yakula da ita
Amma zai auri sarah ne saboda khadeeja ....
Nan yabata labarin yanda sukayi da khadeeja
Kai ta girgiza cike da tausayin kanwarta tace ahmad nayi kuskure a aurena banaso kayi nadama irin yanda nayi kai namiji ne taya zaka zauna da macen da bakaso ina anfanin auren idan har bazakuyi farin cikiba
To asma'u yazanyi khadeeja tadaina kulani tace sena auri sarah ko zan shekara ina kwatantama AK matsalar dake cikin aurennan bayarda zaiyi ba
I am doing it for my deeja and nothing can stop me
Yana kainan yajuya Yakoma wurin AK
Kusa da asma'u AK ya matso cikin rada yace
chitti this time ur magic doesn't work on ahmad
I feel sorry for u
Wane kalan magic kuma anya kwa yau baka sha wani Abu ba
bansha ba amma zansha anjima coz I will celebrate abokina yadawo kuma kanwata zata auri Wanda takeso
Nakusa rabuwa da kaya
Barin wurin tayi batace komai ba tanufi sama tana share hawayenta tasan ahmad yana auren sarah AK zai saketa yazatayi da ummanta
Ba adau lokaciba se gata ta sakko da gudu gudu tasha handbag dinta tun tada datana gida
Har takusa kofa grany tace a'a asma'u ina kuma zakije haka kamar ankoroki
Fita tayi tana fadin grany gida zanje ana nemana yanzu zan dawo
Kusan AK da aysha sarah tamatso tana fadin ina kuke ganin asma'u zataje
Dariya yayi yace kan cinyar ummanta zataje tarera kukan bakin ciki
dariya suka sa aysha tace zataje takona photunan ahmad dake wurinta ne
Asma'u tana fita ta tari addedeta se gida
Khadeeja ta isko tana wanke wanke Umma kuma na daki
Khadeeja na ganinta tazo dagudu ta rungumeta tana murnan ganinta
Shafa gefen fuskanta asma'u tayi cikin rawar murya tace deeja kinsan ahmad zai auri sarah
Kauda kai khadeeja tayi tana maida hawayen idonta tace eh nasani
To meyasa zakisashi ya auri sarah bayan kina sonsa
Ni bana sonsa ammah kawai kimanta dazancan karma Umma taji
Jin muryan Umma sukayi abayansu tana fadin meye ba'aso naji
Bayanta khadeeja takoma tatsaya tana kallon asma'u tace
Umma wai kewarki take shine tazo tadubaki amma bataso kisan tazo
Kusan asma'u Umma tamatso takama hannunta tana fadin asma'u lafiya naganki haka meyake damunki
Anya kwa kina samun kuanciyar hankali agidan mijinki kuwa
Murmushi asma'u tayi takai Umma Palo tazauna sannan tazauna kusa da ita tace
Haba Umma meyasa kike damun kanki ne akan abunda ba gaskiya ba ina zaune lafiya agidan mijina yan uwansa suna sona suna kula dani to me kikeso
Gaskiya zanje nasamu abba yazama dole ki koma wurin inna kuzauna tare ko kya rage kewa in yaso nan se asa yan haya
Murmushi Umma tayi tace
To shikenan ni dama damuwata bansan wane kalan zama kike agidanki bane
Kuantar da hankalinki Umma komai lafiya kalau
To shikenan dazu munyi waya da haleema tace tunda basu samu zuwa bikinki ba zasuzo itada Ali suga gidanki
Shiru asma'u tayi da alamun damuwa afuskanta
Kama hannunta Umma tayi tace nasan abunda kika tuna asma'u kimanta da komai yanzu bagashi kinyi aurenba kinma auri Wanda yafishi komai ai nafiso suzo sugani da idonsu wannan dai asma'un dasuka hana dansu ya aura saboda suna so ya auri yar attajiri gashi ta auri mijin dakowace mace ke fatan samu
Tashi asma'u tayi tana fadin Umma bari natafi kar yamma tayi
Rakota sukayi har waje da mamaki Umma tace asma'u duk ina motocin mijinki zaki zo a napep
Dariya dole asma'u tayi tace ohhh sauri nakene Umma shiyasa banjira ankawoni ba
Tana dawowa dakinsu tanufa tayi alwala tayi sallar la'asar tana ninke hijabinta AK yashigo
Kan gado yazauna yana fadin chitti kin fara parking ne
Da kin kyewtama kanji dan jibi warahaka tuni nayi waje dake daga gidan nan
Ijiye hijab din tayi tanufi dressing mirror tana fadin ni ba chitti sunana ba kuma basai ka koreni daga gidanka ba ni zantafi dakaina
Kusa da ita yamatso yana fadin ina kika je dazu
Jadabaya tafarayi tanakallonsa tace badai sokake na nemi izini awurinka kafin nafita ba
Girgiza kai yayi yamatseta da bango suna kallon cikin idon junansu yace inaso namiki kashedi ne idan har kika yi wani abunda dazaisa ahmad yafasa auren sarah se na kwakulo wannan idon dakike yaudaran maza dashi
Turesa tayi tawuce batace komai ba amma jikinta yayi sanyi
Komawa yayi yazauna yana fadin cigaba da parking nidai zansa ido kar amun sama dafadi da wasu abubuwana
Hijabin tasa a drowan kayanta tana fadin base nayi parking ba saboda ba abunda zan fita dashi daga nan gidan
Dole kitafi da tsummanki wazaki barmawa
Idan ka auro aysha setasa
Ba abunda aysha zatayi da kayanki tafi karfin kwance
To ai ni duk kayan dakaga inasakawa daga gidanmu nazo dasu nawane bana bukatar Wanda yafito daga hannunka
Karya kike kice ba kyason abun hannuna bayan saboda shi kika aureni
Kusa dashi tazo tatsaya tana kallonsa tace wai meyasa kakeso ahmad ya auri sarah bayan kasan bayasonta kana tunanin tunda ta auri Wanda takeso zatayi farin ciki kenan
Dagowa yayi yana kallonta da mamaki yace wai shawara kike bani ko fada kike mun
Kauda kai tayi batace komai ba
Wa yagayamaki ahmad baya son sarah ?
Suna son junansu ke kika shiga tsakaninsu Yanzu kinga asirinki yatonu shine zaki fara kame kame aurene dai ba fashi kuma daga andaura aurensu ni kuma zan warware nawa dake
Fita tayi daga dakin tana fadin nakasa gane wane kala ne kai u keep making the wrong decision
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Tana sakkowa kasa ta isko mutanen gidan zaune apalo kusan grany taje tazauna suna fira
Cike da takaici aunty sadiya ke kallonta kusan inna ladidi tamatsa cikin rada tace
ladidi natsani yarinyar nan duka duka yaushe tashigo gidan nan amma ji yanda grany tawani jata ajiki ni tsoro na ma kar abata jan ragamar gidan
Dariya ladidi tayi tace haba wa ai wallahi bata isaba barima kigani
Tana fadan haka tamike tanufi wurin asma'u tana murmushi tace gaskiya yau yakamata musan dandanon girkin surikarmu tunda tazo bamuci abincinta ba koya kuka gani
Aysha tayi carab tace wallahi kwa gaskiya yau yakamata tamana girki
Daure fuska grany tayi tace dacan wayake maku girki yanda kuke dinnan tukunya nawa zata daura muku
Sadiya tace grany tukunya daya ta isa base tayi daban daban ba mudai yayi dadi kawai
Shuru grany tayi batace komai ba
Tashi asma'u tayi tace ba komai grany zan musu girkin ai dama aiki nane amatsayin surikarsu
To shikenan asma'u jeki amma aysha kitashi kitayata
Carab sadiya tace a'a grany aysha aikenta zanyi wani wuri
Haka tashiga kitchen tafara aiki sauran ma'aikatan natayata se bayan mangariba tagama suka taimaka mata ta jera a dining sannan taje tayi wanka tayi sallah
Koda ta sakko suna zaune gaba daya akan dining sunsa kuloli agaba suna hadiyar yawu grany tahana kowa ci wai se wacce tagirka tazo
Tana zuwa tazauna kowa yafara ci ana santi AK dashigowarsa kenan shima yaje yazauna kusa da grany yafara ci
Lomar farko yace um um um grany amma yau ke kikayi girkinnan ko
Bashir yace Yaya narigaka azuci ka rigani afili nifa tunda nabude kular nan nasan abincin nan ba kalar nakullun bane Shiyasa naga uncle jamilu an karkace hula
Harara uncle jamilu ya watsamai bashiri yayi shuru yana kunshe dariyarsa
Cike da farin ciki grany tace yo ai asma'u ce tayi girkin
Shuru AK yayi baice komai ba se bashir ne keta koda abincin
Daure fuska grany tayi tana kallon AK tace nace matarka ce tayi girkin kuma kayi shiru
Dagowa yayi yana kallonta yace to mezan ce
Harara tawatsamai tana kara daure fuska
Kallon asma'u yayi yace ohhh Ashe haka kika iya girki darling shine ba kya mana gaskiya daga yau girkin ki zamu rika ci agidan nan
Zaro ido tayi tana kallonsa takasa cewa komai
Ladidi tace gaskiyarka AK daga yau mun samu kuku
Dariya sukayi gaba daya sarah tace tunda takasa wurin daukan wanka da kwalliya se tamana girki mai dadi muci
Kallon asma'u AK yayi yaga yanda fuskanta yacanza kamar zatayi kuka suna hada ido tasunkuy dakanta kasa tana wasa da yatsunta
Murmushi yayi yace wa yagayamuku hardaku zatayi girkin dani da grany kawai zatama kuma bandamu darashin kwalliyarta ba ina sonta ahaka
Dagowa tayi damamki tana kallonsa yayi saurin kauda kai yacigaba dacin abincinsa
Shuru sukayi bawanda yace kala aysha kwa tuni ta tashi tabar wurin tana jan tsaki
Dariya grany tayi tace gaskiyanka abidi kwalliya bashi kadai ne mace ba girki shine kan gaba
Washegari dasafe asma'u na bangaren grany suna shirye shiryen bikin sarah tana gayamata abubuwan da zasu bukata da gyaran gida da sauransu
Sarah tashigo tana hade fuska tace grany inaso naje shopping amma kowa yaki rakani gashi banaso naje nikadai
Dariya grany tayi tace to ba ga asma'u nan tarakaki ba ...
Murmushin mugunta tayi tace to shikenan
Da mamaki asma'u ke kallonta tasan dole akwai abunda tashirya
Kallon grany tayi tace a'a grany ni bazani ba inada aiki agabana
Grany tace a'a asma'u kuje mana daga nan sekiyo ma sauran mutanen gidan sayayya tunda kinga gobe za'afara bikin nan
Badan taso ba hakanan ta amince suka tafi
Suna isa shop owner din yataresu yana murmushi yace hajiya sarah barka dazuwa
Daure fuska tayi tana amsa gaisuwarsa
Ina kawarki yau bakuzo tare ba kika zo da mai aikinku
kallon asma'u tayi takwashe da dariya
Shima dariyar yayi yace Koda yake naji ance yallabai yayi aure nasan ita ya aura ko
Nuna mishi asma'u tayi tace to ai ga matar sa nan
Dariya yayi yajuya yana fadin aaaa haba kinma rainamun hankali
Daure fuska asma'u tayi tana kallon sarah tace
idan kin gama cimun fuska se muyi abunda ya kawomu
Wucewa sarah tayi tana fadin kije dai kiyi abunda yakawoki ni daban inda zanje
Tsaki tayi tanufi wurin atanfofi tafara zaba
Mutumin dazu ne yakara zuwa wurinta yana fadin malama lafiya kike tattaba mun kaya kibari uwar gidanki tazaba mana
Hararansa tayi tanunasa dayatsa tace
Kaga malam kafita ahanyata kajiko inace dai kudi zanbiya ina ruwanka da abunda zan dauka
Bayan sun gama sayayya akayi lissafi sarah tace ma asma'u tafita da kayan tajirata awaje
Iya nata tadauka tafita tabar na sarah awurin
Murmushin mugunta sarah tayi tana kallon shop owner din tace ina so Karage kashi 50 cikin kudin kayanta
Da mamaki yace haba hajiya kamar ya kashi hamsin yau kece da Neman ragi haka
Damen kudi ta ijiyemai kan table tace kasan Nafi karfin haka ga kufinka kawai kayi abunda nace
Dawkan kudin yayi yana dariya yace angama hajiya nan take yamika mata recite na abunda aka kashe amma yarage kudin kayan da asma'u tasaya atanfan dubu ashirin yasata adubu goma
Bayan sun iso gida sarah tacema asma'u takawo jakanta tashiga da kayan ita setashigo da sauran
Suna shiga ciki ta mika ma kowa nashi sun yaba kyan kayan sunata jin dadi
Sarah tace asma'u banga recite dinba muga jakanki naduba koyana ciki
Daukan jakan tayi taciro recite din tana dubawa
Kallon asma'u tayi cikin daga murya tace wannan wane kalan rainin wayaw ne
Damamaki kowa ke kallonta grany tace meyafaru
Tsaki tayi Tamika ma grany recite din tana fadin tarage kashi hamsin cikin kudin dakika bata tasiyo kaya masu arha
Damamaki kowa ke kallon asma'u har AK dake kwance kan 3siter yana kallo
Nan take aysha ,ladidi da sadiya suka dawo dakayansu wai sunfi karfin kayan dubu goma
Cikin rawar murya asma'u tace grany wallahi karya takemun ban rage komai aciki ba
Karban jakanta sarah tayi taciro bandir din kudi tana fadin su kuma wannan daga ina kika samesu tsiyar talaka kenan daga ansakemaku sekuyi abunda kukaga dama
Kusan asma'u grany tamatso tana fadin asma'u dagaske kin rage kudin danabaki
Shuru tayi tasadda kanta kasa tana boye hawayen fuskarta
Murmushi grany tayi tace se yanzu nayarda nayima abidi zaben daya dace
Da mamaki kowa yadago yana kallonta
Daure fuska tayi tana kallon su sadiya tace kafin kuji kudin kayanku duk kuyabasu kuma kunce sunyi kyew amma da kukaji kudin daga kuka dawo dasu
Yakamata kukoyi tattali adano daga wurin asma'u
Dakuna haka dayanzu kundaina family meeting din da kuke kuna tatsar abidi
Daure fuska sarah tayi dan ita bahaka taso ba
Tashi AK yayi yanufi bangarensa yana waya
Dariya aysha tayi tace shikenan komai ya wuce jibi dai sarah zata auri ahmad karyan mutum takusa karewa
Sarah tace wallahi kwa gobe ma zamu hada party anan gidan mu ba marada kunya
Tsaki asma'u tayi tanufi bangaren grany da sauran kayan da tasiyo
Washegari da safe ...
AK yana bayi asma'u tashigo bata saniba
tana daga labule tagansa atsaye yana balle maballan rigarsa
Atsorace tasaki labulan tana rufe fuskarta
Murmushi yayi yace kinzo yimun wanka kuma miye na tsorata
Bude fuskarta tayi tana fadin malan dan Allah kafita wanka zanyi
Cire rigarsa yayi yace Nima ai wankan zanyi kuma nan wuri nane kije ga shower can kiyi
Allah yakayewta nayi wanka wuri daya dakai kuma bazan fita ba senayi wankan grany tana jirana
Banza yayi da ita yashiga bathtub din da 3quater dinsa yana fadin to kizo muyi wankan tare
Juyawa tayi dasuri zata bar wurin santsi ya kwasheta se cikin ruwan tafada saman AK
Yar kara yasaki yana dafe bayansa yace Hajiya ai se kishigo ahankali ko
Atsorace ta tashi zata fita yakara janyota tafado kansa
Kallon cikin idon junansu sukayi nadan lokaci kana ta tureshi ta tashi da gudu tabar wurin
Kallonta yake yana dariya har tafita
Bayan dan lokaci yafito sanye da kananun kaya yayi kyew sosai
Tana zaune ta rufa da bargo tana atishawa
Dariya yayi yace tashi kishiga nafito
Hararansa tayi bata ce komai se atishawa take jerawa
Ruwan dumi ya mikomata batare dayayi magana ba
Da mamaki tace don't tell me that
u care about me
Kauda yayi yace karma kiyi tunanin haka I am doing it for my self
Banaso kiyi effecting dina
Karban ruwan tayi tasha tana fadin thank u
Bai kulata ba yafita daga dakin
Murmushi tayi tatashi tashiga bayi
Su sarah da aysha anci ado anyi kyew kowa yataru apalo ana party
Grany takalli asma'u tace kin gayyato ummanku kuwa
Girgiza kai tayi tace a'a grany tace bazasu samu daman zuwa ba se Gobe zasu zo camu amma zata turo khadeeja
Dariya grany tayi tace to Allah yakawosu nima yau kanwata zata zo
atsorace AK yace badai ameena ba
Daure fuska grany tayi tace ita ko kanada matsala ne
Dariya asma'u tayi tace meyasa bayaso tazo
Daure fuska yayi yace idan tazo zaki sani
Gida yacika da yan uwa kowa yazo har ahmad da Momy ga fa'iz da nusaiba sunzo
Sedai ahmad Sam baya cikin walwala se waige waige yake kozai ga khadeeja dama saboda ita yazo wurin
Kusa dashi sarah tazo tazauna tana murmushi tace honey ya kazauna kai kadai muje mudan taka mana
Daure fuska yayi yace I am not in the mood
Hannunta takai ta tabashi yayi saurin tashi yabar wurin
AK dake gefe yana kallonsu baiji dadi ba amma ya zaiyi
Lhadeeja ce tashigo gidan da wata mace mai kama da Umma se kuma wani kyekkyewan saurayi tare dasu suna shigo palon kallo yakoma Kansu
Sukuma sebin gidan suke da kallo dagudu asma'u tazo tarungume matar suka gaisa sannan takalli saurayin tana murmushi tace Ali ya kake
Murmushi yayi suka gaisa sannan takaisu wurin grany suka gaisa tagayamata matar kanwar Umma ce sawrayin kuma danta ne sannan tanufi kitchen dan kawomusu wani abu
Hannu Ali yaba AK suka gaisa yana musu fatan alkhairi a aurensu
Ahmad nahango khadeeja ya saki murmushi yana kallonta
Kamar ance ta kalla sukayi ido biyu kauda kai tayi kaman bata gansa ba tana daure fuska
Aysha da Sarah na tsaye daga gefe suna kallonsu tsaki aysha tayi tace ni wallahi nagaji daganin yarinyar nan kuma ni banga abunda AK yake mata ba banda kowane lokaci suna tare
Dafata sarah tayi tace kuantar da hankalinki aysha yanayi ne saboda kar grany ta fuskanci wani Abu amma nafiki tsanar yarinyar nan
Suna cikin magana Sega kanwar grany ta iso cike da farin ciki suka gaisa da kowa tun kafin tazauna tafara tambayar ina amaryar AK
Murmushi grany tayi tace bari akiramaki sarah kiganta
a'a nidai Nafi so naga amaryar AK sarah ai nasanta
Daure fuska sarah tayi tana gaisheta
Sama sama ta amsa gaisuwar tana waigen waigen mutanan wurin
Tunda asma'u tanufo wurin takafeta da ido tana washe baki
Tana zuwa suka gaisa tace gaskiya AK kayi dacen mata zuuuuuki
Dariya akasa gaba daya banda sarah data bar wurin tana jan tsaki
Bayan anyi shagali kowa ya watse aysha ta matsama AK akan seyafita da ita
Hakanan suka shirya suka fita yana driving tana mishi shagwabar yadaina kulata tunda yayi aure kamar yadaina sonta
Daure fuska yayi yace haba aysha ya isa haka mana yanzu bagashi nafito dakeba
Inda bana sonki kema kinsan ko kallo baki isheni ba
Ganin ya hasala yasa tafara bashi hakuri banza yayi da ita yana bin wakar da yake sawrare amotar
Sunkuyowa tayi gefen fuskarsa wai zata mai kiss
Birki yafara kokarin takawa yana fadin aysha miye haka kimatsa bana ganin gabana can't u see I am driving bai karasa ba yaji ya kade wani mutum saurin taka birki yayi yana salati
Ganin mutane sun nufi mutumin yasa yayi kokarin Barin motar amma aysha tarikosa tana kuka tace dan Allah sutafi kar agansu mutuncin shi zai zube idan aka ganshi da ita cikin Daren nan
Bashiri yataka motar suka tafi amma yanaji abunda yayi baidace ba
Suna isa gida yawuce bangarensa yana tunanin wane hali mutuminnan yake ciki
Baiga asma'u apalo ba kuma bata daki kayan baccinsa yasa yauna bakin gado yana danna laptop
Can anjima tashigo rike da mug ahannunta kan bedside drawer tadora tana fadin nagayamaka idan zaka fita da aysha kasan lokacinda yadace kufita yanzu da grany taga lokacinda kuka shigo mezaka cemata
Banza yayi da ita yana duba laptop dinsa da damuwa afuskansa
Kusa dashi ta tsaya tana fadin meyake damunka
Dagowa yayi yakalleta yace inada damuwan da tawuce kine
Murmushi tayi taleka laptop din da mamaki tace
Hukuncin tukin ganganci kuma kayi accident ne
Banyiba ....yafada atakaice
To meyasa kake Neman hukuncinsa ...
Kofa yanuna mata yana fadin dan Allah malama je ki kuanta kindameni
Talkative girl kawai
Dariya tayi tashinfida blanket dinta akasa tace ai ni yau ma nan zan kuana yafi dadi ...
Washegari dasafe...
Asma'u na goge goge apalo AK yafito cikin shirinsa tsap se kanshi ketashi
Kallonsa tayi tana dariya tace wai har kashiraya wannan har kafi amaryar zumudi
Harara ya watsamata yafita yana fadin Dan allah dai yau dai kiyi shigar kwarai kar kibani kunya gaban abokanai
Yana sakkowa kasa daidai yan sanda sun shigo gidan
Dariya yayi yana kallonsu yace malamai ba yau bane daurin auren gobene
Karasowa sukayi kusa dashi babbansu yace yallabai ba daurin aure mukazoba munzo tafiya dakai ne
Ahasale sarah tace kai karamin da iska mind ur language
Kasan dawa kake magana kuwa
Katseta grany tayi tahanyar daga mata hannu sannan takalli dan sandan tace akan wane dalili zaku kamashi
Shidai AK yayi shuru yakasa magana dan ko ba'afada ba yasan laifinsa
Kallon grany police din yayi yace hajiya yaronki yayi tukin ganganci jiya da da daddare har yakade wani mutun kuma bai tsayaba yagudu da motar to acikin mutanen wurin wani yarike numban motarsa shine suka shigar da kara kuma sunyi kashedin idan dai ba abimusu hakkinsu ba zasu yada ma yan jaridu amatsayin sa na Babban mutum kwa hakan ba karamin bakin jini zai janyomasa ba
Salati inna tayi tana kallonsa tace abidi yaushe haka tafaru baka sanardani ba
Cikin karfin hali yakalli dan sandan yace kunada wata hujjar datanuna ni nayi laifin
Murmushi dan sandan yayi yace kwarai kuwa yallabai saboda mutumin daka kade yaganka lokacinda kake kokarin fitowa daga motar kuma ya tabbatar mana akwai wata mace atare dakai cikin motar sedai bai tantance fuskartaba amma kai yashaidaka
Kuma muje muna so muduba motarka nasan zamu samu wata shaida tunda mutumin akan mashin ka kadesa dole motarka zata nuna
Fita sukayi gaba daya asma'u dafitowar kenan taji abunda yafaru tayi saurin bin bayansu
Waya sarah tadauka takira aysha bugu biyu tadaga cike da takaici sarah tace jiya kunyi accident da AK meyasa baki gayamun ba
Meyafaru ....
Aysha tafada tana yamutsa fuska
Yan sanda sunzo nemanku kina ina ...
Bata karasa ba aysha tayi saurin katse kiran atsorace tama kasheta gaba daya
Suna isa wurin motocin AK yayi saurin nufar motarsa yana kare scratch din dake jikin motar kusa dashi asma'u taje tana fadin jiya kunyi accident ne ?
Girgiza kai yayi baice komaiba
Matsardashi tayi tana kallon scratch din tace to meyasamu motarka
Juyowa yan sandan sukayi suna kallon motar
Dafe kai AK yayi yana fadin ohhhhh chitti bazaki iya yin magana ahankali bane
Janshi tayi gefe cike da damuwa tace jiya da natambayeka meyasa baka gayamun ba kai da waye amotar
Indai bake bace to kinsan aysha ce kidaina mun wawiyar tambaya
Murmushi dan sandan yayi yace yallabai shaidu sun nuna kai kade mutuminnan saboda haka zamu tafi dakai mudawki statement dinka sannan kagayamana wacece tare dakai amotar
Kauda kai yayi yace bakowa atare dani ni kadaine
Kuka grany tafara tana basu hakuri
Riko hannunta yayi yace grany ki kuantar da hankalinki yanzu zan dawo kawai bayanaina zasu dawka
Yana kai nan yashiga motarsa tare da biyu daga cikin yan sandan sukuma suka shiga tasu suka tafi
Cikin gida grany takoma dasauran mutanan gidan
Asma'u kuma nan take tabi bayansu police station
Tana zuwa tayi magana da police din akan yataimaka yahadata da mutumin da aka kade se dakyar yahadata da mutumin
Dafari kin sauraronta yayi seda tahadashi da Allah sannan yatsaya sukayi magana tarokeshi yajanye karar sa base takai ga yan jariduba
Ya yarda zai janye amma setabashi kudi masu yawa
Bayan AK yadawo gida yanemi ganin lawyoyinsa akan maganar
Sunce gaskiya case din yanada girma saboda yahada da tukin ganganci kuma dole se mutumin ya janye kararsa kafin aji da police
Gida asma'u tadawo tadauki sarka da yan kunnanta na zinare da abbanta yataba sayamata
Tazo fita kenan tahadu da AK
Cike da takaici yake kallonta har tafita yana fadin ba ma abunda yadameta yawo kawai tasa agaba
Camun dai ake amma kowa na zillimin abunda zai faru da AK
da rana sega yan sandan sundawo da mutumin da aka kade yasha bandage hannu dakafa
Tunda grany tagansu tafara kuka cike da damuwa sarah tarike AK tana fadin Yaya dan Allah karka bari sutafi dakai
Umma dabatasan abunda yafaru ba tace lafiya mekuma yaka yan sanda
Inna ta katseta tana washe baki tace
Inaga kamun sukazo suma
Juyawa AK yayi yana kallon asma'u dake kan dining tana cin abincinta hankali kuance jiyayi kamar yaje ya shakota dan takaici
Wurin yan sandan yanufa yana fadin muje karna batamuku lokaci
Rikosa dan sandan yayi yana murmushi yace sorry sir bamunzo tafiya dakai bane munzo baka hakuri ne akan shiga lokacinka da mukayi
Da mamaki kowa ke kallonsu
Kamar ya ....
AK yafada yana kallon Wanda yakade
Police din ya nuna mutumin yace wannan ne Wanda ka kade shi yashigar da kara kuma yanzu ya janye
Tukin gangancin dakayi kuma matarka tace bakai bane ke driving din ita tace tana so tayi shine kake koyamata Muncita tara tabiya kuma tabada hakurin hakan bazata kara faruwa ba
Saboda haka zamu tafi se anjima
Tunda yafara magana AK ke kallon sa cike da mamaki yakasa magana har suka fita
Cike da farin ciki grany takalli Wanda aka kade tana mai godiya
Murmushi yayi yace hajiya bani zaki godemawa ba waccan yarinyar zaku godema saboda ita tasa najanye karar
Alama asma'u tamishi da yayi shiru
Murmushi yayi yace a'a yarnan barni nafada kin birgeni matuka da kika tsaya akan matsalar mijinki dan kirufamai asiri najima banga mace kamarki ba
Sarah takatseshi dafadin dallah malam dakata tunda kajanye karar ai sekabar nan da kudin wa tabiya tarar ba kudin gidan nan ba
Bawanda yakulata
Sarkan yanuna ma grany yana fadin kinga abunda tabani akan najanye karar
Da mamki Umma tace asma'u wannan basarkan da babanki yabaki bane shine zaki sayar
Murmushi tayi tace Umma meyasa zan ijiyeta bayan ga anfaninta yazo
Cike da farin ciki grany tace ma mutumin yasaida mata sarkan bada bata lokaci ba ya amince tabashi kudi masu yawa yatafi
Godiya tama asma'u tana samata albarka sannan tabata sarkanta tace kar takara saida sarkan tanada mahinmanci tunda babanta yabata
Bangarensu tanufa dan ijiye sarkan
Aysha ce tashigo gidan adan tsorace dan tahadu da yan sandan suna fita
Kusan AK tamatso cikin rada tace AK naga yan sandan sunfita Allah sa dai baka fadamusu tare Muke ba
Da mamaki yake binta dawani irin kallo yakasa cewa komai
📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KaNWATA_ 👩👧
9⃣0⃣
Sosa kai tayi tana kame kame tace kar kamun wata fassara kawaidai natambaya ne
Ahasale yace meyasa kanki kawai kika damu dashi kina ikrarin kina sona ita wacce bata sona bana sonta ta ysaya mun alokacinda nake Neman taimako
Ke kina ina awannan lokacin kuma inada tabbacin kinsan da zancan amma baki dawo ba seyanzu kuma kina tambayar wai nafadi sunanki
Juyawa yayi ahasale yabar wurin
Hannu tadora akai tace nashiga uku ni aysha
Wurin Asma'u yanufa tana shirin shiga wanka ya iskota
Chitti bansan meyasa kika yi haka ba akan wane dalili amma thank you
Daure fuska tayi tace nagayamaka kadaina kirana chitti kuma karma kayi tunanin nadamu dakaine saboda Umma da grany nayi hakan nasan bazasuji dadi idan aka kamaka ba shiyasa so stop thanking me..
tana kainan tawuce bayi
Murmushi yayi yajuya yafita
Yana sauka kasa yazauna kusa da inna yana tambayarta abba
Fira suka fara yi suna dariya
Kusan sarah aysha tamatsa tana gayamata yanda sukayi da AK takare dafadin
Yanzu zaiga kamar asma'u tafi damuwa dashi ni bandamu ba
Sarah tace to ai dagaskiyansa kema wayakaiki yimai wannan tambayar
Tsaki aysha tayi tana kallon Ali tace ni wallahi guy dincan tunda nashigo yake kallona bai San haushi yake bani ba
Dariya sarah tayi tabar wurin
Kiran kowa tayi akan za'afara rawa sawrayi da budurwa mata da miji
Ai kaman jira Ali yake yazo wurin aysha wai suje suyi rawa Da har taki amma dataga AK na kallonsu tamike suka fara rawa
Inna ameena tace AK yatashi suyi da Asma'u
Dariya yayi yace bata iya rawa ba
Daure fuska tayi tace kamar ya daga ganinta zatayi kyew da rawa kirata kuyi
Murmushi yayi yace kedai kawai kice tabirgeki amma wane kyew da rawa yarinya kullun alullube
To ai shine kyen ni duk nan wajan banga yarinyar da lullubi yakema kyew ba kamar Asma'u
Dariya yayi yace akwaisu dayawa ma
Ina suke
Waige waige yafara can yahango wata yarinya atsaye ta juya baya tana magana dawata
Nuna ta yayi dayatsa yace gawata can
To tashi kirata muganta
Gyara kuanciyar sa yayi kan 3siter yana fadin dan Allah kibarni ba inda zani
Jan kafanshi tafara tana fadin tashi dai ka kira ta inkasan da gaske kake ni ban yarda ba se naganta
Tashi yayi yana yarfa hannu yanufi yarinyar
Bayanta yatsaya yace hello !!!
tana juyowa yaga asma'u tana murmushi tace hi!!!
How me I help u
Juyowa yayi yakalli inna ameena tana kwasan dariya
Sannan yakalli asma'u da mamaki yace meyasa zaki canza kayan jikinki
Murmushi tayi tace saboda nayi wanka idan abunda kazo tambayata kenan sekatafi ....
tana kai nan tayi gaba abunta
Juyawa yayi yana kallon su aysha dake rawa haushi yaji yabar wurin
Murmushi tayi dan ganin AK yana kishinta
tana ganin yatafi tadaina rawan takoma tazauna
Kusa da ita sarah tazo tazauna tana mata magana akunne suna kallon fa'iz da yadage yana daukan khadeeja photo
Ita kwa se daure fuska take tana kauda kai
Dariya sukayi suka tafa hannu sannan sarah tace je kifito da jakan kidora kan gado bari nakirashi
Aysha natafiya sarah takira fa'iz tace yaje dakinta ya dawkomata jakanta yaso yaki tace zata gayama Umma hakanan yatafi yana gunaguni
Aysha nashiga dakin AK yaturo kofar atsorace ta jiyo tana kallonsa
Kusa da ita yamatso yana fadin rawa kike dawani agabana ko ??
Murmushi tayi tace to ai nadauka kadaina sona ne tunda kayi aure
Ashe kana kishina
Rungumota yayi yace ina sonki amma kishindai ban saniba dan banji komai ba lokacinda naganko
Tunowa tayi da plan dinsu tafara kokarin turesa tana fadin AK katafi kar wani yaganmu bata gama rufe baki ba sukaji anturo kofar
Atsorace yasaketa sukajiyo atare dan ganin Wanda yashigo
Fa'iz suka gani atsaye yana kallonsu idonsa cike da hawaye
Me kake anan....
AK yafada yana daka mai tsawa
Shuru yayi yakasa magana yana binsu da kallon tuhuma
Janshi AK yayi dakarfi yafito dashi Waje
Damamaki kowa ke kallonsu
Ahasale grany tace kai abidi sakeshi mana meyamaka
Aysha tayi saurin fadin grany lekani yake ina canza kaya
Juyowa fa'iz yayi yana kallonta da jajayen idanuwansa
Zaiyi magana kenan AK ya wankesa da mari yana fadin me ya kaika dakinta
Zai karamishi kenan asma'u tarike hannunsa tana kallon fa'iz tace dagaske kaje dakinta
Zai yi magana AK yarigashi dafadin tambayarsa ma kike kenan karya zan masa kome
Inna ameena tace yo kai AK ya akayi kasan yaje dakin kana daga ciki kodaga waje
fa'iz zaiyi magana AK yakara katseshi dafadin wallahi idan nakara ganinka kanufi dakinta sena tattaka ka
Kwaceshi asma'u tayi daga hannun AK tanuna mai hanyar fita tana fadin wuce gida
Cikin rawar murya yace ammah listen
I said out ....
Saurin barin wurin yayi khadeeja tabi bayansa
Hakuri AK yaba su inna akan abunda yafaru
Murmushi tayi tace ba komai abidi ai fa'iz kaninka ne zaka iya hukuntashi idan yayi badaidai ba
Fita asma'u tayi tabi bayan khadeeja akarkashin bishiyar kofar gida ta iskosu yasa kai aguywa yana kuka khadeeja na zugunne kusa dashi tana lallashi
Asma'u nakarasowa yamike zai bar wurin tayi saurin rikosa tana bashi hakuri
Cikin sheshshekar kuka yace yanzu amma kema kinyarda na aikata abunda tace wallahi karya takemun
Rikoshi tayi tana murmushi tace nasan ba halinka bane fa'iz amma bayanda zanyi inkareka
Kauda kai yayi yana share kwalla yace amma meyasa kika auri AK Sam bai dace dake ba ba mutumin kwarai bane kuma wacece wannan yarinyar danagansu tare
Murmushin dole tayi tace haba fa'iz meyasa zaka ce haka kaifa kake yabon AK hausawee kuma yau kana kushisa wannan yarinyar kanwarsa ce shiyasa kaga yamaka haka akanta amma ba halinsa bane yanada kirki kuma yanada hakuri bayada saurin fushi kuma ko yayi nantake yake mantawa
Da kyar tasamu ta lallasheshi suka wuce gida da khadeeja ita kuma tadawo ciki
Karo sukaci dasu inna zasu fita hakuri tabasu kuma taroki kar su gayama Ummi da abba abunda yafaru sannan sukayi sallama suka tafi
AK natsaye yana kallon sarah da aysha dake dariya karasawa yayi wurinsu fuska ahade yace inafata dai Baku kuka shirya wannan wasan kwaikwayon ba
Kame kame suka fara suna kallon kallon zai yi magana kenan ahmad yakirasa awaya yana tambayar ya yake yaji wai police sunzo Neman sa
Murmushi yayi yace I am fine friend yanzuma nakeso nazo company
Dariya ahmad yayi yace har kagama cin amarcin ne
Katse kiran yayi batare dayace komai ba
yana dubawa yaga harsun bar wurin girgiza kai yayi
Yajuya zai fita sukaci karo da asma'u tazo wucewa dafe goshi sukayi atare cike ahasale yace wai meyake damunki ne
Murmushin yake tayi tana mai alama da grany tana kallonsu
Shima kalan murmushin yayi yana taba goshinta yace meyasa ba kya kula dakanki ne kinfiso kiyita jima kanki ciwo kina bani aiki
Inna ameena dake kallonsu tayi dariya tace ai kakanninmu sunce in mata da miji sukayi karo sau uku to ba mai rabasu sai Allah saboda haka kunyi daya saura biyu
Kan asma'u Yakama yahada danasa da karfi saida taji zafi seda yayi har sau biyu sannan yawuce yana shafa goshinsa ....
Da daddare yana kuance kan gado yayi rub daciki yana kallon TV ga bowl din gyada ahannunsa yana ciki
Asma'u tashigo dakin rike da mug din coffee dinsa kusa dashi ta ijiye batace komai ba da alamun damuwa afuskanta
Binta yayi da kallo yana fadin fushi kike ne dan nadaki kaninki
Juyowa tayi tana kallonsa tace meyasa zanyi fushi dan yayi laifi ka hukuntashi
Sedai inaso nasan meyasa kamareshi
dan yashiga dakin
Kodan yaganka tare da aysha
Shuru yayi baice komai ba yaci gaba da cin gyadarsa
Bathroom tanufa tana fadin kunasaka familyna amatsala saboda makauniyar soyayyarku
Dakallo yabita har tashiga sannan yadauki coffee dinsa yanasha
Can anjima tafito sanye da doguwar rigan baccinta ga towel akanta tana tsane gashinta
Remote din kusa dashi tadauka takashe AC tanufi dressing mirror tana gyara gashinta
Da mamaki yake kallon dogon gashinta dan Sam bai San tanada gashi haka ba
Remote din yadauka yakunna AC
Juyowa tayi takallesa yayi saurin kauda kai yana kallon TV
Zuwa tayi tashiga gaban TV tahanashi kallo
Kashe AC din yayi takoma wurin dressing mirror
Kara kunna AC din yayi yana murmushi
Juyowa tayi tana yarfa hannu tace wai miye haka kakeyi
Gyana nakeci....
Yafada batare da yakalleta ba
Kusa dashi tamatso dan ita se alokacin ma ta lura da gyadan hadiye yawu tayi tana murmushi tace tsammun gyadan
Make kafada yayi yace naki kije wurin grany tabaki
Grany tayi bacci
To kijira dasafe tabaki
Dawke bowl din tayi daga gabansa tana fadin Allah senaci
Dirowa yayi daga kan gadon yana fadin to kikawo na tsammiki da kaina
Guduwa tafarayi tana cin gyadar shikuma yana kokarin kamata seda suka zagaye dakin kap sannan takara cika hannu da gyadan ta mika mai tana fadin to tsaya gashi Allah kadan naci
Kin karba yayi yana kokarin kuace na hannunta suka fada kan gado shi Asama ita akasa
Kallon juna sukafarayi alokaci guda suna tuna lokacinda suka fara haduwa da zamansu awuri guda
Asma'u ce ta tuna lokacinda AK kecemata gobe ana daura auren sarah zata bar gidan
Tureshi tayi tatashi tana gyara balanket dinta dake kasa ta kuanta tana hawaye
AK ma shiru yayi yaci gaba da kallon TV har bacci yadaukesu
Washegari dasafe ....
Khadeeja nazaune adaki tun jiya take kuka har yau tana tuna shikenan yau ahmad zaizam nawata shikenan zata rabu dashi
Umma ce tashigo dakin cike da tausayi take kallonta tace khadeeja kiyi hakuri shi aure nufi ne na Allah tunda kikaga bai aureki ba Allah yayi ke ba matarsa bace
Shuru khadeeja tayi tan sharan kwalla
Cikin sassanyar murya Umma tace zaki samu zuwa bikin kuwa
Girgiza kai tayi batace komai ba se hawayen ta dasuka karu
Abangaren ahmad ma haka Zaune yake atakure ga idonshi yayi ja da alama kuka yasha bakadan ba Momy batayi wani taron biki ba dan tasan ahmad ba son aurennan yakeba dafashi tayi da damuwa afuskanta tace ahmad kaifa namiji ne za a iyama mace auren dole tazauna amma ba namiji ba idan har kasan baka son sarah to karkayi kuskuren aurenta
Namiji shine ginshikin aure idan har bazaka iya jan ragamarsa ba to baida wani anfani
Girgiza kai yayi yace Momy banason sarah amma zan aureta saboda wani dalaili
Tashi yayi yafita yana fadin Bari nashirya natafi AK yana jirana
Asma'u na bangaren grany bayan tagama hada breakfast ta fito tana kallon grany tace
Grany har kinshirya lalle kin kosa sarah tayi aure
Dariya grany tayi tace eh mana asma'u ai rana tafarayi gashi har mutane sunfara taruwa jeki kema kishirya
Zama asma'u tayi tana fadin bari har nacika tumbina grany
Ina wani tumbi anan Abu kaman faranti
Wai ina abidi banganshiba yau
Yana bacci ....
Oh to nidai yau Allah sa yasa manyan kaya wallahi natsani kananun kayannan daurin aure guda amma kagansu da kananun kaya kamar wasu turawa
Dariya tayi tace karki damu grany tunda ba kyaso bazai saka ba
Wa ya isa ya hanasa asma'u mutumin da kika ga ko juma'a kananin kaya yake sakawa
Tashi tayi tafita tana fadin
Grany idan kasan halin mutum zaka ita sashi yayi abunda kakeso
Tana isa bangarensu ta iskoshi kwance yana bacci murmushi tayi tanufi bayi tayi wanka kayanta taduba taciro wata doguwar riga mai kyew da dogon wandonta kamar na India se gyalen kayan
Datasakasu ita kanta sunbirgeta mai kawai tashafa sedan kunne datasaka kalan kayan
Drowan AK taduba taciro mashi kananun kaya masu kyew sannan tafito
Azaune ta iskoshi bakin gado tunda tafito yake kallonta seyaga tayi kyew yau
Murmushi tayi tadawra kayan kan gado tana fadin ABI....bata karasa ba yawatsamata harara tayi shuru tana kunshe dariyarta
Can kuma tace to ai ban fada duka ba tunda ka kirani da chitti ai nima zan iya kiranka da ABIDI amma sunan yamun yawa shiyasa na rageshi
Daure fuska yayi yace to kikirani da AK ko ABID mana
Miye nawani ABIDI
Dariya tayi tace ashe ba dadi idan bakaso nakiraka ABI to nima kadaina kirana chitti
Shuru yayi yana kallon kayan da ta ijiye kan gadon murmushi tayi tadauko kayan tana nuna mai tace ga kaya nazaba maka kasa zasuma kyew
Kauda kai yayi yace karki manta matsayinki awurina so stop acting like my wife
Dariya tayi tace banmanta ba amma ai duk dahaka ni matarka ce kuma kananun kaya suna maka kyew inason ganinka acikinsu shiyasa nakeso yau kasa
Kwace kayan yayi ahannunta yanufi dressing room yana fadin tunda kinaso kwa bazan saka ba kuma kidaina tabamun kayana daga yau
Murmushi tayi tana kallonsa har yashiga sannan tafara gyara gadon
Can anjima yafito sanye da manyan kaya sunmasa kyew bakadan ba
Dariya takusa kwacemata ganin yanda yake tattare rigar ga hular akarkace
Daure fuska yayi yanufi dressing mirror yana fesa turare
Kallonsa tayi tana dariya tace yallabai hularka akarkace
Banza yayi da ita yana gyara zaman wandonsa
Dagowa yayi yana kallonta tana dariya yace ai gwara ni koba komai ansan nayi kyew ke kuma fa dako janbaki baki iya sakawa ba kin wani yafa gyale kamar dillaliya ...
Fita tayi tana dariya tace wani gwara kai dawata hularka har tarufe girarka Allah sama kana gani da kyew
Bin bayanta yayi suka fito tare yana rike da rigar da yakeji tamai dabaibayi
Tasashi agaba se dariya takemai tun yana daure fuska har yabiyemata suna dariyar
tunda aysha ta tsinkayesu taji kamar andaba mata wuka suna sakkowa aka hau yima AK dariya bashir ne yagyara masa hularsa kowa nafadin yau ya canza kamar bashiba grany tace manyan kaya sunfi yimasa kyew
Matsowa aysha tayi taja asma'u gefe ahasale tace ke wai meyake faruwa ne
Bige hannunta asma'u tayi tana murmushi tace abunda idonki yaganemaki
Firan me kuke da AK dazu dakuka sakko
Barin wurin asma'u tayi tana fadin sirrin ma'aurata ne baizama dole ke kiji ba
Da kallo tabita tanaji kamar ta kurma ihu
Gyada kai tayi tana cije lebe tace dole nadau mataki naga alama ina sake dabaki zan jini asalansa ....
Shigowar Ahmad da sauran abokanansu ne yakatsemata tunaninta nan take aka hau shewa ana murna banda ango dakana ganinsa kasan yana cikin damuwa
Tunda yashigo sarah takasa dauke idonta akansa tana ji ba macan da takaita Sa'a saboda ahmad daban ne yahadu iya haduwa
Dining suka nufa gaba daya suka fara cin abinci suna fira
Kitchen aysha taja sarah tana fadin amarsu zo mu dakko masu dambun naman da grany tace aba abokanan ango gift idan sunzo
Da kallo asma'u tabisu dan tasan wata gulmar zasuyi
Tashi ahmad yayi yanufi bangaren grany yazo wucewa kenan yaji suna magana
Aysha tace wallahi yau senakeji nafiki farin ciki mun kusa rabuwa da annoba
Dariya sarah tayi tace ai jira kawai nake adaura aure muyi waje da ita
Dariya sukayi suka tafa ...
Girgiza kai yayi yana fadin kai inaaaaa bazai yuwu ba bazan yi biyu babu ba
Narasa khadeeja kuma bukata bata biyaba auren asma'u yamutu
Wayanshi yaciro yana kiran khadeeja amma bata dauka
Fita yazoyi yahadu da asma'u zataje wurin khadeeja taga yatake
Shan gabansa tayi ta tareshi tana fadin ina kuma zakaje bayan lokaci yayi idan ma kana tunanin khadeeja ne to koma wurinta zanje yanzu
Zaiyi magana yaga sarah atsaye tana kallonsu
Runtse ido yayi yana cije lebe yajuya Yakoma ciki """"
Ur's.......
*MHD*
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na ( *Maryam Mhd* )
( _nasadaukar dawannan page din gareki Aisha(anna) da kuma Dr Aisha tnx for ur support
Sa'ata da xee Allah yabar zumunci )_
9⃣5⃣
Bayan anci ansha AK yafara Neman ahmad amma bai gansa ba yakira wayarsa yafi akirga amma baidaga ba daga karshema ya kashe wayar baiyi tunanin wani Abu ba yaje yatambayi sarah ko yagayamata Inda zaije
tace bata ganshiba nan fa aka fara nemansa gashi kowa yataru amasallaci ana jiransu adaura aure
Hankali tashe yake kiran wayar ahmad amma akashe
Sarah dake gefenshi tana rusa kuka ta mike zunbur tana fadin ina asma'u
Juyowa sukayi shida aysha suna kallonta
Aysha tace kina nufin tasan inda yake
Bata bata amsa ba tafita aguje tasauka kasa tana kwalama asma'u kira
Amma bata ganta ba
Jan hannunta AK yayi yamaidata sama ganin yanda mutane ke kallonsu
Dakinsa yakaita yana fadin ki kuantar da hankalinki sarah nasan bai yi nisa ba kila wani uzuri ne yafitar dashi
Tureshi tayi tafada kan gado tana kuka tace Yaya duk laifinka ne kai kaja haka tafaru kasake mata dayawa ka aureta ne dan kahukunta ta amma kabiyemata kana mata wasa kana mata dariya kana fira da ita shiyasa tasamu damar yin haka yanzu gashi tarusa mun farin cikina kuma naganta tana ma ahmad magana dazu nasan ita tacanza mai ra'ayi yafasa aurena wallahi bazan barta ba sena kasheta
Ahasale yafita daga dakin yana banko kofar dakarfi
Aysha tazo binsa kenan tahango wata farar takarda akan dressing mirror har tawuce se kuma tadawo tadauki takardar ganin ansa
from ahmad to AK
Yasa tafaki idon sarah tafara karantawa kamar haka
Nasan lokacinda zakaga wannan takardar kana nemana friend
kayi hakuri naso na sadaukar da soyayyata na auri sarah amma daga baya na fuskanci hakan bashida wani anfani
Nadauka idan nahakura da wacce nakeso na aureta komai zai wuce amma naji da kunnena tana cewa zaka saki asma'u idan na aureta
Friend kayi hakuri naboye maka gaskiyar lamarin amma ni ba asma'u nakeso ba
KHADEEJA kanwarta ita ce budurwata da ita muke soyayya baku fahimci abun yanda yadace bane
I am really sorry amma bazan iya gyara daya nabata goma ba
Bazan iya auren sarah narabu da khadeeja ba
Kai kuma daga karshe karabu da asma'u
Nasan zaka ji haushi amma kayi hakuri
I am sorry but i can't
Ur friend ....ahmad
Zufa ce taji tana karyomata lokacinda tagama karanta wasikar cike da tashin hankali take fadin na shiga uku ni aysha yanzu dama ba asma'u bace budurwan ahmad
boye takardar tayi aranta tana fadin ai wallahi bazan bari kusan da wannan zancan ba dama can naga takeken asma'u tafara jan hankalin AK inaga inyaji gaskiyar maganar nasan bazai saketa ba
AK na sauka kasa ita kuma tashigo hannunta yaja dakarfi yanufi sama da ita
Yanayin da taganshi aciki ya tsoratata tana magana amma yayi banza da ita se fizganta yake da karfi har tana neman faduwa
Sadiya takalli ladidi tana fadin wai meyake faruwa ne
Dariya ladidi tayi tace ango ne ya gudu annemesa anrasa
Tashi tayi tanufi bangaren grany tana murmushin mugunta tace bari naje nagayama tsohuwar can Allah sa ma hawan jininta yatashi tamutu muhuta
Tana isa bangaren grany tafara kukan munafunci tana fadin grany munshiga uku za'akunyataki gaban baki
Daure fuska grany tayi tace kunya takare akanki meyafaru
Ahmad ya gudu yace yafasa auren sarah
Jiri ne yadibi grany inna ameena ta tarota tazaunar da ita kan kujera
Bayan wani dan lokaci tasauke ajiyar tana salati tace shikenan haka Allah yakaddara amma ahmad bai kyewta ba yasan bazaiyi auren nan ba meyasa bai fada tun wuri ba gashi yanzu muntara mutane mezamuce masu
Cike da takaici sadiya ke kallonta ahasale tace wai grany bakiji komai ba
Inna ameena tamaka mata harara tace to munafuka mai bakin labari me kike so taji
Juyawa tayi tana jan tsaki tabar wurin
AK na shiga daki ya wurga asma'u kan gado kusa da sarah cikin kakkausar murya yace daga ina kike ina ahmad
Cikin rawar murya tace meyafaru ...
Shako wuyanta sarah tayi tabaya tana fadin munafuka tambaya ma kike meyafaru ke baki ji kunya ba da aurenki amma kinabin wani wallahi se kinfadamun ina ahmad dina yake
Da kyar AK ya kwaceta a hannun sarah
Kallonta yake da rinannun idanuwansa yace tambayar ki nake ina ahmad kigayamun ko yanzu in cimaki mutunci abainan jama'a
Fashewa tayi da kuka tarikoshi tana fadin dan allah kayi hakuri wallahi bansan inda ahmad yakeba Ni yanzuma nashigo gidan nan ban San meyake faruwa
Nufota sarah tayi aguje tana fadin wallahi karya kike kinsan inda yake dazu batare naganku ba narantse idan baki fadi inda yake ba sena kasheki
Riko hannunta AK yayi sannan yakalli asma'u yana daka mata tsawa yace get out of my room
Fita tayi tana kara fashewa da kuka
Zaunar da sarah yayi bakin gado cikin sigar lallashi yace calm down sarah koma ina ahmad yake zan nemosa kuantar da hankalinki kar mutane sugane halin da ake ciki
Cikin sheshshekar kuka tace to Yaya adaura auren mana ai ba dole se yana nan ba
Girgiza kai yayi yana share mata hawaye yace ba yanda za'a daura aure batare da amincewarsa ba sarah kidan bani lokaci zansan abunyi
Kuantawa tayi akan gadon tana rera kukanta mai cin rai
Tsaye yayi yana kallonta nadan lokaci kafin yasauke nannauyar ajiyar zuciya yana fita daga dakin
Asma'u nafita takira wayar khadeeja tana tambayr ko taga ahmad
Da mamaki khadeeja tace a'a ammah bangansa ba meyafaru
" khadeeja ahmad bayanan annemesa anrasa kuma ana kiransa baya dagawa
ko yakiraki ne
" bansaniba naga kiranshi dazu amma bandauka ba nakashe wayar
" OK to ki kirashi yanzu muji ko zai daga
abangaren Momy ma Neman ahmad take har zata kira AK taji wayanta na ringing tana dubawa taga ahmad
Bayan tadauka tayi sallama
Cikin wata iriyar murya kaman mai shirin fashewa da kuka yace
Momy nafasa auren sarah khadeeja nakeso kuma ita zan aura kome zai faru yafaru nagama yanke hukunci
Murmushi Momy tayi tace
Ahmad kayanke hukuncin da yadace akurarren lokaci
amma ba komai haka allah yakaddara
Jin anturo kofa yasa ta ijiye wayar
AK ne yashigo cike da damuwa ko gaisawa basuyi ba yace Momy ina ahmad
"Banganshiba AK rabona dashi yatafi wurinka....
Bata karasa ba ya juya yabar palon
Yana fita ta kira Ahmad tace AK yazo nemansa
Kiran AK yayi awaya bugu biyu yadaga ahasale yace ai bandauka zaka iya kirana ba ahmad meyasa zaka mun haka meyasa kake so ka tozartani ne
Wai natambayeka miye laifin sarah da kake wulakanta ta
Cikin rawar murya ahmad yace AK katsaya kasaurare ni bakaga wasika...
Bai karasaba ya katseshi dafadin
Mezaka gayamun Wanda bansani ba
Bazaka iya auren sarah ba kanada wacce kake so
Soyayya soyayya
Koba abunda zaka gayamun kenan ba
To tsaya kaji zan iya yafe komai amma bana abunda yashafi familyna
Yana kainan yakatse wayar hade da dukan sitiyarin motar da karfe
Ahmad ma kuance yake acikin motar sa ga idonsa yayi ja kana ganinsa kasan yana cikin damuwa
Wayarsa ne yafara ringing yana dubawa yaga my flying bird
Saurin daukar wayar yayi yana fadin haba deeja meyasa zakiki daukar wayana kikasan mezan gayamaki
"Mezaka gayamun kwa banda kafasa auren sarah
Kasan halin da kajefa yayata aciki kuwa wannan shine sonda kake ikrarin kana mun ...
" deeja please dan allah kisaurareni inaso muhadu dake maganar bana waya bane
Shuru tayi nadan lokaci kana daga baya ta amince ya gayamata inda zasu hadu
Tana kashe wayar takira Asma'u tagayamata
Asma'u tace taje suhadu itama zata zo wurin suyi magana
Ganin magariba tagabato yasa akaba mutane hakuri akan anfasa taron bikin se wani lokaci
asma'u na idar da sallar magriba tafito danufin tafiya wurin su ahmad tahadu da aysha
Riko hannunta aysha tayi cikin sassanyar murya tace asma'u kiyi hakuri akan abunda yafaru kwanaki se yanzu nagane bakida laifi Ashe kanwarki ahmad keso bakeba yanzu gashi kina fuskantar matsala ta dalilin hakan
Murmushi Asma'u tayi tace bakomai nagode da kika fahimceni amma dan allah karki gayama kowa yanzu ma haka wurin ahmad zani narokeshi yadawo saboda nayarda sarah tana tsananin sonsa
Murmushi aysha tayi tace OK kunyi magana da ahmad yana ina
Batare da tunanin komai ba asma'u tagayamata inda zata sannan tawuce tana sauri
Da kallo aysha tabita tana murmushin mugunta sannan tanufi wurin AK da sarah dawata takarda ahannunta
Tana shiga Tamika ma AK takardar tana fadin gawannan nasamu adakinka kuma yanzu nahadu da asma'u zataje wurin ahmad
Karban takardar AK yayi yana karatawa afili kamar haka
I am sorry friend naso na hakura na auri sarah amma bazan iya jure ganin asma'u amatsayin matarka ba gaskiya idan dai kanaso na auri sarah to se kasaki asma'u tukunnan ...
Ur friend ahmad
Runtse ido yayi cike da takaici yace wai yaushe ahmad yazama hakane dama wannan ce wasikar dayake maganar ko nagani
Dafashi aysha tayi tana fadin AK to kasaki asma'un mana tunda yace hakan ne kawai zaisa ya auri sarah
Harara ya watsamata bashiri tayi shiru tana ja dabaya
Tambayarta yayi ina asma'u zataje
Tana fadamai ya dauki makullin motarsa yafita
Khadeeja na isa ahmad yatareta da damuwa yace deeja meyasa kike wahalar danine
Daure fuska tayi tace ko ni kake wahalar daniba kasan bazaka cikamun alkawari ba meyasa ka dauka akan wane dalili kafasa auren sarah
Ahasale yace wai khadeeja meyake damun kine meyasa kike takura zuciyarki kihanata abunda takeso kawai dan kifarantama wasu
Itama ahasale tace ni bantakurawa zuciyata ba Tarzan kawaidai sonka ne nadaina yi kakasa ganewa ada nasoka amma yanzu bana sonka saboda kai kajefa yayata ahalin da take ciki yanzu
Zaiyi magana kenan asma'u ta iso
Karasawa yayi wurinta yana fadin yawwa asma'u dan allh kima khadeeja magana tagane abunda nake kuatanta mata munason junanmu meyasa zamu takura kanmu
Daga inda khadeeja take tace bana sonka ni kuma bazan aureka ba
Janshi gefe Asma'u tayi cikin sassanyar murya tace ahmad meyasa zakamun haka seda nace karkaje ko ina amma bakajiba yanzu miye anfanin abunda kayi
Shafa kansa yayi yana runtse ido yace aunty kigane nibazan auri sarah ba naji da kunnena tana fadin daga na aureta AK zai sakeki to mezai sa na aureta
"Ahmad kamanta dawannan zanji dashi amma sarah tana mutuwar sonka ahmad kar kaso kaga halin da tashiga lokacinda ka tafi she lost her mind bcoz of u
Meyasa bazaka tausayamata ba
Zaiyi magana kenan sukaji karan rufe mota dakarfi
Juyowa sukayi atare dan ganin waye AK suka gani yana nufosu kamar mayinwacin zaki
Yana zuwa ya cakumi wuyan ahmad yahada shi da mota yana fadin how dare u ahmad kawai dan kaga ina kyaleka bakajin kunya kana kebewa da matar aure
Me kanwata tamaka kake wulakantata dame wannan tafita
Riko hannunshi asma'u tayi tana kuka tace ABI please stop it
Katsaya muyi magana atsanake kar....
Bata karasa ba yasaki ahmad ya riko kafadunta da karfi cikin kakkawsar murya yace maganar me zamuyi dawa zanyi maganar da matar da kecin amanar aurenta ko abokin da kecin amanar amininsa
Kawai dan kinga ina ragamaki
To na kyaleki ne saboda ina tunanin zargin da muke maki ba gaskiya bane amma yanzu nagane kuskurena
Sakinta yayi yana fadin shikenan bari nahutar daku base kuntsaya labe labe zan sawwake maki kawai kowa yahuta
Sarah kuma ba ahmad kadai bane namiji bare tamutu ba aure
ai khadeeja najin haka tayo kukan kura tacafki kafan AK tana kuka tace Yaya dan Allah kar karabu da yayata wallahi ba ita ahmad kesoba ni yakeso kawai Baku fahimci abunda bane amma dani ahmad ke soayayya ba ammah ba dan Allah kar kasaketa takarashe maganar tana fashewa da kuka
Cak ya tsaya yana kallon ahmad da mamaki yanuna khadeeja yana fadin yanzu ahmad wannan yar karamar yarinyar kakeso mekagani ajikin wannan dayabirgeka
Matsowa ahmad yayi yadago khadeeja daga kafan AK fuska ahade yake kallon AK yace
Eh ita nakeso AK kuma ita zan aura shi so nagaskiya ba yabukatar girma ko shekaru kafin afara shi amma bazaka fahimci hakan ba se ranar da kafada irin halin da nake ciki
Kana bani mamaki yanda kacanza lokaci guda ada kana son duk abunda nakeso amma ayanzu kai kake kokarin hanani abunda nakeso
Nagaji da boye boye AK zan fito nagayama kowa wacce nakeso idan aka takura ni kuma wallahi se indauketa mugudu
haba katsaya karamar kanwarka tana juyaka kamar remote control abunda takeso shikake yi kayi kokarin koyamata yanda zata nemi Abu dakanta saboda ba kullun kuke tare ba
Yana kainan yaja hannun khadeeja yatafi yana fadin ga asma'u nan kayi abunda kaga dama da ita amma kasan ka tanadi amsar da zakaba iyayenta dakuma grany
Kuka khadeeja tafara tana kokarin kwace kanta tana kiran asma'u amma yaki sakinta seda suka shiga mota yatada aguje yabar wurin shikanshi titi kawai yakebi aguje kamar zai tashi sama amma baisan inda zashiba
Da kallo AK kebin motar har tabacemai sannan yashiga motarsa yabar wurin
Durkushewa asma'u tayi awurin tana wani irin kuka mai ban tausayi tasan shikenan yanzu kowa zaisan abunda yake faruwa AK zai rabu da ita ga ummanta nafama da ciwon zuciya tun rasuwar abbansu yanzu idan taji tasan tabbas bazata ita jurewa ba ga abba da inna wane hali zasu shiga
Seda tayi kukanta mai isarta sannan tawuce gida
AK na isa gida bangaren grany yanufa yasanar da ita zancan ahmad kanwar asma'u yakeso kuma yafasa auren sarah
Lallashinshi tayi tana kuantar mai dahankali
Yaso yagayamata komai amma ganin bata cikin koshin lafiya yasa ya barshi akan idan taji sauki zai gayamata komai sannan yabata hakuri akan zai sawwakema asma'u tunda ba son junansu suke ba
Tana isa gida tazauna apalo hade da dafe kai tana tunanin ina ahmad zai kai khadeeja dan ba hanyar gida taga yanufa ba
jin anfizgota dakarfi yasa tadago atsorace dan ganin waye
Sarah tagani atsaye tana huci ga idanunta dasuka kunbura sunyi ja
hannunta tafara ja tana fadin dan ubanki ko mayyace ke yau sekinbar gidan nan
Fizge hannunta tayi tana fadin ke baki isa kifitar dani ba sekibari Wanda yakawoni yafitar dani dakanshi
Dariya aysha tayi tana tafa hannu tace kaji wani karfin hali to albishirinki AK da kansa yabamu izinin fitar dake daga gidan nan kije kijira takardarki zata biyoki daga baya
Hannunta tazo kamawa tayi saurin kawcewa tana fadin base kunfitar dani ba nizan fita dakaina
Sannan takalli sarah tace ke kuma kinba mata kunya wallahi kina ba kanki wahala kina hauka akan namijin da baimasan kinayi ba yayanki yana kokarin hadaki da Wanda kike so amma ke kinzama silar rabashi da amininsa kindaga mai hankali kin hanashi sukuni shame on u
Tana kainan ta juya tafita daga gidan tana sharan kwalla
[18/07, 15:05] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣0⃣0⃣
Tafe take akan hanya tana kuka tunaninta daya ummanta mezata ce mata wane hali zata shiga idan taganta awannan daren wai ankorota daga gidan mijinta
Amma yata iya yazama dole ummanta taji amma tasan dubarun dazata mata yanda abun bazai daga mata hankali sosai ba
Gudu ahmad yake amotar kamar zai bar gari se kuka khadeeja ke masa amma bai saurareta ba sunyi nisa sosai
Mai yakare amotar gashi ba kowa akan hanyar
Bude motar yayi yafita yana rufo kofar dakarfi
Fitowa khadeeja tayi cike da masifa tashiga gabansa tana fadin meyasa katsaya ai na dauka garin zamu bari what is wrong with u Tarzan
ahasale yace karki kara cemun Tarzan Duk bake kika sakani ahalin da nake ciki ba miye laifina
dan nasoki ko kuma dan nakasa saka son sarah araina
Wallahi da ina da hali da nacire sonki na saka nata koba komai nasan tana sona
Kuma da itace bazata taba hakura dani dan wasu ba koda kwa AK ne dakanshi
juyawa tayi tana fadin to kaje ka aureta mana tunda kasan tana sonka meyasa zaka daukoni ka kawoni nan
Binta yayi da kallo yakasa cewa komai seda yaga tayi nisa sannan yabi bayanta yana kiranta
Banza tayi dashi tana tafiya seda taga tafara shiga daji tsoro yakamata ta tsaya
Karasowa yayi cikin sigar lallashi yace deeja wai meyasa kin cika rigima ne kinga nan wurin baida kyew kizo mukoma can ko zamu samu wani ya tsammana mai mukoma gida nasan yanzu anfara nemanki
Kamar tafashe da kuka tace bani wayarka inkira Umma
"Wayana tafadi dazu awurin da AK ya iskomu
Ina taki wayar
"Ba caji
Juyawa yayi yanufi mota yana fadin
OK muje in munsamu mai se kiyi caji amota
Bin bayansa tayi suka dawo
Bude motar yayi suka zauna shi agaba ita abaya amma kofofin motar abude
Kuka tafara tana fadin yanzu gashi kajamun nasan ana nemana agida ni damuwata ma bansan wane hali yayata take ciki ba
Handkerchief yamika mata yace dan allah kidaina wannan kukan kinga wurin nan ba kyew ne dashiba kar ki tona mana asiri
Cikin kukan tace matsoraci kawai...
Dariya yayi yace ahaka kika gani kina so ba
Kauda kai tayi tace ni allah bana sonka
Shiru yayi baice komai ba yana sauke ajiyar zuciya
Grany ce tace AK ya kira mata asma'u zasuyi magana
Bayan ya fito ya dudduba ko ina baiganta ba yazo wurin su sarah dake zaune Palo yana tambayar asma'u bata dawo bane
Da mamaki aysha tace lafiya kake nemanta
zama yayi yana fadin Kawai dai grany ke nemanta
Kauda kai Sarah tayi tace mun koreta
What ???
Yafada yana kallon bangaran grany
Aysha tace bakaso mukayi hakan bane ko kafara damuwa da ita ne
harara ya watsamata yana fadin
come on shut up dallah !!
meyasa zaku koreta awannan lokacin ba kwa tunanin grany ne kunsan bata jin dadi dawanne kuke so taji
To kumasani ba ita ahmad kesoba kanwarta khadeeja itace budurwansa
Azabure sarah tamike tana fadin Yaya kasan me kake fada kuwa khadeeja fa kace
"Kwarai khadeeja da ita suke soyayya ahmad dakansa yafadamun kuma nagansu tare da khadeeja akan idona yadauketa suka tafi kawai kin gansu tare ne ke kuma kikayi tunanin itace yakeso nan yakwashe yanda sukayi yagayamusu
Yakare maganar dafadin
Yanzu gashi kun koreta me kukeso nagayama grany
riko hannunsa aysha tayi tana fadin AK kayi hakuri amma aikin gama ya gama kawai kasan yanda zakayi da grany
Kuace hannunsa yayi yanufi bangarensa
Damamaki sarah ke kallon aysha ahasale tace amma dazu wace takarda kika bama AK ina kika sameta
Yama naga zancan bai baki mamaki ba hakan yana nufin kinsan da maganar kome
Sosa kai aysha tayi tana kame kame tace yi hakuri sarah nima se dazu nasani naji tsoron idan AK yasan gaskiya bazai rabu da asma'u bane shiyasa naboyemaku zancan amma kiyi hakuri
Tsaki sarah tayi tace karki kara mun irin haka banaso da kingayamun tun alokacin da nasan matakin da nadauka
AK yana tura kofar palonsa yafara tuna asma'u kujeran da take bacci yakalla yatuna lokacinda yake tashinta da sassafe ya hanata bacci
Kauda kai yayi yawuce daki yana shiga ya hango blanket dinta aninke akan gado murmushi yayi da yatuna draman su tajiya
Zama yayi bakin gado yacire hularsa yana tuna lokacinda takemai dariyar bai iya sa hula ba
Saurin tashi yayi yanufi bathroom yana fadin mema yasa nake tunaninta
Umma nazaune apalo itada inna kasancewar sundawo nan gidan dazama
Cike da damuwa Umma tace inna wai kin aiki khadeeja ne
Inna ta tabe baki tace inafa zan aiketa da wannan daren yarinyar dako darana na aiketa setaga dama takezuwa
Shuru tayi nadan lokaci sannan tasauke ajiyar zuciya tace ni wallahi yau naji gabana na faduwa asma'u nayawan fadomun arai gashi bansan inda khadeeja tajeba rabona da ita tana wurin su Ummi kuma fa'iz yace tun dazu tabar can
Inna tace kikira asma'u mana kiji ko suna tare tunda dai khadeeja ba inda take zuwa da daddare
Daukan waya Umma tayi takira numban asma'u
Su sarah na zaune apalo sukaji waya na ringing
Dauko wayan aysha tayi tana fadin kinga mutuniyar ki tabar wayanta
Kauda kai sarah tayi tana jan tsaki
Aysha tayi dariya tace ba dai ummanta ce lagonta ba to bari mudan buga game
Daukan kiran tayi tana yamutsa fuska
Umma naji andaga kiran tace asma'u ya kike
Tundazu khadeeja tafita bata dawo ba kuna tare ne
Murmushin mugunta aysha tayi sannan tace ba asma'u bace
Da mamaki Umma tace to waye ina asma'u
"Kina magana da aysha
Karkidamu asma'u tana nan zuwa wurinki saboda mijinta ya korota daga gidansa
Kedai inaga bakiyi dacen haihuwa ba yarki khadeeja ma tagudu da saurayi yanzu haka suna tare da ahmad tasa yafasa auren sarah
ga babbar miji ya korota cikin dare
Ta kare maganar tana kwashewa da dariya ....
Nan take jiri yafara dibar Umma zama tayi akan kujera ta dafe kai tana salati
Dafata inna tayi tace lafiya meyafaru
Cikin rawar murya Umma tace inna kinji wannan yarinyar aysha tana mun maganar banza wai Abid yasaki asma'u kuma wai khadeeja sun gudu da ahmad
Salati inna tayi tana fadin anya kwa wannan yarinyar da gaske take nifa banyarda ba
Tashi Umma tayi tana yafa gyale tace inna ana karya da maganar saki ne kuma idan bahaka ba ina khadeeja take nakira wayar ta yafi akirga amma akashe ni gaskiya zanje naga asma'u
Hanyar fita tanufa tana fadin baiwar allah nasanta da zurfin ciki yanzu haka tana tunanin halin dazanshiga shiyasa taki zuwa
Binta inna tayi tana fadin ina zakije cikin wannan daran ki...
Bata karasa ba kawai taga Umma tayi baya tafadi kasa asume
Da gudu takarasa wurinta tana salati tashiga kwala ma Abba kira
aguje suka fito su duka aka nufi asibiti da ita
Fa'iz da baisan meyake faruwa ba ya kira wayar asma'u jin ba adauka ba yakira ta grany ya gayamata Umma ba lafiya tagayama asma'u
Sannan yafara Neman numban khadeeja amma akashe
Asma'u na is a gida tahadu da nusaiba abakin get nan tagayamata labarin da daga mata hankali
Ko gidan bata Shiga ba aguje tanufi asibitin akafa tana rera kuka 😭
ahmad yanata surutunsa khadeeja tayi banza dashi
Kuantar dakansa yayi jikin kujera yana magana shikadai
yace baby yaushe zamuyi aurene
never.....
Khadeeja tafada tana kauda kai
Juyowa yayi yana kallonta yace malama ba dake nakeba tunda kince ba kyasona nima baruwana dake dawata daban nake magana so stay out of it
Daure fuska tayi tace kasan tadi zaka zo wurin aljanar ka meyasa baka ijiyeni agidan mu ba kataho dani
Murmushi yayi yace saboda ina so kisan inada wacce tafiki dan haka kidaina jamun aji
Lumshe ido yayi yana hango khadeeja ranar dayafara ganinta
Murmushi yayi yana shafa kai ahankali ya furta
she was so beautiful like a flower in the garden
Ita dabance acikin mata komai tayi kyew yake mata
Takun tafiyarta daidai yake dakowane bugu naziyata
Idan nakalli idanuwanta yaruwata gaba daya nake hangowa acikinsu
Idan tana magana nakan shagala wajan kallon kyewawan lips dinta har bana iya fahimtar
Metake fada
Idan tayi murmushi jinake kamar nunfashina zai dawke
Idan tana dariya kuma ban kiba nazauna nayita kallonta har tsawon rayuwata
Bantaba sanin ina tsananin sonta ba se lokacinda nafuskanci kalubalen rabuwa da ita
Sunkuy dakai khadeeja tayi tana murmushi dan ko baifada ba tasan da ita yake
Murmushi yayi shima yacigaba dafadin zamuyi aure ta haifamun yan biyu talle da mudi
Saurin dago kai tayi tana fadin allah ya kyewta talle da mudi fa
Juyowa yayi ya kalleta yana dariya yace ke kuma asuwa zaki sakamana baki a firarmu
Kauda kai tayi tana daure fuska dan Sam bata masan lokacinda maganar tafito bakinta ba
Shuru sukayi basu kara cewa komai ba har bacci yadauki khadeeja amma ahmad yakasa bacci yana gadinta
A asibiti kuwa bayan doctor ya duba Umma yace masu zuciyarta ce tabuga zasu mata aiki amma senior doctor din bayanan dole ajira se yazo
Haka suka zauna jigum har asma'u ta iskosu suka gayamata abunda doctor din yace kuka tafara inna na lallashinta gashi annemi khadeeja anrasa
Suna zaune suna jira asma'u se zarya take office din doctor din yana gayamata baizoba sukara jira har safiya tayi shiru
Dasafe grany taja AK sukaje asibitin amma harsuka isa ba ayima Umma aiki ba
Inda tahango su inna azaune tanufa AK nabinta abaya bayan sungaisa Yaje kusan Abba yazauna ita kuma grany tana wurinsu inna
Da mamaki takalli asma'u tace yo kekuma asma'u sekitaho baki gayamun ba haka ake
Shuru asma'u tana sadda kai batace komai ba
Saurin mikewa tayi tanufi doctor din dataga yafito daga office tana fadin doctor har yanzu baizoba
Daure fuska yayi yanufi wani wurin yana fadin malama kinfa dameni sonawa zan gayamaki bai zoba da yazo aida kinganshi ko
Shan gabanshi tayi cikin kakkausar murya tace wai ba kwada tawsayine ??
Tunjiya baiwar allah take wahala amma ko ajikinku ko dabbace yakamata Ku tausayamata bare mace
ko zakaso ganin mahaifiyarka awannan halin
Wucewa yayi abunsa batare dayace kala ba
Durkushewa tayi awurin tana fashewa da kuka mai ban tawsayi tasowa inna tayi takamata tana lallashi
duk abunda suke AK na kallonsu sedai baiji dadin abunda doctor din yayi ba
tashi yayi ahasale yabi bayan doctor din ya cakumo rigarsa cikin daga murya yace mekuke jira ne dabazaku mata aiki ba
Atsorace doctor din yace sorry sir doctor din dazai mata aikine baizoba nakirashi kuma yace karna damesa daga karshema yace in nakara kiransa se yasabamun
Hannu yamika mashi yace bani wayanka
Jiki narawa ya Ciro wayar yayi dialing number yabashi
Seda takusa katsewa yadaga ahasale yace kai wai banace kar ka kara kirana ba wacece ita dazakadameni akanta bazasu iya jira bane ko zan iya hanata mutuwa ne in lokacinta yayi
Runtse ido AK yayi yana shafa kai cike da Bacin rai yace
Kana magana da AK hausawee kuma marar lafiyar mahaifiyata ce wallahi kaji na rantse nabaka nan da minti 30 idan ba'afara mata aiki ba senasa ankulle asibitin nan tunda banga anfaninshiba
Kasan bazaka kula da marasa lafiya ba uban wa yace kabude
atsorace yafara ba AK hakuri
Bai saurareshi ba yakatse kiran yamikamata doctor din yana fadin Ku kaita dakin operation yanzu zaizo
Juyowan dazaiyi yaga asma'u agabansa tana murmushi tana sharan kwalla
Tace
ABI nagode allah yasaka da alkhairi...
Kauda kai yayi yana daure fuska yace badan ke nayi ba
nadauki Umma matsayin uwata ne
kuma naga inna tana kuka ni kuma banaso
To karma kiyi tunanin saboda kene
Murmushi tayi tace duk dahaka ma nagode
Juyawa yayi yatafi baice komai ba
Kusan inna tadawo tazauna tana fadin wai inna ya akayi haka tafaru
Nan inna tabata labarin wayar da Umma tayi da aysha ce sila
ahasale tamike tanufi gidan AK
Da kyar ahmad yasamu mai yasa amotar kana suka baro wurin khadeeja nasa caji kiran fa'iz ya shigo wayar
tana dauka yagayamata halin da Umma take ciki
Asma'u na isa gidan tahadu da sarah da aysha sunfito zasu fita wurinsu tanufa fuska ahade
aysha naganinta tafara dariya tace mekuma yadawo dake ko wayarki kika.....
Bata karasaba taji saukan lafiyayyen marin da yakusa sa tasaki fitsari
Nuna ta tayi da yatsa cikin kakkausar murya tace
wannan kashedi ne idan kika kara irin wannan ni kaina bansan mezan maki ba
Idan ke bakisan darajar uwarki ba to ni nasani kuma wallahi idan wani Abu yasami ummata se nabaki mamaki
Tana kainan tajuya tana fadin banza mara kamun kai
Da kallo aysha tabita tana dafe da kunce har tafita sannan takalli sarah tace wai ni wannan yarinyar zata mara
Motar tashiga tana fadin wallahi sena nuna mata ruwa ba sa'an kuando bane
dayan gefen sarah tazauna tana murmushi tace mezaki mata bayan ta taxi
Tada motar tayi suka fita tana huci tace
badai saboda ummanta tamareni ba to agaban umman nata zan rama marina inyaso tamutu
[18/07, 15:05] Hubbey Frd Ameena Kn: asibiti ahmad yanufa direct khadeeja na gefe se kuka take duk ya gama rudewa ko parking bai gama ba tafita aguje tanufi cikin asibitin
Koda taje har anfito da Umma daga dakin operation tana dayan dakin amma bata farfado ba
Aguje tanufi dakin inna tayi surin riko hannunta ahasale tace
Daga ina kike mara kunyar yarinya ke yanzu bakiji kunyar zuwa nan ba
Rungume inna tayi tana kuka tace inna dan allah kuyi hakuri wallahi bazan kara ba dan allah kibarni inga Umma
Rikota Abba yayi yana fadin zo nan khadeeja daga ina kike meyafaru muna ta nemanki wayanki akashe
Shuru tayi taci gaba da kukanta takasa cewa komai
Shafa kanta yayi yace shikenan yanzu kije gida kuyi abinci keda nusaiba se Ku kawo daga baya mayi magana
tashi tayi jiki asanyaye tafito daga wurin tana sharan kwalla
Karo sukaci da ahmad zai shiga atsorace yace deeja menene yanaga kinfito meyasami Umma
Banza tayi dashi taje jikin mota takifa kai tana rera kuka
dawowa yayi wurinta yana tambayar meyafaru
Daidai nan su sarah suka iso asibitin aguje tanufo inda suke ta matse khadeeja jikin motar tana fadin allah yakamaki munafuka wallahi yau nizanyi ajalinki
Kokarin rabasu ahmad keyi amma yakasa
Kamar mahaukaciya haka sarah tadawo gashi tarike wuyan khadeeja gam taki sakinta
Ahasale yafizgota daga jikin khadeeja yayi wurgi da ita gefe seda tafadi sannan yanunata da yatsa yace wallahi kika kara tabata se tattakaki awurin mahaukaciyar banza kawai
Tasowa tayi tanufosa tana kuka tace eh nayarda ni mahaukaciya ce ahmad amma kuma kai kahaukatani
Riko hannunsa tayi tana nuna khadeeja tace dame wannan tafini ahmad mezakayi dawannan karamar yarinyar dabata masan miye soba
Nice nakesonka da gaske ahmad zan iya mutuwa in narasaka
Kwace hannunsa yayi yabudema khadeeja mota tashiga sannan shima yazaga yashiga suka wuce
Da kallo tabisu baki bude se hawaye dasuka wanke mata fuska
Jan hannunta aysha tayi suka koma mota suma suka bar wurin
Bayan dan lokaci Umma tafarfado tana kiran asma'u
Aguje suka fada dakin su duka kusanta asma'u taje tazauna tana kuka tace na'am Umma
Shafo gefen fuskanta tayi cikin muryar mara lafiya tace asma'u dagaske ne AK yasakeki da gaske khadeeja tagudu da ahmad
Shiru asma'u tayi takasa cewa komai se hawaye dake diga daga idonta
Damamaki grany tace wane saki kuma take magana kodai tayi mafarkine
Shuru kowa yayi adakin bawanda yabata amsa
Juyowa tayi tana jifan AK da kallon tuhuma
Saurin matsawa yayi kusan gadon yakamo hannun Umma yana murmushi yace haba umma wace irin magana ce wannan taya zan saki asma'u haka kawai batayimun komai ba bayan ina sonta koma wa yafadamaki karyane kidaina damun kanki yan....
Bai karasaba takatseshi dafadin amma dagaskene ahmad yafasa auren sarah sun gudu da khadeeja ko
Kauda kai yayi ya zare hannunsa daga nata yana fadin Umma kibar wannan maganar khadeeja tana nan bataje ko ina ba yanzu dai kina bukatar hutu kidaina daga hankalinki
fita yayi yana fadin bari naje doctor nason ganina kudan barta tahuta
Binbayansa asma'u tayi sukashiga office din doctor din
Bayan yagama yan rubuce rubucensa yadago yana murmushi yace waye nata acikinku?
Atare sukace ni..
Juyowa sukayi suka kalli juna sannan AK yakalli doctor din yace muduka ya'yanta ne meyafaru
Cire glass din idonsa yayi yana sauke ajiyar zuciya yace well
Wato zuciyarta ce tabuga sanadin ji ko ganin wani abunda yadaga mata hankali dama kuma tana fama da ciwon zuciya to yanzu dai munyi nasarar yimata aiki amma akiyaye nan gaba kar irin haka takara faruwa zaku iya rasata duk wani abunda zai bata mata rai akiyayeshi
sannan akula sosai da maganinta
Bayan yagama yimasu bayani yabasu list din magungunan daza abukata da sauran abubuwan sannan suka fito
Wurin Abba AK yanufa yabashi takardar sannan yace zaije mota yadauko kudi se asiyo maganin
Gudiya yamasa yana samai albarka
Murmushi yayi yace Abba bana bukatar godiyarku ni Dane awurinku kome nayimaku addu'a kawai zakumun ita nafi bukata ba godiya ba
Yana kainan yaraba tagefen asma'u yawuce batare da yakalleta ba
Da kallo tabisa tana murmushi yar yabacema ganinta sannan tazauna tana sauke ajiyar zuciya
Washegari da yamma aka sallami Umma gaba dayansu suka koma gida harda su grany
Bayan sunci abinci sundan yi fira suka shirya zasu tafi
Ganin asma'u batada niyyar tafiya yasa Umma tace asma'u kitashi kutafi mana
Langwabe kai tayi tace Umma kidan barni nazauna har kiji sauki
"a'a tashi kitafi ni naji sauki alhamdu lillahi kuma ga inna da Ummi ai ba nikadaibace
Shagwabe fuska tayi tana kallon grany tace grany kirokammun Umma tabarni se gobe
Murmushi grany tayi tace a'a ni ba ruwana tashi ga mijinki can awaje kitambayeshi idan yabarki ba matsala
Ganin dagaske suke yasa bashiri tafito waje Neman AK
Cikin mota ta iskoshi zaune yana jiransu
Karasawa tayi jikin motar tatsaya kanta akasa tana tunanin mema zatacemasa
Sauke glass din motar yayi yaleko yana fadin kinada magana ne
Sosa kai tayi tace dama dama sonake inkuana anan harzuwa gobe
Kauda kai yayi yana maida glass din motar yace u don't need to ask me dama zaki zauna gaba daya sonake
Shuru tayi takasa cewa komai kuma takasa motsawa seda tadan jima kana tajuya takoma ciki tana mamakin meyasa taji zafin maganarsa bayan tasan ba sonta yakeba
[19/07, 16:58] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam mhd*)
1⃣0⃣5⃣
Washegari dasafe AK yasauko daga bangarensa yana naman sarah dan tun jiya rabonshi da ita aysha ya tambaya tace sarah tana dakinta tun jiya take kuka har yanzu bataci komai ba
Dakinta yanufa ahankali yatura kofar yana sallama
Can karshan gado ya iskota zaune tasa kai aguywa tana aikin kuka
Yajima atsaye bakin kofar yana kallonta kafin ahankali yataka zuwa inda take
Kusa da ita yazauna yana shafa kanta cikin sigar lallashi yace
Sarah idan nace nasan halin dakike ciki nayi karya saboda duk yanda ake fadin soyayya ni bahaka nasanta ba
nakanyi mamakin yanda mutane keshiga tashin hankali idan suka rasa masoyansu
Nasan zakaji zafi amma bansan yazafin yakeba
Ni hasali ma banyarda akwai wata aba ba wai soyayya
ganinki awannan halin yasa nafara tawsaya ma masoya kuma hakan yasa tafita araina tunda ba komai acikinta se kunci dawahala
Nasan kina son ahmad kina kaunarsa kina son rayuwa dashi amtsayin mijinki
Amma inaso kigane akan yima mace auren dole tazauna amma ba namiji ba
ada nadauka ahmad zai iya aurenki yazauna dake ahakan amma lokacinda nagansa da khadeeja natabbata koda kin auresa bazaki ji dadin zama dashiba saboda nafuskanci bakaramun so yakemata ba
Dan haka kiyi hakuri kimanta da ahmad kiyi addu'ar allah yabaki miji nagari Wanda yafi ahmad kuma yasoki fiye da yanda zaki soshi
Ko kuma ni kibani dama cikin abokanaina nazaba miki Wanda nayarda dashi nasan zakiji dadin zama dashi
Tunda yafara magana bata dago takallesa ba sema kukanta dayakaru
seda yasa hannu yadago kanta sannan tabude jajayen idanuwanta tana kallonsa
Handkerchief yaciro a aljihunsa yafara share mata hawaye yana fadin kinyi shiru bakice komaiba ko kinbani damar nazaba miki ne
Kauda kai tayi cikin dasashshiyar muryanta tace
Yaya ni nagirma nakai lokacinda zan tantance abunda yadace dani da Wanda baidace ba basai kazabamun ba
Ko limamin kasar maka zaka kamun bana bukatarsa kuma bazan so shiba ni ahmad nakeso kuma shi kadai zan aura idan bazaka sa ya aureni ba leave it to me ni zan iya ...
Cike da mamaki yake kallonta tunda tafara magana
Cikin wata iriyar murya yace sarah ni kike gayama haka
Ni kike gayama kin girma kinsan abunda yadace dake
Koda yake ba laifinki bane ni nabata ki
tun kina Karama nareneki da hannuna duk abunda kikeso shi nake maki baki taba Neman wani Abu kinrasaba sedai inyafi karfina
nayi kokarin bata abotar dake tsakanina da ahmad duk saboda ke
amma yanzu ki kalli kwayan idona kina gayamun wai basai nazabamaki ba kinsan abunda yadace dake
Tashi yayi yanufi hanyar fita daga dakin yana fadin
Fine nabarki kizabi abunda yadace dake amma karki kara sakani cikin duk wata damuwarki
Saurin tashi tayi tarungumo shi tabaya tana rusa kuka tace Yaya dan allah kayi hakuri bahaka nake nufi ba raina ne abace I am sorry
janyeta yayi daga jikinshi yafita batare da yace komai ba
bangaren grany yanufa bayan yayi breakfast yakwanta anan Palo yana kallo
Fitowa grany tayi daga daki tazauna daga gefe tana fadin abidi yau kaje kaduba Maman su asma'u kuwa
girgiza kai yayi alamar a'a
"Bangane a'a ba to tashi kaje daga can ma kabiyo da matarka
Pilo yasa yarufe kansa kamar zai yi kuka yace ooooo grany dan allah kibarni nadan huta ita batasan hanya ba da intaje ni nake zuwa dawkota
Haba tarike tana salati tace yau naga abunda yafi karfina ni mairo
Kai yanzu abidi matarka bata kuana gida ba amma kana mitar zuwa dawkota
anya kwa abidi kanada cikakkiyar lafiya kuwa
tashi yayi yana yarfa hannu yafita daga Palon
zaune yake abayan mota driver ketukasa har suka isa
fa'iz dake filin gidan yana buga kwallo ne yazo yabude masu get
bayan yashiga yayi parking AK yafito daga motar yana kallon fa'iz dayayi kamar baisanshiba
Murmushi yayi yakarasa wurinsa yafara buga ball din
tsaye fa'iz yayi yana daure fuska yagaidashi ciki ciki kamar mai koyon magana
Dafashi AK yayi yana amsa gaisuwarsa yace come on boy wai fushi kayi dan namareka ranan
Kauda kai fa'iz yayi baice komai ba
"OK I am sorry bansan meyakaika dakin ba amma nasan abunda tafada karyane
She is my sister kaga bazanso hakan yafaru da ita ba
Kaima kuma kanina ne bazan so ace ka aikata hakan ba
Amma nagane rashin fahimta aka samu tsakaninku
Karkato da kuncinsa yayi yana shagwabe fuska irin nayara yace
Idan kuma kana fushine dan namareka to gashi Karama
Dariya fa'iz yayi yana fadin haba yaya allah ya kyewta
Dariya shima yayi ya wuce cikin gidan yana fadin bari nagaida Umma nazo muyi kwallo
Yana tura kofar palon yahadu da khadeeja tafito daga kitchen rike da plate din indomie ahannunta
Sunkuy dakai tayi tana gaidashi
Bayabo ba fallasa ya amshi gaisuwarta yana zama apalon
Ciki ta wuce ta sanardasu ga AK yazo
Bayan sunfito suka gaisa yakoma kusan Umma yazauna yana fadin Umma ya kike ji yanzu bawata matsala daiko
Murmushi tayi tace ba komai abid nagode da kulawa allah yasaka da alkhairi
Ameen yafada yana kallon inna yace inna kefa
nifa harmukaje asibiti banyarda Umma ce batada lafiya ba nadauka kece
Daure fuska tayi tace ni makiyiyarka ko to ta allah bataka ba
Dariya yayi yace allah baki hakuri daga magana ai ni masoyinki ne
kallon khadeeja Umma tayi tana fadin Ashe abunda wainnan sakarkarun yaran sukayi kenan ai da kazanemun ita wallahi khadeeja bataji ko ina ita ina ahmad oho
Tashi tayi tafita idonta cike da kwalla
Murmushi inna tayi tace harkan yara se hakuri
Sannan takalli AK tace kungaisa da Abba kuwa
Girgiza kai yayi yace a'a ni yanzu nashigo yana nan ne
"eh yana bangarensa
Tashi yayi yanufi bangarensu Abba
yana Isa ya iskosu zaune apalo suna fira harda asma'u
Bayan sungaisa yashiga firan anayi dashi sedai jifa jifa yana kallon ALi da asma'u dasuka koma gefe suna tasu firar
kiran khadeeja tagani yashigo wayanta da mamaki tatashi tafito daga palon
karo sukaci da khadeeja zata shigo fuskanta sharkaf hawaye
Gefe tajata tana fadin lafiya khady meyafaru kike kuka AK yamiki wata maganar ne
Daidai nan AK yazo wucewa yatsaya yana sauraronsu
Cikin rawar murya khadeeja tace baicemun komai ba amma naji kunyar hada ido dashi
Gaskiya koda son ahmad zai kasheni dolene nahakura dashi saboda bandace dashiba
Sarah tana sonsa idan ya aureta ahankali zai fara sonta
Farin cikin sarah shine na AK ni kuma naki shine nawa
Gaskiya dole ne ahmad yazaba ko ya auri sarah ko yahakura damu gaba daya amma ni bazan iya aurensa ba
Barin wurin AK yayi yanufi motarsa yashiga
fa'iz yabudemasu get yana fadin Yaya har zaka tafi bakace zamuyi kwallo ba
Murmushi yayi yana daga mai hannu harsuka fita batare da yatankasa ba
Yana fita yakira ahmad awaya seda takusa katsewa yadaga
Bayan sungaisa sama sama AK yace kana gida ne
eh.....
Yafada atakaice
Katse kiran yayi yagayama driver gidansu ahmad zaikaishi
Numban sarah yakira amma har yamata 5 missed call bata daga ba
Shuru yayi ya jingina da kujera hade da lumshe ido yana tunani kala kala aransa har suka isa
yana isa bangaren ahmad yatura kofar yashiga zaune ya iskosa apalo
Ahmad naganinsa yamike tsaye
Kusa dashi yamatso yadafa kafadarsa yace
Friend inaso ka rufe idanuwanka kamanta lokacinda muka fara samun matsala dakai kamanta lokacinda sarah da khadeeja suka shigo rayuwarka katuna lokacinda muke dagani sekai kana kirana supper hero ina kiranka supper man
Lokacinda dayanmu baya iya bacci se yatabbatar da lafiyan dan uwansa lokacinda za'a dakeka amma nine zanyi kuka lokacinda banada lafiya amma kai ne kejinya lokacinda zanji ciwo amma sekafini jin radadinsa
Shuru ahmad yayi idonsa arufe yana tuna duk abunda AK kefada seyaga kamar lokacin abun ke faruwa baisan lokacinda hawaye suka fara zuba daga idonsa ba
Cikin rawar murya AK yace
Yanzu gani agabanka ba amtsayin AK hausawee ba
amatsayin supper hero dinka
shin zaka amince ka auri wacce nakeso takasance matarka ??
Rungumesa ahmad yayi yana fashewa da kuka yace na amince supper hero nayarda zan aureta ko yanzu kake so muje adauramana aure wallahi zan zauna da ita kuma zan kula da ita
Jan hannunsa AK yayi yana sharan kualla suka fita daga gidan
Kofar gidansu khadeeja driver yayi parking
da mamki ahmad yace amma wannan ai gidansu khadeeja ne nan nakawota jiya meyasa muka zonan
Murmushi AK yayi yace inaso mubasu hakuri ne kuma kuyi bankuana da khadeeja kagayamata ka amince da auren tunda itama haka takeso
Bude kofa ahmad yayi yafita baice komaiba
Murmushi AK yayi yafito suka shiga tare
tunda AK yafita sarah ke kuka tana ganin kiransa amma taki dauka aysha dake kusa da ita tace sarah AK yamiki 5missed call amma baki daga ba
Kauda kai sarah tayi tana sharan kwalla
Daukan wayan aysha tayi takira numban amma yabarta amota har takatse ba adaga ba
Zama tayi kusa da sarah tana fadin meyasa baki dauki kiransa ba kikasan kome zai gayamaki
Numban drivernsa takira bugu biyu yadaga yana gaidata
Bata ansa ba tace kuna tare da AK ne
"Eh munatare dashi amma yanzu sunshiga wani gida shida sir ahmad
" ahmad fa kace wane gida suka shiga kenan
"bansani madam amma naji suna zancan wai sir ahmad ya amince zai yi aure
wurgi tayi dawayan tana daka tsalle tace sarah barka natayaki murna ahmad ya amince zai aureki
Saurin tashi sarh tayi tana washe baki tace allah dagaske wa yagayamiki
Kama hannunta tayi tana jujjuyata tace yanzu driver yacemun AK natare da ahmad kuma ya amince zai aureki
tsalle sarah tayi tafada kan gado cike da farin ciki tana kankame pilo
zaune suke apalon inna sunyi jigum jigum suna jiran abunda AK zai fada
ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Umma yace
Umma kintabbata bakida matsala akan duk hukuncin da nayanke
Gyada tayi tace kwarai kwa abid nabaka dama kayanke musu duk hukuncin dayadace
Murmushi yayi yana kallon inna yace inna kefa
Tabe baki tayi tana juya furar dake hannunta tace yo ni meruwana dasu
Fa'iz dake kusa da ita se hadiyar yawu yake nabin furar dakallo
harara tabankamai yayi saurin kauda kai yana hade fuska
sunkuy da kai AK yayi yace
To ba wani Abu bane dama ahmad nazabama mata kuma ya amince da aurenta to shine nazo Baku hakuri akan abunda yafaru
Dagowa ahmad yayi yakalli khadeeja suka hada ido tayi saurin kauda kanta tana share hawaye
Murmushi AK yayi yana kallon ahmad yace
Friend zan baka auren kanwata kariketa amana da gaskiya ka kularmun da ita yanda yadace idan kacutar da ita to zan manta kai abokina ne nayima rashin mutunci
Shuru sukayi gaba daya ba Wanda yace wani Abu
Idon asma'u ne yakawo kwalla tana kallon kanwarta cike da tawsayi Umma ma haka kawai dai juriya take
Maida kallonsa yayi kan khadeeja yace
Deeja ga abokina nan nasan kina sonsa to kiyimai biyayya kuzauna lafiya banda rashin ji idan har kika muzguna masa to kema zanmanta cewa kanwata ce ke zan iskoki har gidanki nahukuntaki kinji ko?
Gaba daya suka dago suna kallonsa cike da mamaki
Murmushi yayi yace yakuke kallona ko baku gane menake nufi bane
cike da farin ciki ahmad yace friend kana nufin ka amince na auri khadeeja
Gyada kai yayi yace bama amincewa kadai ba nizan shirya komai kuma agidana za'ayi komai
Rungumesa yayi yana dariya mai sauti har yakasa magana
Cike dafarin ciki asma'u tadaka tsalle tafada kan khadeeja suka rungume juna suna murna
Ganin kowa ya rungume dan uwansa fa'iz yajuya yana washe baki garin rungume inna yabige furar dake hannunta tawatsamata afuska
Sadap sadap yatashi yabar wurin tun kafin tabude idonta
Sunjima ahaka kafin kowa ya natsu juyowan da AK zaiyi yaga fuskan inna sharkaf da fura har ba'aganin komai se idonta atsorace yamatsa gefe yana salati
Se alokacin kowa yalura gaba daya suka kwashe mata da dariya seda sukayi mai isarsu tana zaune tana binsu da ido
Daure fuska tayi tace kun gama ai kamar ta ce suci gaba suka kara sa wata dariyar
Tashi tayi tafita tana kwalama fa'iz kira
Umma tace amma abid idan akayi haka ba'ama sarah adalci ba
Murmushi yayi yace Umma nasan zataji wani iri amma kuma hakan shine yadace
Idan taga ahmad zai auri khadeeja dole tahakura dashi tunda tace batason kishiya
" to shikenan amma gaskiya ba agidanka za'ayiba abun seyamata yawa
Kusa da ita yazauna yana fadin ohhhh Umma kefa kikace duk hukuncin danayanke bakida matsala kuma tun ba'aje ko inaba kinfara complain
Murmushi Umma tayi batace komai ba tana gode allah dayabata suruki irin abid Wanda yadauketa tamkar uwa
Kallonsu Asma'u take da murmushi afuskanta tana jin wani yanayi datakasa fassara shi
Daki tawuce khadeeja nabinta
Abaya
Rungumota tayi tabaya tace ammah I am so happy gaskiya AK daban ne what a wonderful surprise !!!
Juyo daita asma'u tayi tana murmushi tace nima nayi farin ciki kanwata zata auri Wanda takeso
Murmushi khadeeja tayi cikin sigar tsokana tace
hmmmm kodai abunda kike ma farinciki daban ba ammah nahango wani Abu a kwayan idonki kamar kinfara son.....
Bata karasaba asma'u tayi saurin fadawa bayi hade da banko kofar da karfi kamar mai tsoron akamata
Dariya khadeeja tayi tafada kan gado tana ma allah godiya
Mutanan gidan kowa nazaune apalo sarah da aysha suka sauko cike dafarin ciki aysha tace kushirya fa zamu sha biki ahmad ya amince zai auri sarah
Carab grany ta amsa da fadin to in yakara guduwa fa
Dariya akasa gabadaya
Inna ameena tace nidai nashajin amarya tagudu ranan aure amma ango kam se akan sarah
Bashir yace gaskiya wannan karon inyagudu za'afara tsoron sarah
sadiya tace sedai muba dai cikin ma'aikatan mu
ahasale sarah ta dakatar dasu akan zata gayama AK inyadawo bashiri sukayi shiru
tashi AK yayi yama Umma sallama suka fita ita kuma tawuce daki kiran asma'u
Suna bakin mota ta iskosu
Bayn mota AK yashiga yana kallon ahmad yace muje ko??
dariya ahmad yayi yajuya yana fadin muje ina ??
Hahaha kuje dai ni sena gana da masoyiyata
Kofar asma'u takama zata shiga yarike yana fadin malama ina zaki shiga
Nan ...tafada tana nuna gefensa
Harara ya watsamata yana nuna mata daga gaba kusan driver yace ga wurinki can inzaki shiga inbakyaso kuma dama kinsaba da hawa mashin
Ganin ba alamun wasa afuskansa yasa tabude gidan gaba tashiga suka tafi
[19/07, 16:58] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣1⃣0⃣
suna isa sarah tazo dagudu tarungumeshi tana fadin Yaya u are the best thank you so much
Dagota yayi daga jikinsa yace banganeba why are u thanking me
menayi
karasowa wurinsu aysha tayi tana dariya tace hmmmm kana so kamana surprise ko to nariga nasani Ahmad zai auri sarah yanzuma daga wurinsa kake
Kusa da grany yaje yazauana yana fadin
Ahmad zaiyi aure amma khadeeja zai aura ba sarah ba kuma nariga nagama magana karnaji wani yace wani abu
Cak sarah tatsaya tana kallonsa da mamaki bakinta bude amma takasa magana
Juyawa tayi wurin asma'u dagudu tahadata da bango cikin gunjin kuka tana fadin wallahi basu isa ba sedai bayan ranta
Saurin tasowa yayi yabanbaro sarah daga jikinta yana fadin sarah wai meyake damunki ne wai yaushe kika zama so stubborn ne
Kwace hannunta tayi takara nufan asma'u tana surutai
Fizgan hannunta yayi yanufi sama da ita yana zuwa dakinta ya wurgata kan gado cikin kakkausar murya yace wallahi kika kara tabata se nasabamiki what is wrong with u
Da mamaki take kallonsa cikin rawar murya tace Yaya ...ni...akan waccan ..
Katseta yayi dafadin ba laifinta bane sarah tayi kokarin hadaki da ahmad amma hakan baiyuwu ba ni nashirya auren dakaina badan nakuntata miki ba sedan kihakura da ahmad kinema wani
Saurin dirowa tayi daga kan gadon tanufi hanyar fita tana fadin wallahi banyarda kai kayi hakan ba Yaya itace tashirya komai kuma wallahi bazan barta ba
Janyota yayi tana kokarin kwacewa baisan lokacinda yadauketa dawani gigitaccen mari ba jikake tasssss
Cak sukatsaya daga ita harshi kamar gumaka
jadabaya tafarayi tana jifansa dawani irin kallo mai cike da mamakin abunda ya aikata
Hannunsa yakalla sannan yakalleta yana matsawa kusa da ita cikin rawar murya yace sarah I am sorry bansan...
Katseshi tayi dafadin karkatabani katafi kabani waje kai ba Yayana bane Yayana bai taba kai hannunsa ajikina danufin dukana ba
Tabata yaje yi tayi saurin shigewa bayi hade da banko kofar da karfi tana kara fashewa da kuka
Fita yayi daga dakin yanufi bangarensa
Dakarfi yatura kofar yashiga hade dazama kan kujera yana dafe kai
Kusa dashi asma'u tamatso adan tsorace tace
Ya....sarah...take...
is she ok...
Girgiza kai yayi yace she is not amma komai zaiwuce dama nasan sarah zatayi abunda yafi haka idan tarasa ahmad
Ruwa tazubomai mai anyi akopi tamikamai
ahankali yakai hannu yakarba yasha sannan yamika mata sauran
Zama tayi kusa dashi cikin siriruwar murya tace karka damu nasan tayi fushi yanzu amma zata sauko daga baya
abunda zakayi shine kasamu wani Wanda kayarda dashi kasan zai iya jure wulakanci daga gareta kuma kasan yana sonta seka....
Katseta yayi da fadin se inyi me wai inhadasu aure ? nifa natsani hade haden nan..
Dawawa tayi gabanshi tazauna daga kasa tana fadin ha'an to kabari kaji mezan ce mana ai bangama ba
Kauda kai yayi yace to inajinki
Murmushi tayi tace yawwa idan kasamu sawrayin sekasan yanda zakayi kahadashi da sarah batare da saninta ba shi kuma kagayamasa idan har yana son kabasa auren kanwarka to seyanemi soyayyarta kafin nan
Juyowa yayi yana kallonta yace to amma miye hikimar yin hakan
Gyara zama tayi tana murmushi tace uhmmm kaga yanzu matukar sarah tana ganin ahmad kawai amatsayin saurayinta to bazata taba hakura dashiba amma idan taga Wanda yake haukan sonta tun tana wulakantashi tana koransa har tafara sawraronsa daga nan kuma bazama tasan lokacinda ahmad zai fita aranta ba
Murmushi yayi yace wow!!! what a brilliant idea chitti
dan kwalinta ta turo gaban goshi tana kauda kai tace ahh dabakaki saurarena ba
Murmushi yayi yace hmmm I am really impressed amma kintaba soyayya ne
Saurin joyowa tayi tana kallonsa tace no bantaba yiba banmasan ya akeyiba
dariya yayi yace shiyasa naganki gaki ga kamarki amma wannan Ali din nagidanku ai nadauka saurayinki ne
" ina ba saurayi na bane cousin dina ne da dai yaso ya aureni iyayenshi suka hanashi
dariya yayi yace kice kema kintaba kwantai shiyasa kika samu experience akan rasa masoyi
Hade fuska tayi tace allah ba kuantai nayiba kawaidai wai suna so ya auri wata yarinyane babanta yanada kudi to daga baya kuma yarinyar tafasa auren
zaiyi magana kenan sukaji anturo kofa
Aysha ce tashigo taci kwalliya tana taunan cingam
Juyowa AK yayi yana kallonta yace ohhh hello babyyyyy!!
Karasowa tayi cikin yanga tazauna kusa dashi tana hura hanci
Kallonta asma'u tayi takwashe da dariya
atare suka kalleta aysha na hade fuska
Daure fuska AK yayi yace ke kinada hankali kuwa me akayi nadariya
tashi tayi tawuce daki tana dariya
hade fuska aysha tayi tace wallahi AK kasakema yarinyar nan dayawa tagama raina mutane
Shiru yayi baice komai ba yana kallonta
Da daddare AK na zaune bakin gado yana danna laptop ga Earp akunnensa yana jin waka se gyada kai yake yana bin wakar
asma'u tashigo rike da coffee dinsa kan bedside drowa tadorashi tana fadin ga coffee dinka nan
Baimasan tanayiba yamika hannu zai dauki wani Abu kawai yajishi cikin zazzafan coffee
Yar kara yasaki yana yarfa hannun cike damasifa yace wayace ki ijiye anan baki gayamun ba
Karasowa tayi tana duba yatsunshi tace bakajiba nace ga coffee dinka anan
Kallon bakinta kawai yake yana motsi amma baijin metake fada
Kuace hannunsa yayi yace dubawan me zakiyi bayan dagangan kikayi dakika kawo ai sekibani ko kigayamun
"Wai bakaji menace bane
"Jiki kawai bawani hakurin dazaki bani
damamaki take kallonsa secan tahangi Earp akunnensa hannu takai tacire Earp din tawuce dressing mirror tana maimaita mishi abunda tafada dazu
Painkiller tadauko takama hannunsa zata shafamai ya kwace yafara shafa ma kansa
bathroom tawuce tayi shirin kwanciya cikin kayan baccinta wando da riga mai dogon hannu
Bayan tagama tafito yana kuance kan gado yarufa da bargo
Tsaye tayi daga gefe tana kallonsa idonsa arufe amma da alamun damuwa afuskansa kamar daga sama taji yace
Malama idan abun kallo kike nema ga TV can ki kunna stop staring at me
Saurin barin wurin tayi tanufi bookshelf( drowan litattafai) din dake jikin bangon dakin daga gefe tana fadin
ina ai ni bana kallo da daddare sedai nayi karatu
Wani storybook tadauko tadawo kan stool tazauna tafara karantawa afili sedaga baya tagane tatsuniyoyin naban tsoro ne
Shiru AK yayi yana kara cusa kansa cikin bargo
Kallonsa take tana kunshe dariyarta tacigaba da karantawa cikin muryan ban tsoro tace
Dazaran yamma tayi se kowa ya kulle kofarsa saboda wannan aljanan tana yawo cikin dare duk Wanda tahadu dashi to yagama yawo
Wannan tsohon yana kuance cikin dakinsa yalulluba dabargo yana karkarwa gashi garin ana wata irin iska mai karfi kamar daga sama yaji ana bugamasa kofa dakarfi .....
Daidai nan grany ta aiko Rebeka da wayan asma'u takamata kawai sukaji bugun kofa
atsorace AK yafito dakansa daga cikin bargo yana kallon asma'u itama adan tsoracen take kallonsa
atare suka juya suna kallon kofa
Dariya asma'u tayi tana kallon AK tace wai yanaga kamar katsorata ne to bari na aje
Daure fuska yayi yana gyara kuanciyarsa yace tsoron me zanji awannen shirmen
cigaba tayi dakarantawa ...
atsorace tsohon nan yatashi zaune jikinshi narawa jin ba akara buga kofan ba yasa yakoma yakuanta can anjima yakara jin anbuga kofar dakarfi ....
daidai nan Rebeka takara kuankuasa kofar
Wannan karon gaba dayan su sunkasa boye tsoronsu
kallon AK tayi tana hadiye yawu tace ABI kaima kaji buga kofar koni kadai keji
tashi zaune yayi yana fadin naji mana to amma waye zaizo awannan Daren
Jin shiru ba abude ba yasa rabeka tatura kofar ahankali ta ijiye wayar kusan TV tafita
ai sunaji anbude kofa asma'u tadaka tsalle tafada kan AK atsorace yaja bargon yarufesu tana kankame dashi har suna musayar nunfashi
cikin rada yace inajin motsi anan dakin
Itama cikin rada tace banan dakin bane Palo ne kuma kamar anfita muje muduba
Ahankali yafito dakansa daga cikin bargon yana bin dakin dakallo ganin bakowa yasa ya sauko ahankali daga kan gadon
Itama tasauko suka nufi kofa
turata yayi gaba yakoma baya yana fadin lady first
Saurin dawowa baya tayi tana fadin to ai kai namiji ne kamata yayi ma kace inzauna kaje kaduba
Wata wahalalliyar dariya yana kara turata gaba yace
to ai saboda naga yawanci nabaya akafi fara cabkewa shiyasa nasaki gaba
wata zungureriyar kwalba tadauka tarike ahannunta dayan kuma tana bude kofar dashi
seda suka dudduba ko ina bakowa sannan taga wayarta akan table
Ijiye kwalban tayi tadauki wayarta tana kallon AK tace kamar wayata aka kawofa
Murmushin yake yayi yana waskewa yace dama ai nasan ba komai kawai ina gwadaki ne naga ko kinada tsoro ashe ke matsoraciya ce
kallon ka rainamun hankali take mai seda yagama sannan tasaki yar kara atsorace tana nuna bayansa
Haba lokaci guda yadaka tsalle se gashi agabanta
Dariya tafara mishi harda rike ciki tawuce daki
Binbayanta yayi yana murmushi
Suna shiga daki yadauke blanket dinta daga kasa yadora kan gado
daukan blanket din tayi tana fadin miye haka malan
kwace blanket din yayi yadora kan gado yace nan zaki kuana yau kina tare mun hanya idan natashi dasafe
buga kafa tafarayi dakasa tana fadin ni gaskiya ban yardaba daacan bakace haka ba seyau dakake jin tsoro
pilulluka yajera atsakiyar gadon ya kuanta yana fadin ga wurinkinan ki kuanta idan ma kina tunanin wuri daya nakeso mukuana
Kuma kika ki allah gobe zan gayama grany gaskiya akan aurenmu
zagayawa tayi takuanta tana zunbura baki
Murmushi yayi yana Jan bargo yajiyo yana kallonta yace chitti
Kyaleni.....
Tafada tana juya baya
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣1⃣5⃣
Gyara zamansa yayi yana kallonta dakyew yace aysha ni nakasa gane wannan lamari abun yadaina bani mamaki yafara bani tsoro tunda naga AK ya yima sarah haka akan yarinyarnan to tabbas akwai wani Abu atsakaninsu
sadiya tace nima dai haka nagani Abba aysha halin da namiji ne bakisani ba yarinya kar azo garin kallon ruwa kwado yamana kafa tanadin da mukayi shekara da shekaru yazo yaruguje mana muzama yan kallo
Dariya aysha tayi tana tafa hannu tace kai wallahi kun ban dariya ai wallahi ba Wanda zaishiga tsakanina da AK koda kuwa grany ce dakanta bare wata banza wai asma'u
Ku kwantar da hankalinku dady insha allahu wannan dukiyar tamuce mu kadai bawanda zaicita se mu
dariya jamilu yayi harda kyajyatawa yace ai nasanki ya'ta bakya wasa kunsan me duk lokacinda narufe idona kawai jina nake natashi daga jamilu nadawo jamil hausawee
Dariya sadiya tayi tace ni kuma Mr's jamil hausawee
Mikewa aysha tayi tafita tana fadin ni kuma Mr's AK hausawee
ladidi da bashir ne zaune adaki suna fira
ladidi tace wai kai bashir har yanzu ba'abaka albashinka bane
Murmushin gefe yayi yace to in anbani meza'ayi dashi badai inbaki ba
Daure fuska tayi tace kai kar kamun rashin kunya kaji ko wai kai kodan ciwa ciwa da babakere dinnan ma duk baka iya ba company nan fa nakune kabude aljihunka kadiba kudi amma katsaya wasa
Girgiza kai yayi yace a'a mama nifa ba abunda yakaini wurin ba kenan nayarad idan ina son kudi intambayi AK yabani amma bawai insata ba
" yo wayace kayi sata kai kowafa daka gani agidannan tasa ce takawosa kowa soyake yakwasa na kwasa kafin ayi waje dashi
saboda haka kaima kasan nayi gaka jamilu da wannan kinibabbar matar tasa allah kadai yasan abunda aysha ke kwaso masu a aljihun AK
amma kai katsaya wasa to tsaya kaji dazaran AK ya auri aysha to tamu takare agidannan dan wallahi gaba daya kawye zasu maidamu daga ita se iyayanta ne zasu muri wannan dukiyar
yashi yayi yana fadin insha allahu ma bazai aureta ba dan da ace matar nan tasa ta kile irin yan duniyan nan ne to wallahi ko kallon aysha bazai yi ba
tsaki tayi tana binsa da kallo har yafita sannan tace aikin banza ana ga maciji kana ga tsutsa dadin ya'mace kenan wallahi da ameena na nan dayanzu ta taimaka mun ga salma tayi Karama bata San komai ba ...
sarah na kuance kan gado da photon ahmad ahannunta tana kallo idonta sunyi ja sun kunbura tun hawaye nazuba har sun kafe
Tunowa tayi da AK kefadin wai tahakura da ahmad tunda khadeeja zai aura
Wurgi tayi da photon tafara wawwatsa kayan dakin tana fadin ina bazai yuwu ba sedai idan bana raye bawacce ta isa ta auri ahmad seni
Kwalba tadauka tarusa madubin dressing mirror tasulale akasa cikin dasashshiyar muryanta tana fadin
nawa ne nikadai ....ni kadai nake sonshi...kuma ni zan aureshi...inba haka ba zan mutu
Wayarta ta dauka takira numban khadeeja
bugu biyu tadaga tare da sallama
Shiru tayi nadan lokaci sannan cikin dasashshiyar murya tace
sarah ce nakira namiki barka ina tayaki murnan samun ahmad amatsayin mijinki amma ni kuma zanbaku wedding gift din sekun mutu baku manta dani ba kigayama ahmad idan har bashi arayuwata to batada wani anfani
tana kainan takatse kiran
mamaki ne Yakama khadeeja tana maimaita wedding gift
saurin kiran asma'u tayi tana dauka tagayamata yanda sukayi da sarah
atsorace asma'u tamike tana fadin me sarah zata aikata
ohh my god ....tafada tana fitowa dagudu daga dakin
aguje tanufi dakin sarah tana bugamata kofa amma shiru
aysha ce yazo wucewa tadawo tana fadin malama lafiya what is ur problem
Banza tayi da ita takwala ma nura kira yazo suka fara balla kofar
aguje tafada dakin sedai cak tatsaya tana kallon sarah dake kuance ga hannunta duk jni alamun yanka awurin
Durkushewa tayi akusa da ita tana kuka aysha ma hannu tadora akai tafashe da kuka
ganin jinin baitsayaba yasa asma'u tayi saurin yaga gualenta tadaure wurin sannan aysha ta taimaka mata suka kaita mota se asibiti
Suna zuwa aysha takira AK awaya seda takusa katsewa yadaga yana fadin baby I am busy zan kiraki anjima
Cikin rawar murya tace AK sarah ta kashe kanta kayi sawri kazo asibiti
Dariya yayi yakatse kiran yana kallon ahmad dake kusa dashi yace kaji wani shirme wai sarah takashe kanta
azabure ahmad yamike yana salati yace AK yana yiwa dagaske ne kasan sarah fa bata iya shiga damuwa ba
"No wasa ne nasan aysha tana mun irin wannan wasan in tanason ganina
Girgiza kai ahmad yayi yace a'a AK nifa tsoro nakeji kar azo dagaskene kakira grany ko asma'u mana
Wayansa yadauka ya lalubo numban asma'u dayayi saving da chitti yakira
yana fara ringing tadaga tana fadin ABI ina kashiga ina kiranka bana samu
kazo asibiti sarah bata jin dadi
Azabure yamike yana fadin meyasami sarah kina nufin dagaske tamutu
cikin rawar murya tace a'a bata mutu ba ABI kaidai kawai kazo
aguje yafita daga office ahmad nabinsa abaya
Cikin minti 30 suka iso asibiti yana isa doctor nafitowa wurinsa suka nufa atare suna tambayar ya jikinta
Kallonsu yayi daya bayan daya sannan yace dafari dai inaso insan wa yadaure mata hannu da kyalle
baigama rufe baki ba aysha tayi saurin nuna asma'u dayatsa tana fadin wannan ce
juyawa sukayi atare suna kallonta sanan suka maida kallonsu kan doctor
itama asma'u kallonsa take dafargaban abunda zaifada
Murmushi yayi yana kallonta yace gaskiya kinyi dubara mai kyew saboda badan kinyi hakan ba da kafin kuzonan tarasa jni mai yawa kuma jijiyarta zata ita bushewa ko iska yakai ga zuciyarta hakan kuma shi zaisa tarasa ranta amma yanzu alhamdulillah taji sauki zaku iya shiga kuganta sedai akula irin haka kar takara faruwa
Sannan yakalli AK yace muje office ina son ganinka
gaba yayi AK da ahmad suka bisa abaya aysha kuma tashiga dakin da sarah take
Nuance take tana kallon sama hawaye nazuba a idonta ga igiyar Karin jini ana mata
se hannunta da aka ma bandage
Kusa da ita aysha tazauna tana fadin sannu sarah gaskiya AK bai kyewta miki ba koda yake ba laifinsa bane wannan munafukar yarinyar ce tasashi wayasan metagayamasa ...
Muryan asma'u tajiyo tana fadin tashi kifita
Juyowa tayi tana hararenta tace dawa kike kehar kin isa kice nafita
dan karamin table din da ake dora magunguna ta rarumo tanufota dashi bashiri tayi waje aguje har tana bigewa da kofa
ijiye table din asma'u tayi takarasa kusan gadon tana duba hannun sarah
Kwace hannunta tayi tana fadin wayace ki kawoni asibiti meyasa baki bari namutu ba tunda natabbata abunda kike so kenan
Kusa da ita asma'u tazauna tana fadin sarah kina bani mamaki idan kikayi wani abun kamar wacce batayi karatu ba yanzu idan kika kashe kanki riban me zakici Wanda kikayi danshi zai danyi jimamin lokaci kadan daga baya kuma yamanta yayi aurensa yacigaba da rayuwar farinciki
Yanzu dazan tambayeki da allah da ahmad wakika fiso zakice allah amma kuma kinyi kokarin aikata laifin da allah bazai yafemaki ba saboda ahmad
Akan rayuwar duniya kikayi kokarin ruguza ta lahirarki
Miye laifin AK dazaki daga mai hankali yana matukar kokari wurin faranta miki amma ke kanki kawai kika sani bakya tunanin halin dazai shiga idan kika aikata wannan kazamin aiki
Sarah kefa macece mata ansansu da juriya da danne soyayya aransu saboda gudun wulakanci amma ke kinkasa yin hakan shiyasa kike wahala
Ki godewa allah dayabarki da ranki yana sonki shiyasa baidauki rankiba yabaki dama akaro nabiyu dan kyallen danasa maki bashi yahanaki mutuwa ba lokacinkine baiyiba
Bakowa yakesamun irin damar dakika samu ba yau da kin mutu da zaki dawwama kina nadama har abada
ina gayamiki hakane ba amatsayin asma'un dakika tsana ba
Ina gayamikine amatsayin musulma kuma mace yar uwarki
Ga glass nan da wukake kina iya dauka kikara yanka hannunki ko wuyanki amma kisani ba kyada hujjar dazata hana allah yakonaki
tana kainan ta tashi ta fita daga dakin
Tana fita AK da ahmad nashigowa aguje AK yakarasa bakin gadon yana kallonta cikin rawar murya yake fadin
sarah why!! Why sarh!! Why!!
yakasa cigaba da maganarsa se hawaye dake zuba daga idonsa
Itama kukan take tana fadin yaya i am sorry
dafasa ahmad yayi yace friend kaje waje zanyi magana da ita
fita AK yayi yana sharan kwalla gefe guda yaje yazauna hade da dafe kai
AK nafita ahmad yadawo kusan sarah yazauna cikin sassanyar murya yace
Sarah base kinfadamun dalilin dayasa kika aikata hakan ba nasan saboda kinji zanyi aure shiyasa
Na fahimci halin da kike ciki saboda nima nashiga wannan yanayin abaya
sarah nasan kina sona kuma nagode da kaunarki agareni amma bayanda na iya sarah
Ina miki kallon kanwata ne kuma kawata idan kika hakura kika manta dakomai zanci gaba da kallonki ahakan amma idan kika kara aikata wani abun to zaki rasa wannan matsayin awurina
Shiru tayi tana kallonsa takasa cewa komai
tashi asma'u tayi tanufi inda AK kezaune tazauan kusa dashi
Dagowa yayi yakalleta yakara maida kansa kasa
ahankali takai hannunta tadafa kafadansa cikin sigar lallashi tace
kar kadamu kaji she will be fine
dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanuwasa cikin rawar murya yace chitti meyasa sarah zatayi abunda ko jahili bazai yiba meyasa zata zabi tarabu dakowa nata tahadu da fushin ubangiji akan tarasa ahmad
bazatayi tunanin halin da zan shiga ba bana kewar iyayenmu saboda ita da grany aduk lokacinda nakalleta fuskan ummarmu nake gani atata
hawayene suka zubo daga idanuwansa yacigaba dafadin
Chitti nasan zakiyi tunanin nabata sarah dayawa ko duk abunda takeso ina mata kinsan dalili ?
Girgiza kai tayi hawayen datake makalewa suka zubo
cije lebensa nakasa yayi yana saita muryansa yace
Tun ina karami nataso ina son yima iyayena hidima inaso naga sunkawo bukatrsu namusu kodan naga murmushi afuskansu ta dalilina
Naci burin yi musu hidima na kyewtata musu in sungirma amma allah bai kaddara ba
Kinga sarah to yadda take haka ummana take ita kuma grany sak yanda take haka abbana yake
daga ranar da suka rasu daga ranar duk wani son danake masu da burin kyewtata masun danake yakoma kan sarah da grany haka nataso har kawo wannan lokacin banason ganin abunda yabata musu rai ko sun nemi Abu sun rasa amma gashi yau nakasa wurin farantama kanwata ...muryanshi ne yakarye yakasa cigaba damagana
Hannu takai tana share mai hawaye cikin muryan kuka tace
ABI kai ba allah bane mutum ne duk yanda kaso ka kyewtata musu dole wata rana sunemi wani abunda su rasa kuma dama haka rayuwa take kowa kaduba akwai abunda yakeso yakasa samu
ABI u are not just a brother but u are a real hero
kayi ita kokarinka sauran kuma sekabarma allah amma please stop blaming ur self
Gyara zamanta tayi tana kallonsa cikin sigar tsokana tace
Yanaga kayi saurin karayane ko kamanta maganr damukayi jiya idan bazaka iya samomata ba ni kabani dama nasamo mata handsome guy
Murmushi yayi yace a'a nizan zaba dakaina ke kinsan handsome ne
haka kawai kije kidaukomata dan jagaliya murasa yazamuyi dashi
Kwaikwayon yadda aysha tashigo jiya tayi tana fadin
wai me kadaukeni ne naga fa kana nema karaina mun class dina
Dariya yayi yace to ya isa masoyiyar tawa kike kwaikwayo komai abunki dai bazaki kaita haduwa ba
"Allah sedai in banyi niyya ba abun ai ba wuya ne dashiba nidai kawai banda lokacinsa ne
tashi yayi suka nufi dakin sarah
Rungumeshi tayi tana kuka tace
Yaya na amince nahakura ahmad ya auri khadeeja
Dagota yayi da mamki yace dagaske kin amince amma abunda da mamaki da zaki kashe kanki yanzu kuma kin amince kodai kin hango malakal mauti ne
kara rungumesa tayi tana murmushi tace Yaya kabari banaso
dariya sukasa gaba dayansu banda aysha dake jifan sarah da kallon tuhuma
Dagowa tayi tana kallon asma'u tace sister nagode dakika ganar dani abunda nakasa ganewa tun tuni
Gaskiya ke tadabance thank u once again
Juyowa AK yayi yana kallon asma'u da murmushi afuskansa
Sunkuy dakanta tayi itama tana murmushin
Da yamma aka sallemesu suka dawo gida dakin sarah suka fara zuwa seda ta kwanta sannan suka fita akabari daga ita se aysha
Bayan kowa yafita aysha tazo tarufe kofar da key takoma kusan sarah da mamaki tace sarah what is ur plan?
kauda kai sarah tayi tace kamar ya ?
"Hahaha sarah kar kirainamun hankali nafasanki kamar yunwar cikina u won't give up easily
Ya akayi haka
Share hawayenta tayi tace to aysha yazanyi ahmad yariga yazama na khadeeja Dana tsaya inaba kaina wahala ba gara nafita hanyarsu ba nima nayi addu'ar allah yabani mijinagari
Hanyar fita aysha tanufa tana fadin kin bani mamaki sarah Ashe bama son Ahmad kike ba kawai cika baki ne
Dakallo sarah tabita har tafita sannan tarufe idonta ahankali hawaye nagangarowa gefen fuskarta
Aysha nafita wurin AK tanufa yana zaune apalo ta iskosa kusa dashi tazauan tana shagwabe fuska tace darling wai mekake jira da yarinyar nan ne naga bakada niyyar korarta daga gidannan
Gefen fuskanta yashafo yana murmushi yace aysha kifahimci halin da grany take ciki kinsan tana son asma'u dayawa to kafin in rabu da ita ina bukatar hujja ko dalilin dazan kare kaina dashi awurin grany idan bahaka ba gaskiya bazan iya sakinta haka kawai ba
to mezan gayama iyayenta idan ita tasan dalilin dayasa na aureta su basu saniba
Murmushi tayi tace OK I understand amma dan allah kadaina shishshige mata dazu fa ina ganin lokacinda kuke dariya a asibiti
Nidai gaskiya kadaina sake mata fuska kaga tafara raina mutane tun ba'aje ko inaba
kauda kai yayi yana fadin nasan menakeyi base kin gayamun yadda zan zauna da ita ba
Yana kainan yamike yanufi masallaci
Dakallo tabisa har yafita sannan ta tashi ahasale tawuce dakinta
dakarfi ta tura kofar dakin tashiga tana fadin ina bazai yuwu ba wallahi wannan ai shirmene
dolema nasan abinyi ina ganin abun kamar wasa gashi yafara zama babbar barazana wa farin cikina """"
0 comments:
Post a Comment